TANA RAINA CHAPTER 6
Washe gari da safe bayan sabreen ta gama sharan gida tas ta gyara ko ina sannan suka zauna a tsakar gida suna suna shan koko da kosai😋, sabreen tace mammina ina sauraronki akan lbrn mahaifina, mammi tace to bari mu gama karyawa koh, to mammi da sauri ta kare ta tattare komai seta dawo ta zauna ta zubawa mamminta ido👀. Mammi tace haba sabreen wannan irin ido da kika samin haka, sabreen tayi murmushi tace nafiso inyita kallon fiskarki yayinda kike magana mammina sam bana gajiya da kallon kyakkyawar fiskarki, mammi tace fiskar nawa har takai naki kyau? To mammi ai kyawunki na d’auko😀, mammi ta mik’e tare da shafar kumatun sabreen tace Allah ya rayamin ke sabreen Allah ya miki albarka bari naje band’aki sena dawo kinji, Ameeen mammina toh ina jiranki, har mammi ta dauki buta zata shige bayi, se sabreen tace mamminah, juyowa mammi tayi ta kalleta seta taso aguje ta rungume mamminta sosai kawai se taji hawaye nabin kumatunta, mammi ta ajiye buta tace sabreen hawayen me haka kuma? Sabreen tace wlh mammina haka kawai naji inaso in rungumeki kuma in zubar da kwalla😥, mammi ta share kwallan idanunta ita tace to shikenan sabreen jeki jirani yanzu zan fito, seda suka rungume junansu kafin ta koma ta zauna. Hayaniya sabreen taji a waje ana cewa maciji maciji, ai da sauri ta fito waje dan ganin macijin, mutane ta gani dewa suna bin macijin a guje ana cewa wannan macijin babbane gaskya zai cutar da mutane idan ba’a kasheba, itama seta fara binsu can setaga macicin ya haura ta katangar band’akinsu tun kafin ya gama haurawa aketa kai mai jifa da duwatsu har an samesa daga wutsiyarsa amma seya haura band’akin, nan jama’a suka ce ya shiga gidansu sabreen muje mu kash…basu karasa maganaba sejin ihu sukayi daga cikin gidan, da gudu sabreen tayi cikin gida dan jin mahaifiyarta na ihu, tana shigowa taga mamminta ta fito da buta a hannu idanunta sun fara juyawa, da sauri mutane suka karaso sabreen ta fara kuka tare da rungume mamminta tana cewa lfy mammina meya samekine, mammi ta fara mata nuni da bayan wuyanta, lekawa tayi taga saran macijine a bayan wuyanta, seta hango macijin yana nema hanyan guduwa, da sauri tace gashican ku kasheshi ya ciji mahaifiyata, ai kuwa macijin kamar yaji abinda akace ya juya zai koma ta katangar, lokacin mammi tana ta cewa sabreen ki kula da kanki ki rek’e ibada da gaskya, mammi kiyi shuru zamu kaiki gun malam dare yanzu babu abinda zai sameki se kuka takeyi tana rungume da mamminta, saukar mutum taji daga sama ammab kuma bataga komaiba, da sauri mammi ta d’ago kanta dan taji wata irin murya yana cewa kiyi hakuri mammi nazo a makare macijin wannan MACEN ta sari kansa batare dakan ya rabu da jikinsaba sannan tazo hargun dasu mammin suke, su kuwa jama sunga dai macijin akan garu bai saukaba kuma basuga wani nauni a jikinsa dan haka sukayita kai masa sanda da duwatsu da kuma sara, take macijin ya fara fidda jini a jikinsa nan sukaita murna sun kashe maciji, basusan MACEN NAN bane ta kashesa. Mammi takai dubanta ga MACEN, macen tayi murmushi tace kiyi hakuri mammi seyau Allah yayi zaki ganni nine dai wannan yarinyar da mijinki ya rasu ta dalilina, nayi miki alk’awarin kula da sabreen insha Allah bazan bari a cutar da itaba😰, murmushi mammitayi😊 tare da cewa nagode, sabreen ta kalli mammi ta kalli inda mammi take kallo ita dai jama’an da suka kashe maciji kawai take gani, sabreen tace mammi ba godiya zaki musuba ku taimaka mu kaita gun malam dare, hawaye itama macen tafarayi dan yadda taga mammi nayi dan mammin ne kad’ai take kallonta. Atake MACEN ta b’ace,sannan mammi ta juyo tana kallon sabreen tace base ankaini ko inaba sabreen kicewa kakanki ya baki labarin mahaifinki sannan kuma sabreen ki kulada kanki ina kaunarki sabre….😭😭😭