SOORAJ CHAPTER 1

SOORAJ





CHAPTER 1




       

                              

*SOORAJ*

                              

Tsugune yake akan ƙafafunsa, kansa na kallon ƙasa, yayinda  kyawawan idanunsa suke alumshe,  jama’a ne cike awajen, sai hayaniya suke, fuskar kowa ɗauke take da  farinciki, banda wani mutum ɗaya, shima ɗin baƙin ciki  da damuwarsa basu bayyana akan fuskarsa ba, amma tabbas zuciyarsa nacikin matsanancin damuwa.

                              

Sake matse ƴan saffa saffan  idanunsa yayi da ƙarfi, jiyake kansa na juyawa, zuciyarsa nayi masa wani irin tuƙuƙi,  sosai hayaniyar jama’an dake wajen ke hautsina masa ƙwaƙwalwa, sam shiba mutum bane mai son yawan hayaniya, aduk sanda hayaniya yayi yawa awajen da yake, to ciwon kai ne ke kamasa mai tsanani, yanzu haka shikaɗai yasan abunda yakeji, jiyake kamar ya buɗe bakinsa ya kwarara ihu, koda zaiji sauƙin abun da yakeji.

                              

“ALHAMDULILLAH AURE YA ƊAURU YAU ASABAR AN ƊAURA AUREN SOORAJ MAI NASARA DA AMARYARSA AISHATU KABEER MUNA TAYA ANGO MURNA!!!”  abunda wani maroƙi keta faɗa kenan cikin ɗaga murya.

                              

Wannan maganan da maroƙin keyi shiyayi sanadiyar dawo da SOORAJ dake tsugune cikin hayyacinsa,   wani yawu mai ɗaci ya haɗiya, lokaci guda idanunsa suka rikiɗe suka zama jajaye, ƙoƙarin tashi tsaye yasomayi. Da sauri wani kyakkywan matashi dake gefensa yariƙe hanunsa, cikin murya ƙasa ƙasa yace “Please SOORAJ karkayi haka mana, acikin jama’a fa muke, kuma kasan tunda mukazo nan idanun jama’a akan mu yake”

                              

Tsuka wanda aka ƙira da Sooraj yayi, tare da fusge hanunsa daga riƙon da wannan ɗin yayi masa, kallonsa yamayar ga Abbansa, karab idanunsu suka sauƙa akan najuna, da sauri Sooraj yayi ƙasa da kansa.  

                              

A hankali Tururuwan jama’ar da suka taru a ƙofar gidan Alhaji Kabeer suka soma raguwa, kowa na ƙoƙarin kama gabansa,    ganin haka yasa Sooraj miƙewa tsaye yasoma nufar inda motarsa take, ko ɗaga kansa baiyiba balle har wasu daga cikin mutanen da sukayi ragowa su fahimci wani irin yanayi yake ciki.   Hanunsa yaɗaura akan murfin motar zai buɗe, yaji muryar  MAS’UD ta daki dodon kunnensa.

                              

“Inazakaje?” abunda Mas’ud yatambaya kenan.

                              

Juyowa Sooraj yayi ya watsawa Mas’ud harara, ransa amatuƙar ɓace yake, wani irin haushin Mas’ud ɗin yakeji, gani yake komai daya faru hadda sa hanun Mas’ud ɗin aciki,  takaici ne yasake turnuƙe zuciyarsa,  sai kawai yasaki tsuka yabuɗe motarsa yashige, Mas’ud na ƙoƙarin zagayawa gefen mai zaman banza yashiga, Sooraj yayiwa motar key, aguje yafigeta haɗe da turbuɗawa Mas’ud dakuma sauran jama’an dake kusa dasu ƙura.  Hakan yasa kowa yabisa da kallo, ciki kuwa hadda Abbansa dake can gefe suna ganawa da Baban Amarya. 

                              

Sheshsheƙan kuka ne ketashi acikin ɗan madaidaicin ɗakin, wata yarinyace rakuɓe ajikin bango, ta takure kanta waje ɗaya, daga yanda take sauƙe ajiyar zuciya akai akai zai tabbatar maka da cewa kuka taci ta ƙoshi son ranta,   idanunta da suka kaɗa sukai jajur ta buɗe haɗe da kai kallonta sama.   “YA ALLAH!” abun da ta ambata kenan cikin wata irin raunanniyar murya, dake cikin halin matsanancin naiman taimako,   tabbas ta yarda cewa idan Ƴa Mace tarasa Uwa to tarasa babban gata aduniya, Uwa itace komai itace ginshiƙin rayuwa, kamar yanda ruwa keda matuƙar amfani aduniya, haka uwa take awajen kowani ƴa/ɗa, ayanda take da ƙananun shekaru, tunaninta da hankalinta basukai ɗaukar wasu matsalolinba, amma saboda halin rayuwa duk tazama wani iri, rayuwarta duhu ne, rayuwarta ƙunci ne, HASKE take nema akoda yaushe, da fata dakuma burin wani wanda zai taimaka mata. 

                              

“Dan Ubanki wai maikikeyi acikin ɗakinnan ne? baƙar munafuƙa, Allah dai yayi wadaranki ZIYADA natsani waƴannan halayyartaki, muguwa mai baƙar zuciya, zaki fitone kosai nashigo cikin ɗakin nayi ƙasa ƙasa dake!?”   faɗan wata mata dake tsaye abakin ƙofar ɗakin da yarinyar ke ciki, matar tacika fam sai jijjiga ƙugu take. 

                              

Jinmuryan Inna Ma’u acikin dodon kunnuwanta baƙaramin tsoritata yayiba, jikinta na rawa tanufi hanyar fita daga ɗakin. 

                              

Tana fitowa Inna Ma’u ta bita da wani irin kallo. 
  “Wallahi natsaneki Ziyada, natsani koda jin sunanki ne, adole nake rayuwa dake acikin gidannan, keda uwarki kun riga da kunzamemin JARABA, ƴan iska masu fararen fuska!” Inna Ma’u tafaɗi haka cike da takaicin Ziyada.

                              

Itadai Yarinyar da ake ƙira da sunan ZIYADA shiru tayi tare da sunne kanta ƙasa,  ƙirjinta kuwa jitake kamar zaiyo tsalle yafito waje sarai tasan wacece Inna Ma’u, yanzu zata kuma sake jibganta fiye da wanda tayi mata ɗazu.   

                              

“Ungo wannan naira ishirin ɗin kije maza ki ɗauko min niƙa na, kuma wallahi idan kika sake baki dawo da wuri ba, yau saina ƙona wannan ɗan iskan fuskan naki, mai zubin mayu”  Inna Ma’u tafaɗi haka tana mai sanya hanunta ta  mangare Ziyada harsai dakanta ya bugu da bango,  sosai taji zafin bugewa dakuma mangareta da Inna Ma’u tayi, amma babu halin tayi kuka, naira ishirin ɗin ta amsa, cikin yanayinta mai sanyi tanufi hanyar ficewa daga gidan.
Tana ficewa Inna Ma’u tayi ƙwafa haɗe da cewa.
“Wallahi bazaki ƙara min cikakken sati biyu agidannan ba, ko kasheki ne ma gwamma nayi na huta, komai na mayyar uwarki kin kwashe”…. 

                              

Gudu sosai yake tsalawa akan babban titin, saida yayi tafiya mai nisa kafun yayi parking motar agefen titi, hanunsa yasanya ya bugi steering motar, tare da furzar da iska daga bakinsa,  wata drawer dake jikin motar yajawo haɗe da ciro goran ruwa, ɓalle murfin goran yayi haɗe da kafa goran abakinsa, saida yasha ruwan  fiye da rabin goran kafun ya ɗauke bakin goran daga kan nasa bakin,   numfashi yake fitarwa ahankali, jiyayi ƙirjinsa yayi masa nauyi,   ɗaga kansa yayi ya kalli madubin dake cikin motar, da sauri ya kauda kansa gefe, wani irin tsananin tausayin kansa ne ya kamasa, jiyayi zuciyarsa tayi wani irin karyewa,    kifa kansa yayi ajikin steering motar, baisan yazaiyi da rayuwarsa ba, baikuma san taya zai fahimtar da iyayensa lalura da damuwarsa ba, akodayaushe su kansu kawai suka sani, koda sau ɗayane basu bashi dama yasanar dasu matsalarsa ba, ako da yaushe basu da wata magana saita Aure, burinsu ɗaya shine yayi aure, baruwansu su basu wani damu da sanin shiɗin yayakeba,   ɗago kansa yayi daga jikin steering motar, idanunsa ne suka sakeyin ja, kamar anwatsamusu garin barkono,   bayajin cewa zai iya zama da kowace mace aduniyarnan, yanaji ajikinsa cewa shi ba’ayisa don yayi aure ba,  rayuwarsa cike take da DUHU baisan wani HASKE ba,   “Sai yaushene zasu fahimci hakan?” yatambayi kansa.  Shiru yayi naɗan wasu mintuna kafun yatada motarsa, yanzu kam ahankali yake tuƙin motar bakamar ɗazu ba, saidai kuma zuciyarsa cike take da tarin tunani kala kala lallai dolene zaiyi abun da ya saba, duk da yasan hakan ba daidai bane kuma ALLAH Ma bayaso, amma baida wani zaɓi da ya wuce haka…

                              

*(Sunan labarinnan SOORAJ shima ƙirƙiransa nayi kamar yanda na ƙirƙiri sauran, kamar yanda kukasani labarina ina ginashine akan mutum biyu, to wannan labarin ma hakanne, domin akan SOORAJ da kuma ZIYADA na ginashi, kamar yanda nagina SHU’UMIN NAMIJI akan ZAID da ZAHRAH,  nakan tsayawa nayi komaina akan daidai, ina iyaka ƙoƙarina wajen ganin nabaku nishaɗi, nasamu ƙalubale sosai akan Labarin dana gama wato SHU’UMIN NAMIJI duk da nasan matakin nasara yana tarene da ƙalubale, amma wasu sunta faɗamin maganganu son ransu so please kuna kiyayewa, bakowacce magana yakamata ace wasunku na furtawa ba, karku manta magana mai daɗi sadaka ce.Agaban wani tankamemen gate yayi parking motarsa, fitowa yayi daga cikin motar ya nufi ƴar ƙaraman ƙofar dake jikin gate ɗin, ahankali yatura ƙofar yashiga, Manu mai gadi naganinsa ya kwaso aguje cike da girmamawa yace.
“Ranka ya daɗe barka da zuwa, Ango, Ango kasha ƙamshi….” 

                              

Kallon da yayiwa Manu mai gadine yasa yaja bakinsa yayi shiru, batare daya ƙarasa maganar dayakeyi ba. 

                              

Direct wani dogon gini dake tsakiyan compound ɗin gidan yanufa. 

                              

Wata ƴar dattijuwar mata ce ke zaune acikin katafaren falon, kayane zube agabanta tare da wasu manyan akwatuna masu kyau da tsada. 
Da sallama ɗauke abakinsa yashigo cikin falon, amsa masa sallaman matar tayi fuskarta babu yabo ba fallasa. Baidamu da yanayin yanda yaga fuskarta ba, don yasan dalilin daya sanya tayi kicin kicin da fuska damace batason bashi, kuma amma duk da haka baijin zaiƙi furta abundake cikin ranshi.

                              

“Barka da gida Ummu” 
Sooraj yafaɗi haka bayan yayiwa kansa mazauni akan lallausan carpet ɗin da ya mamaye ƙasan falon. 

                              

“Yauwa sannu” Ummu tafaɗa tana mai ƙoƙarin tattare kayan dake gabanta. Shirune yashiga tsakaninsu, dama shi haka yake idan yayi magana saiyaja wasu mintuna baisake cewa wani abu ba, bakuma don baida abun cewa ba, a’a haka ya sabarwa kansa. Ummu kuwa afakaice ta ɗan saci kallonsa, yanda taga fuskarsa ya tabbatar mata da cewa akwai magana abakinsa, itakuwa bazata so taji komai daga bakinsa ba. Miƙewa tayi daga zaunen da take, wayarta taɗauka kana ta nufi hanyar da zai sadata da ɗakinta.

                              

Ganin da yayi cewa idan yabari tatafi yarasa damansa ne, yasanyashi gyara zama haɗe da cewa. “Ummu dama inaso….” 

                              

“Banason kacemin komai, ya isa haka, munriga da mungaji da halinka SOORAJ, wallahi kaji na rantsema awannan karon kasaki matar da muka aura ma, ranka saiyayi mummunan ɓaci, zakuma kaga fushinmu irin wanda baka taɓa gani ba!” Ummu takatseshi ta hanyar faɗan haka cikin ɓacin rai. 

                              

Jajayen idanunsa yaɗago ya watsawa Ummun, itakuwa ko waiwayosa batayiba ta wuce ɗakinta.

                              

Wani irin tsannin baƙinciki ne yasake kawo masa ziyara, babban abun takaicin shine yanda akaƙi basa dama, jiyayi kansa na sarawa kamar zai rabe gida biyu, tashi yayi ya fice daga cikin falon, ko iya kallon gabansa bayayi haka yakoma motarsa, kafa kansa yayi ajikin steering motar, yana fidda numfashi mai zafi, “Wannan wace irin rayuwace yakeyi? sai yaushene zai samu sauƙi daga raɗaɗin da yakeji?” tambayar dayaketa yiwa kansa kenan acikin zuciyarsa. Ya kusan mintuna 10 a wajen, kafun ya iya tada motarsa yabar unguwartasu gaba ɗaya, kaitsaye gidansa ya nufa. 

                                              

                        

Koda ya isa bedroom ɗinsa kayan dake jikinsa ya cire tare da shigewa cikin bathroom, wanka yayi tare da ɗauro alwala kana yafito, dogon wando na jeans yasanya tare da wata farar T-shirt, kallon agogo yayi yaga da sauran time kafun aƙira sallan Azahar, kwanciya yayi akan makeken gadonsa tare da lumshe gajiyayyun idanunsa…..

*** 
Idan hankalin Ziyada yayi dubu to atashe yake, domin kuwa tana zuwa injin niƙan tasamu ba’a niƙawa Inna Ma’u niƙan garin kunun tsamiyanta na gobe ba, hawayene suka cika idanunta, yayinda tashiga haɗa mai injin da Allah akan yaniƙa mata sauri take, da ƙyardai tasamu ya yarda ya niƙa mata. Tunda ta shawo kwanan ƙofar gidannasu take hango wata yagalgalalliyar mota, wanda taji tsufa harta gode Allah, cikin yanayinta na sanyi taƙaraso ƙofar gidannasu. 

Wani dattijone wanda aƙalla shekarunsa zasukai 60 tsaye ajikin wata ragwaɓaɓɓiyar mota dagani motar taci wahala, mutumin irin baƙaƙen tsofinnan ne, sannan kuma ko wani gashi najikinsa yatashi daga baƙi yakoma fari, kai tsaye zaku iya ƙiransa da tsohon najadu, domin daganin idanunsa zakasan cewa baƙaramin ɗan duniya bane, yanayin yanda yake kallon Ziyada kamar wani tsohon maye ne yasanya tayi ƙasa da kanta, tashige cikin gida, Murmushi Tsohon yayi haɗe da jijjiga kansa, wani irin daɗi yaji aransa alokacin dayaga Ziyada’n.

“La’anatu sai yanzu kikaga daman dawowa? halin asaran dai shine bazaki fasa ba?” Inna Ma’u ta tambayeta.

“Kiyi haƙuri Inna Ma’u, wallahi ba ayi miki niƙan da wuri bane, shine kuma…..”

“Da Allah rufemin baki shine kuma me? waye baisan fetsarancinki ba, shashasha kawai, yanzu da kika ebo ƙafa kika shigo cikin gida, shin bakiga Tsoho ɗan dashe natsaye a waje yana jiranki bane?”

Wani irin bugawa ƙirjin Ziyada yakumayi, a tsorace tace 
“Tsoho ɗan dashe kuma?”

“Ƙwarai kuwa, zakije kisamesane ko kuwa saina ɓaɓɓallaki yanzu anan wajen!” Inna Ma’u tafaɗi haka a hasale. 

Jikin Ziyada ne yasoma ɓari amma bata da wani zaɓi daya wuce zuwa tasamu tsohon najadun dake tsaye a waje yana zaman jiranta. 

Tana fitowa daga gida Tsoho ɗan dashe yasaki dariya irinta tsofaffin ƴan duniya. Kallonsa yamayar kan ƙirjinta, saida ya haɗiyi wani yawu, “Ƙaraso mana Amaryata” yafaɗa yana washe wawagegen bakinsa. 

Kallon tsananin tsana Ziyada tabisa dashi haɗe da soma ƙare masa kallo, idanunta ta sauƙe akan jajayen haƙoransa dayaketa washewa, gaba ɗaya bakinsa cike yake da tsakin goro, komai nasa dagajaja ba kyaun gani, duk da itama acikin dauɗa da ƙazanta take, sannan kuma bata da wani suturun kirki, amma duk da hakan ƙazancin Tsoho ɗan dashe daban take dana kowa, duk garin babu wanda baisan wanene Tsoho ɗan dashe ba, tsohone da bai riƙe mutumcin kansa ba, bashida wani aiki sai lalata yaran jama’a, matansa huɗu, kuma acikin garinnasu sosai akeji dashi, kasancewar yana da shanaye dakuma dabbobi, saboda tsabar duniyanci irin nasa har mota yake dashi, irin ko ohon motocinnan, nanma ƙaryan raine kawai irin nasa, ko iya tuƙata baiyiba, akwai wani ɗan ƙullinsa Ɗan liti shike tuƙasa yakaisa duk inda zashi, yanzuma tare suke.

Saida tagama ƙare masa kallo kafun ta kawar dakanta gefe, wani sabon tsanarsa taji acikin ranta, ganin da yayi cewa yarinyar nada taurin kai bazata ƙaraso garesaba yasanyasa soma takowa zuwa inda take, da sauri taja da baya. 

“Wai Amaryata badai tsorona kikeji ba? ai gwamma kisaki jikinki dani domin ina tabbatar miki da cewa mako mai zuwa za’a ɗaura mana aure dake” Tsoho ɗan dashe yafaɗi haka yana mai sake washe ƙaton bakinsa.

Jin ya ambaci kalmar aure yasanya taƙara ja da baya, ganin da tayi kamar baya cikin hayyacinsa ne yasanya ta juya ta koma gida yana ƙiranta amma ko waiwayosa batayiba, ashe Inna Ma’u na laɓe tanajinsu, Ziyada nashigowa cikin gida Inna Ma’u ta ɗauketa da wani irin faskareren mari, cike da takaici tace. “Amma kedai anyi yarinyar banza, ke inbanda hauka har Tsoho ɗan dashe zaizo miki da maganan aure kinemi wulaƙantasa, to kijini da kyau, ninan nabada aurenki ga Ɗan dashe, ko kinaso ko bakyaso, munafuka kawai, mai baƙar zuciya da aniya!” 

                

                        

Kai Ziyada tashiga jijjigawa lokaci guda kuka ya ƙwace mata, durƙushewa tayi aƙasa haɗe da kama ƙafan Inna Ma’u cikin muryan kuka tace. 

“Dan Allah Inna Ma’u kimin rai, karki haɗani da Tsoho ɗan dashe, kowa dake garinnan yasan halinsa ɗan iska ne, kuma ba tsohon kirki bane dan Allah kiyi haƙuri !!”

Ƙafa Inna Ma’u tasanya ta shure Ziyada cike da tsanarta tace “Idan kinga baki auri Ɗan dashe ba to saidai in mutuwa kikayi, ke ko mutuwa kikayi sai ankai masa gawarki” tanafaɗin haka tazari mayafinta da koyaushe ke akan igiya ta fita zuwa waje. 

Kuka Ziyada tasanya haɗe da tashi ta nufi ɗan ƙaramin ɗakinta. Zama tayi akan tabarma tare da cusa kanta tsakankanun cinyoyinta kuka tashiga rerawa mai taɓa zuciya, tasan tunda Inna Ma’u tafaɗi haka to sai ta aikata. 

Inna Ma’u kuwa koda taje tasamu tsoho ɗan dashe sosai suka tattauna akan Ziyada, inda yatada hankalinsa akan cewa shi lallai bayason aja lokacin auren, idan da ta sonsa ne ma shi koda yau abasa ita, idan yaso daga baya sai a ɗaura auren sosai yarinyar tashiga ransa, musamman daya lura cewa komai nata ɗanyene shakaf, da’alama zai kwashi garaɓasa mai romo, kuɗi sosai ya dumbulawa Inna Ma’u ita kuwa sai washe baki take da haka sukayi sallama.. 

Saida tayi kuka mai isarta kafun ta fito daga cikin ɗakin takama aikace aikacenta daya zame mata dole. 

Sallaman Babanta da tajine yasanya taji gabanta ya tsananta bugawa, muryarta na rawa ta amsa sallaman nasa.

“Baba Sannu da dawowa!” tafaɗa murya a sanyaye.

“Daban dawoba ai da bazaki ganni ba!” Fari kyakkyawan dattijon da taƙira da sunan Baba yafaɗi haka ahasale. 

Cikin sanyi ta sunkuyar da kanta ƙasa, wannan halin shi kullum Babanta ke nuna mata, tun tana ƙarama harkawo yanzu bata taɓa sanin ya soyayyar mahaifi yake ba, babanta ko kusa dashi bayaso tazo, tsanar dayake nuna mata haryafi wanda Inna Ma’u ke nuna mata, cigaba tayi da aikinta, shikuma kai tsaye ya wuce ɗakin Inna Ma’u jikinsa na rawa, gudun kada ta leƙo ta fara zazzaga masa masifa, don kamar yaron cikinta haka tamaida shi.

*** 
Bayan yadawo daga sallan Azahar bacci mai nauyine ya ɗaukesa, kusan awa uku ya share yana bacci, kasancewar yau weekend babu aiki. Ahankali yake buɗe kyawawan idanunsa masu ɗauke da zara zaran gashi asamansu (Eye lashes) akan agogon dake saƙale jikin bangon ɗakin ya sauƙe idanunsa. 3:00 pm daidai yagani, cikin nutsuwa ya zuro ƙafafunsa ƙasa daga kan gadon, bathroom yashiga yakumayin wanka tare da ɗauro alwala.

Tsab yagama shirya kansa cikin riga da wando na jeans masu kyaun gaske, ya feshe jikinsa da turarukansa masu ƙamshi da kama jiki, combat shoe yasanya aƙafarsa haɗe da ɗaura agogon Apple a hanunsa na dama, sosai yayi kyau, ɗago kyawawan idanunsa yayi ya kalli kansa acikin madubi, shikansa yasan cewa shi cikakken kyakkyawan Namiji ne mai aji dakuma ɗaukar hankali, amma kuma saidai yana da tarin matsaloli. SOORAJ namijine kyakkyawa, komai nasa abun burgewa ne, Yana da cikar halitta sosai, jikinsa amurɗe yake kasancewarsa ma’abocin yin gym, farine shi tas banda lallausan sajen dake kwance akan ƙuncinsa babu wani abu dayake ɓaƙi ajikinsa. Yana da wasu irin idanuwa ƴan madaidaita masu kyaun gaske, kamar yanda gashin idanunsa suke zara-zara haka gashin giransa ma suke, yana da dogon hanci, dakuma ɗan ƙaramin baki mai ɗauke da pink colour lips. 

Ya ɗauki sama da 3 minute yana ƙarewa kyakkyawan fuska da jikinsa kallo, ahankali ya sauƙe idanunsa ƙasa cike da raunin zuciya, yasani ahaka idan kowa ya kallesa zaiyi masa kallon Cikakken Namiji Mai lafiya da kuma jin daɗi, amma shiyafi kowa sanin kansa yana da RAUNI sosai. Wayarsa ƙirar Galaxy S20 ne tasoma ƙara alamar shigowar ƙira, ko kallon wayan baiyiba yasakai yafice daga cikin ɗakin, yayarda da abun da zuciyarsa tagama yanke masa, bazai bari awannan karon yasake faɗawa cikin irin halin daya faɗa abaya ba, ɗaukar ƙaddara yazame masa dole, don hakane ya yankewa kansa hukuncin nesantar duk wata ƴa mace, mahaifiyarsa ce kawai bazai iya nesanta kansa da’ita ba, amma sauran mata kam hakan yazame masa dole, kodan rufewar sirrinsa.

*** 

“Nagama yanke shawara Aure zamuyiwa Ziyada” Inna Ma’u tafaɗi haka ga Malam Garba bayan takai loman tuwo bakinta.

Malam Garba dake zaune akan ƴar tabarma ya ɗago kansa ya kalleta, cikin murya mai sanyi, yace… “Aure kuma Ma’u?”

“Ƙwarai kuwa Aure, ko so kake muzaba mata idanu tacigaba da yawon bin maza? to idan kuwa haka kakeso wallahi saina cire hanuna akan lamuranku!” Inna Ma’u tafaɗi haka cikin ɓacin rai.

“A’a bawai nace bazatayi aure bane Ma’u, duk hukuncin da kika yanke akan Ziyada aini bazance a’a ba, amma kinsan banda kuɗin aurenta a yanzu!” ya ƙare maganar cike da tsoron Inna Ma’un.

“Kai dai kawai kazubamin ido, domin nariga dana gama yanke shawara, gobe Tsoho ɗan dashe yace zai kawo kuɗin aurenta, kuma kadai san yanda tsoho ɗan dashe yake, idan yace zai auri yarinya, to baya buƙatar komai daga wajen iyayenta, hakanan zamu kaita mu wurgar “

Da sauri Malam Garba yasake ɗagowa ya kalli Inna Ma’u bakinsa na rawa yace 
“Tsoho ɗan dashe kuma? ɗansa zaki aurawa Ziyada’n?” 

Harara Inna Ma’u ta watsa masa cike da takaici tace “Atunaninka akwai wani matashin saurayin da zai jajiɓawa kansa wannan maƴyar ƴartaka? Ɗan dashe ne ke nemanta kuma nariga dana basa, ko kana da maganane?”

Kansa yagirgiza alamar “A’a” amma kuma har acikin zuciyarsa baiji daɗin hakan ba, kowa yasan Tsoho ɗan dashe ba mutumin kirki bane, tsohon banzane dabai riƙe mutumcin kansa ba, sannan kuma sam baisan darajan aure ba, ya auri mata sama da 15, daya auri mace tana samun ciki, zai koreta tare da takardan sakinta. To amma mai zaice, shi awajensa komai Inna Ma’u tayi dai dai ne…                      

Tunda yafita baidawo gidannasa ba har sai ƙarfe goma da rabi na dare, saida yagama daidaita tsayuwar motar tasa, kafun ya cire sit velt ɗin dake saƙale ajikinsa, aƙalla yakusan 7 minute acikin motar baifito ba, ahankali ya zuro ƙafafunsa waje cike da isa irin nasa, dama shi gwanine wajen jin kai da kuma miskilanci, baka gane gabansa baka gane bayansa. Sam yamanta da cewa wai yau aka ɗaura masa aure, saboda haka baiyi tunani ko tsammanin samun wata halitta acikin gidan nasa ba, kamar koda yaushe idan yashiga falon gidan direct bedroom ɗinsa yake wucewa, yauma hakance takasance. Wanka yasoma yi kafun yadawo yayiwa kansa mazauni akan gado, laptop ɗinsa yajawo yasoma latsawa, long jeans ne ajikinsa sai kuma wata farar riga wacce aka jere aninaye agabanta, saidai bai maƙala aninayen duka ba, hakan yasanya faffaɗan ƙirjinsa bayyana, kusan koda yaushe irin wannan shigar shine shigansa, duk da kasancewarsa farin mutum amma kuma yanason kalan fari, shiyasa yawancin kayansa suka kasance farare, duk da cewa idanu da nutsuwarsa suna ga abun dayakeyi acikin laptop ɗinsa, amma hakan baihanasa jiyo motsi a ɗakin dake kusa danasa ba, mamakine yakamasa don baiyi tunanin akwai wani agidan bayan shiba, sai alokacin auren da aka ɗaura nasa yau ya faɗo masa, jiyayi gabansa yafaɗi, yayinda bugun zuciyarsa ta tsananta, da sauri yakawar da ruɗun dayake ƙoƙarin shiga, tare da miƙewa tsaye, ƙirjinsa na bugawa haka yafice daga cikin ɗakin nasa. 

                      

7 minute yaɗauka yana tsaye yayinda yaɗaura hanunsa akan handle ɗin ƙofar, kokonto yake akan shigarsa cikin ɗakin, ganin baida wata mafita da ta wuce ya shiga yasanya yaturo ƙofar ahankali bakinsa ɗauke da sallama. 

                      

Daidai lokacin wata matashiyar budurwa da bazata wuce 21 years ba tafito daga bathroom jikinta duk ruwa da’alama wanka tayi, idanunsu ne yasauƙa acikin na juna, da sauri ya ɗauke kansa daga kallonta, itama akunyace tayi ƙasa da kanta, durƙusawa tayi har ƙasa cikin sanyin murya tace “Ina wuni” shiru yaɗanyi nawasu sakanni kamar bazai amsa mata ba. “Lafiya” yafaɗa ataƙaice haɗe da juyawa yafice daga cikin ɗakin, bayansa tabi da kallo tare da lumshe idanunta, wani irin sanyi taji na ratsata, ahankali tace. “Lallai samun cikakken Namiji mai kyau da aji kamar ka Sooraj babban sa’ane ga kowacce ƴa mace”

                      

Yana fita daga cikin ɗakinnata yaji kansa dake tsananin yi masa ciwo, yayi masa nauyi. haka yaji gaba ɗaya duniyar na juya masa, ƙirjinsa ne keta luguden duka, da ƙyar ya iya dafe kansa yakoma ɗakinsa, faɗawa kan gado yayi tare da rumtse idanunsa, shikaɗai yasan abunda yakeji, Ƙunci, Raɗaɗi, sune suka mamaye zuciyarsa, haƙoransa yasanya ya datse laɓɓansa, acikin zuciyarsa yaketa karanto addu’o’i’n samun nutsuwa,, ahankali kuwa yaji nutsuwa tasoma sauƙar masa, yayinda yaji ransa nayi masa sanyi, bai tsagaita dayin addu’anba har bacci ɓarawo ya ɗaukesa.

                      

Ɓangaren amarya kuwa kwalliya ta tsantsara tanajiran dawowan ango, saidai kuma ko motsinsa bata sakejiba, shiru shiru har 12 hakan yasa ta rakuɓe jikinta ajikin gado tasoma kuka, tun tana kukan har bacci itama ya saceta.

                      

*** Kamar koda yaushe kuma kamar kowacce rana, ƙiran sallan asuban fari akan kunnuwanta, duk da cewa bacci bai isheta ba amma kuma tashi yazame mata dole, kodan aikin gida dake kanta, tashi tayi daga kan ƴar tabarmar da take kwana akai ta zauna, hanunta takai kan wuyanta tashiga sosawa, daren jiya saurayene sukayi lugude ajikinta, suncijeta son ransu, dama ɗakinnata bawani wadataccen rufi yake dashi ba, gashi ko ƙofa babu, labulene kawai da aka sakaya ajikin ƙofar, ako wani dare sauro cizonta suke sosai, tun bata saba da cizon nasuba harta saba, kuma sosai cizon dasukeyi mata ke illatata, saboda kusan kullum fama take da zazzaɓi da kuma ciwon kai, amma dayake bata da wani gata haka take yawo cikin ciwo, saidai idan wahala tayi wahala tasamu ruwa akofi ta tofa Fatiha ƙafa uku tasha, da yardan Allah shike yaye mata ciwon kai.

                                      

                        

Ruwa ta samu tayi alwala haɗe da kabbara salla tana idarwa kuwa ta ɗauki tulu tawuce rafin da suke ebo ruwa. Sanyi ake busawa sosai amma haka take tafiya babu ko mayafin kirki ajikinta, tunda tafito daga gida harta isa rafi bata haɗu da kowa ba, kowa nagida yana bacci banda ita wahalalliya marar gata. Zama tayi agaban wawakeken kogin haɗe da ƙurawa ruwan dake gudana acikin kogin idanu, wasu hawayene masu ɗumi suka gangaro daga cikin idanunta. akullum kuma ako da yaushe, addu’a take Allah yakawo mata ɗauki, tana buƙatar farinciki acikin rayuwarta, Kwantar da kanta tayi akan guiwowinta, hawaye nacigaba da tsiyaya daga cikin idanunta. Tajima sosai tana zubda ƙwalla kafun daga bisani ta ɗauki ruwan da ta iba tabar wajen, lokacin har gari yasomayin haske. Gaba ɗaya ayyukan gidan ita tayisu tundaga kan shara da wanke wanke harzuwa ɗumamen tuwo, tana tsugune agaban murhu tana ta kiciniyar iza wutan murhu, Inna Ma’u tafito daga ɗaki hanunta ɗauke da tulin kayan wanki, watsawa Ziyada kayan tayi, ayatsine tace.

“Nanda mintuna 20 nakeson nagansu awanke”

Idan da sabo Ziyada ta saba da wannan wahalan, saboda haka bataji komaiba taɗauki kayan tasomawa wankewa.

*** 

Yafi mintuna 20 yana juya biron dake riƙe ahanunsa, gabansa kuwa wata ƴar ƙaramar farar takarda ne aje, so yake ya rubuta abun da shine mafita agaresa amma kuma yana fargaban abun da zaije yadawo, maganganun Mahaifiyarsa ne suka shiga yi masa yawon acikin kunnuwansa, inda take cewa….. “Wallahi kaji na rantse ma awannan karon kasaki matar da muka aurama, ranka saiyayi mummunan ɓaci, zakuma kaga fushinmu irin wanda baka taɓa gani ba!” 
Tun ɗazu kalamannata keyawo acikin kansa, lumshe idanunsa da suka soma sauya kala daga farare zuwa jajaye yayi, tare da sanya haƙoransa ya datse lips ɗinsa, tsikar jikinsa ne yasoma tashi yayinda gashin jikinsa suka soma mimmiƙewa tsaye, jiyayi kansa yasoma juyawa, yayinda tunanin wasu abubuwa ke son hautsina masa ƙwaƙwlwa, da sauri yaɗaura alƙalami akan farar yakardan yasoma rubutu, bawani rubutu mai tsayi yayi ajikin takardan ba, ya nannaɗeta tare da sanya ta acikin wani envelop. 
Tashi yayi daga zaunen dayake yashige cikin bathroom. Wanka yayi kana yafito sanye da rigan wanka ajikinsa. 

Kayan training ɗinsa da sukeyi masa matuƙar kyau yasanya, tare da ɗaukan wata ƴar doguwar jaka, ɗaukan takardan dayayi rubutu acikinta ɗazu yayi haɗe da sakai yafice daga cikin ɗakin.

Yana murɗa ƙofar ɗakin ta buɗe hakan yasa ya kutsa kansa ciki. 

Tanaganinsa tatashi zaune daga kwancen da take, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke idanunsa akanta, a kuma wannan kallon dayayi matane ya gane cewa taci kuka ta ƙoshi.

Cikin takunsa na isa yaƙaraso har wajen da take zaune. 

Miƙa mata takardan hanunnasa yayi batare dayace da ita komai ba. 
Karɓan takardan tayi tana mai kafesa da idanunta, juyawa yayi yanufi hanyar fita daga ɗakin, har yakai bakin ƙofa saikuma ya tsaya cak, murya ashaƙe yace.

“Kada kiga laifina, haka tawa ƙaddaran take” 
yana gama faɗin haka yafice daga ɗakin, ko waiwayowa gareta baiyiba.

Kallon mamaki tabisa dashi 
“Kenan miye maganganunsa suke nufi?” tatambayi kanta tambayar da babu amsa. Buɗe envelop ɗin daya bata tayi tare da zaro ƴar ƙaramar takardan dake ciki.

Wani irin bugawa zuciyarta tayi yayinda gaba ɗaya jikinta yaɗauki rawa, sake waro idanunta tayi tana karanta abun dake rubuce ajikin takardan. Kukane yaƙwace mata, lokaci guda ta shiga Jijjiga kanta, azabure tatashi daga kan gadon tafice daga cikin ɗakin.

Tana ƙarasawa compound ɗin gidan shikuma motarsa na ƙarisa ficewa daga cikin gidan. Wani irin ƙara tasaka haɗe da zubewa aƙasa tashiga rera kuka, ganin kukan bazai mata maganin komaiba yasa ta koma cikin gida, mayafinta kawai taɗauka saikuma envelop ɗin dake riƙe ahanunta.

Tazo fita daga gidan maigadi yatsareta da tambayar lafiya take kuka. Ko kallonsa batayiba tafice tana ƙara volume ɗin kukanta..

Shikuwa Tanimu mai gadi komawa yayi kan benci ya zauna, aransa kuwa yana tsananin mamakin hali irin na SOORAJ, ko tantama bayayi abun da yafaru da sauran matanne itama yafaru da ita, shiyasa tatafi tana kuka… 

Yana tsaye agaban madubi, wani ɗan madaidaicin towel ne riƙe ahanunsa, yana goge gumin dake tsastsafowa ta goshinsa, kasancewar yanzu gama training ɗinsa. 

Wayarsace tasoma ƙara alaman shigowan ƙira, saida yaji gabansa yafaɗi alokacin dayaga sunan dake yawo akan screen ɗin wayartasa, maganganun Ummu ne suka shiga dawowa kunnuwansa filla filla. Jiki a sanyaye ya ɗauki wayar tasa ya kara akan kunnensa.

Ko sallaman da Sooraj ɗin keyi masa bai amsa ba, cike da ɓacin rai yasoma cewa….. ” Yau katabbatarmin da cewa kacika ishashshe Sooraj, yau kuma kaƙara tabbatar min da cewa kai mutumin banza ne, wanda baida tunani, ashe har abada bazaka daina kunyatamu ba? shikenan kaci gaba duniyace, ita kuma yarinyar da kayiwa saki har uku kasani wallahi Allah bazai barkaba, sai ya saka mata, Shashasha kawai!!!” 

Jikin Sooraj ne yaɗauki rawa cikin inda inda yace “Dan Allah Abba ka sau…..” 

“Bazan taɓa sauraranka ba Sooraj, wallahi ko ganinka banasonyi, gargaɗi na ƙarshe kada kasake ka zomin gida, tunda haka kazaɓa kaci gaba, mukam munzare hannuwan mu daga cikin al’amuranka!!!”

Abba yafaɗa murya a kausashe.

Baibawa Sooraj damar sake cewa komaiba yakatse wayar. 

Zamewa Sooraj yayi daga tsayen da yake yazauna daɓas, hannayensa duka yasanya ya tallafi kansa, idanunsa ne suka kaɗa sukai jajur, take jijiyoyin dake kwance akan goshinsa suka fito raɗa raɗa, saurin rumtse idanunsa yayi, domin idan yace zai barsu a buɗe, to tabbas ruwan hawayene zasu fito daga cikinsu…

*ZIYADA*

Tun safe take ta faman jibgan aiki kamar wata jaka, har zuwa yanzu kuwa bata huta ba. Shigowarta gidan kenan tasamu Inna’ Ma’u tsaye sai rangaɗa guɗa take, hanunta riƙe da kuɗaɗe masu yawa, gefenta kuwa Malam Garba ne zaune yayi jigum, shidai baida tacewa, komai Inna Ma’u ne keyi, tamaidashi kamar wani yaronta, shikuwa biyayya yakeyi mata kamar raƙumi da akala duk hanyar da ta jasa nan yake bi. 

Harara Inna Ma’u ta aikawa Ziyada da ta tsaya tana kallonta.

“Mayyar banza miye kika tsaya kina kallona?” 

Da sauri Ziyada tayi ƙasa da kanta, sumu sumu ta wuce cikin ɗakinta, hakanan taji gabanta na faɗuwa, jitake ajikinta kamar wani babban al’amari na kusantota, wanda kuma da dukkan alama ba abubane mai daɗi. 
Tunda ya zauna ya tallafe kansa da duka hannayensa biyu  baisake wani ƙwaƙƙwaran motsiba, numfashi kawai yake fitarwa a hankali..

                      

Mas’oud dake tsaye akansa tuntuni yasanya hanu ya dafa kafaɗansa.

                      

Jin sauƙar hanu akan kafaɗansa ya tabbatar masa da cewa Mas’oud ne, ɗago kansa yayi ya kalli  Mas’oud da rinannun idonsa.

                      

Yanayin yanda Mas’oud yaga cikin idanun SOORAJ saida ya tsorita,  saboda bai taɓa ganin abokinnasa acikin matsananciyar damuwa irin wannan ba.  Zagayowa yayi ya zauna akusa da SOORAJ ɗin. Cike da kulawa yace.  
 “Basai na tambayeka ba RAJ nasan kana cikin damuwa, amma kuma bantaɓa ganinka acikin irin wannan yanayin ba, ina fata dai ba halinnaka kasake gwadawa ba?”

                      

Sauƙe hannayensa dake kansa  yayi ƙasa, haɗe da furzar da wani irin iska mai zafi daga bakinsa, kallon Mas’oud ɗin yayi kamar zaice dashi wani abu saikuma ya fasa, kawai ya kawar da kansa gefe.

                      

Murmushi Mas’oud yayi  tare da girgiza kansa, tun suna ƙanana suke tare shida SOORAJ saboda haka kusan gaba ɗaya halayyar SOORAJ ɗin Mas’oud yasani,  idan SOORAJ bayason yin magana, akwai wani irin kallo dayakeyi, dazaran Mas’oud yaga SOORAJ yayi irin wannan kallon, to yasan mene kallon ke nufi.

                      

“Bazan tilastaka kacemin wani abuba RAJ amma kuma kada kamanta cewa nidakai tamkar ƴan uwan juna ne, har sai yaushene zaka tsaya kana ɓoye damuwarka? yanada kyau ko bazaka faɗa duniya tasani ba, muda muke tare dakai, muncancanci musan damuwarka, amma maiyasa ako da yaushe kake ware kanka? idan har bazaka iya faɗamin damuwarka ba RAJ banda wani amfani awajenka, haka tarayyata dakaima bata da wani amfani!”  Mas’oud yafaɗi haka cikin ƙunan zuciya, saboda shi kansa al’amarin SOORAJ yasoma basa haushi, koda yaushe SOORAJ acikin damuwa yake, abune mawuyaci kaga dariyan SOORAJ, gaba ɗaya yasamo wani banzan hali ya arawa kansa, baida aiki sai zaman ƙunci.

                      

Kallon takaici Mas’oud yashiga bin SOORAJ ɗindashi, ganin ko alamar ɗaukar maganarsa baiyi ba, azuciye yatashi zaibar wajen.  Riƙo hanunsa SOORAJ yayi, cikin wata irin murya mai sanyi yace.  

                      

“Bazan iyaba Mas’oud, niba namiji bane dazai iya riƙe mace, itama Nasaketa!”

                      

Idanu Mas’oud yazaro waje cike da mamakin jin kalaman dake fita abakin SOORAJ ɗin.

                      

“Kasaketa fa kace?” Mas’oud yatambaya cike da mamaki.

                      

Kai kawai SOORAJ ya kaɗa masa alamar “Eh”

                      

Wani irin tuƙuƙin baƙinciki da takaicin SOORAJ ɗinne suka turnuƙe Mas’oud, yanzu kam ya yarda cewa  akwai matsala a ƙwaƙwalwar SOORAJ domin maihankali bazai aikata irin abun da SOORAJ ke aikatawa ba.

                      

“Anya kuwa kana cikin hankalinka RAJ? kodai asiri akayi maka ne? shin kakuwa san abunda kake aikatawa? kasaketafa itama kace? mata huɗu fa kenan yanzu ana aurama kana sakinsu, daga ankai maka mace yau washe gari kake sakota,  wai kodai aljanune dakai ??”  Mas’oud yatambayesa cike da tsananin mamaki, saboda duk wani maihankali dole ya tsoraci lamarin SOORAJ.

                      

Kallon Mas’oud ɗin SOORAJ yayi da jajayen idanunsa, araunane yace   “Inada hankali Mas’oud kamar yanda kaima kake dashi, abu ɗaya kawai nasani shine wannan itace ƘADDARATA!”  yana kaiwa ƙarshen zancennasa ya miƙe tsaye tare da soma tattara kayan training ɗinsa,  Mas’oud na kallonsa ya tattara komai nasa yafice daga cikin ɗakin  training ɗin. Mas’oud kam kasa tashi yayi yazauna daɓas, sosai al’ajabi da kuma mamakin abokinnasa RAJ ke ƙara kamasa, shikam yanzu yayarda cewa aljana ce tashafi Abokinnasa.

                                      

                        

SOORAJ kuwa yana fita daga wajen training ɗin direct  motarsa yanufa,   yana shiga yayi mata key tare da cillata kan titi.. 


Yana komawa gidansa yayi wanka, dakansa yashiga  cikin makeken kitchine ɗinsa, wanda yazuba masa kayan amfani, babu abun da babu na amfani acikin kitchine ɗin.     Ruwan tea yadafa kana ya juye a flask, kan dinning area yadawo yazauna tare da haɗa tea, ahankali yake sipping tea ɗin yayinda ɗayan hanunsa ke riƙe da wayarsa yana latsawa.  Safiya rana dare SOORAJ bayida wani abinci sama da ruwan tea,  arana sai yasha tea sama da sau uku,  abune mawuyaci yazauna yaci abinci kamar yanda kowa yakeci.  Yana shanye tea ɗin ya miƙe tsaye,  mug ɗin da ya haɗa tea ɗin aciki ya ɗauka ya wuce kitchine, wankewa yayi yamaida shi mazauninsa.   


Falo yadawo yazauna akan ɗaya daga cikin lallausan kujerun  falon,  remote ɗin receiver yaɗauka, ya sanja tasha.  Knocking ƙofar falon akasomayi,  cikin gajiyawa yace “Yes come in” 


Piter ne yashigo hanunsa riƙe da wasu zabga zabgan tsintsiyaye dakuma moper, ɗurƙusawa yayi cike da ladabi yace “Good Morning Sir”


“Morning” kawai yace tare da tashi yatattare wayoyinsa ya nufi bedroom,  don bawa piter daman yin aikinsa da kyau.  


Yana shiga ɗaki yafaɗa saman gado haɗe da jawo pillow yaɗaura kansa akai. Shiru yayi yana mai lumshe idanunsa, tun ɗazu kalaman Abbansa ketayi masa yawo acikin kunnuwansa, tabbas yasan dolene iyayensa suyi fushi dashi, amma shima bayin kansa bane, ƘADDARA ce baikuma isa kauce mata ba, amma yanda iyayen nasa suka ɗauki zafi sosai shine abun dayasanya yaji gaba ɗaƴa duniyar tayi masa ɗumi,   shi kaɗai yasan kansa, shikaɗai yasan wanene shi, shine wanda yasan matsalarsa,  taya ayanda yake zai iya zama da mace? sai yaushene  iyayensa zasu fahimci matsalarsa? sama da shekaru 7 kenan yana fama da matsala guda ɗaya, shiɗin namijine, baida wani wanda zaije yafaɗawa damuwarsa,  dole shine zai nemi maganin matsalarsa, haryau  kuma akan neman maganin matsalannasa  yake amma  baidace ba, shikansa bazai iya fitowa fili yafaɗi abun dake damunsa ba,   yabarwa kansa cewa matsalansa itace sirrinsa,   zama da mace kamar mafarin tonuwar asirin sa ne, yajima yana tunanin cewa shi ba’ayisa don yazauna kuma yasan wata ƴa mace ba, amma dazaran yafara wannan tunanin yake saurin furta astagfirullah domin yasan saɓone yakeyi, to amma yazaiyi shima bayida zaɓi ne, akullum akuma koda yaushe da Allah kawai ya dogara….  


***   Tana zaune aɗaki tayi jigum abubuwane suka haɗe mata, aƴan kwanakinnan sosai take mamakin sauyan da  Inna Ma’u tayi, tarage sata yawan aikace aikace, sannan kuma koda aikanta ne yanzu andainayi bakamar daba da kullum ƙafarta na waje tana yawon zuwa aika,  yanzuma tana zaune ne aɗakinta tana sauraran hayaniyar ƙawayen Inna Ma’u dake tashi a tsakar gidan,  itadai batasan meke gudana acikin gidannasu ba amma tabbas tasan cewa akwai wani abu da za’ayi acikin gidan.   Zulai ƙawar Inna Ma’u ce ta yaye  yagalgalellen labulen dake ƙofar ɗakin nata. Ayatsine ta watsowa Ziyada dake zaune harara,   “Uwar munafurci saiki fito ae” cewar Zulai, tana gama faɗan haka kuwa tasake labulen tayi tafiyarta.


Jiki asaɓule Ziyada tafito daga cikin ɗakin nata,   Gani tayi su Inna Ma’u sun baje akan tabarma yayinda suka kwaɓa lalle awani babban fanteka.


“Zo maza ki zauna” ɗaya daga cikin ƙawayen Inna Ma’u tace da Ziyada.


Cikin sanyin daya zame mata sabo taƙaraso ta durƙusa agabansu, ƙirjinta sai bugawa da sauri yake saboda tsabar tsoronsu da take.


Zaunar da ita sukayi agabansu, yayinda suka sanya ta kwaye musu cinyoyinta,  da ƙarfin gaske suka shiga durza mata ƙwaɓeɓɓen lallen ajikinta, hatta fuskarta saida suka mulke mata shi da lalle,   itadai ganin abun take awani baƙon yanayi, saboda tasan agarin nasu  idan za’awa mace aurene kawai ake yi mata haka,  suna gama shafa mata lallen sukace taje ta wanke,  wani irin daɗine yaziyarci zuciyarta, domin albarkacin wannan lallen da suka shafa mata yasa zatayi wanka, bata mantawa rabonta da wanka yau sati guda kenan, dokace mai zaman kanta Inna Ma’u takafa mata akan cewa duk randa tayi wanka, bazata sake yi ba sai bayan wani satin, ruwa takandama abaho tayi bayinsu, alokacin da tacire kayanta tasoma watsawa jikinta ruwa, saida ta sauƙe wasu lafiyayyun ajiyar zuciya harsau uku, saboda wani irin sanyin daɗi daya ratsata, dama ita tuncan haka nan Allah yayita, tanada tsananin sonyin wanka, amma kuma bata samu tanayi saboda uƙubar Inna Ma’u.   


                

                        

Inna Ma’u kuwa masifa ta rufe ƙawayennata dashi wai akan mai zasu kwaɓa lalle su shafawa Ziyada.  Zulai ce tagyara zama haɗe da turo ɗaurin ɗankwalinta gaba.    “Wallahi yanzu na tabbatar baki da wayo Ma’u, kinga wannan lallen damuka shafa mata, shizai sanya jikinta yaƙara kyau, hasken fatarta yasake fitowa, kinsan yarinyar shegiya ɗanbanzan kyaune da ita, to kinga yanzu zata ƙara kyau akan nada, idan Tsoho Ɗan Dashe kuwa yaganta, saiya ƙara susucewa akanta, kinga ke kuwa kinsamu hanyar da zaki amshe masa ƴan kuɗaɗe kice kuɗin gyaran jiki, ai abirni haka akeyi kinsan nifa nayi zaman birni”

Shewa Inna Ma’u tasanya haɗe da bawa Zulai hanu suka tafa, cike dajin daɗi tace “Wallahi shiyasa nake mugun sonki Zulai, kinsan kan duniya,  aikuwa ayau yau saina karɓi wani abu daga wajensa”     sake tafawa Inna Ma’u da Zulai sukayi daidai lokacin Ziyada tafito daga wanka, zanine ɗaure aƙirjinta kanta gaba ɗaya yajiƙe yake da ruwa, tana shigewa ɗakinta, Zulai tadawo da kallonta ga Inna Ma’u cike da mamaki tace “Wai Ma’u dama haka wannan yarinyar keda diri da kyau? nikuwa anya basu haɗa iri da larabawa ba?”

Taɓe baki Inna Ma’u tayi, domin ita aduniyarta babu abun datafi tsana kamar taji anyabi Ziyada,  “To wama yasanine tsinannu, ai tunda nasamu nagama da uwarta itama yarinyar bawuya zata bani ba, wannan shegen idanun nasu masu kama dana aljanu yana ɗaya daga cikin abun dayasa na mugun tsanarsu, gashi komai na halittar uwarta ta kwashe!” Inna Ma’u tafaɗi haka cike da baƙin ciki. 

“Aikuwa Ma’u kinyi farar dabara da kika haɗa auren ta da Ɗan Dashe, kinga zata ƙare rayuwarta cikin ƙasƙanci, kinsansa baya riƙe aure, duk da yagama tsofewa, amma baijirayi kansa ba,  dakin tsaya kuwa kina nan zakiga wani sarki ko senata sunzo neman aurenta”  cewar wata daga cikin ƙawayen Inna Ma’un, wato Lantana.

“Cab iye bakinki Lantana, ina darai kam ƙaryane wani mai arziki ya raɓi Ziyada, sam hakan bamai yiwuwa bane, koda kuwa zanyi yawone tsirara na gwammace nayi, dana bar jinin Maryama ta auri wani mai kuɗi, nama kashe maciji bansare kansaba kenan” Faɗar Inna Ma’u.  Dariya suka sanya sudukansu, yayinda ƙawayennata sukacigaba da fonfata….

Ziyada kuwa tsabar taji daɗin jikinta da tayi wanka tana kwanciya kawai sai bacci ɓarawo ya saceta…

Washe Gari. 

*** Tun tashinta yau takejin faɗuwar gaba, babban abun daya ɗaure kanta shine, ƴan uwan mahaifinta da tagani sun cika gidan, da’alama dai kamar biki za’ayi agidannasu bata kuma san bikin waye za’ayi  ba.   Tazo wucewa zata shiga banɗaki  wata ƴar addar babanta  ke cewa “Amarya Amarya bakya laifi Amarya agidan Tsohon najadu” 

Jitayi gabanta yafaɗi cike da mamaki tajuyo tana kallon Hajara wacce tafaɗi maganar, bakinta na rawa tace.   “Yaya Hajara wacece amaryan?”

Harara Hajara ta watsa mata domin dama tun can su bawani sonta suke ba.   “Wace amarya kuwa inbanda ke, ko baki da labarin cewa gobe za’a ɗaura miki aure da tsohon najadu?” Dariya Hajara tasanya haɗe dacigaba dacewa “Abun yayifa yarinya ta auri wanda yagirmi ubanta” sai takuma sake bushewa da dariya.

Jikin Ziyada ne yasoma rawa, lokaci guda taji cikinta yayi wani irin murɗawa atsorace ta ƙaraso gaban Hajara tazube aƙasa, murya na rawa tace  “Dan Allah Adda Hajara kifaɗamin gaskiya, auren waye za’ayi?”

Kallon kinma rainamin wayo Hajara tashiga yiwa Ziyada  ahasale tace..   “Bansaniba munafuka, waye baisan cewa kema son auren kikeba? dama ai kowa yasancewa ke tsohuwar hanuce, wayasanima koshima Tsohon najadun ya ɗana”   

Kuka Ziyada ta fashe dashi da gudu ta tashi tanufi ɗakin Inna Ma’u, tana shiga ta zube agaban Inna Ma’u dake tsaye, cikin kuka tace. 
 “Dan Allah Inna Ma’u kimin rai, kifaɗamin cewa maganar da Adda Hajara kefaɗi bagaskiya bane, wai dagaske aurena za’ayi, kuma ɗan dashe zan aura?” 

Wata uwar tsuka Inna Ma’u taja haɗe da ɗauko ashar ta bankawa Ziyada cike da takaici tace 

“To idan bakiyi aure ba kwaɗaki zamuyi mucinye?   inbanda ƙaddarama me Ɗan Dashe zaiyi dake, shima dai dayake tsohon maye ne shiyasa, amma bacin haka banga maiyagani awannan busheshshen jikinnaki ba, da Allah nitashi kibani waje, kuma aurenki da ɗan dashe babu fashi, gobe iwar haka kinzama matarsa”   

Kuka Ziyada tashiga rerawa hadda majina tana roƙon Inna Ma’u, amma Ina Inna Ma’u haka ta murje idanunta.

Komawa cikin ɗakinta tayi hankalinta amatuƙar tashe, zama tayi daɓas aƙasa haɗe da ɗauko wani mayafin mamanta ta rungumeshi ƙam acikin ƙirjinta, kuka take tamkar zararriya… 

“Wayyo Mamana kinga rashinki abundaya jawomin, Ya Allah kataimakeni kakawomin ɗauki!” Ziyada tafaɗi haka cikin matsanancin kuka.  Tsabar kukan da Ziyada tayi harsaida muryarta ta dashe.     Tana zaune aɗaki taji muryan Babanta, a tsakar gidan nasu, da sauri ta ɗaga labulen ɗakin tana leƙensa, sosai takejin tsananin tausayin mahaifinnata, duk da cewa tana da ƙananun shekaru amma hakan baisa takasa fahimtan cewa wasu abubuwan dayake aikatawa ba acikin hayyacinsa yakeyinsu ba,    ganin yafice daga cikin gidanne, yasa tafaki idon mutane tarufa masa baya, zaune ta iskeshi akan ɗan dakalin dake ƙofar gidannasu.  Tsugunnawa tayi agabansa  Cikin da shashshiyar muryarta da ta ƙoshi da kuka tace

“Baba!”  

ɗagowa yayi ya kalleta, batare da ya amsa mata ba.

“Dan Allah Baba kataimakeni, wallahi banason ɗan dashe!”  tafaɗi haka hawaye suna mai kwaranya daga cikin idanunta.

Shiru Malam Garba yayi cike da tausayin ƴartasa, lokaci guda kuwa ya zabura kamar anjona masa shocking.  

“Uban maikikeyi anan?” yatambayeta atsawace.  

Jikintane yasoma rawa, yayinda kuka yasakecin ƙarfinta,  cikin kukan tace.  “Dan Allah Baba kaceci rayuwata, katunafa ni amana ce Allah yabaka, dan Allah Karka bari acutar da rayuwata!!”

Wata uwar tsawa yakuma doka mata, haɗe da rufe idanunsa yakorata gida.

Haka takoma gida tana kuka maicin rai, lallai tasake tabbatarwa da kanta cewa ita cikakkiyar marar gata ce, zama tayi akan  tabarmarta haɗe da sanya hanu ta share hawayenta, lokaci guda taji zuciyarta tayi wani irin bushewa, yayinda wani tunani yaɗarsu acikin ranta…
Wanene SOORAJ? 

                      

Alhaji Mansur Mai Nasara shi ne yakasance uba ga SOORAJ, Alhaji Mansur Mai Nasara wani hamshaƙin mai arziki ne dake zaune acikin garin Kaduna, Alhaji Mansur  tsohon commissioner’n  Ilimi ne dake zaune a cikin garin Kaduna, cikakken ɗan boko ne shi, wanda yatara dukiya, sannan mutum ne  dayake jure gwagwar mayar rayuwa, wannan yasa mutane suka masa laƙabi da suna MAI NASARA, saboda duk wani  abu daya sanya agaba saiyayi nasara akai.    Hajiya Sulaimiya  itace matarsa kuma mahaifiya ga SOORAJ, Hajiya Sulaimiya dai irin wayayyun matan nan ne, don asalinta yar ƙasar  Sudan 
ce,  tana da kyau sosai, tsananin kyawunta yana ɗaya daga cikin abun daya sanya Alhaji Mansur, narka maƙudan kuɗaɗe wajen  ganin ya aurota,   zama sukeyi cike da so da kuma ƙaunar juna, koda yaushe cikin farinciki suke, shekaransu uku da aure Allah ya azurtasu da samun ƙaruwan yaro namiji,  tun daga randa aka haifi SOORAJ Alhaji Mansur yaƙara ganin buɗi acikin arzikinsa, soyayyar duniya suka ɗauka suka ɗaura ta akan yaron nasu,  komai Na SOORAJ irin na Mahaifiyarsa ne domin kyawunta ya ɗauko.  sosai SOORAJ ke zuba tashen kyau da burgewa tun yana ƙarami,  saidai yataso da wani irin hali, miskiline na ƙarshe, sannan sam baida yawan magana, komai nasa atsare yakeyinsa, tun yanada shekara 12  mahaifinsa ya turasa England acan yayi gaba ɗaya karatunsa, tundaga kan secondary school har zuwa Masters ɗinsa, P.H.D ɗinsa ne kawai yayi aƙasar America. Sosai SOORAJ yake da ƙwazo akan dukkan komai, babu ruwansa da kowa, rayuwarsa kawai yake,   bashida wani aboki aduniya sama da Mas’oud, sosai abotarsu tayi ƙarfi da Mas’oud, kasancewar sun fara abotanne tun suna ƙanana, gaba ɗaya sirrin Mas’oud SOORAJ yasani, haka shima Mas’oud ɗin yasan wasu sirrukan SOORAJ, saidai akwai wani sirri da SOORAJ ɗin yaɓoyewa kowa, shikaɗai yasan matsalarsa.  Tun daga kan SOORAJ Alhaji Mansur baisake haihuwa ba,  amma hakan baisa sun tashi  hankalinsu ba, kasancewarsu wayayyun ƴan boko, dama ba wani son tara ƴaƴa suke ba,   ayanzu dai SOORAJ yana da shekara 30 aduniya, cikekken matashine mai tsananin ji da kansa, rayuwarsa yakeyi maicike da burgewa baruwansa da kowa,   abune mawuyaci kaga dariyansa,   duk yanda Ƴan Mata keson samun daman kai kansu garesa, hakan baya yiwuwa, domin SOORAJ wani irin mutum ne, da akomai nasa baya sanya mata aciki, duk wata mu’amalarsa baya sanya mace aciki,  mace duk kyau da haɗuwarta sam bata gabansa, batama burgesa, duk wani irin karairaya da mace mai lafiya zata zo tayi agabansa bazata taɓa burgesaba, duk tsananin kyawun mace, SOORAJ bata burgesa, shi yariga daya sanya aransa cewa  mace bata cikin tsarinsa.  Ayanzu yana akine a babban bankin Nigeria dake cikin garin Abuja  wato Central Bank Of Nigeria (CBN)  yanzuma hutu ya ɗauka  shiyasa ya zo Kaduna wajen iyaye da danginsa.  A rayuwarsa yana tsananin son iyayensa, sai gashi kuma daga zuwansa sun laƙaba masa auren dole. Wannan shine taƙaitaccen tarihin SOORAJ MAI NASARA.

                      

Kamar koda yaushe idan yana acikin damuwa  yakan fita yazaga gari, wani lokaci har ƙauyukan dake kusa dasu yake zuwa, sosai yakejin daɗi idan yaziyarci ƙauyuka musamman irin ƙauyukan da fulani ke rayuwa acikinsu,  yauma hakance  takasance dashi,   hakanan yaji yanason fita daga cikin gari, bayaso yakoma Abuja baije yaɗan zaga gari ba…  

                      

Tsab yashirya kansa cikin long pencil jeans black colour,and Black t-shirt, agaban t-shirt ɗinnasa anrubuta ( THE MAN) da farin fenti.   white denim jacket fara irinta maza  yaɗaura akan rigar dake jikinsa, sosai kayan suka amshi jikinsa kasancewarsa mai farin fata,  wasu fararen takalma combat wanda aƙalla kuɗinsu zasu haura sama da 30k yasanya aƙafarsa, hmmm SOORAJ yanason gayu sosai, hakan yasa koda yaushe cikin ɗaukar hankali yake.   Da turarukansa masu tsada ya feshe jikinsa,  take ko ina naɗakinnasa ya gauraye da ƙamshi.  Wayoyinsa haɗe da key ɗin Range Rover ɗinsa ya ɗauka, kana yafice daga cikin ɗakin.

                                      

                        

Yanashiga cikin motarsa ya kunnata, maigadi ne ya wangale masa gate,   yana cilla motar tasa kan titi yasoma murza steering motar ahankali cike da salo.. 


*ZIYADA*

Gaba ɗaya ko ina acikin garin yaɗauki shiru, babu wani abu dake kai kawo, kowa yana gida akillace, adai dai irin wannan lokacin mafi yawancin mutane suna kwance ne aɗaki suna bacci,     duhun dare ne sosai, babu wani abu dake motsi, sai ɗan abun da baza’a rasa ba,  kamar yanda ko ina yaɗauki shiru haka gidannasu ma yake shiru, babu motsin kowa, gaba ɗaya jama’ar gidan suna bacci, amma banda ita, idanunta sun ƙeƙashe sun bushe, babu wani alamun bacci acikinsu, tun tana kuka da iyaka ƙarfinta, harta koma sauƙe ajiyar zuciya akai akai, babu wani abu dake ɗaga mata hankali, kamar idan tatuna cewa gobe za’a ɗaura mata aure da Tsoho Ɗan Dashe, tsohon dakowa yasan cewa ba mutumin kirki bane,    shiru tayi tana mai sake nazartan abun da zuciyarta ke raya ma ta.   Tabbas awani ɓangaren tunanin dake kwance cikin  zuciyarta awajenta shine daidai, amma kuma tawani wajen tanaga kamar hakan ba daidai bane, duk duniya bata da kowa sai mahaifinta da kuma danginsa da suka ɗauki karan tsana suka ɗaura mata.     Tana zaune awajen taji ansoma ƙiraye ƙirayen sallan asuba, jitayi gabanta ya tsananta bugawa,  lokaci ɗaya taji zuciyarta na ingizata,  ɗan dangwalin kayanta taɗauka, haɗe da yaye labulen ɗakinnata tasako kanta kaɗan tana leƙa tsakar gidannasu, ganin bakowa yasa tafito saɗaf saɗaf ta nufi hanyar fita daga gidan, saida takai bakin ƙofa kafun ta tsaya tare da juyowa tana mai kallon ƙofar ɗakin Babanta, wata irin karyewa zuciyarta tayi, take sai ga hawaye nasauƙa akan kumatunta, sosai takeson Babanta, tasan duk wani abu dayakeyi mata balaifinsa bane, amma bata da yanda zatayi, dole ko duniya ne ma tashiga, dole tanesanta kanta ga faɗawa halakar auren tsoho ɗan dashe.  Juyawa tayi aɗari tabar cikin gidannasu, gudu takeyi sosai harta yi nisa da gidajen dake cikin ƙauyen tasoma shiga jejin dazai sadata da bakin hanya, komai tanayinshine acikin ƙarfin hali, amma har aƙasan zuciyarta tsorone shimfuɗe..


Bai kwana acikin garin Kaduna ba, kasancewar dare yayi masa, sam shi ba mutum bane mai son tafiyar dare, hakan yasa ya gangara gefen hanya, anan ya kwana cikin motarsa.   Asuban fari yakamo hanyar dawowa cikin gari, saboda yau ɗin yakeso ya koma Abuja.   Gudu sosai yaketa shararawa akan titi kasancewar babu wasu yalwan motoci dake tafiya akan titin. 


Ba ƙaramin tafiya bane daga cikin ƙauyen nasu zuwa bakin titi saboda haka sosai tagalabaita,  ganin takusa  kawo bakin titi ne yasa ta rage sauri tasoma tafiya ahankali, dama ƙarfinta yasoma ƙarewa.   Jitayi kamar anabin bayanta, da sauri tawaiwaya aikuwa wasu maza tagani su biyu abayanta,  waro manya manyan idanunta tayi cike da tsoro tana kallonsu, dariya suka bushe dashi,  ɗayanne ya sanya harshe yalashi laɓɓansa, cikin yanayi irin na ƴan iska yace.   “Baaba yau fa munyi babban samuwa, ɗanyen kaya ce” 

Dariya wanda aka ƙira da suna Baaba yayi, ya karkace tsayuwarsa tare da kai hanunsa kan belt ɗin wandonsa.    “Ay gaye yau zamu more”  yafaɗi haka yana me zare belt ɗin wandonsa.  
Ganin haka yasa Ziyada shiga cikin wani  irin matsanancin firgici, aruɗe tasoma ja  baya,  da ƙarfin gaske ɗayan ya fusgota, ihu tashiga yi tare da yunƙurin ƙwace kanta amma riƙon da yayi mata bana wasa bane,  ɗan kwalin dake kanta ya fusge ya yi cilli dashi gefe, ganin haka yasa taƙara fasa ihu haɗe da turjewa, amma takasa ƙwacewa, hanunsa yasanya da iyaka ƙarfinsa ya ja rigan koɗaɗɗiyar atamfan dake jikinta, ɓesss kakeji rigar ta yage, dama tuni kayan sunyi laushi.  Ganin saman ƙirjinta ya bayyana afili, yasa samarin suka bushe da dariya, kowanne acikinsu jikinsa yaɗauki mazari, burinsu kawai shine suga sun farketa.    Wani irin ihu Ziyada tasa tare da kafa bakinta akan hanun wanda ke riƙe da ita ta sakarmasa cizo, awahalce yasaketa yana fidda wani irin ƙaran azaba, itakuwa aguje ta lula cikin jejin.   Ganin haka yasa suka rufa mata baya, gudu take sosai  suna biye da ita, sam batasan cewa takawo bakin titi ba,  aguje ta zo zata bi takan titin tasake faɗawa wani jejin… Kafun ƙiftawan ido wata mota da tataho aguje tayi sama da ita, tim haka ta faɗo ƙasa.   Amatuƙar razane yafito daga cikin motar yayo kanta,  waro kyawawan idanunsa waje yayi tare dasa hanu ya toshe bakinsa, lokaci guda jikinsa yaɗauki rawa ganin irin ɓarnar da yayi,  kwance take cikin jini ba ako iya gane kamanninta,  wani irin rawa jikinsa keyi kamar anjona masa shocking, hannayensa duka yasanya yaɗagota, buɗe motar yayi yasata agidan baya, yanashiga wajen driver ko gama rufe murfin motar baiyiba, ya figi motar da gudun gaske.   Samarinnan naganin abun daya faru sukayi saɗaf saɗaf suka bar wajen, cike da haushin rashin samun nasara da basuyi ba.


Gudun da yakeyi har ya wuce hankali, tamkar zaitashi sama, gaba ɗaya ya ruɗe, ganin yanda jini ke fita ajikinta.  Alokacin daya shigo cikin garin Kaduna, gani yake kamar motar tasa bata gudu, hakanne yasanya yaƙara gudun motar mintuna kaɗan saigashi a cikin asibiti,   amatuƙar ruɗe yaje yaƙira likitoti suka zo suka ɗauketa aka wuce da ita emergency room.   Ganin yanda kanta ke zubda jini yasa likitoti suka duƙufa akanta wajen bata taimakon gaggawa.

Shikuwa SOORAJ yana nan awaje yakasa zaune yakasa tsaye, hankalinsa amatuƙar tashe yake, tsoronsa ɗaya kar ace masa ta mutu,  wani irin gumi ne ke fesowa ta goshinsa, kowa yagansa yasan cewa yana cikin tashin hankali.

Aƙalla sama da awa ɗaya da rabi likitoti suka ɗauka suna bata taimakon gaggawa,  cikin ikon Allah Kuwa sun shawo kan lamarin, saidai bata farfaɗo ba, amma sun tsaida jinin dake fita daga goshinta dakuma gefen kanta da ya fashe.

Yana tsaye likitotin suka fito daga Emergency room ɗin.  Da sauri yataho wajen  Dr.Salees, baikai ga cewa komaiba Dr.Salees yasakar masa murmushi tare da sanya hanu ya dafa kafaɗan SOORAJ ɗin.    
 “Karka damu SOORAJ munshawo kan matsalan, sai dai mujira farkawanta, muje office saina ƙarasama sauran bayanin” 

Babu musu SOORAJ yabi bayan Dr.Salees zuwa office ɗinsa.

Suna shiga cikin office ɗin Dr.Salees ya nunawa SOORAJ wajen zama, kana shima ya zauna.

Sakeyin musabaha sukayi kafun Dr.Salees yacigaba da cewa. 

“Ka kwantar da hankalinka ba wani babban damuwa bane, buguwane  kawai, tabugu sosai gaskiya, amma dayardan Allah munshawo kan komai, saidai kuma bamusan awani irin yanayi zata buɗe idanuba, amma muna kyautata zato, Insha Allahu ma zata tashi lafiya, Allah dai yatsare na gaba” 

Da “Ameen” Kawai SOORAJ ya amsa yana mai sauƙe ajiyar zuciya akai akai. 

Bisa umarnin SOORAJ aka maidata wani special room,,,,   ahankali yaturo ƙofar ɗakin yashigo, sauƙe idanunsa yayi akanta, tana kwance flat kanta na kallon sama, gaba ɗaya rigar dake jikinta ta ɓaci da jini, kanta kuwa a ɗaure yake da farin bandeji (bandage) yayinda tulin gashin kanta ke watse akan pillow, ɗauke kansa yayi daga kallonta tare da ƙarasowa cikin ɗakin, kan wata kujera yaje ya zauna haɗe da kai dubansa kan ledan ruwan da aka saƙalashi ajikin wani dogon ƙarfe, yana shiga cikin jikinta ahankali, kallonsa yakuma dawowa dashi kan agogon kamfanin Gucci dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.  Ƙarfe goma na safe daidai haka agogon yanuna masa,  hanunsa yaɗaura akan haɓansa haɗe da furzar da iska daga bakinsa,  miƙewa yayi tsaye tare da nufar ƙofar fita, haryaje bakin ƙofar kuma sai ya tsaya juyowa yayi ya kalleta, idanunsa ne suka sauƙa akan ƙirjinta da kusan rabin breast ɗinta suke a bayyane, da sauri yakawar da kansa, wani irin bugawa yaji kansa yayi, kamar andoka masa guduma,   jacket ɗin dake jikinsa ya cire tare da nufar inda take kwance, saidai koda wasa baisake barin idanunsa sun kalli ƙirjinnata ba,   jacket ɗin nasa yarufa mata ajikinta, kana yafice daga cikin ɗakin.     Office ɗin Dr.Salees yaje ya biya kuɗi, aka tura nurses guda biyu wanda zasu tsaya akanta don bata kulawa, shikuwa motarsa yashiga yabar asibitin.     Direct gidansa ya nufa ransa ajagule, sam baiso haka takasance ba, yau yatsara tafiya Abuja, amma ga abun daya faru, zaman cikin Kaduna yakamashi dole harzuwa farfaɗowar yarinyar.

Wanka yayi kana yazo ya kwanta akan gado, lamo yayi yana tunanin yanda accident ɗin ya kasance, sai alokacinne ma mamaki ya kamasa,  ƙaramar yarinya irinta mai zai fito da ita awannan lokacin? da dukkan alamu kuma ba acikin hayyacinta take ba.  “To kodai mahaukaciya ce?” ya raya hakan azuciyarsa, da sauri ya kawar da wannan tunanin acikin ransa,  wayarsa yaɗauka ya kunna karatun Al’Qur’ani mai girma, yana cikin jin karatun bacci ɓarawo ya sace shi….. 
Tunda ya kwanta bacci bashi ya tashi ba sai da aka soma ƙiraye ƙirayen sallan Azahar.  Toilet yashiga yayo wanka.  Still riga da wando na jeans yasanya ajikinsa. Masallacin dake kusa da gidansa ya nufa donyin sallah.   Tun da yafita yin sallah baidawo ba sai ƙarfe huɗu na yamma, wanka yasakeyi.   Combat jeans ne ajikinsa baƙi sai kuma wata farar riga mai ɓaƙaƙen aninaye.    Yana tsaye agaban dressing mirror yana taje tulin sumar kansa, wanda yasha aski irin na zamani, screen ɗin wayarsa ya soma kawo haske, ɗan matsawa kusa da yawartasa yayi.   Sunan  Mas’oud ne ke yawo akan screen ɗin wayar, kasancewar ya sata a silent shiyasa batayi ƙara ba, ɗan ɓata fuska yayi haɗe da ɗaukan wayar yakara akan kunnensa.  

                      

 “Ina falo” Inji cewar Mas’oud.

                      

 “Okay”  kawai Sooraj yafaɗa akasalance tare da aje wayartasa,   bai fita falon ba yaci gaba da taje sumar kanshi, saida ya kammala duk wani abu dazaiyi kana ya ɗauki wayarsa dakuma car key ɗinsa yafita zuwa falo.

                      

Cike da takaici  Mas’oud ke kallonsa,  duk da yasan cewa halin Sooraj ne shanya mutane, amma kuma abun da yayi masa yauɗin yayi masa ciwo.   

                      

“Inakuma zakaje?” Mas’oud yatambayesa yana me ƙare masa kallo.

                      

“Asibiti”
SOORAJ yabashi amsa ataƙaice.

                      

“Abiti kuma? Baka da lafiya ne?” Mas’oud yajero masa duk waƴannan tambayoyin alokaci guda.

                      

Ɗan ya mutsa fuska yayi haɗe da sanya hanu ya shafi kwantaccen sajen dake shumfuɗe akan fuskarsa.   
  “Accident mukayi, zanje na duba yarinyar dana bugene kota farfaɗo”  ya faɗi haka yana me nufar hanyar fita daga falon, kai kawai Mas’oud ya girgiza haɗe da miƙewa tsaye yabi bayan SOORAJ ɗin.   SOORAJ ne ke tuƙa motar yayinda Mas’oud ke zaune agefen mai zaman banza.  Tafiya suke babu wani wanda yace da   ɗan uwansa wani abu, ahaka har suka kawo asibitin,   sam Mas’oud baiwani damu da shirun da SOORAJ ɗin  yayi ba, because yasan hakan halinsa ne, bakoda yaushe yacika yawan magana ba, amma idan kafahimcesa yana da daɗin zama, dan bayashiga abun da babu ruwansa… 

                      

Atare suka jera suka shiga cikin asibitin.   Office ɗin Dr.Salees suka nufa, shiyayi musu jagora zuwa ɗakin…  dama yana shirin zuwa dubata kenan suka shigo.

                      

Tananan har yanzu bata farfaɗo ba, wasu allurai Dr.Salees yayi mata,  juyawa yayi ya kalli SOORAJ dake zaune akan wata plastic chair….  “Zata iya farfaɗowa akowani lokaci da yardan Allah, Yana da kyau katsaya atare da ita.” Inji cewar Dr.Salees.

                      

Kai kawai ya iya jinjina wa Dr.Salees alaman yaji, fita Dr.Salees yayi daga cikin ɗakin.  

                      

Kallon Mas’oud daya kafe yarinyar da idanu SOORAJ yayi, tsayawa yayi yana kallon yanda idanun Mas’oud ke yawo ajikin yarinyar ko ƙyaftawa ba yayi,  takaicin Mas’oud ɗinne yakamashi, sam shi kam baiga wata mace aduniya dazai tsaya ɓata lokacinsa wajen kallonta ba, yaga manyan mata da suka amsa sunansu mata baiji komai gamedasu ba balle wannan ta tsitsiyar yarinyar, inbanda ƙaddara ma maizai haɗashi da ita,  sam shi baya shiga sha’anin mata, saboda yasan menene matsalarsa, wannan ma don dolene kawai, amma dazaran ta farfaɗo zaisa amaidata inda ya ɗaukota.

                                      

                        

“Tunda kana nan ni inaga kawai zantafi yau nakeso nakoma Abuja, please kakula da ita, idan tafarfaɗo tagayama garinsu saika maida ita!” SOORAJ yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye. 

Da sauri Mas’oud ya kallesa cikin mamaki yace “Zaka koma Abuja kuma?”

Kai SOORAJ ya jinjina masa alamar “Eh”

“Hmmm lallai SOORAJ baka da imani, kabuge yarinya kuma katafi kabarta? wato nine marainin wayonka shine kakeso katafi kabarni da ita ko?”

Murmushin gefen baki SOORAJ yayi wanda yayi masifar ƙarawa fuskarsa kyau. 

“Mene matsalarka Mas’oud idan kakula da ita? Kasan inada abubuwan yi da yawa, banjin kuma zan iya ɓata lokacina akan mace” SOORAJ yafaɗi haka yana me kai dubansa ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa.

“Nima ai bazaman banza ne sana’ata ba, kai kabugeta kuma kai kake da alhakin tsayawa akanta kakuma bata kulawa harsai ta warke, saboda haka ni kaga tafiyata” Mas’oud yafaɗi haka aƙufule, don ya lura tsagwaran iskanci ne ke damun SOORAJ ɗin.

Still murmushin gefen baki yayi haɗe da bin Mas’oud ɗin da kallo harya fice daga cikin ɗakin.      Kan kujera yakoma ya zauna, yayinda ya juyawa gadonnata baya, wayarsa yaciro ya soma latsawa..

Ahankali take ware manya manyan oily eyes ɗinta masu kyau da burgewa,  dishi dishi tasoma gani, kafun daga bisani idanun nata suka soma washewa,    ɗakin tasoma ƙarewa kallo, yayinda ƙwaƙwalwarta ke tunano mata abubuwan da suka faru, amatuƙar razane ta ƙwalla ƙara..     “Wayyo Allah Nashiga Uku dan Allah karku cutar dani!!”

Azabure yajuyo jin ihunta abayansa,   yunƙurin tashi zaune tasomayi amma ina jin kanta take yayi mata wani irin nauyi, ga wani raɗaɗin azaba dake ratsata…

Tsuka yayi ƙasa ƙasa tare da maida kansa ga wayarsa yacigaba da latsawa, yatsani mutumin da baida nutsuwa.

Babu yanda ta iya haka takoma ta kwanta tana gunjin kuka, saboda kotafi kowa ƙoƙari ayanzu bazata iya tashiba.   Idanunta ne suka sauƙa akan bayansa, domin dama yabata baya.   Ganin namiji na zaune ya bata baya yasa taƙara volume ɗin kukanta,  jikinta na rawa tace “Dan Allah kuyi haƙuri ku ƙyaleni, nakoma inda nafito, wallahi nayarda ma ni Zan auri tsoho ɗan dashe’n, nidai kada ku cutar dani, wallahi ni marainiya ce, dan Allah ku ƙyaleni natafi!” kuka take tsakaninta da Allah tana zabga magiya da roƙo, amma ko motsi baiyiba balle tasaran zai juyo gareta, duk atunaninta shiɗin ɗaya daga cikin mazan da suka ka mata ɗazu ne.  

Ganin baijuyo gareta ba yasa tacigaba da kukanta,    yana zaunene kawai amma jiyake kamar ana hautsina ƙwaƙwalwarsa, kuka yana ɗaya daga cikin abun daya tsana,   wata tsuka yaja me ƙarfi haɗe da juyowa ya watsa mata wani irin kallo, idanunsu ne suka sarƙe acikin na juna,  wani irin shock Ziyada taji acikin jikinta, lokaci guda ta haɗiye kukanta,  ɗauke idanunsa yayi daga cikin nata yaci gaba da latsa wayarsa.  

Ajiyar zuciya tashiga sauƙewa akai akai, neman kukannata tayi ta rasa, sai jikinta daya ɗauki wani irin zazzaɓi mai zafi.   Idanunta na kallon bayansa, cikin wata irin murya mai sanyi tace…. 
“Kamaidani gidanmu kaji!” 

Tsayawa yayi daga latsa wayar  da yake yayi shiru…  Bugun zuciyarsa ne ke ƙara tsananta, lumshe kyawawan idanunsa yayi, tare da sauƙe wata irin ajiyar zuciya.   Tashi yayi ya fice daga cikin ɗakin batare daya kalli koda ɓangaren da take ba.

Ganin yafita daga cikin ɗakin yasa  Ziyada fashewa da kuka. 

“Shikenan na mutu yatafi ƙiran sauran ƴan uwannasa, shikenan zasu zo su lalatamin rayuwa!” Cikin gunjin kuka take maganar.

Jin anbuɗe ƙofar ɗakinne yasa, tayi saurin kallon bakin ƙofar,  murmushi Dr.Salees yasakar mata haɗe da cewa 
“Yauwa Patient kintashi ko? sannu, yanzu inane ke miki ciwo ?” 

Kasa amsa masa tayi saima kafesa da idanunta dake ɗigan ruwan hawaye da tayi,  kamar yasan tunanin da take acikin ranta, murmushi yakumayi akaro nabiyu haɗe da cewa “Ki kwantar da hankalinki nan asibiti ne, ba wai wajen da za’a cutar dake ba.”

Rumtse idanunta tayi da ƙarfi sai alokacin tatuna da cewa tana cikin gudu taji wani abu ya doketa har saida ta ɗagu sama, to daga wannan lokacin bata sake sanin maiya faru ba sai yanzu data ganta cikin wani ɗaki.

Hanu Dr.Salees yakai jikinta ya taɓa, zafi zau yaji ajikinnata,   alluran daya shigo dasu yasoma ɓarewa,  ganin allura ahanunsa yasa Ziyada sake fashewa da sabon kuka, murya adashe tace “Don Allah kayi haƙuri karkamin, wallahi bazan sake guduwa ba!”

Mamakine yakama Dr.Salees sai kawai yatsaya yana kallonta.  Dai dai lokacin SOORAJ yashigo cikin ɗakin.

Kallonsa Dr.Salees yayi haɗe da cewa. “Yauwa SOORAJ gwamma daka shigo ai, kaga wannan ƙanwartaka tsoron allura takeyi, kuma akwai zazzaɓi ajikinta dole sai anyi mata allura sannan zata samu relief, bayan haka kuma yakamata kanemo mata ko tea ne tasha, akwai yunwa ajikinta sosai”

“Okay, kayi abun daya dace kawai!” SOORAJ yafaɗa a gajarce, domin baison yawan surutu. 

Kai kawai Dr.Salees yagirgiza aransa yana mamakin miskilanci’n SOORAJ.

Ziyada na kuka haka Dr.Salees yayi mata allura, SOORAJ kuwa yana zaune ko kallon inda suke baiyi ba, earpiece ma yasa akunnensa yana sauraran cool music.   Dr.Salees nagama aikinsa yafita daga cikin ɗakin.

Cusa kanta tayi acikin pillow tana kuka, hakanan taji haushin  mugun mutumin daya sanya akayi mata allura, dama ance mata turawa mugayene to gashi yau ta tabbatarwa kanta, domin kuwa tana da tabbacin  cewa shiɗin idan ba bature bane to kuwa balarabe ne, don wannan farinnasa ba’a banza ba. 

Yana zaune aka soma knocking ɗin ƙofar ɗakin. 

“Come in” yafaɗa da ɗan ƙarfi.  Wani matashin saurayine ya turo ƙofar ɗakin yashigo, jikinsa sanye da wata jar riga  wacce agaba da bayanta aka rubuta MUZAFAS HOTEL da manyan harufa.   Manyan ledodin dake hanunsa ya miƙawa SOORAJ cike da girmamawa,   kuɗi SOORAJ yaciro daga cikin wallet ɗinsa ya miƙawa matashin saurayin.     Kallon SOORAJ saurayin yayi zaiyi magana, SOORAJ yaɗaga masa hanu, haɗe da cewa
“No badamuwa jeka kawai” 

Godiya Matashin saurayin yashiga yiwa SOORAJ cike da murna yafice daga cikin ɗakin. 

Ɗaukan leda ɗaya daga cikin ledodin SOORAJ yayi, cikin Unigue Voice ɗinsa yace
“Tashi kici abinci!”  yanayin yanda yayi maganar ne yasata saurin juyowa takalleshi, saidai kuma yanda ya fusge, yasa tashiga raba idanu kozataga wanda yayi maganar, domin ayanda yasha mur bazaka taɓa cewa shine yayi maganan ba.   Aje mata ledan akan ɗan ƙaramin drawern dake kusa da gadon yayi,  juyawa yayi cikin takunsa na isa yafice daga cikin ɗakin.   

Tana ganin fitansa ta sauƙe wata irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya, har acikin zuciyarta tsoronsa takeji. 

Shiru yayi bayan yagama sauraran jawabin  dake fita daga bakin Dr.Salees. 

Hanu yasa yashafi sajensa,  sam bayajin yiwuwar abunda Dr.Salees ɗin ke faɗi,  daransa da lafiyansa bayajin zai iya kwanan asibiti.  Tashi yayi tsaye yabawa Dr.Salees hanu suka sakeyin musabaha kana yafice daga cikin office ɗin bayan yasanya hanu acikin wata takarda.   Ɗakin datake kwance ya nufa, bayajin abunda zai aikata akanta daidai ne, amma kuma hakan shikaɗai ne mafita.   Yasan abun da zuciyarsa ke raya masa ba abu bane mai kyau, amma kuma baida wata hanyar dazai samawa kansa hutu sama da wannan, idan kuwa har maganar da Dr.Salees yafaɗa masa gaskiya ne, to yazama lallai ya aikata abun da zuciyarsa ke umartansa daya aikata, a wani ɓangaren baidamu da wani irin kallo mutanen duniya zasuyi masa ba, yasan kansa yasan ba irin sa mata ke ɓuƙata ba, kyawunsa da haɗuwarsa afili kawai suke, amma abaɗininsa yafi kowani irin namiji rauni….
A ƙalla yaɗauki kusan mintuna 4 ajikin ƙofar, yayinda hanunsa ke kan handle ɗin ƙofar. Cije laɓɓansa yayi kana yatura ƙofar ahankali yashiga.

Duka hannayensa ya zuba acikin aljihun wandonsa yana kallonta cike da takaici. Kallonsa yakuma maidawa ga ledan daya aje mata, yananan ayanda ya aje, don ko taɓa ledan batayi ba. +

Ƴar ƙaraman tsuka yaja, haɗe da sanya hanu ya ɗan bugi kansa. “Wannan yarinyar da’alama itace ƙaddarata ta biyu!” yafaɗi haka cikin wata silent voice, sam bayason damuwa, gashi yafahimci cewa ita kanta Yarinyar Damuwa ce mai zaman kanta agaresa. “Yanzu da tayi bacci, shine takeso ya ɗauketa ko kuma me?” yatambayi kansa cike da takaicinta. 
Tsuka ya kuma ja kana yafice daga cikin ɗakin.

Mintuna kaɗan wasu nurses su biyu suka shigo cikin ɗakin, kasancewar alluran da Dr.Salees ya mata nada matuƙar ƙarfi bazata iya farkawa nan kusa ba, yasa Nurses ɗin suka ɗaurata akan wani gado wanda keda ƙafafun taya, haka suka turota akan gadon har bakin motarsa, buɗe musu gidan baya yayi suka sanyata aciki. Da wani irin gudu ya figi motartasa yafice daga cikin asibitin, shikaɗai yaketa zuba tsuka, har ya iso makeken gidansa dake cikin unguwar Malali, yana gama daidaita parking ɗin motar tasa, yaɗauki goran ruwan dake gefensa, ɓalle murfin yayi haɗe da kai goran bakinsa, gaba ɗaya ruwan dake cikin goran yashanye tas, ko kaɗan bai rageba, yanaganin wayarsa na ƙara amma yaƙi ɗagawa, duk da bai duba sunan dake yawo akan screen ɗin wayarba, amma yasan wake ƙiransa, tunda yatafi yabarsa kuwa to shima bazai ɗaga ƙiransa ba, idan wulaƙancine shima ya’iya salo salo.

Direct ɓangaren da zai sada sa da part ɗinsa ya nufa. Yana shiga cikin bedroom ɗinsa yasoma rage kayan dake jikinsa. Wani farin towel ya ciro acikin drawer’nsa ya ɗaura, bathroom yashiga tare da kwanciya acikin haɗaɗɗen jakuzzie’n da ruwan cikinsa ke ta tashin ƙamshi. lumshe gajiyayyun idanunsa yayi, Sosai yakejin sanyin ruwan na ratsa sa. Aƙalla yakusan 30 minute yana kwance acikin jakuzzie’n. Da ƙyar ya samu ya iyayin wanka, jinsa yake amugun gajiye. Koda yafito a wanka sama sama yashafa mai, da body spray ɗinsa mai matuƙar ƙamshi, ya feshe duka jikinsa, take ɗakin yasake gaurayewa da wani ni’imtaccen ƙamshi. 3 guater combat jeans yasanya, sai kuma wata riga da bata da nauyi. Ƙara gudun AC’n ɗakin yayi, haɗe da faɗawa kan gado, pillow ya jawo ya ɗaura kansa, tare da lumshe idanunsa.

Ƙarar wayarsane takaraɗe kunnuwansa, tsuka yayi cikin baƙin ciki yajawo wayar ya kara akan kunnensa, shiru yayi batare da yace komaiba, baiduba wake ƙiransaba alokacin daya ɗaga wayar, amma tabbas yasan cewa bawani wanda zai ƙirasa adaidai wannan lokacin in banda Mas’oud.

Jin yayi shiru baice komaiba yasa Mas’oud buga tsuka cike da haushin SOORAJ ɗin yace… “Karkayi tunanin nawani damu da kaine, tausayin yarinyar mutane kawai nake, yanzu yajikinnata? inafata dai ta farfaɗo ba wata matsala?”

Ƙirjinsa ne ya buga, da sauri ya buɗe idanunsa da suke a lumshe, haɗe da tashi zaune, hanu yasa ya ɗan doki kansa, harga Allah shi ya ma manta da batun wata yarinya, sam yamanta da tana cikin motarsa, da sauri ya kashe wayar, tare da sauƙowa daga kan gadon. Bedroom slipper ɗinsa yazura aƙafafunsa kana yafice daga cikin ɗakin. 2

STORY CONTINUES BELOW


Key yasa ya buɗe murfin motar, tananan kwance tana sheƙa baccinta cikin kwanciyar hankali.

Hararanta yayi kafun ya tura kansa cikin motar, ɗaukota yayi kamar wata ƴar baby yayi cikin gidan da ita. Ɗakin dake gefen nasa yashiga da ita, komai na ɗakin neat kamar akwai wani wanda ke rayuwa acikinsa. Yana zuwa daidai gadon ya saketa, ji kake tim tafaɗi akan lallausan katifan dake kan gadon. Tabbas da badon alluran da aika mata mai ƙarfi bace, da ayanda ya wurgatan nan dole saita farka. Juyawa yayi yafice daga cikin ɗakin. Ɗakinsa ya koma, rigar jikinsa ya cire, komawa kan gado yayi ya kwanta. Shi kaɗai yake ƙunƙuni acikin zuciyarsa har bacci yaɗaukesa…..

1:30 am

Tsananin yunwan dake damunta, shiyayi sanadiyar farkawanta daga bacci.. Buɗe gajiyayyun idanunta tayi tana jujjuyasu ahankali. Azabure tatashi tana ƙarewa ɗakin data ganta aciki kallo, tabbas idan zata tuna, wannan bashine ɗakin da ta ganta ɗazu aciki ba, da sauri tashiga waige waige, dirowa tayi ƙasa tana ƙarewa royal bed ɗin data ganta kwance akansa kallo, jingina tayi da bangon ɗakin zuciyarta cike da tarin tsoro da kuma tambayoyi, hanu tasa ta dafe cikinta, da takejinsa kamar babu ƴaƴan hanji acikinsa, tsabar yunwan dake nuƙurƙusanta, wani irin juwa ne ke ibanta, durƙusawa tayi aƙasa haɗe da fashewa da kuka, da duka hannayenta ta kama cikinta, tunda take adunia bata taɓa jin yunwa irin wanda takeji ayanzu ba, jitake kamar wani abu na tsakalan cikinta. Miƙewa tayi ta buɗe wata ƙofa dake cikin ɗakin, atunaninta ko wani ɗakine da zata iya samun abinci taci, gani tayi ɗakin ba komai sai fanfo da kuma wasu fararen abubuwa, saikuma wani abu da tagani asama kamar famfo, duk da cewa bata taɓa zuwa birni ba, amma jikinta yabata cewa nan ɗin banɗaki ne, jan ƙofar tayi ta rufe haɗe da nufar wata ƙofar, tana jan ƙofan kuwa ya buɗe, ahankali ta buɗe ƙofar ta fita, ganinta tayi acikin wani katafaren falo wanda yagaji da haɗuwa, duk da cewa babu yalwataccen haske acikin falon, amma hakan baihanata ganin kyawun falon ba, wurga idanunta dake ɗigar da ruwan hawaye tasomayi tako ta ina, tsorone yasake kamata, kawai saita sulale awajen tashiga rera kuka.

Bayida nauyin bacci ko kaɗan, sama sama yakejiyo gunjin kuka acikin kunnuwansa, ɗan ya mutsa fuskarsa yayi, haɗe da buɗe idanunsa. Shiru yayi yana maijin sautin kukan naƙara ratsa kunnuwansa, Ahankali yace “Najidowa kaina masifa!”

Gyara kwanciyarsa yayi cike da takaicin tashinsa daga daddaɗan baccinsa da tayi, hanu yasanya ya toshe kunnuwansa, sosai yatsani jin kukan mace arayuwarsa, so yayi ya shareta amma kukan da takeyi masa yakasa barinsa yayi hakan. Sauƙowa yayi daga kan gadon, batare daya sanya riga ajikinsa ba ya fice zuwa falo.

Hanunsa ya ɗaura akan makunnin wutan dake falon haɗe da ɗan matsawa, take haske ya gauraye cikin falon, saurin ɗago kanta da ta cusa acikin cinyoyinta tayi, idanunsu ya sauƙa acikin na juna, wani irin bugawa kirjinta yayi kamar zai faɗo waje, take jikinta yaɗauki rawa, da sauri ta rumtse idanunta, ganinsa a haka babu riga da tayi, ya mafi yunwar da takeji ɗaga mata hankali.

“Wai Uban me kikewa kuka?” ya tambayeta a tsawace. 1

Bakinta ne ya ɗauki rawa, ƙanƙame jikinta tayi guri guda, ahankali ta shiga jijjiga masa kanta alaman “Babu”

“Mcheeww” yaja tsuka cike da takaicinta.

Kallonta yayi a ƙufule sakamakon yanda yaga gaba ɗaya jikinta na rawa. Harara ya wurgamata haɗe da nufar inda zai sadashi da kitchine ɗin dake cikin falon.

Tana ganin tafiyarsa, ta saki wani irin marayan kuka, aranta tana cewa, inane takawo kanta, wataƙila ma saida ita zaiyi, shikenan itakam ga abun da guduwa yajawo mata.

Mintuna kaɗan yadawo cikin falon, hanunsa ɗauke da wani cup, ƙarasowa gabanta yayi haɗe da miƙa mata cup ɗin. Jikinta na rawa haka tasanya hanu ta karɓi kofin, ruwan tea ne aciki, hanunta har ɓari yake alokacin da takai kofin bakinta, abun da batasani ba shine Tea ɗin da zafi sosai, da sauri ta furzar da wanda ta kurɓa, sakamakon ƙona mata harshe da yayi, ta gefen ido yakalleta, haɗe da yin wata muguwar murmushi, yana sane ya haɗa mata tea ɗin da tafasheshshen ruwa.

STORY CONTINUES BELOW


Hawayene suka gangaro daga cikin idanunta, harshenta ya ƙone sosai, amma Allah yasani bazata iya haƙura da shan tea ɗin ba, saboda yunwa takeji sosai. Haka ta daure ta cigaba da shan tea ɗin tun tanajin zafinsa har ta daina ji, tas ta shanye tea ɗin ta aje kofin, lokaci guda jikinta ya soma tsatstsafo da gumi, sake jin gina bayanta tayi da jikin bango tana sauƙe ajiyar zuciya akai akai.

Fitowa yayi daga kitchine ɗin haɗe da sanya key ya rufe ƙofar, plate ne ahanunsa, wanda ke ɗauke da yankakkun kayan fruit, miƙa mata plate ɗin yayi cike da haushinta yace 
“Gargaɗi na ƙarshe kada ki sake tashina idan ina bacci!”

Itadai kanta na ƙasa bata sake ɗagowa ta kallesaba tun ganin farko da tayi masa, jin ƙaran rufe ƙofarsa ne, yasa ta sauƙe ajiyar zuciya, da bibbiyu take tura yankakkun kayan fruit ɗin abakinta, fruit ɗin nada yawa, amma saida taci fiye da rabinsa sannan taji ta dawo cikin hayyacinta, hamma tayi haɗe da tashi tsaye tanufi wajen da fridge ke aje, bata iya buɗe fridge ɗin ba, hakan yasa tasoma kiciniyar ɓalle murfin, da ƙyar dai tasamu ta buɗe dayake murfin na glass ne, kana iya hango komai dake cikin fridge ɗin, goran ruwa ta ɗauka tasha, mayarda sauran ruwan tayi cikin fridge ɗin, saɗaf saɗaf haka ta koma ɗakin da ta ganta aciki tun farko, jingina tayi da jikin ƙofar tana mai ƙarewa ɗakin kallo, tsananin tausayin kantane ya kamata, yau gata a wata duniya wacce batasan ina bane, gata acikin gida tare da wani, wanda batasan ko shiɗin waye bane, ahalin yanzu batasan menene makomarta ba, zamewa tayi akan yalwataccen carpet ɗin dake malale a tsakar ɗakin, kuka tashiga rerawa marar sauti, sosai tayi kuka harsaida taji kanta yayi mata nauyi, sannan ta tsagaita ajiyar zuciya tashiga sauƙewa akai akai, tana jingine ajikin bango, wani wahalallen bacci ya ɗauketa…..

Tunda kukanta ya tashesa yakasa komawa bacci, toilet yashiga ya ɗauro alwala, dardumansa ya shumfiɗa yatada sallah…. Yajima yana salla kafun ya idar, laptop ɗinsa yajawo ya soma gudanar da wasu ayyuka, yananan har aka ƙira sallan asuba, rufe laptop ɗin yayi yafita zuwa masallaci…

Sauri Sauri yake shirya kansa kasancewar angayyacesa meeting ɗin gaggawa anan branch ɗinsu dake cikin Kaduna.

Sanye yake da riga da wando na suit masu mugun tsada da kyau, navy blue colour, takalmin ƙafarsa kuwa toms ne mai kyau shima navy blue colour, sosai yayi kyau acikin kayan, nikaina bansan haɗuwarsa takai hakaba, sai yau dana gansa acikin shigar suit. Lol.
Agogon Rolex yake ƙoƙarin ɗaurawa a tsintsiyar hanunsa, babu abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshin turarensa mai sauƙar da nutsuwa, gashin kansa kuwa sai ƙyalli yake fitarwa, sosai yasha gyara da mayuka kala kala, wayarsa mai tambarin Apple abaya ya ɗauka, tare da key ɗin motarsa, kana yafice daga cikin ɗakin..

Haɗaɗɗiyar sabuwar motarsa BMW ya hau, mai gadi na buɗe masa ƙofa ya cillata kan titi ahankali yake murza steering motar cike da nutsuwa..

Tun ƙarfe 7 tatashi zama tayi jigum acikin ɗakin, kallon kayan jikinta tashigayi gaba ɗaya sunɓaci da jini, gashi sunyi bala’in yin dotti, banda ɓarkewan da saman rigarta yayi.

Tun tana zaune tana nazari harta kwanta, juyi kawai take tayi, amma gaba ɗaya bata da nutsuwa, jin ana knocking ƙofar ɗakinnata yasa taji ƴaƴan cikinta sun sake hautsinawa saboda tsoro, cigaba akayi da knocking ƙofar, yayinda itakuma ta matse jikinta waje ɗaya, mugun tsoronsa takeji.

“Good Morning Madam” taji muryan mai knocking ƙofar na faɗan haka. 1

Tsorone yasake kamata, raba idanu tashiga yi tana neman wajen ɓuya don batasan meyake cewa ba, tasan dai wani yare kawai yake yi.

Peter dake tsaye jikin ƙofa hanunsa riƙe da leda ɗin abinci, yaji yasoma gajiya saboda haka, yaciro wayarsa yaƙira ogansa, bansan mai SOORAJ yafaɗa masa ba, sai gani nayi ya aje ledan abakin ƙofa yajuya yayi tafiyarsa.

Jin shiru andaina ƙwanƙwasa ƙofarne bakuma alamar motsin mutum, yasata sauƙo daga kan gadon ahankali. Saɗaf saɗaf take tafiya harta buɗe ƙofar ɗakin, bugewa tayi da ledan da Peter ya ajiye. ko kallon ledan batayi ba tashiga takawa harzuwa tsakiyan katafaren falon. Gaba ɗaya bata cikin nutsuwarta sai waige waige take, ƙirjintane keta bugawa da sauri sauri fatanta ɗaya Allah yasa kada wani yakamata. Wata ƙofa dake cikin falon tanufa, tana buɗe ƙofar kuwa ta buɗu, wani irin ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya tasauƙe sakamakon ganinta a waje da tayi. Da sauri sauri ta nufi inda ta hango wani ƙaton gate, burinta ɗaya shine ta ganta awaje, sam batajin zata iya zama agidan ƙattin maza, wataƙilama da wata manufa suka ajiyeta. Taci sa’a kuwa babu kowa abakin gate ɗin saboda haka gadan gadan tanufi ƴar ƙaramar ƙofan dake jikin gate ɗin ɗaura hanunta tayi ajikin ƙofan tare da buɗewa….
Tana buɗe ƙofan idanunsu ya sarƙe acikin na juna, wani irin tsorone taji ya kamata, take jikinta ya ɗauki rawa. +

Kallo ɗaya yayi mata ya watsar agadarance yace.

“Wuce mukoma ciki”

Samun kanta tayi da kasa musa masa, tana gaba yana biye da ita abaya, suna shiga cikin falon ya murzawa ƙofar key, direct ya wuce ɗakinsa ko kallonta baiyiba, tana ganin wucewarsa cikin ɗaki ta saki wani irin marayan kuka. Yana shiga cikin ɗakin yasoma rage kayan jikinsa. Toilet yashiga yayi wanka, fitowa yayi dagashi sai towel dake ɗaure a ƙugunsa. Sama sama yashafa mai, farin riga da blue ɗin wando yasanya, ba abun dake tashi ajikinsa sai daddaɗan ƙamshi, buɗe ƙofar ɗakinnasa yayi yafita zuwa falo, ko kallon inda take durƙushe tana kuka baiyi ba, kitchine ya nufa, mintuna ƙalilan yadawo hanunsa ɗauke da wani faranti wanda samansa ke ɗauke da kayan fruit.

Zama yayi akan ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falon, haɗe da ɗaura ƙafansa akan rug, apple ya ɗauka yana gutsura ahankali, jingina bayansa yayi da jikin kujera haɗe da lumshe idanunsa, ahankali yake tauna apple ɗin dake cikin bakinsa, a rayuwarsa idan yaji kukan mace sosai hankalinsa ke tashi, amma a yau ko ajikinsa, daɗima kukannata keyi masa, gani yake ita damuwarta ma mai sauƙice tunda hartana iyayin kuka, shi kuwa shi kaɗai yasan abun da ya keji, idan da zai samu daman yin kuka to tabbas da yayi, idan da za’ace dashi idan yayi kuka matsalarsa zata yaye to tabbas da shikam yayi kuka irin kukan da ya amsa sunanshi kuka, ba irin nata kukan na shagwaɓa da sakalci ba. Ahankali sautin kukanta ke tashi acikin falon, ware idanunsa da suka somayin ja yayi haɗe da watsa mata su. “Keee!!” yafaɗa murya akausashe.

Ɗago fuskarta da yayi caɓa caɓa da hawaye tayi ta kallesa. Yanayin yanda taga idanunsa sunyi jajur ne yasa taji gabanta ya faɗi, miƙewa tsaye yayi, haɗe da takowa harzuwa inda take, hanunsa yasanya ya finciko nata hanun, yana janta haka suka fita daga cikin falon, yana zuwa bakin motarsa ya buɗe murfin motar haɗe da cillata ciki da ƙarfi, har saida ta buge goshinta, shiga cikin motar yayi haɗe da kunnata, baijira mai gadi yagama wangale masa gate ɗin bama, ya figi motar da wani irin gudu haɗe da cillata kan titi. Gudu yaketa shararawa akan titi, bai tsayaba harsai da ya kusan fita daga cikin Kaduna, parking yayi agefen titi.

“Fita!”
yace da ita cikin wata irin murya.

Tsaida kukanta tayi cak, haɗe da ƙura masa ido.

“Kifitarmin amota nace!!” yanzu kam atsawace yayi maganar.

Jikinta na rawa tasoma kiciniyar buɗe murfin motar. Yanajin fitanta yayi reverse haɗe da cilla motarsa kan titi, bayan ya buleta da ƙura yabar wajen.

Tana ganin ɓacewar motarsa ta saki wani irin kuka haɗe da durƙushewa a wajen, kuka take mai cike da tsananin tausayin kanta, kuka take nakasancewarta marar gata, kuka take nakasancewarta ƴa mace marar galihu… Sama da mintuna 14 ta kwashe tana durƙushe a wajen, jifa jifa motoci ke wuceta.

Wata haɗaɗɗiyar motace ta tsaya adai dai gabanta, da sauri taɗago atunaninta shine yakuma dawowa, wani saurayi tagani ya sauƙe glass ɗin motar sa, haɗe da sakar mata murmushi.

STORY CONTINUES BELOW


“Ƴan mata mai yasameki haka kike kuka?” yatambayeta yana mai ƙarewa ƙirjinta kallo.

Sunkuyar dakanta ƙasa tayi batare da ta tanka masa ba.

Ganin bata kulasa bane yasashi fitowa daga cikin motar, batasan cewa yafito daga motarba sai ganinshi kawai tayi agabanta, har numfashinsu na dukan na juna. Da sauri ta matsa baya tana mai rau rau da idanunta. Murmushi saurayin yayi mata haɗe da sake matsota, kallonta yake kamar tsohon maye.

“Wai tsorona kikeji ne? haba karki bani kunya mana, zo muje nakaiki masauƙina kiyi wanka kinji!” yanayin yanda yayi maganar saida yasa tsikar jikinta ya zuba. Da sauri tashiga girgiza masa kai tana mai sake ja da baya, shikuwa sai ƙara matsota yake, hanunta ya cafke haɗe da yunƙurin jawota jikinsa, tureshi tasomayi yayinda ruwan hawaye keta ambaliya akan fuskarta.

“Ka…ƙyale..ni” tafaɗi haka cikin rarrabewar murya cike kuma da tsoro. Idanunsa ɗaya ya kashe mata haɗe da sanya harshensa ya lashi laɓɓansa, cike da iskanci yace.
“Haba Babe karkimin haka mana, nafa kamu, please ko 30 minute ne kiban, muje mota please!” yanzukam kuka mai sauti tasanya haɗe da soma turjewa, hanunsa yakai zai taɓa kafaɗanta, yaji anyiwa hanunnasa wani irin riƙo, da sauri yajuya don ganin wanda yayi masa katsalandan. Ido huɗu sukayi, take saurayinnan yaji gabansa yayi wani irin faɗuwa, bakomai ya tsoratashi ba kamar ganin ƙwayar idanun SOORAJ. da gudu Ziyada tayi bayan SOORAJ ta ɓuya haɗe da sakin wani marayan kuka. Irin kallon da SOORAJ keyiwa matashin saurayinne yasashi sulalewa yashige motarsa da gudun gaske yabar wajen.

Aƙalla sun kusan mintuna 9 ahaka yana tsaye ya rumtse jajayen idanuwansa, yayinda ita kuma ke tsaye abayansa ta saƙala hannayenta akan cikinsa, fuskarta ta ɗaura akan bayansa tana kuka.

Hanunsa yasa ya zare hanunta daga kan cikinsa, baice ƙalaba, yakama hanunta suka nufi wajen da motarsa ke fake. gidan baya ya buɗe ya sanyata aciki, kana yaja motar suka ɗauki hanyar komawa cikin gari.

Tunda suka shiga cikin motar ta kifa kanta acikin cinyoyinta taketa faman rera kukan maraici. Shikuwa ko ƙala baice mata ba har ya iso gaban wani tafkeken mall. Fita yayi daga cikin motar yashiga cikin mall ɗin. Aƙalla ya ɗauki kusan sama da 20 minute acikin mall ɗin, fitowa yayi, yayinda wani yaro ke binsa abaya hannayensa riƙe da ledodi, inda Ziyada ke zaune SOORAJ ya buɗe masa yaron ya zuba ledodin aciki. Shiga motar yayi suka sake ɗaukan hanya.

Horn biyu kacal yayi maigadi ya wangale masa gate, a parking space yayi parking motar.

“Biyoni” 
yace da ita ataƙaice batare da ko kallonta yayi ba, babu musu tafito daga cikin motar, dai dai lokacin Tanimu maigadi ya iso wajen. 
 “A kwai kaya acikin mota kashigomin dasu ciki!” SOORAJ yafaɗi haka ga maigadi, kana yasa kai ya wuce ɓangarensa Ziyada na biye dashi.

Harsuka ɓace Tanimu maigadi baidaina kallonsuba, tsantsar gulmane ke cinsa, a iya tsawon rayuwar da sukayi da SOORAJ baitaɓa ganin SOORAJ yashigo da wata mace cikin gidanba, ko auren da yakeyi ma kawo masa matan ake, amma yau abun mamaki gashi da wata ƴar ƙaramar yarinya, ganin cewar gulma bazata kai mishi bane yasashi kwashe kayan ya bi bayansu SOORAJ ɗin.

Suna shiga cikin falon SOORAJ ya buɗe fridge ya ɗauko ruwa, ɓalle murfin goran yayi, haɗe da kai bakin goran kan nasa bakin, baicire bakin goran daga kan nasa bakinba har sai da yashanye ruwan cikin goran tas, a durstbin ya jefa roban ruwan haɗe da dawowa tsakiyar falon ya zauna akan kujera. Dai dai lokacin Tanimu maigadi yashigo, aje ledodin dake hanunsa yayi kana yafice daga cikin falon sumu sumu.

“Zo!” yace da Ziyada dake tsaye tana ta aikin murza ƴan yatsun hanunta.

Kanta aƙasa tatako harzuwa inda yake, durƙusawa tayi agabansa haɗe da cewa “Gani”

“Kinci abinci?” yatambayeta ataƙaice.

Kanta ta girgiza masa alaman “A’a”

“Tashi ki ɗaukomin ledan da aka kawo miki ɗazu” yafaɗi haka batare daya ɗago kansa ya kalleta ba.

Babu musu taje ta ɗauko masa ledan, dama ledan tananan abakin ƙofa kamar yanda peter ya ajiye tun farko.

Har ƙasa ta durƙusa haɗe da miƙa masa ledan.

“Zauna kici !” yafaɗa ataƙaice tare da tashi yanufi hanyar ɗakinsa.

Zama tayi akan carpet tare da buɗe ledan take away ɗaya ta ciro haɗe da buɗewa. Soyayyen chips ne da ketchup sai kifi, ahankali take tsakuran abincin tanaci.

Koda yashiga cikin ɗakin zama yayi abakin gado haɗe da sanya duka hannayensa ya dafa kansa. Maganganun mahaifinsa da yayi masa ɗazune ke dawowa cikin kansa filla filla, Damuwa da rashin gamsashshiyar nutsuwa sune abun dake damunsa ako da yaushe, haƙiƙa Allah bai tauye masa komaiba nadaga arziki da abubuwan jin daɗi, saidai kuma atawani ɓangaren yana da babban rauni, akullum da tunanin ciwon dake damunsa yake kwana yake kuma tashi, tunanin zuwa gida wajen Ummu ne yaji ya ɗarsu acikin ransa, tashi yayi yashige bathroom, yana tsaye agaban shower ruwa na dukansa amma tunanin yanda zaiyi da rayuwar Ziyada ne yacika zuciyarsa, a yanda ya fahimta shine bata da wani gata, kuma tabbas akwai tawaya acikin rayuwarta, ya fahimci cewa kamar yanda yake cikin ƙunci haka itama take cikin ƙunci, saidai kuma damuwarsu sun banbanta, duk da baisan menene damuwarta ba, amma tabbas yasani matsalarta mai sauƙine akan nasa.

SOORAJ sarkin ado yanzuma sanye yake da riga da wando farare ƙal ƙal sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake.

Aƙalla yaɗauki sama da 10 minute yana tsaye abakin ƙofar ɗakin, duka idanuwansa ya kafa mata, komai nata acikin sanyi take yinshi tundaga kan yanda take tsakalan chips ɗin harzuwa yanda take taunasa acikin bakinta. Murmushin gefen baki yayi haɗe da girgiza kansa. Ahankali yashiga takawa harzuwa tsakiyan falon.

“Kije kiyi wanka, kiɗauki kaya acikin ledanan kisa” yace da ita yana mai ƙoƙarin gyara zaman touch watch ɗin dake saƙale a tsintsiyar hanunsa.
Baisake bi takanta ba yasanya kai yafice daga cikin falon.

Tana kammala cin abincin ta koma ɗaki. Banɗaki tashiga haɗe da cire kayan jikinta, soso da sabulu ta ɗauka haɗe da tsugunnawa aƙasan wani fanfo, sosai ta durje duk wani datti dake jikinta.

Tana fitowa a wanka ta ɗauki ledan haɗe da buɗewa. Wata doguwar riga mai kalan ruwan ƙasa taciro daga cikin ledan, ƙurawa rigan ido tayi, irin shape gown ɗinnanne mai kyau, anyiwa gabanta ado da kyawawan duwatsu masu ɗaukar hankali, zura rigan tayi ajikinta, take rigan tayi mata ɗas ajiki, zama tayi abakin gado tana mai wasa da yatsun hanunta, har acikin ranta taji daɗin wankan da tayi, harwani bacci bacci takeji.

“Meye kuma kazo kamin? hala duk ɓacin ran da muka gwada maka bai isheka bane dole sai kazo ka gani a aikace ko? katashi ka fitarmin daga falo tunkan nayi maka ba dai dai ba!” Abun da Ummu ke faɗa ga SOORAJ kenan cikin ɓacin rai.

Langwaɓar da kansa gefe yayi cikin yanayi mai ɗauke da rauni yace. “Dan Allah Ummu kiyi haƙuri, bawai inayin haka ne don ɓacin ranku ba, bayin kaina bane, Ummu banjin zan iya zama da wata mace aduniya, dan Allah Ummu ku ajiye maganan aurena agefe, ƙaddarata ce haka bazan iya zama da mace ba”

“Saboda Sarauniyar Aljana ce ta duniya ta aureka ko? wallahi SOORAJ kayi kaɗan da muzu ba maka idanu katafiyar da rayuwarka yanda kakeso, kaɗaukemu mutanen banza, mata ɗai ɗai har huɗu muna aura ma amma kana sakarsu, wai shin kodai kana shan giya ne?” Ummu ta tambayesa.

Da sauri SOORAJ ya ɗago kansa ya kalli mahaifiyarsa, sam baiyi zaton jin haka daga gareta ba.

“Wallahi Ummu…..”

“Katashi kafitarmin daga ɗaki nace, kar kuma kasake zuwarmin gida, zan sanarwa mai gadi kada yasake barinka kashigomin gida!!” Ummu takatseshi tahanyar faɗan haka a tsawace.

Jikinsa a sanyaye ya miƙe tsaye, har acikin ransa baiso hukuncin da Ummu tayanke masa ba, amma babu yanda ya iya,, sumu sumu haka yafice daga cikin ɗakinnata.

Jingina bayansa yayi da jikin ƙofar fita daga falon, haɗe da lumshe idanunsa, yana maijin raɗaɗi acikin ransa… Cikin zuciyarsa yace. “Kodai na sanar da Ummu ciwon dake damu nane?”Sake lumshe gajiyayyun idanunsa yayi, aransa yanaso yaje yasanar da mahaifiyarsa matsalan dake damunsa, saidai kuma sosai wata zuciyar ke gaya masa hakan badai dai bane. Jikinsa asanyaye ya nufi wajen da yayi parking motarsa.
***
Bacci tasha sosai ba ita tafarka ba sai lokacin da aketa ƙiraye ƙirayen sallan la’asar. Banɗaki tashiga ta ɗauro alwala, kan lallausan carpet ɗin dake malale a gefen gadon ta hau haɗe da tada Sallah, bayan ta idar da sallan ta zauna jigum haɗe da sanya hannayenta ta tallafi kyakkyawar fuskarta. Jitayi ruwan hawaye sun cika idanunta, tausayin kanta take, musamman ma yanzu da take cikin rayuwa irin ta BULAYI. 
***
Kallon Mamaki Mas’oud ke yiwa SOORAJ, da ƙyar ya iya cewa. “Me hakan yake nufi kenan SOORAJ? kakuwa san illan abun da kake shirin aikatawa? ajiye mace’n da ba muharramanka ba acikin gidan ka fa abune da baidaceba sannan kuma hatsarine babba” +

Murmushin gefen baki SOORAJ yayi, haɗe da ɗaukan cup ɗin fresh milk ɗin dake aje agabansa yaɗanyi sipping kaɗan, miƙewa tsaye yayi tare da kai dubansa ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa. 

“Ni zan wuce” yace da Mas’oud ataƙaice.

Kallonsa kawai Mas’oud yayi haɗe da girgiza kansa.
“Nasani dama SOORAJ ba zaka taɓa sanjawa ba” Mas’oud yafaɗi haka acikin zuciyarsa. SOORAJ baisake bi takan Mas’oud ba yanufi wajen da motarsa take.

Yana shiga cikin motar ya murza mata key haɗe da cillata kan titi. Direct babban asibitin dake cikin Garin Kaduna ya nufa.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Dr.Waleey yayi haɗe da gyara zamansa, kallon SOORAJ yayi cike da tausayawa…. “Ka kwantar da hankalinka SOORAJ, akwai wani sabon magani idan na ɗauraka akai wata ƙila adace”

Kallon Dr.Waleey Sooraj yayi da shanyayyun idanunsa.

“Banatunanin akwai wani maganin da zan ƙarasha Dr.Waleey, zan haƙura kawai, zamana ahaka wata ƙila shine abu mafi alkhairi!” yafaɗi maganar cike da raunin zuciya.

“Karkace Haka SOORAJ, kada ka karaya, sauƙi zai iya samuwa ako da yaushe, kasan Allah Babu yanda baya ikonsa, amma nikaina al’amarinka yana matuƙar girgizani, nasha samun case ire iren wannan, amma naka yayi worse.” Ɗan tsagaitawa daga maganan Dr.Waleey yayi, haɗe da sauƙe ajiyar zuciya, cigaba yayi da cewa. 
“Kada kadamu Sooraj Insha Allah watarana sai labari.” ya ƙare maganar cike da son ƙarfafawa Sooraj guiwa.

Murmushi Sooraj yayi haɗe da cije lips ɗinsa, jin Dr.Waleey kawai yake, amma ji yake ajikinsa kamar shikam ahaka zai mutu, ahaka zai ƙare rayuwarsa babu wata ingantacciyar farinciki. 
Sunan wasu magunguna Dr.Waleey ya rubutawa Sooraj a ƴar wata farar takarda. Hanu Sooraj yabasa sukayi musabaha, kafun ya fice daga cikin office ɗin.

Direct Pharmacy yaje yasaya maganin, sannan yabar cikin asibitin.
*** 
Idar da salla’n isha ɗinta kenan ta zauna akan gado, haɗe da kama cikinta daketa yi mata kukan yunwa, gawani tsoro daya lulluɓeta, ayanda tafahimta shine ita kaɗaice ke rayuwa acikin gidan, domin kuwa tunda ta zauna bataji motsin kowa ba. Sam bata saba irin wannan zamanba, tasaba gaba ɗaya rayuwarta cikin aiki take, sam bata da hutu, yi wancan ɗauko wancan, da haka ta saba, shiyasa gaba ɗaya takejinta amatuƙar takure.

STORY CONTINUES BELOW


Ƙarfe takwas na dare daidai motarsa ta kunno kai cikin gidan. Yana gama daidaita parking ɗin motar tasa ya tattaro ledodin dake cikin motar yafito.

Sake matse jikinta tayi haɗe da soma ƙif ƙifta oily eyes ɗinta, jin motsi acikin falon yasa taɗanji gabanta ya faɗi.

Direct bedroom ɗinsa ya wuce, kayan jikinsa ya cire kana ya wuce toilet.

Fitowa yayi ɗaure da towel aƙugunsa, jikinsa duk danshin ruwa. Agaban dressing mirror ya tsaya, tare da ɗaukan ɗan ƙaramin towel yashiga goge ruwan dake jikinsa. sama sama yashafa body lotion ɗinsa mai daɗin ƙamshi, 3 guater jeans yasanya haɗe da saka wata riga marar nauyi, da turarensa mai sanya nutsuwa ya feshe jikinsa. aje comb ɗin dake hanunsa yayi, haɗe da sanya hanu ya shafi lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa, wayarsa ya ɗauka yafice daga cikin ɗakin.

Tsayawa yayi ajikin ƙofar ɗakin, haɗe da ɗaura hanunsa akan handle ɗin ƙofar, kamar zai tura ƙofar ciki kuma sai ya fasa, hanunsa yakai jikin ƙofar yayi knocking.

Da sauri takalli ƙofar jin ana ƙwanƙwasawa, shiru tayi haɗe da ƙurawa ƙofar ido. Sooraj dake tsaye ajikin ƙofar yasake ƙwanƙwasawa.

Saɗaf saɗaf ta sauƙo daga kan gado, zuwa tayi ta buɗe ƙofar, karab idanunsu ya sauƙa acikin na juna, wani irin bugawa taji ƙirjinta yayi, abubuwa biyune suka haɗe mata, ganin kyawawan eyeballs ɗinsa da kuma daddaɗan ƙamshinsa mai sanyaya zuciya.

“Biyoni!” yace da ita ataƙaice haɗe da juyawa ya koma cikin falon, sumu sumu haka ta bi bayansa tana matse jikinta domin kuwa mayafin rigar dake jikinta iya ƙirjinta kawai ya tsaya.

Zama yayi akan lallausan carfet ɗin dake malale tsakiyan falon, tare da tanƙwashe ƙafafunsa. Cikin sanyi ta ƙaraso cikin falon, durƙusawa tayi aƙasa haɗe da sunne kanta ƙasa.
“Gani”
tace dashi in a silent voice.

“Kinci abinci?” yatambayeta batare daya kula sashin da take ba.

Mamakin tambayar da yayi matane ya kamata, ta ina zata samu taci abinci bayan babu abincin.

“Bakiji bane?” yasake tambayarta cike da ƙosawa.

“A’a banci ba” tafaɗa masa haka a sanyaye.

Ledan dake aje agefensa ya jawo. “Ɗauko min plate” yafaɗa still batare daya kalleta ba.

Inda take tunanin nanne kitchine ta nufa, sum sum ta dawo riƙe da plate a hanunta.

Durƙusawa tayi haɗe da miƙa masa plate ɗin.

Ledar ya buɗe ya ciro take away guda ɗaya, haɗe da tura mata gabanta, ɗaukan ɗaya yayi ya juye abun dake ciki acikin plate ɗin da ta kawo masa.

Spoon yasa acikin plate ɗin yasoma tsakalan jalop rice ɗin da yaji busashshen kifi.

Shiru tayi ta kasa cin abincin, tsoron tashi take, sannan kuma bazata iya sakewa taci abinci a gabansa ba.

Tunda yafara tsakalan abincin bai ko da ɗago kansa ya kalleta ba, abincinsa kawai ya ke cusawa, fiye da rabi yaci sannan ya ture plate ɗin gefe, goran peach ɗin dake gefensa ya ɗauka, haɗe da tsiyayawa acikin wani ɗan ƙaramin glass cup, ahankali yake sipping peach drink ɗin, yana kammalawa ya miƙe ya wuce ɗakinsa.

Tanajin rufe ƙofarsa ta saki wata ajiyar zuciya mai ƙarfi, take away ɗin ta jawo gabanta, buɗewa tayi, amma amaimakon taga shinkafa kamar yanda taga nasa, sai taga ferfesun naman kaza ne aciki, wani yawu ta haɗiya haɗe da soma ci ahankali, bata wani ci sosai ba taji gaba ɗaya cikinta ya cushe, rufewa tayi tare da ɗaukan goran ruwan dake gefenta tasha. Ɗauke plate da take away ɗin tayi tamayar kitchine, zama tayi afalon tana daɗa ƙarewa falon kallo, idanunta ta sauƙe akan makeken tv plasma’n dake cikin falon, kasancewar ba akunne yakeba yasa ta ɗauke idanunta daga kansa, kanta ta jingina ahanun kujeran da take zaune aƙasanta, shiru tayi haɗe da lumshe idanunta da suka kawo ƙwalla, tunanin babanta ne ya faɗo mata arai, take taji zuciyarta ta ƙara karaya,, tana cikin wannan tunanin bacci ya ɗauketa ahaka.

STORY CONTINUES BELOW


Tsab ya gama shirin kwanciyarsa, bayan ya gama latsa laptop ɗinsa. Kwanciya yayi flat akan gadon haɗe da lumshe idanunsa, sosai yakejin daɗin sanyin Ac’n dake hurasa, wani abune yazo ya toshe masa maƙoshi, akowacce dare baya samun wata gamsashshiyar nutsuwa, yanaji ajikinsa akwai wani gibi a tattare dashi, haƙoransa yasa ya datse laɓɓansa, sakamakon tunowa da korar da Ummu tayi masa ɗazu da yayi, sam baya ganin laifin iyayennasa, saboda kowa tunani yake cewa ason ransa yake sakan matan da ake aura masa, tunowa da magungunansa da yasayo yau yayi, miƙewa yayi jiki a sanyaye ya ɗauko magungunan, ruwa ya ɗauka ya sha.

Luf yayi akan tattausan katifarsa, duk yanda yaso bacci ya ɗaukesa ya kasa shikaɗai yaketa juyi akan gado, saƙƙowa yayi daga kan gadon haɗe da zura slippers ɗinsa, falo ya nufa hanunsa riƙe da wayarsa.

Bai lura da itaba sam saida ya zauna akun kujeran dake facing ɗin wanda ta ɗaura kanta akai.

Shiru yayi haɗe da ƙura mata idanu, kallon yanda tayi kwanciyar nata yasoma yi, duka jikinta na ƙasa yayinda kanta kuwa ke kan hanun kujera, dagani kasan baccinne ya ɗauketa batare da ta shiryawa hakan ba, kallon ɗan ƙaramin bakinta dake ɗan buɗe yayi, tare da kawar da kansa gefe.

Ɗan zamewa yayi ya jingina bayansa da jikin kujera, lumshe idanunsa yayi haɗe da soma sauƙe numfashi ahankali.

*** *** ***

4:50 am dai dai ya shiga buɗe idanunsa ahankali, azabure ya tashi zaune yana bin inda ya gansa akwance da kallo, yana jingine akan kujera bacci ya ɗaukesa batare daya sani ba, hanu yasa ya dafe goshinsa haɗe da furzar da wani iska mai zafi daga bakinsa. Kallon gefensa yayi tananan kamar ɗazu saidai yanzu tadawo da kanta ƙasa, yayinda ta takure jikinta waje ɗaya da alama sanyin AC ne ke damunta.

Miƙewa yayi ya wuce ɗakinsa yana me mamakin kansa, tunda yake bai taɓa kwana afalo ba sai yau, sam baisan yaushe bacci ya ɗaukesa ba.

Toilet yashiga haɗe da sakarwa kansa ruwa. Yana fitowa ya zura maroon jallabiya tare da ɗaukar sallayansa ya fice daga cikin ɗakin.

Haka ya wuceta afalon tana ta bacci ko kallon inda take baiyi ba ya fice.

Ahankali ta ware idanunta akan haɗaɗɗen zanen POP’n dake mamaye saman falon, fuskarta ta ɗan yatsuna haɗe da sanya hanunta akan wuyanta, jitayi wuyannata ya ƙage waje ɗaya sosai yakeyi mata ciwo, ahankali ta miƙe tsaye, kallon falon tayi sannan ta wuce ɗaki, banɗaki tashiga ta ɗauro alwala, tana idar da sallan ta zauna akan sallayan haɗe da sake lumshe idanunta, ciwo wuyanta keyi mata sosai hakan yasa ko motsa kanta batason yi.

Tunda yafita daga gidan baidawo ba sai Ƙarfe 9 na safiya, yana shiga bedroom direct toilet ya nufa, kwanciya yayi luf acikin jakuzzien daya ji ruwan wanka wanda aka cakuɗasa da daddaɗan turaren wanka mai ƙamshin gaske, lumshe idanunsa yayi, kansa ne ke ɗanyi masa ciwo kaɗan kaɗan, ajiyar zuciya yayi, sakamakon tunawa da yayi cewa gobe zai wuce Abuja, sai dai kuma baisan ina zai saka wannan kayan daya ɗaukowa kansa ba.

***

Acan Ƙauye kuwa, Inna Ma’u sun wayi gari anata shirye shiryen ɗaurin aure, basu farga da cewa Ziyada bata gidan ba saida jama’a suka hallara don ɗaurin auren, tashin hankali kam Inna Ma’u ta shigesa, babu inda ba su bazama ba wajen nemanta amma babu ko wani wanda yace ya ganta. Sosai hankalin Mahaifinta ya tashi, har baisan sanda wasu ƙwalla suka gangaro daga cikin idanunsa ba, Inna Ma’u kuwa bala’i tashigayi haɗe da tsinewa Ziyada tana cewa wai ta cucesu ta kunyatasu, shikuwa Tsoho Ɗan Dashe ai masifa yadingayi kamar zai tashi sama, take rashin mutumcinsa ya tashi, nan yakafe kaida fata lallai sai Inna Ma’u ta biyasa kuɗaɗen daya dinga narka mata, idanu Inna Ma’u tashiga zarewa kamar munafuka…..
***

Riga da wandone ajikinsa wanda suka matuƙar yi masa kyau, cike da ƙosawa ya ture laptop ɗin dake gabansa, kusan awansa biyu yana aiki da ita, gaba ɗaya jinsa yake agajiye, kitchine ya wuce ya haɗa tea ɗinsa, dawowa cikin falon yayi ya zauna, kallon ƙofar ɗakin da take ciki yayi, kana ya dawo da kallonsa ga agogon dake saƙale ajikin bangon ɗakin 2:00pm dai dai yagani, sake kallon ƙofar ɗakin yayi, sai alokacin ya tuno da cewa ko break bai bata ba, kallon tea ɗinsa yayi haɗe da sake kallon ƙofar nata, yakan manta da cikinsa ma balle na wani, shi dama sam abinci bai dameshi ba, sannan ba ɗawainiyar kowane akansa ba, shiyasa baiwani damu da wani yaci ko karyaci ba, baisan ya ake kula da wani ba, saboda shikaɗai yake rayuwarsa bawani a ƙasansa, Saida yagama shanye tea ɗinsa kafun ya tashi daga zaunen da yake. Wayarsa ya ɗauka ya turawa wata number text message, yanaganin alamar saƙon yatafi ya ajiye wayartasa. Kwanciya yayi akan kujera haɗe da lumshe idanunsa.Baijima da kwanciya ba aka soma knocking ƙofar falon, yana daga kwance yabawa maiyin knocking ɗin izinin shigowa. +

Peter ne yashigo cikin falon hanunsa riƙe da wasu ledodi, cike da girmamawa ya rusuna ya gaida ogan nasa.

Amsan ledodin Sooraj yayi haɗe da ciro wallet ɗinsa ya zaro fararen ƴan dubu dubu har guda uku ya bawa peter, karɓa peter yayi yana godiya ya fice daga falon.

Ɗaukan duka ledodin yayi haɗe da nufar ɗakin da take, amemakon yayi knocking kamar yanda ya sabayi kullum, sai kawai ya tura ƙofar ya shiga ciki, a zuciyarsa kuwa yana maijin haushin bautar da yakeyi mata.

Tana kwance akan gado tayi kwanciyar ruf da ciki, bacci takeyi hankalinta a kwance, harara yaɗan wurga mata haɗe da aje ledodin, har ya juya zai fita daga ɗakin kuma sai ya tsaya, kallonta yashigayi tundaga ƙafanta har zuwa kanta, ahankali yataka zuwa inda take kwance, ƙafansa yasa ya ɗan zunguri nata ƙafan, azabure tatashi ta zauna tana mai murje manya manyan idanunta da sukayi ja. Sake kallonta yayi, sai alokacin ya lura tun rigar jiya itace har yanzu ajikinta. “Ƙazama” yafaɗi haka acikin zuciarsa.

“Ki tashi kije kiyi wanka, ke wace irin ƙazamace zaki wuni da kaya ki kuma kwana dashi?” yatambayeta yana mai kawar da kansa daga kallonta.

Ɗago idanunta tayi ta kallesa, gani tayi kamar bashine yayi maganan ba, saboda yanda ya fusge yawani kawar da kansa gefe guda.

Kallon kanta tashigayi, sam rigar jikinta bata da wani alaman abu wai shi datti, ita lokacin da take ƙauye ai sai kaya suyi sati ajikinta ma bata cireba, to inama taga yawan suturun balle ta dinga sanjawa akai akai.

“Idan kin gama ki sameni a falo” yanagama faɗan haka yafice daga cikin ɗakin.

Kamar yanda yace haka tayi, kayan jikinta ta cire taje tayi wanka, tana fitowa awanka still wata doguwar riga ta ɗauka ta sanya, sai dai wannan ba kalan waccar da ta cire bane. Ledan da ya aje mata ta ɗauka haɗe da buɗewa, yau madai robobin take away ne acikin ledan har guda uku, ɗaukan ɗaya tayi haɗe da buɗewa ta soma ci, sosai taci sannan tasha ruwa. Mayafin rigar tayafa asaman kanta sannan tafito zuwa falo.

Yana tsaye agaban fridge yabawa cikin falon baya, jin motsinta afalon yasa batare da ya juyoba yace. “Muje” nufar hanyar fita daga cikin falon yayi.

Yana gaba tana biye dashi abaya har suka ƙaraso inda motarsa ke fake. Buɗe murfin motar yayi ya shiga, key yasanya zai ta da motar, gefen da take tsaye ya kalla cike da takaici. 
“Sainace ki shigo sannan zaki shigo?” yatambayeta cikin yanayi naɗan jin haushi. Buɗe murfin motar tayi ta shiga ta zauna, ƙirjinta kuwa bugawa yake kamar zai fito waje.

Tunda suka hau titi bata ɗago kanta ba, wasa take da yatsun hanunta, yayinda ƙwalla suka cika idanunta, ita kanta batasan ƙwallan na menene ba.

Yana gama daidaita parking ɗin motar ya cire earpiece ɗin dake saƙale acikin kunnensa.

“Muje” ya faɗa yana maiƙoƙarin fita daga cikin motar.
Sai alokacin ta ɗago kanta ta kalli inda ya kawota, batasan ina bane, saidai taga mutane nata shiga da fice a wajen, haka ta fito daga cikin motar ta shiga bin bayansa, saida suka shiga cikin wajen sannan tafahimci cewa asibiti suka zo, ji tayi gabanta ya faɗi, aranta tace “Allah Yasa ba allura yakawoni ayi min ba.”

STORY CONTINUES BELOW


Tafiya suka ɗanyi sosai itadai binsa kawai take kamar jela, abakin wani ƙofa suka tsaya, knocking ƙofan yayi, daga ciki aka bashi izinin shigowa.

“Ki tsaya anan” yafaɗi haka yana mai ƙoƙarin buɗe ƙofar, tana ganin shigewarsa taja ta tsaya haɗe da sauƙe ajiyar zuciya.

Dr.Salees Yana ganin Sooraj ya miƙe haɗe da soma haɗa kayan aikin dazai buƙata, atare suka fito daga cikin office ɗin.

Murmushi Dr. Salees Yayi haɗe da kallon Ziyada.

“Ƴan mata yajikinnaki?” yatambayeta cike da kulawa.

“Da sauƙi!” tabasa amsa murya araunane, saboda tana ganinsa taji ƙirjinta ya tsananta bugawa.

Kansa yajinjina haɗe da cewa “Biyoni muje ko”

Da sauri takalli Sooraj saidai gani tayi idanunsa ba akansu yake ba, earpiece ne ma sanye akunnensa, ya wani haɗe fuska, hakan yasa cikin sanyin jiki tabi bayan Dr. Salees.

Akan wani ɗan gado ta zauna, yayinda Dr.Salees dakansa ya soma warware mata bandage ɗin dake nannaɗe akanta, yana gama cirewa ya ɗauki auduga haɗe da ɗan ɗiga wani farin ruwa mai ɗauke da sinadarai akai, hanunsa ya sanya ya kama goshinta ahankali yasoma goge ciwon da audugan dake hanunsa, wani irin ƙara tasa haɗe da cije laɓɓanta, sake riƙe kanta yayi cike da kulawa yace. “Sorry da zafi ko? ki nutsu awanke miki hakan shine zai sa ciwon ya bushe”

Sake sakin wani ƙara tayi haɗe da soma ƙoƙarin ƙwace kanta daga hanunsa, sosai takejin zafin ruwan dayake sawa yana goge ciwon, sake kama kannata yayi da ƙarfi, haka yashiga wankewa, ita kuwa banda kuka babu abun da takeyi, duk yanda taso ta ƙwace kanta ta kasa, saida ya wanke ciwon tsab sannan ya sake naɗa mata wani sabon bandage ɗin. kallon innocent face ɗinta Dr. Salees Yayi haɗe da ɗan sakin murmushi.
“Sarkin raki, sai ki tsayar da kukan hakanan tunda angama”

Harsuka fito daga cikin ɗakin Ziyada bata daina zubar da hawaye ba, gaba ɗaya idanunta sunyi ja, fuskarta kuwa duk yayi face face da ruwan hawaye. Wasu magungunan Dr. Salees yabata sannan suka bar cikin asibitin.

Kamar yanda suka zo haka suka tafi babu wani wanda yace da ɗan uwansa ƙala, gaba ɗaya hankalinsa nakan tuƙin dayake, ahankali yake ɗan kaɗa kansa, sosai yake enjoying cool music ɗin dake tashi acikin earpiece din dake saƙale acikin kunnensa. Duk abun da takeyi yana lure da ita. Sauƙa yayi daga kan titi haɗe da ɗan gangarawa gefen hanya, tsaida motar tasa yayi haɗe da ɗaukan goran ruwa ya kafa akan bakinsa, sauƙe goran ƙasa yayi haɗe da fitar da wani dogon numfashi.

“Kukan me kikeyi?” yajefo mata tambayar da bata taɓa zato ba.

Ɗago kanta tayi ta kallesa, daidai lokacinne kuma wani guntun hawaye dake maƙale acikin idanunta, yasamu daman gangarowa.

A fakaice ya kalleta ta gefen idanunsa… “Inaganin lokaci yayi daya kamata ki koma ga iyayenki, saboda haka zan ajiyeki anan peter zaizo saiki nuna masa garinku zai kaiki gida” yafaɗi haka cikin halin ko inkula yana mai latsa iphone 11 pro ɗin dake riƙe a hanunsa.

Hawayene suka shiga gangarowa daga cikin idanunta kamar an buɗe famfo, murya araunane tace.

“Bansan kowa ba, bani da kowa sai mahaifina wanda kwata kwata bai ɗaukeni a matsayin ƴarsa ba, tun farko na fara rayuwata ne acikin ƙunci, bansan wani abu waishi ɗan ɗanon farinciki ba, kataimakeni banaso rayuwata ta salwanta!” tuni hawaye sun gama wanke mata fuska.

Tunda tafara maganan bai ɗago ya kalleta ba baikuma daina abun dayakeyiba, sai ayanzune ya ɗago kansa daga latsa wayar da yake… “Wani irin duhu ne acikin rayuwarki da har kika zaɓi salwantar da kanki? wacece ke?” yatambayeta batare daya ɗaura idanunsa akan ta ba.

STORY CONTINUES BELOW


Hawayen da kebin kan kumatunta ta sanya hanu ta share.

“Nima bansan koni wacece ba, saidai kawai nasan tsananin duhu ne ke bibiyar rayuwata” tafaɗi haka tana mai sharce hawayen dake kan fuskarta.

Sai alokacin ya ɗago idanunsa ya kalleta, gaba ɗaya idanunta sunyi jajur dasu, bai sake ce da ita wani abuba ya tada motar suka bar wajen. Harsuka isa gida bata daina sheshsheƙan kuka ba.

Yana shiga cikin ɗakinsa ya zauna akan gado haɗe da sanya hannayensa ya dafe kansa, baisan meyasa yakejin son taimakon yarinyar acikin ransa ba, sai dai tawani ɓangare na zuciyarsa bata aminta da abun dayake ƙoƙarin aikatawa ba, sam bayaso wata ko wani su shigo cikin rayuwarsa, amma kawai yana ganin zaiyi abun daya dace.

** ** **

Ajiyar zuciya yasauƙe akaro na barkatai haɗe da jawo trolly ɗin dake gefensa, tun adaren jiya ya gama shirya kayansa, ƙarfe 6 na yamma jirgin da zai hau zuwa Abuja zai tashi, kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa yayi ƙarfe 5:20 na yammaci dai dai, ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da fitar da numfashi daga bakinsa. Jan ɗan ƙaramin trollyn nasa ya yi haɗe da ficewa daga cikin ɗakin.

Tsayawa yayi abakin ƙofar haɗe dayin knocking. Kamar dama jira ake yayi knocking ɗin aka buɗe ƙofar.

Ganin ta buɗe ƙofar ne yasashi juyawa yasoma tafiya, batare da yace da ita wani abuba. Ganin haka yasa ta fito jikinta asanyaye tashiga bin bayansa.

Ganin yana ƙoƙarin shiga cikin motar yasanya itama tashiga ta zauna haɗe da takurewa waje ɗaya.

Ga mamakinta sai gani tayi yashiga gidan baya ya zauna yayinda Peter ya zo yashiga mazaunin driver. 
Tafiya sukayi mai ɗan nisa kafun suka isa inda zasu, baki hanci da ido duk ta buɗe tana ƙarewa wajen data tsinci kanta aciki kallo. A hankali tafara bin mutanen dake ta hada hada a wajen da idanu ɗaya bayan ɗaya, yawancin jama’ar dake wajen ɗauke suke da ƴan akwatunansu, yayinda wasu kuwa ke tsai tsaye.

“fito muje” Sooraj yace da ita yana maiƙoƙarin cire sit belt ɗin dake jikinsa. 
Tana biye dashi abaya sai wurga idanunta takeyi takota ina, daga bayanta kuwa peter ne ke riƙe da ƴar jakan Sooraj, tunda suka shigo cikin wajen, idanun yawancin mutane musamman ƴan mata ya dawo kan Sooraj, suna ƙarasowa wajen ana sanar da cewa matafiya Abuja su shirya jirginsu yakusa tashi. Tsayawa daga tafiyar da yakeyi yayi haɗe da juyawa ya kalli peter. “Kawuce gida kawai peter sai munyi waya” yafaɗa yana duban lokaci a gogon dake hanunsa.

Kai Peter ya jinjina alaman gamsuwa haɗe dayi masa Allah Ya Kiyaye hanya.

Pass yaciro daga cikin aljihunsa guda biyu ya miƙa mata ɗaya, amsa tayi tana mai kafesa da ɗara ɗaran idanunta.

Suna zuwa bakin ƙofar shiga yanuna pass ɗinsa, ganin abun da yayi yasa itama ta nuna ƴar takardan daya bata, dan batasanma takardan ko ta mecece ba, sannan aka barsu suka wuce.

Idanu ta ware tana bin jiragen dake wajen da ido, tunda take aduniarta bata taɓa ganin jirgi ido da ido ba sai ayau, hakanne yasa take ganin abun kamar almara, direct inda jirginsu yake ya nufa, har yaje kusa da matattakalar jirgin ya juyo donyi mata magana, amma abun mamaki bai ganta abayansa ba, ɗan kalle kalle ya somayi, can ya hangota tsaye tana ta kallon jirage. (Like ƙawata hauwa lokacin da ta fara zuwa airport.Lol) takaicine ya turnuƙeshi, nufar inda take yayi, yana zuwa ya kamo hanunta, haɗe da turata gabansa, suka soma tafiya, saida suka kawo ƙofar shiga jirgin, ta tsaya tana kallonsa lokaci guda idanunta sukayi raurau dasu, zuciyarta ta karye, wani tunanine yashiga yawo acikin ranta. Da Kyawawan idanunsa ya kalleta, aƙufule yace. “Wuce muje!”

Kasa koda motsa ƙafafunta tayi, tsanin tsoro takeji, bazata iya taka matattakalan ba.

Kamar yasan abun datake tunani kenan, ganin tana masa wasting time yasa ya kama hanunta suka soma haura matattakalan.

Direct ɓangaren Business class suka nufa, suna shiga ya nufi inda kujeransa yake ya zauna wacce take kusa da window, tsaye tayi takasa zama sai raba idanunta take, abun kamar amafarki wai yau itace acikin jirgi. Ganin ta tsaya mai aka yasa shi ɗago da kansa ya harareta, aibatasan lokacin da ta zauna akan kujeran dake kusa danasa ba. Sit belt ya ɗaura ajikinsa, haɗe da kwantar da bayansa ajikin kujera, kana ya lumshe idanunsa. Gaba ɗaya Ziyada amatuƙar tsorace take, jitake kamar tazama tsuntsuwa ta fire. Lokacin da aka soma announcement cewa kowa ya ɗaura sit belt ɗinsa, ɗan ranƙwafowa kusa da ita yayi, har suna iya jiyo hucin numfashin juna, sit belt ɗinta ya ɗaura mata, kana yakoma ya kwanta ajikin kujeransa, sannu ahankali jirginsu ya ɗaga sararin samaniya.

Tsananin sanyin AC’n dake ratsa cikin jirgin, shine dalilin da ya sanya tatakure jikinta waje ɗaya, sam bata saba da sanyiba ko kaɗan.Tunda jirgin su ya ɗaga bai buɗe idanunsa ba har jirgin nasu ya sauƙa a NNAMDI AZIKWE Internation airport. Buɗe idanunsa yayi a hankali tare da zare sit belt ɗin dake jikinsa, dubansa ya kai zuwa gareta, wani babban abun mamaki ganinta yayi tana bacci, fuskarta ɗauke da wani bushashshen hawaye, takaicinta ne ya sake kamashi, shi sam baisan ita wace irin bagidajiya bace ba, yanzu aɗan tafiyan da bai wuce 30 minute ba har ace tayi bacci ? +

Hanunsa yasa ya zunguri kanta, da yake baccin nata baiyi nisa ba, hakan yasa ta buɗe idanunta, ta sauƙe ƙwayar idanunta a kansa.

Nuni yayi mata da ta cire sit belt ɗin dake jikinta, cire sit belt ɗin tayi tana mai mutsutstsuka idanunta da suke cike da bacci.
Gudun kada tayi masa halinnata na ƙauyanci ta ba da shi agaban mutane yasa ya tusa ƙeyarta gaba suka nufi hanyar fita daga cikin jirgin.

Cikin takunsa na isa yake sauƙowa daga kan matattakalan jirgin, sanye yake da riga da wando na jeans baƙaƙe sai kuma facing cap white colour daya sanya akansa, kalan takalman dake ƙafansa. 
Kallo ɗaya zakayi masa kafahimci cewa shiɗin cikakken ɗan gaye ne wanda yake murza naira. babu wani makusa atattare dashi, komai nasa yayi hundred percent, sam a halittarsa ta bayyane bazaka taɓa kawo cewa yana ɗauke da wata damuwa ba, saboda shiɗin irin mazan nanne masu aji da wayewa, sannan yanada cikar halitta, komai nasa abun so ne ga ƴa macen da tasan kanta. yanada kyawun jiki data fuska, ajikinsa dai kam baida wata makusa, amma kuma saidai shikaɗai yasan menene aibunsa, wanda idan da zai bayyana rauninsa a fili, to tabbas da sai kowacce mace ta gujesa, saboda aibun dayake ɗauke dashi, yafi tsananin kyawu da dukiyarsa tasiri wajen rugujewar farincikinsa. idan akayi dubi da lalurar dake damunsa shekara da shekaru to tabbas kyawunsa da haɗuwarsa ba zasu amfana masa komaiba, dama kuma hakane yawanci kowani bawa da irin tasa tawayan.

Yana gama sauƙowa daga kan matattakalan ya gyara zaman facing cap ɗin dake kansa. Wani matashin saurayi ne ya ƙaraso wajen da suke da sauri. Cike da girmamawa ya ce.

“Barka da zuwa Oga”
yaƙare maganar yana mai karɓan jakan dake hanun Sooraj ɗin…

“Yauwa!” Sooraj ya amsa ataƙaice.

Juyowa yayi ya kalli Ziyada dake ta faman murje gajiyayyun idanunta, tana kuma ƙarewa haɗaɗɗen wajen kallo, domin kuwa wannan airport ɗin ya ɗarawa wanda suka baro.

“Kuje mota ina zuwa” yafaɗi haka yana mai ƙoƙarin shiga wata babbar ƙofa ta glass dake cikin airport ɗin.

“Ranki yadaɗe muje ko” wannan saurayin yace da Ziyada, da haryanzu take ta kalle kalle. Babu musu tabi bayansa, sai dai a ƙasan zuciyarta shumfuɗe take da tsoro, zuwa yanzu wata zuciyar na sanar da ita cewa “Sai da ita Sooraj zaiyi” hakanan zuciyarta tasa mata cewa ba banza yake ɗawainiya da ita ba, saidai kuma ta wata fuskar sam baiyi kama da mugayen mutane ba, duk da bayi da sakewa, amma baiyi kamanni da mugaye ba.

Direct wajen wata dan ƙareriyar mota taga sun nufa, buɗe mata gidan gaba ɓangaren mai zaman banza matashin saurayin da ake ƙira da Kamalu yayi, yana mai satan kallon fuskarta, mamakine cike azuciyarsa, yana mamakin a ina ogansa ya samota, yasan Sooraj yakuma san baida wata ƙanwa mace balle yace itaɗin ko ƙanwarsa ce, ya kuma san halin ogan nasa baya neman mata, balle ko yace wata ya ɗauko zasuyi zaman haramci, da wannan tunanin yashiga ɓangaren driver ya zauna.

STORY CONTINUES BELOW


Fuskarta ta manna ajikin glass ɗin window’n motar tana mai kallon mutanen dake ta hada hada a wajen.
Kallonta ta mayar ga ƙofar da taga ya shiga, daidai lokacinne kuma ta hangoshi ya fito, fuskarsa ɗauke da wata ƴar guntun murmushi da iyakanta kan leɓe, tunda take arayuwarta bata taɓa ganin mutum irinsa ba, haka kawai take ganinsa wani daban acikin mutane, komai nasa special ne. Gani tayi wani ya biyosa abaya yana dariya, atare suka jero da Sooraj ɗin fuskar wannan ɗin ɗauke take da fari’a saɓanin Sooraj da fuskarsa ke ɗauke da yanayi irin na ba yabo ba fallasa. Har wajen motar Ma’arouf ya rako Sooraj. (Ma’arouf abokin Sooraj ne sannan babban matuƙin jirgin sama ne)

Buɗe gidan baya Sooraj yayi ya shiga, ɗan ranƙwafowa Ma’arouf yayi haɗe dayin knocking glass ɗin window’n motar ta inda Ziyada ke zaune, a hankali Kamalu yayi ƙasa da glass ɗin window’n, atunaninsa gaisawa Ma’arouf ɗin keso suyi dashi, don yasan halin Ma’arouf akwai kirki, baruwansa komin ƙasƙancinka zai sake kuyi mu’amala dashi.

Waro idanunsa yayi haɗe da sanya hanu ya shafi fuskarsa, “Masha Allah!” yafaɗa acikin zuciyarsa bayan yayi tozali da kyakkyawar fuskar Ziyada.

“Wow!! Raj ina kasamo mana wannan haɗaɗɗiyar baby’n haka? i hope dai ba kayan ka bace?” Ma’arouf yatambayi Sooraj yana mai sake ƙarewa fuskar Ziyada kallo, saboda yarinyar tayi matuƙar tafiya da imaninsa musamman ma Innocent face ɗinta.

“Kaya na?” Sooraj ya maimaita tambayar da Ma’arouf yayi masa abakinsa cike da mamaki.

Dariya Ma’arouf yayi haɗe da dawo da kallonsa ga Sooraj. Gira ɗaya ya ɗage masa haɗe da cewa

“To ya kagani idan da ace zata zama MALLAKINA?” 1

Murmushin gefen baki Sooraj yayi haɗe da cewa ” ko zaka jarraba hakan ?” yanayin yanda yayi maganar cikin halin ko inkula, shiya sanya Ma’arouf yin murmushi haɗe da kallon Ziyada wacce idan da za’a kasheta bata fahimci inda kalaman nasu suka dosa ba, ita hankalinta ma ba akansu yake ba.

“Zan jarraba idan kabani dama, amma bayanzuba zaifi kyau nayi kiwonta” Ma’arouf yafaɗi haka cike da shauƙi. 1

“Banda enough time zaka iya jan motar mutafi?” Sooraj yafaɗi haka ga Kamalu cike da halin ko inkula da zancen da Ma’arouf ɗin keyi.

Jin kalaman Sooraj yasa Kamalu saurin tada motar.

Ma’arouf dake tsaye yana kallon Sooraj yasaki murmushi haɗe da maida kallonsa ga kyakkyawar yarinyar dako sanin sunanta baiyi ba. Maida Glass ɗin window’n Kamalu yayi ya rufe, haɗe da yin reverse. Juyawa Ma’arouf yayi yakoma inda ya fito yana sakin wani murmushi.

Tunda suka hau titi ta sake baza idanunta wajen kalle kallen shukokin dake jere gefe da gefen titi, dogin gine gine masu kyau suketa wucewa, komai gwanin burgewa. 
Shikuwa tunda ya ɗauki jarida yamai da hankalinsa akai, ko ɗago kansa baiyi ba, sai dai har aƙasan zuciyarsa yanata juya kalaman Ma’arouf da yake tambayarsa “wai itaɗin kayansa ce?” Hmmm lallai yasake yarda babu wani wanda yasan sirrinsa, inbanda ma rashin aiki irin na Ma’arouf mai zaiyi da wannan ƴar mitsilan yarinyar? shi bayaji idan ma akwai wani abu acikin iskanci to zai samu atattare da ita, duka dukanta bata wuce 18 to 19 years ba to me zai ɗauka ajikinta? balle ma shikam mace kodaga wacce duniya tafito bazata amfanesa ta fannin mu’amala ba, saidai ko tawani ɓangare kamar aiki da sauransu.

Asokoro.

Gaban wani tangamemen gate mai kyau da tsari Kamalu driver ya tsaya haɗe da soma danna horn ɗin motar, da sauri wani daga cikin gidan ya wangale musu makeken gate ɗin, shikuwa Kamalu driver ya shigar da motan ciki.

Yana gama daidaita parking ɗin motar ya juyo ga Sooraj cike da ladabi yace “Ranka ya daɗe mun ƙaraso”

Batare daya ɗago kansa daga karatun jaridan dayake ba yace “Okay!” 
Fita daga cikin motar Kamalu driver yayi bayan ya ɗauki jakar Ogannasa ya yi cikin gida da ita.

Ganin yana ƙoƙarin fita daga cikin motar yasa itama ta buɗe murfin motar ta fito, compound ɗin gidan take ta kallo.

Kamar jela haka take biye dashi a baya, kafun yaƙaraso ma tuni Kamalu yasa key ya buɗe ƙofar da zata sadasu da cikin katafaren falon gidan.

Ganin ya buɗe ƙofar yashiga yasa itama ta bi bayansa Tana jefa ƙafafunta acikin falon suka soma nutsewa acikin wani lallausan carpet dake malale aƙofar shigowa falon, wani sanyin AC ne ya ratsata. Kamalu driver na ajiye jakan hanunsa ya fita daga cikin falon haɗe da rufo musu ƙofar, sam tamanta ma tare suke dashi, falon tashiga ƙarewa kallo, komai na cikin falon milk colour ne daga kan kujeru har zuwa kan labulaye, falo ne haɗɗaɗɗe mai ɗauke da tsari irin na mazan da suka san kansu.

Sooraj kuwa kota kanta baibi ba direct ɗakinsa ya wuce, yana shiga yarage kayan dake jikinsa haɗe da shigewa cikin bathroom. Al’adansane idan yaje wanka kafun yayi wanka sai ya kunna shower ruwa ya dakesa sosai, yau ma hakance ta kasance, sosai ruwan shower yadaki jikinsa, sannan yayi wanka.

Fitowa yayi daga cikin bathroom ɗin sanye da rigan wanka ajikinsa.

Akan kujeran dressing mirror ya zauna haɗe da ɗaukan comb yashiga taje sumar dake kansa wacce take a jiƙe da ruwa.
Yana kammalawa yayi amfani da handryer wajen busar da gashin kansa, hakanan yake shi mutum ne maison tara suma akansa, sannan kuma koda yaushe, askin kansa irin na turawa ne, shiyasa always yake yanayi dasu, sosai kuma askin keyi masa kyau, saboda gashin nasa yana da laushi, ga kuma gyaran da yakesha na mayuka masu tsadan gaske.

Sosai yake son combat trouser saboda hakanema yawancin wandunansa suka kasance Combat. Yanzu madai Combat jeans yasanya a jikinsa. kwanciya yayi akan makeken gadonsa, lumshe idanunsa yayi haɗe da jawo wayarsa ya saƙala earpiece akunnensa, waƙa yakeji mai sanyin sauti, hakan yasa duk yaji jikinsa yayi weak.

Jin ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Isha ne yasashi miƙewa, jallabia ya sanya ajikinsa, haɗe da zura flat shoe aƙafafunsa ya fice daga cikin ɗakin. 
*** *** ***

Biro ya ɗauka ya cike wata farar takarda dake aje kan babban table ɗin dake gabansa. Ɗaukar takardan yayi yashiga jujjuyata acikin hanunsa, kamar wani maiyin nazari, kallon katafaren office ɗinsa yayi haɗe da fitar da wani dogon numfashi ta bakinsa.

Hanu yasa ya shafi tarin sumar dake kansa, ware idanunsa da suka soma rikiɗa daga farare zuwa kalan ja yayi, wani zafi zafi ya keji aƙasan ƙirjinsa, ga wani zazzaɓi dake shirin dirar masa lokaci guda, haka yake aduk sanda yayi yunƙurin tuna wani abu da ya danganci sha’awa sai yayi wani zazzaɓi mai zafin gaske, abun yakan fin ƙarfin brain ɗinsa, duk yanda yaso yayi wani tunani mai ƙarfi abun ya faskara. Tashi yayi yanufi wata ƴar ƙaraman drawer dake cikin office ɗinnasa, buɗe drawer’n yayi haɗe da ciro wata allura, tun ɗazu ya haɗata amma hatsarin dake cikinta yasa yaɗan jinkirta yinta, shikansa baisan mai zai biyo baya ba idan yayi alluran, amma bashi da wani zaɓi wanda ya wuce yayi ta. 
akan jijiyar dake hanunsa na dama ya saita alluran, rumtse idanunsa yayi haɗe da soma matse ruwan alluran acikin jikinsa, yana gama yiwa kansa alluran ya buɗe durstbin ya jefa alluran aciki, suit ɗin sa dake rataye kan kujera ya ɗauka yariƙe ahanunsa, haɗe da ɗaukan wayoyinsa. Fitowa yayi daga cikin office ɗin haɗe da sa key ya rufe ƙofar office ɗin. Ta ƙofar baya yabi direct inda zai sadasa da parking space ya nufa, yana zuwa ya faɗa cikin motarsa, haɗe da kunnata yafice acikin Bank ɗin baki ɗaya….

Yanayin yanda yake murza steering motar kaɗai ya isa tabbatar maka da cewa ba ƙalau yake ba, saboda a slow yake tuƙa motar kamar wani wanda baida ishashshen ƙarfi ajikinsa, ahalin yanzu yakai wani stage da ko iya kallon gabansa bayayi sosai, idanunsa sun yi jajur dasu yayinda suka ƙanƙance alokaci guda, yanayin yanda yake danna horn ɗin motar ne yasa mai gadi ya yi saurin wangale masa gate, kashe motar yayi haɗe da kifa kansa akan steering motar. Jiyake gaba ɗaya duniyar na juya masa, gawani zazzaɓi da ya rufesa, hatta numfashinsa saida ya sauya. Da ƙyar ya iya buɗe murfin motar ya fito. Direct babban falon gidan ya nufa.

Tana zaune akan sofa ta ƙurawa TV plasma’n daketa aiki idanu, sosai kallon ya ɗauki hankalinta. Ahankali ya tura ƙofar falon ya shiga, idanunsa a lumshe haka yasoma takawa zuwa cikin falon, ɗago da manya manyan idanunta tayi ta kalleshi, kasa ɗauke idanunta tayi akansa ganin yanda yake tsaye kamar ma baya cikin hayyacinsa. Yana ɗaga ƙafansa yaji gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi komai nasa ya tsaya cak, take numfashinsa ya ƙwace mai, yanke jiki yayi ya faɗi a wajen baya ko numfashi.Arazane ta tashi daga zaunen da take haɗe da waro manya manyan idanunta. Lokaci guda jikinta ya ɗauki rawa, ƙafafunta na rawa haka ta nufi inda yake a yashe baya numfashi. +

Hanunta dake rawa ta ɗaga haɗe da kaiwa kan fuskarsa, hanunta tasa adai dai saitin hancinsa, saidai bataji abun da takeson jiba, wato numfashi.

Tsorone yasake kamata, hanunta ta ɗaura akan kafaɗunsa ta shiga jijjigasa, cikin wata irin murya mai ɗauke da tsantsar tsoro haɗe da ruɗewa tace. “Katashi ka buɗe idanunka Don Allah!” wasu hawaye masu zafi ne suka soma sulalowa daga cikin idanunta suna sauƙa akan fuskarta. Ganin jijjigashi da takeyi bazai kawo mata wata mafita ba, yasa aguje ta fice daga cikin falon, wajen mutumin dake zaune a bakin tankamemen gate ɗin gidan ta nufa. Yanayin yanda yaganta abirkice har yaso yaɗan tsoratashi. Kafun yace wani abu ta rigashi cikin haki tasoma cewa…. “Baya numfashi kataimakeni kada ya mutu!”

Zaro idanunsa waje Sammani mai gadi yayi cike da tsoro. Yana ƙoƙarin tambayarta meke faruwa, yaga ta sake rugawa aguje ta koma ciki. Cikin hanzari shima ya rufa mata baya.

Sake zube guiwowinta tayi a ƙasa haɗe da cigaba da jijjigashi, Dai dai lokacin Sammani mai gadi ya shigo, ganin Ogan sa kwance aƙasa baya motsi yasanyashi ƙarasowa cikin falon da sauri har yana jin tuntuɓe.

“Meke faruwa mekikayi masa?” Sammani dake a ruɗe ya tambayi Ziyada wacce gaba ɗaya hawaye sun gama wanke mata fuska.

Cikin tsoro tashiga girgiza kanta cikin sarƙewar murya tace.

“Wallahi banyi masa komai ba, bani bace, kawai nima gani nayi ya faɗi, Allah banyi masa komai ba!” Taƙare maganar tana mai fashewa da wani irin kuka mai sauti.

Da gudu Sammani yafita daga cikin falon, Kamalu driver yaje ya ƙira suka dawo falon a tare, hankalinsu amatuƙar tashe.

Da ƙƴar Kamalu driver da Sammani suka iya ɗaga Sooraj suka yi waje dashi, ganin haka yasa itama ta rufa musu baya, mota Kamalu ya buɗe suka sanyashi agidan baya.

“Kajira gidan, mu zamu kaishi asibiti” Kamalu driver yace da Sammani mai gadi. Kallon Ziyada da har yanzu idanunta ke fitar da ƙwalla yayi. “Muje” yace da ita yana mai buɗe mata murfin motar, da saurinta ta faɗa cikin motar shima Kamalun yashiga. Sammani ya buɗe musu gate suka fice daga cikin gidan, gudu sosai Kamalu keyi hakan yasa basu wani jima ba suka isa asibitin da yasan Sooraj ɗin nazuwa.

Da taimakon wasu likitoti aka ɗaura Sooraj akan wani gado mai ƙafafun taya, sannan aka gungurasa zuwa Emergency Room..

Kai Ziyada ta cusa acikin cinyoyinta, haɗe da sakin wani sabon kuka, addu’a take aranta Allah Yasa ba mutuwa yayi ba, hakanan takejinsa acikin wani ɓangare na jikinta, ko ba komai yayi mata hallacci, ya killace rayuwarta daga gurɓacewa, bazata taɓa son wani abu ya sameshi ba. 1

A Emergency Room kuwa sosai likitoti suka duƙufa akansa wajen basa taimakon gaggawa, da ƙyar suka samu suka shawo kan al’amuran, alokacin da suka gano matsalar kuwa baƙaramin mamaki sukayi ba, domin sun gano cewa allura akai masa ko yayiwa kansa, wacce take da mugun haɗari sannan tana da ƙarfin gaske, aƙalla idan a kayiwa mutum ita zai iya kaiwa sati ɗaya batare daya san inda hankalinsa yake ba, koda kuwa ya farfaɗo ba zai dawo cikin hayyacinsa da wuri ba, sai dai ma shi Sooraj ɗin yaci sa’a jininsa na da ƙarfi sosai, amma duk da haka ƙarfin alluran yayi tasiri acikin jikinsa. Drip suka ɗaura masa sannan suka wuce dashi wani ɗaki na musamman, kasancewar kusan duka likitotin asibitin sun sansa, don yana zuwa lokaci zuwa lokaci yana dubawa koda akwai waƴanda suke da buƙatar taimako shi yakan zuba dukiyarsa ya taimaka musu.

STORY CONTINUES BELOW


Dr.Haisam wanda yake ɗaya daga cikin manya manyan likitotin asibitin ya kalli Kamalu driver, dawo da kallonsa ya kuma yi ga Ziyada wacce har yanzu kuka take….

“Tare kuke ne?” Dr.Haisam ya tambayi Kamalu yana maiyi masa nuni da gefen da Ziyada’n ke zaune.

“Eh ƙanwar Oga ce” Kamalu driver yafaɗi haka, don ya rasa ma mai zai ce.

Kai Dr.Haisam yajinjina alaman gamsuwa, kallon Ziyada ya kumayi wanda itama a yanzu kallonsa takeyi.

“Biyoni Office” yace da ita yana mai nufar hanyar office ɗinsa.

Kallon Kamalu driver Ziyada tayi, kansa ya jinjina mata alamar ta bi Dr. Haisam ɗin, jiki a sanyaye tabi bayanshi.

Zama Dr.Haisam yayi akan kujera haɗe da yi mata nuni da wata kujera dage aje gabansa yace “Ta zauna”

A ɗaɗare ta zauna akan kujeran tana mai murje ƴan yatsun hanunta.

“Ya Sunanki?” Dr.Haisam ya tambayeta.

Murya araunane tace “ZIYADA”

Kansa yajinjina haɗe da maimaita sunan ZIYADA acikin ransa.

“Ki kwantar da hankalinki Ziyada, ki daina kuka kinji, yayanki zai warke insha Allah, Ina iyayenku suke? don yana da kyau na tattauna matsalan dake damunsa dasu”

Ɗago jajayen idanunta tayi ta kallesa, murya asanyaye tace.
“Basanan sunyi tafiya!” ita kanta batasan ya akayi taji ta furta wannan ƙaryan ba, sai dai kuma bata da wani abun da zata ce masa ne wanda ya wuce hakan.

Ajiyar zuciya Dr.Haisam yayi haɗe da cewa.

“Shikenan ba damuwa, amma a wannan yanayin yayanki yana tsananin buƙatar kulawarki, bazance miki zai farfaɗo a yau ko gobe ba, wannan na Allah Ne, amma ki zauna atare dashi ki basa kulawa har zuwa farfaɗowansa, idan drip ɗin da aka sanya masa ya ƙare kizo ki ƙirani saina cire masa ko”

Kanta kawai ta kaɗa masa alamar “To”

“Tashi kije” yace da ita yana mai ƙoƙarin haɗa wasu takardun dake kan table ɗin gabansa.

Tana fitowa Kamalu driver ya tambayeta wai me Dr.Haisam ɗin yace mata.

“Babu” kawai ta basa amsa ataƙaice, wata Nurse ce tazo garesu, kallon Kamalu driver tayi haɗe da cewa “Oga yace katafi ƙanwartasa sai ta kula dashi” kai Kamalu driver ya jinjina alaman gansuwa, sannan nurse ɗin ta wuce gaba Ziyada ta rufa mata baya.

Nurse ɗin na nuna mata ɗakin da yake kwance ta juya tayi tafiyarta. Ahankali tatura ƙofar ɗakin ta shiga.

Yana kwance akan gadon asibitin, kansa da jikinsa duk suna fuskantar sama, yayinda idanunsa kuwa suke a rufe ruf, wata na’ura ne mai kamar computer agefensa, yayinda aka saƙala masa wata ƴar waya da tafito daga jikin na’urar a ƙirjinsa. Wasu hawayene taji sun taru sun cika idanunta, wani irin tausayinsa ne mai ƙarfi ya ɗarsu acikin zuciyarta.

Ahankali ta taka har zuwa jikin gadon, kan kujeran dake kusa da gadonnasa ta zauna, a kusa da inda hanunsa yake ta ƙifa kanta. Kusan 30 minute ta ɗauka tana zaune a wajen, a hankali ta ɗago kanta haɗe da duban ledan ruwan da aka ɗaura masa, gani tayi saura kaɗan ruwan ya ƙare. Dawo da kallonta tayi zuwa jikinta, kwata kwata ta manta da shigan dake jikinta, baƙar doguwar riga ce ajikinta mai dogon hannu, sai kuma mayafin rigan dake ɗaure akanta, warware mayafin rigan tayi da yake yana da girma ta rufe jikinta dashi, fita daga cikin ɗakin tayi, da ƙyar ta iya gane office ɗin Dr.Haisam, yana zaune tashigo tasanar masa cewa ruwan yakusa ƙarewa..

Cire masa ledan ruwan Dr.Haisam yayi kana ya barsa sai zuwa anjima asake sa wani.

Dr. Haisam na fita daga cikin ɗakin tasoma jin ƙiran sallan Magriba, wanda yake fitowa daga cikin masallacin dake gefen asibitin.

STORY CONTINUES BELOW


Kallon ƙofar da Dr.Haisam yace mata nanne banɗaki tayi, ahankali tatura ƙofar tashiga, banɗaki ne mai kyau da tsafta, gaban sink taje ta ɗauro alwala sannan ta fito.

Tsayawa tayi tana nazarin yanda za’ayi tayi sallah babu sallaya, duk da cewa rayuwar rashin ƴanci da kuma ƙauyanci tayi, hakan baisa ta zamo mace mai wasa da sallah ba, duk da bawani ilimi take dashi akan addini ba, amma tana kyautata zaton wajen bazaiyi sallah ba idan har ba a shumfuɗa sallaya ba, kallonsa tayi yananan dai a yanda yake, ahankali ta ƙarasa jikin gadon, aƙalla ta ɗauki sama da 7 minute tana kallonsa, jitayi duk ƙwalla suncika idanunta, buɗe ƙofar ɗakin tayi ta fice. Tana fita daga ɗakin taga wata nurse zata wuce, da sauri ta ƙarasa gareta haɗe da gaisheta.

Amsa mata gaisuwar nurse ɗin tayi tana mai ƙare mata kallo.

“dama Sallah zanyi shine kuma banda sallaya ko zaki ɗan aramin” Ziyada ta tambayi nurse ɗin tana mai sanya mata fuskar tausayi.

“Biyoni muje ki amsa” nurse ɗin tafaɗi haka tana mai ci gaba da tafiyarta. Sallaya hadda Hijab nurse ɗin ta bata, ta kumace ta riƙe a wajenta zuwa gobe, godia Ziyada tayi mata sannan tadawo ɗaki, shumfuɗa sallayan tayi haɗe da tada Sallah. Sosai ta jima a sujjadanta na raka’an ƙarshe, addu’a tayi sosai akan Allah yabawa Mai taimakonta lafiya. “Mai Taimako” shine sunan da Ziyada ta raɗawa Sooraj acikin zuciyarta. Tananan zaune akan sallayan har aka ƙira sallan Isha.. Shima a sujjadan ƙarshe saida tajima tana addu’a kafun ta ɗago. Shiru haka ta zauna akan sallayan haɗe da jingina bayanta ajikin bango. Har ƙarfe 9 Ziyada na zaune agefen gadon, sannu ahankali yunwa ke ƙwaƙulan cikinta, gyan gyaɗi ta fara mintuna kaɗan bacci ya ɗauketa. Cikin dare Sanyin AC ya dameta, tashi tayi ta lulluɓe jikinta sannan ta koma bacci.

Washe Gari.

Tunda ta tashi da asuba tayi sallah, wani bacci yasake ɗaukanta, ba ita ta farka ba sai wajen ƙarfe 8 na safiya. Ban ɗaki ta wuce taje ta wanko fuskarta, tana zama akan kujera Dr.Haisam ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, gaishesa tayi cike da girmamaw, fuskarsa ɗauke da murmushi ya amsa mata.

Checking ɗin Sooraj ya sakeyi, yaji daɗin ganin komai Normal kuma zai iya farfaɗowa ako wani lokaci.

Hannayenta ta ɗaura akan kumatun ta haɗe da kafesa da manyan manyan idanunta, kyakkyawar fuskarsa take kallo, babu wani abu dayafi saurin ɗaukar hankali akan fuskarsa kamar yalwataccen sajen sa, wanda yake baƙi siɗik, ga zara zaran eye lashes ɗinsa da suke a mimmiƙe, sosai suka ƙarawa fuskartasa kyau, hakan yasa bata taɓa gajiyawa da kallonsa…

Wasa Wasa har ƙarfe 5 na yamma Sooraj bai farfaɗo ba, haka Ziyada ke zaune awajensa, batare da ta ci wani abu wai sunansa abinci ba, ruwa kawai take ta zubawa cikinta. Tun yunwar na damunta har tazo ta daina ji, yanzu bata da wani buri daya wuce taga Mai Taimakonta ya buɗe idanunsa.

9:30 pm Babbar yatsan ƙafarsa ta dama ne ta soma motsawa sai kuma yatsun hanunsa, sannu sannu bugun zuciyarsa ta dai dai ta, yayinda cikin sakannin da basu wuce huɗu ba brain ɗinsa ta soma aikin.

Ahankali ya soma buɗe idanunsa, da kaɗan kaɗan yake ware idanun nasa hakan yasa ya soma ganin komai dishi dishi. Sannu ahankali idanun nasa suka washe, kallon saman ɗakin daya gansa aciki ya soma yi. Sake ɗan lumshe idanunsa yayi, komai daya faru ya dawo cikin kansa, ɗan yunƙurawa yayi ya tashi zaune haɗe da jingina bayansa da pillow, juyo da kansa yayi zuwa gefen damansa, idanunsa suka sauƙa akanta, tana zaune akan sallaya ta jingina bayanta da kanta a jikin gadon da yake, bacci takeyi cikin yanayi na takura, da dukkan alamu bata shiryawa baccin ba ya ɗauketa, domin kuwa hadda goran ruwa riƙe ahanunta, ƙurawa fuskarta idanu yayi, hango wasu zanen busassun hawaye yayi kwance akan fuskarta, kallon yanda ɗan ƙaramin bakinta ke ɗan buɗe yayi. Janye idanunsa yayi daga kanta, haɗe da ɗan tattaro ragowan ƙarfin daya rage masa ya sauƙo daga kan gadon.

Ƙofar da yake tunanin nanne toilet ya nufa, yana shiga ya soma rage kayan jikinsa. Kunna shower yayi ya tsaya ruwa ya dake shi sosai. Dogon wandonsa kawai ya maida batare da ya sanya rigar shi ba ya fito daga cikin toilet ɗin.

Zama yayi abakin gadon haɗe da sanya hanu ya dafe kanshi dake yi masa ciwo sosai, hakanan yakejin shi wani iri, gaba ɗaya babu wani isashshen kuzari ajikinsa, yasan hakan kuma duk yana daga cikin sharrin Alluran da yayiwa kan shi ne.

Kallon shi ya kuma maidawa zuwa gareta, har yanzu tananan tana wahalallen baccin daya ɗauketa, gaba ɗaya jikinta a tukuikuye yake da Hijab, tashi yayi ya ƙarasa jikin window’n ɗakin, hanu yasa yaɗan buɗe labulen window’n kaɗan, gani yayi gaba ɗaya duhu ya mamaye sararin samaniya, hanu yakai yashafi aljihun wandon dake jikin shi, atunanin shi wayar shi na tare da shi. sai dai kuma saɓanin haka yaji shi wayam, ɗan kalle kalle yasomayi acikin ɗakin ko zai hangota amma baiganta ba, komawa yayi ya zauna akan gadon yana mai lumshe idanunsa, saboda wani juwa da yaji yana neman ka da shi. Aƙalla yakusan mintuna goma idanunshi suna lumshe, jin da yayi juwan yasoma lafawa ne yasanya ya tashi tsaye, inda take zaune ya nufa, tsayawa yayi akanta ya kasa ta ɓuka komai. Ɗan ranƙwafowa yayi ya ɗagota caɗak, kan gadon da aka ajiye musamman don taya majinyaci kwana ya ɗaurata, a hankali ya zare hijab ɗin dake jikinta ya ajiye mata shi agefe. Ziyada da baccinta yayi nisa sam batasan meke faruwa ba, saima ƙara gyara kwanciarta da tayi, sakamakon jin ta samu sauyin makwanci. Komawa kan nashi gadon yayi ya kwanta, lumshe idanunsa yayi bawai kuma don yanajin bacci ba saidan kawai babu wadataccen ƙarfi ajikinshi..

Yatsun ƙafanta ya ƙurawa ido, azahirin gaskiya yatsunnata yake kallo, amma kuma hankali da tunaninsa ba agareta suke ba, yayi nisa acikin wani tunanin daban, baiso ace ya biyewa zuciyarsa ba, baiso ace ya kasa haƙurin ɗaukar ƙaddaransa ba, duk da cewa shiɗin mai raunine amma yana fatan dacewa anan gaba, saidai aduk sanda yayi wannan tunanin sai wata zuciyar ta gargaɗesa da kada ya yaudari kansa, dolensa haka yake haƙura ya watsar da tunnin acikin ransa.

Buɗe gajiyayyun idanunta tayi, ganin haske tarwal acikin ɗakin yasa ta tashi aɗan zabure, kallonta takai wajen window gani tayi har hasken rana yasoma bayyana ta jikin window’n. Da sauri ta zuro ƙafafunta daga kan gadon, dai dai lokacinne kuma idanunta suka sauƙa akansa, yana kwance ya bata baya.

Sake waro idanunta tayi haɗe da mutsutstsukasu atunaninta ko gigin bacci takeyi ganinsa da tayi babu riga, bayan koda zata kwanta tabarshine sanye da riga ajikinsa. “Kodai likita ne yazo ya cire masa riga’n tana bacci bata sani ba?” tambayar da tayiwa kanta kenan.

Ahankali ta sauƙo daga kan gadon, cikin sanɗa tataka harzuwa inda yake kwance.

Kanta ta ɗaura ajin gadonnasa, lokaci guda idanunta suka kawo hawaye murya araunane tace.

“Mai Taimakona Allah yabaka lafiya, tausayinka nakeji sosai, banso wani abu ya sameka!” taƙare maganar daidai lokacin da hawayen dake cikin idanunta suka samu daman gangaro zuwa kan fuskarta, daidai lokacinne kuma shima da tun tashinta zuwa yanzu yanajin abun da takeyi ya ɗan buɗe idanunsa kaɗan….Wani numfashi mai ɗumi ya fesar daga bakinsa, haɗe da maida idanunsa ya rufe, kalamanta ne suka shiga yi masa yawo acikin kunnuwansa, ji yayi tsikar jikinsa na tashi, hakanne ma yasa ya kasa yin koda kyakkyawan motsi ne. +

Ban ɗaki ta wuce ta je ta ɗauro alwala, sam bata san ya akayi bacci ya ɗauketa ba, taso ace bata makara ba, kasancewar yanzu har hasken rana ya bayyana. Tana idar da sallan ta gyara zamanta akan sallayan, sai alokacinne ta tuno da cewa aƙasa ta kwanta ba akan gado ba, “To kenan ya akayi ta koma kan gado?” tambayar da tayiwa kanta kenan, ƙaran buɗe ƙofar ɗakin da akayi ne ya katse mata tunaninta. Dr.Haisam ne yashigo cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, amsa masa tayi haɗe da gaidashi. Fuska asake shima ya amsa mata gaisuwar. Ƙarasawa gaban gadon da Sooraj ɗin ke kwance yayi. “Ya jikinna ka dai?” Dr.Haisam ya tambayi Sooraj wanda har yanzu bai sauya kwancia daga juya bayan da yayi ba.

Ziyada nashirin ce da Dr.Haisam bai farfaɗo ba, taji muryarsa ta doki dodon kunnenta.

“Da sauƙi!” Sooraj ya bashi amsa ataƙaice, sai alokacin ya juyo ya fuskanci Dr.Haisam ɗin.

“Masha Allah dama kullum haka mukeso, yanzu babu wani inda yake maka ciwo?” Dr.Haisam yatambayeshi cike da kulawa.

“Babu” ya bashi amsa ataƙaice.

“Masha Allah zamu baka sallama zuwa anjima, amma yana da kyau ka riƙa kulawa da lafiyarka, kasan fa lafiya itace komai arayuwa, sai da itane mutum yake sanin daɗin rayuwa, saboda haka kakiyaye abun da zai cutar dakai!”

Kai kawai Sooraj ya jinjina alamar yaji, sam baison magana mai tsawo.

Kallon Ziyada dake zaune tana kallonsu Dr.Haisam yayi. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace. “Congrat ƴar ƙaramar ƙanwa, da alama brother ɗinki ya samu lafiya”

Murmushin daya bayyana kyawun fuskarta tayi haɗe da sunkuyar da kanta ƙasa, hakanan taji wani irin sanyi acikin ƙirjinta. Dr.Haisam na fita ta ɗago da kanta takai dubanta ga Sooraj wanda yake ta murza fatan hanunsa, kallon yanda jijiyoyin jikinsa suka fito sukayi raɗa raɗa tayi, gani tayi ya sanya haƙoransa ya danne lip ɗinsa na ƙasa, tamkar wani wanda yakejin wata azaba ta daban, tashi tayi daga kan sallayan cikin sanɗa tashiga takowa zuwa inda yake.

Muryarta na rawa tace “YAH…YAH!!” ita kanta batasan ya akayi ta ƙirasa da wannan sunan ba.

Cak ya tsaya daga murza hanunnasa da ya keyi haɗe da buɗe idanunsa da suka zama jajur dasu, ɗago da kansa yayi ya kalleta.

Sai da taji gabanta ya faɗi alokacin da idanunsa suka sauƙa acikin nata idanun, bakomai ya tsorata ta ba kamar yanda taga idanunsa sun rikiɗe daga farare zuwa jajaye.

Ko second biyu bai ɗauka ya na kallonta ba ya sauƙe idanunsa ƙasa.

Ƙwalla ne suka cika idanunta, murya araunane tace “Dama…. dama.. Bansani ba ne ko kanajin yunwa” tafaɗi haka tana mai murza ƴan yatsun hanunta.

“Miƙomin rigana” yafaɗi haka batare daya ɗago kansa ko ya tanka mata maganan da takeyi ba, babu musu ta ɗauko rigan nasa tazo ta miƙa masa, tashi tsaye yayi daga kan gadon haɗe da sanya rigarsa, Kallon ƙafansa ƴayi yaga ko takalmi baida shi. Hanu yasa ya dafe goshinsa.

STORY CONTINUES BELOW


“Ina wayata?”
yayi mata tambayar yana mai tsareta da idanunsa.

“Wayanka?” tafaɗa tana mai rarraba idanunta.

Yanayin yanda tayi maganar ne yasashi ƙanƙance idanunsa haɗe da ware su alokaci guda.

“Wa ya kowani nan?” ya tambayeta yana mai ƙoƙarin maƙala aninayen dake gaban rigarsa.

“Ni da Kamalu driver ne” tabashi amsa tana mai wasa da ƴan yatsun hanunta.

Ɗauke kansa kawai yayi daga kallonta, dai dai lokacin Dr.Haisam yashigo cikin ɗakin.

Sooraj na ganinsa yace “Ko zan iya samun aron waya?”

Murmushi Dr.Haisam yayi haɗe da cewa “Eh” ciro wayarsa yayi ya miƙawa Sooraj ɗin.

Number’n Khalid yasanya acikin wayan Dr.Haisam haɗe dayin dialing. Ringing biyu Khalid yaɗauki ƙiran, “Ina Mahfuz Specialist Hospital, kazo kayi dropping ɗina a gida” Baijira mai Khalid ɗin zaice ba ya kashe wayan, miƙawa Dr.Haisam wayar yayi. Takardan sallamansa Dr.Haisam ya miƙa masa.

Mintuna kaɗan Khalid ya iso cikin asibitin. Yana shigowa ɗakin, cikin tashin hankali ya kalli Sooraj cike da kulawa yace “Raj maiyasa meka haka, harda zuwa asibiti?”

Murmushin gefen baki Sooraj yayi haɗe da cewa ” stress ne kawai, muje ko” yaƙare maganar cikin yanayi na ƙosawa.

Motar Khalid suka shiga, suna zaune agaba ita kuma tana zaune agidan baya, Khalid ne ke ta tambayar Sooraj jikin nasa cike da kulawa, amma kuma shi Sooraj ɗin cikin halin ƙosawa yake mayar masa da amsa.

Suna isowa gida Khaleed yayi musu sallama ya koma, dama aiki yabari a office ɗinsa ya zo.

Wanka yayi haɗe dayin brush sai alokacin yaji wani ɗan iskan yunwa na ƙwaƙulan cikinsa, dogon wando yasanya da wata riga marar nauyi, kana ya zura slippers ɗinsa ya fita zuwa falo.

Direct kitchine ya wuce, ruwan zafi ya tafasa haɗe da juyewa acikin flask. Cup ya ɗauka ya haɗa tea, hannayensa ya sanya akan waist ɗinsa, yana ƙarewa kitchine ɗin kallo. itace ta faɗo masa arai, yasan gaba ɗaya zaman yunwa tayi acikin a asibitin.

Ruwan zafi ya ɗaura akan gas, mintuna ƙalilan ruwan ya tafasa indomie ya jefa acikin ruwan haɗe da sanya spiece. yana tsaye acikin kitchine ɗin, har Indomie ɗin ya nuna, acikin wani plate na tangaran mai kyau ya juye indomie’n. hanunsa riƙe da plate da kuma cup ɗin tea ɗin ya fita zuwa falo.

Zaune take akan gado, tayi jigum fitowanta daga wanka kenan, ta sanya wani riga da sket ƴan kanti. Zuwa yanzu idanunta har sun soma rufewa sbd yunwa, gaba ɗaya ƙarfin jikinta ya gudu, duk da zama da yunwa ba sabon abu bane a wajenta.. 
Wani irin murɗawa taji cikinta nayi. Hanu yasa ajikin ƙofar ya ƙwanƙwasa, batare daya jira anbuɗe ƙofar ba ya juya ya koma cikin falon. Zama yayi akan kujera haɗe da ɗaukan cup ɗin tea ɗinsa ya soma sipping da kaɗan kaɗan.

Cikin rashin ƙarfi ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito, ganinsa zaune a falon yasa ta nufo cikin falon.

Durƙusawa tayi agabansa, kafun tace wani abu, ya turo mata plate ɗin imdomie ɗin gabanta.

Ɗago da kanta tayi ta kallesa, gani tayi kwata kwata idanunsa ba’akanta suke ba. Ɗaukan plate ɗin tayi ta ɗaura akan cinyarta, loman farko da tayi ta lumshe idanunta, wanda suke cike da gajiya da kuma bacci, sosai takecin indomie’n harta manta ma da cewa agabansa take.
Duk abun da takeyi yana lure da ita, duk wani motsin da tayi yana kallonta ta gefen idanunsa. Bata gama cin indomie’n ba har ya kammala shan tea ɗinsa yatashi yabar wajen, tana kammala cin indomie ɗin taji wata nutsuwa ta sauƙar mata, ɗaki ta koma tana kwanciya bacci yaɗauketa.

*** *** ***

Tun tashinta yau ta riga da ta gyara ɗakin da take kwana tsab, hakanan taji sha’awar shiga kitchine ɗin gidan, gani take kamar wahala take bashi don kullum saiya saya mata abun da zata ci, duk da cewa baya wuni agidan amma yana turowa ana kawo mata. Yanzu rabonma da ta sanya shi acikin idanunta kusan kwana biyu kenan. 1

Tsayawa tayi a kitchine ɗin tana ƙarewa ko ina da ina kallo, ita sam bata wani iya girkin zamani ba, shinƙafa kawai ta iya dafawa, wata drawer dake cikin kitchine ɗin ta buɗe, kayan abinci ta gani shaƙe acikin drawer’n, ruwa ta ɗaura akan gas, wanda da ƙyar ta iya kunnasa, saura ma kaɗan wuta ya kama hanunta. neman inda zata samu kayan miya tashiga yi, saidai neman duniya tayi bataga wani abu mai kama da kayan miya a kitchine ɗin ba, dolenta haka ta kashe gas ɗin ta fito daga kitchine ɗin.

Fitowarta yayi daidai da shigowarsa cikin falon. Sanye yake da suit coffee colour, ya yinda ƴar cikin rigan ta kasance milk colour, Sosai yayi kyau. Har batasan sanda tasake baki tana kallonsa ba.

Kallonta yayi tare da kawar da kansa gefe. “Ɗauko mayafinki” yace da ita ataƙaice.

Babu musu ta koma ɗaki ta ɗauko mayafinta.

Tafiya suke kowannensu da abun dayake saƙawa acikin zuciyarsa. Gaban wani tangamemen gate taga sun tsaya yayinda yasoma danna horn ɗin motar. Wangale musu gate ɗin akayi ya tura hancin motar ciki. adai dai wani ƙaton parking space ya yi parking motar. “Muje” yafaɗa yana mai ƙoƙarin buɗe murfin motar, yana gaba tana biye dashi abaya, gaba ɗaya hankalinta naga tsirarun mutanen da tagani suna shawagi a tafkeken farfajiyan wajen, daga mata har mazan dake wajen sanye suke da uniform maroon and milk colour. Direct office ɗin Mr. Isyaka Nuhu suka nufa, har cikin office ɗin akayi musu iso. Cike da mutuntawa Sooraj yabawa Mr. Isyaka Nuhu hanu suka gaisa. Fuska cike da fari’a Mr.Isyaka Nuhu ya dubi Ziyada haɗe da dawo da kallonsa ga Sooraj. “Wannan itace yarinyar?” Ya tambaya.

“Eh” Sooraj yabasa amsa.

Wayarsa ya ɗauka haɗe da danna ƙiran wata number, yanajin an ɗaga ƙiran yace “Kasameni a office ɗina” yana aje wayar bawani jimawa saiga wani mutumi yashigo cikin office ɗin.

Kallonsa Mr.Isyaka Nuhu yayi haɗe da cewa.

“Kuje da yarinyarnan kayi mata interview”

“Okay Sir!” mutumin daya shigo ya faɗi haka haɗe da kallon Ziyada yace “Muje ko”

Kallon Sooraj tayi saidai kuma taga sam idanunsa ba akanta yake ba, wayarsace ma ahanunsa yana dannawa..Basu wani jima ba suka fito daga ɗakin da akeyiwa duk wani ɗalibi da yakasance sabon zuwa interview. Direct office ɗin principal ɗin suka koma zuciyar Ziyada cike take da farinciki da kuma jin daɗi, addu’anta ɗaya Allah yasa hasashen da takeyi yazamanto gaskia. +

“Har kun gama interview ɗin?” Mr. Isyaka Nuhu ya tambayi Sir. Yusuf wanda shine ke yiwa duk wani sabon ɗalibi dazai shigo makarantar interview.

“A’a Sir ai ma bata taɓa zuwa makaranta ba, inaga kawai sai dai afarayi mata lesson”
Sir.Yusuf yafaɗi haka cikin siga irinta bada shawara.

Jinjina kai Mr. Isyaka Nuhu yayi haɗe da dawo da kallonsa ga Sooraj wanda har yanzu wayarsace riƙe ahanunsa yana latsawa.

“To kaji abun da yace, ya kagani ko za’a fara yi mata lesson ɗin, idan ta ɗan soma iya wasu abubuwan sai abata ko s.s.one ne”

Sai alokacin ya ɗago kansa, wannan murmushin nasa da baya wuce kan laɓɓansa yayi haɗe da cewa. 
“Bakomai hakan yayi, yaushe za’a fara lesson ɗin?”

“Ai tunda kusan munkammala komai ko yau ma idan kun shirya sai afara yi mata” Inji cewar Mr. Isyaka Nubu (Principal).

“Okay ba damuwa, ni zan wuce” Sooraj yafaɗi haka yana me miƙewa tsaye, hanu yabawa Principal ɗin sukayi musabaha, kana yabawa Sir. Yusuf ma suka gaisa, ko kallon gefen da take baiyiba ya fice daga cikin office ɗin.

Principal ne yace da Sir.Yusuf suje ya samo mata malamin lesson su fara tun 


yau, hakan kuwa akayi, Wani Teacher Abdallah Sir.Yusuf ya samo mata, wanda shine zaina koyar da ita lesson everyday, hatta ranan saturday da sunday zai na zuwa koya mata gida, domin biyanshi za’ana yi.

abubuwa masu sauƙi Teacher Abdallah yafara koya mata, sam babu wani abu da ta fahimta tana dai jinsane kawai, duk kuwa yanda taso ta fahimci abubuwan sam ƙwaƙwalwarta takasa ɗauka.
***
Zaune yake atamfatsetsen office ɗinsa, dagashi sai dogon wandon suit da kuma rigan parking shirt dake sanye ajikinsa, laptop ɗinsa ne agabansa yana shigar da wasu bayanai gaba ɗaya hankalinsa nakan laptop ɗin, turo ƙofar office ɗin akayi tare da shigowa, yaji motsin buɗe ƙofar amma sam baiɗago kansa ya kalli wanene ya shigo cikin office ɗin ba, yau sosai ƴan miskilancin nasa suke kusa.

Jingina bayanta tayi da jikin ƙofar tana kallonsa, wani irin murmushine ya bayyana akan fuskarta, kallonsa kaɗai idan tayi yakan sanya mata nutsuwa, sosai take jin son sa acikin ranta, komai nasa yana burgeta tana son duk wani abu nasa, musamman yanayin yanda yakeyin adonsa, uwa uba kuma kyau da kwarjininsa dake tafiya da imanin duk wata mace da zatayi tozali dashi, cikin takunta nason ɗaukar hankalinsa tasoma takowa zuwa cikin office ɗin. Ƙaran takalman dake ƙafanta shiya fara sanar dashi wacce ta shigo cikin office ɗin nasa, jiyayi wani abu ya toshe masa maƙoshi, sam yatsani ganinta ko kaɗan bayaso tana raɓarsa, baisan ita wace irin mace bace wacce bata da zuciya ko kaɗan. Harta ƙaraso gaf da inda yake bai ɗago dakansa ya kalleta ba, cikin muryar shagwaɓa tace.

“Barka da hutawa ranka ya daɗe”

Kamar ma baisan da mutum a wajenba haka yayi banza da ita, bakinta da yaji pink lips stick taturo gaba. “Maiyasa kakemin hakane wai Raj? at least dai ko kallona yakamata ace kayi wajenka fa nazo” taƙare maganar tana ɗan bubbuga ƙafafunta, alaman shagwaɓa.

STORY CONTINUES BELOW


Sai alokacin Sooraj ya ya ɗago kansa, saidai bai kalli inda take ba. “Kina da buƙatar wani abu ne?” yatambayeta ata ƙaice.

“Kainake da buƙata Raj, wallahi kainake da buƙata, kafi kowa sanin yanda na damu dakai, maiyasa kake min haka ne? kadubeni Raj nacika mace irin wanda take girgiza zuciyoyin maza amma maiyasa bazaka dubeni ba? na amince ma kayi duk wani abun da kakeso dani amma maiyasa bazaka amince min ba!” taƙare maganar kamar zatayi kuka.

Murmushin gefen baki Sooraj yayi haɗe da tashi ya ƙarasa gaban fridge, buɗewa yayi ya ɗauko ruwa mai sanyi, saida yasha sosai kafun ya sauƙe goran ƙasa, inda suit ɗinsa ke aje ya nufa, ɗaukan suit ɗin yayi ya saƙala ahanunsa, touch watch ɗin dake hanunsa ya duba, gani yayi akwai sauran time sosai kafun lokacin tashinsa ya cika, amma a yanda Aneesa tashigo masa office baya jin zai ƙara mintuna biyu acikin office ɗin.

Wayarsa ya ɗauka haɗe da rufe laptop ɗinsa, juyawa yayi ya nufi ƙofar fita yana mai karkaɗa key ɗin motarsa dake riƙe a hanunsa.

Da sauri Aneesa tasha gabansa, idanunta cike da ƙwalla tace “Please Raj ka tsaya atare dani, kasani kaine burina da kuma fatana, maiyasa kakemin haka ne?” hawayene suka gangaro daga cikin idanunta.

Sai alokacin Sooraj ya ɗaura idanunsa akanta, kallonta yayi tun daga samanta har zuwa ƙasa. sannan yasaki wani killer smile.

“Bani hanya na wuce” ya faɗa mata haka cikin halin ko inkula.

“Bazan baka hanya ba Raj, harsai kamin abinda nakeso, please Raj kasani akullum da buƙatarka nake kwana, please kabani dama ko sau ɗaya ne.”

Ƙanƙance idanunsa yayi haɗe da tamke fuskarsa alokaci guda, cikin takaici yasanya hanunsa ya turata gefe, harsai da kanta ya bugu da bango, ƙofar office ɗin ya buɗe ya fice abunsa.

Kuka Aneesa tasanya mai ɗauke da tsananin ɓakin ciki da takaici, takardun dake kan table ɗin office ɗin ta soma watsarwa a ƙasa tana kuka, ta tsani wannan banzan halin na Sooraj, a kullum baida wani buri da ya wuce ya wulaƙantata, mai tarasa wanda har zai tsaneta haka? alƙawari tayiwa kanta matuƙar ta rasa Sooraj to kowacce mace aduniya ma tarasashi domin bazata taɓa ɓari ya auri wata mace ba idan ba ita ba.

Yana fita ya wuce wajen da yayi parking motarsa, sama sama yake amsa gaisuwar ma’aikatan dake gaidasa. Yana shiga cikin motar yayi mata key haɗe da ficewa daga cikin bank ɗin, direct wani hotel ya nufa……

Sosai Teacher Abdallah ya dage ya zuba mata lesson, lokacin da aka kaɗa ƙararrawan tashi ga duka ƴan makarantan dai dai lokacin shima ya dakata daga koyar da ita english lesson ɗin da ya keyi. Tana fitowa ƙofar ajin taga cincirondon ɗalibai maza da mata kowa na ƙoƙarin kama gabansa, ko ta ina acikin makarantar ɗalibaine, yayinda parking space ɗin makarantar kuwa ke cike da tarin motoci, har waje motoci ne a fake, duk wani ɗan makarantan dazaka kalla, kallo ɗaya zakayi masa ka hango alamun zaman naira ajikinsa, domin daga mata har mazan gaba ɗayansu ƴan gayu ne, da alama kuma kowa yanaji da kansa.

Kamalu driver ta hango ya nufo inda take, wata ajiyar zuciya ta sauƙe, domin kuwa da har tafara tunanin yanda za ayi ta koma gida ita kaɗai.

Gaba ɗaya yau tsananin farincikinta ya kasa ɓoyuwa, jinta take cikin farinciki. Haka ta koma gida zuciarta cike da jin daɗi. Wunin ranan gaba ɗaya haka tayishi cikin jin daɗi, duk yanda taso ganinsa tayi masa godiya abun yaci tura, domin kuwa ko motsinsa bata jiba

*** *** ***

Kullum sai Ziyada taje Lesson Kamalu driver ne ke kaita shine kuma ke dawo da ita, sosai ta kejin daɗin lesson ɗin nata, yanayin yanda ta dage tasanya son karatun acikin ranta shi ya ƙara sanya teacher Abdallah dagewa wajen ganin ya koyar da ita yanda zata fahimta, zuwa yanzu dai tana ɗan fahimtan abubuwa da kaɗan kaɗan, musamman ma wajen karatun Hausa da kuma rubuta shi, ta ɗan ƙware ta wajen wannan fanni, har ma idan taga abu zata iya karantashi, English ɗinne dai sai a hankali.

STORY CONTINUES BELOW


Tun ɗazu aka tashe su saidai ga mamakinta yau Kamalu driver baizo ɗaukanta ba, gashi ɗaliban da suka rage acikin makarantar basu wuce ƴan tsiraru ba sam basu da wani yawa. Kalle kalle take tayi ko zata hango Kamalu driver amma babu shi babu alamarsa. Tsaye take a harabar makarantar, sanye take da doguwar riga da kuma Hijab, hannayenta nannaɗe suke akan ƙirjinta.

Tun daga nesa yayi parking ɗin motar, jingina bayansa yayi da jikin kujeran motar haɗe da lumshe idanunsa, ahankali ya ware idanunsa haɗe da sauƙesu akanta, hakanan ya tsinci kansa da tsaida idanunsa akanta, kusan 2 minute ya ɗauka yana kallonta, mai da idanunsa yayi ya rufe, wani irin gajiya haɗe da kasala ne yaji sun sauƙar masa alokaci guda. Buɗe murfin motar yayi haɗe da zuro ƙafafunsa waje. Tun fitowarsa daga cikin motar idanun ɗaliban da ke wajen ya dawo kansa. Yanayin yanda yake taku cike da nutsuwa shine abun daya burgeta, har batasan sanda ta saki wani murmushi ba. Yana ƙarasowa inda take yace.

“Kijirani a mota” baijirayi mai zata ce ba, yayi gaba abunsa, tana kallonsa ya shige cikin office ɗin principal. Juyawa ita tayi ta nufi inda ya aje motar tasa, jingina tayi da jikin motar tana jiran zuwansa. Baiwani jima ba ya dawo hanunsa riƙe da wata leda.

Tunda suka ɗauki hanya babu wanda yace da ɗan uwansa wani abu kowa da irin tunanin da yake saƙawa acikin zuciyarsa, yarda da abun da zuciarta ke gaya mata da tayi yasanya ta gyara zama cikin wata murya mai sanyi tace. “Nagode Yaya”

Bai kalli inda take ba, bai kuma tanka mata ba, jin yayi shiru bai ce da ita komai ba yasa taji jikinta yayi sanyi. Saidai kuma kamar daga sama ta tsinkayi muryarsa. .

“Waye yayan naki?” yafaɗa cikin tsare gida, batare daya kula sashin da take ba.

Jin tambayar nasa yasa ta ɗago da kanta ta kallesa, tsintar kanta tayi da kasa ɗauke idanunta akansa, musamman ma data ga hankali da idanunshi ba akanta suke ba.

“Kallon kuma fa?” yafaɗa adaidai sanda yake shiga wata kwana, da zata sadasu da gida.

Da sauri ta janye idanunta daga kan nasa azuciyarta tanajin wani iri…..

Monday.

Yau ne zata fara shiga Class itama tayi karatu kamar yadda ko wanni ɗalibi keyi. Fitowarta daga wanka kenan. Ledan daya bata jiya da dare ta ɗauko, kayan shafa ne aciki sai kuma uniform da takalman makarantar ta. gefe kuwa wasu biscuit ne manya manya.

Sama sama ta shafa mai ajikinta, babu powder bare wata uwa kwalli haka tabar fuskarta, uniform ɗinta wanda suke riga da wando ta sanya, wandon irin mai tsukakken ƙafannan ne amma ba har canba, yayinda tsawon rigan ta kasance har zuwa guiwarta, rigan milk colour ce, wandon kuwa shike da kalan maroon. Warware hijab ɗin makarantar tayi tana ƙare masa kallo, bashi da wani girma da kaɗan tsawonsa ya wuce cikinta. Tana sanya hijabin taje gaban makeken mirror’n dake ɗakin ta tsaya tana mai kallon kanta aciki, duk da cewa uniform ne amma sosai tayi kyau, white skin ɗinta yasake fitowa acikin maroon colour hijab ɗin, jinta tayi awani ta kure, sam batajin zata iya sakewa acikin mutane da irin wannan shigartata, sam bata saba ba,hakan yasa take ganinta wata daban. Zama tayi akan gado haɗe da ɗaukan safanta ta sanya, tana kammala sa safa ta zura takalminta me kama da toms, sosai takalmin yayi mata kyau gashi milk colour kalan riganta. Tunowa da maganan teacher Abdallah tayi inda yake ce mata “tazo da wuri kada ta sake ta makara” tashi tayi da sauri tafice daga cikin ɗakin.

Tana fitowa falo daddaɗan ƙamshin turarensa da daɗinsa ke sanya taji wani bacci ya daki hancinta, hakan ya tabbatar mata da cewa bai jima da fita daga falon ba. Da saurinta itama ta fita daga cikin falon, tana fita ta hango ficewar motarsa daga gidan. Ajiyar zuciya ta sauƙe haɗe da nufan inda Kamalu ke tsaye, ba wani ɓata lokaci ta shiga suka ɗauki hanyar makarantar…

Suna zuwa direct office ɗin teacher Abdallah ta nufa, don dama anan yace ta sameshi.

Teacher Abdallah yana ganinta yasaki murmushi..
“Student!” yace da ita yana mai faɗaɗa fari’arsa. Murmushi kawai tayi masa haɗe dayin ƙasa da kanta. Yana kammala abubuwan da yakeyi ya ce suje ya nuna mata ajin da zata zauna, yana gaba tana biye dashi a baya.

S.S 1 A shine abun da aka rubuta asaman ajin daɗan manyan baƙi, ɗalibaine waƴanda aƙalla zasu kai su 25 acikin ajin maza da mata, wasu suna zazzaune, yayinda wasu kuwa ke tsaye, wasu kamma akan desk suke zaune, suna ganin shigowar Teacher Abdallah ko wanne daga cikinsu ya shiga cikin nutsuwarsa, cike da girmamawa suka tashi tsaye dukansu suka gaidashi, amsa musu yayi haɗe da basu izinin zama. Gyara tsayuwarsa yayi haɗe da cewa

“Ga sabuwar ɗaliba nan nakawo muku, ina fata zaku karɓeta hanu bibbiyu, sannan idan bata gane abuba, inaso kuyi mata ƙarin haske” cikin harshen turanci yake maganan. Kallon Ziyada dake tsaye tama kasa ɗago kai ta kalli mutanen ajin yayi.

“Ga wajen zamanki nan daga yau” yafaɗi haka yana maiyi mata nuni da wata kujera wacce take tsakiyan wasu ƴan mata…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *