TANA TARE DANI CHAPTER A
ANAS
K’auyen Bama dake jihar Maiduguri, Borno.
Da yammacin ranan Asabar misalin k’arfe biyar da mintuna aka. Ruwan sama akeyi me ni’iman gaske, ga wani iskan dake hurawa me kad’a bishiyoyi da flawoyi, ko ina ya d’au sanyi. Tsit kukeji a garin, yara da manya, maza da mata kowa na cikin gdajensu, masu tafiya akan hanya kuwa sun faka gu d’aya, motoci dabasu fi a k’irga ba ke wucewa time-to-time. Can k’ark’ashin wata bishiyar ’yim na hango wasu samaruka guda hud’u wanda barasu gaza kuma barasu fi shekaru 17-18 ba.
Daga nesa nake, amman hakan be hana ni tantance kyakkyawan cikin wad’annan samarukan ba. Wani kyansan ma sanda na gama k’arisowa, fari ne yellow shar da gashi kwance a duk sassan jikin d’an Adam da akasan na tsirar da gashi. Gashin kansa nada yawa saidai bawai afro tayi ba saboda tsantsin gashin bai tsayuwa, luf-luf yake kwance a kansa, bak’i k’irin yana yalk’i wane yasha mai.
Saje ne kwance akan farar fatar fuskarsa wanda da ace yanada gemu da sun had’e. Gashin girarsa ba a cike take erin thick dinnan ba, silky yake a kwance d’an siriri wane yayi carving nasu. Dogayen eyelashes nasa wanda suke kallon k’asa santsi ne dasu. Bashida dara-daran idanunu, idanun nasa suna nan madaidaci da k’wayoyin idan nasa light blue wane na bature.
Nasha jin ana cewa a Africans akoi masu blue eyes ban tab’a yarda ba sanda naga wannan saurayi. Hancinsa ma ba dogo har bakan nan bane, daidai yake cikin ‘yar fuskarsa wanda yakasance shi ba dogo ba bakuma gajere ba. Bakinsa light red yake d’an madaidaici cikin fuskar tasa. Dukda cewar ya d’aure fuska hakan be hana dimple na kumatun damarsa lotsewa ba wanda babu hakan a na hagun.
A zaune yake amman hakan be hanani tantace tsawonsa ba, dogon na miji ne, yanada faffad’ar k’irji duk da cewar siriri ne. Ofcourse ana cewa d’an Adam bai cika goma but za’a iya kiran wannan saurayi hallitar data cike goma bansani ba halan ya gaza ta hali amman inde ta hallita ne kam masha Allah, Allah yabasa, ban tsammanin akoi macen da zata ga wannan saurayi bata kuma kallonsa ba. I mean ba mace kad’ai bama kowa in all.
Sanye yake da mint blue T shirt wanda ya mugun amsar farar fatarsa, jeans na jikinsa kuwa tad’an kod’e alaman tasha ruwa. Rik’e yake da kara a hannunsa yana wasa dashi da siraran yatsunsa wanda suke nan kan ba na miji ba.
Gefensa saurayi ne me kama da shi sak, saidai komi na wannan kyakkyawan yafi nasa, kuma shid’in be kai kyakkywan fari da k’war jini ba, duk yadda akayi wansa ne na jini saidai na kasa tantance wane babba cikinsu. Sauran biyun k’arshen kuwa chocolate skinned suke, saidai still d’aya yafi d’aya haske.
“ANAS na mata kenan!” Cewar d’an bak’i na k’arshen tare da kewayo da kallonsa kan kyakkyawan cikin nasun wanda nake da tabbacin shine ANAS d’in yana mai murmushi wanda hakan ya bayyano da brown teeth nasa, tabbacin kanuri ne shi kenan. “Uhm uhm fa BAANA!” cewar me haske na gefen d’an bak’in da yayi magana yanzun kenan. BAANA yace, “ah’ah barni in tsokanosa de.” Shide kyakkywan nasu da ake kira da ANAS be tanka saba, hasali, yi ma yayi kamar besan ana magana a gefensa ba se b’antare karan dake hannunsa yakeyi yana kallon yadda ruwan saman ke sauk’owa.
Wanda nake kyautata zaton wan Anas d’in ne yace da d’an bak’in gefen nasa “barsa de KASHIM, neman magana yake yau gun ANAS.” KASHIM ya karkato da kallonsa kan BAANA “aikam naga alama rad’au a fuskarka, kuma wallahi kasan inya shak’ure ka bame k’wato ka, kasan halin mazan namu. Ko mata ma bai ragar masu ba bale kai,” ya d’an yi shiru sannan ya k’arisa “gardi” Yafad’a cike da gatsine.
BAANA yace, “hummm zagen dai, naga kap nan gardawa ne har Shettima k’anin mun ma(k’anin Anas knan)” Duk suka k’yalk’yale da dariya illa shi wannan kyakkywa da suke kira da Anas wanda yayi burning face sekace besan me kalmar dariya ba.
Niko miemie na matsu injiyo muryan wannan kyakkyawan da suke kira da Anas. Yawancin anacewa wanda yafiye kyan fuska bai fiye zaqin murya ba kuma hakan ne sanda na jiyo muryan Anas na k’aryata wannan batu.
“You see, ruwan nan na tsayawa barama kuganni anan ba to talk more of kumin tsiya mtschww.” Cewar Anas tare da watso musu harara sekace mace.
Lallai! Allah yayi murya anan, muryar Anas sautin na miji ne da anji amman saidai ba tattausar murya bace, zaqi ce ga me sauroro, bakuma zaqi erin ta mata ba saboda yadda muryar ke cracking a hankali in yana magana.
“Toh Anas meyayi zafi daga fad’in gaskiya? Ai gaskiya ce wallahi kap ‘yan matan garin nan basu san wani na miji sekai, narasa menene kake dashi bamuda, ni da bansanka bama se ince asircesu kayi.” Cewar Baana yana nuna yadda abin ke damunsa.
“Ahhh lallai Baana ka soma zarewa” cewar Kashim cike da mamaki. “Yanzu har seka tambayi ko mesa matan garin nan basu kula kowa se Anas? Bakada ido ne?” Shettima ya karb’esa “gaskia da alama.” Kashim ya cigaba, “k’warank’wasa ace yau ni mace ce nima sena so Anas wanga blue eyes sekace bature, ko ka manta teacher’n English namu da ke sansa.” Suka sake sheqewa da dariya at once kuma sukayi shiru suna jiran tsiwar Anas to thier suprise be ce masu ko uffan ba miqewa yayi da niyar tafiya dukda cewar ruwa akeyi fuskarsa a tamqe kwata kwata abin be basa dariya ba.
“Haba maza yi hak’uri mana karka fad’a min cikin ruwan nan zaka tafi!” Cewar Shettima wansa tare da rik’o shirt na Anas. Harara Anas ya galla masa da nufin ya sake masa kaya, kafin ace me k’arfin ruwan saman ya dad’a k’aruwa ba yadda ya iya dole ya koma ya zauna. “Wai zanso inga Anas yayi aure wataran, muga ya zena controlling wannan uban temper’n nasa da matarsa.” Cewar Baana. Take Shettima ya juya ya kallesa tare da zaro masa ido yana me masa warning.
Dukda cewar Anas be tanka sa ba amman fuakarsa takoma ja alokaci d’aya ya had’e girarsa gu d’aya kallo d’aya za’a masa asan ransa ya b’aci ko dan meh oho? Kodan kiran kalmar ‘aure’ da abokin nasa yayi ne?
Cikin tsiwa yake maganar ba alamar walwala a tattare dashi. “Baana don’t push it, nasha fad’a maka time without number bana san kana min maganan aure ko kuma ‘yan mata in muna tare, that goes to both of you” ya nuna Kashim da Shettima. “Banaso! Banaso! Inhar kuna sona yaci ace kundena for goodness sake!” Shettima ya dafe kafad’arsa “toh maza we are sorry.” kallonsa yayi ba tare da yace masa komi ba sannan ya kau da kai. Baana ya numfasa sannan yace, “toh ka fad’a mana why mana, kullum se kace bakasan kalmar aure ko budurwa amman baka tab’a gaya mana mesa ba, as friends we have to know ko bahaka ba Kashim?”
Kashim ya giad’a kai “sosai mah kayi gaskiya.” Shettima kuwa dayasan mesa wan nasa bayasan wannan kalmomi guda biyu kawai ya kad’a kansa cike da nadama, yayi yayi ya ganar da d’an uwansa gaskia yakuma sa ya yafe wa mahaifiyar su amman ina abin ya gagara sam saboda abinda tayi ta sa Anas ya kariya, zuciyarsa a toshe take da bak’ar kiyayya is hardly aga Anas yana dariya, murmushin ma se in abu yakai ya kawo ne yakeyi.
“I can’t tell you guys, I’m sorry saboda talking about it makes me sick kawai ni kudena tareraya ta da wannan magana banaso give me a break please.” Baana ze sake magana Shettima ya dakatar dashi ta aza yatsa kan lips nasa. In akoi abinda yafi damun wannan abokai guda biyu, (Baana da Kashim) befi wannan halin abokin nasu ba, ace da an kira kalmar aure se mutum ya b’ata rai, aure da ta kasance sunnah me k’arfi wanda kowani d’an Adam keda burin cikata. Gaskiya da abun duba.
Kashim yakasa hakura shikam sanda ya kuma tambaya “Anas munsan baka san maganan nan amman ka dage ka fad’a mana, who knows! we might be of help.”
Juyowa Anas yayi ya kalle sa tare da wata murmushin takaici ta gefen lips nasa wanda a sakamakon hakan ya bayyano da fararan hak’waransa da suke kamar an daidaita tsawonsu “help? Hmmm, k’arshen k’ok’arin da zaku iyayi shine ku dawo da ita kuma koda kunyi hakan ma barinyi appreciating ba saboda tafita a raina, bana san sake sata cikin idanu na, ta cuceni ta cuci two siblings d’ina Shettima da Amal, and most of all ta cuci Abuu (mahaifinsu). I don’t want her ever in my life.”
Cike da mamaki Baana yace, “subhanallah wa kenan?” “Bade mahaifiyarku ba?” Kashim ya tambaya. Anas bece dasu komai ba Shettima ne ya giad’a masu kai da nufin eh mahaifiyar su Anas ke nufi. “Subhanallah! Subhanallah! Anas be kamata kana maganar mahaifiyar ka da ta kawo ka duniya haka ba, uwa uwa ce. Kome tayi maka ka tuna ita ta kawo ka duniyah.”
“Thats my point!” Anas ya fad’a a masifanche. “Ita ta haifeni, ita ta kawo ni duniyah abin dayafi ban haushi fiye da komai kenan. Taya matar da ta kawo ni duniyah zata tafi ta bi wani na mijin daban ta bar family’nta a baya, How? Why? Mesa mata basuda tausayi? Mesa Allah yayi su mugaye masu san kai da abin duniyah mesa? Mesa basuda Imani? Mesa tayi breaking heart na Abuu haka? Har yau yakasa trusting wata ‘ya mace a duniya. Why does it have to be this way? Why? Mstchww!” yaja tsaki cike da haushi.
“We are sorry” Kashim yafad’a cike da tausayi, so wannan grudge d’in Anas ke holding a zuciyarsa har yanzu saboda abinda mahaifiyarsa da Shettima tayi musu. Yau shekaru kusan bakwai kenan da sanin junansu amman be tab’a sanin mesa Anas ke cikin k’unci ba, kullum ba walwala a tattare dashi se yau. Tun ba yau ba yakeson jin me tarihin Anas amman Anas ko kad’an baisan maganar haka zalika ya hana wansa Shettima fad’a ma kowa. Yau d’inma halan saboda sun tak’ura masa ne yasa ya fad’a.
Tun da suke a secondary school haka Anas yake, ko erin secondary school dating da akeyi d’innan Anas be tab’ayi ba hasali betab’a showing koda slightest interest akai ba ma. Unlike his brother Shettima daya d’au komi as k’addara yake living life nasa peacefully cikin walwala da dariya.
Tunanin ya zeyi ya karkato da hankalin friend nasan kan gaskiya yake. Gyaran murya yayi sannan a hankalche yace “Anas we are all here for you, we are like brothers yanzu. Nasan how hard this must be for you amman dole kayi haquri ka rungumi qaddara kamar yadda Shettima yayi.”
“No Kashim, I can’t baran iya ba. Karka had’ani da Shettima, Shettima was a small kid back then time da abin yafaru, definately ya manta komai bare iya tuna koda abu ba, but me? Da wayona da komai na wannan matar ta tattara kayakinta, we were all begging on our knees muna roqarta karta tafi… Mschww I don’t want to talk about it banasan ciwon kai, you two have heard enough.” Anas ya fad’a tare da miqewa daga mazauninsa. “Finally ruwan ya tsaya” yayi qoqari canza topic d’in, yana miqa wanda a sakamakon haka joints na jikinsa suke sakar k’ara. “Shettima lets get going, yakamata mud’an taya Ummee da aiki kafin Maghrib yayi” (Ummee; k’anwar mahaifinsu wacce takasance tamkar uwa a garesu tunda mahaifiyarsu ta tafi ta barsu take kula dasu).
Shettima ya mik’e shima suka d’anyi manly shake da juna, “alright! Se mun had’u a masjid” Anas yace da Baana da Kashim da suke zaune har yanzu sannan ya juya shida Shettima suka soma tafiya.
“Huh!” Kashim ya numfasa, “ina tausaya wa abokin nan namu, like sosai. Zuciyarsa ta riga ta toshe da tsantsan k’iyayya.” “Sosai fa Kashim, but tsaya kaga wani abu yanzun nan ze dawo” cewar Baana yana murmushin jin dad’i. “Bade ya manta blessing d’inba?” (Yaren da masu shaye shaye ke amfani dashi wajen kiran ‘wiwi’). Baana yace, “Yup!” Tare da d’aga girarsa sama yana murmushi.
© miemiebee
TANA TARE DA NI… PAGE 02
BY MIEMIEBEE
Tafiya suke a sahu d’aya, tsayin nan nasu na nan d’ai da kad’an Anas ya d’ara Shettima inba wai ance ya da k’ani bane za’a zata agemates ne. Daidai lokacin da suka yanko wata corner kenan Anas yasa hannu a aljihu yaji wayam ba komai, cak ya tsaya hakan yasa Shettima tsayawa shima. “Ya maza lafiya?” “Ba lafiya ba, go ahead I’ll catch up nayi mantuwa.” cewar Anas. Shettima ya tsaya ya k’are ma d’an uwan nasa kallo sannan yace, “bade blessing d’in ba.”
Anas ya kallesa da gira d’aya d’age sannan yace, “toh meh? Kadega yadda su Kashim suka sani tono maganan chan definately nasan ciwon kai ze kamani and despite that, yadda akayi ruwan saman nan I’m gonna enjoy sleeping.” tare da d’anyin murmushi wanda ya sake bayyano da kyansa tare da lotsar da dimple nasa dake kumatun dama. “Kona yau baraka hak’ura ba?” Shettima yasake tambaya. “Se in na amso karka sha” cewar Anas.
Dariya kad’an Shettima yayi “zan d’an tab’a mana, naji ance da akoi dad’i cikin tea.” Anas ya dafe kafad’arsa “lets go?” Da d’aga kan da Shettima yayi suka juya suka dawo gun Kashim da Baana. Suna iso wurin nasu, Anas yace, “maza bani!” Baana yaci fuska “ban gane baka ba, mezan baka?” “Wai me ka maidani ne? Give me!” Anas ya fad’a a little bit pissed. Dariya Kashim yayi “basa please kaga har yafara losing temper.”
Nan Baana yasa hannu a aljihu yaciro wata leda ya raba into two saidai d’aya yafi d’aya yawa sannan ya mik’a wa Anas kad’an din. “Are you serious? Naga fa wannan abu ni nasaya da kud’ina so kabani me yawan ko in hanaka duka.” Baana yace, “haba! Anas namu na kanmu, kap qauyen nan fa kai kad’aine me blue eyes yi hakuri mana. Aikasan da inada kud’i dana siya nima.” “Toh ni na hanaka yin noma ka samu kud’i? Abeg give me and stop wasting my time.” “Dan Allah fa nace” Baana yafad’a pleadingly. “Okay naji talaka kawai semun had’u a masjid then.”
Daidai sunkai ga shiga corner’n gdansu kenan wata budurwa tafito daga wani gida, sanye take da hijabi iya guiwarta, dududu barata fi shekaru 15-16 ba. Idanunta suna sauk’a kan Anas ta sakar dawata murmushi. Tsuka Anas yaja yasa qaninsa a gaba yana tunkud’esa dan suyi sauri subar gun shiko Shettima daya gano haka tuni ya rage saurin tafiyarsa dukda tunkud’in da Anas kemasa.
Se k’arisowa wajen nasu wannan budurwa ke. “Anas kamar kayi bak’uwa ko? Wannan ba Aisha bace? Ka tsaya kaji me zatace mana.” Cewar Shettima yana murmushi. “Wallahi in bakayi shiru ba zan mareka, kuma barakayi tafiya bane?” Daya wani tunkud’a gaba Shettima besan sanda yasoma matching dasauri sauri suka bar wurin ba.
Isarsu gidah keda wuya suka tarar da Ummee a tsakar gidah tana tsince shinkafa. Da sallama suka shiga ta amsa da fara’arta. ‘yar dattijuwa ce wacce barata fi shekaru 45 a duniya ba, tanada haske sosai amman bara’a kirata da fara ba, ga kyau daidan gwargwado masha Allah!. “Ohhh mazan nawa sun iso ne? Sekuma ruwa ya tareku a hanya ko?” “Eh Ummee” cewar Anas yana k’arisowa wajen da take. “Me kikeyi haka?”
“Tsince nake baba na, tuwon shinkafa Abuu keson ci gashi har ruwan ya tafasa ban gama ba.” “Toh Amal fa mesa bata tayaki ba? Anyways kawo in tayaki Ummee.” “Kai Baba na kaide Allah shi maka albarka” ta d’ago kai tana kallon Shettima dayayi kamar besan ma me suke fad’i ba. “Kai yanzu Shettima koda aiki ze taru ya kasheni ba ruwanka da bari ka tayani ko? Baka ganin wanka ne?”
“Toh Ummee fisbailillahi ina aka san maza da tsintar shinkafa.” Baki wangalau ta bud’e tana kallon Shettima dududu shekarunsa sha shida ne fa da abu aka yake wannan tsiyar bayan ga wansa Anas me shekaru sha takwas bece komi ba. “Ehh hakane, sannu fa” tafad’i cike da gatsine. “Oyoyo Ya Anas” cewar wata kyakkyawar yarinyar da baratafi 8years ba fitowarta daga wata d’aki, ba shakka itace sistersu da suke kira da Amal, kyakkyawace sosai kamar sauran yayun nata bata gama kai Anas fari ba amman tafi Shettima. Su uku kap kamanninsu d’aya.
(Bayan tafiyar mahaifiyarsu daga gdansu da wata takwas ta turo da Amal da wasiqa na cewa tabar gidan da cikin Amal ga ’yarsu nan ta haifota, kwanan ta d’aya a duniya kenan) sanadin haka Anas yake mutuwar san Amal duk rashin kunyarta bata masa saboda duk fitar da zeyi seya siyo mata abun k’walama unlike Shettima da cikinsa kawai ya sani thats the reason why basu shiri da Amal kullum cikin fad’a sukeyi duk sanda Anas yazo kuma seya bata gaskiya, wani sa’in har taran dangi suke masa.
“Oyoyo my angel” yafad’i tare da bud’e hannunsa tazo da gudu tayi hugging nasa. “Ina sweet d’ina ya Anas?” kafin ya amsa mata ta zira hannu cikin aljuhunsa taciro ’ya’yan wiwin da Anas ya amso gun Baana sekuwa idan Ummee yakai kai. “Baba na meh wannan!?” Ta tambaya tare da zaro idanu waje. Nanfa Anas yasoma kame-kame can yace, “laaa Shettima kalli wannan abin da abokin Baanan can yace na rik’e masa” yama Shettima ido. Shettima yace, “ohh yamanta be karb’a ba kenan?”
“Gashi anan kuwa!” Cewar Anas. “Anyways meh abun nema?” ya amshi daga hannun Amal. Ummee tace, “maza ka mayar masa wannan abu shaye shaye akeyi dashi, mayar masa maza!” “Toh Ummee amman bansan ina gdansu ke ba, agidansu Baana muka had’u.” “Nide koma me ka mayar masa.” “Toh Ummee bari in muka fita Maghrib zan bawa Baana ya mayar masa.” Anas yafad’i a hankali
“Toh” tace tare da numfasa. “Ya Anas to ina sweet d’ina toh?” Cewar Amal.
“Angel bansamu na saya miki ba, shops d’in duka a rufe I promise gobe kinji?” A hankali ta giad’a kai tare da turo baki. “Tsaya kiji wani batu” nan ya daidaita tsawonsa yakamo nata tare da rad’a mata wata magana a kunne aikuwa tahau tsalle suna ido hud’u da Shettima ta galla masa harara. “Wallahi Amal niba sa’anki bane wa kke harara? Maras kunya kawai.” Kafin Ummee ta masa magana Anas yace “ah’ah karka zagarmin k’anwa now go inside okay? Anyi ruwa kar mura ya kama ki.” Tana tsalle takoma ciki.
Ba tare da b’ata lokaci ba Anas yataya Ummee suka gama tsince shinkafar banda Shettima daya tsaya kansu yana kallonsu cike da mamaki yarasa meke burge Anas a aikin kitchen bama aikin kitchen kad’ai ba. Bayasan ganin abinda ze tab’a Ummee ko Amal, he is so protective of them, duk abinda zeyi zeyi inhar it will keep them save and happy.
*****
Bayan sunfito daga masallaci iyayensu sukayi gaba a yayinda Shettima, Anas, Baana da Kashim suke tafiya a bayansu suna tattauna warsu ta maza. Wata budurwa ce ta b’ullo gabansu, dakatar dasu. “Ina wuni?” ta gaishesu duk suka amsa illah Anas dake neman any chance yabar wajen. “Anas ina wuni?” tasake fad’i cikin wata anniyar murya ganin shine be amsa ba. Shiru yamata, “Shettima ko nama Anas wani abu ne baimin magana?”
Murmushi k’adan Shettima yayi sannan yayi k’arya “ko kad’an Hafsah mura yake saisa bai iya magana.” Wani kallo Anasa ya watsa masa wanda shi Shettima yamayar da murmushi. Kafin yace wani abu Hafsah tace, “dama zuwa nayi na tayaka murna ne kan scholarahip daka samu cewa nanda ‘yan kwanaki zaka London shine na had’o ma wannan pepper soup sekuma gashi kana mura I’m sure ze d’an wassakar maka da muran ma. Gashi please ka amshi”
Ganin Anas baida niyan karb’a Shettima yasa hannu ya amsa “kai sannu Hafsah kamar kinsan mura na damunsa kika kawo wannan.” Shettima ka tabatta Anas yasha please ze taimaka masa sosai.” “Aii karki damu” cewar Kashim “consider it done, zamu tabbata yasha.”
Da murmushi a fuskarta tace, “toh nagode seda safenku.” Sanda ta sake kallon Anas sannan ta fice. Nan Anas ya finciko Shettima tare da kama masa kunne ya murd’a da iya k’arfin da Allah ya basa. “Awchhhh!” Shettima ya sakar da k’ara. Karb’e kulan abincin Anas yayi ya soma tafiya. Baana yace, “ya haka kuma? Nad’au ai baraka ci ba.” Duk suka k’yalk’yale da dariya. Bece dasu komi ba yacigaba da tafiya, “anji kunya” cewar Shettima nan ma be tankasu ba. Yana isa gida ya tarar da Ummee tana ‘yan wanke-wanke kafin ya b’oye flask d’in har ta riga ta gani.
“Baba na me wancan kake k’ok’arin b’oyewa?” Cewar Ummee da murmushi fal a fuskarta. “Oh wannan!” Ya d’ago flask d’in sama “erm… Erm… Na-”
“Iyye baba na manya har ‘yan matan naka sun soma kawo maka abinci ne, to yayi kyau. Me aciki?”
Kamar ya mata k’arya sekuma ya fasa, “pepper soup ne nakawo wa Amal ko kema zaki tab’a?” “Noo haba! Budurwa takawo wa Baba na kaji kuma se inci je kaci abinka.” “Kai Ummee da Allah bafa budurwata bace.” “Hehe!” tayi dariya sosai “yanzu uwar taka kake jin kunya?” Rashin sanin me zece mata yasa ya wuce ta kawai ya kira Amal suka wuce d’akinsu ya bud’e masu suka sha pepper soup nasu. Ni miemie nace Anas ba kunya yanzu sha yake!? Lol
Sun ci kusan rabin kazan Shettima yashigo senishi yake da alama gudu yayi ya iso nan. “Yanzu Anas cinye kazan nan zakayi da wannan maras kunyan baraka d’an bani ba nima?” “Eh bara’a bayar ba” cewar Amal “Ya Shettiman nan shegen kwad’ayi wallahi ko Ya Anas?” Ta sake p’antarar kazar ta kai baki. “Sosai ma Angel” Anas ya amsata. “Wallahi Amal ki kiyaye ni” gwalo ta masa sanin in Anas na gefe da ita ba abinda Shettima ya isa ya mata.
“Ka kwantar da hankalinka bari mu fita sallan Isha har gidansu Hafsah zanje in fad’a mata ka cinye kazan kap ko k’ashi baka bari ba.” Murmushi kad’an Anas yayi “to ai ko ka fad’a mata ba yadda zatayi ba saboda ban bata fuska ba.” Haka ya dake sanda suka cinye kazan tas shida Amal, pippike da wuya suka ragar sannan Anas ya ceda Amal ta mik’a ma Shettima da yawunsa ke d’iga k’asa.
Itako ta d’aga ta ajiye mai “gashi Ya Shettima.” Hannunta ya rik’e tare da danna mata nank’washi aiko tasaki kuka harda na munafirci take Anas ya k’ariso ya rama mata.
***
Haka ma da suka dawo sallan Isha Aishar d’azu ta tsaresu tare da masu sallama kap suka amsa illa Anas. Sak batun da Hafsah tayi haka Aisha ma tayi sede nata chips da omalet ne, itama na taya Anas murnan samun scholarship da yayi. Anas na jiran Shettima ya amsa kamar na d’azu aikuwa yak’i. “Dan Allah kayi hak’uri ka karb’i Anas ni badan kasoni na kawo ma ka ba, consider it as a friendship gift please.”
D’ago blue eyes nasa yayi ya kalleta ciki ciki wanda tuni ta soma shaking tare da kawar da kanta. Ajiye flask d’in tayi a k’asa “dan Allah ka d’auka se da safenku.” Aiko tana shigewa cikin gdansu ba kunya Anas ya d’aga yakama tafiya. Baana yace “andeji kunya” haka suka ta masa tsiya amman ko a kolan rigarsa, duk yasan so suke suci kuma bayarwan ne bareyi ba. Nanma dashi da Amal ne suka cinye wannan karan ko ragowar ma ba’a baiwa Shettima ba.
**
Da misalin k’arfe goman dare bayan kowa ya kwanta a gdan. Anas da Shettima suna kwance kan seperate gadonsu bayan sun gama shan wiwinsu cikin tea. Shettima daya zura wa Anas kallo na kusan mintuna yace, “tunanin me kake haka?”
“Anas?” Nanne ya dawo hankalinsa “yes! kace me?” Shettima ya kuma nanata kansa “nace tunanin me kake?”
Murmushi sosai Anas yayi wanda yasa dimple nasa lotsewa sosai, kad’an daga cikin fararen hakwaransa suka bayyano. “My dreams are about coming true.” “Wani dream kenan?” Shettima ya tambaya tare da tasowa ya zauna kan gadonsa tare da jingina bayansa a jikin kan gadon.
“Don’t tell me bakasan dreams d’ina ba! Ofcourse to be a billonaire se in samu inyi breaking hearts na thousand of women by then kaga na ramawa Abuu abinda mamarku ta masa.”
“Wai wace erin magana kakeyi Anas? Wai yanzu kana ganin in Abuu yaji wad’annan munanan kalamu daga bakinka zeji dad’i? Haba mana kai baka yafiya ne?”
“Yafiya! Har yau bansami defination na word d’in a dictionary ba plus in wa’azi kakeson yi kaje masallaci kayi, kagannin nan? Banasan jin wannan wa’azi allow me to get some sleep yadda nasha ’ya’yan wiwin nan.” Nan yaja bargo tare da rufe kansa ciki a hankali bacci me nauyi ya daukesa.
© miemiebee
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 03
BY MIEMIEBEE
FANNAH
‘kauyen Bama dake jihar Maiduguri, Borno.
Kyakkyawar budurwa ce zaune cikin wata ‘yar k’aramar d’aki bisa gaban wata ‘yar madubin da aka mak’ala a jikin bango. Ba komai bane a d’akin illa katifan dake shimfid’e a k’asa seda bakunan sa kaya da leather carpet ciki. Ba shakka basu da arziki. Dududu wannan ‘yar budurwa baratafi 15 years old ba. Tanada haske sosai, da sirirn hanci dakuma plumpy lips, idanunta ba laifi ‘yan manya ne dadai. Gashin girarta acike yake mekyawun gaske ba ruwanta da zana artificial gira [ba erinsu ni ba;( ] in kuwa aka k’are mata kallo sosai za’a ga alamar had’ewar girar ta guda biyu gu d’aya sede be munanta taba hasali kyau ma yak’ara mata. Gashin idanunta a cike suke kuma dogaye, saje ne a fuskarta kwance luf-luf wane na miji (kaman nawa, lol) gashin kanta dana girarta sun had’e dan yawansu. Hannunta gashi ne a kwance dogaye masu mugun kyau.
Siririya ce de tanada tsawo daidan shekarunta, tana sanye da wata atamfa maroon da torches na white and green, se murza wata ‘yar jan baki pink take a lips nata hankalinta kwance da anganta ansan batada matsala. A lokacin da wayarta k’irar Nokia Asha dake kan cinyarta tayi k‘ara, a hanzarce ta duba tana ganin sunan daya bayyana kai Ya Ahmad tayi murmushin jin dad’i sannan ta bud’o sakon ta karanta kamar haka;
my Fannah I’m outside waiting for you yanzu shigowa na gari ko gida ban lek’a ba just wanted to see you
“yeyy!!” Ta fad’a a fili tana murna. Data gama sa jan bakin ta shafa powder tareda sa kwalli a fararen idanunta take ta dawo wata balarabiya. A garin mike’wa d’an kwalinta ya since ya fad’i k’asa tare da ribbons data k’ukk’ula gashin nata dashi. Fans ko kunsan ya gashin buzayen Maiduguri yake? Erin bak’i k’irin me santsi da tsawo kamar haukan nan? Haka gashin wannan ‘yar budurwa yake.
Ni kaina miemie dana gani sanda na tsorata dukda cewar ita kad’ai ce a d’akin hakan be hanata yin saurin tattara ribbons d’in gu d’aya da sauri ba tasoma k’ok’arin faka gashin nata gu d’aya saidai dan cikar gashin ta kasa, hannun nata suna nan sirara ba fad’i ga uwa uba gashi har tsakiyar bayanta. Kamar wacce zatayi kuka tafito d’akin “Mami! Mami!” Shiru kukeji wani mutum ne wanda bara’a kirasa da dattijo ba danko befi shekaru irin 44-45 dinnan ba ya lek’o daga wata d’aki wanda ya kasance opposite daga d’akin da Fannah tafito da alama mahaifinta ne dukda cewar basu kama kuwa. “Fannah uwata ya akayi? Tsaya mesa kike yawo da kanki a bud’e haka?”
Kamar wacce zatayi kuka tace, “Baba ribbon d’in ne yafita kuma nakasa d’aure gashin, Mami nake nema ta tayani.”
“Shine zakiyi kuka uwata?” Cewar mahaifin nata “Mami batanan tashiga mak’ota.”
“To baba Ya Ahmad fa yazo yana jirana a waje ko gida be wuce ba ya zosa nan.”
“Oh! Keda Ahmad d’inkin nan se Allah. Ina Afrah da Aiman toh?”
“Sun tafi islamiya Baba.”
“Yoh! Kekuma fah?”
“Kai Baba wai yanzu so kake kace ka manta sauk’an nawa? Abinda har Hajji kaje da kujerar da aka bani danayi na biyu.” “Haka fah, taho to in kama miki kan.”
“ Yawwa Baba na.” Da gudu taje ta zauna gabansa shima sanda yayi dagaske sannan ya kama uban gashin nata gu d’aya. Banda tsawon gashin gu d’aya. Wawan cika ne dashi saisa Fannah batta iya kamawa. “Toh nagode Baba.” “Yawwa ‘yar akbarka se ganin Ahmad ko?” Ta giad’a masa kai. “Ki sa hijabi fa tukun kuma kice ya gaishe min da mahaifinsa naji wai ya d’anyi rashin lafiya kwana biyu kuma ban samu na lek’a sa ba.” “Toh Baba zan fad’a masa in shaa Allah.”
D’akinta takoma tad’au wata maroon hijabi wanda ya sake ciro da hasken ta tasa, tare da d’aukar wayarta sannan tafito waje idanunta suna sauk’a kan Ahmad nata ta sakar dawata murmushin jin dad’i. Ahmad saurayi ne me k’imanin shekaru 23. Chocolate skinned yake, yana da kyau dadai gwargwado gasan murmushi. Tsayyayen na miji ne masha Allah!
“Ga sarauniyata ta fito.” Ya fad’a yana mai murmushi. “Gaskiya wankan nan yayi kyau sosai Fannah, kin ganki kuwa? Looking so take away.”
“Ya Ahmad kaide kullum seka riga zolayata. Ina wuni? Ya hanya? Gashi ko ruwa ban samu na d’auko maka ba duk na k’osa in ganka.”
“Laaa ai sarauniyata bata laifi ae, karki damu ni ganinki kad’ai ya kashe min k’ishi.” Hannu tasa ta tare fuskarta a kunyance. “To ya Ahmad mu zauna anan mana kar ka kaji a tsaye.” ta nuna wat benchi.
“Haka sarauniyar tawa tace? “Haka to za’ayi.” Bayan sun zauna Fannah tace, “ya hanya toh? Ya makarantar?” Hannu yasa ya dafe goshi sannan yace, “so hectic fa Queen, biochemistry akoi wahala. Ga Maiduguri zafi like hell”
“In shaa Allah ka kusa gamawa, Allah baka sa’a yaya na.” “Ameen sarauniyata.” Kefa ya school ‘yan matan ss2 koh?”
“Kai yaya! School alhamdulillah” Ta fad’a tana murmushi. Hira suka d’an tab’a na ‘yan mintuna. Shi Ahmad ba abinda yake sake jan ransa kan Fannah kamar san addininta dakuma yawan yarintar ta dakuma sa sa dariya da takeyi in suna tare. Fannah batta magana d’aya biyu seta sa alhamdulillah, subhanallah, masha Allah ko jazakallahu bikhair ciki. Yarinyace me tarbiyan gaske, ga hankali da girmama na gaba da ita koda wasa bata tab’a kiransa da sunansa gatsau ba dole seta sa yayan nan kuma bawai they are related bane tsantsan girmamawa ne kawai.
“Toh yaya na kar na ta jan ka da surutu nasan su Mama duk suna jiran ganinka, kaje gida ka huta.”
“Toh sarauniyata” hannu yasa cikin jakarsa yaciro wata leather sannan ya mik’a mata.
“Me wannan kuma yaya na?” ta tambaya suprisingly.
“ ‘yar tsarabar Maiduguri ne nace barin kawo wa sarauniyata, yi hak’uri ba wani abu me tsada bane.”
“Yanzu yaya karatu kakeyi amman seka rik’a kashe kud’inka a kaina? Ni gaskia kadena banso nafison kana kula da kanka a school.”
“Ko kad’an Fannah baran iya zuwa nan ba tare da na kawo miki komi ba. I prmise you this duk sanda na fara earning salary’n kaina I will spend it on you, ina sonki sosai Fannah ta.”
“Nima ina sonka yaya na. Nagode sosai, jazakalllahu bikhair Allah taimaka ya baka sa’a yaya.” nan ta mik’e.
Mik’ewan yayi shima “ameen my Fannah inasan addu’o’in ki agareni, ba k’aramin taimaka min suke ba.”
Ai saisa kullum nake including d’inka cikin prayers d’ina. Baba na naka sannu dazuwa also, yace ka mim’a gaisuwan sa gun Abba da jiki”
Toh my Fannah, I’ll tell him so se munyi waya ko?” kai ta giad’a a hankali. Wai! Ai na manta kun kusa fara exams ma, barinso jn hana Queen d’ina karatu ba”
“Haba mana yaya ko wayan minti ishirin baramuyi ba?”
Da murmushi a fuskarsa yace ai baki tab’a neman abu kirasa guna. Allah kaimu daren toh”
“Yawwa yaya bo-bye” tamasa murmushi. Murmushin ya mayar mata “bo-bye Queen.” Ahaka tashigo ciki.
Tun kafin ta yo d’aki ta soma bud’o ledar, abaya ce me kyan gaske ga stones kota ina. “Wowww!” kukeji tana fad’i kamar Ya Ahmad yasan yadda nakeson abayah. Nan ta hau gwada wa kan kayarta bayan ta cire hijabin nata. Aiko daidanta tazo gwada yafa gyalen se kud’i ya fad’i daga ciki tana irgawa taga dubu biyar. “Yanzu Ya Ahmad wannan d’inne zece ba yawa. Baba! Baba!” Ta k’olla masa kira tana nufo d’akin nasa.
“Ya akayi uwata ta kaina?” Ya tambayeta a kishingid’e tare da kashe radio’n dayake ji. “Wannan kaya fa daga ina?”
“Masha Allah Ya Ahmad ne yakawo min yanzu kaga harda dubu biyar kuma.”
“Kai Allah shi mashi albarka, shi kullum cikin wahala yake miki? Gashi ko kayan yamiki kyau kika fito kamar balarabiya.”
“Kai! Baba dagaske?” Ta tambaya tana tsalle. “Sosai ma kuwa uwata.” ya amsata. Nan ta irga dubu biyu ta mik’a masa “gashi Baba ka rik’e wannan, Mama ma dubu biyu nida Afrah da Aiman kuma semu raba wannan.”
“A’a uwata rik’e abinki kinji? Ki saya abubuwan da bakida dashi” ya mik’a mata.
“Baba ni komai danake buk’ata inadashi ka karb’a kaji? Ko cafani sekayi dashi.”
“Toh nagode uwata, Allah miki albarka ya cigaba da kare min ke.” “Ameen Baba zan koma d’aki.” Nan ta fice, isarta d’aki bada jimawa ba k’annenta Afrah da Aiman suka dawo.
Atare suka shigo d’akin d’ayan tana nan kamar Fannah baratafi 13 years old ba whereas d’ayan kuma dududu intayi shekaru shine 3. “Ke wai Aiman kullum ne sekin tsaida mu akan hanya da sunan fitsari?” cewar ‘yar babban (Afrah) kenan. “Anyin!” cewar Aiman yarinya ‘yar shekara uku se uban baki.
“Ni kike ma rashin kunya? Iyye?”
Fannah dake kwance kan katifa tana karatun History ta d’ago ta zauna “wai ke Afrah me damuwarki? Shikenan yarinya bara tayi fitsari ba?”
“Ya Fannah ni ban tsoma bakinki ba, nida Aiman nake magana.”
“Aww rashin kunya zakimin? Dama d’azu Ya Ahmad yazo ya bani kud’i nayi niyan baki kad’an daga ciki amman tunda rashin kunya zakimin na fas-”
Afrah ta katse ta, “a’a yi hak’uri Ya Fannah ta.” Da gudu ta haura kan katifar “yaushe Ya Ahmad d’in yadawo?”
“D’azu bakiga abayan daya kawo min ba!” Nan ta mik’a hannu taciro daga cikin wata bako take Afrah data kusan kamota tsayi ta amshi zata soma gwadawa Fannah ta k’wace “kefa bakida seti, akawo min kaya kiwani ce zaki gwada?”
“Su Ya Fannah manya masu samari.”
“Samari? Ai Ya Ahmad ba saurayi na bane miji na ne, kinga yana level 5 yanzu ina ss2 ina ss3 yana neman aiki ina gamawa se muyi aure by then yasamu aiki in shaa Allah”
“Ahh lallai fa soyayya ruwan zuma. I’m envious.” Cewar Afrah.
“Don’t be, kema lokaci ne beyi ba Allah ze had’aki da mijin dayafi Ya Ahmad sona.” “Allah sa!” Afrah tafad’a da sauri “Ameen habibti” cewar Fannah.
****
“Fannah! Fannah! Zo da sauri da Allah” kirar Mami. “Na’am Mami gani zuwa.” Sunnah take da niyar yi kafin tayi nafilar Maghrib kasancewar lokaci ya kusa yi amman dan kirar Maminta ta fasa tajeta. “Gani Mami”
“Fannah yi hak’uri ki siyo min maggi ashago nan kusa wallahi bansan ya akayi ba har ya k’are ban sani ba yi hak’uri kinji mamana?”
“Yanzu Mami aike zakiyi shine sekin had’ani da Allah harda bani hak’uri. Ina kud’in?”
Nan Mami taciro hamsin ta mik’a mata. “Kinga ai kece babba Afrah yakamata in aika amman shegen yawonta tashiga nan mak’ota ganin jaririyar da Ameenatu ta haifa.”
“Ayya ba komai Mami barin yi sauri kafin su rufe shagon.”
“Toh Allah kare.” “Ameen” ta amsa sannan ta fice.
ANAS
“So Anas sauran ka 3 days kafire London kenan?” Cewar Shettima suna zaune a kan wata benchi a bak’in k’ofar gidansu. “Gonna miss me?” Anas yafad’a yana d’aga gira.
“Eh mana I will miss you, nide Anas wallahi ka canza tsoron zuwanka London d’innan nake nan da Bama ma kana shaye shayenka a b’oye bale ace kaje can inda ba idan kowa.”
“Toh yau kuma wa’azi zaka min? Kagannin nan yanzu haka akoi inda mukayi appointment da su Baana I will have my last drink a Bama yau kasan gobe zamu wuce Maiduguri, so kaga dole in sha in bugu tunda na k’arshe ne.”
“Amman kasan Abuu nagari ko? In ya ganka a buge fah?”
“Make up stories for me then, kamar yadda ka saba kace masa fad’a mukayi da wani. I’m going now.”
“Toh masallaci fah?” Cewar Shettima.
“Sena dawo zanyi sallar.” Daga nan ya fice inda suka saba had’uwa in zasuyi shaye shayensu ya je chan suka bugu like never, ko sanin ina suke in aka tambayesu ba sani zasuyi ba.
Daidai Anas ya tashi ze tafi gida kenan aka soma wani erin masifaffen ruwa ba yadda Baana basuyi dashi yajira ruwan yad’an tsaya kafinnan ma hankalinsa yad’an dawo jikinsa ba amman sam yak’i jinsu ana ruwan yasoma tafiya, yazo ma besan ina yake dosa ba dan yadda ya bugu.
**
FANNAH
“Oh No! Shagon Ya Wakil a rufe gashi Mami battada maggin da zata yi amfani dashi dole in k’ara gaba” haka tatayin gaba duk shagunan a rufe amman still bata hak’ura ba. Bada jimawa ba aka soma ruwa me k’arfin bala’i gashi daga can tana hango wata shago a bud’e ta koma gida ba maggin kuma battaso. Cikin ruwan ta cigaba da tafiya daidai ta shiga wata lungu taga wani na miji daga gani a buge yake, duda acikin duhu ne hakan be hanata tantance kyansa da blue eyes nasa daya d’ago yana kallonta ba. Take ta soma b’ari Allah sa ba gamo tayi ba. Mutum da blue eyes.
Addu’o’in kariya tasoma yi jikinta se rawa yake gu d’aya ta tsaya jiran yazo ya wuce tayi gaba itama. Daidai yazo kusa da ita seya tsaya hannu ya d’aga yakai kan fuskarta tuni Fannah ta soma kuka tunda take ba d’a na mijin daya tab’a tab’ata inba Babanta ba. Ga k’arfin ruwan saman koda tayi ihu bame jinta shagon data gani a bud’en ma har sun rufe.
©miemiebee
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 04
BY MIEMIEBEE
Cikin kuka tace, “dan girman Allah bawan Allah kayi hak’uri I beg of you please.” Jikinta se rawa yake tana hawaye. “Bawan Allah dan Allah kayi hak’uri I’m just 15 ba abinda zan iya baka have mercy on me please dan Allah.” Ko k’adan be saurareta ba hijabin jikinta yasoma k’ok’arin cirewa. “Wayyo Allah Mami na! Baba! dan Allah kuzo ku taimakeni! ihu take sosai.”
Hannu yasa ya rufe bakinta. “Duk mata haka kuke, mesa zanji tausayinki? Data gudu tabarmu ta tausaya mana neh? Why will I have mercy on you? I hope you tell her abinda zan miki yanzu saboda itama ta d’and’ana little daga cikin bak’in cikin data sanyamu time da ta tafi ta barmu” Yana d’aga hannu daga bakin nata ya yaga hijabin nata into two. Ihu ta sake sakarwa “bawan Allah dan Allah kayi hak’uri karka lalatani dan girman Allah, kaji tausayi na I’m just 15 years dan Allah ka rufa min asiri karka b’ata min future”
“Data tafi ita taji tausayin mu ne?”
A rikice bakin ta na rawa tace, “ww..wa ce? Ni bansan wacce kake fad’a ba bawan Allah ban tab’a ganinka ba seyau kayi hak’uri dan Allah, karka lalata ni.” Be saurareta ba ya yaga kayanta. Nan ta shiga tare k’irjinta kuka sosai Fannah takeyi tana rok’an wannan bawan Allah’n haka ba tausayi ba inani yayi raping (fyad’e) nata.
Tun tana iya jure zafin har ta sume wajen, kaca-kaca yayi da ita sannan ya fice yabarta ruwan sama ma dukan sumemmiyar jikinta. Shi kansa besan ya akayi ya isa gida ba a daren, kawai ganin kansa yayi bisa kan gado.
A hankali ya bud’e blue eyes nasa wansa Shettima yagani a kansa. Tunanin meya faru yakuma yake nan ya soma lokacin da aka soma ruwa yace dasu Baana ze tafi sukayi k’ok’arin hanasa amman ya k’i jinsu ya hau tafiya can cikin wata lungu.. Wata lungu… Daga.. Can kwata kwata seya kasa tuna meya sake faruwa.
“Anas how are you feeling? Sanda na fad’a maka karka bi su Baana kak’i kasan yadda ruwan saman nan yamaka duka kuwa? In akayi wasa seka kamu da mura.” cewar Shettima fuskarsa a d’aure
“Ina Abuu?” Anas ya tambaya. “Ka gode wa Allah be ganka ba sanda nashigo dakai nan. Anas fisabilillahi mesa baraka rungumi k’addara ka manta da zancen Ummimi (mahaifiyarsu) a rayauwarka ka yafe mata ba? You’re blaming yourself for her mistakes, misleading your life in the process. Haba mana Anas. Saboda Ummimi kasoma shaye shaye me haka please? Yanzu saboda ita ka kusan kashe kanka, abinda tayi ya riga ya wuce se mu rungumi k’addara mu barta da halin ta.”
“No Shettima I can never do that, tariga ta juya min rayuwa, my life can never be normal kamar yadda kakeso, I can never move on barni haka kawai inta misleading rayuwar nawa har zuwa sanda zan mutu. Images of yadda ta tafi ta barmu will never leave my head, they are stuck in it forver”
“Anas wai kai mesa bakajin magana ne ko dan ni k’aninka ne kafisan babba ya maka magana? Bari Abuu ya dawo I think is about time yasan gaskia shima, I’ve been keeping your secret for how many years now? A ganina with time zaka mance komai amman tunda you are not ready to change, tunda baka iya rungumar k’addara ba zan fad’a wa Abuu komi idan ya dawo.”
Sede daya juyo ya kalli Anas yaga ko k’adan ma hankalin sa ba a gunsa yake ba, yayi nisa cikin duniyar tunani.
“Anas?” Ya kira sunansa. Shiru Anas yayi be amsa ba dan haka ya d’an jijjik’a sa. “Yarinyar…” Anas yace fuskarsa cike da damuwa. Se yanzu ya tuna yaga wata yarinya acikin lungun. Amma sam ya kasa tuna ya fuskarta take ko fara ce ko bak’a ko kyakkyawa ko munana, ko doguwa ko gajeriya shide yasan yaga yarinya cikin lungun.
“Wata yarinya kuma Anas? Yau kai ke kirar mace cikin gidan nan?”
“Yarinyar Shettima ina take?”
“Wai wace yarinya Anas, me kake fad’i?” Shettima ya fad’i fuskarsa cike da mamaki
“Yarinyar Shettima, ina take? Ina ka tsince ni?” Cewar Anas.
“Can gaba da gidan gona and also meya sami kayanka duk jini na duba ka banga ciwo ba.”
“Jini fa kace? Ina kayan nawa?” Anas ya fad’a a rikice.
“Na wanke already.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.” Abinda Anas keta nanatawa kenan duk yasa Shettima kid’imewa.
“Wai meke faruwa ne Anas? Wani abu ne?” “A’a nothing thanks please in baraka damu ba I want to be alone in d’an huta thanks.” Shettima na fita Anas ya rufe ido so yake ya tuna fuskar wannan yarinya amman ya kasa, “ina take? Mena mata? Mesa Shettima yace yaga jini ajikin kayana. Oh no! Nayi blaming yarinyar da batasan komi ba akan laifin da Ummimi tayi. Oh no! Nayi raping d’inta subhanallah shikenan nazama mazinaci, Ummimi baran tab’a yafe miki ba abinda kika min, kin cuceni” Dakyar bacci yayi gaba dashi…
**
FANNAH
“Malam wallahi aiken maggi nan shagon bakin titi nace taje mun kuma har yanzu bata dawo ba, wayyo Allah inaji a jikina abu yasamu Fannah tah.”
“Maman Aiman ki kwantar da hankalinki Fanmah yarinya ce me hankali tasan abinda takeyi barata tab’ayin abinda zesa mu cikin damuwa ba.”
“Abin da nake nufi kenan Malam” Mami ta fad’a cike da tashin hankali.
“Fannah bara ta tab’a yin abinda ze samu cikin damuwa ba saidai in za’a tilasta mata.”
“Me kike nufi kenan Maman Aiman?”
“Malam wallahi ji nake a jikina Fannah ba lafiya ba wayyo Allah tun kafin Maghrib fa na aiketa yanzu har Isha bata dawo ba, Allah ba lafiya ba nashiga uku!”
“Maman Aiman ki kwantar da hankalinki yanzu d’auko hijabinki ga lema anan muje mu duba nan mak’ota ko halan tashiga tana jiran ruwan saman ya d’an saurara.” Nan ta d’auko hijabi sunzo fita kenan Aiman ta fito daga d’aki “Mami ina zakuje?”
Idan Mami cike da hawaye tace, “nemo Ya Fannah zamuyi Aiman, bata dawo gida ba tun d’azu” daidai lokacin Afrah ma tafito “zan biku Mami.” tace idanta cike da hawaye tunda take bata tab’a shiga tashin hankali kamar na yau. Fannah ba mutumiyar yawo bace, ba inda take zuwa banda boko tunda ta kammala haddan Al~Qur’aninta. Dole ne wani abu yasameta a hanya, fatansu Allah sa ba sharri bane.
“A’a Afrah ki zauna da Aiman a gida in shaa Allah yanzu zamu dawo.”
“Mami what if something bad ya samu Ya Fannah fa? Please kibarni inje” tafad’a hawaye na tsiyaya a idanunta cike da tausayi da tsoro.
“In shaa Allah ba abinda ze sameta” cewar Baba “ku zauna yanzu zamu dawo.” “Toh Allah kare” Afrah tace. “Ameen” Mami da Baba suka amsa a tare sannan suka fice cikin ruwan sama. Aiman ce ta rik’o hannun Afrah, “Ya Afrah me ze samu Ya Fannah?”
Murmushin dole ta k’irk’iro “in shaa Allah ba komai karki damu kinji? Ya Fannah will be alright.”
*
“Malam suka ce Fannah bata shigo nan ba innalillahi malam dan Allah ina zataje? Ina aka kaimin ‘yata?!”
“Maman Aiman panicking is never a solution kizo mu dudduba kusa ko zamu ganta cikin shagu nan bakin titi” Haka fa iyayen Fannah suka ta duba sak’o sak’on unguwar tasu ba Fannah ba alamarta har sun fidda rai se Mami ta tuna shagon dake gaba da wata lungu a sabuwar unguwa tace suje su duba, sunayin wajen kuwa sega Fannah kwance a k’asa half naked ruwan sama yamata tsinannen duka ko numfashi battayi.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” kawai ke tashi gun both Baba da Mami were shocked hawaye gangara suke daga kumatunsu suna kallon yadda aka walak’antar masu ‘yarsu. Mutuwan tsaye Mami tayi Baba ne yayi k’arfin hali yaja zanin ta dake gefenta ya rufe mata jikinta dashi tare da rungumota yana kiran sunanta sam bata amsa ba dake ko numfashi battayi. Alokacin Mami ta sakar dawata erin k’ara
“FANNAAAHHHHH!!! WAYYO ALLAH!” Da gudu tayo kansu tare da jefar da leman ta karb’e Fannah tareda rungumota tana kiran sunanta “FANNAH! FANNAH! Dan Allah karki tafi kibarmu dan Allah kitashi wayyo Allah!” Kuka kenan!
Mota Baba yasamu da k’yar aka sa Fannah ciki suka wuce babban asibitin dake hukumar Bama. Nan take akayi emergency da ita sam Mami ta kasa daina kuka shikansa Abba kuka yakeyi duk yadda yayi ya hana kan sa kuka ya kasa. Hannun Mami ya rik’e yana bata hak’uri tana kuka tace, “mesa Malam? Mesa se Fannah ta za’ai wa haka? Hankalinta yayi yawa ace an mata wannan tsiya. Malam shikenan an rusa wa ‘yata future Allah ya isa ma duk wanda ya mata wannan d’anyen aiki barin tab’a yafe wa ba…” ta fashe cikin wata erin matsanancin kuka.
Rungumota Baba yayi yana bata hak’uri shima yana kukan. “Nima kaina abinda ke d’aure min kai kenan, wani azzalimi ne kawai yayi taking advantage na innocence nata saboda Fannah bawai tana mu’amala bane da maza bale ace saurayi ne yamata wannan abu, Ahmad ne kawai ke zuwa wajenta kuma nasan Ahmad bare tab’a aikata mumunar abu kamar haka ba.”
**
3 hours later
K’ofar d’akin da Fannah ke ciki ya bud’u likita ya bayyana daga bayansa. Da sauri su Mami suka taresa. “Ya ‘yar tamu likita ya jikin nata?” cewar Mami da Baba a tare. Kai ya k’ada a hankali fuskarsa cike da tausayi. “Likita dan Allah karka fad’a min ta rasu, dan girman Allah” Mami ta fashe da kuka Baba yana bata hak’uri.
“Iyayen Fannah kuyi hak’uri amman munyi duk iya abinda zamu iya dan ceto ran ‘yarku, mun kasa, ya gagare mu, mun kasa at all ruwan saman ya mata duka sosai har na fitan hankali, yabi ta kunnenta da hanci har baki, bayan haka kuma ga raping nata da akayi wanda aka mugun ji mata ciwo. Zafin datayi witnessing yafi k’arfin jikinta yafi k’arfin shekarunta. Yarinya ce sosai. Kuyi hak’uri dan Allah amman kar kuyi losing hope anyi waya dawani likita daga Maiduguri Teaching Hospital gobe da sassafe ze iso ya dubata inhar da abinda ze iya toh se mu godewa Allah.”
Mami dake kuka kamar zata cire ranta tayi k’arfin halin fad’in “likita me kake nufi kenan? har yanzu ban fahimce ka ba ‘yar tawan tana raye ne kokuwa ta mutu?”
“Maman Fannah ni kaina banda amsar wannan tambaya zuciyarta na bugawa yana aiki amman kuma bata numfashi, mun samata oxygen munyi komi still ba progress, kwata kwata bata responding to stimuli.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Malam sun kashe min ‘ya shikenan Fannah ta tafi ta barni, ta barmu Malam” takuma fashewa da wata masifaffiyar kuka Baba na bata hak’uri, shikansa hawaye yake zubdawa shar shar.
“Baban Fannah ‘yarku bata gama mutuwa ba tunda tana numfashi, duk me numfashi aikuwa nada rai kenan. Addu’a kawai zaku sata ciki sosai, Allah sa tayi making it through the night in shaa Allah in gobe likitan yazo seya duba ta. Allah bata lafiya ya k’ara maku hak’uri. Excuse me please.” Nan ya fice. Har k’asa Mami ta sauk’a tana kuka.
In ta rasa Fannah ta rasa komai a duniya cikin yaranta uku ba wacce takai Fannah hankali, ‘yar da zaka aiketa sau d’ari a rana barata b’ata rai ba bara kuma tayi fushi ba. ‘yar da kana ce mata bari ta bari kace yi kuma tayi. ‘yar da is ready to sacrfice the last kobo she have just to make her parents happy. Barata iya rayuwa ba Fannah ba. If only zata iya bada ranta asawa Fannah da tayi.
Kuka take sosai, abin tausayi, tanayi Baba nayi tabbas shima kap cikin ‘ya‘yan sa babu kamar Fannah. Kalmar son kai ko k’adan Fannah bata sani ba, she can give up her own happiness for others…
©miemiebee
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 05
BY MIEMIEBEE
“Malam baran iya shiga ganin Fannah ba, if only zan iya bata raina wallahi zanyi.”
“Addu’a zamu mata Maman Aiman kinsan dole ke zaki kwana da ita.”
“Yanzu Malam kud’in asibitin fa? Taya zamu biya? Wallahi duk d’an iskan da yama Fannah wannan abu be kyauta ba.” Ta kuma fashewa da kuka hak’uri Baba ke ta bata. “Karki damu da wannan, zan sayar da shanu na in shaa Allah zamu biya bills nata dashi, fatan mu Allah bata lafiya”
“Shikenan yanzu dama shanun nan kad’ai muka mallaka, Allah ya isa wallahi.” A sanyaye suka mik’e zuwa d’akin Fannah, Baba na bud’e k’ofa suka hango Fannah kwance kan gado ba alaman nishi a tattare da ita.
Da gudu Mami tayi kanta ta tsuguna tare da rik’o hannunta se kuka take zubawa. “Maman Aiman addu’a zamu mata kuka baida amfani barin koma gida in d’ibo muku abubuwan da zaku buk’ata, kiyi hak’uri” ahaka ya fice isarsa keda wuya ya tarar da Afrah se safa da marwah take a parlour tana ganinsa tayo kansa. “Baba ya kun sami Ya Fannah?” Kallon daya mata yasa jikinta yayi sanyi take idanunta suka cike da hawaye “Baba dan Allah meya sami Ya Fannah?” ta tambaya tana kuka.
“Afrah da rungumar k’addara aka san musulmi, mun samu Fannah amman yanzu haka tana asibiti.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Baba me kake nufi? Meya samu Ya Fannah?”
“Bata da lafiya Afrah, mun… Mun…” Sekuma yayi shiru hawaye na cika a idanunsa sakamakon hakan ya sake tada ma Afrah hankali. Tana kuka tace, “Baba dan Allah ka fad’a min meya samu Ya Afrah.” Zaunar da ita yayi ya bata labarin komai kuka Afrah keyi sosai kamar zata cire ranta sam tace seta bisa asibitin taga yarta.
Ba yadda Baba beyi ba dan hanata amman ta dage setaje. Aiman kuwa ta jima da bacci, bayan sun gama had’a abubuwan da zasu buk’ata Baba ya rakata ya tsara mata abin hawa sanda suka b’ace ya dawo ciki. Tafiyar minti 15 ya isar da Afrah asibitin, bayan ta biya sa kud’insa tashigo ciki direct d’akin Fannah ta wuce.
Tana bud’o k’ofar taga Mami tsugune gefen Fannah se kuka takeyi take itama wani kukan ya faso mata da gudu taje ta rungumi Mamninsu suna kuka sosai. Sunjima suna abu d’aya sannan Mami ta tambayeta “Afrah me kkeyi anan ina Babanku?”
“Mami yana gida na zo ne in tayaki kwana.”
“Afrah bekamata kiga yarki a wannan yanayi ba da kin koma gida.”
“Haba Mami! Ya Fannah fa yayata ce taya zakice haka?” Nan ta jiyo tana kallon Fannah wacce take kamar gawa. Wani sabon kukan tasoma ta rungumeta, tana kuka “Ya Fannah dan Allah karki mutu ki barmu, Allah ze sak’a miki in shaa Allah.” Da kyar Mami ta lalasheta tayi shiru.
Mami ko kayan tean da Afrah ta had’o musu susha tea ma takasa sha hankalinta duk yabi ya tashi. Afrah bata tab’a ganin Maminsu cikin tashin hankali irin wannan ba.
Kwana Mami tayi tana nafilfilu tana rok’an Allah haka itama Afrah bawanda yayi bacci cikinsu.
****
Washegary da safe misalin k’arfe 8:00AM babban likita daga TH na Maiduguri ya iso. Aikin kusan awa uku akayi kan Fannah sannan likitan yafito. Baba, Mami, Afrah da Aiman dake rik’e a hannun Afrah duk sukayi kansa “likita ya jikin ‘yar tawa?” Cewar Mami jikinta se b’ari yake.
“Ku kwantar da hankalinku in shaa Allah ‘yarku zata samu sauk’i tana cikin state of coma ne yanzu within 5-7 days in shaa Allah zata farfad’o.”
“Alhamdulillah!” kukeji a wajen. “Likita amman har kwana biyar? Kana nufin barata san inda take ba har nan da tsawon kwana biyar ko bakwai?”
“Eh Hajiya, she’ve been through alot, raping at this tender age ba k’aramin abu bane, tamugun jin jiki, gakuma ruwan daya mata duka again yasa ta kamu da pneaumonia but in shaa Allah inta farfad’o everything will be alright za’a bata magani karku damu.”
“Toh likita mungode sosai Allah biya.”
“Ba komai” ya fad’i sannan ya fice.
A hankali Umma ta soma kuka “Malam yanzu har kwana biyar ko sati ‘yata zatayi batasan inda take ba? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”
“Maman Aiman godiya yakamata muyi tunda Allah yabar mana ita be karb’i abinsa ba, mu cigaba da addu’a in shaa Allah zata samu sauk’i.”
*ANAS*
_Bawan Allah dan Allah kayi hak’uri kar ka lalata min future, wallahi baran iya baka abinda kake nema ba I’m just 15 dan Allah karka lalata ni kayi hak’uri ka rufa min asiri_
Firgit Anas ya farka daga bacci yana numfashi da k’arfi sosai wanda hakan yasa Shettima tashi shima daga bacci tun jiya yaga yanayin wansa ya canza koda ya tambayesa meh kuwa ce masa yake ba komai, wannan karan ne na farko da Anas ya soma b’oye masa abu. Gadonsa ya bari yaje yasamu Anas tare da dafe kafad’arsa. “Anas lafiya? Ka jima fa bakai mafarkin Ummimi ba, meya faru kuma yau?”
“Ba mafarkin Ummimi nayi ba.” cewar Anas yana raba ido.
“Mafarkin me kayi toh?”
“I don’t want to talk about it karka damu its okay.” Anas yayi k’ok’arin calming kansa.
“Its not okay Anas, tun jiya nake lura da kai, something is bothering you and you’re keeping it to yourself. Tell me.”
“Nace maka ba komai” Anas yayi insisting. A hankali ya mik’e ya wuce bayi. Tun shigarsa bayin ba abinda yakeyi se tunanin mafarkin dayayi akan yarinyar jiya, ko kad’an besamu yaga fuskarta ba a mafarkin. Ruwa ya riga watsa wa a kansa sannan yayi wanka yafito ya shirya kayakinsa da komai dake yau ze tafi Maiduguri, gobe ya wuce Abuja daga can kuma se London.
Yana fitowa daga d’akin nasu ya rufo k’ofar yana juyawa sega Amal idanunta sunyi ja “my Angel waya tab’aki?”
“Ya Anas wai yau zaka tafi baraka sake dawowa ba se nan da 5 years?”
“Waya fad’a miki haka?” Ya fad’a yana wasa da gashin kanta.
“Ya Shettima ne kuma wai kana barin gidan nan ze dakeni wai dama tarani yake, Ya Anas dan Allah kar ka tafi” ta rungumesa da tsayinta daidai kunkuminsa. Sama ya d’agata “stop crying kinji Angel? very soon zan dawo kuma duk sanda Shettima ya tab’aki ki d’au wayan Ummie ki kirani I promise in na dawo zamu rufesa a d’aki mumasa dukan tsiya.”
“Dagaske Ya Anas? Zamu masa duka?”
“Sosai ma bulala zan baki ki zanesa se yayi kuka.”
“Yeyyy!” Hugging nasa tayi “I love you Ya Anas.” “I love you too Angel. Sauk’o to muje wajen Abuu.”
“O’o ni muje a haka ka d’aukeni for the last time.” “Okay Angel” ya manna mata kiss a goshi sannan yaja akwatinsa suka fice. Suna isa parlour ya sauk’eta tare da gaishe da Abuu sannan Ummie.
Breakfast suka ci bayan sungama Abuu ya zaunar da Anas.
“Anas kaga karatu zakajeyi ba hutu ba kuma kafi kowa sanin wahalar da mukayi kafin muka samo maka wannan scholarship I’ll be very angry inhar baka je kacika mana burinka na zama architecture ba.”
“In shaa Allah Abuu” cewar Anas dake kallon kan carpet.
“Kasani kuma duk abinda kakeyi Allah na kallonka, kowa yasan ya rayuwar London yake, inbanda iskanci ba abinda sukeyi, ba ruwanka da zuwa beach bale kaje kaga abinda ze hana ka d’aukan karatu. Qur’ani shine guidance naka, karka kuskura kabari rana ya wuce ka baka d’au Qur’ani ka karanta ba. Ba ruwanka da ‘yan mata ko friends na banza. Ba ruwanka da shaye-shaye Anas. Kajini ko bakaji ba?” ya gargad’i Anas tare da rik’e kunnensa.
“Naji Abuu na gode in shaa Allah zan kiyaye duk wannan abubuwan daka lisafo, nagode.”
“Toh Baba na nikam nasan ko ban ja maka kunne ba kasan what is right and wrong, ban tab’a doubting tarbiyarka ba. Allah baka sa’a ya kareka daga kowani irin sharri Baba na.” Cewar Ummie.
“Ameen Ummie nagode.”
**
“Amal kukan me ne kuma haka sekace mutuwa yayan naki zeyi? Makaranta fa zasa in shaa Allah ze dawo.” Cewar Ummie tana lalashin Amal dake ta kuka.
“Bar shakwab’a de Ummie ke kike biye mata ma ai, tayi kukan jini tagadama ta mutu.” Shettima ya fad’i yana ma Amal dariyan mugunta. Harara ta watsa masa me rai da lafiya “toh nak’i kukan” tasa hannu ta share hawayerta “kaine zaka mutu mugu kawai.”
“Ke! Rashin kunya kike min?” Ya mik’a hannu ze finciko ta daga jikin Ummie, hannu Ummie tasa ta make hannun nasa da k’arfi “okay dan Amas yatafi zaka soma cin zalin Amal ko? Toh kasani Anas yace duk sanda ka tab’a ta in kira sa a waya in fad’a masa dan haka ka mayar da hankalinka. Kai kullum kata biye wa ‘yar yarinya duk kabi kasa ta raina ka.”
Gwalo Amal tamasa harda sa hannu kan kunnenta. “Ni shikenan Ummie kullum ma wannan maras kunyan zaku na ba wa gaskiya wallahi kicigaba Allah kawo rananda za’a barni dake gidan nan.” ya cize yatsa.
“Karki kula sa Amal taho muje mu siya miki sweet ga kud’i nan dayawa Anas ya ajiye miki.” Juyawa tayi tasake ma Shettima gwalo sannan suka fice da Ummie.
***
Da misalin k’arfe 1:00pm Ummie ta kira wayar Anas ringing kad’an yayi ya d’aga “hello Ummie” yafad’a cikin muryarsa me dad’in gaske.
“Baba na ya gajiyan hanya?”
“Alhamdulillah Ummie tun d’azu muka iso ai, ina gidan chairman ahaka.”
“Toh yayi kyau, Babana kaji abinda Abuu ya fad’a maka ai? Nasan kanada hankali kuma kasan abinda ya kamata kar kayi abinda ze haddisa mana matsala kaji ko Babana?”
“In shaa Allah Ummie karki damu, ina Angel d’ina?” “Tana parlour tana kallo barin kai mata.” Nan ta mik’e takai wa Amal “ga Ya Anas nasan yanason ku gaisa.”
“Ya Anas ina wuni?”
“My angel ya kike?”
“Lafiya, har kun isa London d’inne?”
Murmushi kad’an yayi wanda hakan yasake bayyano da kyansa. “A’a Angel da saura sosai ina Maiduguri ne yanzu se gobe zamu wuce London.”
“Okay! Nagane. Ya Anas kaga d’azu Ya Shettima ya nank’washeni akai dan yaga baka nan.”
“Shettiman? Bari ki riga irgamin duk mugunta daya miki ina dawowa zamu masa duka.”
“Yeyy! Ya Anas I love you ina kallon frozen se anjima.”
“Yawwa Angel d’ina bo-bye.”
FANNAH
6 days later…
“Mami kukan ya isa mana dan Allah, ki dubi yadda kika rame dan Allah.” Cewar Afrah dake rik’e da Mami itama tana hawaye.
“Afrah kiyi hak’uri ba san ra’ayi na bane nima, yau kwanan ‘yar uwarki shida bata san inda take ba taya baranyi kuka ba. Gani nake kamar zata tafi tabarmu. Allah ya isa, haka kawai Fannah bata masa komai ba ya zab’i ya wulak’an ta ta. Allah ze sak’a mata.”
“Shhh Mami dan Allah karkiyi magana haka, in shaa Allah Ya Fannah zata farfad’o lets not lose hope Mami.”
*
Da azahar misalin k’arfe 1:30PM wani dattijo yashigo cikin asibitin, kallo d’aya za’a masa asan wan Baban su Fannah ne. Zekai shekaru irin 50 a duniya. Baba dake zaune a bakin k’ofar d’akin Fannah ne ya hango wan nasa nan ya mik’e “sannu da zuwa Ya Khaleel.”
“Sannu dazuwa fa kace? Ashe iskancin da ‘yarkan tayi kenan shine ka b’oye min kak’i gaya mun, toh Allah ya sanar dani gaskia.”
“Haba ya Khaleel ya kake magana haka? Kafi kowa fa sanin halin Fannah ba halinta bane tarayya da d’a na miji.”
“Ni ba abinda nake nufi ba kenan, my point is adena kirar ‘yata kariya. Alhj Suleiman kai da d’anka zaku iya tafiya, abincin wani gub’an wani kamar yadda ka k’yamaci Fannah haka wani zeji kamar ya mutu mata. Ahmad Allah had’aka da rabonka, ka kasance masoyin Fannah na hak’ik’aamman there is nothing you can do now dole ka hak’ura kabi umarnin mahaifinka, in zakumin uzuri, I need to see my daughter.” Yana kaiwa nan ya shige d’akin Fannah.
Idanun Ahmad take suka kad’a sukayi ja, koda wasa be tab’a tsammanin akoi abinda ze shiga tsakaninsa da Fannah ba, yana santa fiye da yadda yake san kansa. “Abba dan Allah kar muyi haka, wallahi nasan Fannah is innocent.”
“Ahmad kaji na rantse maka kasake min maganan wannan kariyan zan tsine maka, ai saisa akace a bincike mutum shiru-shiru. Maza mu wuce gida, Alhj Khaleel nagode sosai Allah bar zumunci.”
“Bakomai Alhj Suleiman, ita gaskiya haka take daga k’in jinta kuma se b’ata. Allah rufa mana asiri.” Da fad’in “ameen” Ahmad dake hawaye shida mahaifinsa suka bar asibitin. Suna ficewa ya Khaleel ya b’alle da dariyar mugunta. “Ai dama nace in shaa Allahu ‘yarka barata auri wani ba inba d’ana ba. Kyakkyawar mace me addinin muslinci Farouq ya cancanta kuma ba kowa bace illa Fannah saboda haka tana warkewa zanje in samu Baba (mahaifinsu) in masa magana.”
Gida ya zarce yana isa ya soma k’olla ma d’ansa Farouq kira. “Farouq! Farouq! Zo nan” alokacin ya zauna kan wata tabarma bada jimawa ba Farouq d’in yafito da angansa an ga d’an iska wata shegiyar crazy wando ne a jikinsa da singlet. Ba laifi yanada kyau dadai dakuma tsawo. Bayan ya zauna yace, “gani Baba.” Ya Khaleel ya kallesa sannan yace, “d’ana ka kwantar da hankalinka Fannah ta kusan zama taka, Fannah taka ce! Yanzu ana sallamota daga asibiti zan wa kakanka magana.”
“Baba dagaske!” Farouq ya tambayi mahaifinsa cike da jin dad’i. “Da dana ce maka seka auri Fannah ka d’au wasa nake maka ne? Ai Fannah taka ce.” “Kai Baba na gode amman da akoi matsala Baba.”
“Ina jinka Farouq mecece matsalar yanzu in warkar maka da ita?”
“Fannah… Bata so na Baba ko kad’an zan iya irga sau nawa muka tab’a magana da ita, sam bata sona ta tsane ni.”
“A da kenan…” Ya khaleel ya fad’a yana murmushin mugunta.
“Ban gane a da ba kenan Baba.” Farouq ya fad’a a little bit confused.
“A da datake da tabbacin cewa akoi masu santa amman banda yanzu data rasa budurcinta, kap ba na mijin da ze so ta yanzu, ta zamo tamkar k’azantar da akeson a yasar ne yanzu. Ko baka gane ba?”
“Sosai na gane Baba na gode.”
*
Afrah ce tsaye kan Fannah tana kallonta hawaye suna gangara kan kumatunta a yayinda Baba da Mami suke zaune kan wata kujera, Aiman kuwa an mata shimfid’a a k’asa tana bacci. Hannu Afrah ta mik’a dan ruf’e Fannah mekyau da bargo taga kamar Fannah tad’an motsa.
“Barin je in kama ruwa” cewar Mami “ina zuwa yanzu.” Kai Fannah ta kad’a a hankali again. “Ya Fannah! Baba! Mami! Fannah tayi motsi.” Kafin su Mami su k’ariso Fannah ta soma bud’e ido a hankali tagama bud’e idanun nata ta sauk’esu kan family’nta dake tsaye a kanta suna murmushi da zubda hawaye a lokaci d’aya, murmushin tayi k’ok’arin mayar masu da k’yar.
“Ya Fannah!” Cewar Afrah
“Fannah! ‘yata” cewar Mami.
“Mama na!” Cewar Baba.
Kallonsu take a hankali cikin wata dashasshiyar murya tace, “Mami, Baba, Afrah.” Dad’a k’aruwa murmushin fuskarsu yayi Baba yace, “Afrah jeki kira nurse kice mata Fannah ta farfad’o.” Bayan minti d’aya Afrah dawata nurse suka shigo d’an dube-dube tayi wa Fannah sannan taceda su Mami “Alhamdulillah condition na ‘yarku is stable. Inda hali a had’a mata tea me kauri tasamu tasha se abata magunanta. Excuse me.”
Hugging nata sukayi one-by-one kowa na muranan dawowarta. “Ina Aiman?” ta tambaya a wahalance kusan a tare suka amsata “gata can tana bacci.” “Fannah ya jikin naki?” cewar Mami
“Da sau… Argh!” Tasaki k’ara.
A rikice Mami tace. “ina ke maki zafi Fannah?” Take idanunta suka cike da hawaye, “k’asa na Mami, zafi.” “Malam ko zaka d’an bamu waje dan Allah” cewar Mami cike da tausaya wa ‘yarta. Bayan Baba yafita Mami ta umarci Afrah ma da tafita ba gardama ta fice.
“Fannah kiyi hak’uri dole k’asarki ya miki zafi anji miki ciwo.”
Tana kuka tace “Mami ya rabani da budurci na ko? Mami banida martaba yanzu.” Ta fashewa dawata erin matsanancin kuka.
“Fannah ‘yata dan Allah kiyi hak’uri kukan nan k’ara miki rashin lafiya zeyi, kiyi hak’uri. Ki d’au wannan k’addara ce Allah ya turo miki.”
Cikin kuka tace, “Mami yanzu akoi d’a na mijin da ze yarda ya aureni? Nasan ko Ya Ahmad ze gujeni.”
Shiru Mami tai batace komai ba hakan ya sake tabbatar wa Fannah zancenta. “Yama riga ya tafi ko Mami?” Har yanzu Mami batace da ita komi ba se kuka ba sautin da takeyi. “Mami talk to me please, ki fad’a min gaskia.”
“Fannah kiyi hak’uri wannan jarabawa ce Allah keson gwada ki, in baki rungumi k’addara ba seki fad’i. Ahmad be k’i ki ba mahaifinsa ne ya tilasta masa se ya rabu dake saboda Kawu Khaleel yace masa saurayin kine ya miki wannan abu.”
“Mami amman ai k’arya ne, wallahi bansan shi ba acikin lungu kawai ya tsareni wallahi ban tab’a ganinsa ba inba ranan ba.”
“Shhhh! Fannah basekin min bayani ba sanin kanki ne Kawu Khaleel tinba yau ba baya sanki, yayi hakan ne kawai dan ya shiga tsakaninki da Ahmad dan yaga Ahmad nasanki tsakani da Allah.”
“Mami me na masa ya tsaneni haka? Mena ma wannan saurayin daya k’wace min martaba ta Mami? Shin na kasance mutumiyar banza ce da duk munanan abubuwa suke faruwa dani?” Hannu Mami tasa ta goge mata hawayen dake gangara kan kumatunta, “ko kad’an habibti, ita duniya haka take mutane masu kind heart su Allah yake jarabta saboda ya gwada nauyin imanin su. Wannan jarabawa ce Fannah you have to be strong.”
*****
*ANAS*
D’aki ne babba da gadaje guda uku ciki, haka wardrobe ma, sannan da bathroom aciki. A d’aya daga cikin gadajen Anas ke kwance akai da earpiece a kunnensa wanda ke had’e da wata sabuwar Iphone 6s ajiye kan cikinsa. Sanye yake da ¾ wando da vest bak’a ya zura wa ceiling ido se tunani yake. Bada jimawa ba wasu samaruka guda biyu suka shigo wanda suke nan sa’anin Anas, da angansu anga ‘yan hutu. Gado d’add’aya suka d’auka suka kwanta kai har alokacin Anas besan da shigowarsu ba.
Pillow d’ayan ya wulla masa a firgice ya mik’e ya zauna ganin su ne yasa ya sauk’e ajiyar zuciya. “Mehn! Yaushe kuka shigo bansani ba.”
“Well kayi nisa a tunani taya zakayi noticing shigowarmu?” cewar na k’arshen. “Waima tunanin me kake haka? Kullum fa cikin tunani kake ko ka bar mata da ‘ya‘ya ne acan gda 9ja?”
suka k’yalk’yale da dariya illa Anas daya tsaya yana kallonsu.
“Musty waikam meke damun Anas ne?” cewar d’ayan.
“Ji Abdul de da wata magana budurwarsa ce ni da zan sani?”
“Oh oh no please banda maganan budurwa anan” Anas ya fad’a in an angry tone.
“Wai Anas kai kullum haka kake ne? Ban tab’a ganin kayi dariya ba wallahi, whats wrong with you? And anytime aka kawo maganan girlfriend you seem so moody.” Cewar Abdoul.
“Nima de, abin have been bothering me.” Hannu yasa yaja d’aya daga cikin bedside drawer’n gadonsa tare da ciro wani syrup ya wulla wa Anas karap ya cafke. “Meh wannan kuma?”
“Wannan!” yad’an murmusa “lets say anti-problem kokuma problem reliever.” Shida Abdoul suka kwashe da dariya. Kallaon syrup d’in Anas yayi sannan ya ajiye kan bedside drawer’n nasa “no thanks barin sha ba.”
“Chill bro!” cewar Musty. “It’ll ease all your problems just give it a try.” Haka suka ta cika masa baki kan in yasha ze manta yanada problem ko d’aya akansa seya d’auka ze sha seya tuna wa’azin da Abuu yamasa amman kuma problems sun masa yawa right now gana Ummimi gakuma na yarinyar daya yi raping. Rufa ido kawai yayi daga k’arshe yasa kwalban syrup d’in a baki. “Dude (maza) karka shanye duk-” be k’are maganar ba Anas ya kauda kwalban syrup d’in daga bakinsa sanda ya kwankwad’e tas.
Fuska ya yamutsa trying to adjust and in just 3 minutes Anas ya fad’a bacci, baccin daya jima beyi ba in a lifetime.
_7 hours later_
Daidai 8:30PM Anas ya tashi, ko sallan la’asar, maghrib da Isha beyi ba duk yini yayi yana bacci. “Holy shit!” Ya fad’i. Sede kuma kap ya nemi problems nasa ya rasa, da yayi niyan bare sake shan syrup d’inba amman dan yadda ya masa aiki he can’t resist it. Daidai ya mik’e ze shiga toilet Musty da Abdoul suka shigo da angansu anga wad’anda suka dawo daga party, dan aikinsu kenan. “Ya dude har ka tashi ne?” Musty ya tambayi Anas yana k’ok’arin zama.
“How did you like the syrub? Your problems will all be gone for good two days and after that seka nema ka sake sha, continiously” Abdoul ya ma Anas bayani tare da fad’awa kan gadonsa da baya.
“Great!” Anas ya ce, “I can’t remember any of my problems now saidai nata bacci ko sallan la’asar banyi ba.”
Tsuka Abdoul yaja “yanzu dan kawai yau ka rasa sallolin nan shine wani abu? Kaifa Anas kanada case, wannan blue eyes naka basu taimake ba. Nifa the first time I saw you nad’au American ne kai to seme dan ka share sallolin yau?”
“Tell him bro” cewar Musty. D’an murmushi Anas yayi lallai duk iskancin mutum dubu sun fisa, can a Bama sune ‘yan iskan gari nan kuwa a tafin hannun su Abdoul yake be sauraresu ba yashige toilet yayi alwala yafito ya rama sallolinsa.
Da misalin k’arfe 11:30PM su Musty suka kuma yin wanka suka yi shiri tsaf a yayinda Anas keyin zanen project da aka basu a school. Da suka zo fitane suka juya suka kallesa tare da kad’a kai. “Anas wai kai ko kad’an baraka gwada zuwa clubbing d’innan bane? Wallahi its fun, more fun than wannan jakin project da kakeyi na 5 marks kacal.” Cewar Musty ransa a b’ace.
“No kuje kawai, I have to get this done, maybe next time.” Anas ya sanar dasu yana d’an murmushi.
“Dude listen to him, ko na yau ne kazo muje club d’innan.” Cewar Abdoul. Kai kawai ya kad’a masu bayan sun fice yayi rounding up abinda yakeyi ya kira Ummie bayan sun gaisa yasa ta mik’a ma Angel nasa suka ta hira abinsu. Anas na mutuwan san Amal badan komai ba dan abinda Ummimi ta mata.
Ace yarinya kwanan ta d’aya a duniya amman dan rashin imani tasa a dawo da ita gida ko shayar da ita batayi ba.
_2 days later_
Da misalin k’arfe 12:30PM Anas na kishingid’e kan wata couch (kujera me fad’i da akan iya bacci akai) yana bacci. Ya soma mafarki;
_“Ummimi dan Allah karki tafi kiyi hak’uri indan plates dana fasa ne I promise baran sake ba. Ummimi I am sorry dan Allah karki tafi. Abuu ka hana Ummimi tafiya dan Allah kace mata I will be a good boy from now on.”_
_“Yanzu Aysha bara kiji tausayin yaranki ki hak’ura ki zauna dasu ba. Kalli yadda suke kuka fa?_
_“Mstww wannan kuma ku ya shafa nagaji da zama cikin talaucin nan, ace kullum se atashi ba’a san me za’a karya dashi ba gaskia nagaji daman tun farko sanda Abba na yace kar in aureka matsiyaci ne kai amman nak’i sauraronsa. Ga can miji Allah yamin har k’asar waje ze kaini saboda haka ban ga abinda zesa in cigaba da zama a wannan gidan ba.” Jakarta ta ja ta soma tafiya da sauri naje na kama k’afarta ina kuka ina rok’arta wani wawan ball tayi dani da k’afa sanda na ji ciwo a elbow na…”_
“UMMIMI!” Anas ya kira da k’arfi a yayinda ya farka daga baccin dayakeyi duk zufa yakeyi se nishi yake da k’arfi ganin mafarki yake yasa hankalinsa yad’an kwanta. Wani erin mahaukacin bacci yakeji saboda jiya kwana sukayi a studio amman saboda duk sanda ya rufe idansa mafarkin Ummimi yake yasa ya kasa baccin abu d’aya ne yasan inyasha ze gusar masa da problems nasa which is syrup na problem reliever (giya) da Abdoul ya basa ranan.
Kash! Saidai basu gida sun fita yawo gashi bacci yakeji. Gwada jirarsu yayi na ‘yan mintuna ganin basu dawo ba yasa ya kira sa a waya kai tsaye ya tambayesa ina yake ajiye syrup daya basa ranan yana san sake sha. Dad’i sosai Abdoul yaji finally Anas is ready to change, bayanin ina yake ajiye wa ya masa yakuma tabbatar masa in zasu dawo gida ze sake siyowa tunda wanda ya rage kad’an ne.
Exactly inda Abdoul yamasa kwatance yasamu syrup d’in bud’e sabon kwalb’a yayi yakafa a baki sanda yashanye tas, ko cikakken minti biyu beyi ba yasoma jin bacci me nauyin gaske tsalle kawai yayi ya fad’a kan gadonsa yasoma wani erin mahaukacin bacci me uban nauyin gaske
*© miemiebee*
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 07
BY MIEMIEBEE
FANNAH
3 days later…
Kwanan Fannah uku a asibiti tasamu k’arfin jiki aka sallamesu, ayau suke shirin dawowa gida, Alhamdulillah jikin nata da sauk’i sosai saboda anti-biotics datake sha masu k’arfi ne sosai. Baba ya sayarda shanunsa da shi ya samu ya biya kud’in asibitin ta da kuma na magunanta.
Daidai sun sauk’o daga keke na pep kenan se ga irin almajiran unguwan nan sunzo sun tsaya gabansu.
“Fannah! Dama ashe ke d’in kariya ce me bin maza, sekitayin abu kamar ‘yar malam saliha to Allah ya tona miki asiri tunda saurayi yayi miki ciki.” Hannu Mami ta d’aga ta wanke sa da mari. “In na sake jin wannan munanan kalamu daga bakinka kaji na rantse seka kwana a asibiti, bakai kad’ai ba dukanku nan. Fannah ba kariya bace abinda ya sametan nan k’addara ce. Maza ku fice min daga kallo.”
Baya sukayi kad’an sannan suka soma wak’a “kariya! Kariya! Fannah kariya Fannah kariya!” Hannun Fannah kawai Mami taja suka shiga ciki a yayinda Baba ya koresu.
Kuka Fannah keyi sosai. “Yanzu shikenan Mami kallon kariya za’a na mun? Shikenan rayuwata ta lalace Mami.”
“Shhh karkiyi magana haka, karki saurare wad’ancan almajiran basu masan me suke fad’i ba.” Hugging nata tayi har sanda Fannah tayi shiru.
Da yammacin ranar around k’arfe 4:45PM Ya Khaleel da d’ansa Farouq suka shigo gidansu Fannah. Mami da Afrah suna had’a girkin dare suka masu sannu da zuwa, ba abinda Afrah ke masu se harara. “Ke Afrah jeki kira min mahaifinku dakuma ‘yar ku kariyan can.” cewar Ya Khaleel.
“Kawu Khaleel bamuda kariya a gidan nan.” Ta fad’a stubbornly.
“Ke ni keke gaya wa magana? Iyye?”
“Kawu kayi hak’uri Afrah kibasa hak’uri kije ki ma Babanku da Fannah magana.” A sanyaye ta mik’e taje ta kira Baba sannan takira Fannah a tare suka fito. Fuskar Baba a tamk’e ya zauna kan tabarman da Ya Khaleel da d’ansa ke kai ba tare da ya musu magana ba.
“Ina wuni kawu?” Gaisuwar Fannah.
“Yawwa sannu an sallamoki kenan. Se a kiyaye aukuwan na gaba kafin wani saurayin yasake fiad’e ki.”
Har tsakiyan kanta tajiyo wannan kalamai ba ita kad’ai harsu Baba da Mami da Afrah. “Ya Khaleel in kasan batun daya kawo ka gidana dan kaci zarafin ‘yata ne dan Allah kayi hak’uri na had’aka da Allah ku tashi ku tafi.”
“Ba seka koremu ba yanzu zamu tafi. Magana d’aya biyu na zoyi nan saboda haka nakeson ku bud’e kunnuwanku ku saurareni. Kunfi kowa sanin yadda ake k’yamatan kariya a gari, ba uban da ze so d’ansa ya auri macen da batada budurci. Fannah kuwa ‘yata ce dukda abin kunyan da ta mana ina san ta saboda haka zan bata wa d’a na Farouq.”
“What!?” Baba yayi exclaiming.
“Bari na gama mana k’ani na. Na riga nayi wa Baba magana kuma ya goyi bayan zancen d’ari bisa d’ari bawai nazo nan bane in baku choices saboda bakuda choice inbanda ku yarda mu rufa wa kariyarku asiri dan na tabbata kap garin nan bame san aurenta. Kinji ai Fannah? Ga Farouq nan mijinki, kina k’are secondary ze rufa miki asiri ya aureki zaki iya gode masa saboda wannan jahadi yayi. Auren kariya ba wasa bane.”
D’ago jajyen idanunta tayi ta azasu kan Farouq dake ta mata murmushi. Hawaye se gangara suke kan kumatunta, kuke take sosai. Tasani a yanzu kam kamar yadda Kawu ya fad’i ba na mijin da zeso aurenta saboda ta rasa budurcinta martabatar ta, amman duk da haka gomma ta mutu batai aure ba data auri Farouq. Farouq baida tarbiyya ko kad’an d’an iska ne ba aikinsa se bin mata Allah kad’ai yasani ko baida cutar k’anjamau ma. Ba yadda za’ayi ta auresa.
“Kawu dan Allah kayi hak’uri ni baran auri Ya Farouq ba, dan Allah ka rufa min asiri.”
“Ji shashasha dabadan Farouq nada imani bama jinki ze yarda ya aureki ne? Ajinki a kariyan da kike yanzu zaki samu na miji kamar Farouq yace ze aureki ne? Inba mahaukaci ba wallahi ba na mijin de so ya aureki gara ma tun wuri kinsan ina ke miki ciwo”
“Enough Ya Khaleel!” Cewar Baba a fusace. “ ‘yata barata auri wannan d’an iskan ba. Mungode da alfarman da kuka bamu amman bamuso da in aura wa ‘yata d’an iska kaman Farouq na gommaci kartayi aure a duniya. Yaro ko gaishe dana gaba dashi be iya ba. Ku tashi kubarmin gida zanje in samu Baba in masa magana yaja da baya da wannan zance. Fannah bata san Farouq saboda haka barin tilasta mata ba.”
“Aww haka kace kenan? Yanzu har zaka bud’e baki ka kira d’a na Farouq d’an iska? Kariyarka kuma fa? ai nakega sede ace mata ‘yar guguwa, aure tsakanin Fannah da Farouq kuma consider it done bari ta k’are shirmen secondaryn nan kuga ikon Allah. Wawiya ana taimaka miki kina wawanci mschww Farouq tashi mu tafi da Allah.” Suna ficewa Fannah ta ruga d’aki da gudu ta baje kan katifar ta tana kukan cire rai. Afrah ce tabiyo bayanta itama kukan take tabbas Fannah tana cikin tsaka me wuya duk wanda ya aikata mata ta’addancin can ya cuce rayuwarta har a bada.
Tun ba yau ba Fannah ta tsani Farouq taya za’ace shi zata aura? Kasheta akeson yayi?
“Yi hak’uri Ya Fannah dan Allah kibar kukan nan in shaa Allah baraki auri Ya Farouq ba.” D’ago jajayen idanunta tayi “Afrah shikenan ni haka rayuwata zata k’are cikin k’unci da bak’in ciki? Mesa se ni Afrah? Mena tab’ayi da ba kyau to deserve all this? Duk abinda addini na yace inyi inayi wanda kuwa ya haramta ina k’ok’arin nisantar kaina daga aikatasu. Mesa seni wancan saurayin zeyi raping? Mena masa Afrah? Mesa seni za’a ce zan auri Ya Farouq kinfi kowa sanin halinsa. Kullum yana nan a bayan gari yana kwanciya da mata, Afrah dan Allah ki taimaka min.” Ta kuma fashewa cikin matsanancin kuka.
Itama Afrar kuka take ta rungumi yarta tana bata hak’uri.
****
“Malam dan Allah kayi wani abu karka bari Kawu ya cimma burinsa na aura wa Fannah aure da Farouq kafi kowa sanin halin Farouq so nawa ake kamasa a bayan gari? Dan Allah kaji k’an ‘yarmu Fannah. Ko kad’an she’s not to blame for what happened to her fiad’e aka mata munyi iya binciken da zamu iya mun kasa samun waye ya mata wannan d’anyen aikin.” Ta fashe da kuka.
“Maman Aiman in shaa Allah barin bar Fannah ta auri Farouq ba. Yanzun nan zanje in samu Baba in masa magana kishiga ciki kibata hak’uri ki kwantar mata da hankali dan Allah. Ni na wuce…”
**
“Ina wuni Baba?” Gaisuwar Malam Aliyu Babansu Fannah ga mahaifinsa da Ya Khaleel.
“Lafya Aliyu, ya jikin Fannan?”
“Da sauk’i Baba.” Ya amsa yana kallon wansa Khaleel da d’ansa dasuke zaune a gefen mahaifin nasu.
“Nasan maganan daya kawo ka Aliyu saboda wan ka Khaleel yamin bayanin komi yanzu. Kasani wan ka bare tab’a maka abinda ze cutar dakai ko iyalinka ba. Kafi kowa sanin halin da ‘yarka tashiga kallon kariya ake mata agari me bin maza-”
Malam Aliyu katse mahaifin nasu “amman Baba ai duk munsan ba haka asalin abar take ba, fiad’e aka mata.”
“It still will not change anything Aliyu, in mu mun yarda da hakan mutane fa? Baramu iya fahimtar dasu ba. Kap garin nan ba mahaifin da ze b’ar d’ansa ya auri wacce batada budurcinta tattare da ita kasani Aliyu. Allah ya kawo mana sauk’i gida ga wan ka nan Khaleel he is ready ya rufa wa ‘yarka asiri ya d’au d’ansa ya aura ma ‘yarka dukda ba cikakkiyar mace take ba yanzu amman har ka bud’a baki kace bakaso? Ina zaka zo ka kai ‘yar taka?”
“Baba in shaa Allah, Allah ze kawo mata miji wanda ze sota a yadda take.”
“Har tsawon yaushe kuma zaka tsaya kana jiran wannan rana da bakasan ranan zuwanta ba? Iyye Aliyu? Bana sake jin wani zance, Fannah zata auri Farouq wannan shine san da muke mata bamusan tak’are rayuwarta batayi aure ba.”
“Baba dan Allah kayi hak-”
Baba ya katse sa. “Aliyu wannan shine karo na farko da kake k’ok’arin bijire min, kar muyi haka da kai. Farouq.” ya waiwayo da kallonsa kan Farouq
“Na’am Baba.” cewar farouq.
“Kanason Fannah zaka aureta koda bata da budurcinta a tattare da ita?”
“Eh Baba ina santa k’anwa tace koda duniya sun k’ita ni baran k’ita ba.”
“Masha Allah” Baba yace. “Kaikuma fa Khaleel ka yarda d’anka ya auri macen da tarasa budurcinta?”
“Na yarda Baba” cewar ya Khaleel. “Fannah ‘yata ce matuk’an ina raye zanyi duk iya abinda zan iya dan in kula da ita in rufa mata asiri.”
“Toh masha Allah kadeji Aliyu. In nine kai godiya zanyi wa Khaleel da Farouq.”
“Baba amman Fannah batasan Farouq, bata tab’a sansa ba, taya zamu tilasta mata auren wanda bata so.” Cewar Malam Aliyu.
“Wannan kuma ba me wuya bane, in suka soma ganin junansu a hankali zasu shak’u. Allah dad’a had’a kawukan ku.”
“Ameen” Ya Khaleel ya amsa banda Malam Aliyu dake ji kamar yayi kuka.
**
“Sannu da dawowa Malam” cewar Mami tana k’ok’arin shimfid’a masu tabarma. Bayan sun zauna take tambayarsa ya had’uwan nasu ya gudana. Kai ya kad’a a hankali take jikinta yayi sanyi.
“Maman Aiman Ya Khaleel ya riga ya saye Baba nuna masa yayi intensions nasa are clean tsakani da Allah yakeson ya aura wa Fannah Farouq saboda tsantsan tausayi.”
“Malam amman ai duk munsan badan haka bane.” Mami ta katse Baba. “Tun ba yau ba idanun Kawu suke kan Fannah shikansa yasan tana da tarbiyya mekyau da hankali so yake ya aura wa Farouq Fannah saboda ta giara masa d’a ita kuma tasha wahala in the process.”
“Ba k’arya cikin magananki Maman Aiman ni kaina abin nan ya dameni bansan ya zanyi ba, tausayi Fannah take ban matuk’a yarinya me hankali ace arasa ma wa za’a d’aura wa k’addara erin wannan se Fannah.” yaja numfashi.
“Uhn uhn Malam kayi istigifaar kar kayi sab’o. Wannan Allah kad’ai yasan mesa ya d’aura wannan mumunar k’addara kan Fannah bekamata muyi ma Allah shisshigi ba.”
“Hakane Maman Aiman Astaghfurullah.”
“Yanzu Malam shikenan sede mu zuba ido muna ganin ‘yarmu zata auri wannan d’an iska? Ba abinda zamu iya mata? Innalillahi!”
“Da akoi abinda zan iya da nayi Maman Aiman banasan Fannah ta auri Farouq ko kad’an. Ran Baba ya b’aci ya dage se Fannah ta auri Farouq inhar na hana aikuwan wannan aure, zamu iya samun sab’ani da mahaifina.”
Fannah dake lab’e ajikin bango tana sauraronsu ba abinda takeyi se hawaye. Daidai lokacin wani yaro yashigo gidan bayan ya gaisheda Mami da Baba yace “wai Fannah tafito inji Farouq.” “Barata fito ba” cewar Baba a fusace. “Kace masa barata fito ba inji mahaifinta.” Nan Fannah dake lab’e tafito “kace masa ina zuwa.” “Fannah!” Mami da Baba suka kira a lokaci d’aya.
Tana kuka tana maganar, “Baba naji duk abinda kuka fad’a barinso saboda ni kasamu matsala da Baba ba. Muyi hak’uri mu rungumi k’addara fatarmu Allah sa hakan shi yafi alkheri, Allah sa auren Farouq ba sharri bane a gareni, addu’an da nake so kumin kenan. Barinje kirarsa kar yaje yasamu Baba ya fad’a masa wani abu daban yajawo maka matsala.” Tana kaiwa nan ta fice.
Kuka me k’arfi Mami ta fashe da shikansa Baba sanda ya zubda hawaye, babu kamar Fannah, yarinya me hak’uri da hankali dole yasan abinda zeyi ya hana aukuwan wannan aure.
Tana fitowa taga Farouq zaune kan benchin da take zama kullum da Ahmad nata take hawaye ya ciko mata a ido. “To ke kuwa Fannah haka ake hira? Haka kika sabayi ne in samarukan ki sunzo wajen ki? Taho nan mu zauna mana.”
Kafin tace meh Farouq ya taso ya cafke hannunta da sauri ta waske hannun nata daga rik’onsa. Tana kallonsa da jajayen idanunta.
“Meh haka kuma? Yau na miji ya soma rik’e hannunki ne? Kinga nifa ki sake jikinki dani tunda nasan ciki nasan waje ba sekin tsaya kina proving min innocence ba.” Hannun nata yasake rikowa da k’arfi sannan ya aza d’ayan hannun sa kan fuskarta yana shafawa. “Ji laushin jiki wai a haka ma kinbar samaruka suna tab’awa kenan.”
K’ok’arin k’watan kanta take amman ta kasa se hawaye take yi “Farouq kasake ni bana so, kadena tab’ani.” K’in saketa yayi “meh aciki dan na tab’a mata ta ko kin manta a matsayin mijinki nake yanzu.” Matso da fuskarsa yayi sosai kusa da nata. Numfashinsu yana had’uwa. Kafin ya hankara Fannah ta tsinke sa da mari wanda besan sanda ya saketa ba.
Hawaye take sosai “karka kuskura ka sake tab’ani in kai d’an iska ne toh ni ba ‘yar iska bace, in ka saba tab’a mata anyhow ni ba d’aya daga cikin ‘yan matan da kasaba tab’awa bane.”
“Dallah can kariya kawai, keda kike bin maza kowa ya sani, zaki wani zo kina min zak’in baki. Kuma barikiji in fad’a miki duk sanda kika kuskura kika sake marina wallahi kinji na rantse sekin sake kwana a asibiti. Humm!” ya sakar da wata shu’umar murmushi “bari a aura min ke zaki yaba wa aya zak’inta. Se gobe ko baby, ki kula min da kanki please karki sake bin wani har abu yakuma shiga tsakaninku nasan you are itching to be with a guy.”
© miemiebee
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 08
BY MIEMIEBEE
Kasa cemasa komai tayi, kallonsa kawai take hawaye na gangarowa kan kumatunta, kuka ne yafi k’arfinta juyawa tayi tashiga gida da gudu ta tsaya daga wata lungu ta share hawayerta sannan ta k’arasa ciki. Mami da Baba ta tarar zaune yadda ta barosu. Basu ce da ita komai ba dan haka tashige d’akinsu da Afrah ta fashe da kuka bata san da wanne zata ji ba da rabata da akayi da budurcinta martabarta na k’arfi da yaji ne kokuma da auren wannan monster me suna Farouq tun be aureta ba ma yasoma mata rashin mutunci yana zaginta bale ace in sunyi aure, kwata kwata baida slightest regard mata.
Bada jimawa ba Mami ta aike Afrah shago siyo man giad’a tun kafin Maghrib yayi gudun kar abinda ya faru da Fannah yakuma samun Afrah. Afrah ne tashigo d’aukan hijabi a d’akinsu, Fannah dake kwance a kan katifa da Qur’ani tana karatu ta d’aga kai tare da tambayarta. “Ina zakije haka?”
“Shago fa Mami ce ta aikeni siyo man giad’a.”
“Okay, jirani muje tare nagaji da zama nan shiru ni kad’ai.”
“Toh sanya hijabinki muje Ya Fannah.” Nan Fannah tasa hijabi suka fito tare, “ya haka ina zaki Fannah?” tambayar Mami ga Fannah.
“Zan bi Afrah ne Mami nagaji dazaman cikin.”
“Toh Allah kare dan Allah in har babu anan shagon Ya Wakil dana mak’otansa karkuyi nisa ku dawo gida kawai, kunji?”
“In shaa Allah Mami” cewar Fannah sannan suka fice. A shagon Ya Wakil suka samu man giad’an sun jiyo zasu fice sega yaran unguwa sun taru suka soma wak’a
“Fannah kariya me bin maza Fannah kariya me bin maza.”
Hawaye tasoma yi bata tab’a tsammanin zatayi witnessing rana kamar ta yau ba, ranan da za’a ce tafita waje ana binta ana zaginta me bin maza.
“Ku wai bakuda hankali ne?” cewar Afrah “wanj irin ‘yan iska ne ku? Wallahi in baku bar nan ba zan jefe wannan munanan bak’ak’en kankun da dutse, jahilai kawai. Bara ku matsa bane?”
Ko ajikinsu ma magana ake masu wak’an su suka cigaba dayi. Mari wani ya sake ma babban cikin nasu Tasss! Kukeji a fuska take ya soma kuka saurayin na juyawa suka had’a ido hud’u da Fannah take ta kau da kanta. Kolar rigarsa Ahmad ya rik’e da hannu d’aya “kanajina in sake jin ka kira Fannah ko wata mace a garin nan da kariya kaga abinda zan maka ba kai kad’ai ba dukanku nan” ya nunasu da yatsa. “Kunjini ko bakuji ba?”
Baki na rawa babban yace, “munji dan Allah kayi hak’uri.” Ahmad na sakesa suka kwasa da gudu suka bar wajen. K’arisowa gabansu Ahmad yayi “Fannah kiyi hak’uri kibar kuka dan Allah, karki bari maganan yaran nan to get to you.”
“Ya Ahmad dan Allah kayi hak’uri” Fannah tace tana hawaye hannu kawai tasa ta rufe bakinta ta ruga a guje se kiran sunanta Ahmad yake ko sauraransa batayi ba. Juyawa yayi ya kalli Afrah da itama idanta suka cike da hawaye. “Afrah kiyi sauri ki bita kar wani abu ya sameta. Tell her tayi hak’uri ta rungumi k’addara in shaa Allah, Allah ze sak’a mata kuma kice mata I will never stop loving her koda ban aureta ba, da santa zan mutu kice mata tayi hak’uri, ina kan mata addu’a.” Kai kawai ta giad’a masa tabi bayan Fannah da gudu.
Tana isa gida ta tarar da Mami a tsakar gida se safa da marwah take. “Mami ga man giad’an.”
“Afrah meya samu Fannah tashigo tana kuka ta rufe k’ofar d’akinku nayi nayi da ita ta bud’e tak’i wani abu ne?”
“Mami wallahi Ya Afrah tausayi take bani, yanzu fitan mu almajirai suka taru suna mata wak’a suna kiranta da munanan suna Mami.” Ta k’are maganar tana hawaye.
“Allah sarki Fannah” cewar Mami itama tana hawayen, “Afrah inda zan iya karb’e pain da Fannah ke feeling danayi wallahi, it hurts me seeing my daughter in a horrible situation like this kuma ba abinda zan iya mata.” Hannu tasa ta share hawayerta addu’a zamu mata Afrah ko a islamiya ki fad’awa Malamanku su sata cikin add’ua kinji?”
“In shaa Allah Mami barinje in sameta.” Tana tashi taje ta k’ofar d’akinsu tun daga bakin k’ofar take jin sautin kukan Fannah. “Ya Fannah dan Allah kibar kukan nan batada amfani, addu’a zamu dage dayi, bud’e k’ofar kinji? Ya Ahmad yabani sak’o in isar miki, yi hak’uri ki bud’e.”
Fannah na jin Ya Ahmad ta tsananta kukanta haka ta tayi kusan na minti ashirin sannan ta tashi ta bud’e ma Afrah k’ofar bayan sun zauna Afrah ta isar mata da sak’on Ya Ahmad, se kuka Fannah ke Afrah na bata hak’uri. Comb ta d’auko da mai ta shafa ma Fannah a gashi sannan ta taje ta kama mata da k’yar, rabuwan gashin Fannah da giara tun kwanciyar ta a asibiti.
Haka fa rayuwa ta cigaba da kasance wa Fannah, bak’in cikin yau daban na gobe daban, sam bata fita daga gida yanzu saboda duk sanda ta fita se yaran unguwa sun taru suna mata wak’a. K’arshen yawonta bakin k’ofar gidansu ne in Farouq matsiyacin yazo. Makaranta ma ko ina tashiga nuna ta akeyi da yatsa haka suka gama exams nasu batasan me take rubutawa ba.
Kwata kwata ta fita daga kamanninta tayi duhu ta sake rama. Abinci ma ba kullum take ci ba rayuwa de takoma upside down wa Fannah baiwar Allah ba abinda ke mata dad’i ciki, Allah sarki!
_One year later…_
Alhamdulillah Fannah is trying to move on from her past. Hasken ta ya d’an dawo, ta rage tunani yanzu addu’a sosai ita da iyayenta suka dage dayi. Abun da yaran unguwa suke mata kuwa yanzu da sauk’i sosai seta fita kusan sau uku-hud’u ba’a samu matsala ba. Watanni uku da suka wuce akace su Ahmad sun bar garin Bama, koda yazo mata sallama k’in fita tayi badan komai ba wai dan ita a ganinta she don’t deserve him anymore bata san ma ya sake ganinta bale yaji yana santa. Shekarunta goma sha shida yanzu this year ta gama secondary school.
Baba kam sanda ya kamu da ciwon zuciya saboda erin wahalar da suka sha wancan shekarar, sak abinda ake ma Fannah haka ake masa in ya shiga cikin jama’a shima, ga bin abu a zuciya haka sanda ya kamu da ciwom zuciyan. Yanzu haka gasu nan ne kawai d’an aikin kanikancin dayake d’an yin ma yadena banda ciwon zuciyan dayake damunsa ga hypertension da ciwon sugar sam da angansa za’a tausayawa masa gashi ba kud’in kaisa asibiti a masa aiki.
Bakuma komai bane ya haifo masa da hypertension d’innan banda halin wansa Ya Khaleel, sam ya dage seya aura wa Fannah Farouq, abinda Baba bayaso kenan ita Fannan da za’a mata auren ma ta hak’ura ta rungumi k’addara yanzu tunda duk saurayin da ya soma zuwa wajenta tun gama makarantar ta se ‘yan unguwa sun korasa, daga yazo yau gobe bara a sake ganinsa ba.
Farouq kuwa ba kalan walak’ancin da baya wa Fannah musamman ma dayaga yanzu Baba bayida lafiya ko magana be cika san yi ba. Fannah kuwa dama ba mutumiya ce me hayaniya ba haka zezo ya zageta yazagi Babanta ba abinda zata ce masa illa tayi kuka, maganan aurensu kuwa Ya Khaleel ya dage se shiri yakeyi.
Yau ranar ta kasance Asabar, Mami, Afrah da Aiman sun je gidan suna a unguwar noma Fannah kuwa tana zaune a gida saboda bata san shiga cikin mutane gudun kar a fara nuna ta da yatsa ana kiranta da sunan data tsana wato kariya. Wanke wanke take tajiyo knocking bam bam bam a bakin k’ofa kafin ta wanke hannu tasa hijabi ta duba ko wayene already meshi ya shigo Farouq taga tsaye da alama ya bugu baya cikin hankalinsa.
“Ya Farouq me kakeyi anan a buge? Dan Allah ka tafi gida” Cewar Fannah murya na rawa.
Bece komai ba sanda ya iso inda take, atake ta soma b’ari incident daya faru da ita shekara d’aya daya wuce ya soma yawo a kanta shima wancan mutumin daya rabata da martabatan ta a buge ya zo mata, gashi ko hijabi batada. Baya baya take Farouq na matsowa kusa da ita sanda suka kai bango. Hawaye ke tsiyaya daga cikin idanunta “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri kabari.”
“In bari ko in fara? Ai kinsha yi da samarukan ki se me dan nayi dake yau? After all ni zan aureki.”
“Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri kabari.” Hannu ya aza kan gashinta me uban yawa yana shafawa. “Baba dan Allah kazo ka taimakeni Ya Farouq dan Allah kabari.” Kuka take tana had’asa da Allah. Finciko gashinta yayi da k’arfi “kice kina sona!” Ya daka mata tsawa.
“Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri ka sake min gashi da zafi.”
“Who cares? Tell me you love me!” Yayi demanding.
Bakinta b’ari yake se hawaye take zubarwa. Gashin nata yakuma ja fiye da yadda yayi d’azu, k’ara ta sakar. “Nace tell me you love me and you’ll marry me ko in miki kaca kaca anan anyways dama ni zan aureki.”
Baba dake kwance a d’aki jikin sa yatashi sosai ko motsi dak’yar yake yajiyo muryan Farouq. Ja da ciki yayi yafito zuwa bakin k’ofar ya d’aga labile. “Farouq… Dan Allah kayi hak’uri kabar ta.” Cewar Baba a wahalance.
“Nak’i hak’urin Baba, seta ce tana sona kuma zata aureni wacce erin uselsess budurwa take ‘yan matan waje na ma suna cemin suna so na se ita wannan kariya me bin mazan.” Gashin nata ya sake ja “tell me you love me and you’ll marry me for the last time.”
“Farouq yanzu magana nake maka baraka jini ba?”
“Da Allah Baba ka rufa min baki da mata ta nake magana bada ubanta ba.”
“Farouq ina sanka zan aureka dan Allah kayi hak’uri ka sake min gashi” Fannah ta fad’i tana kukan azaba.
“Banji ba sake fad’a min.” Shiru tayi tana jan hanci se b’ari take ga shi yak’i sakar mata gashi. “Farouq dan Allah ka sake ta, mesa baka ji ne?”
“Baba nace kamin shiru ko? Kai bakasan addini bane? Ana shiga tsakanin mata da miji ne?” Yadawo da kallonsa kan Fannah “nace tell me you love and you’ll marry me ko sena rage miki kayan jikin kine?”
“A’a dan Allah karka min haka, kayi hak’uri.”
“Ke kariya kike kome baraki fad’a min abinda nakesan ji bane?”
“Ya Farouq ina sanka zan aureka, Ina sanka zan aureka dan Allah kayi hak’uri ka sake min gashi.” Murmushi yayi sannan ya sake ta tare da cusa ta jikinsa k’ok’arin k’watan kanta take amman takasa ga jikinsa duk warin giya. “Yawwa my beautiful Fannah I love you too, karki damu nan da ‘yan watanni za’a mana aure.” Kuka take sosai “Ya Farouq dan Allah ka sakeni.” Yasar da ita yayi a k’asa sannan ya juya yana tafiya nan da can ya fice.
Kuka sosai Fannah keyi so helplessly shi kansa Baba kuka yakeyi bare iya barin Fannah ta auri Farouq ba there has to be a way. Farouq besan darajar Fannah ba be kamata ace an barsa ya aureta ba inbanda wahala ba abinda zata sha a gidansa. “Fannah mama na dan Allah kiyi hak’uri in shaa Allah baraki auri Farouq ba, kiyi hak’uri barin iya tashi in taimakeki ba.”
Hannu tasa ta share hawayenta “karka damu dani Baba kabar kuka kar jikinka ya k’ara tsananta.” A sanyaye ta mik’e zuwa d’akinsu ta baje kan gado tana kuka kamar zata cire ranta.
**
Da dare around k’arfe 8:30PM.
“Abinda d’an mayen yazo yayi ma Fannah kenan Malam? Wallahi abun nasa yayi yawa gaskia k’ara zan kai wajen me gari.” Cewar Mami cikin tashin hankali. Bata tsaya jin me Baba ze fad’a ba ta fire zuwa d’akinsu Fannah a kwance ta sameta tana bacci a wahale numfashinta se sama sama yake dan yadda tasha kuka. Take idanunta suka cike da hawaye tayi kan ‘yarta tare da zura mata ido. “Fannah dan Allah kiyi hak’uri wallahi in shaa Allah baraki auri Farouq ba, zanyi duk abinda nasan zan iya in hana aukuwan wannan aure.”
_“Bawan Allah dan Allah karka lalata min rayuwa kayi hak’uri ka rufa min asiri I’m just 15.” “Nak’i baran hak’ura ba. Ita da ta tafi taji tausayin mu ne? se na k’wace abin yau yaso seki je ki fad’a mata, banga abinda ze hanani miki wannan abu ba yau.” “Dan Allah kayi hak’uri. Wayyo Allah Mami na ze kasheni…!!”_
Firgit! Fannah ta farka daga baccin da takeyi se nishi takeyi me nauyi, zuciyar ta na bugawa da k’arfin gakse jikinta duk yayi zufa se b’ari take. Mami na tab’a ta, ta k’urma wata erin ihu. Daga nan Mami tagane mafarkin incident na ranan tayi dama haka yake mata duk sanda tayi mafarkin seta tashi tana b’ari tana kuka da an tab’ata kuma seta tsala ihu. Yau k’imanin shekara kenan kusan kullum se Fannah tayi mafarkin daren da aka rabata da budurcinta martabarta.
“Fannah Mami ce ba abinda zan miki, Mami ce” a hankali ta sake gwada tab’a Fannah wani ihun ta kuma b’urmawa. “Mami ce Fannah, Maminki” a hankali ta tab’a hannunta sekuma batayi ihun ba hugging nata Mami tayi a hankali tana shafa kanta.
“Mami mutumin… Dan Allah kice karya dawo.”
“Shhhh! Mafarki ne Habibti mutumin yatafi bare sake dawowa ba. Mafarki ne kinji? In kawo miki ruwa?” Kai Fannah ta giad’a a tsorace Mami na mik’ewa taja zaninta “Mami dan Allah karki tafi, ze dawo. Ki zauna dani dan Allah.” Zama Mami tayi Fannah ta rungumeta gamgam wane za’a k’wace mata ita tana hawaye.
© miemiebee
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 09
BY MIEMIEBEE
United Kingdom, London
ANAS
_shima bayan shekara d’aya…_
Acikin babban Beach dake waje da London, Anas ne mik’e kan wata doguwar kujera da blue sunglasses a fuskarsa kwata kwata short nicker ne kad’ai ajikinsa seda headphone dake kansa wanda ya had’a da wayarsa yana nin cool music. Kallon sama yake yayi nisa cikin tunani.
Bottled wata aka wulla masa a firgice ya mik’e ganin Musty ne yasa yayi murmushi wanda ya bayyano da fararen hak’waransa. “Kai! Abdoul where are you? Yau Anas yayi murmushi harda ciro hak’wara. Tell me why do you seem so happy?”
Murmushin ya sake, “my dreams are coming true one-by-one.” cewar Anas.
“Wani dream kenan Anas?” Musty ya tambaya.
“Humm!” yakuma murmusawa ta gefen da dimple nasa yake. “Ni dreams d’ina guda uku ne kacal a duniyan nan.”
Musty ya giara zama “ina jinka!”
“Kaga na farko to be a billonaire not a millonaire but a billonaire. After that kaga in nayi kud’i I can toy with women hearts, saboda one thing I’ve learnt in life is ba abinda mata sukeso fiye da kud’i a duniya, zanyi amfani da wannan damar in saye zuk’atarsu dashi, akan kud’i they are ready to sacrifice everything I mean everything harta family’nsu, kaga ko in nayi kud’i nasan ba macen da zata k’i ni ko akoi?” Ya tsaya ya tambayi Musty.
Musty dake jin dad’in wannan labari yace, “ai ko a yanzun ka ma ba macen da zata k’ika Anas you’ve got the looks and the blue eyes also.” Murmushi sukayi dukansu “ehemm. Ina jinka…”
“Yess! As I was telling you, inason inyi wasa da zuqatan ‘yan mata a k’alla 100-200. So nake na karya musu zuqatansu ta yadda barasu sake san kawo na miji cikin rayuwarsu ba, so nake su d’and’ana how it feels to be left alone.”
Kai Musty giad’a a hankali alaman yana gane abinda Anas ke nufi “so in ka karya masu zuqatan nasu what will you benefit from it?” Daidai lokacin Abdoul yazo ya zauna dawata American babe kan cinyarsa tasha bikini (pant and bra) “Hi Fauzy!” Tace da Anas sunan da ake kiransa dashi a can London kenan kasancewar su turawa sun saba da kiran mutum da family name nasa (ANAS IBRAHIM FAUZY)
Ba tare da ya kalleta ba yace “hey.” Abdoul ya d’ibi k’asa me laushi dake beach d’in ya watsa wa Anas. “Budurwar tawa ma seka ja mata aji ne? Kaifa Anas daban kake I keep on telling you.”
“Abdoul kaga magana muke da mazan nan kuma kallon wannan me farin gashin kusa dani amai yake sani so please ka koreta kokuma ku tafi tare.” Cewar Anas batare da ya nuna damuwa ba.
“Allah…!” Abdoul ya fad’i cike da mamaki wai ace baturiya ma bata burge Anas ba to wace zata burge sa!? Dariya sosai Musty ya fashe da ba k’arya maganan Anas ya sasa dariya. Baturiyar ce ta tsargu danko ba jin yarensu take ba. “Hey Auwal (family name na Musty) whats funny why you laughing?”
Dariyan yake har yanzu “ohh Emily its nothing don’t worry.” Bayanta Abdoul ya shafa “excuse us babe I’ll be right back.” Kiss ta manna masa a cheek sannan ta tashi ta fice.
Fuska Anas ya yamutsa a k’yamance yana mamakin Abdoul wai har baturiya yake bari tana masa kiss. “Seka sake fuskarka ai tunda na miji da na miji kaga suna kiss ba.” Cewar Abdoul a little bit pissed off. Murmushi kad’an Anas yayi “LOL mamaki kawai kuke bani, I can’t waste my time on girls. They aiint worth it”
“Aini Anas da ban sanka ba senace gay ne kai.” Cewar Abdoul “anyways what are you two discussing about da kuka sa na kora Emily.”
“Labari Anas ke bani” cewar Musty yana jin dad’i. “Ehem ina jinka continue.”
Komawa yayi ya jinginu jikin kujerar sa yana kallon sama sannan ya cigaba “kace what will I benefit in nayi breaking hearts na mata?” Musty ya giad’a kai dukda ba kallonsa Anas yake ba. “I will benfit everything, zan ramawa Abuu abinda Ummimi ta masa, dukda ba direct kan Ummimin zan d’au revenge d’inba atleast ‘yan uwan ta mata zasuji jiki tunda ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ce.”
Cikin rashin fahimta Abdoul yace, “wait wait nade san waye Abuu mahaifinka ba? what of Ummimi? Wace ita? As far as am concerned Ummie nasani mamanka har kana bamu waya muna gaisawa.”
Numfashi Anas yaja “well apart from my family you guys are the first people da zan bawa wannan labari so listen closely after na baku labarin seku fad’a min ko inada laifi in nace mata are evil creatures da be kamata a tausaya masu ba.”
_[Abuu kamar yadda kuka sani mahaifi na ne kanurin Bama ne dake jihar Borno. Ummimi kuwa mahaifiya tace unfortunately, asalin shuwa arab ce daga Maiduguri. Mu uku ne gun iyayenmu nine babba I’m 19 years old, followed by my brother Shettima shikuma he is 17½(sha bakwai da rabi) yanzu. Shekara 1½ (d’aya da rabi) ne tsakanin mu sekuma little sister’nmu my angel Amal she’s just 9 years old.]_
_[Base on yadda Abuu yabani labari auren soyayya shida Ummimi sukayi. As you guys know scholarship nasamu nazo nan school d’in not like you guys da iyayenku suke biya muku da kansu. Abuu bashida wani arzikin azo agani, yanada arziki ne dadai na rufin asiri a yanzu haka in za’a kira masu arzikin garinmu Bama nasan definately za’a sa Abuu amman dekam bade da kafin sui aure da Ummimi ba. Shi da kansa yake bamu labarin irin rayuwar talaucin da sukayi shida Ummimi kafin a haifemu harkuma da aka haifemu so dayawa ana tashi a gidanmu ba’a sanin me za’a ci.]_
“You guys must be wondering ya akayi Ummimi shuwa arab da uban san kud’insu ta auri talaka kamar Abuu na ko?” Ya juya ya kalli abokansa. Kai suka giad’a a tare murmushi ya saki kad’an “well you don’t have to.”
_[Alokacin da Abuu yaje Maiduguri yin diploma ne ya had’u da Ummimi tana sayar da abinci a school nasu a lokacin iyayenta sun kasance talaka sosai amman kunsan shuwa arabs koda su talaka ne se masu kud’i sukeso unlike Ummimi back then, dukda tasan Abuu baida kud’i makaranta yake hakan be hanata falling masa ba kamar yadda shima ya juma da falling mata dan kyan ta dakuma hali, sosai Ummimi kyakkyawa ce kap mu yaranta kamanninta muka dauka sede nafi kama da ita fiye da Shettima da Amal wanda har yau in na tuna da haka se inji kamar inje inyi plastic surgery in canza kamanni na sam banasan abinda ze sa ina tunawa da ita but anytime I look at myself in the mirror ita kawai nake gani…]_
Musty da Abdoul da suke duhu sukace “ban gane ba” a tare. “Mesa ka tsani mahaifiyarka haka Anas?” Cewar Musty. “Shin yanzu bata gidanku ne?” Abdoul ya tambaya.
“Zakaji reason dayasa na tsaneta Musty, bata gidanmu Abdoul Allah kad’ai yasan ko tana nan aduniya ko lahira.”
“Babbar magana!” cewar Abdoul “kanada picture’nta inasan ganin ta.” Hannu Anas ya mik’a ya d’aga wallet nasa daga kan wata ‘yar table ya bud’o sannan ya ciro wata hoto “wannan family picture’nmu ne Abuu, Ummimi se nida Shettima time d’in ba m’a haifi Angel ba. Sede bara ku gane fuakarta sosai ba saboda na dirje da biro.” Nan ya mik’a wa Abdoul sosai kam ya dirje fuskar Ummimi a hoton se ansa ido sosai za’a d’an ga kutsirin fuskarta amman ko a hakan ma za’a gano kamanninta da yaranta musamman ma da Anas kamar yadda ya fad’i bayan Abdoul yagama gani ya mik’a wa Musty, shima daya gani yayi returning wa Anas, amsa yayi tare da mayar wa cikin wallet nasa sannan ya cigaba;
_[Sun yi shekaru biyu suna soyayya batare da sanin iyayensu ba lokacin da Abuu yagama polythecnic ne ya sanarda da iyayensa kan yasamu mata kuma yanasan ya aura dukda cewar ba aiki yake dashi ba. Kowa murna ya tayasa seda akaji batun Shuwa Arab ze aura ne hankalin kowa ya tashi gudun heartbreak da suke masa dan sunsan for sure in iyayen Ummimi sukayi learning truth about status na Abuu barasu yarda suba d’ansu wa talaka ba sunfi san wanda ze kawo masu gwala gwale yakai su Hajji da umara.]_
_[As expected da Ummimi tayi introducing Abuu wa iyayenta sam sukace ‘yarsu barta auri talaka ba suka masa kaca-kaca sannan suka koresa. Amman dan erin soyayyan da Ummimi kema Abuu yasa ta bijirewa iyayenta tace ita sam inba Abuu ba zata kashe kanta kuma she was serious duk suka tsorata ba yadda suka iya dolensu suka yarda mata saboda ita kad’ai ce ‘ya a garesu. A munafirce mahaifinta ya tura ‘yan uwansa suka tsare Abuu a hanya suka masa tsinannen dukar mutuwa basu barsa ba sanda suka ga baya numfashi jinyan wata d’aya Abuu yayi kafin ya samu sauk’i alokacin Ummimi ta tada borin inba a aura mata Abuu ba zata fad’a rijiya dole aka musu aure iyayenta wane bak’in ciki ya kashe su]_
_[Bama ta biyo Abuu aka basu BQ a family house nasu Abuu. Aiki Abuu yashiga nema dan earning living and to make his beautiful wife happy but kunsan yadda k’asarmu take sam be samu aiki ba haka ya soma noma, safe, rana, yamma, dare. Duk sanda yayi harvesting shuk’ansa once in a year yakan kai maiduguri ya siyar a wannan lokacin ne yake samun kud’i ya ma Ummimi siyayya and duk abinda ya kawo mata tana appreciating. Bayan shekara d’aya da aurensu aka haifeni Abuu yace ni ko ragon suna ba’a min ba sanda nayi wata uku tukuna. Sam basu ji dad’in haifan Shettima da akayi bayan shekara d’aya da rabi da haifa na ba dukda cewar kowani d’a da arzikinsa amman talaucin nasu yayi over. So dayawa ana wayen gari ba’a san me zamuci ba. Mahaifin Abuu ke turo mana abincin dazamu ciki.]_
_[Daga bayan Shettima kuwa Ummimi bata sake samun ciki ba. Shekarana goma a duniya lokacin Ummimi tasoma staying late at night seta fita tun safe bata dawowa se dare abin ba k’aramin damun Abuu yake ba. Da ya d’anyi bincike kuwa se aka gano wani Alhaji ne daga Yola take had’uwa dashi. Attajiri ne sosai yanada kud’i Abuu yace kullum cikin canza mota yake. Yana ganin Ummimi kuwa ta masa kyau ya fara nemanta ita kuma saboda cin amana tak’i fad’a masa tanada aure. Soyayya sosai suka fara sam Ummimi tadena kula damu kullum cikin dukan mu take kamar ba yaran cikin data haifa ba.]_
_[Koba abin duka ba seta bugemu musamman ma a weekends lokacin da wannan Alhajin nata ya koma Yola ba me bata kud’i. Ranar lahadi da sassafe baran tab’a mantawa da wannan rana ba. Da misalin k’arfe 8:00AM Ummimi ta tashi se had’a akwati take sam nida Shettima bamu damu ba acewarmu ko tafiya zamui duka sede naga kayakinta kad’ai take ta had’awa dana tambayeta in zataje kuwa ba kunya ba tsoron Allah ba tausayi ta kalli cikin idanuna tace min *talaucin mahaifinku ya isheni tattara kayakina nake saurayi na zezo ya d’auke ni in tafi inbar nan* atake kaina naji ya soma juyawa wace erin magana Ummimi take dama mata masu aure sunayin saurayi ne? Danni ban tab’a jin malamin islamiyan mu ya fad’a mana ba. Sema na d’au wasa take na shareta mukaje muna ta wasa nida Shettima. Abuu na zaune a Parlour ya tambayeni. Anas Baba na ina mamarku? Ko yau d’inma ta fita ne? A’a Abuu tana d’aki tana shirya kayakinta tace min wai saurayinta ze zo ya d’auketa. Take Abuu ya mik’e what!? Niko na sake nanata masa. Bada dad’ewa ba sega Ummimi tafito tana jan akwatinta.]_
_[Aysha ina zakije haka?_
_Aww d’an naka bai fad’a maka bane? Tafiya zan saurayi na na jira na._
Haba! Aysha wace erin magana kike? Wani erin saurayi kuma? Cewar Abuu]
_[Ai kasan sa Alhajin Yola, shi nake nufi, rayuwar talaucin nan ya isheni ni tafiya zan inje inji dad’in rayuwa na nima.” For the first time naga idan Abuu yacike da hawaye kafin in hankara naga yana kuka take nima na fara same goes to my brother. Rok’arta na soma haka Shettima ma banda Abuu dayayi mutuwan tsaye.]_
“Huhhh!!! Nagaji I’ll continue some other day.”
“Haba! mana maza da Allah k’arasa mana.” Cewar Musty.
“Nace maku I’ll continue tomorrow or later I promise, baki na yagaji da surutu kunfi kowa sanin ban cika magana ba ai nayi k’ok’ari ko?”
“Sosai kayi Anas namu me blue shining eyes. Yi hak’uri ka gama mana amma” Abdoul ya fad’i yana masa zak’in bak’i.
“Okay toh siyo min soda sena cigaba ishi nake ji.” Ba musu Abdoul ya tashi ya siyo masa ya dawo da sauri. “Gashi toh cigaba muna jinka please.” Bayan ya bud’e sodan ya kwankwad’e tas sannan ya cigaba kamar haka;
©miemiebee
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 10
BY MIEMIEBEE
“Last words da mukayi exchanging da ita are forever stuck up in my head.”
_[“Ummimi dan Allah karki tafi kiyi hak’uri indan plates dana fasa ne I promise baran sake ba. Ummimi I am sorry dan Allah karki tafi. Abuu ka hana Ummimi tafiya dan Allah kace mata I will be a good boy from now on.”]_ “Haka nata had’ata da Allah ko saurarena batayi ba”
_[“Yanzu Aysha bara kiji tausayin yaranki ki hak’ura ki zauna dasu ba? Kalli yadda suke kuka fa?”]_ cewar Abuu
_[“Mstww wannan kuma ku ya shafa nagaji da zama cikin talaucin nan, ace kullum se atashi ba’a san me za’a karya dashi ba gaskia nagaji daman tun farko sanda Abba na yace kar in aureka matsiyaci ne kai amman nak’i sauraronsa. Ga can miji Allah yamin har k’asar waje ze kaini saboda haka ban ga abinda zesa in cigaba da zama a wannan gidan ba.” Jakarta ta ja ta soma tafiya da sauri naje na kama k’afarta ina kuka ina rok’arta. “Ummimi please don’t leave us we love you dan Allah karki tafi, Abuu will find a better job dan Allah karki tafi…” wani wawan ball tayi dani da k’afa nafad’i na ji ciwo a elbow na har d’inki sanda aka min wajen…”]_
“Kun ga ci won?” Ya mik’o hannunsa ya nuna masu Musty. Ciwo ne babba sosai ace yau shekaru kusan goma amman hakan besa ciwon ya rage girma ba. Komawa yayi yasake kishingid’a.
_[ko waiwayo wa ta dubani batayi ba jakarta taja ta fice, asibiti Abuu yayi rushing d’ina. Tun daga ranan Abuu ya rasa walwala, Abuu da mukasani da fara’a da murmushi ya koma wani abu daban. Kullum cikin tunani, nida Shettima tun tafiyar Ummimi muka rasa gatanmu, kakarmu bata raye bale ace ita zata kula damu, abinci ma waninsa’in mancewa ake damu haka zamu kwana da yunwa Ummie sister’n Abuu ce data dawo daga Maiduguri tayi alk’awarin zama damu. A lokacin ina primary 5 zamuyi common entrance, ikon Allah ne kawai yasa nayi passing exams d’in saboda tafiyan Ummimi yayi affecting d’ina psychologically, mentally and socially.]_
_Tun daga lokacin na canza, na dena dariya, nadena wasa koda da Shettima ne kullum cikin tunani nake har wani psysho psycho na soma zama. Ganin haka Kaka yabawa Baba shawara akaini Maiduguri Boarding school a tunaninsa in ina cikin yara zan sake, unfortunately koda aka kaini can abun nawa be ragu ba sede worse da yayi ma, bana cin abinci bana magana da kowa karatu na kawai nakeyi saboda blue eyes d’ina yasa yara dayawa suna san zama friends dani ace warsu ma ni bature ne sam bana basu chance guda biyu ne sukaci galaba a kaina Baana da Kashim, su biyu kawai suka samu na sake dasu muka zama friends.]_
_[A lokacin da mukayi second term hutu bayan na dawo gida na tarar da Ummie da jaririya kuma a iya sani na Ummie bata da aure. Tambayarta nayi ko ‘yar wace me kama dani haka amsar data bani ne ya mugun sake tada min hankali.]_
_[“k’anwarka ce Anas, uwar ku d’aya uban ku d’aya. Shekranjiya Ummimi tasa wani almajiri ya turo ta cikin wata basket da wasik’a.” Zafaffun hawaye ne suka soma gangarowa kan kumatu na. “Mesa Ummimi zatayi haka Ummie? Mesa barata tausayawa wa baby’n nan ba? Me tamata itakuma da zata rabata da d’umin jikinta? Mesa Ummimi ta tsane mu haka Ummie?”]
_[“Anas nima bansani ba hak’uri zakayi, I’m here for you guys, bar kuka Baba na.” “Ina wasik’ar Ummie?”_ Na tambayeta. Acikin wata drawer ta d’auko ta mik’a min na karanta kamar haka…]_
[_ Ibrahim ‘yar da ke cikin wannan basket, ‘yarka ce da cikinta nabar gidanka. Allah ya taimakeni nasamu na haifeta ga abinka nan na kawo maka, banasan abinda ze sake had’ani da kai ko da ‘ya‘yanka…_]
[Hawaye ne suka soma sauk’owa kan kumatu na hannu na mik’a na amshi sister na da ko suna Abuu be sa mata ba dan tashin hankali. Hawayen idanuna na d’iga kan fuakarta ta bud’e idanunta a hankali tana kallo na se kamar Ummimi nake gani, Amal na kirata dashi ina hawaye. Daidai lokacin Abuu yashigo. “Amal kasa mata Anas?” Alokacin ban fahimce abinda yake nufi ba sanda na tambayesa yake fad’a mun yak’i sa mata suna ne saboda ni yake jira nayi naming nata tunda nace mata Amal sunan ta Amal kenan. Tun daga ranan na d’au alk’awari zanyi protecting Amal da raina, zan zame mata uwa.]_
_[Ban tab’a jin inason d’an Adam kamar Amal ba, simply because of tausayin da take bani har yau bata san tanada wata mahaifiya bayan Ummie ba, rok’ar Abuu nayi kar a fad’a mata gaskia banasan rayuwarta ta tab’arb’are kamar yadda nawa yayi. Komai ni nake wa Amal har noma nafarayi tun ina d’an yaro in nayi harvesting se in siya wa Amal kaya da kauan abinci as Abuu har a lokacin be samu aiki ba. Tun tana k’arama take sona ko kuka takeyi ina amsarta zatayi shiru kwana ma tare mukeyi da ita, ko yawo zanje da ita nake zuwa. Sam banso komawa makaranta ba da hutun mu yak’are gudun kar nayi missing nata. Ba yadda na iya haka na koma amman kullum da tunaninta nake kwana in tashi.]_
_[Ina jss 3 aka sa Shettima a school namu, jiki na jasa sosai ko kad’an bana barin school bullies su tab’a sa. Abokai na abokansa ne. Alokacin Abuu ya samu aiki rayuwar mu yasoma canzawa a hankali ya gina mana gida Amal kuwa se girma takeyi a lokacin tana da shekaru biyu da abu akai. Amal completes me, kullum tare muke da ita duk sanda nazo komawa school setayi kuka tace seta bini. Har dan haka nad’au alk’awarin barin sake dawowa gida ba se nagama school d’in gabad’aya bana san ganin kukan Amal. 3 years later nagama secondary school I was 16 years then Shettima kuwa yana ss1 time d’in. I can’t believe Amal dana ganta she was 5 years then, ta girma sosai in na ganta kaina kawai nake tunawa da muguwar Ummimi.]_
“Tun daga lokacin na cigaba da kula da sister na har ila yau. Ummimi kuwa bamu sake jin labarinta ba tunda ta bar gidanmu yau about 10 years kenan.” Numfashi ya saki tare da tasowa daga kan kujerar ya mik’e tare dayin mik’a “kunji labarina you guys are the first to know. Kunji dalilin dayasa na rasa happiness d’ina, dalilin dayasa na tsani Ummimi da kowace mace banda mata guda ukun nan; Amal, Ummie seda yarinyar danayi blaming nata akan laifin Ummimi har nayi raping nata wanda har yau ban san ya take ba, bansan kona kasheta ba bansan irin ciwon dana ji mata ba. I can’t ever forgive myself for what I did to her har se ranan dana ganta na nemi gafararta ta yafemin. She was just 15”
“Anas stop blaming yourself, ba’a cikin hankalinka kayi mata abinda ka mata ba in shaa Allah bata mutu ba someday in the future zaku had’u kuma zata yafe maka inhar ka bata labarin ka. Gaskia Anas kasha gwagwarmaya a rayuwarka, kayi witnessing bak’in cikin rayuwa at a very tender age. Ummininku sam bata kyauta muku ba.” Cewar Abdoul cike da tausayawa wa Anas ashe saisa kullum yake cikin tunani baya dariya, he has been through so much ba laifinsa bane because of how he is now.
“Anas if only zan iya taimaka maka da nayi, you’ve had such a horrible past just know that when ever you need a shoulder to cry on we are here for you.” Musty yayi assuring nasa.
Kallonsu Anas yayi tare da ciri sunglasses nasa rana ya haska blue eyes nasa da skin nasa yayi kyau sosai. Murmushi ya saki kad’an wanda ya bayyano da fararen hak’waransa “thank you guys, so now what? Kun ga laifi na saboda nace na tsani mata barin yi aure ba?”
Kai duk suka kad’a “wallahi ko k’adan Anas you have every single right ka tsani mata fiye da komai sede inda zaka yayyafa wa zuciyarka ruwan sanyi you can find love in your own way I’m sure Allah ze sak’a maku abinda Ummimi ta muku by kawo maku matan da zasu kula daku su soku tsakani da Allah badan kyanku ko kud’inku ba but tsakani da Allah and barasu tab’a barinku ba kai da wanka Shettima se mutuwa.” Cewar Musty. “Sosai dude Musty is absolutely right.” Abdoul ya mara wa Musty baya.
“Ofcourse you guys are right, but niko kad’an I don’t have faith in love to talk more of marriage, I wish to finish my life single ba senayi aure ba. Dama ai ana aure ne dan a haifafa I have Amal, she is like a daughter to me.” Musty ze sake magana Anas ya katsesa by changing topic of discussion d’in. “Yau da kuka sani na tono past d’ina dole se na sha 2 bottle na syrup d’incan if not barin iya bacci ba and also I
Bayan tafiyan Ya Khaleel bada jimawa ba su Mami suka dawo gida, Fannah na d’aki tana kukan cire rai bata ma ji shigowansu ba kawai ganin Mami tayi tsaye a kanta take ta soma share hawayenta “sannu da zuwa Mami, yaushe kuka dawo?”
“Habibti kukan me kuma kike? D’an mayen can yazo ne?”
“A’a ba kuka nake ba Mami, inasu Afrah?”
“Fannah ga idanunki sunyi ja sun kunbura, fad’a min meneh? Keda waye?”
“Ya Khaleel ne yazo…” Nan ta irga mata duk abinda yafaru tana kuka.
Rungumota Mami tayi “Shikenan yi shiru in shaa Allahu Kawu da d’ansa barasu k’arisa da duniya lafiya ba, mugayen mutane kawai bar kuka kinji? Akoi Allah Fannah always have this at the back of your mind, in shaa Allah baraki auri Farouq ba.”
Hannu tasa ta share hawayenta, “Mami ni nasan zan auri Farouq ba abinda zamu iya Ya Khaleel yariga ya gama komi.”
“Fannah kin cire rai daga Allah kenan?” Kad’a kai Fannah tayi “toh ki bar fad’in haka, Allah ba azzalimin bawansa bane. Allah da kansa yace a Qur’ani auren mazinaci se mazinaci aikinsani koh?” Kai Fannah ta giad’a “toh kibar kukan ya iso mik’o mai in taje miki gashinki.” A sanyaye ta mik’e ta d’auko mai da comb mama ta taje mata gashinta takama mata gu d’aya sannan ta bata waje tasa kaya. Itakuwa ta fice zuwa d’akin Baba.
Kwance ta samesa, “Malam ya jikin?”
Baki na k’yarma yace, “da sauk’i.”
“Sannu, Malam ko kanada labari d’azu Kawu yazo ya cicci mutuncin Fannah? Duk nazo na sameta se kuka take.”
“Eh..Mam.. Maman Aiman saisa yazama dole in siyar da gwalagwalen da Umma (mahaifiyarsa) ta tab’a bani dana ajiye kan duk sanda Fannah tazo aure se in sayar mu mata kayan d’aki amman tunda ga yadda abu ya kasance dole mu siyar yanzu…” Tari ya tsaya yayi sannan ya cigaba.
“K’ark’ashin wancan akwatin akoi d’an kunne da sarqa da zobe dakuma warwaro guda hud’u na gwal, da ace ina da lafiya da a gobe zan jeni Maiduguri in siyar amman gajan haka yasa dole seke zaki Maman Aiman.”
“Ina jinka Malam, in mun siyar me zamu da kud’in?”
“Gidan nan zamu bari, garin nan zamu bari gaba d’aya mukoma Maiduguri inason bayan kinje kin siyar da gwala gwalen ki kama mana gida me arha koda 2 bedroom ne kawai wanda zamu iya affording, sekuma da essential abubuwan da zamu iya bu-” tari ne ya tsaida sa sosai.
“Malam shikenan ya isa nagane kar jikin ka ya tsananta. Amman Malam bara mu tafi da kayakin mu ba? Inaga zefi mana sauk’i inda hali ma gidan nan se mu siyar.”
Gyaran murya yayi sosai “inaaa… hakan bame yuwu wa bane Maman Aiman mukayi haka ai kamar mun fad’awa duniya zamu bar garin Bama ne kisani no one must know about this. Fannah kawai na yarda ki fad’a mata itanma dan mu cireta daga damuwa ne kuma ki gargad’e ta karta kuskura ta fad’awa Afrah kar da baki taje cikin jama’a ta tona mana asiri. Dan maganan nan na fitowa fili shikenan namu ya k’are dole Fannah zata auri Farouq, ni na fad’a miki.”
“In shaa Allah Malam, Allah kaimu goben zan wuce Maiduguri dan kasan matsalar samun gida, in bamu soma nema a kan lokaci ba zamu makara har lokaci ya k’ure we have just a month.”
**
“Fannah habibti. Fannah!” Kirar Mami dake tsaye daga bakin k’ofa.
Sanda Fannah takai k’arshen ayan datake karantawa sannan ta amsa “na’am Mami am sorry bansan yanke ayan ne.”
“Bakomai karatu kike ne?”
“Eh Mami wani abu ne?”
“Ina Afrah da Aiman?”
“Suna can parlour suna assignment.” Fannah ta amsa a takaice.
“Oh toh magana daman nazo miki.”
“Toh bismillah Mami” nan Mami ta k’ariso ciki tare da rufo k’ofar tayi joining Fannah kan katifar sanan a hankali ta sanarda Fannah abinda ita da Baba ke da shirin yi. Sosai Fannah taji dad’i harda hawayen nin dad’i.
“Mami dagaske kike? Zamu koma Maiduguri barin auri Ya Farouq ba?”
“Sosai Habibti ai dama na fad’a miki koda bamuda komai munada Allah, kuma Allah ba azzalimin bawa bane kamar yadda na fad’a miki gobe zani Maiduguri.”
“Toh Mami in bi ki mana muje tare.” Cewar Fannah tana share hawayen jin dad’i.
“A’a Fannah kinsan Kawunki wane bodyguard haka yake kusan kullum seya zo gidan nan inkuma yazo bani ba ke kinsan dole yayi bincike the moment asirin mu ya tonu kuwa kinga dole sekin auri Farouq. Saboda haka ni kad’ai zanje addu’a kawai zakimin Allah sa inje a sa’a in dawo lafiya.”
“In shaa Allah Mami Allah baki sa’a. Nagode sosai, keda Baba kun gama min komai aduniya Allah biyaku da gidan aljannah.”
“Ameen Habibti barin koma in had’a akwati na.”
“Toh muje in tayaki shiryawa.”
“A’a Habibti zanyi dakaina, go on da karatunki.”
“Toh Mami.” Har Mami takai bakin k’ofa Fannah ta danna mata kira da
“Mami!”
“Na’am Fannah.” Ajiye Qur’anin dake hannunta tayi ta ruga gun Mami da gudu tayi hugging nata “Jazakumullahu bikhairan keda Baba nagode sosai, Allah sak’a muku da gidan Al-Jannah.”
“Ameen Habibti Allah miki albarka kema.” “Ameen” ta ce sannan ta sako Mami tana kallonta har sanda ta shige d’akinsu da Baba. Sujjada tayi tana gode wa Allah sannan tashiga bayi tayi alwala tayi nafila raka’a biyu tare da sake gode wa Allah ji tayi kap matsalolinta sun gushe. Kan katifar su ta fad’a se murmushi take.
**
4 days later…
“Oyoyo Mami! Oyoyo Mami!” cewar Aiman tana daka tsale. “Oyoyo auta ta” Mami ta d’aga ta sama. Nan su Fannah suma sukazo suka mata oyoyo. Kwanan Mami uku a Maiduguri tadawo, tafiyar ta kuwa was a success kap addu’o’insu Allah ya amsa musu. Kud’in data samu bayan ta sayar da gwala gwalen ta kama musu gidan haya 2 bedroom dashi a unguwar jiddari polo, na shekara, seda katifu guda biyu da d’an kayan abinci da kayan kitchen. Alhamdulillah!
2 weeks later…
Farouq ne tsaye bakin gidansu Fannah shi a dole yazo ganin matarsa nan da sati d’aya da ‘yan kwanaki zata zama mallakinsa tsabagen iskanci ba abinda yake imagining illa first night nasa da Fannah. Wani almajiri ne yazo wucewa take ya tsaida sa “kai shiga nan kace wai inji Farouq matarsa ta fito.” Da “toh” yaron yashiga gidansu Fannah suna zaune tsakar gida suna tsintar shinkafa ita da Afrah.
Ita kanta Afrah mamakin yadda Ya Fannah ke walwala kwana biyu ke bata kukan data sobayi safe rana dare yamma duk tadena yanzu, dukda batasan reason nayin hakan ba itade tana ma yarta murnan dawowar farin cikinta.
“Assalamu Alaikum” cewar almajirin. “Wai inji Farouq wai matarsa tafito” dadai lokacin Mami tafito daga kitchen. “Me kace?”
“Farouq ne ya aiko ni wae matarsa ta fito.”
“Dan ubansa kace barata fito ba yaushe tazama matartsa? Fice kabani waje.”
“Almajiri tsaya” cewar Fannah “kace masa ina fitowa.” Kallo Mami ta watsa mata “Fannah baraki fita ba kinsan wannan d’an mayen yanzu seya saki kuka ki zauna.”
“A’a Mami kibari inje ai ba abinda ya isa yamin a waje a idan mutane, kiyi hak’uri.” Mami zata sake magana Fannah tace, “please Mami.” Da d’aga kan da Mami tamata Fannah ta shiga ciki ta d’au hijabinta sannan ta fice a zaune ta samesa kan benchi da alama yau ba a buge yake ba.
“Ke zo nan kizauna yaci ace kin saba dani yanzu, nan da ‘yan kwanaki zaki zama tawa.” A zuci Fannah tace, _taka? never! Allah ya riga ya kare ni daga auren mazinaci kamar ka._ Kawai jin hannun sa tayi kan kumatunta firgit ta matsa baya. Yasake matsowa kusa da ita “wai tunanin me kike haka? Kode tunanin first night namu?” Ya d’an murmusa “karki damu I’ll take it easy on you” batace dashi komai ba illa kallonsa da take.
“Ke wai yau azumin magana kike ne?” Juyawa tayi zata tafi ya danna mata kira cak ta tsaya bata tanka sa ba. “Kiyi sha’aninki iya san ranki kimin rashin mutunci iya san ranki amman kisani nan da sati d’aya da ‘yan kwanaki ni zanna ja miki aji. You can go daman nazo inga kyakkywar fuskarki ne kafin na wuce bayan gari.” Kai kawai takad’a tashige ciki.
Tsaye ta tarar da Afrah da Mami da damuwa karara a fuskarsu. “Ya haka Mami wani abu ne?” Ta tambayesu
“Farouq fa inade be miki komai ba?” Cewar Mami.
“Kai Mami da Allah ki kwantar da hankalinki Mami, kema haka Afrah ba abinda Ya Farouq yamin banda suratan banzan daya saba wai yanzu haka ma bayan gari zasa.”
“Shege mazinaci” cewar Mami. “In shaa Allahu baraki auresa ba.”
“Amman Mami yau fa sauran sati d’aya da kwana uku ne bikin anya akoi abinda ze hana aukuwan wannan aure?” Afrah ta fad’i cike da damuwa.
“Akoi Allah Afrah, always have this at the back of your mind. Jeki huta Fannah nida Afrah zamu gama girkin.”
“Toh Mami, ina Aiman tazo mu mata tsifa.”
_3 days later…_
Ana saura sati bikin Fannah da Farouq. Ya Khaleel ne tsaye cikin tsakar gidansu Fannah. Mami, Fannah da Afrah suna tsaye kansa. “Toh nide nafad’i nawa tun ana wata bikin nan na fad’awa Fannah ta sanar dake batun gadon nan gashi har yau baku sai ba wallahi zakusha mamaki dan kuwa amaryarku kan tabarma zata kwana. Wasu erin matsiyata ne ku? Ace ‘yarku zatayi aure ko gado kun kasa yi mata? Wai ahaka ma dan na d’auke maku nauyin kayan kitchen. Allah wadar in erinku wallahi.”
“Kawu kayi hak’uri nan da ‘yan kwanaki zan kwashe adashe na se in sai wa Fannah gadon dan Allah ka k’ara hak’uri.” Cewar Mami.
“Wannan kuma ku ya dama, ko ku sai gado ko amaryarku tayi kwanan tabarma. Ni na tafi.”
Yana ficewa Mami taja hannun Fannah sukayi d’aki gudun kar Afrah ta fahimce wani abun. Itade Afrah tasoma zargin abu da a da ne Kawu yayi wannan magana definately Fannah zatayi kuka sega yau ko nuna damuwa batai ba.
Da daren ranan Fannah da Afrah suna zaune d’akinsu Aiman tayi nisa a bacci. Afrah tafi minti biyu tana kallon Fannah har sanda tasa ta tsarguwa. “Afrah wannan kalo haka?” Cewar Fannah tana duba pages nawani Government text book.
“Ya Fannah kallen.” D’ago fararen idanunta tayi wanda suka sha bak’in kwalli ta azasu kan Afrah. “Na kallekin” tace. “Kina b’oye min wani abu kinsan na sanki fiye da yadda nasan kaina I can tell in kina b’oye min bu.” Cewar Afrah
“Me zan b’oye miki Afrah? Kawai de inajin dad’i ne.”
“Dad’in me fah? Dad’in zaki aura Ya Farouq??” Ta tambaya tare da d’age gira.
Dariya kad’an Fannah ta saki “ko kad’an Afrah ina murna ne saboda inaji ajikina barin auri Ya Farouq ba.”
“Toh Ya Fannah Allah sa, kinsan happiness naki ya fiye min komai a duniya.” Hugging junansu sukayi cike da so da k’aunar juna.
**
Ana saura kwana biyu biki…
Da misalin k’arfe 8:00AM
“Farouq! Farouq!” Kiran Ya Khaleel yana zaune kan tabarma. “Na’am Baba” Farouq ya amsa yana isowa sannan yasamu waje ya zauna.
“Ni ya jiya ka had’u da Fannah kuwa? Mahaifiyarta tace mun cikin satin nan zasu kawo gadon gashi saura kwana biyu bikin naku basu aiko ba. Anya mutanen nan lafiya kuwa?”
“Ni Baba kawai mu share zancen gadon nan kafa san basuda kud’i ni Fannah ta zamo mata ta shine babba ban damu ba ko kan tabarma zamuna kwana bale ma ai ina gado se in tafi mana dashi.”
K’eyarsa Ya Khaleel ya tand’e “ai dama kai wawa ne, taya mu zamu masu komai tashi muje gidan nasu yanzu.” Ba gardama Farouq yabi bayan Babansa suka fice zuwa gidansu Fannah.
“Salamu alaikum!” Cewar Ya Khaleel a yayinda Farouq kuma ke knocking shiru kukeji ba amsa “waiko wannan matsiyatan bacci suke ne?” Ya Khaleel ya tambayi Frouq. “Toh ya zansani Baba inba wai shiga zamuyi ba.” Sa kai sukayi a tare Ya Khaleel na sallama sede har da suka iso tsakar gidan ba amsa dan haka Ya Khaleel yayi d’akin Baba yayi knocking nanma shiru hannu kawai yasa ya bud’e k’ofar yaga d’akin wayam! Daga katifa se katifa ba bakunan kaya ba komai. “Tashin hankali!” ya kira a fili. Farouq dake tsaye tsakar gidan yace, “lafiya Baba?”
“Ba lafiya ba” cewar Ya Khaleel “zo kaga ba kaya a d’akin nan. Tsaya duba d’ayan d’akin yaran tukunnah” nan Farouq yaje ya bud’e same story. “Nan ma ba kaya Baba.”
“Tashin hankali! Bade Aliyu da iyalansa sun gudu sun bar garin Bama ba.” Y fad’i cike da tashin hanakli. “Amman ai basuda inda zasu ma, through out rayuwarmu anan mukayi, baida ma kud’in biya masu kud’in mota bale ace ya kama masu gida a inda sukaje. Dole suna cikin garin nan suna b’oye cikin wani gida taho muje mu sami kakanka mu irga masa.”
Bayan sunje sun samu kaka Ya Khaleel ya irga masa komai. Matuk’a Baba yasha mamaki. “Tunda haka d’an uwanka yayi deciding, mu barsa mu ga iya gudun ruwansa. Mun nuna masa halacci ya nuna mana butulci. Ni badan komai na amince da wannan maganar ba dan kar ‘yarsa ta rasa mijin aure ne amman tunda haka yace se mu barsa.”
“Haba! Baba haka zakace!? Nida na d’au tsine masa zakayi. Guduwa fa yayi Baba ya bijire wa umarnin ka.”
“A’a Khaleel ba maganan tsinuwa anan fatan mu Allah sa hakan dayayi shine mafi alkhairi garesa da ‘yarsa dakuma iyalansa gaba d’aya.” Ko “amin” d’inma Ya Khaleel be amsa ba shida yagama sa rai Fannah zata haifo masa kyawawan yara ace sun gudu basu gidansu. IMPOSSIBPLE. “Tashi Farouq yau ko shadda suka shiga suka b’uya semun tonosu bayan nagama bazawa a gari zakayi aure se ace amarya ta gudu wallahi k’arya ne tashi nace. Aliyu be isa ba yau duk inda suke a b’oye sena nemo su!” Baba na k’olla masa kira ko a jikinsa yaja hannun Farouq a fusace suka bar gidan.
*Masu karatu kui hak’uri yau bansamu nayi typing kamar yadda na saba ba, severe back pain ke damuna in shaa Allah gobe zanyi dayawa. I love you guys!*
*©miemiebee*
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 12
BY MIEMIEBEE
Da misalin k’arfe 7:30AM su Fannah suka isa garin Maiduguri daga can suka tsara taxi se sabon gidansu. Ba laifi gidan gaskia yayi arha d’akuna biyu ne da bayi biyu dakuma kitchen. Fannah takasa b’oye murnanta, finally barata auri Ya Farouq ba.
Ya Kaheel da d’ansa Farouq kuwa haka kaman zararru suka riga bin gida one-by-one a Bama su a dole suna neman Fannah da family’nta sam hankalinsa be basa Maiduguri su Fannah suka tafi ba. Har dare suna neman su Fannah ganin ba mahalicci se Allah yasa suka hak’ura suka dawo gida disappointedly.
Fannah kuwa yanzu rayuwa yasoma mata dad’i, a hankali ita da family’nta suke settling a Maiduguri hankalinsu akwance basuda wata tsoro yanzu, Government school me kyau Mami tasamu aka zuba Afrah da Aiman. Fannah kuwa ko kad’an bata sa rai kan zata cigaba da makaranta ba se sanda Baba yayi suprising nata kud’in daya kamata abiya akaisa asibiti ya yafe kan Fannah tayi proceeding karatun ta. Admisson aka nemo mata a Polythecnic course na Business Administration.
Sosai taji dad’i. Koda ta soma zuwa makaranta kuwa kullum cikin hijabi da nik’af take, mazan makarantar su basu ma san ya fuskarta take ba bale ace su gano kyawunta su soma binta. Haka Allah ya cigaba da yima rayuwar Fannah albarka, karatu take sosai ba wasa, Mami tana d’an sayarda irin gwanjon kaya hakan nan dashi suke cafanin gida. Baba kam jiki se worse yake ba kud’in kaisa asibiti a kullum burin Fannah ta gama karatu tasamu aiki ta kai Babanta asibiti.
Ya Khaleel kuwa koda ya kira Mami a waya bata d’aukawa haka yagaji ya bari. Rayuwa de alhamdulillah…
★★★★
4 YEARS LATER…
★★★★
Abubuwa da dama sun gudana a both rayuwar Fannah da na Anas. Fannah tanada k’imanin shekaru ishirin a duniya yanzu. Kyanta yagama fitowa, hips nata da dukiyar fulaninta daidai jikinta beyi yawaba kuma be kasa ba masha Allah. Fannah takai mace duk inda ake neman mace, shekarunta kusan biyu da gama poly tayi graduating under Business admin da excllent result. Sede aiki ne har yau babu ta kasa samu, duk wad’anda ake bata ba related to course nata bane daga baya dole ta hak’ura ta karb’a aiki as a waitress (me serving abinci ko drinks a shago kokuwa wajen taron jama’a) a wani babban coffee shop. Dad’in abin Coffee shop d’in nasu sananne ne sosai cikin garin Maiduguri yawancin meetings kokuma party ko biki da akeyi a Maiduguri a Coffee shop nasu Fannah ake zuwa a d’ibi waitresses kuma duk lokacin da akayi haka kud’i suke samu sosai. Da wannan take samu ta biya kud’in school fees na Aiman dana Afrah, amman de yanzu Afrah itama tagama makarantar tana neman kusan shekara da gamawa.
Fannah na k’ok’ari sosai dan tasa Afrah a makaranta sede abun ya gagara, jarin Mami ya jima da karyewa lokacin da jikin Baba yatab’a yin tsanani dole ta tattara ribanta da uwarkud’in business natan duka aka kaisa asibiti. A takaice de yanzu Fannah ce breadwinner’n family’nta duk akanta sukayi depending. Allah sarki Fannah ‘yar Albarka Allah cigaba da miki albarka, ameen.
Samari kuwa ba ta kansu take ba, sau afi a k’irga in aka d’ibesu serving food and drinks a meetings alhazai masu ji da naira suka ganta sesun neme ta amman saboda duk sanda ta tuna da past nata, ta tuna bata da budurcinta martabarta setaji barata iya k’ara yin soyayya ba saboda definately randa aka gano gaskia ita ba budurwa bace za’a guje ta abinda bataso kenan. Bature yace prevention ia better than cure sesa tun farko ma bata sa kanta cikin soyayyar. Daga wanda zata musu k’arya tace takusa aure se wanda zata ce musu tanada aure.
Zancen mafarki kuwa har yau bata dena ba kusan kullum setayi mafarkin mutumin dayayi raping nata wai ya dawo ze sake raping nata, Mami kullum ke calming nata in tayi mafarkin rananda Mami batta kusa kuwa haka zata riga kuka tana b’ari har wayewan garin Allah, Allah sarki!
K’arfe 2:00PM…
Dadai lokacin tashin Fannah daga aiki kenan kafin ta tsari napep ta dawo gida kuma 2:30PM yayi. Tana shigowa gida Aiman dake carafke tsakar gida tasoma mata “Oyoyo Ya Fannah” cewar Aiman dake da shekara 8 kenan baki kam masha Allah. “Oyoyo Aiman” cewar Fannah tare da hugging nata. “Ina sweet d’ina Ya Fannah?”
“Laaa kinga yau na mance ban siyo miki ba in shaa Allah zan siyo miki gobe, yi hak’uri kinji?”
“Ai dama haka kike cewa kullum inda saurayin kine ai baraki mance ba.” Cewar Aiman tana guna-guni.
“Ya SALAM!!!” Fannah ta zaro ido “ban hanaki maGanan saurayi ba? Ni narasa ina kikejin wanga zance.”
“Sekin tambaya ne Ya Fannah?” cewar Afrah data fito daga d’aki “wannan maras kunyan kuma.”
“Ai wallahi Ya Afrah ko kiyi shiru ko in fad’awa Ya Fannah batun wancan saurayin dayazo wajen ki d’azu da Mami batta gida.”
Kai Afrah ta dafe “banza! ai kin riga kin fad’a matan kuma wallahi kisani baran sake baki chocolates ba in yakawo min.”
“Wait wait wait Afrah saurayi kika soma kawo wa gida bada sani na ba?” Cewar Fannah in a serious tone.
“Ya Afrah fa ba saurayi na bane munafircin wannan munafukan ne, Ibrahim nefa classmate d’ina na secondary school.”
“Meaning? Afrah bawai zan hanaki yin samari bane kawai becareful karki yarda da maza so easily zasu kaiki ne su baro ki.”
“In shaa Allah ya Fannah I’m very vigilant.”
6 hours later…
Mami da su Fannah ne zaune a d’akinsu suna d’an tab’a hira. “Fannah nace wannan karan se ankai har k’ashen wata za’a biyaku?”
“Eh Mami” ta amsa da fara’arta “wani abu ne?”
“Fannah Habibti nasan kina mana sosai in ba ke family’n nan would have been dead by now, mungode sosai Allah cigaba da miki bud’i ya miki albarka kuma.”
“Ameen Mami dan Allah kidena min godiya, you guys deserve all that I’m doing for you. We are family. Kina buk’atan kud’i ne? Kaman nawa?”
“San samu dubu biyu kinga Maman-”
Katseta Fannah tayi “a’a Mami ba sekin min bayanin me zakiyi da kud’in ba” nan ta ciro wallet nata ta irga N4000 gashi jiya mun samu ankai mu wani meeting da akayi na commissoners so anbiya mu kud’i. “Nan N4000 gashi zdmiki aiko?”
“Fannah N2000 ma ya isheni dan Allah ki rik’e sauran kema kinada buk’atunki ai.”
“Mami dan Allah ki amshi ai ni na baki.” Hannun Mami tabud’e tasa mata kud’in ciki. “Nagode Habibti Allah miki albarka yakuma k’ara bud’i.”
“Ameen Mami nagode da addu’arki Jazakillahu khairan. Barinyi sallah in kwanta k’arfe bakwai zan fita gobe akoi meeting da za’ayi muzamuje muyi serving abinci can.”
“Toh ki huta gajiya nima barinje in samu Babanku. Seda safe.” A tare Afrah da Aiman da Fannah duk sukace “Allah bamu alheri” sannan Mami tafice bayan ta amsa da “Ameen karku manta kuyi addu’a”
Ya Fannah zan d’an samu d’ari biyun kati ne? Cewar Afrah tana b’oye fuskarta.
‘Yar murmushi Fannah tayi “saboda kisamu na kiran samari ba”
“Haba! Dan Allah Ya Fannah wallahi a’a.”
“Toh Allah kaimu gobe zan baki, kwanan nan bana spending much muku kuyi hak’uri tara kud’in nake ne Afrah inason kai Baba asibiti kinde san ya jikin nasa yake.”
Kai Afrah ta giad’a alaman tasani sosai. “Mun gode sosai Ya Fannah Allah k’ara bud’i.” Da amsar “Ameen” suka kashe wuta suka kwanta.
★★★★
ANAS
Sosai Anas ya k’ara kyau, fari da fresh, shekaru sun k’aru yazama cikakken saurayi yanzu me shekaru ashirin da uki (23) a duniya. Jikinsa muscular yake, packs nasa na nan guda hud’u dadai ba guda shida irin na wrestlers ba. Tsayayyen na miji yake yad’an k’ara kauri kad’an kan sirancinsa wanda yasake fito da kyansa. Sede kam hali na nan na shaye shaye dukda cewar har a yau Abuu da Ummie basu san yanayi ba, duk wanda yaji ance Anas na shaye shaye ma bare yarda ba saboda erin hankalin dayake nuna wa mutane, kominsa a b’oye yake. A da se in yayi mafarkin Ummimi ko na yarinyan dayayi raing yake sha amman banda yanzu, haka kawai in ya rasa abin yi ze kurb’a abinsa. Allah shirya.
A wannan shekaran yagama makarantarsa na London. Tun tafiyarsa be dawo gida ba sanda ya k’are shekaru biyar d’in cur! Cikin ikon Allah kuwa yafito da excellent result, school nasu sunyi dashi ya soma musu aiki dan iya zanen Anas as an architecture amman sam yak’i saboda san cika burinsa na karya wa mata zuqatansu, yafisan yayi da matan Nigeria kaman sa ba tsinannun turawa ba. Amal tasa ta girma sosai shekarunta 13 yanzu, ba abinda ya rabata da Anas kyau kawai ya d’ara ta da kad’an. Amal an d’an soma wayo amman har yanzu halin autan ta nanan dakuma rashin kunya da rashin shiri da Shettima. Shettima har yau besan ya girma ba shekarunsa ishirin da d’aya da abu a ka amman hakan be hanasa papiro Fannah da gudu in tamasa rashin kunya. Cat and dog Ummie ke ce musu.
Anas kuwa saide in bai gida sarai fa yasan Amal ce da laifi amman haka zebata gaskia yabawa Shettima laifi se in sun keb’e yake basa hak’uri. Sosai Anas yaya ne me hankali, yana kula da k’annansa ba kamar da ba kuma yanzu in yana cikin family’nsa yana murmushi da walwala sosai seda Amal ne kawai yake dariyan da har za’a ga fararen hak’waransa tas. Su Baana da Kashim ma suna nan sun bud’e ‘yar sana’a tare and alhamdulilah Allah na sa musu albarka. Shettina kuwa yasa san jiki a gaba, sam bayasan yin abu wa kansa yayi depending da Abuu kawai ‘cause yanzu masha Allah Abuu arziki se bunk’asa yake tunanin komawa Maiduguri ma yake sede har yanzu nothing is certain yet.
A yanzu haka Anas yana garin Maiduguri yazo neman aiki kwanansa uku kenan yau yakeda shirin fara fita neman aikin, Allah bada sa’a.
Construction industries yasoma bi sede yawancin su se suce basu d’iban masu aiki yanzu ya dawo bayan wasu ‘yan watanni dukda kyan result nasa kuwa haka ya gama yawo a ranar farko besamu aiki ba. Ranar biyu ma haka ya jera kusan sati yana neman aiki kap babu har yayi giving up kan monday ze koma Bama ze huta yanzu a weekends a gidan chairman daya sauk’a.
Yana kwance a guest room kan gado Iphone nasa yayi ringing yana kai dubansa yaga “My angel” Amal kenan. Da murmushi kan fuskarsa ya d’auka.
“My Angel” ya fad’i.
“Na’am Ya Anas d’ina ina wuni?”
“Lafiya qalau Angel ya kike ya school?”
“Lafya qalau Ya Anas, yaushe zaka dawo baka samu aikin bane har yanzu?”
“Ban samu ba Angel ina kan nema har yanzu amman nakega monday zan dawo. Kinasani cikin addu’a ko Angel?”
“Sosai Ya Anas yanzu ma dana idar da sallah sanda nasaka ciki”
“Yawwa My Angel ya Ummie toh?”
“Lafiyarta qalau. Ya Anas kaga Ya shettima d’azu ya mareni.” Ta fad’i kamar zatayi kuka.
Yana kishingid’e jin Amal tace Shettima ya bugeta yasa ya zauna tare da zaro blue eyes nasa. “Ya mareki? A dalilin meh?”
“Wallahi ba abinda na masa Ya Anas kawai fa abokansa ne sukazo yace in gaishesu nikuma nak’i saboda hak’ori na na ciwo shine bayan da suka tafi ya mareni a bayana wajen har yayi pink.”
Sarai yasan Amal da rashin kunya daga ji ba k’in gaishe da abokan nasa kad’ai tayi ba in aka bibiya halan har zaginsu ma tayi.
“Toh yi hak’uri Angel yanzu zan kirasa in sissilesa na dawo kuma zan rama miki.”
“Yawwa Ya Anas ba-bye.” Ding! Ta kashe.
Komawa yayi ya kwanta tare da zira wa ceiling ido yana murmushi wa kansa daidai lokacin wayarsa tayi k’ara yana kai dubansa yaga number ke kira, zurawa screen d’in ido yayi yana nazarin wacece can yace wannan number Meenor ce. Sanda ya kusa tsinkewa sannan ya d’aga batare da yace komi ba wata murya ce me zak’in gaske ta soma magana a hnakali dukda cewar cikin tashin hankali kuwa take.
“Haba dan Allah blue eyes, menayi kuma wannan karan? Tun jiya nake ta trying number’nka sarai kana gani ignoring d’ina kawai kake.”
“Toh nayi, zaki iya yin wani abu ne?” Gatsau ya bata amsa.
“A’a dan Allah blue eyes kar muyi haka dakai I’m sorry, I love you.”
“Meenor nomore of that we are done, karki sake kira na please ko kin kira ma barin d’auka ba.” Karap ya katse wayar. Kafin ya ajiye ta soma kira again sa number’n nata yayi a call divert tare da sakar da murmushi hakwaran samansa suka bayyana. “7 of 100 kenan.” ya cize light red lips nasa. Ma’ana cikin mata d’ari daya d’au alwashin ze kariya masu zuciya yaci nasara kan guda 7 wannan ma tun kafin yasamu aiki yazama billonaire kenan!
© miemiebee
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 13
BY MIEMIEBEE
washegari…
Kasancewar yau Asabar bayan Anas yayi wanka yayi breakfast yayi shirinsa na kullum T shirt da pencil trousers ya feffeshe da turare tare da taje gashin kansa yayi styling nasa me kyau sannan ya rataya jakar laptop nasa da credentials nasa ke ciki. D’an fita ganin gari zeyi tunda Monday ze koma Bama.
Tafiya yake cikin unguwar Old GRA yana d’an kalle-kalle yadda kowa yake aikin gabansa can yaga mutane sun taru gu d’aya se hayaniya ke tashi wajen, a hankali ya taka izuwa wajen shima dan ganin meke faruwa. Yawancin architects ne awajen seda masu construction kuma zane ne babba a gabansu se musu suke sun rasa gane ya zasu gudanar da aikin. Daga wata gefe kuwa wani dattijo ne zeyi erin shekaru 65 d’innan yayi tagumi ya zuba musu ido sunata shirmeh. Kallo d’aya Anas yayi wa zanen wajen ya gano zanen babban gini ne ko erin company ko industry haka. Daya sake kallo kuwa seya gano matsalar da suka samu wajen zanen murmushi yayi sannan yayi giaran murya “may I interrupt?” yace dasu.
Tas kowa wajen ya juya yana kallonsa, wasu suna admiring kyansa wasu kuma mamakin blue eyes nasa suke kode bature ne? Amman kuma farin sa bekai na turawa ba toh fah. Na zaunen ne yace “sure please” tare da mik’a ma Anas paper’n. Dattijon kuwa har yanzu na zaune yana kallonsu. Amsar pencil da cleaner Anas yayi yad’an goge wani waje a zanen ya giara daga k’asa sannan yayi haka ma daga sama. Yana gamawa ya juya paper’n yana kallon babban nasu na zaunen bayan ya d’an kalla aikuwa sega abinda suke san sucire d’in yafito, building d’in is in perfect position. “Wow!” Yayi exclaiming “saurayi you are incredible! ku tafawa wa wannan saurayi please.”Nan take duk mutanen wajen suka d’iba da tafi suna hailing Anas.
Dattijon dake zaunen ne ya taso da karar tafiyarsa irin na gayu me kan gwal d’innan ya iso wajen a hankali. Cikin muryar manyanta yace, “meke faruwa anan?” Babba na zaunen ne ya juya da paper’n yana nuna masa “gashi Mr Muh’d toilet da ake buk’ata a last floor d’in yafita building d’in is in perfect position yanzu.” Kai Mr Muh’d ya giad’a a hankali “good.” yace. Babba na zaunen ya cigaba da cewa “wani saurayi ne anan yanzu ya giara yana zuwa kawai ya amshi papern ya d’anyi goge goge kawai ya fitar he must be a genius. Ina kake ne?” Yana dubawa kuwa se ba Anas har ya juya ya cigaba da tafiyarsa.
“You two” Mr Muh’d ya nuna yaran aikinsa guda biyu “ku bisa ku kira min shi.” A papare suka yi inda Anas yabi suna gudu suna binsa can suka gansa ya tsaida taxi ze shiga “hey! Hey! Bawan Allah ka tsaya” sam be jisu ba gashi basu san sunan saba. Can d’ayan yace, “me blue eyes!!!” da k’arfi cak Anas ya tsaya ya juya yana kallon inda yajiyo kiran. Bada jimawa ba suka iske sa. Hannu d’ayan ya mik’a masa suka gaisa. “Uhm I’m Kacallah wannan co-worker nane Yunus mune wanda kayi saving building drawing namu yanzu. Thank you”
“Oh!” Anas yad’anyi murmushi, “that was nothing kar ku damu” ya juya ze shiga taxin. Yunus ya tsaida shi “erm dan Allah d’anyi hak’uri ka tsaya Boss na wajen aikin mu neh CEO’n Flames Enterprises babban company’n dake Maiduguri keson maka magana.”
Zaro blue eyes nasa yayi “me?” Ya nuna kansa cike da mamaki.
“Eh” Kacallah yace “you! You did what muka kasayi duka for that yanason ya maka godiya and am very sure zeyi honouring naka saboda Mr Muh’d mutum ne me kirki.”
“Okay” Anas yace… Har yanzu ji yake kamar a mafarki wai CEO’n Flames Enteeprises keson masa godiya, sosai yasan Enterprise d’in kullum cikin NEWS se anyi maganan enterprise d’in yadda suke successful. Shi koda yake neman aiki ma be lek’a can ba a tunaninsa ma barasu kallesa ba bale su d’auke sa.
Kacallah ne ya katse masa tunani, “blue eyes baka ce komai ba.”
D’an murmushi Anas yayi “you can call me Anas, suna na Anas.” Kacallah yace, “wow suna me dad’i but still I prefer blue eyes sorry to ask muslimi ne kai?”
Kallonsa Anas ya tsaya yi daman ina kama da christians ne? Ya tambayi kansa.
Ganin Anas be amsa saba yasa ya giara zancen nasa “uhm don’t feel offended please bawai kamin kalan arne bane kawai your eyes…” ya nuna idanun Anas da yatsa “nad’au bature ne kai.”
Sosai Anas yayi mrmushi, “toh ai ban kaisu fari ba” yace.
“Eh nasani ko irin black Americans d’innan ne kai.”
“To ka kwantar da hankalinka ni nan da kake gani na kanuri ne daga Bama dangi na kap ba christian.”
“Ohhhh!” Kacallah da Yunus suka fad’i a tare suna giad’a kai. “Ikon Allah!” cewar Yunus. “Kanuri amman zallah? Baka had’a dawani yare ba?”
Toh fa an tab’o gogan namu, ya washi yakira yaren Ummimi amman ya ya iya dasu? dole ya fad’a musu ko zasu bar kallon da suke masa.
“Mahaif-” se zece mahaifiya ta seya gagara dan koda wasa baisan kiran Ummimi dasunan mahaifiyarsa shi Ummie yasani mamansa ba Ummimi ba. Ganin sun zura masa ido yasa kawai yace, “mahaifiyata shuwa arab ce, mahiafina ne kanurin.”
“Aihoooo aiko da alama” cewar Kacallah “sesa kake da kyau haka, masha Allah. Toh blue eyes muje Boss namu nasan ganinka.” Sallamar me taxi d’in yayi sannan ya bisu har gaban Mr Muh’d suka kaisa. “Mr Muh’d gashi nan” suna fad’in haka suka ja da baya duk suka bar wajen ya rage daga Anas se Mr Muh’d.
“morning sir?” Anas ya gaishesa tare da durk’ushewa har k’asa mutumin be amsa ba illa kallon Anas dayake har Anas ya shiga tsoro daga bisani Mr Muh’d yace, “morning boy, get up please.” Nan Anas ya mik’e yana kallon k’asa. “I will first of all like to thank you for saving my men and company in all.”
Anas na murmushin dole yace, “ba komai Sir, don’t make an issue out of it.” Cike da mamaki Mr. Muh’d ke kallon Anas jin yayi hausa. “Kanajin hausa kenan?” ya tambayesa.
Mamakin erin tambayan Anas ke wai dagaske aka gansa bara’a d’au yana jin hausa bane? Dole ya sai black lens (k’wayan ido) a kasuwa ya soma sawa.
“Sosai inaji Sir d’an nan ne ni ai, kanuri nake daga Bama.”
Sanda idan d’an dattijon ya warwaru. “Kaid’in?” Ya tambaya in disbelief.
“Eh sir” kafin Mr Muh’d yasake wata maganar Anas yace, “nasan you must be wondering ya nake da blue eyes haka aka haifeni amman d’an nan ne ni kuma muslimi ne ni my name is ANAS IBRAHIM FAUZY.”
Kai Mr. Muh’d ya giad’a alamam ya yarda. “Toh masha Allah Mr. Fauzy kanada kyau tubarkallah.” Murmushi Anas ya masa “na gode Sir.”
“Kana kirana da Baba, I once had a son as you.” Sekuma mood nasa ya canza.
Nan Anas ya gano rasuwa d’an nasa yayi kenan. “I’m sorry Sir.. I mean Baba.”
“Bakomai Mr. Fauzy. Aeroplane crash ne ya samemu time da zamuje hutu Paris nida d’ana Sultan da matata sekuma da iyayena, bayan jirgin yayi crashing atake duk suka rasu ni kad’ai nayi surviving a family na dukda nima naji ciwo sosai a sanadin haka na rasa k’afata na hagu anyi aiki sosai amman ina yak’i gyaruwa sesa kaga ina tafiya da stick (sanda).”
Tausayin bawan Allah’n nan Anas yaji ya kamasa, sarai yasan how it feels to be alone, not to have a family shi Ummimi kawai suka rasa amman rayuwarsu ta tab’arb’are bale shi nasa da ya rasa komai. “I’m so sorry Baba Allah ya jik’ansu da rahmah.” “Ameen Mr Fauzy sede ana nema na awani meeting yau gashi har…” Ya d’aga hannunsa ya kalli agogon hannunsa “8:30 yayi.”
“Ba komai Baba I’ll sit here in jiraka its my honour meeting with you, nasha ganinka a NEWS you’re such a successful man.” Murmushi kad’an Mr. Muh’d yayi “lets go” cike da rashin fahinta Anas yace, “excuse me?”
“Lets go to the meeting together.”
Blue eyes nasa ya zaro “Baba thank you for the offer but I’m not invited kar inje a koreni.”
“Hahaha!” Mr. Muh’d yayi dariyan manya. “Not in kana side d’ina so lets go?”
Kai Anas ya giad’a masa. Waya Mr. Muh’d yayi bada jimawa ba wata prado 2016 bak’a tasha wanki har kamar mirror jikinta yake ya zo yayi parking a gabansu. Fitowa wani yayi daga gaba ya bud’e k’ofar baya, hannu Mr Muh’d ya nuna wa Anas da nufin ya shiga a sanyaye ya shiga tare da rik’e jakar laptop nasa daya rataya a kafad’arsa kan cinyarsa, bayan shigansa Mr. Muh’d ma yashiga a hankali driver’n yasoma tuk’i.
Basu tsaya ko inaba se wata babban conference hall tun fitowarsu daga motar mutane suka soma layi jiran su gaisa da Mr. Muh’d. Mamaki ne yacika Anas mutane kamar su cinye Mr. Muh’d wasu kuwa tambaya suke kowaye Anas amsar dayake basu ne yasa Anas shocking wai “he is my son.”
Wajen VIP aka zaunar da Mr. Muh’d shima Anas yasamu kujera a gefen sabon Babansa (lol). Tambayoyi sosai Mr. Muh’d ya riga yi ma Anas kan ina yayi karatu? Sheraunsa nawa? Tambayoyi de turum. Daga k’arshe ya buk’aci Anas da ya nuna masa CV’nsa dan yagani Allah yaso Anas kullum yana yawo dashi nan ya ciro yamasa presenting.
**
“Fannah! Fannah” kirar Boss na wajen aikinsu. “Yes Boss” ta fad’i bayan da ta iso. “Ga can table na VIP Mr Muh’d ne CEO’n Flames Enterprises.” Ido Fannah ta zaro tare da kewayo wa tana kallonsa ba shakka tana ganinsa a NEWS kap Maiduguri ba wanda yakaisa kud’i.
“Kinga saboda kinfi sauran ‘yan uwanki fasali yasa ke zanbawa chance d’innan kije kiyi serving nasa drinks dashi da saurayin gefensa dukda cewar yau na soma ganinsa naji ance wai Mr. Muh’d da bakinsa yace d’ansa ne kinga ko sekije kid’an tatso mana su. Kiyi amfani da kyanki ki ja attention na d’an nasan.”
Fuska Fannah ta d’aure ko juyawa ma takalli saurayin da akace d’an Mr Muh’d d’in batai ba. “Ya Suleiman wai mesa kake magana haka ne? Nikama b’ata min rai nafasa kai musun gasu Asma’u ka kira sukai masu.”
“Haba Fannah ke bakisan wasa bane? Ai wasa nake miki. Ungo ga plate nasu na shirya yi hak’uri ki kai musu.” Kallo ta watsa masa sannan ta d’aga ta fice. Murmushi yayi haka suke cikin fad’a kullum shida Fannah sarai yasan batada interest cikin samari shikuwa yata neman taokanarta, in aka ajiye wannan agefe kuwa shida Fannah suna shiri sosai tamakar sister’nsa ya d’auketa. Shine d’an me coffee shop na wajen aikin su Fannah’n. Saboda haka duk wani aikin da akeyi shike bada orders.
Tunda Fannah ta soma tafiya zuwa table na Mr. Muh’d dan kai masu drinks da d’ansa bata d’aga kai ba. Kanta a k’asa tana isa table d’in ta gaishe da Mr. Muh’d da fara’arsa ya amsa sannan ta ajiye mishi cup nasa, ta mik’a hannu ta ajiye wa Anas nasa shima. A yayinda yake answering call ko d’aga ido ya kalli wacece ma beyi ba kawai “thanks” yace. Fannah itama da kanta ke k’asa bata d’aga kai ta kalle sa ba kawai de tasan waya yake. Ta juya zata tafi kenan Mr. Muh’d ya kira ta da “waitress” cak ta juyo “yes sir.” “Take this away” ya nuna cup na gaban Anas dake kan waya har yanzu ko kallon direction nasu baiyi “ki kawo masa irin nawa” “okay” tace sannan ta d’aga tana juyawa taga Asma’u sekuwa gashi kan plate nata akoi erin na Mr. Muh’d nan ta d’aga ta aza kan table d’in. “Here you go Sir” tace sannan ta juya zata tafi dakatar da ita yayi sannan ya zira hannu a aljihu ya ciro bundle na d’ari biyar ya mik’a mata. “Gashi ko mungode.”
Fannah tasha jin ana cewa Mr. Muh’d nada kyauta bata tab’a tabbatar da hakan ba se yau. Amsa tayi hannu bibbiyu ta masa godiya. “Ba komai wannan nakine bawai na baki bane kije ki kai wa boss naki, wancan na zuwa daban. Keep this”
Murmushi take sosai “Thank you sir! Thank you” nan ta fice daidai lokacin Anas ya katse wayar dayake yi tare da kewayo wa. “Kai da waye ne?”
“Nida Abuu ne mahaifina.” Ya amsa a takaice.
“Okay gashi an canzo maka tunda you are allergic to wancan flavour’n.” “Thank you” yace “gashi ban samu na bata hak’uri ba nasa ta tayi sahu biyu.”
“Bakomai don’t worry.” Atare suka sa cup nasu a baki suka d’anyi sipping sannan suka mayar suka ajiye. “So Mr Fauzy naga credentials naka you have such an excellent result, I’m ready to offer you a job a Flames Enterprises as my Personal Assistance (PA) akan albashi N500,000 (dubu d’ari biyar) dakuma weekly allowances N5000 (dubu biyar) kowani sati for a start kenan inhar naga ka iya aiki kana kiyayye komai kuma naji dad’in aiki dakai there will be additional salary for you. So? Will you accept my offer?”
Anas ji yake kamar a mafarki albashi dubu d’ari biyar? “Yes! Yes Baba nagode sosai, in shaa Allah zaka sameni me kiyaye duk wani dokokin da ka kafa min. This is amazing nagode sosai yau sati na a nan Maiduguri ina neman aiki ban samu ba segashi ka bani wanda ban tab’a zaton zan samu irinsa ba I can’t wait in kira Abuu in sanar daahi. Nagode sosai Baba Allah saka da alkhairi.”
Kallonsa Mr. Muh’d yake yana murmushi he made Anas happy, kawai tunawa yake da d’ansa.
*© miemiebee*
NAGODE LOADS FOR THE WARM CONCERN YOU GUYS HAVE SHOWN ME, I LOVE YOU ALL!
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 14
BY MIEMIEBEE
“Hello Abuu?” Cewar Anas ta waya.
“Anas Baba na ya kake?”
“Lafiya Abuu I have a suprise for you”
“Toh inaji Baba na.”
“Nasamu aiki!” Anas yayi exclaiming.
“Ahh toh Alhamdulillah a ina haka?”
“A Flames Enterprises Abuu, kuma as Personal Assistance na CEO’n wajen.”
“Wai wai! Kana nufin Alhaji Muh’d Muh’d??” Abuu ya tambaya cike da mamaki.
“Shi Abuu salary na N500,000 da weekly allowances N5000.”
“Kai Baba na namaka murna barin fad’awa Ummie se add’ua take ta maka.”
“A’a bari Abuu I’ll call her dakaina banasan Amal tasan she is not the first person I called to tell.”
“Uh!” Abuu yayi exclaiming “kai da wannan ‘yar takan.”
Murmushi Anas yayi “Aikam Abuu ina karb’an first salary na shopping zankai Amal.”
“Toh Allah maka albarka Anas yacigabada bud’i congratulations.”
“Thank you Abuu se mun sake magana.”
“So yanzu zaka shigo Monday d’in still?”
“Eh zan shigo saboda in d’iba kayakina I have untill next week inyi resuming office.”
“Okay toh yayi kyau, welldone.” Ahaka sukayi sallama.
Anas na cikin searching contact na Amal wayarsa ta soma k’ara number ke kira bayan yad’an zura wa number’n ido ya gano Teema ce. Murmushi yayi sannan ya d’aga batare da yace komi ba.
“Hello angelic blue eyes” cewar budurwar.
“Yes” ya amsa ba tare da ya nuna damuwa ba.
“Blue eyes fad’a muke ne? Tun jiya nake expecting call naka shiru.”
“I have far worth important stuffs to attend to than you Teema.”
Har tsakiyar kanta ta jiwo wannan zagi amman ta danne zuciyarta. “Blue eyes dama so nake in sani ko you are free zuwa anjima da yamma inason mu fita ne, like a date.”
“What are you implying Teema? Kina nufin ni bansan abinda yakamata ba se kece zaki bani time da zamu fita date dake?” Ya fad’a a tsawace.
“Blue eyes please calm down ba abinda nake nufi ba kenan naji kace gobe zaka koma Bama I want to spend some time with you kafin ka tafi.”
“Huh!” Ya saki numfashi. Tare da jawo kad’an daga cikin gashin kansa yana wasa dashi da wata mirmushin mugunta a fuakarsa. “Nikuma banaso kinsan me Teema? Lets just end it bana sonki anymore lets break up, we are done karki sake kira na ko kin kira barin d’auka ba.”
“Blue ey-” bata k’are maganar ba ya katse nan take ta sake kira kalan abinda yama Meeno ya mata. 8 of 100 ya murmusa sosai wanda ya mugun k’ara masa kyau.
Amal nasa ya kira ya fad’a mata yasamu aiki. Tsalle ta riga dakawa haka suka sha hira sannan yace ta kai wa Ummie wayar. Sosai Ummie ta masa. Shettima ne k’arshe ya kira ya fad’a masa aikin daya samu, sosai Shettima uwar san jiki yamasa murna at long last ze soma jin dad’i dan yasan halin Anas be iya rowa ba inba wai dagangan zeyi ba, mutum ne me kyauta amman fa ma wanda yaga dama.
★★★★
Da misalin k’arfe 3:30PM Fannah ta dawo gida da ledoji manya manya hannunta siyayya tama family’nta sosai. Mami, Afrah da Aiman duk suna tsaye tsakar gida hankali tashe a tunaninsu ko wani abu ne yasamu Fannah saboda duk sanda zata wani waje daga gun aiki tana kiran Mami ta sanarda ita wanda yau batayi ba.
Tana shigowa Mami tayi kanta tare da rungomata “Fannah ina kikaje? You made us worried sick gashi nata kiran wayarki akashe.”
“Wallahi game natayi seta mutu, kubar tada hankalinku please in shaa Allah ba abinda ze sameni. Kasuwa na wuce nad’an mana siyayya.”
Nan Afrah da Aiman suka k’ariso tare da karb’an ledojin akan tabarma suka zauna tare da zazzage kayakin.
Kitchen utensils ne, food items, seda sweets da chocolates dakuma atamfofi guda hud’u masu kyan gaske seda shadda guda biyu, se sauran k’ananun abubuwa irinsu tissue, toothpick da sauransu. “Fannah ina kika samu kud’i haka ko har anbiyaku albashin ne?”
“Ko kad’an Mami, ina meeting dana fad’a muku za’a kaimu serving d’insu yau?” Mami ta giad’a kai “ashe harda Alhaji Muh’d Muh’d CEO’n Flames Enterprises.”
“Haba keh!” Cewar Mami.
“Ya Fannah kap Maiduguri fa ba wanda yakaisa kud’i!” Cewar Afrah.
“Ya Afrah shine wanda muke gani a NEWS yawancin kullum?” Aiman ta tambayi Afrah. “Eh shi” Afrah ta amsa ta a takaice.
“Toh shida d’ansa sukaje ni akace na kaimusu drinks nasu bayan nakai nakega se d’an nasa yace baya shan flavour’n drink d’in baban nasa ya kirani na canzo masa nazo tafiya kawai Alhj Muh’d d’in ya kirani ya mik’a min bandir na N500 kyauta bayan da aka k’are meeting d’inkuma da muka raba kud’in da aka bamu na tashi da dubu goma albashi na na wata fa kenan ga kuma dubu hamsin. Daga can na wuce kasuwa namana d’an siyayya dududu kayan dubu talatin ne anan.”
Aiman mathematician har an buga lisafi “sauran miki N30,000 kenan.”
Kallonta Fannah tayi tana murmushi “welldone ashe surutun nan naki ba’a banza bane tunda kin iya math haka.”
“Math d’in ‘yan primary three ba” cewar Afrah tana duba zannuwan. Aiman zatayi magana Afrah tace, “Ya Fannah wannan zannuwa fah?”
“Namu ne biyu na Mami ta zab’a ciki, guda biyu iri d’ayan kuma naki da Aiman.”
“Haba Ya Fannah mena siya min turmin zani iri d’aya da wannan maras kunyan.”
“Yo! Ked’inma ance miki inasan yin anko dake ne? Ya Fannah mungode sede har yanzu banga sweet d’ina ba.” Cewar Aiman.
Nan Fannah ta bud’o jakarta ta ciro packet na sweet “ungo wannan duka naki ne kika rabawa ‘yan ajinku kuma ni ba ruwa na.” Amsa tayi tana tsalle “nagode Ya Fannah ai ko Ya Afrah ma barin bata bale ‘yan ajinmu masu kwad’ayin nan, wallahi Falmatan nan har k’wai na sanda taci ranan” Zani biyu iri d’ayan ta d’au d’aya tashige d’akinsu dashi. “Ke dawo nan waya ce miki ki d’auka?” cewar Afrah jan d’ayan tayi itama ta ruga tabi Aiman cat and dog kenan.
“Fannah Allah miki albarka, Allah k’ara miki bud’i yaci gaba da kare mana ke. Mungode matuk’a da d’awainiyan da kike mana dukda kuwa ba responsibility’nki bane wannan aiki na ne da Babanku amman kinayi. Kiyi hak’uri.”
Hannun ta Fannah ta rik’e bibbiyu cikin nata “Ameen nagode da addu’arki Mami amman dan Allah kidena min godiya ba godiya tsakani na daku Mami. Na ware dubu ishirin cikin kud’in gobe seki kai Baba asibiti a duba shi ko magani a basa tunda baramu iya affording aikin da za’a masa ba.”
“Toh Fannah, sannu da k’ok’ari Allah miki albarka.” “Ameen” tace “barin je in samu su Afrah ciki, ki d’au zannuwa biyu anan shaddojin kuma na Baba ne.” “Toh mungode sannu.”
Fannah na shigowa d’aki tasamu Afrah da Aiman se dambe suka dak’yar ta rabasu zani de gasu iri d’aya amman ahakan ma se anyi fad’a. Bayan ta rabasu ta kori Aiman dawayo in bahaka ba sun hau wasan habaici kenan. Ana kawo wuta ta had’a wayarta a charging. Kayakinta na cikin wardrobe take shiryawa a yayinda Afrah ke kishingid’e kan gado tana game a wayarta. Can ta nisanta sannan takira Fannah. “Ya Fannah!” “Na’am Ya Afrah, mene kuma yanzu?” cewar Fannah tana ninke kayakinta.
“Kikace d’azu kinga Alhaji Muh’d Muh’d?” Kai Fannah ta giad’a batare da ta kalleta ba. “Okay da d’ansa kuma kikace sukaje wajen?” Afrah ta fad’i kalma d’ai d’ai.
Barin abinda takeyi tayi ta juyo ta kallon Afrah “what are you implying?”
D’an dariya Afrah tayi “guilty concious?? Ni bance komi ba kawai cewa nayi kinga d’an Alhj Muh’d?”
“Nope ni bangansa ba.” Fannah tabata takaicaccen amsa.
“Wow! Yau me hana mutane k’arya keyi? Hilarious.” Cewar Afrah tana mocking smile.
“Kuma se akace miki k’arya nake. Allah ban ga d’an nasa ba.”
“Toh ikon Allah kuma ke fa ke kika kai musu drinks nasu? Kodan had’ewarsa yasa baki gansa ba?”
“Ke wallahi Afrah suratan banza sun miki yawa. Ni ko zaki samin wuk’a a wuya bansan kalar fatar sa bama bale insan ko kyakkyawa ne ko mumuna. Muryarsa kawai naji.”
“Haba!” Afrah ta daka tsalle tare da baro inda take ta matso kusa da Fannah. “Ya muryar tasa take Ya Fannah? Fad’amin please kinsan su yaran masu kud’i muryarsu ma daban take.” Shiru Fannah tayi tana nazarin muryar Anas dasuka d’au d’an Alhj Muh’d ne. “Well ba hassada muryarsa nada zak’i irin zak’i ta mazan nan and yana cracking hakan nan. Barin miki bayanin yadda zaki gane kinsan muryar Lancelot nacikin season film Merlin ba?” Kai Afrah ta giad’a sau uku. “Toh haka murayarsa take sede kamar zatafi na wancan d’inma dad’i. Toh kinji, matsa min nacigaba da abin dake gabana.”
“Iyye! Har kinsa na fara imagining wannan d’an billonaire nasan definately zeyi kyau sesa hakan ma ba’a nuna sa a NEWS gudun kar ‘yan mata su bisa.” Kallo Fannah ta bita dashi “kefa wallahi surutun banzanki sunyi yawa.”
“Hummm! Afrah taja numfashi “Ya Fannah kenan. Kinsan muryarsa meaning kunyi magana kenan.”
“Wai meke damunki bamuyi magana ba acewarki yaran da ubansu billonaire suna magana wa mutane anyhow ne? Ko kallona ma beyi ba dana ajiye masa drink d’in kamar yadda nima ban kallesa ba thank you kawai naji yace.”
“Iyye! Amman daya miki magana fa? Zaki amsa?”
“Ke qaniyarki, Afrah kika sake maganan wancan saurauyin bake ba kud’in kati se next month.” Tsit Afrah tayi bata kuma cewa komi ba, ahaka Fannah tasamu tagama had’a kayakinta cikin wardrobe.
_One week later…_
Anas ne tsaye gaban dressing mirror a d’akin da chairman yabasa. Yau ze soma zuwa office he is feeling nervous sosai. Sanye yake da mint blue shirt me long sleeves da cufflinks, seda jean trousers. Simple shiri ne amman yamugun amsar sa he is looking way smart. Jakar laptop nasa ya d’ago yasa laptop d’in ciki da sauran takardu kad’an sannan yasake kallon kansa jikin madubin sannan ya fice bayan ya karya ya wuce office.
Yana isa gaban building d’in da za’a iya kira da mini sky scrapper ya tsaya. A k’alla floors za suyi 7-8, dogon gini ne sosai wanda jikin bangon yake glass. Building ne babba bakin k’ofar an rubuta FLAMES in caps. Wani button ya danna k’ofar glass d’in ya bud’u yana shiga k’ofar yayi scanning nasa bayan ya tabbatar baya d’auke da makami sannan wata k’ofar ta sake bud’uwa nan ne mutanen cikin ginin suka bayyana. Maza da mata kowa se aikin gabansa yake very organised. Wajen shiru ba hayaniya. Wajen dayaga an rubuta RECEPTION ya k’arisa mace ce tsaye wajen gabanta telephone ne da pack na pencil da biro seda files kuma. Tun kafin ya mata magana tace dashi “Hi” tana washe 32 inta acewarta taga bature.
“Hello” ya gaisheta back, “erm I want you to direct me to Mr. Muhd’s office, the CEO.”
“Okay American’s most handsome” tace dashi. “Whats your name?”
“Anas Ibrahim Fauzy.” Ya amsata a takaice. Baki tasake wangalau wai dama ba bature bane?
“Excuse me, I mean your name. Name.” dan bata yarda muslimi bane.
“Yes Anas Ibrahim Fauzy. Ko kema kin d’au Joseph ko Andrew ne sunan nawa? My name is Anas for goodness sake.” ya fad’a a tsawace.
“I’m sorry blue eyes” ta fad’a tare da kashe masa ido. Tsuka yaja tare da kawar da idanunsa daga kanta.
“Uhm are you two having an appointment with the CEO yasan da zuwanka?”
“What nonsense? Da inbe san da zuwa na ba zanzo nan ne? Take me to your CEO” yayi demanding ba alaman dariya a tatare da fuskarsa. “Mesa yawancin kyawawan mutane basuda hali ne?” Cewar receptionist d’in a hankali aikuwa Anas ya jiyota harara ya watsa mata bayan d’an dube-duben da tayi a system dake gabanta tace, “I’m sorry Mr. Fauzy seems like ba sunanka acikin wad’ana zasu ga Mr. Muh’d yau maybe next time.”
“Kinsan wani abu? Tunda nake a duniya ban tab’a ganin senseless mutum kamar ki ba.” Dadai lokacin elavator ya bud’u Mr. Muh’d ya fito daga ciki. Taku d’ad’ai kamar yadda ya saba yayi yatako zuwa gabansu Anas cike da girmamawa Anas ya gaishesa.
“Ya Anas me kakeyi baka shigo ba har yanzu? I’ve been waiting for you”
“Baba wannan receptionist d’ince ta rik’eni wai baran shiga ganinka ba.”
“No Sir ba hak-”
Katse ta Mr. Muh’d yayi rai a b’ace “this should be the last time da zaki sake hanasa shigowa nan he is Anas my son, copy that!” ya daka mata tsawa.
“Yy..yyess sir, my aplologies please.”
“You apologise to him not me.”
Kallon Anas take yana mata murmushin mugunta, “Mr. Fauzy I’m sorry.” Harara ya watsa mata sannan yace, “apology accepted.” Nan Mr. Muh’d yaja hannunsa “come lets go in nuna maka office naka.” A floor na k’arshe yakai Anas inda aka rubuta Mr. Fauzy a bakin k’ofar d’akin. Office ne babba da split AC ciki, office kujeru ne manya guda biyu da table d’aya. Akoi telephone da flat screen desktop kan table d’in seda notepad, da pen dakuma pencil pack. Gefe guda kuwa fridge ne seda plasma TV. “This is your office, inda abinda be maka ba let me know se a giara” Godiya sosai Anas ya masa tun daga ranan Anas ya soma aiki.
He is very punctual, duk meetings da schedule na Mr. Muh’d shi yake maganing kasancewar duk Enterprise d’in ba architecture’n daya kai Anas duk sandq za’ayi zanen project Anas keyi.
© miemiebee
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 15
BY MIEMIEBEE
★★★★★
5 months later…
Shak’uwa ne me k’arfin gaske ya shiga tsakanin Anas da Mr. Muh’d, ladabi da biyayya kam Anas ya iya duk wanda yaji ana cewa Anas na shaye-shaye ze k’aryata zancen. Basu tab’a samin matsala da Mr. Muh’d ba aikinsa duk yanayi me kyau tun da yayi joining enterprise d’in abubuwa suka sake improving fiye da da. Family’n Anas a yanzu haka sun dawo Maiduguri da zama a unguwar New GRA. katafaran gida Abuu ya sai masu da taimakon Anas. Gida ne mansion d’aki kota ina. Rayuwa alhamdulillah yanzu, ansa Amal a Ruby Springfield College. Shettima kuwa ya soma attending UNIMAID a inda yake karanta accounting.
Anas yayi introducing family’nsa wa Mr. Muh’d sosai suka shak’u da juna. Sanin yadda Anas keson Amal yasa shima Mr. Muh’d yakeson Amal sosai, musamman yadda take sasa dariya duk sanda suke tare in su Anal sunyi hutu kullum tana office wajen Mr. Muh’d datake kira da grampa, wane family haka suka zama. A birthday’n Anas Mr. Muh’d ya basa sabuwar mota pil cikin leather k’irar mercedes-benz SLK. Tunda Anas yayi mota walak’anci ya k’aru ahaka yanzu a list nasa yanada mata 33 da yayi breaking hearts nasu. Leaving life nasa yake to the fullest duk sanda su Baana suka shigo Maiduguri kuwa shan giyan ranan na daban ne. Suna waya sosai da friends nasa Abdoul da Musty.
Yau ranar ta kasance Monday as usual ya soma shirin office, Shettima da ba lectures se da rana se bacci ake sha. Amal da ba office zata ba amman ta riga Anas tashi tare suka had’a breakfast su biyunsu sukaci bayan sun gama ta rakasa har parking lot yashiga cikin sabuwar motarsa sukayi ba-bye da juna sannan ya fice. As usual yashirya wa Mr. Muh’d schedule nasa na ranan yakai masa. “Welldone Anas, kana k’ok’ari sosai nace zanen project d’incan kasamu kayi kuwa? Kasan mutanen daga Ghana zasu zo yau akoi board meeting da za’ayi by 4:00PM zamu masu presenting.”
“Eh Baba nayi yana nan ajiye cikin shelf a store room floor 2.”
“Good, se meeting d’in zanbar care d’in a hannunka. Akoi inda ake samun professional waiters a Fahmaz coffee shop (inda Fannah ke aiki) kayi waya da masu wajen kamana booking.
“Okay Baba, I’ll be going” nan ya zarce office nasa inda ya kira number’n me Fahmaz coffee shop d’in.
***
“Ya Suleiman ga call from Flames Enterprises.” Fannah ta danna kira wa Ya Suleiman dake waje. “Ki d’aga kiji meneh, I’m busy here.” Hannu tasa ta d’aga tare da yin shiru bata ce komai ba. “Hello?” Anas ya fad’i cikin muryarsa me tafiya wa kowace mace da imani. “Hello” Fannah ta fad’i in return. This is Fahmaz Coffee shop, how can I assist you?”
Jin muryar mace ne yasa ransa ya b’aci take. A fusace yace, “ai nasan Fahmaz Coffee shop d’inne saisa na kira so just shut up plus haka aka koya miki wajen aikin naku in kun d’au waya kuyi shiru?”
“Lalle ma wannan mutum anyi d’an iska” cewar Fannah a zuci “shi ya kira kuma yana jiran nice in soma yin magana?” Dukda bame san magana bace amman taji barata iya hak’ura ba so take ta sa koma waye ne shi in his rightful position sekuma ta tuna wannan business related matter ne she shouldn’t take it personal.
“I’m sorry. How can I assist you?”
“Mstchww” yaja tsuka sannan ya cigaba “we need 5 waitresses and 5 waiters from your coffee shop here at Flames Enterprises by 4:00PM.”
“Okay copied” tace.
“Bama tolerating late coming you guys should make sure 4 d’in ya muku anan.”
“Lalle ma wannan mutumin” cewar Fannah a zuci.
“Ko baki ji bane?” Zatayi magana ya katse dagangan. Ciro telephone d’in tayi daga kunnenta tana kallon wayar cike da namaki wannan wani irin bawan Allah ne me uban jijji dakai haka? Mstcw taja tsaki daidai lokacin Asma’u ta shigo “yau Fannah ke tsaki? Keda waye ne haka?” Ta bud’e baki zatayi magana Flames Enterprises d’in yasake kira sanda ya kusan tsinkewa sannan ta d’aga “yes.”
“Don’t use that tongue with me young lady” cewar Anas in a serious tone daya tsorata Fannah kum tayi shiru. “Incase clueless mind naki be baki idea ba, you have to be here now saboda coffee zakuyi serving ba drinks ba. So zakizo in baki details d’in plus don’t be late bana jiran mutum sede a jirani.” Shiru tayi tana mamakin wannan bawan Allah. “Are you there? Cause bana repaeating kaina twice”
“Yes I’ll be on my way.” Nan ya katse wayar. Tsuka takuma ja “lallai akoi arrogant people dayawa a duniya what is he feeling like? D’an Adam de ba wanda yafi wani we are all equal.” Asma’u dake kallonta tace, “ji yadda kike magana sekace bakisan Anas ba.”
Fannah tace, “Anas? Waye shi?”
Asma’u tace, “no wonder sesa kike tada jijiyoyin wuyanki haka, ni rananda ya kira na d’aga bakiga zagin duniyan daya min ba aike yamiki mutunci ma.”
“Toh waye shi? Whats he feeling like?”
“Shine PA’n Mr. Muh’d na Flames Enterprises kuma ance Mr. Muh’d nasan sa tamkar d’an cikin daya haifa, cewa ma yake Anas d’in d’ansa ne.”
“Ikon Allah! Lallai kam.” cewar Fannah cike da mamaki.
“You better go kafin yasake kira ya balbale ki.” A sanyaye Fannah ta fice bata tsaya ko inaba se Flames Enterprises can akayi directing nata zuwa office na Anas tsaye take a bakin k’ofar office nasan takasa shiga zuciyarta se bugawa take musamman ma data d’aga kai taga ansa *Mr. Fauzy* asaman. Tafi minti biyu tsaye a wajen sannan jiki na k’yarma hannu na b’ari tayi knocking k’walli d’aya tal jin ba’a amsa ba yasa ta k’ara d’aya “come in” taji muryan na miji ya fad’i authoritatively. Tabbas tasan wannan murya shine wanda yace mata thank you rananda Mr. Muh’d ya bata bandir na N500 kawai haka taji zuciyarta na bugawa tarasa dalili.
Haka har da aka tashi Anas be sake neman Fannah ba. So yake ya nisantar da kansa daga gareta as possible enough as he can, saboda ya soma ji kamar maganganun Shettima gaskia ne. Saboda when it comes to Fannah he is weak abubuwa dayawa take masa wanda yaci ace ya koreta koya hukunta ta amman seyaji bare iya mata komai ba. Yasoma yarda eh he is feeling something for Fannah amman ba love bane tausayi ne kawai, yana tausayawa mata sede ko daya tambayi kansa tausayin me take basa yakasa answering. Fannah is his weakness.
Fannah kuwa dad’i taji da be sake nemanta ba dan da wannan kayan kunyan da tama kanta na masa shisshigi harda karance diary’nsa bata san da wani idan zata sake kallonsa ba. Ita abinda yafi bata mamaki ma shine yadda Anas yabata hanky wai ta goge hawayenta bayan abinda ta masa, shin meke damunsa yau? Ta d’au atake zeyi firing nata kokuma ya mata wani abu makamancin haka amman seyayi sab’anin abinda take expecting. He is acting wierd yau, bata tab’a ganinsa haka ba shida yake fad’in kukanta bai damunsa segashi yau bayasan ji.
Hanky’n ta ninke tasa cikin jakarta sannan ta mik’e tare da rufo k’ofar ta dan ganin lokacin tashi yayi. Ta rufe k’ofar office nata ta juya kenan sega Anas shima yafito suna had’a ido tayi saurin kawar da kanta. Public elevator tabi a yayinda Anas ke binta da kallo so yake yace mata ta zo su shiga elevator’nsa amman kuma girman kansa bare bar sa ba, wai mesa ma yakesan su shiga elevator’n sa bayan abinda ta masa d’azu? Sanda ta b’ace sannan ya nufa nasa ya shiga shima, kafin ya sauk’o kuwa tuni Fannah ta k’ara mai. A d’an wani shago ta tsaya tare da yima family’nta d’an siyayyan kayan k’walama. Isarta gida keda wuya.
Mutane biyun data gani tsaye cikin gidansu ne suka mugun razana ta. Ido wuru wuru ta zaro tare da dafe k’irjinta tana me salati a zuci. “Baffah Khaleel?! Ya Farouq?!” Kai tasoma kad’awa danko bata yarda da abinda idanunta suke gane mata ba. Mami dasu Afrah dake tsaye gefe guda suma fuskarsu d’auke yake da damuwa.
“Mami dan Allah kice min basu bane, tell me idanu na wasa suke min.”
“Fannah manyan gari wato har gidan TV ake nuna ki, ‘yan matan nawa fa duk sun girma sosai tunba Fannah surikata ba.” Cewar Ya Khaleel yana wani murmushin mugunta.
“Kai Farouq baka ga matarka bane da baraka mata magana ba? Jeku gaisa mana.” Wani tantirin dariya ne a fuskar Farouq a yayinda ya soma takowa gaban Fannah. Baya tayi take ganin haka “Fannah mata ta ya haka kuma? Mijinki ne fa ni, bekamata kina min haka ba, matso mana mu gaisa.” Sosai Farouq ya sake girma yazama cikakken na miji yanzu kyansa ya sake fitowa, sede iskancin nan nasa daya saba har yanzu yana yi be bari ba.
“No don’t touch me.” Kamar kyaftawan ido Mami tashigo tsakaninsu, “Ya Khaleel meh amfanin haka dan Allah? Nasan kai da d’anka kunfi k’arfin mu dan Allah kuyi hak’uri ku koma inda kuka fito. Fannah bata san Farouq Ya Khaleel kayi wa Allah ka hak’ura da kai da d’anka dan Allah.”
“Maman Aiman kenan, in kinga mun koma Bama toh wallahi da Fannah ne. Wace karuwar ‘yarkun ma wacce ko martaba battada, dan ni da Farouq zamu rufa mata asiri zaku wani tsaya kuna mana tsiya yau shekarunta nawa takasa yin aure, ba d’a na mijin da ze amince ya auri Fannah inba Farouq ba.”
“Baffah Khaleel dan Allah kayi hak’uri ka rufa min asiri banasan sake komawa Bama, banasan Ya Farouq ni na rungumi k’addara zan gama rayuwata duka ba aure dan Allah kar ka aura min Ya Farouq.” Fannah ta fad’i hawaye na gangarowa kan kumatun ta abin tausayi. Tajima bataji tashin hankali kamar na yau ba. Ta riga da ta ajiye past nata a gefe mesa su Baffah Khaleel zasu dawo su hargitsa mata komai??
“In baki son shi to shi yana sanki sakariya kawai, aure tsakaninki dashi kuma farillah ne nan da ‘yan watanni, gomma tun wuri ku fara shiri, karatu ne Farouq yayi. Yanada diploma’nsa dakuma aiki me albashin da ze iya rik’eki. Kinga ko wannan karan ke zakiyi kayan d’akinki tunda kema kinada aiki. Abinda ya kawo mu dama kenan, bayan biki zaki bi mijinki Bama ku fara zama acan, in qaninan ya tashi ku gaishesa. Farouq mu tafi.”
“A’a Baba ni ba yanzu ba semun gaisa da matar tawa tukuna.”
“Karka damu akoi gobe ai, gobe zaka dawo har girki seta maka tunda matar kace, mu tafi.” Nan suka fice. Kuka me k’arfi Fannah ta rushe da. Mami na bata hak’uri haka Afrah da Aiman ma. “Mami ni shikenan Ya Farouq zan aura? Duk inda mukaje se sun tsakuro mu. Mami dan Allah do something wallahi banasan Ya Farouq mugu ne, azzalimi banasan sa Mami.” Ta k’ara shigewa jikin Mami tana kuka me tsuma zuciya.
“Yi shiru Habibti in shaa Allah baraki auri Farouq ba kamar yadda Allah ya k’wato ki kwanakin baya haka ma ze miki yanzu mu dage da addu’a kawai.”
“Ya Fannah kiyi hak’uri zamu tayaki da addu’a” cewar Afrah cike da tausayi. Kuka sosai Fannah takeyi haka yadda taga rana taga dare ta kasa bacci. A ranan kowa hankalinsa tashe yake basu san kuma ina zasu sake zuwa ba, basu san ko in sun bar Maiduguri akoi inda zasuje Fannah tasamu aiki me kyau kamar na nan ba. Baba ya tausaya wa ‘yarsa sosai ba kuma abinda yafi bak’anta masa rai kamar in ya tuna ba abinda ze iyayi ya cheto ‘yarsa daga halaka. Dan auren Farouq halaka ne yaron da besan darajar mace ba ko kad’an, d’an giya d’an iska.
Daga Fannah ta rufe ido seta soma mafarke mafarke ganin ba mahilicci se Allah ta tashi tayi alwala tariga nafilfilu har seda k’arfinta ya k’are sannan tayi zaman istighfaar. Da safe ta tashi tana shirin office sanyi sanyi kamar wacce k’wai ya fashe ma aciki duk Afrah na kallonta takasa koda ce mata uffan dan tausayi. Mami ce tashigo ta tarar da ita tana sa kaya bayan gaisuwa Mami ta tambayeta cike da tausayi “Fannah ba se kinje office ba yau ki huta”
“Mami gomma inje saboda zama anan ba abinda ze haifar min inbanda bak’in ciki jiya Baffah Khaleel yace Ya Farouq ze dawo yau, bana san ganinsa Mami na gwammaci naje office.”
“Toh shikenan Fannah Allah kare kicire damuwa daga ranki kinji? Muna nan muna kan miki addu’a.”
“Nogode Mami ni na tafi.” “Allah kare” both Mami da Afrah suka mata sannan ta fice.
8:01AM daidai ya mata a office na Mr. Fauzi kanta sauk’e a k’asa ta gaishesa, sama sama ya amsa. Jakarta ta bud’o tare da ciro hand kerchief daya bata jiya ta ajiye kan table nasa. “Gashi, nagode.” D’gawa yayi ya sake mik’a mata “na baki keep it.”
“But Sir-” katse ta yayi “I said keep it” yace a hankali. Amsa tayi tare da masa godiya ta mayar cikin jakar ta.
Har yanzu basu had’a ido ba dan kanta a sunkuye yake.
“Ina schedule d’ina na yau?” Ya tambayeta yana danne danne a laptop nasa.
“I’m sorry bansamu na had’a ba excuse me yanzu zanje in had’a maka.”
“Mesa? Me kikeyi tun jiya da baki had’a ba?” Ya tambayeta cike da tsiwa.
“I’m sorry” tace nan ma bata d’aga kai ba sede daga yadda take maganar Anas ya gano wani abu na daminta ya tambayeta meneh kuma girman kansa bare barsa ba. Kallonta ya tsaya yi kusan na minti biyu amman sam bata gwada yunk’urin d’ago kai ba bale ya kalli cikin idanunta ma. “Miss Aleeyu” ya kira sunanta a hankali.
“Yes Sir” ta amsa ba tare da ta d’ago kai ba. “Make me coffee” ya fad’i. A sanyaye ta juya ta nufa wajen machine d’in sede hankalinta ko kad’an baya jikinta tayi nisa tunanin abubuwan da suka faru jiya she actually can’t believe Baffah Khaleel da d’ansa Ya Farouq sun dawo suna san maida ita Bama da bata sake tsammani zata koma wataran ba.
Bayan ta gama had’a jagual-gualenta ta juyo dan ba coffee ba sunan abinda ta had’a. D’an k’usa ne ya kama mata hijabi agarin cirewa tayi b’arin coffeen duka ya zube a k’asa cup d’in kuma ya fashe. Kid’imewa tayi a lokaci guda batasan lokacin da ta tsuguna ba dan tattarawa. “Don’t Miss Aleeyu karki ki tab’a” Anas yayi warning nata da ihu chak ta maida hannunta. “I’m sorry” ta fad’i hawaye na cikowa a idanta. “I’m sorry please” ta sake basa hak’uri.
Toh kuma kukan meh? Ai be tab’a taba, bekuma mata masifa ba kodan d’an ihun dayayi dan kar ta tab’a glass d’inne ya sata kuka? Tasowa yayi daga mazauninsa ya nufo gabanta har yanzu tana tsugune “get up” yace mata. A hankali ta mik’e kanta sunkuye se hawaye takeyi side bag nata ya mik’a hannu yaja a hankali, batace masa komai ba, bud’ewa yayi ya ciro handkerchief daya batan “wipe off your tears” amsa tayi ta na gogewa sede the more tana gogewa the more kukan yake k’aruwa harda me sauti da k’yar ya zaunar da ita.
Besan me ba se kawai yaji ya damu da ita bayasan ganin ta tana kuka. “Miss Aleeyu mesa kike kuka na miki wani abu neh?” ya tambayeta a hankali. Kai ta kad’a masa da nufin a’a tana me cigaba da kukan.
“Toh mesa kike kuka? Sabida glass cup da kika fasa min ne? Don’t worry I have lots more.”
Kukan take har yanzu ba makawa hasali se k’ara volume na kukan nata ma take. “Miss Aleeyu what is it?” Kai kawai take kad’a masa chan ma ta tashi ta ruga office nata a aguje kan table nata ta baje sekuka take shark’af shark’af abin tausayi. Anas nason bin bayanta amman girman kai irin nasa bare barsa ba. “For goodness sake what is wrong with me? Mesa nake damuwa da Fannah? She is not my responsibilily so let her be, duk abinda ke damun ta ita taji wajen.” Mik’ewa yayi tare da zama kan kujerar sa yana me cigaba da abinda yakeyi. Sede inaa mind nasa gabad’aya yana wajen Fannah. What if har yanzu kuka take? Me aka mata ko daga gida ne aka b’ata mata rai? Wayarsa ya d’ago dan kiran Mami se in ya soma shiga se ya katse haka ya kasa kirarta dan tambayen meke damun Fannah. Meeting dayake dashi ma yau shi kad’an sa yaje saboda yasan there will be no point yaje da Fannah tunda haka ta taho yau tana kuka. Shi kad’ansa yaje though shima duk hankalin sa na kan Fannah bayan da meeting d’in ya k’are as usual driver ya wuce dashi hotel dan cin abinci.
Ga abincinsa a gabansa amman yakasa chi, dududu sau nawa suka chi abinci da Fannah amman yaji yau inba ita bare iya chi ba kuma bawai fa baya jin yunwa bane kawai seda ita ze iya chin abincin. Kacallah ya kira kan ya sanar da Fannah driver ze zo d’aukanta yanzu dan bayasan ya kirata da kansa ta raina sa, hakan kuwa akayi bayan 20minutes aka kawo Fannah hotel d’in tana shiga tagansa zaune dan bata masan nan za’a kawo ta ba ce mata kawai akayi Boss na nemanta. Idanunta sun kumbura sunyi ja dan kukan datasha a hankali ta k’arisa gaban table nasa ta tsaya ba tare da tace uffan ba.
“Sit” yace mata hakan ko tayi bada jimawa yasa aka kawo mata abinci sak irin na jiya. Nan ma “eat” yace mata.
“I’m not hungry” ta masa k’arya dan kuwa ko breakfast batayi ba yunwa takeji amman batada appetite na cin abincin saboda damuwar dake kanta kad’ai ya isheta. Spoon biyar yakai yaga ko yunk’urin tab’a abincin ta batayi ba.
“Miss Aleeyu bakiya so ne akawo miki wani daban?”
Kai ta kad’a masa. “Then why are you not eating?”
“Sir I’m sorry bana jin yun-” bata k’are maganar ba cikinta yayi wani irin kuka.
“Yes kinajin yunwa eat.” Nanma kai ta kad’a masa. “Kichi kokuma in baki 500 papers kiyi correcting nasu” ya gwada taorata ko dan haka zata chi. “Okay I’ll do it in muka isa office d’in.” Mamaki sosai amsarta ya basa itan da kullum take had’asa da Allah in ya bata aikin yau ita ke fad’in zatayi kai tsaye? Toh meke damun ta?
“Miss Aleeyu meke faruwa? Meke damunki? Tell me.” Ya tambayeta cikin sanyin murya dan duk yashiga cikin damuwa ganin Fannah a damuwa.”
“Babu Sir thanks for your concern, zan jiraka a waje in ka gama se mutafi in fara correcting papers d’in da wuri saboda in gama on time.”
“Barakiyi correcting komi ba, I don’t mean it kawai kichi abincinki kinji? You are sick har yanzu zama da yunwa won’t help, eat.” A hankali ta d’aga spoon nata ta soma ci sede ba hab-hab kamar yadda ta saba ba. Anas ko da jimawa yagama cin nasa yayi zaman jiranta saba’anin yadda ya saba. Dududu quarter kawai taci tace ta k’oshi. “Are you sure?” Ya tambayeta kai ta gaid’a masa. Bayan ya biya kud’in suka fice.
Shigarsu mota Anas yace da driver “ba office zamu wuce ba gidansu Miss Aleeyu zaka kaimu.” Cike da mamaki ta d’ago kai se yanzu suka had’a ido dashi tun had’uwansu yau. “Gidan mu kuma Sir? Mesa?”
“Saboda inji meke damunki.” Yabata takaicaccen amsa.
“No Sir please don’t ba abinda ke damuna kawai fad’a mukayi da Afrah” tanasa k’arya
“Ban yarda ba” ya bata amsa yana duban agogon sa.
“Sir I’m serious.” Ita tsoronta kar in sunje su had’u da Baffah Khaleel kamar yadda ya saba kiranta da karuwa ko karya ya kirata gaban Anas. “Sir please mu juya na bar wayana a office I need to get it.” ta masa k’arya ko ze canza mind nasa.
Resting kansa yayi jikin kujerar “karki damu zansa Ahmad ya kawo miki.”
“Sir-” hannu ya aza kan lips nasa “shhh! Banasan surutu dayawa.” Ahaka har suka iso gaban gidansu Fannah zuciyarta se bugun d’ari d’ari yake. Driver na parking Fannah ta fito da sauri dan duba ko su Baffah Khaleel suna gida takai da shiga k’ofar gidansu kenan kawai suka ci karo da Ya Farouq kafin tayi wani k’wak’waran motsi ya cafko ta da hannu daidai lokacin Anas yake fitowa daga motan shima, idanunsa basu tsaya ko ina ba se kan hannun Farouq rik’e dana Fannah se k’ok’arin k’wata take amman ta kasa. Wani erin mahaukacin kishi yaji ya bugesa inba wai kashe koma waye mutumin yayi ba yana ganin bare samu sukuni ba.
A fusace ya k’ariso wajen. “Matata me haka dan na kama miki hannu? Ke wai bakiyi missing d’ina bane? Ko d’an shafaki bara ki bari inyi ba?” Cewar Farouq dawani shu’umin murmushi fal a fuskarsa.
“Ya Farouq ka sake min hannu niba matar ka bace let me go” ta fad’i tana hawaye tare da k’ok’arin k’wace hannunta.
“Ka sake mata hannu!” Anas ya fad’a cike da isa. Fannah da Farouq tare suka juya suna kallon Anas. “Waye kuma wannan baturen?” Farouq ya tambaya.
“Mr. Fauzi please ka tafi, don’t involve yourself in here.”
“Kinsan sa kenan” Farouq ya sake tambaya. “Bade shima saurayin ki bane kina kwana dashi, kinsan sana’a sa’a.” Anas be san lokacin daya kai wa Farouq naushi a fuska ba da zobobin azurfa a hannunsa. Take hancin Farouq ya fashe gefen bakinsa yasoma na d’igan jini.
© miemiebee
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 42
BY MIEMIEBEE
Baki Fannah ta bud’e tare da aza hannunta bibbiyu kai cike da mamaki da tsoro duka. Hannu Farouq yasa tare da tab’a inda yaji moisture a fuskarsa yana dubawa yaga jini ta hanci da bakin sa, “Kai! Ni ka fasawa baki? Dama nasha jin cewa ku turawa bakuda tarbiyya yau zan koya maka.” Hannu ya d’aga da k’arfin da Allah ya bashi shima ze kai wa Mr. Fauzi punch ai karap Anas ya kama hannun nasa tare da murd’awa cike mugunta ta bayansa. K’ara sosai Farouq ya saki dan azaba.
Fannah duk ta rikice “Mr. Fauzi please ka sake sa ya isa please” ko saurarenta Anas beyi ba k’ara murd’a hannun nasa yayi a bayansa k’ara sosai Farouq ya sake saki dan azaba. “Repeat what you just said.” Anas yace dashi, daga yadda yake magana ma kad’ai za’a san ransa a b’ace yake, na bala’i ma kuwa. Duk zafin da Farouq ya keji be hanasa misbehaving ba. “K’arya nayi dan nace kuna kwana tare karuwarka ce”
“You really want to die” Anas ya sake shi, kafin Farouq ya sake wani k’wararren motsi Anas ya sake kai masa punch a fuska fiye da yadda yayi d’azu sosai jini yake fita daga baki dakuma hancin Farouq.
“Mr. Fauzi please ya isa dan Allah” Fannah ta fad’i duk a kid’ime idanta tuni suka cike da hawaye.
“Kai ko kasan waye ni? Mijinta ne fa ni, aurenta zanyi banza da kai zakazo kana intruding. In ita karuwan kan bata fad’a maka yanzu ai kaji I’m her husband. Ke Fannah dan iskanci ya miki yawa kin kusa aure ma baraki fad’awa ‘yan iskan samarukan kin su hak’ura bako?” Hannu ya mik’a ze jata dan wanke ta da mari. Kamar a kyaftawan ido Anas yajata bayansa kamar ‘yar baby tare da rik’e hannun Farouq, rik’o kawai ya masa amman idan Farouq sanda ya cike da hawaye. D’ayan hannunsa ya d’aga ze sake kaiwa Farouq mumunar punch Fannah ta rik’e hannunsa da nata bibbiyu. Hawaye take sosai “Mr. Fauzi please ya isa kayi hak’uri ya isa please.”
Hawayen da takeyi ne kawai ya hana Anas kaiwa Farouq punch da ze iya kwantar dashi a asibiti. Kwalan rigar Farouq ya chukumo. “In bakada manners na magana wa kamilallaiyar mace I will teach you some, the next time ka sake kwatanta Fannah da wad’annan munanan suna I assure you zakayi kwanan cell, pathetic fool kawai, idiotic bastard.” Sannan yayi wulli dashi har k’asa Farouq yayi landing, daidai lokacin Ya Khaleel ya yanko kwanan gidansu Fannah shi a dole yazo cin abincin ranan da surikarsa ta dafa masa kamar yadda yace jiya.
Ai ganin his only son a k’asa ga kuma jini ko ta ina fuskarsa ya falfala da gudu yayi kan Farouq. “Farouq meya same ka? Wani d’an shegiyan ya maka wannan tsiyan, waye shi?”
“Baba kafin ka kira wani da d’an shegiya make sure ka cire sunan d’anka daga number a list d’in. Nayi warning nasa but I think I have to warn you too, the next time ya sake shiga harkan Fannah bare kwana a garin Maiduguri qalau ba.”
“Tohh sannu fa, sannu shugaban k’asan Nigeria. Toh kaine d’an shegiyan ba d’ana ba, kai har kanada da right da zaka hana Farouq shiga harkan Fannah ne? Ka tab’a jin inda aka shiga tsakanin mace da miji?”
Fannah dake tsaye bayan Anas tace, “Baffah Khaleel Ya Farouq ba miji na bane.”
“Ke karuwa rufa min baki.”
Ran Anas in yayi dubu be b’aci ba, taku yayi yunk’urin yi zuwa gaban Ya Khaleel dan kai masa had’add’en punch shima, “how dare you call Fannah karuwa!” yace a yayinda Fannah ta rik’e rigansa dan hanasa aiwatar da abinda yayi niyyar yi. “Mr. Fauzi let them be please, ya isa ka tafi wannan problem d’ina na ne bansan na jaka ciki, please go.” Wayarsa ya ciro a fusace bayan an d’aga yace, “Hello send me 10 men, I mean 10 a unguwar Polo…” Nan ya masa kwatance. Baki na b’ari police d’in yace, “yy.yyyes Sir right away!”
Aiko cikakken minti biyar da gama wayan Anas beyi ba sega motan polisawa guda biyu. Farouq harda rud’ewan ciki Ya Khaleel kuwa sanda ya saki fitsari a wando shi be d’au dagaske baturen yake ze kira polisawa ba, toh waye shi.
“Take them both, kuje ku rufesu right away” ya fad’a a fusace.
Farouq da baki ke jini yace, “wallahi kayi k’arya me mukayi da zakace aje a rufe mu?” Can k’asa k’asa Ya Khaleel yace, “kai kayi shiru se yanzu nagane waye wannan mutumin, ba bature bane shine wanda aka nunasa da Fannah ranan a BRTV wallahi babban mutum ne mu basa hak’uri in bahaka ba in aka rufemu me bailing namu se Allah.”
“Mr. Fauzi ko? Dan Allah kayi hak’uri, wallahi misunderstanding aka samu anan my apologies please karka sa a rufe mu dan Allah. Farouq baraka basa hak’uri bane?”
“Officer take them away banasan jin komai.”
Nanne bakin Fannah ya bud’u. “Mr Fauzi please kayi hak’uri karka rufesu dukda cewar basuda kirki ‘yan uwana na ne, Ya Khaleel Baffah na ne Ya Farouq kuma cousin d’ina kayi hak’uri and set them free please.”
“Miss Aleeyu why? Bakiji munanan sunan da suke kiranki dashi bane?”
“Naji Sir just please set them free, please.” Ta fad’a idanta na cikowa da hawaye.
“Officer let them be zaku iya tafiya sorry for the disturbance.”
“Ba komai Mr. Fauzi muna da godiya”
“Zuwa anjima zakuji alert thanks.”
“Mungode sir, mungode sir” a haka suka ja motocinsu suka fice.
“Miss Aleeyu kinasan in samusu retricting order from the law yadda barasu sake zuwa kusa dake ba? So they won’t disturb you in na bar nan?”
“Sir thank you but karka damu in shaa Allah ba abinda zasu iya min you can go kadena b’ata lokacinka akaina please, thank you”
“Call me in wad’annan foolish mutanen suka sake miki wani abu” ya k’are maganan yana ma Ya Khaleel da Farouq kallon banzaye cikin banzaye. Farouq zeyi magana Ya Khaleel ya taka masa k’afa dan haka yayi shiru.
“Ki shiga ciki.”,Ba musu bale gardama ta shige ciki sanda ya tabbata ta shiga ya dawo da kallonsa kan like father like son yana nuna su da yatsa “kun ji na rantse in kukayi ma Fannah wani abu zaku k’are rayuwanku a jail, assholes.” Yana kaiwa nan yashige motarsa driver ya rufe yajasa suka fice.
Se yanzu bakin Farouq ya bud’u. “Shege se meh? Wallahi kasani ka tab’o tsuliyar dodo, zancen kakeso.”
“Kai Farouq ya isa saurayin nan babban mutum ne a garin nan ka rufa mana asiri muyi abinda ya kawo mu mukoma da Fannah Bama cikin kwanciyan hankali.” cewar Ya Khaleel.
“Wallahi Baba be isa ba ya zubar min da jini ya kwana lafiya Allah kaimu gobe. A ina yake aiki kace?”
“Wai meka isa kayi masa ne dawani fashasshen bakin ka da hancin ka, se uban kurin baki wai kana zuwa gym ji yadda kabari wancan Fauziya ne ko Fauzi ya maka tatas. Kona fad’a maka inda yake aiki me ka isa ka masa?†
“Niko nasan me zan masa just tell me ina yake aiki?”
“A Flames Enterprises shine CEO’n wajen naga sun sa a TV”
“Good” Farouq yace tare da ficewa. Babansa na kiransa ko a kwalan rigarsa, Ya Khaleel kuwa shegen tsoro ne dashi sekace farar kura. So yake ya shiga cikin gidansu Fannah amman kuma yana tsoron abinda Mr. Fauzi ya fad’a masa. Dan haka ya nufa masauk’insu kawai.
Anas kuwa isar sa gida ya wuce d’akinsa tare da sa lock ba tare da yace da kowa komi ba. Wani irin tausayin Fannah yaji ya kama sa, ba abinda yakeso yanzu kamar yayi protecting Fannah daga wannan shegun Baffan nata da d’ansa. Mesa zasu na kiranta da karuwa? Mesa zasu na kiran yarinya me tarbiyya kamar Fannah da karuwa? To kode ta tab’a yin hakan ne da a baya se Allah yamata shiriya? “No!” ya fad’a a fili no matter what Fannah batayi kalan wanda zata iya aikata abinda uncle nata yake fad’a ba. Ai inhar dagaske karuwan ce da bare so ya aura wa d’ansa ba k’azafi kawai suke mata, ayyah ashe shiyasa taketa kuka a office yau, shiyasa ko abinci ta kasa ci. “I will protect you Fannah no matter what.” Ya fad’a a fili.
*****
9:23PM
Fannah da family’nta ne zaune d’akin Baba yanzu tagama basu labarin abinda ya faru d’azu, abinda Mr. Fauzi yama su Ya Khaleel. Kowa wajen yasha mamaki matuk’a.
“Alhamdulillah! Alhamdulillah! Allah sak’a wa Anas da alhkairi, abinda yama Ya Khaleel daidai ne Allah saka masa da alkhai” “Ameen” kowa ya amsa wajen.
“Habibiti amman har duka Anas yama Farouq?” Mami ta tambaya cike da mamaki.
“Eh Mami, Mami tsoro nakeji wallahi Ya Farouq ze iya cewa ze rama dukan akaina.” Rungumota Mami tayi gam ajikinta tana shafa jelar gashinta da d’ankwalinta be samu ya rufe ba. “In shaa Allah ba abinda ze miki kina da Allah bayan haka kuma ga Anas na tabbata bare bari wannan shegen Farouq d’in ya miki wani abu ba.”
***
10:30PM
“Wai ina wannan hegen yaron yajene?” Cewar Ya Khaleel da kansa for the 100th time yana duban k’ofar one room apartment da suka d’an kama da d’ansa. Chan ya hango shadow’n mutum, torchin hannun sa ya haska, ganin Farouq ke tahowa ya saki hamdala tare da nufan wajensa. “Kai Farouq ina kashiga tun d’azu? Kasan na rasa mahaifiyarka barin iya juran rasaka ba kaima. Kuma dan rashin hankali haka kata yawo a gari da fashasshen baki da hanci?” K’eyarsa ya tand’e “wuce ciki mu goge maka.”
5 minutes later…
Farouq ne mik’e kan ‘yar katifarsu a yayinda Ya Khaleel ke treating masa ciwon da Anas yaji masa a fuska da dettol. “Ina kaje ina tambayarka tun d’azu kamin shiru.”
“Kai de Baba Allah kaimu gobe se Mr. Fauzi ne ko Fauziyan nan ya raina wa kansa nan gaba ko kafad’an juna muka buga bare min koda kallon banza ba.”
“Wai me kake nufi Farouq? Kaga fa ka rufa mana asiri ni na fad’a maka kokuma in anzo tafiya damu in ce mai kai kad’ai ne banda ni, am warning you.” Lebb’an sa yacize irin mazan nan mana aikuwa yacize wajen ciwon.
★★★
Washegari…
K’arfe 8:10AM ya ma Fannah a office na Mr. Fauzi tun 8:00AM yake jiranta a zatonsa ma ko barata samu zuwa ba se kawai ya ganta, har cikin ransa yaji sanyi sede yau ma fuskarta ba walwala kamar jiya. As usual ta k’ariso gaban table nasa ta gaishe sa kanta a sunkuye. “Good morning Mr. Fauzi.”
“How are you feeling?” ya tanbayeta a hankali.
“Alhamdulillah, thank you for yestarday.”
“Ba komai” yace mata.
“Sir bansamu nayi making schedule naka jiya ba am sorry.”
“Is okay” yace mata ba tare da ya nuna damuwa ba. “Mesa baki fad’a min ba?” Ya tambayeta. A hankali ta d’ago kanta idanunsu na had’uwa ta sake sunkuyar da kanta, “I’m sorry” tace sincerely.
“Baki amsa min tambaya na ba, mesa baki fad’a min abinda wad’ancan biyun suke miki ba. Saisa kikazo jiya kika ta kuka kenan koh? Akansu ne?” Kai ta giad’a a hankali.
“Mesa baki sanar dani ba?”
“Sir I thought there will be no point in fad’a maka sesa kawai nayi shiru.”
“Next time call me up and tell me kinji?” Kai ta giad’a tare da godiya.
“Sun sake miki wani abu?”
“A’a.”
“Dagaske ne zaki auri wancan Farouq d’in?” Ya tambayeta kamar me jin kishin ta. Kai ta giad’a a hankali.
“Mesa? Kina son shi ne?” Nanma kai ta giad’a.
“Miss Aleeyu” ya kira sunanta “na’am” ta amsa kan ta a sunkuye. “Look at me.” A hankali ta d’ago kanta tana kallonsa kamar yadda shima yake kallon nata. Ba komi ne tattare da idanunta ba inbanda tsoro. “Do you really love him?” Ya sake tambayar ta cikin sanyin murya.
Hawaye tajiyo na ciko mata, “no Mr. Fauzi banasan sa, ban tab’a san sa ba, mugu ne, azzalimin da besan daraja ta ba.”
“Shhh is okay kar kiyi kuka, bakiya sansa baraki aure sa ba kinji?” Har hawayen nata sun soma sauk’owa ya ciro hanky ya mik’a mata amsa tayi ta share hawayen. “Sir how? Baffah Khaleel is powerful ni nasan dole zan auri Ya Farouq.”
“No baraki aure sa ba I promise, jeki huta Kacallah ze kula da aiki ki yau.”
“Sir don’t worry zan iya yin aik-” bata k’are maganar ba ya katse ta “banasan musu idanunki sun riga sun nuna baki samu bacci ba jiya so just go before I change my mind.” A hankali ta juya sanda takai bakin k’ofa sannan ta juyo tana kallonsa taga yana tattara files na gabansa “Mr. Fauzi” ta kira sunansa chak ya bar abinda yakeyi tare da d’ago blue eyes nasa yana kallonta. “Yes?” Ya bata amsa.
“Thank you” tace dashi. D’an murmushi ya saki wanda ya sake bayyano da kyan sa. Giad’a mata kai yayi as an answer sannan ya cigaba da abinda yake a yayinda tafice zuwa office nata ita kuwa.
Batasan me ba amman kwana biyun nan in _TANA TARE DA_ Mr. Fauzi setaji she is safe kuma setaji ta ba damuwa. Kan cushion nata ta baje a hankali bacci me uban nauyin gaske ya isketa wanda takasa yi jiya da daddare dan yadda damuwa suka mata yawa.
30 minutes later…
A nitse kuma a hankali Anas ya bud’e office na Fannah. Taku d’ai d’ai yake a hankali har yashigo cikin office d’in zube ya sameta kan 3 seater tana bacci peacefully. Har gabanta ya tako tare da tsugunawa d’an hijabin daya tare mata fuska yasa hannu ya gyara dogayen eyelashes nata yatsaya yana kallo sannan yakoma kan girarta dayake nan kamar na Kajol na india yadda ya had’e me kyan bala’i. Sekuma d’an siririn hancinta dayake nan madaidaici dakuma d’an bakinta dakenan ba k’aramin chanba bakuma babba ba tsakatsakiya.
Besan dalili ba amman kawai ya tsinci kansa cikin jin dad’i, killer murmushi ne kwance kan kyakkyawar fuskarsa wanda ya lotsar da dimple nasa na gefe d’aya. Jakanta dake saqale a kafad’arta ya zira hannu ya cire a hankali yadda bare tada ita ba, tare da ajiye wa a gefe guda, k’afafunta ya daidaita kan kujerar tare da kunna AC’n a medium ta yadda beyi yawa ba bekuma yi kad’an ba. Ficewa yayi zuwa d’akinsa ya d’au wani arabian bargonsa me uban laushi da pillow yazo ya rufeta dashi tare da aza kanta kan pillow’n ya juya ze fita kenan Fannah ta kama bakin suit nasa ta baya chak ya tsaya tare da juyowa hannun nata ya raba da kayansa a hankali sannan ya rufo mata k’ofar ya fice zuwa office nasa. Yau yagama had’a model nasa sauran asalin gini yanzu. Already filinsa na nan kawai abinda yarage shine asa drawing d’in into action.
© miemiebee
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 43
BY MIEMIEBEE
Bacci meh rai da lafiya Fannah tayi wanda ta jima ma batayi ba se chan bayan azahar ta tashi. A hankali ta bud’e idanunta jin kanta tayi kan pillow cike da mamaki ta duba harda bargon ma, toh waya shigo ya rufeta? Waya kunna mata AC? Ko kad’an bata kawo Mr. Fauzi arai ba saboda tasan halinsa, toh kode Yusuf ne? Toilet ta nufa ta wanke fuskarta tare da brushing sannan tafito ta ninke bargon tsab ta had’a da pillown sannan ta d’aga tafito dashi a hannunta floor na office nasu Yusuf ta nufa akan table nasa ta tsincesa bayan sun gaisa tace, “gashi nagode, shine akan ka tada ni narufe kaina kayi min wahala haka?”
Cike da mamaki Yusuf ke kallon Fannah totally speechless. “Nikuma?” ya fad’a a k’arshe. “Ina zan samu bargo da pillow a office Fannah? Kode har yanzu baccin naki be wassake bane?”
“Yusuf banasan wasa please amshi kayan ka, inkuma so kake kabarmin seka fito fili kace Fannah na baki.”
Murmushi me sauti ya saki. “Fannah wallahi am serious ni banma san wai kina bacci ba kide zagaya ki tambaya waya sani ko Boss ne dakanshi nema ya rufe ki.”
“Dariya kakeson bani komeh? Boss ya rufeni ina bacci? Impossible barinje in tambayi Ahmad da Kacallah.”
“Zaki b’ata lokacin ki ne saboda Boss ya aikesu tun d’azu.” Yi tayi kamar bata jisa ba what if abinda Yusuf ke fad’i gaskia ne? ahaka har tashiga elevator ta hauro sama tana tsaye bakin k’ofar office na Anas amman takasa shiga inkuma ba nashi bane fah? Yace tacika shisshigi da k’yar de tasamu tayi knocking a hankali.
Daidai Anas ya d’au bottle na beer nasa ze sha kenan knock yashigo. Haka kawai yau yaji yana san yad’an bugu saboda ya kwana biyu be sha ba tunda Fannah na bacci bare d’an sha abinsa kuma ba ma haka ba so yake yabar tunanin Fannah, ba abinda ya tsinana wa kansa yau, wai mesa ma yaje ya rufeta d’azu da take bacci? Tausayi ne ya fad’a a fili. I don’t love Fannah I just pity her yayi reminding kansa. “Who is it?” Ya tambaya.
Chan murya k’asa k’asa a hankali tace, “Fannah ce.” Da sauri ya rufe bottle d’in tare da jawo drawer’n gefensa ya rufe. Turare ya feffesa cikin office d’in dan kashe warin giyan tare da kimtsawa sannan yace, “come in.” Tana shiga yaganta da pillow da bargon, kallonta yake har sanda ta k’ariso gaban table nasa. Shiru tayi tana nazarin taya zata fara masa maganan, shima shirun yayi tare da had’a hannayensa biyu k’ark’ashin hab’ansa yana kallonta kamar hoto. Can ta fara kamar haka;
“Ermm Mr. Fauzi ban sani ba ko wannan naka ne, na tambaya su Yusuf duk sunce ba nasu bane.”
Kallonta har yanzu yake da wani murmushin tsiya karara a fuskarsa. “Wato dan kin maidani dustbin shine zaki kawo min?”
Kai ta d’ago tana kallonsa “No Sir ba abin da nake nufi ba kenan-” katseta yayi
“Shine mana, kin tambayi saurayinki Yusuf yace ba nashi bane shine kikace bari ki kawo wa dustbin shikam ze karb’a koba haka ba?”
“No Sir thats not what I mean, in ajiye maka a ina?”
“Ba nawa bane” ya bata takaicaccen amsa. Kanta ne ya d’aure. Kamar ya ba nasa ba? Toh na waye? Ita se yanzu ma ta tuna ranan da Mr. Fauzi ya rufeta a d’akinsa ai taga bargon nan akan gadonsa, to mesa zece ba nasa bane?
“Sir but ranan naga bargon nan a d’akinka.”
“Aww mak’aryaci kikeson ki kira ni dashi kenan, ince miki ba nawa bane kice nawa ne”
“No Sir ba abinda nake nufi ba kenan.”
“Inma tunani kike wai da kike bacci ni naje na rufe ki toh you are mistaking dan ni ko shiga office naki banyi ba.”
“I’m sorry” tace cike da kunya ita de tasan ranan tabbas taga wannan bargo a d’akin Mr. Fauzi kuma gashi yace ba nashi bane. “Jeki ajiye kidawo am waiting for you.” Bayan minti d’aya Fannah ta dawo “yes Sir.” So yake ya ce mata suje suci abinci amman girman kai ya hanasa. Seya bud’e baki ze fad’a se yayi shiru.
Ganin baida niyyan magana Fannah tace, “Sir you called me.”
“Ina sane ai” yabata amsa. “Ko ban tambaya bama nasan kinajin yunwa lets go and eat.” ya fad’a in an I dont care tune.
Qarya tayi niyyan masa tace tana azumi seta tuna yasan batada tsarki. “Sir I’m not hungry thanks.”
“Toh ni inaji lets go” zata sake magana yace, “banasan musu” bayan sa ta nufa bayan ya rufo k’ofar office nasa Fannah ta juya zata nufa public elevator, hijabinta ya rik’o. A tsorace ta juyo tana kallon had’add’un yatunsa daya k’ayata su da zobunan azurfa masu tsada rik’e da hijabinta sannan back to fuskarsa. Beso suka had’a ido ba “mu shiga nawa” yace mata. Kai ta giad’a masa a sanyaye tabi bayansa suka shiga private elevator’nsa ba wanda yace ko uffan ahaka har suka sauk’a driver yayi driving nasu zuwa wani hotel na daban ma yau. Abinci me rai da lafiya Anas ya mata ordering. “Eat” yace mata alokacin daya d’aga spoon nasa, ba musu ba gardama itama ta d’au spoon suka soma ci.
Ko da yagama cin nasa zaman jirarta yayi data gama ya tambayeta, “a k’ara miki?” Kai ta kad’a masa bayan ya biya suka koma office d’an errands kad’an Fannah tayi wa Mr. Fauzi, lokacin tashinsu nayi ta wuce gidah.
Shima Anas yana gama abinda yakeyi ya kama hanyan gida, tuk’i yake hankalinsa kwance ya d’ibo bottle na giyansa biyu yau a paint house nasa ze kwana, unguwar shiru yake ba mutane sosai yana cikin tuk’i yaga mota ya fito from nowhere yayi blocking nasa, ikon Allah ya tsaya gani reverse ya gwadayi a take yaga bayan san ma anyi blocking. Toh su waye ne? Kafin yanemi amsa wa tambayan daya ma kansa yaga maza uku sun fito daga motar gaban nasa da angansu anga ‘yan maye ‘yan bayan gari. Murmushi kad’an ya saki dan in ‘yan su uku ne acikin minti biyar ze gama dasu. Kafin ya yi yunk’urin yin wani abu yaji ana knocking jikin window’nsa. Window’n yayi wining “munada problem neh?” Ya tambaye gayen.
“Dade ka fito tukuna.” cewar gayen. Ba gardama ya fito ya tsaya nanne yaga duka duka mazan guda biyar ne. “Will you guys let me pass or senayi muku abinda bakuwa so?” Familiar murya ya jiyo daga behind nasa yana cewa;
“Kokuma mu mu maka abinda baka so ba Mr. Fauzi” yana kai dubansa gun da ya jiyo muryan idanunsa suka sauk’a kan Farouq yawani pake kan driver’s sit cike da isa ya taso tare da takowa gunsu Anas.
“You’ve had your time the other day now is mine.”
Wani erin dariyan rainin hankali Anas ya saki harda tafi “you are such a genius Farouq. Wai ka d’au dakai da wannan mashirmatan daka taran zaku iya min wani abu ne?”
Dariyan bosawa Farouq ya saki “Mr. Fauzi kenan kasani sarkin yawa yafi sarkin k’arfi. Apologise to me, tell me sorry akan abinda kamin jiya and I will let you a save passage.”
“Ni in ce maka sorry?” Yayi murmushi “never!”
“ATTACK!!!” Farouq ya fad’i nan maza biyar d’in suka soma nufuwa wajen Anas. Sleeves nasa yayi rolling tare da ciro Rolex agogonsa kafin ace me suka b’arke cikin mumunar fad’an BIYAR akan D’AYA. Farouq na tsaye a gefe yana kallon yadda Anas yake destroying masa mutane, duk se kamar yafi k’arfinsu dukda suma suna k’ok’ari dan har sun fasa masa baki amman yafi cin uwarsu. Tsawa Farouq ya daka musu “wai zakuce shi kad’ai yafi ku duka k’arfi ne?”
Ai se kamar maganar Farouq k’arfi ya k’ara musu. Sunayi Anas yanayi har suka samu sukaci galaba akansa hanci, baki ba wanda basu fasa masa ba. Hannayensa suka kama ta kowani gefe a lokacinda Farouq ya taso daga inda yake. “Ohhh look at you Mr. Fauzi abin tausayi, ina k’arfin naka yaje? Ina polisawan naka? Kud’in ka ya ceto ka mana.” Fuskar Mr. Fauzi dayake yoyon jini Farouq ya d’ago “tell me meh had’inka da mata ta Fannah?”
Murmushi Anas yayi dukda azaban dayake ji. “Kaikuma tell me meh had’inka da alak’a na da ita? Mind your damn business.”
“Bakinka be ruhu ba kenan har yanzu. Rik’e min shi dakyau” yace da mazan nasa. Gagam suka sake damk’e Mr. Fauzi punch me rai da lafiya Farouq ya kai masa wanda seda idanun Anas suka juya. “Nace meh alak’arka da matata?”
“Fannah is not your wife” ya fad’a a wahalince. “Take note”
“Har yanzu baka bugu ba.” Naushi yakai ma Anas a ciki wanda sakamakon hakan ya saki k’ara sosai dan azaba.
“For the last time me had’inka da Fannah?”
“Kanason kaji me had’ina da Fannah? FANNAH IS MY GIRL, I LOVE HER.”
Cike da b’acin rai Farouq ya cukumo kolar rigan Anas “me kace? Sake nanata abinda ka fad’a inji”
“I LOVE FANNAH, KUMA NI ZAN AURETA BA KAI BA, FANNAH TAWA CE!!!”
“You really want to die.” Naushi lafiyayyu guda uku ya kai wa Anas aciki biyu kuma a fuska. Kaca-kaca suka ma Anas, duk wanda ya kallesa bare so sake sa idanunsa kansa ba duk jikinsa jini.
“Me alak’ar ka da Fannah? Kace min baka son ta kuma baka santa ba.”
Da k’yar yake maganan “NEVER!! I LOVE FANNAH, ko kasheni zakayi bare canza komai ba.”
A fusace Farouq yace, “Baaba” na gefen daman Anas “je cikin trunk na motan can kaciro min sandan chan nakega inba dukan mutuwa na masa ba bare shiga hankalinsa ba. Zakace baka son Fannah ko yaya?” Shiru Anas yamasa bece komai ba se nishin wahalan dayake yi abin tausayi.
“Farouq ga ‘yan patrol zuwa fa!” Baaba yayi exclaiming da ihun gaske ai kamar kyaftawan ido su Farouq suka lodu a mota suka bar wajen a 360. Anas na kwance helplessly a k’asa. Bayan motan patrol d’in ya k’ariso polisawan suka diddiro ganin mutum a k’asa, plate number’n motar Anas d’ayan ya karanta yaga “Mr. Fauzi.”
“Guys Mr. Fauzi ne!” da gudu sukayi kansa suka d’ago sa zuwa motar sa tare da miqar dashi a back seat. “Abba lets go, mu kaisa asibiti push the start button.” d’ayan officer’n ya fad’i. A wahalince Anas yace, “no karku kaini asibiti just drive me home, to my paint house.”
“Sir but you are badly injured.”
“I know, ku kaini paint house d’ina kawai.”
“Okay sir ina ne paint house d’in?” Nan Anas ya musu kwatance murya yana d’aukewa. “Sir su wa suka maka haka?” Har ya bud’e baki ze kira sunan Farouq seya tuna in ya fad’a musu definately zasu kama Farouq su rufe sa kuma, in hakan ya faru kuwa Fannah barata ji dad’i ba. “Nima bansan suba” yama officers d’in k’arya “ ‘yan iskan unguwa ne kawai.”
Daidai gaban paint house nasa suka iso. “You can go now zan k’arasa da kaina nagode.” Cewar Anas idanunsa suna kafewa.
“Sir amman kace barakaje asibiti ba? Wannan mutane sunji maka ciwo fah.”
“Don’t worry I can take care of myself.” Bottles na giyansa guda biyu yaciro da k’yar yake iya tafiya dan kalan dukan dayasha wajen Farouq da mutanensa, ahaka har ya samu ya isa ciki ko k’ofan ma yakasa locking. Bayi ya nufa da rarrafe da taimakon sink ya mik’e ya kalli fuskarsa a madubi. Sam beso sake kalla ba dan irin ciwon da suka ji masa. Ruwa ya gwada wanke fuskar nasa dashi. Aiko ruwan na tab’a fuskar ya saki k’ara dan azaba daga k’arshe hak’ura yayi yakoma d’aki tare da rage kayan jikinsa yabar short nicker kawai. Kwalba d’aya ya kwankwad’e tas dan samun bacci, yana shanye wa kuwa bugeggen bacci ya d’ibesa ko sallan maghrib beyi ba bale na isha. Wayoyinsa dake cikin mota kuwa se kiransa su Ummie suke ba iyaka amman bai d’aukawa hankalin kowa ya tashi, ko da sukaje office nasa suka tambaya kuwa, kowa ya shaida Mr. Fauzi yabar building d’in lafiya.
***
Washegari…
8:10AM yama Fannah a office sede tata knocking a bakin k’ofar office nasa amman shiru chan ta gwada bud’ewa taji a rufe alaman Mr. Fauzi bezo bama kenan! To meya rik’esa? Shida ko lattin minti d’aya baya yi. Meya faru? Mesa bezo ba? Ko baida lafiya ne? Minti 15 ta k’ara tana jiransa amman ba alamansa. Gashi yanada board meeting by 10:30AM. Ganin ba mahalicci se Allah kawai ta sauk’a k’asa ta samu Kacallah tare da tambayansa ko sunyi waya da Mr. Fauzi.
“A’a wallahi nima Fannah na kirasa ta duka layinsa baya d’agawa tun jiya na rasa dalili.” Kawai setaji gabanta na fad’i. “Toh nagode” tace masa.
Wayarta taciro ta kirasa har ya tsinke be d’aga ba. Tashin hankali. To ina yashiga? Amal ta kira ta tambayeta ko Anas na gida cike da tashin hankali Amal tace mata itama tun jiya suke neman Anas bedawo gida ba.
Napep ta tsara bata tsaya ko inaba se paint house na Anas motarsa tagani fake gaban gidan wani hamdala tasaki har ta ciro wayarta zata kira Amal ta sanar da ita se kuma ta fasa, bari de ta tabbata ko yana ciki tukuna. Door bell ta danna sau uku amman ba response. Tana gwada murd’a hannun taga k’ofar abud’e ba sak’e sak’en da bezo mata ba toh kode barayi ne suka shigo masa? Subhanallah amman ai kuma ga motarsa. Ciki tashiga ta lek’a kitchen ba alaman ko motsin mutum “Mr. Fauzi!” ta kira sunansa shiru d’ayan d’akin ta bud’e taga nan ma bayanan toilet dinma haka, guest toilet ma ta duba bata gansa ba. Daga k’arshe d’ayan d’akin ta bud’e a hankali kwalban giya ta soma cin karo dashi, se fad’i gabanta yake ta d’aga tare da k’arisawa cikin d’akin tana taku a hankali cike da tsoro. “Mr. Fauzi!” Ta kira sunan sa alokacin data gansa kwance kan gado yayi ruf da ciki se bacci yake yi ba ko riga jikinsa se bedsheet daya ja zuwa tsakiyar cikinsa.
A nitse ta k’arisa gefen gadon tare da ajiye kwalban kan side drawer. “Mr. Fauzi!” Ta sake kiran sunansa shiru be amsa ba. Toh kode mutuwa yayi ne? Sede kuma tajisa yana numfashi. Jijjik’asa ta hau yi har se lokacin daya soma motsawa. “Waye ne?” Ya tambaya cikin bacci.
“Sir Fannah ce, Fannah Aleeyu.”
“Fannah? Me kikeyi anan? Ban rufe k’ofan bane?”
“Eh sir baka rufe ba, you need to get up kanada board meeting by 10:30AM.”
Cikin bacci yace, “barinje ba kiyi cancelling, tell them barin samu zuwa ba.”
“Sir but why? Kayi hak’uri ka tashi please.” Bece da ita komai ba ya cigaba da baccinsa. Pillow’n daya rufe fuskar sa dashi ta d’aga. Ido ta zaro tana salati alokacin da taga irin ta’addancin da aka ma Anas a fuska. Meya samesa? Waya masa duka haka?
“Subhanallahi Mr. Fauzi meya sameka? Omg!” ta tambaya a kid’ime a lokacin da ta tsuguna gabansa.
Da k’yar ya iya bud’a baki yace, “ki rufe min fuska banasan hasken nan.”
Ignoring nasa tayi “Mr. Fauzi waya maka haka da fuska? Fad’a kayi da wani neh? Meya sameka?”
“Bansani ba nima just leave me get out.” Haka kawai yaji baya san Fannah tagansa a bad condition irin na yau, bayasan yasa ta cikin damuwa bayasan taji tausayinsa.
“No Mr. Fauzi I’m not leaving you like this.” Hannu tasa ta dafe goshinta bata ma san ta ina zata fara ba. Hawaye kawai taji yana gangaro mata kan kumatu dan uban tausayi irin nata. Hannu ta aza ta tab’a gefen idansa daya kumburo dan bugun daya sha. K’ara ya saki wanda yasa ta mayar da hannunta baya da wuri. “Sorry” tace cikin kuka. Idanunsa na sauk’a kanta yaga tana hawaye abinda baya so kenan.
“Miss Aleeyu leave please, goo.”
“I can’t leave you like this, Mr. Fauzi asibiti yakamata muje su duba ka.”
“Barinje ba” yabata takaicaccen amsa idanunsa a rufe.
“Please” ta rok’esa tana hawaye ganin yadda aka masa destroying kyakkyawar fuskarsa da a yanzu mutum bare so ya kalla sau biyu ba.
*© miemiebee*
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 44
BY MIEMIEBEE
“Miss Aleeyu barin je ba kema leave I can take care of myself” hannu ya mik’a ze amsa pillow’n se kawai ya saki k’ara dan zafin dayaji a cikinsa saboda blows da Farouq ya riga kai masa. A rikice tace, “meneh Mr. Fauzi?” Kafin ya amsata ya mata k’arya ta kwaye bedsheet d’in daya ruhu dashin, hannu ta aza kan bakinta cike da mamaki “Subhanallahi Mr. Fauzi dan Allah meya sameka? Ina kasamu wannan ciwuka? Kalli cikin ka? Ya Salam!!!” Ta fad’i tana hawaye tana kallon cikin Anas da yayi har wani purple brownish colour dan azaba.
“Mr. Fauzi meya same ka please?” Ta sake tambaya hankali tashe.
“Nace miki babu in kinsan kuka zaki tayi anan kuma go, leave, I can take care of myself.”
Innalillahi! what do I do now ta tambayi kanta barata iya barin Anas haka ba he is badly wounded ga fuska ga ciki meya samesa ko b’arayi ne suka shigo suka masa duka? Amman kuma ai gidan tsaf yake ba abinda aka b’arnata. Toh meneh?
“Mr. Fauzi please kayi hak’uri mu kaika asibiti kaji? Yi hak’uri.” Ta fad’a still tana hawaye dan tsantsan tausayi. Danko ba wanda zega ta’addancin da aka ma Anas be tausayawa masa ko be zubda hawaye ba.
“Nace miki barinje ba kitafi please.” Wayarta ta ciro zata soma dialing number’n Amal dan sanar da ita halin da ake ciki.
“Me zakiyi?” ya tambayeta.
“Zan kira Amal ne in sanar da family’nka I’ve found you tun jiya suke neman ka.”
“No karki kira su hang up.”
“But Sir-” katse ta yayi ta hanyan daka mata tsawan da seda shi kansa ya masa ciwo “I said hang up!” Kansa ya dafe yana muntsika fuska cike da azaba. Nan ta katse ta matso kusa dashi “Sir kanka ke ciwo?” Niyan shareta yayi da farko sekuma ya giad’a mata kai a k’arshe. Jakarta ta ajiye kan side drawer ta nufa toilet tare da fitowa da bowl cike da warm water data d’iga dettol ciki dakuma towels guda biyu, jakarta ta ture gefe tare da ajiye bowl d’in akai. Kallonta yake “me zakiyi?”
“Sir your face is a mess, zan goge maka ne.”
“Banaso just leave.”
“No Sir I’m not leaving mesa kai zaka taimaka min amman ni bakasan na taimaka maka? Saboda bankai inyi offering maka help bane? Saboda ka raina ni banida standard? Saboda ni talaka ce? Is that it Sir?”
“No Miss Aleeyu that is not my point…” sekuma yayi shiru.
“Toh kabari in biyaka taimakon dakake min koda na yau ne.” Shiru yayi chan ya giad’a mata kai.
A ranta tace, Ya Allah kar ka kamani da laifi saboda zan tab’a na mijin da ba muharrami na ba, baida lafiya ne taimako zan masa, astaghfirullah.
Nan ta tsoma d’ayan towel d’in cikin ruwan d’umin tare da matsewa a hankali ta d’an tab’a gefen bakinsa daya fashe. Towel d’in na tab’a wajen yajiyo zafi sosai hannunta ya kama “Sir nasan zeyi zafi hak’uri zakayi kaji? Sorry” a hankali ya sake hannun nata. Tana sake tab’a wani waje ya saki k’ara “arghhh! Ya isa kibari ze warke da kansa, go home”
“Mr. Fauzi please mana kabari koda germs d’inne a kashe tunda baraka je asibiti ba. Please”
Haka a nitse cike da tausayi ta riga bin duk ciwon da ke kan fuskarsa tana gogewa a hankali, sosai Anas ya riga sakin k’aran azaba in towel d’in ya tab’a masa kan ciwon ita kuwa duk lokacin daya yi d’an ihu seta basa hak’uri. Tagama da fuskarsa sauran cikin. D’ayan tsumman ta d’aga ta sa cikin ruwan kamar yadda tayi d’azu bedsheet daya rufe jikinsa dashi tasa hannu ta kwaye zuwa cibiyar sa.
“Me kuma zakimin?” Ya tambaya yana k’ok’arin jan bedsheet din gam ta rik’e tana me hanasa yin hakan. “Ba abinda zan maka Sir zan d’an matse maka wajen ciwon ne.”
“Don’t worry ze warke da kansa. Wai ke bakia jin tsoron zama da namiji kad’ai ne under thesame roof?” ya gwada tsorata ta ko zatace ta hak’ura zata tafi.
“Ina ji amman in da kaine bana ji, I trust you Mr. Fauzi nasan ba abinda zaka min shiyasa. Yi hak’uri in d’an matse maka cikin kaji?” sanda ya k’are mata kallo sannan ya giad’a kai.
A hankali ta aza hannunta kan cikinsa ta matse towel d’in kai. K’ara ya saki sosai dan azaba tare da rik’o hannunta. “Awwchh! Kibari ya isa ze warke da kansa, arghhh!”
“Sir hak’uri zakayi sauran kad’an sorry.” Haka tata lalashinsa kamar d’an yaro. Towel tasake canzowa tare da k’aro ruwan zafi kan ruwan dan ya riga ya huce. Bayan ta zauna ta sake tsoma towel d’in ciki, cikin siririyar muryarta tace, “Sir did you get drunk yestarday” Shiru yayi kamar be jita ba. “Sir?” Ta kirasa. “No” ya mata k’arya danko besan taga kwalban a bakin k’ofa ba.
“Toh wancan fa kwalban meh?” Ta tambayesa a nitse. Kai ya d’aga yaga kwalban sekuma yaji kunya. “Toh me ruwanki dan nasha? You are not my mother ko ita mahaifiyar tawa bata isa ta hana niba, stay out of my personal li-” be k’arisa fad’in ‘life’ ba yasaki ihu “arghh!” Sanadiyar tab’a masa kan inda ke masa zafi sosai da Fannah tayi. “I’m sorry” tace “sauran kad’an.” Chan ta nisanta, “Mr. Fauzi will you listen to me in na fad’a maka wani abu?” Kamar wanda bare ce komai ba seyace “meh abun?” Sanda ta sake matse towel d’in ta mayar kan cikinsa tana daddanewa kan ciwon a hankali tace, “if I were you, in za’a maidani kai abani kyanka da kud’inka da ilimi da komai da kake dashi I will thank God barin na wasting rayuwa na akan shaye shaye ba. Masu shaye shaye sune wanda basuda aikin yi, wanda basuda ilimi basuda komai se shaye shayen da sukeyin. Amman kaga kai komai Allah ya baka Mr. Fauzi, you are handsome, rich and very intelligent, me kake nema? Don’t you think bakayi adalci wa Allah ba ta hanyar masa godiya da shaye shayen da kakeyi?” A hankali ta d’ago idanunta tana kallonsa shima kallon nata yake da blue eyes nasa sannan ya kawar da kallonsa daga gareta.
“Kayi shiru Mr. Fauzi, do you think you are fair to Allah? Bayan ya gama baka komai seka gode masa ta hanyar bijire wa dokokinsa na hana kowane muslimi shaye shaye”
“No I’m not” ya fad’a ransa b’ace, muryarsa cike da weakness. “Ke bakisan mesa na mayar da drinking abinyi ba kidena intruding min cikin personal life. Get up and leave” yace a lokacin daya d’aga hannunta daga kan cikinsa.
“Yafi ace ka rasa mahaifiyar ka ko mahaifinka kokuma d’aya daga cikinsu ya gudu ya barku? Is that the reason kake shaye shaye?” Kallonta yake totally speechless chan kuma ya tuna ashe ranan ta karanta masa diary, cikin chan tagani. Hannunta ta raba da nasa ta mayar kan cikin nasa.
Hannun nata ya kuma d’aga daga kan cikinsa “ya isa you can go banasan maganan nan, saboda kin karanta min diary hakan be baki daman fad’a min whats right or wrong ba. I’m still your Boss”
“I know Mr. Fauzi, you are my Boss. Ammana in saboda mahaifiyar ka kake misleading precious rayuwarka ta hanyar shaye shaye you are destroying your bright future. Hakan na nuna you are weak yana nufin ka barta taci nasara kanka kenan. Show her you are strong ko ba ita you can live your life, ka mance da ita and move on if possible forgive her if not ka mance da ita. You have a very bright future kadena b’atawa ta hanyan shaye shaye kaji Mr. Fauzi?” Shiru yayi bece komai ba as ya wula cikin duniyar tunani yana nazarin duk abinda Fannah ta fad’a masa. Tabbas ba k’arya ko d’aya cikin abinda ta fad’a masa dan kuwa haka Shettima ma kullum ke fad’i masa sede koda Shettima ya masa magana bai san sauraro amman yau da Fannah tamasa maganar seyaji yanasan yayi moving on ya manta da abinda Ummimi ta masa sede bawai ze yarda ko ya aminta da mace bane a rayuwarsa ever again he is already broken.
“Can you do that Mr. Fauzi for Amal’s sake?” Kai ya kad’a mata da nufin “a’a.” “For mahaifinka?” Nanma ya girgiza kai. “Ummie?” girgiza kai still yayi. “For Shettima?” Nan ma haka. Cike da kunya tace, “for me?” Jiran masifar sa take setaji yace, “yes” a hankali sounding defeated.
Idanunta ne suka sake bud’uwa cike da jin dad’i da murna. “Dagaske Sir? Zaka dena shaye shaye and move on?”
“Yes” ya sake fad’i. Dad’i taji sosai wanda ta kasa b’oyewa. “You promise Sir?” ta tambaya dan sake tabbatawa.
“I promise” yace. Sede duk maganan nan da suke baya kallonta. “Look at me please Sir” tace cikin murya me dad’in sauraro. Yi yayi kamar be jita ba. “Please” ta rok’esa a hankali ya dawo da blue eyes nasa kanta. “Da gaske baraka sake tab’a giya ba?” Ta tambayesa suna kallon juna. Kai ya giad’a a hankali “I promise.”
“Mr. Fauzi thank you, thank you so much nakega am the happiest woman on earth yanzu, tun ba yau ba nake addu’ar Allah nuna min rananda zaka dena shaye shaye se gashi Allah ya nuna min yau, thank you so much.” bece me komai ba. Nan da nan ta gama matse masa cikin yadawo clean ba jini ko d’igo d’aya jikinsa sede zafin da yakeji. Tashi tayi zata toilet ta zubar da ruwan Anas ya rik’o hannunta a hankali takai dubanta kan hannun nasa sannan kuma zuwa kan Anas d’in tanasan tace masa ya sake mata hannu amman kuma tana tsoro kar yace ze canza mind nasa batun shaye shayen da yace ya dena.
Godiya yakeson mata amman girman kansa ya hanasa, seya bud’e baki zeyi magana se wani abu ya tsaida shi. Da k’yar ya iya ya sauk’e girman kan yace;
“Thank you.” ya fad’i a hankali ko kallonta baiyi. For the first time daya soma mata godiya kenan. Ita kanta abin ya bata mamaki, yau Mr. Fauzi ne yake mata godiya?! “You’re welcome Sir” ta amsa sa a takaice da murna fal a ranta. Hannun nata ya sake ta fice zuwa toilet bayan ta fito ta zauna bakin gadon kamar d’azu “sir kayi sallan Asuba?” K’arya yakeson mata yace ‘eh’ sekuma yaga ba amfani tunda ta riga tasan kad’an daga cikin sirrinsa. Kai ya girgiza mata. Kawai se jikinta ya bata ko isha ma beyi ba.
“Isha fa?” ta tambayesa a hankali cikin dabara yadda bare fusata ba. Nan ma girgiza kai yayi. “Toh Maghrib da La’asar fah?”
Can k’asa k’asa yace, “nayi la’asar.”
“Masha Allah its not too late, barin had’a maka warm water sekayi wanka dan jin dad’in jikinka sekuma kayi yi alwala ka rama sallolin da ake binka koh?” Haka kawai ya tsinta kansa cikin san cika wa Fannah qudiri dakuma burinta.
Kai ya giad’a mata. Nan ta mik’e cikin minti biyu ta had’a ta dawo. “Sir ina bath towel naka?” Nuni ya mata da hannu wajen ta nufa ta ciro “gashi” ta mik’a masa zan jira ka a parlour tana kaiwa nan ta fice.
Sanda yayi dagaske sannan ya samu ya miqe daga kan gadon, bayi ya fad’a. Shigansa bayi da minti d’aya Fannah ta dawo ta nemi sallaya ta shimfid’a masa bayan tayi amfani da wayarta ta gano Qibla. Nan ta fice, kitchen nasa ta nufa ta d’anyi dube dube sede bataga abinda zata dafa masa ba. Fridge nasa ta bud’e froze chicken data gani ciki ta ciro takoma kitchen d’in. Soya masa tayi duka incase ko zeci zuwa rana. Flask ta nema ta juye ciki, tare da had’a masa coffee cikin flask sannan taje tayi arranging dining table masa. Daidai lokacin Anas yafito, k’amshin designer turarukan daya feshe kansa dashi tun daga sama har k’asa ne ya bugi hancin Fannah. Kai ta d’ago tana kallonsa. Sanye yake da ¾ wando fari da farar vest wanda ya bala’in masa kyau, ga wani sheqin da jik’ak’k’en gashinsa ke, kumburin fuskarsan ma ya ragu sosai, sede alamun ciwo da yankan dake ta bakinsa da gefen ido. Da sauri ta kawar da kanta kafin yace ta cika kallo dayawa. A hankali yake tafiyar har ya iso kan dining table d’in, zaman ma da k’yar yayi harda d’an k’ara “argh!” Tare da rik’e cikinsa.
“Does it still hurts?” Ta tambayesa cike da damuwa. Kai ya girgiza mata amman ita tasan zafi yake masa. “I made you breakfast I hope you like it.” Yana kallonta tayi serving nasa kajin tare da juye masa coffeen cikin cup ta tura masa gabansa. “Zan jiraka a parlour, eat please.” Kallon abincin yayi sannan ya kalli Fannah. A hankali ta juya zata fice, hijabinta ya rik’o chak ta tsaya bata juya ba.
“Lets eat together” yace da ita.
“Sir naci abinci I’m full nagode.”
“Please.” Ya fad’i wanda besan lokacin daya fad’a ba shi kansa, meke damunsa? Haka kawai yaji in ba ita bare iya cin abincin ba.
‘Please?’ ta nanata a zuciyar ta. Dagaske Mr. Fauzi ne yau yace mata please? Lallai!
A nitse ta juyo, kujera opposite him ta zauna tana watsa da yatsunta. Plate ya jawo ya juye mata ragowar kazan duka. “Eat” yace da ita. Baki ta bud’e data d’ago kai taga uban kajin daya tara mata gabanta.
“Sir ina zan kai wannan? Yayi yawa.” Hannu ta mik’a zata ja flask d’in a yayinda ya d’aga daga kan table d’in gabad’aya ba tare da yace komi ba.
“Sir please ka rage yayi yawa.” Ignoring nata yayi “lets eat I’m hungry.” Nasa ya soma chi itako har yanzu bata tab’a plate d’in ba ina zata kai wanga kaji?
“Miss Aleeyu eat.” Miyau ta had’iye a hankali ta d’au cinya d’aya ta soma ci. Zaman makokin ne ya isheta tayi gyaran murya sannan tace, “Sir do you want to talk about it?” Sanda ya nisanta sannan yace, “about?” Ba tare da ya kalle ta ba.
“Abinda ya sameka.” Kai ya girgiza “No.”
“Okay…” tace a hankali “but Sir next time ka kiyaye please koma mene neh.”
“Okay” yace mata kamar d’an yaron da mamansa ke masa fad’a. Haka kawai yaji bayasan fad’awa Fannah gaskian al’amarin yasan definately zatayi blaming kanta zatace duk akanta fad’an ya tashi kuma hakan ne komai a sanadin ta ya faru sede bayasan tayi feeling guilty.
“Sir?” ta kira sunansa. “Yes” ya amsa yana sipping coffeensa. “Mesa kace kar na kira Amal na sanar da ita I’ve found you?”
“Saboda banasan susan inada gida anan.” Sam bata fahimce me yake nufi ba, so yake yace bawanda yasan yanada gida?
“Ke kad’ai na fara kawo wa cikin nan, ko Shettima besan I have a paint house ba.”
Meh Mr. Fauzi yake nufi kenan? Does this mean tanada wani matsayi a zuciyarsa da har ya b’oye wa kowa gidan sa hatta family’naa amman ita ya sanar da ita ya kuma barta tana shiga???
© miemiebee
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 45
BY MIEMIEBEE
THANK YOU SO MUCH DA ADDU’O’INKU MASU SO DA K’AUNA TA, ALHAMDULILLAH NAJI SAUK’I SOSAI
Shiru tayi bata ce komi ba as tana nazarin abu a ranta.
“Say it out” yace yana kallonta. Mamaki ne yacika ta how comes ya gane ta nada magana a ranta.
“Errm babu” tayi k’arya.
“Akwai say it.”
“I was thinking ko za’a zubar da abubuwan da suke cikin fridge d’in kar in-” katse ta yayi “jeki d’iba ki zubar, kiyi flushing duka.” Dad’i sosai taji nan take ta mik’e. “After kin gama cin abincin ki amma.”
“Sir na k’oshi thank you” bata tsaya jiran me zece ba ta nufa fridge d’in tafito da duka kwalabe guda 15 d’in. “Sir akwai wani bayan wad’annan?” kai ya gyad’a mata.
“Are you sure Sir?”
Kai ya girgiza “akwai kwali d’aya k’ark’ashin gado na a d’aki.”
“Thank you Sir.” Uku-uku ta riga d’iba tana kaiwa toilet tana zubarwa har tagama duka kwalaben kuwa tayi disposing nasu. Bayan ta gama ta d’au first aid box daga toilet tafito dashi zuwa dining space inda ta tsinci Anas zaune yayi zurfi cikin tunani. “Sir?” Ta kirawosa tare da dawo dashi daga duniyar tunanin daya wula. Kallonta kawai yayi ba tare da yace komi ba.
“I think ciwon fuskan kan zefi healing da wuri in aka rufe” ta fad’i tana ciro wasu transparent bandages guda biyu. B’antare d’aya tayi. “May I?” Ta tambayesa kai ya giad’a mata nan ta manna masa na gefen bakin nasa a hankali sannan na kusa da idansan shima a hankali. “Get well soon” tace dashi a lokacin data rufe first aid box d’in ta mayar toilet, fitowarta ta nufi bakin k’ofa.
“Miss Aleeyu” ya kira sunanta chak ta tsaya tare da kewayo wa. “Yes Sir.”
“Ina zakije?”
“I’m going home, jikin naka da sauk’i ba?”
Alokaci d’aya kuma se yaji bayasan ta tafi, shi yake korarta d’azu amman yanzu kuma so yake ya cigaba da kasancewa _TARE DA_ ita, bayasan ta tafi wanda shi kansa besan dalili ba.
“Must you go?” Ya tambayeta.
A hankali tace, “Sir I have to, bareyi in cigaba da zama anan ba.”
“Okay” yace blankly. Bata ce dashi komai ba ta fice. So yake ya tsayar da ita yace mata ta zauna dashi baya san ta tafi amman bayasan ta raina sa bayasan ta d’auka da wata manufa, ta zata ko santa yake.
Isar Fannah gida ke da wuya ta tarar da Farouq tsaye bakin k’ofa da alama ita yake jira. Bugun zuciyarta taji ya k’aru in akwai d’an Adam data tsana a doron k’asa toh Ya Farouq ne. Bayan ta sallami meh napep d’in ta sunkuyar da kanta tayi kamar bata gansa ba se tafiyarta take a yayinda idanunsa suke biye da ita. Takai da shiga cikin gidansu kenan kawai Farouq ya jawo ta da k’arfin gaske, kafin tayi yunk’urin yin wani abu ya matseta jikinsa gagam shi a dole yana hugging nata. “Ya Farouq me haka? Ka sakeni” se k’ok’arin k’watan kanta take amman ta kasa. Batasan lokacin data fara kuka ba. Se bugin k’irjinsa take amman kamar super glue yak’i sakinta. “Fannah mesa bara ki soni ba? Mesa Fannah? Ke bakisan ina sonki bane? Akan ki kowa ze iya mutuwa, mesa se wancan me idan turawan zaki so? Me yake dashi da banida? Tell me mesa bakiya sona?” ya k’are maganar yana wani erin zakin nishi kamar ze cinye ta tare da shunshuna hijabinta sekace ze cire.
“Ya Farouq ka sa
tana-tare-dani.jpg TANA TARE DA NI… PAGE 70 BY MIEMIEBEE Miyan kap jikinta ya zube shima Anas yad’an tab’a sa kad’an. Irin rikicewa da b’arin da Fannah keyi ko gamo mutum yayi da aljan bareyi irinsa ba take ta tsuguna tasoma tattarawa abinda Anas ya tsana kenan ya washi yaganta tana picking broken glasses da hannu. Kafin yace tabari ko ya d’aga ta aikin gama ya riga ya gama kyat! Ta yanke a yatsanta k’ara sosai ta saki kamar a kyaftawan ido ya k’ariso gabanta hannayensa na sauk’a akan jikinta ta tsala wani irin rikicaccen ihun da shi kansa seda ya firgita. “Fannah please what is wrong with you? Anas nefa ba wani ba, its Anas your husband mesa kike haka da zaran na tab’aki ki rikice? Muga hannun” da zaran ya matso ze tab’a ta seta sa ihu ko magana takasa masa duk tabi ta tsure ta gefensa tabi da gudu da sauri ya cafko ta da hannu ya dawo da ita baya. “Fannah what is your problem why are you acting like this? Mena miki kike gudu na kamar kinga mala’ikan d’aukan rai, what is it tell me?!” Ya k’are maganar cikin sautin tsawa saboda he can’t take it anymore taya matarsa zata na gudunsa haka. Hannun nata take ta k’ok’irin fisga amman takasa hawaye kam sekace lalacaccen famfo. Bright blue eyes nasa da suka zamanto dull and weak dan tsantsan tashin hankali ya d’agosu a maraice yana kallonta se k’ok’arin karb’an hannunta take amman takasa. “Fannah mena miki? Ki fad’a min please, OMG!” Yayi exclaiming alokacin dayaga yadda jinin jikinta ke zuba a k’asa. Hannunta yasoma ja zuwa d’akinsa. Sam tak’i bud’e baki ta masa magana se hawayen da takeyi ganin sunkusan kai ga d’akinsa ta ja hannunta da k’arfin da Allah yabata seda ta fisge daga rik’onsa. “Fannah please don’t go…” bata ko sauraresa ba ta ruga d’akinta a guje tare da sa lock. Har k’asa ya sauk’a wasu irin zafaffun hawaye na maza suna sauk’owa tsili-tsili a fuskarsa. “Why Fannah? Mena miki? Your silence is killing me why are you punishing me like this?” Itama Fannar ba abinda take banda kuka, wanke ciwon nata tayi se kuka take ga wani irin yunwan dake azabartar da ita batajin zata iya kwana inbatasa wani abu acikinta ba. Rarrafawa tayi zuwa fridge na d’akin hamdala ta saki ganin da akoi cookies da drinks uku ciki. Ledar cookies d’in ta ciro ba makawa ta soma kaiwa cikinta seda taci fiye da rabi sannan ta kora da fanta nan ne tad’anji dama-dama. K’aran shigowar sak’o taji a wayarta kamar wacce barata duba ba sekuma ta miqe ta bud’e taga saqo ne daga Anas ta karanta kamar haka; Fannah please in wani abun na miki ki sanar dani stop punishing me like this zuciyana bare iya d’auka ba please Flower I’m missing your smile, body, and fragrance already open the door for me please. I love you #crying Wani sabon kukan ta fashe da har k’asa ta sauk’a tana birgima a kan rug na d’akin. Anas dake bakin k’ofar ji yake kamar ya b’alla k’ofar yashiga if only he could. “Fannah please stop crying kinji dan Allah kibari… Kidena please stop it” yayi stating cikin sautin kuka. Zama yayi bakin k’ofar yana hawaye tana kuka. Isha nayi ya rok’eta da ta tashi tayi Sallah ba gardama ta d’au hijabin ta tayi Sallan kamar yadda shima yayi a parlour bayan yagama shafa’i da wutr nasa ya dawo. “Fannah kifito kichi abinci kinji? I get it bakison sake sani a ido, zan koma d’aki sekin gama infito kinji? I love you.” Yana kaiwa nan ya juya a sanyaye kamar wanda k’wai ya fashe mai a ciki ya nufa d’akinsa bayan minti ishirin ta bud’o d’akinta a hankali, parlour ta nufa dan tattara wajen da plate ya fashe mata d’azu to her suprise taga wajen tsaf ko alaman miya babu tsaf Anas ya share yayi mopping. Dining area ta nufa ta d’iba abincin kad’an se sauri take kar ya fito su had’u gefen flask d’in taga wani paper hannunta na b’ari ta d’aga ta karanta. Flower please wear the plaster and cover your wound please kinji? I’m sorry. Wani sabon kukan taji yana k’ok’arin rufeta ga plaster’n tana gani amman batajin zata iya d’agawa, miyar da paper’n tayi ta ruga d’akinta a guje ta baje kan gado, ta cigaba da kukan daga inda ta tsaya. Bayan shiganta da kamar minti uku Anas yafito daga d’akinsa wajen daya ajiye mata paper’n ya nufa disappointedly yaga bata d’aga plaster’n ba to ko bata fito bane? Flask d’in ya bud’e yaga da alaman ta d’iba abincin mesa bata d’au plaster’n toh? “Fannah haka kika tsaneni yanzu? Bakiya son koda help d’ina?” Ya k’are maganar da hawaye na gangarowa daga kumatunsa guda. Hannu yasa ya share ya koma bakin k’ofar d’akin ta ya zauna yana sauraron sautin kukanta yana hawaye shima har bakin sa yayi dogo da ce mata tayi shiru amman tak’i. K’arfe 9:00PM na bugawa ya mik’e “Fannah anan zaki kwana?” Ya tambayeta tana jinsa amman tak’i amsawa dan batada burin sake masa magana a rayuwarta again. “Fannah kifito muje mu kwanta kinji? I can’t sleep without you by myside please kifito.” Sautin kukanta yaji ya k’aru. “Flower kibar kukan nan please…” ba irin rok’ar duniyan da be mata ba amman tak’i bud’e k’ofar ta kuma k’i barin kukan, ga wani uban ciwon kan da ke cinta. D’akinsa ya koma ya d’ago pillonsa da bargo ya dawo bakin k’ofar d’akinta ya shimfid’a ya kwanta kai be damu da uban sauron Maiduguri ba all he knows is that he don’t want to leave his flower alone. “Fannah goodnight, I love you so much.” Alokacin da yayi maganan tana kwance kan gado ta d’au tafiya yayi wani irin tsoro taji ya ratsa ta ko kashe wutan d’akin ta kasa, duk’unk’une kanta tayi cikin bargo se b’ari take cike da tsoro. Tafi awa d’ai tana neman bacci sannan a wahale yazo mata. Anas kam sam ya kasa bacci he is missing her in his hands se juyi yake amman ya kasa bacci bare iya kwatanta how he is missing her legs wrapped around his body ba. *** 2:34AM Firgit Fannah ta farka dan wani erin masifaffen mafarkin datayi. “Anas!” ta kira sunansa da ihu take ya jiyota dake daman baccin nasa beyi nisa ba. “Fannah” ya kira sunanta tare da mik’ewa. “Fannah I’m here kinji?” Kuka take sosai cike da tsoro duk ta duk’unk’une kanta da bargonta ta cusa kanta cikin cinyoyinta se kuka me sauti take. “Anas” ta sake kiran sunansa. “Yes Fannah I’m here please stop crying bud’e min kinji please I beg you…” Har a yanzu bata bar kukan ba. Zaman gadon ne ya gagareta ta tako zuwa bakin k’ofar ta tsaya adaidai lokacin yake kiran sunanta again “Fannah.” Kuka ta fashe da, yana jin muryarta kusa dashi hankalinsa ya sake tashi. “Fannah, Fannah ki bud’e min kinji? Let me in please.” Kuka take sosai ta inda yakejin sautin kukan nata ya matso tare da had’a kansa da wajen “Fannah I’m here please kibar kukan.” K’asa ta sulale kamar yana ganinta shima ya sauk’a. Hannunta ta aza jikin k’ofar tare da dafe kanta jikin k’ofar tana me cigaba da kukan. Daidai inda hannunta yake ya aza nasa shima “Flower I’m here you are not alone I’m here with you kibar kukan kinji?” A hankali taji tsoronta na gushewa da dad’ad’d’un kalamun Anas awajen bacci ya d’auketa tun Anas najin k’arfin nishinta har yazo yaji shiru hakan ya tabbatar masa tayi bacci anan ne shima yasamu ya d’an kwanta although sauro sunk’i barinsa saura na masa waqa a kunne saura suna cizon sa farin fatarsa duk yayi pink amman haka ya hak’ura dan baison barin Fannah ita kad’ai ahaka har Asuba tayi bayan ya idar da nasa ya gama addu’o’insa ya dawo ya soma kirar sunanta a hankali cikin baccin tasoma jin sunanta. “Fannah ki tashi kiyi Sallah kinji? Asuba yayi. Fannah tashi kinji?” A kasalance ta mik’e ta nufa bayi ta d’auro alwala tayi Sallah sannan ta koma kan gado ta kwanta har a yanzu Anas ya kasa bacci. Ko kad’an baijin ma ze iya zuwa office yau, bare iya barin Fannarsa awannan hali ba. Se anan ne yasamu yayi bacci shima 9:45AM ya tashi har anan Fannah na bacci tattara bargon nasa yayi ya wuce d’akinsa yayi wanka sannan yayi shirinsa na kullum fridge ya dosa ya ciro irin sliced potatoes d’innan da ake packaging ya musu frying da omalet ya had’a musu breakfast. Cikin awa d’aya dining table is set agogon hannunsa ya duba yaga 11:02AM knocking yaje yayi a k’ofar d’akinta alokacin da take fitowa daga wanka kenan. “Fannah kin tashi? If yes good morning kifito ki karya kinji? I love you” yana kaiwa nan ya koma dining ya soma zaman jirarta. Kukan dake son k’eto mata ta shanye simple doguwar riga tasa bak’i me silky jiki. Babban akwatinta ta ciro ta soma tattara kayakinta wanda zatayi amfani dasu ciki. Dam ta cika da essential stuffs nata ba mantuwan da tayi tana gama had’a akwatin ta ja ta rufe sannan ta zira hijabinta dogo har k’asa ta d’au wayarta sannan ta soma ja, a hankali ta bud’e k’ofar ta fito tafiya take kanta a sunkuye da jakarta tana ja daidai ta iso parlour ta bayyana a idon Anas. Kasa believing abinda idanunsa suke gane masa yayi. What is he seeing? Ina Fannah zataje da wannan babban akwati? Ganin se dosan bakin k’ofa take ya k’urma mata kira “FANNAH PLEASE STOP!” A guje ya nufa inda take, k’ara saurin tafiyar ta take gabanta yasha da wuri idanunsa take suka kad’a sukayi ja. B’ari bakinsa yake kalamunsa suna stammering “Fa.. Fan.. Fannah meh wannan? Ina za kije? Meke faruwa Fannah? Tafiya zakiyi ki barni? Mena miki Fannah? Dan Allah karki tafi in wani abin na miki tell me I’m sorry for everything that I’ve done I’m sorry please karki tafi.” Ya k’are maganar cikin sautin kuka. Zuciyarta taji ya karye, batasan seda hawaye suka soma ambaliya a fuskarta ba sam ta kasa dena kukan musamman ma dataga alaman cizon sauro all over his face and hands nufin a waje ya kwana yana gadinta jiya. “ Fannah please karki tafi mena miki da zaki tafi? Kiyi hak’uri dan Allah.” Hannunta yayi yunk’urin rik’ewa baya taja da wuri taja akwatin nata tabi ta gefensa da wuri ya rik’o hijabinta. Abin da be tab’a faruwa ba ya faru yau. Mr. Fauzi ya sauk’e girman kai da duk wani feeling daya keyi ya sauk’a har k’asa akan knees nasa duka biyu. Hawaye yake sosai “Fannah please don’t go dan Allah karki tafi. In wani abun na miki please let me know.” A nitse ta juyo ganinsa akan guiwowinsa ba k’aramin mamaki ya bata ba. Idanunsa a raunane ya d’agosu yana kallonta duk setaji wani iri tasa mijinta kneeling tace masa ya tashi kuma batason sake masa magana ganin yadda yake kuka itama ta k’ara k’arfin nata kukan. Juya masa baya kawai tayi batason ganin hawayensa kamar yadda shima baison ganin nata. “Fannah turn and look at me please mesa zaki tafi? Mena miki? Kinsan barin iya rayuwa ba ke ba please karki tafi Fannah in wani laifin na miki ki sanar dani dan Allah.” Juyowa tayi cikin sautin kuka ta soma magana har wani sama sama nishinta yake. “Anas are you serious? Bakasan me kamin ba? Kana nufin har a yau baka gane ni ba? Kana nufin baka san yarinyan dake _TARE DA KAI_ ba har a yau?” Cike da rashin fahimta ya taso “Fannah what are you talking about? Wace yarinya kike nufi?” Hannu tasa ta share hawayenta kamar yadda yayi shima. “Anas kaine mutumin, kai nake mafarki kullum zaka dawo ka sake azabartar dani kamar yadda kayi 5 years back. Anas don’t you get it? I’m the girl, nice yarinyan… Ni kayi raping 5 years bacm. Nice yarinya from the incident a Bama na yammacin Asabar 23rd of March…” Sekuma ta fashe da wani irin masifaffen kuka. K’wak’walwarsa kasa d’aukan abinda ke faruwa yayi. Se kai yake kad’awa yana salati a ransa da k’yar bakinsa ya bud’u cike da tashin hankali da rashin yarda yace “no you are not Fannah, you are not the girl inda kece da nayi noticing naki bake bace Fannah baki gane bane taya ma kika sani? I never told you.” “It doesn’t matter ‘cause I read your diary Anas ni kayi raping. Anas nice yarinyan da ka raba ta da budurcinta, ka cuceni Anas saboda kai nida family na muka bar Bama muka bar ‘yan uwanmu, saboda karya me bin maza da ‘yan unguwa ke kirana dashi muka bar Bama a sanadin abinda kamin, saboda abinda kamin Anas ka rabani da first love d’ina AHMAD wanda yasoni tsakani da Allah, saboda kai na rasa gatana, sabida kai Ya Farouq da Baffah Khaleel suka samu baki suke zagina suna kirana karuwa saboda abinda kamin kasa Baba ya kamu da ciwon zuciya Anas you are the source of my sorrow and fear. Mena maka Anas? Mena tab’a maka daka gommaci ka k’untata min? A rayuwa ba abinda naso kamar in gyara maka rayuwarka and I did mesa ni baka min haka ba? Mesa ka shafawa rayuwata bak’in fenti Anas? Barin iya zama dakai ba, barin iya cigaba da zama da mutumin daya cuceni kamar yadda kayi ba. Ka sallameni in tafi gida ka sallameni inkoma gun Mami na dan Allah karka hanani takarda na. Anas I’ve loved you but not anymore, I thought I could trust you why is the handsome Anas I know turning into a monster? Ka sallameni dan Allah…” © MIEMIEBEE