TAGWAYE
CHAPTER 37
Babu sallama Zaid ya fad’a cikin d’akin Mahaifinsa tamkar daga sama, “Baba meye anfanin wannan vidiyon daka turomin, bangane abinda take nufl ba. Ya mike ahankali yanacewa” Zaid wannan ba tarbiyan dana d’ouraka akai bane, ldan zaka shiga wani wuni ka tabbata kayi sallama tukunna, as a good Muslim. Yayi shiruuu nawasu mintuna, sannan yakoma waje, ya’kara shigowa da sallama” I’m sorry ba halina bane, I’m just so confused batun wannan vidiyon daka aikomin.
Murmusawa baba yai, ya gyara muryarsa’ Ba wani abun ta’da hankali awajen because Halinta kenan, na da’de ina bincike a’kanta sai yanzu na tabbatarda zarginda nakemata gaskiya ne. “Bannn ganeba kana nufln???
Zaid bai karasa furucinsaba, Baba ya katse shi” ina nufln Daga yau ba kai ba Ma’inah, na datse wannan soyayyar dake sakaninku, sabida Ma’inah maciya amana ce, tana tareda Mai gidanka Doctor Manav Muhammad Al’siddique. Zaid bazaka taba aurentaba. Baimasan halinda Zaid yake ciki awannan lokacin ba, har saida ya kammala bayanansa Tas!!!, Yana waigawa ‘Dannasa yagani kwance a ‘kasa tamkar matacce ya sume awajen “Doctor Manav, Doctor Manav. Haka yakama ihu yana kwala masa ‘kira da karfln gaske.
Miemah ta dade a ba’kin kofa tana sauraron tattaunawar Zaid da Mahaiflnsa, Mutuwar tsaye tai awannan lokacin’ Ma’inah bazata taba aikata wannan mumunar zarginda akemata ba. Nan da nan hawaye suka fara sirnanowa a idanuwarta ‘Yar Uwata bazata aikata wannan mumunar zarginda akeyi a’kanta ba. Jikinta na karkaruwa yayinda taja’ da baya ahankali, ahankali take tafiya tana tunani.
Zayyad yafito d’aki yana rabe rabe ko Allah zaisa suhadu da Miemah, tun d’azu yake zaman jiranta a d’aki, ta’ce masa zataje ta’kira masa Zaid da Babansu amma haryanzun ya’jita shiru. Muryarsa ciki ciki yake ambaton sunanta “Miemah, Miemah. Saida yaci comer wani Gangare suka ci karo da juna dasauri yariketa “Miemah inasuke?
Babu amsarda tamaidamasa, “Miemah Ina Zaid da Baba na? Ya’kara tambayanta, Sai yanzu yakula da irin hawayenda suke saukowa a idanuwanta, Nan da nan yabi ya tsargu, dasauri yasa hannu yana share mata Hawaye ‘Miemah meye ya sameki? Kidena kuka, seeing your tairs really hurts me inside please. Ja da baya tai, tana kokarin kaucemasa inda ya damke hannunta tana kokarin kiftowa ya rungumeta “Miemah I truly love you.
‘Khul! Kar’ka Soma, Ba’a nan gidan ba, ba’a gidana ba. Muryar Baba ne ya doso kunnuwansu a wannan lokacin, A tsorace Zayyad yabud’e Baki zaiyi magana, Baba ya janyoshi gefensa “Zayyad na’san kayimun laifl dani da Zaid ka zalunceni kuma kaci amanar y’an uwan takanku da ‘Dana, but kai jini nane, no matter how much we try to seperate you from our family you will still remain my Son Zayyad you are my flesh and blood.
Sanda ya share hawayenda suka tseiyan masa a ido sannan yafara magana” Ma’inah ta’rigada ta zubamin ‘kasa a Ido sabida haka Zayyad kacire son Miemah daga cikin zuciyarka, A matsayina na mahaifinku na yanke hukunci cewa bazaku taba had’a jini da zuri’ar Sambo Maidugu ba.
“My twins? Wannan maganar dayai, yaje dedei da shigowar Daddy Falon “My twins? Kalmarda yafara furtawa kenan Sannan ya’kara tambayansu “Ma’inah ta Kuma? Me tayimuku? Dasauri Miemah ta’koma bayansa “Daddy cewa yake wai Ma’inah na tareda Doc Manav Kuma na tabbata sharri ake Mata. Miemah ta ‘karashe kalmar natane tana bala‘in kuka.
Sunana Doctor Manav Muhammad Alsiddique” Yamika mata hannu domin su gaisa. ‘Daga idanuwana tai tazuba masa ido, Ganin irin muguwar had’uwar da gayen yai yasa farin ciki mai sanani ya mamayeta, Gyara muryarta tai “Sunana Ma’isha Samb… Sorry Maisha Saminu Maidugu Y‘ar gidan Hajiya Turai Mafiya how may I help you?
Dr Manav ya gyara murya” Can i have your contact? Dasauri tamika masa Catin wayanta “Sure. Cikin sany’in murya yace okay dear sai munyi waya. Hakoranta sun kasa bacewa” Alright handsome bye. Yana barin wajen, yakoma motarsa “Ma’inah I don’t think this plan of yours will work. Meyesa? Don Allah Doctor ka taimakamana,you are our last option sir please help us. Ta tura kai ‘kasa tana neman alfarmarsa. Shiru Dr Manav yai “Bakomai I will handle everything Don’t worry. Da wannan yaja mota suka kama hany’an Manav Alsiddique Mansion. Daga nan Ma’inah ta matsu taganta a gida domin ta sanar musu da sabon salon datazo dashi Kuma babu shakka duk zasuyi farin ciki musamman Zaid da Teddy Miemah.
Ta bangaren Manav Alsiddique Mansion kuwa’
Baba yahad’asu a falo zuciyarsa na tafasa inda ya yanke hukunci cewa y’ayansa bazasu taba had’a jini da zuri’ar Sambo Maidugu ba sabida zarginda yake akan Ma’inah ta tabbata tinda kowa ya’sheda tun da safe Ma’inah tabar gidan tareda Dr Manav basu ‘kara dawowaba har zuwa wannan lokacin.
Kowa yazauna shiru, Miemah da Mommy kam se kuka suke,Anisa ma kukan takeyi Mamy da Aunty Nasiba sunyi jugumm. Daddy ko Zama yai yana kokarin kwantar wa iyalansa hankali.
Baba yana gama bayaniyansa yasa Zayyad agaba suka wuce ciki duk dacewa Zayyad ya‘kasa gane dalilin dayasa laifin Ma‘inah zata shafl alakarsu da Miemah. Suna zuwa ba’kin kofa dap! Zaid ya dakatar dasu babu alaman wasa afiskarsa yace”Baba idan ka hanani auren Ma’inah zan iya rasa rayuwana because I can’t live without her, try to understand me please Zarginda kakeyi akan Ma’inah ba gaskiya bane.
Babu amsarda ya maidamasa cikin sananin bacin rai, yajuya afusace yakoma falo fuuu! zuciyarsa tamkar ci take da wuta. Zayyad baisan Sanda murmushi ya bayyana a fiskarsa ba dayaganshi tare da d’an uwansa tamkar a mafarki. Yayi ajiyar zuciya, muryarsa chan ciki yace ZMZ can I atleast hug u please, I miss you so much? Sai yanzu Zaid ya maida kallonsa inda yake, Babu abinda yafad’a ransa ne ya’kara baci inda batareda bata lokaci ba
yabarwajen shima yabiyo Mahaifinsa zuwa falo.
Wannan lokacin tayi dedei da dawowan Mainah gida, ita kad’ei tashigo, Tayi sallaman
musulunci sannan ta’karasa ciki. Ta shigo ta tsamesu duka a tare saidai alamu sun nuna cewa akwai matsala a gidan sabida dukjikinsu a mace, wasunsu k0 fiskokinsu suna nuna alaman hawaye.
Daddy Lafia? Budan ba’kinta ke da wuya Miemah ta fara jero mata wainar da ake tauyawa agidan tun safiyar yau har zuwa wannan lokaci. Ba shiri Ma’inah ta zube anan wajen tana ambaton Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Hawaye ne suka fara saukomata tamkar ruwan sama “Zaid ba halina bane Sharri akemin. Dasauri tayo wurinsa anan ta zauna agabansa tana hawaye “Zaid wallahi karya akemana wannan ba halina bane.
Taso ta fad’amasa abinda ke faruwa amma Daddy ya hanata yin hakan janyota yayi cikin sananin bacin rai tareda Miemah suka wuce bangarensu inda Momy da Umma Aisha suka biyosu abaya Suma rai abaci.
Tun daga wannan ranan Zaid yashiga damuwa da tunani, kwata kwata Baba bai zaci hukuncinda ya d’aura akansa zai galabaitashi har ya maida shi shiruu tamkar Dunkum, Ya dena magana, ya dena kula kowa agidan daga d’akinsa sai kuma idan zai fita harkansa a waje. Tin Baba na masa magana haryagaji yadena,yanayin d’annasa na d’aure masa kai har yakai da yanzu ya’fara d’anasanin hukuncin da yayo masa. Zaid yazama wani iri kaman ba shiba, kwana biyu kacal yabi ya rame tsanadiyan rashin cin abincinda yake. ldan ya dawo gida d’akinsa zai wuce kai tseye ya rufe kofa da makulli, duk bugawan duniyan da za’ayi baza tasa shi bud’e kofan ba.
Baba da Mamy sunfi kowa damuwa, barin ma Mamy kwana biyu ta rame sosai sabida itan ma kusan tadena cin abinci, kuka shine sana’arta ta rasa yedda zatayi da Zaid yakoma ainihin ‘Danta ZMZ kamaryedda yake ada. Zayyad ne ya maya gurbin Zaid a gidan kowa ya yafemasa suna zama dashi lafiya Baba na d’aukan d’awainiyarsa ta uba, inda Mamy take kula dashi tamkaryedda take kula da Zaid. Shiyasa ya sakejiki dasu tamkar babu abinda yataba rabasu dajuna.
Tun daga faruwar wannan al‘amarin Doctor Manav ya tattara ya bar musu gidan, Zaid ya nemeshi sama da ‘kasa domin su tattauna ainihin abinda yafaru amma ya shedamasa cewa idan ya’kara dawowa gidan, zai dawo musu da duk amsoshin dasuke nema agareshi. Da wannan, ya tafi yabarsu shiruu har yau bai ‘kara lekosu ba.
Shiyasa duk sallamar da akayi agidan Zaid yakan leko yaduba kila k0 Dr Manav ne yadawo musu da amsoshin tambayoyin dake yawo a kwakwalwar kowannensu.
……..
Shima Zayyad da tunanin Miemah yake kwana dashi yake tashi, Mafarkinsa ako da yaushe
flskar Miemah ce, Baya taba mance ranar da ya warke ya sinci kansa agidan Dr Manav, inda Miemah tashigo d’aki ta rungumeshi tana farin ciki matuka, Sabida a wannan lokacin ne soyayyar ta yashige zuciyarsa cikin nan ta’ke, kuma yaji ajikinsa cewa babu wata macenda zata dace dashi bayan Miemah”. Sedei shi Zayyad, duk wannan damuwar data addabi rayuwarsa baya nunawa afiskarsa, ldan ma ka ganshi sai kazaci babu abinda ke daminsa kalau yake. Hakan yasa Baba yai saurin janyosa ajiki sosai sabida atunaninshi Zayyad yabi umarninsa, babu musu yacire Soyayyar Miemah a zuciyarsa kaman yedda ya umarcesu. Duk dacewa Zaid baya kulasu a gidan Zayyad bai fasa aikomasa text a waya kamar yedda ya saba ba, ako yaushe yakan aikomasa sako da harshen ‘turanci kamar haka ko Allah zaisa wataran yadace.
“I say again my dear brother, I miss you. I ask you again, for your forgiveness. I’m so sorry
for not being there when you needed me the most, but I really don’t believe I would have
been any help to you anyway, since thinking back to how our mother abandond us. I remember] was just as much of a mess and practically useless, Zaid I’m sorry you really went through a Iot just because of me. I don’t seem to do well with my own crisis situations. I’m sorry Twin Brother I love you. And please try to forgive me one day” ’
Wannan kenan.
Yana anfani da harshen turanci wajen rubuta Sa’kon ne, sabida ita ya’saba, kwata kwata Zayyad bai iya harshen hausa ba sedei yana kokartawa dakyar yake magana. Turanci, Larabci da Chinese su’ne abinda ya iya, zai iya yinsu confidently tamkar Shan ruwa. Tsanadiyar tasowa dayai achan kasashen waje (China,Abu Dhabi, Washington).
Zaid baya bata lokacinsa wajen karanta sakon, yana shiga wayarsa zai gogeta nan ta’ke. Sati guda kenan, Zayyad bai fasa aikamasa wannan sakon ba, har saida yafara mamakin ko meye yake rubutawa acikin message d’in, wannan tunanin yasa Zaid yayi ajiyar zuciya yabud’e Sa’kon ya’karanta.
Anisa ta tattara kayanta caf! Ta maidasu shashin su Ma’inah, tun faruwar wannan al’amarin Daddy ya hana y’ayansa ko iyalansa ta’ka kafa a shashinsu Zaid. Ya chanzawa y’ayansa waya harda Sim Card. Yaran sunyi kuka sosai a farko, musamman ma Ma’inah rashin Zaid ya kusan hau’katata , Daddy ne yai tsaiyin daka ta hanyan farantawa y’ayan nasa dakuma nunamusu cewa shi kad’ei da Mommy sun isa suzama farin cikin su, Kuma sunfi ‘karfin wani namiji yawulakanta su. Bisa dagewa da jajircewar Mommy da Daddy, Mainah da Miemah suka Saba rayuwar su ahaka sedei babu shakka damuwar Bata bacemusu a chan cikin zuciyarsu ba, musamman ma Ma’inah da tunanin Zaid d’inta take kwana dashi take tashi, Miemah koh addu,ar ta akoda yaushe shine “Allah ya dedeita tsakanin Zayyad da ‘Dan uwansa Zaid dakuma Mahaiflnsu. Daddy ya shedawa Dr Manav cewa zusubar gidansa sukoma gidansu na ainihi, ya dakatar dasu cewa” su d’an bashi lokaci sai bayan ya dawo zasu dedeita komai. Bai musa masa ba, Haka suka cigaba dazama, Mamy da Aunty Nasiba ma kusan kullum suna zuwa lekasu agidan duk dacewa suna fama da sauyewar halin Zaid.
“Please forgive me daughters, I’m so sorry dear kids for been such a bad Father. Ku gafartamin, Mainah please try to forgive Daddy, a matsayina na mahaiflnki na’kasa kareki daga wannan mumunar zarginda Mahaifln Zaid yakemiki, na rabaki da Zaid wanda kuke tamkar Hanta da Jini, na rabaki da Farin ciki a rayuwarki. Yasa d‘ayan hannunsa a fiskar hoton Miemah dake makale agabansa, Hawayen dasuke zubomasa ne suka ‘kara gangarowa tamkar ruwa “Miemah I don‘t even know what to say, because I don‘t deserve your forgiveness my dear, na rabaki da Mahaifiyarki dakuma ni Mahaiflnki tun kina yarjinjira na dankaki a hannun ‘dan uwa na maci Amana, munafuki Kuma azzalumi Miemah I am sorry.
Abban Tagwaye lafia, Yedda taga mijin nata yasa hotunan y’an_biyunsu agaba yaketa zubda kwalla Yana magana shi kad’ei yasa hankalinta yatashi sosai. Dasauri ta’karaso inda yake “Abban Tagwaye meyesa kake kuka haka. Babu shiri Daddy ya damke ta, sauke kansa yai akafad’arta Yana kuka “Safeenah kin tuna lokacin da muke soyayya nakan fad’amiki burina a rayuwa shine bayan munyi aure idan munsamu Y’aya, I just want to be the best father in the world.
Tun tuni mommy take kokarin rike hawayenda suka taron mata a Ido, Amma dataji karshen furucin Daddy, batamasan sa’inda hawayen suka fara saukomata ba, Rufe Masa baki tai da hannu tanacewa’ “Sweety please don’t feel guilty you are the best Father, Na’san munyi kuskure abaya but we can solve everything together Ma’inah da Miemah sune rayuwar mu, na tabbata bazamu taba barin sucutu ba, we will protect our dear TWINS till the end, we will always be by there side. Mugodewa Allah sabida Kuskuren damukayi a farko ne, yanzu muna tareda TAGWAYEN mu babu wanda zai shiga tsakanin mu da Yayanmu har abada, Kuma a Sannu Miemah da Ma’inah zasu d’aga maka trophy’n Best Daddy In the World, Promise. Wani irin farin Ciki Daddy yaji a zuciyar sa “Allah ya nuna masa wannan ranan” , Murmushi ya sakar Mata “you are right my dear, I love you so much, You are the best Wify in the whole universe. Nan ta rungumeshi suka sake bude wata sabuwar pejin hawaye.
Minti talatin kenan sukayi anan wajen zaune suna jiran Dr Manav, suna gida ya Kira layin Ma’inah yace suhadu da ita da Miemah awannan hotel d’in yanason su tattauna wata muhimmiyar zance.
“Wannan mutumin zai taho kuwa, I’m 99% sure, Daddy da Mummy suna nan suna jiranmu
a gida, sunma kosa mu dawo. Dan Allah tashi mu tafi kinsan Mommy za tayi mita “My Twins are not back yet this house looks empty without them.
Miemah ta karashe zancen ne tana gyara kwanciyarta a kafafun Ma’inah “Come on nagaji
da jira wallahi. Ta turo baki gefe.
Fashewa da dariya Ma’inah tai “Mudai jira muji dame zaizo dashi, Uwarson jiki tashi karki karyamin kafa Gam Miemah ta rike kafafun nata cikin sigar zolaya tace’ Baza‘a tashin ba so kike bayana ya karye na gaji da zama. “Aww ni’ce jaka ko, Mlkewa tai aguje tafara bin Miemah suna gudu kwatsom sai cin karo sukayi da Dr Manav. Dasauri kowa ya kame kansa.
Sun koma wajen zamansu, kowa ya zauna suna kurban koffee dake gabansu, Bayan sun gaisa, Dr Manav yafara magana ” kuyi hakuri nabarku kunyita zaman jirana shiru sai yanzu na taho. Murmusawa Ma’inah Tai ‘Ba komai, tana nuna Miemah yayinda takecewa “Dazaran Ina tareda Y’ar Uwata bana taba gajiya barema bakawani dade ba ai. Gyara murya yai shima yanabin Miemah da kallo “Mai gida na Tanason ta tattauna wata muhimmiyar zance taredaku tace idan kun amince in danna mata Kira yanzu zata taho. Dr Manav yafad’a cikin nunfashi d’aya. Cikeda rud’ani Ma’inah ta gyad‘a masa kai “Kira ta. Miemah ko mamaki ne ya isheta a wannan wajen wace ce wannan ogan tasa Kuma meye alakarta dasu?
HAJIYA TURAI, Bata ‘karasa wannan tunanin ba yayinda idanuwarsu suka fad’a kan Hajiya Turai Mafiya dake tahowa daga chan nesa. Mikewa sukayi har saida ta karaso inda suke sannan suka zauna sedei haryanzu idanuwarsu a zare suke sosai tsabar mamakin ganinta dasukayi. Mutuwar tseye kowannensu tai sabida tunda suke rayuwa aduniya basu taba ganin hawayen Hajiya Turai Maflya ba, kai ko a television bare a mujalla. Sai yau datake zaune agabansu tana zubda kwalla tamkar a mafarki.
Tsoro yasa Miemah ta mike dasauri tana damke hannun Ma’inah “Tashi mutafl Ma‘inah. Tarad’a mata a kunne. “Babu inda zakuje Hajiya Turai Maflya tana bu’katar magana daku sabida haka yazama dole kuyi hakuri kuzauna kuji k0 dame tazo da ita. A hankali suka koma kamar yedda ya umarcesu suka zauna, sedei tamkar a kan ‘kaya suke. cikin sananin hawaye Hajiya Turai tamike, Sanda tazo dedei wajen Ma’inah tazauna a kasa tafara zubda kwalla “Mainah ki gafartamin. Babu shiri Ma’inah ta mike a guje takoma Bayan kujeran Miemah, Nan ta labe jikinta sai karkaruwa suke tamkar ta shafa mako a gadon asibiti.
Hajiya Turai bata fasa maganar taba” Thank you Ma’inah for taking good care of my little son Zaid alokacinda bananan taredashi na gode. Anan kasa tazauna tanaja har saida takai wajen Miemah “Na’gode Miemah, Dr Manav yashedamin cewa kece kika taimakawa ‘Dana Zayyad. Bazan taBa mance wannan karamcinda kukayimun ba har abada.
“What is happening, I can’t believe this, I’m I dreaming??? Mainah tamike Cikeda rud‘ani “Dr Manav laflya kuwa meke faruwa anan? Meye yafaru da Ammi? kodei itama su biyu ne maybe twin sister Hajiya Turai ce. Hajiya Turai ta gyara zamanta a kujera sannan tafara basu labari ……
FLASH BACK
Dr Manav abokin kasuwanci nane, tare muka fara business kuma kusan zance muku na yarda dashi fiyeda yedda na yarda da Kaina. He is the most respectful man among all my business colleagues. Shi ne ya taima’kamin alokacin da nake gidan yari, Da taimakonsa Kotu ta wankeni daga zarginda akemini cewa ni ce na kashe Amaryan Mijina Zabir, Alhalin babu hannuna awannan kisan. Babu shakka Mijina Zabirya yaudareni Kuma alokacinda ya’kara aure na nunamusu damuwata sosai harma na tsorata Amaryan cewa ni zan zama ajalinta.
A lokacinda kisan yafaru, na shirya kayana tareda kayan autata Maimunatuh akan aranar zamutafl America. Sanda na kammala shiri na tsap! Nayo bangarenta domin na gargadeta cewa kada mudawo gida musameta cikin gidana, sabida gidana ne zan iya korar kowa alokacin da naga dama. Sedei ina shigowa falonta, ba’zan taba mance wannan ranar ba, na tararda Amarya kwance a ‘kasa jina jina da wuka a gefenta. A tsorace na d’auki wukar narike a hannu na Ina kokarin ihun Kiran jama’a. Saiga Zaid yashigo, daga shigarsa baisan hawaba bare sau’ka ya kwace ‘kanwarsa dake hannuna, Ina faman masa bayani amma inaa ya’ki saurarata. Tura kofar yai yarufemu a ciki saida ya’kira Mahaifinsa yataho tareda y’an Sanda sannan suka bud‘e kofan y’an jarida sai buga rahotanni suke da hotunana.
Wannan dalilin yasa, tsanar Zaid da Mijina ya shiga zuciyata nan ta’ke nacire dukkan Imani da tausayi a zuciyata, Musamman ma Zabir butulcin dayai min tayi yawa, na sha alwashin daga wannan ranan zan fara bibiyar rayuwarsa har sai naga bayansa. Nayi kukan takaici da damuwa na sanarwa yan Sanda cewa bani ce nai kisan ba Amma dayake mutumin dayai kisan ya shiryamata sosai har CCtv cameras duk ya cire bare hotonsa a camera. wannan dalilin yasa y’an Sanda suka ‘kasa yarda da maganata sabida babu hujja.
Ina gidan yari amma ban fa’sa bibiyar rayuwar Zabir ba, Nasha barin gidan yari sabida kawai nacinma burlna na kashe Mljina. Wahalardanasha a gidan yari bat’a misaltuwa har saida wannan bawan Allah Dr Manav yasamomin lawyer kwararre. Bamuyi mako guda da wannan lawyer ba yaga’no wannan CCtv camera dake d’akin Amarya anan muka gane ainihin wanda yai kisan sannan aka wankeni daga zarginda aka Dade ana tuhumata da ita. Bisa wahalar danasha a gidan Yari, Gwannnati ta d’ankamin wasu d’inbin dukiya rabin Wanda na mallaka ayanzu.
Bayan dawowata Nigeria nahad’u da Y’ar uwarku Maisha da Mahaifinta Saminu inda suka shedamin cewa ‘Dana Zaid da Mahaiflnsa zasu hallakani dazaran sun’kara ganina. Maisha ta shedamin cewa ita budurwar Zaid ce amma Y’ar uwarta Ma’inah ta shiga bokaye ta saceshi daga wajenta shiyasa takeson ganin bayan Ma’inah domin ta mallaki Zaid. Babu kalar karyar dabasu pe’samin ba, har na amince na yarda dasu tamkar y’an uwana muka zauna ina kashe musu kud’i iya gwargwado.
Ban taba zaton Maisha da Saminu maciya amana tabane har saida Dr Manav ya shedamin kowanene Maisha dakuma Saminu, Ban amince da maganar saba yace zai proving kansa sannan yadawo da shedu ya nunamin. Daga wannan ranan Dr Manav ya Fara zuwa gun Maisha dasunan yana Santa, ban taba nunamata cewa na’san Dr Manav ba har saida shakuwa da soyayya mai zurfl tashiga tsakaninsu har tasakejiki dashi sosai. Nan tashedamasa abinda ke ranta da ita da Mahaiflnta suna son su kasheni domin su mallaki dukkanin dukiyata. Dr Manav ya’nuna musu cewa yana taredasu, alokacin da sukasa ranar kisan ne ya shedamin abinda suke shirinyi. A ranar ban kwana a gidan ba. ‘Dan Sanda mu’kasa yakwana a d’akina, akan shinfld’a ta ya lunlube tamkar Hajiya Turai.
Tsakar dare Maisha da Mahaifinta suka dire cikin d’akin da wukarsu, Maisha tazo dap da wukarta zata aikata niyarta kenan Wannan ‘Dan Sandan yami’ke da Handcuff “You are under arrest”. Sauran y’an Sandan dasuke labe a lungu duk suka firfito suka zagayesu da bindiga ba halin gudu. Haka suka kamasu daga ita har Mahaifin nata yanzu hakama suna hannun hukuma, a Babban ofishin Y’an Sanda. Wannan kenan …..
Hajiya Turai tana gama basu labari Miemah da Ma’inah duk suka mike cikin sananin kukan farin ciki suka rungume ta “Mun gode Ammi kuma daga yau kin dawo cikin mu babu abinda zai tsameki da yardan ubangiji na tabbata Zaid da Zayyad zasufl kowa farin cikin dawowarki, Baba ko dazaran kin fad’amasa wannan labarin no second thought zai
yafemiki. ‘ Share hawayenta tai, “Thank you Ma’inah da Miemah, na’godewa Allah da irin wannan ranar tazomin a rayuwa…