TAGWAYE
CHAPTER 29
“Inspector babu shakka abunda Matata take fad’i Gaskiya ne. Tbe Baki Inspector Bashar yai,Ya’kara zuba musu ido “Alhaji ban musa makaba toh amma dei gaskiyan magana bazaku samu damar ganin Miemah ba sai kun gabatarmana da shedu masu karfi wanda zasu tabbatar mana
cewa batada hannu wajen kisan Asad, Maisha ce ta kasheshi kamar yedda kuka fad’a.
“Bawan Allah idan bakabarni na’ga Y’ata awannan lokacinba wallahi zan iya rasa rayuwata, so nake in roki gafararta Inspector kadubi girman Allah kakaini wajen yata.
Wuf!!! tamike cikin zazzafar hawaye ta kwance gabansa “Maisha ce ta kashe Asad wallahi Miemata batada laifi kadaku d’auki hakkin ta. Daddy ne yami’ke nan ta’ke yana kokarin shawo ‘kanta. Amma inaa ta’kasa Jin abinda yake fad’a anan kasa tazube sai kuka da tunani, babu yedda Daddy baiyi da itaba amma da dukkan alamu hankalinta tai nisa.
A fusace ya daka teburin inspector ransa abace ya daka masa tsawa“ Musulmine Kai kuwa, wani irin rashin imani ne Wannan kana ganin matata tana cikin wani yanayi Amma ka ‘kasa bata abunda take bu’kata.
Doguwar nunfashi Bashar ya sauke inda ya kad’a Kai” Alhaji kayi hakuri Miemah tana d‘akin horo Kuma gaskiya abu d’aya ce Tak! Zata iya fidda ita cikinta shine idan kun kawo shedar dazata gamsar damu cewa batada hannu wajen wannan case d’in.
“Shut up” Daddy ya damke collar rigarsa inda ya had’e hakoransa yana magana cikin zafin rai” Idan Matata ta rasa rayuwarta sanadiyarka, Inspector wallahi wallahi i won’t spear you. Dasauri Bashar yaja da baya “ASP Nasir, Security. ‘Daga murya yai Yana ambaton sunan Security.
Shiruu Daddy ya tsaya awannan lokacin Yana binsa da kallo, Sanda ya’kure Masa Ido sosai sannan ya bankado kofa yafitce, yana fita yai kacibus da mutanen gidan Zabir “Zaid, Ma’inah, Mamy, Aunty Nasiba dasauransu. Bai tankamusu ba, duk sunamasa magana amma babu amsarda taf‘ito daga bakinsa, “Ma’inah kije ki kula da Mahaifiyarki yanxu zanje inkawo shedarda zata fidda Miemah daga wannan sharrin da aka kalamata. Yashafa kanta sannan yabarwajen.
Jiki a sanyaye Ma’inah ta gyad’a kai. Azuciyarta take farin cikin dawowar Mahaifin nata gida sabida ta’ san koda wasa Daddy ba’zai taba barin Miemah awannan wajenba coz itama amasayin y’a yad’auketa. “
“Ma’inah meye kikeyi awaje kowa ya shige ya barki. Sai yanzu tadawo cikin hayacinta inda tahango sauran chan cikin office.
Come on Ma’inah kizo mukarasa ciki don Allah”, Kam kace kobo Anisa ta janyo hannayenta aguje suka shige offishin tamkar wa’inda suka tado daga sama.
Ma’inah be careful” Zaid ya mike nan ta’ke ya riketa ayayinda take kokarin fad’uwa, A tsawace yajuyo bangaren Anisa “Meyesa kika janyo Ma’inah haka, What’s if she fall? Zunbura baki Anisa tai tana binsa da kallo cikin bacin rai, azuciyarta take tunanin “How dare him meyesa zai kunyatani a cikin bainin jama’a”.
“Ma‘inah, Mahaifiyarki tana chan ba’kin cell tana kuka, yaukuma bansan dawace irin kisisina tashigo mana nan wajen da itaba”. Da wannan maganar Aunty Nasiba ta karaso inda suke inda ta’kara dacewa “Kowa ya’san dei Safeenah ba’tajituwa da Miemah wace gulmar ce takawota nan wajen tanata damin mutane da koke koke sekace wacce tarasa iyaye.
Momy kuma? Meyakawota nan? Kuma meyesa take kuka. Kije kiji daga ba’kinta, Fad’ar
Mamy. Kad’a kai Ma‘inah tai “A’a Mamy barta kawai na‘san duk yedda akayi momy da Maisha sunada hannu kuma babu shakka su suka kalawa Miemah wannan sharrin sabida haka bazan taba bin bayanta ba. Da ‘karfi Aunty Nasiba ta kad’a guud’a “yeuwa y’ata gaskiya wannan mahaifiyar ta’ki bata kamaceki ba. Shiruu Ma’inah tai yayinda take kokarin hana hawaye sau’ka daga idanunta. It’s Okay, Zaid ya janyota gefe “kada ki hana kanki kuka Ma’inah coz it will affect you… Yana fad’an wannan ta rungumeshi kai tseye tafashe da kuka.
A yanzu y’an sanda sun taru awajen trim! Daman interview ce takawosu, Mamy da Aunty Nasiba sun amshi tambayoyinsu cikin nitsuwa hakama Anisa da Mainah, akarshe Zaid ne yabasu nashi bayanan sannan shima ya amshi nasa tambayoyin.
Ahankali Ma’inah tayo gefen kofa nan ta labe bakin kofan tanabin Momy da Kallo cikin kuka da tunani, ta’rasa dalilinda yasa yau momy tazo cell tana zubarda hawayenta abanza haka, kuma ba tareda Maisha’n taba ko meke faruwa oho?
Wata zuciyar nacewa” Ma’inah kada kije wajen Mommy, wata zuciyar kuwa tana bata “Go Ahead” kije wajen mahaifiyarki kiji daga ba’kinta. Ahaka ta’karaso wajen ahankali, ahankali, muryarta na rawa tace’ Mom Mo Mommy lafiya????
Ta’ke mommy ta rungumeta tana zubda kwalla masu tsananin zafl“ Y’ata ki gafartamin, Ma’inah ki yafemin, ki gafantamin yata Zan iya sadaukarda rayuwata kawai sabida nasamu yafiyarku y’ayana , Son zuciyata ta’sa na wulakanta y’ayan cikina naci amanarku, na “kasa baku soyayyar dayakamata uwa tabaiwa y’ayanta, duk soyyayar na d’aura akan d’iyar daba nawa ba.
Shiruu tai na y’an wasu mintuna sannan tai ajiyar zuciya, sanda tarike Hannayen Ma’inah sosai sannan tace’ Mainah, Maisha ba y’ata bace, ke da Miemah kune y‘ayayana kuma kune TAGWAYE na ……
Dasauri Ma’inah ta kifto Hannayenta, cikin sananin mamaki da rud’ani ta sake ldo, baki, harda kunne tana binta da kallo tamkar a mafarki. Zubewa momy tai har kasa tasa guiwowinta “Ma’inah wannan sirrin a boye take tun tuni babu wanda yasanta sai mahaifinki da Mahaifm Maisha wato kawunki Saminu.
“Kawu Saminu“ Ma’inah ta ‘kara zuro idanuwana sosai tana bin momy da kallo cikin matsifar rud’ani ta ‘kara tambayar ‘kanta “Mahaifin Maisha Kawu Saminu? Kai tseye momy ta gyad’a kai “Kwarai da gaske Kawu Saminu shine Mahaifln Maisha, alokacinda Aisha ta haifi Maisha kamar yedda kikasani tana dauke da ciwon amosanin jini shiyasa suka chanza y’ayan cikin sirri suka baiwa Aisha Miemah ta sannan suka bani Maisha sabida Saminu bashida kudaden jinya ciwon dake damin Y’arsa Maisha.
Ma’inah ta kasa fad’in komai awannan lokacin barin wajen Tai a guje tafitce, Mommy na
biye da ita abaya har Sanda suka fitce waje, Aunty Nasiba, Mamy, Zaid da Anisa duk mamaki ce ya mamayesu inda suma suka biyosu suna tambayar abindake faruwa. lrin hawayen dasuke gangarowa a idanun Ma’inah ce ta’kara tsoratasu, dakuma irin tsananin damuwar data nuna a idanuwan Mommy.
“Kana ganin wannan wajen?” Maisha ta Kara lekowa sosai tanacewa’ Saminu this is what they call ‘Aljanna_thud_Duniya’. Fashewa da dariya Saminu yai “Matar nan billionaire kanta ce kuttuman nan gida haka sekaceta al_jannu. Matsowa kusadashi Maisha tai a kunne take rad’a masa “Hajiya Turai Mafiya kakeji Mahaifiyar Zaid duk duniya babu wanda zai buga yawan dukiya da ita, She is a multi billionaire woman”. “Hmmm lallai babu shakka, Aiko naga alama, toh Allah sa mudace.
Amin” Saminu yaji wata zazzakar murya ta amsa abayansa “Maisha I’m so proud of you my dear. Hajiya Turai ta’karaso inda suke cikin ta’kun girma ta zaune kan wata kujerar cin abinci dake gefensu “Bismillah ku zauna mana feel at home. Kai tsaye duk suka zauna kamar yedda ta umarcesu. Doguwar nunfashi tasau‘kar sannan tafara magana’ Maisha kinyimun abunda babban ‘Dana da Mijina duk suka ‘kasa, Kin share sunana daga wannan muguwar zargin da’akeyi akaina, kin bani dama da yancin fitowa dakuma zuwa ko ina ba tareda boyewa k0 tsoron y’an Sanda ba, I completely trust you my dear Thank you.
Murmusawa Maisha Tai “Babu komai Aunty ai duk yiwa Kai ne. “Gaskiya ne“ Saminu ya gyad’a kai cikin fuskar mutunci “Y’ata tanada tausayi matuka kuma idan tace zatayi abu ba’ta given up shiyasa ake mana kikari da “Like Father Like Daughter”. Da gefen ldo Maisha ta watsa masa harara sannan kinsa dacewa” Gaskiya ne.
Mikewa Hajiya Turai tai “Good, kun burgeni sosai zaku iya Zama anan gidan sabida so nake ku taimakamin. “Taimako” Saminu da Maisha suka had’a ba‘ki alokaci d’aya.
“Kwarai da gaske, Maisha na’san kinason ‘Dana Zaid amma ya yaudareki yana soyayya da Y’ar Uwarki Ma’inah, it’s really painful isn’t it? Cikin sananin bacin rai ta gyad’a kai ‘bazan taba mantawa da wannan ba kuma shiyasa nakeson nad’auki mataki akansu.
“So nake Zaid da Mahaifinsa susan anfanina, Kuma so nake suyi danasanin rabuwa dani, So nake Zaid ya fahimci illar Zama da mahaifinsa. Ma’ana lokaci yayi dazan kwace dukiyata gaba d’aya daga hannunsu, Zasu d’andana rayuwar talauci kamaryedda talaka yake rayuwa cikin yunwa da rashin kayan sakawa.
Murmushi Maisha ta sake, nan ta’ke tajuyo suka had’a ldo da Saminu suna dariya…. 9
Shiruu d’akin nan ta‘ke tamkar makabarata, inda hankalin kowa ke kan bidiyon CCTV‘n da Daddy yagabatar gaban Commissioner of police. Video’n tana nuna gidan Sambo inda
Maisha tadawo tana tsanarda Mommy cewa ta kashe Asad kuma shigar Miemah tai sabida
Iaifin takoma kanta.
Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun‘ Abinda suka amabata kenan alokaci d’aya, yanzu suka tabbatar dacewa Maisha ce tayi Kisan. Miemah batada laifl ko hannu aciki da wannan suka wanke Miemah daga wannan mumunar zarginda suka d‘aura akanta. a Nan ta’ke aka turo y’an Sanda cikin gari sunemo Maisha maza akawota gaban hukuma.
Miemah ta fitojikinta babu kyaun gani duk datti, ga raunuka da sauransu babu dankwali a kanta bare hijabi, gaba d’aya ta’koma tamkar Y’ar Almajira. Babu wanda ta tan’ka wa cikinsu wajen Ma’inah tai suka rungumejuna suna hawaye. Dasauri suka biyota, Zaid, Mamy, Aunty Nasiba duk neman gafarta suke, Amma ta’ki sauraronsu. Daddy ne yazo wajen shima ya rungumeta nan ne yabata labarin duk abubuwanda suke faruwa dakuma irin halinda momy zata iya shiga idan ta’ki tayafemata laifuffukanta.
Bai karasa abunda yake fad’i ba, Miemah tamike aguje takoma bayan Ma’inah “Karya kuke, bazan taba amincewa ba,Aunty Safeenah ba Uwata bace. Ta fad‘a cikin sananin rud’ani da mamaki.
Dasauri momy tamike, hawaye duk sun jike mata kaya, “Miemah ki gafartamin, wallahi Zan iya rasa rayuwata idan ban sami yafiyarki ba, Y’ata na rabu da Maisha nadawo gunku TAGWAYE na, ayanzu babu abinda nake bu’kata irin yafiyarku, soyayyarku, kulawarku dakuma kasancewa taredaku.
Kada ki matso kusa dani , Tafara ja da baya “I’m sorry bazan taba yafemiki ba Aunty Safeenah kuma har abada bazan amince dakeba, Ke ba Uwata bace har abada.
lrin kukan da Momy keyi yasa tausayinta tashige zuciyar Ma’inah, dasauri takoma gun Miemah tana kokarin shawo kanta “Miemah kiyi hakuri.
“Ma’inah please kada ki rokeni abinda nasan har abada bazan taba amincewaba just go home with your parents, Ni zan koma gida wajen mahaifiyata Aisha da Mahaifina Saminu, su ne iyayena har abada.
Daddy ne yasoma bakinsa “Look Miemah we are sorry kiyafewa mahaifiyarki.
“Kawu Sambo ka gafartamin, kuma na amince karokeni komai banda wannan zan iya aikatamaka Amma bazan taba amincewa daku amasayin iyayena ba kuyi hakuri wannan shine gaskiyar zance …..
“Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun. Abinda suka fad’a kenan yayinda Mommy takwance har kasa ta sume awajen. Daddy ne ya daka ihu “Safeenah ki tashi Safeenah I can’t live without you. Aguje Ma’inah takawo ruwa tana yayyafa Mata yayinda Zaid dasauran suna mata fifita Amma shiruu take har yanzu ba’ta motsi.
“Check her heart beat”, Daddy yasa hannu a kirjinta “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun ba’ta nunfashi. Ya’kara fashewa dawata sabuwar hawaye. Nan ta’ke Zaid yakira mota suka wuce asibiti.
A window’n d’akin Ma’inah ta tsaya tana lekowa “Mommy karki mutu ki barni. Abinda take fad’i kenan tun tuni hawaye sun ‘kasa tsayuwa a idanuwarta, Nan ta’samo benci tazauna tacigaba da sana’arta na kuka.
“Sister”, Juyowa Ma’inah tai dasauri, sai ko taga Miemah ce tsaya awajen itama tana hawaye, wandama zakace hawayen Ma’inah. Mikewa Ma’inah Tai nan ta’ke itama tace’ My real sister” ta’kara fashewa da hawaye. Ahankali suke matsowa kusa da juna har saida suka fuskanci juna sosai. Nan ne suka zubama juna ido suna tuna yarantarsu.
A wannan lokacin dariya suke suna Kuma kuka a lokaci d’aya amma kukan ta farin ciki ce.
Dasauri suka rungume juna sosai suka mannu da junansu, ‘Daya tace’ I love you sister, ‘Dayan tace’ I love you more sister. Haka suka ringa fad’a cikin farin ciki.