SOYAYYAH

SOYAYYAH CHAPTER 9






CHAPTER 9








Kuka tasha sosai sannan ta mik’e ta cire kayan ta chanza, toilet ta wuce ta d’aurayo fuskan
ta takwanta abinta dan batajin zata iya fita duk da tanajin yunwa.
Ahaka Granny tazo ta same ta tayi zurfi cikin tunani dan ko noticing shigowan ta batayi
ba har saida ta dafa ta, a firgice ta d’ago amma ganin Granny yasa ta saurin juya mata baya
ta sake sanya kuka wane yar Baby, aiki ne ya samu Granny dan dakyar ta samu ta rarrashe
ta tayi shiru.
Mik’ewa tayi ta wuce babban falour dan having breakfast anan ta iske su Mammy suna hira,
gaishe su tayi ta wuce dinning tayi serving kanta ta soma karyawa.
Tunda Mammy ta kalle ta tasan Suwayd ya d’aura a inda ya tsaya nan take taji ranta yayi
masifar b’aci, Ummy kam ma d’auke kanta tayi daga Safwah’n yayin da Mummy ke
tausayin ta sosai.
Saida ta gama tsaf ta tako inda su Ummy suke ta durk’usa ahankali tace ” Ummy please
wayan ki zaki aramin”.
Batare da tace komai ba ta mik’a mata, tsokanan ta Mummy ta somayi wai bataji muryan
twiny nata ba shine tayi kuka, ita kuwa murmushin yak’e kawai ta sake ta mik’e ta koma
part d’in Granny.
Ad’aki ta iske ta tana sallah’n walha dan haka saida ta bari ta idar taje tayi locking k’ofan
d’akin ta dawo ta zaunaa kusa da Ita.
Unlocking password ta wayan tayi, sannan tayi viewing contact na Sadiya, da Ummy tayi
saving da Ammey cause haka yaran ke k’iran ta, video call ta mata inda ba tare da b’ata
lokaci ba tayi picking.
Gaisawa sukai sosai_sosai cike da k’aunan juna kaman yadda suka saba.
Granny kam mutuwan zaune tayi jin dagaske muryan Sadiyan ta take ji, hannu na rawa
ta K’arfa wayan idon ta a runtse, ahankali ta bud’e idonta ta sauke su kan Sadiya da
shocked na ganin mahaifiyar tata yasa ta kasa koda kwakwkwaran motsi.
Kallon_kallo suka shigayi yayin da wani irin farin ciki da annashuwa ya soma ratsa zuciyan
su both, ahankali Granny ta soma magana ” Sadiya na is that you? Is that really you? Dan
Allah karku tashe ni idan bacci nake, Ya Allah idan mafarki nake ka dawwamar dani a
haka…”
” Mummy ” tayi saurin tare ta tana kuka sosai ” Mummy please forgive me ” tayi pleading
kukan ta na tsanantuwa.
” Shii Baby ni ya kamata in nemi tuban ki, na rok’eki dan Allah ki yafe min forgive me
please daughter, idan kin so please allow me nazo in ganki in nemi yafiyar ki, i miss you so
much I terribly miss you and want to be with you, do me this favor nasan ban cancanci
hakan ba but please let me this is the right time da ya kamata na dai_dai ta tsakanin mu”
” Mummy ki daina fad’an haka please if not barin tab’a iya yafewa kaina ba, ni ya kamata
na nemi tubarki for the pains i have made you went through, idan baki yafe min ba hak’k’in
ki babban masifa ne agare ni “.
Nan dai suka sha kukan su kaman ba gobe, sai da sukayi mai isan su sannan suka yafi juna
sai kuma hiran yaushe gamo ya biyo baya, a kama wancan a sake a kama wannan haka har
suka gangaro kan auren da tai da ‘ya’ya ukun da take da, duk saida ta had’a ta da yaran ta
suka gaisa inda wonders ya kusa kashe ta ganin tsananin kaman da Safwah da Sayyada ke
hatta da blue eyes nasu.
Sosai yaran sukayi farin ciki dan suna damuwa sosai da rashin sanin family’n Ammy’n su,
Abuh kad’ai suka sani dan yana kai musu visit sai Safwah da Safwan su kuma ta waya suke
gaisawa.
Ranar ta kasance kyakkyawan rana gurin Sadiya da Granny dan sallah kawai ke katse musu
hira, anan Sadiya ke shaidawa Granny k’arshen wata zata zo, badan sun gaji ba suka kashe
wayan cike da kewan juna.
Safwah tasha albarka a gurin Granny dan through out ranan suna tare.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullum Granny da Sadiya basu da aikin yi sai waya, yayin
da muguntan Suwayd toward Safwah sai abinda ya dad’u ahaka kuma mugun so da
k’aunar sa ke sake building cikin zuciyan ta amma koda wasa bata tab’a aikata abinda zai
sa ya gano ta ba.
Family’n Zee sunyi farin ciki sosai da dawowanta, ga yadda take walwala ba k’aramin dad’i
ya musu ba.
Tarba mai kyau ta samu inda don dad’i ta rasa ina zata tsoma ranta, abinda yake damunta
bai wuce ganin da tayi har sunyi two weeks da dawowa ba amma sam Suwayd ko k’iranta
baiyi ba dan haka yau ta yanke shawaran k’iran sa taji ko lafiya.
Missed call goma ta masa amma koda wasa ba’a d’aga ba kawai saita shiga tura masa text
but still shiru ba respond, hakan ba k’aramin k’ona mata rai yayi ba kawai ta baje abinta
tayi ta kuka wane dan shi aka turo ta duniyan.
Suwayd na zaune a falour’n su yana chatting da Abdul da Musty cikin wata group tasu da
sukayi creating su ukun wayan sa ta soma ringing, wani mugun haushi ne ya kamasa dan
yadda yake enjoying chart nasan.
Wawan tsaki yaja yayi jifa da wayan side not minding k’iran da keta shigowa, ganin an
koma turo text ya jawo wayan ahankula ya soma karantawa yana murmusawa shi kad’an
Sa.
” She never get angry ” ya fad’a ahankali
Da gudu Kadsah ta shigo tana faman kuka tana kwad’awa Suwayd k’ira,wani
mahaukacin tsawan daya daka mata ne yasa ta sake rud’ewa.
” Lafiya zaki shigowa mutane babu sallama?”
K’ofa kawai ta shiga yi masa pointing tana fad’in sunan Safwah dakyar.
Kyawawan maruka ya sauke mata guda biyu hakan yasa ta shiga hankalinta.
“Now tell me what is wrong?”
In stemming ta soma magana ” Saf.. Safwah zata mut…”
” Shut up idiot ” ya buga mata wani hautsinan nan tsawa, fuskan nan tayi wani mugun ja
yayin da jijiyoyin kansa suka mik’e saboda tsananin tashin hankali da fargaban what is
about to happne.
Jikin tane ya shiga rawa tanajin dama Granny ba ita ta aiko ba.
“Ina Safwah’n? ” yayi maganan fuska a d’aure.
Tana d’akin Granny sai suma take ” tayi maganan hawayen ta na tsanantuwa.
” Find your way out banza dak’ik’iya daman akan wannan 1Q-dummy’n kikazo zaki tadawa
mutane hankali ” ya fad’a yana pretending in i don’t care manner.
Cikin tsananin kuka ta juya ta fice tana tunanin wane irin zuciya Ya Suwayd yake da, dan
wani lokacin idan yayi wani abun sai tai tayin tunani anya kuwa ciki d’aya suka fito dashi!!.
Tana fita yayi saurin janyo wanyan sa yasa a pocket yabi bayanta, da saurin sa ya nufa part
d’in Granny sai da ya kai k’ofan shiga ya tsaya ya nitsar da kansa.
Safwah ya hango kwance kan cinyan Samha sai murk’usu su take yayin da hannun ta ke
damk’e da maranta, cike da tsananin azaban ciwo take ta murza kanta cinyan Samha tana
yarfe hannun ta.
Su Kuwaysah kuma sun baibaye su sai hawaye suke cike da tausayin ta dan sau uku tana
suma.
Da sauri Granny tace ” yauwa mai sunan manya asibiti zaka kaita”
” Ni kuma? ” yayi maganan yana pointing kansa, in shocked du su Lubna suka zuba masa
ido.
” Dan uwarku ku daina kallo na shegu mayu, du ‘yar iskar da ta sake kallo na sai na karya ta
wallahi banzaye kawai ” yayi maganan a tsawace.
Nan take kowacce ta shiga hankalin ta sai tausayin Safwah dan sun sa k’ila kafin ya kaita
asibitin masifan sa ya kasheta.
” Idan ka gama sai ka wuce ka kaita asibitin ” Granny tayi maganan rai a b’ace.
” Dallacan wawiya taso dan ba iya tab’a wannan k’azamin jikin naki zan ba”
Safwah dake cikin mawuyacin hali sam batasan mai yake yiba, make sa a k’eya Granny tayi
ya saki ‘yar k’ara.
“Banason shiririta ka d’auke ta ku tafi kafin raina ya b’aci”.
Yana k’unk’uni ya k’arasa ya d’auke ta in a bride like-style yana wani tab’e fuska shi a dole
kyankyamin ta yakeji.
Yana fita daga fallour’n Granny yayi saurin nufan parking space dan yadda ta k’ank’amesa
ya isa shaida masa yadda take suffering, a front seat ya sata ya zaga driver side gate man ya
bud’e masa gate yaja motan da wani mugun speed.
Gudu yake wane zai tashi sama har suka isa asibitin da zai soma aiki, Ita kuwa sam batasan
meke faruwa ba dan ta riga da ta sake suma.
Da sauri ya zaga ya d’auke ta ko kashe motan bai tsaya ba ya wuce office d’in DrAlkasim, ko
sallama baiyi ba ya kunna kai ya kwantar da ita kan gadon dake office d’in.
“Dr do something please “ya fad’a a rikice sam ya kasa nutsuwa.
“Calm down please, calm down she will be Alright okay?”.
“Dr wani irin magana kake haka just do something l can’t watch her suffering ike this “.
Gani bare nutsu ba kawai Dr Alkasim ya wuce ya soma duba ta nan dariya ya kusa kwace
masa ganin period ne ta fara amma ya moze.
Allurai da zasu rage mata pain yaje ya had’o ya dawo, yana k’ok’arin nufan gadon Suwayd
yayi saurin shan gaban sa ya kwace sannan ya nuna masa hanyan waje meaning ya fita.
Dariya sosai Dr alkasim yayi dan yana d’aya daga cikin wad’anda suka san yana son Safwah
yasan jarababban kishin nasa ne ya motsa dan haka ya fice ya bashi guri.
Alluran ya aiiye a side ya haye gadon ahankali ya janyo ta jikin sa dan ta farfad’o, skirt
nata ya soma sauk’ewa k’asa tayi saurin rik’e hannun nasa tana girgiza kai dan ta tsani
allura.
Ganin haka ya matse ta gaba d’aya ajikin sa da hannun d’aya yayi using d’ayan hannun ya
mata, k’ank’ame sa tayi sosai wane zata koma jikin sa hakan kuma ba k’aramin electric
sparks ya mar sending ba, dakyar ya iya ya k’arasa mata.
Lafewa tayi ajikin sa sosai inda not long enough bacci ya d’auke ta, gyara mata
kwanciyar yayi ajikin sa yana jin mugun son ta na fuzgar sa, Pink lips nata ya tsare da idanu
zuciyan sa na raya masa abubuwa da dama.
Matso da fuskan sa yayi tayi har nose tip nasu ya had’e, ahankali ya lumshe idanun sa ya
had’e bakin sa da nata, kissing ta yake sosai wane dan shi aka turo sa duniya.
Ringing wayan sa yasa ya zame bakin sa badan yaso ba ya..
Mik’ewa yayi a kasalance, saida ya saita nutsuwan sa sannan ya d’aga wayan.
“Ya jikin nata? ” Granny ta jefo mar tambayan.
” Da sauk’i ” ya bata answer a tak’aice.
Gargad’i sosai ta masa karya yarda ya barta ita kad’ai sannan ta katse wayan.
Komawa yayi kan gadon ya zauna yana ta kallon yadda take bacci tana sauke ajiyan
zuciya.ya had’e hannun sa da nata not letting go yana jin azaban sonta da k’aunar ta na
ratsa du wata sassa ta jikin sa he just can’t imagine life without her, he is “Blinded by her
love” yanaijin inhar bai same ta ba matuwa zai, dan bare tab’a iya juran ganin ta da wani ba.
K’iran sallar la’asar yasa sa mik’ewa badan ya gaji da kallon kyakkyawan fuskanta da
feeling softness na hannun ta ba, a bakin k’ofa suka had’e da Dr Alkasim, duk yadda yaso
Suwayd ya barsa ya shiga ya d’aura alwala aciki yak’i dole ya hak’ura suka wuce masallacin
dake cikin asibitin yayi a chan.
Koda aka idar basu koma office d’in ba zagaye asibitin sukai tayi Dr Alkasim na nunawa
Suwayd gurare da dama aciki, har Office d’in Suwayd seda sukaje amma a kulle take.
K’arfe biyar suka koma suka tarar harta farka sai k’ananun kuka take, ganin yanzu she is in
a right state of mind ya had’e fuska kaman bai tab’a dariya ba ya k’arasa jikin gadon.
” Is better for you to shut that your mouth, inba haka ba yanzu zan mammake ki, kar
kiyi tsammanin wai dan baki da lafiya zaki mun iskanci in kyale ki ” yayi stating in a serious
note.
Lokaci d’aya ta nemi kukan ta rasa saboda tsoro, daman ita bakomai ya sata kuka ba sai jin
da tayi jini nabin ta sosai gashi Ya Suwayd baya son ganin jini at all
Alluran da zaiyi mata da daddare ya had’a sannan ya kalle ta
yace ta tashi su tafi, tsantsan kunya irin nata yasa ta kasa yi masa bayanin halin da take
ciki.
Shi kuwa tsayawa yayi kallon ikon Allah ganin ta ciro d’an kwalin ta tana k’ok’arin d’aura
wa kan skirt d’in ta.
Fizge d’an kwalin yayi a hasale yace ” ke wace iriyar lunatic ce wai? Ko ina in baki gwada
hauka ba bakyajin dad’i ne? Wait ma me hakan Kike k’ok’arin yi? “
Ahankali ta saki kuka ba tare da ta tankasa ba saboda kunya, takaici da bak’in cikin da suka
lullub’e ta.
A tsawace yace ” ba kuka nace kiyi min ba, uban me zakiyi da d’an kwalin nake so na
sani!”.
Runtse ido tayi tana kuka sosai sannan ahankali wane mai magana da kanta tace “jiki na ta
b’ace ina son na rufe ne “
Idanun dakejin kunyan sa ya tsare with so much adoration a zuciyan sa ya furta ” Ya
Allah this girl is driving me crazy, Allah ka mallaka min ita a matsayin uwar ‘Ya’ya na Amin”
murmushi yayi ganin ta kasa bud’e idon ya juya gun Dr Alkasim only to find his empty seat,
ficewa yayi yai locking office d’in kaman nasa ya ware abin sa.
Wata had’ad’d’iyar boutique dake nearby ya shiga,idanun sa basu sauka ko ina ba sai
kan wani maroon colored Arabian gown mai adon black stones,nan take ya hango flower’n
sa aciki dan yasan sosai zata yi fitting ta.
D’auka yayi ya ajiye a side sannan ya wuce inda ya hango panties, tunanin size na Safwah
ya tafiyi amma sam bayada idea akai duk yadda yaso tunanowa ya kasa dole ya soma
duddubawa ko zai samu.
“Halo Handsome ” ya jiyo wata ‘yar siririyar murya a kansa.
Kallon rainin wayo ya bita dashi amma ganin ta ‘yar cacas wane Safwah ya sake killer
smile tasan yace ” Hy Baby doll “
Nan take fuskanta yayi ja kaman k’osai acikin mai saboda tsabar blushing ” Do you need
any help? ” tayi questioning nasa in a sexy-like voice nata.
“Yes ” ya d’age mata gira d’aya yana binta da kallon you don’t know what you are
doing
“Awwwn inaji fad’a mai kake so” tayi sounding? agerly.
“Pant size nakin zaki fad’amin “yayi maganan nan take batare dajin kunya ba.
Fad’ad’a fara’anta tayi dan du tunanin ta itane zai siyawa, wani shegen fari tayi da ido ta
nuna masa raw na tsadaddun dake gurin, dozen biyu ya d’iba ya wuce abinsa ya barta sake
da baki, tsaban takaici ji tayi wane ta rusa ihu shiko ko a kwalan rigan sa ya wuce ya biya
bills nasa aka sanya masa a leda ya tafi.
Akwai store a gefen boutique d’in dan haka ya shiga ya siyo mata pads ya wuce asibitin.
Da angry Dr AlIkasim ya fara had’uwa a parking lot amman yayi kaman bai gansa ba ya
wuce, yana cikin bud’e office d’in ya isko sa.
A hasale yace ” Ka d’auke ta haka ku tafi malan am in need of my office “
Bai ko tanka sa ba ya shige ciki yayi saurin maido k’ofan yasa lock.
Bugawa ya soma yi kaman zaiyi kuka ganin yanaji yana gani ana buga masa iko da office
nasan, ganin Suwayd ba bud’ewa zai yi ba kawai ya nemi d’aya daga cikin iron chairs d’in
da patients ke zama in sun zo ganin sa ya zauna abin tausayi.
STORY CONTINUES BELOW
Yana shiga ya hango ta zaune kan gadon bayan ta jingine da fuskan gadon ta d’aura kanta
kan gwiwowin k’afan ta da alama kuka take, tausayin ta ne yayi bala’in kamasa amma ya
moze.
K’arasawa jikin gadon yayi ya tsaya yana Kallon ta, ganin har lokacin batayi noticing
shigowan sa ba ya kai hannu ahankali ya tab’o ta, a firgice ta d’ago jin saukan lallausan
hannu a kafad’an ta ganin shine ta sake ajiyan zuciya feeling safe and relieved.
Ganin fuskan sa babu annuri tayi saurin kawar da kanta tana mamakin laushin hannu irin
tasa wane na jariri.
“Amsa kije ki sanya, kuma karki yarda kisa ruwan sanyi ajikin ki ” yayi maganan yana
kallon wrist watch nasa.
Mik’a Hannu tayi ahankali zata karb’a, mistakenly hannu su ta had’e na sosai hakan tayi
affecting su amma kowa bai bari d’an uwan sa ya fuskanci halin daya shiga ba, ajiye mata
yayi yai saurin zaro hanky yana wiping inda hannun ta ya tab’a cike da kyankyami.
Ji tayi wane ta had’iye zuciya saboda takaici dan ta k’ona masa rai itama ta mik’e dan yaga
yadda tayi staining dan sosai ganin jini ke d’aga masa hankali, da sauri kuwa ya d’auke kan
sa zuciyan sa na some tashi.
Ahankali ta shiga takawa kaman hawainiya saboda neman tsokana, ganin hakan
Suwayd ya buga mata wani shegen tsawan da ba shiri ta tsinci kanta acikin toilet d’in.
Warm wata tayi using ta gasa kanta sannan ta d’auka pant d’aya cike da mamakin yadda
akayi yasan size d’inta ta had’a da pad ta saka, rigan ta d’auko ta sanya taje gaban k’aton
mirror dake toilet d’in tana jujuyawa happily yanda rigan ya kamata ta sama ya bud’e ta
k’asa yafi komai burge ta, nan take k’aunan rigan ya shige ta.
Kayan ta data rasa yadda zatayi dasu ta soma d’auraye wa, gajiya yayi da jiranta ya
k’araso bakin toilet d’in a masife yace ” wai uban me kikeyi aciki ne?”
” Ina zuwa Ya Suwayd na kusa gamawa ” ta fad’a da d’an ihu yadda zai jiyo ta.
“Ba wannan na tambaye ki ba stupid girl just answer my question”.
“Kayan dana cire nake wankewa ” ta fad’a finally.
“What? ke wai baki da hankali ne? Wait ma kina tunanin zaki sake sanya wannan
najasassun kayan? Gaskiya da kin tabbata Miss world k’azama, dallacan fito kafin na shigo
na b’ab’b’ala ki banza good for nothing kawai “.
Fitowa tayi rik’e da ledan ragowan kayan daya siyo kanta a k’asa saboda kunya, kallon ta
ya tsaya yi totally out of word ganin yadda tayi masifan kyau, nan take jarababben kishin sa
ya motsa ganin mayafin rigan d’an k’arami, d’agowa take son yi dan jikin ta yabata kallon
ta yake yi amma ta kasa.
Wawan tsaki yaja yace ta wuce su tafi, ba tayi musu ba ta shige yana binta a baya suka
fice daga office d’in.
Cillawa Dr key d’insa yayi yace ” thankyu and make sure an Yasar da kayan dake toilet
please”
Dirty glares ya masa sending cike da takaici ya bud’e office d’in sa ya shige.
Duk inda suka gifta sai an kalle su dan yadda suka yi mugun dacewa har suka isa parking
space, da sauri ya bud’e musu suka shiga ya bawa motan wuta, yayi niyyan mata shopping
amma kalle masa ita da akayi yasa ya fasa yayi leading nasu gida.
Horn yayi gate man ya bud’e musu suka shiga, yana gama parking ya jingina da kujeran
sa ya lumshe ido.
Bud’e k’ofan ta tayi ta zura k’afafun ta har zata fice sai ta juyo kai a k’asa cike da kunya tace
“nagode ” daga haka ta fice tayi cikin gida.
Like a fool ya rik’a nanata nagode shi kad’an sa yana murmusawa, ganin ba mahalicci
sai Allah ya fito shima ya wuce part d’in su, yana shiga toilet ya wuce yayi wanka ya d’auro
alwalan magrib dan lokaci yayi.
Na sosai tasha tsokana gurin su Kadsah wai sai tayi musu bayani ya akayi yasan size d’in
ta,koda lokacin dinner yayi k’in zuwa tayi saboda kunyan sa yayin da shikuma yake can
duk ya damu bai ganta ba yana tunanin ko ciwon ne, bai wani ci abincin kirki ba ya tashi ya
wuce part d’in su ya d’auko alluran ta ya wuce part d’in Granny
Tana gama cin abinci ta shige d’akin su ya shigo, ganin bata falour’n kai tsaye ya wuce
bedroom d’in su, nanma bata nan amma jiyo k’aran ruwa da yayi a toilet ya shaida masa
tana nan.
Gefen gadon ya nema ya zauna yana jiran ta, bata wani b’ata lokaci ba ta fito inda tayi
turus ganin sa zaune yana daddanna waya, Allah yaso ta this time around da hijab ajikin ta
data sha wani wulak’ancin.
Sunkuyar da kai tayi tana wasa da ‘yan yatsunta lokacin daya d’ago ya kafeta da ido, sai
da ya gama k’are mata kallo yayi faking tarin munafinci irin ganin ta da yayi ahaka disgust
him, “kin san lokaci na bana b’atawa akan shashashu irin ki bane dan haka kizo na miki na
tafi inada abinyi “
K’in motsawa tayi gano allura a hannun sa dama haryanzu ma bata gama warkewa daga na
d’azu ba, ” dake fa nake magana ” ta sake tsinkayo voice nasa.
A shagwab’e tace ” Ya Suwayd Allah na warke a barshi haka banaso”
” Sai akace miki dan bakyaso zan kyale ki? To bari kiji wallahi tunda na shigo ko zaki mutu
sai nayi miki”
Tunda taji ya rantse ta soma neman mafita, ganin da ‘yar tazara a tsakanin su tayi saurin
juyawa zata koma toilet d’in dan harga Allah tsoron alluran take, murmushin gefen baki ya
saki dan ya fuskanci what she is capable of doing, taku d’aya yayi ya damk’o ta, du kalan
magiyan da rok’on da take masa baisa ya sake ta ba sai da yayi mata, k’ank’ame sa tayi
tana kuka sosai kaman wadda aka zarewa rai yayi saurin tureta ya fice dan shi kad’ai yasan
mai yake ji.
Dakyar ta mik’e ta sanya kayan baccin ta tabi lafiyan gado, batare da b’ata lokaci ba kuwa
tayi falling into a beautiful sleep.
The following day
Duk yadda Suwayd yaso ganin ta hakan ya faskara dan tayi blocking du wani abu dazai
had’a su saboda kunya, tun yana d’aukan abin wasa harya daina dan yau kwana uku kenan
bai sanya ta a ido ba.
Tana zaune a falour’n Granny taji tana son jin muryan Twiny d’inta dan haka ta mik’e ta
wuce part d’in Ummy, suna zaune ita da Ya Haidar suna hira tayi salama ta shiga
Amsa ta sukayi ta durk’usa har k’asa ta gaishe su sannan ta d’ane kan cinyan Ummy tana
sauraron hiran da suke.
Wani azababban kishin da bata tab’a sanin tana dashi bane ya rufeta jin labarin da Ya
Haidar ke bawa Ummy na Zee da Suwayda Cyprus and duk yadda taso b’oyewa ta kasa
dole ta mik’e da sauri tabar falour’n, ko gaban ta bata gani saboda tsaban kishi ta ture shi
ta wuce.
Kallon mamaki Suwayd ya bita dashi amma ganin sam ba a hankalinta take ba yaji kaman
ya bita ya ji damuwanta, duk yadda yaso binta ya kasa dole ya hak’ura ya shige gun Ummy
ko zaiji daga bakin ta.
Garden ta wuce ta shiga rusa kuka kaman ba gobe tanajin mugun tsanan Zee a ranta,
bazata tab’a bari ta kwace mata Ya Suwayd ba a shirye take komai zaiyi mata ta fayyace
masa sirrin zuciyan ta she can’t afford to lose him, tana son sa tana k’aunar sa and she is
ready to die for his love, ta yarda ta b’ata da kawo akansa.
Ummy da Haidar kuwa kallon mamaki suka bita dashi amma sai suka bar abin a batason
jin hiran Suwayd d’in ne, ahaka yazo ya same su duk yadda yaso ayi maganan abinda ya
b’atawa Flower’n sa rai basuyi ba dole ya hak’ura amman ya kud’irce a ransa no matter
what it takes saiya gano.
Two weeks later
Ya kama sunday the long expected day agurin Granny dan yau one and only daughter nata
zata zo gurin ta bayan shekaru da dama da suka kwashe separated.
Kowa Ya lura da tsantsan farin ciki da Granny, Safwah, Abuh da Ummy keyi, Safwah’n
ma saida ya dawo gida dan ranan daya dad’e yana jira ce tazo.
Girki na musamman Ummy da Safwah suka shirya, k’arfe biyar dai_dai Abuh ya fito tafiya
d’auko ta a airport d’an k’arfe shida irgin su zaiyi landing.
Aijikin motan sa ya iske ‘yan biyun sa, bayadda baiyi dasu su hak’ura yaje shikad’ai ba
suka ki, wuin shiga mota saida suka b’ata masa lokaci fad’an shiga gaba, ganin zai tafi ya
barsu Safwan ya hak’ura ya shiga baya.
Basu wani d’au lokaci ba suka isa a lokacin kuma jirgin harya sauka passengers sun fara
fitowa.
Ahankali ta fito ta lumshe idanun ta tana shak’ar ni’imtacciyar iskar k’asar ta, nan take
abubuwa da dama suka bijiro mata, kafin kace wani abu hawaye sun wanke mata fuska,
ahankali Baby Asmeey takai hannu tana sharewa Ammey’n ta tears, da sauri ta dawo
nutsuwanta suka sauka daga steps d’in jirgin.
Safwah ce ta soma hango ta takwaso da gudu ta rungumeta not letting go, hugging nata
back tayi itama cike da sonta da k’aunar ta sun dad’e ahaka kafin suyi breaking hug d’in,
sannan ta rungumo angry Safwan dake jin haushi Safwah ta cinye sa deal d’in su na fara
hugging Ammey’n tasu, sake sa tayi ta rungumo Abuh da ke d’auke da Asmeey yana Kallon
su with so much love.
Shafa kanta yayi ahankali yace ” Welcome home sweetheart “
Atare Safwah da Safwan ma suka ce “Welcome back Ammey”
Murmushin jin dad’i da hawayen farin ciki ne suka zubo mata Safwah tayi saurin kai hannu
tana share mata.
Hannunta Abuh ya rik’e suka nufa inda yayi parking motan sa ya bud’e mata gaba ta shiga
ya zagaya driver side, Safwah, Safwan da Baby Asmeey suka shiga baya yayi starting motan
suka tafi dan already d’an dako ya sanya kayan ta a but.
A hanya Abuh ke tambayan ta meyasa bata tawo da takwaran sa da Sayyada ba.
Tayi murmushi tace ” Arif sun tafi England da Daddy’n sa, Sayyada kuma kafin lokacin
komawa na sun fara Exam shiyasa ta zauna tare da kakannin ta “
Hiran su suka cigaba dayi dangane da changes da ta bani sosai a Nigeria, Safwah kam
sai faman dariya suke saboda shiriritan da Baby Asmeey ke musu haka har suka isa gida.
Granny tayi musu waya yafi biyar saboda zak’uwa, kasancewar suna hanya akayi magrib
yasa suna parking Abuh da Safwan sukayi joining Baba mai gadi sukayi alwala suka wuce
masallaci, Safwah na d’auke da Asmeey yayin da itakuma ta shiga k’arewa gidan Kallo tana
tunanin lokacin da d’an uwanta abin alfaharin ta ya d’auke ta da hannun sa ya fita da ita
lokacin da ake k’ok’arin halaka ta.
” Shid’inne sai alot of changes ” ta fad’a tana fashewa da wata iriyan masifaffiyar kuka,
rik’o hannun ta Safwah tayi tana kuka itama suka nufa part d’in Granny.
Granny tunda ta idar da sallah ta zauna a falour zaman jiran su, kaman a dream ta jiyo
muryan crying Sadiya tana mata sallama, da saurin ta tamik’e ta tsaya, idanun su na
had’uwa tears of joy suka ziraro mata kasa magana tayi kawai ta bud’e mata hannayen ta,
da sauri ta k’araso suka yi hugging juna so tight suna kuka sosai.
Safwah na tsaye agefe tana kallon su cike da tausayawa, Granny ma calming kanta tayi
ta koma rarrashin d’iyar tata da nata kukan yak’i tsayawa, sai da tayi mai isan ta tayi shiru
suka wuce d’akin Granny tayi wanka ta d’auro alwala tayi sallah, Safwah ma alwalan tayi
tai sallah sannan taje ta k’irawo Ummy.
Abuh ma daga masallaci takurawa su Abbah yayi suka wuce part d’in Granny nan suka iske
the biggest surprise of their life, gaisawa kawai sukayi gaba d’aya aka wuce dinning nan fa
kaf yaran suka shiga rud’ani ganin mai kama da Abuh kaman an tsaga kara, Kadsah uwar
gulma kasa hak’uri tayi tace ” Abuh dama ku ‘yan biyu ne “.
Kafin yayi magana Sadiya ta taresa ” Kadsah kici abinci zakisan komai but not now”
“Lahh naga du nan bawanda ya fad’i suna na how do you know?”
“Shut up you idiot ” Suwayd ya buga mata wani shegen tsawan da yasa ba shiri ta nutsu.
“My Mrarrogant halin na nan kenan? “
Dad’an mamaki ya kalle ta amma ya shanye mamakin sa ya d’auke kai, murmusawa kawai
tayi ganin ita d’in ma sai an gwada mata halin ta cigaba dacin abincin ta tana santi.
Suna gamawa duk aka wuce main falour aka sake gaggaisawa, Granny na mak’ale da
d’iyar tana tattali dan jitake da ita wane kwai d’aya acikin duniya, yaran duk sun k’osa suji
wace amma banda Suwayd dake jin duk an takure shi zaman da akayi agurin.
Sam basu samu jin abinda suke sonji ba dan Granny tace kowa yaje ya kwanta ayi magana
gobe, na sosai Abbah da Daddy sukaji dad’in haka dan sosai suke jin kunyan k’anwar tasu
kuma basu san ta ina zasu soma neman tuban ta ba.
Tare da ita, Safwah and Granny suka raba dare suna hira, saida sukayi sallah’n asuba
sannan suka kwanta ramuwan bacci.
Sai k’arfe goma sha biyu suka tashi, breakfast nasu ma sai part d’in Granny’n aka kawo
musu.
Bayan sallah’n azahar angama lunch kowa ya amsa k’iran Granny harta da Ya Sadeeyq
da Aunty Zahra sun zo, anan ne aka fayyace abinda ke b’oye sannan aka soma neman
yafiyar kowa.
Duka yaran Ammey’n su ta basu tausayi inda through out the day suna tare da ita, sam
Suwayd ya kasa sakewa ayi hiran dashi saboda ma yaran karsu samu daman raina shi.
Haka kullum take kasancewa da yaran, yayun ta kuma sai dare in sun dawo daga aiki,
azaman one week d’in da tayi dasu ta karanci halayen kowa acikin yaran musamman ma
Suwayd.
Matan yayyan ta kuwa kaman k’awaye haka suke harta k’arasa one month nata.
Washe gari gaba d’aya hankalin Granny a tashe yake dan gani take kaman idan ta tafi sun
rabu har abada kenan, itama gani take one month d’in da sukayi kaman kwana d’aya
badan mai gidan ta yayi waya ba da babu inda zataje.
Tare da Haidar da Sayyid suka wuce Abuja tabar su anan gidan Aunty’n Sayyid tabi flight
na Saudi ta tafi cike da kewan family’n nata.
A week Later
Safwah ce zaune tana ta trying solving wani maths ta kasa, du yadda taso yi ya faskara
gashi har lokacin Ya Haidar da Sayyid basu dawo ba, ita kuma bata shirya mutuwan ta ba
balle taje gurin Ya Suwayd, gashi gobe ne zasu soma third term exam nasu kuma da maths
zasu fara and teacher’n yace dole wannan topic d’in ta fito dan 9996 ‘yan class d’in basu iya
ba.
Idean k’iran Imran class captain d’in sune ya fad’o mata nan take taje ta d’auka wayan
Ummy ta kirashi, inda ya nuna mata karta damu five zaizo.
K’arfe hud’u da arba’in da biyar tayi applying simple makeup ta zauna zaman jiran sa, biyar
dai dai kuwa ya k’irata ya shaida mata yana parking space, dogon hijab daya mugun
amsan ta tasanya ta tafi.
Tun daga nesa ya hango ta ya kafeta da ido yanajin kaman ya fito ya fayyace mata abinda
yake ji game da ita, harta k’araso baiyi noticing ba har saida tayi clapping hands nata
sannan ya dawo nutsuwan sa.
Iron chairs da aka k’awata gurin da su ta nuna masa suka k’arasa suka zauna, gaisawa
sukayi sannan ya shiga koya mata yadda zata gane, sosai kuwa ta gane ganin yanzu lokacin
sanyi da wuri ake magrib yace da ita zai tafi, rako sajikin motan sa tayi suka tsaya hira sai
labarin abin dariya yake bata tana kyalkyala dariya, shigowan motan Ya Suwayd yasa
gaban ta wani mugun fad’uwa, saurin kallon inda take kallo Imran yayi ganin gaba d’aya ta
rikice.
Ganin Suwayd dake nufo su kaman mayunwacin zaki yasan lallai wannan Yayan nasu ba
wasa, fitowa yayi daga motan ya gaishe da Suwayd.
Ko amsa shi baiyi ba da lion tasa yace ” Meya kawo ka gidan nan?”
” Nazo koya mata assignment ne” ya ansa nan take.
” Tace maka babu wanda ya iya a gidan su ne? ” ya sake jefa masa tambayan zuciyan sa na
tsananin tafasa.
“A’ah bata fad’a ba ” ya fad’a calmly.
” Okay zaka iya tafiya”.
Sallama yayi musu ya shiga motan sa ya tafi, ko kallon ta baiyi ba saboda yasan idan ya
tab’a ta a lokacin zai iya kashe ta saboda tsananin kishin dariyan dayaga tana yiwa wani
namijin bashi ba.
Part d’in su ya wuce ya fad’a toilet yayi wanka ya fito, kaya ya sanya ya wuce masjid Dan
an soma k’iran sallah.
Saida aka idar da isha ya dawo har kuma lokacin bai dawo dai_dai ba, two glass cup na
wine ya kora ganin da yayi su Haidar basa nan yasa yake sha a gida batare da sanin kowa
ba, sannan ya d’au waya ya k’ira Ummy yace ta turo masa Safwah.
Kuka sosai ta sawa Ummy tana begging ta takira shi tace masa batanan amma sam
Ummy tayi banza da ita, data gaji ma bar mata falour’n tayi ta wuce bedroom d’in ta.
Saida tayi kuka ta gode Allah sannan ta tafi, a bakin k’ofa ta tsaya tana kuka sosai ta kasa
shiga, jiyo kukan ta da yayi a kofa ya taso a masifance ya finciko ta cikin d’akin.
Wani irin k’aran azaba ta sake lokacin data mugun bigewa a kwankwason ta, kafin ta
dawo daga zafin bigewan ya haske ta kyawawan maruka har hud’u nan take ta kurma wani
uban ihu saboda azaba, gefen bakin ta harta soma jini, wayan charger ya ciro tana ganin
haka ta soma ja baya tana bashi hak’uri, saukan wayan dataji a gadon bayan ta yasa ta
kusan shid’ewa dama gashi lokacin sanyi duka yafi shiga.
Bata gama farfad’owa daga suman zaunen da tayi ba ya rufe ta da duka ta ko ina, tun
tana iyayin ihu harta kasa, sai da ya mata dukan da koda tsautsayi akace ta sake k’iran
wani ya koya mata assignment bazata yiba sannan ya kyale ta.
Yana sake tuno yadda takewa Yaron dariya ya nufa fridge ya d’auko ruwa masu k’ank’ara
ya..Ya juye mata ajiki, duk inda ta fashe ajikin ta saida ruwan k’ank’aran ya ratsa, saboda
tsananin azaba batasan sadda ta soma addu’an Allah ya d’auka rayuwanta ta huta ba.
ldanun tane suka k’akk’afe gaba d’aya ta sank’ame, yana ganin haka ya sake goran
ruwan yayi kanta hankali a tashe.
Hugging nata yayi so tight ya fashe da wata matsananciyar kukan da tunda Mammy ta
haifesa bai tab’a yin irin ta ba, ” Flower meyasa kike min haka? Meyasa bazaki gane
tsananin kishin da nakeyi ba akanki? Meyasa kike son forcing d’ina hurting ki? What I Did
Was Foolish & Impulsive, IfI Cud Take It All Back I’d Do This So Instant, I Truly Didn’t Mean
To Hurt You In Any Way, I’m Sorry For Hurting You Flower, I Love you, I Love you, I Love
you,words can’t never ever explain how much I love you Safwah, the love I have for you is
far beyond imagination, ni kaina har tsoron kalan soyayyar da nake miki nak..”kukan
daya ci k’arfin sa ne yasa sa k’ank’ame ta wane za’a kwace masa ita yana ta surutan sa
wane zararre.
Zame ta yayi daga jikin sa ya mik’e ya bud’o wata safe, nan take ta bayyano da expensive
wines nasa, kwalba biyu ya cire ya maida ya rufe ya zauna ya soma bankawa cikin sa, du ya
had’a ya shanye batare da tsoron illar da zatayi masa ba, komawa yayi kusa da ita ya had’e
hannun su yana ta sumbatu har wani wahalallen bacci ya d’auke sa.
3:00 am
Ta bud’e idanun ta tayi saurin rintsewa dan gaba d’aya d’akin ya juya mata upside down,
mugun zafin da jikinta ya d’auka ya isa shaida maka mawuyacin halin da take ciki, dakyar
ta iya ta mik’e zaune ta jingina da bango tana fitar da numfashi a wahalance.
Bud’e idanu tayi dakyar tana bin d’akin da kallo, nan take tsoro ya baibaye ta jan jiki ta
somayi tana dafa bango tabar d’akin dan karta sake jawo wa kanta bala’i, ko lura da
Suwayd dake kwance ta d’ayan side d’in ta bata yi ba, gashi dai a zaune take amma mugun
jiri take ji, kanta saboda azaban ciwo ji take wane ta cire sa ta huta.
Dakyar ta fita mazaunan ta du sun d’au sanyi saboda jan jikin da tayi, a bakin k’ofan ta sake
jingina tana maida numfashi sai da ta d’au tsayin lokaci sannan ta daddafa ta mik’e dakyar
tana tangad’i tana had’a k’afa wane ‘yar maye ta nufi part d’in Granny, duk wani tsoron
dare da takeji yau ta neme shi ta rasa sai mugun tsoron Ya Suwayd.
Luckily k’ofan a bud’e take dan sun manta basu kulle ba, ahankali ta shiga kai tsaye ta
wuce d’akin su, toilet ta shiga ta had’a warm water a bathtub ta shiga ciki tana gasa jikin ta
daya fashe, tanayi tana kuka saboda azaba harta gama ta fito, sai dai kuma ba laifi ta d’anji
dad’in jikin ta.
Kaya masu nauyi ta sanya saboda sanyi then ta d’auko Teddy’nta ta rungume ta zauna
akan sallaya tana kuka ahankali dan karta tashi ‘yan uwanta.
K’iran sallah’n asuba ya sata mik’ewa taje ta d’auro alwala ta fito, Kallon su ta rik’ayi abin
sha’awa ganin yadda suke bacci peacefully, hawaye ne suka ziraro mata tayi saurin gogewa
ta soma tada su.
Tashi a wannan lokacin ya zame musu jiki dan haka nan take suka tashi aka soma layin
toilet ita kuma ta soma nafila.
Bayan sun idar ba wadda ta koma bacci aka soma shirin school, ” innah lillahi wa’innah
ilaihir raji’un Sisi me haka ajikin ki? ” Kuwaysah tayi ex claiming cike da k’in yardar abinda
take gani idanun ta na cikowa da kwalla.
Nan take du attention d’in su yawo kanta suna kallon yadda jikin ta ke a fashe, sai lokacin
suka lura da yadda jikin ta ke rawan zazzabi.
Kuka ta fashe musu sosai ta rik’o hannun Kuwaysah dake hawaye tace ” Sis dan Allah ki
fad’amin daga yarinta na zuwa yanzu mai nayiwa Ya Suwayd ya tsaneni? nasan zai fad’a
miki, meyasa baya sona kaman ba jinin sa ce ni ba?..”
Toshe mata baki tayi ta rungume ta suna kukan tare abin tausayi, ta sani du gidan ita da
Safwah sunfi cin wahala a gurin sa amma compared to yadda yake wa Safwah nata nafila ne.
Samha ce ta k’araso tana rarrashin su, dakyar ta samu sukayi shiru aka cigaba da
shiryawan, badan ranan zasu soma Exam ba da babu inda zata je, amman zuwan ya zama
dole inhar ba repeating take so ba cause third term Exam ne daga shi kuma sai final year tasu.
K’arfe bakwai suka nufi dinning hannun Kuwaysah rik’e da na Safwah, kowa yazo banda
Suwayd ahankali du suka soma cin abinci amma banda Safwah da kanta ya matsanta
mata, ture abincin ta tayi ta kifa kanta a table hannun ta dafe da kanta.
Ajiye spoon d’inta Mammy tayi ta mik’e tsam ta nufi Safwah, ahankali ta d’agota
Safwah’ahn tayi saurin rungume ta ta janyo hannunta ta d’aura akan ta, cike da azaban
ciwon kai da zazzab’i tace ” Mammy dan Allah ki taimaka min kaina zai cire”
Hannayen Safwah’n ta shiga bi da kallo cike da mamaki, ta riga tasan ansan tambayan ta
dan haka rai a matuk’ar b’ace ta kalli Lubna tace “jeki k’iramin yayan ku “.
” Tohm ” ta ansa a nitse ta mik’e ta fice.
Da sallaman ta tashiga amma ko arzik’in amsa mata bata samu ba, cike da haushin sa ta
durk’usa ahankali tace ” Ya Suwayd ina kwana? ” amma yadda kuka san da dutse take
magana, rai a b’ace tace ” Kazo Mammy na k’iran ka ” daga haka ta mik’e tay ficewan ta.
Bata dad’e da shiga ba ya shigo ya gaida iyayen nasu suka answer cikin sakin fuska illa
Mammy dake binsa da kallon takaici.
” Meya faru tsakanin ka da Baby? ” Mammy ta jefo masa tambayan ba wasa tattare da ita.
Shiru yayi ya sunkuyar da kai batare da yace komai ba, ” dakai fa nake, mai tayi maka kayi
mata wannan dukan kaman ta aikata zina? ” shiru yayi again.
Zame Safwah tayi daga jikin ta ahankali ta kwantar mata da kanta kan table sannan ta
tako inda yake, tassss kakeji ta wanke shi da wani irin firgitaccen mari, bai gama dawowa
daga mamakin abinda ke faruwa dashi ba ta sake tsinke sa da mari.
Murya na rawa idanun sa sunyi jajir yayin da jijjyoyin kansa duk suka mimmik’e yace”
Mam… Mammy ni. nine fa Suwayd, ni kika mar… Mara yau da hannuki?”
D’aga hannu tayi da niyyan sauke masa wani Ummy tayi saurin rik’e hannun nata rai a
matuk’ar b’ace dan ko kad’an hukuncin ta Mammy bai mata dad’i ba
” Na mare ka, nace na mare ka ko zaka rama? Dama ai girman ka yakai shiyasa kakeji
kaman ka haifi mutane, idan ramawa zakayi sai a mik’o maka charger nima ka dake ni
tunda ba kanka farau ba bakuma kanka za’a k’are ba, Ummy dan Allah ki sake ni na mare
shi naga matakin da zai d’auka”.
” Enough Mammy! Yanzu fisabilillahi hakan da kikayi ya dace? Ki duba fa kiga agaban
Kannen sa kika hukun tashi wanda sam hakan bai cancanta ba, du ma da kika d’au laifi
kika d’aura masa kinsan me tayi masa ne? Shikenan bazai hukun ta k’anwar sa ba intayi
badai dai ba ?”
” Dan Allah ya isa haka Ummy aikin san bak’in halin sa, wallahi na tabbata batayi masa
komai ba tsabar bala’i da masifa ne irin nasa da indai baiyi ba bayajin dad’i “.
Saboda tsabar tashin hankali Safwah neman rashin lafiyan ta tayi ta rasa, yau saboda itane
Mammy ta d’aura hannun ta akan Ya Suwayd abinda bata tab’ayi ba, har cikin ranta taiji
zafin hakan saboda tasan shikenan k’ara tsanan ta zaiyi dan this is the first time Mammy ta
tab’a daura hannu akan sa.
” Kinji dad’i kin had’a shi da mahaifiyar sa saiki zuba ruwa a k’asa kisha ” ta tsinkayi
muryan Ummy rai a b’ace.
Rik’e hannun Suwayd tayi suka fice daga part d’in zuwa nata, suna zama ya fad’a jikin ta
yana kuka mai ban tausayi, rasa ta ina zata soma rarrashin sa tayi dan haka ta barshi yayi
mai isan sa sannan ta rarrashe shi inda ta samu Dakyar yayi shiru.
Su Ummy na fita ta fashe da wani irin matsanancin kuka, da sauri ta mik’e ta fice ta nuf
motan su ta cigaba da kukan ta harsu Kadsah suka zo suka tarar da ita, rok’on duniya sun
mata tayi shiru tak’i har suka isa school.
Exam ta ranan kuwa kawai rubutawa tayi dan tasan ko a saraka barata samu koda five
marks bane, Imran sai tambayan ta damuwan ta yake amma tak’i fad’a masa.
Har aka tashi suka koma gida kuka take gashi zuwa lokacin jikin ta yayi tsanani, kwanciya
kawai tayi saboda ciwo.
In tak’aice muku sati biyu suka d’auka suna Exam har suka gama har lokacin kuma bata
dawo saiti ba dan ko kula ta Ummy batayi, haka shima sam Mammy ta fita daga harkan sa
ba kalan hak’urin da bai bata ba amma tak’i sauraron sa.
Yau ya kama Sunday, Ummy na zaune Safwah ta shigo duk ta fita daga hayyacin ta, tausayi
ta bawa Ummy’n sosai inda ta kasa share ta a lokacin, hak’uri ta bawa Ummy’n sosai ta
nuna mata komai ya wuce, a ranar har hira sukayi sosai gwanin sha’awa.
Ranar shima ya samu Mammy ta yafe masa.
K’arfe hud’u Granny ta aiki Safwah bayan layin su, tana dawo wa ta jiyo waya muryar
yar budurwa tana mata magana, tsayawa tayi tana k’are mata kallo sannan tace ” Lafiya
dai ko?”
” Lafiya dan Allah Suwayd zaki kirawo min ” tayi maganan tana murmusawa.
“Kece Zee? ” kawai ta tsinci kanta da tambaya.
“Eh nice ” tayi maganan tana fad’ad’a fara’ an ta.
Nan take duk wani annurin fuskan Safwah ya b’ace saboda kishi a masifance tace” andai
ji kunya wallahi mace har mace amma ki kwaso k’afa wai kinzo gidan su saurayi, saurayin
ma da ba sonki yake ba to wallahi ko zaki mutu yau in baki ganshi ba sai dai ki mutu dan
bazan kira shi ba Mtsweee aikin banza kawai”.
Juyawa tayi zata shiga idanun ta sukayi mummunan gani, ko lura da Ya Sayyid dake
bayan Ya Suwayd batayi ba saboda rud’u.
“Lallai Safwah yanzu rashin kunyar taki harta kai ki kalli matar da zan aura ki fad’a mata
magana? Bata hak’uri kafin ranki yayi mummunarb’aci “.
Sunkuyar da kai tayi zuciyar ta na tafasa saboda tsananin kishi hawaye kam kamar an
bud’e lalataccen tap, ya zama dole ta bayyana masa sirrin zuciyan ta she can’t hide it
anymore, barata jure ganin Zee ta kwace mata shi ba.
Saida tayi gathering courage ta d’ago tana kallon cikin idanun sa yadda zaifi yarda da
abinda zai fito daga bakin ta tace ” Ya Suwayd ina son k..
Den den guys do you think zata fad’a masa? Wat wil be his reaction? Me Zee zatayi akai?
Sayyid fa? Mai zai faru dashi?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *