SIRADIN RAYUWA CHAPTER 9
BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
Tun daga ranar da abun yafaru tasake zama so silent,takoma dabi’arta tada koma fiye da da,yawan shuru shuru,zaman kadaici dakuma tunane tunane,ta sanyawa daren suna da baqin dare a wajenta,duk da cewa mama sodangi na iyakar qoqarinta na ganin ta daidaita lamuranta,abinda bilkisu ta lura dashi shine,maman tasanya wani distance na daban tsakaninta da rukiya,bata fiya barinsu xama tare ba,hakanan rakiyan ta sauya mu’amalarta da ita,wani girma take bata kamar yadda suke a baya,kwatankwacin kuyanga da uwar gijiyarta.
Sai yanzu take ganin wautar data tafka da har tasaki jiki,ta manta silar zuwanta mexico,ta manta abinda ya kawota,takuma manta wacece ita,sa’an nan ta manta dukkan qalubalen da takan iya fuskanta har sai daya zo ya cimmata.
Duk yadda mama sodangi taso.dai daita komai abun yaci tura,abun yana damunta yana kuma taba ranta sosai,bata gane ba qaramin sabo sukayi da bilkisun ba har sai data maida kanta wannan yanayin nata na baya sa’an nan tagane sun shaqu da juna,ganin tana neman illata kanta yasanya tazauna da ita,maganganun da tayiwa bikisun suka sauketa daga matakin da take kai daga kaso cikin kaso dari zuwa suka kwashe kaso saba’in suka barta da talatin,sannu a hankali lokaci dakuma juyawar zamani tsawaitarsa da abubuwan da yakanzo dasu ya sanya ta kuma saki kamar baya,saidai duk da haka bata bar ɗari ɗari tsoro dakuma fargaba ba,duk da cewa daga baya itama ta ragu,saboda rashin jin duriya motsi ko sautin muryarshi tun daga ranar da abun yafaru.
*_BAYAN WANI LOKACI_*
Nannauyar ajiyar zuciya yasaki bayan shigowarsa dakin nasa wanda a baya yake zaune a ciki kafin ammin tasa tayi masa sauyin gida tare dasu mama sodangi,tafin hannunshi ya sanya yana murza fuskarshi gamida fuskar da iska daga bakinsa,tsabar gajiya ce ta taru tayi masa yawa,uwa uba kuma da yanayin da yake ciki wanda yana tsammanin wanzuwar al’amarin zai kawo qarshen duk wani abu dake damunsa,saidai ga mamakinsa ko sau daya lamarin yaqi barin kwanyarsa ta huta,tamkar wani famine yayiwa ciwonsa,kullum kwanan duniya rana bata taba fitowa ta fadi na tare daya tuna da daren ba,daren dako yaqi ko yaso dole ya sanyashi cikin jerin dararen da zai dinga tunawa tsahon rayuwarsa,saidai baisan a wnne bigire zai saka shi ba?,na farinciki ko na baqinciki ne?,har yanzu ya kasa tantancewa.
Abinda kawai zai iya tunawa shine,zuciyarsa ta kasu gida biyu,yana da tabbacin cewa a ranar yasamu sauqi daga nauyin zuciya,yasamu wani irin inner peace da baisan akwaishi ba a duniya,yaji kansa tamkar jaririn da aka.haifa yau,yayin da wani sashen na zuciyarsa yake iya tuna mishi sautin kukanta,muruyart da taketa magana wdda bai fuskantar me take cewa,amma yana da tabbacin bazai wuce roqo na,zuciyarsa na yawan tambayarsa kayi dai dai?,yakan amsawa kanshi da eh duk da bada wani cikakken qwarin gwiwa ba,amma.yana da hujjar cewa matarshi ce.
Bai fiya son abinda zai dameshi ba,don haka tun daga ranar yayiwa gidan qaura,yakan iya kwana daya zuwa biyu a wannan gidan nasu kafin yaje wancan gidan,wanda yawanci idan yaje din kwana daya biyune shima yabarshi yasauya muhalli.
Kamar yau din dai a gidan nasu ya kwana,wanda wani lokaci hirarrkin su mustapha suna debe masa kewa,koda bazai tofa komai ba,amma.yakan zauna cikinsu yana sabgar gabanshi yana kuma jinsu.
Wani dogon tsaki yaja kana ya miqe,ya rasa tunanin me yake daya sanyashi ya zauna har haka,baisan mene yake dagula lissafinsa ba,karatunsa ne daya dauki zafi saboda watanni qalilan da suka rage masa ya kammala ko kuwa a’ah,iya saninsa ba kasafai karatu ke damunshi ba,saboda baiwar qwaqwalwa da fikirar da Allah ya bashi,bai sani ba wannan karon….kodon hausawa sunce idan aski yazo gaban goshi yafi zafi?…..
Wanka yayi yashirya cikin wasu qananun kaya da suka fidda sigar kyan da Allah yayi masa,mai cakude da kwarjini izza da jinin sarauta,yadauki maqullin motarshi bayan ya gama feshe jikinsa da turaruka kana yayo hanyar waje yana qoqarin kunna wayarshi dake kashe tun dazun,saboda baison yawan kira hakanan yakeji.
Kusan dukansu yanzu suna falon,sabanin daxu da mustapha ne kawai a zaune,yanzun kamal da jabir hadi da wani abokinsu mudassir dukka suna zaune,jabir dai kallo yake na wani wasan qwallon raga da ake haskawa live,kamal da mudassir hirarsu data shafesu suke,yayin da mustapha yamaida hankalinsa kacokam kan allon computer din dake saman cinyarsa,da alama karatu yake dubawa.
Fitowarsa tadan ja hankalinsu gaba daya,idanuwan kamal dake cike da hassada dukka suna kan azeez,yana jin inama yana da iko da a daren yau saiya qwace dukkan abinda azeez din yake taqama ya mallakeshi,saiya qwace duk wani abu da xai dinga nuna fifiko da daukakarshi a cikinsu,ciki kuwa harda kyau da kwarjininsa.
Mustapha ne ya daga kai ya dubeshi
“Zaka dawo ne koka tafi kenan?” Agogon hannunshi ya duba kana ya amsa mishi
“No,zan danyi wani uzuri ne nadawo” kamal daketa kallonshi wanda duk bibiyarsa ya gaxa cimma gacin inda azeez yake zuwa ko kuma yakoma,ya kasa haqurin yin shuru
“Wai yarima ya kake mana asha ruwan tsuntsaye ne kwana biyu?ina kakeyin layar zana?” Wani kallo ya jefawa kamal din wanda ya sanyashi shan jinin jikinsa,saiya janye idanunsa daga cikin na azeez din
“Ka sani shima ko yabi sahun ‘yan morewa quruciya da rayuwarsu” jabir ya fada cikin tsokana yana qyalqyala dariyarshi harda buga qofa,don ya fadine shi har zuciyarshi ba tare da yasan meye a zuciyar kamal ba,harara zeez ya jefawa jabir din kana yasoma yin gaba zai fice ba tare daya amsawa kowa cikinsu ba
“Abinci fa?” Mustapha yadan daga murya yana fada
“Saina dawo” ya bashi amsa a taqaice yana qarasa ficewa daga falon.
Sannu a hankalin yake tuqinsa a nutse,harya shiga cikin unguwar,idan bai manta ba yau kwana biyu ko uku kenan rabonshi da ita,da wannan tunanin ya faka motar a qofar gidan yakasheta yafito,kana ya sanya muqullinsa ya bude gidan,ya tura falon yashiga.
Shuru yake babu kowa ciki,dama ya tsammaci hakan,don lokacin kwanciya barci ne ga duk mutumin da bashi da wani aikin da zaiyi,saboda dare daya soma yi,karaf idanunshi suka fada sashen da dakinta yake,saiya lumshe idanu yana dauke kanshi,kana ya durfafi samansa.
Dakin fes yake,kamar yadda ya zame masa dabi’a,baya barin dauda ko qura a duk muhallin da yasan zai zauna,ya buda duk inda yake da buqata yadauki abinda yake buqata din sannan yakuma rufe dakin ba tare daya zauna ba yafice a dakin.
Karo na biyu idanunshi suka sake sauka a qofar dakin sanda yake saukowa daga saman,tamkar wanda magnet yaja ganin nashi haka yaci gaba da kallon dakin,har ya gama saukowar,saiya durfafi qofar fita da sauri yanason daqile duk wani abu dakeson masa tasiri cikin ranshi.
Murus jikinsa ya mutu lokacin daya shigar motar da niyyar tada ta,saiya kasa tabuka komai,kasala da mutuwar jiki na baibayeshi,wani irin shauqi yana mamaye gabbansa,ya tabbatar da cewa bazai iya maida kanshi gida ba a yanayin da yake ciki ba,don haka saiya kashe motar yafito yakoma cikin gidan.
Tamkar wanda ake sauyawa direction,kamar wanda wani abu mai qarfi yake janshi saiya samu kansa da sauya akalarshi zuwa dakin nata.
A hankali ya tura qofar,duhune yasoma yi masa sallama bisa dukkan alamu tayi bacci,a nutse yanufi inda yasan zai samu haske bedlamp,ya sanya hannunshi ya kunna,qaramin haske mai duhu ya bayyana.
Tarwai fuskarta ta fito dab da fitilar,kamar wadda tasan da faruwar hakan,saitin fuskartata wayarta ce a yashe,da alama tana tsaka da dannata bacci yayi awon gaba da ita,saiya samu kanshi da xubawa fuskar tata idanu,karon farko daya fara aikata hakan tunda yasoma saninta,kamar ba bacci take ba,kamar idanunta biyu,idanunsa yakai kan qaramin bakinta dake dauke da pink lips,wani shock yaji wanda ya sanyashi yasoma tafiya da baya da baya,har sai daya dangana da muhallin daya soma tsaiwa farkon shigowarsa dakin yana ci gaba da kallon baby face dinta.
Cikin baccinta tasoma jin wani irin yanayi,yanayin da yayi mata kama da wani yanayi wanda ta taba shiga watanni biyu baya da suka shude,a firgice tabude idanunta sannan ta waresu gaba daya,duk da babu abinda take iya hange sai qaramin hasken da fitilar gefan gadon take iya bayarwa,wanda bai isa yasa taga komai ba,tattausan qamshinsa da hancinta ya sheqo ya aikawa qwaqwalwarta shi ya bata amsar tambayar dake zura gudu cikin kwanyarta,lokaci guda tayi wani mugun laushi,tashin hankali ya sauko mata wanda hakan ya sanya zuciyarta ta qara gudu kan gudunta na qa’ida,bata da sauran wani abunyi illa zubawa sarautar Allah idanu,tanajin lokacin bautarta ne yayi kamar yadda sauran bayi suke,abu na qarshe daya faru shine saukar zafafan hawaye daga kuncinta.
Ta cikin qaramin hasken take iya hango inuwar takunsa zuwa qofar dakin da niyyar ficewa bayan shudewar wasu mintuna,saita lumshe idanunsa sauran hawayen da suka cika mata idanu suka sake kwaranyowa karo na barkatai,wani irin tsanarsa taji tana ratsata karo na farko,ta wani gefe na zuciyarta taji xallar laifi mai girma akan mahaifinta,shi dinma karon farko a rayuwarta,taji zuciyarta tana jefa mishi tuhuma da zargi mai girma,abinda bata taba jin zuciyarta tayi masa ba duk da girman laifin daya ringa musu tun daga quruciya har girma sai a wannan karon.
Wannan karon da kanta ta tashi ta gyara kanta,ko mama sodangin bata bari ta sameta a wani hali ba,saidai wanda ya rigaka kwana dole saiya rigaka tashi,yanayin qunci da rashin walwalar data ga bilkisun a ciki ya fayyace mata komai,sannan ganin yariman a gidan ya qara mata haske,wanda kwana yayi a gidan kana ya qare wuninsa gaba daya a samanshi,bai bar gidan ba sai qarfe wajen shidda na yammaci.
Tunda yafita kamal ke ankare da yaushe xai dawo?,a wanne yanayi kuma zai shigo kamar yadda ya saba mishi,baiga shigowarsa ba sai yammaci,hakan ya qarfafa zarginsa a kansa,yakuma ci alwashin sake matsa masa lamba kozai karanto komai.
Tun daga ranar saiya zamana indai ya fahimci azeez din zai fita saiya qirqiri wani abun da zai sanya su fita tare,koda ba waje daya zasuje din ba kuwa,sam bai kawo komai cikin ranshi ba,illa iyaka ya dauka kamal din yasoma tattara hankalinshi kan abubuwa masu muhimmancin da suka kamata dashi.
Shudewar wata guda da sake faruwar lamarin tsakaninta dashi,a wani dare azeez din ya shirya kamar yadda yasaba lokaci zuwa lokaci don zuwa gidan yadauki abinda yake da buqata cikin gidan.
Falon yau kamal dinne kawai zaune,wanda dama yazauna ne kawai saboda azeez din
“Zaka dan ragemin hanya mana idan babu damuwa” sai daya waiwaya ya dubeshi sanda yake daukan muqullin motar daya arawa jabir,yadda yake yawan takurashi da rage hanya masa hanya abun yasoma ankarar dashi,harya soma shan jinin jikinsa azeez din ya janye qwayar idanunsa yana yin gaba,ya fidda ran xai amsashi sai yajishi yana cewa
“Taho mu tafi”.
Duk yadda kamal din ke sanyo hirarrki azeez din bai tankashi ba,daya fuskanci yau ‘yan wulaqancinne saman kanshi dole ya kama kanshi shima ya tsuke bakinsa,babu wanda ya sake cewa komai a cikinsu,saima azeez din daya tura plate din waqa,wanda cikin sakanni yasoma tafiya.
Gefan titi yaga ya gangara kana yayi parking din motar ya waiwayo ya dubeshi sai kuma yadauke kai
“Iyakata nan,kana iya sauka” bashi da sauran abun cewa,duk da baiso sauka anna din ba,yaso ne yaga yau maqurar inda yake zuwa,amma gudun tonuwar asirinsa yasa yace
“Ohkey,ba case,thanks,saimun hadu a gida ko?” Kai kawai ya kada masa,ya tashi motar yayi gaba,yayin da kamal.yaci gaba dabin motar da kallo,yana fatan Allah yakawo taxi da zai samu damar binsa kafin ya bace masa.
Daga nesa yasoma hango tahowar wata taxi,cikin sauri ya sanya hannu yasoma tsaidata kamar ance mishi wucewa zaiyi bazai tsaya ba,a gabanshi ya tsaya,sai daya shiga sannan cikin nuna alamun yana hanzarine ya nuna mishi motar azeez data kusa qulewa,yace ita yakeso yabi,bayaso suyi missing,yayi mantuwar wasu abubuwa nashi masu muhimmanci a ciki,motar drivern ya tayar kana yasoma bin motar azeez cikin qwarewa,da alama tsohon driver ne.
Yana tuqinsa yana dan tunane tunanensa har ya shiga unguwar,a nutse yasamu waje ya aje motar,dai dai lokacin da kamal yayiwa drivern umarnin yasaukeshi nesa kadan da inda azeez ya tsaida tashi motar,ya zaro kudinsa bayan ya gaya mishi adadin kilomitres din ya biyashi sannan ya fito.
Cikin sanda yake bin jikin varender da bishiyoyin dake titin har ya isa wani gida dake kallon gidan da yaga azeez ya shiga,ya lafe sosai a bishiyar dake wajen gamida bada hankalinsa kan gidan yana nazartarshi,gami da xuba mishi ido,yana karantar yanayin gidan dakyau,tare da fatan samun wani abu da zai zama hujja a gareshi.
Ya jima tsaye a wajen,babu abinda bai saqa ba cikin ranshi,zargin da zuciyarshi tafi bashi shine,azeez din ya aje zuqa zuqan ‘yammata ne yana hutawa dasu,shine yake boyewa bayason su sani,tabbas haka zatonshi yake babu shakka.
Fitowar azeez ta sanyashi sake lafewa,ta gabanshi yaja motarshi yafice,sai daya daina ganinsa sannan yafiti yana bin inda motar tawuce da kallo,kai.ua girgiza yana wani shu’umin murmushi,sa’annan ya maida dubanshi ga gidan.
Har ya nufi gidan gadan gadan kanshi tsaye,sai kuma ya dakata jin wayarshi na ringing,denial ne abokinsa,ya amsa kiran na wasu mintuna sannan ya maida wayar aljihunsa,ya sauya akalar tafiyar tashi yasoma neman taxi,hannu daya kuma yana laluben lambar wayar mom dinsa da niyyar shaida mata abinda yasamu gani.
Bugu biyu ya dauka,tamkar dama tana kusa da wayar ne
“Son,ya akayi”
“Mom,breaking news!”
“Me yafaru son?,mun cimma nasara ne?” Sai daya gyara zamanshi yana murmushi sannan yace
“Alamunta dai sun fara bayyana….kinsan me yake faruwa?” Kai ta gyada cikin qaguwa
“A’ah,yi sauri ka gayamin da Allah,banason wannan kauce kaucen”.
Dukkan abinda yafaru ya gaya mata,wanda hakan yayi masifar faranta mata,harta kasa zama
“Na jiyo qamshin nasara,wulaqanci da tozarci suna gab da tabbata kan abdul’azeez da uwarsa,amma meya hanaka qarasa cikin gidan ka ganewa idanunka badalar da yake tafkawa?”
“Da zan shiga,so wani abokina yana jirana,zamuje wani waje,saina bari kawai nasoma shaida miki daga baya na koma” fada sosai tasoma yi masa
“Wanne irin shashancine wannan?,ko meye ake jiranka kayi yakai girman wannan ne?,wannan fa rayuwarka ce gaba daya akeso a gina maka ita”
Cikin nuna qaguwa da takura da fadan da take masa yace
“No mom,ba zaki gane bane,wajen da zamuje alqawari nayi,idan na saba kuma zasu dinga kallona as qaramin mutum….dole dole zanje,dole zan shiga gidan naga me yake aiwatarwa,ai kin sanni mom,meye na daga hankalinki kuma ha’an?”
“Is ok shikenan,amma duk rintsi karka wuce gobe”
“Relax mom,dole saina dai daici lokacin da nasan bazamu hadu ba,u know azeez very well,dole sai mun kula fa”ajiyar zuciya tasauke,wannan kafirin yaron tun kafin yakai wadan nan shekarun yake basu wahala
“Shikenan….saina jika” da haka sukayi sallama da juna,kamal ya aje wayar yana taune lips dinsa na qasa,saqa kawai yadda zai.kama abdul’azeez dumu dumu yakeyi,yana kuma qissima irin tonon silili nacin mutunci da zasuyi masa.
Wani irin yammacine mai cike da wani irin yanayi mai dadi,dai dai lokacin da sukan xauna karatu a gidan,yauma hakkane,tana zaune da littafi a gabanta tana budawa shafi bayan shafi tana dan nazari tana jiran rakiya data tafi duba girki tadawo su dora a karatunsu,yau mama sodangi bata nan,ta fita siyo musu fruits na gidan da suka qare,amma bawai nisa tayi ba,don basu da nisa da wajen da ake saidawa.
Wani lallausan yadine da akayi mishi dinkin doguwar riga da hijabinta,butter colour ne,haka yake zuwa readymade,kayan sun amsheta sosai,sun fidda kamarta qwarai,banda dan duhun fata da take da ita zaka tsammaci ba ‘yar nijeria bace,uwa uba kuma yadda fatarta tayi kyau saboda cima me kyau dakuma zaman waje daya.
Dai dai sanda kamal ke tsaye qofar gidan,yana duban qofar gami da sakin murmushi yana kuma shafan gemunsa zuwa gefan fuskarsa,yana cikin farinciki mara misaltuwa idan yatuna ayau zai toni asirin azeez,mutumin da a rayuwa ya tsaya masa a wuya fiye da kowacce halitta,a hankali yadora hannunshi kan qararrrawar dake shaidawa masu gidan cewa suna da baqo ya dannata.
Doorbell ce tayi qara har sau biyu kusan a jere,hakan yasanya bilkisu daga kai ta dubi bakin qofar,saita dubi kitchen inda rakiya ke ciki,tasan babu lallai taji,kuma wala’alla mama sodangi ce,ta tsaya kiran rakiyar kamar bata lokacine,tunda maman tana da dan ciwo qafa lokaci zuwa lokaci,kuma a kwanakin yadan tasar mata,saboda haka rufe littafin ta miqe da sauri ta doshi qofar.
Murmushine akan fuskarta sanda tabude qofar,tashin farko idanuwansu ya hadu da kamal dake tsaye,murmushin fuskar tata saiya gushe ganin baquwar fuska,tana masa duban rashin sani,yayin dashi kuma hakan yabashi damar qare mata kallo tun daga sama har qasa.
“Wow….wow” yasamu bakinsa da furtawa ba tare daya shiryawa fadan hakan ba,ya dora da fadi a zuciyarsa
“Shege azeez…komai nashi na dabanne?why?”ba qaramin razana yayi ba da ganin bilkisun,baiyi zaton ganin halitta irin wannan ba mai kyau quruciya dakuma kwarjini a wannan muhallin ba.
Sakin qofar tayi ta juya zata koma ciki,ganin ta tambayeshi har sau biyu bai amsa mata ba,sai wani kallo da yake binta dashi,abinda ta tsana a rayuwarta kenan mugun kallo irin wannan,uwa uba ma sai taji sam bai kwanta mata ba
“Hey babe” ya fada da sauri,saita tsaya gamida waiwayowa tana dubanshi,fuskarta a gintse,sai yaga hakan yayi masifar qara mata kyau
“Sorry baby…baki sanni ba ko?,muje ciki zan miki bayani,i think yarima bai miki bayani na ba” wani muguwar faduwar gaba taji ta saukar mata,tashin farko bayan rashin kwanta matan da taji bai mata ba sai taji tsanar data yiwa wannan mai suna yariman tana shafarsa,bata ce masa ci kanka ba taci gaba da tafiya,ya take mata baya yana ci gaba da qare mata kallo,gamida lashe lips kamar tsohon maye,ba shakka bayan komai ya kammalu saiya tabbatar da cewa ya mallaki wannan babyn.
Inda tatashi takoma tazauna,tasake jan littafinta tana ci gaba da dubawa,yayin da shi kuma yasamu saman kujera yazauna idanunsa a kanta
“Dole azeez dole,ashe babbar harka ya samu irin wannan ya aje yana hutawa?,a ina yasamo wannan halittar?,a hakan ma ba’a ganin komai sai fuska da hannaye?,inaga anga sauran?” Saiya sake lashe labba gamida hadiye yawu muqut.
Ya bude baki zaiyi magana rakiya tafito daga kitchen,cikin matuqar girmamawa tazube tana gaidashi,don tasan wayeshi,ya amsa mata yana mamakin me kuma ya kawota gidan ita?,me takeyi?,yaushe tazo qasar?,duk da baisan fuskarta sosai ba amma ya tabbata daga masarautar kaisa take,zai dan iya shaidata.
Bai gama wannan mamakin ba aka sake taba qofar,rakiya ce tamiqe da hanzari taje ta bude,mama sodangi ce dauke da ledojin siyayya,rakiyan ta amsa kana ta matsa mata don tasamu damar shigowa.
Da mamaki suke kallon juna ita da kamal,saboda duk sunsan juna farin sani,saidai ita maman ta boye mamakinta qwarai,saita maye gurbin fuskarta da murmushi gamida miqa mishi gaisuwar barka da zuwa,ta sanya rakiya ta cika mishi gabansa da drinks da kuma fruits din data shigo dasu.
Duka sai hankalinsa ya kasu kashi kashi,ya gaza fahimtar komai,ga sodangi da rakiya daga masarautar kaisa,ga kuma wata baquwar fuska da baisan wacece ba,sannan alamu sun nuna dukka suna zaune ne a gidan,bakuma zuwan shekaran jiya jiya ko yau bane bisa dukkan alamu,to amma me azeez keyi a gidan?.
Kusan mintuna talatin ya kwashe a gidan yana karantar komai da idanunsa,yana kuma sauraren karatun su bilkisu,yayin da mama sodangi taketa takatsantsan,don tayi yaqinin wannan zuwan da yayi babu masaniyar fulani aisha ko kuma yarima,tunda kusan tana daga cikjn mutane na gaba gaba da suka san dukkan abinda yake wakana,hankalinta bai kwanta ba har sai daya miqe da zummar tafiya,idanunsa akan bikisu wadda bata sake daga kai ta kalleshi ba tun kallon farko har zuwa sanda yafice daga gidan.
Ajiyar zuciya mama sodangi tasaki,tana ankare da irin kallon da yake jifan bilkisu dashi,wanda sam bata gamsu dashi ba,tana ganin babu wata mafita datayi saura face ta shaidawa fulani zuwan kamal din,don koma meye a dauki.mataki,uwa uba kuma batason wani mummunan abu dazai shafi bilkisu ya bullo.
Zaman dirshan a ranar kamal yayi yana dakon dawowar azeez din,saidai kuma ya daki gurbi,don daga makaranta ranar saiya wuce gidansu mama sodangi,can dinma bai shiga da wuri ba,ya tsaya a makaranta duba wasu karatuttuka,abinda yasa ya gagara kenan kaf cikin makarantar,sunansa yakuma tumbutsa,hakanan farinjinsa ya kere na kowanne matashi dake ji da samartaka,tako ina azeez din ba baya bane,baya ga baiwar kyau aji izza da miskilanci da yake dashi,sai baiwar qwaqwalwa,wanda nacinsa da yawan maida hankalinsa kan karatun ya maidashi haka,sau da dama yakanyi mamaki idan akace wane daqiqi ne ko kuma baya ja,saboda a iyakacin saninsa yasan Allah bazai tana halittar dan adam daqiqi ba,saidai ace kaifin ganewarka tafi ta wane,hakanan dabi’ar karatu tanason mutum mai maci da jajircewa,shi kuma haka yake,baya wasa da dukkan wani abu da yasan mai muhimmanci ne,hakanan duk abinda ya sanya a gaba saiya kaishi.
Yana tsaka da hutawa bayan yayi ɗai ɗai saman tattausan gadonshi yana amsa wayar safwa kiran amminsa yashigo a daya wayar tasa,daga can bangaren tana tsaye ne cikin qawataccen falonta,duk da tarin kujerun da aka qawata falon dashi amma ta kasa zama,jira take kawai ya daga kiran nata
“Barka da warhaka ammi”
“Abdul’azeez,kana cikin hankalinka kuwa?” Yanayin yadda tayi maganar ya tabbatar masa lallai babu lafiya,kawai abinda ke faruwa,don haka saiya zauna sosai saman gadon fuskarshi na nuna alhini da mamaki,ko kadan baya qaunar abinda zai tashi hankalinta,har abada ammin ta musammance a wajensa,sama take da duk wata mace dake duniya,ya janyo daya wayar da yake amsa kiran safwa dashi,wanda daa yace karta katse kiran bari ya amsa wayar ammi,yayi qasa qasa da murya yace mata
“I wil cal u back,bani wasu mintuna” ba tare da ya jira amsarta ba ya katse kiran ya tattara hankalinsa kan ammi
“Nace kana cikin hankalinka kuwa?”
“Ammi….me hake faruwa?”
“Ta yaya zaka bari har kamal!….kamal yasan muhallinku,yakuma sako qafafunsa har gidan yashigo?” Boyayyar ajiyar zuciya yasauke yadda ba zata jishi ba,ya zaci wata gagarumar matsala ce,shi a wajenshi sam wannan ba wata damuwa bace mai girma
“Ammi meye a ciki?” Cikin muryar dake nuna maganarshi ta sake tunzurata tace
“Au,meye ma a ciki?,bayan kafi kowa sanin abinda yake gudana?,kasan nasan halin uwar kamal sarai….hakanan kaima kasan halin kamal din,kanason komai ya tarwatse ya lalace a lokcin da bamu shiryawa hakan ba kenan?” Idanunsa ya lumshe yakuma budesu lokaci guda,ha fuskanci me take tsoro,kada su karanci wani abu,har suje su shaidawa mai martaba
“Relax ammi….cool down please…,a sanda yazo bana nan,kuma ko ina nan na tabbatar bazai fuskanci komai ba,tunda ba’a rubuce yake a goshi ba,kin manta?” Shuru yadan ratsa tsakani,hakan yana nuna maganarsa tadan saka mata nutsuwa,jin hakan yasa ya dora
“Amma duk da haka,i wil take a seriouse action,bazan kuma bari qafarsa tazo gidan ba,kin gamsu da hakan?” Kai ta girgiza kamar tana gabanshi
“Hankalina ya tashi azeez,i know fauziyya na daya daga cikin mutanen da basu qaunata,basu qaunar su bude ido su ganni nida abinda na haifa,bare ace har nakai wani mataki ni ko su….hankalina yadan kwanta amma kadan,inajin kawai zan canza muku wani gidan ne” duk sai yaji hukuncin bai masa ba,sai passing passing ake dashi duk don aci gaba da boyeta,cikin son yardar da ita yace
“Believe me ammi,babu wani abu dazai faru,babu abinda kamal.ya isa yayi,beside ma duka duka baifi saura watanni uku komai ya qare ba,kin manta?” Da qyar da dabara yasamu yasha kanta,bayan tayita zabga mishi warning din ya kula yakumayi taka tsantsan.
Ta bangaren kamal kuwa bayan ya gama xaman jiran nashi,har zuwa wajen biyu na dare yaji shuru,saiya miqe yana tsaki yanufi dakinsa,gefan gadonsa yazauna yaciro wayarsa yana yunqurin kiran mom,don baiyi maganar da ita ba,ya kuma tabbatar tana can tana jiransa,daya kintata lokaci yasan a lokacin bazai wuce tara na safe ba nigeria.
Ringing daya kacal tayi ya daya,tamkar dama tana zaman jiran kiran nashine
“Ya ake ciki?” Kansa ya shafa yana qiyasta inama ace xai bata labarin ya kama azeez dinne cikin qazantaccen yanayi
“Naje mom….saidai kusan basu samu wani abuba,hakanan banga wani abu baqo ba,sai baquwar fuskar yarinya guda daya dana gani” cikin son lallai sai sun kamashi da laifi tace
“Kaman yaya?,ita baquwar fuskan itace dadiron nashi duk da ban gani ba” goshinsa yahau murzawa yana tuna zazzaqar muryar bilkisu sanda take karantawa rakiya iziyya,wadda saura qiris su sauketa,da yadda kyakkyawar fuskarta ke hade tsaf
“Bana tunanin haka mom,don karatun qur’ani natarar sunayi” shuru hajja fauziyya tayi,fadin hakan da yayi ya warware mata dukkan tunaninta,saita koma ta zauna tana sakin ajiyar zuciya
“Sauran dake cikin gidan su waye da waye”
“Daga masarautar kaisa suke,babbar mace da yarinya,kamar naji yarinyar ana kiranta da rakiya,babbar mace kamar…” Sai yadanyi jim yanason tuna sunan,daga bisani yace
“Sodangi”.
Shuru tayi tan gyada kai,sannan daga bisani tace
“Dakyau hakanma,zansa amin bincike cikin masarautar kan su waye,meye kuma dalilin barinsu masarautar kaisa zuwa mexico” daga haka ya katse kiran,bai damu ba ya cilla wayae gefansa yana shafa kanshi da hannu daya,bilkisu na mishi yawo cikin idanunshi,saiya saki murmushi a hankali yana mamakin yadda yakeso ya jarabtu da ita cikin qanqanin lokaci haka.
Misalin hudu da arba’in ne na yamma agogon nigeria,tara da arba’in na safe agogon mexico sanda ya shiga gidan,kusan a gaggauce yake sauri yake ya debi wasu takaddu nashi zai wuce makaranta,don qarfe goma yana da lacture.
Dai dai lokacin da kamal yake zaune a falon gidan yana kallon news,hannunsa daya kuma yana kurban ruwan baqin tea.
Bin azeez yayi da kallo sanda yake sallama a gaggauce yana shigowa falon,saiya aje cup din hannunshi murmushi yana subucewa fuskarshi,yana ganin ya kamata yace wani abu,ya kamata azeez din yasan yaje gidan,ya kuma kamata yaji wani abu ko yasan wani abu komai qanqantarshi akan yarinyar,don haka yamiqe bayan ya bada tazarar mintuna uku da shigar azeez dakin nasa ya rufa mishi baya.
Da mamaki ya waiwayo sanda yaji an turo qofar dakin ba tare da sallama ba ana kuma shigowa,saboda kusan kowa ya sani,dokarshi ce,bai yadda da shigar mishi daki haka sakaka ba kai tsaye ba tare da neman izininsa ba,hakanan shima bai shiga dakin kowa cikinsu,idan ma ya shiga din to tabbas lalura ce ta kaishi ko ta kama yashiga din.
Ganin kamal ne ya sanyashi ci gaba da gyara takardun dake saman mirrow dinsa,dama koda bai shigo ba shi zai sameshi ya masa warning,don yadan fuskanci tamkar bibiyarsa yakeson ya dinga yi,wanda shi bazai lamunci hakan ba.
Cikin muryarsa da saman fuskarsa dukka zaka fahimci akwai nishadi da walwala a ciki,ya qaraso cikin dakin sosai yana dan qarewa dakin kallo a fakaice
“Shegen….komai nashi saiya banbanta dana kowa,kamar yana zabawa kanshi rayuwarshi” yayi maganar can qasan ranshi,amma a fili saiya tattaro dukkan juriya da dakiyarsa yace
“Hey man” banza yayi dashi kamar baiji ba,har sai daya gama abinda yakeyi ya riqe takardun sosai sannan ya juyo yana dubanshi,idanunsa ya sanya sosai cikin na kamal din,yana masa wani kallo dake qara fidda kwarjininsa,tsahon wasu sakanni,shima kallon nashi kamal yake,duk da yadda kwarjininsa keson dakusar da duk qoqari da yunqurin masa magana da yakeson yi.
Nakai maka ziyara a gidan ajjiyr baqinka na musamman,duk da ban shaida maka ba,but….amma naso nayi suprising dinka ne,tunda na fuskanci akwai abinda ake boye mana,kuma da naje din sai naga hakane,ashe akwai abun boyewar….” Ya qarasa fada yana daga gira irin na ‘yan duniya,yana fidda murmushi.
Azeez na tsaye yana dubanshi harya gama,saiya soma takawa kamar xai fice,saidai ba fitar zaiyi ba,zai rage nisan dake tsakaninsa da kamal ne,har sai daya zo dab dashi sannan ya tsaya yana dubanshi.
Cikin muryarshin nan mai cike da izza mulki da kuma qasaita,wadda a wannan karon ta cika da gargadi da jan kunne yace da kamal
“U break my rules….kamal,nasha gaya maka…ka daina yunqurin shigomin daki ba tare da sallama ko neman izini na ba,secondly kuma….iam warning you,ka fita daga sha’anin rayuwata,abinda kaketa yunqurin shiga bazai maka da kyau ba,wannan itace shawarata” saiya ci gaba da takawa,harya wuceshi kamal na binsa da kallo,har yanzu baiji komai game da yarinyar ba don haka yace
“Idan banda akwai abinda kake boyewa meya hanaka ci gaba da zama damu ummm?….and ita din wacece ita?” Shuru ne ya ratsa dakin,azeez ya dakata daga tafiyar da yake,yana jefa masa tambayar bilkisu ta dawo masa tarwai a kwanyarsa,yana magana ne a kanta ko kuwa?.
Sake takowa kamal din yayi zuwa bayan azeez,sannan yasake cewa
“Ita kadai nakeson sanin wacece ita,coz she attract me,na kuma ji ina da interest a kanta,so pls ko zaka hadani da ita” karon farko yaji wani mugun bugun zuciya,wanda tsahon rayuwarshi bazai iya tuna when last da yaji haka ba,saiya juyo sosai yana jifan kamal da wani irin kallo,take yasha jinin jikinsa,yana jin yana masa kallon ne da fassara ta daban,don haka ya gyara tsaiwarshi
“Am seriouse man….sonta nake da gaske,ba irin soyayyar da kake min fassararta ba….” Dakatar dashi yayi ta hanyar nuna masa qofa da hannu,sannan ya motsa labbansa a hankali
“Get out pls…zan kulle dakina” fuskar kamal din akwai damuwa sosai,amma yasan halin azeez din,dama kadan daga aikinshi ne,don haka ya daga kafadunshi sannan yasoma takawa yafice daga dakin.
A zafafe ya rufe dakin,kana yazo yawuce kamal din dake tsaye a falo,ya tada motarsa cikin zafi kana yafice a layin.
Har saman fuskarshi yake jin zafin,yadinga shafa sumarshi zuwa sajensa yanason lalubo meya zafafa kanshi haka da yawa bayan yayi ‘yar tafiya,iskar sassanyan bishiyun dake jere gefan titin sun bugeshi,fresh air ce mai kyau ta tatattciyar safiya,daga baya abinda yayi realising kawai shine,yana da kishi qwarai,ta yaya kamal zai nemi yayi tarayya dashi kan wani abu dashi ya taba tarayya dashi?,bawai don ya damu da wanzuwarta ko wani abu bane,a’ah,kawai.har zuwa yanzu tana qarqashin ikonshi ne,idan da bayan nan ne bashi da matsala dashi,sai daya qaraci yawonsa ya tabbatar duk wata temper tashi game da kamal ta sauka sannan ya shiga aji,a sannan malamin harya kammala yafice,sai saura ya taras.
****************
“Auta” fulani adama ta kira sunanta cikin izza tana mata wani duba dake nuna koma meye zata fada mai matuqar muhimmanci ne,tun kafin ma tayi magana yanayin wajen da suka kebance kadai ya isa ya gayawa auta cewa ba qaramar magana zasuyi ba. A ladabce ta masa mata
“Ranki shi dade,Allah ya baki nasara”
“Akwai mutane guda biyu a gidan nan da tabbas basa cikinsa,kuma hadiman gidan nan ne,baya ga haka suna aiki ne a sassan aisha….” Saita tsagaita gami da yin shuru,yayin da ita ta jinjina kai
“Auta inason a bincikamin cikin sassanta su waye basu nan?,idan an samu ina suka tafi,auta….” Ta sake kiran sunanta,ta amsa mata tana sadda kai
“Banason wannan karon acemin ba’a samo wani bayani game da aikin nan ba,inason kota halin qaqa nasamu wani bayani da zai gamsar dani” kai ta jinjina
“Da ikon Allah wannan karon ranki ya dade sai inda qarfina ya qare,Allah ya baki nasara zakiyi farinciki da samun baya nan”
“A tashi a bamu waje” ta fada tana juyawa autan baya.
Koda ta fice zurfin tunani ta fada,tana tuna yadda abubuwa suke son su jagule musu,tako ina aisha ta toshe kowacce kafa ko qofa da za’a samu wani abu daya danganceta,bata taba shiga matsi da wahala kan wani abu data sanya gaba ba irin wannan lokacin,dan ko fulani saratu bata wani bata wahala ba,a yanzunma mantawa take da ita da abinda ya shafeta,don tasan ta rufe babinta,aisha yanzu itace target dinta.
Cikin sati guda auta ta dinga shige da fice ta kowanne fanni don gano su waye basa nan din?,sannan ina suka tafi?,me suka tafiyi din?,saidai dukka qoqarinta ya cimma tura,abu qwaya daya tal tasamu ganowa shine,sodangi da rakiya ne basa nan,dole haka ta tattara abinda tasamu ta shaidawa fulani adama.
“Allah ya tsinewa yarinyar nan,Allah ya isa tsakanina da ita” fulani adama ke fada wanda batasan harya fito fili ba saboda takaici da baqincikin daya mamayeta,tuni ta kora autarma,wadda ita tana ganin tayi namijin qoqari,saboda dukkan hadiman fulani aishan ‘yan amana ne,samun wani bayanai daya danganceta daga wajensu ba qaramin aiki bane,tana da wani tsari,ba dukkan komai zata gudanar bane take bari ya fita har a sani,hakan ya sake sanyawa ta zama mai ciakakken sirri akan dukkan al’amuranta.
****** ******* *********
Sannu a hankali kwanaki suka dinga tuawa,lokuttan da sukayi musu saura na barin qasar mexico bai wuce sati takwas ba watanni biyu kenan masu zuwa.
Ta fannin mama sodangi da kadan da kadan take tattara dukkan wasu kayansu da tasan cewa zasu tafi dasu,dakuma wadanda zasu barsu a nan inda suka samesu.
Bata taba yin zancan da bilkisu ba,hasalima wani irin tausayin yarinyar takeji sosai har cikin ranta,tana jinta tamkar diyar cikinta data haifa,takan zauna sau tari ita kadai tayi ta tunanin yadda rayuwarta zata kasance a nan gaba,bayan anci moriyar ganga a yarda qauronta,dukkan wani fata nata da burinta na ganin manufar auren ta sauya sai taga ko kadan babu alamu dake nuna samuwar hakan,taso ace inama inama wannan zaman nasu ya haifar da shaquwa da soyayya mai matuqar qarfi,wadda zata zama silar wanzuwarsu a matsayin miji da mata har gaban abada.
Tasan azeez tsaf ciki da bai,tunda itadin tamkar uwa ce a wajensa,daukar ciki da naqudarsa ne kawai batayi ba,amma ita tayi rainonsa kaf,hakanan bilkisu,adan zaman da sukayi na watanni goman nan ta karanci wasu daga cikin halayenta,wadanda dukka masu kyaune,bataga guda mara kyau ba ko abun tur,taga dacewarsu da azeez fiye da yadda ta zata,tana da tsammanin cewa tabbas babu shakka fulani aisha batasan wacece bilkisu ba,a iya nata nazarin da hangen,da kuma karantar yanayi da halayyarta da tayi,bilkisun itace irin macen da kowacce ywa zatayi kwadayin ta zama suruka a wajenta,tana da halayya da dabi’u masu kyau nagarta da kuma jan hankali.
Abinda bata sani ba shine,itama bilkisun ta nata fannin tama irge da duk kwana daya data ragu cikin kwanakin da suka rage mata,zumudinta na komawa zuwa gida yana qaruwa,ba don komai ba,sai don tazo taga ‘yan uwanta,jininta,wanda kullum kwanan duniya dasu take kwana take kuma tashi dasu,saidai kuma karsashinta yakan ragu idan ta tuna meye makomarta anan gaba?,ta rasa karatunta,ta rasa mutuncinta,sunanta bazawa a yanzu?,eh tabbas!,wannan shine sunan da zata ci gaba da amfani dashi.
Cikin satin da ya zamana shine satinsu na qarshe cikin qasar,sai dukka yanayinta yasake canzawa,hakanan take jin wani iri a dukka.jikinta da zuciyarta,duk wata walwala tata ta tafi,sai takejinta wani iri,tamkar ranar da zata taho daga nigeria zuwa qasar,tafison zaman kadaici fiye da komai,tafison zama shuru ita daya,duk sanda ya kadaice din tana zaman takurawa kanta ta hasasowa kanta meye makomarta,dukka mama sodangi na lura da ita,tsananin tausayin bilkisun ne ke sake kamata,don ta riga data sani,koma wace macace akayiwa rayuwarta haka daga mai manufa zuwa mara manufa zataji fiye da abinda bilkisun takeji,musamman idan tasan rayuwa fiye da bilkisu,ma’ana shekarunta sun daranma nata.
******* ****** ********
Gagurumin shiri take na tarbar yaron nata,wanda takejinsa daya ne tamkar da dubu,shiri tayi na kece raini na bikin murnar dawowarshi tare da kammala karatunsa,saidai a wani sashe na zuciyarta tana jin cewa,koda ya dawo din zai dora ne daga inda ya tsaya,bawai zaizo yayi zama na dindin bane a masarautar,saidai tana sa mishi ran zan dan zauna dasu adadin kwanakin daya jima rabon da yayi irinsu.
Wannan karon kusan duk wani wanda ya kwana yatashi a masarautar kaisa yasan da dawowar yarima azeez,bama masarautar kawai ba,duk wanda ke cikin garin na kaisa harma da maqwaftansa,saboda shiri fulani aishan take dan gaske,irin shirin da akecewa tsone idon maqiya.
Kamar yanxun da take xaune gaban mai martaba,cikin ado na kece raini,har yau bata bar ado wa mai martaba ba,hakanan dabi’arta take,macace mai masifar tsafta da son ado da kwalliya,shi yasa har kwanan gobe tauraruwarta take haskawa a zuciyar mai martaba,har kullum aishansa ta dabance,tasan kanshi hakanan tasan yadda take tafiya dashi.
Dan gyaran murya yayi yana gyara zamanshi,idanuwansa bisa kanta
“Yanzu uwar abdul’azeez da akazo aka tsareni har haka me ake buqata?,ni naga alamun ma fa anasone gaba daya a ture gwamnatina daga zuciyar yarona,tako.ina kinbi kin dha gabana a wajensa ba tare dana ankara ba?” Wata qawatacciyar dariya tayi tana lanqwasa wuyanta,tana mishi wani kallo da duk duniya shi kadai yake samunsa
“Ni na isa Allah ya baka yawan rai,abdul’azeez ai naka ne,bama shi kadai ba,uwar sa taka ce bare shi” murmushi ya fidda wanda ke nuna kalamanta sun mishi dadi,ta iya lafazi mai kyau da kwantar da zuciya,duk cikin matansa babu mai irin harshenta,shi yasa ko zaman hira yafi jin dadin yi da ita fiye da kowacce a cikinsu,duk da yana qoqarin boye fifikon kowaccensu a cikin zuciyarsa.
“Kamar nawa zan bayar?,amma fa kada a manta,nidin almajirin dan kasuwa ne….kece hajjaju guda,don naga saida komai yazo qarshe aka nemi na bada nawa kason” murmushi tasake yi wanda yasake fidda kyanta duk da shekaru da suka fara ja
“Ko nawa ran sarki ya dade ya bayar fulani tana maraba,amma kada ya manta,kome fulani tayi da bazarsa take rawa” harar wasa ya jefa mata sanda ya dauki wayarsa
“Dadin baki ko?,salon na miki transfer duka kudin account din nawa ba tare dana ankara ba” dariya tayi
“Da na zama daya daga cikin jerin miloniyoyi mata matuqar dukiyar cikin accnt din sarkin kaisa ta dawo hannuna” dariya ta bashi sosai,yana murmushi ya mata transfer kudade masu nauyi,har tayi mamakin yawansu ta dubeshi,saiya daga mata gira shima yana duban nata yace
“Kina mamakine?,kaman ban taba hidima me yawa haka kan lamarin abdul’azeez ba kamar yau ba ko?” Kai ta gyada,saiya gyara zamanshi yana murmushi
“Nima inason yarona sosai aisha,wala’alla ma fiye da yadda ke kike sonshi,amma dole a matsayina name iyali da yawa,wanda Allah ya wajabtamin yin adalci a tsakaninsu,dole na dinga takatsantsan da kuma qoqarin daidaita matsayinsu cikin zuciyata,koda ace wani yafi soyuwa a zuciyata fiye da wani,inason abdul’azeez bawai don matsayinsa na da namiji ba,a’ah,inasonshine saboda soyayyarsa daga Allah take a zuciyata,bugu da qari a yanayin da Allah ya azurtani dashi koda daga wanne jinsi ya fito,inajin xan soshi fiye da kowa cikin ‘ya’yana,ubangiji ya daukemin mahaifina a ranar daya musanyamin dashi” sai ya tsagaita yana sauke ajiyar zuciya.
Kai fulani ta gyada,har cikin zuciyarta tana jin dadin yadda yau yake sake jadda da mata soyayyar shalelenta,iya wannan kawai ya isheta alfahari gami da farinciki tsakanin abokan zamanta
“Allah ya yiwa mai martaba raham,ya kyauta makwanci,yasa can tafi nan”
“Amin,amin ya Allah indona” ya fada yana murmushi,itama saita murmusa tana jin yana bata kunya.
“Amma ina ganin zuwa yanzu da abdul’azeez zai dawo gida,ya kamata ace anyi maganar aurensa,saboda shekaru suna tafiya,inason ya zama babban mutum kamili,hankalinsa yasake game jikinsa,don shine magajina anan gaba kamar yadda kowa yasani” maganarsa sai tadan sanya zuciyarta rawa da yayi zancan aure,saita tuna da nata plan din duk da yake kwanaki qalilan suka rage a gamashi,hakanan ta gama shirya komai akansa shima.
A karan kanta itama tana lissafin zuwa yanzu ya kamata ayi magana tsakanin magabatan abdul’azeez din dana safwa,a qalla asan da xaman juna,amma furucin me martaba shi yanke zaren tunaninta ba tare data shirya ba,yakuma so daga hankalinta
“Kinsan diyar wajen professer Amk?,wadda tazo kwanaki hutu ko?” Da sauri ta gyada kai,duk da bata shaida yarinyar wani can can ba,don data zo din ta sauka ne sassan fulani saratu a matsayinya na uwar gida kamar yadda shi mai martaban ya tsara,saidai kawai ta shigo ta gaidasu,sa’annan data tashi tafiya tabiyo ta mata sallama,ita kuma ta mata halin girma kamar yadda ta saba da kyaututtuka kala daban daban,tana sone taji abinda ya dauko xancan yarinyar,kamar yasan me take saqawa kuwa saiya dora
“Da mun fara magana dashi professor din,kan yiwuwar hada aurensu da abdul’azeez…” Ai yana ajewa ta kama,don ita sam maganar ma bata tsaru a kunnenta ba,ina ‘yar professor ina azeez din?,tana ganin kwata kwata ba ajinsu bane
“Ai Allah ya taimakeka…..abdul’azeez tuni yana da wadda yakeso,kuma sun jima da fahimtar juna,maganar karatunsu duka ita dashi shiya kawo tsaikon shigar manya maganar” Da dan mamaki yadubeta kana yace
“Af…kice na kusa tafka kuskure….to amma,ya akayi haka?,bamu taba maganar dashi ba”
“Ni na dakatar dashi saboda karya hada karatunsa da soyayya” murmushi yasaki
“Kamar yaya?,saikace wani mace” murmushi tayi tana son sauya akalar zancan
“Kasan halin yaran nan sarai,matuqar suka sanya soyayya cikin ransu karatunsu saidai addu’a kawai,basu iya daukar abu da sauqi ba” kauda wannan zancan yayi ta hanyar cewa
“Diyar wacece ita?”
“ƴar alh ibrahim khalilu attah,diyar qawata kuma” idanu sosai mai.martaba ya zuba mata,wanda hakan yayi mata kwarjini sosai,saita dan basar kana ya jeho tambayarsa
“Ni dake kusan dukka musan waye alh attah….ina fata aisha ba auren hadi zaki masa ba saboda ‘yar aminiyarki ce?,don kinsan na soke auren hadi a tsarina gaba daya,kaf yarana babu wanda zan sake yiwa auren dole?” Kai ta girgixa
“Sam ba haka bane Allah ya baka yawan rai,abinda kake tunani bashi bane” shuru ya ratsa tsakani sa’an nan yace
“Shikenan….duka mu ajjiye maganar tawa da taki,idan yadawo zan tuntubeshi naji nashi ra’ayin”
“Allah ya nuna mana” ta furta tana sauke boyayyar ajiyar zuciya.
Dukkan wani abu da azeez din zai buqata ta riga data kammalashi,hatta da dukkan wani furniture na bangarensa tasa an musanya masa da wasu,ko tsinke bata bari ba,duk da cewa ba tsufa sukayi ba,tayi hakanne da biyu,na farko tasa an caje dukkan sassan nasa lungu da saqo,an tabbatar babu wani abun cutarwa a rataye ko a bunne,kana ta sanya aka qara matakan tsaro bayan an gama shirya komai tsaf.
Hatta da gidan da mai martaba ya bashi kyauta sukutum da guda sai data sanya aka tsarashi aka kuma gyarashi yadda zai dace da tsarinsa dakuma son ranshi.
Kyautar gidan da yafi kowanne gida qawatuwa cikin gidajen da mai.martaba kedashi ya jawo cece kuce tsakanin matan nashi,gwara adama tayi qoqari ta boye tsananin bacin rai da kuma adawarta cikin kirsa da munafurci,amma fulani saratu dake abunta gaba gadi takanas ta iske mai martaba da zancan,murmushi yayi sanda ta gama jawabinta
“Banda abinki saratu…..shifa yaron nan da kike gani dole idan yatashi aure idan bashi da yadda zaiyi na bashi gida,idan ta kama ma harda auren inyi masa dungurun gum,qannenshi kuwa daga daya wataran shine a makwafin mahaifinsu,babu wani abu dana gaza tsakanin yarana,kowanne ina bakin qoqarin biya masa buqata da sauke nauyinsa daya rataya a wuyana,hakanan ina qoqarin ganin na daidaita komai tsakaninsu,babu son kai ko fifici” jikinta ya danyi sanyi,saboda tasan cewa hakanne,tabbas yana bakin qoqarinsa na ganin yayi adalci yakuma daidaita matsayin kowannnesu,to amma tana matuqar kishi da aisha ne,da yadda akomai ta fisu,tun daga farinjini cikin gidan da kuma yawan masoya,duk da cewa wasu da yawa suna boyewa ne saboda ganin idanunsu.
“Kayimin afuwa Allah ya baka yawan rai,amma maganar gsky wannan kyauta sam batayi ba” murmushi yasake yi ganin ta kasa bada cikakkiyar hujja
“Kinga saratu…na riga na bawa abdul’azeez gida,bawai don baya da,wannan kawai ra’ayina ne,kamar yadda nake hidimtawa gamida kashe kudi wa qannensa a duk sanda zan aurar dasu,ba kuma tare da tashi mahaifiyar tayi qorafin na musu abu banwa nata yaran ba” hakanan ta qaraci qananun mitocinta da gunguni tamiqe ta fita,tanajin kamar taci wuta saboda bacin rai kishi da masifa dake cinta.
Tsanar abdul’azeez na sake qaruwa a zuciyarta,tana jin gaba daya ya zame musu qarfen qafa,ko qadangaren bakin tulu,kullum kwanan duniya sai taji ko taga wani abu game dashi dazai sanyata bacin rai,bazata iya tuna mutum nawa ta hukunta cikin barorin sassanta ba akan abdul’azeez da tsohuwarsa,sukan manta su kirashi da sunan da tuni ta haramtashi ta kuma yi jana’izarsa a sassanta,ko suyi subutar baki su yabesu,da wannan bacin ran ta qarasa sassanta tana qulla abunyi a zuciyarta.
Ƙarfe biyu da mintuna ne na rana a qasar ta mexico,tun daga unguwar zuwa gidan gaba daya ya dauki shuru,baka jin motsin komai saina abubuwan da ba’a rasa ba,saboda qarancin zirga zirgar al’umma cikin unguwar da kewayenta,wanda dama ba kasafai kake jin hayaniya sosai cikinta,har dama dama ranakun qarshen mako.
Dai dai lokacin da bilkisu ke zaune a falon gidan ita da rakiya,wayarta ce a hannunta tana danne danne,wanda ita kanta bata ce ga abinda takeyi a ciki ba,duk da tasan tana duba wasu hadisaine data sauke su take bibiya kullum har ta kusan kammalawa su duka,saidai a yau bata gane karatun,yinsa kawai take,yayin da rakiya wadda ke zaune a gefanta take kallo a tv plasma din dake girke a falon,mama sodangi kuwa tana daki tana ci gaba da tattara kayayyakinsu waje gida.
Qararrawar dake qofar falonsu ta dauki qara,dukkansu suka kalli bakin qofar,sam babu wani kuzari a jikinta saboda haka rakiya ta rigata miqewa ta nufi qofar don budewa.
Hausa taji rakiyan tanayi na wasu sakanni,ta saki qofar ta dawo ciki,saita wuce kai tsaye zuwa dakin mama sodangi,bata jima ba suka fito ita da maman,rakiyan takoma inda ta tashi ta zauna,mama kuma ta zarce bakin qofa
“A’ah,lawal…..shigo mana,ya zaka tsaya a nan?” Tayi maganar tana dawowa ciki,babu jimawa sai gashi ya bayyana a falon.
Kakkauran matashi mai duhuwar fata,yana da tsaho dakuma jiki,da alamu shekarunsa ba zasu haura talatin da takwas zuwa da tara ba,kallo daya zaka masa kasan baiyi kala da zallar bahaushen nijeria ba,yayi zubi da ‘yan mali sosai,da alama jinin can ne.
Bata zauna ba sai data gabatar masa da ruwa da lemo sannan ta zauna suka gaisa sosai,ya karkata ya zura hannunsa a aljihun wandonshi yafito da passport da kuma ticket yana miqawa mama sodangi
“Wannan passport dinku ne da ticket dinku,an kammala komai”
“Hala fulani ta iso”
“Eh suna can tare da yarima,sunzo bikin kammala karatun nashi,kuma ina tsammanin duka tare zasu kom…..” Da sauri bilkisu tamiqe ba tare data tsaya jin sauran maganar ba,tunda taji an ambaci sunayensu ta gundura da xaman falon,tun can batasan ma meye ya zaunar da ita ba,a hankali ta taka tashige dakinta.
Gefen gadonta ta zauna cikin wani irin kasala da mutuwar jiki,tana ci gaba da danna wayarta,wanda zuwa yanzu ta daina fahimtar komai,sai wani nisan kiwo da qwaqwawarta tayi cikin duniyar tunani.
Mintina wajen ashirin kyawawa tana zaune a haka,bata motsa ba sai lokacin da aka turo qofar sa’an nan ta daga kanta,mama sodangi ce take takowa cikin mutuwar jiki da kasala,bata ce komai bs itama harta iso gefan bilkisun ta zauna,sannan ta miqa mata wani dan koren littafi da wata paper,sai data kalli abinda take miqo matan sannan ta sanya hannu ta karba tana juyasu
“Passport ne da ticket,na fitarmu daga mexico,nan da kwanaki biyar masu zuwa idan Allah ya yarda”.
Ba zata iya tantance mai taji ba,saidai abu guda da zata iya ganewa wani sashe na zuciyarta ya cika da farinciki da murnar samun ‘yanci,yayin da wani sashen ya cika fal da fargaba da tsoro,ga wani irin cushewa da qirjinta yayi wanda batasan na meye ba
“Allah ya kaimu” ta fada cikin sauri sauri tana lalubar lambar wayar umma katti wanda kusan yawancin lokuta da wayarta take magana da ƙannenta
**************
A hankali doguwar motar ta alfarma wadda ke dauke da iyali da kuma ahalin masarautar kaisa,wanda ya hada da fulani aisha,da yaranta duka,Aarifa uswa sumaira da afnan,tana tare da amintattun hadimanta har mutum hudu,sai kuma fulani adama wadda ta buqaci zuwan itama,tana tafe da hadima daya sai diyarta da bata aurar ba afra.
Ko kadan fulani aishan bataso zuwan adaman ba,amma saita dake,ko a fuska bata nuna ba,tunda mai martaba da kansa ya buqaci hakan.
Da fari adaman itama zuwan sam bai mata dadi ba,amma daga bisani da sukayi magana da haj fauxiyya saitace da ita
“Aikamar dama ce kika sami,dama da xaki nunawa duniya dashi kansa yaron kina qaunarsa,dama ta biyu kuma zaki iya sanya idanu qwarai da bin diddiginsa har zuwa ranar da zaku dawo,wala’alla idan ska dace ki samu wani hujjan kamawar komai qanqantarta”. Wannan magana ta fauziyya ta sauko da ita har ta saki murmushi,tana kuma sake tabbatarwa kanta maganar fauziyya haka take bayan tayi nazari.
Gidane wanda zai ishesu sauka su duka,babu matsi ko takura,falo ne yalwatacce mai dauke da dakuna a wani corridor na daban,fulani aisha daki daya ita da autarta afnan,uswa sumaira da Aarifa da yaran uswan biyu daki daya,daya dakin kuma fulani adama ce da afra wadda taqi xama dakinsu uswa ta koma dakin mamanta,sai wami spare dakin Kuma dake falon gidan daura da kitchen sauran barorin da suka taho dasu suka sauka a ciki.
Kowa dakinsa ya shiha ya kintsa yakuma huta gajiya,dai dai lokacin fulani aisha data gama wanka tana zaune saman daya daga cikin tuntun dake dakin,uswa na zaune a gabanta tana sake gyara musu kayansu,gamida jerasu yadda zasu musu dadin sawa,afnan na amsa tana jerawa cikin wardrobe din dakin.
Ita daya tayi nisa a zurfin tunani,duk da cewa ta gama tsara yadda zata kauda dukka tunanin adama,tasan cewa anzo gabar qarshe,kuma hausawa sukace aski idan yazo gaban goshi yafi zafi,idan batayi wasa ba komai zai iya kwabe mata ta hanyar adama,a wannan lokacin da akazo gangara,sam bata tsara plan na tafiyarta da ita ba,amma dole tayi shuru da maimartaba ya buqaci hakan,don kada ta tsammaci wani abun,tuntuni ta kula,ta kuma karanci halayen fulani adama da kyau,tana da sanya idanu dabin diddigi,shi yasa take takatsantsan da duk wata mu’amala da zata sanyasu su xama a bigire daya.
Duk da cewa hankalinta yadan kwanta data aikawa sodangi da ticket dinsu na komawa,amma dole ta tabbata sunbar qasar ba tare da fulani adama taga daya daga cikinsu ba.
“Afnan….maza kiramin yayanku” ta fada bayan takai qarshen tunaninta gamida suke ajiyar zuciya,dan tsaiwa da abinda takeyi afnan din tayi sannan ta bata rai
“Amma gaskiya ammi saidai a wayarki,kinsan halinsa,yanzu dana cika kiranshi zaimin halin nasa”ta qarasa fada a shagwabe,kai ammi ta gyada,kafin ma tayi magana uswa ta rigata
“Nima na kirashi,amma baiyi picking ba,yamin tex dai suna school suna qarasa wasu abubuwa”
“Ohkey,babu damuwa,rabu dashi ma,nasan zai shigo gidan nan da anjima”.
Babu jimawa kukun gidan ya shaida musu ya kammala abinci,ya kuma shiryashi saman babban dining na gidan,kusan kowa a buqace yake da abinci,hakan ya sanya lokacin fitowrsu cin abincin yazo dai dai da juna.
Kowacce jinta take ta cika ta kuma hamshaqa,fulani aishan na tsakiyar yaranta suna tsaka da cin abincin sanda fulani adama tafito,kamar zata maze itama yadda taga fulani aishan taga tayi,sai kuma ta tuna cewa ita din me nema ce wanda aka ce baya gajiyawa,don haka bayan ta zauna tasoma zuba abincin ta dubeta
” har yanzu abdul’azeez bai samu damar shigowa ba hala?” Cikin izza da sarauta ta amsa
“Eh…bai samu ba” sam amsar bata mata ba,amma saita danne,tsanarta da haushinta na ninkuwa a ranta,fatanta na zuwansu hannu yana sake qaruwar mata.
Fulani adama din ce tafara tashi daga zaman ta wuce dakinta,sai fulani aishan da yaranta,sai kuma afra dake zaune tana charting gami da cin abincin ba tare data kula kowa ba.
Sallamarshi cikin muryarshi dake cike da sarauta ta ratso falon,yanayin tafiyarsa ne kawai zai gaya maka tabbas a gajiye yake,waiwaya tayi tana amsa sallamar,fuskarta ta cika da fara’ar ganin gudan jinin nata,shima kai tsaye teburin cin abincin ya nufo,kowacce tasoma qoqarin shiga taitayinta,yayin da afra ta kasa zama ganin yaja kujera yana niyyar zama,saita yiwa kanta qiyamullaili ta miqe,badon taso ba tace
“Barka da yamma”
“Yauwa” ya amsata a taqaice,ta juya tawuce tana tura baki bayan ta tabbatar bazai ganta ba,cikin ranta tana ta jero mita,dama tasan koya amsa amsawar tashi bata wuce haka.
Afnan da sumaira suma miqewa sukayi bayan sun gaidashi,don kowa yasan hali,sai wajen ya zamana daga shi sai uswa sai fulani aisha,cikin girmamawa ya gaidata ta amsa tana tambayarsa
“Lafiya lau…..ya shirye shiryen?” Ya murxa goshinsa da tafin hannunsa
“Alhmdlh….komai ya kusa zuwa qarshe”
“Ma sha Alla” ta fada tana jin dadi har cikin ranta na yadda komai yake tafiya dai dai kusan dai dai da yadda ta tsara.
“Me zakaci?” Uswa ta tambayeshi cikin kulawa bayan ta kammala cin nata abincin,so take kuma ta rashi ta basu waje,don tunda taga ammin na nemansa tasan zasuyi magana ne,baice komai ba sai daya gama kallon duka abincin dake wajen,sannan ya mata nuni da abinda xata zuba masa,sannan yace
“Ba mai yawa ba” kai ta jinjina,sai data zuba mishi komai ta tura gabanshi sannan ta miqe tana duban ammi
“Ammi zanje na shirya zandan fita,munyi da abban aira zan je gidan anty umma mu gaisa” kai ta jinjina mata,daga haka tasauka tashige ciki itama.
Shuru ne ya ratsa tsakani lokacin da yake tsaka da cin abincin,fulani aisha tayi gyaran murya sannan tace
“Na aikawa sodangi da yarinyar nan passport dinsu har da ticket na komawa nigeria….zasu wuce daga can,don babu yiwuwar mu hadu,na gama tsara komai,da zarar sun sauka zasu danqata ga mahaifinta,abu daya yanzu ya rage takardarta,ka rubuta yau ko.zuwa gobe da safe,ahmad xaizo ya karba yakai musu,idan muka koma gida komai zai dora,mai martaba yayi magana kan yiwuwar fidda macen aure,nasan za maka magana kan diyar abokinsa prof,basai mun maimaita zance ba,ka san bayanin da xaka yi masa,da zarar ka gaya masa kuma abinda zai faru shine xai aika ga iyayen safwa….wannan shine mataki na gaba na rayuwarka da nake saka rai,kafin kuma zancan ci gaba da karatunka ya daidaita,muga wacce qasa yakuma kamata ka canza”.
Idanu ya daga ya kalli ammin,har yanzu kenan lokacin da zai zauna a qasarsu cikin masarautarsu baiyi ba kenan,ya raya haka cikin ranshi
“To” ya amsa mata dashi,daga haka wani shirun ne yakuma biyowa baya har zuwa sanda ya kammala cin abincin shima ya shige dakin daya rage guda daya yayi wanka ya sake fita.
Washegari kusan dukansu babu wanda yazauna,duk yawo suka fita,sun zagaya garin na mexico sosai,hakan yasa fulani aisha bata samu sake zama da azeez ba,duk da cewa hankalinta yana kan maganarsu,saboda haka washegari da daddare ta nemi ganinsa.
Cikin dakinta ya taddata ita dasu afnan gaba daya,suna ware wasu kaya da suka siyo,ita kuma tana zaune daga gefan gado,sanye da wata doguwar riga wadda tasha ado daga wuya hannu har zuwa gaban hular dake hade da rigar,idanunta nakan yaran,saidai kallo daya zaka mata ga mai hankali ya fuskanci duniyar tunani tashiga.
Sallamarshi ta sanyasu dukka daga kai suka amsa,suka gaidashi,ya amsa yana nufar wani dan qaramin carfet dake shimfide gaban fulanin ta dora qafafuwanta akai
“Ku bamu waje” fulani tayi.magana dasu sumaira,sai duk suka ajjiye kayan hannunsu suka miqe suka fita zuwa falon gidan.
“Barka da warhaka ammi”
“Yauwa barka kadai” ta amsa mishi fuskarta babu walwala,tana sanya hannunta gefanta ta dauko takarda da biro,wanda da alama musamman ta tanadesu,miqa masa tayi yabisu da kallo,kana ya kalli ammin,sai kuma yasa hannu ya karba
“Rubuta mata sallamarta,don ina tunanin gobe ne zasu koma”.
Baice komai ba saiya sadda kai saman takardar yasoma rubutu,sai kuma ya tsaya cak,don baisan me zai rubuta,baisan me ake rubutawa ba,idanun ammin duka suna kanshi,har zuwa sanda ya tsaya din,kai ya daga ya dubeta
“Ammi….bansan me zan rubuta ba,me ake rubutawa?” Fuskarta ta hade sosai kana tace
“Koma meye ka rubuta” shuru yasake ratsawa,haka kawai yakejin banbarakwai a lokacin da yake rubuta kalmomin NI ABDUL’AZEEZ ABDALLAH KAISA NA SAKI MATATA SAKI…..
Jim yayi yana qiyasta saki nawa,saki nawa nema?,maida bironshi yayi ya rubuta adadin da yake gani shine daidai,kana ya ninke takardar ya miqawa ammi,bata damu ta duba ba tunda tana da yaqinin ya aiwatar din ta amsa ta aje gefanta,kana ta dauki wuyarta takira ahmad shima ta nemi ganinsa,sannan ta dawo da hankalinta kan azeez
“Da qarfe nawa za’a fara gabatar da taron naku?,ina tunanin mai martaba zaizo,yakuma buqaci sanin yaushene ainihin lokacin,ban tunanin xaizo ya kawana ne,xaizo a ranar ya juya washegari wala’alla” Miqewa yayi yana amsawa
“Qarfe shida na yamma za’a fara” kai ta jinjina kana yasoma takawa
“Zanje ammi,wala’alla nasake dawowa,wala’alla kuma sai gobe”
“Allah ya nuns mana” ta amsa mishi,yana fita ta sauke ajiyar zuciya,tana jin wani nutsuwa da kwanciyar rai na ratsata,kullum ta Alla cikin fargaba take kan auren nan,kullum babu irin saqe saqen da zuciya batayi mata kan auren,sai gashi duk yadda ta zaci abun yazo mata a dai dai,kuma da sauqi fiye da yadda ta zata.
_uhmmm,nidai nace ba girin girin na tayi mai_😊.
********* ***** ********
Ita kadai ahmad yasamu zaune a falon,duk bilkisu da rakiya na backyard na gidan,kusan tun daxun,batasan me sukeyi ba acan,bata takura musu ba hakanan bata nemesu ba,don ta fuskanci dukkaninsu kowa alhinin rabuwa da dan uwanshi yake,ita dinma kawai dakiya take,amma abubuwa da yawa ne cunkushe a ranta,lamarin bilkisu ya tsaya mata a rai sosai fiye da yadda ta zata.
Lokacin daya miqa mata takardar tuni ta fahimci ta meye,haka ta dinga juyata bayan tafiyarsa,tanajin cikin jininta kamar saqon akanta yake,kamar itace bilkisu,tana jin wani nauyi da jinjina yadda zata miqa wannan mummunan saqo ga bilkisu,inama ace fulani nata dora mata wannan nauyin ba,inama ace ita da kanta ko azeez da kansa ta bari ya bata saqon,da hakan ya fiye mata sauqi,kuma an sauqaqa mata wani nauyin,tanajin fuskantar bilkisu da wannan saqon kamar wani zunubi ne a rayuwa.
Tana tsaka da juya takardar aka turo qofar kitchen wanda yayi linking da backyard din,rakiya ce a gaba bilkisu na biye da ita,kallo daya zakawa fuskokinsu ka gane sam babu walwala,sabo turken wawa,kuma tasan dole suji babu dadi,don iya zaman da sukayi na shekarar sabo da shaquwa mai girma ya shiga tsakaninsu,sai ta aje takardar gefanta tana binsu da kallo.
Haka ta kwana da takardar har wayewar washegari da zasu bar qasar,sam ta kasa miqawa bilkisun,hakanan batayi wani isashen bacci ba a ranar,sanin cewa tafiyar safe zasuyi,hakan ya sanya tun bayan sallar asuba bata koma ba,ta sanya rakiya tasoma.shiri,sannan ta nufi dakin bilkisu da kanta da niyyar tadata,saidai ta sameta saman abun sallah,hannayenta a sama da alama kukanta take kaiwa ubangiji,don haka saita koma da baya tana ja mata qofar dakin yadda ta ganta,zuciyarta na karyewa itama,tanajin kamar ta saki kuka.
Sosai mama sodangin ta dinga sanyawa kanta dakiya da jarumta,hakanan ta hana rakiya shiga wajen bilkisun,don kada ta haifar mata da karyar zuciya da gazawa,ta tsareta da aiki a daki,ita kuma tashiga kitchen tana hada musu breakfas na qarshe,wanda bata da tabbacin cikin su ukun akwai wanda zai iya ci.
Tana tsaka da aikin rakiya ta kawo mata wayarta,takuma shaida mata fulani ce ke kira,cikin girmamawa ta amsa wayar,takuma gaidata,daga can bangarenta tadora da bayani
“Ina fata saqona ya iske ku ta hannun ahmad?”
“Eh Allah ya taimakeki”
“Da kyau…..qarfe sha biyu jirginku zai tashi,zan aiko driver ya daukeku yakaiku airphort,daga can idan kun sauka akwai motoci biyu….daya zata dauki yarinyar ta sadata da iyayenta,daya kuma zata maidaku gida,banason asamu wata matsala,ki tabbatar komai ya tafi yadda na gaya miki” wani nauyi da rashin dadi taji yana ratsa zuciyarta,da gaske kenan rabuwar zasuyi?,rabuwar da har ba’aso susan gida ko matsugunnin bilkisun?,bata da yadda zatayi,don ita din ba kowa bace,a qarqashin iko da mulkinta take,dolenta ta amsa da to,kuma ta tabbatar mata za’ayi dukkan yadda tace.³³