SOYAYYAR MU CHAPTER 4

SOYAYYAR MU

CHAPTER 4

A yau Aliyu zai yi tafiya zuwa Abuja, tafiyar kwana uku don kammala shirye shiryen taron bude sabon kamfanin shi da aka gama ginawa.

Ammi tsaye a gaban durowar kayan shi tana hada mishi kayan da zaiyi tafiya da su yayin da shi kuma yana bisa gadon shi yana shigar da wasu saqonni a laptop. Ammi tace “Allah dai ya kaimu bikin ka da Hanifa ta cigaba da hidima da kai”
Murmushi yayi yace “idan zata iya ba”
Ammi ta gane me yake nufi don haka ne tace “ai ta fara koyon yadda zata zauna da kai baby na”

Wani bangare na durowan shi ta kalla tace “yanzu Aliyu manyan kayan da ka dinka gaba daya gasu nan babu wanda ka taba saka wa? Wai yaushe zaka girma ne?”
Dariya yayi yace “yi haquri Ammi zan sa, wadannan ma zan bada su sai in dinka wasu tunda naga kaman sun dan kwana biyu ko?”

Cikin mamaki ta waigo ta kalle shi tace “zaka bada su dukda baka taba sakawa ba? Ka dinko wasu suma ka ajiye su cikin durowar? Wato dai idan ba qananan kayan nan ka sa ba baka jin dadi ko? Allah ya shirye ka”
Wannan karon dariya kawai yayi ba tare da yace komai ba.
Ammi ta gama hada mishi kaya kenan Hanifa ta shigo tana fadin “yaya na sa maka magungunan ka a mota sannan na hada maka snacks din da muka yi jiya” yace “nagode Hanifa” ya rufe laptop din ya sauko daga kan gadon.
Ammi ce tace “koma ka zauna” cikin mamaki ya zauna yana fadin “Ammi lafiya?”
Kunnuwan shi ta ja har sai da yace “oouch Ammi it hurts fa”
Hanifa tana ta dariya.
Ammi tace “ofcourse I know it hurts, ka tabbata ka sha maganin ka kuma ka ci abinci kana ji na?” yace “toh ai Ammi abincin wajen ne babu dadi wallahi”
Tace “dukda haka dai ka ci saboda kada ulcer dinka ta tashi kaji babyna?” yace “yes Ma”.

Da suka fito harabar gidan ne Hanifa tasa mishi jakar shi a motar shi yayin da ya wuce gidan Nafisa, ba da jimawa ba sai gasu sun fito riqe da hannuwan juna tana tambayan shi “kwana ukun zaka yi?” yace mata “insha Allah anty Feena, please take care” tace “you too bro” suka rungume juna.
Ya dawo ya rungume Ammi ma sannan ya ce ma Hanifa “take care”
*************

Aisha dai bata ji dadin tafiyar Aliyu ba, zamu iya cewa ta damu sosai da rashin ganin Aliyu wanda ko ita Hanifa bata damu ba kamar yadda ita Aishar ta damu.
Gaba daya ta rage walwala, ko da Ammi ta tambaye ta sai cewa tayi ba komai.
Abin mamaki har zama take yi tana kallon qofar dakin shi ko zata gan shi ya fito.

A koda yaushe dai Yusuf baya leqowa gidan Ammi har sai ya tabbatar Aisha ta tafi gida.

Ni kuwa nace for how long is he gonna keep hiding??🤔🤔

***********

Ranar da Aliyu zai dawo ya kasance ranar asabar.
Da rana ne Ammi da Nafisa suka fita domin halartar bikin wata diyar qawar Ammi watau Hajiya samira. Sun bar Hanifa da Hafsat a gida.
Bayan la”asar ne Hanifa ta jira Aisha ta ji shiru don haka ne ta neme ta a waya amma bata samu ba, ta bar ma Hafsat saqo akan idan Aisha ta zo tace mata ta jira ta zata je salon ta dawo. Hanifa bata dade da fita ba ne Aliyu ya dawo.
STORY CONTINUES BELOW
A gajiye ya dawo sannan ga wani zazzabi da yake neman rufe shi, ko motar ma ya kasa faka ta a parking lot, nan ya barta a tsakar gida ya wurga ma Dauda makullin ya wuce cikin gida.
Hafsat ce ta bude mishi qofa tayi mishi sannu da zuwa ya amsa tare da tambayan ta “su Ammi basu dawo ba?”
Tace “eh” ya wuce dakin shi. Bayan yayi sallah ne ya ji qirjin shi ya fara yi mishi zafi don haka ne ya koma bisa gado ya kwanta.
***************

Aisha dai ko da ta shigo gidan ta ga motar Aliyu wadda tasan da ita yayi tafiya a dalilin mugun sa mishi ido da tayi. Wannan ya tabbatar Mata da lallai ya dawo.

Bayan sun gaisa da Dauda ne ya miqa mata makullin motar Aliyu akan ta shiga mishi dda shi.
Hafsat ce ta bude mata qofar, bayan sun gaisa ne Hafsat din ta fadi mata saqon Hanifa.

Ko da tayi tambayar su Ammi ta sanar da ita sun tafi biki.
Bayan Hafsat ta koma kicin ne Aisha ta ajiye ma Aliyu makullan shi akan dinning yayin da ta zauna a qaramin falo tana kallon TV tana kuma kallon qofar dakin shi.

**************

Cikin bacci ne ya dafe qirjin shi yayin da yake ta addu”o”i tare da ihun sunan Ammi, Aisha da ta qura ma qofar dakin shi ido tuni ta miqe a dalilin jin muryar Aliyu da tayi.
A guje ta nufi qofar dakin shi yayin da ta natsu tana sauraron abinda yake fadi.
Jin yana ta kiran Ammi ne ta shiga dakin kai tsaye, tsayawa tayi cak yayin da wani asirtaccen qamshi ya bugi hancin wanda ya gauraye da sanyin AC ya bada wani yanayi na daban.

Da qyar ta qarasa shiga dakin, cikin few seconds ta qare ma dakin kallo wanda yayi bala”in kyau, a da tayi tunanin dakin Hanifa yayi kyau amma kuma ganin na Aliyu sai ta ga ashe na Hanifan ma ba wani kyau yayi ba.
Hango Aliyu tayi kwance cikin bargo dafe da qirjin shi yana ta juyi.
A rude ta qarasa wurin shi ta zauna gefen gadon, muryarta tana rawa tace “lafiya?”
Muryar shi qasa-qasa yace “kira mun Ammi da likita na”
A rude ta miqe zata fita yayinda yayi saurin riqo hannunta yace “ki dauki waya na ki kira su”
Ba tare da ya saki hannun ta ba har ta zauna yace “kada ki tafi ki barni please”
Aisha dai tuni jikin ta yayi sanyi hawaye ya fara wanke fuskan ta.
Har a wannan lokacin yana riqe da hannun ta kamar wanda yake tsoron zata gudu ta bar shi, haka tayi amfani da dayan hannun ta dauko wayar shi a kan bed-side drawer ta juyo ta tambaye shi “wane suna zan duba?” yace “Dr Sadiq”.

Aisha ta kira shi ta shaida mishi halin da Aliyu yake ciki sannan ta kira Ammi itama ta shaida mata.
Tana shirin kiran Hanifa ne ta ji kan Aliyu a bisa cinyar ta wanda saboda zabura da tayi bata san lokacin da wayar ta kufce a hannun ta ba, shi dai Aliyu bai ma san me yake yi ba a dalilin fita hayyacin shi da ya fara yi.

Hannuwan ta suna rawa ta dafa kan shi wanda yayi zafi rau tana fadin “kayi haquri gasu nan zuwa”
Gashin kan shi da ta taba ne ta ji wani irin laushi kamar na jarirai, wani asirtaccen qamshi ne kawai ke tashi wanda ko ita mace gashin ta baya qamshin da nashi ke yi.

Ajiyar zuciya ta saki yayin da ta cigaba da tofa mishi addu”o”i.
Abinda Aisha bata sani ba shine ashe Aliyu ya suma wanda a tunanin ta ya samu bacci ne.

****************

Zaune take akan gadon yayin da kan shi yake bisa cinyarta tana ta kuka.
Dr Sadiq wanda ya shigo tare da Hafsat ne yayi saurin dudduba Aliyun yayin da ya kalli Aisha yace “ki daina kuka, suma yayi”
STORY CONTINUES BELOW
Zaro idanuwa tayi cikin tashin hankali ta sa hannuwanta ta tallabo fuskar Aliyu tana fadin “ya suma? Inna lillahi wa”inna ilaihir raji”un, Garin yaya? don Allah ka taimaka mishi kada ya mutu”
Dr Sadiq yana shirin yi ma Aliyu Allura yace “Ulcer din shi ce ta tashi, kada ki damu zai Farfado ba da dadewa ba Insha Allahu. Ina su Ammi fa?”
Tana kuka tace “sun fita, na kira su a waya yanzu zasu dawo”
Ganin zai yi mishi allura ne tace “kada kayi mishi mai zafi please”
Dariya Dr sadiq yayi yace “banda abinki mutumin da baya cikin hayyacin shi ina zai ji wani zafin allura”
Bayan yayi mishi ne suka maida kan shi bisa filo.
Aisha ta qura ma Aliyu idanuwa yayinda hannunta yake cikin nashi tana jira ya Farfado wanda har yanzu tana ta share hawayen da yake gangarowa daga idanuwan ta.
Ganin Dr sadiq zai zura mishi allurar drip ne tayi saurin fadin “don Allah ka bi ahankali kada yayi mishi zafi, ka ga baya da lafiya”
Wannan karon hatta Hafsat sai da tayi dariya wanda har yasa ma ta fita daga dakin.
Dr sadiq yace “hala dai ke matsoraciyar allura ce?” ta zaro idanuwa ta kalle shi tace “wallahi zafi gareta” yayi dariya yayin da ya cigaba da aikin shi.
Cikin minti biyu da sa mishi drip din ne ya Farfado, Aisha wadda har yanzu tana riqe da hannun shi ya fara kallo.

Ganin yana kallon ta ne tayi saurin miqewa tana qoqarin zare hannun ta daga nashi amma kuma abin mamaki sai shi ya riqe hannun ta sannan ya janyota ta zauna a gefen shi.

Muryar shi qasa-qasa yace “thanks alot” sannan ya saki hannun ta ya rufe idanuwan shi.
Da sauri ta kalli Dr sadiq tare da matsawa daf da Aliyu tana shafa fuskar shi tace “duba ka gani ya qara suma ne?”
Dr sadiq dai yayi dariya sosai yace “bacci zai yi, he is weak”
Aliyu yana jin su sannan yana jin lallausan hannuwan Aisha tana shafa fuskar shi wanda hakan yasa shi jin wani sanyi a zuciyar shi, dayake ya riga ya sha wuya bai san lokacin da bacci ya tafi da shi ba.
Ammi da Nafisa ne suka shigo hankulan su a tashe suna tambayar jikin Aliyun yayin da Ammi ke ta masifan Hold up da ya hana su dawowa da wuri.

Likitan ne yayi musu bayanin abinda ya faru sannan yace “zai samu sauqi Insha Allah”
Nafisa wadda ta haye gadon tana shafa kan Aliyun ce tace “hala yayi wasa da abinci ne?”

Likitan ne yace “ina tunanin har magungunan shi ma yayi wasa da su, banda amaryar nan tashi da ta kira ni akan lokaci gaskiya da ya shiga wani hali”
A lokacin da yayi maganar ne Hanifa ta shigo yayin da zuciyarta ta buga, tana kallon Aisha wadda itama ta zaro idanuwa.
Ammi ce tace “ai ba Aisha bace amaryar tashi”, ta nuna Hanifa wadda ke bakin qofa tace “ka ganta nan Hanifa ce amaryar”.
Dr sadiq yayi mamaki, Murmushi yayi yace “ai ban san Hanifa ce amaryar tamu ba, Allah ya sanya alkhairi” suka amsa da Ameen.
Ammi ta kalli Aisha wadda da alama ta shiga damuwa tace “ki daina damuwa Aisha, haka yake fama idan ciwon nan nashi ya tashi, Allah ya saka miki da alkahairi da qoqarin kiran likita akan lokaci da kika yi. Allah kuma yayi miki albarka” Nafisa tace “Ameen”.
Hanifa ce ta qaraso tana tambayan abinda ya faru wanda Aisha ta bata labari.
A lokacin da Dr sadiq zai tafi ne yace ma Nafisa idan ruwan drip din ya qare ta sa mishi wani wanda dama tuni ta iya tunda a duk lokacin da ciwon nashi ya tashi irin haka sai an qara mishi ruwa, ya kuma gaya musu idan ya farka a bashi abinci marar nauyi ya ci yayin da yayi musu alqawarin dawowa anjima.
Bayan likita ya tafi ne Aisha ta ja Hanifa suka shiga kicin domin su dafa ma Aliyu abinci kafin ya farka.

Nafisa ta kira Yusuf a waya ta shaida mishi abinda ya faru, a dalilin sanin cewa Aisha tana gidan ne yace yana nan dawowa zuwa anjima idan aiki yayi sauqi.
Aisha ta hada abinci kala kala kamar su fried rice wanda ya ji kayan lambu da su hanta, tayi farfesun nama wanda baiyi yaji ba sosai sannan ta hada fruit salad lafiyayye.

Gaba daya tana yi hankalin ta baya tare da ita. Tunanin Aliyu take ta yi, duk ta bi ta shiga damuwa.
Hanifa dai kallon ta kawai take yi yayin da take wani tunani a ranta wanda ita kanta bata san na meye ba.

************

Gab da magrib ne Aliyu ya farka yayin da jikin shi yayi weak, a lokacin har Nafisa ta canza mishi drip din.
Ammi ta na shafa kanshi tace “baby na ya jikin? Ina yake maka ciwo yanzu?”
Ya mayar da kan nashi bisa cinyar ta yace “ba ko ina Ammi, i am just weak ne kawai”

Anan ne Hanifa da Aisha tare da Hafsat suka shigo dakin riqe da kayan abinci kala kala.
Tun da suka shigo Aisha da Aliyu ke ta kallon juna, ganin kallon nashi yayi yawa ne har ta fara tsarguwa.

Saurin dauke idanuwan ta daga kan shi tayi.

Hanifa ce tace “Yaya ya jikin?”
Har yanzu idanuwan shi na kan Aisha yace “da sauqi Hanifa” Hafsat ma ta gaishe shi ya amsa.
Aisha ma ba tare da ta kalle shi ba ne tace “ya jiki?”
Murya qasa-qasa yace “da sauqi”
Ita dai Aisha tayi mamakin jin ya amsa Wanda har sai da ta kalle shi don tabbatar da shi din ne ya amsa ta.

Ammi ce tace “me aka dafo mana ne haka?”
A lokacin Hafsat da Hanifa sun ajiye warmers din da suka shigo.

Hanifa ce tace “Ammi abinci ne kala kala, sai wanda yaya ya zaba”
Ammi ta tambaye shi “me zaka ci?”
Hanifa ta fara lissafo abubuwan da suka dafa ne sai suka ga ya nuna hannun Aisha.
Gaba dayan su suka juyo suna kallon Aisha wadda take riqe da bowl na fruit salad a hannun ta.

Duk ta bi ta rude yayinda hannuwan ta ke rawa, sa”a daya da bata saki bowl din ba.
Nafisa ce tace “Aisha meye a bowl dinnan?”
Da qyar ta saita murya tace “fruit salad ne”
Ta ajiye sannan ta zuba mishi a wani qaramin bowl sannan ta miqa ma Ammi.
Hanifa ta lura da kallon da Aliyu yake ta yi ma Aisha shigowar su.
Tun hakan bai dame ta ba har ya fara damun ta wanda ta fara wasu tunanin da ita kanta bata gane kan su ba.
A tunanin su Ammi ba wani shan fruit salad din zaiyi ba sai gashi ya kusa shanye tas har Ammi na fadin “lallai Aisha sannun ki da qoqari, na tabbatar fruit salad dinnan yayi dadi tunda gashi baby na ya shanye shi”

Aisha dai gaba daya a rude take.
Nafisa ce take ta dariya tana fadin “Aikuwa ki koya ma Hanifa irin shi saboda ta dinga yi mishi idan sun yi aure”
Aliyu dai rufe idanuwan shi yayi, a ranshi yana fadin “anya zan cuci kaina in auri Hanifa kuwa???”2
Bayan Sallan magrib ne Aisha ta tarar da Ammi zaune a dakin Aliyu, a lokacin drip din da Nafisa tasa mishi ya kusa qarewa.+
Idanuwan shi a rufe ne lokacin da ta shigo dakin tace ma Ammi “zan tafi gida, Allah ya bashi lafiya” nan da nan ya bude idanuwan shi suka hada ido wanda kafin Ammi ta amsa ne yace “ameen thanks a lot for saving my life”.
Ammi ta ji dadin godiyar da Aliyu yayi ma Aisha don ko ba komai tasan fada a tsakanin su ya qare, itama Ammi tayi mata godiyar dawainiyar da tayi sannan tayi musu sallama ta tafi.

Gaba daya Aliyu bai so Aisha ta tafi ba, asali ma ji yayi kamar yace kada ta tafi wanda ya rasa dalili.
Ko da ya mayar da idanuwan shi ya rufe babu abinda yake tunani sai abubuwan da suka faru, yadda duk ta bi ta rude harda kuka tayi saboda shi.
Wata zuciya ce ta tambaye shi “ko dai ka fara son ta ne?” a fili yace “hell no” wanda har Ammi ta ji.
Dafa shi tayi tace “babyna lafiya?” Aliyu da bai san maganar ta fito fili ba ya saki ajiyar zuciya yace “ba komai Ammi”.
*************

Aisha dai ta koma gida cike da tunanin Aliyu wanda cikin dare kasa bacci tayi musamman idan ta tuno irin kallon da yake ta yi mata, abu daya ne ya bata mamaki, godiya da Aliyu yayi mata.
Bata taba tunanin akwai abinda zata yi mishi da zai iya yi mata godiya ba, sai gashi yau yayi.
A zuciyar ta har ta fara addu”a Allah yasa ya fara son ta ne, wata zuciyar kuma tace ya so ki? Hanifa fa?.
A daren ma kasa canza rigar jikinta tayi saboda qamshin turaren Aliyu da ya ke kan kayan wanda gaba daya kayan ya dauki qamshin kamar a bisa su aka fesa.
***********

A bangaren Aliyu ma bayan Dr Sadiq ya dawo ya duba shi ya tafi, yana jin su yusuf, Ammi, Hanifa da Nafisa suna ta hirar rashin lafiyar shi yayin da yayi kamar yana bacci, tunanin Aisha ne ya addabi zuciyar shi wanda yayi qoqarin kawar da tunanin amma ya kasa.
A bangaren Hanifa dai ta so tasa tunanin kallon da Aliyu ya dinga ma Aisha a ranta amma kuma sai ta watsar tunda dai tasan ba wani shiri suke yi ba.

**********

Washegari tun da safe Aisha ta kira Hanifa don jin yadda Aliyu ya kwana wanda sai a lokacin ne hankalin ta ya kwanta jin jikin nashi yayi sauqi sossai.
A yau dai ta qagara lokacin zuwan ta gidan yayi don ta ganshi.
A waya ne ta ba salma labarin abinda ya faru har Salman tana fadin kada ta fidda ran Aliyu zai so ta, ta cigaba da Addu”a.

**************

Yusuf a kullum tunanin shi shine yadda zaiyi idan aka fara yajin aikin da ake shirin yi a ma”aikatar su, qarshen tika-tiki tik domin dai yana zuwa ofis a yau ne aka ce kowa ya koma gida sanadiyyar yajin aikin da ma”aikatar ta fara.
A lokacin da ya dawo gida Nafisa tana gidan Ammi.
Kwanciyar shi yayi a daki domin yasan idan ya sake ya shiga gidan Ammin Nafisa na iya hana shi tafiya har lokacin zuwan Aisha yayi su hadu asirin shi ya tonu.
***************

Dukda Aliyu yaji sauqi iyakar shi falo.
Tun da safe ake ta kiran shi a waya ana mishi gaishe shi da jiki, ya amsa wayoyi har ya gaji ya bar ma su Nafisa da Hanifa suna ta amsawa.
STORY CONTINUES BELOW
Da ya koma daki don yin sallar la”asar ne bai sake fitowa ba, kwanciyar shi yayi a kan gado ya cigaba da kallon labaru.
Aisha dai ko da ta iso gidan taso ta gan shi amma inaaa, ta jira ta ga ko zai fito har suka gama abinda zasuyi da Hanifa amma bai fito ba, ashe shi yana can garin kallon labaru har bacci ya kwashe shi.
Ko da Ammi ta leqa shi sai da ta taba jikin shi domin ta ji ko jikin ne ya tashi, jin alamun lafiyar shi lau ne ta gyara mishi bargon da ya rufa da shi har tana fadin “yau wacce rana ka rufa da bargo saboda ciwo” bayan ta gyara mishi ne ta fita.
Aliyu dai bai farka daga bacci ba sai gab da magrib wanda yana farkawa yayi addu”ar tashi daga bacci ya kalli agogo yayi tsaki, miqewa yayi ya fita falo ya taras da su Ammi suna ta hira, ganin Hanifa da yayi a zaune ne ya tabbatar mishi da cewa Aisha ta tafi.
Juyawa yayi zai koma dakin shi sai ya ji Ammi na tambayan shi “babyna me kake so?” yace “ba komai Ammi” ya shige dakin shi.
Gaba daya Aliyu bai ji dadin rashin ganin Aisha ba a yau, yayi ma kanshi alqawarin Insha Allahu sai ya ganta gobe.

*****************

A bangaren Aisha ma ran ta a bace ta koma gida saboda rashin ganin Aliyu, har zagin kanta tayi akan me ya hana ta duba dakin nashi, wata zuciya tace mata ki ce mishi kin zo yin me? Tsaki tayi tana addu”ar Allah ya yaye mata sonshi daga zuciyar ta.
Ni kuwa nace anya???

**********

Washegari jikin Aliyu ya qara warwarewa domin a yau har ya duba saqonni a laptop din shi.
Bayan sallar azahar ne Ammi ta mishi maganan abinci wanda aka jera a kan dinning amma yace bazai ci ba, da ta matsa mishi ne yace “toh Ammi idan akwai fruit salad irin na shekaran jiyan nan zan sha”.
Ammi tayi shiru sannan tace “toh ai babyna wannan fruit salad din Aisha tayi shi, saidai mu ji idan Hanifa ta koyi yadda tayi shi sai tayi maka”.
Ammi ta kira Hanifa ta ce “kin iya fruit salad din da Aisha tayi ma Aliyu shekaran jiya?”
Hanifa ta dan yi shiru sannan tace “ai Ammi cikin sauri tayi don haka ma bata tsaya ta nuna mun ba”
Aliyu a ran ne yace “gaskiya bazan iya auren wannan yarinyar ba, she is not my type”

Ammi ce ta dauki wayarta ta kira lambar Aisha. A lokacin ma suna kallon cartoon ne ita da zaid. Ganin lambar Ammin ne tayi tunanin ko wani abu ya samu Aliyu ne.
Tana amsa waya ba tare da ta gaida Ammin bane tace “Ammi wani abu ya samu Aliyu ne?”
Ammi tana murmushi tace “lafiyar shi lau Aisha, gashi nan ma a gefe na” ajiyar zuciyar da Ammi taji Aisha ta saki ne ya bata mamaki.
Tambayar ta tayi “zaki zo anjima ne? Aliyu ne yake son shan fruit salad din da kika yi mishi shekaran jiya”
Cike da murnan jin maganar Ammi tace “insha Allahu Ammi, idan nazo zanyi mishi. Sai nazo” bayan sun gama wayar ne Aisha tayi ihun “Alhamdulillah”.
Zaid ne ya kalleta cikin mamaki yace “lafiya sis?” ta tashi zata tafi daki tace “kar ka damu zan baka labari”.
Shi kuma Aliyu haquri Ammi ta bashi akan ya ci abincin kafin Aisha tazo. Hanifa ce ta zubo mishi abincin ta kawo mishi, haka nan ya ci ba don komai ba sai don saboda hankalin Ammi ya kwanta.

***************

Bayan sallar la”asar Aliyu da Ammi suna zaune a falon qasa suna kallon labaru Aisha ta danna qararrawa, Hafsat ce ta bude mata, bayan sun gaisa ne ta shiga tare da yin sallama, jin muryarta ne yayi saurin maida kallon shi akan ta, sanye take cikin jallabiyya baqa, tayi bala”in yin kyau.
STORY CONTINUES BELOW
Aliyu bai taba ganin Aisha tayi mishi kyau ba kamar yau
(dayake dama a da ba kallon ta yake yi ba).

Haka a bangaren Aisha ma dukda yayi ciwo ya dan rame ya masifar yi mata kyau.
Da sauri ta mayar da idanuwan ta akan Ammi ta gaishe ta, ta amsa.
Ta dan kalli Aliyu shima ta gaishe shi wanda tayi mamakin yadda ya amsa normal ba kamar da ba da ko kallon ta baya yi balle ya amsa.

Tambayar Ammi tayi “Ammi ina Hanifa fa?”, Ammi tace “aikuwa tana gidan Nafisa”
Ta wuce kicin tana fadin “bari in hada fruit salad din kafin ta iso”
Aliyu dai bin Aisha yayi da kallo har ta bace mishi.
Ammi wadda ta lura da hakan tace “babyna yaya?” ya ce “nothing Ammi”.
A zahiri Ammi ta gane akwai wani abu da yake shirin faruwa tsakanin Aliyu da Aisha wanda da babu maganar Hanifa da ta fi kowa jin dadin al”amarin domin dai tana bala”in son Aisha tun daga ranan da ta fara ganin ta.
Yanzu haka Addu”ar ta daya kada Aliyu yace ya fasa auren Hanifa domin dai tasan ba qaramin aikin shi bane.
Ba da dadewa bane Aisha ta fito da fruit salad din a hannunta, Aliyu ya sa mata ido yayin da Ammi ta cigaba da lura da hakan.
Bayan ta zuba mishi ne ta miqa mishi, wurin karba ne har hannuwan su suka shafi juna wanda ita Aishan ta ji kamar yayi mata shocking.
Hanifa ce ta shigo tana fadin “Aisha yi haquri please, Anty ce ta tsayar da ni wallahi”
Aisha tace “ba komai Hanifa, lets go”.
Aliyu dai nan da nan ya shanye fruit salad din har Ammi na fadin “gaskiya yakamata Hanifa ta dage ta koyi irin wannan fruit salad din ko don saboda kai” shi dai bai ce komai ba domin ya ma riga ya fara tunanin fasa auren Hanifan.

Bayan ya shanye fruit salad din ne yace ma Ammi bari ya dan miqe qafa ko zuwa garden ne.

****************

Wuraren qarfe shida saura ne Aliyu ya dawo cikin gida, a lokacin Ammi da Nafisa suna falon sama.
Ko da ya shigo falon qasa babu kowa don haka ne ya wuce kicin domin dauko fresh milk a dalilin bakin shi da baya yi mishi dadi.
Hanifa ce tsaye a kan stool tana qoqarin dauko ma Aisha vegetable Oil yayinda Aisha ta dafe mata stool din wai don kar ta fado.
Aliyu ya iso kicin din yayin da yake kallon Aisha wadda ga dukkan alamu ta sa duka qarfin ta wurin riqe stool din.. Ya kula har cije baki take yi.
Abin har dariya ya bashi.
Qamshin turaren shi da ta ji ne ta dago fuskar ta. Ganin shi tayi tsaye yana kallon ta, anan ne itama ta sa mishi ido wanda har ta manta ta saki stool din, basu ankara ba sai gani suka yi stool din ya fara rawa da Hanifa a bisa.
Stool din ya tafi zai yadda Hanifa ne Aliyu yayi sauri ya janye Aisha daga wurin wanda yayi haka ne saboda kada stool din ya fado mata a qafa.
Tuni Hanifa ta fado qasa.
Ihun da tayi ne ya ankarar da su abinda suka yi, cikin kuka ne Hanifa tace “haba yaya Aliyu kana gani na zan fadi shine maimakon ka cece ni sai ka janye Aisha wadda take qasa?”
Aliyu dai kasa magana ma yayi domin shi kwata kwata ya ma manta da Hanifa

Aisha wadda ta cika da mamakin abinda yayi ne tayi sauri ta daga Hanifan tana yi mata sannu, ba tare da ya kalli Hanifa ba yace “sorry” ya wuce.
Aisha ce ta riqo ta har suka haura sama wurin su Ammi.
Ganin Hanifa tana ta kuka ne yasa hankalin su Ammin ya tashi, tambaya suka yi “lafiya?” Cikin kuka ne Hanifa ta basu labarin abinda ya faru wanda ita Aisha ta tayi shiru tana mamakin yadda al”amarin ya faru.
Su Ammi suka lallashe ta sannan tayi shiru.

Ammi tace “ko in kira likita ne yazo ya duba ki?” tace “no Ammi ai ban ji ciwo ba, kawai na dan bugu ne” anan ne Nafisa ta dan ja mata hannuwan ta tare da shafa mata ointment.
Bayan Nafisa ta shafa mata maganin ne Ammi ta dafa kanta tace “yakamata ki sha magani kada zazzabi ya rufe ki” Hanifa tayi murmushi tace “I am fine Ammi” Aisha ce ta taimaka mata ta kai ta dakin ta.
Ammi ta kalli Nafisa tace “akwai abinda ke faruwa tsakanin Aliyu da Aisha a “yan kwanakin nan domin na lura gaba daya Aliyu ya canza. A da ko ganin Aisha baya son yi amma kuma yanzu idan kin ga yadda yake sa ta a gaba yana kallo sai kin yi mamaki”
Nafisa tayi murmushi tace “nima nayi wannan tunanin Ammi musamman da naga wayar da ya siyo mata. Dukda nasan cewa Aliyu yana da halin kyauta, wayar da siyo ma Aisha ba qaramar waya bace musamman idan mun tuna rashin jituwan da ya shiga tsakanin su. Aikuwa idan dai sonta yake zaiyi wuya ya auri Hanifa saboda dai dama yace mata daya zai aura itama wadda yake bala”in so”

Ammi ta saki ajiyar zuciya tace “kin dai ga abinda ya faru yanzu ya qara tabbatar mun da akwai wani abu, idan ba haka ba me zai sa ya janye Aisha bayan ga wadda ke neman taimako”
Nafisa dai dariya ta dinga yi tace “Su Aliyu kenan, ya bi ya tsani baiwar Allah sai gashi kuma yanzu yana nema ya fara sonta”
Ammi tace “sonta ma yake, Allah dai ya zaba mafi alkhairi” cikin dariya Nafisa tace “Ameen”.
************

A bangaren su Hanifa dai Aisha ta dauki hutun sati daya a dalilin bikin qawarta Yusra da za”a yi sannan kuma ga faduwar da ita Hanifan tayi wanda da alama tana dan buqatar hutu.
Aliyu dai ko da ya shiga dakin shi kasa zama yayi. Gaba daya ya rasa gane me ke damun shi a game da Aisha. Yana cikin wannan tunanin ne Nafisa ta shigo don tsokanan shi.
Tambayar shi tayi “lafiya na gan ka a tsaye? Ko jikin ne?”
Komawa yayi ya zauna yace “i”m fine Anty Feena” kallon shi tayi tace “ya aka yi naji ance a gaban ka Hanifa ta fado baka cece ta ba sai ka janye Aisha wadda ba son ta kake ba?”
Miqewa yayi ba tare da ya kalle ta ba yace “ni kaina ban san ya akayi hakan ta faru ba”

dariya Nafisa tayi tace “ka tabbatar ba son Aisha ka fara yi ba kuwa?” da sauri ya kalli Nafisa yace “haba Anty, in rasa wadda zan so sai wannan marar kunyan?”
Miqewa tayi ta isa wurin shi tare da riqe hannun shi tace “Bros, kai ma kasan Aisha tana da hankali da natsuwa, gata kyakyawa ga iya girki sannan kuma gata mai dogon gashi irin wanda kake bala”in so, Idan ka san kana son Aisha gara ka fadi mata, dukda nasan cewa akwai Hanifa amma ai ba sonta kake ba, asali ma kana kallon abun akan auren dole za”a maka don haka kada ka bata lokacin ka, ka bi abinda zuciyar ka take so”.
Ta saki hannun shi ta juya ta fita.
Bin ta da Kallo yayi yana tunanin abinda tace mishi. shafa kan shi yayi da hannuwan shi biyu yace “ya salam, what the hell is wrong with me??”.
◇◇◇◇◇◇◇◇◇◇
Aisha dai ko da ta koma gida al”amarin Aliyu ya tsaya mata a rai, wani lokaci sai tayi tunanin kaman ya fara son ta wani lokaci kuma sai ta ga ba haka bane. Ko ma dai menene ta ji dadin yadda yake yi mata yanzu ba kaman da ba da ko kallon ta baya yi.+

Kwana biyu Yusuf ya samu sassaucin boyon da yake yi tunda Aisha bata zuwa. Yanzu tare da shi ake hira a falon Ammi.
Akwai ranan da suna hira aka dauko labarin Aisha, Nafisa ce tace “dear kai kadai ne baka san Aisha ba gaskiya yakamata ku hadu ku gaisa”

Yusuf yayi dariya wadda tafi kama da a kira ta yaqe yace “wata rana zamu hadu ai” wanda a ran shi yana Addu”ar kada Allah ya kawo wannan rana.

(hahahahahaha, ayi dai mu gani).

*************

An fara bikin Mansir da Yusra. Maigidan shi Aliyu ya bashi kyautar kudade masu yawan gaske na hidimar biki domin kuwa yana ji da Mansir din.
Ranar da aka daura auren a gidan su Yusra aka yi yinin biki, an sanya anko gwanin ban sha”awa amma fa banda Aisha. Dukda kuma ba wani gayu tayi ba duk inda ta bi sai an kalle ta saboda kyau da haske.
**************

Aliyu zaune a dakin shi tare da abokanen shi Bilal da Sulaiman wadanda suka sa shi a gaba suna bashi shawara akan ya sanya manyan kaya don halartar bikin dinner din Mansir.
Aliyu dai ko alama baya son manyan kaya don haka ne ya qi daukan shawaran su.
Ganin zai bata musu lokaci ne suka kira mishi Ammi, lokacin kuwa Nafisa da Yusuf suna gidan.
Gaba dayan su suka shigo dakin inda Ammi ke fadin “haba Aliyu, bikin dinner fa zaka je, kuma gashi bikin na ma”aikacin ka, idan ka je da manyan kaya za”a fi ganin girman ka ai, kayi haquri ka sa manyan kayan kaji baby na?”
Su Sulaiman suna ta mishi dariya jin Ammi ta kira shi babynta yayin da Yusuf ke fadin “banda abun ka ma ai dama da manyan kaya ake zuwa biki, suit kuma ai sai ofis”
jin kowa ya hau ne yasa yace “toh shikenan zan sa”
Ya miqe ya nufi wadrobe dinshi ya zabo wani farin yadi mai bala”in kyau domin dai ko a lokacin da yayi odan yadudukan wannan farin ya birge shi amma fa ba don ya sa ba.
Ya shiga dressing room ya sanya ya fito.
Yana fitowa ne Ammi tace “masha Allah yarona” su Bilal dai dariya suka dinga yi, Nafisa ce tace “aikuwa dai Hanifa tayi sauri ta same ka a wurin dinnan nan kada ayi mata snatching”
gaba daya aka fashe da dariya yayin da ta nufi wurin hulunan shi ta dauko wata Zanna Bukar mai kyau ta dora mishi a kai.
Nan da nan ya murtuke fuska tare da fadin “haba Anty feena gaskiya banda hula, ai nauyin sai yayi mun yawa”
gaba daya dariya suke ta yi mishi.
Yusuf ne yace “haba Aliyu, ai hula ita ce mahadin manyan kaya. Meye abun nauyi anan banda abinka. Please ku tashi ku tafi kafin kuyi latti”
Bayansu Ammi sun fita ne Aliyu ya tsaya gaban madubi ya dan yi murmushi yace “not bad”, Suleiman ne yace “Allah dai ya kiyaye kada Hanifa ta sha qasa” dariya Bilal yayi yayinda Aliyu yayi murmushi ya fesa turare wanda nan da nan wurin ya dauki qamshi.
**************

Sabuwar mota qirar Mercedes Benz baqa wuluk Aliyu ya dauko wanda shi da Bilal ne suka shiga yayin da Suleiman ya shiga tashi wadda suka zo da ita.

STORY CONTINUES BELOW
Ita dai Hanifa ta je gidan wata qawar ta wadda ta gayyace ta birthday party dinta ne, sun shirya akan idan ta baro partyn zasu hadu da Aliyu a wurin bikin. Wannan ne ya sa Aliyu bai tafi tare da ita ba.
Ango da amarya sun iso harabar yayin da qawayen amarya da abokanen ango na tsatsaye suna jiran su.
Daga cikin mota ne Yusra ta kira Fiddausi tana tambayan ta Aisha, Fiddausi tace “mun rabu da ita akan zata koma gida wai ta manto takalmin da zata sa amma nasan yanzu zata iso”.
Motar Aliyu da ta doso harabar ne “yan mata suka mayar da kallon su gaba daya kanta, motar ta masifar birge mutane (kun san Aliyu da son mota, motar ma latest) yayinda kowa ya qagara ya ga wane hamshaqi ne zai fito daga motar dayake tint ce.

Tun a cikin motan ne Bilal yake fadin “mutumina kallo fa ya dawo kan ka, kaga yadda “yan mata suka danna ma motar ka ido kuwa?”

Tsaki yayi tare da fadin “wallahi abokina saboda Mansir na zo wurin nan, amma banda haka babu abinda zai sa ni zuwa inda mata zasu taru haka” dariya Bilal ya dinga yi.
Suna fitowa daga motar ne hankulan “yan mata ya tashi a dalilin ganin hearthrobe din su, Aliyu Muhammad kankia. Wasu dayawa sun san shi, wasu kuma labarin shi suke ji.
Duk inda ka wuce labarin shi kawai akeyi ana nuna shi.
Kai tsaye motar amarya da ango suka nufa yayin da Mansir din ya bude qofa yana shirin fitowa, Aliyu ne ya dakatar da shi tare da fadin “haba ango yi zaman ka, ai yau ranar ka ce sai yadda kayi da mu” gaba daya wadanda ke kusa da su suka yi dariya, bayan sun gaisa ne Yusra ma ta gaishe su, suka amsa.

Mai gabatar da taron ne ya ba amarya da ango izinin shigowa domin gaba daya su ake jira a cikin hall din.
Su Aliyu suka wuce suka shiga hall din kafin shigowar amaryar da angon.
Kujerun da aka nuna ma su Aliyu ta VIP ce, bayan sun zauna ne amarya da ango suka shigo tare da qawayenta da abokanen shi a jere suna biye da su. Har yanzu dai babu Aisha babu alamar ta, Fiddausi ta neme ta a waya bata samu ba.

************

A wannan lokacin Aisha tana can gida tana jiran Zaid wanda ya fita da mota. Yayi mata alqawarin dawowa da wuri don ya kai ta bikin amma kuma gashi har yanzu shiru.
Sanye take cikin wata doguwar riga zubin dinner gown sky blue an bi ta da kwalliya duwatsu silver wadda akayi fitting dinta daga sama yayin da ta bude daga qugu, Aisha ta zabi wannan kalar ne domin dai ankon Yusran leshi ne sky blue da raw silk silver.
Ta nada gyale a kanta yayinda ta fito tamkar balarabiya.
Banda lip gloss da ta shafa a bakinta bata shafa komai a fuskar ta ba, ta bala”in yin kyau dukda bata yi kwalliyan ba. Wani takalmi tasa silver mai kyan gaske, ga tsawo.
Ta feshe kanta da turaruka ta tsaya a gaban madubi tana qare ma kanta kallo, ita kanta tasan ta hadu.
Tsaki tayi tace a fili “yanzu kuma mutum yaje ayi ta kallon shi”.
Falo ta wuce inda ta samu Inna tana kallo, Innan ce tace “kin ko yi kyau matar Yusuf, yarinya son kowa qin wanda ya rasa”
Aisha ta bata rai tace “Inna ban dai riga na zama matar tashi ba” dariya Inna tayi tace “ahap, an dai kusa” Zaid ne ya kira Aisha a waya inda yace mata ta fito yana waje.
Bayan tayi sallama da Inna ne ta fita.
Zaid kuwa yana ganin ta yace “kai sis anya bazaki fi amaryar haduwa a wurin ba kuwa??”

Hararar shi tayi tace “dukda nayi dressing simple din? Muje don Allah kada ka qara bata mun time, nayi latti”
Dariya yayi ya tada mota tare da fadin “yau dai Yusuf zai sha wuta” wannan karon itama dariyar tayi.
STORY CONTINUES BELOW
Ko da suka isa ce mishi tayi zata kira shi idan an gama.

**************

A wurin bikin kuma mai gabatarwa yana ta wasa amarya da ango yayinda yake ta sa mutane dariya. Aliyu dai yana ta latse latsen shi da ya saba a waya yayinda hankalin “yan mata kaf yake kan shi.
Su Bilal sun lura da hakan, Suleiman ne ya kalli Aliyu yace “mutumina a dalilin ka dai munyi kasuwa, ina ga kafin taron nan ya watse zaka cike ma Hanifa sauran” dagowa yayi cikin rashin fahimta yace “sauran me?”
Bilal yayi dariya yace “kishiyoyi” murmushi yayi yace “Allah ya rufa mun asiri, ita kanta Hanifan ya zan qare da ita balle in qaro wasu”.

Hasken da ya bayyana a bakin qofa ne ya dawo da hankalin kowa wurin, Ba wata bace ta shigo illa Aisha wadda ta tsaya cak saboda razana da tayi.
Wannan shirin Yusra ne da Fiddausi wanda suka shirya cewa idan Aisha ta shigo a haska ta da hasken spotlight don su ga reaction din Aliyu .
Aikuwa dai daga kan shi da yayi ne ya ga fuskar Aisha wadda tayi masifar kyau, bai san lokacin da ya ajiye wayar shi ba akan tebir.
Bilal ne ya yi ma Sulaiman signal da ido akan ya kalli Aliyu, suka fashe da dariya yayin da Bilal yace “wannan ba yarinyar nan bace wadda kuka yi rigima da ita a ofis Aliyu?”
kwata kwata Aliyu bai ji shi ba har sai da Suleiman ya dan taba shi sannan ya dawo da kallon shi garesu yace “me kace?” dariya suka sake yi yayinda Bilal yace “cewa nayi har ma an samu wadda ta ture Hanifa kwata kwata”
Wayar shi ya dauka ba tare da fadin komai ba ya cigaba da latse latsen shi domin dai shi kanshi ya zama confused.
Dariya suka cigaba da yi mishi.
Mai gabatarwa ne yake ta wasa Aisha har yasa ta dan yi murmushi.

A lokacin da ta fara tafiya ne Aliyu ya sake dawowa ya kalle ta, wannan karon sai da zuciyar shi ta motsa, a cikin ran shi ne yake fadin “subhanalillahi, why is she so pretty??”

Juyawa yayi ya hango yadda guys ke ta kallon ta wanda duk ya ji bai ji dadi ba.

Aisha ta qaraso table din su Fiddausi tana ta mata masifa wadda ita kuma take ta mata dariya, Aisha ce tace “haba fiddausi wannan wane irin wulaqanci ne zaku sa a haska ni cikin mutane?”
Janyo hannun Aishan ta zauna sannan tace “saboda Aliyun ki” cikin mamaki Aisha tace “wane Aliyun?” tace “wanda kike mutuwar so”
A rude tace “ina yake don Allah?” fiddausi tayi dariya tace “bazan nuna miki shi ba saboda yanzu haka ke yake kallo idan kuma so kike ku hada ido toh” Aisha ta saki ajiyar zuciya tana tunani.

Biki yayi nisa, an ci an sha anyi rawa. Aisha tana zaune a kujerar ta ne samari suka dinga sintirin zuwa yi mata magana, kwata kwata ma ko kallon su bata yi balle ta amsa su. Akan idon Aliyu hakan yake ta faruwa inda ran shi ya bala”in baci har Bilal na fadin “mutumina gayu sun tasar ma mutuniyar ka fa”

Sulaiman yana ta dariya yayin da yace “ni na rasa me tayi ma Aliyu da har basu shiri, kuma wallahi ya fi dacewa da ita akan da Hanifa” ba tare da ya kalle su ba yace “rashin kunya tayi mun amma ta gyaru” Bilal yace “toh zaka taya kenan?”
Kafin yayi magana ne kiran wayar Hanifa ya shigo, ya amsa tare da fadin “where are you?” tace “wallahi ina gida yaya, na gaji ne kuma nasan an riga anyi nisa a dinner din, bazan iya zuwa ba please ka ba Mansir haquri on my behalf” yace “shikenan sai na dawo” ya kashe wayar.
Gaba daya zaman wurin ya ishi Aisha yayinda duk ta kasa samun natsuwa, har yanzu bata ga mutumin nata ba Aliyu.
Da qyar ta bi Fiddausi wurin amarya da ango inda suka dauki hotuna, lokacin da zata dawo kujerar ta ne ta hango Aliyu wanda yayi mata bala”in kyau, bata taba ganin shi da manyan kaya ba sai yau.
Haka kuma bai taba yi mata kyan da yayi a yau ba. A daddafe ta koma kan kujerar ta tana ta sauke numfashi.
Su Bilal da Sulaiman suka matsa ma Aliyu akan su je suyi hoto amma sam ya qi, ce musu yayi su je kawai. Sun tafi daukar hoto kenan “yan mata suka fara kai gaisuwa wurin Aliyu, tun suna bashi mamaki har suka fara sa shi dariya ma.
Aisha wadda ta kafa mishi ido ganin yana dariya ne tayi tunanin ko matan sun birge shi ne.
Nan da nan ta kifa kanta a kan table ta fara kuka yayinda zuciyar ta take ta tafasa da tsananin kishi. Dawowar su Bilal ne ya samu sauqi.
Aliyu ya lura da Aisha wadda ta kifa kanta bisa table, yayi mamakin dalilin ta na yin haka.
Wata zuciya ce tace mishi ko bata da lafiya ne? Nan da nan hankalin shi ya tashi.
Fiddausi ta so ta je wurin ta don ganin abinda ke faruwa amma Yusra ta hana ta saboda ganin yadda Aliyu yasa mata ido.
Aliyu dai da ya kasa jurewa ne yace ma su Bilal “ni fa zan tafi saboda dare yayi kuma manyan kayan nan sun ishe ni” dariya sukayi suka miqe, Suleiman ne yace “gaskiya dare yayi”.
Bayan sunyi ma Mansir sallama wanda Aliyu ya ba Mansir haqurin rashin zuwan Hanifa ne suka kama hanyar fita.
Aliyu ya ja baya tare da ce musu “ku je kawai sai mun hadu gobe” fashewa suka yi da dariya suka tafa, Bilal ne yace “best of luck mutumina, kun dace wallahi” murmushi yayi kawai ya koma.
Qamshin turaren shi da ta ji ne tayi saurin dago kan ta.+
Zaune ta gan shi a kan kujerar dake gefenta yayin da yake ta latsa wayar shi.
Aisha dai har murza idanuwan ta tayi don tabbatar da abinda take gani.
Su fiddausi ne suka tafa hannu tare da fadin “yess” wanda har Mansir ke tambayan su “lafiya?” Yusra tace “ba komai” yayin da Fiddausi ke ta dariya.
Cikin mamaki muryar ta na rawa tace mishi “ina wuni” ba tare da ya kalle ta ba yace “if you are done crying tashi mu je in kai ki gida”
Gaba daya ta rude da jin abinda yace, da qyar ta saita muryar ta tace “i”m not crying” dagowa yayi ya kalle ta yace “whatever, tashi mu je” jikin ta na rawa ta miqe ta bi bayan Aliyu har suka fita daga hall din ba tare da ta waiwayi qawayen ta ba.
Dariya kawai Yusra da Fiddausi sukayi.
Gaba daya “yan matan da suka sa ma Aliyu ido ji sukayi kaman su bugi Aisha domin a kan idanuwan su Aliyu ya taka zuwa wurin ta ya zauna sannan suka bar hall din tare.
Haka ma”aikatan kamfanin shi da suka halarci bikin suma sunyi mamakin ganin Aliyu tare da Aisha wanda kowa yasan yadda ta sha wahala a hannun shi.

Tun kafin su iso wurin motar ne ya danna makullin motar tayi “yar kara, alaman an bude ta. Abun mamaki har zagayawa yayi ya bude mata qofar ta shiga sannan ya zagayo shima ya shiga.
Gaba daya motar ta birge ta, banda lafiyayyen qamshi babu abinda ke tashi. Yana kunna AC nan da nan motar ta dauki sanyi.
Suna kan hanya ne ya lura har yanzu tana ta goge hawayen fuskarta, ganin haka ne ya faka gefen titi ya kunna wutan motar.
Juyowa yayi yana kallon kyakyawar fuskar ta yace “why are you crying?”
Da sauri ta kalle shi wanda gaba dayan su sai da tsigar jikin su ya tashi, da qyar ta iya fadin “wani abu ne ya shiga idona”
Fuskar ta ya dago wanda ya sa dukkan jikin ta ya fara kyarma, ya buda idanuwan nata sannan ya fara hurawa.

Yanzu dai suma ne kawai bata yi ba don dai gaba daya jikin ta ya mutu.
Tambayar ta yayi “ya fita?” daga mishi kai kawai tayi domin ta kasa magana.
Hankicin shi ya fiddo ya goge mata fuskar ta yace “yanzu saboda wani abu ya shiga idon ki shine kike ta kuka? maimakon ki ba wani ya hure miki?” a ranta tace “aikuwa gashi nayi sa”a ka hure mun”.
Bayan ya tada motar ne suka cigaba da tafiya, Motar tayi sanyi sosai wanda har Aisha ta fara kyarma, amma ta lura shi Aliyu kwata kwata baya jin sanyin.
A zuciyar ta ne tace “ikon Allah, shi kam ya saba da irin wannan sanyin, shiyasa gidan Ammi ko wanne lungu akwai AC”.
Ba tare da ya kalle ta ba ta ji yace “you looked beautiful when you came into the hall dazu, gashi kuma kinyi kuka duk kin bata kwalliyar”
har cikin zuciyarta ta ji dadin maganar da yayi mata

Kai tsaye tace “ai dama ban yi kwalliya ba, bana ma yin kyau idan na yi” sai yanzu yayi tunanin fa lallai bai taba ganin ta da kwalliya a fuska ba, a ran shi ne yace “Ya salam, she is a natural beauty”
murmushi yayi tare da fadin “naga ma har sabon saurayi kika yi a wurin bikin” zaro idanuwa tayi cikin shagwaba tace “ni babu wanda nayi ma magana a cikin su” ajiyar zuciya ya saki tare da jin dadin maganarta.
STORY CONTINUES BELOW
Kallon shi tayi tace “kai ne dai naga kaman kayi ma Hanifa kishiyoyi” maimakon yayi magana sai kawai yayi murmushi wanda ya bata ma Aisha rai domin a tunaninta ya samo wata ne shiyasa yayi murmushi. Daga nan bata qara kallon gefen shi ba har suka iso gida.
Ko kallon shi bata yi ba ta bude qofa tare da fadin “nagode” ta wuce.
Murmushi kawai yayi ya bi ta da kallo har ta shiga gida sannan ya ja motar shi.

***************

Aisha tana shiga gida Zaid ya biyo ta yana fadin “ya akayi baki kira ni in zo in dauke ki ba da aka gama dinan? Ko dai kin samo sabon saurayi ne?” murmushi tayi tace “me ya ruwanka? Kaidai ba ka huta ba?” bayan ta gaida Inna ne ta wuce daki yayin da Zaid ya bi ta.
Tsare ta yayi yace “sis ni na san akwai abinda ya faru don haka ki bani labari kawai”.
Tsakanin Aisha da Zaid babu wani abinda suke rufe ma juna, don haka ne ta zaunar da shi ta bashi labarin abinda ke tsakanin ta da Aliyu a yanzu da kuma bala”in son da take mishi.
Zaro idanuwa yayi yace “yanzu ya zaki yi da Yusuf?”
tsaki tayi tare da hararar shi tace “kai ina maka maganan mutumin da ya mamaye zuciya ta kana kira mun wani Yusuf, go jor” dariya yayi yace “yi haquri sis, amma dai daga dan labarin nan da kika bani ina mai tabbatar miki da cewa shima yana son ki, just wait and see”
Aisha dai murmushi tayi tare da fadin “Allah ya sa” yayi dariya yace “ameen”.

************

Fiddausi ta kira Aisha a waya tana ta yi mata tsiya akan ta qi zuwa kwana gidan amarya ta bi masoyi.
Aisha wadda take ta dariya tace “yi haquri qawa ta, ko sallama ban yi muku ba, yanzu zan kira Yusra in bata haquri, gobe tun da asuba zan zo”.
Fiddausi tace “toh dama ina zaki yi mana wata sallama bayan kina tare da sweetheart dinki? Kin kuwa ga yadda mutane suka dinga kallon ku??”
Aisha ta fashe da dariya tace “wallahi Fiddausi ban taba tunanin cewa ya gan ni ba balle har ya zo ya nemi kai ni gida, kin fa san ko kallon inda nake baya son yi”
Fiddausi tayi dariya tace “a da kenan, amma a yanzu dai kam duk motsin da kika yi idanuwan shi suna kan ki, sai kin ji yadda “yan mata suke ta maganar ki”
Dariya Aisha take yi yayinda tace “I am soo happy I caught his attention. Bala”in son shi nake dukda aure zai yi. gabadaya na kasa cire shi a raina”
Fiddausi wadda ta tausaya ma qawar ta tace “shima yana son ki Aisha, its just a matter of time trust me, kwanan nan zai fito fili ya fadi miki, but tell me something, me ya faru dazu kika kwantar da kanki bisa tebir da har ya zo wurin ki baki sani ba?”
Aisha ta saki ajiyar zuciya tace “wallahi Fiddausi gani nayi mata suna ta zuwa wurin shi kuma na ga har murmushi yake yi musu shiyasa na ji haushi na fara kuka”
Fiddausi cike da mamaki tace “kuka Aisha?? Like seriously?? Lallai kam a gaishe ki da kishi”
Aisha tace “fiddausi ba laifi na bane, son shi nake kuma bana so in gan shi tare da wata, wani lokaci idan na tuna aure zasuyi da Hanifa duk sai in ji haushin ta”
Fiddausi tace “kar ki damu Aisha, Aliyu zai so ki fiye da yadda kike son shi Insha Allah”
Daga nan dai suka cigaba da hira har suka yi sallama.
Ta kira Yusra ta bata haquri wanda ita Yusra ma bata damu ba domin kuwa ta ji dadin abinda ya faru tsakanin ita Aishan da Aliyu.

************

Bayan an gama bikin Yusra ne Aisha ta cigaba da zuwa gidan Ammi wanda ita Hanifa har yanzu babu wani abun kirkin da ta koya a dalilin rashin mayar da hankali.
STORY CONTINUES BELOW
Shi kuma Aliyu yana ta shiga rudani akan tunanin Aisha da yake yawaita yi wanda har ta kai ga idan bai ganta ba na kwana daya hankalin shi tashi yake, a yanzu ma saboda Aisha yake dawowa daga ofis da wuri ba don komai ba sai don ya ga fuskar ta.
A bangaren Aisha itama kullum qagara take yi ya dawo don ta gan shi, dukda ba Magana suke yi ba amma dai ganin juna da suke yi kawai yana sa su farin ciki marar misaltuwa.
A yanzu haka kullum sai tayi mishi fruit salad wanda ta lura yana bala”in so, dukda ba ce mata yake ta mishi ba amma tunda ta lura yana son shi kawai sai tana yi mishi kullum wanda shi kuma baya gajiya da shan shi.
Dayake Aisha da Hanifa sukan je gidan Nafisa idan sun gama abinci sai Yusuf ya tsirfo qaryan zuwa library na Kaduna da sunan yana bincike akan wani Project da zasu fara idan an gama yajin aiki a ofis dinsu, ba don komai yayi hakan ba sai don kada Aisha ta gan shi.

***********

Wata Juma”a ne Mustapha yazo Kaduna. A ranan yana gidan ne Aisha tazo.

Tambayar Ammi tayi “dama Aisha tana zuwa gidan nan ne?” Ammi tayi dariya tace “eh wallahi, tana koya ma Hanifa girki ne. Kana nan ai mutumin naka ya bada sharadin zai aure ta amma sai ta koyi girki”
Mustapha ya fashe da dariya yace “ai Aliyu akwai principles, itama dai Hanifa don dai tana son shi ne amma sai in ga kaman ba halayyar su daya ba. Toh wai ya ma akayi ya bari Aisha take koya mata bayan basu shiri?”

Ammi ta tabe fuska tace “ni ina ma gani kaman son Aishar yake yanzu” aikuwa Mustapha yayi dariya sosai sannan yace “wallahi Ammi yarinyar ta dace da Aliyu, don dai Hanifa “yar uwa ta ce amma da sai in ce gara ya auri Aisha kawai”
Ammi tace “ni ma na so ma Aliyu ita wallahi amma Allah baiyi ba”.
Suna cikin hira ne Aliyun ya dawo daga ofis. Nan ya zauna suka shiga hira inda Aliyu yace ma Mustapha “haba mutumina shine ko kace mun ka iso?”
Mustapha yace “yi haquri, wayoyi na ne suka mutu wallahi”.

*************

Aliyu zaune da Mustapha a dakin shi suna hira. Mustapha yace “mutumi na kazo muje gaida sirikai na gobe mana” yace “yaushe ka samu mata ban sani ba? A ina take??”
Mustapha yayi dariya yace “Katsina” murmushi Aliyu yayi yace “kace “yar gida ka samo mana, hope dai kai ka gani kace kana so?” dariya sosai Mustapha yayi yace “haba mutumina, ni na gani nace ina so. infact ka ma san ko wacece. Yayar Aisha ce… Salma”

kallon shi yayi yace “dagaske?” Mustapha yace “kaima ai naji ance ka fara son qanwar, dagaske ne?”
Shiru yayi bai ce mishi komai ba.
Mustapha yayi dariya yace “wallahi kai miskilin mutum ne na qarshe. Wato dai har yanzu a rayuwa bazaka taba iya ce ma mace kana sonta ba, kuma kai baka son su ce suna sonka, toh zauna nan har son nata ya kashe ka” ya dauki waya yace “bari ka ga yadda ake yi”.
Lambar Salma ya kira suka fara hira yayin da ya bar Aliyu yana tunani wanda a qarshe ma tashi yayi ya bar mishi dakin.

**************

Aliyu dai ya amince zai raka Mustapha wurin sirikan nashi domin dama akwai meeting din da zaiyi da ma”aikatan shi a katsinan, dukda dai a da sati mai zuwa yayi niyyan zuwa amma a dalilin matsa mishi da Mustapha yayi ne akan dole ya amince.
**************

Tun kafin su bar kaduna Mustapha ya sanar da Salma zuwan su shi da Aliyu. Sunyi akan bayan sallar Isha”i zasu zo.
Wuraren qarfe sha biyu na rana suka isa Katsina inda suka wuce gidan su Mustapha. Mummy tayi murnan ganin su, har tana tsokanan Aliyu tana fadin “angon Hanifa yaushe ne bikin?” Aliyu dai babu alamun fara”a a fuskan shi yace “mummy ba yanzu ba, sai Mustapha yayi sannan”

Mummy tace “maimakon a hada kawai da na Mustaphan?” Mustapha ne yace “ai Mummy ki bar miskilin nan kawai inda kika ganshi, shi kanshi a rude yake, he doesn”t know what he wants”
miqewa Aliyu yayi yace musu “bari in je in dan huta kafin azahar, meeting dina qarfe biyu ne” Mummy tace “kaidai kawai ka gudu saboda ka ji anyi maganar Hanifa, ni na rasa gane wannan irin aure da za”a yi” Mustapha dai har yanzu dariya yake yi.

****************

Salma ta kira Aisha a waya ta gaya mata su Aliyu zasu zo duk ta bi ta rude.

Aisha tace “Ummi dama ina nan wallahi” Salma tace “idan kina nan me zakiyi? Ko zaki gaya ma Abban cewa kina son Aliyu ne?”

dariya kawai tayi tace “Ummi bazaki gane bane, wallahi son da nake mishi ni na tabbatar Hanifan ma bata mishi rabi”.
Salma tace “ga wanda ke son ki kin qi, kina son wanda bai san kina yi ba” jin haka ne Aisha tace “toh ni dai mu bar maganan, idan sun zo anjiman ki dan gaya mun please” cikin mamaki Salma tace “toh gimbiya”.
Bayan sunyi sallama ne Salma ta cigaba da mamakin Aisha da irin son da take ma Aliyu har tana fadin “Allah yasa ya so ki sis”

*************

Bayan sallan Isha”i ne su Mustapha suka iso gidan su Salma a cikin wata sabuwar motar Mustapha qirar Honda accord baqa.
Salma tayi musu jagora har cikin falo, bayan sun gama gaisawa ne ta dauko kayan ciye ciye ta ajiye musu sannan ta sanar da su Abba bai dawo daga masallaci ba amma yanzu zai shigo, ta shiga ta sanar da Umma zuwansu.
Da Umma ta leqo don su gaisa gaba dayan su sai da suka durqusa har qasa sannan suka gaisheta ta amsa, a yanzu ne Aliyu ya gano inda Aisha ta debo kamannin larabawa har ta zarce.
Umma bata dade da komawa ciki bane Abba ya shigo cikin sallama suka amsa, shima har qasa suka durqusa suka gaishe shi. Cikin fara”a ya amsa yace “ku tashi ku zauna a kan kujera mana” Mustapha yace “babu komai Abba nan ma yayi”.

Abba yayi murmushi yace “toh waye Mustapha?” Aliyu ya nuna Mustapha tare da fadin “ga shinan Abba” yayin da Mustaphan yake murmushi. Abba yace Masha Allah, kai kuma ya sunan ka?” Aliyu ya fadi mishi yayinda Abba yace “toh Allah yayi muku albarka” suka amsa da “ameen”.

Salma dai tana daga daki tana sauraron hiran su Abba, tun su Mustapha basu sake da Abba ba har suka zage suna ta hira, sun fada ma Abba taqaitacen tarihin su da dangantakan su wanda a cikin hiran ne Abba ya gane daga gidan da suka fito domin kuwa iyayen su sanannu ne musamman mahaifin Aliyu lokacin yana raye, sannan shi kanshi Aliyun babu wanda bai san kamfanonin shi a arewacin Najeriya ba.
Abinda ya birge Abba shine natsuwan su wanda ya tabbatar mishi da cewa “yar shi Salma bazata fada hannun sakarai ba.
Salma ta kira Aisha a waya ta sanar da ita abinda ke faruwa, Aisha tana ta murna ba don komai ba sai don Aliyu ya je gidan su.

Da su Mustapha zasu tafi ne suka karbi lambar wayar Abba akan zasu dinga gaisawa, har Abba yana ce ma Aliyu yayi qoqari ya nemi mata shima yayi aure kamar dan uwan shi, Aliyu ya yi mishi godiya sossai.
Abba ya kuma ba Mustapha izinin turo magabatan shi kamar yadda shi Mustaphan ya roqa don shirya maganan aure.

***************

Bayan sati daya ne aka je neman auren Salma a gidan Abba wanda harda Baba daga Kaduna ya halarata.
Su Abba sun mutunta sirikan nasu wanda Daddy ya ji dadin hakan matuqa.
An tsayar da magana akan nan da sati biyu mata zasu zo domin sa rana da kuma kawo lefe.

◇◇◇◇◇◇◇◇

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *