SOYAYYAH CHAPTER 10

SOYAYYAH





CHAPTER 10





“Ya Suwayd ina son kasa ni wallahi ko zaka kashe ni bazan ba wannan abar da kake k’ira
matar da zaka aura hak’uri ba, sai dai kamin duk abinda zakayi ” ta k’arasa maganan tana
pointing Zee yayin da take binta da kallon tsana.
Lokaci guda Sayyid da Suwayd suka sauke wata wahalaliyar ajiyar zuciya, rab’a sa tayi ta
wuce cikin gida da gudu tana kuka sosai, saurin bin bayan ta Sayyid yayi yana k’iran ta
amma tayi burus dashi.
Dakyar ya cimma ta ya rungume ta k’ank’am yana rarrashi sai da ta tsagaita da kukan yace
Baby na rashin kunya ba halin ki ba meyasa kike so ki koya? Meyasa zaki fad’a masa haka
bayan kinsan halin sa?”
Kuka ta sake masa sosai dan tasan baya jura nan take kuwa ya rik’a ce ganin haka ta lafa
suka K’arasa ciki.
Haushi da bak’in cikine suka kusa kashe Suwayd dan haka ya sauke duk wani b’acin ransa
akan Zee, yayi tafiyar sa ya kyale ta tana kuka a k’ofan gidan su wane zata cire ranta.
Yana tsaye a parking lot yana k’ok’arin barin gidan wayan sa yayi ringing, share wa yayi
amman ganin kiran yayi yawa yayi answering.
“Quess what? ” Musty ya soma da cewa.
“You know ain’t good at itjust tell am the damn business”
” Kai dai a haka zaka k’are always angry, now idan kaga dama kazo ka d’auke mu a airport
“You must be joking Man”
” Joke ba? “
“No, not at all ‘ll be right there”
Nan take ya nema duk wani b’acin ransa ya rasa though yasan may be k’arya suke masa.
Not long enough ya isa ya soma da neman layin Musty but switch off, nan take zuciyan sa
ya soma tafasa sai ji yayi an dafasa ta baya, ganin Abdul yasa ya sauke wata kyakkyawan
ajiyan zuciya farin ciki na mamaye sa.
Dariyan mugunta Musty ya shiga yi ma Suwayd, ya basa kyakkyawan punch a kafad’a,
hugging juna Abdul da Suwayd sukayi happily suna fad’a ma juna yadda sukayi missing
rayuwan Cyprus, jona su Musty yayi akai group hug, Suwayd ya soma breaking hug d’in
dan yasan akwai gajiya tattare dasu, mota suka wuce aka sanya kayan su sannan suka
wuce, a hanya Musty ke cewa Suwayd sufa a hotel zasu sauka dan ya fuskanta Sayyid da
Haidar ba son su suke tare da Suwayd ba.
Bayadda baiyi dasu ba amma suka k’i dole yayi leading nasu to NI’IMA HOTEL, nan take
sukayi booking room suka yada zango, sai da sukayi wanka suka ci abinci sannan aka shiga
hiran yaushe gamo, a hiran nasu Musty yake tambayan sa abinda ya b’ata masa rai d’azun
daya k’irasa, nan kuwa ya musu narrating all that happened.
Kallon sa Abdul yayi sosai sannan ya numfasa yace ” and baka tunanin Safwah tana son
ka?”.
” Lallai kana hauka inba haka ba tayama clumsy mind nakan zata baka haka”.
In serious note yace” Am damn serious may be tayi niyan fad’a maka tsoron ka ya hanata
cause da bakin ka kace ko sunan ka taji jikin ta rawa yake, wait ma kana tunanin haka
kawai Dan mace tazo wurin ka zatayi kuka? Seriously there is something behind her tears
and bare wuce kishin ka ba, what I want you to do now is ka kula da duk wani motsin ta
tahaka ne zaka gane what’s in her mind”.
Ajiyan zuciya ya sauke wane an tabbatar masa da abinda Musty keson fahimtar dashi
though bai yarda ba amma zai fara sanya ido akan ta kaman yadda Musty’n ya fad’a.
Through out the day suna tare sai bayan sallah’n isha ya wuce gida, dama yaci abinci acan
dan haka kawai ya nema guri ya kwanta abinsa, badan baison fad’a ba da har su Abdul su
tafi tare dasu zaina spending night harsu tafi.
Yana nan kwance yana ta tunanin maganan da Musty ya fad’a masa Sayyid da Haidar
suka shigo, k’arasowa ciki sukayi Sayyid ya nema guri ta gefen Suwayd yayin da Haidar ya
tsaya a tsaye fuska a had’e, binsu yayi da kallo batare daya tanka ba.
Ahankali Sayyid yace ” Akheey kaida waye kuke kwana a d’akin nan da bama nan? “
Kallon rainin hankali ya bisa dashi sannan a k’ufule yace ” kana iya shak’e ni sai na fad’a
maka”
“Aina fad’a maka kawai mu fad’awa su Abbah kace sai anyi bincike ai ga irinta nan zai b’ata
maka rai a banza, mu idan bazai fad’a mana ba ai nasan su zai fad’a musu ” Haidar yayi
maganan angrily.
With Cool like voice nasa yace ” Haba mana Akheey du abin baiyi zafi haka ba ka bari muji
ta bakin sa, ko a musulunci ai bincike halal ne Allah ma dakan sa ya fad’a acikin alqur’ani
mai girma _Fas alu ahliz zikri inkuntum la ta’alamun”_(ku tambayi ma’abota sani in kun
kasance baku sani ba), naga yanzu bare yu ace bamusan komai akan abinda muka gani ba
mun soma da tuhumar sa dole ya kamata mu nemi sani akan abin daga garesa”
Cike da fahimta Haidar ya gyad’a masa kai, maido da attention nasa yayi kan Suwayd yace
“Am sorry Akheey I don’t mean to hurt you but inaso nasan kai da waye kuke kwana idan
kuma kai d’aya ne me ya kawo kwalban wine d’akin nan? Waye kuma yasha? Idan kuma
shima baka sani ba zan kaiwa Abuh inyaso sai ka tanadi amsan bashi”.
Ya tsorata sosai amma ya moze yace ” Nifa bangane what you are all talking about ba idan
kuma an shirya muku zance ne kunzo ku sawa mutane ciwon kai sai ku fad’a “.
” Har wannan ma baka gane? ” Haidar yayi maganan a tsawace yana nuna masa
kwalban giyan da hannu.
Mik’ewa yayi cike da bala’i yace ” da ka fito fili ka fad’amin abinda ke cikin zuciyan ka da
yafi wannan kame_kamen da kake, and I don’t bloody care koma wa zakaje ka nunawa
tunda nasan ni bani da had’i da abinda kake jona min, tun Cyrus na riga da na fuskanci mai
kake nufi dani kawai dan ina tare da Abdul da Musty, to koma mai zakayi ni ba damuna
zaiyi ba ka sani ” ya mik’e ya fice falour.
Three seater ya nema ya kwanta akai yana maida numfashi, babu abinda yake buk’ata
alokacin sama da wine dan har wani zazzab’i_zazzab’i yakeji, he just can’t wait gari ya waye
ya wuce wurin shaid’anun abokan sa.
Jiki a sanyaye Haidar ya zauna kusa da Sayyid ya rik’o hannun sa, hankali a tashe yace”
Akheey meyake nufi da kalamun sa? Yana tunanin nima asan raina ne nake son rabasa da
abinda yake so? Meyasa zai min bahaguwan fahimta?”
A nitse Sayyid yace ” kasan halin sa da miyar da abu k’arami Babbal think kawai muje mu
basa hak’uri insha Allah one day the truth will be known”
Atare suka fito suka same sa ya lumshe idanun sa ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya.
” Kayi hak’uri wallahi ni bawai ina zargin ka bane is just that tun da naga kwalban wine
d’in nake tunanin ko kayi bak’i ne buh am sorry for hurting you ” cewan Haidar calmly.
Kayi hak’uri let’s just assume hakan bai faru ba ” Sayyid ma ya fad’a kindly.
Seda ya d’au about fifteen minutes sannan ya bud’e idanun sa ya aza akan su, ahankali ya
mik’e zaune wane baison magana yace ” komai ya wuce “, d’an hira kad’an sukayi suka
wuce duka suka kwanta.
The following day”
K’arfe bakwai Suwayd ya shiga part d’in Granny su gaisa, bata falour dan haka ya wuce
d’akin ta tana kwance ya k’araso ya gaishe ta, ta amsa ba kaman yadda ta saba ba.
Hakan ne ya tabbatar masa ba lafiya ba, tunani ya soma kodai su Sayyid sun fad’a mata
abinka suka gani muryan ta ya tsamo sa daga tunanin.
” Ina son magana da kai ” tayi maganan tana mik’ewa zaune.
Sallaya yaja ya shimfid’a ya zauna akai ya sunkuyar da kai wane mutumin kirki.
” Muhammad!! ” tunda yaji sunan sa kai tsaye bakin Granny yasan da matsala dan haka
dakyar ya daure yace ” Na’am”
” Inaso ka bud’e kunnen ka kaji abinda zan fad’a maka, kasan dai ba wasa nake dakai ba
ko?”
With Nod kawai ya ansa ta sannan ta d’aura da bayani ” Kana son Safwah ko baka son ta? “
Da sauri ya d’ago ” Haba Granny me kike fad’a haka? Kefa shaida ce akan “MAKAHON SON
da nake mata “
” Ba wannan na tambaye ka ba, kana son ta ko baka son ta? just answer me ” tayi stating in
serious note.
” Ina son ta ” ya fad’a from the bottom of his heart.
Alhamdlillah, so let’s put an end to it ko ka nunawa Baby kana son ta ka nemi soyayyar ta
ko kuma wallahi na cire hannu na akai, kuma insha Allah duk wanda ta fito tace tana so shi
za’a bata dan bazan bari a mata dole ba tunda kai na fuskanci bakasan mai kakeyi ba, ba
kasan kuma ina ke maka ciwo ba duk wani cewa da kake idan baka same ta ba mutuwa
zakayi da ne yake tsorata ni but not any more, so tun wuri idan zaka yiwa kanka fad’a kayi
idan ba haka kanaji kana gani zatayi maka nisa, tashi ka tafi ka bani guri “
Jiyayi kansa na juyawa gaba d’aya duniyan ya masa zafi, Granny da yake gani itace only
hope nasa gurin mallakan Safwah yau ta cire hannun ta, ina zai sa rayuwan sa ta ina zai
soma fad’awa Safwah yana son ta, hankali a matuk’ar tashe ya mik’e ya fice ko Safwah data
fito daga d’akin su bai lura da ita ba fice, tunda ya shiga mota yake uban horn kaman tashin
sense da sauri gate man ya bud’e masa yaja motan da wani mugun speed ya fice.
A yanayin da yake yasan Abdul da Musty ne zasu iya maganin matsalan sa batare da b’ata
lokaci ba dan haka ya wuce wurin su.
A kalan bugun da yake musu Abdul yasan ba lafiya dan haka without hesitation ya bud’e
masa, yana shiga ya nema guri ya zauna ya dafe kansa dake barazanan tarwatsewa ganin
haka yasa Musty d’auko wasu Syrups ya d’aura masa a cinya.
Kaman wani sauna haka ya bud’e d’aya ya kafa kai saida ya shanye tas ya yasar da empty
bottle d’in, ya bud’e wani take shima ya gama masa aiki ya soma neman k’ari, Musty na
k’ok’arin basa Abdul ya hana dan ya fuskanci ba a hankalin sa yake ba.
Baifi twenty minutes ba yaji duk damuwan sa sun gushe zamewa yayi a kujeran da yake kai
ya kwanta tun yana surutu har bacci yayi taken nasa.
Tausayin sa sosai Abdul yake ji dan ya fuskanci yadda yake mahaukacin son Safwah gashi
ya riga ya kashe kansa ta yadda ko ya fito ya fad’a mata barata yadda ba.
K’arfe sha biyu ya tashi saida yayi wanka ya yaci abinci ya nutsu sannan ya fad’a musu
abinda ya faru ya kuma fad’awa Musty yadda Syrup d’in yayi masa aiki.
A zuwan da sukayi gaba d’aya rayuwan Suwayd ya sake tab’arb’arewa gashi tun abinda
Granny ta fad’a masa haryau yak’i komawa gida almost five days.
Gida kuwa kowa hankalin sa a tashe yake more especially Granny da Safwah, Mammy da
Abbah ne ko a jikin su duk da cewa they are burning inside amma basu bari ya fito fili ba.
Kowa mamakin lalacewar Safwah yake amma tace ita mafarkin da take ne, sosai kuwa
suka yarda dan ko ishashshen bacci bata samu, idanun ta duk sun chanja kala.
Kiran duniya anwa Suwayd amma kullum wayan a kashe, har asibitin su aka k’ira suma
suka bada complain na rashin zuwan sa.
Sai da yayi sati d’aya cif bayan ya raka Abdul da Musty ya wuce gurin Dr lmran, sosai
hankalin sa ya tashi ganin yadda ya zabge ya rame kaman wanda yayi jinyan shekara,
shikuwa bakomai ke damun sa ba sai tunanin mafita.
Rok’on Dr Imran yayi daya saka masa drip sannan ya k’ira gida ya shaida musu yana
kwance a asibiti, dakyar ya samu Dr ya amince.
Ai kuwa ana kira duk suka shirya suka tawo duba sa, yanajin alaman zuwan su ya sake
marairaicewa, Granny na ganin halin da yake ciki du ta d’aurawa kanta laifin.
Safwah kam kasa jure ganin sa ahakan tayi ta fice taje ta samu gurin da babu kowa tasha
kukan ta kaman ba gobe.
Sai da yayi kwana biyu aka sallame shi suka koma gida har kuma lokacin bai sauk’o daga
fishin marin da Mammy tayi masa ba, shiyasa ma da tazo duba shi yak’i koda kallon ta talk
less of yi mata magana.
Haka rayuwan keta tafiya yayin da shaye_shaye ya zamo jinin jikin Suwayd wanda kullum
sai yayi yake samun nutsuwa, sosai ya sanya ido akan Safwah amma haryanzun baiga wani
alama da zai nuna tana son sa ba dan haka ya watsar da lamari.
Su Safwah sai murna ake finally za’ayi graduation kuma tare zasu had’e da saukan su.
Sayyid kullum cikin yin abinda zai farinta ran Safwah yake yayin da itama take k’ok’arin
farin ta masa dan ko kad’an bata bari yaga chanji tattare da ita ba duk da sometimes yana
mata k’orafi.
Bayan candy’n su Safwah da sati d’aya aka tsayar da bikin Ya Omar da Samha sai Ya
Uthman dazai auri ‘yar k’anwar Mummy.
Suna Exam suna tsare_tsaren biki sun riga da sun tanadi komai, with success kuwa suka
gama Exam nasu inda sukayi gagarumar walima saboda candy da sauka suka had’a
shiyasa basuyi party ba, a ranar Suwayd kaman ya cinye Safwah dan yadda ta mugun tafiya
masa da imani, yayin da Sayyid kuma sai nan_nan da ita yake.
Gifts har rasa inda zata sasu tayi kuma yawanci Suwayd ne ya ajiye mata which ita bata sani
ba.

Ya kama Thursday ranan da za’a soma event ta biki, kamu dashi za’a soma inda za’ayi a
DARUL TAUHID” rawar kai gun su Safwah ba kama k’afan yaro.
K’arfe biyar duk aka soma tafiya amma har lokacin Safwah bata shirya ba dan ita tayiwa
kowa make-up, sai da ta gama duk sun tafi sun barta sannan ta shiga wanka, bata wani
jima ba ta fito ta tsane jikin ta sannan ta soma tsara kwalliya kaman baza’a a mutu,
had’uwa iya had’uwa tayi gashi sam bakin ta yak’i rufuwa, ankonta ta sanya ta kafa d’aurin
Zara buhari ta fito caras da ita kamar itace amaryar, had’ad’d’iyar wayarta ta d’auka to
soma selfie.
Saida tayi mai isan ta sannan ta zari zililin mayafinta ta sak’alaa kafad’a, Sayyid ta k’ira
tana ta zub masa shagwab’a ta fad’a masa ta shirya.
Haka kawai taji tana son zuwa garden tayi hoto dan haka ta wuce tana ta zuba k’amshi
wane mai aiki a company’n perfumes, mutum ta hango zaune a kujerun dake wurin
Swimming pool nan take ta soma tunanin to mai yake yi.
Tun da ta shigo mayataccen k’amshin turaren ta yayi masa sallama lumshe idanun sa yayi
dan shaf ya manta da kwalaban whiskey d’in dake gaban sa, gashi ya fara ficewa a hayyacin
sa dan sosai ya shawu.
Haka kawai taji tana son k’arasawa gurin taga waye duk da jikin ta ya gama bata Amirul
qalb d’in tane, da takun ta kamar hawainiya ta taka ta isa inda yake, kaman me neman abu
ta d’urk’ usa k’asa ta soma lalube, saijin saukan lallausan hannun Suwayd dake sending
shivers down her vain tayi akan lallausan gashin bayan ta, kasantuwar show me your back
ne d’inkin yasa ya bayyana.
A tsorace ta d’ago nan idanun ta sukayi mummunan gani, kallo Suwayd ya kai inda take
kallo gaban sa yayi wani irin mummunan fad’i, mik’ewa tayi a razane jikin ta na rawa zata
gudu yasanya mata k’afa ta fad’o kansa.
A rikice ta soma k’ok’ari kwatan kanta amma ta kasa dan yadda ya rik’eta k’ank’am, shafa
fuskan ta ya somayi yana maganan yan maye jin hakan ya tabbatar mata da zargin da
zuciyan ta take, ganin yana matso da fuskan sa zuwa nata ta ture sa da k’arfin da Allah ya
bata ta gudu.
Bata tsaya ko ina ba sai d’akin su tasa lock tayi throwing kanta a bed ta shiga rera kuka
kaman ba gobe, tanaji wayan ta na ringing amma tak’i answering daga k’arshe ma
kashewa tayi gaba d’aya.
Sosai hankalin Sayyid ya tashi gashi Granny tace masa duk sun tafi, dan haka ya wuce ya
koma amma sam she is no where to be found.
Suwayd describing tashin hankalin daya shiga b’ata baki ne he just can’t believe Flower’n
sa ta kamasa red handed a wannan hlin, mik’ewa yayi ya kwashe komai yana had’a hanya
ya isa part d’in su yana shiga yasa lock shima ya soma aikin kuka, bai tab’a nadaman shan
giya ba sai yau da Safwah ta kamasa abinda yafi d’aga masa hankali bai wuce yadda yaga
disappointed k’arara a idanun ta ba.
Ina zai tsoma rayuwan sa shi shaida ne akan mugun tsana da kyankyamin mashayin giya
da mazina ci da Safwah tayi, ta ina zai soma wanke kansa a gurin ta not that ma idan ta
fad’awa su Abuh ya zaiyi wani mataki zasu d’auka akan sa wannan duk Allah ne yabarwa
kansa sani, amma wani shashi na zuciyan sa na tuna masa yadda Safwah ke barin abu a
zuciya koda kuwa ita d’in zai cutar da ita.
Anata b’angaren saida taji kanta na tsananin sarawa ta tsagaita da kukan ta soma da
tambayan kanta, mai Ya Suwayd ya rasa dazai gurb’ata rayuwan sa haka haba mana no
wonder sometimes idan yayi wani abin kaman yana shaye_shaye ashe dagaske yanayi, ya
Mammy da Abbah zasuji wannan mummunan labari, sabon kuka ne ya kwace mata nan
take kuma maranta ya soma ciwo, zafi biyu gana zuciya gana ciwo haka ta kasance cikin
mawuyacin hali har aka soma dawowa daga bikin.
Dakyar ta lallab’a taje ta bud’ewa su Lubna k’ofa, duk fishin da suka d’auka da ita da
sukaga halin da take ciki sai suka nema fishin suka rasa, kowa ya soma jera mata sannu
itakuwa bawai ciwon maran ne yafi matsanta mata ba sai tunanin Ya Suwayd, rok’on Allah
ta somayi Allah yasa yabar garden d’in dan apart from ita bataso kowa ya sani.
Pain killer nata Kuwaysah ta mik’a mata batare da b’ata lokaci ba kuwa amsa ta had’iya
sannan ta shige toilet tayi wanka ta fito ta tayi shirin kwanciya ta kwanta dan batason
takura.
Sam bacci ya k’auracewa idanun ta dan data rufe Ya Suwayd take ganowa, lokacin da bacci
ya d’auke ta kuwa lokacin ta soma Mafarkin nata na kullum, a rikice ta mik’e zaune taga
yadda du suke baccin su hankali kwance.
Had’a kai tayi da gwiwa tana kuka ahankali.
Suwayd sai da yayi kuka mai isan sa sannan ya shiga toilet yayi wanka ya fito yayi shirin
kwanciya yabi lafiyan gado.
Da asuba dasu Haidar suka ga yadda idan sa suka kumbura sai ce yayi musu ciwon ido yake
yi, shiyasa ma bai samu daman zuwa gun bikin ba.
Suna dawowa daga masallaci su Sayyid suka shige cikin gida shikuma ya wuce part d’in
su, can bedroom ya wuce yasa lock ya k’ira Abdul ya irga masa halin da ake ciki dan yasan
Musty ba hankali ya cika ba when it comes to this situation.
Arikice yake ce da Abdul a chanza shawara dan bare iya abinda yace masa ba, nuna masa
Abdul yayi that’s the only way zasu bi in ba haka ba kuma bai san ya za’ayi ba, saida ya
tabbata Suwayd ya amince sannan ya kashe wayan.
Sai a lokacin nutsuwa ta saukar masa nan take kuwa bacci ya d’auke sa, k’arfe goma ya
tashi yayi wanka ya shirya dan ranan za’a d’aura aure da daddare kuma dinner.
K’arfe sha d’aya dubban al’umma suka shaida d’aurin auren Omar Sufyan Muhammad da
amaryar sa Hauwa lbrahim Muhammad dana Uthman Sufyan Muhammad da Amaryar sa
Zahra’u Adam Yusif akan sadaki dubu hamsin da galleliyar mota.
Hotuna akayi sosai sannan aka soma tafiya reception d’in da za’ayi walima, neman
Suwayd su Haidar sukayi suka rasa dan haka suka tafi.
Part d’in Ummy yaje yaci abinci ya k’oshi sannan ya wuce gun Granny, suna cikin gaisawa
Safwah ta fito chas da ita kaman asace ta a gudu, ahankali ta k’araso ta d’urk’usa duk da
cike take da haushin sa tace” Ya Suwayd ina kwana?
Lafiya lau Alhamdlillah ki d’auko mayafin ki zamu fita ” yayi maganan fuska a had’e.
Granny kuwa wani farin ciki ne ya mamaye mata zuciya ganin Suwayd ya soma hankali
tunda har zai fita da Safwah.
” Ya Suwayd akwai abinda zan taya mammy.
Bai bari ta k’arasa ba ya buga mata wani firgitaccen tsawa, batasan lokacin data tsinci
kanta a d’akin su ba ta d’auko mayafin ta dawo, sanya ta yayi a gaba suka fice ya bud’e
mota suka shiga yaja suka tafi.
Hawaye take sosai dan tasan mai kwatan ta yau agurin sa sai Allah ga yadda marar ta ke
ciwo sosai, k’in Kallon side d’inta yayi dan bazai iya juran ganin ta ahaka ba, haka har suka
isa gaida kuka uku, bakin wata ‘yar K’aramar gida yayi parking motan sa suka fito su duka.
Ganin shi yake bud’e gidan yasa tsoro ya sake kama ta, juyowa yayi fuskan nan babu
annuri yace ” shige muje”
Daurewa tayi tace ” Ya Suwayd wai mai zamuyi aciki? “
” Bansani ” yayi maganan a hasale ya fuzgi hannun ta ya tura ta ciki.
Shiga yayi shima ya maida k’ofan ya rufe sannan ya cigaba da janta har cikin falour’n,
suna shiga ya sake ta yaje ya rufe k’ofan ya dawo ya nemi guri ya zauna ya d’aura k’afa
d’aya kan d’aya.
Tana tsaye tana hawaye jikin ta banda rawa babu abinda yake ta tsinkayo muryan sa.
“Uban me kika gani jiya a garden? “
Girgiza kai ta somayi tana kuka sosai ta jiyo had’ad’d’an mari a kuncin ta nan take ta bud’e
baki tace ” Wallahi Ya Suwayd banga komai b…”
” Shut up you asshole idan kika kuskura kika min rantsuwa kan k’arya sai naci uwar ki
wallahi”.
“Me kika gani… “
Bata bari ya k’arasa ba tayi saurin tare sa “Wallahi kai nagani and nothing else”
2:26 PM
OL *o*
Wallahi kika yarda kika sakeyi min k’arya sai ranki yayi mummunan b’aci, ko zaki ce
wannan ma baki gani ba? ” ya k’arasa yana pointing mata kwalb’an whiskey da wine dake
ajiye akan center table.
” Nagani ” ta ansa finally.
” Good me akeyi dasu?”
D’agowa tayi tana Kallon sa amma ganin fuskan sa yawa pregnant sky ta runtse ido tace”
shaye_shaye”
” Wa yake yi? ” ya sake jefa mata tambayan.
Sosai amsan tambayan ya mata tsauri dan haka tace ” Ya Suwayd dan Allah kayi hak’uri ka
kyale ni let’s just assume banga komai ba..”
“Shut up you stupid bitch and answer me”
” Tana kuka sosai tace ” kaine”.
Murmushin mugun ta ya sake yana binta da wani mitsiyacin kallo yace ” ki bud’e kunnen ki
kijini zan baki zab’i biyu kuma aciki dole zakiyi d’aya, ko ki d’auka kwalban nan ki shanye
mu zama at the same position ko kurma ki wuce muje d’akin can “
” Subhanallahi, innah lillahi wa’innah ilaihir raji’un ya Suwayd kana nufin nasha giya?
Yanzu tsanan daka min harya kai kasa na sab’awa mahalicci na? Me nayi maka kake
treating d’ina haka? Wallahi Wallahi ko zaka kashe ni bazan sha ba sai dai duk abinda
zakayi kayi tunda nasan kai d’in baka isa kamin abinda Allah bai min ba “. Ta k’arasa tana
kuka sosai yayin da ciwon maran ta ke tsanan tuwa.
” Tabbas nayi sake har raini ya shiga tsakanin mu amma yau basai gobe ba zanyi maganin
abin, yadda nan gaba koda kud’i akace ki kalle ni ki fad’amin magana bazakiyi ba”
mik’ewa yayi ya cire rigan sa ya rage daga shi sai singlet.
Wani mugun tashin hankali da tsoron sane suka rufe ta a rikice ta soma ja da baya yana
nufan ta har takai jikin bango, k’ank’ame jikin ta tayi tana kuka sosai da sosai taji ya zame
mayafin ta ya cillar gefe.
” Ya Suwayd dama bayan shaye_shaye har neman mata kakeyi ” ita kanta batasan lokacin
da kalama suka sub’uce mata ba tsantsan tashin hankali yasa ta furtawa.
” Kamar yadda kika gani, nasan daga jiya zuwa yau kin zaki gama sani na da halina “.
Tura k’ofan bayanta yayi ta tafi zata fad’i ya rik’o ta d’an k’ofar ce ta mata garkuwa.
Cike da rainin hankali yace mata ” Baby suke ce miki ko me oho miki dai, zaki bari muyi a
nutsuwa ko saina sa k’arfi?”
Ture hannun sa tayi dake yawo ajikinta ta durk’ushe a k’asa ta rik’e k’afafun sa tana
apologizing.
Ahankali shima ya durk’usa ya d’ago hab’an ta yana yawo da hannun sa guda d’aya a
fuskan ta yana maisa duk wani gashi a jikin ta mik’ewa, in a sexy voice yace ” dama kinyi
saving kukan ki dan a yanzu bazai miki amfani ba sai nan da d’an wani lokaci, in kina
tunanin kukan ki na sa naji tausayin ki tun wuri ma ki daina dan Allah ne kad’ai yasan halin
da nake shiga idan naga hawayen ki saboda farin ciki, yanzu ki tashi kinga anjima zamuje
dinner gashi kuma zakiyi jinyan kanki kafin lokacin “.
K’ara ta kwalla da damk’e maran ta cike da tsananin azaba, tausayi ta basa amma ya kawar
dakai dan karta fuskan ta.
Hannu sa ta rik’o tanaji wane bayan ta zai b’alle hawaye na forming rapidlya idon ta tace
” Ya Suwayd na rok’e ka dan Allah ka kaini gurin Ummy na namutu a hannun ta “
“Harkin manta abinda muka zoyi kenan?”
In crying tone tace ” ka chanza wani abun Ya Suwayd wallahil promise to keep your secret
no matter what, koda kuwa hakan yana nufin rasa rayuwa ta amma barin iya abubuwan da
kake so mu aikata ba “
You promised kika ce?”
” Yes I do ” ta basa answer confidently.
Idan kika karya alk’awari na miki me?”
“Duk hukuncin da kaga ya dace”
“That’s good then tashi mu tafi and banyarda kowa yasan maganan gidan nan ba'”
” Tohm insha Allah”
Dakyar ta mik’e tana takawa a wahalance ya d’aukar mata mayafin ta suka wuce, har suka
kusa isa gida hankalin ta ya kasa kwanciya dan in ba ganin ta jikin Ummy tayi ba
bakwanciyar hankali.
A gate ya ajiye ta yaja motan sa ya tafi gurin su Haidar sai da aka gama komai sannan suka
wuce masallacin juma’a.
K’arfe bakwai an gama shirin tafiya dinner amma banda Safwah dake a matuk’ar tsorace,
sai da Ummy ta mata jan ido sannan ta samu ta shirya tabi Ya Sadeeyq da Aunty Zarah suka
tafi tare, surna zaune a baya ita da Baby Amal har suka isa “Meenah Event Center’ dan a can
za’ayi.
Aunty Zarah da Ya Sadeeyq sai kod’a ta suke tana binsu da murmushin yak’e dan har
lokacin bata dawo dai_dai ba.
Tana rik’e da hannun Amal suka shiga, guri suka nema suka zauna suna kallon yadda ake
gudanar da al’amura.
Suna nan su Suwayd suka shigo inda sam ya kasa d’auke ido akan Safwah ita kuma saita
alak’an ta hakan da yana bin movement nata ne yaga ko zata fad’awa wani, gaba d’aya ta
kasa sakewa shiko tsananin kyan da tayi masa ne yasa ya kasa dena kallon ta.
Kamar a mafarki taji Mc na kwala mata k’ira, k’in fita tayi Aunty Zarah ta takura mata dole
sai da ta fita.
Gaba d’aya aka bada fili aka mata playing shaku_shaku dan ta taya amare da angwaye
farin ciki, bata da option daya wuce soma rawan kowa binta da kallon sha’awa yake yadda
take rawan a nitse kafin kace me ‘yan lik’i sun bai baye ta, haushi ne ya ishi Suwayd ganin
yadda maza suka cika gurin harda masu yin lik’in badan Allah ba, ga d’an banzan Mc da
yaga yadda ake masa ruwan kud’i sai ya sake playing mata wasu wak’ok’in.
Kishi ne yasa Suwayd zuwa ya janyo ta gaba d’aya daga filin ya miyar da ita kusa da Aunty
Zara fuska a had’e ya kalle ta yace ” kika sake shiga wallahi sai ranki ya b’aci tunda baki da
hankali useless kawai “..
Neman kujeran kusa da ita yayi cike da takaici ya zauna, duk wanda ya kunno kai wurin
Safwah da yaci karo da fuskan angry Suwayd sai ya juya but still sai da aka samu masu
k’arfin halin cewa Suwayd sunga k’anwar sa suna so.
Jarababben kishi yasa yace sai ta tashi sun tafi, badan ranta yaso ba ta mik’e yasa ta
agaba suka wuce.
Yana gwada cewa bari ya chanza hanyan gidan Safwah ta soma kuka tana rantse_rantsen
ita bata fad’awa kowa ba, yadda ta K’ank’ame hannun sa yafi komai basa dariya amma ya
moze, ya tsaida motan a road side ya had’e rai yawa pregnant sky.
Ke!!”
Da sauri ta d’ago tana kallon sa da kumburarrun idanun ta, murya a dishe tace ” Na’am “
“Ki bud’e kunnen ki kiji, kin riga kinyi promise and no backing out, da bakin Ki kikace if
you break the promise na miki duk abinda naga ya dace right?”
Saurin gyad’a masa kai tayi jin yadda ya murd’a mata kunne cike da mugunta ta sake siririn
k’ara idanun ta na cikowa da kwalla tace ” Eh na fad’a”
” Good girl, now listen to me very careful duk wanda kika yi kuskuren fad’awa hukuncin
ki shine aure na ko kina so ko bakya so and karkiyi tunanin da wani manufa zan aure ki, zan
aure ki ne dan inyi making life naki miserable hell saboda sirri na da kika sani, in fact ban
tab’a kallon ki a mace ba balle kiyi tunanin ko wani abu naki yaja hankali na nake son na
aure ki not at all zanyi hakan ne dan na cigaba da muzguna miki har k’arshen rayuwar ki,
am I clear?”
Cike da tsananin tsoron sa tace ” Ya Suwayd aure?”
“Yes ko kina tunanin wasa nake? Oya try me and see “
“I need a favor ” tayi maganan tana kuka sosai.
“Bazan yi ba ” ya answer ta finally
Cusa kanta tayi tsakankanin cinyoyin ta tashiga rera kuka abin tausayi sosai taji dad’in
kalamun sa at the same time kuma tsoron dalilin da yasa zai aure ta, agaban iyayen ta ma
bai rangwan ta mata ba balle ta zamo ak’ark’ashin sa bazata iya b’oyewa Safwan ba cause
shine abokin shawaran ta, ya zamo mata dole ta shaida masa dan bata da mafita a wannan
al’amarin dake shirin faruwa da ita.
Tsawan daya buga mata ne ya sanya ta yin shiru ta koma jera ajiyan zuciya, har suka isa
gida ba wanda ya sake magana.
Part d’in su ya wuce cike da farin ciki ya dannawa Abdul k’ira, yana d’agawa ya fuskanci
how happy Suwayd is.
“Maza!! Nagode, nagode sosai words can’t describe how much you mean the world to
me, shawara ka have sort things out “
“Don’t tell me mutumina “.
“Ka bari kawai na riga na gama da ita again yanzu haka na samu solutions wa Granny’s
issue
” Fad’amin ya hakan ta faru so easily? “
Nan take kuwa ya masa narrating all that happened cike da tsantsan farin ciki.
“Na tayaka murna mutumi na ai dama na fad’a maka da kayi attempting raping ta ko
sanya ta shaye_shaye zata tsorata, so yanzu kana tunanin zata fad’ama wani har ka samu
daman tilasta ta auran ka?”
“Yes I have once tell you duk duniya bata b’oyewa Safwan damuwan ta so zanyi amfani da
wannan daman na sanya ido akan ta, dan duk lokacin da tayi abin rashin gaskiya I use to
understand it by her actions, kaga na gama da wannan sai dai inajin tausayin Sayyid sosai
bansan kuma ya zai d’auki lamarin ba dama su Abuh bansan ya zasu kalla abin ba? “.
” Karka wani damu kanka Granny na k’aunar ka sosai kasan yadda zakayi ka sata basu
umarni ba shawara ba, Sayid kuma is so cool nasan zai yarda da k’addara amma wallahi
Safwah na bani tausayi ina jiye maka tsoron ranan da zaka shiga hannun ta, yanzu kai ke
playing role naka nan gaba kuma ita zatayi dan nasan da zaran ka mallake ta you can’t hide
the love you have for her anan ne zaka gane baka da wayo maza, ni wallahi when the time
comes ma Nigeria zan dawo na dinga kallon show “
” Lmao you are so funny wallahi dana mallake zuciyan ta shikenan na gama da ita dan
nasan ita abinda zatayi ma sai yafi na Zee”
Dariya sosai Abdul ya tsaya yi kafin yace ” Ohhh haka kace?”
“Ai hakan ne ma ” yayi. answering confidently.
” Shikenan Allah ya kaimu lokacin zan tuna maka kalamun ka word by word insha Allah,
now back to business Musty na nan yana fama da kansa tun wuri ka koma shan hankali if
not wallahi you will regret all this shit ranan da nadaman bare ma amfani ba “
” Subhanalla meya same sa?”
” Sunce dai k’odan sa ya soma samun matsala sai appendix, yanzu ma aiki aka masa “.
Innah lillahi wa’innah ilaihir raji’un yaushe haka ta faru baka fad’amin ba?”
“No need to tell you tunda kaima lokacin you are not in a good situation and karka damu
fa yaji sauk’i dan harya koma ruwa, na d’au ma zai rage amma kaman k’ara masa akai dan
sai abinda yayi gaba ya riga ya zama so addict shiyasa yake so ku taru ku zama d’aya “
” Zan shigo insha Allah next week “
“Wow kace Ghana zatayi bak’i ai kuwa ba kanta “.
” Kai dai ka bari sai na shigo kawai”
Hira suka yi sosai sannan suka kashe wayan.
Da sauri Mammy tabi bayan Safwah ganin yadda ta shigo a hargitse, tana shiga ta iske ta
flat tayi ruf da ciki akan gado tana rusa kuka wane wadda akace uwar ta da uban ta sun
mutu, gashin ta duk ya barbaje kaman zararriya.
Ahankali Mammy ta k’arasa ta d’agota ta janyo ta jikinta ta soma aikin rarrashi, dakyar ta
samu tayi shiru sannan ta d’ago ta suna fuskantar juna, sai da ta had’e hannayen su gu
d’aya sannan ta soma magana ” d’ago ki kalle ni Baby”.
D’ago da jajayen idanun ta tayi ta d’aura su kan na Mammy tana ta jera ajiyan zuciya,hakan
kad’ai ya isa shaida maka yadda taci kuka ta gode Allah.
Cike da kulawa tace ” me yake damun ki? me yasa kullum kike kuka? Kina kallon kanki a
mirror kuwa dubi fa yadda kika bi kika rame alamar bakya tare da kwanciyar hankali me
yayi zafi haka? Fad’amin kar kiji tsoro insha Allah damuwan ki yazo k’arshe ko Ya Suwayd
n.
Ai bata bari Mammy takai k’arshen zancen ta ba tayi saurin tare ta ” A’ah wallahi Mammy
mara na ke ciwo ” tayi maganan tana fashewa da matsanancin kuka.
Murmushin takaici Mammy ta sake tace ” Halayyan ki sun soma chanzawa Safwah why?
Meyasa kike min k’arya? Saboda ni ba Ummy bace?”
Girgiza kai ta somayi tana kuka sosai “A’ah Mammy tsoro nakeji bana iya bacci sosai da
zaran na kwanta nake soma mummunan mafarki, shiyasa kika ga du na zama haka…”
Kukan da yaci k’arfin ta ne yasa ta yin shiru, janyo ta Mammy tayi jikin ta cike da tausayin ta
sannan ta soma magana a nitse ” kici gaba da addu’a kinji Allah yana tare dake, kukan nan
da kike was never a solution kinji? “
With nod ta answer sannan Mammy ta mik’e ta shiga toilet ta had’a mata ruwan wanka,
sai da tayi wankan ta fito ta kwanta bacci sannan Mammy ta tofe ta da addu’o’in tsari ta
tafi.
Juyi tayi tayi har bacci ya d’auke ta.
Washe gari aka k’are biki aka kai amare su Safwah sun sha kukan rabuwa da Samha saika
ce wadda ta tafi kenan har abada.
Yanzu duk tunanin Safwah bai wuce yadda zata fad’awa Safwan damuwan ta ba, amma ta
rasa hanyan da zata bi ta fad’a masa saboda tsoron Ya Suwayd.
Ab’angaren Suwayd kuwa k’arya yama su Abbah wai zaije duban patient Ghana, basu gano
komai ba dan haka suka masa izini, kafin ya tafi Saida ya tsorata Safwah sosai wai yasa
CCTV camera a ko ina inta ga dama ta fad’a zata ga mai zai biyo baya.
Tad’an samu nutsuwa da tafiyan nasa amma dai still tana d’ar_d’ar.
Shi kuwa tunda yaje Ghana Iskanci ya dad’u har tsautsayi ya kusa auka masa ya shiga trap
d’in wata yarinya, one week yace dasu Abbah zaiyi amma sai gashi da one month a hakan
ma badan son ransa ya dawo ba sai dan yadda su Abuh suka dame sa da waya.
Yau Safwah na zaune a falour’n Granny sanye da black three quarter skin tight da dark pink
best, kanta ko d’an kwali babu ta baza gashin ta a bayanta tana playing favourite game
nata Subway a wayan ta, sai ihu take kaman k’araman yarinya dan tasan monster natan
haryau bai dawo ba ga Sayyid ma yaje Abuja bai dawo ba.
Ahankali sukayi sallama suka shigo jin shiru ba’a amsa su ba suke sake nanatawa for the
second time but still no respond, sai da sukayi na uku kawai suka k’ara sa shigowa.
Sayyid ya lallab’a ahankali ya rufe mata ido ” Ohh Granny please ki bari za’ayi gaming ina”
tayi maganan a shagwab’e tana d’an buga k’afa.
Hannun ta tasa guda d’aya da niyyar cire hannun daya rufe mata ido, ” Ya Sayyid!! ” tayi
ex claiming da k’arfi dan karya ce bata murna da dawowan sa, ajiye wayan tayi a gefe ta
mik’e da sauri tayi hugging shi tana fad’a masa how much she misses him, ahankali shima
ya zagayo da hannun sa ta bayan ta hugging her back yana fad’a mata shima yadda yayi
kewan ta, du anan bata kula da angry Suwayd ba.
Shikuwa wani jarababben kishi da bak’in ciki ne yasa ya nemi guri ya zauna yaga iya
gudun ruwan su.
D’agata Sayyid yayi yana juyi da ita with so much adoration yayin da ita kuma keta dariya
kaman Baby.
Da fara’a Granny ta fito tana fad’in ” sannun ku da zuwa mutan Ghana da mutan Abuja “,
aijiye Safwah Sayyid yayi cike da kunya ya k’arasa gun Granny yana tsokanan ta wai tabi ta
damu kanta bata ga mijin ta ba, to gashi nan yaje ya tawo mata dashi.
Juyowan da Safwah zatayi idon ta ya sark’e dana Suwayd dake binta da wani banzan kallo
saboda shigar dakejikin ta.
Mozewa tayi tai kaman bata san mai yake nufi ba.
“Dan uwarki wuce kije kisa hijab ” ya buga wata wani shegen tsawa hakan kad’ai ya isa
shaida maka yadda yake mahaukacin kishin ta.
Banza tayi masa tana k’unk’uni shikenan ya dawo zai d’aura a inda ya tsaya.
“Don’t let me repeat myself ” ya nanata da kakkausar murya.
Mik’ewa tayi badan ranta yaso ba ta nufi d’akin su, tana rik’e handle ta jiyo ringing d’in
wayan ta and ko ba’a tasan waye dan shi kad’ai ta sanyawa wannan wak’an, cike da
zumud’i ta juyo dan harga Allah ta manta da warning d’in Suwayd, tana kai hannu zata
d’auka taji saukan gigitaccen marin da saida hab’o ya b’alle mata.
Sound d’in marin ne ya janyo hankalin Granny da Sayyid, har cikin ransa Sayyid ya jiyo
marin amma ba yadda ya iya.
Fincikar hannun ta yayi bai tsaya ko ina ba sai d’akin su wane kayan wanki haka ya cillata,
sannan ya dube ta a wulak’ance ” ke mahaukaciyar inace wai? Sau nawa kike so na fad’a
miki ganin ki a haka disgust me? Wallahi, wallahi, wallahi kinji nayi rantsuwa har sau uku
duk sanda kika yarda na sake ganin ki haka bazan b’ata lokaci ba gurin cin bura’uban ki
shegiya mai idon aljanu kawai mtsweee” yaja wawan tsaki ya barta yashe a k’asa tana
kukan fitar rai.
Sayyid ne ya shigo d’akin cike da damuwa, ahankali ya k’arasa inda take ya d’ago ta yana
aiki rarrashi hanky ya ciro a aljihun sa ya soma goge mata jini dake fita ta hancin ta, dakyar
ya samu tayi shiru amma yatsun Suwayd na nan tar akan kyakkyawan fuskan ta, hannu
yakai gurin cike da tausayi ta soma yarfe hannu dan shagwab’a.
” Sorry princess shiyasa na damu ki bari nayiwa su Daddy maganan auren mu kowa ma ya
huta, amma da zaran na soma magana saiki b’ata fuska na fad’a miki Allah zan barki ki
cigaba da karatun ki kinji? “
Ita fa Ya Sayyid ya soma takura ta yanzu kullum bashi da magana daya wuce na auren su
shin bare gane ita bashi take so yanzu bane!!
Turo baki kawai tayi ta had’e rai ganin haka ya ciro wayan sa ya k’ira mata Safwan yaba ta,
2:28 PM O.
l. 58)
tana k’arfa ta sake sabon kuka, ko ba’a fad’a ba yasan sarkin mugunta ne ya tab’a masa ita
dan haka ya soma da rarrashi sannan suka shiga hira.
“Ai ka dawo shikenan yarinya bata da kwanciyar hankali, tafiyan da kayi harta ciko ta soma
dawowa dai_dai amma yanzu bala’in ka zai maida ta gidan jiya, nad’au kayi hankali kan
abinda na fad’a maka ashe ba haka bane, fisabilillahi kabi ka takura rayuwan yarinya
kamar ba ‘yar uwar ka ba, haka ake rayuwa? Wallahi ina guje maka ranan nadama dan
wannan abin da kake zai kaika ne ya baro ka, ni ban tab’a ganin inda ake maida S0*
k’iyayya ba sai akan ka, wallahi in baka yi taka tsantsan ba hukuncin da zan yanke bazai ma
dad’i ba”
“Tuba nake Kakar mu mai ran k’arfe, ba laifina bane wallahi kishin ta ne yake sa nakasa
controling kaina “
” Dallacan rufamin baki ni, kishin banza kishin wofi da ana sonka ne sai ka zak’alk’ale haka
aikin banza kawai ” tayi maganan cike da takaici ta wuce d’aki ta barsa falour’n cikin
k’unan zuciya.
“Sayyid kazo mu wuce kasan su Ummy basu san mun dawo ba ” yayi maganan da d’an ihu
yadda zai jiyo sa.
Fitowa yayi ya jona sa suka fice.
Two weeks Later
Ya kama Sunday gaba d’aya family’n suka had’e a babban falour after dinner suna hira,
hira suke sosai with so much love.
Ahankali Safwah ta zame jikin ta tagudu part d’in Granny, bedroom d’in su ta shige ta
nema bed side ta zauna tayi dialing number’n Safwan dan barata iya b’oye masa ba
anymore, tsorata ta da Suwayd yake yayi yawa gashi in suna zaune guri d’aya duk wani
movement nata a idon sa.
Ko gaisawa ta kasa tsayawa suyi ta fashe masa da kuka, cike da tashin hankali ya soma jera
mata tambayoyi, sai da tayi kukan mai isan ta sannan ta fayyace masa duk abinda yake
faruwa tun daga ranar da ta kamasa yana shaye_shaye.
“Innah lillahi wa’innah ilaihir raji’un Twiny meyasa baki fad’amin ba sai yanzu? “
” Na kasa Twiny tsoron sa nakeji”.
“l ave got you okay, yanzu ki kwantar da hankalin ki maganan bareyu ta waya ba next
week zan shigo kinji and please stop worrying yourself he don’t mean any of his words “
” No Twiny he mean it, he really mean wallahi ranar harfa..”kukan dayaci k’arfin ta ne
yasa ta yin shiru.
shima wane mai shirin yin kukan yace ” O’o Twiny dan Allah kibar kukan haka babu abinda
zai faru kinji?”
Gyad’a kai tayi kaman yana ganin ta tana share hawayen nata, sai da ya tabbatar ta saki
ranta sannan sukayi sallama.
Ajiyan zuciya ta sauke tanajin wane ta sauke dala da goron dutse a akanta, tana d’agowa
kuma zuciyan ta ya bada wani mugun sound.
Suwayd ne jingine jikin k’ofa yayi folding hands nasa a chest yana binta da wani
shu’umin murmushi, tun lokacin data baro babban falour ya biyo ta amma sam batayi
noticing ba.
Duk sanyin Ac’n dake busawa da sanyin fankan dake kad’awa hakan bai hanata yin zufa ba,
fad’ar ma tashin hankalin data shiga b’ata baki ne just ku hango ta.
Juyawa yayi yasa lock jikin k’ofan ya zare mukullin yasa a alijihun sa, wane mayunwacin
zaki haka ya soma takawa yana nufan ta, k’ank’ame jikin ta tayi cike da tsoron abinda zai
biyo baya tana karanta duk addu’an da yazo bakin ta.
Kusa da ita ya nemi guri ya zauna ya d’ago da kanta cike da mugun ta, d’amk’an daya yiwa
gashin ta yasa ta sake siririn k’ara wanda bai bari ta rufe bakin ba ya make sa.
Why do you break the promise? is it because you want to be my wife?”
Girgiza kai ta somayi cike da azaban yadda yake sake d’amk’e mata gashi, ya tsinke ta da
wani azababben marin da sai da taga wuta.
“Ki bud’e kunnen ki kiji daga yau zuwa k’arshen watan nan zaki iya tsintar kanki a
matsayin matata and when that happens ki shirya bankwana da farin ciki har abada, kuma
wallahi duk wanda ya tambaye ki kika ce bakyason auren sai kinyi dana sanin kawo ki
duniya da Abuh da Ummy suka yi ” dariyan mugunta ya sake ya janyo ta jikin sa, a kunne ya
rad’a mata ” Ina taya ki murna ‘yan mata, zaman gidan Suwayd sai jarumar mace so tun
wuri kisan abin yi.
Ture ta yayi daga jikin sa ya mik’e yayi ficewar sa abinsa.
Ita kuwa kifa kai tayi tana kuka sosai at the same time kuma neman mafita, zata so ace ta
zamo matar Ya Suwayd amma bata wannan hanyar ba.
Yana fitowa falour yaci karo da Granny fuskan nan sam babu annuri yasan tana iya wargaza
masa farin cikin da yake ciki dan haka ya wuce zai tafi abin sa.
“Na riga na yanke hukunci akan Safwah dan iya adalci na maka ka kasa ganewa, ban
yarda ba nan gaba kalman ba’ayi maka adalci ba ta fito a bakin ka saboda zuciya ma na son
wanda yake kyauta ta mata tana kuma k’in mai muna na mata ” ya tsinkayi muryan Granny
sounding damn serious.
” Granny amma…”
“Banason jin komai ” tayi cutting nasa mid sentence.
Hankali a matuk’ar tashe ya fice yana juya kalamun Granny dake ta ansa kuwwa a kunnen
sa, zuciyan sa kawai basa take Granny ta bawa Sayyid Safwah tunda shine mai kyauta ta
mata.
“Nol willnever let that happen ” yayi maganan da k’arfi, har ita Granny d’in sai da ta jiyo
sa.
Da sauri Sayyid ya k’araso yana tambayan sa mai ke faruwa ya ture sa ya wuce.
Daga yadda yaja mota ya isa shaida maka baya cikin nutsuwan sa, hankali a tashe Sayyid
yaja tasa motan shima yabi bayan sa sai dai sam Suwayd ya b’ace masa saboda gudu yake
na tashin hankali.
gajiya yayi da yawon neman sa ya koma gida abin tausayi, sosai hankalin Haidar ma ya
tashi haka suka zauna cike da zullumi suna jiran sa.
Suwayd kuwa b’oyayyen gidan sa ya ware ya shawu iya shawuwa hakan yasa dole ya
kwana a can.
Da asuba bayan su Sayyid sun dawo daga masallaci Abbah ya tsare su da tambayan ina
Suwayd, rashin gaskiya ne k’ara ra ya bayyana a tare dasu amma Haidar ya daure yace”
Emm em Abbah yana ciki bayajin dad’i ne shine muka ce yayi sallah’n sa a gida “
Kallo Abuh ya bisu dashi nan ya gano k’arya ce kawai Haidar yayi, muryan Abbah ya jįiyo
yana cewa ” Toh to muje sai muga ya jikin nasa ” dan shima ya fuskanci k’arya suke.
Da sauri Sayyid ya d’ago yace ” Abbah ai jikin bai wani yi zafi ba zuwa anjima ma zai iya
warware wa.
“Another lie ” Daddy ya fad’a a zuciyan sa amma bai furta komai ba.
Kodai bai kwana a gida ba? ” Abbah ya jefa musu tambayan yana tsare su da ido.
“N. No. Aah a gida ya kwana ” suka had’a baki.
Toh muje ko? koya kace Abuh?”
With nod kawai Abuh ya amsa cike da tausayin yaran.
Agaba Abbah ya su suka wuce part d’in nasu, gaba d’aya a rikice suke dan basu san
matakin da Abbah zai d’auka akan su ba in ya gano k’arya suke.
Suna k’ok’arin shiga Abuh yace ” Ohhh Yaya na manta Mummy nason ganin mu “
” Muje to muji mai ke faruwa”
Atare Sayyid da Haidar suka sauke wata kyakkyawan ajiyan zuciya, kallon da Abuh ke musu
ne yasa suka gane yasan komai rufa musu asiri kawai yayi.
Wucewe sukayi part d’in Granny’n sai da suka zo shiga Abuh yace ” Ya ilahi nasan yanzu
bata idar da sallah ba why not mu bari sai da safe “.
Hararan sa Abbah yayi dan ya fahimci raina masu hankali zaiyi, Daddy kuwa dariya yayi
dan dama yasan Abuh kare ‘ya’ yan nasa zaiyi.
Hasken rana ne ya farkar da Suwayd daga baccin asaran da yake yi, hankali a tashe yake
duban agogo ganin tara saura, da sauri ya mik’e ya fad’a toilet yayi wanka ya d’aura alwala
ya fito ya tada sallah.
Yana idarwa ya zauna yana maijin takaicin sakacin da yayi yau sallah’n asuba ta sub’uce
masa, dan du iskancin sa lokacin sallah bai cika wuce sa ba.
Sai k’arfe sha biyu ya koma gida, Haidar da Sayyid na zaune jigum_jigum ya shigo k’in bi
takansu yayi ya shige d’aki abinsa, basuyi zuciya da halin ko in kula daya nuna akan su ba
suka bishi ciki.
” Sannu da hutawa ” Haidar ya fad’a yana masa tausa.
“Yauwa ” ya ansa blankly.
Ganin ya kula Haidar Sayyid yace ” Sannu Akheey hope ka kwana Lafiya?”
“Inace kai ba “MAKAHO” bane sai ka duba ka gani”
Sosai Sayyid yaji haushi amma ya danne, ” ka sani ko baccin da ban samu nayi jiya bane
ina tunanin halin da kake ciki ya makantar dani?”
“Aikin banza mutum sam ko an b’ata masa rai baya fishi ai sai kai tayi “.
Dariya ya basu duka ganin hakan ya sake fusata a k’ufule yace ” inace ni ba mahaukaci
bane balle ku sani a gaba kuna dariya “.
Had’iye dariyan Sayyid yayi amman still Haidar bai dai na ba saboda tsabar k’eta hark’asa
sai da yakai dan dariya.
Mik’ewa Suwayd yayi Haidar na fuskantar mai zaiyi yayi saurin shigewa toilet d’in, bugawa
Suwayd ya tayi amma Haidar yak’i bud’ewa wane zaiyi kuka haka ya koma gefen gado ya
zauna, ganin dagaske Haidar bazai fito ba Suwayd ya soma yi masa magiya amma yayi
banza dashi.
A ciki kuwa ganin bashi da abinyi ya zaro wayan sa yana playing game kawai dan ya
Cusawa Suwayd takaici
Sai da ya gama raina masa hankali sannan ya fito, yana fitowa Suwayd ya mik’e da sauri ya
shige toilet d’in.
Yana fitowa yayi kan Haidar da masifa Sayyid kuwa mai zaiyi banda dariya, ganin sun
girma ma basu dena abin yara ba.
Rayuwan Safwah ya soma zama abin tausayi duk wani abin jin dad’i ta daina, kullum tana
takure a d’aki cikin tsananin fargaba, gashi tun ranan bata sake sanya sa a ido ba amma
tana cin karo da scary massages nasa.
Bayan ta gama taya Mammy had’a lunch taji tanason yin bacci dan ta mugun gajiya gashi
ranan Safwan yace mata zai zo.
Wanka tayi ta kwanta nan take baccin gajiya ya d’auke ta.
K’arfe uku dai_dai Safwan ya iso idan ka ganshi saika rantse da Allah shine yayan Haidar
dan shi jikin Abbah yayo yana da k’iba ba kaman su Sayyid da sukayo jikin Daddy da Abuh
ba.
Kai tsaye d’akin su Safwah’n ya wuce ya nema guri a gefen ta ya zauna yana mamakin
yadda ta rame
Mafarki ta soma yi tana tafiya ita kad’ai acikin wani had’ad’d’en forest me matuk’ar kyau,
baka jin komai sai kukan tsuntsaye da k’amshin furanni, wata yellow flower ta gano me
kyau data mugun tafiya mata da imani, ahankali ta soma takawa harta isa inda flower’n
take, tana zuwa ta iske sa yana haske ta da beautiful smile nasa ya mai sanyaya zuciya,
murmushin itama ta miyar masa in return tana d’aga k’afa tayi da niyyan k’arasawa gurin
sa taji anjata baya.
A tsorace ta juya shi d’in ne kuwa kaman yadda tayi tsammani again yau ma yana sanye
da bak’an riga me had’e da hula data covering half of his face, ya rufe bakin sa da bak’in
hanky wane Ninja, bata ganin komai sai kyawawan idanun sa da ke sa jikin ta rawa in tayi
tozali dasu.
Janta ya shiga yi tana tirjewa tana girgiza masa kai at the same time kuma tana k’ok’arin
kwatan hannun ta amma ta kasa dan rik’on daya mata bana wasa bane.
Juyawa tayi tana kallon sa ganin yadda tari ya sark’e shi har jini na fita ta bakin sa yafi
komai d’aga mata hankali, fizge hannun ta tayi ta nufe sa kafin ta K’arasa ta farka.
Wata irin razananniyar k’ara ta kwalla hakan yasa Safwan saurin janyo ta jikin sa,jikin ta
sai rawa yake hawaye kuwa kaman an bud’e lalataccen famfo, k’ara ta sake kwallawa jinta
jikin mutum, Safwan ya k’ank’ame ta sosai yana shafa bayanta ahankali ya shiga tofa
addu’o’in tsari cike da damuwa.
Ahankali ta fara dawowa nutsuwar ta harta dawo dai dai ta koma sauke ajiyan zuciya, sai
da ta nutsu tsaf Safwan ya tambaye ta mai ya faru a mafarkin.
Kuka tasa masa tayi masa bayani ahankali yace” Twiny please in kinyi mafarki mai tsoro
addu’a zaki dingayi ba ihu ba, Wai ina azkar naki ne ma? Na lura sam yanzu kaman bakyayi
inma kinayi not as before, Ki daina wasa dashi kinji? “
With nod ta ansa sa sannan ta mik’e ahankali ta shiga toilet ta d’auro alwala ta fito,
Sallah’n La’asar ta gabatar inda ta dad’e akan dadduma tana kaiwa Allah kukan ta.
Atare suka fito yaje ya gaida Granny sannan suka wuce cikin gida, sai da ya fara shiga part
d’in Mummy suka gaisa sannan ya shiga gun Mammy daga nan kuma part d’in Ummy suka
wuce yayi wanka yaci abinci yai sallah sannan suka soma hira, yana bawa Safwah labarin
barrack dan haryanzu tak’i nutsuwa.
Suna zaune Suwayd da Haidar suka shigo ai tanajin muryan Suwayd gaban ta ya soma
fad’uwa tayi saurin tashi ta shige d’akin Ummy ta kwanta akan gadon ta tana maida
numfashi wane wacce tayi tsere.
Gaishe su Safwan yayi amma bai tashi ba dan kar Suwayd ya zargi wani abu dan bata
fad’a masa Suwayd ya kamata tana fad’a masa ba.
Hira sosai suka tayi suna tsokanan sa wai in sun jera cewa za’ayi ya girme su, sai da akayi
sallah’n magrib sannan suka tashi suka wuce masallaci.
Itakuma tare da Ummy suka yi sallah’n su.
Zuwan Safwan ya rage mata 30% cikin damuwan ta, ya kuma gargad’e ta komai Suwayd zai
mata karta yarda ta ansa auren so easily, ranar da zai tafi wane k’araman yarinya haka
tasha kuka.
Zee na cikin tsaka mai wuya dan yadda Daddy’n ta ya matsa cikin Ammar ko Amiz cousin
d’in ta sai ta zab’i d’aya saboda yadda suke matuk’ar k’aunar ta, idan ka ganta sam bazaka
gane ta ba dan yadda ta koma abin tausayi ga ciwo dake mugun cinta, idanun ta har ciwo
suke saboda kullum cikin aikin kuka take.
Duk yadda taso cire Suwayd a zuciyan ta abin ya faskara dan kullum gobaran son sa ke
sake ruruwa a zuciyan ta.
Safwah ta d’an sake ganin sati biyu kenan amma bata ga wani alaman aure da za’ayi a
gidan nasu ba.
“Saudi Arabia
” Ammey dan Allah kice Abuh karya fad’a musu zamu zo, munfi so muyi surprising nasu “
cewan Arif dake duba wrist watch nasa dan saura thirty minutes a soma k’iran passengers.
“Eh please Ammey dan ni ina zuwa kayan Safwah zan rik’a sawa na ringa rikita su”
Sayyada ma tayi stating.
Murmushi tayi tace ” ai kuna da banbanci da Safwah sosai dan haka nan da nan zasu gano
ki, ke kina da dauriya ita kuma when it comes to that raguwa ce, ko magana da shagwab’a
take and kefa kinga hakan ma kad’ai ya isa su gano ki”.
Murmushi sukayi both jin an soma kiran passengers sukayi pecking mahaifiyar tasu suka
tafi.
Bayan Sallah’n isha jirgin su ya sauka dama already Abuh yana nan yana jiran su.
Cike da farin ciki suka rungume sa suna gaishe shi, shima hugging su yayi both cike da
K’aunar su suka tafi gida.
Part d’in shi ya wuce dasu suka yi fresh up suka ci abinci, Ummy sai nan_nan take dasu
dan Arif akwai barkwanci.
Bud’e wadrop d’in Ummy Sayyada tayi ta ciro kayan Safwah ta sanya nan kuwa ta fito caras
da ita kaman Safwah’n dan harta da tafiya da voice nasu iri d’aya ne.
“Ummy ya kika ganni? ” tayi maganan tana juyi.
Dariya Ummy tayi tace ” Safwah zam”
Cike da murna tace ” Ummy ina zanyi inje part d’in Granny?”
Fad’a mata tayi nan take kuwa ta fice ta bar Arif da Ummy na hira.
Ahankali take takawa dan bataso tayi abinda zai sa su gano ta, Sayyid na zaune a d’akin su
yaiji yana son ganin Safwah dan haka ya tawo part d’in Granny.
A wurin k’ofan Garden suka had’e da Sayyada murmushin sa mai narkar da zuciya ya sake
mata itama ta sakar masa nata heart melting smile d’in, ahankali ya tako inda take ya janyo
ta jikin sa yayi hugging so tight.
Bata son b’ata plan nata dan haka itama tayi hugging sa back, Safwah da fitowan ta kenan
k’am ta k’ame ta kasa motsawa.
Tunda Sayyid ya fito Suwayd ya biyo bayan sa dan ganin mai zaiyi, tsayawa shima yayi yana
kallon ikon Allah.
Ahankali Sayyid ya soma magana ” Sweetheart dan Allah ki bari muyi aure, i really need
you by my side dan Allah ki barni na fad’awa su Abbah mun daidaita kan mu “
Shiru tayi jikin ta yayi mugun sanyi ahankali taji yayi breaking hug d’in yana matso da
fuskan sa zuwa nata, juya tayi zata gudu yayi saurin juyo da ita yayi shutting ta da wani
had’amammen kiss.
K’aran da Safwah ta kwalla ne yasa Sayyid saurin pulling out, da gudu ta juya zata koma
Suwayd ya bud’e mata hannayen sa ta fad’a jikin sa yayi hugging ta so tight yana jin dad’in
faruwan wannan lamari, sai dai shima kan sa ya kulle wace wannan d’in dake tsananin
kama da Safwah to.
Sunkuyar da kai Sayyada tayi cike da nadaman abinda ta aikata, Sayyid kuwa gaba d’aya
ko kwakkwaran motsi ya kasa.
Sai da ta tsagaita da kukan Suwayd ya janye ta daga jikin sa ya rik’e hannun ta k’ank’am
suka shige part d’in Granny.
Juyawa Sayyada ma tayi hankali tashe ta koma part d’in Ummy ta kwanta ta lumshe ido
tana tuna abinda ya faru.
Acikin su hud’un ba wanda yayi baccin kirki kowannen su da abinda ke masa yawo a mind,
musamman Safwah da ke tunanin yaushe Sayyada tazo meyasa kuma Sayyid zaiyi kissing
ta, tabbas zatayi amfani da wannan daman ta fita daga sark’ak’iyan da take ciki.
Washe bayan an gama breakfast akai introducing Arif da Sayyada wa family, har anan ita
da Sayyid kunyan juna suke saboda abinda ya faru.
Sayyid gaba d’aya ya rasa ta ina zai soma bawa Safwah hak’uri gashi tayi blocking duk
hanyan da zata had’a su, wayan ta ma gaba d’aya ta kashe haka har aka kwashe sati.
Hak’uri sosai Sayyada ta bawa Safwah inda ta nuna mata babu komai, Sayyid ma sai da
taje ta basa hak’uri shima ya nuna mata babu komai tsautsayi ne.
Dakyar Sayid ya samu Safwah ta sauk’o amma ba kaman da ba.
Ya kama Friday tunda Safwah ta tashi takeijin gaban ta na fad’uwa haka dai take ta yin abu
a sanyaye wane kazar da kwai ya fashew aciki and same goes to Sayyid.
Dakyar ta lallab’a shi ma yabi su Haidar masallaci, Arif nata tsokanan shi wai tun kafin suyi
aure ya zama mijin tace, shi kuwa da murmushin yak’e kawai yake binsa, Suwayd na d’an
shakkan yiwa Arif abu dan shima ba kanwar lasa bane.
Bayan an idar da sallah’n juma’a a masallacin jafar dake gadon k’aya, miliyoyin mutane
suka shaida d’aurin auren Ruk’ayyah Sufyan Muhammad da..
Huh bara muga waya fi fans Suwayd ne ko Sayyid?? toh fa wai ma taya d’aurin auren
Safwah’n ya faru??? Dawa kuma aka d’aura??? Waya dace ta aura?1? And who is behind it??
Bayan an idar da sallah’n juma’a a masallacin Sheik Jafar dake gadon k’aya, miliyoyin
mutane suka shaida d’aurin auren Ruk’ayyah Sufyan Muhammad da Muhammad Nasir
Muhammad sai Sa’adatu Muhammad Mubarak da Nasir lbrahim Muhammad again aka
d’aura na Hafsa Nasir Muhammad da Aliyu Sufyan Muhammad you won’t believe if i tell
you harta Sufyan Muhammad Mubarak sanda aka d’aura nasa da Sadiya lbrahim
Muhammad akan sadaki dubu d’ari da k’osassun mayan rak’uma guda biyar_biyar.
A matuk’ar razane da tsananin firgici Arif da Sayyid suka mik’e they just can’t believe the
goddamn thing kunnen su take jiye musu, Haidar baka iya tantance halin da yake ciki
saboda k’arfin zuciya, is not that abin bai dake sa indeed it does but to believe in it abin ya
faskara yayin da uban gayya shocked ta kashe sa a gun even blinking of an eye become
something worst difficult.
Ahankali haidar ya tashi wa ya soma magana in a manly like-manner.
“Man Up and Just calm down dudes we are all in this let’s not create any scene here”.
“To Hell with you and the goddamn calm down, for goodness sake mai hakan! we all
know it’s true tinda duk munjiyo family name tamu, how could they? How on earth… “
bak’in ciki yasa sa ture hannun Haidar dake tapping shoulder’n sa ya wuce mota yana huci
wane mayuwan cin zaki.
Sayyid wani irin zugi da rad’ad’i zuciyan sa keyi zafin da yake jiyowa deep inside is just
unbearable, Who is behind all this? Ashe shiyasa suke ta jiyo strangge feelings shida “Very
Own’ tasa? Meyasa ya biye ta Safwah da tak’i yarda yakai maganan auren su wurin elders?
Me had’in sa da Sayyada da za’a jona masa? Tambayoyin dake ta yawo kenan a zuciyan sa.
Kallon Suwayd yayi da haryanzu yak’i tashiwa a wurin nan take wani bala’in tausayin
Safwah da tsoro ya rufe sa k’ok’arin calming kansa yayi at the same time kuma b’oye halin
da yake ciki.
Tsugunawa yayi ahankali ya rik’o hannun Suwayd cike da k’arfin hali yace “Akheey please
do remember “Ma asaba min musibatun k’alu innah lillahi wa’innahilaihir raji’un””
Like a brazen bastard haka Suwayd yata bin Sayyid da ido du iyakar nacin ka baraka gano
halin da yake ciki ba buh deep inside Allah ne kad’ai yasan how happy he is, tsantsan
tausayin Sayyid yasa sa d’ukan da kai k’asa.
Gently Sayyid ya shiga mik’ar da Suwayd suka wuce mota, front seat ya bud’e ya shigan da
shi then ya koma yayi joining Arif a back seat, Haidar ke driving du cikin su kuma ba wanda
ya sake magana.
In less than five minutes suka isa gida kunsan yahya gusau to gadon k’aya ko a k’afa zaka
iya kaje.
Surprisingly Abbah yake duban Daddy da Abuh kansa na kullewa badan yajiyo sunan
family na mijin Sadiya ba da bare tab’a yarda da ‘ya’yan su aka d’aura wannan auren ba, he
really need an explanation there are so many things going through his mind, kallon
tuhuma kawai yake bin Abuh da Daddy yayin da suma suke binsa da same look amma du
anan ba wanda ya iya furta ko wani kalamu.
Acan gida du ‘yan matan na kwance flat a tsak’an falour’n Granny suna hira cike da
nishad’i, jona su Safwah tayi dan ta rage abinda take taji is about to happen to her.
Teasingly Sayyada ta kalla Safwah tace “wato Babe ina fad’a miki Ya Sayyid is damn hot, du
ranan da kika shiga hannun sa zakiji maza”.
Dariyan mugunta suka fashe duka ita kuwa forceful smile tayi forcing out tana kaiwa
Sayyada bugi a zuciyan ta tana cewa “du hotness nasa yakai Ya Suwayd ne”
Gocewa tayi ta kalla Kuwaysah jokingly tace “wannan abar kuwa bamu san ya za’ayi ba in
akace yau an kaita gidan Ya Haidar” dariya suka sa both.
You Little brat me akanki ne yau?” Cewan Lubna in between laughter.
“Baraki gane ba girl haka nan yau nake jina some how pathetic, shiyasa nake son keeping
kaina busy and same goes to Safwah I ave been observing there is something so burden to
her buh she is just pretending to be alright which she isn’t”.
“Just chill girls it’s normal” cewan Kadsah tana latsa wayan ta.
Haka dai tata sasu a kwana sai da ta gaji don kanta ta kyale su suka koma hiran future
ambition.
A hargitse ta shigo falour’n Granny ko sallama ta kasa saboda tashin hankali, surprisingly
Safwah ta bud’e baki wide open, duba duka suka kai inda Safwah ke kallo nan suka ga
biggest surprise of there life.
In Crack Safwah tace “Amm… Ammey is that you?”
Ignoring question nata tayi tace “Where is Granny?”
Daga expression na Ammey’n ta tasan something isn’t good dan ko a jiya da sukayi waya
bata ce mata zata zo Nigeria ba.
At that very instant k’ofan d’akin Granny ta bud’u revealing the gorgeous and happy old
woman.
Da tsananin mamaki ta shiga bin Sadiya da kallo.
Da sauri Sadiya ta k’araso ko yanda ake gaisuwa ma ta manta “Mummy dan Allah ki janye
maganan, the kids are not meant to be together, don’t force the innocent child am scared
something bad is about to happen, barin iya jurewa ba na rok’e ki dan Allah ki dakatar da
aukuwan lamarin” tayi pleading wane zata sanya kuka.
“You know everything right?” muryan Abbah ta ratso falour’n.
Su duka ukun suka k’ari so ciki suka zauna suna bin mahaifiyan tasu da kallo mai cike da
neman k’arin bayani.
“Du ku k’ira matan ku l ave alot to discuss, Lubna je ki k’iramin yayyan ku” waya du suka
fitar suka k’ira su yayin da Lubna ta mik’e jiki a sanyaye gaban ta na tsananin fad’iwa ta tafi
k’irawo su.
Su duka suna zaune a falour kowa da kalan tunanin da yake ta shigo d’auke da sallama, du
aka rasa gwanin da zai ansa ta dan ko kallon ta ba a samu maiyi ba.
Ahankali Arif ya d’ago yana binta da wani irin kallon da ta kasa jura ta sunkuyar da kanta
k’asa, kallon ta yake from head to toe yana jin wane ya fasa kuka, ama rasa dawa za’a
had’asa da aure sai wannan kwailar yarinyan da yasan ba abinda zai tsinta a jikin ta, kallo
ya sake binta dashi yana ganin k’ank’antar ta yasan abu mai wuya ne ta iya d’aukan needs
nasa dan tsaf zaiyi destroying nata a bed.
Siririyan muryan ta ya tsamo sa daga gajeran tunanin daya ke.
“Ance du kuzo inji Granny” sannan ta juya da sauri ta fice dan ta kasa juran kallon da Arif ke
jifan ta dashi.
“Ahhhhsssh” ya sake k’ara yana hargitsa curly hair nasa da yayi styling irin na larabawa.
Rik’o sa Haidar yayi cike da damuwa yace “Haba mana Akheey man up, me haka kake yi?
Aure ne an riga an d’aura and nothing will change the fact, idan zaka yi hak’uri gara ma kayi
tun wuri now sai ku tashi muje muji k’iran “.
Atare suka mik’e amma banda Suwayd dake kwance idanun sa a lumshe wane mai jin bacci
nan ma Sayyid ne yayi k’ok’arin rik’e sa suka wuce.
Falour’n yayi tsit kowa is so eager yaji bayani daga Granny amman tayi shiru sai binsu take
da kallo d’aya bayan d’aya.
“Nasir! Ibrahim! Sufyan! Sadiya! Maryam! Ummuhani! Safiyya lemme start with you guys,
shin ina da iko akan ‘ya’yan ku ko bani dashi? Na isa na zartar da hukunci akan su batare da
sanin ku ba ko ban isa ba?”
“Haba Mummy mai ya kawo wannan maganan mu dasu duka ai muna a k’ark’ashin ikon ki
ne, so feel free and go straight to the point” Abbah yayi replying with assuring smile on his
face.
“Kufa me kuka ce?”
“Ya riga ya gama magana Mummy” suka fad’i in chorus.
“Masha Allah Alhamdillah since that’s it, Sayyid! “
Sunan sa da Granny ta ambata yasa siraran haweye suka soma kwarinyo masa duk yadda
yaso controlling kansa ya kasa dan haka ya had’a kansa da gwiwa uncontrollable tears
nasa na cigaba da kwarinya yayin da zuciyan sa ke mugun zafi, hankalin kowa sai da ya
tashi ganin yadda yake kuka wiwi wane k’aramin yaro.
“Sayyid d’ago ka kalle ni” Granny tayi maganan cike da tsantsan tausayin sa.
D’agowa yayi ya kalle ta yayi saurin miyar da kansa dan bare jure ba, Safwah ma na gefe
tana hawaye cike da tausayin Ya Sayyid duk da batasan mai dalilin kukan nasa ba amma
she can sense it koma miye ba alkhairi bane.
Sauran yaran ma duk a tsorace suke ganin halin da Sayyid yake ciki, dama kuma tun
zuwan Ammey suka fara sensing da matsala.
“Sayyid nasan ka yarda da k’addara nasan kuma zaka fahimce ni, na d’aura auren ka da
Sayyada dan nasan baraka bani kunya ba, nasan kuma zaka kula da ‘yar uwar ka I trust in
you, bazan ja maganan ba in kuka dai_dai ta saiku fixing date na bikin auren”.
Afirgice Sayyada kebin Granny da kallo sam ta gaza gane inda maganan Granny ya dosa
tsabar rud’u, yayin da Safwah taji wani abu ya tokare ta wanda ta gaza gane kishi, bak’in
ciki, takaici ne ko mai.
Kuka sosai Sayyid keyi ya kasa furta komai zuciyan sa kaman zatayi bursting k’irjin sa ta
fito.
“Allah yasa haka shi yafi alkhairin” kowa yaji ya furta yana kuka heavily, shikan sa baisan
sadda kalamun suka sub’uce masa ba.
Wani irin kallo Safwah ta soma jifan sa dashi cike da mamakin furucin sa “Why will he
believe with it so easily? Those that means he don’t love and care for her anymore?”
Sayyada kam ta kasa koda kwakkwaran motsi jokes tasu ta d’azu ce kawai ta soma dawo
mata, k’arfin zuciya irin tata yasa ko kukan ta kasa sai binsu da ido kaman fool
“Allah yayi maka Albarka and insha Allah you won’t regret it” cewan Granny cike da son
sanyin hali irin na jikan nata.
Arif kuwa kallon you don’t really know what is wrong with you ya shiga jifan Sayyid da shi
yana tsara yadda in anzo kansa zai rufe ido ya fad’i what is in his mind.
Sosai zuciyan Suwayd ta raunana badan bare iya rayuwa babu Safwah ba daya hak’ura ya
barwa Akheey d’in sa, kukan da yake sosai yake burning sa and sai yake gani kaman he is
the reason behind all that is happening.
“Amin” du iyayen suka furta a sanyaye.
Jan numfashi Granny tayi ta miyar da kallon ta kan Haidar “Haidar!”
“Na’am” ya amsa kindly.
“Nasani batun yau ba kuka dai_dai ta kanku kai da ‘yar uwar ka and this is the right time ya
kamata musan abinyi duba da abinda ya faru wancan lokacin, bawai karatun ne banson
suyi ba sai dai nafiso kowacce ta tayi a d’akin ta hankali zaifi kwanciya, Allah ya albarkaci
rayuwan ku ya bada zuri’a d’ayyiba, kuma kuyi fixing lokacin da kuka ga ya dace wa auren
naku
“Amin mungode Allah ya k’ara nisan kwana” ya fad’a a kunyace yana kallon k’asa.
“Amin Aliyu Allah yayi maku albarka”.
“Amin” nan ma both iyayen suka had’a baki wurin fad’i.
Kallon Suwayd pretender da Arif Granny tata yi tana tunanin takan wa zata soma dan su
duka biyun first class ‘yan daru ne.
Dakyar tayi gyaran murya ta kalla Arif tace “Arif!”
“Yes” ya ansa yana kallon ta without any fear, tun anan Ammey tasan zai tafka rashin
hankalin nasa gashi yak’i yarda su had’a ido.
“Sai kaji d’aurin auren ka da k’anwar ka ko?”
Eh wai haka naiji liman ya fad’a “‘yayi stating ba wasa tattare dashi.
Murmusawa Granny tayi tace “Lamarin aure ya wuce wasa dan haka ba wai bane, is true
your lil sis is now your wife”
“Wife P” Ya nanata cike da renin wayo.
“Yanzu Granny har kina tunanin wannan abar zata iya dani? Infact ma ni babu tsarin auren
k’araman yarinya a gaba na so better tin wuri asan abinyi, dan am not accepting this
goddamn thing you call marriage, haba mana dube..
“Shut up you foolish fool kafin na sab’a maka du anan waye sa’an ka? To bari kaji aure ya
riga ya d’auru kuma kayi kad’an ka warware shi koda kuwa hakan na nufin mutuwan ka,
uban naka ma da kake tak’ama dashi ya amince da auren balle kai piece of trash, mara
kunyan banza kawai Allah yasa ka k’ara magana wallahi sai nayi mummunan sab’a maka,
du acikin su wa kaji yayi magana ko finsu kayi?..”
“Cut it please Sadiya you know tursa sasa akai dole sai mun had’a da lallashi” Granny tayi
saurin katse ta.
“My Dear said what’s in your mind we are listening”
Ya bud’e baki zaiyi magana suka had’a ido da Abuh, yadda yaga disappointed k’ara ra a
fuskan Abuh yasa sa yin shiru batare da ya shirya ba.
“Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya, kuma idan kun gama daidaitawa sai kuyi
magana”
Nam ma du tare iyayen suka furta “Amin”.
Har wannan lokacin ‘yan matan an rasa mai magana sai zare ido suke wane munafukai,
muna iya cewa Lubna tayi farin ciki da wannan aure though bataji dad’in abinda yayi ba
dan tun ranan data soma sanya sa a ido taji tana son sa.
Idan ka kalla fuskan Suwayd dole ya baka tsoro dan Sam_sam babu annuri a fuskan sa
saboda tsabar pretending, kowa mai do da kallon sa yayi kansa nan take kuwa iyayen suka
d’an tsorata da lamarin, yaran kuwa gaba d’aya tausayin Safwah ne ya kama su bama
kaman Sayyid da kukan sa ya dad’u.
Dariya yaso bawa Granny amma ta moze, “Suwayd!”
Shiru ya mata shi bai ansa ba bai kuma d’ago ba.
“Suwayd!” Ta sake nanatawa for the second time.
Da wata irin murya da kowa ya kasa gane me take nufi yace “Na’am”
“Sai kaji an d’aura auren ka da Safwah.”
A birkice ya d’ago yace “What? Wa?” acting like he don’t know any single thing she is damn
taking about.
“Nasan kaji ni so no need to repeat my self, karku damu akwai dalili na nayin haka wanda
bazan fad’a ba sai nan gaba”
Mik’ewa Safwah tayi jikin ta na tsananin rawa ta fashe da wata masifaffiyar kuka “No please
Granny don’t do this to me, bana son sa na tsane sa he is nothing to me face monster, ko
ganin sa bana sonyi Ya Sayyid nake so, Ya Sayyid ka fad’a musu kar su raba mu muna son
junan mu, dana zauna da Ya Suwayd na kwammace na mutu babu aure, bana son sa
banason ganin sa”.
Wani irin tashin hankali ne ya riski Suwayd, meyasa Safwah ta tsane sa haka! Why did she
keep repeating ta tsane sa? Shin batasan yadda yake mahaukacin son ta bane? Meyasa
barata gane “MAKAHON SO” da yake mata ne duk ya jawo yake mata abubuwan da yake
ba?.
Lokaci guda kalamun sa na ranar suka soma dawo mata “karkiyi tunanin da wani manufa
zan aure ki, zan aure ki ne dan inyi making life naki miserable hell saboda sirri na da kika
sani, in fact ban tab’a kallon ki a mace ba balle kiyi tunanin ko wani abu naki yaja hankali
na nake son na aure ki not at all zanyi hakan ne dan na cigaba da muzguna miki har
K’arshen rayuwar ki”.
Wani bala’in tsoro ne ya dirar mata nan take kuma zuciyan ta tayi mugun harbawa, jiri ne
ya soma d’ibanta ta tafi ta baya luuuuu ta fad’a, ji kake tassss fashiwan center table da
kanta yayi wani jakin buguwa da, nan take jini ya wanke fuskan ta gaba d’aya.
K’ara Sayyada ta kwala cike da tashin hankali tayi kan Safwah amma ina ko motsi bata yi,
hannu takai da sauri ta jiyo yanda zuciyan ta ke harbawa ahankali_ahankali.
Fad’in tashin hankalin da kowa ya shiga bare iya fad’uwa ahankali komai na jikin Sayyid ya
dai na functioning sumammiyar jikin sa ta fad’i.
Da sauri Haidar yayi kansa yana tapping sa amma inah babu alamun nasara, tare da
Suwayd sukayi saurin d’aukan sa suka wuce mota Arif kuma ya d’auko Safwah da kanta
keta zuban jini, rigan sa ya cire ya nad’e kanta suka wuce asibiti.
AKTH suka wuce akai gaggawan k’artfan su both.
Suna nan suna safa da Marwa ragowan family members d’in du suka iso, bayan minti
talatin aka turo Sayyid a stretcher zuwa d’akin hutu, fuskan nan looking so pale, lokaci
guda du ya fice a hayyacin sa, ahankali_ahankali yake sauke numfashi yana baccin wahala
yayin da ruwan da aka d’aura masa ke shiga jikin sa ahankali.
Jigum jigum suka yi duka kowa da abinda ke yawo a zuciyan sa da kuma tunanin halin
da Safwah take ciki tunda Doctor ya tabbatar musu damuwa ne yasa Sayyid yayi collapse.
Acan kuma sosai likitoci suka tsorata da lamarin Safwah dan sunyi iyakan k’ok’arin su
amma abin ya gagara, du wani rauni da taji anyi treating.
Yadda aka nad’e kanta duka da bandage sai yafi komai baka tsoro, da taimakon Allah da
taimakon oxygen suka samu dawowan numfashin ta.
Tura ta ita ma akayi zuwa d’akin da Sayyid yake aka kwantar sannan Doctor ya musu
bayani dole sai ta farka zasu san halin da take ciki dan suna ganin kaman kwakwalwan ta
ya had’u da jini.
K’iran sallah’n la’asar yasa mazan wucewa toilet yayin da matan suka soma layin shiga
toilet d’aura alwala.
Sai bayan sallah’n Magrib Sayyid ya farka, da fuskan Safwah ya soma cin karo nan take
kuma ya soma remembering abinda ya faru, kuka ya fashe dashi yana dafe saitin zuciyan sa
dake mugun zugi.
Ahankali Suwayd ya haura kan gadon cike da tsananin tausayi ya d’aura kan Sayyid a
cinyan sa yana tausan sa, k’ank’ame Suwayd Sayyid yayi yana sauke numfashi a wahalance
in crack voice yace “Akheey meyasa? Shin ban cancanci ta zamo mata ta bane? Meyasa
zasu raba mu?”
Runtse ido yayi yana murza kansa dake tsananin sarawa akan cinyan Suwayd, had’e
hannun su guri d’aya Suwayd yayi ya k’ank’ame hawaye na kwarinyo masa sosai, ahankali
ya bud’i bakin sa yace “Akheey please be normal idan komai ya dai dai ta zan saki Safwah
ka aura”.
“No” Sayyid ya fad’a cikin karajin daya mugun firgita kowa, “‘Safwah ta haramta a gare ni,
ina son ta amma ta riga da tamun nisa, Akheey please promise me you will not hurt her
anymore, promise me no matter what it takes you will be with her, promise me baraka sake
sanya ta kuka ba, Akheey ina son tal really love and cherish her, amma k’addara ta raba
mu dan Allah kamin alk’awarin bata kariya from any harm…” Kukan daya ci k’arfin sa ne
yasa sa yin shiru yana damk’e setin zuciyan sa the more.
“Nayi alk’awari Akheey insha Allah kuma barin yi breaking ba”.
“Nagode, Nogode, Allah ya saka da Alkhairi Akheey indeed you are such a darling”
Ahankali ya mik’e daga kan cinyan Suwayd ya mik’e dakyar, dafe kansa dake barazanan
tarwatsewa yayi ya soma tafiya yana had’a hanya, tambayoyi aka shiga jifan sa dashi
amma yayi burus dasu duka ya fice.
Kifa kai Suwayd yayi akan gadon yana kuka heavily he just can’t forgive him Selffor his
selfishness, bare tab’a yafewa kansa ba cause of the pains he made his Akheey went
through.
Sayyid dakyar ya iya ya fice daga asibitin gaba d’aya, cab ya tare yace ya kaisa any place da
yasan zai sama wine cause that’s the only damn thing he needed.
Mazeeda Club cab man d’in yayi dropping nasa ya basa kud’in sa ya shige club d’in, wuri
ya samu ya zauna cikin k’unan zuciya yana kuka wane d’an k’aramin yaro, koda order nasa
ya iso kasa tab’awa yayi cike da tsoro, glass cup yaja ya zuba aciki ya runtse idanun sa ya
Soma sha.
Saida ya shawu iya shawuwa sannan wani wahalallen bacci yayi taken over nasa.
Haka Sayyid ya koma rayuwa abin tausayi yayin da shan wine ya zamo masa kaman ruwa,
a club d’in yayi wani aboki huzzy, first class d’an iska inda ya taka rawar gani sosai a
gurb’acewar Sayyid.
Can gida kuwa gaba d’aya hankula a tashe suke game da b’atan Sayyid dan tunda ya fice
daga asibiti basu sake ganin sa ba, Mummy kullum cikin kuka take da addu’an Allah ya kare
mata tilon d’an ta a du ina yake.
Safwah sai da tayi kwana uku ta farka kuma babban tashin hankali she seems to forget
everything, lokacin da aka had’a ta da likitan kwakwalwa ne yake shaida musu tayi loosing
memory.
Fad’ar tashin hankali da suka shiga ma b’ata baki ne amma Doctor ya nuna musu in six
months time ma zata iya regaining memory’n ta inta samu kulawa.
Tunda Suwayd yaji halin da Safwah take ciki ya kasa zuwa duban ta saboda tsananin
tashin hankali da tsoron halin da zai ganta dan Dr yace duk wani abinda ke tsorata ta da
b’ata mata rai a guje sa.
Yana kwance ya zurawa ceiling ido banda hawaye ba abinda yake dan tunda al’amarin ya
faru ya zama mai raunin zuciya, du wani masifa, bala’i, had’a rai ya daina sai miskilanci
daya ci uban na da.
K’arisowa Haidar yayi cike da jimami ya zauna kusa dashi.
“Ina Akheey na? Kun gansa? Wani hali yake ciki?” Ya soma da jifan su da tambayan.
Girgiza kai Haidar yayi cikin wani yanayi da yake nunin haryau babu nasara, kuka ya fashe
sosai ya k’ank’ame Haidar abin tausayi, rasa abinyi Haidar yayi kawai ya jona sa suka ci
gaba kukan tare.
Sanda suka yi mai isan su sannan suka sake shiryawa suka fice neman sa, har bayan isha
suna yawo amma babu Sayyid ba labarin sa Suwayd duk ya lalace ya fita a hayyacin sa, du
wani arrogancy yanzu babu.
Kai tsaye asibiti Haidar yayi leading su, kallon tsoro Suwayd ya bisa dashi yace “Akheey no
please take me home”
Cike da haushi Arif yace “Idan baka yi ba ai bara ace dat wicked bitch bane, fisabilillah
matar ka na a asibiti amma haryau ka kasa zuwa duban ta, ina alk’awarin daka d’auka shin
ka fara cikawa ko karya wa? For heaven sake me Safwah ta tare maka ka tsane ta haka
huh?”
“No please Arif stop this shit tsoro nikeji, for all this while to Safwah ama monster taya
kake tsammanin zan iya tunkaran ta ithout any fear?”
“Calm down, just calm down please okay?” cewan Haidar calmly.
Koda suka iso asibitin sai da sukayi da gaske suka samu yabi su, runtse idon sa yayi lokacin
da zasu shiga d’akin.
Safwah na zaune da teddy bears nata sai wasa take wane two years old kid, a yanayin da
take dole ta baka tausayi dan ita tsakanin ta da Allah wasa take, Mammy sai fama take da
ita tazo tasha complex nata daya zame mata favourite amma tak’i dan yadda wasa ya
d’auke mata hankali.
D’agowan da zatayi idanun ta suka sauka cikin na Suwayd, wani razanannan k’ara ta fasa
tayi cilli da bears d’in ta fad’a jikin Mammy ta K’ank’ame ta tana fad’in “dodo”.
Duk yadda Mammy taso ta nutsu tak’i dole ta rungume ta cike da tausayin sabon abinda ta
tsiro dashi kuma yau.
“Baby d’aga kiga babu dodon ya tafi” cewan Mammy tana d’ago ta.
Ahankali ta d’ago ai tana ganin Suwayd ta fasa k’aran daya ci uwar uban na d’azu tana ex
claiming “dodo, dodo”
Tashin hankali Suwayd ya shiga a rud’e ya k’ara so yace “Baby tashi kiga ba wani dodo”.
Muryan sa ma sake razana ta yayi dan haka ta shiga kwalla k’ara kaman ba gobe tana ihun
“Mammy walahi dodo ne ki kore sa zai kama ni”.
Sake maganan da Suwayd yayi suka ga gaba d’aya jikin ta ya sake, a firgice Mammy tace
“Arif call Doctor please”
Da sauri ya fice suka dawo a tare, labarta masa komai Mammy tayi ya juyo yana kallon
Suwayd yace “Wannan shine dodon da take fad’a du yadda akai kafin rashin lafiyan ta yana
tsorata ta, dan haka daga yau karya sake zuwa inda take, if not zamu na yin aiki yana
wargazawa ko gida kuka koma sai kun hanashi dosan ta'”.
Daskarewa Suwayd yayi wurin nan take ya soma raira kuka wane k’aramin yaro wanda
kowa ya kasa gane kukan mene except Granny, Ahankali ta mik’ar dashi suka fice daga
d’akin.
Wasu empty chairs data hango taja sa suka k’arisa suka zauna sannan ta soma da lallashi
sai dai the more kalamun Doctor ke hitting sa the more kukan sa ke dad’uwa.
Cike da damuwa Granny ta soma magana “kaga ba wannan abin tun tuni nake jiye maka,
yanzu mai gari ya waya? Tun ba aje ko ina ba ka fara girban abin da ka shuka, ba baki nake
maka ba amma wallahi indai alhakin Safwah da ka d’auka ne kad’an ma ka gani, zakace na
fad’a maka kuka kuma better save it dan baka ma fara ba tukunna sai nan gaba”.
“Granny please mana, can’t you see how am suffering i regret every single bit of it, wallahi
nayi nadaman du abubuwan dana aika ta, dan Allah karki bari su hanani ganin ta that’s the
only way for me to survive, ya ake so nayi da rayuwa na babu wad’annan special ones to
me d’in? Akheey ya tafi ya barni da kewan sa and itama anaso ace za’a rabani da ita i can’t
take it, i just can’t take it inba so kuke zuciyana ya buga ba, ni kad’ai nasan how am feeling
deep inside… “kukan da yaci k’arfin sa ne ya sanya sa yin shiru.
Sosai ya bawa Granny tausayi dan haka ta jawo sa jikin ta tana rarrashi sanda yayi mai isan
sa sannan yayi sallama ya tare napep ya shiga zuwa b’oyayyiyar gidan sa and that’s the first
time ya tab’a shiga, he is just imagining how life start turning back at him, yana shiga
falour’n ya rage sutturan jikin sa ya zamo daga shi sai shorts da singlet ya baje akan carpet
ya dafe zuciyan sa dake zugi, nan take incident nasu da Safwah ya shiga dawo masa.
Yana ji wayansa na ringing amma yayi banza da ita ya d’auko wines nasa ya soma tittilawa
cikin sa.
Haka rayuwan yaci gaba da tafiya, Suwayd ya sake zuwa har sau hud’u amman the same
thing ke faruwa dan haka likitoci suka dakatar dashi.
Tsakanin shida Sayyid yanzu ko ni na kasa gane wa yafi birkicewa dan yadda suka maida
shaye shaye wane ibada, Sayyid bai tsaya iya wine ba harta da codeine, cocaine, sigari da
makamancin su bai kyale ba.
Yauma suna zaune shida Huzzy a haraban club d’in da kayan maye birjik a gaban su.
Cocaine ne a hannun sa sai shak’a yake yana lumshe ido hakan ne zai shaida ma ba
K’aramin enjoying abinda yake yakeyi ba, yayi bak’i ya rame lips nasa have now turn to
black color saboda zuk’an sigari.
Wata jarababbiyar yarinya dake ta hunting sa ce ta k’araso inda suke, kallo d’aya in kayiwa
shigan ta bazaka so ka K’ara ba saboda da ita da babu du d’aya, fad’awa jikin Sayyid tayi
tana masa wasu shaid’anun abubuwa masu rikitarwa tun yana shunning nata har yayi
giving in wa abinda take masa.
D’aukan ta yayi chak in a bride-like style ya wuce d’an k’aramin d’akin da suka yi renting,
kan gado ya ajiye ta yabi bayan ta ya soma romancing ta da zafi_zafi, yana k’ok’arin aika ta
abinda ba halin sa ba fuskan Safwah ta shiga yi masa gizo tana kuka so hard.
Ture yarinyar yayi daga jikin sa ya fad’a toilet ya maida k’ofan yasa lock ya zame a bakin
k’ofan yana kuka like never before.
“Why Sayyid meyasa ka zama haka? Meyasa bazaka yarda da k’addarar ka ba? Bayan
believing in destiny the good or bad is there in the five pillers of Islam” yana magana shi
kad’an sa yana kuka so hardly, wani abu yaji ya toshe masa mak’oshi nan take tari ya sark’e
sa ya soma ba k’ak’k’autawa yana fitar da bak’in jini harda guda_guda.
Ya d’ad’e cikin wannan mawuyacin hali sannan ya zame flat a k’asan toilet d’in yana
kokawa da numfashin sa.
Yafi thirty minutes sannan ya iya ya mik’e cike da tsananin azaban zafi da zugin zuciya ya
tsarkake jikin sa ya gyara gurin ya fito, bai ganta ba bai kuma damu ba ya fito ya sama
Huzzy yace shi gida zai koma.
Bayadda Huzzy baiyi dashi ba ya zauna amma yak’i, koda yaje gida a bakin gate ya zauna
ya rasa taya zai shiga, bai san da wani ido zai kalli iyayen sa da yan uwan sa ba, kuka ya
saka tuno yadda ya maida kansa bigdog just in a week.
Ahankali Suwayd ya fito mutuwan tsaye yayi yana kallon Sayyid dake kuka surprisingly,
yana d’agawa idon su ya sark’e da juna kowannen su sanda zuciyan sa ta buga soboda
rama rashin kwanciyar hankali da nutsuwa daya bayyana a tattare dasu both.
Like a bloody idiot Suwayd ya taka ya isa inda Sayyid yake ya mik’ar dashi yai hugging sa so
tight yana kuka wiwi, chak Sayyid ya nema kukan sa ya rasa yana shakkun anya kuwa
wannan Suwayd daya sani ne, kuka Suwayd ke sosai ya k’ank’ame Sayyid sannan ya soma
magana “Akheey you scared me so bad, please don’t go again it kills me rashin ka kusa
damu babban tashin hankali ne please don’t do it again, we really need you meyasa zaka
tafi ka barmu?…”
Zamewa yayi on his knees yana rok’on Sayyid yana kuka sosai, da sauri Sayyid ya d’agosa
cike da tausayin d’an uwan nasa shima ya sanya kuka.
Ganin an soma ta ruwa kallon su suka shige gida.
Fad’a yasha sosai inda ya nemi tuban iyayen nasu, lokacin da ya samu labarin matsala
Safwah heartbreak ce ta sake samun sa, yayi kuka harya godewa Allah amma abin mamaki
da yaje duban ta mak’ale masa tayi, haka sukayi spending ranan tare Suwayd dake lek’en
komai ta taga ganin yadda Safwah ke shiga jikin Sayyid kishi yasa yabar asibitin, a ranan sai
da yayi shaye _shayen da bai tab’a yi ba.
Har tsautsayi yasa ya tab’a wani area boy suka had’u da gangs nasa suka yiwa Suwayd
dukan mutuwa, a hannun Dr Alkasim ya tsinci kansa bayan kwana biyu da faruwan lamarin
inda Dr ya tsorata sa sosai cewan indai bai rage shaye_shaye ba sai ya fad’awa su Abbah.
Haka dai har aka sallamo ta suka dawo gida ganin halin da Suwayd ke shiga yasa Sayyid
rage zuwa gurin Safwah, amma haka zata ta ihu sai an k’irawo mata shi in ba haka ba babu
kwanciyar hankali.
Ka kaf sai da aka kwashe hotunan Suwayd daga sashin Mammy dan anan ake jinyan ta,
kuma razana ta suke.
Du abin nan da ake Sufyan bai sani ba cause shima yana can cikin mawuyacin hali
sakamakon harbin sa da akayi a kafad’a an d’an tura su bawa wani d’an gari kariya.
Ya Sadeeyq ne kawai ya sani kuma ya rok’e sa da karya fad’awa kowa, so ganin halin da
yake ciki yasa yak’i fad’a masa wanda Twiny d’in sa ke ciki.
Two Weeks Later
Alhamdlillah ana samu ci gaba a tattare da Safwah dan yanzu lokacin sallah nayi take tashi
tayi again kuma yanzu ita keyi wa kanta komai.
Batun Sayyid kuma kullum suna mak’ale da juna, yau ma kamar kullum suna zaune su
biyu sai uban shagwab’a take zuba masa, nan take kuwa ta soma turning nasa on ba
abinda yafi janye hankalin sa irin yadda take turo small cute mouth d’in ta da yasha
reddish lipstick.
Nan take shaitan ya soma buga masa ganga, a nitse ya zamar da ita kan gadon ya soma
matsar da fuskan sa zuwa nata.
K’amshin sassanyan turaren ta na bugin sa ya sake birkicewa, ya kai kansa tsakan kanin
wuyan ta ya soma shinshina yana fidda wahalallen numfashi, Kisses ya shiga peppering
mata tako ina har seda ya haura sama zuwa fuskanta, Kisses yata raining mata a fuska daga
bisani kawai ya had’e lips nasu gu d’aya yana bin jikin ta da wani shafa.
Duk da bata san mene yake mata amma sai taji tana so dan sosai take enjoying thunder
touches nasa, bud’e baki tayi Sayyid ya samu daman kama harshen ta yana sucking gently,
yayin da ya soma k’ok’arin cire rigan ta.
Suwayd na zaune kansa na tsananin ciwo yaiji zuciyan sa ta shiga harbawa da sauri da
sauri, nan take wani irin tsoro ya lullub’e sa.
Ahankali ya mik’e yaja paralyzed leg nasan ya nufa part d’in Mammy dan kawai sai yaji
yana son ganin Safwah.
Yana sanya k’afa a falour’n yaji tsoron ya sake kama sa nan take kuma jikin sa ya soma
rawa, dakyar ya taka ya k’arasa k’ofan d’akin da Safwah ke ciki, runtse ido yayi lokacin da
ya rik’e handle d’in k’ofan.
Ahankali ya soma furta “Innah lillahi wa’innah ilaihir raji’un” sai da ya maimaita so uku
sannan ya bud’e k’ofar.
Ahankali ya shiga bud’e idanun sa inda basu sauk’a ko ina ba sai kan su, jikin sa ne ya shiga
rawa kaman mazari cike da tsananin kishi bak’in ciki da tashin hankali, gaba d’aya kan sa
ya kunce ya ma rasa meye ne zai yi.
Gefe da gefen sa ya kalla dan zuciyan sa ke basa duk abinda ya samu ya bugawa Sayyid,
rasa komai yayi ya taka like a hungry angry lion ya finciko Sayyid yayi jifa dashi, gaba d’aya
idon sa ya rufe zuciyan sa sai burning take kaman zata tarwatse saboda azaban kishi, he
just can’t believe abinda idanun sa ke gani, d’an uwansa da yake matuk’ar k’auna da matar
sa akan gado d’aya.
“Acccshhh” ya saki wata razananniya k’ara yana damk’e kansa dake barazanan tarwatse
Wa.
Ihu ta kwala lokacin da tayi arba da Suwayd ta k’ank’ame Sayyid ta baya tana b’uya.
“Wonders should never end” abinda Suwayd ya iya furtawa a zuciyan sa kenan.
Yau inhar bai tab’a lafiyan Safwah ba hankalin sa bare tab’a kwanciya, wato lokacin da ake
mata Iskanci bata yi k’aran an kawo mata d’auki ba sai yanzu data gansa, lallai she really
want to die she is going straight to the hell dan ya gama gane du abin nan da take yi
pretending ne.
Sayyid kuwa runtse ido yayi cike da bak’in cikin abinda yayi wa matar d’an uwansa da yake
matuk’ar so da k’auna, yanzu yasan badan yazo ba Allah kad’ai yasan iya kan abinda zai
aikata, zuciyan sa ce ta shiga zafi yayin da k’ank’ame sa da Safwah tayi ke affecting sa the
more.
Fuzgo ta Suwayd yayi ya d’aga hannu zai wanke ta da mari Sayyid yayi saurin shiga
marin ya sauka akan kyakkyawan fuskan sa.
Ware ido Suwayd yayi cike da tashin hankali yana ja da baya wane wanda yayi kisan kai,
hannun da yayi marin da shi kuwa wani irin rawa yake.
Kallon kyama da tsana kawai yake bin hannun dashi yana jin dama zai samu wanda zai
raba sa da shi right away.
In crack voice yace “Akhe… Akh.. Akheey please.”
D’agawa Sayyid da jajayen idanun sa yayi ya sauk’e kan Suwayd, hakan ya tilasta masa yin
shiru batare da ya shirya ba.
Rab’a sa Sayyid yayi ta gefe ya wuce, Sayyid na fita ta soma ja da baya da baya cike da
tsoro, wani irin kallo ya jefe ta dashi ya juya da sauri yabar d’akin dan yasan inhar anger
tayi taken over nasa zai iya aikata komai.
Sayyid na shiga part d’in su ya fad’a toilet yasa lock ya zame a bakin k’ofan ya shiga rusa
kuka kaman ransa zai fita, kuka yake sosai wanda duk rashin imanin mutum in yayi arba
dashi sai ya zubar masa da kwalla, mik’ewa yayi ya nufa mirror dake a toilet d’in ya buga
kansa yana jin gwara ya kashe kansa ya wuta da yaci gaba da aikata rayuwan dabbobin da
ya sanya kansa ciki.
Sosai jini ya wanke masa fuska buga kansa dake tsananin sarawa ya shigayi ajikin bango.
Jiri ne ya d’ebe sa ya fad’i a k’asa yana wani irin tari na fitar hankali, nan take ya soma
feshin jini not as kaman yadda yake amai da.
Buga k’ofan toilet d’in Suwayd yake yana kuka helplessly amman ina Sayyid baima san
yana yi ba dan ya dad’e da ficewa a hayyacin sa.
Bugawa yake wane zai b’alla dan hannayen sa har sun soma jini.
Back inside the toilet kuwa shi kansa Sayyid sai da ya firgita da halin da yake ciki, yafi thirty
minutes acikin wannan halin sannan cike da k’arfin hali ya mik’e ya sakewa kan sa shower.
Ya dad’e kafin ya samu ya bud’e ya fito, kallon tausayi yabi Suwayd dashi kawai ya kawar
da kai.
Kaya ya sanya pretending to be alright ya fice daga gidan, ikon Allah kawai ya kaisa asibitin
da yake ganin Dr.
Bai iya k’arasar da kansa cikin asibitin ba ya fad’i daga nan kuma bai sake sanin mai ya faru
dashi ba..
Kuka Suwayd yayi tayi yana tunanin abin yi dan aam bazai so k’aunan da suke wa juna da
d’an uwan sa ya tafi ba dole he has to do something…
Sai bayan kwana biyu Sayyid ya farfad’o, d’akin ya shiga bi da kallo ya sauke idanun sa
akan Dr Salis.
Murmushi Dr Salis yayi yace “Sannu Nasir ka farka?”
Gyad’a masa kai Sayyid yayi yana forcing out force smile.
Taimaka masa Dr yayi ya shiga toilet yayi wanka ya d’auro alwala ya fito.
Saida ya sauk’e sallolin dake kansa sannan ya koma ya jingina jikin sa da gadon.
Shayi mai kauri Dr ya had’a masa ya basa yasha, sannan ya mik’a masa Magungunan sa
yasha.
Sai da ya tabbatar ya samu nutsuwa sannan Dr Salis ya k’ira sunan sa kindly.
D’agowa kawai yayi yana kallon sa batare daya furta ko wani kalamu ba.
“Sayyid why? Meyasa? Anya kuwa the religious, kind and calm Sayyid d’in da na sani ne ba
wani aka chanza ba? Why are you acting in this way? Meyasa kake abu kaman wanda
baisan mihimmancin yarda da k’addara ba?”
Hawaye ne suka soma kwarinyo wa Sayyid nan take ya soma kuka wane d’an k’aramin
yaro.
Ahankali Dr Salis ya koma kusa dashi ya janyo sa jikin sa ya rungume cike da tausayi dan
shi shaida ne akan son da yakewa Safwah da yadda yake tsara musu rayuwan auren su.
Rarrashin sa ya tayi inda ya samu yayi shiru dakyar, had’e hannayen su Dr Salis yayi
ahankali ya soma magana “Nasir na rok’e ka dan Allah ka hak’ura da Safwah haka ka
barwa d’an uwanka, lokaci yayi da zaka cire matar data haramta agare ka a ranka, ka karb’i
jarrabawar da Allah ya jarabce ka hannu bibbiyu insha Allah you won’t regret it, ka karb’i
matar ka insha Allah zakayi farin ciki nan gaba, kayi hak’uri Nasir “Innallaha Ma’assabirin”
In Crying tone Sayyid ya soma magana “Nagode Dr Insha Allah bazan sake ai kata ba
dai dai ba, zan kuma rungumi k’addara ta, na hak’ura na bar masa zan kuma karb’i
Sayyada a matsayin zab’in AIkhairi da Allah yayi min'”
Yana k’are maganan ya fashe da sabon kuka yana fidda wani irin numfashi, ganin ciwon
na k’ok’arin tashi Dr Salis yayi saurin yi masa alluran bacci.
Not long enough wani wahalallen bacci ya d’auke sa.
Alhamdlillah Safwan yaji sauk’i sosai dan haka ya d’auka hutu ya tawo gida, lokacin da ya
riski Twiny d’in sa a wannan halin ba k’aramin kuka yayi ba.
Amma kullum suna tare da juna day and night yana d’an tuna mata memory’s d’in da
suke sharing together.
Tunda Sayyid ya dawo ya kasa kula Suwayd saboda kunyar abin da ya aikata, tun Suwayd
na binsa yana bashi hak’uri har shima yayi zuciya ya fita daga harkan sa.
Yanzu haka lamarin ya zamo wane gaba a tsakanin su dan inhar d’aya na zaune a wuri
d’aya baya zama, Arif da Haidar sunyi fad’an sunyi fishin sunyi masifan harsun gaji.
Ya kama Sunday, k’arfe shida saura kwata Safwah na zaune tana wasa da Teddy bears nata
ta d’an buga d’aya nan wak’an “Wait for Me” ya soma tashi, nutsuwa tayi tana saurara.
Wani abu take son tunowa amma ta kasa nan take kanta ya soma wani irin ciwo, tana ci
gaba da son tuno wani abu game da Teddy bear d’in.
Wak’an tata maimaita wa amma sam ta kasa tuna komai dan haka ta kwalla k’ara, nan take
kuwa Mammy tayi saurin fitowa da goran ruwan sanyi a hannun ta, du ta rikice har ta sake
goran ruwan ajikin Safwah.
Take kuwa Safwah ta shiga ja da baya tana k’ok’arin tuno wani abin again buh still ta
kasa, zamewa kawai tayi a gurin bata motsi.
A rikice Mammy tayi kanta tana k’iran sunan ta du tama rasa abinyi, Safwan ya shigo ya
tarar da abinda ke faruwa da sauri ya k’arsao yana tapping kumatun ta.
Ajiyan zuciya taja amman bata bud’e idon ta ba, d’ago ta Mammy tayi ta k’ank’ame ajikin ta
tana tambayan ta mai ya faru.
K’in magana tayi kawai ta shiga rusa kuka wane k’araman yarinya tana shure_shuren k’afa,
Ammey data shigo sallama da Mammy sanda ta zubar da kwalla ganin abinda Safvwah’n
keyi.
K’arisowa tayi ciki tayi pecking Safwah da Safwan dake kuka sannan tayi saurin yin
sallaman da Mammy ta fice dan har in ta tsaya itama tasan kukan zatayi.
Mammy ma daurewa kawai take dan sosai Safwan ya bata tausayi yadda yake kuka kaman
k’aramin yaro, kaman ba great Soldier’ n da akeji dashi ba.
Ahaka Granny tazo ta same su, fad’a sosai ta shiga yiwa Safwan dan kukan da yake yayi
yawa, there is no day goes by bai zubar wa Twiny d’in sa tears ba.
Bayan an had’u a Babban falour after dinner Sayyid ke shaidawa Granny ya tsayar da
ending of the month lokacin bikin auren, and same goes to Haidar ganin haka Abuh yace
har Suwayd da Arif d’in ma a had’e.
K’unk’uni Arif ya farayi wai shi bai shirya ba dan ko kud’in had’a lefe bashi da, 2mil
Granny ta musu transfer dukan su kowa yaje yayi shiri.
Akwati dozin_dozin sukayi illa Suwayd da yace shi ba yanzu zaiyi ba dam dole aka kyale sa.
Event bakwai aka shirya wanda insha Allah za’a soma a next week…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *