SOYAYYAH
CHAPTER 7
” Idan ka kuskura hannun ka ya tab’a fuskansa believe me tsinuwa na ya tabbata akan ka”
ya tsinkayi voice ta Mummy sounding damn serious.
Chak ya tsaya batare da yayi wata k’wak’k’waran motsi ba, ahankali ya sauke hannun heart
nasa na burning wane zatayi busting k’irjin sa ta fito.
Juyawa yayi ya nufa kan Safiyya dake kwance cikin mawuyacin hali ya janyo ta jikin sa ya
rungume k’amk’am wane za’a kwace mar ita, alokaci guda wani irin mugun so tausayi da
k’aunar ta suka shige sa, zai iya jurar komai amma banda tab’a mutuncin matar sa da
lokaci d’aya yake ganin future tasa a tare da ita.
Salati Mummy ta shiga jerawa tana tafa hannu, hakan ce ta dawo dashi reality daga zancen
zucin da yake.
Muryan Ibrahim ya jiyo ” Mummy dan Allah ki bani dama na b’ab’b’alla wannan kilakin
yanda zata gwammaci yin zina da ubanta bada k’anina ba “
Runtse idanu sukayi both zuciyan su na tsananin k’una, an raba shi da ‘yar uwar sa da
yake k’auna da wannan kalmar dan haka ba zai yadda hakan ta faru dashi ba a karo na biyu
dole he has to do something koda kuwa barata yiwa kowa dad’i ba.
” Karka kuskura ka sake kiran ta kilaki idan ba haka ba anything might happen, when I said
anything I mean har kisan kai ” Sufyan yayi maganan da wata lion voice wadda har ita
kanta Safiyyan dake jikin sa sai da ta razana ta sake k’ank’ame sa, ga wani irin zugi da
rad’ad’in da zuciyan ta take game da abinda lbrahim ya fad’a zata iya jure komai amma
banda wulak’anta mata iyaye da “K’ADDARAH” ta rabasu just one day sam_sam barata iya
jurewa ba .
” Lallai Sufyan ka girma, idan bai k’irata karuwa ba uwarka kake so yace? Nace uwarka kake
so yace answer me? “
Enough Mum!! da wannan kalman kuka ruguza duk wani farin ciki na dana ‘yar uwata
har kukayi sanadiyan data shiga duniya ta barni, dan hakan bazan tab’a yarda hakanta
sake faruwa ba, idan gidan ne yanzu zamu bar muku dama ina zaune cikin sa ne dan babu
yadda zanyi, amma duk wanda yayi k’ok’arin tab’a mata ta wallahi I won’t spare him”
” Mata!! ” Mummy da lbrahim sukayi ex claiming cike da k’in yarda, anya bayan neman
matan da ya jefa rayuwan sa ciki bai soma shaye_shaye ba, he has totally change into
something different tin bayan incident d’in da ta faru, the cool, handsome gentle Sufyan
has now turn to harsh, arrogant heart hearted and insolent .
“Yes i really mean what i said, idan kuma akwai wanda yake da ja akan hakan gata nan sai
ya tambaye ta ” muryan sa ta tsamo su daga duniyan tunanin da suka lula.
Tsoro ne ya lillib’e ta ganin yana k’ok’arin mik’ar da ita, hijab nata ya janyo mata ya sa mata
sannan ya mik’e tsaye ya mik’ar da ita, hannun su ya had’e guri d’aya not letting go sannan
ya jata har zuwa gaban Mummy dake tsaye wane an dasa ta.
” Mummy ga Safiyya mata ta ki sa mata albarka ” sannan ya juyo ya kalli Safiyya data rintse
ido saboda tsananin tashin hankali yace ” Safiyya Sweetheart here is my Mum, meet your
in law ” da sauri ta d’ago jin sunan daya kirata da shi, shikam yayi kaman bai ma san tanayi
ba.
Saukan maruka kawai Sufyan yaji, da sauri Mummy ta kai kallon ta kan Daddy da Nasir da
suka shigo yanzu, makirin murmushi Sufyan ya sake yace ” well come Dad, Safiyya meet
my Dad ” sannan ya d’ago ya kalla Daddy cikin ido without any fear or sorrow yace ” Dad
here is Safiyya your in law ka sa mata albarka “
Fusgo shi Nasir yayi cikin tsananin bak’in ciki ya bashi kyakkyawan punch a fuska, tuni
nose tasa ta soma bleeding amma ya daure ya saki murmushi yace ” Big bro ga mata ta nan
” numfashi yaja cike da azaba yace ” Safiyya ga Babban Yaya na nan say hello”.
Jijigasa Nasir yayi ya k’ara masa wani punch d’in ” You bloody idiot bastard just come back
to your normal sense
Cike da rainin hankali ya shigà nanata masa abinda ya fad’a sannan ya kalli Ibrahim ma
yace ” Ya lbrahim ga mata ta nan da ka kusa hallakawa Allah ya tsare da sai na d’au mataki,
Darling Safiyya I know you hate him but please at least say hal.
“
Bai rufe baki ba wasu punch d’in suka sauka a fuskan sa, nan take fuskansa yayi moisture
amma kuma still bakin sa tak’i rufuwa, punch kam ya sha ta dan both Nasir da lbrahim
suka had’u idan wannan ya daka ya cilla wa wannan, Safiyya kam na gefe tana wata irin
masifaffiyar kuka duk ta dalilin ta hakan ke faruwa gashi ta rasa meye ne zatayi ta tai make
sa.
Sai da ya fita daga hayyacin sa suka yasar a k’asa, kansa tayi muryan Daddy yayi saurin
tsaida ta.
” Idan kika kuskura wannan k’azaman hannayen ki suka tab’a sa wallahi saina yanke su
with my bare hands, and I won’t rest sai na koya miki lesson d’in da duk wata karuwa ‘yar
uwarki tagani baza ta sake gangancin shiga rayuwar family na ba, karki d’au wai b’atamin
yaron da ki kayi zai tashi a banza I will make sure uwarki da ubanki sun haifi wata”
Wayan sa ya ciro ya shiga dialing wani number, not long enough aka d’auka ” Dpo ka
turomin mans naka right away ” bai ko bari an answer sa ba yayi hanging.
Duk addu’an daya zo bakin Safiyya yinsa take ga mutuwa dai ba’a sonta amma yau kanta
take wa fata.
lya b’acin rai kam ya chusa musu both musamman Nasir da lbrahim gashi dai su suke
dukan sa amma zafin da sukeji a zuciyan su yake ya linka nasa.
Dakyar Sufyan ya samu ya mik’e yana tangad’i kaman d’an kwaya ya nufi Safiyya, hannun
ta ya rik’o cike da azaban ciwon kan da ya addabesa yayi hanyan barin d’akin da ita,
bakomai ne ya sanya sa yi musu haka ba sai dan ya k’ona musu zuciya suma suji yadda
yake ji na raba sa da “‘yar uwarsa da sukayi kuma suke zaune happily batare da wani
damuwa ba.
K’afa Nasir yasa masa ya fad’i kansa yayi wani mugun buguwa da tails daga nan kuma bai
sake sanin inda kansa yake ba, wata iriyar k’ara ta sake lbrahim ya wawwanke ta da marin
da saida ta kifa.
Bata gama hucewa daga zafin marin ba ta soma jiyo jiniya, kan Sufyan ta fad’a tana ta kuka
tana jijigasa, ” Sufyan dan Allah ka tashi ka tai make ni bani da kowa sai kai, Sufyan zasu
hukunta ni ba da laifi na ba, na rok’e ka dan girman Allah karka tafi ka barni, na rok’e ka
katashi ka musu bayanin k’addararren auren mu… “kuka take sosai kaman ranta zai fita.
Tausayin ta ne ya kama Mummy ta bud’e baki zatayi magana Daddy yayi saurin d’aga mata
hannu, kallon polisawan da suka shigo yayi yace ” gata nan ku tafi da ita ku gana mata
azaban da zaisa taji inama uwarta da ubanta basu kawo ta duniya ba “
“Yes sir ” sukayi saluting nasa sannan suka janye ta da k’arfin tsiya tana ihu tana komai ga
babban abin takaicin towel da hijab ne kawai ajikin ta.
Suna isa inda sukayi parking motan su Malam na shigowa idan sa bai sauka akan kowa ba
sai Safilyya” Safiyyal! ” yayi ex claiming not believing what his eyes are seeing.
Jin muryan Malam yasa wani sanyin dad’i kamata finally Allah ya amsa addu’an ta ya kawo
mata mai ceton ta, wani irin k’arfi ne ya zo mata ta kwace kanta ta gudu bayan Malam ta
b’oye.
Kanta ‘yan sandan sukayi da sauri amma tsabar kwarjinin da Malam yayi musu sun kasa
aikata komai.
Daddy da idon sa ya rufe da masifa ne ya k’araso yace” uban me kuke jira baku fitar da ‘yar
iskar yarinyar nan daga gidan nan ba?”
“Ba ‘yar iska bace ” ya jiyo muryan Malam the voice seems familiar da wata wadda ya sani
dan haka yayi saurin d’agowa.
Totally out of word ya tsaya kallon Malam sannan cike da girmamawa ya durk’usa yana
gaishe sa, amma sam Malam bai amsa ba dan yadda yaga halin da ya tarar da Safiyya a
wannan gida mai albarka.
Juyawa yayi ahankali ya kalle ta yace ” ina mijin naki ake wulak’anta ki haka?”
In crying tone tace ” sun kashe shi”
“Subhanallahi kinko san mai kike fad’a Safiyatu? ” yayi questioning nata.
Gyad’a masa kanta tayi tana sake fashewa da matsanancin kuka.
” Ina yake? ” hanyan part d’in Sufyan ta masa pointing yasa ta agaba suka tafi.
Daddy kam ya kasa d’agowa daga tsugunan da yake kalman ina mijin naki yake na ta masa
yawo aka.
Sosai hankalin Malam ya tashi da yaga yadda Sufyan yake, kallon ta yayi yace taje ta sanya
kaya tazo su tafi, bata dad’e ba ta fito Malam ya sab’a Sufyan a kafad’an sa suka tafi.
AKTH suka wuce kai tsaye akayi emergency room da Sufyan, suna zaune Daddy, Mummy,
Nasir da lbrahim suka iso dan suna neman k’arin bayani daga bakin Malam har zuwa
lokacin kuma Daddy ya kasa koda had’a ido da Malam saboda kunya.
Hour biyu Doctors d’in suka kwashe aciki sannan suka fito, Safiyya da Malam ne sukayi
saurin nufan su sana tambayan ya jikin, gani fuskar sa d’auke da kyakkyawan murmushi
suka sauke ajiyan zuciya a tare sannan in brief ya musu bayani ya wuce office tasa.
Bayan minti sha biyar wata Nurse ta nufo inda suke, ” wace Safiyya? ” tayi questioning nasu
both.
Da sauri Safiyya dake takure a gefe ta mik’e, ” patient d’in na son ganin ki ” kawai tace da
su ta wuce.
Tare da Malam suka nufa d’akin hutun da aka maida sa, yana kwance an nad’e kansa da
bandage sai drip da aka sanya masa.
Malam ya soma gani dan haka ya sauke wata kyakkyawan ajiyan zuciya dan yasan finally
Allah ne ya turo sa dan ya ceci Safiyya.
Malam na k’arasowa bakin gadon Sufyan yayi saurin rik’o hannun sa yace ” Malam kaje ka
taimake ta karsu cutar da marainiyar Allah, dan Allah kayi sauri “.
” Kwantar da hankali ka Sufyan gata a tare dani safely”, sa lokacin yakai duban sa gefen
Malam ya ganta, hamdala yayi ganin babu abinda ya same ta.
Shigowar su Daddy ta sanya sa runtse idanun sa dan sam baya k’aunar ganin ko d’aya daga
cikin su.
Sai da suka k’araso suka zauna sannan Malam yayi clearing duk wata doubt, na sosai ya
yiwa Daddy fad’a kan yake hukunci ba bincike, nadaman da bata da amfani Daddy ya soma
yi da dana sanin abinda ya yiwa Sadiya, gashi babban tashin hankalin sa bata wuce cewa
da Sufyan yayi ba ta shiga duniya ta barsa.
Kallon Safiyya Mummy dake hawaye tayi tace” zo ‘yata “jiki a sanyaye ta nufi Mummy’n
tana k’ok’arin tsugunawa tayi saurin tarota ta rungume ta aijikin ta.
Sunan mahaifin Safiyya Malam ya fad’a nan take Daddy ya d’ago a firgice yana nanata
sunan.
” Sufy’n Abbah ” ya fad’a da rawan murya.
Duk duniya abokin Abbah’n ta d’aya ne ke kiran ta da sunan dan haka ta daure itama ta
ansa sa da yadda suka saba.
” Na’am Daddy’n Twins”
“Kece wallahi kece ” ya fad’a hankali a tashe sannan ya k’araso yayi kneeling a gaban ta “
forgive me daughter i was so stupid to be harsh on you, dan Allah Sufy’n Abbah ki yafe min
Tsugunawa tayi itama tana kukan da kowa ya kasa gane na farin ciki ne ko akasin hakan
tace ” Daddy dan Allah ka tashi wallahi na yafe maka nasan zuciya ya sanya kayi hakan da
lokacin ka gane nice nasan hakan bazata faru ba”
Share mata hawayen ya shigayi cikin tsananin tausayin ta sannan ya mik’ar da ita ya nufa
jikin gadon ya had’a hannun ta dana Sufyan yayi blessing auren nasu.
Malam yasha kyauta da godiya dan dama mutumin Daddy ne, Safiyya kuma ita aka bari
tare da Sufyan tayi jinyan sa, Ibrahim kuma yaje gida ya kawo musu kayan da zasu buk’ata.
Kowa ya nemi yafiyarta ta kuma yafe masa illah Sufyan da ko magana yak’iyi musu.
Daddy na koma wa gida yasa aka bud’e babban part d’in da suke gefe, yasa aka soma gyara
babban ciki.
Kud’i sosai ya bawa Mummy ta siyawa Safiyya duk wani abinda uba ya dace yama d’iyar sa
in tayi aure, kafin sati d’aya komai ya had’u perfectly fine sai jiran tarewar masu shi.
Alokacin aka sallami Sufyan dan haka Safiyya ta koma part d’in Mummy ta soma gyarata.
Sufyan Daddy ya kira ya masa maganan events ta biki amma sam yace baya so dan haka ya
hak’ura, duk k’ok’arin Nasir da lbrahim najan Sufyan ajiki su koma kaman yadda suke da
ya k’iya dan dole suka bashi space ya gama hucewa.
Mummy kawai ya sakewa suka koma like before itama dan yasha kamata ne a garden tasa
hotunan Sadiya agaba tana kuka yasa.
Bayan wata d’aya ya tare da amaryar sa inda suke rayuwar su gwanin sha’awa, Daddy har
cigiyan Sadiya ya bada amma shiru ba labarin ta, haka damuwa ta shiga cin sa har ciwon
zuciya ya kamasa wanda yak’i bari kowa ya sani daga shi sai Allah sai doctor’n sa.
Watan su Sufyan biyu Safriyya ta samu ciki kula ba kalan wanda bata gani a cikin gidan har
yakai wata tara ta haifa kyakkyawan d’an ta ranar suna aka sanya masa Abubakar suke
k’iran sa Sadeeyq.
Duk yadda Sufyan yaso Sadiya tazo tak’i dole ya hak’ura, amma kam tayi bajin ta dan sosai
ta turowa Baby kaya.
Sadeeyq nada shekara l ta sake samun wani cikin inda hankalin ta ya tashi sosai ta damu
Sufyan sai an cire dan tasha wahala kaman zata mutu a ai’uwan Sadeeyq.
Kwantar mata da hankali yayi tayi harya samu ta cire tsoron in 9 month time ta sake
ai’uwan namiji aka Sanya masa Farouq suke k’iran sa Omar.
Har lokacin kuma Nasir da lbrahim basuyi aure ba amma Sufyan ya sauko sun dai_dai ta
ganin an soma tara ‘ya’ya.
Shirye shiryen auren Sadiya Sufyan yake ba kama hannun yaro dan tuni ita da Khaleepha
sun dai_dai ta.
Lokacin kuma Omar nada shekara 1 har Mummy’n sa ta sake samun ciki duk yadda taso
wannan karan Sufyan ya yarda su cire yak’i dole ta hak’ura ta mik’awa Allah lamuran ta.
Wata biyu nayi Sufyan ya wuce Saudi Arabia bikin gudan jinin sa, komai yayi dai_dai sai dai
amarya data gaza walwala ganin duk inda ta kalla dangin mijin ta ne, her only family is
Sufyan haka dai har aka gama komai, Sufyan yayi wakilcin d’aurin auren ta duk abinda
akewa d’iya idan tayi aure saida yayi mata.
Duk yadda Khaleepha yaso hanasa k’i yayi dole ya hak’ura ya zuba masa ido, washe garin
d’aurin aure ya dawo Nigeria.
Watan sa biyu da dawo wa Safiyya ta sake ai’huwa still namiji aka sanya masa Uthman.
Uthman nada six months Nasir da Ibrahim sukayi aure har kuma lokacin Sadiya bata samu
ciki ba hakan yasa ta soma damun Sufyan shikuma yana kwantar mata da hankali.
Watan su hud’u da aure matar Ibrahim ta samu ciki, lokacin kuma Uthman nada 1 year
tuhumar Safiyya Sufyan ya somayi ganin bata samu wani cikin ba inda ta shaida masa ita
dai batayi komai ba.
Wata tara matar lbrahim ta haifi kyakkyawar ‘yar ta ranar suna aka sanya mata Fatima suke
k’iran ta zara, farin ciki gurin su Sadeeyq ba’a magana kullum yana mak’ale da ita ko
makaranta yaje ya dawo saiya soma zuwa ya ganta sannan zai wuce part d’in su.
Na sosai matar Nasir ta shiga damuwa da rashin samun cikin ta ganin tare aka kawo su
gata ko b’ari bata tab’a yi ba, haka ma b’angaren Sadiya duk tabi ta d’aga hankalin ta.
Sufyan ma saida suka haura da Safiyya danya dage wani abin tayi shiyasa tak’i samun wani
cikin ta yiwa Uthman k’ani
Yaji ya mata har saida Mummy ta fuskanta ta sulhun ta su, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya.
Yanzu Baby Zara nada 1% years abin kaman had’in baki su duka suka samu ciki Safiyya,
Maryam d’in Nasir da Ummuhanin lbrahim har ma da Sadiya, fad’in irin farin cikin da
Sufyan yayi b’ata baki ne dan har dubo ta yaje yayi.
In nine months time duk suka haifa kyawawan zaratan yan maza, Maryam ce ta fara
haihuwa kwanan ta biyu Ummuhani ma ta haihu sai Sadiya itama tskanin ta dasu just three
days, Safiyya kuma itace last.
Ranar suna d’an Maryam yaci Muhammad sunan Daddy suke k’iran sa da Suwayd,
Ummuhani kuma yaci Nasir akayiwa babban Yaya takwara suke k’iran sa da Sayyid na
Sadiya ku Sufyan aka sanya masa suke k’iran sa Arif sai Safiyya ita kuma Aliyu suke k’iran sa
Haidar, a tare aka had’e suna akayi yayin da kowa yake mamakin barin k’asar da Sufyan
yayi ana saura kwana biyu suna.
Shikam yana can da ‘yar uwarsa buduri sosai akayi na sunan d’an ta sannan ya had’a kit
uku na barkan takwaran sa, bayan suna ya dawo ya tarar da gimbiyar tasa na fishi ya samu
ya rarrashe ta dakyar.
Ciwon Grandpa kaman yanda yaran suke k’iran sa kullum gaba yake, sosai damuwa da
tunani ke k’ara tsanan ta ciwon nasa amma sam ya kasa denawa he just can’t forgive him
self dangane da abinda yayi wa tilon ‘yar sa, kuma har lokacin babu wanda yasan halin da
yake ciki Hajiya Ruk’ayya tasha kamasa yana tunani amma amsar tambayan ta kullum
itace shi ba tunani yake ba.
At Aisha and Lubabatu’s side ‘yan iska suka zama na tashin hankali, ita Aishan ma hartayi
joining wani hatsabibin team na karuwai.
Yau itace da wannan Alhajin gobe wancan, yau tana wannan k’asar gobe tana waccan haka
dai ta koma rayuwa wane tinkiya uwar tunb’ele, tuni iyayen ta suka sallama ta hakan kuma
ya k’ara bata lasisin cin duniyan ta da tsinke, yanzu duk burin ta bai wuce janyo Lubabatu
cikin team tasu ba dan tayi promising wa kanta tunda ta rasa budurcin ta sai tayi duk
yanda tayi tasa itama ta rasa natan.
Lubabatu kam sam tak’i yarda da wannan Harkan nasu Aishan ita kawai chilling tasa a
gaba amma ganin yanda Aishan ke kama ‘ya ‘yan banki yasa kwad’ayi, hassada da bak’in
ciki suka soma rufe mata ido, Aishan ta fad’a mawa inda ita kuma ta mugun jin dad’in
hakan dan haka batare da b’ata lokaci ba tayi magana da leaders nasu, jin cewa Lubabatun
virgin ce ya sa sukayi saurin accepting nata dan akwai wani Alhaji da ya bada kwangilar
20mil kawai dan a samo masa virgin.
Nan take kuwa aka had’a ta da Alhajin, ranar daya fafeta taci wuya amma kuma tasha
kyautan da ko a mafarki bata tab’a tunanin samu ba, tun daga nan ya miyar da ita kaman
matar sa kasantuwar baya da aure, duk inda za sa yana mak’ale da ita dan ya hanata huld’a
da kowa sai shi, itama dake ta riga ta saba dashi yasa bata da lokacin kowa sai shi.
Shekaran su biyu da Alhajin ta soma samun changes ajikin ta dan haka ta nufa asibiti dan
tana tunanin ko ciki ne da ita gashi kuma Alhaji yace mata har abada ita da samun ciki, dan
haka ta nufi asibitin dan bazata jure haifan shege ba.
Koda ta samu Doctor sosai ya kad’u dajin symptoms d’in da take zayyano masa amma ita
ta dage in ciki ne ya zubar mata bata so, blood test yasa aka yo mata inda nan take result ta
nuna HIV AIDS.
Tausayin tane ya kamasa dan shi duk tunanin sa ko mijin tane ya shafa mata, ko da ya
sanar mata k’in yarda tai saida taita zuwa asibiti daban_daban ana bata same answers
sannan ta yarda taci kuka kaman ba gobe yayin da sukayi baran_baran da Alhaji dan har
mahaifanta yasa aka cire bata sani, duk yanda yaso ta zauna ya cigaba dayi mata magani
kaman yanda yake ma kansa ta k’iya dole ya kyaleta.
Ita kam lasan takobin yak’i tayi dan tace barata tab’a yarda ta zauna da ita ita kad’ai ba,
haka duk saida tabi team members nasu tayi injecting.
Aisha najin symptoms ta nufa asibiti inda Doctor ya tabbatar mata da tanad’auke da cuta
mai karya garkuwan jiki, kai tsaye Rocky ta tunkara wai shi ya shafa mata aikam ya mata
dukan tsiya ya tattare duk abinda ta mallaka ya ware ya samu nayiwa kansa magani.
Saida tayi kwana biyu sannan ta samu wata daga cikin members d’in ta kaita asibiti ta ware
abin ta dan suma yanzu duk sun Kama magani, tana cikin mawuyacin hali Lubabatu tazo
inda ta mata narrating all that happened tayi tafiyar ta tabarta, kud’in da aka biya mata na
k’arewa aka kore ta daga asibitin.
Gidan su ta nufa inda sukayi mata koran kare dan sosai ta wulak’anta su lokacin da duniya
keyi da ita.
Lubabatu ma har gida Alhaji ya turo yaran sa ‘yan fashi suka yashe ta dan dama cikakken
d’an fashi da makami ne.
Gaba d’aya rayuwan su ya shiga garari har sun soma bara a bakin titi, wata rana sunje
karb’an magani da ake rabawa a asibiti na kyauta suka had’e.
Rungumarjuna sukayi kowa tana neman ya fiyar kowa sannan suka yanke shawaran zuwa
neman yafiyan iyayen Sadiya dan Alhakin ta dana iyayen ta ke bibiyar su.
Ranar ya kama 6h da faruwan komai Daddy na d’akin sa yana ta aman jini dan zuwa
lokacin ciwon ya gama cinye sa Hajiya Ruk’ayya ta shigo, hankalin ta yayi matuk’ar tashi
inda ta nemi su tafi asibiti amma sam yak’i, na dole ta kira ‘ya’yan ta tafad’a musu halin da
ake ciki.
A ranar kuma Aisha da Lubabatu suka iso inda suka samu dakyar baba mai gadi ya barsu
suka shigo dan yadda suka mugun basa tsoro, in har mai karatu zai gansu alokacin na
tabbatar bazai iya cin abinci ba.
Yar aiki suka samu a falour’n inda suka samu ta k’ira musu Daddy da Mummy already
dama su Nasir duk sun iso dan haka duk suka had’u a falour’n.
Aisha da Lubabatu na kuka suka fayyace musu duk abinda ya faru sai ji kawai sukai Daddy
ya fad’i, Sufyan da Nasir ne sukayi saurin d’aukar sa suka wuce asibiti yayin da lbrahim
kuma ya zauna dan kar su gudu ya kira polisawa sukayi gaba da k’eyar ‘yan iska.
Emergency ward aka nufa da Daddy’n amma duk iya k’ok’arin likitocin sun kasa komai
dole suka barwa Allah ikon sa, Sufyan daya kasa hak’uri danna kansa kawai yayi duk yadda
aka so ya fita yak’i dole suka kyale sa, video call yayi wa Sadiya inda ta d’auka batare da
b’ata lokaci ba, kusa da Daddy ya matsa ya saka masa wayar yadda zaina ganin ta.
Daddy na ganin ta ya cire oxygen d’in da aka sanya masa sannan cike da azaban ciwo ya
soma magana ” Sadiya’n Daddy ki taimaka ki yafewa Daddy yanzu tasa tazo k’arshe, Daddy
is so stupid to believe in abinda aka fad’a masa batare da yayi bincike ba, Dan Allah ‘yata ki
yafe min ni Nasan mutuwa zanyi”.
Kuka sosai Sadiya keyi tana girgiza kai ” No Daddy bara ka mutu ba, bara ka tafi ka bar mu
ba we really need you in our lives, zan tawo Nigeria yanzu just stay ehen yanzu zanzo na
nemi ya fiyan ka “
” Shii Sadiyan Daddy ni ya kamata na nemi tuban ki ni nariga da na yafe muku daga ke har
yan uwanki Allah ya muku albarka ya raya abinda zaku hayayyafa “.
Nan ya soma kalman shahada zuwa wani lokaci rai yayi halin sa, akan idon ta Daddy ya
rasu jifa tayi da wayarta ta fashe da wata irin masifaffiyar kuka.
Sufyan kam saida wani Doctor ya taro sa dan yadda mutuwan mahaifin nasu ta dake sa,
Hajiya Ruk’ayya najin mutuwan uban ‘ya’yanta ta sume, Nasir da lIbrahim kuwa zafi biyu ne
ya had’ar musu.
Haka nan aka sutur ta gawan Daddy aka kaita gidan ta na gaskiya da muma namu kenan
tana jiran mu.
Allah dan isar manzon ka kasa muyi kyakkyawan k’arshe, kasa kalman shahada ya
kasance kalmun mu na k’arshe a gidan duniya, kasa Aljana ta zamo makoma a gare mu, ka
jik’an wad’anda suka rigamu gidan gaskiya Amin_
Haka akayi zaman makoki kowa ya bud’i baki alkhairin Daddy yake fad’a ba sharrin sa ba,
har aka gama aka watse.
Mummy na gama iddarta ‘yan uwan ta suka so d’auke ta amma su Sufyan suka k’i dan dole
suka hak’ura suka bar musu ita.
Aisha da Lubabatu kam kullum da kalan azaban da ake gana musu dan har Rocky ma an
kamasa, sam halittun su ya chanza in ba farin sani kayi musu ba bazaka tab’a gane su ba.
Sadiya tayi kuka sosai da Sufyan ya fad’a mata sune hakan kuma ya sake linka mata tsanan
k’asar ta a zuciya dan haka tak’i zuwa, har fad’a sai da sukayi da Sufyan akan hakan amma
at last ma shiya zo yana bata hak’uri.
Bayan shekara biyu Ummuhani ta sake haifan d’iya mace ranar suna aka sanyawa yarinyar
Hauwa suke kiran ta Samha, tun daga kan Samha kuma bata sake haihuwa ba.
6 years later
Zuwa lokacin sosai family’n suka saki ransu dan su Suwayd nada 10 years alokacin auta
Samha kuma 8 years.
Alokacin ne Maryam maman Suwayd ta sake samun ciki da Safiyyan Sufyan abun mamaki
ma harda Sadiya.
Suwayd wani mugun so da k’aunar cikin Ummy yake sunan da suke k’iran Safiyya dashi,
Maryam kuma Mammy sai Ummuhani Mummy.
Kullum cikin yiwa Granny hiran cikin yake dan saboda tsabar miskilancin sa da ita kawai
yake sakewa.
Wata tara Mammy ta Haifa kyawawan twins d’in ta aka sanya musu Hafsa da Amina, Hafsa
suna k’iran ta Kuwaysa Amina kuma Kadsah.
Ranar sunan su Ummy ta Haifo nata twins d’in mace da namiji aka sanya musu, Ibrahim da
Ruk’ayya ana k’iran su Safwah da Safwan, aranar itama Sadiya ta haifi kYakkyawar d’iyar ta
mai tsantsan kama da Safwah har blue eyes nasu aka sanya mata Sa’adatu suna k’iran ta
Sayyada.
Tun daga kan Kadsah da Kuwaysa Mammy bata sake koda b’atan wata ba haka ma Ummy.
Dama Mummy ba’a magana dan tunda tasamu miscarriage bata sake samun ciki ba.
Kulawa sosai Suwayd ke bawa Safwah amma tunda ta soma girma ya zame mata monster,
sosai Granny ke masa fad’a sai ya sa mata kuka hakan ne yake tabbatar mata shima ba’a
3:08 PM
son ransa yake ba.
Haka rayuwa ya cigaba da tafiya har Sadeeyq ya kammala karatun sa akayi bikin sa da Zara
har suna da 2years old Baby Aisha Amal.
Omar da Uthman kuma aiki sukeyi sai su Suwayd dake final year a secondary, su Safwah
kuma primary.
Saida Sayyada sukayi 12 years Sadiya ta sake haihuwan Mace aka sanya Mata Maimuna
suna k’iran ta Asmeey.
Safwah da Safwan ne kawai suka san da Mama Sadiya sunan da suke k’iran ta da shi, su
d’in ma dan Safwah ta kama Abuh red handed ne suna video call shiyasa ya fad’a mata
saboda kallan zargin da ta rik’a jifan sa dashi a lokacin.
Daya fad’a Mata ita kuma ta fad’awa Safwan dan bata b’oye masa komai idan ta sani.
Ummy kuma mama Sadiyan ce take k’iran ta da kanta suna gaisawa dan wani zuwa da
Sufyan yayi ta d’auka number’n a wayan sa tunda yak’i had’a su.
Wannan shine tarihin wannan Family mai albarka, cigaban labara..
A haka Abuu yazo ya tarar da Granny, hotunan ya tattare yayi keeping aside sannan
ahankali ya soma wiping mata unstoppable tears nata yana kwantar mata da hankali.
Hulan sa ya cire ya mik’a mata kansa yana neman blessings nata, cike da so da k’aunarsa
ta mik’a hannunta kansa ahankali ta bud’i baki tace ” Allah ya ci gaba da yi muku albarka
kai da yan uwan ka da zuri’ar ku “
Cike da jin dad’in addu’an nata yace ” Amin Mummy Allah ya k’ara nisan kwana ki ga auren
mai gidan naki dana takwarar ki “.
Murmusawa tayi tace “Amin ” hira yata janta dashi harya samu ta saki ranta sannan ya
mata sallama ya mik’e ya fice.
D’akin Sadiya dake yanzu a matsayin nasu Safwah ya shiga dan duba jikin nata, nan ya iske
su da Mammy suna hiran su with so much adoration.
Gaida sa Mammy tayi sannan su Safwah ma, ya jiki yayi mata kawai ya fice dan he has a lot
to do.
Kallon su Sayyid Kawai Suwayd ya tsayayi ganin yadda suka hau manyan kaya wane masu
shirin d’aurin aure, faran shadda suka sanya wadda tasha aiki da bak’in zare, sai hulan da
suka sanya ma bak’a mai kyau.
Sai da ya dai_daici sun gama shirin su yayi saurin mik’ewa ya nufa falour yayi locking su
acikin bedroom d’in.
Ba kalan rok’on da basuyi masa ba amma yak’i bud’e su dan ya riga da yayi promising
kansa indai yana raye bare tab’a barin su suje duban wannan jakan yarinyar ba.
Ganin ma zasu takura sa ya fice daga falour’n again nanma ya sa ma k’ofan lock ha ya wuce
site ta Ummy.
Tana zaune a falour yayi sallama ya shigo, amsawa tayi sannan ya k’araso ciki ya kwanta
akan kujeran da take kai yayi placing kansa akan cinyan ta kaman wani k’aramin yaro.
Murmushi tayi takai hannun ta kansa ahankali tana shafawa ” d’an gidan Ummy da alama
yau rigiman ce ta motsa ko?”
Turo baki yayi kaman mace yace ” dan Allah Ummy kisa baki Abuu ya barmu anan muyi
karatu ni wallahi l don’t wanna miss you guys more especially Baby”
Murmusawa kawai tayi dan ta d’au Baby’n budurwan sa ce, shikam yana sane ya linke ta
bai_bai dan yasan bara ta tab’a kawo Safwah yake nufi ba.
“Don’t worry Son ai kaman yau ne zakuje ku dawo, wait ma who is the luckiest Queen data
sace mun zuciyan handsome har bai so yayi missing ta haka? Ko Zee d’in ce? “
D’ayan hannun sa ya had’e da d’ayan nata yayi wearing sad face sannan in a husky like
voice nasa ya soma magana ” God forbid Ummy dan Allah ki daina ma kawo wannan jakan
yarinyar i ‘ave nothing to do with her, she is just like a piece of trash to me and nothing else,
ni yarinyan ma da nake so batama san inayi ba and duk sanda na kalla cikin idanun ta bana
hango komai sai tsananin tsanata da take, Ummy Allah in bansame ta ba mutuwa zanyi
kuma zan iyayin komai just naga na mallake ta kota halin K’ak’a saboda dani kad’ai ta dace,
amma abin haushin shine yadda ta tsane ni haka ta tsani mutuwan ta ni kad’ai nasan
yadda nake ji Ummy ki taimaka min “ya k’arasa maganan yana tears.
Sosai hankalin Ummy ya tashi ganin yana tears tasan duk duniya mawuyacin abu ke Sanya
sa kuka lallai ba k’aramin so yake wa yarinyan ba tunda harya zubar da hawayen sa akan
ta.
Ahankali ta sa hannu tana wiping mar tears d’in sannan ta soma magana ” amma Son sai
nake ganin kaman alhakin Zee d’in can ke bibiyar ka just kwatanta kai namiji so na wahalar
dakai haka balle ita na mace, du kalan abinda kakeji ta linka ka tunda kai namiji ne zaka iya
trying as much as possible ka danne ita fa? Do you think is easy for her? Nowjust assume
Safwah ce tayi falling ma wani yake wulak’anta ta haka will you feel good, nasan baraka
tab’ajin dad’i b..
Ganin yadda duk wani annurin fuskan sa ta kau yasa ta yin sai sannan ta tuna sunan
mak’iyar sa ta ambata, shikam bak’in kishi ce ta tokare sa jin Ummy tayi comparing
Flower Queen tasa da wani bashi ba.
Saurin changing musu topic tayi ” karka damu Son nasan itama tana son ka kawai dai tana
ja maka ajine, but believe da kanta zata ce tana son ka “.
Kansa ya shiga kad’awa yace ” no Ummy barata tab’a cewa tana so na ba, gashi duk yanda
naso nayi confessing mata feelings d’ina na kasa “
“Worry not dear ni jikina ma yana bani ita d’in taka ce za kuma ka same ta, kai dai ka dage
da addu’a sannan ka rage abinda kake yiwa Zee saboda itama ba laifin ta bane and yanda
kake suffering d’in nan na tabbata ta fika”.
Shiru yayi dan shi baya son zancen Zee d’in nan da Ummy keyi, duk conversations nan tasu
a kunnen Granny dan ta shigo taji suna maganan ta kuma san wa Suwayd yake nufi.
Murmusawa tayi a zuciyan ta tace ” wato dan iskanci yazo ya samu maman yarinya ya linke
ta bai_bai”sannan tayi musu sallama ta shiga.
Gaida ta Ummy tayi sannan Suwayd ma ko answering batayi ba ta soma yiwa Ummy fad’a
ganin haryau d’in tak’i zuwa ta duba jikin Safwah.
Rai a b’ace ya mik’e daga cinyan Ummy yace ” yanzu dan Allah saboda wannan yarinyar
za’a zo a d’aga mana hankali ni wallahi harkin sa Kaina ma ya soma ciwo”.
Ya mik’e ya fice ita Granny ma dariya yake bata sometimes in yana d’an iskan pretending
nasan.
Duk yadda Ummy taso Granny ta kyaleta tak’i dole ta mik’e suka tafi tare.
Lokacin da Zee ta farfad’o k’in kula kowa tayi sai binsu da ido, duk yanda suka so tayi
magana tak’i dole suka kyale ta dan in aka takura mata kuka take sanya wa.
Sai da tayi kwana uku ahaka a kwana na hud’un ne ta tada hankalin kowa sai an sallema
ta, ganin abinda take bana hankali bane yasa akayi discharging nasu.
Kaman ba ita ba duk ta rame suna isa gida wayan ta tasoma d’auka ta shiga turawa
Suwayd sweet love masaages masu tafiya da imani.
Abinci kam tunda ta kwanta jinya ta yayewa kanta cin sa sai yau da Mummy ta Sanya ta
agaba tana kuka sannan taci kad’an.
Washe gari tunda asuba ta soma shirin school duk da bata gama dawowa dai_dai ba.
Sam kuwa Daddy’n ta yace babu inda zataje dan yasan akan Suwayd ne take rawan k’afan
taje school d’in.
Bore ta shiga yi musu ganin hakan ya sanya ya barta cike da tausayin ta, shi da yasan
asibitin da zai kaita a cire son daya kaita sai dai shi so “MAKAHON” abune sauk’in shiga
gare sa wurin fita kam sai anci wuya.
Ganin ta fita da wuri yasa tace da driver’n ta ya fara kaita “SAHAD STORE”, had’ad’d’un love
cards ta siyo da Flowers masu mugun kyau sannan suka wuce school d’in.
Lokacin da go slow ya tare su kaman zatayi kuka dan tasan duty’n Suwayd ne zai iya mata
fiye da abinda ya Mata ranan da taje gidan su.
Acan school kuwa tunda Suwayd yaga 7:50 am k’awar Zee bata zo ba ya fito daga class ya
tsaya a gate dan yau yad’au niyyan koya mata hankalin da bara ta sake masa kallon banza
ba balle har akai tsaki.
8:00 am kuwa ta shigo da alama ba asan ranta ta makara ba, idon ta bai sauka ko ina ba sai
kan Suwayd dake tsaye ya sanya hannayen sa cikin aljihun wandon sa fuskan nan sam
babu annuri.
Wuce sa tayi niyyan yi yayi stopping nata sannan ya nuna mata wani garbage da yasa yara
suka tara meaning ta gyara.
Kallon rainin hankali ta bisa dashi tayi gaba abinta, sai ji tayi ya fusgo hannun ta yana
waina wa cike da mugun ta duk yadda taso kwatan hannun nata ta kasa ga attention na
juniors nasu da sukayi late duk ya dawo kansu.
Sai da yaga idon ta ya ciko da kwalla sannan ya sake mata hannun ya sake nuna mata
abinda zatayi amma taurin kai ya hana ta yi.
Saukan mari Kawai ta jyo a fuskanta, cike da k’in yardan abinda ya faru ta d’ago tana
kallon sa, ganin yana k’ok’arin cire belt tasa yasa tayi abinda yasa ta tayin tana ji wane ta
mutu dan tak’aici.
Juniors nasu sai dariya suke dan ba laifi ita ma tana d’ana discipline.
Zee da komai a idon ta ya faru tuni jikin ta ya soma rawa dan tasan ita ma nata na nan yana
jiran ta.
Dakyar ta iya ta k’araso inda suke, wani makirin murmushi Suwayd ya sake yace da Zee “
Sweetheart” why are you late?”
Jin saukan kalman tayi har tsakar ka da sauri ta d’ago tana kallan sa du da tasan ba har
zuciyan sa yake fad’a ba har lokacin kuma murmushin bata b’ace daga fuskan sa ba, dakyar
ta samu ta nemo excuse ta basa ta dau ma bazai yarda ba amma sai taga akasin haka.
Hanyan class ya nuna mata ta wuce sannan shima yayi joining nata suka jera a tare dan ya
gama abinda ya kawo sa gurin.
With so much adoration suka nufa class yayin da Zee keji wane an tsunduma ta a aljanna,
wani mugun so da k’aunar sa ne suka sake huda zuciyan ta suka shige, har aka tashi tana
cikin farin ciki duk wani rashin lafiya ta neme sa ta rasa.
Sosai ‘yan gidan su ma suka sha mamakin ganin ta dan sun d’au ganin akasin hakan.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har lokacin exams nasu yazo.
Alhamdlillah sun fara lafiya sun kuma k’are lafiya sai shirye_shiryen party da zasuyi ake.
Ta fannin muguntan Suwayd wa Safwah sai abinda ya dad’u haka ma Zee wataran ya Mata
kirki wataran kuma ko kare ya fita daraja a gurin sa.
Safwah taji sauk’i sosai dan yanzu babu abinda batayi da hannun ta school kuma tun
Suwayd na WAEC” ta koma..
Shirye_shiryen party’n candy tasu Suwayd aka fara ba kama hannun yaro, abinka da
‘ya’ yan manya kowa saida ya bada 50k wanda su kansu basu san yane zasuyi da ita ba.
Zee na cikin matsanancin hali na rashin love of her life da zatayi amma haka nan ta daure
tana tsara duk abinda tasan zai burge Suwayd.
Duk wanda ya kalla Suwayd, Sayyid da Safwah yasan suna cikin matsanancin damuwa
amma tambayan duniya anyi sunk’i fad’in abinda ke damun su.
Safwah na zaune a falour’n Mamy tana karanta wani English Novel ‘Desire and destiny
Suwayd ya shigo sanye da 34 army colored short da bak’ar singlet, jarababben earpiece
tasan na nan mak’ale a kunnen sa yana jin wak’an ‘_Stupid in love_”.
Tunda ya shigo ya kafe ta da firgitattun idanun sa dan ba k’arya black with touches of blue
atamfan data sanya yayi mugun fitting ta, babban abinda yafi tafiya masa da imani reddish
lipstick d’in data shafa yayi shaping small cute mouth nata, kallon sa ya miyar kan
zara_zaran eyelashes natan da suke kallon k’asa an k’awata su da gazal, ga yatsun ta da
suka sha jan lalle ba k’aramin burge sa su kayi ba he just can’t afford to loose her he really
don’t want to miss herji yake kaman ya sata a jakan sa yana tattalin ta kaman kwai d’aya
acikin duniya yana yawo da ita.
Jin yadda aka kafe ta da ido yasa ta feeling guilty, ahankali ta soma d’agowa dan ganin mai
kallon natan,kyawawan blue eyes natan basu sauka ko ina ba sai kan Suwayd daya ke mata
wani shegen kallo da ta kasa gano manufan sa.
Da sauri ta miyar da kanta k’asa cike da fargaban abinda zai biyo baya, shima nan take duk
wata annurin fuskan sa ta kau, fuska a d’aure ya k’araso cikin falour’n ya zauna a kujeran
dake opposite natan ya fiddo iPhone s+ tasan yayi facing direction nata giving his damn
attention to the phone, kana iya rantsewa da Allah wani important abun yake yi nan ko pics
yake snapping nata like never before.
Ahankali ta mik’e da niyyan bar masa falour’n dan ta mugun tsanan duk wani abu dazai
had’a ta inuwa d’aya dashi.
Hijab natan dake hannurn kujeran da yake ta k’arasa zata d’auka a nitse, ya sanya mata
K’afa ta hard’e ta fad’a kan center table kanta yayi wani mugun buguwa.
“Arrrshhhh ” ta sake k’ara cike da azaba tana yarfe hannayen ta nan take hawaye suka
wanke mata fuska, saboda tsabar iskanci ma irin tasa video ya soma yi mata.
Dakyar ta mik’e hannun ta dafe da kanta tanajin wata muguwar tsanar sa na mamaye duk
wani lungu da sak’o na zuciyan ta.
” Ki d’auko ruwa mai sanyi a fridge ki kawo min ” ta tsinkayi husky like voice nasa in serious
tone.
Tsoron muguntan da zai sake yi mata tasa jiki na rawa ta wuce ta d’auko masa, goran
ruwan kawai ya kalla ya mik’a hannu kaman gaske ya k’arfa.
Bud’ewa yayi sai da ta juya zata soma tafiya ya watsa mata a baya sannan ahankali ya tako
inda take ya soma juye mata ruwan tun daga kanta har k’asan k’afan ta.
Shid’ewa ne kawai Safwah batayi ba take tsigan jikin ta ya tashi dan yadda sanyin ruwan ke
ratsa ta har cikin k’ashin ta take jiyo sa, runtse idanun ta tayi tanajin wane ta janyo ranan
tafiyan su duk da tasan zatayi missing very own nata.
“Banza mahaukaciya a duk iya tsawon rayuwan ki kin tab’a ganin nasha faro?”
Girgiza kanta ta shigayi hawaye na forming rapidly a idon ta, fusgo hannun ta yayi ya
shiga waina wa da mugun k’arfin da yake ji dashi.
Dakyar ta iya bud’e baki tace” ya Suwayd dan Allah kayi hak’uri you are hurting me”
“Ohh really? ” yayi questioning nata cike da rainin hankali yana sake waina hannun nata
the more.
Gyad’a masa kai tayi ya sauke mata wani firgitaccen marin da saida ji da ganin ta suka
d’auke na wucin gadi sannan ya soma magana a tsawace ” this should be the first and last
time da zanna miki magana ki answer ni da body language if not wallahi na lahira ma sai ya
fiki jin dad’i banza Aljana kawai ” ya tunkud’ata ta fad’i ta bige sosai a gwiwan hannun ta,
kuka ta shiga rerawa sosai agurin shiko not minding halin da take ciki yabi ta k’afan ta ya
wuce.
Kai tsaye garden ya wuce ya nema gurin da ta saba zama ya zauna yanajin wane ya kashe
kansa dan takaici ” meyasa nake mata haka? Meyasa bana iya nuna mata kalon son da
nake mata? Meyasa kullum burina na k’untata mata? Meyasa? Meyasa? Meyasa? ” ya
k’arasa maganan yana hargitsa curly hair tasa da tasha gyara.
Gallary ta wayan sa yayi viewing yana kallon pics natan kala_kala, hannun sa yakai yana
shafa wani pic nata da ta mugun yin kyau dan dariya take sosai ajiki gashi daga gani kasan
unexpected snap ne, ahankali ya bud’e baki ya soma magana ” am terribly sorry for the
pains I have always made you went through forgive me ‘Flower, Ya Suwayd is truly sorry
for all that he has been doing to you, he is sorry for making you feel that he doesn’t love
and care for you, Ya Suwayd uhibbuki hubban shadidan”
Dafa san da akayi ya sanya sa ya d’ago a firgice ganin Granny yasa ya sake wani wawiyan
ajiyan zuciya feeling relieve and safe with out uttering a word ya fad’a jikin ta ya soma rera
kuka kaman ba namiji ba.
Rarrashin sa ta soma yi amma the more ya tuno yadda yake treating Safwah the more
kukan sa take dad’uwa, sai da yayi mai isan sa sannan yayi shiru ya had’e hannun sa da na
Granny ” Granny ki taimakamin you are my only hope wallahi idan na rasa ta nima rasa ni
zakuyi na riga na gama tsara rayuwata da ita amma the most painful thing ever is that ta
tsane ni bata so na, dan Allah ki taimakamin nima ba’a son raina nake k’unta ta mata ba
MAKAHON SOn’ da nake mata ne ya jawo ” ya k’arasa maganan in between cry.
“Shi is okay l’ave got you just keep calm ” ta fad’a cike da tausayin sa dan tabbas tasan
ba asan ransa yake yi ba, janyo sa jikin ta tayi ta rungume tanajin yadda yake sauke ajiyan
Zuciya.
Saida ya nutsu ta rik’e hannun sa kaman small kid suka wuce part d’in ta.
Safwah sai da tayi kuka mai isan ta agurin ta mik’e ta wuce part d’in Ummy’n ta, kallo d’aya
Ummy ta mata tasan ansan tambayan da zatayi mata, jikin ta tazo ta fad’a ta ciga da kuka
kaman zata cire ranta.
Ummy kam tama rasa ta ina zata Soma dan haka kawai tayi hugging nata back tanajin
kukan nata har cikin ranta ahaka Abuh ya dawo ya iske su.
Sallaman sa tasa Ummy zame ta daga jikin sa ta mik’e tana welcoming nasa, briefcase tasa
ta k’arfa ta wuce d’aki.
Da dishash shiyar murya Safwah ta masa sannu da zuwa nan ya tabbatar wa kansa lallai
anyi tsiyar, gurin da Ummy ta tashi yayi replacing ya rik’o Safwah sannan ya soma yi mata
nasiha, sai da ya tabbatar ta saki ranta sannan yayi placing mata pecka goshi yabi bayan
Ummy.
Kwanciya tayi akan kujera ta lumshe idanunta ta lula duniyan tunani, ahaka Safwan yazo
ya same ta dan neman tsokana yazo dai_dai kunnen ta yayi ex claiming sunan ta, a firgice
ta mik’e dan matuk’a ta tsorata ganin Safwan tayi Frauning face natan.
Gwalo yayi mata ya gudu ta d’au pillow ta bisa suka shiga zagaye falour’n, sai da ya gajiyar
da ita lilis sannan ya tsaya.
Tana haki tana komai ta sake bin sa na sosai ya wahalar da ita amma tak’i hak’ura ahaka ya
Haidar yazo ya same ta shi ya kama mata Safwan ta rama dan yasan ita ba iyawa zatayi ba.
Ramawa tayi suka shiga yi masa dariya, shiko sai mita yake wai Ya Haidar baya son sa ita
kad’ai yake so.
Gwalo tata yi masa har yayi zuciya zai bar mata falour’n ta bisa tana apologizing, dirty
glares ya mata sending yace” ai dama dan kinsan bana fishi dake dole ki mun abinda kika
ga dama “
Dariya tayi ta jawo hannun sa suka koma falour’n suka zauna, suka shiga hira harda Ya
Haidar nan takejin gobe party’n candy tasu.
Kiran magrib yasa Ya Haidar da Safwan suka tafi masallaci ita kuma ta wuce part d’in su
dan tayi Sallah.
8:30 pm_
Kowa ya had’u a dinning dan having dinner, cike da kwanciyar hankali suke cin abincin su
illah Suwayd dake ta juya spoon.
Safwah kam duk ta kasa nutsuwa dan duk sanda ta d’ago sai idon ta ya had’u dana Suwayd
saboda mayataccen kallon da yake binta da shi.
Granny ce ta masa magana sannan ya soma ci, two spoon kawai yayi zuciyan sa ya soma
mugun tashi da sauri ya mik’e ya nufa toilet ya soma kwara amai wane zai amayar da ‘yan
hanjin sa, hankali a tashe Ummy ta bisa ta dafasa tana jera masa sannu ruwa ta basa ya
wanke fuskan sa sannan ta rik’o sa suka dawa falour ta zaunan dashi.
Jingina yayi da jikin kujeran yana maida numfashi yana sauke ajiyar zuciya, ruwa mai sanyi
Ummy ta d’auko ta tsiyaya a glass cup ta basa yasha.
Saida ya samu nutsuwa ya mik’e ya fice a falour’n, kallon tuhuma Granny ta shiga aikawa
Mammy amma ta moze.
Mik’ewa Safwah tayi dan ta rasa appetite nata, da ido Sayyid yayi questioning nata ta basa
answer with nod ta wuce.
Bayan angama cin abinci Abuh ya shaidawa su Haidar tafiyan su saura kwana biyu suyi su
gama shirye_shiryen su.
Washe gari tun 7:00 am Zee ta wuce gidan k’unshi ba ita ta dawo ba sai 11 daganan kuma
aka wuce saloon, kwata_kwata ta kasa nutsuwa dan sosai take so ta burge Suwayd agurin
party’n.
Daga saloon gida ta dawo ta fesa wanka ta wuce gurin make-up k’arfe 6:00 pm aka gama
make-up d’in gashi tun 4 akace za’a soma.
Dakakken lace daya amsa sunan lace ta sanya Black colored with touches of dark-blue,
d’inkin riga da skirt d’in ya mugun amsar ta dan yadda aka bawa komai hak’k’insa, Jaka,
takalmi da veil natan du blacks ne sai phone cover da ear piece natan dark-blue duk
hassadan Ka in kaga Zee saita burge ka dan yadda tayi kyau ko wata Instagram bride d’in
albarka.
Ita kanta tasan tayi kyau, MieMie kam tama kasa magana pics kawai take d’aukan ta wane
photographer, Mummy ma sam ta kasa d’auke ido kan d’iyar tata sai take gani kaman ranar
bikin ta ne sannan tayi magana jin yadda Zee tayi wanka da perfumes, dariya Zee d’in tayi
ta nuna mata is not a big deal ai.
4matic ML50 ta Mummy’n dake nan sabuwa kar ta tad’auka ta tafi, a tare da friend tata
Hafsa suka isa dan haka suka shiga tare.
Tunda suka shiga kowa ya kasa d’auke ido akan Zee harta da wanda bata magana dasu sai
gasu sunzo d’aukan selfie dan freely suka nuna mata ta musu kyau.
Beelkeey Shuwerh fans’ basu wani b’ata lokaci ba suka tawo d’aukan selfie abin harda
ture_ture, Ummu islam da Hassana ma sai da suka kusa dambe wai su sai sun tsaya jikin
Zee Allah ya temaka Binth Uthman na kusa ta rabasu lolx.
Guri suka nema suka zauna Zee ta fara baza ido taga ta ina ne zai b’ullo.
Sai da na kusan cin tuntub’e lokacin da nayi tozali da Suwayd, masha Allah gaskiya banga
laifin Zee ba dan nima ji nayi inama_inama.
Yana sanye da bak’in pencil swag jeans daya mugun amsar sa, belt tasa ma kad’ai abar
kallo ce dan ta had’u sosai har wani shining take wane sun light, double S da akayi
designing ajiki tayi matuk’ar yin kyau, sai dark blue armless body huge da kallo d’aya inka
mata kasan an kashe kud’i gurin siyan ta, yadda aka tsara rubutun jikin ta ma ya isa
shagaltar da mai kallo “YOU MEAN THE WORLD TO ME RS” ne ke rubuce boldly, kasancewar
rigan sa armless yasa tattoo nasa ta bayyana da murd’ad’d’un packs nasa, to the coo
Suwayd yakai duk inda bakwa tunani gurin had’uwa gashi giant with gigantic body
structure da kowace lafiyayyiyar budurwa inta gansa zatayi burin kasancewa dashi.
Curly hair nasa yayi styling wane “_Lee min ho acikin boys before flower_” ga yanda sajen
sa ke kyalli gwanin burgewa, diamond wrist watch nasan tayi matuk’an kyau duk yadda
zan kwatanta muku Suwayd ya wuce hakan da Haidar da Sayyid ma kansu kasa d’auke ido
sukayi akansa.
Duk da suma ba k’arya sunyi kyau, Mercedes Benz S550 ta Ummy ta basu suka tafi, bakajin
komai sai sanyin Ac da k’amshin daddad’an perfume tasu dake tashi suna sauraran wak’an
Perfect na Edsheeran”.
Both Suwayd da Sayyid sun tafi wani tunani na daban dan yadda baitukan wak’an ke ratsa
su, Haidar ne ya soma lura da tattoo d’in dake Hannun Suwayd tambayan duniya yayi yak’i
ya fad’a masa wace dan haka ya kyale sa.
Ko daga yadda Suwayd yayi parking motan da suka iso kasan arrogancy nasa ya motsa,
wurin fitowa ma sai abin ya baku mamaki sai kace wani basarake.
Shine a tsakiyan su suka shiga kaman superstars take gurin ya kaure da ihu, flash kam
harda masu vivo ba’a barsu a baya ba irin su “Hanee in da shi writer Lolx jxt kidding
Zee numfashin tane ya kusa barin jikin ta ji take wane taje ta rungumeshi ta fad’a masa
how much she miss, love and ready to die for him.
Hotuna ta shiga snapping sa kaman ba gobe, kaman dama su ake jira suna zama aka fara
shagali.
Zee gaba d’aya ta rasa nutsuwan ta kallon Suwayd take wane zata cinye sa, duk sanda ya
d’ago sai ya kamata tana kallon sa amma ko d’an kunya ta kasaji ta daina kallon nasa.
Shima sosai tayi masa kyau sai shegen kishi daya turnuk’e sa dan cleavage natan sun fito
kuma veil d’in rik’e sa akayi a hannu irin na gayun nan.
K’arfe 10:00 pm suka gama duk wani shagali sai wani game da za’ayi wanda daga shi an
tashi, wadda zatayi wakilcin mata aka buk’ata inda kaman had’in baki sukayi assigning
Zee.
Haka ma mazan Suwayd suka zab’a inda saida aka kai uwa rana ya yarda yaje stage d’in .
Papers aka mik’a masa ya zab’a d’aya then back to her, atare aka umarce su da su bud’e.
Ahankali suka soma warware wa, wide open Suwayd ya bud’e baki yana kallon paper’n,
yayin da itama ta zare idanu tana kallon nata paper’n.
Tunda Hafsa taga haka tasan bad thing is about to happen dan sam bataso aka had’a
Suwayd da Zee inuwa d’aya ba.
Paper’s d’in aka had’a gu d’aya inda du abu d’aya suka zab’a ita nata “Kiss Him shi nasa
Kiss Her.
Ihun da suka jiyo ne ya sanya su dawowa reality, mazan na ihun yayi kissing ta kar yayi
failing su matan ma nayi wai kar tayi failing su, juyawa Zee tayi zata bar stage d’in dan ta
yarda matan su fad’i, ta jiyo lallausan hannun sa ya rik’o nata in a romantic way ya shiga
juyo da ita.
Runtse idanun ta tayi cikin tsantsan tashin hankali ta sani barata iya hanasa duk abinda
zaiyi da ita ba amma gaskiya tsoro take ji, tana wannan halin ne ya sak’alo hannun sa a ‘yar
k’unk’umin ta moving her closer to him, sosai gaban ta ya shiga dukan uku_uku dan this is
the first time hakan zata fara faruwa da ita.
Nose tips nasu ya had’a sannan ahankali yayi owning lips nata kissing her like danshi aka
turo sa duniya, na sosai jikin ta ya shiga rawa sai da ya d’au like 5 minutes sannan yayi
pulling out ya juya kaman bashi ya gama kissing ‘yar mutane ba yabar stage d’in.
Ihun winner aka ta yiwa Suwayd yayin da Zee saida Hafsa tazo tazo ta jata dan motsi ta
kasa sai rawan jiki.
Kowa viewing video nasa ya shigayi saboda mamaki dan kowa Zee ya bawa winner tunda
ita take son shi.
Ahaka dai party’n ya watse kowa cike da kewan d’an uwan sa dan wasu dama had’uwan
school rabuwan gate, dad’in abin ma ansha hotuna an kumayi exchanging digits
Har aka gama Zee ta kasa tab’uka komai ko magana ma ta kasa sai bin mutane da ido,
Hafsa ce ta taimaka ta kaita gida dan gaba d’aya a firgice take
Tana shiga falour’n su tayi turus ganin Mummy’n su ba’a nitse ba Daddy’n su kuma sai safa
da marwa yake fuskan sa sam ba annuri, yayin da MieMie ke zaune a gefe tana kuka.
Dakyar tayi gathering courage tai sallama amma ba wanda ya kulata, jiki a sanyaye ta tako
tsakiyan falour’n ta tsuguna tace ” Daddy, Mummy sannun ku da gida…”
Shegen kallon da Daddy ke mata ya sanya ta had’iye ragowan kalamun ta, wayan sa ya zaro
ya cilla mata sannan a tsawace yace ” Uban mene wannan?”
Hannun na rawa ta d’ago wayan abinda ta gani ne yasa ta kusan sake fitsari a wando, inna
cracky voice ta soma magana ” Da.. Daddy dama… “sai kuma tayi shiru.
“Dama me? Dama abinda zakije kiyi kenan shiyasa kike ta rawan k’afa ko? To ki bud’e
kunnen ki dakyau kiji ni karatun ki a Cyprus ko zaki mutu na soke ta, dan inaji ina gani da
kud’i na bazanyi sanadiyan lalacewan ki ba, tunda har haka ta soma faruwa nasan
gaba gaba har kwanciya dake in ya buk’ata nasan wannan shegen “MAKAHON SO”n da
kike masa zai sa ki amince, shasha shar banza shasha shar wofi da bakisan ina ke miki ciwo
ba, now get out of my site ” ya k’arasa maganar a tsawace.
Rik’e k’afan Daddy’n tayi ta shiga rusa kuka kaman zata cire ranta tana apologizing amma
sam yayi burus da ita, take nishin ta ya soma sama_sama zuwa wani lokaci numfashin ta ya
d’auke.
Har rige_rigen yin kanta sukayi su duka ukun, jijigata Mummy ta shigayi amma ina duk ta
wani sank’ame, a rikice Daddy ya kira family Doctor nasu shi sai lokacin ma ya tuna Doctor
yace su guji b’acin ranta.
Lokacin da yazo sam ya kasa komai dole sai da suka dangana ta da asibiti sannan ta
farfad’o, kuka ta shigayi tana wani irin tari dake had’owa da jini, sosai lamarin ya tsorata
iyayen ta inda Daddy ya shiga kwantar mata da hankali kan indai Cyprus ne karta damu zai
kaita.
Kwanan ta d’aya aka sallemu su ta soma shiri dan gobe itama zata wuce.
******
Yau tunda Suwayd ya tashi wani mugun zazzab’i ya lullub’e sa dan tunowa da yayi gobe zai
tafi yabar flower’n sa, gaba d’aya bayason tafiyan nan gashi yasan ko mutuwa zaiyi sai yaje.
Ba yadda Granny batayi dashi ba yaje asibiti yak’i dole ta hak’ura ta zuba masa ido taga iya
gudun ruwan sa.
Safwah da Sayyid through out the day suna mak’ale da juna sallah kawai ke rabasu, kallo
d’aya zaka yiwa Safwah kasan taci kuka ta gode Allah dan yadda fuskan ta da idon ta ya
mugun kumbura.
Sayyid ma daurewa kawai yake dan kar ya sake sata cikin damuwa.
Bayan sallan magrib kawai Safwah taji tana son zuwa garden, gurin data saba zama taje
inda tayi kyakkyawan gani.
Wata k’atuwar had’add’iyar teddy bear fara tagani ajiye agurin da wasu had’add’un love
cards a gefe da flowers masu kyau da dad’in k’amshi, without any fear ta k’arasa ta zauna
ta soma bud’e cards d’in tana karantawa, ita kad’an ta sai murmusawa take dan sunan ta
du tagani ajiki.
Sai da tagama karantawa tsaf sannan ta tattare su a gefe ta d’iba flowers d’in tana smelling
d’addad’an k’amshin da suke tanaji wane ita kad’ai ne acikin duniyan sai blushing take dan
ita duk tunanin ta Sayyid ne ya ajiye mata.
Suwayd dake can gefe yana kallon ta with so much adoration sosai yaji dad’in yadda tayi
farin ciki da surprise nasan daya mata.
Teddy bear d’in ta d’auko mistakenly hannun ta ya tab’o wani guri wak’an “Johnny drill
Wait for me’ ta soma tashi, nutsuwa tayi sosai tana sauraron wak’an wanda kafin ya K’are
tuni tears suka fara forming rapidly a idanun ta.
Nan take gaban ta ya soma fad’uwa dan sai take gani kaman idan ya Sayyid d’inta ya tafi
bare dawo ba.
Suwayd ma hawaye yake sosai dan gani yake kaman idan ya tafi bazai dawo ya samu wife
to be d’in sa ba.
Kwantawa tayi tana kallon moon and star da suka fito, kalman_Safwah the moon that will
never escape from the star, you are the moon and am the star S love S_ na mata yawo aka,
meyasa du cards da take gani a wadrop ko school bag natan sai taga an rubuta hakan a
K’arshe, meyasa du ba’a rubutan suna in full sai S love S tabbas ya Sayyid bazai mata haka
ba amma zata tambaye sa meyasa, kawar da tunanin tayi ta janyo Teddy’n ta tayi hugging
so tight tana sake jin wak’an ta lumshe ido tana bi ahankali.
Motsin data jiyo ne ya sanya ta mik’ewa nan taga du fitilun garden d’in sun d’auke duhu ya
mamaye gurin.
Da lalube ta nemo flowers da cards natan ta mik’e ta soma takawa hankali dan barin
garden d’in, jin tayi Karo da mutum ya sanya ta bud’e baki zata kwalla k’ara Suwayd yayi
shutting ta da wani had’amammen kiss, kissing ta yake possessive yet passionate in a
demanding way.
Sosai jikin ta ya d’au rawa duk abubuwan dake hannun ta suka tarwatse, jin k’afafun ta ba
zasu d’auke ta ba ta zame k’asa shima ya bita ya sake owning lips natan kissing her like dan
shi aka turo sa duniya, sai da ya kashe mata jiki liss sannan yayi pulling out ya rik’o hannun
ta ahankali ya d’aura mata bracelet mai tsananin kyau da tsada yayi pecking hannun
sannan ya tattare mata flowers da cards natan ya d’aura mata a hannun ya janyo teddy’n
yayi placing a cinyan ta.
Mik’ewa yayi da sauri yabar garden d’in, yana fita kuma wutan ya dawo, dakyar ta iya ta
mik’e ta fito daga garden d’in zuciyan ta cike da zargi kala_kala dan tayi imani ba Sayyid
bane, gashi wanda kwakwalwarta ke kawo mata tasan over his dead body bazai tab’a
aikata hakan ba a gare ta.
Tsoro ne ya lullub’e ta lokacin da ta shigo taga Suwayd kwance akan cinyan Granny suna
hira.
Sallama kawai tayi musu ta shige d’akin su tasa lock a k’ofan tayi throwing kanta kan bed
ta shiga rusa kuka.
Kuka take sosai wanda ita kanta bata san dalilin sa ba, haka har su Kuwaysa suka zo suka
iske ta, dakyar ta iya ma ta bud’e musu k’ofar suka shigo.
Sayyid ma kulle kansa yayi a toilet yasha kukan sa kaman ba gobe, haka ma Suwayd dake
ta jin wak’an “Wait For Me” yana kuka.
Su duka ukun a matsanancin hali suka kwana musamman ma Suwayd.
Washe gari kuma tun asuba da aka tashi ba wanda ya koma dan flight na 8:0 am zasu bi.
Safwah tak’i kula kowa sai aikin kuka yayin da Suwayd ma Ummy tasa shi a gaba da lallashi
dan tasan damuwar sa.
7:30 am suka fita duka aka tafi yi musu rakiya har kuma lokacin Suwayd bai saki ransa ba
gara ma Sayyid dake daurewa yana yak’e.
Suna isa airport hankalin Suwayd ya sake tashi dan sai lokacin ya gama yarda tafiya dole
ba fashi.
Lokacin da aka soma kiran passengers hugging Sayyid da Haidar Safwah tayi tana kuka like
never before.
Suwayd kam na gefe yana fama da tsananin kishi da bak’in cikin rabuwa da ita, nasiha
sosai akayi musu sannan suka wuce suna waving ma family’n nasu Hannu Suwayd sai
waiwaye yake yana kallon Safwah har ya daina hango ta.
Fad’a sosai Daddy da Mummy’n su Zee suke mata a hanyan su na zuwa airport inda tayi
promising nasu insha Allah zata yi iyakan yinta ta tsare mutuncin ta.
Haka nan itama ta rabu da nata family’n cike da kewan su..
Safe flight Mr Arrogant
_Safe flight Zee
A baya munyi mentioning Lubna a family, a labari kuma mun manta da it so am srry you
know nobody is perfect and ba wanda baya wuce gyara, itama k’anwar Sayyid ce bayan
Samha sai ita daga nan kuma Mummy bata sake aihuwa ba_