TAGWAYE
CHAPTER 19
Dasassafe Miemah tabar gidan makwabciyar ta’su, bayan tayi Sallah Rana ta dan fara bayyana tafito ba’kin hanya tana tambayar mutane koda akwai wanda
yasan cikekken labarin abunda yafaru a gidansu har zuwa yedda aka sinci gawan Lawan (Mai Gadi). Wani Matashin saurayi
ne yafad’a mata cewa babu shakka aranarda abun yafaru misalin karfe Sha biyu sunji ‘karan bindigogi sedei dashike daman garin zaman lafiya bata ishesaba babu wanda yafito bare ai tunanin taimakamusu.
“Kenan kana nufin Garayi ne suka shigo gidan? Miemah ta ‘kara tambayansa Kai tseye ya girgiza kai yanacewa” Tohh Wallahu A,alamu babu wanda yatabbatar da hakan, kuma idan kina anfani da kwakwalki Zaki
iya fahimci cewa idan barayi ne suka shigo meyesa masu gidan suka gudu a tsakar dare.
Tabe baki Miemah tai sannan tagode masa, daga nan gidan nasu tawuce, nan dei inda tasaba zama a bakin kofan backyard na gidan tazauna tanabin abundake faruwa cikin gidan
da kallo tareda littafinta da biro a hannu sabida idan takalli hujjoji tarubutosu domin tasamo isassun hujjojinda zata bayyana agaban kotu….
****
Miemah bata tashi daga wajenba, nan take Sallah kuma nan take sayan abinci tana Ci saidai idan tahango yan Sanda sai ta boye kanta. Cikin wannan yanayin take har zuwa Magriba ba’tareda ta’samo wata hujja ba,
k0 a ina hotunan Mahaifinta aka mammanna ana nemansa ruwa
a jallo.
Ta rasa yadda zatayi tataimakawa iyayenta, ita kad’ei ce suka mallaka Kuma babu wandake taimakamata, ba‘a damu da damuwarta ba, uwa uba kuma babu wanda yadamu da lafiyarta. sai Kawu Sambo shima ya tafi harkokinsa a kasar Amurka, Yanzu batada wani gata aduniya, Allah shine Gatanta.
A wannan lokacin babu abinda take sai kuka da takaici gatada mura ga sanyi gakuma tsauro duk sun hade mata saidei batayi kasa a guiwa wajen neman hujjojinta ba haka tacigaba da zama tana expecting evidence masu ‘karfi cikin Daren.
Wata ‘Kauye chan!, Saminu yakoma tareda Matarsa, inda ya dan hada musu Gidan ‘kara da ciyawi, dashike ya iya irin wannan gidajen tun suna almajiranci. Tinda suka dawo Aisha batada wata sana‘a sai kuka da mamaki domin rasa abindake faruwa da Mijin nata tai, ta rasa gane dalilinda yasa Saminu yake irin wannan gangancin da rayuwarsa, kawai sabida wata Yarinya wacce ba jinin saba, Y’ar d’an uwansa wacce k0 isashshen tarbiya batada ita bare yace Yar tanada hankali. Wannan wace irin jaraba ce da jarrabawar da Allah Yakeyi akansu.
Cikin wannan yanayin take har zuwa safiya Saminu ya sha barcinsa isassu masu kwanciyar hankali da nishad’i, Aisha k0 idanuwarta gar suke ta ‘kasa barci, tana tsoron dajin dasuke,
dakuma gidan ‘kanta gani take tamkar zata fadi akansu, dashike bata taba rayuwa cikin irin gidaje hakaba sedei tagani a TV,. A kwance take shiruu… Bayan tayi Sallan asuba, tinda suka taho basuyima juna maganaba har zuwa yanzu da Saminu yafita cikin daji domin yanemo musu ruwa.
Kwata kwata ran Aisha ta’kasa kwanciya, tunanin Miemah take sosai, hankalinta ya’kasa kwanciya ji take tamkar diyarta tana cikin mawuyacin Hali na nemansu. Wannan tunanin yasa tabude jakar Saminu asulale tazaro wayarsa ahankali tai bayan gida nan ta kunna wayar atsorace tasa layin diyarta,
aiko tayi sa’a nan da nan ‘Kiran tashiga sedei tayita ringing babu amsa haka tacigaba da gwadawa
tanakuma leke leke kada Saminu yashigo ya tsameta …..
*****************************
Ta’koma gidan makwabciyarsu kamar yedda ta’saba takwana duk dashike idanuwarta gar suke har izuwa wayewar gari, batayi gengediba bare barci, Kuma ta yanke shawara gobe da yardan Allah zataje Kotu, walau ta’samo hujja k0 bata samuba haka zataje tagabatar da kanta, Kila ko Iyayenta zasu bayyana idan tayi hakan.
Tama ‘kosa gari yawaye, tana Sallan Asuba tai wanka kamar yedda ta’saba tafito, ta’kara zuwa ba’kin kofan gidansu k0 akwai abunda zata samo kamin taje kotu, sedei kamar kullum babu abinda ta’samo haka tai giving up, jiki a sanyaye tajuye zata tafl kenan taji ’kara kamar
waya ce take ringing, Kai tseye taduba wayarta taga ba itabace, nan tashiga neman wannan wayar dataji yake ‘kara, tanabin sautin har tashige ciyawi se k0 tahangota Chan iPhone ce mai Kyau awajen, da dukkan alamu fad’uwa tai ba’tareda sanin
Mai itaba. Miemah tanazuwa wajen wayar tafara ‘kara bata dagaba, dannawa tai kutun takai silent ba’tareda ta’san wandake kirantaba. Da Bismillah ta d’auki wayar dake cikin ciyawi tana kunnata taga message aka turo cewa; Kada ku dade agidan, amma ku tabbatar kun anso mata kudadenta dedei yedda na umarceku ga addreshin gidan nan…. make sure you did the right thing.
Miemah tana ganin addreshin gidansu zuciyarta ta buga “Inna
lillahi wa Inna ileihi rajiun’ abunda tafad’a kenan sannan tasa wayar cikin jaka takama hanyarta.
************************
Umma (Aisha) ta’kira layin Miemah ta’kai sau Goma babu amsa, haka tacire Rai tazauna awajen takama kuka tamkar a mafarki taji wayan tana ringing tana d’agowa kuwa lambar diyartata tagani dasauri tasa a kunne “Miemah Umma ce ya kike? Kuka Miemah tasaka cikin sananin damuwa tace’ Umma a Ina kuke dan Allah kudawo ina Maiduguri Kuma nayi kwana uku ina neman hujjojinda zata bayyanawa Kotu cewa bakuda hannu wajen ‘kisan Lawan Mai gadi duk dacewa banida wata hujja Mai ‘karfi, Amma akwai wayarda na tsinta a bayan
gidanmu zata iya zama hujja akan case d’in naku dan Allah kudawo. Umma ina shan wahala anan babu wandake kuladani…
Bata ‘karasa kalamantaba Umma ta katseta, tana hawaye tace” Muna nan lafiya a ‘kauyen mai riga bayan babban gonan auduga Yata karki damu damu don Allah kikoma gidan kawunki kicigaba dazama achan you are too young to go through all this my dear.
“Umma wallahi bazan koma
ba, har se na gano wannan makiyin namu wanda bashida wata buri a duniya irin ganin bayan zuri’armu, Umma sai na kwato mana yancinmu I promise. Ta fadi wannan ne tana hawaye masu zafi Kai tseye Umma tace’ Maisha ce, Maisha ce taturo mutanenta gidanmu ……
“Maisha?” Miemah ta‘kara tambayarta cikin sananin mamaki, sai kawai taji wayar ta katse. Saminu ne yashigo ban dakin ya tsameta red handed tana waya kuma adeden alokacinda ta‘kira sunan Maisha, yafado kamar daga sama ya sameta awajen, wayar yakwace yana ganin sunan Miemah haka yajefota cikin daji ya damke wuyar Aisha tamkar zai kasheta yadaka mata tsawa” How dare you, Naji duk maganarda kukayi da ita, Aisha Wallahi, wallahi, wallahi rantsuwar musulmi nai miki cewa idan har Miemah ta ‘kai wannan ‘karar kotu yazama dole murufawa Maisha Asiri …… Babu tsoro Aisha ta rufeshi da duka “Wacece Maisha? Saminu fadamin
Wacece Maisha awajenka? Meyesa kake fifitata akan jininka kuma y’arka Miemah Why?
Kai tseye ya amsamata” Sabida Miemah ba yarmu bace, Maisha ce asalin jininmu dani dake °° . Mutuwar tsaye Aisha tai tanazuba masa ido, kunnuwarta sunyi matukar kad’uwa dajin wannan maganar cikin sanyin jiki tarike hannayensa tanacewa” Saminu kada wannan al’amarin tai tsanadiyar gushewar hankalinka man, meye kake nufi dawannan maganar dakakeyi Saminu wace laifl Miemah ta aikata maka har kake kokarin …….. Kai tseye Saminu yasa hannunsa yarufemata Baki ” Aisha trust me Maisha Yarmu ce, kada mu tona mata asiri she is our child our own flesh and blood…
Aisha ta’kasa gaskanta maganarsa, a yanzu ganinsa ma take tamkar mahaukaci. Ganin babu yedda zatai dashi
yadena fadan wannan munanan maganganun, haushi ne yakai ma‘kokoronta tafito ban dakin aguje tabarsa achan inda takomo d’aki tana rusa kuka na fitan hankali. Saminu bai tsaye anan wajenba, sake biyota dakin yayi ransa abace yace” A‘uzubillahi, wai ni Aisha wace irin halitta ce ke? tun tuni ya’kamata ki fahimci wannan sirrin wanda muka dade muna boyewa, ya‘kamata
ki fahimci cewa Miemah ba jininmu bace Maisha ce diyarmu Kuma jininmu, Yata Maisha Saminu Maidugu… “Ya Isa haka, Takatseshi “wace hujja kake dashi wacce zata gamsar dani cewa Yata Miemah ba jininmu bace Maisha ce jininmu?
Tana fadan wannan Saminu bai ‘kara k0 da kalma guduce ba, akwatin kayansa yafara
bincika Kai tseye yazaro wata takarda yamiko mata yanacewa” Wannan takardan haihuwarta
ce, original birth certificate dinta guda biyu akayi daya wandake hannun Sambo dasunansa aka rubuta wannan k0 dasunana aka rubuta Maisha Saminu Maidugu duba da Kyau. Juyowa Aisha
tai ta wurgomasa takardansa “Ba’nida Bu’kata. Tafada yayinda nunfashinta ke kokarin tsinkewa.
**************************
A gidan Alhaji Zabir, kowa na
nan busy da maganar Hajiya
Turai, polisawa se shiga da fita suketayi, Yan jaridu sunata wayon daukan labaru, Zaid ya’kira sojojinsu dake China dukkansu suka taho gida sabida tsaro, tinda Safe yaketa zirga zirga tareda Yan Sanda da sojoji
Aunty Rahila da Aunty Nasibah ma duk basuga tazamaba fita sukayi tin dasafe tareda Attorney Bilkis (Family Lawyern su) wacce akafi sani da Atto. Babu wanda sukabari a gida face Anisa da Mainah sai kuma Abban Zaid tareda likitocinsa, Ma’inah batada abokiyar hira ita kadei take zaune tindasafe tana dannanna wayarta, Anisa ko na ta isgilancin ta, tamkar Kashi take ganin Ma’inah se wani hararanta take tana kuma wasu ‘kananan maganganu.
Se Chan baya Asad yashigo Gangaren suke hira jifa jifa da Mainah dashike Zaid ya bar confani ahanunsa aduk ranakunda basu samu zuwaba yana d’an shedamata abubuwnda suke faruwa awajen. Nan ne Ma’inah tasamu damar yi masa wata
tambayarda tadade aranta cewa “Wacece Anisa awajen Zaid kuma wace alakace take tsakaninsu.
Ya d’anyi shiru nadan wasu mintuna sannan yashedamata cewa tsohuwar budurwar Zaid ce tin suna China.
“Aiko biri yayi kamada mutum; Se yanzu Ma’inah tagano zagewarda yarinyar keyi, akwai dalili. Amma sedei babu abinda tafada, tsit suka zauna ayayinda kowa yakama harkan gabansa. Asad bai dade a gidan sosaiba Zaid yai masa waya, nan da nan sukayi sallama da Mainah ya tafi.
******
Bayan tafiyar Asad, Anisa tadawo falo kai tseye tafara zuba ashar tana za’gin Mainah cewa; ta cika biye biyen mazajenda sukafi karfinta. Babu abinda Mainatu tamaido mata daman
hausawa sunce shiru ma magana ce, Fitcewarta tai tabar mahaukaciya a falo se zuba take tamkar lalatacciyar fanfo.
Tanafita tsakar gida ta hango mutane masu bakaken kaya suna dirkowa daga sama aka daurosu da igiya suna sauka daga saman jirgin Helicopter da bindigoginsu, Nan da nan suka fara harbi “TaaTatatattataaa” cikin tsananin damuwa da tashin hankali Mainah takoma ciki a tsorace. Anisa tanajin sautin bindigogin tafito itama a tsorace
suka rungume juna itada Ma’inah
tamkar basu ke fada da junaba, jikinsu na karkaruwa suka labe karkashin dining (teburin cin abinci) Sautin matsowa ake tamkar yaki ake cikin gidan nasu. “Innalillahi wa Inna ileihi rajiun’ babu wata kalmar dake fita abakunansu a yanzu sai Salati, Amma dashike bangunan gidan bullet proof ce babu wani bullet d’in dake shiga ciki.
Ganin Kofar Falon nasu abud’e yasa Ma’inah tamike jikinta na rawa tanufo ba’kin kofa tana faman rufeta sausayi tarisketa, sake bindigar akayi kai tseye tashige deden gefen cikinta, Haka tafad’i awajen, second guda bata ‘karaba, tafita hayacinta.
“Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Mikewa Anisa tai wuf!!! Ta rapka wata dan banzan ihu tanufo
jikinta amma babu alamun motsi tattare da ita. “Lailaha illahu Muhammadu Rasoulul Allah (SAW) Ma’inah karki mutu.
Tafada da karfi cikin damuwa da tashin hankali ….
*****************************
Gyara muryarsa yai yafara bata labari kamar yedda tabu’kata;
” Wato kamar yedda kikasani a rana daya kuka haihu da Safeenah Matar Sambo Maidugu, saidei kin rigata dawasu dan awanni, Safeena ta haifi yan biyu laliyayyu, ayayinda kika haifl jaririyarki da cutar amosanin jini wacce turawa suke ‘kira Blood Cancer, Ganin bamuda isassun kudadenda zamu aika jaririyarmu Amurka domin
jinya wannan muguwar cutar dake yawo cikin jijiyoyin jikinta, Sambo shi yakawo wannan shawarar, sabida nafi kowa sanin dan uwana akwai shi
da tausayi dakuma taimakawa mabu’kata, hakan yasa mukayi chanjin Yara. alokacin dake
da Safeenah duk baku Cikin hayacinku, mukayi shawara da likitoci suka tabbatarmana cewa yin hakan ce kadei zata iya ceton ran diyarmu Maisha sabida
tana bukatar kulawa da jinya na gaggawa.
Anan mukayi rantsuwa cewa bayan Sambo, dani dakuma likitocin guda biyu wanda mukayi shawara babu wanda zai san wannan sirrin, Sambo yayi rantsuwa cewa zai rike Maisha amana tamkar y’arda suka haifa dashi da matarsa kuma ba’zai taba barin matarsa taji wannan sirrin daga gareshi ba, Ayayinda nima nad’auki nawa rantsuwar kamar yedda yayi, likitoci suka tabbatarmana cewa wannan
maganar ta tsaya tsakaninmu babu wanda zai sani bayan mu hud’u, da haka muka rufe ta’ron, ayayinda likita yad’auki Maisha daga wajenmu ya dankawa Sambo, Sambo Kai tseye ya danka mana Yarsu Miemah hannu bibbiyu duk dacewa yasha kuka alokacin ba kadan ba.
Wannan abubuwn duk abayanku tafaru, ku dei dakuka tashi akabaiwa kowa dansa, Sambo
da Matarsa suntafi kasar waje tareda Maisha yayinda Ma’inah tadawo hannunmu, atakaice dei Tagwayen dan uwana (Miemah da Mainah) duk kece kika
sha’yar dasu Allah kuma yaimiki Albarka.
Mutuwar tsaye Aisha tai tanabinsa dawata kallo na mamaki, ayayinda yacigaba da
maganarsa“ fadamiki wannan sirrin nayi abisa dalili amma kisani ba ason raina na tone wannan sirrin, wanda tadade a binne ba, Aisha kada kisake wannan maganar tafito daga bakinki na haramce miki kuma amasayina na mijinki Amanace idan kin tonata kuwa wallahi barinki da Allah zanyi, Sannan kisani idan kintona wannan sirrin Yarmu Ma’isha zata iya rasa rayuwarta Gabadaya k0 tahaukace abun bakin cikin kuma k0 da zatasan gaskiya wallahi bazata taba karbanmu amasayin iyayenta ba, kuma inaga yamafi mubarta achan tamore dukiya da rayuwan gata cikin daula.
Matar Sambo kanta matsala ce domin zata iya Ma’ka mu akotu idan wannan sirrin tafito sabida rayuwarta gabadaya bautar
diyarmu takeyi ba‘tareda sanin cewa Miemah da Mainah su sukafi bukatar wannan kulawar daga garetaba amasayinta na mahaifiyarsu. Dazaran kintona wannan sirrin Miemah bazata taba yafemanaba har abada. Sabida haka gwara kawai abar kaza cikin gashinta hakan zai fiyewa Yarmu Ma‘isha kwanciyar hankali …..
Hmm