TAGWAYE CHAPTER 5

TAGWAYE

loading…
CHAPTER 5
Asubahin farko Ma’isha ta tashi, bayan ta ‘yi sallah, ‘karfe biyarta shirya zuwa office, Jiya daman cikin zumudi takwana da Farin cikin samun aiki ababban confaninda kowa ke burin shiga aduk fadin Duniya. Daman chan kunya take idon ‘kawayenta k0 samarinta suka tambayeta aikin me takeyi, Amma ayanzu ta samo irin aikinda take burin samu, wanda babu mai raina mata aduk cikin abokananta da samarai. 
Motarda tafi kyau aduk cikin motocinta ta zaba, afarkon zuwanta office. Alokacinda tafito motoci basuyi yawa akan titinba, daman saurin kada motoci suyi yawa yasa tashirya tunda wuri tafita don gudun Go_Slow. 
After a very long drive. ‘Karfe biyar da rabi ta’karaso. “Wow Al_jannar dunya” Gaskiya wurin yayi ba laifi. Sake baki tayi tana kallon tsarin ginin Confanin wanda ko achan America se wane da wance suke Gina irinta. Tamkar bakauyiya tashige tanata kallace kallace, Inda wani Security ya tse da ita yace”Madam from where, tsaya daga nan lokacin shiga bayyi ba, sai ‘karfe shida?” Se yauzu hankalinta yadawo, ta rufe baki ahankali tachanza launin tafiya tana rangwada cikin yanayin birgewa “Excuse me security ina ne ofishin Oga Kashim Sa’ad Mahmud?” 
Sake bakinsa yayi shima, cikin mamaki yace; Madam kina nufin ba kida labari cewa Oga Kashim Sa’ad Mahmud ya tseyar da wannan Confanin?”… Tseyarwa kuma? kaman ya? Ma’isha ta tabe Baki tana tambayarsa cikin rudani. Kai tseye Ma’aikacin ya amsa mata cewa; Kashim Sa’ad Mahmud ya tseyarwa Zaid Muhammad Zabir wannan Confanin wanda yanzu takoma ZMZ Builders. “Zaid Muhammad Zabir” Ma’isha ta nanata a hankali “Who is he?” Ta tambayeshi a bayyane… 
“Ke dallah Malama dakata haka, ke yarjarida ce? ko aikanki akayi kizo kiringa Mana irin wannan wawan tambayoyin naki, kawai malama inzaki koma gida ki koma domin yau babu aiki Sabon CEO zaizo daga Beijing (China) ganin confaninsa, idon baza ki koma ba kuwa se musan yedda zamuyi dake kamin Tawagar CEO su’iso Sabida Zaid bashida lokacin kananan kwari irinmu. ‘Kai ‘dan tala‘kawa ka’iya bakinka, wallahi na fika tashanci, nima yar tasha ce na fika iskanci wallahi, Banza mai gadi’. Ta zunburo masa baki tana nunashi da dan yasa: Wawa dan wahala, anan zaka ‘kare wallahi. 
Daga nan ne, Mai gadin yafara maka mata ashar, Ma’isha ma dei Yar tsiyan ce bata barin bashi. Haka suka cigaba da zagin juna har yan Sandan cikin Confani sukaji hayaniyar tasu. Nan da nan sojoji da yan sanda suka taru awajen. 
“What are you guys doing here? ‘Katon Muryan wani Soja ne ya daka musu tsawa. Inda a firgice Mai gadi ya daga hannunsa sama yanacewa; Kayi hakuri sir, I surrender wallahi ba laifi na bane. Ma’isha koh ko tseyuwarta bata chanzaba ballentana idanuwanta su nuna tsoron yan sandan dasuka kewayesu, a tseye take tana musu wani banzan kallo da gefen ido. “Ke, mekikeyi anan  Kuma? ‘Dan Sandan yajuya bangaren Ma’isha. 
“Aiki nazo. Ta amsa masa Kai tseye; Domin na san ko da bakuje makarantaba idan kunga mutum da Paper a hannunsa yana shigan company kunsan abunda takawoshi; Ta amsa da muryar mannin hauka, rashin biyayya da tsananin tsiya. ‘Daga hannu sergeant yayi zai tsinke ta da Mari kenan akaji jiniyar sojoji, hayaniyar mutane dana motoci manya da ‘kanana sunata gangarowa hanyan companyn. Daga nan yan sandan duk suka watse suna koran mutane a kan hanya anata sanarwa cewa CEO Zaid yakusan ‘karasowa, ya sauka a ZMZ Hotel cikin awanni ‘kalilan zai ‘karaso cikin company. Da sauri Ma’isha tashige motarta tana nunfashi sama sama, haushi kamar zai kasheta dama so take wannan sojan yasa hannu yamareta, da kuwa yau zaiga bala‘i, wallahi se Abuja ta kama da wuta. Da wannan tunanin taja motarta kan hanya aiko tana haurowa titi taga babu hanya.Yan Sanda da Sojoji sun rufe ko ta’ina Motoci ne Manya Manya a wurin. 
Dafa kanta tayi cikin bacin rai ta tseda motarta agefen titi, tasa head phone akunnuwarta tana sauraron Waka. 
“” MA’INAH___““ 
‘Karan Alarm din wayarta ne yatasheta. lnda a Firgice tatashi daga cikin barcin da tadade tanayi. Wutar Dakin takunna Kai tseye idanuwarta suka fada kan agogon bango wanda yanuna ‘karfe tara da minti goma sha biyu. “Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun” lya abunda bakinta ya iya furtawa kenan saboda irin makarar datayi. Tun ‘karfe Biyar na Safe ta tashi daman tayi sallah da wanka daga nan ne tasa alarm na ‘karfe shida awayarta sabida barci barawo ne, kada ya saceta Ashe dei kuskure tayi tasaka alarm din ‘karfe tara. ‘ Ai kuwa duk wannan shirin datayi jiya ta zama abanza domin ko kayan barcin dasuke jikinta bata ciresu ba, ahaka ta zunburo doguwar hijabi wanda suka rufe dukjikinta. cikin sauri tadau takardunta wanda tun jiya tarigada ta shiryasu waje daya tareda key’n motarta. Tana daukowa ta ruga aguje tamkar ga ‘san gudu takeyi inda tagangaro ‘kasa Momy na ‘kokarin mata magana amma inaa tun tuni tayi waje, tashige motarta full speed 
loading…

take ta ‘kata, gudu take akan titin tamkar firewa da motar zatayi. Aiko tana shan konan unguwar companin tasu tahango tarin jama’a. Mutane ne ko ta ina akan hanyan, Motoci iri daban daban, duk sun rufe hanya babu wurin wucewan mutum Barre tamota. Mamakin hakan yasa ma’inah fitowa daga motarta, daman saura mintuna ‘kalilan tayi latti zuwa wajen aiki koma ince ta mayi”such a crowd meyake faruwa anan neh?”. Ta tambayi wani Security dake tseye cikin rundunar mutanen. 

Hajiya yau hanyan nan bazata biyuba domin Oga yasa anrufe duk hanyoyin shigewa, Sabida akwai wani dan aikin damukeyi anan. ‘Dan Sandan ya amsa mata kai tseye. “Wace irin aiki? Takatseshi cikin bacin rai “Shi Ogan naku bashida hankali neh? Ko don shi kadei akayi hanyan? muma nan aikin za’mu se yaya? maza kubudemin hanya in wuce saboda banida lokacinku 
Wani Matashin Saurayi dake tseye a gefensu neh ya soma bakinsa cikin maganar “Hajiya ki iya bakinki, gwara ma kijuya kiyi gida domin idan Mutanen Master Zaid Muhammad Zabir sukaji wannan maganr dakikeyi bazayyi dad’i ba, domin Zaid ba mutunci ne dashiba. 
“Zaid Muhammad Zabir” Shi waye? Shi din banza, shi d’in wofi wallahi nidei qaton banza bazai hanani zuwa wajen aikina ba;. Tana wannan maganar ko tseyawa batayiba tashige aguje tanacewa; Ina ogan naku na tabbata idon nayi masa magana zaisa abarni intafl, don darajar Allah kuhadani dashi, ina yake? Se shigewa takeyi bata fasa ba har seda takai ba’kin kofar ZMZ hotel anan yan sandan suka tse da ita tun awaje suka hanata karasowa ciki. ‘karfe Goma dedei tagani a gogon wayarta ‘inna lillahi wa Inna ileihi rajiun, shikenan Daddy na ‘karya alkawarinda na cewa zanyi iya bakin kokarina wajen ganin na cika maka burinka’ Anan tazauna tana hawaye ta rasa meke mata dadi arayuwar duniya ‘ko Ma’isha taje interview oho, itakam tarasa me zata fadawa Daddy idsn ya tambayeta dalilin rashin zuwanta’ haka tacigaba da zama zuciyarta na’ta sake sake, se chan anjima tamike cikin tsananin bacin Rai ta fece a guje tasubuce musu. Aiko se gata cikin ZMZ Hotel, bata tsaya ko inaba se CEO louge inda Kai tseye tafara bubbuga kofan “Zaid kadubi girman Allah kasa masu gadinka subarni inwuce wallahi ina matukar bu’katan wannan aikinda Daddy yasamomin”…. Bata rufe bakintaba yan sandan suka ‘karaso wajen suna mata korar kare, wasu har duka suke mata wasu suna zagi. 
Autan Maza Zald, yaro da kudi abokin tafiyar manya. Kekkyawa ne mai tsananin Farin jini wajen Yan mata yanada suran models, idanuwansa sunada tsananin kyau wanda zayyi wuya kuhada idanu ba tareda kaji wani iri azuciyarka ba. Hakan yasa mata suke bala’in mutuwan Sonsa, yanada gashi agefen fuskarsa wanda suke matu’kar sheki suna ‘kara masa kyau, dimples dinsa kuwa a bayyane suke no matter what, ldanunsa daban suke daduk sauran idanuwa, sunada tsananinjan hankali wanda adalilin haka yasa Zaid baya kuskuren 
had’a idanu tareda mace ko ita wacece. 
Zaune yake kan wata kujera mai tsananin laushin tsiya yana daddanna wayarsa tahanu 
inda yafara jin hayaniyan mutane a kofar louge dinsa. Zaid kuwa babu irin abunda yafi tsana a duniya irin hayaniya. Mikewa yayi Kai tseye aka bude masa kofa Yana tamabayar 
masinjansa meke faruwa? 
Wani dan Sanda ne ya tsara masa “Boss this girl is trying to create a scene here, tace tanason kuyi magana wai abuda mata hanya tanaso taje office”. Kashe muryarsa yayi ahankali yace; tashigo. Wanda Ko da kusa dashi kake ba lallai bane kaji abunda yafad’a. Ma’sinjansa ne ya’kara fadamusu; Boss yace abarta tashigo. 
Ma’inah kuwa ana cewa tashigo, dadi ya mamaye ta, da sauri ta haura sama inda a kofa security ya tse da ita “Madam remove your hijab muyi checking inki”. “Kuyi hakuri kananan ‘kaya nasaka bazan iya cire hijabi na ba, Amma na tabbatar muku babu komai ajikina; Ma’inah tafada cikin ladabi da biyayya. 
Bata kaiga rufe bakintaba wani soja yazo Kai tseya ya zare hijabin dakejikinta yanacewa; Boss baya zaman jira, ke kuma bakya Jin magana maza shige ki sameshi aciki. ‘kunya ce matuka tamamaye ta, alokacin jikinta duk tayi sanyi inda tafara zubar da hawaye tana rokansa yabata hijabinta. Bai tankamata ba, ahaka take tseye akayi checking d’inta gaba d’aya daga nan yamiko mata hijabinta, ita kuwa ranta yarigada yagama bacewa alokacin ko kulashi batayiba, ahakan tabude kofan Zaid Louge tashige ranta a bace babu inda ta tsaya se wajensa inda ko tsoro bai bayyana afuskarta ba tadaga hannu ta sinkeshi da mari. 
Shiko tunda yake rayuwarsa  ta duniya babu wanda yataba marinsa se Ma’inah, ko daga masa murya babu wanda ya Isa aduk fadin duniya Amma a yau wannan garbage din tawuce gona da iri. Allah wadaran masu kudi irinka, mara mutunci Wanda ko kadan baka ganin bukatar mutum se takanka’ Ma’inah ta tseya akansa tanata sauke haushinta. Shi kuwa se yanzu yamike, inda Kai tseya yasa hannunsa yarufe bakin nata. Yace’you talk too much‘ Zaid tunda yake rayuwa a duniya bai taba daga idonsa yaga cikin tsabar idanun ya mace ba se yau akan Ma’inah kenan inda cikin sassanyan muryarsa yace; Watch your mouth, ba’a fadamin banzan magana a kwana lafiya. Ina kike saurin zuwa haka, har kikeson 
ki gagari Zaid Security Agent?
Ma’inah tana ganin Idanuwarsa jikinta yayi sanyi inda zuciyarta ya fara bugawa, yana dukan uku uku, nan da nan tsoronsa yashige zuciyarta domin bata tabajin irin wannan feelings dataji alokacinda Zaid yakura mata ido ba. Muryarta na karkarwa tace; In… Inter… Interview za ni a KSM Bulders. 
Tana fadan wannan tasanya hijabinta, tayi waje cikin rawanjiki.
Zaid koh komawa kan kujerarsa yayi Yana murmushi; KSM Bulders, now ZMZ Builders, Zaid Muhammad Zabir Builders. Welcome to hell young lady…. 
IYA ABUNDA YA SAWWAKA AYAU KENAN KEEP 
CHAPTER 6 (SIX) SPOILER ® 
Banason mu sake had’uwa dashi a rayuwata, idanuwansa sun hanani barci, zuciyata ta ‘kasa sukuni tun lokacinda muka hada ido dawannan kekkyawan hallitan, Ya Allah karabani da sharrinsa, inma Aljani ne ya Allah rabani dashi har abada. 
Daga nan Ma’inah tayiwa annabi sallati ta tofa, bayan ta kammala karatun al_Qur’ani ta kwanta ko barcin zai ‘kara daukanta. Ai kuwa tana fara gengedi idanuwan Zaid suka sake dawo mata ‘Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun wannan wani irin masifa ne’. Haka tamike ta ‘kara daura al_wala taci gaba da Sallah har zuwa wayewar gari. 
Bayan ta idar da sallan asuba, tashige bathroom tayi wanka cikin mintuna ‘kalilan tasanya Kaya ko Hoda bata shafa a fiskarta ba haka tashirya ta fita suka gaisa da Momy tawuce 
office. Tunda tafara tuki take ko’karin kauda tunanin Zaid amma abun yaci tura harta kai Confanin aikinta. 
Tayi parking motarta a wajen daya chanchanta, tafice cikin sanyinjiki tayi cikin office inda taketa mamakin girman wajen dakuma tsarin ginin hartakai wajen receptionist cikin wannan tinanin “Madam you are welcome to ZMZ Builders how may I help you?”… Idanuwarta ta zaro kororo kororo, gabanta yafadi cikin mamaki tace; What Zaid Muhammad Zabir? 
Inda yayi dedei da lokacinda Zaid da bosawansa suke shiga, Tsayawa yayi batareda ya fuskanceta ba yace; Show some respect, confanina Kike so call me Boss or CEO… 
Hmm
KUBIYONI A TAGWAYE PART 6 DOMIN JIN CIGABAN LABARIN. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *