SOYAYYAH CHAPTER 17 THEND QARSHE

SOYAYYAH






CHAPTER 17 THEND QARSHE




Tun Suwayd na d’aukan abin na Zee da wasa harya dena ya koma aikin rarrashi buh the more yake tausan ta the more qanwar mamarta ke zuge ta, still yauma suna zaune shi yana zaune da little Safwah a laps nasa yana aiki a laptop ita kuma tana can zaune kan gado ta had’e giran sama da qasa wane bata tab’a dariya ba, murmusawa yai ya cigaba da abinda yake sanda ya gama tsaf ya mik’e ahankali yadda bazai tayar da Little ba ya kwantar da ita then ya qarasa kusa da ita ya zauna, banza tayi dashi wane wani trash daman yasan haka zata faru dan haka ya ajiye pride and ego nasa ya riqo hannayen ta yana wasa da yatsun ta.
Qoqarin kwacewa ta soma amma ta kasa dan riqon dayama hannun bana wasa bane, surutu yata zuba mata amma ina Zee tayi nisa batajin kira dan kaman dutse haka ta zama harya qaraci abinsa ya qyaleta.
Daren ranan bata rintsa ba tana aikin saqa da warwara cause time na tafiyan qara matsowa yake, har aka qira sallah ta gaza samo solution dan haka ta yanke shawaran qiran qanwar mamarta da safe, saida tayi sallah wahalallen bacci yai gaba da ita.
The following day, da wuri ta qira Aunty’n tata ta irga mata halin da ake ciki, nan ta sake bud’e sabon babin zuge ta aikuwa luckily ta sake hawa kai ta zauna, cikin sati d’aya Sam Suwayd ya kasa gano kanta dan gaba d’aya ta sake birkicewa, abinda yafi qona masa rai shine sometimes yana fad’a tana fad’a dan haka ya fice harkan ta gaba d’aya.
Haka al amura sukai ta faruwa har Allah ya kawo wannan rana da wasu kejin tsoro wasu ke jin takaici, already sunyi sallama da kowa qarfe biyar duk yadda Suwayd yaso Zee ta saduda suyi sallaman arziqi taqi dan haka kawai ya ajiye mata kud’i ko wani buqata zaizo suka tafi, mutane dayawa aka musu rakiya anata yi musu fatan nasara, Safwah banda kuka Babu abinda take dan sosai Zee ta bata tausayi.
Qiran passengers da aka soma yasa Suwayd riqo hannun ta suka wuce suna waving ma familyn nasu hannu har suka shiga jirgi, tunda suka zauna banda kuka Babu abinda Safwah keyi da tunanin halin da Zee ke ciki har bacci ya d’auke ta, Zee kuwa kuka ta shigayi tsakani da Allah haka har Hafsa tazo ta same ta.
Shafa hannun ta da yake ne yasa ta farkawa duk idanun ta sun mata nauyi saboda yadda tasha kuka, sanda ta nutsu ta soma bin ko ina da kallo only to find kowa ya fice sai su, murmushi ya mata ya miqar da ita suma suka fice, abokin sa dake jiran su nan take ya qaraso suka gaisa yasa kayan su a mota suka shiga yaja suka tafi, had’ad’d’iyar flat d’insu ya wuce dasu suka soma wanka sukaci abinci suka bi lafiyar gado.
Sai almost nine suka tashi, sallah’n magrib da isha suka soma yi suka qaracin abinci ya chanza layin wayan sa ya qira gida, saida suka gaisa da kowa ya soma qiran layin Zee though yasan ba d’auka zatayi ba, k’a idan sa da mutum three missed call amma yau sai gashi yama Zee har goma tak’i d’agawa, haqura yai ya qyale ta suka wuce zasu kwanta nan Suwayd yace bai san zance ba dan tun Ana saura sati biyu tafiyan su yana tare da Zee, du yadda taso yabarta yaqi dole ta haqura takoji maza dan gyara na musamman su Mummy suka mata kafin su tawo, time in daya qyaleta ko hannu bata iya d’agawa wanka ma sai shi yayo mata suka kwanta.

Without any hesitation ya soma mata processing komai, nan take komai ya zamo perfect suka soma abinda ya kawo su, karatu suke cike da burgewa dan kowa yasan su cikin makaranta as the best perfect lovely couple ever.
Du hutun sa a Nigeria yake tare da Zee yadda yake nuna mata zallan so da qauna yasa ta manta du wani zuga ta kama mijin ta hannu biyu, Little Safwan da Safwah kam sai girma suke gwanin burgewa yayin da kyansu ke qara fitowa, sam babu abinda little Safwah ta baro ana mamarta yayin da little Safwan ba abunda ya baro ana Safwan.
As life moves on yanzu just a month ya ragema Suwayd abinda ya kawo sa yayin da Safwah Keda two years ahead, du tunanin Suwayd bai wuce yadda yana ji yana gani zai bar *Flower* d’insa ba ya tafi, cikin wannan watan ba abinda suke fuskanta a makarantan dan du wani lokacin su ya tafi gurin ririta juna, she never believes dagaske tafiya zai ya barta sai ranan, she cries so much lokacin da yake hawa steps na jirgi haka har suka tafii, ranan kwana tayi kuka buh tuna promise d’in data masa na giving her goddamn attention wa karatun ta yasa ta rarrashi kanta ta zama strong.
Karatu take sosai yayin da kullum suke cike Video call.
Tsayin shekara da tafiyan sa kenan amma ko sau d’aya baiyi visiting ta ba, tun tana qorafi harta gaji ta zuba masa ido yayin da in missing sa ya isheta sandai ta zauna taci kuka ta gode Allah, qoqari da basirarta yasa duk wani school competition sai kajiyo ta aciki yanzu duk duniya damuwan ta d’aya rashin haihuwa ganin almost four years kenan da auren nasu amma ko b’atan wata bata tab’a yi ba.
At Zee’s side wani irin farin ciki take ciki ganin ko ta tambayi Suwayd when zaije gurin Safwah yana shashantar da zancen not knowing that tsaf ya gama shirin tafiyan cause an yaye little Safwan zai kai mata shi yanda zasu saba sosai kafin ta dawo, ana hakan Zee ta fuskanci tana da wani cikin dan tare suka yaye yaran.
Da farin ciki ta fad’awa Mum inta ita kuma ta shaida ma Aunty’n ta, a ranan kam ta qira ta dunga zigata wai inhar baso take ta tsufa ba ta zubar da cikin, yanda ta dinga nuna mata Suwayd da Safwah had’a baki sukai sukayi planning dan karta tsufa yasa ta hau ta zauna , da yamma kuwa sai ga tabs ta tura yarta ta kawo mata batare da tsoro ko tunanin komai ba ta bankawa cikin ta, qarfin kwayoyin yasa ko minti sha biyar batayi ba ta fara bleeding kafin wani lokaci gaba d’aya ta fice cikin hayyacin ta, luckily time na dawowan sa yayi dan haka yana shigowa ya same ta a wannan mawuyacin halin, bai tsaya b’ata lokaci ba ya d’auke ta suka wuce asibiti.

Emergency ward akai da ita likitoci suka rufa akanta dan bata taimakon daya dace, sunfi two hours kafin su samu su tsayar da bleeding d’in sai dai tun kan suzo cikin ya riga ya zube, saida aka mata wankin mara aka fito da ita zuwa d’akin hutu.
Lokacin da Dr Alkasim ke masa bayani ko tsayawa gama ji baiba yabar asibitin gaba d’aya, rai a matuqar b’ace ya had’o kayan little Safwah ya d’auko ta daga gidan Sayyid ya wuce ya d’auko Little Safwan ya wuce kai tsaye dama flight in ranan zai bi, da qoqarin wani friend d’in sa ya samu yai ma Little Safwah Visa qarfe takwas Jirgin su ya d’aga.
Safwah na zaune a falour tana hutawa tana murnar gama jarrabawan da sukai ranan ta jiyo doorbell, bata wani tsorata ba sanda ta kalla time taga yanda dare yai, take ta soma tunanin to waye dakyar taja jiki ko hijab bata sanya ba in fact tama manta kayan dake jikin ta taje ta bud’e, surprisingly ta tsaya da baki wide open tana kallon su.
Wasu pathetic looks da yake jifan ta da yasa ta had’iyan yawu dakyar dan sai lokacin da tuna me ajikin ta gashi ta masa promise no matter what in zata bud’e qofa zata sanya hijab, jikin tane yayi wani irin Sanyi ta sunkuyan dakai tana wasa da yan yatsun ta looking pitiful.
Bai kula ta ba ya sake hannun yaran ya wuce ciki, durqusawa tai ta bud’e musu hannu sukai hugging ta, breaking hug in tai taja su suka shige ciki suma, d’ayan bedroom in ta wuce da su ta soma yi musu wanka suka dawo falour ta zuba musu abinci.
D’akin da yake ta shiga ta same shi ya shirya yai flat akan gado ya zurawa ceiling ido, ahankali taja paralyze legs nata ta qarasa ta zauna ta side, dakyar ta iya gathering courage ta soma magana ” *Habibi* please am sorry wallahi it was not intentionally..”
Shiru tayi ta tsaya tana kallon sa taga ya yake d’aukan zancen amma yadda tai noticing bai ma san tanayi ba nan ta gane lallai ba laifin data yi ne yasa sa b’acin rai haka ba.
Ta miqe zata fita ya riqo hannun ta kafin ta fuskanci abinda yake shirin yi ya fuzgota ta fad’a kansa hugging her so tight, yanda yake sauke ajiyan zuciya akai_akai yasa hankalin ta tashi amma zata bari Harya sauko saita tambaye sa damuwan sa jin ana buga qofa yasa tai saurin Zame jikinta ta miqe kafin ta gama saita nutsuwanta yaran sun kunno cikin d’akin, murmushi Suwayd ya musu ya nuna musu kusa dashi suka qaraso kan gadon ya qanqame su not long enough bacci ya d’auke su both, qare musu kallo tayi ta fita ta gyara inda sukaci abinci ta zauna tana tunanin rayuwa, tuno Safwan d’inta yasa gaba d’aya ta fita daga nutsuwanta ta soma sana ar tata ta kuka saida tai mai isarta ta miqe ta d’auro alwala ta tayar da Sallah, bayan ta idar ta dad’e tana masa addu’a har bacci ya d’auke ta agun.
Qarfe uku Suwayd ya farka ahankali ya zame yaran ya fice nan ya hangota kwance gefen kujera ta takure, d’aukan ta yai ya wuce d’ayan bedroom d’in ya rungume ta sukayi bacci.
The Following day
Duk sun riga ta tashi, tana tashi ta soma qoqarin had’a musu breakfast bayan sun karya tama yaran wanka ta wuce itama ta shirya, simple make-up tai applying ta same sa a d’aki a nitse ta soma tambayan sa amma sam yaqi fad’a mata exactly what is bothering him, mayar ma da laifin kanta yai bataji maganan sa ba in zata bud’e qofa bata sanya hijab, cike da kissa ta bashi haquri suka manta da komai.
One month ya mata ya tafi yabarta da yaran kasancewar tana da Nanny yasa take bar mata yaran in zata tafi school, in ta dawo kuma ita kanta bata da lokacin kanta saina yaran, yarda yaran ke qaunan Juna ya tabbatar mata lallai Little Safwan bazaiyi maraici ba.
Tunda ya koma ko takan Zee baibi ba dan tana gida ma ta kuma fad’ama iyayen ta duk abinda ya faru, jin haka yasa Dad inta yai fishi da ita ya kuma tsorata ta da sai yasa Suwayd in ya sake ta, hakan yasa hankalin ta mugun tashi gashi kullum cikin kiran sa take baya d’auka.
Saida Granny tasa baki ya yarda yaje ya d’auko ta daga gida amma kowa harkar sa yakeyi.
Musty duk qoqarin sa yanzu bai wuce mallakar Kadsah ba amma ina Sam ita baya gaban ta dan inya fara mata maganan aure ma kuka take masa hakan yasa ya kyale ta yai magana dasu Granny suka roqi daya qara mata lokaci.
A kwana a tashi babu wuya agurin Allah yau Safwah ke rubuta final paper inta farin ciki Sam yaqi barin ta yau burin ta ya cika ta kammala karatun ta, gagarumin party ake had’a mata acan gida Wanda Sam bata san dashi ba.
Saida ta had’a takardun ta da komai ta had’o ya nata ya nata tayo qasarta , kowa sai yaba kyau da girman data qara yake, mamaki tata yi da taga yanda yaran su Ya Sadeeyq suka zama ‘yan mata yaran su Sayyid ma duk sun girma yayin da nata yaran Keda shekaru uku, dawowanta ya mugun yiwa Zee dad’i ko bakomai zata sa ya yafe mata laifin da tayi tunda haryanzu yaqi sakkowa.
Kwana biyu da dawowanta akai k’ayataccen Partyn suka koma makeken gidan su da Suwayd ya gina Wanda Zee Sam bata da labarin sa, ranan da Safwah ta cika sati da dawowa Zee ta same ta tafad’a mata duk abinda ke faruwa, sosai taji tausayin ta dan haka a daren ranan ta same sa da kuka ta bashi haquri, kukan da take da abinda take fad’a yasa tausayin ta kamasa ya haqura ya yafe ma yar Uwar tata suka koma living happily ever after.
Two Months Later
Safwah da Zee zaune a babban falour suna hira gwanin burgewa, tunda suka zauna ta lura da hamman da Safwah take jerawa kafin wani lokaci bacci ya d’auke ta, mamaki ne ya cika ta dan gaba d’aya Safwah ta chanza wane wata me sleeping sickness ba daman a zauna hira da ita sai bacci, ga shegen tsurfa da masifa wanda Sam da bata dashi, bata kawo komai a ranta ba ta qira Suwayd ta fad’a masa ko minti goma ba ayi ba sai gasa tsaban mamaki ma kasa kula sa tai ta zuba ma sarautar Allah ido……..
Neman guri yayi ta gefen Safwah ya tsare ta da ido dan tabbatar da zargin da zuciyar sa take, ahankali ya riqo kyawawan hannun ta yana qurama tafin hannun ta ido, wani irin faria ciki mara misaltuwa ne ya mamaye sa he just can’t believe abinda idanun sa suke gani, dagaske akwai cikin sa jikin ta gyaran muryan da Zee tayi ne yasa sa dawowa hankalin sa.

Kallon ta yayi a tsanake yana son karantan yanayin ta jin motsin Safwah yasa sa saurin kallon ta, surprisingly ta soma binsa da kallo ganin dai time in dawowan sa baiyi ba, maidan da kallon ta kan Zee tayi with questioning expression. 
Kafin takai da bata amsa husky voice nasa ta tare su ” *Flower*!! Are you alright?”
Kallon sa ta tsayayi da mamaki kafin ta soma jera hamma not long enough kuma bacci ya sake daukan ta dan sosai take jin sa, “sleeping sickness” ya fada ahankali yana shafa fuskan ta. 
Murmusawa Zee tayi ahankali tace “Baby ni gani nake kaman *Flower* is pregnant”. 
Murmushin ya miyar mata batare da yabi takan zancen nata ba yace “Sweetheart wanka zanyi”. 
Ahankali ta miqe taje dan hada masa ruwan. 
Kafin ta dawo ya maida Safwah d’akin ta ya kwantar, komawa part d’in Zee yayi dan yin wanka, yana gamawa ta tayasa shiryawa suka fito falour suna kallo suna hira jefe_jefi, gaba d’aya hankalin sa yana kan Safwah lura da haka da Zee tayi yasa ta miqe jiki a sanyaye ta tafi part d’inta, bayanta yabi da kallo cike da tausayin ta kafin ya miqe ahankali ya nufa part d’in Safwahn. 
Farkawan ta kenan taji alamun shigowan mutum wanda ko ba’a fada ba tasan waye cause tun kafin ya qaraso qamshin sa ya mata sallama, lumshe kyawawan idanun ta tayi son sa na qara fusgarta harya qaraso ya zauna a gefen ta. 
Hannayen su ya had’e guri d’aya batare da yayi magana ba ya zaro wayan sa dake faman ringing, kafesa tayi da ido tana jin yadda yake bayani a nitse da alama da ogan sa yake magana, jin yanda cikin ta ke kukan yunwa yasa ta zame hannun ta ahankali ta wuce toilet, wanka tayi ta d’auro alwala jin an soma qiran sallah ta fito sai dai bata same sa ba da alama ya wuce masallaci, kaya marasa nauyi ta sanya ta d’auka hijab d’inta ta tada sallah, tana idarwa ta fito dan tsaban yunwa ji take wane taci babu, duba warmers da Zee ta jera a dinning tayi taji du k’amshin abincin bai mata ba saima tashin zuciya da suka sata. 
Juyawa tayi ta koma part d’inta ta bud’o fridge inta ta d’auko _Abu bilal yoghurt_ daya zama favorite inta ta zauna akan kujera ta soma sha, tsaban yanda take jin dad’in sa har wani lumshe ido take, kafin ta farga harta shanye amma ji take kaman ba abinda taci. 
Haka taita ciro abubuwa kala_kala a fridge in tana ci, jin qiran sallah yasa ta komawa d’akinta dan sauke farali, kafin ta idar da Sallah zuciyan ta ya soma mugun tashi. 
A daddafe ta samu takai ta wuce toilet da sauri ta shiga kwara amai, dawowan Suwayd da Little Safwan kenan daga masallaci suka wuce part inta, ganin bata falour suka wuce d’akin ta, cike da tashin hankali Suwayd ya qarasa toilet d’in jin yanda take kakarin amai da alama ya dena fita ne, iya galabaita ta galabaita dan gaba d’aya ta fice hayyacin ta ga wani mugun zazzab’i da ciwon kai da suka rufe ta, a tsugune take amma jiri take ji Little Safwan ganin halin da take ciki yasa sa fashewa da kuka dan bai tab’a ganin Ammah’n tasa a wannan halin ba, rikicewa Suwayd yayi yama rasa yane zaiyi riqo hannun sa yayi in sorting tone yace ” Je gurin Mummy kaji! Ammah will be fine”. 
Kasantuwar sa yaro mai ladabi yasa ba musu ya gyad’a kai ya wuce jiki a sanyaye, thought shikad’ai yasan halin da yake cikin ganin beloved Ammah’n sa ahaka, yana fita ya koma toilet d’in ya kamata harya samu aman ya lafa ya had’a ruwa ya mata wanka ya nad’o ta da towel yazo ya kwantar sannnan ya koma toilet d’in ya gyara gurin, bayan ya fito ya same ta still yadda ya barta, da kansa ya shirya ta sannan ya wuce ya had’o mata lipton ya dawo wanda ya samu tasha dakyar sai dai kuma kusan rabin sa saida ya dawo ga temperature nata daya mugun hawa. 
Taimakon da zai iya bata yayi inda ya 
acci ya d’auke ta, zama yayi ya tsare ta da ido cike da tausayin ta ya shafo cikin ahankali ya furta “Allah ya albarkaci abinda ke ciki”. 
Mik’ewa yayi yaje ya samu Zee dake ta faman rarrashin Little Safwan yaqiyin shiru, yana gano Dad in nasu ya taso da sauri ya qanqamesa yana sake fashewa da kuka, d’agesa sama yayi ya rungume yana rarrashi harya samu yai shiru then suka wuce dinning dan cin abinci sandai Zee da Little Safwah ne kawai ke iyaci dan su banda juya spoon ba abinda suke, du tunanin Suwayd bai wuce halin da Safwah take ba gashi yana ji yana gani a d’akin Zee zai kwana abinda ya hargitsa masa lissafi kenan dan yasan dole tana buqatar kulawar sa a wannan halin da take ciki, wane Zee ta karanci zuciyan sa ta miqe ahankali taja Little Safwan da Safwah ta wuce ta kimtsa su kowa ya wuce d’akin sa ta dawo agurin sa, zama tayi tana qoqarin mayar da kwallan da suka taran mata a ido ta riqo hannun sa ahankali ta soma magana ” Baby kaje gurin ta har lokacin da zata samu sauqi nasan ayanzu tana buqatar ka fiye dani” tana gama fada ta miqe da sauri saboda kwallan data zubo mata yai saurin riqo hannun ta ya miqe ya qanqame ta qam ajikin sa sonta da tausayin ta na ratsa sa, kuka da take ta riqewa ne ya samu daman kwace mata ta soma yi ba qaqqautawa, kasa rarrashin ta yayi sai bayan ta da yake shafawa ahankali sanda tayi mai isan ta ya d’ago ta without uttering any word suka wuce part inta, da kansa ya mata wanka ya shirya ta ya nema guri ta gefen gadon ta ya zauna ganin ta kwanta ta juya masa baya, hannu yasa ahankali ya juyo da ita kafin ta fuskanci abinda yake shirin yi yai shutting ta da hot kisses, du yanda taso qin basa had’in kai ta kasa dole tai giving in wa kiss nasan suka shigayi passionate yet affectionate, sunfi minti goma kafin yai pulling out ya gyara mata kwanciya ya fice. 
Yana fita ta fashe da masifaffiyar kuka sanda tai mai isanta tayi shiru wahalallen bacci yai taken over nata.
Yana komawa wanka yayi ya shirya ya kwanta ya qanqame ta ajikin sa zafin da jikin ta ya d’auka na ratsa sa, ga wani bala’in tausayin Zee da yake matuqar ji na mamaye zuciyar sa duk yadda yaso bacci ya d’auke sa abin ya faskara dan haka ya kwantar da ita ahankali yaje ya d’auro alwala ya dawo ya soma jera nafila. 
Har uku baiyi bacci ba yana addu’o’i lokacin ne kuma jikin Safwah ya rikice banda rawan sanyi ba abinda take, haka suka kwana dan sai da sukayi Sallah’n asuba ya samu bacci ya d’auke ta, qiran gaggawa da aka masa a office yasa ko karyawa baiba ya fice, koda yaje kasa aikata komai yayi saboda tunanin halin da *Flower* d’insa take dakyar dai ya daure. 
Acan kuma koda safiyan ciwo tayi sosai sai dai sha biyu nayi ta nemi komai ta rasa harta fito suka sha hira da Zee, qarfe uku ya dawo ganin ta dayai cikin qoshin lafiya ba qaramin farin ciki yai ba, wanka yayi yaci abinci ya zauna cikin su aka cigaba da hiran dashi. 
Yamma nayi zazzabi yace salamu Alaikum haka ta kasance cikin mugun laulayi ga sleeping sickness,ga morning and evening sickness har tsayin wata zuwa lokacin duk ta gama fita hayyacin ta dan ma tana samun kyakkyawan kulawa, both dangi kowa yasan batun cikin wane akan cikin aka soma musu haihuwa haka suka dauko so da qauna suka daura masa. 
D’aki guda a part d’in Safwah yasa aka soma gyarawa, wani irin gyara yasa akama d’akin na ban mamaki dan gaba daya yanda akayi decorating insa ne zai shaida ma saboda d’iya mace aka tanade sa, haka nan jikin say ke basa *PureLamp* insa mace zata haifa. 
Luckily Abdul da Musty sun samu sun dai_daita da matan nasu har ankai kudi an tsaida rana sai jiran lokacin biki idan Allah ya nufa.
As life moves on yanzu cikin Safwah nada takwas months a duniya ya fito sosai ga wani mugun kyau daya mata kasancewar ta doguwa, already Granny tasa an dawo da ita gida dan anan zata fi samun kulawa tunda haihuwan fari ne, gaba d’aya Suwayd ba ason ransa ba amma haka ya daure but kullum yana tafe a hanya, kulawan da Safwah ke samu ta kowani b’angare dole abin ya burge ka dan kowa yana iyakar qoqarin sa, sai dai wani tashin hankali gaba d’aya tasa tsoro aranta hakan yasa kullum cikin fargaba take, anyi fada anyi nasiha amma a banza haka zata kulle kanta a d’aki tata kuka. 
Yauma tana zaune ta zubawa ceiling ido banda tunanin naquda ba abinda take kawai taji maranta ya mugun murd’awa, damk’e ciki tayi cike da azaba tana cije baki kafin taji abu nabin qafan ta, duk yadda taso daurema ciwon abun ya faskara haka har Mammy ta shigo ta iske ta, hankali a tashe tayi kanta amma ina abu ya faskara dan the pain is just unbearable in an eye blink gaba d’aya ta rasa kanta, Mammy na juyawa da niyyan samo wanda zai taimaka mata su wuce asibiti sai ga Suwayd nan, ko takan Mammy baibi ba ya d’auke ta tabisa suka wuce asibiti. 
Acan ma baqaramin wahala tasha ba har aka samu aka tsayar da bleading d’in dan lokacin haihuwan ta baiba, sanda aka tabbatar da lafiyan Babyn aka wuce da ita d’akin hutu.
Mammy na ganin Suwayd ya fito yana goge zufa tai saurin qarasowa tana tambayan sa halin da ake ciki, ajiyan zuciya ya sauke ya riqe hannun ta suka wuce office d’in sa, zaunan da ita yai ya wuce ya d’auko mata ruwa mai sauqin sanyi. 
Gaba d’aya hankalin ta nakan jin halin da Safwah take amma sanin inhar bata kwantar da hankalinta ba fad’a mata zai ba yasa ta d’auka ruwan tasha ahankali ta fuskance sa, a nitse ya fayyace mata komai ganin yadda ya runtse ido tasan ba qaramin hurting sa abin yayi ba, ahankali ta riqo hannun sa in sorting tone ta soma lallashin sa, sanda ya saki ransa ta tashi ta wuce gurin Safwahn. 
Sai bayan sallahn isha ta farka yana zaune akan kujera yana staring ma beautiful face inta ta bud’a ido, maida idon tai ta kulle ganin kallon daya soma binta da suna haka har Mammy ta fito daga toilet, “She is awake” kawai yace ya miqe ya fita. 
Zama gefen ta Mammy tayi ta riqo hannun ta tana mata sannu, taimaka mata tayi ta tashi then ta wuce toilet ta had’a mata warm water da zata gasa kanta, tunda ya fita bai dawo ba har saida tayi bacci lokacin daya dawo dakyar Mammy tasamu ta korasa gida kar a shiga haqqin Zee, haka ya tafi badan ransa yaso ba.
Kullum saiya zo d’akin amma ko kallon ta saiya faki idon ta yake dan fishi yake sosai da ita, har aka sallame ta magana bai had’a su ba tasan bata da gaskiya shiyasa bata wani damu dan kullum cikin kwantar mata da hankali yake amma ita d’in ta kasa kwantar da hankalin nata, koda suka dawo ma bata sauya zani ba dan saita yi bacci yake zuwa ganin ta, ta fuskanci hakan ne lokacin da tayi pretending in yin baccin qarya, harya gama kallon nata da gyara mata kwanciya bata motsa ba sanda ya fita sannan ta bud’e ido tana bin k’ofan da kallo, murmushi tata yi son sa da qaunar sa na sake shigan ta. 
A month Later Safwah an shiga month d’in haihuwa nan sabon tashin hankali ya saukar mata, gaba d’aya an gama shirya komai sai jiran tsammani Ga bikin Abdul da Musty daya zamo sauran sati biyu wanda ake fatan had’ewa da suna inta haihu kafin lokacin, Suwayd duk ya shiga cikin rud’ani dan mafarki yake sosai da Safwah kuma abinda yake gani yafi komai d’aga masa hankali dan wasiyya ce take bar masa akan Little Safwah da Babyn da zata haifa, kowa ya kasa gane kansa illa Granny daya fad’awa sai Zee data fuskanci Sam baya samun isashshen bacci yana raba dare yana roqan Allah karya tabbatar masa da mafarkin sa da abinda zuciyan sa ke zargi. 
Daren wata Alhamis ciwo ya tasan mata, kansantuwar ciwon ya had’e mata da ragwanta, tsoro da fargaba yasa kafin suje asibiti ta fita daga hayyacin ta, kowa ya gama tsorata da lamarin naqudar tata, yana kan sallaya wayan sa ya soma ringing ganin Granny yasa sa saurin d’auka yadda muryanta ta bayyanar da tsantsan tashin hankalin yasan babu lafiya a rikice ya miqe yaja car keys insa, Zee da duk taji abinda ya faru itama dogon rigan kawai ta zura da hijab tabisa, d’akin Little Safwan ta soma shiga ta same sa zaune yana kuka ba lokacin tsayawa tambaya shiyasa kawai ta riqo hannun sa suka wuce, kafin ta Fito ya d’auko little Safwah dan haka kawai suka wuce ko gidan sai mai gadi aka barwa ya kulle cause sun yarda dashi.
Da wani Mugun speed yake jan motan muna iya cewa ikon Allah ne kawai ya kai su, d’akin da take kawai ya fad’a kallo d’aya ya mata yaji wani mugun sanyin jiki da karayan zuciya sun saukan masa, banda sunan sa dana Ummy ba ba abinda take kira. 
Ummy dake waje banda kuka ba abinda take dan gaba d’aya ta karaya tana jiyo ihu da kukan Safwahn amma ba taimakon da zata iya bata, runtse ido tayi da qarfi jin wani ihun azaba data saki tana kiran sunan ta, duk addu’an dayazo bakin ta kawai yi take she wish duk ciwon zai dawo kanta Safwah ta samu sauqin abinda takeji, sake rintse ido tayi jin yadda Safwah ke sake kiran ta a Karo na ba adadi. 
Qanqame Abuh Little Safwan yayi yana kuka sosai he can’t believe Ammah’n sa zata tafi ta barsa kaman yadda ta fad’a masa a mafarki, kuka yake sosai Abuh da Abbah na rarrashin sa amma wane tunzura sa suke.
At Labor room gaba d’aya Suwayd ya ma manta wane shi, gaba d’aya jarumtar sa ta tafi sai wani mugun rauni da zuciyan sa tayi, he just can’t bear seeing his half of deen suffering like this. 
Ciwon na lafa mata ta soma kiran sunan sa dan neman yafiya, ahankali ya qaraso inda take ya zauna akan gadon ya d’aura kanta a cinyan sa, zaro hanky yayi ya soma goge mata zufa, sharp pain na sake hitting ta ta qanqame hannun sa cike da tsananin azaba har sanda faracunta suka fasa masa hannu, runtse ido yayi cike da tausayin ta dan yasan wannan zuqi da rad’ad’in da yake ji bakomai bane compared to situation inta, ahankali yake hura mata isakan bakin sa saboda yadda take zufa, du wani fans da Ac dake d’akin wane babu. 
Sake damqe hannun sa tayi cike da azaba tana ya kira mata Ummy, cike da tsantsan tausayin ta da rad’ad’in da hannun sa data damk’a yake ya cigaba da hura mata iska yana goge mata zufan. 
Idanun sa sun kada sunyi jajir saboda tashin hankali, du yadda ake tunanin abin ya zarce haka dan gaba d’aya kowa ya soma karaya da lamarin, gadan_gadan naqudan ya sake taso mata amma ina sai so suke tayi push ta kasa banda sunan Ummy ba abinda take qira dole aka kira Ummy itama ta shigo, zama tayi ta d’ayan side in tana shafa kanta ahankali tana karanta mata du addu’an daya zo bakin ta, nishin datayi mai qarfi yasa kan Baby b’ullowa amma Kuma ina duk tayi weak batajin Kuma daganan zata iyayin wani abin, lallab’a ta sosai aka shigayi kan ta daure if not they might lose the Baby amma ina. 
Hankali a tashe Suwayd yace ” *PureLamp* please save our Baby”
” I can’t *Habibi* bazan iyaba, am dying Ummy forgive me”. 
Ahankali wata Nurse ta qaraso cike da tausayi tace ” Haba *PureLamp* in *Habibi* ki daure kinji! ” kuka tasa hakan yasa Suwayd bugawa Nurse in mugun tsawan daya sa ba shiri Safwah tayi wani kyakkyawan nishi dayasa Babyn tare da mahaifa fad’owa duniya take aka yanke cibi banda kuka babu abinda Babyn ke canyarawa, ajiyan zuciya ta sauke wane an sauke mata dala da goron dutse, Ummy kuwa banda hamdala ba abinda take, yama manta da Ummy agurin ya d’agota ya qanqame yana sa mata albarka. 
Miqewa Ummy tayi ta fita then akata congratulating Mr nd Mrs Suwayd, ana wannan hali jini ya b’alle mata cike da tashin hankali suka rufa akanta amma ina………………
Du inda tashin hankali yake Suwayd ya shige sa he can’t watch her suffering like this, he have to do something but how?? Tambayan da yake tama kansa kenan dan yama manta mene aikin sa, ganin lamarin ya soma d’aga ma kowa hankali yasa wata jarumta shigarsa nan take ya koma Dr Suwayd d’in sa, da azama wata nurse ta miqo masa hand glove ya sanya, du yadda yake tunanin lamarin ya zarce tunanin sa, Ahankali duk wata naqura dake tare da ita ta tsaya chak. 
       Wani mugun sanyi jikin kowa yayi a d’akin yayin da Suwayd gaba d’aya ya daskare a tsaye cike da qin yarda, dafa sa Dr Alkasim yayi cike da tsan_tsan tausayi da raunanniyar murya yace ” We are sorry to say Dr but…..”
       Bai samu daman qarasawa ba saboda wata iriyar qara da Suwayd in ya saki ganin wata nurse na qoqarin rufe mata fuska da farin qyalle, a tsorace ta janye hannun ta cike da tausayin sa dan kowa shaida ne akan son da yake ma Safwah’n sa, gashi yanzu ta tafi ta barsa a dai_dai lokacin da yake matuqar so da qaunar son kasancewa da ita. 
Jikin sa na ya wani mugun sanyi yayin da yake kallon al’amarin tamkar a mafarki, me amfanin zamantowar sa likita tunda harya kasa taimakon ta a lokacin da take buqata, da jan jiki ya qarasa jikin gadon ya zauna ta gefe idanun nan jajir wane barkono, hannun sa dake rawa yakai ahankali ya riqo nata ya damqe not letting go dai_dai lokacin kuka me qarfi ya kwace masa, du rashin imanin ka in kaji abinda bakin sa ke ambata dole ka tausaya masa, jiyo kukan Babyn da yayi daga waje sosai ya qara sasa a rud’ani wani masifar qaunar Babyn yake ji a zuciyan sa yayin da wani sashi ke ankarar dashi itace fa dalilin rasa *Flower* d’insa, dafe kansa dake tsananin sarawa yayi ahankali ji da gani ya d’auke masa bai sake sanin inda kansa yake ba, tashin hankalin da ba’asa masa rana yayin da Suwayd ya zama unconscious lokacin kuma na’urorin suka cigaba da aiki, rabuwa likitocin sukai wasu kansa wasu kanta cikin ikon Allah kafin minti talatin komai ya daidai ta. 
Su duka suna a d’aki d’aya kowa da drip ahannun sa sai Baby dake hannun Mamy itama tans bacci peacefully, kwana biyu aka sallame su though Suwayd qarfin hali kawai yake, tsare_tsare aka shigayi sosai yanda bikin Abdul da Musty da suna zai kasance.
A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah har an soma gudanar da shagulgulan bikin, kana iya rantsewa da Allah Safwah ba ita ta haihu ba dan wani sheqi da walwali da takeyi wane sabuwar Amarya, angama taro lpy Alhamdlillah haka nan Baby tayi goshi ta kuma ci sunan Mamy wato Maryam zasu na qiran ta *Inayah* meaning cuteness. 
Wani bala’in qaunar yarinyar Suwayd da Musty suke wane ransu, kowa ya soma lura da hakan dan baya iya b’oye qaunarta haka ma Safwah kulawa babu kama hannun yaro. 
    Babu laifi yana qoqarin kamanta adalci dan sam da yake Safwah na gida bata dawo ba Zee batasan meke faruwa ba. 
    Ranar da tayi arba’in yazo ya d’auke ta suka koma gidan su, as life moves on yanzu *Inayah* nada 5months se girma take wane Kazan agric, like father like daughter babu abinda ta bari ana Suwayd kwayoyin idanun ta ne kawai na Safwah hakan yasa wata kyakkyawar qaunar ta a zuciyan baban ta, haka ma yan uwanta sosai sukeji da ita though sun fara fuskanta baban su yafi ji da ita,dan abu suke buqata da sun hada da sunan ta angama. 
Kwanaki nata wucewa wanda cikin yarda da ikon Allah yanzu *Inayah* nada shekaru biyu a duniya, abubuwa da dama sun faru kafin kawowan yarinyar wannan lokacin saboda wani Irin gata da babanta ke bata yasa ta tashi da wasu kalan dab’i u ga miskilanci harna innah lillahi wa innah ilaihir raji’un, baka cika ganin dariya ko murmushin ta ba sai tana tare da Dadanta sunan da take qiran sa dashi, ko kuma Daddy Musty sunan data bawa Musty dan sune ja gaba a b’acin ta. 
   Some months later 
Little Safwahn ne zaune a falour yana koya ma little Safwah assignment sai sauri yake saboda Dada ya kusa dawowa zasu wuce massallaci, ahankali take taku sanye da blue gown me zanen princess ajiki ta qaraso, wane sa anninta haka ta tsaya musu aka tana tura baki d’agowa little Safwah Tayi in sorting tone cause wataran itama tana biye mata tace ” Dada’s Princess me kike so? ” sai lokacin Little Safwan ya d’ago ya kalle ta ya d’auke kai cike da takaicin halin ta. 
Without uttering any word ya miqe dan yasan inya zauna za a sama matsala kuma Ammah ta hana sa biye mata, “Ya Safwan bamu gama ba fa” cewan Little Safwah a ladafce. 
    “Karki damu Baby zamu qarasa anjima”. 
Haushi ne ya kama *Inayah* dan dama shi tazo neman tsokanan sa ganin Dadan ta ya kusa ya dawo, bai gama barin falour in ba Dada yai sallama ya shigo jin muryan sa yasa ta fasa qara wane wadda ake qwaqulewa ido, sakin baki Safwah da komai ke wakana akan idanun ta tayi tana kallon ikon Allah, bata gama mamaki ba saida taga ya shigo hankali a tashe yana tambayarta me aka mata, babu kunya ba tsoron Allah tace ya Safwan ne ya mare ta gashi taqi sake kuncin alaman ba qaramin shigan ta Marin yayi ba.
Yadda gaba d’aya annurin fuskan Dadan nasu ya chanza yasa Safwan tabbatarwa shikenan yau tasa ta same sa, in shocked Safwah ta tsaya ranta na wani irin suya saboda baqin cikin halayen *Inayah*. 
“Safwan!!” Yai exclaiming da qarfi cike da qin yardar abinda yakeji. 
   “Na am Dada” ya amsa cike da nutsuwar sa. 
“Come here”. 
    “Dada wallahi qarya take” Little Safwah tayi stating angrily dan itama sosai ranta ya b’aci and tasan shikenan yanzu Dada zai fara musu fada. 
    “Shut up” ya katse ta kaman zai make ta. 
Ahankali Safwan ya qaraso cike da ladabi kafin ya tsuguna Safwah ta riqo shi dan yau ta d’au ma kanta alqawari komai zai faru sai dai ya faru saboda ta gaji she can’t take it, she just can’t take it anymore. 
Kallon ta Suwayd ya tsaya yi da mamaki dan abinda bata tab’ayi ba kenan, daure zuciyan ta tayi ta masa narrating all that happen amma ina Sam Suwayd yaqi yarda wai dole sai *Inayah* ta rama marin ta, Safwah kuwa tace indai haka ne wallahi sai dai subar musu gidan, hakan ce ko ta faru tsayin zaman su bata tab’a yaji ba sai a ranan, data je gida kuwa kowa bayan ta yabi dan sun soma jin tsoron irin gatan da yake mata. 
  Sati d’aya babu Suwayd ba labarin sa go gaishe da Granny da yake zuwa yaqi dan ma karya ganta a ganin sa inta gaji da zaman gidan ta dawo tunda bai mata komai, Inda yaji dad’i ma an riga an yaye *Inayah*. 
Yau tsayin sati biyu kenan dan haka Abbah ya qira sa a waya inya tashi a aiki ya biyo gida, yau tunda Granny ta tashi batajin dad’i amma tana b’oyewa suna zaune da Little Safwan yana ta mata hira jikin ya rikice, hankali a tashe ya shiga jera mata sannu kafin yai cikin gida da sauri ya qira Abuh da baije aiki ba ranan, without hesitation suka d’auke ta akai asibiti. 
     Nan take aka karb’e ta aka bata duk taimakon daya dace, Suwayd dake can yana Cs sam baisan meme faruwa ba yana fitowa idanun sa basu sauka kan kowa ba sai *Flower* d’insa, ba qarya he really misses her but meya kawo ta Asibitin bai gama tunanin ba yaji muryan su Haifar na tambayan me jiki, qarasowa yayi da sauri yana tambaya ai tanajin muryan sa tabar masa gurin hakan kuma ba qaramin qona masa rai yai ba, a bakin su Haidar yakeji Granny ce babu lafiya, d’akin hutu da aka kaita yaje ya dubata ya sake tabbatar da tana cikin qoshin lafiya sannan ya dawo cikin dangin sa, nan ya tarar da Dr Alkasim na musu tsiya su shikenan dan Allah yayi su da yawa in d’aya yana cuta sai sun cika ma mutane asibiti, su kam banda dariya babu abinda suke.
A daren ranan aka sallame su duka suka wuce gida saboda tana son magana dasu, tuni Ammey ma ta qara so dan tunda Abun ya qira ta hankalin ta ya kasa kwanciya, suna zaune gaba d’aya ‘ya’ya da jikoki harda tattab’a kunnen ta sai qare musu kallo take har idon ta ya sauka akan gold in Suwayd dake maqale ajikin sa showing the whole world that he is her Dada. 
   Murmushi tayi ta miqa mata hannu aikuwa ta taso da sauri dan dama tana son Granny in Dadan ta, zama tayi a cinyan Granny’n tana wasa da kyawawan yan yatsun ta, rad’a Granny ta mata a kunnen hakan yasa ta yin dariya ta sauko ahankali ta tafi gurin da Safwah ke zaune murya qasa_qasa kaman ana busa sarewa tace “Ammah! Ya Safwan!  please come back home i and Dada miss you alot it will not happen again”. 
   Ko kallo bata isa Safwah dan dama tasan pride and ego bazai tab’a bari tayi apologizing musu ba sandai tace it won’t happen again dole ta tashi tsaye akan yarinyar nan, Inda Allah ya taimake ta Dadan nata ma inta masa laifi bata cewa Sorry sai dai it won’t happen again. 
Ganin sunqi kulata ta durqusa har qasa in  a Baby like manner tace “Ammah please i promise”. 
  Ganin za tayi kuka yasa Safwan kallan Ammah’n tasu in calming tone yace “Ammah she is sorry please “. 
       Hankalin Safwan na burge kowa murmushi tayi ta kalle sa not minding taking glance at *Inayah* tace “is okay Ammah’s prince God bless you each day!”
“Amin Habibty” ya ansa cike dajin dad’in addu’ar Mahaifiyar tasa. 
    Wani bala’in kishi ne ya danne inaya amma ta moze ta miqe ta koma gun Dadan ta, tun kan ta qaraso ya karanci yanayin ta amma ganin basu kad’ai ne a gurin ba yasa yai hugging ta yana shafa kanta. 
Nasiha sosai Granny ta musu a daren nan wadda kowa yakejin ta kaman bankwana a lokacin tasa Suwayd ya bawa Safwah haquri sanda ta tabbatar komai ya zama dai_dai sannan tai freeing kowa ya tafi, Mammy kuma tace gobe Suwayd in yazo ya d’au Safwah. 
    A Cikin wannan dare mai albarka Allah ya karb’a ran Hajiya Ruqayya wadda jikokin ta ke qira Granny, mutuwar data matuqar gigita dangin dama mutane da dama saboda tsananin kirkin ta, labarin na zuwar wa Suwayd ya fad’i dan shine yayi rashi kowa ma shi yake tausayawa dan yadda ya taso ba abokin shawara, hira, wasa sai ita, ita kad’ai dai gashi Allah ya karb’a abar sa.
Wasiyyar data barma Ammey yasa Suwayd ne ya wanke gawarta ya suturta aka sallace ta aka kaita gidan ta na gaskiya, dagaske Suwayd ya kwanta ciwo dan babu shima ake karb’ar gaisuwa yana asibiti. 
Haka nan aka share makoki har ranan sarakan bakwai kowa ya tafi, har lokacin kuma Suwayd na asibiti kullum Abuh sai yazo ya kwantar masa da hankali amma inah, ga kuka da yake so yayi ko yaji sauqin abinda yakeji amma babu hali, *In ayah* ita kadai yake kalla yad’anji sanyi aransa har tsayin wata d’aya komai nasa ya tsaya chak babu farin ciki atare dashi hakan ya soma d’aga hankalin iyayen nasa. 
     Ranar sarakar arba’in ya samu qarb’an gaisuwa kowa nata jin tausayin sa dan yadda ya rame, da dare suka koma gida su Zee nata qoqarin faranta masa amma a banza, d’akin sa ma ya tafi ya kyale su. 
Kallon Zee Safwah tayi tace “Mummy’n yara kije gurin sa “. 
    Murmushi qarfin hali tayi tace “ke ya kamata kije “. 
    Kafin ta bata ansa *Inayah* ta fito da gudu cike da tashin hankali dan bata tab’a ganin Dadan ta ahaka ba ta riqo hannun Safwah, “Ammah kizo muje”. 
Kallon Zee tayi ta gyad’a mata kai meaning Yes, miqewa tayi hannun ta riqe dana *Inayah* d’in suka shiga d’akin, yana can zaune a gefe yana kuka helplessly, kallonta ta mayar kan *Inayah* tace “Princess go to Ya Safwan kinji! ” 
     Gyad’a kai tayi cike da tsoro tace “Ammah take care of him” sannan ta fita. 
Maida qofan tayi ta rufe ta qarasa Inda yake ta d’ago sa cike da rauni, bai bari sun had’a ido ba kawai ya fad’a jikin ta ya qanqame ta yana kuka sosai, jiki a sanyaye take shafa bayan sa tana calming sa harta samu yayi shiru taje ta had’a masa ruwan wanka, a tare sukayi wankan suka fito suka shirya suka kwanta, sai da ta samu yai bacci taje ta d’au *Inayah* ta mayar da ita d’akin ta sannan ta dawo gunsa. 
    Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yanzu *Inayah* nada shekara biyar a duniya babu abinda ya ragu a halayen ta saima qaruwa da suke dan ma Safwah nacin ubanta idan Dada baya nan, har kuma lokacin bata samu wani cikin ba. 
Yau ya Kama Thursday Safwah zata fita da yaran shopping cause babu islamiyyah, *Inayah* ce a gaba sai Little Safwan da Safwah da suka girma a baya, shopping sukai sosai suka fito Safwah na qoqarin shiga mota taji sallama, ahankali ta d’ago only to find the biggest surprise of her life. 
    “Imran! ” ta fad’a cike da qin yarda. 
“Na am Safwah” ya ansa yana dariya. 
Murmushi tayi ta gaishe sa ganin haka Little Safwan da Safwah ma suka gaishe sa yayin da *Inayah* ko kallo bai ishe ta ba, sai alama Safwan ke mata da ido amma ina mota ma ta shige ta bugo qofan, Allah sarki Safwah sosai taji kunyan abinda yarinyar tayi, lura da hakan da yai yasa ya musu sallama ya tafi bayan ya karb’i digits inta. 
   Tun amota Safwah ke mata fad’a kaman zata dake ta hakan ya qara fusata tata, suna zuwa gida ko kayan ta bata d’iba ba tai shigewar ta nan ta iske Dada a falour yana kallo, kusa dashi ta qaraso ta zauna rai a had’e dama yasan za’a rina shisa yafi so ya kaita shopping dakansa. 
“Mamana! ” yai stating.
Na am! “Ta ansa tana tura baki. 
“What’s wrong? “
   “Ba Ammah bace dan ban gaida wani data kula ba tamin fad’a😭” ta qarasa tana hawayen munafin ci. 
“Wani kuma? “
    “Yes Dada gata nan ka tambaye ta kuma har digits inta ta bashi😩”. 
Kallon Safwah yai with questioning expression cike da bak’in kishi yai rising mata eyebrow meaning is it true, kallon Safwan da Safwah tayi tace ku wuce ciki sannan ta kalle sa. 
    “Eh Habibi gaskiya ne amma…. “
“Shut up! Amma me? Dama abinda kikeyi kenan da aure na akanki kike bana wasu numbers inki…. ”  bai qarasa ba wayan ta ya soma ringing. 
Ganin sunan dake flashing kan screen in yasa gaban ta fad’uwa, “bazaki iya d’agawa ba ko?”
  Shiru tayi tana hawaye ya fuzge wayar ya d’auka abinda kunnen sa ya soma ji shine ” dafatan dai gimbiyar taje gida lafiya? “
         Buga wayar yai a tiles ya mik’e riqe da hannun *Inayah* zuciyarsa na tafasa zasu wuce “Amirul Qalb please let me explain…. ” dirty slap in daya kashe ta dashi yasa ta yin shiru batare data shirya ba, ita kanta *Inayah* sanda ta tsorata. 
Da gudu tayi d’akin ta tafad’a kan gado tana kuka abin tausayi wani irin ciwon mara ya tasar mata, ahaka Zee tazo ta same ta kafin ta kaita asibiti tuni ta soma bleeding suna zuwa asibiti aka tabbatar da zubewar cikin jikin ta, Dr Alkasim yayi_yayi dashi yazo amma yaqi hakan yasa Zee zuwa gida d’ibo kaya ta dawo nan kuma ta tarar da tashin hankali dan yayi rantsuwa inhar ta koma asibitin abakin auren ta. 
    Kwanan Safwahn biyu nurses na kula da ita aka sallame ta, gashi dai kullum yana zuwa asibitin amma ko nakan ta baiyi ba, badan tayi alqawari tagama yaji a gidan sa ba tun a wancan karon da babu abinda zai maida ta gidan sa. 
Koda ta koma gidan d’auke musu qafa tayi daga *Inayah* har Suwayd in babu mai ganin walwalarta. 
   Sati biyu kenan da faruwar lamarin yau Abdul da Musty suka kawo musu ziyara, gaisawa akayi sosai anata hira amma tuni Abdul ya fahimci akwai matsala tsakanin Suwayd da Safwahn saida suka tafi masallaci sannan yake tambayar sa, nan ya kwashe duk abinda ya faru ya fad’a masa mamaki sosai Abdul ya shigayi kafin ya rufe shi da fad’a akan bincike da bayayi sai yanke hukunci, sannan kuma yace in bai nemi sulhu da matarsa ba dakansa zaije ya fad’awa Abbah. 
Daren ranan bayan su Abdul sun tafi yaje d’akin Zee ya mata saida safe as always saida suka gama kissing junan su sannan ya d’aga rigan ta yai packing inta yace ” ki kularmin da ajiya ta”. 
   Murmushi tayi tace cike da qaunar sa tace  “insha Allah Rania “. 
Kashe mata haske yayi sannan ya wuce d’akin Little Safwah ya gyara mata kwanciya ya mata addu’a ya wuce d’akin Safwan, the same thing yama Little Safwah haka shima ya masa sannan ya wuce d’akin *Inayah* ya dad’e yana kallon ta yana mata addu ‘a kafin ya wuce gurin *PureLamp* zata shiga wanka kenan ya shigo dan haka yai joining ta suka shiga, tare suka fito ya taya ta shirya wa though ko kallon sa taqiyi.
Nafila ta gabatar sannan ta nemi guri abinta ta kwanta, ahankali ya haura gadon ya janyo ta jikin sa ya qanqame cikin rad’a yace “Haba *Flower* ba dai fushi kike dani ba? ” yanda yai maganan sanda yasa tsigan jikin ta tashi, ture sa ta somayi amma ina, haquri ya bata sosai nan ta masa explaining du abinda ya faru, duk sai kunya ta kamasa gaskiya ya kamata yana bari ana tsawatarwa *Inayah*. 
    “Am Sorry *PureLamp insha Allah daga yau haka bazai sake faruwa ba”. 
“Allah yasa” ta ansa blankly. 
    “Haba mana *Zawajah* am serious “
“Okay let’s Sleep”
“No Rabba’atul bait qanwa ko qani zanwa *Inayah* may be ta rage abinda take “. 
   Dariya ma abun ya bata tace ” Ai the best solution shine in tayi rashin hankalin ka doke ta”. 
Shiru yayi kamar me tunani sannan yace ”  an gama LOML❤😘, I love you “. 
    “I Love you more HOMD❤😘”. 
Jan bargo yayi ya lullub’e su yace ” *Flower* ya kamata in bada himma yau in aje twins”. 
    “Stop it’s embarrassing you know! “. 
Dariya yayi yace ” ka tashi ka tafi bana son ganin ka, kuma sai Allah ya sakamin mugu kawai….”
     “Habibi please mana!” Tayi stating bashful yayin da shikuma yake ta mata dariya………. +

_Happily Ever After_

*ALHAMDULILLAH!!!*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *