TANA TARE DANI CHAPTER B KARSHE

 TANA TARE DANI CHAPTER B KARSHE

TANA TARE DA NI… PAGE 71 BY MIEMIEBEE Kai yake kad’awa cike da tashin hankali a yayinda zuciyarsa tak’i amince masa da abubuwan da Fannah ta fad’i masa, hawaye yake sosai abin tausayi sam yakasa koda bud’e baki yayi magana because of how shocked he is. Ina ma ace ba’a tab’a qaddara masa wannan rana ba, mesa se Flowersa? Nufi kenan itace yarinyar data ta had’asa da Allah karya mata abin amman ya mata? Just how much pain have he made her gone through? Itace yarinyan datake fito masa kullum a mafarki tana ce masa _TANA TARE DA SHI_ there’s nomore denying Fannah ce yarinyar mesa betab’a noticing nata ba? Why? Sede a sosai yanajin yatab’a saninta wani wajen amman baya iya tunawa. Da k’yar bakinsa ya iya bud’uwa cikin wani irin murya cike da nadama yace “Fannah… Fannah I… I’m so so sorry dan Allah kiyi hak’uri Fannah kece yarinyan kece ita, kece yarinyan danayi taking advantage naki Fannah bansan ta ina zan soma baki hak’uri ba, raping naki danayi shine BABBAN KUSKUREN DANA TAFKA (littafin rash kardam) if only I can tell you how sorry I am danayi. I’m sorry for everything that I’ve done, I’m sorry for breaking you precious heart. Fannah barin iya baki hak’uri ba tun rananda abin ya faru nasoma living a life full of guilt tun daga ranan nakasa samun sukuni kullum cikin tunani da mafarkin ki nake. Fannah please karki tafi ba’a cikin

hankali na na aikata abinda na miki ba I was drunk that evening takaicin abinda Ummimi ne duk ya sani I needed someone to blame it on sekuma Allah ya kawoki path d’ina. Fannah wannan k’addaran ba naki kad’ai bane I know you’ve suffered morethan alot amman kisani nima I did wallahi I will do everything I mean everything inga kin yafemin. Fannah I was just 18 nayi wrecking naki I was young and stupid kema kinsani barin tab’a aikata abin danayi da a baya ba yanzu, kisani ba’a son raina na rabaki da martabarki ba, Fannah ba’a son raina na rabaki da Ahmad, kamar yadda ba’a son raina nasa Baba yakamu da ciwon dayake fama dashi ba dakuma saku barin ‘yan uwanku a Bama. Fannah kece yarinyan danayi spending shekara da shekaru ina nema saboda in nemi gafararta…” Matsowa kusa da ita yayi ganin zatayi baya ya dakatar da ita sake sauk’a yayi kan guiwoyinsa ya ajiye duk wani girman kai da feeling nasa a gefe. A raunane ya d’ago idanunsa ya azasu kan kumburarren fuskarta da hawaye ke ambaliya kai. “Fannah please forgive me dan Allah ki yafemin I’m so so sorry for breaking you heart for making you go all through those meseries, dan Allah kiyi hak’uri nasan banida right na neman gafararki but nasan kinada pure and good heart ki tausayamin kiyafemin please I’m sorry for everything that I’ve done to you, Fannah inda zan iya reversing time in miyar da komai normal da nayi, abinda ya faru ya riga ya faru mu d’ausa as k’addarar a rayuwanmu Fannah I don’t want you to leave please stay with me kamar yadda kikecemin a kullumKINA TARE DA NI_ prove it to me. I will never hurt you Fannah this I promise. Wallahi ban tab’a son wata macbayan keba Fannah bame matsayinki a zuciyana koda kuwa Amal ce banida kamarki ki tausaya min karki tafi dan Allah…_ ya k’are maganar cikin hawaye. Sosai ta tausayawa Anas kalamunsa ba wanda be kwanta mata a rai ba, tana son Anas tana sonsa sosai amman batajin zata iya yafe masa abinda ya mata… Aduk lokacin data tuna da irin azaban datasha alokacin dayayi forcing kansa cikinta cike da azaba da rashin imani ko tausayi setaji barata iya yafe masa ba dukda kuwa a bige yake a lokacin amman still hakan be basa daman yayi raping duk wanda yagani kan hanya ba. Hannu tasa ta share hawayenta har a yanzu idanun Anas basu bar kanta ba ya zura mata jajayen idanunsa yana jiran amsarta yana nan a kneeling position d’in har yanzu. “Anas dan Allah ka tashi stop kneeling infront of me, katashi please” “Fannah har senaji kin yafemin baraki tafi ba zantashi kiyu hak’uri please.” Muryarta daya dishe dan kuka tayi clearing sannan tasoma kamar haka; “zama na dakai ya k’are Anas. Batun yafiya kuwa zan yafe maka Anas saboda d’an Adam ajizi ne musamman ma danasan labarinka nasan duk wani abinda ka aikata na haramun Ummimi ce sanadi ga kuma yadda ka tuba, na gamsu da tubar dakayi. Zan yafe maka duk wani abinda kamin Anas amman hakan bawai yana nufin zan cigaba da zama dakai bane tafiya yazamo min dole ka sawwaqe min please.” Hijabinta ya tattara ya rik’e a hannunsa yana hawaye “Fannah karki min haka dan Allah ki dena fad’in zaki tafi, kina nufin kin tafi har abada baraki sake dawowa ba kenan? Ya kikeson in rayu? Fannah wallahi da in rasaki gwara in rasa komai koda kuwa raina ne wallahi barin iya rayuwa ba keba dan Allah karki tafi, I beg of you please Fannah nasan kinada tausayi baraki iya tafiya kibar masoyinki ba…’ ya k’are maganar hawaye na fitowa bibbiyu a idanunsa. “Anas dan Allah kadena” ta karb’e hijabinta “kace zakayi everything dan in yafe maka. Ka taimaka wa rayuwata ka sakeni dan Allah. Anas tsoronka nakeji I don’t know what you are capable of doing. Yafiya kace kanaso with time in shaa Allah zan yafe maka amman dan Allah karka hanani takarda na.” duk yadda tayi ta had’iye kukan ta kasa. “Fannah barin iya rubuta miki takarda ba barin iya sakan kiba, barin iya karya promise dana d’auka nacewa duk rananda Allah ya bayyano min ke zan kula dake ba I can’t let you go, I can’t lose you for the second time. Fannah wallahi I will never hurt you inda zanyi da na jima da aikatawa. Fannah can’t you see? Ko hak’k’i nama na tauye wa kaina just so as not to hurt you, tunda na fara sonki ki fad’a min abu d’aya wanda nayi yayi hurting naki, I love you morethan I love my own soul. Fannah tausayinki yamin yawa barin tab’a iya sakanki ba dan Allah kibar had’ani da Allah akan in baki takardan ki saboda I can’t kamar yadda I can’t say no to your offer anymore.” “Anas in baraka bani takarda na ba zan tafi, Allah k’ara mana hak’uri dukan mu I wish you farewell. Thank you for all the help daka min right from day 1 na had’uwan mu barin tab’a mancewa dasu ba, kasani I’ve loved you and har in mutu kanada gurbi a zuciyata.” Tana kai nan taja jakarta ta juya besan lokacinda ya tashi yajata ta fad’a jikinsa ba. “Anas ka sakeni ple-” bata k’are maganar ba ya lalubo lips nata ya had’a da nasa yana mata wani irin kiss, kissing nata yake hungrily. Sam tak’i basa had’in kai ba abinda take se hawaye tana ta shuresa amman kaman maye yak’i hak’ura sam yak’i giving up seda ya tabbata ya kashe mata jiki dakanta tabar bugin da take masa tabasa free passage. Hannunsa ya zagaye akan ‘yar kunkumin nata yasake matso da ita jikinsa itama a hankali ta zagaye hannayenta a wuyansa sun d’au tsawon lokaci suna abu d’aya. Suyi su tsaya suyi gasping for air su cigaba se chan da yayi pulling out ta manna goshinta a hab’arsa ta soma hawaye. Hugging nata yayi gagam har yana affecting mata numfashi. “You can’t go Fannah, wallahi barin iya rayuwa ba keba, punish me kimin duk wani abinda kike ga ya kamance ni Fannah inma kotu zaki kaini ki kaini amman dan Allah don’t leave me, don’t ever please. I love you, I love you Flower don’t leave me please. Abinda ya faru ya riga ya faru tafiyarki will not solve anything kizauna muyi magana please you’ve changed me banason tafiyarki ya kuma canzani.” D’an sanarwa please masu karatu in kun kura zaku ga page d’innan yayi gajere compared to sauran. Kamar yadda wasunku suka sani inada ciwon baya kuma akwana biyun nan danake yawan zama ina typing seya k’aru saboda haka likita ya buk’aceni da in rage zama saboda haka zaku d’an jini shiru na kwana biyu haka, ina me baku hak’uri, I love you all © MIEMIEBEE

 Wani irin wawan mutuwa jikinta yayi ga kuma wani erin tausayin Anas daya kamata lokaci guda mara misantuwa. Kasa ce masa koda uffan tayi, alokaci d’aya k’wak’walwarta ta toshe, ta rasa me zatayi ta zauna ne kokuwa ta tafi? Kalamunsa duk sunbi sun kamata batason tafiyarta ya kuma canza mata shi ya koma gurb’arcacciyar rayuwarsa na da. In hakan ta faru barata tab’a iya yafe wa kanta ba. Hawayen da suke gangarowa kan kumatunta se k’aruwa suke a yayinda zuciyarta ke k’ona in ta tuna ta auri mutumin daya jefa mata rayuwa cikin k’unci, worst part d’inkuwa shine irin zazzafar soyayyar da take masa wanda bata zaton ta tab’a yima wani mahaluk’i ba, soyayyar da bata tsammanin akoi takwabin daze iya kashesa tasani ba na mijin da ze zauna da ita da mutunci kaman yadda Anas zeyi aduk fad’in duniya tunda gashi da gaskia ya bayyana ma ya nuna yana sonta kuma ze cigaba da zama da ita still kuma koba dan haka bama tunba yau ba yake bata labarin yarinyan cewa duk lokacin da ya sameta zeyi all he can ya yafe mata amman ita batajin zata iya cigaba da zama dashi saboda abin da zafi kuma da ciwo. Sun d’au tsawon lokaci suna ahaka sam Anas yakasa sake ta k’ak’am ya matse ta jikinsa wane za’a k’wace masa ita, itako takasa hugging nasa back tana manne kawai a jikinsa se chan a hankali ta zagaye hannayenta bibbiyu a bayansa duk suna feeling turaren jikin junansu me tafiyar masu da imani, hugging juna suke cike da so da k’auna kowannen su na fatan ina ma ache wannan moment will last forever. Cikin sautin kuka ta kira sunansa. “Anas.” Kamar me jira takirasa ya amsa “na’am Fannah.” “Anas promise me baraka sake tab’a giya ba.” Bayanta yake shafawa, “Fannah anything for you I’ve promised you before and zan sake yau barin sake tab’a giya ba in shaa Allah I promise please don’t go.” “Promise me baraka sake firing workers naka ba” “Flower barin k’ara ba I promise.” “Promise me baraka sake aikata wani aikin haramun ba” “Flower I promise.” nanma yace. “Thank you” ta fad’a a hankali. “Does this mean zaki zauna dani? Baraki tafi kibarni ba?” Da k’yar ta iya ta raba jikinta da nasa ta d’ago jajayen idanunta da suke tsiyayar da hawaye har ayanzu ta kafasu kan fuskar Anas sosai shima idanun nasa suka kad’a hannu yasa ya share mata hawayen ‘yar murmushi tasaki masa sakamakon hakan wanda yasa yaji sanyi sosai aransa. “Fannah I love you so much.” Hannun sa ta sauk’e daga fuskarta a hankali tana murzawa sannan ta d’au d’ayan hannunta ta aza a nasa fuskar. “I love you too, I love you so much Anas.” Ta miqa kai tayi pecking nasa a kumatu. “But I have to leave” kamar a kyaftawan ido taja jakarta ta juya. Sauri sauri take ta bud’e k’ofar ta fita. “Fannah!” Ya kira sunanta da k’arfi cike da tashin hankali tare da shawo gabanta. “Fannah you musn’t go dan Allah ki zauna please.” Hawaye ya ke sosai kamar yadda itama take sam batason tafiyar dan de batada wata mafita ce a tunaninta. “Anas dan Allah karka hanani tafiya inhar kanaso na kamar yadda kake fad’a let me go please.” ta sanar dashi tana k’ok’arin shanye kukanta tare da bin gefensa, hijabinta ya riqo “I can’t let you go Fannah barin iya rayuwa ba keba dan Allah kiyi hak’uri niko da barakina min magana ba but please don’t go stay with me.” K’arfin hali tayi ta fisge hijabin nata dayayi yunk’urin sake tab’ata ta tsawata masa “DON’T TOUCH ME ANAS! DON’T!” mutuwan tsaye yayi a wajen yana hawaye kamar ba gobe yana kallonta tana jan akwatinta har ta fice masa daga kallo. “Fannahhhhh pleasssseeeeeee don’t gooooo…” yana sauk’a k’asa yayi wannan magana kuka yake kamar d’an yaro abin tausayi. Tana fita tasamu adaidaita sahu ta shiga ciki ta tsaya kuka kasa koda fad’a masa inda takeso ya kaita tayi tafi minti ishirin zaune ciki tana kuka sannan da k’yar ta sanar dashi a sannu sannu yakaita har gaban gidansu d’ari biyar ta dank’a masa ba tare da ta jira amshan chanjinta ba. Tana shiga ta tarar da Mami da Afrah da alama sun dawo daga rakiya ne. Mamaki ne ya mamaye fuskarsu duka ganin Fannah da akwati ba saqe-saqen da basuyi ba daga bisani Mami ta nufa bakin k’ofar ta rik’o Fannah ganin jiri nason d’ibanta, Afrah che ta amshi akwatin nata sukayi da ita d’aki. Har a yanzu ba wacce ta iya tambayar Fannah meke tafe da ita duk hankalinsu yabi yanayin datake ciki. Wani erin nishi take da inta ja d’aya ciki kamar na mutane goma sosai Mami ta tsorata ba kamar Afrah dake kuka already. Hijabin jikinta aka tub’e mata tare da k’ure fankan d’akin. Se anan bakin Mami ya bud’u “Habibti kukan ya isa dan Allah ya isa haka kinji? Yi shiru” ta sanar da ita tana jijjik’ata da k’yar kukan ya lafa sekuma ciwon kai bayan tasha magani ta d’an dawo hayyacinta Mami ta zaunar da ita. “Fannah meke faruwa? Ya na ganki haka? Kimin magana Habibti.” Wani sabon kukan taji ya faso mata, kwantar da ita Mami tayi a jiki tana bubbuga bayanta “fad’amin kinji?” Ba yadda Mami batai da ita ba amman Fannah tak’i tanka ta se kuka ba sauti da take tayi, tabari akira Anas ma tak’i duk tasasu cikin rud’ani da kuma san jin meya faru tsakaninta da Anas ga dukan alamu ba lafiya ba. Se chan Mami ta tura Afrah waje ta zaunar da Fannah tata yi mata magana cikin wani irin salo tana rok’arta. Se anan bakin Fannah ya bud’u “Mami ina Baba?” abinda ta soma tambaya kenan. “Yayi tafiya zuwa Bama Habibti kinason masa magana ne?” Kai ta kad’a “Mami banason Baba ya sani dan Allah kiyi min alk’awari baraki fad’a masa ba kosu Afrah ma baraki sanar dasu ba kuma baraki kira dangin Anas ki sanar dasu ba suma wannan abu da nakeson sanar dake yazama tsakani na dake ne kawai banason wani ya sani” ta k’are maganar hawaye na cikowa a idanta. “Fannah na d’au alqawarin dukda bansan me kikeson fad’a min ba amman na d’auka barin sanar da kowa ba. Meya faru?” Hawaye na tsiyaya a idanunta tace, “Mami shine mutumin, shine…” sekuma ta fashe da kuka. Cike da rashin fahimta Mami ta d’agota daga jikinta “wani mutumi Fannah kuma waye mutumin?” “Mami shi, shine mutumin wallahi shine.” “Fannah ki kwantar da hankalinki ki sanar dani gwara-gwara” tasa hannu ta share mata hawayen nata. “Anas, Anas ne Mami shi ne mutumin.” Kai Mami take gyad’awa nufin tasoma fahimta. “Anas ne wani mutumi Habibti?” “Shine mutumin mafarki na, shine wanda yayi raping d’ina a Bama Mami shine silar komai” ta fashe dawani irin matsanancin kuka. Salatin Mami kawai ke tashi a d’akin kwanto da Fannah tayi a jikinta tana bubbuga bayanta tana fad’a mata dad’d’un kalamu sam takasa yarda da abinda takeji. Anas? Yanzu Anas dama shi yama ‘yarta kaca-kaca haka? Shi ya lalata wa Fannar ta rayuwa sannan kuma yazo ya aureta yanzu ya sako ta kenan komeh? Gaskia Anas yacika butulu. Seda ta tabbata kukan Fannah ya d’an lafu ta d’agota daga jikin nata. Cikin wani erin salo cike da tausayi ta kuma kwantar da ita a jikin nata tana bubbuga bayanta itama kukan taji na k’ok’arin fin k’arfin ta inta tuna kalar wahalar da Fannah tasha shekaru bakwai da suka wuce (masu karatu kuka lura zaku ga d’ayan wajen nasa 5 yrs mistake ne) yadda suka tsinceta kwance a walaqance. Kukan Fannah ne ya tsananta da k’yar tasamu tad’an rage kukan. Cike da tausayi Mami ta tambayeta “Fannah kin tabbata da hakan kuwa? Taya ma hakan ta faru? Had’uwanku da shi Anas d’in tun yaushe ace baki ganesa ba be gane kiba se yanzu? Anya kuwa Fannah ba b’atan kai kikayi ba? Ace yadda Anas yake da mutunci da hankali gakuma daga gida me mutunci yafito ace har yasan yayi raping mace? Habibiti anya kuwa?” “Mami wallahi shine…” Nan ta labarta wa Mami kap abinda ta karanta cikin diary’n Anas bata bar komai ba harda labarin Ummimi komai ta kwashe tabawa Mami dasu shaye-shayen da Anas yakeyi wanda bayayi yanzu sam bata bar komai ba. Mamaki ne yacika Mami sosai takasa koda furta ‘A’ duk wani haushi da takaicin datake ma Anas kuma gabad’aya taji ya koma kan Ummimi itace silar komai dukda kuwa shima Anas da nasa laifin amman Ummimi ce me babban laifi anan. Wace erin uwa ce? Ance Uwa Uwa ce amman ba’a sa jerin kalan su Ummimin Anas ciki. Talauci hauka ne? Taya zata tafi tabar ‘ya‘yan data tsuguna ta haifa taya zata k’yamaci abunda yafito daga jikinta? Aiga irin abinda ya haifo nan tasa d’anta yata aikata haramun ko kad’an bata ga laifin Anas ba laifin sa data gani na k’in tawakalli da qaddara, nak’in accepting faith nasa shine kad’ai laifin daya tafka ita bama wannan ba yanzu nan tabar sak’e-sak’en zucin da take. “Fannah yanzu ya kenan? Sako ki Anas yayi bayan da gaskiya ya bayyana? Shi ya koreki? Bayan shi ya rabaki da budurcinki ya koro ki yanzu? Kuma kice kar in sanar da iyayensa abinda yayi? Wallahi a’a Fannah inke bakisan ciwon kanki ba ni nasani ina wayata.” Hannunta Fannah ta riqo “Mami calm down Anas bashi ya koreni ba hasali ma yanzu haka nasan kuka yake saboda yana cikin hakan nafito na barsa.” Komawa tayi ta zauna “ban fahimce kiba Fannah.” “Mami ni na k’are zamana da Anas yak’i bani takarda na shiyasa nadawo hakan.” Mamaki ne kwance a fuskar Mami. “Kinsan ban fahimce kiba har yanzu” abinda ta iya cewa kenan. Nan Fannah ta kwashe labarin komai tabata. “Haba Habibti! Taya zaki tafka sokanci haka? Kina ganin akwai d’a na mijin da ze rik’e ki da mutunci kaman yadda Anas zeyi ne? Wallahi babu. Tunda yayi nadama Fannah gakuma dalilin dayasa faruwan hakan ai seki yi hak’uri ki yafe masa nasan da zafi amman hak’uri zakiyi. Ni wallahi na d’au ma ko shi ya koroki dan shine babban tashin hankali, Anas na sonki so na hak’ik’a ba kowa neba ze iya yin abinda yayi ko baki tab’ajin inda za’a kama yaro nama d’iya fyad’e amman ya bushar da ido yace ba shine ba kuma ba yadda aka iya haka za’a barsa amman Anas fah? Ya yarda shi ya miki kuma ahakan kin still yakeson ki kiyi tunani Habibti.” Ta k’are maganar tare da riqo hannun Fannah cikin nata. Hawaye take sosai “Mami bawai yafiyan bane barin iya ba tsab zan yafe masa, ni nama yafe masa komu muna ma Allah laifi kuma ya yafe mana muddin mun tuba kamar yadda Anas yayi na yafe masa har abada kuma zan sanar dashi amman Mami barin iya zama dashi ba again, Mami abinda yamin da ciwo.” Kwantar da ita Mami takuma yi ajikinta. “Shhhh! na gane halin da kike ciki Habibti is not easy you need some space, da zafi sosai ace bada sanin kiba kin auri wanda ya miki tabargaza da rayuwa amman Habibti yariga ya wuce lets face the future ko ba haka ba?” Kai ta gyad’a a hankali. “Good kuma kema nasan kinason Anas ko bahaka ba?” Nanma kai ta gyad’a. “Toh alhamdulillah zaki cigaba da zama ana har nan da lokacin da kikejin zaki iya komawa d’akin ki shikuma Anas zan masa bayani.” Kai ta d’ago a raunane “Mami banason sake-” katseta Mami tayi da wuri ta hanyan aza yatsanta kan bakin ta tana kad’a mata kai. “Karkice haka Habibti karki kuskura kinji? Dole zaki koma gidan mijinki d’akinki tunda be sallameki ba kuma tambayan takarda haramun ne kema kinsani tsinuwa ake gaggautawa duk macen datayi hakan, ki hak’uri Fannah nasan yadda kikeji amman hak’uri yazama dole kinada nan da sati biyu ki huta hankalinki ya kwanta kafin Babanku ya dawo, kinsan muddin yaganki anan ze tambaya dalili, ko kinason yagano Anas ne yayi raping naki?” Da sauri ta kad’a kai. “Masha Allah kinga sekiyi hak’uri Anas nasonki Fannah godiya yakamata kiyi wa Allah ki tuna da irin walaqancin da Farouq da Ya Khaleel suke miki ada dakuma gori acewarsu ba d’a na mijin da ze tab’a aminta ya aureki karkiyi ma Anas haka Fannah, abinda ya miki ya riga ya wuce hak’uri zakiyi wannan shine jarabawarki a rayuwa kinji? Accept it Mamana.” Kai ta gyad’a a hankali badan tanaso ba. Mik’ewan Mami yayi daidai da shigowar Afrah d’akin a gurguje. “Ya haka?” Mami ta tambayeta. “Mami Ya Anas ne yazo” ta fad’a tana haqi “kuma.. Kuma.. Mami kuka yakeyi wallahi Ya Anas yazo yana kuka.” “Subhanallahi to kekuma me haka? Sekace kinyi gamo da aljan.” Kukan Fannah ne ya katse Mami daga magana. “Mami wai meke faruwa?” Cewar Afrah bayan ta kalli Fannah. “Babu kifita ina zuwa” badan tanaso ba tafice. “Fannah wai baraki bar kukan nan ba? Ko sena sa kinbi Anas kukoma tare?” Kai kawai ta girgiza mata “taso muje mu samesa.” “Mami banaso dan Allah kije ke kad’ai dan Allah.” Ba tare da ta saurareta ba taja hannunta tare da dank’a mata hijabinta “sa!” ta buk’aceta a tsawace. Da shegen tsoronta batasan lokacin da tasa suka fito ba hannunta na rik’e cikin na Mami. Zaune kan tabarman da Afrah ta shimfid’a masa suka tarar dashi ya had’a uwa uba tagumi kamar wanda yayi ciwon amai da gudawa ya zube arana d’aya tsantsan tashin hankali kawai, ko noticing su Mamin ma beyi ba tsabagen yadda ya zurfafa cikin tunani seda ya jiyo muryar Mami tana kashe wa Fannah warning hankalinsa ya dawo a garesa. “Ya isa haka!” tace. A raunane ya d’ago jajayen idanunsa ya azasu kansu Fannah. Zamansa ya daidaita ayayinda suka k’ariso kan taburman suka zauna a nitse, Fannah na a lab’e bayan Mami ko d’ago kai ta kallesa bataiba dukda jin idanunsa da take akanta. K’ok’arin dakatar da hawayen nasa yake amman ya kasa Afrah dake lab’e jikin k’ofa Mami ta umarceta da ta fice wajen gida kuma koda Aiman ta dawo karta barta tashigo se in sun gama maganan da zasuyi ba gardama ta fice. A sannu Mami ta dawo da kallonta kan Anas tana ganin yadda yake hawaye kamar ba gobe kallonta ta kewayo kan Fannah itama same story sede ma kamar Anas yafita yin kukan. Daga bisani Anas ya soma magana cikin sautin kuka cike da nadama. “Mami I’m sorry dan Allah kiyi hak’uri keda Fannah daduk wanin danayi hurting sanadin abinda na ma Fannah kuyi hak’uri dan Allah I’m truely sorry.” Sam yi tayi kamar batada labari saboda so take ta tabbatar da ko eh dagaske Anas yake ya tuba. “Wani abu kenan Anas? Meya faru? Kai kuka Fannah kuka ku fahimtar dani meke faruwa nayi nayi Fannah ta sanar dani amman taqi.” Alokaci d’aya Fannah ta d’ago kai tana kallon Mami fuska d’auke da tambaya amman kuma se tayi shiru. Idanunta na had’uwa da na Anas tayi saurin sadda kanta. “Mami kina nufin Fannah bata fad’a miki mena mata ba?” ya tambaya cikin dashasshiyar murya cike da rashin yarda da abinda Mami ta fad’a mai. Kamar ya Fannah bata sanar da ita abinda ya faru tsakaninsu ba??? “Eh Anas nide na ganta da akwati gakuma kukan datazo tana tayi shin meya faru? Sakinta kayi neh?” “Mami barin tab’a sakin Fannah ba har abada barin tab’a iya rubuta mata takardan saki ba, ina matuk’ar son Fannah fiye da yadda nakeson kaina…” Sekuma yayi shiru yana tunanin koya sanar da Mami abinda ya had’asa da Fannah ko a’a. But what if Mami tak’i yarda da tuban da yayi kamar yadda Fannah tayi kuma fah? What if ta tilasta sa seya saki Flowersa fah? No bare iya ba, he will never let that happen on the otherside kuma yanason yayi clearing komai tsakaninsu ko halan inyayi hakan Mami taji k’ansa tabarsa da matarsa. Tunanin wani ra’ayi d’aya zebi yake. Shirunsa yabawa Mami daman magana “Anas kayi shiru” dankuwa ta riga ta yanke hukuncin cewa inhar Anas bare iya confessing laifin daya aikata ba to be tuba dagaske kamar yadda Fannah ta fad’a mata ba inkuwa yayi toh Fannah is his! ina fatan each and every fan tayi sallah lafiya, Allah maimaita mana Ameen, love you loads © MIEMIEBEE
 Hannu yasa ya share hawayensa tare da jan numfashi sannan ya soma maganar a hankali cike da nadama. “Mami tabbas na tafka babban kuskure a rayuwa na, kuskuren da har a yau ina nadaman aikatasa but believe me when I say this wallahi nima ba’a son raina hakan ya faru ba. Kuma wallahi tun ranan da abin yafaru nakasa samun sukuni a rayuwa na akullum ina tunanin wani hali na jefa yarinyar if only I can reverse time da nayi dan daidaita komai. Mami shekaru bakwai da suka wuce ni nayi raping Fannah, nine nan silar duk wani abin takaici da bak’in cikin rayuwa da kukayi witnessing dan Allah kuyi hak’uri…” Kuka ne yafi qarfinsa yakasa k’arisa maganan duk anan Mami batace masa ko k’ala ba ido ta zuba masa ga wani uban tausayinsa dake shiganta, Fannah dake gefenta ba abinda take itama se kuka daga bisani ya cigaba “kuyi hak’uri dan Allah Mami wallahi inason Fannah karku rabani da ita, ni na raba ta da budurcinta kuma zan cigaba da zama da ita kar a rabani da ita dan Allah na tuba…” Ya k’are maganar cikin sautin kuka. “Naji bayanin ka Anas kuma na gamsu hak’ik’a ka tuba kuma kayi nadama tunda har ka iya ka yi confessing babban laifi irin wannan tabbas ka tafka babban kuskure amman tunda kayi nadama komai ya wuce yanzu sede abu d’aya da nakeson sanar dakai shine shi muslimi da tawakalli aka sansa, Fannah tamin bayanin komai na maka k’arya akan bata fad’a min ba saboda inason ji daga bakinka inkuma tabbatar da eh ka tuba dagaske kuma kayi. Hak’ik’anin gaskia ba na mijin da zeyi zaman mutunci da Fannah kamar yadda zakayi Anas hasali ma mune da godiya zanyi iya qoqari na dan ganin Fannah ta koma gidanka amman barin tilasta mata ba saboda abinda yafaru a tsakaninku da ciwo Anas she needs some space kuma ni na yafe maka duk mun yafe maka ina fatan Fannah ma zata yafe maka wannan abu yazame sirri a tsakaninmu ko Babansu barin sanar dashi ba zan barku tare” tana kai nan ta mik’e haka Fannah ma. Da sauri ta dakatar da ita “A’a Fannah ki zauna ku gana kikuma yafe masa kinji Habibiti?” Kai kawai take girgizawa tana hawaye “yi hak’uri ki zauna” nan ta shige d’aki. Itama Fannar hanyan d’akinsu ta kama bi dan ko batasan me zata fad’a mai ba, kamar a kyaftawan ido Anas ya mik’e ya riqo hijabinta “Fannah dan Allah karki tafi I’m sorry please forgive me.” Har a yanzu takasa furta koda ‘A’ a nitse ya juyo da ita suna fuskantar juna yunk’urin sauk’a kan guiwoyinsa ya gwada tasa hannu da sauri ta tarosa cikin sautin kuka tace “Anas dan Allah kabari dan Allah stop it na gamsu da tubar da kayi kuma na yafe maka zaka iya tafiya.” Hannunta daya gwada tab’awa taja da sauri tak’unsa cikin hijabinta. “Fannah thank you, thank you so much yanzu ne zan iya samun sukuni a rayuwa na, I can be free now amman dan Allah karki barni Fannah lets go home please I love you.” “Anas I can’t dan Allah kabarni katafi please” tana kaiwa nan ta fisge hijabinta ta shige d’akinsu. Kuka sosai ya tsaya yatayi awajen Mami ce tafito ta riga basa hak’uri takuma tabbatar masa cewa Fannah zata dawo a garesa saboda tana sonsa da k’yar ta iya tura Anas ya tafi koda yafito beyi takansu Afrah ba motarsa ya nufa ya wuce a 360 isarsa gida keda wuya ya had’a akwatin kayansa dawani duk abinda ze buk’ata ya rufo gidan ya wuce paint house nasa daga ranan ya soma rayuwa achan abinci ma ba ci yake ba se in yunwa ta gasa sa. Koda su Ummie suka mai waya za suzo dubansa da Fannah kuwa k’arya ya musu yace sunyi tafiya basu gari. A kullum cikin tunanin Fannah yake har kamar ya fara zarewa dan yana zaune shi kad’ansa seyaji wai Fannah na kiran sunansa cikin sarqarqiyar muryarta me bala’in masa dadi hotunanta ne suka zamo masa farillah dan a kullum pictures nata na a gabansa yana kalla. Akwai lokacin da damuwa suka ma Anas yawa kad’an ya rage ba’a koma gidan jiya ba tunda ya sanar da Mustea halin da yake ciki Mustea ya k’arfafa masa guiwa kan yanemi syrup kawai yasha amman dan promise daya d’aukar wa Fannah ya hana kansa da k’yar, bare iya explaining how much yayi missing Fannah ba duk yabi ya rame ya fita daga kamanninsa gabad’ai office ma yabar zuwa duk yamusu k’arya yace yayi tafiya. Morning, afternoon and night messages kam bebar sending ma Flowersa ba dukda ba replying nasa take ba. Ya kirata har ya gaji amman bata picking koda ya kira ta wayar Afrah dan a had’asu ma nan bata karb’a. A takaice de rayuwar wannan masoya biyu ya jagule cikin sati biyun da sukayu batare da sunsa juna a ido ba. Ba aikin Fannah a kullum se kuka, bata tab’a sanin tanason Anas ba seda ta dena ganinsa a ganga da ita da daddare kuwa kullum tazo bacci seta rungumo pillonta setanaji kamar Anas nata ne. Wayarta na maqale a hannunta a koda yaushe tana karanta lovely heart touching messages da Anas yake mata sending wanda take matuk’ar jin dad’insu amman batajin zata iya replying nasa back aduk lokacin da tunanin abinda ya faru tsakaninsu yayi crossing mind nata. Ba yadda Afrah batai da ita ta gaya mata meke faruwa ba amman tak’i ta d’au alk’warin riqe wa mijinta sirri. Abinci kam ba takansa take ba se sunyi fad’a da Mami take chi shid’inma kad’an take tab’awa. Akoi lokacin da su Mami sukayi Eghusi soup da pounded yam tana gani kawai ta tuna da Anas ta tuna da yadda yakeson miyan kawai ta b’arke musu da kuka. *** “Fannah! Fannah!” Kiran Mami daga d’akinsu da Baba. Fannah dake d’akinsu miqe kan sallaya tana aikinta na kullum wato kuka tayi saurin share hawayen ta danko in Mami taganta zasuyi fad’a. “Na’am” ta amsa agigice tare da zabura ta nufa d’akinsu Baba chan ta samu Mami. “Bade kuka kike ba?” Cewar Mami kafin Fannah ta amsata ta cigaba, “karki damu na riga na ma Anas waya yau zezo ya d’aukeki kowa ma ya huta kinsan gobe Babanku ze dawo-” katseta Fannah tayi. “Mami dan Allah karkimin haka ko kwana biyu kibarni in k’ara anan.” “Nak’i Fannah ke wai bakida tausayi ne? Kinsan irin halin da kika jefa Anas tafiyarki kuwa? Yaron nan ya tuba mesa baraki yafe masa kukoma ku cigaba da zaman ku tare kamar yadda kuka saba ba? Ko wai acewarki akoi d’a namijin da ze kula dake ne kamar yadda Anas zeyi? Tun ina ganin abin naki da hankali na dena yanzu maza wuce ki shirya kayakin ki da La’asar Anas zezo ni na fad’a miki.” Har k’asa Fannah ta sauk’a tana had’a Mami da Allah amman ko a bakin zaninta ta fice tabar mata d’akin. Seda tayi me isarta sa’annan takoma d’akinsu takasa koda shirya kayakin nata zube take kan gado tana kukan da ita kanta batasan dalilinsa ba tana cikin haka taga call daga Anas bayan ya kwana biyu be kiranta se saqonnin dayake mata me zece mata yau? Ze zo ya d’auketa ko meh? Tana gani har yamata 2 missed calls tak’i picking bada jimawa ba ya turo mata message. Flower please don’t be mad I’m sorry and I love you #kisses Wani sabon kukan ta fara seda tayi ta godewa Allah sannan ta tashi ta jawo akwatin ta sam takasa cika kayakinta ciki daidai nan da shigowar Mami kenan baki ta sake ganin akwatin Fannah empty batako soma shirya kayakin nata ba. “Yanzu Fannah baki ko fara shirya kayakin naki ba bayan kinsan La’asar ya kusa?” A marairaice ta d’ago idanunta tana kallom Mami. “Mami dan Allah kibari ko gobe se in tafi.” “Mschww! maganan banza” wardrobe nasu tanufa ta bude tare da ciro kayakin Fannah kap tasasu cikin akwatin tayi zipping se roqarta Fannah ke amman ko ta kanta Mami batai ba tsab ta had’a mata kayakinta masu dotti tasasu cikin leda ta had’esu gu d’aya. 4:12PM Shigowar Anas gidansu Fannah kenan Mami kanta data gansa seda ta tsorata tana cewa Fannah ta rame ta lalace amman farillah ramanta yake aganga dana Anas sam kamar ba shiba bayan gaisuwa Mami ta sake basa hak’uri sosai sannan kuma ta masa nasiha daga nan tashiga dan fito da Fannah drama sosai suka riqayi sannan da qaqani qaqa tasamu ta fito da ita, akwatin ta Anas ya amsa. Wa’azi me ratsa jiki Mami ta musu sosai duk jikinsu ya sake mutuwa barin ma Fannah, da k’yar tafito daga gidan iya bakin k’ofa Mami ta musu rakiya ta koma ciki. “Fannah please lets go kinji? Kiyi hak’uri kibar kukan nan please lets go.” Sam tayi kamar bada ita yake ba sun kusan minti biyar tsaye wajen ganin batada niyyan ko motsawa ya finciko hannunta. “Anas ka sakeni ka sakeni nace” da dambe ya k’arisa motan da ita ya bude’e mata gidan gaba yasata sannan ya sanya jakarta a baya yazagayo shima ya shiga. Tunda suka fara tafiya take masa kuka a mota koda suka isa gida kuwa tafito bata ce masa komai ba akwatinta taciro ya karb’e mata. Shigarta ciki ta nufa d’akinta ta baje kan gado, bayanta yabi yakai mata akwatinta. “Flower kinci abincin rana?” Ya tambayeta baya ta juya masa. Nufowa gabanta yayi nanma ta sake juyawa “Flower meh kikeson ci? Yi hak’uri ki fad’a min” nanma banza dashi tayi haka yata suratansa har yagaji bata tanka sa ba seda ya fita ta mik’e tashiga bayi ta watsa ruwa fitowarta yayi daidai da shigowar Anas da plate na kaza a hannunsa. A farko tayi niyyan komawa cikin bathroom d’in dankuwa gajeren towel ne ajikinta daga baya data tsaya tayi tunani cikin d’an k’ank’anin lokaci kuwa setaga yin hakan bayida amfani tunda ya tab’a ganinta ba kaya ma a jikinta. Ignoring nasa tayi ta nufa wajen dressing mirror har anan bebar kallonta ba he can’t explain how much he missed her body. Daga bisani ya girgiza kai “Fannah I’m sorry bansan…” Sekuma yayi shiru yaja k’ofar ze rufe kenan ta ce dashi “ba komai.” ba tare da ta kallesa ba. Sam be yarda da abinda kunnuwansa suka jiye masa ba be d’au Fannah zata sake masa magana bama, lallai inta haka he has a chance. A nitse ya k’ariso cikin d’akin “gashi incase you are hungry eat please” ya ajiye mata plate d’in kan dressing mirror. Seda ya kai da bakin k’ofa sannan tace masa “nagode.” Dad’i sosai yaji “you are welcome Flower.” Yana kaiwa nan ya fice yakoma parlour ya zauna yana jirar ko zata fito. Bada dad’ewa ba k’ofarsu yayi k’ara yana dubawa yaga sabin fuska guda biyu da alama ma mata da miji ne wani button ya danna se main gate ya bud’u nan ya fito dan tarerayarsu. Bayan ya shigo dasu sika gaggaisa. “So gidanmu ne kusa da naku by the left lokacin da kuka zo nan munyi tafiya nida HASKE NA dawowan mu kuma mukaji wai kuma kunyi tafiya d’azu Haskena kecemin ta ga shigowarku shine nace mata yakamata mushigo mu muku sannu dazuwa.” Cewar mijin. “Suna na MUS’AB wannan kuma is my wife NAINAH” yajuyo ya sakar mata dawata lallausassar murmushi, murmushin ta miyar masa itama. Haka kawai se Anas yaji sun burgesa se ya tuna lokacin da suke a haka shima shi da Flowersa he misses her alot, da k’yar ya iya bud’a baki yayi magana drinks yayi serving nasu ganin Fannah batada niyyan fitowa ya shiga mata managa mik’e kan gado ya tarar da ita. Bayan ya k’arisa ya zauna agefenta yace, “Flower munyi bak’i neighbours namu ne suka shigo mana inda zaki iya fitowa seku gaisa da matarsa.” Kai ta gyad’a masa. Daman da hijabi jikinta bayansa tabi suka fito daya gwada yunk’urin riqe mata hannu kuwa setaja da baya. “Flower just for this once se mun nuna musu we are not on good terms ne? Please corperate” Sam tak’i barinsa ya tab’a mata hannu haka ba yadda ya iya suka fito kai a rabe idanunta basu sauk’a ako inaba se hannun Mus’ab da Nainah data gani a had’e se hirarsu suke suna dariya gwanin sha’awa a hankali ta dawo da kallonta kan Anas ita kanta she miss yadda suke a da. Ahakan suka k’ariso parlour’n suka zauna a seperate kujera tun anan hankalin Mus’ab yabasa da akwai matsala bayan sun gaggaisa cike da dabara ya buk’aci Fannah dasu shiga ciki da Nainah, hakan kuwa akayi. Alokaci guda Fannah taji san Nainah yashigeta ganin yadda take small of age amman ga hankali da ladabi da biyayya sede ashe ba Mus’ab ne kad’ai yagano abinda ke faruwa tsakanin Anas da Fannar ba har ita Nainan ma tayi. Suna zaune kan gado bayan Nainah tagama yabawa d’akin Fannah dama gidan entirely tayi gyaran murya. “Aunty Fannah” tace da ita. “Na’am Nainah” ta amsata. “Ba shisshigi ba Aunty amman senaga kamar da akoi matsala tsakaninki da Uncle.” Bata bar Fannah tayi magana ba ta cigaba “shi zaman aure se hak’uri Aunty koni da kike gani na nan inada kishiya kuma bawai shiri muke da ita ba sau dayawa tana cewa seta kasheni hakan be bani daman fad’a da miji na ba ina sonsa kuma shima yana sona kamar yadda nasan kuma kuna son junanku.” Wa’azi sosai Nainah ‘yar shekaru sha bakwai ta tama Fannah liqis ta kashe mata jiki gakuma wani kunyan dataji ache k’anwar bayanta tamata gyara bisa ganganci irin nata dan ko bata tambaya ba tasan Afrah ta girmi Nainah. Godiya sosai Fannah ta mata tare da bata kyautan wasu bangles had’ad’d’u. Shima Anas tun zamansa da Mus’ab ya riga masa wa’azi da nasiha sosai. ** Bayan sun yi masu rakiya suka dawo ciki har Fannah takai da bakin k’ofar d’akinta sekuma ta tuna alk’awarin data ma Nainah nacewa zata bawa Anas hak’uri bisa hurting nasa datayi. Seta juya zata masa magana sekuma ta kas, shiko yana tsaye a tsakar parlon ya k’ura mata ido ji yake kamar yaje yayi hugging nata ya fad’a mata how much he loves her. Da k’yar ta iya kiran sunansa muryarta se rawa take. “Anas” daman jira yake ya amsa “na’am Flower” tare da takowa har gabanta dududu space daya rage a tsakaninsu befi inches shida ba. Kanta ta sunkuyar “Anas I’m sorry kayi hak’uri” ta fad’a dashi sincerely. Hannunta duka ya rik’o cikin nasa d’aya yana murzawa a hankali tare da mata wani erin kallo alokaci guda yaji bak’in cikinsa duk sun gushe, murmushi ne fal kwance a kan fuskarsa. Dad’i yaji sosai da bata hanasa rik’e mata hannu ba. © MIEMIEBEE
 D’ayan hannunsa ya aza a hab’arta tare da d’ago fuskartata. “Flower you don’t have to be sorry baki min komai ba, ni ya kamata in baki hak’uri and not the other way round I’m sorry kinji?” Kai ta gyad’a ba tare da tabari sun had’a ido ba. “Flower baraki kalleni ba?” ta kad’a masa kai. “Then look at me” ba musu ta miyar da kallonta kan kyakkyawar fuskarsa, murmushi ya saki mata yana kallon cikin idanunta. “I miss your body can I hug you?” Hannun ta taraba daga nasa tare da gyad’a masa kai nan ta rungumeshi shima haka, hugging juna passionately “I miss you too Anas.” Sun d’au tsawon lokaci suna manne da juna suna jin dad’in k’amshin jikin junansu sannan daga bisani tayi breaking hug d’in tare da juyawa zata shiga d’akinta, hannunta ya riqo da wuri “Flower muje muci abinci kinji?” Kai ta girgiza masa nufin bazata ba. “Flower bakiya jin yunwa?” Ta gyad’a kai “please muje nasan kinaji lets go.” “Barin jeba” ta fad’a tare da shigewa d’akinta. Badan yanaso ba yajuya ya shiga d’akinsa ya canza shiri bayan ya fito ya rufo k’ofar juyawansa kawai ya tarar da Fannah tsaye gefen motarsa idanunsa ya sosa da kyau dan tabbatar da abinda yake gani. Murmushi ta saki masa “yi sauri ka bud’e min rana.” Kasa danna security d’inma yayi duk ya kid’ime sosai navy blue hijabin dake sanye jikinta ya mata kyau seda ya gama k’arisowa gabanta ya tab’a hannunta dan tabbatar da ko eh dagaske itan ce sannan ya bud’e motar mata da kansa, bayan tashiga ya rufe sannan ya zagaya shima ya shiga suka fice. Hira d’ad’d’aya yake mata wanda ba duka take amsa shiba har suka isa inda zasu. Daidai gaban DERIBE HOTEL suka tsaya dan chan yayi reserving bayan ya bud’e mata k’ofa ya rik’o hannunta, shigansu ciki taga yayi reserving as always. Cikin wani irin salon da bare basa haushi ba tace, “Anas baka iya chin abinci se kayi reserving?” Kai ya gyad’a mata “why?” Ta tambayesa “saboda banason hayaniya.” ya amsata. “Kasan meh?” “A’a meneh Flower?” “Inason yau muje inda bakayi reserving ba muci abinci inason ka koyi cin abinci in public its fun.” Sam beji dad’in wannan shawara na Fannah ba haka yake bai iya cin abinci in public ba, ko days back dayake boarding school sede ya taho da abincinsa hostel yaci inkuma aka hanasa, abincin da bayya chi kenan. “Anas Habeebi” ta kira sunansa ganin baida niyyan magana. “Bakaso?” “Inaso Habibti lets go” ya mata k’arya nan suka juya GRAND PINNACLE HOTEL LUXURY suka dosa bayan sunyi placing order bada jimawa ba abincin nasu ya iso tun anan yanayin Anas ya canza daya juya yaga mutane anan mutane achan ga wasu yara masu uban surutu se distracting nasa suke abinda ya wasa kenan. Har takai spoons biyar Anas be tab’a nasa ba. “Anas mesa baka chi?” “Flower the truth is am not used to it ban iya chin abinci cikin mutane ba.” Qasaitacciyar murmushi ta sakar masa tare da matso wa kujeran dake kusa da nasa ta zauna spoon d’aya ta d’aga ta kai masa baki. Kallonta yake kawai cike da adoration wani sabon santa na sake shigansa. “Ahhh” ta buk’ace sa. Murmushi ya mata sannan ya bud’e bakin nasa ta basa, haka ta riga basa seda yace ya k’oshi anan ne itama ta jawo na ta plate zata cigaba daci amsar plate d’in yayi “my turn my lady.” “No nikam zanci da kaina.” “No Flower let me kinji?” Kai ta gyad’a masa haka yariga bata itama seda tayi nak! “Look around you” ta buk’ace sa bayan ya juya ya k’are wa mutanen cikin kallo sosai yaga lessons kowa da kalan rayuwarsa ga masu jiran mutane su gama cin abinci su d’au nasu suma su samu su chi, da wanda suke sharing abincin plate d’aya mutane de daban-daban. “Kaga yawan shiga cikin jama’a nasa mu sake godewa Allah cikin yanayin da muka tsinci kanmu for instance kalli wanda suke tsaye bakin k’ofa achan ko kud’in abincin ma basuda kaga anan se ka sake godewa Allah right?” “Right Flower” ya amsata cike da jin dad’i “Alhamdulillah!” nan ya biya musu kud’insu da suka fito kuwa irin mutanen wajen nan duk yabisu ya rarraba musu kud’i dad’i sosai Fannah taji tun daga ranan Anas ya koyi chin abinchi cikin jama’a although atimes seyayi reserving waje still. Koda suka dawo gida shi ya taimaka mata ta had’a kayakinta cikin wardrobe nata bayan nan suka miqe kan gado suna hira abinsu gwanin sha’awa Fannah na viewing pictures nata da Anas yakeda su cikin wayansa wanda kap batasan lokacin daya d’aukesu ba tana cikin haka Angel ta soma kira nan ta miqa wa Anas. Bayan sun gaisa Amal tasoma k’orafi. “Shikenan Ya Anas tunda kayi aure kadena sona nasani yanzu se Ya Fannah kakeso.” Dariya sosai shida Fannah sukayi “inji wa Angel? I love you both, no one like you kinji? Kibar had’a kanki da Fannah.” Amsar wayar Fannah tayi. “Amal karki ce haka kinga nima yanzu mukayi fad’a da Anas cemin yayi yafi sonki akaina.” “Kai Ya Fannah bawanin nan.” “Dagaske Angel na Ya Anas.” Dad’i sosai taji toh shikenan ba-bye tayi hanging. “Toh Mr. Fauzi kaji Amal tana k’orafi gobe yakamata ka mata shopping ka kaimata.” “Angama Mrs. Fauzi your wish is my command.” Oh hakane yanzu? Ko ka manta kaine Boss d’ina? “Ada kenan Flower but now kece Boss… Me kikeyi?” ya tambaya ganin ta seta cameran wayarta kansa. “Abinda ka saba min, now I have 5 of your pictures” “LOL kin rama kenan? Let me see them” “Fad’i gaskia de so kake ka goge barin bada ba” tana kaiwa nan ta miqe da sauri ya jawota ta fad’a jikinsa k’ok’arin k’wace wayar yake ta duk’un’kunesa cikin hannunta tasa a kayanta acewarta ahakan bare iya amsa ba. Murmushi yasaki sannan yasa hannu cikin kayan nata ya zaro wayar sanadin haka yasata dariya se kamar chakulkuli yake mata. Fuska ta maraice “karka goge please kaji Habeebi.” “Tell me you love me.” “In nafad’a baraka koge ba?” “Yes Baby” ya gyad’a mata kai. “Okay Mr. Fauzi I love you I love you so much” tayi pecking nasa a kumatu. “Bani toh.” *** 5:20AM Bayan sun idar da Sallah suka koma suka kwanta kamar yadda suka saba a kullum. Hannunsu ya had’a “Flower yau bakiyi mafarki ba” “Yes I’ve found you already ai bawani mafarki kuma.” “I’m sorry kinji Flower for hunting you like that.” “Nima I’m sorry lets sleep kasan akoi office yau.” “Ni barinje ba.” “Lallai kuwa Mr. Fauzi kafara wasa da aiki.” “I don’t want to leave you Flower.” _“INA TARE DA KAI_ My Lion am never leaving you.” Dad’i sosai yaji yayi pecking cikin gashinta. “Aha! I have a suprise for you yau around 1:30PM zanzo in d’aukeki kinji?” “Naji meh suprise d’in?” “Ai ba’a fad’an suprises Flower just keep calm.” Ahaka suka koma bacci. 7:40AM “No goodluck kiss Flower?” Cewar Anas suna tsaye bakin k’ofa hannunsa rik’e da nata d’ayan kuma lunch nasa. Murmushi ta saki masa “babu sakemin hannu inkoma ciki take care of yourself for me, I love you.” “You must kiss me first.” Kafad’a ta buga masa “seka dawo.” “No ni yanzu nakeso” “Then ka fad’a min meh suprise d’in ko hint ne kabani kaji Habeebi then I will kiss you” ta k’arisa maganan hannunta biyu zagaye a wuyansa. “Flower suprise ne I can’t tell you.” “Shikenan nima I can’t kiss you” hannayenta ta cire daga wuyansa, da sauri ya zagaye nasa hannun a ‘yar kunkuminta “you must Flower.” murmushi ta masa sannan tayi d’agel tayi grabbing lips nasa batasan a lokacin da ta kai hannayenta cikin gashin kansa da yayi styling ba d’azu kap ta hargitsa masa dan yadda kissing nasa ke tafiyar mata da imani se chan da tayi pulling out ta masa murmushi, shima murmushin ya mata. Idanunta na sauk’a kan gashinsa ta waro idanu. “Ya Salam Habeebi kaga gashinka its all a mess!” “Toh ai kece, ke kika hargitsa min.” “Toh ai kaine I lose control whenever I’m kis-” sekuma tayi shiru takasa k’arisa maganan dan wani kunyan dataji ya ratsa ta ita kanta batasan ya akayi ta fad’i wannan maganganu ba. Kai ta sunkuyar a yayinda yasa hannu a k’ark’ashin hab’arta ya d’ago fuskarta, fuskarsa d’auke dawani shu’umin murmushi. “Flower me kikace?” Kamar wacce baratayi mgana ba kuma setace “babu zakayi latti katafi kaji?” “Se kin d’ago idanun ki kin kalleni ki kuma nanata min abinda kika fara fad’i dazu zan tafi.” Sun d’au minti uku suna tsaye ahaka ganin baida niyyan tafiya tasa ta d’ago idanunta ta azasu kansa. Hannu ta d’aga ta soma gyara masa gashin kansan duk anan yana binta da kallo seda ta gama sannan ta maido da kallonta garesa. “Habeebi I lose control whenever I’m kissing you.” “Mesa?” ya tambayeta “Because…” ta aza yatsanta kan lips nasa “they are sweeter than honey.” Sam seji yake kamar a mafarki anya kuwa wannan ce Fannar daya sani me uban kunya? “And yours too Baby.” Murmushi tamasa “off you go nima I have a suprise for you se in ka dawo.” I love you sukayi exchanging sannan ya fice farin ciki fal kwance a fuskarsa. By 12:30PM Fannah tagama had’a girkinta wanka tashiga da wuri-wuri tayi ta fito ta shirya cikin wani A shaped doguwar riga na lace, light makeup tayi applying ta kama gashinta gu d’aya sannan ta sanya hijabinta violet akai. K’arfe d’aya nayi ta idar da sallah tasoma zaman jirar Anas yau tunda ya tafi office be kirata ba ko aiki ne ya masa yawa oho. 1:40PM Anas ya dawo gida d’aukanta, kasa ignoring kyan da tayi yayi daya sata a ido seda ya sata gaba ya riga d’aukanta pictures, sam yak’i sanar da ita ina ze kaita sede daga baya taga sun fara dosan Enterprise nasa. “Habeebi meh zamuyi a Enterprise naka kuma?” “Kede tsaya ki gani mana Flower” kafin su kai da Enterprise d’in ya tsaya tare da ciro wani d’an bak’in k’yalle. “Turn around” ya buk’ace ta. “Meh zaka min da wannan kuma?” “Just trust me Flower.” Ba gardama ta juya ya d’aure mata ido sakwa-sakwa yadda bare dameta ba. Bayan sun k’arisa ciki yayi parking sannan yafito da ita a hankali daidai gaban Enterprise d’in ya tsaya da ita. “Are you ready?” Ya tambayeta. Kai kawai ta gyad’a. “Okay” anan ya kunce k’yallen. Kallonsa take a yayinda ya mata nuni da idanunsa akan ta kalli sama hakan tayi. Mamaki ne sosai ya cikata ganin sunan Enterprise d’in Anas ya canza daga FLAMES Enterprises zuwa FAHNAS Enterprises. “Woowww!” Ne kad’ai abinda bakinta yake iya furtawa har ayanzu takasa believing. “Habeebi this is amazing yayi kyau sosai, OMG! FAHNAS… me ma’anarsa?” “FAH-FANNAH NAS-ANAS.” “Awwwn! This is so romantic yayi kyau Allah k’ara bud’i ya karemin kai Baby I love you.” Hannunsa ya zagaye a kunkuminta daga gefe “I love you too Flower.” peck ta manna masa a kumatu. “Yaayi kyau sosai and I love it, much appreciated” wayarta ta ciro ta d’au gaban Enterprise d’in hoto. “So zamu koma gida kokuma zaka zauna anan se 4 kadawo gida?” “Kinason in biyoki mukoma gida yanzu?” “Ofcourse yes Habeebi.” “Toh muje Mrs. Fauzi” dad’i sosai taji bayan isowarsu gida duk suka rage kayakin jikinsu. “Ina suprise nawa Flower?” “Yana nan a dining table muje muchi abinci.” Hannunsa ta riqo bayan sun k’arisa dining ta bud’e d’aya daga cikin manyan flasks d’in tuk’ek’k’en tuwon semovita ne had’ad’e ciki nan tayi serving nasu duka shide Anas ya zuba mata ido tana bud’e flask na miyan ya toshe hanci tare da miqa wuya dan tabbatar da abinda zuciyarsa ke saqa masa. “Flower what is this?” “Meh kuwa ? Abinci mana Babe.” “Da gangan kikayi hakan koh? Eww! Close it please kinfa san banason wannan miyan kukan.” Nan ya miqe da wuri ta sake zaunar dashi. “Wai me haka Habeebi? Se wani toshe hanci kake sekace something is smelling.” “This is smelling Flower” ya nuna flask d’in “dan Allah ki rufe.” D’ago flask d’in tayi ta matso dashi gabansa tare da sauk’e hannunsa daya toshe hancin sa dashi daga fuskar nasa. “Flower stop it please” sewani yamutsa fuska yake. “Wannan ne suprise d’in? Na gani thanks sosai zanje in dafa noodules yau kowa yayi dining shi kad’asa kuma kisani nima se na rama ewww!” Ya watsa wa miyan kukan kallo. Kafin ya miqe ta dakatar dashi ta hanyan zama kan cinyarsa. “Flower yau neman tsokana na kike ko? Tashi please warin ya isheni.” “Haba Babyn Fannah, my Habeebi, my lion, my life and happiness” ta zagaye hannayenta a wuyansa cikin wani erin salon dake sosa masa zuciya. “Wani wari kuma miyan yakeyi? Trust me Allah ka tab’a kaji da akwai dad’i.” “Flower baya min dad’i please ki rufe.” “Yi hak’uri Baby ka tab’a kaji?” Kai ya girgiza mata “I will kiss you over and over and over yau kaji?” Nanma kai ya kad’a. Haka itama tak’i tashi masa daga cinya miyan ta zuba kan d’ayan plate d’in ta wanke hannunta sannan ta gutsira kad’an daga tuwon ta had’a da miya takawo masa baki. Hannu yasa da wuri ya toshe hancinsa “Flower please kibari” d’ayan hannunsa yasa ya shure hannunta baya aiko ta maidoshi gabansa. “Open up mana Baby.” Kai kawai ya kad’a mata, dabara ce ta fad’o mata. “Okay toh naji baraka chiba zan dafa maka noodules” nan ta miyar da plate d’in ta ajiye kan dining. “Toh ta-” bata bari ya k’are maganan ba ta cusa masa tuwon a baki nan danan ya fara yunk’urin cirowa “uhm-uhm Habeebi” ta kad’a masa kai tare da toshe masa hanci. “Had’e kaji Babe in bahaka ba barin sake maka hancin ba, sekace baturen gaske kace bakacin miyan kuka! Oya had’iye” da k’arfin da Allah ya bata ta matse hancin nasa ko kasa koda k’watan kansa ya yi. Idanunsa sun kad’a sunyi ja dan rashin numfashi sam yak’i had’iwa ganin ba mahalicci se Allah ya rufe ido ya had’iye badan yanaso ba. Se anan ta sake mai hancin tare da miqa masa ruwa tas ya kwankwad’e “tashi min Flower” ya buk’ace ta yana k’ok’arin k’irk’iro amai. “Ina zakaje?” Ta tambayesa. “I need to throw up kitashi please.” “Ai ina nan Anas yau seka koyi cin miyan kukan nan ina zanzo in kaika? Bakacin cous-cous, d’an wake, kuka, kub’ewa komai ma bakaci se abincin turawa? Gomma ka kwantar da hankalinka dan yau sekaci tuwon nan.” “Naji zanci tashi toh.” “Saboda kasamu chance na guduwa ba? Ba inda zani” nan ta d’au plate d’in ta sake had’a tuwon da miyar “oya open up.” Se toshe hanci yake har a yanzu yak’i bud’e bakin “Flower wai d’anki ne ni? Kibari in kika haihu sekiyi ma d’anki wannan forcing d’in ni baran ci ba.” “Naji amman kafin in samu d’an da zan masa zan fara akan Daddynsa oya open up.” “Naqi.” “Aw in sake toshe maka hancin kenan koh?” “Flower manaaa.” ya maraice fuska. “Yi hak’uri ka bud’e Baby na…” seda ta kusan kuka sannan Anas ya yarda ya bud’e bakinsa ta basa bayan ta basa kusan sau biyar sekuma yaji kukan ya masa dad’i compared to wanda ake musu a boarding house lokacin wanda sanadin rashin dad’insa yabar cin kuka kwata kwata. © MIEMIEBEE
 Sede still bayason miyan kukan yafison ire-iren abincin daya saba ci a London su burger, pizza, bufallo wing, glorified rice, louisiana da sauransu. Datazo sake basa hannunta ya rik’e “na k’oshi a banza bakin mutum ya fara warin kukan nan” “Ai sekayi brushing bale ma bawani warin nan, open up” “Na k’oshi” “Dameh?” Ta tambayesa. “Wannan” ya nuna mata da yatsa. “Haba Habeebi guda biyar fa kacal kachi yi hak’uri ka k’ara nasan kana jin yunwa yi hak’uri Baby” haka tariga lalashinsa kamar d’an yaro tana basa abincin da wayo cikin k’issa kafin su hankara har yagama plate nasa bakinsa ta wanke masa da kyau se anan ta tashi mai daga chinya dan chin nata itama. Tana tashi shima ya mik’e zasa toilet ya k’wak’ulo amai. “Mine ina zakaje? Bade toilet ba! Please karka je ka harar da abincin nan.” “Ohh! Flower ni barin iya zama da wannan kukan acikina ba.” “Nasani hak’uri zakayi Habeebi na zauna a parlour kajirani I want us to play a game today.” “Wani game?” “Just wait for me.” “Toh naji excuse me” nan ya juya. “Baby promise baraka je ka harar ba.” Shiru yayi yana nazari. “Baby please.” “Okay okay I promise shikenan?” Nan ta gyad’a kai bayi ya nufa yayi brushing shi wai a dole miyan kuka nasa bad breath (warin baki) dawowansa ya zauna kan d’aya daga cikin sofas na parlour’n tare da kunna cinema. Kasa kallon news d’inma yayi se kallon Fannah yake yadda take chin tuwon sekace wani abun arziki me dad’i. Da idanunsu ya had’u ya wani yamutsa fuska “zaka k’ara neh?” Da sauri ya kad’a kai “a’a banaso thank you.” Murmushi ta saki “karka damu gobe dashi zamuyi breakfast zanyi mana d’umamensa.” Blue eyes nasa ya k’wararo “zaki d’uma meneh?” “D’uma wannan ko bakasan meh d’umameh ba? Zan sake reheating tuwon mana muyi breakfast dashi.” “Keda wa?” Ya sake tambaya “Nida Habeebi na.” Kai ya gyad’a “lallai kam zaki nemi new Habeebi dan ni barinci d’umamen wannan abin ba.” “LOL” tad’an murmusa “ai kai ne kad’ai Habeebin nawa, trust me d’umamen ma yafi dad’i yafi taste kasan da me yau zamuyi dinner?” “A’a bansani ba and banason sani ki rik’e please ni kawai zansha coffee in kwanta barin chi komai ba.” “Kai Habeebi d’an wake de zan mana inyi slicing egg and cabbage akai its way yummy. Gode kuma in Allah ta kaimu miyan kub’ewa zanyi” Yamutsa fuska yayi “a’a Flower please kiyi abinki ke kad’ai naji yunwa ko sausages zan soya inchi.” “Oho nide d’an wake zamuci da Baby na.” Be sake ce mata komai ba har tagama chi ta tattara dining d’in sannan ta dawo ta samesa da paper dakuma biro biyu a hannunta, gefensa ta zauna. “X and O zamuyi.” Yana jin haka ya kad’a mata kai dan ko sam be iya game d’inba bayason kuma yayi losing a gabanta ta raina sa kokuma ya fad’a mata be iya ba ta masa dariya. “Baby kayi shiru.” “Barinyi ba ki kawo wani game daban wannan ba dad’i.” “Toh Habeebi ni shi kad’ai nasani Allah da dad’i lets try kaga.” “Ohh!” dabara ta fad’o masa “ni se yanzu ma na tuna inada aikin da yakamata inyi attending to a laptop” ya k’arisa maganan yana k’ok’arin miqewa hannunsa ta riqe ta dakatar dashi “Habeebi I can tell you are lying kode kana tsoron kar inyi winning naka ne” tamasa gwalo. “Ke kiyi winning d’ina? Impossible lets play it muga.” Nan da nan ta zazzana musu sannan ta mik’a masa pen d’aya zuciyan Mr. Fauzi fa se bugu yake dan sam be iya game d’in ba at all. “So deal d’in shine if I win zan d’aneka anan” ta nuna goshinsa. Shiru yayi yana nazarin yau d’ani nawa zesha gun Flower. “Baby kayi shiru ko kanajin tsoro ne? Karka damu I’ll take it easy on you” tana masa wani shu’umin murmushi. Ina irin shikuma bari ya nuna mata shina miji ne bayajin tsoron nan. “Ba tausayi in na nad’e ki se goshin naki yayi ja.” “Haka kace?” “Yes Flower haka nace.” “Fine lets start.” Shi yafara placing X bayan yayi itama tasa O kafin ya hankara Fannah ta masa baki biyu kafin yace meh tariga tayi crossing ta chi sa. Tsalle ta daka “yeyy! I won nachi!” “Taya ya kikaci? Ai wannan cuwa-cuwa ne niban yarda ba.” “Kamar ya Baby? Gashi nan nacika kuma kana gani bring your forehead.” “Gaskia ban yarda ba asake wani kinyi magud’i anan.” “No vex asake wanin.” Hankali sosai ya miyar yana coffan yadda tayi d’azu shima dan mata baki biyu sede nan ma kafin ya hankara tasake chi nanma tata daka tsalle “yes!! yanzu ka yarda na cika?” “Ni fa gaskiya ban yarda ba kina min cuwa-cuwa ne kawai.” “Koma me ka kawo goshinka saboda deal ne.” Fuskarsa ya ajiye mata daidai tsakiyan goshin sa tasa hannu ta danna masa d’ani me uban zafi take wajen yayi pink. K’ara ya saki “argghhh!” “Aww” tayi pouting bakinta “da zafi ne Baby?” “Nima bansani ba” ya watsa mata kallo. Zuciya yayi “lets play again I must win this time.” Nanma da suka buga ita ta sake chi haka ba yadda ya iya ta ya sake a jiye mata goshinsa ta d’anesa fiye dana d’azu nanma k’ara ya saki sosai amman kamar maye yak’i hak’ura shi a dole seyaci ta aiko sun buga har sau 7 duk Fannah kechi gashi ko saurara masa batayi tunda yace no pity haka take d’aninsa da zafi-zafi goshin Anas daga fari yakoma pink yanzu jazir ya koma duk yabi ya galabaita. “Mschww! Ni na fasa game d’in.” a fusace ya mik’e yashiga d’akinsa. Murmushi kad’an tasaki sekuma ya bata tausayi ga dukkan alamu be iya game d’in bane daman shegen ajeboncin sannan dama ina ze iya? K’aramar hand towel da warm water tasa a bowl tabi bayansa mik’e kan gado ta tarar dashi yana ganinta ya juya mata baya a nitse ta k’ariso ta ajiye bowl d’in akan side drawer sannan ta zaro robe daga ciki ta ajiye a gefe. “My Baby” ta kira sunansa. Ko juyawa ya kalleta ma beyi ba. “Habeebi yi hak’uri ka juyo kaji inga goshin naka.” Nanma shiru ya mata. “Yi hak’uri mana Baby.” “Me zaku gani? So kike ki gani kimin dariya komeh?” “Ko kad’an Habeebi taya zan maka dariya? Gani zanyi kaji yi hak’uri kajuyo.” Ganin baida niyan juyawa tasa hannu ta juyo dashi a hankali tare da aza kansa kan cinyoyinta ita kanta seda ta tsorata ganin abinda ta mai da goshi, wani erin fata ne dashi sekace na mace da baison wahala haka? “Ya Salam Baby I’m sorry bansan haka goshin naka yayi ba.” hannunta ta miqa ta tab’a goshin nasa k’ara ya saki sosai. “I’m sorry kaji? Kai kace fa no sympathy ba tausayi shiyasa.” “Toh kuma seki yarda? Aikinsan in nine barin miki haka ba.” yayi maganar kamar wanda zeyi kuka. “Baby I’m sorry da ka fad’a min baka iya ba ai.” “Flower its embarrassing ace ban iya playing simple game kaman wannan O and X d’inba.” “Baby its X and O ba O and X ba.” “Naji whatever” kansa ya d’ago daga cinyar nata ze juya mata baya kenan ta rik’o hannunsa. ”Don’t be mad kaji Habeebi? Game ne kawai ba komai ba I’m sorry kuma bar kan naka kan cinya na zan d’an matsa maka wajen ne” “Kin manta kwanaki da cintoyin sukayi tsami ne?” “Ina sane ai ba dad’ewa zakayi akai ba tsaya” Batare da yace da ita komai ba ta matse towel d’in ta aza kan goshinsa da wuri yasa hannu ze d’aga dan azaba ta dakatar dashi “sorry kaji? Nasan da zafi hak’uri zakayi” haka tata matse masa a hankali yana sakin k’ananun k’ara time to time bayan data tabbata ta matse masa ta bud’e robe d’in ta lak’uta tasa a goshin nasa tana fara murzawa yayi saurin d’aga hannunta. “Flower ya isa haka barshi.” “Habeebi ka tsaya ko kad’an ne in mirza in bahaka ba ze iya kumbura fah” “Toh ai laifin ki ne, ke kika riga d’ani na sekace ba mijin kiba” “Baby nace I’m sorry be wuce ba? yanzu tsaya mu shafa maka semu kwanta mu huta… Yawwa Baby naa” a hankali take shafa masa har tasamu ta gama taje ta zubar da ruwan sannan ta dawo suka d’aura alwala tare da yin Sallah. Gado suka haye suka kwanta tana a gefensa suna fuskantan juna. “I love you Anas.” Shiru ya mata shi a dole har yanzu yanajin haushi. “Baby baraka cemin I love you too ba?” Kai ya gyad’a. “Har yanzu wai baka hak’ura ba?” Nan ma kai ya gyad’a. Matsowa tayi gab dashi kafin ya gane me takeson yi kawai ta hau kissing nasa ganin basuda niyyan tsayawa nima naja legediz benz d’ina na bar musu d’akin gudun kar su cinye kansu a idanu na (LOL) Koda na leqosu bayan minti uku still basu bari ba haka na sake komawa nabasu minti goma anan ne dana leqo naga Fannah kwance kan k’irjin Anas murmushi fal kwance kan fiskokinsu yana shafa doguwar sumanta a hankali cike da soyayya. “So can I hear it now?” Ta tambayesa. “Yes Flower I love you too.” Dad’i sosai taji ta sake matse jikinta a nasa ahaka har sukayi bacci. *** 7:30PM Tun idar da Sallan Maghrib da sukayi Fannah ta shjge kitchen ta fara aikin d’anwake acikin d’an k’ank’anin lokaci tagama ta had’a musu dining table tayi serving kowa a saucer, Anas na ganin haka ya saci jiki ya koma d’aki ya miqe kan gado shi a dole yana bacci bare chi d’anwake ba. Har d’akin ko ta biyosa “Habeebi tashi muje dinner is ready.” tayi maganan lokacin da take tsaye akansa, shiru yayi tare da sake gamme idanunsa shi wai adole yana bacci. “Baby tashi mana” ta gwada jijjik’ashi “meneh?” Ya tambaya sleepishly. “Baby wai bacci kake? Yaushe ne muka tashi daga bacci har kake wani? Tashi muje kaci abinci yaso seka dawo ka cigaba kaji?” “Banajin yunwa Flower.” “Nasani hak’uri zakayi karfa ya huce yayi sanyi tashi kaji My Lion.” Badan yanaso ba ya mik’e yabita bayan sun zauna ta ja mai saucer’n sa gabansa “bismillah lets eat” nan da nan ta soma kai nata ciki shide kallon saucer’n nasa kawai yake seda ta kusan rabin nata taga Anas beko tab’a nasa ba. “Habeebi inzo in baka ne?” “A’a chi naki zanchi da kaina.” “Toh chi mana ai yamayi sanyi” fork ya d’aga yasa ciki tare da danno kan d’aya seya kai baki seya sake maidoshi baya da abin ya isheta seda tabari yakai baki sannan ta tura hannunsa yasa d’an waken ciki yana fara k’ok’arin fito dashi a girgiza masa kai “karkayi please gwada chi mana kaji kaikam.” Tsotse zak’in jikin yayi kap ya jawo plate ya tufar da d’an waken akai. Kallonsa kawai ta tsaya yi cike da mamaki, wasu biyun ya sake kaiwa baki yana gama tsotse zak’in se ya fito dasu ya ajiye. “Wai Habeebi me haka? Haka ake cin d’anwake? Ai wannan almubazaranci ne.” “Kefa kikace senaci yanzu kuma da nake ci kina min surutu.” Nan ya cigaba da abinda yakeyi, ganin yakusan kai rabin saucer’n tace, “Baby kabari mana” sake matsowa kusa dashi tayi ta danna kan d’aya ta kai masa baki gashi karb’a ba musu ya karb’a “kuma karka tsotse Baby ka tauna ka had’iye.” “I can’t.” Ya sanar da ita. “Yes you can” ta tabbatar masa. Bayan ya gama tsotse zak’in yafara k’ok’arin cirowa aiko ta rufe mai baki “Baby ka tauna ka had’iye mana ko so kake yunwa ya soma damunka? Had’iye.” Kai kawai yake girgiza mata aiko daram ta zauna kan cinyarsa “yau seka had’iye in ba haka ba…” ta matso kusa da kunnensa ta rad’a masa abu ai take ya gyad’a kai. “Goood thats my Man” anan ta sake mai baki. Goran ruwa ya jawo kamar yadda ake had’iyar magani haka ya had’iye d’an waken haka yabi sauran yariga had’iyesu sekace meshan magani. Ita de Fannah nata ido ne. Bayan da suka gama dinner ta d’anyi assisting nasa wani aikin da yakeyi se 10:30PM suka kwanta. Washegari Anas yace sam bazasa office da jan goshi bah ba yadda Fanah batayi dashi ba yafa ce shi ba office da zeje haka suka sha baccinsu se to 11 suka tashi sukayi wanka tayi musu d’umamen as promised sam Anas yak’i chi ba yadda batayi dashi baya da yachi yace bare chi ba sede in fresh new one zata dafa bayan ta karya ta masa nasa breakfast daban kasancewar wheather’n garin yayi cloudy ba rana yau yasa suka fita baya wajen garden suna shaqatawa suna hiran masoya gwanin sha’awa abinsu. Honk da ake tayi yasa Anas ya miqe ya duba ko suwaye ne ganin motar Shettima yasa ya danna wani button gate d’in ya bud’u musu duk suka d’uru sukayi ciki. Amal da ba’asan an girma ba chak ta d’ale cinyan Anas tasa Ummie kunya. “Haba Amal ya haka kuma? Sauqo kinji?” Tana maganan tana kallon Fannah. “Ayyah Ummie barta ba komai she missd him thats why.” “Laaaaa Ya Anas me haka a goshin ka?” Cewar Amal nan hankalin kowa ya koma kan goshin Anas a tare Shettima da Ummie suka ce “dagaske fa amma meya samu wajen haka yayi pink?” Hannu yasa ya rufe goshin tare da bin dukkaninsu da kallo yana nazarin wani k’arya ze had’a musu idanunsa na had’uwa dana Fannah ta kawar dakai se k’ok’arin maze dariyan dake san kub’uto mata take. “Kayi shiru Anas” cewar Ummie “meya samesa Fannah?” Ta yi redirecting kallonta zuwa Fannah. Nan ta soma raba ido dan batasan me zata ce dasu ba. “Ermm… Erm-” katse ta Anas yayi. “D’azu ne zuma suka harbeni a garden ina d’an gyaran wani flower.” “Eh zuma suka harb’esa d’azu” ta mara masa baya. “Ayya sannu” duk su uku suka ce alokaci d’aya Amal na tab’awa yaja hannunta “da zafi stop it.” “Sorry.” Hira suka sha sosai da Fannah tama Ummie tayin d’umamen kuwa tace akawo mata haka suka zauna ita da Shettima suka narki tuwon banda Amal dake nan kamar Anas itama wai batachin miyan kuka se bayan Azahar suka tafi. ** “Kai aman gaskia Habeebi ka iya had’a k’arya sosai fah” ta kwashe da dariya. Banza da ita yayi. “Habeebi is a liar.” Wani kallo ya watsa mata “ki ka sake kirana liar sena miki abinda baki tsammani Flower.” “Do your worse” tamasa gwalo “My Baby is a liar” da gudu ta wuce kitchen tasa lock a duka k’ofofin se dariya take masa. “Ai ba kwana zakiyi ciki ba, zaki fito ki sameni.” Ya fad’a mata. “Zakachi miyan kub’ewan?” “Bansani ba kikayi abinki ke kad’an ki zakichi.” “Nida Baby na zamuchi.” “Babyn da one day zaki haifa ba amman bani ba.” ** A d’aki ta samesa da laptop gabansa yana d’an aiki. “Baby fito lunch is ready.” “Banajin yunwa.” “Tun safe banda chips da kachi me ka sake kachi?” “Toh laifin wa? Ba kece kike ajeni da yunwa ba.” K’arisowa d’akin tayi ta zauna kan cinyansa tare da zagaye hannayenta a wuyansa. “Kamar ya Baby? Ni ke ajiye ka da yunwa?” “Eh manah tun jiya kike dafa kalan abincin da bana chi kuma kin sani.” “Baby ai so nake ka saba bahaushe yace ba kullum ake kwana kan gado ba yanzu for instance in one day kaje Bama ina zaka samu irin abincin nan daka saba chi? ” “Even still je kichi abincinki ni baran chiba.” Gajeren hot kiss tamasa sannan tayi pecking nasa a kumatu “tashi muje kaji Habeebi na?” Besan a lokacin da yatashi ya bita ba ita da kanta take basa, ba kamar jiyan ba yau yaci kub’ewan sosai sabida yamasa d’and’ano bayan sun k’are chi suka koma d’aki tayi assisting nasa aikin dayake kai. 10:20PM Daidai nan Fannah tagama canzawa cikin wani had’ad’d’en rigan baccinta Anas kuwa akan nickers nasa da vest as always seda ya bari ta kwanta sannan ya hauro gadon ya had’e hannayenta gu d’aya “wa kike kira da liar d’zu?” “A’a ba kai ba.” “Nide nine liar ba?” “A’a Baby ba kai ba dan Allah kar ka min cakulkuli wallahi ba kaiba please karka-” bebari ta k’arisa maganan ba ya fara mata cakulkuli dariya take tana hawaye sosai tana had’asa da Allah sam yak’i bari. Seda ya tabbata ta galabaita sannan ya sake mata hannu ya share mata hawayen. “Next time zaki sake kira na liar.” Se “wayyo cikina” take tayi har a yanzu. D’agota yayi ya kwantar da ita jikinsa seda tagama dawowa hayyacinta ta d’ago kanta “Liar nasake fad’a” bata bari ya soma mata cakulkulin ba ta rufe sa da kiss sun d’au tsawon lokaci suna abu d’aya har wani su juya nan su juya chan suke alokaci d’aya Anas yasoma fita hayyacinsa dan wani irin kisses da Fannah ke masa kamar yadda shima yake mata all over her face and neck, duk sun zurfafa suna romancing junansu. Yasani in beyi stopping kansa ba yanzu he can’t later in kuma hakan ya faru zeyi breaking mata promise daya d’aukar mata before nacewa seda yardan ta abu ze gudana tsakaninsu. Da k’yar ya iya ya tashi daga kanta yaja baya ya zauna. “Baby meya faru?” ta tambayesa cike da damuwa tana k’ok’arin miyar da hannun rigarta daya fad’i sannan ta matso kusa dashi ta zagaye hannayeta daga bayansa. “What is it Habeebi?” “Babu” ya amsata blankly. “Da akoi Baby tell me.” A hankali ya cire hannayen nata ya juya yana fuskantar ta. “Flower I can’t go further… I..” Sekuma yayi shiru. “Why can’t you Habeebi?” “Flower kin manta promise dana miki seda concent naki zan tab’a ki?” Kai ta kad’a nufin ta tuni. “Kinga in ban tsayar da kaina yanzu ba I can’t later lets just sleep.” “No Baby I’m ready for it.” Ido ya zaro cike da mamaki yana kallonta “Flower me kikace?” kad’ai abinda bakinsa ya iya furtawa dan yadda mamaki ya rufesa. © MIEMIEBEE
 Hannunsu ta had’a tana murzawa a hankali, “I’m ready Habeebi.” Har yanzu ya kasa yarda, “Flower are you sure?” Kai ta gyad’a “I am Habeebi.” “No kawai fad’a kike Flower kinbar tsoro na?” D’an dariya ta saki “tsoronka? Aini bana tsoronka.” “Are you sure?” Ya sake tambayarta yana d’age mata gira d’aya. “Bakiya tsoro kar nayi destroying naki na saki kuka?” “Kukah! Adalilin me zanyi kuka ko ka manta am not a virgin” bata jira ya sake magana ba ta jawo sa ya fad’a jikinta ta cigaba da kissing nasa yana meh mayar mata da martani, hannu ya mik’a yayi switching off wutan d’akin. (Ba halin d’auko rahoto se Fans suyi hak’uri. LOL) Chan de na d’anji k’aran Fannah ai bada jimawa ba ta soma ihu tun tanayi kad’an kad’an zafin ya fara mata yawa. Ko Habeebi da Babyn ma babu yanzu. “Anas I’m not ready dan Allah kabari wallahi I am not wasa nake maka I don’t mean it kabari please.” Ko kad’an Anas be saurara mata ba dan kuwa gabad’ai ya riga yafita daga hayyacinsa. “Wayyoo Allah Mami!! Anas zaka kasheni wallahi I’m not ready please I’m sorry” se hawaye shark’af shark’af take. “Mr. Fauzi please kadena dan Allah kayi hak’uri barin sake forcing naka cin tuwo ba na tuba dan Allah!!!” Ba kalan suratan da Fannah batayi ba a daren ranan, tana me ma Anas rok’an duniya amman ko kad’an Anas be saurara mata ba seda ya gamsu tukunah, anan ne ma yasoma jin sautin kukan datake ta rerawa a hankali tsabagen yadda k’arfin jikinta ya k’are a shurin Anas data tayi, dande bata da faracu ne da Anas yasha yak’ushi kam. Matso ta gam yayi ajikinsa wane za’a k’wace masa ita se kissing gashinta yake yana suburbud’a mata albarka. Har a yanzu sarkin kukan datace she is ready bata bar kuka ba haka yata bubbuga bayanta har seda yaji nauyinta a jikinsa ya dad’u tabbacin tayi bacci kenan se anan shima ya samu yayi baccin. Asuban fari ya tashi a hankali ya raba jikinsa da nata sannan ya fad’a bathroom yayi wankan sunnah tare da d’auro alwala ya had’a mata warm wata cikin jacuzzi sannan yafito bayan yasa jallabiyansa ya koma ya zauna gefen Fannah dake ta bacci har a yanzu, fuskarta duk jirwayen hawaye murmushi sosai wanda ya sake lotsar da dimple nasa had’e da k’ara masa kyau ya sakar se anan kalamunta suka fara masa yawo akai. “Flower” yayi wispering a kunnenta a farko bata bud’e idanunta ba se a karo na biyu. A hankali ta soma bud’e idanun nata har tagama bud’esu, kyakkyawar fuskar Anas ne yasoma mata sallama pillow taja ta kare fuskarta. D’an murmushi ya saki. “Flower good morning.” Nanma bata tanka saba, daya gwada sa hannunsa cikin blanket d’in kuwa setayi sauri ta tattara ta mammanne a jikinta. “Flower tashi kiyi warming jikinki kinji? Bamuyi Sallah bafah.” Nanma shiru. “Flower baraki min magana ba?” Nanma shiru. “Seda fa na fad’a miki I’m a Lion kika ce you are still ready yi hak’uri ki tashi.” “Toh ai daga baya nace maka kabari I’m not amman kak’i ji na.” “I’m sorry toh yi hak’uri ki tashi.” “Naji excuse me in nagama komai zan kiraka.” “Are you sure barakiyi needing assistance d’ina ba?” “Eh kafita please.” Hannu yasa ya cire pillon data rufe fuskar nata dashi “kabani” ta fad’a idanunta a rufe kamar wacce zatayi kuka. Peck ya manna mata a goshi “I love you Flower” k’in replying nasa tayi seda taji ya fita sannan ta bud’e idanun nata sewani tura baki take kayanta dake a k’asa ta d’aga tasa a kasalance sannan ta gwada tsayawa sam takasa da k’yar d’in k’yar tana dafe-dafe ta isa bayin ta shiga, ruwan daya tanadar mata ta gwada shiga nanma se k’ananun ihu take sakarwa sam ta kasa shiga, zama tayi a gefe guda tana kuka ita ta d’au ai tunda this is not her first time barataji komi ba ai duk laifin Mami ne data sani gaba tariga bani wasu jik’e-jik’e. Anas dake tsaye bakin k’ofar d’akin yana jirarta daman yasan ba abin arziki Fannah zatayi ba jin shiru yasa kai ya shiga. D’akin ya duba be ganta ciki ba chan yaji sautin kukanta a bayi da hanzari ya k’ariso bakin k’ofan. “Flower why are you crying?” Tana jin muryarsa ta share hawayenta tare dayin kum da baki. “Flower meya faru? In shigo?” “A’a karka shigo dan Allah.” “Toh kinyi wankan?” Data kalli jacuzzin seta sake b’arkewa da kuka dan batajin zata iya shiga wai ruwan yamata zafi. Take Anas ya bud’e k’ofar ya shiga. Baya ta juya masa da wuri “Anas ka fita banaso ba kyau dan Allah ka fita” ko sauraranta beyi ba ya d’agata chak kamar ‘yar Baby ya tsunduma ta cikin jacuzzin, zafi sosai taji ta sakar da wani erin k’ara tare da matsesa jikinta gagam ta riqesa tak’i sakesa seda jikinta yasaba da ruwan d’umin tukuna. A kunyace ta sake sa ta soma kare k’irjinta tana kallon k’asa. “Zakiyi wankan ko in miki?” “Anas wani erin magana ne? Taya zakamin wanka ni ka fita dan Allah banaso.” “Anas kad’ai yau ba Baby ba Habeebi bakuma Lion?” “Ai kafi Lion mugunta Hyena ne kai nikam kafita min.” Murmushi sosai yakeyi “kiyi sauri ina jiranki” yana kaiwa nan ya fice. Binsa tayi da kallo sannan a hankali tasamu tayi wanka tayi alwala tafiya d’ai d’ai takeyi har tafito. Zaune ta tarar da Anas kan gado tafiyarta tayi k’ok’arin daidaitawa amman sam ta kasa dan zogin da takeji, miqewa yayi ya k’ariso da ita kan gadon ya zaunar da ita tare da d’auko mata lotion nata. “Baby me zakayi?” “Shafa miki.” “A’a nikam banaso zanyi abina dakaina” hannu tasa ta karb’e. Kallonta kawai yake seda yabari tasa man a hannunta sannan ya kama ya kwashe man kafin tayi magana ya fara shafa mata man. “Anas kabari its embarrassing.” “Dan ina shafawa Flower na mai shine abin kunyan?” “Eh mana” ta gyad’a masa kai. Bayan daya gama shafa mata ta masa godiya sannan ta mik’e tasa wata simple doguwar riga bak’a. Suna idar da Sallah suka koma suka kwanta se anan tayi noticing chanza bedsheet da Anas yayi. “Habeebi kai ka canza bedsheet d’in?” “Yes Flower” ya amsata lokacinda yake kwantar da ita kan k’irjinsa. “Dama ka iya changing bedsheet?” Murmushi kad’an yayi “meh kika maidani ne wai Flower?” “Ajebo mana, ajebon da be iya komai ba ma.” “Nine ban iya komai ba?” “Eh mana toh me ka iya?” “Na iya sa Flower kuka, na iya changing bedsheet and na iya girki.” “I agree with number two amman ban yarda da number one and three ba dan ni baka sani kuka ba” “LOL aikua harda majina ma nasaki” “Hyena kawai” “Ko baki yarda ba yanzu in sake saki wani kukan?” bugu takai masa a k’irji “mugu kawai” dariya sosai yake “when will you be ready next?” “Ready? Chab! wallahi na tuba ba ruwana dan Allah kar ka sake” “LOL Flower bade tsoro ba karki damu barin k’ara ba, I will suprise you today zan mana breakfast, me kuka kawai. Anas I’m not ready wayyo Mami” ya kwaikwayeta yana dariya. “Mschw! Seka tayi ai” nan ta tashi daga jikinsa takoma k’arshen gadon tare da juya mai baya. Pillonsa ya matso kusa da nata “nikam ka koma wajenka kabarni inji da abinda ke damu na.” “Meke damunki Flower?” “Bansani ba ai kafini sani Hyena kawai.” “Flower nine Hyena?” Kai kawai ta gyad’a masa “toh Flower I’m sorry.” “Naji lets sleep toh” hanunsa ya zagaye ta cikinta ahaka suka koma bacci. 11:16AM A hankali ta bud’e idanunta juyawanda zatayi taga ba Anas kan gadon k’ok’arin miqewa tayi sede ta kasa dan wani pain da take feeling yanzu har fiye dana da. Kuka ta soma tana kiran sunan Anas ko kad’an be jita ba dake yana chan kitchen yana garnishing masu breakfast. Louisiana me rai da lafiya ya musu yana tsaye gefen microwave yana jiran time d’in yayi ringing. Singlet neda vest baqi sanye jikinsa. Wayar sa dake kan counter ne yasoma ringing yana kai dubansa yaga Flower da sauri ya d’aga kafin yayi magana yaji sautin kukanta. “Baby please kazo” ta fad’a cikin sautin kuka, microwave d’in ya kashe sannan ya fita a gurguje kwance ya sameta kan gado se hawaye take “Flower whats wrong?” Ya tambayeta cike da damuwa yana share mata hawaye. “Baby zafi.” “Zafi a ina?” “A k’asa na.” “Okay sorry kinji? Sannu kinason muje asibiti?” “Asibiti? Se muje mu cemusu meh? Munyi wani abu kajimin ciwo? Gaskia ni bara’ayi wannan kayan kunyan dani ba, just help me in miqe.” Murmushi sosai ya saki ya taimaka mata yakaita bathroom ya had’a mata warm wata sannan ya bata space. Bayan fitowanta ta shafa mai sannan ta sa wani babban vest tsayinsa iya guiwa, gashinta ya taje mata yamata packing dakansa sannan ya takota da kansa yakaita har dining sannan yayi kitchen ya ciro musu louisiana nasu tun anan k’amshin yasoma bugin hancin Fannah duk tabi ta k’osa taga meya girka. “Wow!” ta furta lokacin da ya ajiye abincin kan dining kallon reaction nata kawai yake sannan yayi serving nata tana kai baki taji dad’insa sosai. “Baby meh sunan wannan?” “louisiana” ya fad’a mata. “louisiana” ta nanata. “Akoi dad’i ba?” “Ba laifi.” ta sake kai wani bite bakinta. “LOL yafi wannan shirmen miyan kuka da kub’ewan da kikeyin.” “Be fi ba kawai de ba laifi amman kad’an k’ara min mana yayi kad’an.” “Kefa kikace ba dad’i akoi miyan kub’ewan ki sena miki reheating.” “Haba mana Baby kasani kuka jiya kuma ka hanani abinci yau?” “Bafa hanaki nayi ba Flower tuwon kine in kinaso in miki reheating.” “Toh banaso louisianan nakeso kuma shi zanci.” Nan ta miqa hannu ta d’aga tray d’in seda ta cinye kap kallonta kawai Anas yake yana adoring nata bayan data gama ya b’allo mata pain killers ya bata ta sha. ★★★★★ Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa wad’annan masoya guda biyu Anas da Fannah. K’ara san junansu suke a kowani second kullum suna maqale da juna in Anas yana gida ba ruwansu da wani fad’a. K’imanin wata d’aya da sati biyu kenan yanzu koda Fannah taga period nata yayi missing bata kawo wani abu a ranta ba saboda daman haka yake mata atimes sede kuma yawan kasalan datake ji yanzu tun shekaran jiya da ta zauna se bacci kullum bacci. Da k’yar ta iya shirya Anas office yau se Allah Allah take ya tafi ta dawo ta kwanta haka kuwa bayan ta masa goodluck kiss ta rufo k’ofa ta dawo ciki ta baje se bacci ba ita ta tashi ba se kusan k’arfe d’aya nanma baccin be isheta ba dan de tasan zatayi girkin rana ne bayan tayi wanka tasa wani silky doguwar riga d’inkin booboo. Powder kad’ai ta shafa ta shiga kitchen sam batasan mezata girka masu bama parlour tafito se hamman yunwa da bacci take tayi. Fridge ta dosa ta bud’e taciro ragowar kazan da Anas yaci ya bari jiya, shi ta k’arasa sannan ta kora da ruwa amman sam seji take kamar bataci komai ba tana kurb’an fanta akai kawai seta jiyo amai guest toilet ta nufa a gurguje tariga kwararo amai wane zata harar da kayan cikinta bayan ta gama ta wanke bakinta abin tausayi tayi alwala sannan tayi Sallah, rashin sanin mezata dafa musu har yanzu yasa ta kira Anas. “Halo Baby” tayi maganan cikin wani erin kasalaccaccen murya. “Flower are you okay?” Ya tambayaeta cike da damuwa. “Eh meh ka gaka?” “Your voice sounds not okay.” “Babu karka damu nace me zakaci yau I can’t think of anything.” “Flower cook anything kinji? Karki damu I’ve got to go inada meeting I love you.” “I love you too” ta katse. Duban agogo tayi taga 10 minutes to 2 “barin d’an mik’e zuwa 3 haka se in dafa masa ko spaghetti.” tace da kanta. Throw pillow taja ta miqe kan 3 seater anan tasamu ta kwanta ba ita ta tashi ba 3:10PM brushing kad’ai tayi ta fad’a kitchen da wurwuri ta had’a markad’an ta aza kan gas nanma tana girkin tana kwanciya ahaka har tasamu tagama had’a komi sauran jiran nunansa kad’ai ta juye a flask ganin tagaji da tsayuwan ta dawo dining taja kujera ta zauna chan ta aza kanta kan table d’in aiko daga nan bata sake sanin ina take ba ruwan abinci kam har ya shanye Fannah batazo ta sauk’e ba da kad’an kad’an girki ya fara k’onewa duk anan bataji ba. 4:10PM Anas ya dawo gida tunda ya bud’e k’ofar yafara jin warin k’onuwan abu ko jakansa be ajiye ba ya nufa kitchen yayi turning off gas d’in se anan ya ga Fannah dake kwance a dining area tana sharb’an bacci. “Flower” yayi tapping nata anan ma bata tashi ba seda ya matso kusa da ita yakira sunanta cikin kunnenta sannan firgit ta tashi. “Ya Salam! Abincin ya k’one Baby sannu da zuwa” takama hanyan kitchen kenan ya rik’o hannunta tare da dawo da ita baya. “Baby ka sakemin hannu please abincin is burning.” “Na riga na kashe gas d’in Flower.” “Huh! Ya k’one koh?” Kai ya gyad’a mata. “Ya Salam! Habeebi I’m so sorry bansan meke damuna ba tun shekaran jiya banida aikin dayafi bacci yanzu me zakachi? Kuma kanajin yunwa koh? Tsaya ko indomie ne in dafa maka I’m sorry kaji Habeebi.” “Calm down Flower karki damu banajin yunwa naci abinci a meeting d’in da mukayi.” “Habeebi are you sure?” “Yes Flower, kinsan bakida lafiya kuwa?” “Mesa kace haka?” Ta tambayesa “You are weak Flower meke damunki?” “Baby babu bacci kawai nakeji.” “Akoi tell me.” “Seriously babu kawai amai kad’an nayi d’azu shid’inma nakega saboda gas dake cikin fantan dana shan ne, muje ka huta kaji?” Nan ta ja hannunsa sukayi d’aki bayan ta tayasa ya rage kayan jikinsa ta mik’e gado ta kwanta se bacci, bece da ita komai ba se 4:30PM ya matso kusa da kunneta yayi whispering. “Flower kinyi Sallan La’asar?” Cikin baccin ta amsa sa “banyi ba amman zanyi.” “Se yaushe?” “Yanzu” ta amsa sa. “Then tashi” haka da k’yar ya tada ta tayi alwala tayi Sallah kasancewar shi ya idar tun a office nanma tana idarwa ta koma baccin jikin Anas se basa yake Fannah ba lafiya ba tun shekaranjiya yake monitoring moves nata ba aikinta se bacci ga wani kasalan da take yawan ji. Toh meneh? Kode sleeping sickness ke damunta? Nide Miemie nace ciki ne ya kukace masu karatu…??? © MIEMIEBEE
 Wajenta ya nufa ya tab’a body tempreture nata nan yaji ya d’anyi rising. “Flower bakida lafiya” yayi concluding. “Habeebi kawai stress ne bawani abu ba.” “Wani aikin kikeyi in natafi? Ba girki bane kawai? Toh wani stress kike nufi Flower? Tashi muje asibiti sekace me sleeping sickess ko da yaushe bacci.” Juyowa tayi tana kallonsa “Baby wai me haka? Yanzu bacci ma barin iya yiba sekace seka kaini asibiti? Lallai fah Allah kacika bin diddigin abu, nikam ma inda zani” tana kaiwa nan ta juya tacigaba da baccinta kallonta ya tsaya yayi sannan ya zagaya ya sameta suka kwantan tare. “Flower I’m sorry didn’t mean to upset you.” “You didn’t my Lion nima I’m sorry.” “Your Lion is hungry.” “Baby kaifa kace kachi abinci a meeting yanzu kuma kana jin yunwa?” “Flower bana son tsiya fa sarai kinsan kalan yunwan da nake nufi feed me.” “Ni gaskia bansani ba” tana kaiwa nan ta juya masa baya chan k’asa-k’asa tace “mutum sekace sex machine ni barin iya ba.” Murmushi sosai ya saki lallai kuwa rabuwansa da ita 2 days now shine take wannan magana? “Nafa jiki Flower najiki da kyau kuma fushi zanyi.” Take ta juyo “a’a karkayi dan Allah yanzu bacci nakeji kabari ko anjima yi hak’uri lets sleep yanzu koh?” Shiru… “Koh Habeebi? Wallahi ji na nake ba k’arfi” Kai ya gyad’a mata ta matso kusa dashi ta kwanta. ** Bayan sun idar da Maghrib Fannah ta wuce kitchen dan soya musu scrambled egg a yayin da Anass ke parlour as ysual da laptpp nasa, tana cikin fasa k’wan d’aya ya fad’i ya fashe a k’asa aiko take kitchen d’in ya soma k’arni kafin ta hankara taji bakinta ya cike da amai. Guest toilet ta ruga a guje nan Anas dake parlour shima yabi bayanta. “Anas please karka shigo ka tsaya daga chan” ai kaman shigo tace masa ya k’ariso ciki yana shafa mata baya a hankali se aman take tayi se datayi sosai sannan ya taimaka mata ta wanke bakinta suka fito idanunta se wani kafewa suke a kan 2 seater suka zauna. “Flower whats wrong? Nafa fad’a miki bakida lafiya.” “Baby k’wai ne ya fashe so se k’arnin ya fitine ni dalilin aman kenan if not ba abi-” bata k’are maganar ba ta fad’a jikinsa dan wani jiri datake ji yana d’ibanta ko a zaunen ma. “Baby hold me kaji?” ta buk’ace sa. Hannayensa ya zagaye a bayanta “I’m here karki damu” bayanta ya riga shafawa up-to-down na zuwa wani lokaci. “Flower” ya kira sunanta shiru yana leqa fuskarta yaga tayi bacci mamaki ne sosai ya rufesa Ipad nasa ya jawo ya sake daidaita kanta a k’irjinsa sannan shikuma ya kishingid’a jikin kujerar. Nan ya shiga google yasoma browsing abubuwan dake jawo yawan bacci dakuma amai abubuwa da dama ne suka fiffito masa wanda one by one yake bi yana karantawa dayazo kan wani point seya tsaya yana nazari sekuma ya dawo da kallonsa kan Fannah “it might be true ban tab’a neman Flower tak’i ba se d’azu itan da sometimes ma take nema da kanta, ga wani kasalan da takeji dashi 2 days, ga baccin asara dakuma amai. Flower are you pregnant?” Ya tambayeta chan ciki-ciki. “Kai anya? Na kusan zama DADDY kenan?! Flower!” yayi whispering a kunnenta “na’am” ta amsa. “Please Baby barin d’an kwanta kad’an wallahi I’m weak.” “Kiji nace when last kika ga period naki?” “Baby meya kawo maganan period d’ina kuma anan? Dan Allah barni in kwanta” matso rigarsa tasakeyi a hannunta tare da sake daidaita kanta kan k’irjinsa ta cigaba da baccinta. Duk wannan magana da take kuma idanunta a rufe suke. Jijjik’ata yayi seda ta mik’e ta zauna. “Ohhh! Habeebi meneh?” Ta k’arisa maganan tana k’ok’arin zama, idanunta da take ta k’ok’arin bud’esu kuwa se kafuwa suke. “Good kinga period naki watan nan?” “Mesa kakeson sani?” “Flower mesa kike rashin ji ne waikam? Two days se misbehaving kike kode shima yana cikin symptoms d’inne?” Ya tambayi kansa kasancewar tana kusa dashi yasa tajisa. “Symptoms name Habeebi?” “Bansani ba ki amsani first.” “Babu bezo ba amman nasan sooner or later zezo saboda atimes haka yake min, se yayi skipping 4-5 days.” “Kin tabbata?” “Eh mana shikenan? Zan iya komawa baccin?” “A’a kitchen d’infa? Wa zeyi mopping wajen da egg d’in ya fashe?” Fuska ta maraice “Baby wallahi k’arnin amai yake sani kuma ma banjin inada k’arfin mopping inaji na ba k’arfi ko kad’an ji nake kamar nayi aikin d’aga block please kabari gobe in masu aiki suka zo senayi kaji Baby?” “Another symptom” yace da kanshi nanma ta jisa. “Wai wani symptom Baby?” “Flower look at me” nan ta maido da kallonta a agaresa. “Don’t you think you are pregnant? Mun kusan zamowa Daddy and Mammy?” Cike da rashi yarda tayi maganan, “Kana nufin wai ciki ne dani?” Ta k’are maganar hannunta kan flat cikinta, hannun sa shima yabi ya aza akan nata dake cikinta “sosai ma kuwa Flower karanta nan kiga” nan ya miqa mata Ipad d’in data gama karantawa kuma setaga almost all yadda take feeling haka aka yita bayani ciki toh ko dagaske ne tana da ciki? Ta kusa zama Uwa kenan itama? “Flower what do you think?” maganarsa neya tsamota daga tunanin da takeyi. “I think yes!” Ta fad’a delighted cike da jin dad’i. “I think so too Habeebi I might be pregnant!” “Yes Flower” hannunta yacire daga cikin nata ya sa nasa kai “we have a baby in here.” Hannunsa ta cire ta aza nata kan cikin “tsaya let me feel it.” “No!” ya zare hannunta ya d’aura nasa kai “ki tsaya inyi feeling first bani ne babba ba?” Nan ta sake cire hannunsa “sekaci girma ai kabarni inyi feeling nasa first, nida ciki na abeg d’aga min hannunka.” “Cikinki ko cikinmu?” Haka suka tayi Anas yak’i cin girma yabar Fannah ta fara feeling Babyn nasu kamar yadda itama tak’i cin k’ank’anta. Seda tagaji ganin Anas baida niyan barinta kawai ta barsa yafara feeling hannunsa yafi minti biyu kan cikinta yak’i d’agawa. “Toh ai haka yayi nima let me feel my Baby.” “Flower Allah kika sake cewa Babynki zamu b’ata. Its our Baby.” “Toh our Baby, kasan meh?” Kai ya kad’a mata. Matso da kansa tayi ta rad’a masa wani abu a kunne. “LOL yes I am Flower, so gobe zamuje asibiti?” “Muje muyi meh kuma Habeebi?” “Muje mu tabbatar da cikin naki mana ayi scanning.” “Shine se munje asibiti? “Yes Flower.” “A’a nikam barinje ba zan saya pregnancy test strip in gwada da kaina a gida ba se munje asibiti ba.” “I know Flower but still yakamata muje kinga zamu san how many weeks ne pregancy nakin and za’a bamu shawarwari dayawa kinga this our first time.” “Nikam gaskia Baby kayan kunyan nan badani ba.” “Wai wani kayan kunya Flower? Ciki abin farin cikin ne kuma abin kunya yanzu?” “Eh mana Baby kowa de yasan ta yadda ake samun cikin nan ni kawai mu rufa wa kanmu asiri kar muje.” Dariya sosai ya tsaya yanayi “Flower you are too much to meh? Suma haka akayi aka haifesu kowa ma haka akayi aka haifesa I see nothing wrong with that.” “Nide ba ‘yar iska bace barin jeba” tana kaiwa nan ta mik’e aiko seconds talatin batayi ba ta fad’a kujeran ta dan jiri da sauri ya taro ta. “Flower fa dole muje asibiti final decision.” Chak ya d’agata yakaita d’aki black tea ya had’o mata bayan tasha yajasu Sallah wanda rabinsa ma a zaune Fannah tayi dan jiri. Washegari… Asuban fari Anas ya tashi bayan yayi alwala ya taimakawa Fannah ma tayi suna idar da Sallah suka koma suka kwanta sede unlike jiya yau jikin nata da zafi amman ba chan chan ba gudun karwani abu yasamu lafiyan babynsu yasa Anas yabata paracetamol kad’ai tasha cikin ikon Allah yamata aiki kuwa, k’arfe shida ta tashi as always taje ta had’a musu breakfast hancinta toshe da hanky dan gudun k’arnin fashasshen k’wan bayan tagama ta jera dining sannan taje ta tada Anas. “Baby katashi kayi wanka kaji?” Bayan ya bud’e idanunsa ya k’are mata kallo bakomai ne d’auke a idanunta ba banda kasala. “Flower kinyi wani aiki neh?” “Breakfast kawai na shirya mana se ruwan wankan ka tashi kashiga.” “Flower why? Daga yau banason ki sake yin wani aiki kinji? Its not fit for your condition.” “Baby bamu ma tabbata ko cikin ne dani bafa tashi kayi wanka” towel nasa ta mik’a masa nan danan yayi wanka yashirya sannan yafito suka fara breakfast kad’an daga cikin fried egg d’in Fannah taci ya sata amai aguje ta ruga bathroom shima Anas yabi bayanta yana shafa mata baya, amai ta rigayi abin tausayi, data gama ya tayata kimtsa kanta suka fito tana manne a jikinsa dan jiri. “Flower bara muje asibiti ba?” Kai kawai ta iya ta gyad‘a mai. “Sorry kinji? I can’t leave you alone like this.” “Me kake nufi Baby?” “Nafasa zuwa office I will take care of you.” “Common Habeebi karka damu I will be fine je ka gama breakfast naka kaji? I love you” peck ta manna masa a kumatu da k’yar tare da komawa ta lume cikin kujeran. “Flower in kaiki d’aki?” “Nanma yayi kayi sauri.” Mik’ewa yayi yaje d’aki yafito da blanket bayan ya kunna AC ya lullub’eta dashi sannan yayi pecking nata a goshi. Dining ya koma yayi rushing ya gama breakfast nasa, wayarsa ya d’aga dan kiran Kacallah ya fad’a mai bazasa office ba yau yaga Kachallan na kiransa. Bayan yayi picking Kacallah ya gaishesa “Sir na kira ne dama in tuna maka meeting da zakuyi da board of directors na F&C Enterprises regarding 2% shares nasu da zasu siyar mana dakuma investing da zamuyi.” Kallon sa ya miyar kan Fannah ji yayi bare iya barin ta haka ba dan kuwa batada lafiya. “Hello Sir?” Cewar Kacallah dan jin shiru. “Kacallah baraka iya presenting d’ina ba? My wife is sick I’m afraid barin iya barinta ita kad’ai ba.” “Ayya my regards please kuma Allah ya sawaqa unfortunately I can’t Sir dole se kai in ba haka ba barasu siyar mana ba kuma kasan we can’t lose this oppurtunity please Sir.” “I will see to it” nan yayi hanging. Wajen Fannah ya nufa ya zauna a gefenta. “Flower” ya kira sunanta. “Na’am” ta amsa a kasalance. “How are you feeling? Ki fad’a min tsakanin ki da Allah karkimin k’arya.” “Baby kasala ne kawai sekuma zuciya na dake yawan tashi thats all.” “Bakiya feeling feverish? (zazzab’i)” “Kad’an ba.” Ta amsa shi. “I can’t leave you like this zanyi canceling meeting d’in.” “Wani meeting Baby? Bade na F&C Enterprises ba!” “Shi Flower barin iya barin ki haka ba.” Juyowa tayi tana fuskantanshi “please kar kayi haka kaji? Karkayi losing wannan oppurtunity, karka damu dani in nasamu na kwanta I will be fit.” “Kinsan fa ba ke kad’aice ba yanzu akwai little one namu.” Wahallalen murmushi ta saki “don’t worry I’ll take care of it for its Daddy, off you go kaji? Best wishes I love you.” “I love you too Flower” yayi maganan yana gyara mata blanket d’in “take care of yourselves for me ko in kira Afrah tazo ta tayaki zama?” “A’a karka damu I can manage.” “Sure Flower?” “Yes Baby.” Brushing light kiss ya mata a baki “I love you okay? Ki kirani in wani abu na daminki kinji?” “Yes Sir!” ta masa murmushi har ya miqe sekuma ya dawo ya zauna “kinga banyi greeting baby naba” hannunsa yasa cikin kayanta yashafa kan cikin. “Good morning my baby your Daddy loves you so much.” Murmushi kad’an ta saki dukda kuwa yabata dariya sosai. “Habeebi nothing is certain yet fah kar muta hoping muzo kuma abu yayi turning out in a different way.” “I still don’t care, I love you bye.” Jakansa ya d’aga ya fice a yayinda ta rufe idanunta tare da aza hannunta kan cikinta tana shafawa a hankali da murmusi fal kwance a fuskarta. ** Sosai d’an baccin da tayi ya taimaka mata dan kuwa ta samu k’arfin jiki takuma warware, d’aya daga cikin masu aikin nata ta aika chemist ta siyo mata strips guda biyu, bayan ta kawo mata tashiga toilet tayi carrying out test d’in se bugawa zuciyarta ke bayan daya gama reading ta bud’e ido d’aya da rabi ta leqa tana ganin ‘P’ ta bud’e duka nan ta karanta ”POSITIVE” ta karance. Tsalle ta daka “yeyyy!!! I’m pregnant!! I’m pregnant!!” A gurguje tafito daga bayin ta d‘au wayanta ta kira Anas sede har ya yanke be d’aga ba kasancewar yana a meeting 2 missed calls tamasa ganin be d’auka ba tamiyar da wayar ta ajiye. 1:50PM lokacin da Anas yafito daga meeting d’in ya duba wayarsa yaga missed call na Flower ba tare da b’ata lokaci ba ya kirata back daidai lokacin da take fitowa daga wanka kenan a dole tayi zuciya tak’i picking se a karo na biyu ta d’aga nan ma tak’i cewa komai “Halo Flower?”,nanma shiru. “Flower don’t be mad I was in a meeting kinji? Yi hak’uri kimin magana.” Se anan ta sauk’o. “Ya meeting d’in?” “Alhamdulillah yanzu muka fito, ya jikin ki?” “Da sauk’i me kakeso kachi yau?” “Babu karki dafa komai zan saya mana lunch banason kina wani aiki yanzu.” “Hunmm! As you say Mr. Fauzi yau inada suprise maka.” “Really Flower? I hope ba irin suprise na miyan kukan da kika min ranan bane?” Dariya ta saki “ko kad’an Habeebi” “Toh tell me meh suprise d’in?”,Baki ta cuno. “Suprise nefa Habeebi ai ba’a fad’a seka dawon de, k’arfe nawa zaka shigo?” Rolex agogon hannunsa ya duba “erm… Zuwa 3 haka.” “Okay toh sekazo.” “Wait.. Wait fad’amin kinji meh suprise d’in? Ko hint ne kibani.” “O’o seka dawo I love you!” Bata jira ya sake magana ba ta katse wayar tana murmushi shima murmushin yake. Had’ad’d’iyar kwalya ta tsara tasa wata had’ad’d’iyar light purple lace da torches na fari da dark purple d’inkin peplum da skirt. Bayan nan ta kafa d’aurin network nata me kyau sannan ta feffeshe da turarukan ta meh yima Anas dad’i. Game ta zauna tata bugawa chan takira gida suka gaggaisa. 3:15PM nayi ta b’allo sabon strip ta sake carrying out test d’in ta ajiye 3:20PM Anas ya dawo gida k’ofa na bud’uwa Fannah ta bayyana a bayansa kallonta yake wane a mafarki sekace ba itace ke kwance ba lafiya ba d’azu. Another symptom yace a ransa morning sickness. Bayan ya shigo ya miyar da k’ofan sannan ya juyo yana kallonta har a yanzu tunanin wani kalma ze furta wanda ze dace da kyan da Fannah tayi yake. “Flower you are looking extra ordinary spectacular, you’re looking amazing.” “Thank you Sweetheart” ta fad’a tana mai murmushi matsowa kusa dashi tayi seda ta rufe gap dake tsakaninsu nan k’amshin jikinta me haukatasa ya buga masa hanci besan alokacin daya fara bin wuyanta yana shunshunawa ba. Hannu tasa ta shuresa da k’yar “Baby waittyy manaaa” bata bari ya sake komawa jikinta ba ta mik’a masa strip dake hannunta. “What is this Flower?” Ya tambayeta. “Pregnancy test strip.” “Kina nufin har kinyi carrying out test d’in without me?” “Yes Baby I’m sorry duba kaga result d’in.” Da hanzari ya maida kallonsa kan bar d’in “POSITIVE” yaga rubuce kai. © MIEMIEBEE
      Had’ad’d’un blue eyes nasa yazaro cike da rashin yarda dan jin dad’i, farin cikin da baya iya misaltuwa ne kwance karara a fuskarsa “Flower its positive! you are pregnant!” ya fad’a cike da jin dad’i. Jakansa da ledan abincin ya ajiye kan kujera tare da d’aga Fannah sama dan jin dad’i “Flower we did it!” Murmushi sosai take wanda ya sake qayata ta. Bayan da ya sauk’o da ita yayi pressing mata hot kiss sannan ya rik’o ‘yar fuskarta duk suna murmusawa, rungumota kawai yayi “thank you Flower thank you so much I love you and our little one.”
     “I love you too Hyena.” Bayan ya sakota ya had’e gira “bance miki banason sunan nan ba.”
   “LOL to ai Hyenan ne kai Father to our child.”
    “Lets eat Mammy to be.” Ledan abincin ta miqa hannu zata d’aga yayi sauri ya rigata “uh-uh” ya kad’a mata kai “banason kina aikin komai yanzu zan k’aro masu aiki harda chefs ko girki ma banason ki sake kinji Mammy to be?”
     “Baby ai gatan yayi yawa kod’an girki ne seka barni inayi.”
    “Banaso kinsan abinda nakeso dake?” Kai ta kad’a mai.
    “Abu d’aya nakeso dake just take care of yourself and our baby shikenan, zakimin?”
    “Ofcourse Habeebi.”
       Shi da kansa yayi serving nasu abincin suna ci suna hira gwanin sha’awa har suka gama d’aki ya shiga ya canza suit nasa yasa sweaty pants da longsleeve shirt sannan ya d’auko mata hijabin ta itama. “Baby zamu fita ne?” Ta tambayesa alokacin daya k’ariso cikin parlour’n. Be amsata ba seda ya sa mata hijabin tukuna. “Asibiti zamuje.”
     “Muje muyi me kuma? Ba gashi munyi test d’inba and its positive meh amfanin zuwa?”
    “Trust me Flower lets go no arguement” badan tanaso ba tayi shiru hannunta cikin nasa suka fice, isarsu asibitin keda wuya Fannah ta soma rigima ita barata fito ba da k’yar da lalashi yasamu ya fito da ita daman already ansan da zuwansu basuyi wani zaman jiran doctor ba aka kaisu d’akin sede Anas be d’au na miji neba doctorn acewarsa mace ce. Bayan sun gaisa yayi ma Dr bayanin komai sabida yasan bayi Fannah zatayi ba. D’an k’aramin k’ofan dake cikin office d’in Dr’n ya buk’aci Fannah data shiga bayanta Anas yabi suka shiga tare haka shima Dr’n, kan wani k’aramin gado dake a gefe guda a d’akin likitan ya buk’aci Fannah ta hau kafin ta miqe akai Anas ya dakatar da ita ta hanyan rik’e hannunta “Dr I don’t get it kana nufin kaine zakayi mata scanning d’in?” yayi magnar cike da rashin yarda.
     “Yes Mr. Fauzi this is something I do everyday karka damu.”
    “Inaaaa!!” ya fad’a yana girgiza kai. “A nemo female Dr kawai ba yadda za’ayi matata ta kwaye maka cikinta banaso.” (kishi ya k’osa) Dariya sosai yabawa Dr’n.
      “Toh nid’in acewarka banida mata ne? Ko bakasan har karb’an haihuwa inayi ba. This is my job.”
    “Oho bansani ba nide a nemo female Dr.” Fannah dake tsaye a gefensa ne tasoma jin kunyan abinda yakeyi shegen kishi sekace d’an k’aramin yaro. “Baby kabari please its embarrassing.”
    “No Flower its not nide barin bari ya gane miki ciki ba.” Dawo da kallonta kan Dr’n tayi. “Dr please I’m sorry, haka yakeda wawan kishi in akwai female Dr a nemo mana ita please I’m sorry.” Kai kawai ya kad’a sannan ya fice ya kira wata female Dr in less than 10 minutes ta iso se mita take jin an ambaci Mr. Fauzi tayi shiru ta fara fara’a. Shi da kansa Anas ya kwantar da Fannah ya kwaye mata kayan daidai cikinta sannan ya riqo hannunta cikin nasa yana kissing.
       Cikin scanning machine d’in aka nuna musu d’an d’ayansu wanda yake nan d’an k’ararrami kasancewar Fannah is only 5 weeks pregnant dan marmari har printing photo scan d’in seda sukayi har copies uku. Shawarwari da dama female Dr d’in ta basu takuma buk’acesu da suna zuwa on regular basis bayan ta rubuta musu ‘yan maguna. Godiya sosai sukayi mata sannan suka fice chemist siyan maganin tun achan nurse d’in tasoma yima Anas wani gane gane taga mutum da blue eyes aiko Fannah na noticing haka ta tura Anas ta amshe maganin da kanta shiko basarwa yayi, yi yayi kamar besan meya faru ba.
     Suna zaune cikin mota Fannah taciro photos d’in ta mik’awa Anas d’aya duk sun zurfafa suna kallon photo d’in daga bisani suka ce da juna “what do you think is our baby’s gender?” a tare. Murmushi duka sukayi “you go first” Anas ya buk’ace ta.
    “No you” ta amsa sa.
    “Okay nikam ban damu ba muddin mutum ne like us and zan iya kiransa ko ita Mini Fauzi alhamdulillah.” Dad’i sosai taji dayace haka ba kaman wasu jahilan maza masu cewa se na miji suke so ba basu san ‘ya mace. “Kefa Flower?” ya tsamota daga duniyar tunanin data wula.
    “Me too Baby I love our baby look at it.” Ta matso masa da picture’n se admiring babyn da basu san hannayensa ba bale k’afafunsa suke. A hanya Anas ya riga tsayawa yana siyawa Fannah kayan k’walama kasancewar female Dr tace masa mata masu ciki akoi su da kwad’ayi kuma ana iya k’ok’ari ana biya masu buk’ata.
       “Baby wai ina za’a kai wannan abubuwa ne?”
    “Nakine dana babyn mu in ke bakiso shi ko ita suna so.” Bayan sun iso gida ya cicciro komai da kansa be barta ta ta cire koda tsinke ba suna zaune a parlour suna shan ice cream Anas ya d’ago wayarsa dake kan centre table.
    “Me zakayi Habeebi?”
    “Zan kira Ummie in sanar da ita ne.” Take ta taso daga jikinsa tana zaro idanunta.
    “Ka sanar da ita meh?” Ta tambaya cike da rashin fahimta.
     “That you are pregnant.” Hannu tasa ta wabje wayan. “A’a wallahi bara’ayi kayan kunyan nan dani ba.”
     “Flower wai wani kayan kunya?”
    “Ai kafini sani dawani idan kakeson Ummie ta fara kallo na? Ni gaskia kabari in cikin ya girma da kanta zata gani amman haka kurum ka hau kiranta kana fad’a mata inada ciki banaso”
    “Toh naji sarkin kunya Mami fa? Kawo in sanar da ita.”
     “Danqaree! ashe bakason na sake sa k’afa a gidanmu kenan ai in Afrah taji inada ciki I don’t think zata barni in sake shan iska.”
      “Kefa kike damuwa, kowa ta yadda muka bi aka haifesa kuma shima haka yabi ya haifi wasu, I see nothing wrong.”
    “Eh koma meh ni kar a kirasu.”
    “Toh Mrs. Fauzi naji yaushe zamu fita first shopping wa baby?” Ya k’are maganar tare da dafe hannunsa kan cikinsu (injisa da fad’i) yana shafawa a hankali.
    “Kai Habeebi yanzu cikin wata biyar za’a ma siyayya?” ta k’are maganan tare da kai spoon na ice cream bakinta.
    “Eh mana koda cikin kwana d’aya nema you just don’t know how excited I am nima nakusan zama Daddy.” Gira ta had’e wanda a dalilin haka Anas ya tambayeta ko lafiya.
    “Wani irin lafiya Habeebi? Bayan tun ban haifo baby’n ba ka fara nunawa kafi son sa fiye dani.” Kwashewa yayi da dariya “aww dariya ma nake baka koh?”
     “No Flower I’m sorry, I love you guys all kinji? You guys are my family ai kema kinsani duka inasonku kuma ma nafison ki tunda kece source d’in happiness d’ina.” Ya k’are maganan tare da placing mata peck a kumatu anan ne ta d’anji dama-dama.
   
     “Kuma Baby please kad’au min alk’awari baraka na biyewa ‘yan matan wajen nan ba kaga ko nurse na d’azun nan se kallonka take.”
    “Toh Flower taga Mr. Handsome ba dole ba.” yayi maganar cike da gatsine dakuma gira d’aya d’age.
    “Naji kuma nasani you are handsome and thats why am jealous of you banason ana gani mun kai haka.”
  “LOL Flower is jeolous.”
     “Habeebi I’m serious wallahi banaso” ta k’are maganan kamar wacce zatayi kuka.
    “Shhh! Baby Mamah karkiyi kuka hakan bare k’ara faruwa ba, I promise.” murmushi kad’ai ta saki masa.
 
    ***
      Tun daga ranan Anas ya maida Fannah tamkar gold da ba’asan yasha wahala, ko aikin d’aga tsinke ya hanata yi ba aikinta se kula da kanta dakuma little one nasu. Wani soyayyan ma se a yanzu yasoma nuna mata kamar hauka fiye dana da bayasan komi ya tab’ata kullum hannunsa na akan cikinta yana feeling baby’nsu, Anas ya d’au son duniya ya d’aura wa cikin Fannah, ko kwanciya anyhow ya hanata wai shi kar ajima baby’nsa ciwo wani sa’in har haushi yake bawa Fannah dan abinda yakeyi itan da abu ke jikinta amma batada iko akai.
 
     A dalilin condition nata da rashin samun cin abincin da takeyi atimes yasa ya samo mata nutritionist me kula da cin abincin mara lafiya. Morning sickness kuwa bata dena ba har a yanzu dakuma kasala kamar yadda female Dr ta fad’a musu se ta wuce first trimester’n ta zata dawo old self nata. Sosai Anas yake kula da ita kusan a kullum sesun ma baby nasu shopping duk abinda Anas yagani ina a store kokuma online seya siya wa baby’n, bayi barin komai ya wucesa. Duk yadda Fannah zata iya bi dan hana Anas sanar dasu Mami da Ummie tana da ciki tabi amman haka seda ya kirasu ya fad’a musu tsantsan murna, duk suka tayasu murna babu kamar Afrah dake ma Fannah wak’a wai taci wake.
     Anas fa ba wasa tuni ya bada d’aki d’ayan dake tsakanin d’akinsa dana Fannah aka soma renovating dam aka cikasa da kayakin wasa da had’ad’d’un gadajen baby har guda biyu wanda yayi placing order daga Italy koda Fannah ta tambayesa dalilin dayasa akayi painting d’akin baby pink ce mata yayi wai ji yake ajikinsa mace kyakkyawa zata haifa masu me blue eyes kamar nasa danko har mafarki yayi, dad’i sosai taji, Anas is her everything bata tab’a neman abu k’ark’ashinsa ta rasa ba sesa a kullum take masa addu’a Allah ya cigaba da kare mata shi. A kullum kafin yadawo daga aiki suna kan video call inkuwa ya dawo suna a d’akin babynsu suna admiring d’akin, ga story books dam cike a cikin shelve d’akin baby on board na Mr. And Mrs. Fauzi kam se wanda yagani!
       2 weeks after first visit nasu suka sake komawa asibiti akayi scanning cikin, baby’n na nan cikin k’oshin lafiya kuma sosai ya k’ara girma compared to zuwansu na farko, cikin nata nada 7 weeks yanzu sam kamar bame ciki ba, cikin nata na nan flat shide Anas ya k’osa yaga lokacin da cikin Fannah ze fito kodan yasamu abin neman tsokanarta.
    ★★★★★
        3 Weeks Later…
     
      Cikin Fannah nada 10 weeks cus! 2 months two weeks kenan dake takusan fita a first trimester nata yasa yanzu morning sickness d’in ya ragu compared to da a hankali take gaining back k’arfin jikinta unlike before da kullum take cikin bacci cikin nata wani haske da fresh ya k’ara mata sosai ga wani cikowan datake tayi daga sama har dan haka tasoma zama da hijabi agida wai kunyar Anas takeji  se in an lura yanzu za’a iya ganewa tanada ciki danko ya b’ullo kai kad’an wanda in tasa tight kaya yana d’an nunawa.
 
      Yau ranar ta kasance Tuesday kamar yadda tasaba ada ta cigaba dayi yanzu dukda Anas ya hanata amman sam tak’i jinsa. 6:00AM ta tashi ta had’a musu breakfast sannan ta tada Anas yayi wanka seda ya gaishe da babynsu sannan ya gaishe da Fannah bayan sun k’are breakfast ta tayasa gama shiri tana cikin gyara masa necktie tayi noticing kallon ta da Anas yake danko ‘yar vest ce kad’ai jikinta.
     “Habeebi wai me haka? Kadena kallo na haka.” Tayi maganan a lokacinda ta sauk’e hannunta daga wuyansa bayan ta gama d’aure masa neck tie d’in ta juya masa baya nan tashiga nemo hijabinta daman tasan this is coming. Juyo da ita yayi tare da sauk’e hannayenta data azasu kan k’irjinta tana karewa.
      “Flower kin gani kuwa?”
    “Ga meh?” Ta tambayesa fuskarta ad’an tamk’e. “Kasakemin hannu.”
     “Bakiga…” Yakasa k’arisa maganan dan yadda k’irjin Fannah daya cike dam ke d’aukar masa hankali.
     Hannu tasa ta mari kansa a hankali “Habeebi kabar kallo na haka banaso.” D’an k’ara yasaki “awch! Flower tsaya kiga” hannunta yaja ya kaita gaban dressing mirror “kiga fa” yace da ita yi tayi kamar bata gane me yake nufi ba.
    “Mezan gani?”
    “Flower wai so kike kice bakiyi noticing ba?”
    “Noticing meneh? Nikam bye ga jakanka d’auka ka fice.” Murmushi sosai ya saki “kema kinyi noticing kenan.”
    “Eh mana nida jikina taya barinyi ba, Habeebi yayi muni ne?” Ta tambaya fuskarta kan wanda zeyi kuka.
    “Oh common Flower ko kad’an it actually fits you kin ma fi kyau haka.”
    “Habeebi are you sure?” Ta juyo gaban mirror tana kallon kanta.
     “Yes Flower I love you.”
    “I love you too Baby nace ko driver ka turomun se ya kaini asibitin kasan tace yau mukoma kuma kanada meeting.”
     “Flower kibari mana muje gobe.”
   “Habeebi yau fa tace karka damu I will be fine.”
    “I will cancel the meeting.”
    “Habeebi no need off you go.”
    “Flower are you sure?”
   “Eh mana zuwa asibiti ne kuma sabon abu? Zanje indawo fine and good in shaa Allah.”
    “Okay in driver yazo ki kirani ki sanardani in kuka isa asibitin nanma ki kirani sannan inya dawo dake nanma ki kirani ki fad’amin I can’t afford it in wani abu ya sameki ko baby’n mu Flower.”
    “Yes Sir zanyi as you say in shaa Allah ba abinda ze faru.”
     Kallon d’an k’aramin cikinta ya tsaya yi ganin tasa hannunta cikin rigar ya sasa murmusawa “kinga cikinki ya fara fitowa very soon ze zama k’ato irin na Nigerian police.” Bugi cike da shakwab’a ta kai masa a hannu “haba! Habeebi banaso in shaa Allah ciki na bareyi k’ato ba.”
     
       “Se yayi kijira nan da months kawai kiga wonders”
    “Habeebi manaaa!!!” ta hau bubbuga k’afa.
    “LOL Flower” ya matso da ita jikinsa “karki damu ko ya kike koya girman cikinki yake you are still the slim, elegant Fannah Aleeyu Fauzi that I know nothing will ever change kinji?” Kai ta gyad’a masa tana murmushi sanan tayi hugging nasa.
     Har bakin k’ofa ta rakasa as always ta miqa masa jakansa sannan tamasa goodluck kisses shikuma yayi kissing cikinta tare da cemasa ko ita “I love you” ganin Fannah ta had’a rai ya matso kunnenta itama yayi whispering “I love you also Baby Mamah” se anan ta murmusa “I love you too Habeebi, take care of yourself for me and our baby”
       “I will Flower and you too in na dawo se muyi maganan wani country kikeson muyi proceeding ante natal namu” zatayi magana ya dakatar da ita ta hanyan aza yatsansa kan bakinta “shhh! Flower na fad’a miki ni ba’a Nigeria nakeson ayi rainon babyn mu” tana murmusawa ta gyad’a masa nan ya fice da murmushi d’auke a fuskokinsu both seda gate ya ruhu ta dawo ciki.
    **_10:30AM_
       Dai-dai nan driver yazo d’aukan Fannah kamar yadda Anas ya buk’ace ta haka tayi dasuka isa asibitin ma ta kirasa again bayan angama dubanta driver yadawo da ita gida ko jakarta bata ajiye ba ta zaro wayarta ta danna masa kira bada jimawa ba ya d’aga.
     “Halo Habeebi”
    “Yes Flower… Har ya dawo dake gida ne?”
    “Eh yanzu shigowa na ko jaka ma ban ajiye ba nace barin kiraka.”
    “Thank you honey, so how is our baby?”
     “Its fine Dr tace in pregnancy’n yakai 4 month za’a iya gano sex d’in.” Cike da jin dad’i yace, “wow! Great news I can’t wait.”
     “Me either I have a suprise for you.”
    “Again? Flower bakiya gajiya da bani suprises and I love them.”
    “Saboda ina sonka Baby yau zan baka hint na suprise d’in.”
    “Really? Toh inaji”
    “Its regarding our baby.”
    “Ohh wow! What about it?”
   “Kai Habeebi kanamin wayo kanason in sanar dakai koh?”
     “Please Flower…” Yayi pleading.
     “Okay nasa anyi mana printing photo scan d’in.”
     “Haba! I can’t wait indawo gida.”
   “And guess what?”
   “What?!” Ya tambaya ba tare da b’ata lokaci ba.
     “Legs and hands na baby namu sun k’ara tsayi kuma har sun fara girmar da faracu.”
     “Dagaske Flower?!” Yayi exclaiming cike da jin dad’i.
    “Wallahi Habeebi its soo cute karka damu nayi printing out 3 pictures in kadawo zan nuna maka.”
     “Happy us Mammy and Daddy, kinsan wani abu?”
    “A’a Habeebi seka fad’a.”
    “In nadawo we will think of wani suna zamu bawa baby’nmu.”
    “Habeebi ai toh bamusan gender d’inba.”
    “Nifa na fad’a miki mace ce.”
   “Toh inkuma na miji ne fah?”
   “Se muyi suggesting 5 names na maza 5 names na mata ciki semu zab’a two dayafi dad’i na both sexes.”
     “Yeyy! to seka dawo I love you.”
    “I love you so much more Flower yanzu kije ki kwanta kihuta kinji?”
    “Yes Baby bye.” Nan tayi hanging hannu tasa zata zaro photo d’in dan sake gani aka danna door bell “wayene?” ta tambaya daga nesa.
    “D… Dr… Driver ne Hajiya.”
    “Moosa?” Ta tambaya tana nufowa bakin k’ofar.
     “Eh.. Ehh shine” yayi stammering again.
    “Toh meya faru haka?” Ta tambayi kanta ba tare da b’ata lokaci ba ta bud’e k’ofar ganin fuskarsa tayi duk jini ga idansa d’aya daya kumbura sakamakon bugin daya sha ga dukkan alamu. Hannu ta aza a bakinta tare da zaro idanunta waje “Ya Salam Moosa meya same ka haka? Innalillahi wa inna ilaihi r-” bata k’are salatin ba taga mutum from nowhere ya b’ullo a bayan Moosa rik’e da bingida a hannusa ya d’aga sama.
      Wani erin mumunan fad’i gabanta yayi wanda ta jima batayi erinsa ba da yazo da mumunar k’arshe da cikin dake jikinta ma seya zube take a wajen dan yadda ta tsorata, takuma tsure, zuciyarta se bugun d’ari-dar’i yake a yayinda bakinta ke b’ari ko kiran sunan mutumin ma takasa dukda kuwa bayau tasoma ganinsa ba…
   *© MIEMIEBEE*
 TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 79
BY MIEMIEBEE
     In dedication to *Aunty Sis
   
      Daidai yakai da bakin k’ofa ya murd’a handle d’in a fusace kenan wayarsa dake aljihunsa yasoma ringing dogon tsuka yaja sannan yaciro wayar ganin new number yasan Anas ne dan kuwa beyi registering numban kowa kan sim d’inba. Wani shu’umin murmushi ya saki sannan ya maida hannun k’ofar ya dawo ciki tare da zama kusa da Fannah. “We are having a call from Anas wifey.” yasake murmusawa. Ba tare da b’ata lokaci ba ya d’aga tare da sawa a handsfree yana shafa hannun Fannah a hankali in a romantic manner se k’ok’arin shuresa take amman takasa.
      “Halo Farouq?” cewar Anas. D’an dariya ya saki “huh! How smart you are Mr. Fauzi harka gano nine na ma wannan big suprise d’in kenan? Well bravo.”
     “Shut up you bastard where is my wife? Ina ka kaimin matata?”
     “You shut up Idiot ko kayi behaving kanka kokuwa har abada baraka sake sa Fannah a idanka ba, mschw!”
     “What do you mean Farouq let her go ka saketa dani kake da problem ba Fannah ba niya kamata ka kama ba ita ba, why are you such a coward?”
       “Coward? Dan na karb’o whats mine shine zaka cemin coward?”
     “Fannah was never yours and never will be-” katse sa yayi “don’t you dare Anas karka sake katseni idan ina magana yanzu ba wannan ba idan kanason sake jin voice na Flowerka you do as I say.”
     “Farouq don’t dare touch her karka kuskura ka tab’a Fannah wallahi I will kill you inhar wani abu ya sameta.”
    “LOL” ya k’yalk’yale da dariya “kill me? Ashe I will dye along with your Flower saboda nikeda iko da ranta yanzu aduk lokacin dana ga dama ina iya kasheta inkazo nima seka kasheni kaga ko semuje mucigaba da soyayyar mu kamar yadda muka saba chan a lahira kaikuma a barka anan.”
     “Farouq you are going straight to hell and don’t you dare touch her-”
   “Then behave yourself” ya katsesa.
    “Naji I will karka tab’ata please.”
   “Hohoho did the mighty Mr. Fauzi just said please? Lallai fa kanason Flower nan taka sede ba kamar yadda nakeson taba.”
    “Farouq please shut up kafad’amin inda take banida lokacin jin nonsense naka, ina ka kaimin mata?”
     “In fad’a maka inda take? Karka damu very soon zaka sani sede you’ll pay an amount in return. Kuma the next time ka sake cemin nonsense ka yarda dani baraka sake sa Flowerka a ido ba” ya k’are maganan yana shafa fuskar Fannah.
      “Me kake nufi Farouq? Ransom?”
    “Brilliant sesa nakeson harka da mutane masu ilimi kamarku ransom nake nufi”
    “Farouq kasan meh? You are going straight to hell.”
     “And your Flower is going with me” nan ya d’aga hannu yasake shafo fuskar Fannah da sauri ta kawar da kanta.
     “Ina take yanzu? Taya ma zanyi trusting maqaryaci kaman ka? Taya zan yarda Fannah _TANA TARE DA KAI?”_
       “Smart guy barin maka proving” cike da mugunta yasa hannu ya b’antare cellotape dake bakin Fannah wani irin azabartaccen ihu ta sakar wanda Anas yaji har tsakar kansa sannan kuma ta rushe da wani erin wahalallen ihu. Cike da tashin hankali Anas yayi maganar. “Flower! Flower!… Farouq please karka tab’a ta I will do anything dan Allah nace don’t touch her please…”
     “Shhh!” Yace da Fannah yana shafa bayanta har a yanzu bata bar kukan ba, nan ya dawo kan wayar.
     “Mekace Mr. Fauzi?”
    “Anything Farouq please karka tab’ata I will do anything ka had’ani da ita please.”
    “Zan had’aku na minti d’aya in exchange of N500,000 (dubu d’ari biyar) inkuma kanason kaji muryar Flowerka fiye da minti d’aya sekayi multiplying kud’in per minute N500,000 and karka yimin wasa da hankali zan maka sendn bank details d’ina inhar banga alert ba zuwa yamma believe me baraka sake sa Fannah a ido ba.”
        “Farouq are you crazy? Wani irin hauka ne haka?”
    “Fine and good bakason jin muryarta kenan am hanging up” fuskar Fannah ya juya cike da muguntan da yasata sakar da k’ara.
      “Please don’t okay, okay I will ko nawa kakeso zan baka please kadena sata kuka.”
    “Good boy Anas ga Flower ku gaisa kunada minti biyu” nan yasawa Fannah wayar a kunne cikin sautin kuka ta kira sunansa “Habeebi”
     “Shhh! Flower don’t cry kinji?” magana take cike da tashin hankali dakuma tsoro.
     “Habeebi ina tsoro dan Allah stop him yace ze zubar min da ciki, Habeebi ze kashe mana baby, dan Allah ka barsa ka hanasa karka barsa please Hab-” bata k’are maganar ba Farouq ya ciro wayar daga kunnenta “munafirci kike agabana?” Nan ya mik’e “kuma cikin seya zube, sena zubar kina wasa da Farouq.” fashewa tayi dawani erin matsanancin kuka jin haka Anas ya sake kid’imewa
     “Hello…?” Anas yayi maganar cike da tashin hankali.
     “Hello Farouq please speak up.”
    “Meh? Meh? Kana cika min kunne fah.” Cewar Farouq ganin Fannah nada niyyan sake magana yayi sauri ya toshe mata baki da hannunsa d’aya.
       “Farouq dan Allah kabar sata kuka, karka tab’a lafiyar Fannah I beg you ko nawa kakeso zan baka dan Allah karka mata wani abu she is sick already please karka mata wani abu.”
     “Hohoho!!! Mr. Fauzi ashe ka iya rok’an mutum sede kash! Barin bar shegen ajiyar da kayi cikinta yaje ko inaba I must destroy it” jin haka Fannah tacize masa hannu da k’arfin da Allah ya bata take ya jefar da wayar wanda beyi landing ko ina ba sekan cinyan Fannah. K’ara sosai ya saki se buga hannun nasa yake a iska cike da azaba.
     Anan tasamu daman magana “Anas Habeebi please help me dan Allah karka bari yamin wani abu Anas our baby please stop him.”
     “Shhh! Flower bar kuka kinji its bad for your condition kuma in shaa Allah ba abinda ze miki. I won’t rest sena k’wato ki hannun Farouq bar kuka. Kinsan ina ya kaiki? Kinsan address d’in wajen?”
     “Habeebi bansani ba a sume ya taho dani gidan all I know is babban buildin-” bata samu daman k’are maganar ba sakamakon marin da Farouq ya wanketa dashi wanda har cikin kunnen Anas seda yajiyo k’aran marin kuka tasoma papawa ba makawa abin tausayi.
    “Ni zaki ciza? Eh? Bakida hankali ne?! Karki damu by the time na zubar da shegen abinda ke cikinki zaki shiga hankalinki mschw!” ya sake kallon hannun nasa a fusace sannan ya katse wayar tare da cire sim d’in ya taune sannan ya yasar. Kuka sosai Fannah ke kamar zata cire ranta. Wayanta dake kan gado ne ya soma ringing Farouq na dubawa yaga Habeebi wani dogon tsuka yaja sannan ya katse wayar nan Anas ya sake bugawa Farouq na katsewa kusan sau uku se a karo na haud’u Farouq ya d’aga.
      Cike da tashin hankali Anas ke maganar “Farouq please karka ma Fannah wani abu, karka rabata da babynta ko nawa kakeso zan baka please don’t do such evil please karka rabata da abinda ke cikinta ka fad’a ko nawa kakeso zan baka please Farouq…”
      “Huh! Let me see yanzu senayi tunani, zaman da zanyi dan gudanar da tunanin is 2 million sannan inna yanke hukunci sanar dakai zanyi nanma 2 million, kanaji na?”
     “Inaji Farouq wannan ba matsala bane please karka mata wani abu batada lafiya she is your sister please karka mata wani abu.”
     “Naji seka fad’a mata karta min misbehaving if not I might lose my patience.”
     “Okay zan mata ka bata wayar please.”
     “Kasani each minutes costs N500,000 d’azu kunyi 2 minutes 1 mil kenan.”
     “Farouq yaushe mukayi 2 minutes ba katse wayar kayi ba?”
     “Then fine zan kashe wayar-” da wuri Anas ya katse sa, “A’a please kar ka katse I will pay just give her the phone.”
    “Good” nan ya maido da kallonsa kanta “ke! Gashi sauran kimasa wani munafircin kiga in ban rabaki da shegen dake cikin ki ba.” Hannu d’aya ya since mata tare da bata wayan sannan ya yi gefe guda a d’akin yana me zuba mata ido.
       “Flower kinaji na?” cewar Anas. Cikin sautin kuka ta amsa “eh Habeebi.”
    “Good kibar kuka kinji? And kiyi duk wani abinda ya buk’ace ki muddin be sab’awa muslinchi ba I promise I will let yo out of there, I love you.”
    “Habeebi I miss you please karka d’au lokaci kazo ka d’aukeni, I don’t trust Ya Farouq dan Allah Habeebi.”
    “Flower stop panicking and do as he says I will come in shaa Allah kinji? Kibar kuka zeyi affecting lafiyarki, I love you.”
     “I love you too Habeebi, I love you so much.” Kafin Anas yasake cewa wani abu Farouq ya fisge wayan “time up!” ya sanar da Anas.
   “Farouq please ka bata wayan I will pay you.”
    “Nasani sede kakai limit naka na yau sekuma gobe if you are lucky.”
     “Please Farouq.”
    “Why being so insistant? Wallahi ka sake roqana baraka sake magana da ita ba mschw!!”
     “Okay but please Farouq feed her kabata abinci kasan condition nata zama da yunwa won’t help.” Kallon faracunsa yake sannan yace, “aww! kana nufin wai shegen cikin dake jikinta?”
    “Eh shi Farouq dan Allah feed her karka barta da yunwa.”
    “Toh ai banida kud’in bata kalan abincin data saba ci a gidanka ka turo kud’i kamar miliyan d’aya haka se a siya mata abinci me kyau.”
   “Okay I will do it, zanyi just kar ka barta da yunwa.”
    “Naji kana cika min kunne zan maka sending acct details d’ina sauran ka b’ata a irgen kud’ina kaga tashin hankali” yana kaiwa nan ya katse wayar nan da nan yatura wa Anas acct details nasa ba tare da b’ata lokaci ba Anas yama PA’nsa magana akayi ma Farouq transfering 7 million yana zaune a gefen Fannah yana gasa mata bak’ak’en kalamu alert yashigo ta wayarsa bayan ya duba ya sakar dawani shu’umin murmushi “wifey mijin nakin nan baya wasa now you can have your lunch tunda ya cika alk’awari” wani number yayi dialing a wayarsa;
     “Okay angama had’a dining d’in?”
    “Eh Boss angama komai is ready.”
    “Good!” nan ya katse. Igiyoyin da yabi ya k’ulle mata jiki dasu yabi ya sissince “tashi muje kichi abinci wifey.” K’in miqewa tayi cike da mugunta ya miqar da ita daga saman hannunta k’ara soai ta sakar haka ba tausayi yajata zuwa wani had’ad’d’en d’akin da aka tsara sa as dining room dogon table ne wanda aka cika sa dam da abinci kala kala wane (feast) kujeru biyu ne kad’ai a both ends na table d’in kujera d’aya yaja mata ya zaunar da ita sannan yakoma nasa shima ya zauna.
      “Eat my lady duka wannan naki ne kichi babynki yasamu yaci shima kafin in rabaki dashi.”
      “Ya Farouq mesa kake haka? Me na maka? Yanzu zakaso ache kanada sister sannan wani yana mata haka?”
    Fork yakai baki “unfortunately banida sister so kichi abinci.”
     “Kabani dalili d’ayan da zesa inchi wannan abincin, nasani ko kasa abinda ze zubar min da ciki aciki, banaso.”
    “Wifey kinga karki min rashin kunya anan eat.”
    “Barin chiba Ya Farouq dan Allah ka fitar dani daga nan ka kaini gida gun mijina please.” Banza da ita yayi ya d’au wayarta ya kira Anas ringing d’aya Anas ya d’ga “hello.”
     “Mr. Fauzi”
   “Na’am Farouq baka ga alert d’in bane?”
   “Nagani kama Fannah magana tadena cika min kunne da surutu I might lose my patience and if that happens zaku iya rasa shegen ku.”
     “Kabata wayar please I will talk to her.”
   “Na fad’a maka ka riga kayi exhausting time naku na yau.”
    “Nasani Farouq ka taimaka please.” Ido yama mutumin dake gefensan tare da miqa masa wayan yakai wa Fannah.
      “Hello Flower please kichi abincin kinji? Ko kinason abu ya samu babynmu?” Kai ta kad’a wane yana kallonta.
    “Kinaso?”
    “A’a banaso Habeebi bansani ba koyayi poisoning abincin.”
     “Beyi ba Flower in shaa Allah beyi ba kichi kinji? I’m coming for you I love you.” Bata samu tace masa she loves him too ba mutumin ya k’wace wayan.
      Plate d’in ta jawo tayi bismillah sannan takai kad’an daga cikin pepper soup d’in kifin bakinta a hankali tasamu tad’an cika cikinta fargaba ya hanata k’oshiwa. Bayan sun gama ya buk’ace ta data bi bayansa. “Ya Farouq kai baka Sallah ne? Dukda bansan k’arfe nawa bane amman nasan Azahar da La’asar sun wuceni.”
     “Ohh wifey ni ai banayi had’asu nake duka se isha zan yi amman tunda kince haka taho in rakaki” bejira tace komai ba yaja hannunta zuwa d’akinsu daya tanar masu har cikin bayin ya rakata “ko kinason kiyi wanka?”
       “I wouldn’t mind tunda ba a cikin k’azanta ka d’aukoni ba” tabasa amsa tana me k’arewa bayin kallo mamaki ne yacika ta shin ina Farouq yasamu kud’i haka? Daya karanchi hakan seya murmusa “mamaki kike? Karki damu ba sata nayi ba bashi na karb’a kuma har na miyar musu da kud’in da Anas yaturon” sede har a yanzu bata bar kallonsa ba nufin bata da yarda ba.
    “Wallahi kuwa wifey ko mamakin ya akayi nasan gidanku kike? LOL long story;”
      _“Da barina prison yanzu sati biyu kenan bashin danaci na yi mana wannan siyayyan shine wanda Baba yayi amfani dashi yayi bailing d’ina kuma drugs ne source na kud’in. Inada wani abokin dake siyar da coccaine shine yabani bashin miliyan 5 dashi na aiwatar da komai. Bayan fitowana da kwana biyu na shirya tsaf naje Enterprise na Habeebinki namusu k’arya cewa business man ne ni ina kuma neman appointment dashi sam receptionist d’in ta hanani ganinsa saboda nak’i bata personal information akaina, me gadin wajen nasamu na tsara sa har seda ya fad’amin k’arfe nawa Anas yake tashi daga office anan ne nasamu nayi timing nasa bayan da aka tashi na biyosa anan ne na ga gidanku. Dalilin dayasa nasan rana kinfita kuma bada Anas ba kuwa itace yawan zama dana keyi a unguwanku ganin driver yazo ya d’aukanku naje na shirya nima, dawowa na yayi daidai da shigowarku achan na tsare driver bayan ya ajiyeki namasa tsinannen duka dan k’in bani had’in kai dayayi, seda nayi pulling masa bindiga ya yarda yakaini ciki. Dana jima da kashesa sede kuma naji anacewa security doors ne a gidan naku inba wanda yasani ba baya bud’uwa._ Any question wifey?”
     Kai kawai take kad’awa tana tausayawa d’an uwan nata kalan rayuwar daya d’au ma kansa. “Allah shiryeka Ya Farouq inhar kaid’in me shiryuwa ne shikuma Moosa daka rufesa a d’aki so kake ya mutu ne? Ka tuna d’an Adam ne shima mejin yunwa.”
     “Karki damu wifey your wish is my command yanzu yi wanka abinki cikin wardrobe akwai kaya seki zab’a d’aya ciki kisa, I love you.” Tsuka taja “wifey I said I love you.”
    “I hate you Ya Farouq na tsaneka.” Bakinta ya maquro “what did you say?”
    “I said I hate you, ka sakemin fuska mugu kawai” tahau kai masa bugi.
    “Quit it!” Ya daka mata tsawa. “Kin d’au wasa nake ko?” Hannu yasa ya yage mata hijabi tun daga sama har k’asa kafin ta hankara ya had’a ta da  bango tare da kai hancinsa wuyanta yana wani shunshuna mata jiki. Hannayenta daya matse jikin bangon take ta k’ok’arin k’watansu amman takasa. “Ya Farouq dan Allah kabari” ganin yasoma wuce gona da iri ta qurma wani irin ihu dukda haka be dena gudanar da abinda yayi niyyah ba dabara ce ta fad’o mata k’afanta ta d’aga ta saita daidai abinsa takai masa bugi da k’arfi wani erin k’ara ya saki cike da azaba take a wajen ya durk’ushe anan ne tasamu ta k’wata kanta tare da d’ago hijabinta tana kare k’irjinta dashi.
© MIEMIBEE
81
      Kid’ime wa gabad’ai tayi tama rasa me zatayi ganin yadda Farouq ya rik’e abinsa se disco yake a wajen. Ta gefensa tabi ta papara da gudu har takai da k’ofan d’akin sekuma abin takaici takasa bud’ewa jijjik’awa take amman sam ta kasa tarasa wani irin k’ofa ne. “Fannah!!!” Ya kira sunanta cikin wani irin demanding sautin da yasata sakin fitsari kad’an a wandonta dan yadda ta tsure tana ganinsa yafito daga bayin tahau jijjiga k’ofar fiye dana da, makami take nema amman kap d’akin bata ga makamancinsa ba. Hannunta ya fisgo tare da sake mata wani erin wawan mari, k’ara ta saki sosai in agony.
        “Ni?! Ni zaki gulla?! In my manly place? Zaki yaba wa aya zak’inta yau” hijabin nata yaja seda ya rabata dashi “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri dan Allah” hannunta yaja seda ya fad’ar ita kan gado kafin ta hankara ya haye kanta kuka take sosai bakinta ya hau laluba data gano haka tuni ta maqale bakinta ciki ba yadda beyi ba ta fito da lips nata amman tak’i dan haka ya hau peppering kisses tun daga wuyanta yana sauk’a har cleavage nata yana wani shunshuna mata jiki tamkar tsohon maye. Kuka take sosai tana roqarsa, “Ya Farouq dan darajan ubangiji kabari dan Allah kayi hak’uri barin k’ara ba.” Hannayenta daya matsesu akowani side ta gefen kanta take ta k’ok’arin k’wato su sam ta kasa.
     Wani wawan mari yasake kai mata dan kashe mata jiki kafin tayi recovering daga marin yasa hannu ya yage ‘yar doguwar rigar dake jikinta nan yayi exposing bra nata wani irin popping out idanunsa sukayi ganin irin wannan halitta a gabansa be tsaya ba still ya cigaba da yagawa yakai ga cibiyarta kenan akayi knocking bisa k’ofar afusace ya tsaida abinda yakeyi “waye?” Ya tambaya cikin husky voice nasa.
    “Bello ne Boss you need to come please.” Tsuka yaja “naji I’m coming you can go” anan ya dawo da kallonsa kan Fannah da ba abinda takeyi se kuka ba sauti tana k’ok’arin kare k’irjinta da yayi exposing seda ya k’are mata kallo sannan ya d’ago daga kanta “we are not done kijira dawowa na” yana kaiwa nan ya fice tare da locking k’ofar ta waje.
      Wani erin matsanancin kuka ta fashe da tana tattara kanta a k’asa gefen gadon ta durk’ushe se kukan cire rai take “Ya Allah ka kareni daga sharrin Ya Farouq, Anas dan Allah kazo ka ceceni.” Tafi minti talatin wajen tana kuka sannan a hankali ta bud’o wardrobe d’in taciro wata baqar silky gown cikin wani drawer taga inner wears dubawa tayi seda ta samu size nata sannan tanufa bathroom achan ta yi wanka ta canza sannan tafito. Tafiya take tamkar k’wai ya fashe mata a ciki har ta isa gefen gadon ta sake durk’ushewa tana mai cigaba da kukanta tana tunanin Anas Habeebinta tana hawaye amman fuskarta d’auke da murmushi…
                ANAS
       Zaune yake a parlour idanunsa sun kad’a sunyi jazir, hannayensa duka biyu ya zirasu cikin gashin kansa, tamkar kurma da bebayi haka ya zauna yana zira wa marble floor nasu ido. Kallo d’aya za’a masa asan yana cikin matsanancin tashin hankali yafi minti uku ahaka ganin ba mahalicci se Allah ya d’au wayarsa Abuu ya soma kira bada dad’ewa ba ya d’aga bako sallama bale gaisuwa.
      “Abuu ya sace min ita, ya d’auketa Abuu ya gudu min da ita.” Cike da rashin fahimta Abuu yayi maganar.
   “Me kake fad’a haka Anas? Me ya faru? Waya sace waye?”
   “Fannah, ansace min ita Abuu I can’t live without her.” Salati Abuu ya sakar “ansace Fannah? How? When? Why?” Ya jero masa duka wad’annan tambayoyi cike da tashin hankali. Stammering yake “Aa… Abuu nima bansani ba d’an uwanta ne Farouq he is obsessed with her shiya zo ya sace min ita…” nan ya labarta wa Abuu duk abinda ya sani. Salati yake har a yanzu “calm down Anas don’t panic in shaa Allah we will find a way amman kaima kayi ganganci taya gida kaman naka ba security men iyyeh?”
    “Abuu security doors ne baya bud’ewa seya san mutum.”
    “Then taya akayi ya bud’e wa Farouq d’in? Kayi ganganci Anas.” Shiru Anas yayi yana nazarin how?
    “Ina CCTV naka? Kaje ka duba coverage d’in kaduba kaji?” Kwata kwata Anas ya manta da yanada spying cameras a gidan se yanzu tsantsan tashin hankali da “okay” ya katse wayar nan yayi connecting tun daga shigowar Farouq gidan da kolar Moosa rik’e a hannunsa d’ayan kuma da bindiga coverage d’in ya soma playing  anan ne Anas yaga ta yadda Farouq yasamu ya shigo to waima taya Farouq yasan gidansu?? Adaidai lokacin da yake sa kai cikin parlourn video d’in ya k’are.
    Wani irin urge to kill Farouq ne yake ta bugawa a birinin zuciyansa a yayinda yake cizan bottom lips nasa. “Farouq you are as good as dead, ‘cause I will kill you with my own hands.” Abuu ya kira sede ba kamar d’azu ba yad’an samu natsuwa yanzu bayan yabawa Abuu labari dukansu suka hau nazarin wani hanya zasu b’ullo ma wannan al’amari.
    “Kayi waya dashi kace koh?”
    “Eh har 7 million ma na masa transffering.”
    “7 what??? Anas bakada hankali ne?”
    “Abuu he was serious ze illata ta inban tura kud’in ba, banson abu ya tab’amin Flower.”
    “Shhhh! Karka damu meet me at State Police Station yanzu.”
    “Okay I’m on my way amman Abuu su Mami fa in sanar dasu?”
    “A’a tukuna karmu tada musu hankali.” Da “okay” ya amsa yaje ya d’ago keyn motarsa ya fice a 360 in less than 15 minutes ya isa Station d’in already Abuu na jiransa baya sun shiga ciki akayi ma Anas tambayoyi be b’oye komai ba duk abinda yasani ya fad’i musu bayan nan ya ciro CCTV coverage d’in ya basu sukayi playing daga nan suka d’au investigation.
    MTN office suka nufa dan tracking location da akayi wayar sede ba’a samu anyi ba dalili kuwa itace sim card d’in is no more efficient bara a iya detecting ba saboda karya sim d’in da Farouq yayi. Cikin tashin hankali Anas ke maganar “toh ai munyi waya dashi ta wayar Fannah.”
    “Are you sure?” Abuu ya tambayesa.
   “Yes Abuu munyi.”
    “Good” cewar mutumin dake carrying out detection d’in. Numban Fannah aka basa ganin is efficient duk suka sakar da hamdala detecting location da bai d’aukan koda minti d’aya amman mutumin yafi minti uku kai, yayi nan yayi chan yakasa gane kan abin. Gajiya da ganin abinda yakeyi Anas yayi magana; “wai meke faruwa ne Ilyas? Tun d’azu ka kasa detecting.”
    “Mr. Fauzi we can’t detect the call baramu iya tracking nasa ba”
    “Dalili?” Anas ya tambaya.
   “Dalili kuwa itace anyi disabling GPS radio, bayan nan anyi turning off data d wi-fi radios kaga ko ba yadda za’ayi mu iya tracking down location d’in.”
     “Ilyas please there must be a way” a lokaci d’aya ya fusata “he ran away with my wife, MY WIFE!! kuma kana zaune nan kana cemin ba abinda zamu iya, are you crazy?!”
    “Anas calm down” cewar Abuu yana taresa.
    “I’m sorry” cewar Ilyas “we can only track him down inhar ya bud’e data connection koyayi enabling GPS ka gwada kiransa yanzu ta layin matar taka.” Ba tare da b’ata lokaci ba Anas ya kira layin Fannah, Farouq dake cikin mota acikin gari ta kusa da babban kasuwa ya murmusa sannan ya d’aga wayar.
     “Hello hello Mr. Mr. Mr. Fauzi the smart guy” kafin Anas yayi magana system yafara blinking location da Farouq yake a cikin Maiduguri.
     “Farouq ina Fannah?”
     “Tana nan tare dani ko system nakun be nuna muku inda nake bane har yanzu?”
    “What are you talking about Farouq?” Anas yayi kamar be fahimce sa ba.
   “LOL you can’t fool me you know, ko acewarka bansan kunyi tracking d’ina down bane?” yatsaya ya murmusa ta gefe sannan ya cigaba “nayi installing cellphone spy softwar cikin wayarta kuma ya nuna min ana tracking d’ina bayan nan I aslo noticed zubar da charge da wayar keyi wanda ba’ayi amfani dashi ba same goes to data usage banyi using data nata ba amman yanata k’arewa shi kad’ai kasani Farouq isn’t stupid nayi zaman prison idanu na sun bud’u and trust me baraka sake sa Fannah a idanun ka ba.”
      “Farouq plea-” be k’are maganan ba Farouq ya katse wayar. Kuka wane d’an yaro Mr. Fauzi yahauyi a idanun mutane Abuu yana rumgume dashi. “Abuu ze mata wani abu, please stop him.”
    “Anas kuka fa ba option bane, rayuwar matarka nacikin had’ari katsaya nan kana kuka? Will you man up and do whats right! Will you?” Kai ya gyad’a tare da d’agowa daga jikinsa yana share hawayen nasa. “Good! Yanzu muyi sauri muje nan kasuwan inda system ya nuna.” Waya yayi ma police duk suka shirya kusan a tare suka isa wajen sede sam ba alamar gidan da za’ace anyi kidnapping mutum ciki.
      Rarrabuwa sukayi cikin kasuwan suna neman either Farouq ko Fannah kap suka zagaya kasuwan ba ko alaman d’aya daga cikinsu, Anas ji yake kamar ya kashe kowa kawai tunanin had’uwansa da Farouq kad’ai yake. Waje yanema ya zauna cikin kasuwan tare da had’a tagumi “Anas ka tashi mu koma basu nan kaji?”
    “No Abuu I’m not leaving sena samu Fannah.”
    “Anas nasan da zafi amman hak’uri zakayi basu anan lets go home in shaa Allah nan bada jimawa ba zamu sameta.”
    Kuka ya soma “Abuu wani hali take ciki yanzu? Ina yakai min ita? Meyake mata? Abuu I can’t have peace of mind har sena samu Fannah.”
    “And we will, we will in shaa Allah zamu sameta yanzu muje gida haka” da lalashi Abuu yasamu yasasa cikin mota suka tafi.
                     *FANNAH*
     Bayan data gama shan kukanta wani wahalallen bacci ne yaso yin awon gaba da ita amman dan fargaba takasa baccin se gyangyad’i take ana cikin haka taji an murd’a handle na k’ofar wani babban gyalen kashka datasamu cikin wardrobe d’in wanda ta lullub’e jikinta dashi ta sake maquroshi jikinta ganin Farouq ne jikinta ya hau sabon rawa batasan a lokacinda ta fara sabon kuka ba again tana me matsawa baya.
     “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri na tuba dan Allah karka min wani abu” wani irin kallo ya watsa mata sannan ya maida k’ofan bayan ya zauna kan gadon ya buk’aceta data hauro ta zauna itama sam takasa dan wani erin tsoronsa da takeji sekace dodo. “Kizo ki zauna anan don’t let me repeat myself, dake da wanda kike kira mijinki bansan wayafi wani taurin kai ba come and sit!” Ya daka mata tsawa batasan a lokacin data hauro ta zauna ba se b’ari take.
    “Kinsan meh mijinki yamin? Kinsan meh?”
    “A’a” ta amsa hawaye na gangara kan kumatunta. “Kayi hak’uri dan Allah.”
    “He had the gut to track me, me! Ni yakeson raina ma wayo lallai kuwa ya d’ibo ruwan dafa kansa sena zubar da wannan shegen ajiyan da yayi a cikin naki ze shiga hankalinsa.” A kid’ime tasoma maganar tana b’arin baki “a.. A.. A’a Ya Farouq ddd… daan Allah kaji k’aina karka min haka kayi hak’uri dan Allah karka rabani da baby na please na rok’e ka Ya Farouq” ta k’are maganar cikin sautin kuka.
    “Mijinki zaki rok’a bani ba he should stop getting on my nerves”
    Side drawer yaja tare da ciro kwalin wani baby nokia sabo nan ya bud’e yasa wani sim chiki. Wayarta dake aljihunsa ya zaro ya zuba numban Anas sannan ya kira.
     Anas na zaune a d’akinsa su Ummie, Amal, Shettima da Abuu kowa tsaye akansa yana basa hak’uri amman hakan be hanasa kukan dayake ba jin rurin wayarsa yayi sauri ya d’aga tare da sawa a kunne. “Hello?”
    “Smart guy” cewar Farouq.
    “Hello Farouq.”
    “Miqo wayar nan” cewar Abuu amman Anas ya hanasa.
    “Yess Mr. Fauzi kasani da abinda kayi ka jefa rayuwar d’anku cikin had’ari dan ayanzu haka shirin aborting cikin nake.”
    “Farouq dan Allah kayi hak’uri please karka raba Fannah da babynta I’m sorry barin sake misbehaving ba.”
    “Wannan kuma chan maka gata kuyi magana kafin in gudanar da aikina nan gaba baraka sake crossing d’ina ba.” Nan ya miqa wa Fannah wayar kuka take sosai wanda har ba’a jin muryarta clearly.
    “Anas Habeebi” kad’ai ta iya cewa.
    “Flower please stop crying kinji?”
    “Anas zemin aborting baby mesa barinyi kuka ba? Anas mesa kayi tracking nashi down? Da ka barshi kawai kasan wani erin mutumi ne Ya Farouq bashida imani” jin ance baida imani yasakar dawani murmushi. “Anas he will harm our baby please kayi duk abinda yace banason in rasa baby na please.”
    “Flower I’m sorry bansan yin hakan ze haddiso mana da matsala ba please kibar kuka bare ma babynki komai ba in shaa Allah kibar kuka kinji?” Kafin ta sake magana Farouq ya fisge wayar. “In aka gama aborting cikin zan sanar dakai lafiyar matarka I’m hanging up.” Da sauri Anas ya katse sa “no please Farouq ka fad’i konawa kakeso zan baka dan Allah karka tab’a lafiyar Fannah.” Hannu Abuu yasa ya amshi wayar “hello Farouq?” Jin bak’on murya ya sa ya koma ya zauna kusa da Fannah yana murmusawa.
 
     “Ouuu! Harda baqo nayi ne a wayan?”
     “Farouq mesa bakada hankali da tunani ne? Tsakaninka da Anas wa ya kamata yana abinda kakeyi? Ko ka manta Fannah jinin kace? ‘yar uwarka ce fa, yanzu zakaso ace kanada sister ana mata abinda kake ma Fannah?” Dogon tsuka Farouq yaja “common shut up koban tambaya ba nasan kaine kakan shegen abinda ke cikinta toh kasani in akoi abinda kunnuwana are resistant to shine wa’azi karka ma b’ata lokacinka ehe! Bawa d’an naka wayar kokuma wallahi in zubar mata d cikin dake jikinta take anan kune da asara bani ba.” Zuciyan Abuu tafasa yake kafin ya fad’i wani zancen dazesa Farouq zubar wa Fanah ciki a lokacin Anas ya amshe wayar.
   “Farouq please ya isa ka fad’amin nawa kakeso zan baka amman don Allah karka aikata abinda kake fad’in zakayi.”
     “It depends in bakason na zubarwa Fannah cikinta sekayi abinda nakeso.”
   “Zza.. Zanyi Farouq I will please don’t touch her.”
    “Tab’ata? Tab’ata kam ai yazama missed call abu kad’an ya rage ban shigeta ba d’azu.” Wani irin kishi ne ya cakki Anas wane takwabi a zuciyarsa ba abinda yake fata aransa illa ranan had’uwan shi da Farouq.
      “You are lying you son of a b*tch I’m going to kill you with my own hands I swear.”
    “Hohoho!! Jealous? Sena had’aku kaji daga bakinta” nan ya maido da kallonsa kan crying Fannah “gashi fad’a masa meya faru tsakani na dake d’azu” ya maqala mata wayar a kunne. Cikin sautin kuka ta kira sunansa “Anas Habeebi.”
   “Hello Flower tell me he is lying, be tab’aki ba aiko?”
    “Anas he did, he tried kissing me ya yaga min kaya ba abinda bemin ba, Habeebi ina tsoro dan Allah help me” ta rushe da kukan kuka…
 MIEMIEBEE
 Anas besan lokacinda ya fasa glass cup dake hannun saba daga riqo tsantsan wani irin baqin kishin daya tokaresa jin abinda Farouq yama Flowersa, kasancewar fatar jikinsa bame k’arfi bane take glass d’in yamasa kaca-kaca da hannu. K’ara Ummie da Amal suka sakar ayayinda Abuu da Shettima sukayi kansa suna tattara broken glasses d’in. Idanunsa take sukayi wani irin wawan jaaa a yayinda zuciyarsa ke wani erin tafasa. Amsar wayan Farouq yayi daga kunnen crying Fannah “Mr. Fauzi kaji ka gaskata zance na?” Cikin wani erin muryar da ban tab’a sanin Anas dashi ba yayi maganar “Farouq kaji na rantse I WILL KILL YOU WITH MY OWN BARE HANDS kawai kajira had’uwa na dakai.” “Hohoho!!! Kafin ka kasheni nikuma zana kashe maka Flower I have to go kasan akwai aikin abortion gabana” yana kaiwa nan ya katse wayar koda Anas ya gwada kiransa back cemasa ake the number does not exist kasancewar Farouq ya karya sim d’in yakuma kashe wayar gabad’aya ya cire battery bare sake amfani dashi ba gudun kar ayi tracking nasa down. Haka yayi da wayar Fannah ma ya cire sim nata ya karya yakuma kashe wayan. Wasu erin zafaffun hawaye ne suka soma sauk’o ma Anas akan kumatu. Waje Ummie tayi da Amal ganin Anas na kuka again. Daidai Abuu ya bud’e baki zeyi magana kenan wayar Anas ya soma ruri Abuu nakai dubansa yaga Mami. Kafin ya d’aga ya kalli Anas ganin ko kad’an hankalinsa bai jikinsa ya d’aga wayar kawai. “Hello Maman Fannah.” “Assalamu Alaikum” tace. “Wa’alaikis salam Abban Anas ne.” “Ayyah ina wuni?” Ta gaishesa. “Lafiya alhamdulillah” ya amsa. “Ya kowa da kowa?” “Duk k’alau.” “Masha Allah nace ko Anas na kusa inason muyi magana ne da Fannah nayita kirar wayarta bata d’agawa.” Zuciyarsa yaji yayi dum! Ya buga yama kasa magana. “Hello…?” “Maman Fannah inason ki saurareni dakyau dan Allah kuma kisani muna kan bakanmu na neman Fannah baramu tsaya ba semun sameta.” Gaban ta taji yayi mumunar fad’i. Bayan salatin data sakar cike da tashin hankali tayi k’arfin hali tace, “Abban Anas meya samu ‘yata dan Allah?” “Ki kwantar da hankalinki please, ‘yar ki Fannah ta na wajen Farouq yanzu haka as we speak…” Nan ya kwashe labarin komai yabata. Salati take alokaci guda idanunta suka ciko da hawaye. “Yaushe Farouq da mahaifinsa zasu fita harkar Fannah subarta taji dad’in rayuwa? Me tayi musu?” Hak’uri Abuu ya riga bata sannan daga bisani ya katse wayar. “Anas ka kwantar da hankalinka kaji?” “No Abuu I can’t.” Ya fad’a rai a b’ace. Hannunsa daya yayyanke Shettima yayi yunk’urin tab’awa “don’t touch me Shettima just leave please both of you dan Allah kufita min a d’aki am sorry please.” Kai kawai Abuu ya girgiza he understands exactly what his son is going through. “We will Babana zamu bar maka d’akin just behave yourelf, Shettima mu fita.” Nan suka fice, hankalain Shettima ya matuqar tashi kasancewar yasan halin wan nasa sam be iya rungumar k’addara ba tsoronsa kar Anas yakoma shaye shaye irin na da. Bayan ficewansu Shettima Anas ya miyar da kallonsa kan hannunsa me zuban jini alokaci d’aya ya miqe yashiga bathroom sabon spirit ya bud’e ya bulbula kan hannun nasa k’ara ya saki sosai dan sharp pain dayaji,gritting teeth nasa yake dan azaba idanunsa matse gagam. “Atleast I can feel kad’an daga cikin pain da kike feeling Flower, atleast you are not alone in this, atleast zan iya feeling koda half of your pain.” Fuskarsa ya d’ago yana kallon mirror instead yaga fuskarsa se fuskar Fannah kad’ai yake gani ciki, tunaninta duk yabi ya mamaye masa k’wak’walwa. Da tunanin abinda Farouq ya sake hitting masa k’wak’walwa kuwa besan a lokacin da ya shure kwalabai da robobin mayukan shafe-shafe da suke kan counter d’inba. “Fannah _TANA TARE DA SHI_ No! he can’t take away Fannah from me, Fannah is mine, Farouq I will hunt you down like an animal.” A fusace yabaro bayin besan a lokacin daya ciro wani dogon kara daga k’ark’ashin gadon sa ba yasoma fashe fashe daga kan TV, dressing mirror, hanged mirror ba abinda be fasa ba. Abuu dake parlour ne jikinsa yabasa ba lafiya ba agurguje ya bud’e k’ofar d’akin ya tarar da Anas d’auke da wuk’a yana kan tsaga tafin hannunsa se cize bottom lips nasa yake cike da azaba amman hakan be hanasa cigaba da gudanar da abinda yakeyin ba. “ANASSSS!!!!” ya kira sunansa diabelievingly a yayinda su Ummie ke bayansa suna sakar da salati kansa Abuu ya nufa ya tsinka masa mari tas kukeju take Amal ta b’uya bayan Ummie. “Bakada hankali ne iyyeh? Whats all this?” Yayi maganar yana k’are kallo wa mess da Anas yayi wa d’akin. “Ina ka kai hankalinka?” Hannu yasa ya k’wace wuk’an. Se anan Anas yayi magana; “Abuu give me back kabani please, be kamata inbar Fannah kad’ai tana shan wahala ba kabani wuk’an kaga se muna feeling pain d’in tare.” “Anas get your senses together kanajina koh?! What nonsense. Nasan wannan abu ne meh wuya amman hak’uri zakayi kamar yadda nayi nima da Ummiminku ta tafi ta barni, balle ma kai ba tafiya Fannah tayi ba kidnapping nata akayi kuma in shaa Allah zamu sameta meye amfanin wannan abubuwan da kakeyi iyyeh? It has to stop!” Ummie ce tasa baki; “A’a Ya Ibrahim kamishi uzuri, wannan tsaka che me wuya shi kad’ai yasan yadda yakeji kaima kasan how it feels like. In zaku bani dama kufita ku barni dashi” nan ta k’ariso cikin d’akin da Amal biye da ita batare da Abuu yace komai ba yafice haka Shettima ma. “Amal kema bisu.” “No Ummie please kibarni in zauna da Ya Anas” dagudu taje ta rungomoshi tana hawaye. “Ya Anas in shaa Allah zamu samu Fannah wannan mugun Farouq d’in bare mata komai ba, bare mana harming baby ba because we love our baby ba?” Sam be amsata ba kai kawai ya gyad’a mata daga baya a hankali nan da nan Ummie ta gyara masa kan gado suka hauro dashi ita da Amal. D’akin tashiga tattarawa ayayinda Amal ta aza kan Anas a cinyointa tana shafa gashin kansa a hankali bayan ta tare jinin dake d’iga daga hannunsa da tissue. Bayan Ummie tagama kimtsa d’akin ta taho da bowl d’auke da towel ciki d’an k’ananun yankan da Anas yajijji a jikinsa agarin fashe fahsen dayayi dakuma yankan dayaji wa kansa ta goggoge tayi treating masa cikin k’ank’anin lokaci ta kimtsa sa. “Zakaci abinci Babana?” Ta tambayesa shiru yayi be amsata ba hakan ya tabbatar mata baya jin yunwa. “Amal taso mu basa waje kinji?” Seda ya bari Amal ta mik’e sannan ya rik’e hannunta “ki zauna kinji Angel, don’t leave me too.” “Ya Anas I will never leave you _INA TARE DA KAI_ kamar yadda Ya Fannah ma take _TARE DA KAI”_ calming and soothing wors masu kwantar da hankalin d’an Adam Amal ta riga furtawa yayanta tana sake tabbatar masa dacewa Fannah tasa ce kuma zasu same ta, shi ya jasu sallan isha sam yak’i barinta ta fita daga d’akin cemata yayi a d’akin yakeson ta kwana ita akan gado shi kan couch*** Baa tare da b’ata lokaci ba Mami tasamu Baba ta gaya masa halin da ake ciki hankalinsa yayi matuk’ar tashi tuni Afrah da Aiman suka soma kuka Mami na mara masu baya. Ya Khaleel Baba ya kira sam munafikin Allah ya nuna masa besan halin da ake ciki ba ce musu ma yayi rabonsa da Farouq sati d’aya kenan yanzu. Suna gama wayar ya kira Farouq ya sanar dashi. Dariyan bosawa Farouq ya sakar “barsu Baba basuda hankali ne karka damu inada miliyan 2 yanzu sauran miliyan uku daga nan se muyi proceeding plans namu” “Kayi daidai Farouq danko Fannah taka ce tun kana d’an yaro kake santa.” “Maganar ka dutse Baba will get back to you later” nan ya katse. Maido da kallonsa yayi kan crying Fannah cike da azaba ya d’agota daga saman hannunta, mijinki is trying my patience you will have to bear the burden janta yayi zuwa d’akin d’azu tana had’asa da Allah amman ko sauraronta beyi ba d’aureta ya kuma yi sede wannan karan be toshe mata baki ba. Wani samsung S5 yaciro ya d’auketa hoto sannan yabi ta whatsapp yayi sending takan Anas yasan sarai Anas ba shiga whatsapp zeyi ba dan haka yamasa sending SMS Hurry! Smart guy and check in your whatsapp Amal ce ke kusa da wayar alokacin da saqon ya shigo. “Ya Anas you have a new message.” “Barshi Angel am not in the mood.” “Ya Anas inkuma ya shafi Ya Fannah fah?” jin ba k’arya a magananta ya miqe tare da amsar wayar bayan ya karanta hankalinsa ya sake tashi fiye dana da ba tare da b’ata lokaci ba yayi enabling cellular connection first message da yayi popping up ya bud’e ganin pictures na Flowersa hannaye da k’afafunta a d’aure kansa yayi wani erin mumunar bugawa, hannu yasa ya dafe kan nasa ta gefen migraine d’in. Cike da tashin hankali Amal ta matso kusa da shi tana dafe sa, “Ya Anas mene ne? Meya faru?” Kasa koda furta mata ‘A ’ yayi. Ba tare da b’ata lokaci ba yakira layin karap Farouq ya d’aga. “Hello smart guy now what? Zakayi as I say kokuwa I need to let her suffer some more?” “Farouq please let her go ka saketa dan Allah kai bakasan darajan ‘ya mace bane? Musamman ma me d’auke da juna biyu?” “Bansani ba kuma banason sani do as I say and I will let her go.” “You filthy son of a b*tch what the f*ck do you want? Meh kakeso?! ” Amal dake a gefensa seda taja da baya tsabagen firgita datayi dan kalan tsawan da Anas ya daka. “Zamuyi magana if you are ready, I’m hanging up.” “Kafad’a min meh kakeso and let her go.” “Miliyan uku nakeso… For now.” “Are you crazy Farouq?” “Yes I am, zakayi transferring kud’in kokuwa haka kakeson Fannah ta kwana?” “I will zanyi please ka saketa please.” “Ka turon kud’in first.” “Nace zan maka sending ka sake ta please.” “Senaga alert” nan ya juyo yana kallon Fannah dake ta kuka ba sauti. Fuskarta ya shafa “Farouq please kadena tab’ani banaso.” Maganarta har kunnen Anas. “Farouq me kake mata? Kadena tab’a ta please.” “Meh aciki dan na tab’a wifey na?” “Kai wai bakasan tab’a macen da muharramarka haramun bane?” “Bansani ba kuma banason sani send me my 3 mil and I will let go your wife.” “Son of a b*tch” cewar Anas sannan ya katse wayar nan da nan yama Kacallah magana aka mai transferring kud’in. Kacallah na sanar da Anas yayi transfer d’in yakira Farouq back sede sam layin yak’i shiga kodaya gwada trying na Fannah ma haka, hankalin Anas in yayi dubu be tashi ba he can’t wait gobe a fara investigating, fatan ranan had’uwansa da Farouq kawai yake. ** “Mijinki d’an Amanah Fannah har ya turo kud’in” cewar Farouq alokacinda yake since mata hannu. “Muje muci dinner.” “No way! Ya Farouq I have to pray first.” “Ba matsala zaki iya yin duk wani abinda kikeso tunda mijinki ya cika min buri.” “Burin meh?” Ta tambayesa tana shafa hannunta daidai wajen daya d’aure har seda yayi pink.” “Karki damu sooner zan sanar dake shiga kiyi alwalan ina jiranki.” Tsuka taja sannan ta shige bayan tafito ta had’a Maghrib da Isha yana zaune yana jirarta ko ajikinsa ma beyi Sallah ba, bayan ta idar yajata da hannu zuwa dining room nasu achan sukayi having dinner. “So wifey time to sleep koh?” “Kamar ya time to sleep?” “Ya kike kwana da Anas?” “Ya Farouq shin wai bakasan Anas miji na bane? Kaikuma ba muharrami na bane saboda haka barin had’a kwanciya dakai ba.” “Kinsan me nafiso? Nafison kina fighting d’ina haka ‘cause it gives me more and more reasons to fight you down, dani zaki kwana ko kinaso ko bakiso.” A fusace ya miqe ya doso gabanta tare da miqar da ita da hannunta. Hannun nasa ta hau bigewa “ka sakeni Ya Farouq let me go.” Ko saurarenta beyi ba haka yajata sama zuwa d’akin daya tanadar masu akan gado yayi wurgi da ita. Kuka take sosai. Kayan jikinsa ya hau cirewa boxers zallah yabari. “Ya Farouq dan Allah na had’aka da Allah kayi hak’uri ka kaini wani d’akin in kwana dan darajan manzon Allah.” “Zaki ajiye wannan mayafin agefe ne kokuwa?” Sake matse gyalen tayi ajikinta ganin batada niyyan cirewa ya nufeta tare da jan gyalen seda ya rabata dashi ihu tahau yi tana kiran sunan Anas. Dukiyar fulaninta ya cafko wani irin k’ara ta saki sannan daga bisani ta tsinke sa da marin da bai expecting ba. Cikin kuka take maganar “bakada hankali ne Farouq?” Yau ko yayan ma babu. “Wallahi the next time ka gwada yunk’urin tab’ani I wont hesitate to kill you mugu, azzalimi maras imani kawai wanda besan darajar mace ba Alla-” bata k’are maganar ba ya kawar da ita da mari. “Ni kika d’aga hannu kika mara dan fitsara? Sa’arki ne ni? You are asking for it.” Hannunta ya ja be tsaya ako ina ba se wani d’akin da ba komaj ciki banda uban duhu da poles guda uku ciki. “Ya Farouq ka sakeni mugu, azzalimi kawai ka sake min hannu” wani marin ya sake kai mata anan seda gefen bakinta ya fashe. A k’asa kusa da d’ayan pole d’in ya yasar da ita sannan ya d’ago wani thick igiya ya d’aure mata hannayenta duka biyu daga baya ihu sosai ta rigayi dan yadda ya matse mata hannayenta bibbiyu a bayan pole d’in sannan ya k’ulle da k’arfi gabanta ya sha ya k’ulle k’afafun ma sannan ya matso da fuskarsa gab da nata bata bar kukan ba har yanzu “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri ka sakeni please.” “Mu kwana lafiya kikace min a’a ba? Haka anan zakiyi spending night naki alone in this room.” Nan zuciyarta yawani buga tunda take bata tab’a kwana ita kad’ai ba se yau ita ina ma d’aki ne me fasali da dasauki. “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri.” Fuskarta ya riqo sannan yasoma laluban lips nata dawuri ta maqesu chiki haka yatayi amman tak’i barinsa yayi kissing nata, daya gaji ya d’auko cellotape ya manna mata a bakin “sleep tight wifey” yace mata tare da kashe wutan d’akin wani erin baqin duhu ne ya ratsa cikin d’akin alokacinda ya bankad’e k’ofar. Kuka take sosai tana ta murza hannayenta ko zata iya sinche igiyiyin amman takasa haka yadda taga rana taga dare seda gari ya soma wayewa ne tasamu wani wahalallen baci yayi awon gaba da ita. Shegen se 9:30AM ya tashi ko Sallah baiyi ba, bashin da ake binsa jiya ya sauk’e Asuba da Azahar kad’ai sauran se anjima in ya samu time. Bayan yayi wanka ya shirya cikin black top da jean trousers sannan ya nufa d’akin Fannah har a lokacin bacci take, tsugunawa yayi a gabanta fuskarsa d’auke dawani murmushin tsiya. Ba abinda yake kalla a fuskarta banda lips nata tsabagen k’azanta ko brushing Fannah batayi ba amman ahakan yakeson yayi kissing nata. Fuskarta ya shafo a hankali ganin batako motsa ba ya sake matsoda fuskarsa gab da nata ta yadda nishinsu ki tinkling. Abu k’iris ya rage yayi owning lips nata ta bud’e idanunta lokaci guda. Wani irin nishi taja tare da warwaro idanunta, baya yayi kad’an alokacin dayaga ta maqe lips nata. “Good morning wifey da alama you had a wonerful night” ya k’are maganar yana since mata igiyoyin. Ganin batada niyyan masa managa ya cigaba “muje kiyi wanka ina neman shawararki.” “Kayi duk abinda kakeso daman ka tab’a neman shawara na game da abu?” “Wifey mesa kike min haka ne? Kullum bakida abinyi banda fad’a dani mijinki?!” “Niba matarka bace kamar yadda kaima kake ba mijina ba.” “Nasani ai shiyasa nakeson muyi aure, auren sunnah.” K’irji ta dafe “aure? Ya Farouq dan Allah ka rufa min asiri taya zaka aureni bayan inada igiyan aure akaina??” “Wannan duk ba komai bane, zamu bar Nigeria zamu koma ko Ukraine ko Ghana seki zab’i k’asan da kika fiso.” Hawaye ne suka soma ambaliya kan fuskarta… durk’ushewa tayi har k’asa a gabansa jin ya ambaci barin k’asa gabad’aya. Rok’ansa ta soma “Ya Farouq dan girman Allah kayi hak’uri dan soyayyar da kake ma manzon Allah kayi hak’uri kaji k’aina karka kaini wani k’asa daban karka rabani da iyayena dan Allah Ya Farouq…” Ta k’are maganar cikin sautin kuka. Ina me baku hak’uri da posting da bana samunyi kwana biyu my phone is having a problem, ku k’ara hak’uri I love you guys so much © MIEMIEBEE
TANA TARE DA NI… PAGE 83 BY MIEMIEBEE “Haba! wifey me yayi zafi haka? Tashi please I’m trying to change your future.” “Ya Farouq dan Allah karka gudu dani zuwa wani k’asa daban please.” “Kinsan me wifey? Wannan had’ani da Allahn da kike ba tasiri zeyi akaina ba ki tashi kiyi Sallah muyi breakfast inkuma se anjima zakiyi sallahn then muje mu karya.” “No Ya Farouq! Allah yafika mugu, azzalimi maras imani kawai wallahi baraka gama da duniya lafiya ba, you are going straight to hell such a demon.” “Ki kirani da duk wani sunan daya miki abu d’ayan da nakeson kisani shine ke TAWA CE! YOU ARE MINE!” bejira ta sake magana ba ya finciko ta da hannunta ta sama be direta a ko ina ba se abayin d’akinsu “na baki minti goma kuma” yana kaiwa nan ya ja k’ofar ya rufe. Kuka me tsuma rai takeyi tafi minti biyar tsugune a bayin sannan daga bisani ta miqe tayi brushing sannan tayi wanka da alwala, kayan jikin nata ta miyar sannan cike da tsoro ta fito mayafinta na jiya ta gani a k’asa dashi tayi Sallah tariga roqan Allah daya kareta daga sharrin Farouq. Bada jimawa ba Farouq ya dawo d’akin zaune yasameta ta d’aga hannu sama tana addu’a, waje yanema ya zauna tare da zura mata ido har seda ta tofe. “Excellent ina fatan kinyi addu’an Allah sa d’an cikin kin me cetoh ne.” Cikin dashasshiyar muryar tace, “me kake nufi Ya Farouq?” “Zubar da cikin zanyi bazeyi mu tafi dashi Ukraine ba chan inda na yanke hukuncin zamu, I want us to start a new life.” “Nasan ba point rok’anka amman dan Allah ka rufa min asiri karka min haka Ya Farouq na rok’eka please kamin rai.” “Wifey fa ba ke nace zan kashe ba shegen abinda ke cikin ki nace zan kashe” ya nuna cikin nata da yatsa. “Before then muje mu karya inajin yunwa.” “Banaji kaje ka karya kai kad’anka” ta k’are maganar hawaye na ciko mata a ido. “Wifey kinga banason taurin kai nace muje mu karya” bejira ta amsa shiba ya fisga hannunta be direta a ko ina ba se akan dining chair nata “eat wallahi ko kici ko in zubar da cikin nan at this instant.” Shiru tayi bata amsashi ba, bara kichi bane sena zubar da cikin komeh??” “Meh amfanin chin abincin? Ko nachi ko banchi ba bashi ze hanaka aiwatar da abinda kayi niyyah ba.” “No wifey” ya shafo fuskarta wanda tuni ta bige hannun nasa. “Kichi barin zubar ba.” Idanunta ta d’ago tana kallonsa da nufin bata yarda ba. “I swear wifey, kichi barin zubar ba, ki k’i chi in zubar.” “Kabani reason d’aya da zaisa in yarda dakai.” “Because I’m Farouq, now eat.” Fork d’in ta d’aga tasoma ci bayan tayo bismillah se anan ya koma nasa b’angaren dining table d’in shima yasoma chin nasa kamar jiya yau ma fargaba ya hanata chin abincin sosai kad’an tachi taji ta k’oshi. Bayan da yagama chi ya sake janta zuwa d’akin nasu tare dayin wurgi da ita a k’asa, wardrobe ya bud’e tare da ciro wani powdered substance fari k’ulle cikin leather. Tana gani jikinta yabata abin zubda cikin ne kuka ta soma papawa. “Ya haka sekace kinga mala’ikan mutuwa?” Kai kawai take kad’awa tana baya-baya. “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri.” Hannunta ya cafko “kinga karma kibani wahala ki bud’e bakinki kisha wannan dakanki if not zan d’ura miki na k’arfi da yaji.” “Ya Farouq I beg you dan girman Allah.” Ledar ya bud’e “ungo gashi” sam tak’i karba. Kad’an daga cikin maganin yasa a hannunsa tare da maquro fuskarta “bud’e bakin bud’e nace!” gamme bakin nata tayi se buginsa take a k’irji haka seda ta zubar da maganin hannunsa dana ledar duka a k’asa dan shuresan data tayi. “Ke?! Bakida hankali ne? Maganin kika zubar?” Wani wawan mari ya kai mata “tunda kince bara abi hanya me sauk’i ba by the time na miki fyad’e anan shegen cikin naki ze zube.” Bugata yayi da jikin bango yasoma sunsunar wuyanta yana bin jikinta da filthy harshensa k’afanta ta saita takai masa bugi a daidai manly place nasa fiye da na jiya. “Arrgghhh!!” Ya sakar da wani irin wahalallen k’ara tare da durk’ushewa da gudu ta bi ta gefensa mayafinta daya riqo tasa hanu ta fisge da sauri tasa gudu se k’olla mata kira yake amman sam tak’i juyawa a gurguje tafito daga d’akin ta inda taga staircase tabi wajen. Har a yanzu hannunsa na a rik’e a wajen nasa jikin bango yake dafawa har yafito daga d’akin. “Guards! Securities! restrain her!!” yayi maganar da ihu, k’ara gudun ta tayi bayan ta sauk’o last floor d’in ta dosa babban k’ofan data gani, chan tayi kicib’is dawani giant mutumi bak’i k’irin wane an pentasa, baya tayi da wuri ayayinda yake takowa gabanta. “Bawan Allah dan Alkah kayi hak’uri ka rufa min asiri kabarni in gudu dan Allah…” tana maganan tana ja da baya gum! Taji jikinta ya had’e dana mutum a hankali cike da tsoro ta juya fuskar Farouq tagani nan tashiga wani sabon b’arin. “You can never escape from me you stupid” yakaura mata mari. “Take her Joseph kaje ka k’ulla min ita da chains ka kuma rufe min bakinta.” “Ya Farouq dan Allah kay-” bata k’are maganar ba Joseph ya sab’ata a kafad’arsa achan yaje ya k’uk’k’ulleta**** ANAS 10:45AM Amal ce tsaye akansa yana zaune bisa Sallaya se kuka yake ba makawa, “Ya Anas dan Allah kukan nan ya isa bayida amfani ko bacci fa bakayi ba through out jiya da daddare nafilfili ka rigayi da garin Alkah ya waye yanzu kuma barakayi bacci ba? Please is okay in shaa Allah zamu sami Fannah kabar kukan please.” “Angel how?” Abinda bakinsa ya iya furtawa kenan, “taya zamu sameta bayan bamu ma iya reaching nata duk layin da nasan zan iya samun Farouq na kira basu shiga and I have no idea ina zan sameta bansan wani hali take ciki ba Amal.” Bayansa tahau bubbugawa “is okay Ya Anas zamu sameta in shaa Allah.” Daidai nan Ummie tashigo ma Anas da breakfast haka sam yak’i chi danko bayida appetite ko kad’an, inbega Fannah ba bai tunanin ze iya sake chin abinchi da k’ak’ani k’ak’a Ummmie tasamu yaci kad’an bayan yayi wanka suka fita police station dan fara investigating al’amarin. Daga gidansu Fannah suka fara inda akyi ma su Mami da Baba tambayoyi da dama cikin wuni d’aya Mami ta fita hayyacinta ta canza kamanni gabad’aya. Waya akasa Baba yayi wa Ya Khaleel bayan ya d’aga aka had’asa da police fitsari ne kawai beyi ba daga jin muryan police. Minti goma kacal aka basa da yazo sa gidansu Fannah if not za’a iya using rashin zuwansa against him ayi arresting nasa. 8 minutes later… Daidai nan shigowar Ya Khaleel sekace salihin asali sewani behaving innocent yakeyi tambayoyi da dama aka masa wanda duk ciki be bada amsa d’ayan daya kasance gaskia ciki ba, “ya akayi Farouq yafito daga gidan yari?” “Bansani ba wallahi ranka shi dad’e.” “When last rabuwanka dashi?” “Sati uku da suka shud’e kenan yanzu, tun daga ranan dana kai masa visit dana sake komawa washegari akace min anyi bailing nasa nata gwada layinsa bana iya samunsa, ku tayani nemo d’a na please.” “Are you sure Mr. Khaleel danko kamana k’arya zamuje mu duba record.” “Www… Wallahi Ba k’arya nake ba” ya k’are maganar yana had’a gumi. Ko da aka buk’acesa da ya kawo wayarsa aduba aga, ba fargaba ya bada saboda Farouq ya fad’a mai aduk lokacinda sukayi waya yana deleting logs nasa dan haka ba’a samu aka gano wani abu ba. “Abuu wallahi he is lying he is definately lying yasan duk wani whereabouts na Farouq b’oyewa yake munafikin Allah kawai.” “Haba Anas d’ana-” katsesa Anas yayi “shut the f*ck karka sake misantani da d’anka criminal ass kaji na rantse Ya Khaleel kome kake wallahi in na gano you also have something to do with the disappearance of my wife I won’t hesitate to kill you da hannu na zan kashe ka irresponsible father kawai.” “Nasan da ky-” be k’are maganar ba Anas ya mik’e a fusace tare da shak’uresa jikin bango “ina Farouq yakaimin Fannah?! Tell me! Ina yakaita?!” Abuu ne dasauran police d’in suka yi sauri suka k’wato Ya Khaleel kafin Anas yayi masa illa, d’an banza tuni nishinsa ya canza idanunsa suka wani fito waje dan azaba. FANNAH 1:50PM A hankali aka bud’e d’akin da aka rufeta ciki, a firgice ta maida kallonta wajen idanunta suna tsiyayar hawaye. Bak’in fuska taga d’auke da abinci da ruwa a hannayensa nan tashiga rawa daidai gabanta mutumin ya ajiye abincin tare da since mata bakinta da hannu d’aya yace “ga abincinki inji Boss kichi.” Seda ta bari yakai bakin k’ofa sannan takirasa da “bawan Allah” chak ya tsaya. “Wani abu ne?” Ya tambayeta tare da kewayo wa. “Bawan Allah muslimi ne kai?” “Eh me kika ga?” ya bata takiacaccen amsa. “Masha Allah k’arfe nawa ne dan Allah?” Bayan ya duba agogon hannunsa yace, “1:52PM” numfashi ta saki “dan Allah ka sinceni inyi Sallah banyi Sallan Azahar ba.” “Boss bece in sinche ki kiyi Sallah ba so eat insamu inbar nan.” “Be fad’a ba amman ai kai kasan haqqin Sallah dan Allah ka sincheni.” Wayarsa yaciro ya kira Ya Farouq alokacin yana a airport yana proceeding abubuwan tafiyansa Ukraine da Fannah dakuma Ya Khaleel kasancewar yasamu passport nata acikin jakarta. “Hello Boss gata nan na kawo mata abincin amman tace setayi Sallah.” “Karka damu kabarta tayi amman ka tabbata kana tsaye a kanta har tagama okay?” “Okay Boss” “Good bayan ta gama kuma ka kuma d’aureta karku bari tayi escaping.” “Angama Boss” yana gama wayar ya maidashi cikin aljuhunsa sannan ya nufo gabanta ya sinche mata chain d’in da kwad’on da aka datse. Kamar wanda k’wai ya fashe ma aciki ta shiga bayi tayi alwala sannan tayi Sallah duk mutumin na kallonta, jira yake taci abincin yayi tafiyarsa amman tak’i koda bud’ewa. “Hey Miss kiyi ki ci abincin mana banason wasan cha-chan nan ya wuceni fah.” “Kayi tafiyar ni barin chi ba.” “Suits you right” nan ya mik’e ya kamata ya k’uk’k’uleta again hawaye take sosai “bawan Allah nasan da akoi ragowar imani a tattare dakai dan Allah ka taimaka min nakoma gun mijina dan Allah nace.” “Allah sarki kyakkyawar hallita sede yadda kika gannin nan barin iya cin amanan Boss d’ina ba” yana kaiwa nan ya fice haka tata kuka gawani erin bak’in yunwan da takeji. Har Sallan Maghrib Farouq be dawo ba kamar d’azu ya tura MB daya kawo wa Fannah dinner anan ne daya sinche ta tayi alwala ta had’a La’asar da Maghrib sede yunwa takeji sosai yanzu dan dole tad’an tab’a abincin. Tana cikin chi wayar MB yasoma ruri a hanzarce ya d’aga “hello Mazzaaa yaneh?” On the otherisde aka amsa “gani nan fah ina cikin gari wallahi harka ya taso kana ina?” “Ohh boi! Ina nan bayan gari ta wajen gidan man Mobil.” Gidan man Mobil? Fannah ta nanata a ranta dad’a kasa kunnenta tayi tana sauraronsa. “Mobil wanne d’aya kenan Mazzaa?” cewar abokin nasa. “Mobil daya d’auki hanyar barin Maiduguri mana ta Yobe.” “Oh okay toh zan iso semu had’u.” “Okay toh ina jiranka” nan ya katse wayar tare da kewayo da kallonsa kan Fannah, yi tayi kamar bata masan yana kallontaba se chin abincinta take a hankali. “Hey Miss ko Mrs kike kiyi sauri kina b’ata min lokaci.” “Nagama tace dashi ba imani kaman d’azu ya sake k’uk’k’ulleta sannan yayi tafiyarsa. Tunanin ya zatayi tasamu waya tayi texting wa Anas location da take yanzu take tunda tagano location d’in, sede sam takasa batasan ina zata samu waya ba duk masu ma Farouq aiki zuciyarsu a karye suke kamar nasa. © MIEMIEBEE
 9:30PM Farouq ya dawo gida all tired and exhausted kayan jikinsa ya rage, ya ragar da singlet da shorts zalla sannan yachi abinci. “Ya MB Fannah tachi abincin kuwa?” “Eh Boss tachi dinner amman tak’i chin lunch.” “Good ashe dama nasa mata maganin zubda cikin aciki koda shike nasan yadda zanyi na zubar da cikin.” ya sakar dawata muguwar murmushi. Bayan ya gama chin abincin ya nufa d’akin dayasa aka d’auretan, zaune ya sameta tayi shiru abin tausayi. Tana ganinsa tahau b’ari k’ok’arin magana take amman kasancewar bakinta arufe ta kasa, hannu yasa ya b’antare cellotape d’in yana wani shafa kan lips nata ganin bata maqe lips natan chiki ba bata kuma hanasa yi ba yasa sa shiga duhu. Meke faruwa? “Ya Farouq please ka kunche min hannu nagaji dan Allah” tayi maganan cikin wani erin salo da siririyar muryarta me dad’in gaske. Ba musu bale gardama ya bud’e padlock d’in ya since ta. “Ina kashiga yau Ya Farouq?” tayi maganar ba yabo ba fallasa. “Naje processing mana abin international passport d’innan ne did you missed me?” Kai ta gyad’a, dad’i sosai sokon ya jiyo. “Well am here.” “Ya Farouq akwai wata maganar da nakeson muyi dakai dama.” Ta k’are maganar da ‘yar murmushi kwance kan fuskarta. “Mene ne wifey tell me.” “A farko inason baka hak’ui game da abinda na maka d’azu kayi hak’uri bayan nan sekuma batun barin Nigeria dakace zamuyi na zauna nayi tunani tun ba yau ba nakeson zuwa k’asar nan Ukraine nayi nayi da Anas yakaini amman yak’i bature yace oppurtunity comes to life at once so banason missing wannan oppurtunity na yarda zan bika.” Kamar amafarki yake jin zancen. Idanunsa a waje yayi maganar “Fannah? Anya kece kuwa?” “Sosai nice Ya Farouq zan bika Ukraine.” “Why the sudden change?” “Kamar yadda na fad’a maka na zauna ne nayi tunani.” “Oh sweet wifey” ya shafa fuskarta na d’an lokaci ganin bata hanasa ba yasake jin dad’i shi da kansa ya zaro hannun nasa daga baya. “Wifey ina ba wasa kikeson min da hankali ba koh? Dan wallahi nagano tricking d’ina kike me hanani illata ki se Allah.” Zuciyarta taji ya mugun bugawa ji tayi she can’t proceed with the plans sosai tasan halin Farouq har kasheta ze iya in yagano tricking nasa take, nan tabar maganan zucin. “Ya Farouq na tab’a maka wasa ko k’arya ne? I mean what I said just now.” “Toh Anas fa ya kikeson muyi dashi?” “Ya Farouq muddin baraka rabani da abinda ke cikina ba zan iya sadaukar da son danake wa Anas maka.” Baki ya wage wangalau cike da mamaki. “Fannah kinsan me kike fad’u kuwa? Anas fah? Mr. Fauzi!” “Tabbas nikuwa nasani, Ya Farouq a iya ganinka da banyi ba yau na d’an wani lokaci sena jini incomplete na rasa dalili, dana zauna nayi nazari sena gama soyayya ce Ya Farouq kamar yadda kake sona nima haka nake sonka kawai I failed to notice it ne a da se a yanzu ina fatan am not late zaka karb’i soyayya na.” “Kina sona Fannah? Baki tsaneni ba again?” “Ban tsaneka ba Ya Farouq abu d’aya nakeso agareka kamin shi toh I will be all yours zanyi duk wani abinda ka buk’ace ni.” Baki na b’ari dan jin dad’i yace, “fad’i koma meh Fannah, tell me meh kikeso?” “Karka zubar min da ciki, karka rabani da Baby na kamin wannan ka gama min komai. Shiru yayi na d’an lokaci. “Fannah amman aikema kinsan d’an ba nawa bane cikin Anas ne d’an ze zame mana ciwon idanu a rayuwa.” “Ko kad’an Ya Farouq wannan shine ciki na na farko zanso ace na raine sa nakuma haifar, kaga daga nan kaima se in raini naka cikin ko ba haka ba? Ba kace zamuyi aure ba?” “Tabbas na fad’i haka sede kince baraki aureni ba kinada igiyan auren Anas akanki.” “Ada kenan Ya Farouq, ka kwantar da hankalinka a yanzu haka ban damu da igiyar auren ba ni kawai ka kaini Ukraine dreamland d’ina.” “Amgama wifey zakije Ukraine zakiyi zaman Ukraine achan kuma zakiyi rainon ‘ya‘yanmu.” “Kai amman naji dad’i Ya Farouq toh kud’i fa kanada enough? In babu kayi demanding Anas yamaka sending.” “Eh inada, ina guy daya ara min miliyan biyar d’innan? ba nace miki na miyar masa da kud’in sa ba?” Kai ta gyad’a nufin ta gane. Ya cigaba “toh ai andawo da kud’in d’azu sabida yayi tafiya seko wani sati ya dawo kngga ko kafin wani satin mun tafi Ukraine meaning barin biya sa kud’in nasa ba kenan.” “Are you sure Ya Farouq? Barezo ya kama min kaiba? Kasan banason wani abu ya tab’aminafiyarka.” “Yes wifey kinga yanzu inada miliyan 10 kenan ze ishemu settling a Ukraine.” “Sosai ze isa I really can’t wait so yaushe ne tafiyar? Amman still zanso ace miliyan shabiyar mukeda ina gudun kar goma ya kasa.” “Angama wifey zan kira Anas inche ya dad’o min miliyan biyar.” “You will need my help but.” “Ban fahimce kiba wifey” yayi maganar cikin rashin fahimta. “What I mean is that zaka d’aureni kamar yadda ka saba seka d’aukeni hoto ka masa sending nasan yadda yakesona yana gani na a k’ulle ko miliyan nawa kakeso ze baka.” “Wow wifey wallahi you are a genius!.” “Thank you nace yaushe ne tafiyar namu?” “Bare kai nan da sati ba by God’s grace.” “Okay…” Tace blankly. “So wifey yau zamu kwana tare?” “Don’t rush through Ya Farouq nafison se in munyi aure semu soma had’a kwanciya ka gane?” Kai kawai ya gyad’a “Fannah kalleni.” Idanunta ta d’ago tana kallonsa tare da murmusawa. “Wallahi karki min wasa da hankali I love you amman inhar na gano yo are pranking on me wallahi kinji na rantse ba me iya k’watanki.” “Shikenan Ya Farouq tunda baka yarda dani ba ka sake d’aureni kabani waje, dama ku maza duk haka kuke Anas yak’i kaini Ukraine yanzu kai da kace zaka kainin ma dan kaga inaso kafara corner-corner kaima ba damuwa ka d’aureni ka gudu dani Ukraine amman kasani I will never ever love you.” “Ohh wifey dan Allah karkiyi magana haka I’m sorry kawai I want to be sure ne kuma na tabbata dan Allah karkiyi fushi kinji? Yi hak’uri.” Shiru tayi bata ce komai ba. “Please mana Fannah” ya k’are maganar hannunsa kan nata cike da dabara ta janye hannunta daga nasa “naji amman please karka sake cemin haka zuciyata barata iya d’aukawa ba kasan kalan tashin hankalin dana shiga yau kuwa da bansa wannan kyakkyawar fuskar takan a idanu na ba?” “A’a” ya amsa a takaice yana kad’a kai kamar zombie. Daidai kunnensa ta matso ta rad’a masa wani abu ba tare da tabar wani sassan jikinta ya tab’a nasa ba. Tsabagen dad’in daya ji yayi excusing kansa akan bari yaje ya d’auko mata wani abu yana zuwa. Yana ficewa taja wata doguwar tsuka “Allah ya tsine min ne in fad’a soyayya da azzalimi kamar ka Ya Farouq?” Hannu ta d’aga sama “Ya Allah ka jagoranceni in samu in k’wato ‘yancina k’ark’ashin wannan mugun, Ya Allah kabani sa’an gudanar da wannan plan.” Bada dad’ewa ba yadawo dawani package a hannu “gashi its yours.” “Meshi?” Ta tambaya tana k’ok’arin bud’ewa. Wani had’ad’d’en silver bracelet ne ciki. “Uhm Ya Farouq na waye wannan kuma?” “Naki ne wifey yau nagani a store kawai naji I want you to have it.” “Oh is that so? Thank you” ta miyar ta rufe. “Bara kisa bane?” “Zansa mana, meyesa barinsa ba? Sede Ya Farouq nafison se in munyi aure tukuna in fara sa gifts naka kaji?” “But wifey meh aciki dan kinyi accepting bracelet dana baki.” “Ya Farouq trust me ai yanzun ma nayi accepting zan ajiye a wajena kawai sawane barinyi ba ka gane?” “Nagane wifey muje mu kwanta koh?” “Not yet ka manta zaka tambayai Anas kud’i.” “Ohh haka fa!” Nan ya sake d’ad’d’aureta kamar jiya yayi sending message da pictures d’in wa Anas. Hankalin Anas inyayi dubu be tashi ba ganin pictures na Flowersa d’aure again. *** “Hello Farouq dan Allah me kakeso? Me kakeso please kadena bata wahala what is you problem?” “My problem? My problem is money kabani kud’i se in sake ta takwanta.” “Jiya jiya fa na maka sending 3 mil be isaba ba?” “Be isa ba dan bance kayi signing sunan FAHNAS enterprises koh? Eh Fahnas enterprise under my name ba shine zaka tsaya kana gaya min magana? Karka turo kaga d’anyen aikin Farouq.” “Wait.. Wait zan turo nawa kakeso please let her go” “Miliyan biyar nake buk’ata.” “Miliyan biyar Farouq?” Ya zaro weak blue eyes nasa. Me ka miyar dani? ATM machine? Kanada ma hankali kuwa? Ko an gaya maka bana calculating millions da nake maka sending ne? Ina zaka kai 15million please?” “Ina ruwanka? Oversabi zaka turo kokuwa inbar matarka ta kwana haka?” “Zan turo son of a b*tch zan turo please ka saketa.” “Inga alert” ding! Ya katse wayar. Bayan minti goma alert ya shigo masa wani shu’umin murmushi ya sakar “Allah sarki d’an amanah.” Bayan ya dawo da kallonsa kan Fannah yace, “stupid d’in har ya turo.” Sosai zuciyarta ke mata k’ona jin yadda hankalin Anas nata ke a tashe “Anas Habeebi very soon in shaa Allah all this will be over more patience please.” Tayi wannan magana a zuci. “Wifey baki jini bane?” Firgit ta dawo reality. “Na’am kace?” “Nace yayi transferring kud’in we good to go now.” “Wow great!” ** “Wifey are you sure zaki iya kwana achan?” Farouq yayi maganar yana miqe kan gado ayayinda Fannah ke maqure bisa 3 seater dake d’akin ta nannad’e jikinta da bargon ruhuwan daya bata. “Yayi Ya Farouq good night.” “Sleep good” anan ya kashe wutar d’akin. 2:57AM Bayan ta tabbata Farouq yayi nisa a bacci dan uban minsharin dayake ta rafkawa ta miqe sid’ak sid’ak a hankali tho wutan d’kin a kashene amman kasancewar da akwai hasken moonlight dayashigo ta windown yabata damar ganin duk wan abinda ke cikin d’akin clearly, wajen kansa ta dosa tana taku tsili tsili. Wayarsa ta shiga nema dan texting wa Anas location d’in da take, gefensa ta duba bata ga waya ciki ba. Tunanin koya ajiye wayar k’ark’ashin pillonsa ne ya fad’o mata a rai, farcenta tasoma chi a yayinda take nazarin ya za’ayi ta d’aga pillon nasa ganin ba yadda zatayi ta zaune gefe guda tana me cigaba da tunani chan ta miqa hannunta a hankali takai k’ark’ashin pillon nasa har a yanzu baccinsa yake sha wane wanda ya bugu ko k’ara baiji, lalimar k’ark’ashin pillon tasoma amman takasa jin komai bayan ta tabbata babu achan ta nufo side drawern dake kansa dan dubawa danko jiya ciki taga ya zaro sabon waya. Koya akayi bata lura da glass cup dake gabanta ba oho? K’afanta ya bigesa k’ara ya saki akan tiles d’in adalilin haka Farouq ya miqe zaune. “Way-” be k’are maganar ba yaga Fannah tsaye ganin raba idan da take ba taimakonta zeyi ba ta durk’ushe kawai “awchh!” Tafara faking tana matse babban yatsanta “wayyo Ya Farouq k’afana” wutan d’akin ya kunna sannan ya gwada miqar da ita “a’a karka tab’ani please.” Batasan a lokacinda tayi maganar ba. “Mesa?” Ya tambayeta sounding suspicious. “Uhmm uhmmm I mean karka tab’ani k’afan na min zafi.” “Ohh sorry” a hankali ta miqe takoma kan kujerar ta zauna shima ya zauna a gefenta. “Mugani?” Ya buk’ata. “No karka damu zafin ya ragu.” “Me kika tashi yi da tsakar dare haka? Guduwa kikeson yi komeh?” “Haba Ya Farouq wani erin zance kake haka? Kamar ya guduwa inje ina? Kaima kasan _INA TARE DA KAI_ ba inda zani wutan d’akin nakeson in kunna…” Tana maganar ta neman inda switch na d’akin ke kar Farouq ya gane k’arya take thankfully taga switch d’in a saman inda side drawer’n yake. “So nake in kunna I want to use the bathroom sekuma na bige k’afa na.” “Next time ki tadani kinji?” “Toh” a hankali ta miqe tasoma k’ingishi “bari ina zuwa” bayi ta nufa tasakar dawani hamdala “Ya Allah nagode daka kub’utar dani daga sharrin Ya Farouq yau. Huh! I have to be very vigilant” bayan data fito suka koma suka kwanta har ayanzu tunanin yazata samu waya take “koda shike baringa zuwa safiya there must be a way!” Se a yau ne tasamu ta kwanta peacefully tun barinta gida. © MIEMIEBEE
TANA TARE DA NI… PAGE 85 BY MIEMIEBEE Asuban fari ta tashi tayi Sallah da nafilfilunta bata damu da tada Farouq ba danko tasan bayi zeyi ba, bayan ta kammala addu’o’inta takoma kan kujera ta zauna tata Azhkar har garin Allah ya waye. K’arfe 8:30AM ta shiga bayi tayi wanka wani highwaist skirt da karinat blue tasa sannan ta lullub’e jikinta da mayafi babba se 9:30AM Farouq ya tashi ”good morning Ya Farouq” ta gaidashi. “Morning wifey how was your night?” “Alhamdulillah I hope yours too, na had’a maka ruwan wanka kashiga kayi semu karya” ba musu ya miqe yashiga anan ta ciro masa wani sky blue jampa ta ajiye kan gadon. Wajen bayin ta nufa ta kasa kunnenta jin bulbulan ruwa ta tabbata wanka yake dan haka ta nufa wajen side drawer’n kansa, kwalin baby nokia sabi tagani har guda biyar wanda taga alamun kamar an bud’e ta k’arisa bud’ewa tacire se juya baya take gudun kar Farouq yafito. Abin takaici taga ba sim ciki ta duba sauran drawers d’inma babu. “Mschww! Ya Salam!” Cikin wardrobe nasa ta nufa tasoma neman sim card one by one take bin kayakin nasa achan counter’n k’arshe taga sim packs kusan goma hamdala ta saki daidai tasa hannu zata zari d’aya kenan Farouq ya murd’a handle na k’ofan, a gigice ta miyar da su ciki. Da towel d’aure a k’ugunsa ya doso inda take “me kikeyi wifey?” Ya tambayeta ba wasa a fuskarsa. B’arin baki ta soma ganin bata gama miyar da kayan nasa yadda ya bari ba. “Uhmm… Ermm. Ya Farouq har ka fito?” “Eh meh kikemin cikin kaya?” “Bbb.. Babu kaga kaya nake nema maka na cire wancan” tayi nuni da jampan dake kan gadon “sekuma bemin ba nafison kasa farin jampa.” “Hakane wifey?” “Eh Ya Farouq fari zefi maka kyau.” Dad’i sosai sokon yaji “toh ai ga inda nake ajiye fararen kayaki na” nan ta matsa masa ya zaro wani farin half jampa “good kayi ka shirya muje mu karya am hungry.” “Okay wifey” cikin d’an k’ank’anin lokaci ya shirya suka fice zuwa dining room achan aka had’a musu had’ad’d’en breakfast suna hira suna chi Fannah na iya k’ok’arinta dan sakewa da Farouq tanason yayi trusting nata sosai. ANAS 10:36AM Zaune yake a d’akinsa ya had’a uwa uba tagumi gabad’aya ya fita daga hayyacinsa ba aikinsa banda tunanin Fannah rabuwansa da bacci tun da Farouq ya d’auke Fannah. “Anas!” Cewar Abuu yana buga k’ofar d’akinsa. “Kafito mu karya kaji already police d’in suna jiran mu.” Shiruuu… “Anas in shigo?” Nanma shiruu dan haka ya sa kai kawai. Hannu ya dafe a kafad’ar d’ansa. “Anas take it easy wallahi da abinda kakeyi zaka kamu da ciwon zuciya zamu sameta in shaa Allah. Ba kanada bank details nasa ba? Nayi magana da bank d’in za’ayi freezing account nasa.” Cike da tashin hankali ya juyo yana girgiza wa Abuu kai. “A’a Abuu please kar muyi haka wallahi zamu sake worsening situation d’in karmuyi dan Allah banason yayi ma Fannah wani abu.” “Anas wani erin magana kake?” “Abuu please dan Allah kar ayi freezing account nasa ni nasan Farouq.” “Shikenan zan musu magana abari kamar yadda kace yanzu tashi muje mu karya semu fita.” “Abuu fitan nan baida amfani we can’t ever find her hanyan sauk’i shine mu kama Ya Khaleel. yaji an kama Babansa a hannu ze sake min Fannah.” “Anas hakan bame yuwu wa bane we don’t have any evidence da ze nuna Ya Khaleel na aiki da d’ansa.” “Akwai Baba muje mu duba record na Farouq wa yayi bailing nasa am sure Ya Khaleel ne.” “Toh naji yanzu de katashi muje mu karya” Anas ya bud’e baki zeyi magana Abuu ya dakatar dashi “a’a karka cemin bakajin yunwa tashi muje” shida kansa ya miqar da Anas suka nufa dining. ★★★★ FANNAH 1:15PM… Zaune Fannah da Farouq suke akan dining table daidai zasu fara chin lunch kenan aka k’wank’wasa k’ofa “MB get the door” cewar Farouq kamar yadda ya buk’ata haka MB yayi. “Wayene?” Farouq ya tambayui MB. Kafin MB ya amsa yaron yayi magana; “Bad boy ne ya turoni wai abasa kud’insa.” “Ba yayi tafiya?” Yayi maganar yana barin kan kujerarsa dad’i sosai Fannah taji dataga be d’aga wayar saba, yanzu zata iya texting Anas. Har ya kusan bakin k’ofar sekuma ya dawo ya d’au wayar batasan lokacinda tayi tsaki a fili ba. “Wifey lafiya?” ya tambayeta. “Uhmm lafiya, banji dad’in d’aga kan da akayi bane daidai zamu fara chin abinci.” “Karki damu I will be right back” kai kawai ta gyad’a masa ya fice ya rage daga ita se MB a d’akin, abincinta ta nutsu taci se tunanin ya za’ayi tayi texting Anas location d’inta take. Abu kamar wasa fa Farouq be dawo d’akinba. 32 minutes later… K’ofan akayi banging dalilin firgitan da Fannah tayi seda ta yasar da apple dake hannunta tare da juyowa a kid’ime Farouq tagani idanunsa suna wani juyawa kallo d’aya tayi masa tagano abige yake. MB ne ya taimaka ya k’ariso dashi kan kujera ya zaunar dashi. “Omg! Farouq meya sameka haka?” “He had too much to drink” cewar MB. “Okay excuse us zaka iya fita I will take care of him.” Ba musu MB yayi excusing nasu, anitse ta baro kujerarta ta nufa wajensa. “Ya Farouq meya faru? Me kasha haka?” “Karki damu wifey wannan shegen bad boy d’inne yakeson rusa min plans ya dawo kuma yana buqatan kud’insa”. “Toh ka basa mana.” “Wifey kikace miliyan shabiyar kikeso in na basa kud’insa goma ne ze rage.” “Semu sake tambayan Anas ai karka damu kasan me nakeso dakai? Ka huta yanzu kaji?” Kai ya gyad’a mata. Gabansa tayi clearing ta kwantar da kansa a hankali idanunsa suka soma kafewa har bacci yayi gaba dashi. Side pockets na jampan sa ta dudduba bata ga wayarsa ciki ba data leqa setagansa cikin aljihun chest na rigan tunanin ya zatayi ta ciro take seta kai hannunta se tsoro ya hanata danko tana da tabbacin baccin sa beyi nisa ba at any moment ze iya tashi yakamata red handed. Zama tayi gefensa tana tunani chan ta kira sunansa “Ya Farouq!” Shiru ba amsa “Ya Farouq” tad’an buga table d’in. “Urghmmm” yayi groaning cikin bacci. “Ya Farouq ka tashi muje d’aki ka kwanta kaji? Nan is uncomfortable.” “Bari karki damu.” “Dole in damu mana Ya Farouq d’ina na kwance a tak’ure tashi muje d’aki kaji?” A kasalance ya miqe dan yadda ya bugu ko bud’e idanunsa bai iyawa dan bata da wani hali ne kawai tasa hannu ta taresa ganin yakusa fad’i a k’asa. “Astaghfirullah” ta rigayi har seda ta jibgesa kan gadon d’akinsu. Kamar mamaci ya soma sabon bacci wajen. Bad to worse tace a ranta “yanzu ya zanyi inciro wayar yadda yayi ruf da cikin nan?” dabara ce ta fad’o mata. “Ya Farouq ka cire kayan mana zaka fi jin dad’in baccin…” Shiruuu “Kaji Ya Farouq tashi ka cire kayan se ka kwanta” da k’yar ya tashi ya cire kayan ya wurga mata hamdala ta saki. “Rataya min akan drawer” yayi maganan a bige. Yadda ya buk’aceta tayi a hankali ta juyo ta kallesa ganin idanunsa a rufe tasoma lalimo aljihun nasa dan ciro wayar har takai kai sauran cirewa kawaibFarouq ya miqe, da wuri tabar wajen ta k’ariso wajen gadon “mene ne Ya Farouq?” Bakinsa kawai ya toshe agurguje ya ruga bayi amai ya riga kwararowa hakan yabata daman ciro wayar, b’ari duk wani sassan jikinta ke har tasamu tayi texting Anas kamar haka; Anas Habeebi its me Fannah, Mobil filling station Yobe by pass come ASAP and save me please PS don’t call. Bayan tayi sending tayi deleting a take, kafin tace zata miyar da wayan Ya Farouq ya fito daga bayin idanunsa basu sauk’a ako ina ba se Fannah dake riqe da wayansa seda ya k’ariso gabanta ya tambayeta “meh kike min da waya?” Gabaki d’aya ta tsure kasa koda furta ‘A’ tayi se rawa jikinta ke. “Magana nake miki meh kikemin da waya?” “Bbb… Babbu..” Hannu yasa ya fisge wayar, call logs ya shiga ya duba sannan messages nanma bega wani abu ba sede jikinsa na basa ba lafiya ba. “Baki amsani ba nace me kikemin da waya?” “Bb… Babu Ya Farouq wayar ne ya fad’i garin rataya maka kayan naka shine na d’ago.” Tayi magana cikin murya me rawa. “K’arya kike Fannah meh kika min da waya?” “Allah babu Ya Farouq ka duba kaga.” “Fannah kinsan in na gano wasamin da hankali kike zan mugun sab’a miki.” “Ya Farouq ya kake magana haka ne? Kaima kasan wannan ba trick bane inasonka Ya Farouq.” “Barin ga ko dagaske ne kinaso na.” GPS radio yayi turning off sannan ya kira Anas*** ANAS Yana cikin motarsa acikin gari yanzu barinsa police station an yarda da yamma za’a je a duba record na Farouq. Driving yake a hankali koda yaji wayansa yayi k’aran shigowan new message a while ago be damu yaduba ba acewarsa seya isa gida ya duban. Ganin kiransa kuma ake yanzu ya d’ago wayar ya duba sabon layi yagani kafin ya nemi waje yayi parking ya d’aga wayar ya tsinke. Daidai zeyi calling back kenan yace bari ya duba saqon tukunah. K’wararo idanunsa waje yayi bayan daya karanta. “Flower! Its Flower!” Har ya danna numban ze kira sekuma yatuna tace kar ya kirata take yayi mastering numban kar incase zata kirasa. Yakai kan numban Abuu kenan yaga exact numban da Fannah ta turo masa message dashi na kira, ba tare da b’ata lokaci ba ya d’aga “hello Flower??” Wani shu’umin murmushi Farouq ya saki yana kallon Fannah “so its true you called him with my number koh?” kafin ta hankara ya shaqure mata wuya hannunsa tahau bugi “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri ka sak.” Kasa k’arisa maganan tayi dan yadda ya shaqe mata wuya. “Hello Farouq?! Me kake mata please ka saketa. Flower kina jina?” “Anas Habeebi please help me ze kasheni.” tayi maganar da k’yar. “Farouq me kake mata? Ka saketa please dan Allah don’t hurt her.” “Kasheta zanyi ni zata raina ma wayo kasani kayi ban kwana da matarka dakuma d’anka” yana kaiwa nan ya katse wayar. Koda Anas ya sake gwada kira kuwa bai shiga Abuu ya kira da sauri ya fad’a masa location da Fannah ke, shima Abuu ba tare da b’ata lokaci ba ya sanar da police koda ya cewa Anas ya jira sutafi duka a tare k’i Anas yayi he can’t wait to save his Flower. ** “Kiransa kikayi ko meh? Munafukar Allah kawai ni zaki raina ma wayo kiyi tricking d’ina? Me kika yi da wayan nache?” “Aahh..hahhh” ta soma wani erin nishi. “Yya.. Farouq dan-” sama sama nishinta ya soma ganin zata mutu masa ya saketa tari ta hau yi idanunta sun kad’a sunyi jazir suna tsiyayar hawaye. “Wait what do you mean da kikace Anas yazo ya taimakeki, texting masa location d’innan kikayi? Magana nake miki!” Nanma shiru se tari take tayi. “Kin fad’a masa location da muke koh? Hohoho! Smart girl zakiyi bayani.” Akwati ya ciro yasoma had’a musu kayakinsu har a yanxu Fannah bata yi recovering ba daga shaqentan da Farouq yayi bayan yagama had’a musu kayakin ya tattara abubuwan daze buk’ata “tashi mutafi.” “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri karka kaini wani wajen.” “Maganan banza ina ni zaki raina ma wayo? Semuga ya Anas nakin ze cetoh ki” bejira ta sake cewa wani abu b ya fisgota sannan ya soma janta se rok’onsa take amman ko a kwalan rigarsa. Daidai wajen staircase ta durk’ushe ta kankame k‘arafun “meh haka?! Ki tashi mutafi.” “Wallahi barin bika ba mugu kawai ka sakeni.” “Ina wasa dake ne?! Nace ki tashi!” sam tak’i motsawa ganin ba mahalicci se Allah ya sauk’a ya ajiye jakan nasu sannan ya sake haurowa nan suka shiga dambe sam tak’i sake k’arafun gagam ta rik’e ita barata bisa ba seda yayi dagaske sannan ya samu ya sauk’o da ita se fad’anshi take. Wani syrup ya ciro daga cikin jakar. “Ya Farouq dan Allah kayi hak’uri karka sani shan wannan abun, na tuba dan Allah kayi hak’uri…” Ko sauraranta beyi ba yaja hannunta ya danne ta a k’asa tare da had’a hannayenta biyu gu d’aya, kwalban yakai mata baki sede sam tak’i bud’ewa “ki bud’e nace!” Se hawaye take abin tausayi tana girgiza masa kai, “nace ki bud’e” goshi ya gara musu wanda sanadin haka ta bud’e bakinta tare da sakar dawani irin azabartacciyar k’ara, hakan yabasa daman sa mata kwalban a baki seda ya juye mata tas sannan Ya cire, tarawa tayi a bakin nata tak’i had’iyewa “ki had’iye nace!” ganin tak’i had’iyewan kuma tana cinye masa lokaci ya matse mata hanci tun tana iya jurewa har numfashinta ya soma yankewa idanunta sunkad’a sunyi wani irin jaa bayan riqe numfashinta data tayi daga k’arshe kawai ta had’iye ganin zata iya mutuwa ga mugun yak’i sake mata hanci kuma. Daidai nan aka hankad’o entrance door d’in da wani irin force da seda ya k’ofar ya fad’i a k’asa da hanzari Farouq da Fannah ke kwance bisa cinyansa idanunta suna wani kakkafewa ya miyar da kallonsa bakin k’ofar. Fannah kuwa da k’yar idanunta suka iya comprehending mutumin dake tsaye bakin k’ofar. “Anas! Habeebi” kad’ai bakinta ya iya furtawa. “FANNAAAHHH!!!” Ya kira sunanta cikin tattausar murya me uban sauti. Sandarewa Farouq yayi wajen yarasa taya Anas ya samu ya shigo bayan uban securities daya zuba awaje be k’arisa wannan nazari ba yaji an cukumo mai collar riga. Kafin ya hankara Anas yakai masa wani erin mumunar punch da hannunsa me zobuna uku, take hancin Farouq ya fashe ya soma zuban jini. Wani punch d’in ya sake kai masa aciki tare da miqar dashi ko ta kan Fannah beyi ba, nishi yake tamkar zaki. Dogayen k‘afafunsa ya d’aga d’aya ya tunkud’e Farouq dashi seda yayi tumbling a k’asa Anas be barsa ba ba har yanzu. Sleeves nasa ya sake rolling yabi kan Farouq tareda hayewa kansa yasoma kai masa punches tako ina afuska ko wani spot a fuskan Farouq zuban jini yake har yanzu Anas be barsa ba seda yaji muryar Fannah tana kiransa. “Anassss!!!” Da ihu, alokaci guda ya bar abinda yake tare da kewayo wa. “Anas please help me, wayyo Allah !!” ta k’are maganan hannunta dafe kan cikinta se juyi take a k’asan ga wani erin azaban da ita kad’ai tasan yadda takeji acikinta. Hawaye take me tsuma zuciya. A gurguje Anas yayi kanta tare da aza kanta kan cinyansa. Hannunsu ya had’e “shhh! Flower am here, your Habeebi is here kinji stop crying.” A kasalance ta d’ago idanunta ta azasu kan fuskarsa daba abinda ke kwance akai banda tsantsan damuwa da tashin hankali a raunane. “Habeebi I’m sorry, I‘m sorry plea-” bata k’are maganar ba ta sakar dawai irin wahalallen k’ara; “Arghhh! wayyyooo Alllahh cikina Anas help me please zan mutu wayyyooo Allah!!” ta k’are maganar hannunta dafe kan cikinta. “Flower me Farouq ya miki? Meya miki?” Yayi maganar cike da tashin hankali. Da k’yar ta iya nuna masa kwalban da yatsanta, a hanzarce ya miqa hannu ya d’aga “Nooo!! Nooo!! Nooo!! please” abinda yake ta furtawa kenan bayan ya karance jikin kwalban, wani irin k’ara Fannah ta sake sakarwa tuni ya jefar da kwalban tare da d’aga skirt nata jini yaga yana bin k’afafunta unstoppingly. “Noo!! please NOOO! Fannah please noo Flower.” “Anas I’m sorry ple-” bata samu daman k’arisa maganan ba idanunta suka ruhu ta bar motsi kwata kwata. “Flower I can’t lose you please wake up dan Allah kitashi please Flower I can’t leave without you, don’t leave me please” jinin dake bin k’afafunta se dad’a yawa yake. Rungumota yayi a jikinsa gagam tare da had’a musu goshi se kuka yake yana sunbatu. Daga bisani ya mik’e a fusace ya nufi kan Farouq da har ayanzu ya kasa koda motsa k‘afa dan yadda ya bugu kansa Anas ya haye tare da shaqure masa wuya da k’arfin da Allah ya basa, zuciyansa se tafasa yake yana saqa masa ya kashe Farouq kar yayi sparing nasa. “You must die you filthy son of b*tch you are going straight to hell…” © MIEMIEBEE
 Take idanun d’an banza da sukaji rauni suka kad’a sukayi wani irin jaaa, hannayensa biyu na akan hannun Mr. Fauzi dake wuyansa yanata k’ok’arin cire hannayen amman ko kad’an yakasa dan bayida k’arfi ko kad’an Anas ya riga ya masa liqis. “An.. An… Anas ple…” Tari yafi k’arfinsa har anan Anas yak’i sakesa as ya d’au alwashin seya kashesa. Wani irin nishi Farouq yasoma ja da k’arfin bala’i. “ANAASSSSS!!!!” yajiyo muryan Abuu from far. “Anas don’t kill him ka sakeshi” yayi maganar yana gudu har seda ya iso wajen, k’ok’arin jan Anas daga kan Farouq yake amman ya kasa, “Anas ka sakeshi karka kashesa” seda wasu police guda biyu suka sa hannu sannan aka samu aka d’aga Anas daga kan Farouq. “Noo kubarni in kashe bastard d’innan, he dsereves nothing than to die. Let me go! Ku sakeni!” turesu gabad’aya yayi harda Abuu sannan ya sake komawa kan Farouq yakuma shaqure masa wuyan again, tsantsan azaba k’afafun Farouq se dancing suke, sake binsa su Abuu sukayi sunata k’ok’arin d’ago Anas har a yanzu Abuu bega Fannah ba se da ya juya kansa yaganta kwance so lifeless a k’asa gakuma jinin dake ta fitowa daga jikinta har yanzu. “Fannah!!” Ya kira sunanta da k’arfi hakan yasa Anas dawo da kallonsa wajen shima. “Anas ka sake Farouq its Fannah you need to focus on Anas matarka!” Da k’yar suka d’aga shi, da gudu yayi kan Fannah ya tattara ta a hannunsa se cikin motarsa a yayinda Abuu ya tsaya da police d’in ana carrying investigations, jakan kud’i da komai da komai duk aka sa cikin motar police daga k’arshe Farouq aka d’aga shima aka kaisa asibiti dan ko bara a iya hukuntasa a haka ba dole se ya samu sauk’i. An hour later… Baba, Mami, Afrah, Aiman, Abuu, Anas, Ummie, Shettima dakuma Amal duk zaune suke a harabar d’akin Fannah dukkaninsu fuskokinsu cike da damuwa, daga masu kuka se wanda suka had’a tagumi babu kaman Anas da ya kasa zama gu d’aya se pacing yake. Abuu ne ya miqe ya nufa inda Anas keta jeka ka kadawo tare da dafe kafad’ansa. “Anas you need to calm down in shaa Allah Fannah zata samu sauk’i muna nan muna mata addu’a taho muje ka zauna.” “Abuu I can’t wallahi in wani abu ya sami Fannah ko abinda ke cikinta I must kill Farouq with my own hands.” “Kabar magana haka in shaa Allah ma ba abinda ze samu Fannah” ya kwanto da Anas jikinsa yana bubbuga bayansa a sannu sannu yaja Anas suka koma suka zauna. Hannu yasa ya share hawayensa “Abuu mesa za’a kawo wancan son of a b*tch d’in nan asibitin? Mesa basu kaisa wani asibitin ba? Abuu why? Infact bekamata ma akawosa asibiti ba compared to abinda yama Fannah.” “Anas muyi focussing akan Fannah yanzu Farouq will follow afterwards.” 5 minutes later… Red globe dake a saman k’ofan d’akin da Fannah ke ciki ne ya d’auke in some seconds k’ofan ya bud’u atare duka families d’in sukayi wajen Anas ne a gaba. Cike da tashin hankali yake maganar “D… Dr… Dr how is she? How is my wife?” Ganin yadda Anas ke cikin tashin hankali Dr’n ya dafesa a kafad’a “Mr. Fauzi calm down karka damu your wife’s condition is stable zaka iya shiga ganinta bayan nan duka family zasu iya shiga ganinta also.” “Alhamdulillah! Dr. What of the baby? Shima ya rayu? Were you able to save my baby?” Kai kawai ya iya ya girgiza masa. “No Dr dan Allah karkace kun kasa saving babyna please…” ya k’are maganar cikin sautin kuka. “I’m so sorry Mr. Fauzi there is nothing we could do saboda anriga anyi terminating cikin ba yadda za’a iya saving baby’n it was destroyed already tun kafin kuzo nan, maganin Misoprostol da aka bata yagama aiki, maganin nada k’arfi sosai and yana leading to hard and painfull miscarriage we should be thankful ma maganin be b’ata mata hanji ba saboda overdose da aka bata.” “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” kad’ai ke tashi awajen se kuma sautin kukan da yabiyo baya Mami nayi Baba bata hak’uri haka Ummie da Amal ma, Afrah kuwa Shettima ne ke condoling nata. “I’m sorry excuse me please” yana kaiwa nan ya fice. Anas kuwa kasa riqesa k’afafun sa sukayi suuul ya sulale k’asa da wuri Abuu ya sake Ummie ya tarosa. “Ya kashe min baby Abuu he murdered my child.” “Shhh! Anas kayi hak’uri” A fusace ya miqe Abuu da Shettima suka soma kiran sunansa suna binsa, gudu yasa be tsaya ko ina ba se a d’akin Farouq. Banging k’ofar yayi take Ya Khaleel dake zaune gefen Farouq da kayinsa duk bandage hannunsa kuwa handcuff ne had’e da gadon dayake kwance akai. Kamar a kyaftawan ido Anas ya had’e Ya Khaleel da jikin bango tare da shaqure masa wuya Abuu da Shettima ne suka shigo da wuri suna k’ok’arin karb’e Ya Khaleel amman sun kasa dan yadda Anas ya rik’esa. “Ina kaga abinda shegen d’anka yayi wa Fannah? Kagani koh? And you are the one responsible irresponsible father kawai, wallahi both of you must pay.” da k’yar Ya Khaleel ke maganan “Anas dan Allah ka sakemin wuya dan-” tari ne yafi k’arfinsa da k’yar da taimakon wasu doctors biyu aka k’wata Ya Khaleel se shafa wuyansa daidai inda Anas ya kama yake idanunsa sunyi wuru-wuru. Kamar me aljanu Anas yayi kan Farouq da rai ke a hanun Allah ya shaqe masa wuya shima da wuri aka k’wato sa. “Anas get your senses kowa yasan abinda suka maka da zafi amman in ka kashe Farouq yanzu babban matsala ne a garemu, kotu ne zasu hukunta Farouq bamu ba.” “Nasani sede kafin nan inason inbawa d’an banza kashi” nan yasake yin kan Farouq sede kafin yamasa wani abun aka taresa. Cikin wani irin sauti Farouq ya soma magana “duk kaine Baba wallahi duk kaine barin bari akaini prison ni kad’ai ba.” “Meh kake cewa haka Farouq?” Cewar Ya Khaleel cikin rud’ani yana matsowa kusa da Farouq gudun kar ya tona masa asiri. “Aikasan me nake nufi, da tun farko baka fiddoni daga prison d’inba daduk haka be faru ba.” “So its true!” Cewar Anas “I knew it dama ai na fad’a maka Abuu wannan” ya nuna Ya Khaleel da yatsa “munafiki ne, zakusan no one messes with Mr. Fauzi or his property, musamman kai Farouq” yanuna sa da yatsa “Shariah Court zankai ka su yanke maka hukuncin kisan kai kamar yadda kayi murdering min baby kaikuma uban banza sena tabbata an yanke maka shekaru da dama a gidan yari anan ne zan iya samun peace of mind.” Wani wawan dariya Farouq ya b’arke da, “ko a babu nasan na rabaka da source of happiness naka.” Daidai Anas zeyi kansa dan kai masa punch su Abuu suka riqesa “lets go Anas mu fita kaje ka duba Fannah kabar nan” da k’yar aka samu aka fiddo shi daga d’akin. ** A hankali ya bud’e k’ofan d’akin da Fannah ke ciki. Kwance yaganta bisa gado abin tausayi, besan a lokacinda idanunsa suka cike da hawaye ba if only ze iya amsan rashin lafiyan da yayi, ina ma ace ze iya karb’an duk wani pain da takeji right now da yayi. Kujera ya matso dashi kusa da gadon nata tare da zama. Ko hannunta yakasa riqewa dan tausayi, hawaye yake sosai a hankali ya d’aga hannunta ya had’a da nasa tare da pecking hannun. Da alama bacci take dan kuwa bata bud’e ido ba har a yanzu. D’ayan hannunsa yakai kanta yana shafa uban gashin dake kwancd akan goshinta, ya d’au tsawan minti uku yana ahaka sannan a hankali Fannah tasoma bud’e idanunta har ta bud’esu duka. “Habeebi” tace cikin dashasshiyar muryarta duk yadda yayi dan stopping hawayen nasa ya kasa kai ya miqa yayi pecking nata a goshi. “Flower welcome back” yayi maganar yana mata murmushi itama murmushin ta miyar masa a wahalance. Data gwada zama kuwa sam takasa dan zafin da takeji daga k’asan mararta, wani irin wahalallen k’ara ta saki da sauri ya sake kwantar da ita. “Not yet Flower don’t move kinji? am here sweetheart” ya sake pecking nata a goshi. “Habeebi mesa kake kuka?” Tayi maganar idanunta na cikowa. “Babu, am just happy you are back baki tafi kin barni ba, Flower I love you so very much” ya matse hannunta cikin nasa. “I love you so much more Habeebi barin tab’a barinka in shaa Allah.” “I know Flower nasan baraki barni ba I was just scared.” Yasa hannu ya share mata hawayenta “karkiyi kuka kinji? Its bad for your condition.” Kai ta gyad’a mai, “Habeebi what of our baby? Yana nan?” Ta tab’a kan cikin nata tana shafawa a hankali. Shiruu Anas yayi danko besan ta ina ze fara mata bayani ba. “Habeebi mesa kayi shiru? please tell me baby na nanan kokuwa ya tafi?” Nanma shiru kuka ta soma sosai “Habeebi kafad’amin please, tell me my baby is still with me, tell me burin Ya Farouq na rabani da baby na be cika ba please Habeebi.” “Shhhh!” Ya aza yatsansa kan lips nata “bar kuka kinji?” Ya share mata hawaye. “Habeebi please tell me” seda yayi kissing forehead nata sannan yace, “Flower ki kwantar da hankalinki kinji? I’m so sorry nayi delaying time, da a lokacin da kika turo min da saqon nazo dana hana aukuwan wannan abu, am sorry please.” Maganansa ya tabbatar mata ta rasa babynta. “Habeebi so the baby is gone?” Ta tambayesa. “Ka fad’a min please.” Cikin wani erin salo ya gyad’a mata kai “baby ya tafi ya barmu Flower, we’ve lost our baby all because of me, I’m sorry.” “Habeebi ba laifinka bane laifi na ne, da ban had’iye maganin ba da babynmu be tafi ya barmu ba, ni na kashe babynmu da kaina…” ta rushe da kuka. “Shhh!” yasa hannu yana share mata hawaye “don’t ever talk like that Flower ba laifinki bane, mugodewa Allah you are back, mugodewa Allah Farouq be samu ya kaiki wani wajenba in shaa Allah, Allah ze kawo mana wani baby kinji? Kibar kuka and I promise you Farouq will come nowhere near you again ko fuskarki bare sake kalla ba.” Kai ta gyad’a masa cikin kuka yana share mata hawaye seda ya tabbata tayi shiru ya kirawo su Abuu da su Baba duk suka shigo suka gaishe da Fannah. ★★★★ Tun daga nan aka soma jinyan Fannah, sosai take samun kulawa gun Maminta, Ummie ma kusan a asibitin take yini se dare take tafiya haka Anas ma kullum yana gefen Fannarsa yana bata iya kulawan daze iya, office gabad’aya yabar zuwa yabar Kacallah in charge. Kamar yadda yayi promising kuwa seda ya cika, Shariah court yakai Farouq inda achan aka yanke masa hukuncin rataya na kisan kai dayayi, kafin nan Abuu yace inhar Farouq ze bawa Anas hak’uri yanemi gafararsa za’a janye zancen amman ina Farouq taurin kai wane tsohon k’adangare yace ya gommaci ya mutu daya bawa Anas hak’uri haka a idan mutane aka mai rataya ya wuce lahira. Ya Khaleel kuwa 10 years imprisonment aka basa na bada goyin bayan kisan kai da yayi, daga nan aka rufe chapter’n Farouq da Ya Khaleel. (NOTE: ga masu fad’in kar a hukunta Farouq kusani hukunci ne me tsauri wato kisan kai ya dace dashi saboda yayi aborting baby wanda yake daidai da committing murder, inkuma har wai ba kashesa akayi ba aka yanka masa wasu shekaru a gidan yari toh definately wata rana ze fito kuma ze cigaba da hunting Fannah) *** 1:05PM A yau aka sallami Fannah daga asibiti sosai Dr yabasu shawarwari ciki harda hutun ‘yan watanni da Fannah ke nema kafin ta sake d’aukan wani cikin. Bayan isowansu gida Fannah taga security men as in k’warraru designed security men guda biyar bakin k’ofar. “Habeebi wannan mutane fah?” “Your security men Flower in shaa Allah from now no harm will come to you.” “Habeebi ai dama enemy d’in d’aya ne Farouq kuma he is gone yanzu ba me sake tak’ura mana.” “Even still Flower I want to keep you safe, ban tunanin zan iya yafe wa kaina in wani abu ya sake samunki, you are a like Flower da ba’ason abinda ze tab’a sa” murmushi ta saki masa, bayan yashigo yayi parking motar sannan ya ciro luggages natan yayi ciki dasu, da kansa ya cirota daga motar yakaita har d’akinsu. “Thank you Habeebi.” “Always Flower” yayi maganar yana ciro mata towel nata daga wardrobe “gashi kiyi wanka semuci abinci I cooked your favorite.” “Favorite wanne kenan? louisiana?” “Yes sweetheart kishiga kiyi wanka ko in miki?” Towel d’in ta fisga daga riqonsa “haka kawai seka haumin wanka?” “Barin iya bane?” “Eh” ta fad’a tare da murgud’a mai baki. Gabanta yasha tare da d’agata sama chak! be direta ko inaba se cikin jacuzzi sannan yasoma raba ta da kayan jikinta. “A’a Habeebi wallahi zaka iya kayi hak’uri kabari please.” “LOL shegen kunyan kinnan bansan ranan barinsa ba, ina jiranki” nan ya manna mata peck a kumatu sannan ya fice. Cikin kwanciyan hankali ta samu tayi wankanta ta fito zaune ta tarar da Anas gefensa wani baggi T shirt ne baby pink in color da hoton birds da flowers akai. “Come here” ya buk’ace ta, ba gardama taje ta zauna gefensa, akan cinyansa ya azata sannan yaciro lotion nata ya soma shafa mata sam bata hanasa ba bayan da yagama takallesa cike da so da k’auna tana murmushi sannan tace, “thank you Habeebi.” “Its my job Flower in tayaki sa kayan?” “A’a karka damu” a hankali tasa kayan daya cire mata wanda tsayin yamata daidai tsakiyar cinya. “Toh Habeebi ba leggings da zan sa taciki?” “Babu I missed your sexy legs so yau inason inta kallonsu.” “LOL” ta murmusa “baraka kasheni da kayan dariya ba Habeebi toh muje muci abincin” tayi maganan tana bin jikinta da turare bayan tagama ya rik’o hannunta suka fice daidai gaban d’akin babynsu ta tsaya hakan yasa Anas tambayarta ko lafiya. “Flower wani abu ne?” “Habeebi kawai na tuna da babynmu ne, I miss him/her” ta k’are maganar tare da aza hannunta kan cikin nata. Ganin zata fara masa kuka yayi sauri yayi hugging nata yana bubbuga bayanta. “Is okay Flower Allah ze kawo mana wasu in shaa Allah bar kuka kinji?” Hannayenta ta zagaye a bayansa a hankali tana gyad’a kai “I pray so Habeebi.” Sun d’au minti biyu suna manne da juna sannan Anas ya raba jikinsa da nata “muje muci abincin ko? Se kisha meds naki” “Yes amman inason inshiga d’akin first.” “A’a Flower banason kiyi kuka kuma nasan definately kika shiga zakiyi.” “Please Habeebi” badan yanaso ba yabud’e masu k’ofan suka shiga. Daidai gaban babban gadon ta tsaya tare da sunkuyawa ta ciro d’aya daga cikin cute pink teddy bears d’in tana murmusawa, hawaye kawai tasoma zubarwa, kafin tasa hannu ta share Anas ya riga ya ganta. “Flower kinga shiyasa nace banason kishigo.” “Habeebi ka tuna lokacin da nace mu sayi blue ones kace a’a pink kafiso saboda jikinka na baka mace zamu haifa? Kasan wani name ya fad’o min alokacin?” “No Flower tell me” ya juyo da ita gabansa tare da kwantar da kanta a chest nasa yana shafa bayanta. Kanta ta d’ago tana kallonsa “HANAN Habeebi. Kasancewar kanason baby girl nima na soma ji ajikina mace zan haifa and HANAN zanso muna kiranta dashi amman not anymore Habeebi…” sekuma ta rushe da kuka. Face nata yayi cupping yana share mata hawayen “kibar kuka kinji sweetheart? We will have another baby and many more kuma aduk lokacinda muka samu baby girl I promise you ke da kanki zakiyi naming nata HANAN kinji? Bar kuka.” Kai ta gyad’a a hankali tare da hugging nasa gagam a jikinta. “I love you Habeebi, I love you so much.” “I love you too Flower muje muci abinci.” Teddyn ya amsa ya ajiye sannan ya jata har a yanzu bata bar kukan ba, shida kansa yake bata abincin har ta k’oshi sannan ya b’allo mata meds nata ya bata bayan sun idar da Sallah suka fita waje garden dan shaqatawa kan wani dogon kujera suka zauna ya kwantar da ita ajikinsa me bala’in sata mance da dukkannin damuwanta. Hannu yasa cikin ¾ wandonsa yaciro wani heart-shaped pack tare da miqa mata. “Habeebi meh wannan?” “Its yours bud’e kiga.” Excitedly ta amsa ta bud’e had’ad’d’en silver bracelet taga aciki meh chain d’an dogo seda toliyar heart a k’arshen wanda yake nan d’an babba. “Wowww its a beauty!” tayi exclaiming. “Do you like it?” “I love it Habeebi.” Hannu yasa ya ciro daga pack d’in tare da d’ago siririn hannunta ya sa mata chas ya zauna. “Just as I imagined it” ya fad’a tare da kissing hannun nata. “Tsaya kiga wani abu.” Toliyan heart d’in ya bud’e mata “FAHNAS” taga rubuce ciki in italics. “Habeebi this is way beautiful” fuskarsa ta riqo tayi pressing masa appreciating kiss daya kashe masa jiki lokaci guda, koda ta gwada sakesa kuwa holding lips natan yayi ya cigaba da kissing nata seda suka ji kansu problem free sannan ya saketa, murmushi ta sakar masa “I love you my sugar lips.” Murmushin shima ya miyar mata “sugar lips?” Yayi maganar da gira d’aya a d’age “ofcourse Habeebi I missed your lips and your body” kafin ya hankara ta sake pressing masa another hot kiss, se kissing juna suke passionately and hungrily tamkar yau suka fara tasting juna**** some minutes afterwards… “I love you Flower.” yace da ita yana shafa dogon sumarta. Sake shigewa jikinsa tayi; “And I love you too Habeebi like bohot bohot!” ta sakar masa da best smile nata me mugun amsar ta dakuma birkita wa Anas lisafi. © MIEMIEBEE
 “Yauwa Habeebi nace ya labarin Moosa ne? Har yanzu shiru ba’a samesa ba?” yatsunsu yayi interwining; “D’azu munyi magana da police sunce suna kan investigating har yanzu, kinsan Farouq shege ne Allah kad’ai yasan inda yakaisa.” “Allah sa a samesa a raye Habeebi nasan danni Ya Farouq ya masa duka haka saboda yak’i shigo dashi ciki.” “You are right Flower in shaa Allah zamu sam-” besamu daman k’arisa maganan ba sakamakon ringing da wayar sa yasoma ganin number’n Inspector General yayi saurin d’agawa. “Hello Inspector.” “Yes Mr. Fauzi I will like to congratulate you.” “Yes… About what Sir?” Yayi maganar cike da neman k’arin bayani. “Mun samu Moosa your driver achan Mongunu wai gidan Bad Boy achan Farouq ya kaisa ya b’oyesa.” “Alhamdulillah, Alhamdulillah this is indeed a great news.” “It is kuma shima Bad Boy d’in yana a hannu yanzu according to record babban drug dealer ne partner in crime na Farouq kuma dan da miliyan biyar nasa akayi bailing Farouq a prison 2 weeks ago.” “Okay… Thank you Sir ina Moosan yake yanzu?” “An kaishi asibiti dan duba lafiyarsa I guarantee you ba abinda suka masa.” “Ina godia Sir zamuyi magana anjima.” Nan ya katse wayar tare da juyo da kallonsa kan Fannah dake kallonsa fuskarta d’auke da tambaya. Kafin tayi magana ya aza yatsansa kan lips nata “nasan me kikeson tambaya, an samu Moosa? Ko ba haka ba?” “LOL eh haka please an samesa?” “Yes sweetheart an sami Moosa yana asibiti yanzu as we speak yakamata inje in duba sa, I will be right back.” peck ya manna mata a goshi kafin ya miqe ta riqo shirt nasa. “Habeebi nima zanje.” “Zakije ina?” ya tambayeta disbelievingly. “Asibitin mana nima in duba sa kasan fa nice sila.” Kai ya kad’a mata “inaaa! you are going nowhere ko kin manta kema yau aka sallamoki? Bafa kida lafiya ki zauna ki huta barin d’au lokaci ba zan dawo kinji Flower?” “O’o” ta shakwab’e fuska. “Flower please kiyi hak’uri ki zauna zan isar masa da saqon gaisuwanki bareyi ki bini ba.” Badan tana so ba ta gyad’a kai wearing a sad face. “Flower ba goodluck kiss?” “Eh babu” ta fad’a ba tare da ta kallesa ba. “Oh common! Flower.” Alokaci d’aya ta d’ago fuskarta tana mai murmushi “Habeebi na gabad’aya ze fita barin basa goodluck kiss ba? Impossible!” a hankali ta had’a musu lips tare da kissing nasa a passionately. “Off you go take care okay?” “I will and you too Flower, in shiga dake ciki ko zaki iya?” “Don’t bother zan iya I love you” “I love you too Flower.” har ya soma tafiya ta tsayar dashi “wait wait tsaya in d’aukemu selfie so I can be starring at my husband’s handsome face kafin ka dawo.” Murmushin jin dad’i ya saki tare da dawowa baya ta d’aukesu sannan ya fice, anan yashiga ya fito da key’nsa ya fice itama bada jimawa ba tashiga ciki. ***_3:10PM_ Daidai nan Anas ya dawo gida rashin ganinta a parlour ya tabbatar masa a d’aki take aiko yana shiga d’akinsu ya sameta zaune kan dressing mirror se sosa cikin gashinta take da comb tsantsan k’aik’ayi. “Flower” ya kira sunanta anan ne tasan da shigowarsa ta juyo tana kallonsa cike da so da k’auna “sannu dazuwa Habeebi.” “Thank you, me kikeyi haka?” “Wallahi kaina k’aik’ayi na kwana biyu ban wanke ba, ya jikin Moosa’n?” “He is okay alhamdulillah.” Yayi maganan yana dosowa gabanta. “Toh masha Allah, aha! Mami ma ta kira tana gaisheka” tacigaba da sosa cikin gashintan. “Ina amsawa” yace tare da karb’e comb d’in daga hannunta. “Habeebi bani please k’aik’ayi” ajiyewa yayi kan mirron tare da rik’o hannunta “muje in wanke miki kan Flower.” Dariya sosai ta tsaya yi wanda sakamakon haka Anas ya tsaya kallonta yana admiring nata, dariyan sa na mugun kashesa. “Habeebi baraka isheni da kayan dariya ba, yaushe kazamo hair dresser da zaka wanke min kai?” “Aww bakisani ba Flower? I can be anything fo you, Dr, hair dresser, cooku, servant komi da komi ma, muje.” “A’a please kabari.” “Flower banason dogon surutu” hannunta ya sake ya shiga cikin wardrobe ya ciro mata vest tare da miqa mata “sa muje in wanke miki” anan shima ya rage kayan jikinsa ya ragar da singlet se wando zallah. Ba musu ta cire T- shirt d’in tasa vest daya kawo mata acikin jacuzzi ta zauna ya karkato da kanta direction guda. “Welcome to FAHNAS beauty salon how can I help you Mrs. Fauzi?” Dariya sosai take “thank you, wash and set nakeso.” “You are at our service.” Daga farko seda yayi combing dogon sumanta sannan ya wanke thoroughly da ruwa sekuma da shampoo, a hankali yake mata massaging kan wanda ke mata dad’i sosai cikin d’ank’ank’anin lokaci ta nemi k’aik’ayin ta rasa. Bayan daya gama wanke mata ya d’aure mata kan da towel sannan ya miqa mata babban towel ta nannad’e jikinta dashi. Gaban dressing mirror ya ajiyeta ya ciro hand drier ya kunna sannan yasoma drying mata gashin bayan ya gama ya mata oiling sannan yayi mata packing gu d’aya harda style na donurt. “Wow! Habeebi you are amazing!” tayi maganan tana duban kanta cikin mirron. “Wai nikam ya akayi ka iya komai neh?” “LOL!” yasoma feeling. “Kin manta inada sister ne?” “Thank you so much for making my hair.” “Always Flower.” Yayi maganar yana mata murmushi miqewa tayi tare da pecking nasa a both kunatunsa, sekuma tip na hancinsa kafin ta kai kan lips nasa ya dakatar da ita. “Uhn-uhn Flower I know where this is going.” Murmushi cike da kunya ta saki “then let it happen.” “A’a Flower kin tuna meh Dr. Yace? Cemana yayi kina buk’atan atleast 3 months na hutu before you can get pregnant again.” “Toh ai hutun d’aukan ciki yake nufi bawai totally mubar yin…” Sekuma tayi shiru “ai ka gane me nake nufi.” light red lips nasa yayi pouting “ban gane ba” yayi maganar da gira d’aya a d’age. Bugi cike da shakwab’a takai masa a hannu “wallahi qarya kake ka gane.” Dariya yake sosai “toh naji na gane but even still Flower muyi hak’uri.” “Toh baby ba semuyi using protection ba.” Kai ya girgiza mata “I don’t trust in that, saboda sometimes suna bursting kuma kinga zaki iya samun ciki if that happens which is very harmful to your condition” ya tab’a tip na hancinta. Baki ta murgud’a masa “ina ni kayi rejecting yau Mr. Fauzi nima sena rama.” Hannayenta ya gwada rik’ewa da wuri ta fisge ita a dole tayi zuciya. Daidai zata juya masa baya kenan ya zagaye hannayensa a waist na tare da pulling nata closer to him. “Haba Mrs. Fauzi matar Anas, the mother to my awesome kids in shaa Allah. Taya zanyi rejecting the perfect woman I’m lucky to call my wife? Kema kinsan hakan k’arya ne, Flower ni kaina ina missing naki like hell I miss us on bed amman kinga lafiyarki ya fiye min komai, koda na shekara da shekaru akace inyi avoiding naki zanyi inhar hakan ne ze sama miki lafiya balle ma na d’an months, bawai nayi rejecting naki bane understand kinji? I’m sorry my sugar lips” Kafad’a ta buga uwar zuciyar har yanzu bata sauk’o ba. “Flower meh kikeso in miki ki hak’ura?” “Muje mu kwanta.” “Zamu kwanta amman ba abinda ze shiga tsakaninmu its a deal.” “O’o toh na fasa hak’uran.” “Sena sauk’a akan knees d’ina zakiyi?” Ganin yasoma sauk’a tayi sauri ta hanasa. “A’a please baby don’t na hak’ura but can I kiss you atleast Mr. Fauzi?” Murmushi yamata “ofcourse Mrs. Fauzi” sannan yayi owning lips nata da kansa yasoma kissing nata.*** ** Tun daga ranan rayuwan masoya biyu ya cigaba da kasancewa kamar yadda ya saba da a baya ko inche fiye dana da ma, ba fad’a kullum cikin farintawa juna rai suke, ga uban lovely suprises da Anas yake cikin bawa Flowersa a kullum. A kullum wutan soyayyan junansu dad’a ruruwa ya ke a birnin zuqatansu.
_6 months later…_ Monday, 6:20AM Tsaye Fannah ke a kitchen da shiganta kusan minti uku kenan yanzu amman takasa tsinana komi ciki dan wani irin zazzab’in da takeji wanda ya fara mata tun jiya da daddare amman sam tak’i nuna wa Anas saboda batasan sasa cikin damuwa ‘cause ta lura aduk lokacinda batada lafiya Anas yafita damuwa. Tsugune take gefen sink takasa koda miqewa, tafi minti biyar ahaka sannan da k’yar ta miqe sanadiyar amai da yazo mata, cikin sink d’in ta riga kwararo amai wane zata harar da hanjinta seda tayi emptying cikinta kap sannan ta wanko bakinta, wane k’adangare tabi jikin bango har izuwa d’akinsu. A kasalance ta miqe agefen Anas dake ta bacci hankali a kwance. “Habeebi” ta kira sunansa ko motsawa beyi ba se a karo na uku yayi groaning “uhmmm Flower.” “Habeebi ka tashi kaji? Yau Monday akwai office.” A hankali ya bud’e idanunsa kallo d’aya yama Fannah yagano batada lafiya she is looking so pale. Cike da tashin hankali ya shafa fuskarta “Flower are you okay?” Kai ta girgiza masa “Habeebi I’m sick ko breakfast na kasa had’a maka, I’m sorry.” “Subhanallah, shhhh! Haqurin me kike bani?” body tempreture’nta ya tab’a yaji ya hau sosai yayi zafi. “Omg! Flower kinji tempreture naki kuwa? Ya kikeji?” “Zazzab’i Habeebi sau biyu nake amai yau ko miyau ban iya had’iye.” “Omg! Flower mesa baki fad’amin ba?” I’m sorry kinji?” Kai kawai ta girgiza masa dan batajin ma zata iya magana. “Arghhh!” Ta saki wani irin k’ara hannunta rik’e da gefen cikinta, cike da tashin hankali yakai yana dubanta “Flower wani abu ne?” “Habeebi ciki na tanan, wayyo!” “Sannu Flower ina zuwa” bayi ya fad’a a gurguje yayi wanka sannan ya had’o mata black tea tare da b’allo mata meds. Duk’unk’une cikin bargo ya tarar da ita “Flower tashi ki zauna kisha magani kinji?” Da k’yar ya miqar da ita tare da jinginata jikin gadon, magunan ya miqa mata sam tak’i karb’a. “Flower kiyi hak’uri kisha if not baraki warke ba.” Kai ta kad’a masa nufin barata sha ba. “Why?” Ya tamabayeta. “Habeebi kasan meh?” “A’a meh?” yayi maganar ba alaman kwanciyar hankali tattare dashi. “I think I’m pregnant gani nake kamar ciki ne dani” Bright blue eyes nasa ya zaro waje “Flower you are what?!” Yayi exclaiming cike da k’in yarda dan yadda jin dad’i ya mamaye masa fuska da zuciya. “I’m pregnant again Habeebi kaga ko bareyi insha kowani irin magani ba it may harm our baby.” Tsantsan jin dad’i har a yanzu Anas yakasa believing. Besan a lokacin da ya ajiye tean a gefe ya rungumo Fannah ba. “Flower we are soon going to be Daddy and Mammy again, I love you!” Hugging nasa back tayi dukda ba dad’in jikinta takeji ba. “Yes Habeebi” breaking hug d’in yayi tare da riqe hannayenta biyu cikin nasa “Flower dagaske kike you are pregnant?! Omg! Akwai little Fauzi achan? Ko inche akwai HANAN namu a chan?” murmushi tamasa tana gyad’a kai, hot kisses yahau peppering mata a fuska yana sauqowa kan wuyanta tasa hannu da k’yar ta iya ta shuresa “Habeebi please kadaina, kabari banaso.” Cike da mamaki yake kallonta “bakiya son sugar lips naki yau?” Kai ta gyad’a tana turo baki. D’an murmushi ya saki another symptom yace a ransa “I know this attitude cikin nema dake amman your last pregnancy ai bakiya hanani kissing naki wannan kuma ko kiss d’inma bakiya so?” Nanma kai ta gyad’a. “Humm! Akwai babban aiki Flower ‘cauae I can’t stop kissing you, yanzu kisha black tea d’in seki kwanta zuwa 10 haka se muje asibiti.” Kai kawai ta gyad’a masa shida kansa yabata tean bayan data gama sha ya kwantar da ita. “Habeebi kaifa baraka je office ba?” “Mom Hanan bata da lafiya inje office inyi meh? barinje ba zan sanar da Kacallah.” Kai kawai ta gyad’a masa “thank you.” “Always Baby Machine” yayi pecking nata a kumatu. Hannu tasa ta goge “Habeebi banaso.” D’an murmushi ya saki sannan ya koma d’ayan side d’in ya kwanta tare da janyota zuwa chest nasa ahaka suka koma bacci. 10:30AM Anas ya tashi banda Fannah data kasa bacci tun d’azu se juyi take ajikinsa. Jikinta yayi zafi tamkar wuta shi kansa Anas seda ya razana. “Flower” ya kira sunanta cike da tausayi. “Na’am Habeebi” tayi maganan tana kakkarwa. Kodaya gwada d’gata daga cikinsa sake kankamesa tayi not letting go. “Flower sannu kinji? D’agani mu shiryaki muje asibiti.” “Habeebi mubari anjima ban tsammanin zan iya tashi.” “Sorry kinji? Yi hak’uri” da k’yar ya d’agata ya kaita bayi cikin 30 minutes suka shirya zuwa asibiti achan aka duba Fannah aka tabbatar wa lovely couple cikin sati uku ne d’auke da ita. Murna gun Mr and Mrs Fauzi kam baya misantuwa Anas promised to protect his child with his life wannan karan. ** Tun isowarsu gida Fannah keta tufar da miyau, ga kuma amai a asibiti ma seda tayi dawowansu ma haka, Anas is so worried ko kad’an bara’a had’a laulayin cikinta na farko da wannan ba, bata iya cikakken minti biyu a tsaye se jiri ya kwasheta. Sede bataji k’amshin turare ba in bahaka ba setayi amai na turaren wutan daya mamaye mata gida ma haushinsa takeji. Sallan Azahar ma sauran a zaune ta k’arisa, lunch da Anas yayi musu ma kad’an ta iya tachi shima ta harar. Hankalin Anas yayi matuqar tashi zaune yake akan kujera a gefenta, damuwa ne karara a fuskarsa, ayayinda take kan gado lullub’e da bargo se zufa takeyi. Hannunsa dake akan bayanta ya d’aga dan irin zafin da jikin nata yayi sannan ya share mata zufan. “Sannu Flower, you’ll be fine in shaa Allah I’m here for you.” Moderate cold water ya nemo da towel yana mammatse mata jikin ko ze d’an sauqar mata da body tempreture cikin ikon Allah kuwa zafin jikin nata ya ragu sede bada jimawa ba ya sake rising. Tausayin Fannah duk yabi ya mamaye Anas sam bayason ganinta ba lafiya haka fa suka kwana cikin wannan zazzab’i ba wanda yayi bacci cikinsu se jinyarta Anas yake gabad’aya hankalinsa yabi ya tashi wani irin pegnancy sickness ne haka? Washegari… Rashin lafiyar yau yama fi na jiya ko meh taci seta harar banda black tea tun Anas na iya jurewa har ya kasa Dr. Mansoor ya kira yazo ya sake duba Fannah har ruwa seda aka sa mata, cikin kwana biyu Fannah tazamo abinda tazama ko k’wararren motsi batta iya yi. Maminta Anas yakira ya sanar da ita halin da ake ciki aiko ba tare da b’ata lokaci ba taje tasamu Afrah dake miqe kan gado se hirarta take sha da dearheart nata. “Ke katse wayar” cewar Mami dake tsaye akan Afrah dako noticing shigowar Mami batayi ba. A firgice ta katse wayar, hannunta dafe kan k’irjinta “kai Mami dan Allah yaushe kika shigo? Kinfa bani tsoro.” “Bansani ba kinsa soyayya agaba ina zaki sani dama, mschw! Yarki ba lafiya amman ko a colar rigarki.” “Fannah?!” Tayi maganam ido a waje. “Eh mana yanzu Anas yakirani yake sanar dani. Maza maza tashi muje mu dubata wai har ruwa aka sa mata.” “Oh! Allah sarki Ya Fannah kode wani cikin ne Mami?” “Mukaje ma sani oya tashi kishirya.”**** _GWS FLOWER, MOM HANAN_ *Ina me baku hak’uri and inason ku k’ara hak’uri da irregular posting kwana biyu, somethings came up so se harkoki suka min yawa* MIEMIEBEE
TANA TARE DA NI… TANA TARE DA NI… PAGE 88 BY MIEMIEBEE Kuka ne kawai Mami batayi ba kafin securities na wajen suka barsu suka shigo har take cewa aranta barata sake zuwa gidan Fannah ba ko Villa albarka. Bayan Anas ya bud’e musu k’ofan yamusu sannu dazuwa da Mami tayi oberseving fuskarsa kuwa setaga kamar shi d’inma baida lafiya, batasan saboda yadda ya damu da rashin lafiyar Fannah neba harshima yake affecting nasa. “Anas kaima bakada lafiyan ne?” Murmushin dole ya k’irk’iro. “A’a Mami mushiga daga ciki, she is inside.” Bayansa sukabi zuwa d’akin. “Mami” cewar Fannah cikin wani erin murya. “Subhanallahi Habibti” tayi maganan tana tab’a tempreture’nta. “Sannu kinji? Sannu, Anas meke damunta haka?” Shiru yayi yana nazarin taya ze fara sanar da ita face-to-face. Ganin baida na cewa Fannah ta amsa ta “Mami munje asibiti aka tabbatarmana juna biyu ne tattare dani.” “Kai toh Alhamdulilah, Alhamdulilah Anas shine baka sanar dani jika nane yakusa ko ta kusa isowa ba?” K’eyansa yashafa cike da kunya. “Toh Habibti Allah raba lafiya, sannu kinji? Wannan daman ai is normal nan da ‘yan satuka zaki dawo kanki na da se hak’uri.” “Sannu Ya Fannah, Allah raba lafiya” cewar Afrah tana yimata wani shu’umin kallo. Kai kawai Fannah ta kad’a mata. “Kina iya cin abinci?” Kafin ta amsa Anas ya amsa “a’a Mami tun jiya ba abinda tasha banda black tea.” “Toh ya kikeso d’an naki yay k’wari in bakiya chin abinci iyyeh Fannah?! Afrah zaki koma gida yanzun nan ki taho min da gauta dakuma zogale mu had’a mata miya ta samu taci.” Anas da bashi akace zechi ba shine yakai hannu bakinsa ya rufe kan wanda zeyi amai. “Mami is it necessary? Flower zaki iya chin miyan gauta koh? Zaki iya chi?” Kai ta girgiza masa. Kan gadon yanufa ta d’ayan side d’in ya zauna “zakici louisiana ko bufalo wings?” “Habeebi black tea nakeso.” “Toh ai kinji Mami tace baby’nmu will not be healthy in bakiya chin abinci, ko in miki frying sausage?” “Ni black tea nakeso” Kallonsu kawai Mami take “kun gama?” ta tambayesu. Shiru sukayi suna kallon ta. “Nace kun gama? Afrah wuce gida ki d’ibo min gautan.” “A’a Mami please abin beyi zafi haka ba” cewar Anas yana dakatar da Afrah daga tafiyar. “Akwai ragowar glorified rice na jiya zan mata reheating tachi.” “Shi glorified rice d’in kenan? Anas kaga fa duk wannan abubuwa na shirmeh ba taimakanta zasuyi ba kabari taci tuwo d’anku yasamu lafiya maza jeki Afrah.” Anas kan yayi kuka. Nan da nan Afrah taje ta dawo, Mami tashiga had’a miya bayan ta gama ta kawo d’akin da tuwon semovita. Take warin miyan gautan ya mamaye d’akin. “Habibti tashi kichi, kinji? sannu.” Hanci Anas ya toshe dan warin da miyan ke masa he can’t believe Mami zatasa masa Flower cin wannan abu shi dayasan haka ne ze faru da be kira taba in the first place. Da kanta ta zaunar da Fannah ta soma bata, loma biyu Fannah tayi tajawo bowl tayi amai ciki hakan ba shi ya hana Mami sake d’ura mata ba. “Mami please ya isa haka nan karta sake hararwa.” cewar Anas cike da tausayin Fkowersa. “Anas kasan me nakeso dakai?” Kai ya kad’a mata hankalinsa na akan Flowersa ganin yadda batason chin abincin hankalinsa ya sake tashi. “Kaja Afrah ku fice kubani gu in bata abincin nan, nasan tsayunwanka nan ke hanata ci, in baka nan ita da kanta zata zage taci tashi kufita.” “Habeebi please karka tafi kace mata banaso” Fannah tayi maganar kamar wacce zatayi kuka. “Fannnah banason shagwab’a fa tuwon nan da kike gani shi ze baki k’arfi ba wannan ruwan da ake ta d’ura miki wanda banda kumburi ba abinda ze saki ba” tayi maganar tana bin ledan ruwan da aka sawa Fannah da kallo. “Anas jiranka fa nake.” ta miyar da kallonta a garesa. “Da k’yar ya miqe amman yakasa barin d’akin. “Mami please kibita a hankali kinga batada lafiya.” “Naji zan bita a hankali fita ina jiranka.” Badan yansaso ba yafice Afrah tabi bayansa. Haka Mami tasa Fannah agaba ta riga d’ura mata miyan gautan kamar ba gobe tun tana hararwa har tadaina yazauna acikinta. “Good anjima kad’an kuma zakici miyan zogalen shima yana da amfani sosai, sannu koh?” “Mami kasheni kikeson yine? Dan Allah ya isa ni kitafi ma.” “Ai ina nan Fannah kinga yadda kika zube kuwa? Ace mahaifiyarki na raye amman kikayi wannan rama? Wannan abu da keda Anas kuka raina shi zai taimaka miki bawani bufalo wings ne komeh abin ban ma san shiba.” ** Tun kamin Azahar Mami ta tura Afrah gida gudun kar Aiman ta dawo ba kowa gida itako se bayan La’asr Anas yayi dropping nata bayan tabawa Fannah miyan zogalen kuma alhamdulillah bata harar ba, kunne sosai tajawa Anas da yadaina biye wa Fannah yana barinta tana kwana da yunwa, sauran ragowar tuwon kuma ya tabbata yabata zuwa dare in bahaka zata dawo gobe tabata da kanta. Kafin Anas ya dawo gida Fannah tariga tayi bacci, wani sabon ruwa yasa mata kamar yadda Dr. Mansoor ya koya masa sannan ya rage kayan jikinsa ya haye gadon shima tare da aza kanta a k’irjinsa yana me shafa bayanta a hankali anan shima yasamu yayi bacci se Maghrib ya tashi yayi alwala ya tayata tayi itama sannan yajasu Sallah, jikin nata alhamdulillah tunda har tasamu tayi Sallah duka a tsaye. Tana manne a jikinsa jiki ba k’arfi tace, “Habeebi zansha black tea.” Kai ya girgiza mata “Flower kinga Mami tace kar inbarki kina shan tea zallah tace se in kinci tuwon d’azu inbarki kisha tea.” “Habeebi wallahi tuwon ba dad’i please ka had’amin tea.” “Mom Hanan I know” yayi pecking goshinta “kinason Hanan koba haka ba?” Kai ta gyad’a “good then eat well se Hanan namu tafito healthy, kinji Mom Hanan?” Shiru tayi bata ce komai. “Yawwa Mom Hanan tashi inje in d’ebo miki toh.” Koda ya kawo abincin k’inci tayi da k’yar cike da dabara yasata ta soma ci har ya gama bata bata harar ba anan ne ya had’o mata black tea ya bata. Bayan sun idda Isha yasa mata last drip nata suka kwanta. Washegari ma da zazzab’i ta tashi sede ba kaman na jiya ba nayau da d’a sauk’i, kamar yadda Mami ta buk’acesa ya mata reheating tuwon jiyan yau harda ‘yar kukanta dak’yar yasamu taci sam batason ci gashi kuwa shi kad’ai ne in taci bata hararwa bayan shi duk wani abinda takai baki seta fito dashi waje. Da rana Mami ta turo Afrah da miyan ayayo da d’anyen kub’ewa duka a had’e. Fannah kamar ta k’urma ihu shikansa Anas dayake bata amai abincin ke sasa amma haka ze dage yabata.
Mami bata fasa kawo wa Fannah miyar gargajiya ba, acikin ikon Allah Fannah ta fara samu sauk’i in two weeks time tadawo old self nata sede sometimes da take tashi da morning sickness, jiri dakuma k’warnafi bayan nan bawani ciwo again. Babynsu da suka bata ko shi suna Hanan kuwa nan cikin k’oshin lafiya. Yau ranar ta kasance Sunday Fannah na zaune akan dining table ba abinda babu shi agabanta inde kayan k’walama ne sauran ma ba iya cinsu ta iya ba amman tasa Anas ya siya mata ta tab’a wannan ta tab’a wancan ayayinda Anas ke a parlour se famana latsa wayansa yake da alama abu very important yake dan yadda yayi focussing akai. Chan data gaji da ciye ciyen nata ta tattara ragowar tasa cikin leda sanna ta miqe, sanye take da baggi T shirt da befi tsakiyan cinyarta a tsayi ba da hannunsa d’aya an jefar, gashinta kuwa takamasa gud’aya chan a saman kanta, zare zaren ragowan da basu samu shiga packing d’inba na akan fuskarta kasancewar sakwa-sakwa tayi packing d’in. Parlourn ta iso ta baje kan cinyansa ko uffan bece mata ba se harkar gabansa yake. “Habeebi” ta kira sunansa tana kallonsa. “Uhm Mom Hanan what is it? Har kingama shanye duk tarukuchan dake kan table d’inne?” “A’a.” Ta basa takaicaccen amsa. “Toh me kikeso?” Har a yanzu be d’ago kai ya kalleta ba hakan ya d’an b’ata mata rai. “Habeebi wai me kake haka da ko kallona baraka d’ago wannan blue eyes nakan barakayi ka kalleni ba.” Seda ya sake latsa wayan na kusan seconds talatin sannan ya d’ago blue eyes nasa “yes Baby machine me zan miki?” “Bansani ba seda ka gama replying nata kasan ina a raye ka cigaba da abinda kake” kafin tace zata tashi ya zagaye hannayensa a ‘yar kunkuminta ya dakatar da ita. “Wani irin magana kuma kike Flower? Yanzu har kina tsammanin akwai macen da zata iya snatching maki ni a duniya? (ko Fans albarka) i’m not replying any gurl kiduba wayana kigani.” “Eh daka yi deleting chat d’inba ai nasan baka sonmu da Hanan yanzu.” “Flower wai mena miki yaune kam? Naga alaman ba abinda ke miki dad’i kamar kiga kin k’untatamin, niko meh kikamin it will never change the love I have for you” daidai zeyi kissing nata kenan tasa hannu ta riqo lips nasa “kad’au yau ma wannan magic kiss nakan zeyi tasiri akaina neh? Toh bareyi ba sakeni nikam.” Sake matso da ita jikinsa yayi “tell me Mom Hanan why are you mad?” “Aww ma tambayana kake koh? Bayan tun d’azu kake ta danne dannen ka a wayanka baka damu ko _INA TARE DA KAI_ ko bana *_TARE DA KAI_* ba, your phone is more important than me.” “Inji waye Mom Hanan? Kinason kisan me nakeyi a wayan neh?” “Banaso ai na riga na san-” bata k’are maganan ba yayi shutting nata dawani hot kiss sam tak’i basa had’inkai a farko dan tasan sa sarai he is such a bad kisser nan danan zesa ta mance da dukkannin problems nata ta yafe masa ba tare da tasan tayi hakan ba, sam yak’i sake ta, ya d’au alwashin se ya kashe mata jiki liqis tukuna, yana meh bin duk wani saqo a jikinta da hannayensa yana meh mata sending electric sparks. Ai duk yadda tayi dan k’in basa had’in kai ta kasa daga k’arshe seda tayi giving in wa kiss nasa, ta sa hannayenta duka cikin gashin kansa pulling him closer, se kissing juna suke so deeply, sun d’au tsawon lokaci suna abu d’aya sannan da hanzari suka hau romacing junansu ganin abin bana tsayawa bane na bugo legediz benz d’ina na rufo musu k’ofar parlourn harda cin tuntub’e na. **_An hour later…_ “Nikam kabar kallo na da wannan mayun blue eyes naka haka bad boy kawai.” Fannah tayi maganar tana mayar da T-shirt nata jiki. Anas kuwa na a kishingid’e jikin 3 seater da nickers zallah a jikinsa, ya yi crossing arms nasa a kan chest da wani killer smile a fuskarsa yana mata wani mayen kallo next abinda yaji shine shirt nasa da Fannah ta wurga masa a fuska, hannu yasa ya cire har a yanzu bebar murmushin ba. “Flower menayi kike cemin bad boy?” “Ai kafi kowa sani” daidai tazo wucewa ta gefensa kenan yajata ta fad’a jikinsa ya saketa sam yak’i. “Bansani ba tell me” yayi maganar numfashinsu na had’ewa dan yadda fuskokinsu ke kusa kusa. “Gashi kuwa I can’t resist you koda nace barin baka had’in kai ba at last senayi because you got it all Abu Hanan.” Pecking nata yayi a kumatu “so do you Mom Hanan.” Kanta tayi adjusting a jikinsa sannan tace, “Habeebi meh kakeyi amman d’azu a wayan?” “Baby Mamah bakiyi trusting d’ina bane?” “Nayi mana Habeebi kawai ina son sani ne.” “Okay kinsan yau Baba yacika 1 year 10 months da rasuwa koh?” “Ya Salam! Habeebi wallahi na mance I’m so sorry kaji?” “Is okay nasan bada gangan kika manta ba, ban tab’a fad’a miki bane saboda aikin lada ba’a son ana yad’awa, so kowani 2-2 months nake sa akai kud’i da kaya gidan marayu in memory of Baba.” “Owww! Kayi tunani me kyau Habeebi, Allah tura masa ladan kabarinsa kaikuma Allah cigaba da bud’i dakuma kare mana kai, Hanan and I love you so much.” Tayi pecking nasa shima a kumatu.**** 3 weeks later… Daidai cikin Fannah nada 8weeks (2 months) kenan alhamdulillah jikinta da sauk’i sosai. Yau ranar ta kasance Monday as early as possible k’arfe 4:30AM Anas ya tashi shikad’ansa yahau shirya musu akwatinsu shida Fannah, suprise yakeson mata. Duk wani abinda zasu buk’ata be bari a baya ba seda yagama had’a komai sannan ya d’au ‘yar k’aramar hand luggage ya cika da kayan wasa da teddies na Baby Hanan kafin Asubah yagama had’a komai ya ajiye boxes d’in a parlour yadda Fannah barata gani ba. ** Fitowan Fannah daga bayi kenan tayi alwala, ta d’au hanyan wardrobe nasu dan ciro hijabinta Anas yayi sauri ya dakatar da ita “Mom Hanan wait hijabi kike nema koh?” Kai ta gyad’a masa. “Good gashi.” “Thanks amman banason wannan yanada nauyi nafison d’ayan barin d’auko yana cikin wardrobe d’in ai.” Gabanta yasha sabida kuwa duk hijabanta masu laushi yasa su cikin akwatin bayason ta bud’e wardrobe d’in tayi ruining suprise daya tanadar. “Habeebi wai me haka? Muna chin lokaci fah, kamatsa in d’auko hijabi na muyi Sallah.” “Ga wannan kisa.” Ya miqa mata k’in amsa tayi “banason wannan yanada nauyi.” “Toh nikuma nace kisa wannan.” Haba manah! Habeebi so kake in jik’e kafin mu idar da Sallan ne?” “Flower ai sanyi ake karb’i kisa mana.” Kafad’a ta buga “ni banaji, matsa min.” AC’n d’akin ya k’ure “kinji sanyi ake karb’a kisa.” Seda ta galla masa harara sannan ta amsa tasa bayan da suka idar da Sallan ta nad’e hijabin as always zata miyar cikin wardrobe d’in, takai hannunta kan handle d’in kafin ta bud’e Anas ya dakatar da ita ta hanyan sa hannunsa akai seda ta firgita. K’irji ta dafe “Habeebi kasan ka ban tsoro please kadaina what if wani abu yasamu Hanan fah?” “I’m sorry in shaa Allah ma ba abinda ze sameta kawo in ajiye miki jeki kwanta.” Kallonsa tayi na ‘yan lokuta. “Habeebi wallahi you are hiding something from me, meh abun? Kuma mesa bakason in bud’e wardrobe d’in dakaina?” “Saboda Dr. Yace in hanaki yin any form of labour kuma ai bud’e wardrobe ma aiki ne, prince charming naki ze miki jeki kwanta.” Har a yanzu bata yarda ba. “Sekuma meh? There is still something you are not telling me.” “Oh! Mom Hanan kin cika bincike sekace wani spy” Turata gefe yayi ya sa hijabin sannan yaja hannunta suka koma suka kwanta. Daman tun jiya ya sanar da ita bareje office ba yau dan haka tasamu takwanta peacefully. 8:07AM MIEMIEBEE
      Daidai tashiwan Anas daga bacci kenan, da k’yar ya iya ya raba jikin Fannah da nasa dan wani sabon salon baccin da ta koya bata bacci se in akansa. Bayan ya tura ta gefe yasake lullub’eta da bargo sannan yayi pecking nata a goshi. Bayi ya nufa yayi wanka agurguje yasa mint blue shirt da farin ¾ wando. Kitchen ya nufa yasoma had’a musu Chocolate-chip cookies for breakfast, in less than an hour yagama komai se coffee daya had’a musu, dining table ya shirya tsab sannan ya koma d’aki dan tayar da ita, zaune ya tarar da ita se murza idanunta take. “Good morning Flower har kin tash-” besamu daman k’arisa maganan ba dan yanayin daya tsince ta ciki kamar kuka take, daya gama k’arisowa kusa da ita kuwa seya tabbatar da hakan zama yayi a gefenta.
   Cike da tashin hankali yake maganar. “Omg! Flower why are you crying?” Kasa amsa shi tayi kawai tayi hugging nasa a yayinda kukanta ya tsananta. Bayanta yake bubbugawa a hankali, “shhh! Kibar kuka kinji I’m here stop crying Flower” seda ya tabbata tayi shiru ya d’agota. “Meya faru?”
    “Habeebi promise me baraka tab’a barina ba, promise me please.” Ta sake matsesa ajikinta tana meh cigaba da kuka.
    “Shhh! I will never leave you Fannah, never ki kwantar da hankalinki _INA TARE DA KE_ forever.” Hannu yasa ya share mata hawayen ”meya kawo wannan zance? Kinyi mafarki ne?” Kai ta gyad’a masa. “You want to talk about it?” Nan kuma ta kad’a mai kai “I’m afraid Habeebi.”
    “Toh shikenan is okay, tashi kiyi wanka yanzu.” Ba musu ta miqe ta amshi towel dayake miqa mata bayan ta cire kayan jikinta ta d’aura towel d’in “Habeebi ka rakani bathroom d’in wallahi tsoro nake wai Ya Farouq na ciki.”
     “Mafarkin Farouq kikayi dama?” Cike da tsoro ta gyad’a kai. “Karki damu Farouq is gone foever.”
   “Nasani Habeebi still ina tsoro ka rakani please” hannunta ya riqe yakaita har bathroom d’in tabarsa yafito tak’i labule taja ta tare kanta shiko yana zaune akan hand basin bayan data gama suka fito tare man shafawanta ta nema kap kan mirron babu. “Habeebi kaga lotion d’ina?” Se ayanzu ya tuna ya had’a cikin akwati d’azu. “Bangani ba Flower, babu akan mirron?” yayi qarya.
   “Babu” tayi maganar tana nufan wardrobe dan ciro sabo.
   “Wait wait!” yayi sauri ya dakatar da ita, “babu achan ga vaseline chan ki shafa.”
  “Habeebi wai me kake b’oyewa cikin wardrobe d’innan ne?”
   “Kan Farouq ne aciki kika kuskura kik-” be samu daman k’arisa maganan ba sanadiyar tsallen da Fannah ta daka se a jikinsa ta tsaya chak! hannu yasa ya tare ta kafin ta fad’i. “Na tuba wallahi barin bud’e ba, dan Allah kabari ina vaseline d’in zan shafa.” Dariya sosai ya tsaya yi “toh muje mu shafa miki amman sauk’a tukuna.” ya gwada cire hannyenta dake rataye a wuyansa, kafad’a ta buga nufin barata sauk’a ba tare da sake kankamesa, haka tana zaune kan cinyarsa ta shafa manta. Kayan ta daya cire mata wani baqin abaya ya miqa mata, “gashi sa.”
     “Habeebi abaya nefah.”
   “Ina sane ai” ya gyad’a mata kai.
   “Toh ina zamuje da zan sa abaya?”
  “Ikon Allah! Mom Hanan ko d’an bincike seya baki hanya wani irin bincike ne haka?! Allah kika sake questioning d’ina zan bud’e wardrobe d’in Farouq yafito.”
   “Nabari nabari please kabar fad’in sunansa Hanan zatayi kuka.”
   “Toh Mom Hanan na dena” yayi managar hannunsa na akan cikinta. “Flower yaushe Hanan zata soma motsi I want to feel her.”
    “Dr tace se pregnancy’n yakai zuwa 16 weeks and Hanan is just 8 weeks yanzu kaga da saura.”
    “Ohh kice min se cikin ki yayi k’aaaatoo Hanan zata fara motsi.” Hannunsa ta d’aga daga kan cikin nata “nifa na fad’a maka bawai wasan nan na sani dariya bane banaso.”
    “Toh I’m sorry yi sauri kisa kayanki.”
  “In nasa ina zam-” bata k’arisa maganan ba tayi tsit dan ta tuna da abinda Anas yace mata akan ta sake masa tambaya ze ciro kan Ya Farouq cikin wardrobe. Kamar baby ya riqota a hannu zuwa dining table yasan ta da kewaye kewaye kar idanunta sukai kan akwatinan nasu.
    “Habeebi harda breakfast kamana yau wow!” Yana bud’e flask d’in k’amshin abincin ya mamaye wajen gabad’aya se shaqa Fannah ke tana d’igan miyau. “Baby hurry up and serve me yunwa nakeji.”
   “Kwad’ayi kike ji de.” K’aramar tsuka taja ta bugesa gefe ta amshi flask d’in taja gabanta ta soma chi. Tsayuwa yayi yana kallon ta cike da mamaki ganin takusa cinyewa ba shi yayi magana “Flower nifa ban chiba karki cinye duka.”
    “Ayyah Habeebi, Hanan kuma fah? Kayi hak’uri kabarmu mu cinye mana.”
    “Bawani Hanan d’innan glutton (meh shegen cin abinci) kawai.”
   “Kafad’i koma meh mu cinye?” Kai ya gyad’a mata yana murmushi yadda takecin abinci na bala’in kashesa. Bayan da ta gama yaje yayi frying sausages ya karya dashi shima. Bayan da suka gama ya tattara dining table d’in “Flower jekisa mayafin abayan naki we are going somewhere.”
   
     “Ina kenan Habeebi?”
   “Aww! inje inciro kan Farouq ko?”
   “A’a please nayi shiru.”
  “Better jeki shirya ina jiranki and karki bud’e wardrobe d’in ni na fad’a miki.”
   “Toh Habeebi kazo muje tare wallahi tsoro nakeji” seda yayi ta mata tsiya sannan ya rakata yana ganinta tana shiryawa har tagama tayi arabian rolling mekyau me amsarta sannan ta feffesehe da turare d’ayan da kad’ai tagani kan mirron ta tambayi Anas ina sauran turarukanta kuma tana tsoron kar yaciro kan Farouq daga cikin wardrobe. “Kingama?” Ya k’are maganar hannunsa k’ark’ashin hab’anta yana kallon fuskarta datasha light makeup.
    “Eh nagama semeh kuma yanzu?”
  “Se…” Yakai bakinsa kan nata “Habeeb-” be sake mata baki ba seda ya tand’e maroon strawberry flavor jan bakin data shafa tas.
    “Haba! Habeebi” tayi maganar lokacin da ta juyo tana kallon bakin nata a mirror. “Mena sharemin jan bakin yanzu?” Tayi pouting lips nata.
   “Saboda yamiki kyau sosai and banason in mun fita mutane suna kalla min ke, because you are mine Flower, as from today banason ki sake yin makeup in zamu fita okay?”
   “Nikam wannan Habeebin” tayi maganar chan k’asa k’asa tana zumbure zumbure.
   “Yes Flower kajol da nude lipstick kawai na yarda kina sawa kinji?” Shiruu “nace kinji?”
   “Naji-” katsesa yayi “good, agida kawai na yarda kina kwalya.”
   “Habeebi gaskia akwai ka da son kai amma kaika iya d’aukan wanka kamar me zuwa gidan biki idan zaka fita.”
    “Toh mijinki neni ai” be jira ta sake magana ba yajata waje zuwa mota sannan ya dawo ya kai boxes nasu mota dake se game nata take ta  bugawa ko kad’an bata ga me yake ba seda ya shigo mota ya tambayeta “Mom Hanan are you ready?”
   “Do I have a choice bayan baka sanar dani ina zaka kaini ba.”
   “Karki damu you’ll find out soon.” Seda ta bari sukayi nisa da tafiya ta yadda barasu iya komawa gida ba, balle yace ze ciro kan Farouq tasoma jero masa tambayoyi wanda duk ciki ba wanda ya bata straight answer.
     Wani tambayan ma seda ta ga sun dosa hanyan airport “Habeebi wai me zamuyi anan?†
    “Flower inda zaki d’an k’ara hak’uri everything will turn out cool.” Badan tanaso ba tayi shiru waje yanema yayi parking sannan ya fito da ita a yayinda wani security ya cicciro musu luggages nasu “Habeebi wannan fa akwatina ne a hannun mutumin nan” tayi maganar tana bin mutimin da kallo.
  “Yes ina sane Flower” ya jawota jikinsa.
   “Toh a ina ya samu?”
   “Acikin booth kayakin mune aciki.” Cike da mamaki da rashin yarda tsantsan mamaki ta d’ago kai tana kallonsa. “Kayan mu aciki? Kana nufin tafiya zamuyi?” Gira ya d’aga mata.
    “What?! Habeebi-” yatsansa ya aza a lips nata “shhhh! Nasan me zakice ban fad’a miki ba you are not ready barakije ba but please don’t say so kinji? Don’t ruin this I’ve worked hard for it.”
    Hugging nashi tayi abinda beyi tsammani ba a tunaninsa she will freak out tace masa barata jeba. Cikin sauti cike da jin dad’i tayi maganar, “Taya zance barinje ba Habeebi bayan nasan you worked hard for it I just hope we will enjoy inda zaka kaimu. Me, you and our Hanan Habeebi.” Dad’in kalamunta yaji sosai yayi hugging nata back “we will in shaa Allah Flower, I love you dearly.” Bayan tayi breaking hug d’in ta ciro wayarta daga jakarta “me zakiyi Mom Hanan?”
   “Zan kira Mami in sanar da ita.” Wayar ya amsa “don’t worry na riga na sanar da ita lets just go, hope you are ready to go fly to Abuja?”
   “Abuja? Okay I am ready.” Wajen private jet nasa wanda be tab’a tafiya dashi ba yau ne karo na farko suka nufa se admiring jirgin Fannah ke bata tab’a ganin kalan jirgin ba se a TV.
    “Habeebi mu kad’ai zamuyi tafiyan ne?”
    “Yes Flower this is my private jet ba public jirgi bane.”
   “Ohhh wow! Its amazing baka tab’a fad’a min ba.”
   “Sorry nima ban tab’a using nashi ba seyau tun kafin muyi aure na saya I mean tun lokacin dana fara sonki Flower I was hoping Allah ze kawo min ranan da zan shiga ciki dake that is when we’ve accept each others love just as we did a very long time ago now, I love you Flower” Kyakkyawar fuskarsa ta shafa “I love you too Abu Hanan.” Hannunta ya riqe suka shiga ciki bayan angama komai da komai sauran tashiwar jirgi Fannah tasa suka karanto add’o’in kariya. Tun anan Anas yagano ta soma jin tsoro dan kuwa this is her first time shiga jirgi.
    Seatbelts Anas yamusu tighting aiko ta riqo hannunsa gagam “Habeebi na fasa tafiyan ina jin tsoro please su tsaya.” Dariya yakeson yi amman ya b’ata rai. “Flower just keep calm muna tashi everything will be normal.”
    “No Habeebi ni kawai kace musu su tsaya” a hankali jirgin ya fara tafiya bata wani ji tsoro ba seda jirgin ya fara tashi anan ta fara kuka harda hawaye hannunta Anas ya matse cikin nasa yana fad’a mata dad’ad’d’un kalamu ahaka har suka tashi da suka fara flying kuwa seta bar jin tsoron. A hankali ta bud’e idonta d’aya sannan d’ayan. “Kin dena jin tsoron?” Kai ta gyad’a a hankali “are we flying already?”
   “Yes Flower we are kiduba window kiga.”
   “A’a tsoro nakeji.”
   “Ki leqa ba abinda ze sameki am here.” Cike da tsoro ta leqa kad’an da wuri ta dawo da kanta ciki “calm down Mom Hanan ki kwanatar da hanakalinki ko kinason Hanan ma taji tsoro ne?” Kai ta kad’a masa “good” yace tare da pecking nata, headphone ya ciro yasamata akai tare da kunna mata qira’a. Cikin ‘yan mintuna suka iso Abuja nan ma da suka zo landing kad’an ya rage Fannah batayi kuka ba.
   Transcorp Hilton Hotel Abuja suka sauk’a zuwa Azahar bayan sunchi abinci sun sake wanka suka wuce embassy’n USA  kasancewar a New York Anas yakeson suyi rainon Baby Hanan. Dad’i sosai Fannah taji daya sanar da ita plans nasa, sun gaji iya gajiya wai haka ma dan da sanin ido kenan aka samu aka gama musu abubuwan on time zuwa jibi everything will be ready seya rage sauran tafiya. Koda suka dawo gida Fannah takasa fitowa daga mota dan gajiya Anas ne ya cirota da kansa yakaita har zuwa d’akinsu. Akan gado ya direta kafin ya juya ta riqo kolan rigarsa tajasa jikinta kafin yayi wani k’wararren motsi ta kifa bayansa da gadon ita kuma ta haye kansa. “Habeebi bacci nakeji.”
    “Flower bamuyi Sallan isha bafa.”
   “I know Habeebi mubari zuwa 10-11 haka se muyi please.” Shiru yayi tare da aza hannunsa kan bayanta yana shafawa a hankali. In the next 5 minites Fannah tayi bacci. “Flower!” ya kira ta shiru ba amsa.
    “Flower har kinyi bacci?”
   “Uhmm” tayi groaning cikin baccin. D’an murmushi ya saki tare da pecking kanta. A haka shima ya samu yayi bacci se 11:27PM Anas ya tashi anan sukayi Sallah suka chi abinci sannan suka watsa ruwa suka sake komawa bacci.
     Kwanan su biyu a Abuja Anas ya sama masu visa. Washegari around 8:00AM suka d’au flight zuwa New York kamar sabon shiga haka tata jin tsoro ma yau.
     _10 hours later… Exactly 6:00PM a Nigeria 1:00PM a kuma New York_
 
     Su Anas suka shigo NY gajiya kam ansha sosai, musamman Fannah kusan duk a kwance kan gadon dake jet d’in ta yini amman hakan be hana k’afafunta kumbura dam ba.
    A MANDERIAN ORIENTAL HOTEL NY suka sauk’a. Fannah de takasa b’oye k’auyancinta inwhich Anas found so adorable and cute komai tagani seta tambaya. Warming jikinsu sukayi cikin had’ad’d’en jacuzzin dake bathroom d’in sannan suka yi ordering abinci sukaci.
     Baccin sauk’e gajiya suka yini sunayi ranan da daddare bayan sun idar da Sallan isha sunci dinner Anas yahau massaging wa Fannah k’afafunta da suka kumbura bayan daya gama mata kuma suka kwanta.
     Washegari basu fita ko inaba a d’akinsu suka wuni ba abinda suka tsinana wa kansu banda romancing juna da suka yini sunayi se the next day suka fita ganin gari leisure points da dama erinsu 911 Memorial Guided Tour with Museum, Disney on Broadway Exclusive, Magic Walking Tour, NBC studio, central park, Brooklyn bridge, 9/11 Memorial and Museum, da sauran su suka jejje se killing selfies suke Fannah nawa Afrah da kishi kamar ya kasheta sending. They had alot of fun se Maghrib suka dawo masauk’insu all tired. Sallah kawai sukayi suka miqe kan gado se bacci.
      Haka fa rayuwa ta cigaba da kasancewa Mr. And Mrs. Fauzi cikin so da k’aunan juna, zamansu a New York ba shiyasa Anas hana Fannah sa hijabi ba dukda kuwa in aka gansu se an tsaya ana kallonta amman kamar yaddda bata damu ba haka shima Anas d’in, sosai yake kishin Flowersa. Baby Hanan nasu kuwa se girma take a yanzu haka cikin Fannah nada 5 months da anganta anga me ciki dan ko har ya b’ullo kai tun anan Anas ya fara neman tsokananta dan haka tama bar zama da vest inya nan se baggi kayakin da zasu b’oye mata‘yar cikin nata, ga yadda taciko dam iya cikowa Anas baya iya hak’ura da ita yanzu aduk lokacin da ya kalleta se sha’awan ta ya taso masa kullum suna cikin yin abu d’aya.
   ****
      Yau ranar ta kasance Tuesday ayau ne Mr. and Mrs Fauzi zasuje duban gender’n Baby’nsu tunda cikin yayi k’wari, dukansu bugawa zuqatansu ke barin ma Anas dakeson ‘ya mace kamar hauka.
**
     Murna gun Anas da Fannah baya misantuwa da aka tabbatar musu mace ce baby’nsu. Sabon siyayya Anas yace zasu soma yiwa Baby Hanan yanzu da aka tabbata Hanan d’ince a hanya, inbawani ikon Allah ba.
     Ta ward d’in karb’an haihuwa suka fito aiko Fannah na ganin yadda mata masu ciki ke nak’uda yadda suke shan azaba ta rushe wa Anas da kuka. Kuka na sosai seda suka nemi waje suka zauna hankalinsa duk yabi ya tashi ya rasa meya sata kuka haka, just a while ago she was happy jin sex na baby’nta yanzu kuma tana kuka to meh dalili? Ko ta dena san ‘ya mace sena miji ne?
    “Flower is okay kinji stop crying please ya isa” ya cusa ta ajikinsa yana bubbuga bayanta har izuwa lokacin da tayi shiru.
© MIEMIEBEE
TANA TARE DA NI…
TANA TARE DA NI… PAGE 90
BY MIEMIEBEE
 
     
       “Flower mesa kike kuka? Do you want to talk about it?” A nitse ta d’ago kanta daga k’irjinsa ta share hawayenta sannan ta masa nuni da ward d’in. Cike da rashin fahimta yace, “what about it Flower?”
    “Habeebi baka ga yadda matan suke kuka bane? Yadda haihuwan ke basu wahala Habeebi I’m afraid” tasake rushewa da kuka. Kallonta ya tsaya yi Fannah barata ishesa da kallo ba. Sake kwanto da ita yayi a jikinsa yana bubbuga bayanta “is okay kinji bar kukan ya isa, you will have a safe and easy delivery in shaa Allah zamu cigaba da miki addu’a bar kukan haka ya isa.”
    “Habeebi ina tsoro kasan wasu matan daga labour room se lahira suke wucewa Habeebi banason in mutu ban rik’e Hanan ba.”
    “Flower kibar magana haka wayace zaki mutu baraki riqe Hanan ba? In shaa Allah zaki shiga labour room kuma kifito fine and good banason irin maganan nan kinji? Stop crying ya isa.” D’agota yayi sannan ya share mata hawaye “lets go and eat.”
    Ba musu ta miqe tana manne a jikinsa har suka isa gun motansu. Yana cikin driving ya juyo ya kalleta tayi lamo jikin kujeran tana kallon window.
    “Flower kinsan you are funny koh.” Ba tare da ra juyo ba ta amsa shi, “menayi kuma yanzu?”
   “Kukan da kikayi mana, gaskiya banason Hanan ta d’auko kukanki abu kad’an kuka.”
    “Sekayi ai kai dama in baka nemi tsokana naba bakajin dad’i.”
   “Oh common Mom Hanan chill please wasa nake miki.” daga nan bata sake che masa k’ala ba.
    A Restaurant Manhattan Anas yayi parking bayan ya fito da ita daga motan sukayi ciki, table dake kusa da bakin k’ofar ya zaunar da ita a yayinda ya yi ciki dan yimusu order kasancewar traditional restaurant ne. Fannah na zaune ita kad’ai kan kujerar tayi jugum har a yanzu hankalinta be kwanta ba regarding mata masu nak’uda data gani d’azu daga bisani ta d’ago kai tana kallon k’ofar seji take kamar ana binta da kallo data dudduba kuwa se bataga kowa ba.
     Kamar daga sama taji hannu dafe kan kafad’ar ta a razane ta d’ago kai acewarta ma kidnapping nata za’ayi harta bud’e baki zata sa ihu setaga mace ce ‘yar uwarta anan ne hankalinta yad’an kwanta. Bata tab’a sa matan a ido ba amman kuma she is sure ba a yau ta fara ganinta ba zuciyarta se rad’a mata take she’ve met this woman before amman ta rasa a ina.
    “Sannu Sister yi hak’uri in na razanar dake please.” matar tayi magana cikin muryarta wanda sosai yayi kama da wata wanda Fannah tasani amman ta rasa gane a ina, no matter how tayi ta tuna a’ina tasan muryar ta kasa.
   “A’ah ba komai Aunty” cewar Fannah har a yanzu se kallon wannan babbar mace me k’imanin shekaru 45 take tana me tunanin a’ina ta tab’a ganinta.
    “Toh nagode nace dan Allah wancan da kuka shigo dashi just a while ago mijnki ne?” Shiru Fannah tayi tana  nazarin ko ta bata amsa kokuwa kar ta bata saboda question d’in is too private. Shirunta ya sake bawa matar damar magana. “I’m sorry please karkiji tsoro ba abinda zan miki suna na AYSHA kuma ‘yar Nigeria ce nima kamar ku kawai I want to know ne please ki fad’amin.”
    “Eh mijina ne.” tayi maganan idanunta cikin na Aysha, hawaye ne suka soma gangarowa kan kumatun Aysha wanda yamugun bawa Fannah mamaki toh kode son Anas nata wannan Aysha ke da har zatayi kuka da ga jin ance yanada aure.
    “Aunty Aysha mesa kike kuka?”
  “Babu, babu ba komai sunan mijin naki A… A… Anas koh?” cike da mamaki Fannah ke kallonta har taya tasan sunan Anas? Ta bud’e baki zatayi magana kenan Anas yakira ta from far behind.
   “Flower!” Da sauri ta juya izuwa direction nasa, drinks biyu ne riqe a hannunsa “wannan ko wannan kikeso.” Murmushi ta saki sannan tayi nuni dana hannun daman nasa, ido ya kashe mata sannan ya koma anan ta juyo dan cigaba da magana da Aysha sede ta duba gabas da yamma kudu da arewa bataga Aysha ba. A nitse ta miqe ta fito waje tana kewaye kewaye ko zata ganta amman ko alamarta babu, badan tanaso ba ta dawo ciki ta zauna shima Anas bada dad’ewa ba yadawo da plates nasu a hannunsa nata ya ajiye mata a gabanta. “Thank you Habeebi amman basu da waiters ne sekai zaka kawo mana da kanka?”
    “Ninaso Flower, kinsan white people d’innan da shegen son mata banason su kalla min ke.” Dariya sosai take “over possessive ba” tace cikin dariya.
    “Na yarda whatever lets eat.” Cike da jin dad’i suka soma chin abincin daga bisani Fannah tace, “yauwa Habeebi bakasan meba.”
  “Meneh?” Ya tambayeta tare da kai spoon baki yanacin abincin.
   “Shiganka ciki wata mata ‘yar babba haka tazo ta sameni take tambayana wai ko kai miji na ne dana tabbatar mata mijina ne kai sekuma tasoma min kuka wai sunan ta Aysha kuma abinda yafi ban mamaki ma yadda tasan sunanka, nayi nayi intuna a ina na tab’a ganin ta amman na kasa ‘cause her face seems familiar.”
    Spoon daya kai bakinsa ya maido shi plate d’in tare da d’ago blue eyes nasa yana kallon Fannah. Anan data kuma k’are masa kallo itama se ta tuna a ina tasan kamannin fuskan Aysha, anan tagane a’ina ta tab’a ganin fuskar Aysha ashe cikin family photon su Anas ne wanda ya goge fuskarta, anan ta gane Anas nata ke kama da Aysha, muryar Amal kuwa sak na Aysha ce. Aysha itace Ummimin su Anas. Ummimi na raye bata mutu ba.
    “Kikace meh?” Cewar Anas alokaci d’aya yaji lisafin k’wak’walwarsa na gushewa jin an ambaci Aysha sunan mahaifiyarsa da ya tsaneta fiye da komai a duniya.
    “Habeebi Ummimi nagani, wallahi ita nagani just a while ago.”
    “Whaattt?!” Ya tambayeta cike da k’in yarda.
   “Habeebi itace wallahi itace, Ummimi ce tana raye tashi mu neme ta I know she is somewhere close to us” kafin ta miqe Anas ya zaunar da ita har a yanzu besan meyake ciki ba tunaninsa duk ya jagule kayinsa na juyawa. K’arfin hali yayi yace, “ba ita bace Flower, Ummimi ta mutu inma bata mutu ba tana chan bangon duniya da mijinta da yaranta saboda haka ba ita kika gani ba lets eat and leave this place.”
   “Hab-” katse ta yayi a tsawace “I said enough ba ita bace!” Ta mugun firgita barata iya tuna when last Anas ya mata tsawa haka ba ‘yar k’ollan dake ciko mata a ido tayi sauri ta shanyesu bata sake ce masa komai ba.
    Sunfi minti biyu zaune ahaka ba tare da sunce da juna ko uffan ba, abincin gabansu ma duk sun kasa chi as Fannah ta zura wa Anas daya zurfafa cikin tunani ido.
      _What if abinda Fannah ke fad’i gaskia ne dan kuwa be tab’a fad’a mata asalin sunan Ummimi ba how comes zata sani inhar bawai taga Ummimin bane dagaske. Amman kuma is it possible? Meze kawo Ummimi New York? Dakansa ya amsa wannan tambaya._
     _Ai koda tazo tafiya ce mana tayi wanda ze aureta yace ze kaita k’asar waje meaning k’asar waje nan New York ya kawota kenan?_
    Kai ya girgiza a sauri “No it can’t be!” yayi maganar a fili. Hankalin Fannah yayi matuqar tashi ganin hankalin Habeebinta ba’a kwance ba.
     “Habeebi is okay kaji? Ya isa haka Abu Hanan.” tasa hanky ta share masa zafaffun gumin dake k’eto masa. “Lets go” yace da ita tare da miqewa ya riqo hannunta suka fito suka kama hanyan lot kamar ance Fannah juya ta juya idanunta basu sauk’a ako ina ba sekan Ummimi dake tsaye daga bakin k’ofan Restor d’in, sanye take da hijabi bak’i iyaka guiwa fuskarta duk alamun hawaye, kallo d’aya za’a mata agano tsantsan rashin kwanciyan hankali da wahala tattare da ita amman duk da hakan kyawun halittan fuskarta wanda su Anas suka d’auko be gushe ba.
     “Habeebi” Fannah takira sunansa tare da dakatar da tafiyarta badan yanaso ba yatsaya shima batare da ya raba hannayensu ba. “What is it Flower? Lets go!” Yayi maganar cikin wani erin murya. “Habeebi ka juya ka ganta gata chan” a hankali yake karkato da kansa har ya juya gabad’aya sannan ya d’ogo blue eyes nasa ya miqar basu sauqa ko ina ba se akan Ummimi. Kallonta yake cike da rashin yarda, sam yakasa yarda Ummimi ce yau a gabansa shekaru nawa rabuwansa da yasata a ido? 15 good years, memories na incident daya faru lokacin tafiyar Ummimi ne suka soma masa yawo a k’wak’walwa.
      “Anas” yaji muryar Ummimi dake nan kamar na Amal na tsamo sa daga duniyar tunanin daya wula, a gabanshi yaga Ummimi tsaye idanunta cike dam da hawaye tana kallon cikin idanunsa. “Anas… My.. My… My son… Anas my son” tasa hannu akan kumatunsa tana shafawa a hankali ayayinda k’arfin kukanta ya dad’u, shi kansa Anas idanuwansa sun kad’a sunyi jazir, he don’t even know what he is feeling fatansa kad’ai Allah sa dukkannin wannan mafarki ne.
     “Anas my son kamin magana dan Allah.” Hannunta ya sauk’e daga fuskarsa cike da k’in yardan itance a gabansa. “Ummimi?” Ya kira sunanta. “Kece?”
    “Nice Anas, Ummimi ce mahaifiyarka, Ummimi ce your own very real mother, Anas nice.” Duk yadda yayi dan shanye kukan yakasa besan a lokacinda yasoma zubar da hawaye ba, Fannah dake tsaye a gefensu tayi shiru ta k’ure musu ido tana kallon yadda suke zubar da hawaye.
     “Anas kayi min magana please” yunk’urin hugging nasa tayi wanda sakamakon haka yaja baya da wuri. Hannun Fannah ya rik’o “lets go Flower” nan ya juya.
   
    “Anas!… Anas! dan Allah ka tsaya.” Cewar Ummimi cikin sautin kuka. “Habeebi please ka tsaya ka saurareta kaji please” Fannah tayi maganar tana k’ok’arin tsayar dashi amman sam yak’i saurarenta. Murfin motan ya bud’e mata “get in!”
   “No Habeebi I’m not getting in, taya zaka bar mahaifiyarka haka?”
    “Fannah kinga banason abinda ze had’ani dake just get in” zata sake magana ya daka mata tsawa “I said get in!” Shi da kansa yasata cikin motar sannan ya zagaya ya shiga shima ya kunna motar. Ta window Fannah ke kallon Ummimi dake kuka sosai tana bin motar nasu da kallo amman Anas kota kanta beyi ba.
  ** Some hours later…
     Zaune Anas ke akan wresting chair yayi shiru, tun dawowansu bema Fannah magana ba itama haka bata huce da masifan daya mata ba d’azu ba, zaune take kan gado tana kallon sa a nitse ta miqe taje ta samesa tana tsaye akansa amman ko kewayowa ya kalleta beyi ba. “Habeebi” ta kira sunansa tare da zama kan cinyansa.
    “Yes Flower” yayi maganar not paying attention to her, hannunsa ta d’aga ta had’a da nata. “Habeebi I’m sorry for crossing you earlier.”
   “Is okay Flower ni yakamata in baki hak’uri for shouting at you I’m sorry kinji?”
    “Ba komai ya wuce muje mu huta.” Kai ya kad’a mata “banajin bacci just go, nap well Baby Hanan” yayi maganar hannunsa kan cikin Fannah.
   “Mesa baraka kwanta ba Habeebi ba haka na sanka ba tunanin Ummimi kake?”
    “I don’t want to talk about her Flower jeki huta.”
   “Habeebi yakamata ka cire son zuciya kayi facing reality, duk abinda Ummimi ta maka kamata yayi kayi hak’uri ka yafe mata, uwa uwa ce yanzu zakaso ace Hanan ta min kalan abinda ka ma Ummimi?”
    “For God’s sake Flower kidena kwatanta Hanan da Ummimi, Allah raba Hanan da halin Ummimi banason maganan ta karki sake d’auko min maganar ta.” Zata sake magana ya katse ta “am I clear?” Badan tanaso ba ta gyad’a masa kai ta sauk’a kan cinyansa ta koma gado ta miqe. Batasan a lokacin da bacci yayi awon gaba da ita ba.
     A hankali ya miqe ya nufa wardrobe tare da ciro wallet nasa family picture’nsu ya bud’e yana kallon fuskar Ummimi. “Why do you have to show up Ummimi? Why? Bayan duk mun mance dake munyi moving on mesa zaki dawo ki sake hargitsa mana rayuwa as you did before, why? Mesa bakida tausayi ne?” Ganin bayida amsoshi ga wannan tambayoyi ya haye gadon ya kwanta a gefen Fannah tare da kwantar da ita jikinsa hannunsa na akan cikinta.
   “Hanan in shaa Allah baraki d’au halin Ummimi ba, baraki ma yaranki abinda Ummimi tama Daddy’nki ba.” Daidai nan Hanan dake ciki tayi kicking take Fannah ta tashi “Habeebi Hanan ta motsa yanzu” murmushi ya k’irk’iro mata “yes Flower nima naji” hannunsu duka suka kai kan cikin nan Hanan tasake motsawa. Dad’i kamar ya cinyesu both suna feeling baby Hanan insu.
    **
     _Washegari 1:30PM_
   Anas na tsaye a gaban mirror a bathroom fuskansa shaving cream ne da alama shaving zeyi danko riqe yake da shaving stick a hannu amman sam ya kasa yi, gabad’aya hankalinsa bayya a jikinsa ko bacci yakasa jiya se tunanin Ummimi yake, duk yadda yasan ze iyabi dan hana tunaninta yayi amman ya kasa the more yana hana kansa the more yake tunanin nata, Fannah ma takasa bacci ta zauna awake with him ko kad’an bayason maganan Ummimi koda Fannah ta taso da maganar masifa yake mata sosai wanda shima ba a son ransa yakeyi ba, he just can’t take it.
    Ya zurfafa cikin tunaninsa next abinda yaji shine hannun Fannah akan nasa tana amsar shaving stick d’in kwata kwata besan lokacin da ta shigo ba. Sanye take dawani silky dogon riga me spaghetti hands. “Habeebi take it easy please banason ina ganinka cikin damuwa.” Juyo da fuskarsa tayi ta soma yimasa shaving d’in lightly kamar yadda take ganin yanayi. Bece mata komai ba har seda ta gama masa ta wanke mai fuskar tare da share ruwan da towel. Kallon kansa yayi a mirron, sosai shaving d’in yamasa kyau saboda bata kwashe gashin duka ba, tabar sajen da kuma beard nasa wanda suka had’e kad’an very light irin na larabawan nan sosai yayi kyau.
   “Flower kin ma fini iya shaving d’in ban tab’a leveling haka ba” yayi maganar yana shafa kan gashin fuskar nasan. “Thank you sweetheart.”
   “No big deal Habeebi” Hannayenta ya had’a gu d’aya tare da pecking nasu, “Flower ko baki fad’a ba nasani you are mad at me saboda abubuwan dana riga miki jiya, I’m sorry kinji? I’m sorry for shouting at you and Hanan”
     “Na sani Abu Hanan you don’t have to be sorry komi ya wuce muje muci abinci amman yau ba anan nakeson chin abinci ba.”
    “Fad’i duk inda ke da Hanan kukeso muje muchi.”
  “A Restaurant Manhattan mukeso” (inda sukaga Ummimi jiya) kai ya girgiza mata “no Flower baramu je chan ba choose any other place amman banda chan.”
    “Ayya Habeebi chan nakeso.”
   “Flower NO! And that stays that bara muje chan ba.” Ba tare da tace komai ba ta k’wace hannayenta daga nasa ta fice zuwa d’akinsu tare da kwanciya kan gado tana jin footsteps nasa ta soma rera kukan qarya.
    “Flower yanzu kuka kike saboda nace bara muje chan ba?” Yayi maganar yana k’ok’arin d’agota. Shuresa ta shiga yi “ka sakeni nikam bana so stop touching me.”
    “Haba Mom Hanan I’m sorry kinji?”
  “Banji ba ni ka sakeni.” Kunnuwansa ya riqe both “Flower I’m sorry kiyi hak’uri.” Da hanzari ta suk’e hannayen nasa “ni bance kabani hak’uri ka ka kaini Restaurant Manhattan kokuma karka sake min ko Hanan magana.”
   “Flower kiyi hak’uri mana ki zab’i wani restor daban.” Banza dashi tayi tare da juya masa baya. “Mom Hanan magana fa nake miki…” Nanma shiru “Mom Hanan” still shiru “toh naji tashi muje Restaurant Manhattan d’in” a ransa yana me addu’an Allah yasa kada su had’u da Ummimi. Cike da ji dad’i ta miqe tare da brushing masa ligjt kiss a lips “thats my Abu Hanan! Lets go” kallonta kawai yake cike da adoration.
© MIEMIEBEE

Cike da so da qaunan juna suka shirya suka fita chin lunch a restaurant Manhattan kamar yadda Fannah ta buqata, bayan Anas ya kawo musu order’nsu suka soma ci cike da jin dad’i, sosai Fannah ta zage ta gabza abincin se kewaye kewaye take ko zata ga Ummimi daga bisani k’ofar restaurant d’in ya bud’u atare Fannah da Anas suka miyar da kallonsu wajen Ummimi sukaga tsaye wajen tana rik’e da leda da alama shopping tayi sanye take da rigan cleaners, mamaki ne fal kwance kan fuskokinsu musamman ma Anas bade Ummimi aiki take anan as a cleaner ba? ya tambayi kansa disbelievingly. Sun d’au tsawon minti biyu suna kallon juna sannan daga bisani Anas ya kawar da kallonsa daga gareta ganin hawaye sun soma ambaliya mata a fuska. “Flower tashi mutafi.” Dagangan tace, “Habeebi ban gama chi bafa.” “Nasani zanje in siya miki wani lets leave now” yayi maganar tare da miqewa, kafin Fannah ta sake samun daman magana Anas ya d’agata badan tanaso ba tasoma binsa sunzo daidai bakin k’ofan kenan zasu wuce Ummimi tasa hannu ta tare Anas ta hanyan rik’o hannunsa chak! ya tsaya ba tare da ya juya ya kalleta ba. “Anas dan Allah karka min haka nasan banida iko akanka nasan banida daman tambayar yafiyanka amman dan Allah kabani daman baka hak’uri dan Allah Anas” ta k’are maganar cikin sautin kuka. Shiru Anad yayi totally speechless ayayinda zuciyarsa ke raya masa kar ya kuskura yabata wannan dama zuciyan nasa kuwa yabi ya fisge hannunsa daga nata yakama tafiya, dawani erin force Fannah taja kanta baya tare da k’wace hannunta dake a nasa cike da tashin hankali ya juyo yana kallonta. “Flower lets go!” Yayi demanding. “No Habeebi I’m not going anywhere with you se inhar ka tsaya ka saurari Ummimi, haba mana Habeebi wannan fa mahaifiyarka ce ita ta tsuguna ta haife ka bekamata kana wulaqantata kamar kashi ba, Habeebi nasan kanason Ummimi please give her this one chance to explain herself please for Hanan.” Alokaci d’aya Ummimi taji tana son Fannah dan yadda ta burgeta, “nagode ‘yata, Anas dan Allah kaji maganar matarka kabani daman baka hak’uri dan Allah Anas.” Hannunsa Fannah ta rik’o a hankali tana mirzawa “kaji Habeebi? Zaka iya bawa mahaifiyarka daman baka hak’uri, can you? Please…” Kallonsa ya miyar kan Ummimi daba abinda take banda kuka yana ganinta kawai se last incident daya faru tsakaninsu ya soma masa yawo a k’wak’walwa seyaji he can’t give her the chance she is asking for, gabad’aya ya riga ya dawo daga rakiyarta da ace 15years back ta dawo da yayi accepting nata amman banda yanzu. “No I can’t Flower I can’t mutafi nace!” Yayi maganar a tsawace. “Habeebi is okay calm down okay? Calm down” tayi maganar cikin salon dake kwantar masa da hankali. *“INA TARE DA KAI Hanan NA TARE DA KAI*do this for me please just listen to her” badan yanaso ba ya gyad’a mata kai. ** Zaune Anas da Fannah ke kan wani d’an dogon kujera a yayinda Ummimi ke zaune opposite them fuskarta jik’ap da hawaye. Cikin kuka ta soma magana; “Anas nagode daka bani wannan dama nagode sosai Allah maka albarka” ko kallon direction nata baiyi balle yace ameen. “Nasan banida izinin da zan fara rok’ar gafararka saboda abinda na muku, bansan ta ina zan fara baka hak’uri ba wallahi barin ku danayi shine babban kuskuren dana tafka a rayuwata Anas, kuskuren da har a yau ina nadamar sa kuma har in mutu zan cigaba dayi, wallahi sharrin shed’an ne it wasn’t my intention to leave you guys my family.” Ta tsaya ta share hawayenta tare da jan hanci “Anas I love you, wallahi ina sonka fiye da yadda nakeson kaina, tun tafiya na a kullum da tunaninka dana mahaifinku dakuma na k’annenka nake kwana nake kuma tashi dashi, da abinda na muku tun aduniya na fara ganin sakamakon sa ina ace na tafi lahira ban nemi gafararku ba? Anas dan Allah kayi hak’uri, baka bani dama ba amman ni na baiwa kaina kayi hak’uri ka yafemin please na tuba Anas ka tausaya min mahaifiyarka dan Allah d’ana barin iya samun kwanciyan hankali ba har se in ka yafemin ka tausaya min please.” Ta rushe da kuka miqewa Fannah tayi takoma gefenta ta tsaya tana shafa bayanta cike fa tausayi idanunta itama sunyi jazir. “Ummimi please kibar kukan haka nan ya isa dan Allah.” ‘‘Yata dan Allah kimasa magana ya tausaya min ya yafemin.” “Anas Habeebi ka tausayawa mahaifiyarka please.”Kai ya girgiza cike da takaici “mahaifiya? Yanzu ke Ummimi bakiji kunya ba da kike kwatanta kanki da mahaifiyata nikuma da d’anki? Bakiji kunya ba? As far as I’m concerned Ummie itace mahaifiyata. D’an da kika tunkud’esa kamar kashi 15 years ago, d’anda kika k’yamata d’an da kika masa permanent tabo a hannu” ya yi rolling hannun shirt nasa ya nuna mata tabon tabbas ta tuna itace taji mai ciwon danko kafin ta fice daga gidan taga yadda hannunsa ke yoyon jini amman saboda yadda shaid’an yafi k’arfinta alokacin ta fice ta barsa. Wani sabon kukan ta rusheda. “Kin tuna ciwon?” Ya tsamota daga duniyar tunanin data fad’a. “You think you still have the right to call me your son? Kinsan kalan k’uncin rayuwan da mukayi witnessing bayan tafiyarki? Kinsan ya akayi aka girmar damu aka girmar da Amal jaririyan da kika turo bayan tafiyarki precisely? Kinsan ya aka tarbiyyattar damu?” Zuciyanta taji yawani buga tare da sarin da kanta ke mata tana me k’ara tsanan kanta. “Kinsan ya akayi muka taso ba gatan uwa har muka fara mancewa da labarinki? Kinsan dare nawa muka kasa bacci saboda tunanin ki? Kinsan kwana nawa na d’iba inayi a waje ina tunanin ko zaki dawo mana? Kinsan what hell you made Abuu went through? The answer is No baki sani ba saboda alokacin kina chan da sabon mijinki kina more rayuwa. Its all over Ummimi I’ve loved you, we’ve loved you so dearly bu not anymore banida gurbin da zan sake ajiye soyayyan ki a zuciya na saboda na dawo daga rakiyarki, ke kika haifeni I can’t change that amman abinda nakeson kisani shine ki sa a mind naki baki tab’a haifan d’a me suna Anas ba, so nake ki mance dani kamar yadda na manta dake a rayuwa na cause I can‘t forgive you I will NEVER forgive you.” Yana kaiwa nan ya miqe da sauri tare da juyawa gudun kar hawayen dayake maqewa su fito seda ya shanyesu sannan ya juyo alokacin kuka sosai Ummimi ke wane zata cire ranta ayayinda Fannah ke bata hak’uri. “Anas tabbas ba k’arya cikin kalamunka tabbas nasan namuku laifi, laifin da yayi babban tabo duka a zuqatanku wallahi nayi nadama Anas kabani dama in biyaka 15years that passed, let me make it up for the past 15years da mukayi ba tare ba please kar ka hanani performing obligation d’ina as your mother.” “You are not my mother so you don’t have to saboda I don’t need you ko ayau akace Ummie wacce ta girmar dani wacce nake regarding nata as my mother ta rasu zan cigaba da rayuwa na balle ke, because I’m a grown up now as you can see I’m married saboda haka I don’t need you na yafe miki tsawon 15 years da mukayi ba a tare ba, ba sekin biyani ba, kitafi ki koma inda kika fito banasonki a rayuwa. Flower lets go” yaja hannunta suka soma tafiya, k’ok’arin jan hannunta daga nasa take amman takasa har seda suka isa mota tana kuka tana mai magana “haba Habeebi ban tab’a sanin your heart is as cold ba se yau, mahaifiyarka ce fa your own mother koda laifin kisan kai tayi be kamata ka mata haka ba, ka duba yadda tayi nadama mana kodan haka baraka saurara mata ba?” “Yes Flower barin saurara mata because I don’t need her 15years danayi ba ita yasa na mutu ne? No saboda haka bana buk’atar ta taje tasamu family’nta we don’t need her.” “Hab-” katsesa yayi “enough okay?!” Yayi maganar cikin sautin tsawa ganin yadda ta firgita sekuma yaji ba dad’i hannayensa ya aza kan shoulders nata “Flower I’m sorry banason ina miki tsawa, banason muna musu banason Ummimi ta zama sanadin samu fad’an da bama yi please stop crossing me kibarta let her be kinfi kowa sanin kalan k’uncin data jefa mu especially me, data tafi ta barmu without turning back. Ko kin manta saboda ita nasoma shaye shaye har ya kaiga nayi raping naki Flower duk kin manta? It because of her you suffered itace silan komai Ummimi batada advantage se disadvantages.” “Tabbas ba k’arya cikin maganganunka Anas” cewar Ummimi dake tsaye some inches away from them da alamun ta saurari dukkannin abinda Anas ya fad’a. “Tabbas duk wani abin haramun da ka aikata nima me laifi ce kuma nice sila saboda da ace ina nan da na hanaka aikata hakan, kayi gaskia da kace banida advantage se disadvantages all am asking for is kabani dama to be a mother to you again Anas koda baraka yafemin ba kabani dama insake rik’eka a hannayena in dafa maka abinci this is all I ask Anas please.” “You should hace thought about this 15years ago kafin kika tafi, alokacin ne wad’annan kalamu naki zasuyi tasiri akaina amma banda yanzu da kika riga kika karya min zuciya in baki sani ba kisani I’m not the Anas you left 15 years ago wannan Anas bayida tausayi saboda tafiyar mahaifiyar sa yakoya masa rashin tausayi da imani, my heart is as cold as stone dan haka kibar b’ata yawun bakinki kina bani hak’uri barin tab’a hak’ura ba Flower lets go.” “Okay Habeebi zan bika amman please kabani koda minti biyu ne inma Ummimi magana kaji?” “Flower me zakice mata? Kibarta please.” “Habeebi dan Allah fa nace please minti biyu kad’ai.¢ Kai kawai ya gyad’a mata “thank you so much my Lion.” Wajen Ummimi ta nufa taja hannunta suka b’ace daga kallon Anas bisa wani bench suka zauna Fannah na sharewa Ummimi hawaye. “Please kibar kukan hakanan ya isa dan Allah.” A raunane ta d’ago idanunta tana kallon Fannah “ ‘yata ya sunanki?” “Fannah, Fannah suna na.” “Masha Allah Fannah nagode da kulawarki a gareni Allah sak’a miki da alheri yakuma sauk’eki lafiya” (agarin share mata hawaye da Fannah ke hijabinta ya d’agu anan ne Ummimi taga cikin nata.) Mamaki ne ya mamaye fuskan Fannah taya Ummimi tasan tana da ciki? Cike da kunya tace, “ameen Ummimi please kibar kukan haka nasan Anas haka yake yanada taurin kai ne kuma sonki da yake yasa yake treating naki haka amman in shaa Allah wataran se labari Anas ze yafemiki nan bada jimawa.” “Haka kike gani ‘yata Anas ze iya yafemin abinda na masa?” “Allah ma muka mai laifi ya yafe mana balle d’an da kika haifa? Trust me ze yafe miki kidage da addu’a kawai nima zan saki cikin nawa.” “Nagode sosai ya Shettima yake dan Allah?” “Shettima nanan girmansa kusan d’aya da Anas yana kan karatu.” “Masha Allah nasan da kunya ma in tambayeki ya baby’n dana turo musu da ita bayan tafiya na wanda ko halittan fuskarta ban k’arewa kallo ba.” “Amal? Amal sunanta she is 15 years now itama ta na nan lafiya tana ss2 kinsan wani abu?” Kai Ummimi ta kad’a “sautin muryanku d’aya dakika fara min magana na zata ma Amal ce.” Murmushin takaici ta saki “Allah sarki Amal Allah yi mata albarka” “Ameen barikiga pictures nasu” nan taciro wayarta tana gwada wa Ummimi, hawaye sosai Ummimi ke kamar ba gobe tana me sake tsanan kanta abinda ta ma family’nta. “Amal da Anas sak kaman ni na, Shettima ma ba laifi, ‘ya‘yan Albarka Allah ya cigaba da raya min su yamusu albarka, yamuku albarka gabad’aya” tafad’a tana share hawayenta. “Ameen Ummimi.” “Ya Babansu yake? Wace Ummie da Anas yake fad’a kuma?” “Babansu na nan k’alau, Ummie k’anwar mahaifinsu ce.” “Ohhh Allah sarki nako ganeta itace ta girmar dasu?” “Eh itace.” “Allah sarki Allah ya saka mata da alheri, Babansu be sake aure ba?” “Gaskia be sake ba” “Allah sarki Ya Ibraheem, Fannah awani gari kuke yanzu da zama?” “Dukan mu a Maiduguri muke.” “Okay kunzo nan shaqatawa ne?” “Eh munma kusa komawa zaman nan ya ishemu gida yafi dad’i.” “Hakane ‘yata no place like home, dan Allah kitayani ma Anas magana nasan yana jin magananki koda bare yafemin ba yabani izinin zama mahaifiyarsa again, I want to make up for the past 15 years da mukayi ba a tare ba.” “In shaa Allah Ummimi karki damu sede wani gudu ba hanzari ba am sorry to ask mesa kikesa uniform na cleaners?” Murmushin takaici ta saki tare da share hawayenta. “Anan nake aiki Fannah as a cleaner.” “Subhanallahi cleaner kuma Ummimi? Meya faru? Meyasa?” “Long story ‘yata da wannan aikin kad’ai na dogara.” “Ummimi ina mijniki da ‘ya‘yanki? A yadda Anas yabani labari aure kikayi bayan tafiyanki.” “Tabbas aure nayi, Fannah mijin dana aura d’an cult ne nagudu nabarsa har a yau nemana yake.” “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un to ‘ya‘yanki fa ko babu?” “Akwai har uku nafarin mata ne twins Basmah da Barrah sekuma autan Aleeyu wanda yake nan sak Anas har blue eyes nasu wanda sukayi inheritting dagu gun mahaifin kakana iri d’aya.” Hannu tasa a aljihunta taciro picturen ta nuna wa Fannah. “Woww masha Allah kyawawa dasu.” “Barrah da Basmah are 13 years, Aleeyu kuma 10 daganan ban sake haihuwa ba.” “Ayyah, wallahi Aleeyu sak Anas inda bansani bama cewa zanyi Anas ne haske kawai Anas ya d’ara sa kad’an but Ummimi a ina suke su yanzu? Suna wajenki ne ko wajen mahaifinsu?” “Ko d’aya ‘yata suna wajen mahalicinsu.” Tasa hannu tana share hawayenta. “Ban fahimce kiba Ummimi.” “Babansu yayi kud’i dasu Fannah, ya siyar da ‘ya‘yan cikinsa wa k’ungiyansu.” “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” take itama Fannar tasoma kuka. “Ummimi I’m so sorry kiyi hak’uri dan Allah, Allah sa k’arshen wahalansu kenan Allah sarki kiyi hak’uri dan Allah.” “Bakomai nima abinda yasa na gudo na barsa kenan saboda nice next target nasa jini na ne next abinda k’ungiyansu suke buk’ata dana gano hakan na gudu na barsa.” “I’m so sorry Ummimi shi rayuwa haka yake kowa da kalan jarabawarsa, ki cigaba da musu addu’a bale ma yara ne dukansu Allah sa masu cetoh ne.” “Ameen ya rabb-” bata samu daman k’are maganan ba ganin Anas datayi. “Flower lets go.” yayi i terrupting nata. “Toh Anas ina zuwa yanzun nan” bayan daya koma ta dawo da kallonta kan Ummimi. “Ummimi yanzu a ina kike kwana?” “Anan a d’akin da aka tanadarwa cleaners.” “Subhanallah mesa baki fad’a min ba? Bari zanyi wa Anas magana inshaa Allah zaki biyomu gida.” Hannunta Ummimi ta rik’o da sauri “a’a Fannah karki ma b’ata yawun bakinki please I don’t want to be a burden ni abinda nakso kimin d’aya ne hanyan da zesa Anas yayi accepting d’ina as his mother.” “Duka biyu zanyi Ummimi bareyi kina kwana agidan cleaners ba bayan da gatanki ina zuwa” nan ta fice taje tasamu Anas dake tsaye gefen motansu yana jiranta seda ta iso gab dashi ya saki mata murmushi wanda itama ta miyar masa “lets go?” Kai ta gyad’a masa tare da ajiye masa picture’n su Basmah akan bayan motar. “Meshi?” Ya tambayeta. “Ka duba kaga” ba gardama ya d’aga hoton yana kallo. Be sansu ba amman seji yake kamar yasansu gakuma me kamanninsa dayake gani cikin hoton harda blue eyes d’inma, tunaninsa ne ya jagule alokaci guda he seems puzzled. “Flower suwaye wannan? Waye wannan yaron?” “Kaga kuna kama koh?” “Sosai kuwa the eyes the face everything please suwaye ne?” “Your siblings Habeebi, k’annenka ne.” “K’annena?” Ya d’ago kai yana kallonta cike da mamaki. “Inada k’annen da sukafi Shettima da Amal ne?” “Yes step siblings naka ne.” “You mean yaran Ummimi?” Seta gyad’a kai pucture’n ya miyar mata “gashi banason ganinsu.” “Ayyah Habeebi basu maraye bale kace haka.” “What do you mean?” “Dukan su nan Allah yayi musu rasuwa, babansu your step-father d’an cult ne ya siyar da yaransa wa k’ungiyansu bayan nan yadawo kan Ummimi dalilin dayasa ta gudo tabarsa kenan har kaga take aiki anan ayanzu haka batada wajen kwanciya, Habeebi ka tausaya mata please…” © MIEMIEBEE

TANA TARE DA NI… PAGE 92 BY MIEMIEBEE Tunaninsa yaji ya katse kwatsam! sam yakasa yarda da abinda Flowersa ke ce masa, cikin sauti me rawa yayi maganar “Flower what did you just say?” Sake nanata abinda ta fad’i tayi. “Subhanallah! Flower are you sure?” Yayi maganar tare da karb’e picture’n yana sake kalla. “Kina nufin dukansu nan basuwa nan yanzu?” “Yes Habeebi” ta yi maganar tana gyad’a kai. “Allah sarki… They are in a better place in shaa Allah.” “Toh Habeebi Ummmi fah?” “Meh had’i na da ita? Infact ni banma yarda ba who knows ko duk k’arya take tanason in tausaya mata ne tayi coming up da plan d’innan.” ”Haba! My Lion don’t be like that, taya zakace haka wa mahaifiyarka? Inhar k’arya kake tsammanin tamana uniform na cleaners dake jikinta kad’ai sheda ce, Habeebi mahaifiyarka cefah feel sympathy towards her atleast yara uku fa ta rasa one, two, three” ta irga da hannunta. “Toh Flower laifi na ne? Nine na siyar mata da yara? Kwad’ayinta ya kaita kinga erin disadvantage da nake fad’a miki ai yanzu itace silan mutuwan yaran nan, mschw! What a pity.” “I know Habeebi bara mu iya canja komai ba abinda ya faru ya riga ya faru please ka taimaka wa Ummimi.” “In taimaka in mata meh?” “Mutafi da ita hotel da muke.” D’an dariyan rainin wayo ya saki “intafi da ita? LOL lallai kam Flower you are such a wonder ni magananta ma ya isheni kimiyar mata da photo d’in ki taho mutafi.” Haka Fannah ta riga lalashinsa tana basa hak’uri da k’yar d’in k’yar ya yarda Ummimi ta bisu amman ba’a cikin motarsa ba hakan kuwa akayi. Bayan taje ta taho da Ummimi ta tsare mata cap (taxi) kafin Ummimi tashiga taje gun Anas dan masa godiya, yana zaune cikin mota yana jiran Fannah. “Assalamu Alaikum Anas nagode da taimakon dakamin, Allah saka da alheri ya kuma maka albarka.” Tayi maganan tana tsaye ta bakin windon side na Anas. Ko kallonta beyi ba se latsa wayansa yake chan yace, “thank her not me bani na taimaka miki ba excuse me please” Shiru tayi bata kuma cewa komai ba takoma taje ta shiga cap d’in hawaye na bin k’uncinta har suka isa hotel d’in kuka bata bar kukan ba. Bayan isansu Fannah ta kalli Anas sannan cikin salon da inta mai magana yakeji tace, “My Lion nace zakayi wa Ummimi booking room koh?” Tayi maganan tana murza hannunsa a hankali. “Flower kinga ba haka mukayi dake ba cewa kikayi zata biyomu nan bakice zan mata booking room ba saboda haka figure out me zakiyi da ita” yana kaiwa nan yafito daga motar ya wuce ciki. Binsa da kallo tayi “Habeebi yau ko kafi babarka k’ok’ari seka mata booking room d’innan” ta fice daga motar ta sallami taxi driver’n. “Ummimi muje reception ki zauna achan kafin amiki booking room.” “Nagode ‘yata Allah miki albarka.” “Ameen Ummimi” anan tajata zuwa reception daidai zata juya Ummimi ta riqo hannunta “Fannah karki b’oye min Anas yace bare kama min d’aki bakoh?” “A’a Ummimi ya kike magana haka-” katseta Ummimi tayi “please karki min k’arya” zama Fannah tayi a gefenta hannunta riqe cikin na Ummimi. “Inason kisa a ranki Anas ze yafe miki saboda mahaifiyar sa ce ke kinji?” Kai Ummimi ta gyad’a mata “good kuma please kukan ya isa haka zan masa magana ina zuwa” ahaka suka rabu. ** Miqe Anas ke akan gado da newspaper a hannunsa yana karantawa yana jin k’aran bud’e k’ofa ya ajiye yasoma baccin k’arya agefensa ta zauna “My Lion nasan ba bacci kake ba.” Shiru yayi be tanka taba. “Habeebi katashi please kaji?” Ta hau jijjiqa sa badan yanaso ba ya bud’e ido. “Meh?” “Habeebi Ummimi mana kamata booking room.” “Banida kud’i.” “Youngest billonaire d’in? Habeebi please ka tashi” nan ta miqe ta hau jansa daga gadon sam takasa murmushi ya saki sannan yajata ta fad’a jikinsa. K’ara ta saki sosai sanadin cikinta data buga. “Arghhh! Habeebi ciki na.” “Sorry Mom Hanan” ya zaunar da ita kan cinyansa. Kukan k’arya ta soma tana riqe cikinta. “Flower nayi hitting naki sosai ne?” Kai ta gyad’a tana murzq idanunta. “Am sorry kinji? Muje asibiti?” “A’a nikayi booking wa Ummimi d’aki.” “Flower barinyi ba.” Rushewa takumayi da kuka, “Flower wai bara kibar kukan nan ba?” Ta gyad’a kai ba yadda beyi tayi shiru ba amman taqi daga k’arshe seda ya yarda da k’udirinta. “Okay, okay naji zan mata for Hanan’s sake.” Koma meh tace a zuciyarta tare da share hawayen k’aryan nata. Tana ganinsa ya fice ta saki murmushi. Nan da nan ya sauqa yaje yama Ummimi booking d’aki a chan last floor ta yadda bare ma na kallonta ba bale yana jin baqin ciki. Tana zaune a reception d’in Anas yazo ya wuceta batareda yace mata ko k’ala ba bayan daya gama komai ya nufo inda take tare da ajiye mata key d’in a kujerar dake gefenta “room 116” kad’ai yace da ita. Hannunsa ta riqo kafin ya kub’uce mata. “Anas nagode Allah saka maka da alkhairi.” Hannunsa ya fisge ba tare da yace da ita komai ba. “Anas dan Allah kayi hak’uri kamin magana barin iya jure fushinka ba please talk to me your mother” ba tare da yace da ita komai ba ya haye sama d’akinsu da Fannah. *** Haka nan tun daga ranan Ummimi tasoma zama dasu Fannah ko kad’an Anas baya shiga harkarta magana ma ba mata yake ba, koda ta mai magana baya amsata ba yadda Fannah batayi dashi ba amman yak’i yafewa Ummimi, a dalilin haka tasoma tashi Sallan dare tana roqan Allah. Cikin d’an k’ank’anin lokaci Fannah suka shaqu da Ummimi dan yadda Fannah kebata kulawa tamkar uwarta abinci kullum ita ke kai mata dan kuwa tsoron placing order ma take, haka Fannah tasa Anas agaba seda ya siya wa Ummimi kayan sawa da sauran abubuwan da zata buk’ata. Dukda shariyan da Anas ke mata hakan be hanata yimasa magana anytime she gets the chance to ba fatanta Allah sa Anas ya bata daman da take nema. Sunyi zaman two weeks tare Anas ya fara zancen komawa gida, Nigeria badan komai ba dan ya rabu da Ummimi. 4:30PM Yana cikin harhad’a musu kayaki kasancewar gobe zasu tafi Fannah ta shigo d’akin bayan fitowarta daga d’akin Ummimi, akan gado ta zauna “sannu da aiki Habeebi.” “Yauwa Flower.” “Uhm nace in zamu koma Ummimi zata bimu ba?” Barin abinda yake yayi “waze bi wa?!” Yayi maganar cike da rashin yarda. “Ummimi zata bi FAHNAS nace.” “Humm!” yaja numfashi “sede in wani FAHNAS d’in kam ba wanda nasani ba.” “Toh My Lion ita kad’ai zamu bari anan ne?” “Dama dawa muka sameta? Ita kad’an ta muka sameta haka kuma zamu barta” “Haba! My Lion katuna fa batada family yanzu we are her only family.” “Flower I’m not her family kuma ba inda zanje da ita ta sake messing min family like she did before.” “But Hab-” “Period!” Ya katse ta. Bata sake ce masa komai ba gudun kar suyi fad’a. Chan bayan sallan isha bayan sun k’are chin abinci ta matso ta zauna kusa dashi akan gado tare da riqo hannunsa cikin nata. “Habeebi please badan niba dan Allah kar kabar Ummimi anan baka tunanin in rananda step father’nka ya ganta ze siyar da ita kamar yadda ya siyar da su Barrah? Baka tunanin barinta anan had’ari ne Habeebi? I’m not asking you to forgive her all am asking is mutafi da ita kar mu barta anan please Habeebi don’t say no please.” Shiru yayi harga Allah bai tunanin ze iya ce ma Flowersa no this time akan abinda yasan ba gagaransa zeyi ba sede yanzu in yabar Ummimi tabisu dole gida ze kaita abinda bayyaso kenan yafison kamar yadda suka saba ba ita su cigaba da kasancewa ahakan shi bama wannan ba mezece wa Amal da batasan tanada wata mahaifiya ba bayan Ummie? Abinda ke damunsa kenan. “Habeebi please kayi hak’uri mutafi da ita kaji?” Kai zallah ya gyad’a mata yana me nazarin aina ze kai Ummimi bayan isansu Nigeria. “Thank you so much My Lion” tayi pecking nasa tare da miqewa. “Ina kuma zakije Flower?” “Zanje ince ma Ummimi ta shirya kayanta zamu tafi gobe.” “Flower shine baraki iya kiranta a waya ba? Ni banason kina unnecessary zirga-zirga kinde sani bakida lafiya kuma munada tafiya gobe.” “Don’t worry Habeebi I won’t take long” tayi mai blowing kiss, murmushi ya mata sannan ta fice. Zaune ta tarar da Ummimi kan gado as always ta had’a tagumi bayan tayi sallama ta shigo tazauna a gefenta. “Ummimi ki shirya kayanki zamu tafi gobe.” Cike da rashin fahimta ta d’ago kai tana kallonta “ina zamuje Fannah?” “Nigeria! Zakije kiga su Amal!” ta sanar da ita cike da jin dad’i. “Nigeria?! Kina nufin Anas ya yarda zan biku? “Ai na fad’a miki Anas na sonki he is just taking time to adjust nan bada jimawa zakuyi sorting out komai.” “Allah sa Fannah nagode kuma sosai Allah biyaki.” “Ameen Ummimi ba komai tashi mu shirya miki kayan naki.” “A’a please karki damu kayan nawa dududu nawa ne? Keda bakida lafiya ma kije ki huta dan Allah kar gajiyan ya miki yawa.” “Tunda haka kikace fine kiyi ki shirya ki huta kema Allah kaimu gobe.” “Ameen nagode kima Anas godiya please nasan koda mutuwa zanyi ina mai magana ba amsani zeyi ba.” “Bakomai Ummimi zan masa in shaa Allah seda safe” ta rufo mata k’ofar. ** Bayan Anas ya kashe musu wuta suna kwance kamar yadda suka saba Fannah ta kira sunansa, “Habeebi.” “Yes Flower.” “Thank you so much for everything.” Ta fad’a tare da sake shigewa jikinsa. “You don’t have to thank me Flower, ma godiyan me kike?” “Aika fini sani d’azu Mami takirani tace in maka godiya mekayi musu, nayi nayi da ita ta fad’amin tak’i.” “Haha!” yayi dariya kad’an “hakane?” “Eh mekayi musu?” “Babu.” “Kamar ya babu Habeebi duk alkhairun da kake musu da a baya Mami bata tab’a cemin na maka godiya kamar na yau ba meh ka musu please?” “Nace miki babu lets sleep tomorrow is a big day.” “O’o ni seka fad’amin wani alkhairi kamusu.” “Nace miki babu please kiyi bacci ko Hanan ma zata samu tayi, goodnight” yayi pecking kanta. Shiru tayi chan ta kira sunansa “Habeebi.” “Yes Flower lets sleep.” “Thank you kaji? Allah k’ara bud’i.” Magana yake cike da gyangyad’i “Flower nace miki banason godiyan nan.” “Bakasan akan mefa nake maka godiyan ba.” Ya nisanta “akan meh?” “Ummimi ce tace na maka godiya.” Shiru yayi bece komai ba. “Kaji My Lion?” Nan ma shiru data d’ago kai ta kallesa setaga idanunsa a rufe she is sure ba bacci yake ba, bayason maganan Ummimi ne. “Liar nasan ba bacci kake ba kadeji Ummimi tace ta gode” nanma bece komai ba murmushi ta saki tare da jan hancinsa. “Awwch!” Ya sakar da k’ara “kinsan da zafi koh?” “Aww! kana jina kamin shiru kenan.” “Sa’an ki d’aya Baby Hanan if not da na rama.” Gwalo ta saki masa sannan yajata jikinsa suka kwanta*** washegari… As early as possible suka shirya luggages nasu duk na acikin mota Anas yabari asa akwatin Ummimi a motansu yak’i taxi aka tsare mata ta shiga ciki, kusan a tare suka isa airport akayi musu ciki da akwatinansu. A sama su Fannah suke a yayinda Ummimi ke k’asa ita kad’ai ba yadda Fannah batai da Anas yabar Ummimi ta samesu ba yak’i. 2 hours later… Miqe Anas yake kan wani medium sized bed se baccinsa yake sha ayayinda Fannah ke zaune a d’ayan side d’in da Qur’ani a hannunta se karatu take tayi daidai takai inda k’arfinta ya k’are ta tsaya tare da miqewa ta sauk’a k’asa gun Ummimi as always ta sameta ta ta had’a tagumi bayan ta zauna a gefenta ta dafe kafad’arta se anan Ummimi tasan da shigowarta. “Fannah” takira sunanta a bit suprised. “Na’am Ummimi kin zauna shiru ko TV ne ki kunna mana.” “A’a barshi karki damu, ya Anas yake?” “Yana bacci kema ya kamata ki kwanta.” “A’a nikam, se hankali a kwance ake iya bacci ai.” D’an murmushi Fannah ta sakar mata “toh ga Qur’ani ki karanta” ta miqa mata. “Nagode kema kije ki huta wannan hawa da sauqan ze dameki kinga already k’afafuki sun kumbura.” “Toh Ummimi.” “Nace yaushe ne jikan nawan ze fito?” D’an dariya ta saki dan kunya ma takasa fad’a mata. “Surikar tawa tana jin kunya na ne?” Ummimi tayi teasing nata. “Nanda wata uku in shaa Allah.” “Ahh ashe ma kin kusa toh Allah raba lafiya ‘yata Allah ya sauk’eki lafiya.” “Ameen Ummimi nagode barinje in huta nima.” “Yawwa ‘yata” ahaka suka rabu beside Anas taje ta kwanta alokacin har ya tashi. “Flower ina kikaje?” “Gun Ummimi.” “Baraki koyi zama gu d’aya ba ko kinga k’afafunki kuwa? Wai bakiya jin tausayin kanki ne?” “Habeebi please ya isa ai dama kumburin dole ne kaide kace kanason min surutu ne saboda gun Ummimi naje inda toilet nace na shiga ai barakayi magana ba.” “Ohkayyyy haka kika ce? Toh har mu isa banason kisake sauk’a wajenta am not asking you am ordering you as your husband.” “Sekayi ai” tayi maganar k’asa k’asa. “Kuma najiki nide na fad’a miki.” Baya ta juya masa ba tare da tace komai ba haka tundaga nan bata sake masa magana ba kodaya tasheta Sallan Azahar haka La’asr ma shima be mata magana ba. 10 hours ya d’aukesu sannan suka iso Nigeria inda suka sauk’a a Sandralia Hotel Abuja har anan Fannah bata sake ma Anas magana ba, ruwa ta watsa taso shiga duban Ummimi amman Anas ya hanata. Bayan ta shirya cikin kayan baccinta ta zauna kan gado tana ma kanta tausa a k’afafunta, fitowan Anas daga wanka kenan singlet da nickers yasa ya hauro gadon yana k’are mata kallo. “Flower.” Shiru tayi bata tanka sa ba. Kusa da ita ya matso “Flower bara kimin magana ba?” Nanma shiru se massaging kumburarrun k’afafunta take hannunta ya d’aga daga kan k’afan nata nanma bata ce masa ko k’ala ba. “Flower wai barakimin magana?” Nanma shiru. “Okay I’m sorry kinji? I’m sorry.” “Kasakemin hannu as you can see am massaging my legs.” “Flower I said I’m sorry.” “Naji sakeni toh.” “Bari zan miki.” “Banaso zanyi abuna da kaina.” “I’m sorry” ya sake hannun nata tare da kama kunnuwansa ko kallonsa batayi ba ta cigaba da massaging k’afanta. “Flower please.” “Wai hak’urin me kake bani? Nace kamin laifi ne?” “Baki fad’a ba amman nasan na miki laifi and I’m sorry kije kisameta in kinaso.” “Banaso” ta fad’a stubbornly. “Yi hak’uri mana Mom Hanan” ya sake matsowa kusa da ita closing the gab between them, gashin kanta data barbaza a kafad’anta yahau shafawa. “Yi hak’uri kinji barin sake ba.” Kallonta ta miyar garesa “I’m sorry sweetheart” d’an murmushi ta sakar masa ma’anan ta huce. “Thats my woman!” Lips nata yasoma laluba bata hanasa ba se dab da bakinsu ya kusa had’iye tasa hannu ta kama mai baki “no kisses today thats your punishment” tayi maganar tare da miqewa daga kan gadon ta sanya hijabinta. “Oh common please Flower ko peck ne.” “Nace NO! Gobe zaka sake repeating abinda kayi yau.” Tana kaiwa nan ta fice zuwa d’akin Ummimi. Some minutes later ta dawo har anan Anas beyi bacci ba yana jiranta, a nitse ta cire hijabin ta haye gado ta kwanta ganin bata matso kusa dashi ba yasa ya matso dakansa tare da zama. K’afanta ya miqar kan cinyansa sannan ya fara mata massaging. “Ta nan ka b’ullo kenan? Saboda in ka gama in baka kiss as token of appreciation, uh-uh yau ba kiss na fad’a maka smart guy, wannan logic nakan bareyi aiki ba yau.” Dariya yaso yi dankuwa ta kamasa amman seya matse. “Ni ba haka nace miki ba am massaging your legs because I love to” “Humm! Allah sa de, nagode” bayan daya gama yaja d’ayan ma yamata godiya ta masa sannan ya kashe musu wutan ya koma ya kwanta agefenta yana wasa da gashin kanta duk wani salo nashi yayi applying amman Fannah tak’i bari yayi kissing nata haka yatayi har ya gaji seda tajishi yayi shiru sannan ta juyo tana kallon shi unexpectedly tayi pecking nasa a lips. Kafin ta d’ago kanta ya riqeta gagam yasoma sarrafata haka sukata romancing junansu har seda bacci b’arawo yayi gaba dasu. © MIEMIEBEE

 washegari… Da safe Anas ya tashi yayi wanka sannan ya had’a wa Fannah ruwan ta itama tayi, dakansa ya shafa mata mai ya cire mata d’aya daga cikin had’ad’d’un maternity gowns nata tasa sannan suka karya. “Habeebi ya naga kana zipping mana akwati?” “Yes Baby zamu wuce Maiduguri yau ina zaki iya ko mu bari se gobe?” “No its okay with me toh baka sanar dani ba bale in fad’awa Ummimi, barinje in ce mata ta shirya.” Hannunta ya riqo da wuri “no Mom Hanan baramu tafi Maiduguri da Ummimi ba anan Abuja zan barta zan mata renting gida tayi zamata anan we don’t need her again.” “Haba My Lion wani erin magana kake haka? Ita da wa zaka barta anan?” “Ita kad’anta kamar yadda muka sameta ita kad’ai a NY ai dama cemin kikayi zamu dawo da ita 9ja bawai zata bimu gida ba.” “Oh Habeebi wallahi banajin dad’in abinda kakeyi ko kad’an banaso haba mana Ummimi fa mahaifiyarka ce ko kak’i ko kaso itace mother’nka baka iya canzawa.” “I know ba abinda zan iya thats why I need her out of my life.” “Wai meke damunka ne Baby? Nifa ba haka nasanka ba Ummimi is following us home.” “Sede in ke zaki biya mata kud’in jirgi which I’m not allowing you.’ “Fine karka bari zan kira Abuu in sanar dashi I’m sure shi ze biya mata.” “No Flower you are not doing that I forbid you to call him wai mesa kikeson muna fad’a ne? I’m your husband amman ko kad’an bakiya jin magana na, Ummimi is not following us and that stays that period!” Ya fad’a a tsawace tare da matsawa yakoma kan kujera ya zauna. Kuka ta tsaya tanayi a wajen chan takoma kan gado ta zauna se kuka take wanda ke mugun tayar wa Anas da hankali gani yayi kamar ze iya jure sautin kukan nata amman ina he can’t. “Flower wai baraki bar kukan ba?” K’ara k’arfin kukan nata tayi cike da tashin hankali ya matso kusa da ita yana aza hannunsa ajikinta taja da baya. “Flower kibar kukan mana wai ke bakisan its bad for your condition bane?” “Kai da kasani kuma kake sani kukan fah? Ni ka tashi min akai” ta juya masa baya. Gadon ya haye yadawo ta inda take fuskanta. “Ya isa toh I’m sorry Flower ke kike sani miki masifa nace miki banason zancen Ummimi amman bakiya ji sekita min maganarta. Kiyi hak’uri kinji? Kidena min magananta se baramuna samun midunderstanding ba.” Baki ta murgud’a mai “ni katashi min kuma barin iya tafiyan ba yau mara na naciwo.” “Toh naji sannu, se gobe zamu tafin kenan.” Ta gyad’a mai kai “kuma ni barin tafi ba seda Ummimi.” “Kingani koh?” “Toh Habeebi wani erin magana kake please?” Ta tashi ta zauna “taya zamu taho da ita 9ja kuma semu barta anan ita kad’ai ai gwara ma ace tun farko mun barta achan NY, ni gaskia in bada Ummimi ba barin bika ba.” “Se mu gani ai” daidai ze juya kenan tariqo hannunsa “Habeebi please dan Allah kayi hak’uri mu koma da Ummimi please Habeebi kamin wannan ka gama min komai Habeebi please don’t say no please please sweetheart, the father to my children please say yes kaji Baby? Say yes please.” Shiru yayi bece komai ba dawowa tayi ta zauna kan cinyansa “please Habeebi say yes kaji my Baby?” Nanma shiru “Sweetheart please…” “Toh inta bimun aina zamu ajiyeta?” “A gidan mu zata sauk’a for the meantime.” “A gidanmu? No barin kaita gidana ba never.” “Toh naji ba’a gidanmu ba, a gidanku nasan Abuu ze bata d’aki inbe bata ba ko gun Mami zan kaita please say yes Habeebi.” “Naji” amsar daya bata kenan. Hannayenta ta zagaye a wuyansa tare da pressing masa hot kiss “I love you Habeebi, I love you so much” tayi pecking nasa a kumatun damansa sannan a na hagu se tip na hancinsa “mufita sight seeing (ganin gari) yau kasan bansan cikin Abuja ba.” “As you wish Mom Hanan” yayi pecking lips nata “sa hijabinki muje.” “Yauwa Abu Hanan zamuje da Ummimi?” “Bansani ba in zaki tashi muje toh fine inkuma a’a muyi zaman mu.” “Dama wasa nake nasan ba yarda zakayi ba” daidai zata mik’e kenan Hanan tayi kicking. “Habeebi Habeebi! Hanan moved tayi motsi!” tasa hannunta daidai inda tajiyo motsin, shima hannun nasa yasa wajen kad’an kad’an sukejin motsinta nan da nan suka fita basu suka dawo ba se kusan Maghrib Sallah sukayi Fannah ta wuce d’akin Ummimi inda ta sanar da ita zasu wuce Maiduguri gobe. Hira kad’an suka tab’a Fannah tamata seda safe ta dawo d’akinsu anan suka kwanta da wuri kasancewar zasu hau hanya gobe. ** K’arfe 10:30AM su Fannah suka isa Maiduguri already driver na jiransu a airport, anan ma sam Anas yak’i barin Ummimi shiga motansa haka ta shiga taxi gidansu suka fara wucewa inda shida Fannah suka shiga suka watsa ruwa aka bar Ummimi cikin taxi tana jira, Fannah tayi tayi da Anas yabar Ummimi ta shigo ta watsa ruwa itama amman yak’i ba yadda ta iya haka ta hak’ura bayan sun sake shiri suka fito suka wuce gidansu Anas. Daidai gaban gate Anas ya tsaya bayan me gadi ya bud’e gate ya shiga, itako Ummimi a waje driver ya ajiyeta da kud’in da Fannah ta bata ta biya sa. Fitowar Fannah daga mota ta kama hanyan waje dan shigo da Ummimi ta soma tafiya kenan Anas ya tsayar da ita. “Flower where to?” “Zan shigo da Ummimi ne kafara shiga we will follow afterwards.” “Mschw! Wai ita batasan hanyan ciki bane da sekin shigo da ita? Ni kidena wahalar min da Hanan akan Ummimi.” “I’m sorry Babe yanzu zan shigo da ita ko zaka jira ni neh mu shiga tare?” “Mschw! You are trying me koh?” D’an murmushi ta sakar masa sannan ta fice a waje ta samu Ummimi. “Bismillah mushiga daga ciki Ummimi.” “ ‘Yata nace gidan da muka baro d’azu shine naku dana Anas?” “Eh Ummimi.” “Masha Allah gidan naku yayi kyau sosai kamar a ture wallahi.” “Kai Ummimi mungode Anas ne yayi desinging gidan da kansa kinsan architecture ne ayanzu haka shine CEO na Flames Enterprises one of the biggest Emterprise a Nigeria in whole, he is being referred to as Nigerias youngest billonaire, Ummimi ki godewa Allah Anas naki is very bright.” Hawayen jin dad’i ne suka soma gangaro wa Ummimi “Alhamdulillah! Oh! Allah sarki Anas Allah ya cigaba da mai bud’i ya kare shi daga sharrin maqiya, ameen.” “Ameen Ummimi mu shiga.” “A’a Fannah tukuna, ina ne nan?” “Nan gidansu Anas ne mushiga Abuu na ciki.” “Kina nufin wannan babban gidan na Abuun su Anas ne?” “Eh Ummimi” “Allah mai iko, me azirtawa dakuma talautarwa, Allah sarki ban kyauta wa kaina ba wallahi ko kad’an, da ace na k’ara hak’uri na cigaba da zama da Ya Ibraheem da atare zamuyi wannan arziki, Allah cigaba da masa bud’i yakuma rabamu da sharrin shaid’an gabad’aya.” “Ameen Ummimi mushiga.” “Fannah banida courage na shiga, ina tsoro nasan cikinsu ba wanda zeyi accepting d’ina sabida abinda na musu da ciwo zasu ce ban tashi dawowa ba sedana ga Ya Ibraheem yayi arziki, please ki kaini wani gun daban kokuma in zan iya tuna hanya in je gidanmu that is in iyayena suna raye.” “Ummimi just trust me kinji? Mushiga ciki please na tabbata idan duk sukaji labarin ki zasu yafe miki musamman ma Shettima I know him shi ze fara accepting naki” Hannu tasa ta share hawayen nata sannan tabi bayan Fannah hannunta riqe cikin na Fannah. Amal na bud’e k’ofa taga Anas ne tsaye jikinsa ta d’ale tana mai oyoyo! “Ya Anas I missed you so much, shine zaku dawo baku sanar dani ba tun shekaran jiya nake trying numban ka dana Ya Fannah basu shiga.” “Sorry Angel we wanted suprising you su Abuu suna ciki?” “Yes kowa na gida ina Ya Fannah da Hanan d’ina?” “Gata chan!” yayi mata nuni da yatsa. Tafe Fannah ke da Ummimi behind her. “Ya Anas ita da wa wancan?” “Nima bansan taba kinsan me nakeso dake Angel?” “A’a” ta girgiza mai kai. “Karki kuskura kimata magana kinji? Koda ta miki karki mata magana she is a bad person.” “Really Ya Anas? Mesa toh?” “Trust me kinji Angel? Karki kuskura kimata magana” Yayi pecking nata a goshi. Alokacin da su Ummimi suka gama k’arisowa Amal ta ruga tayi hugging Fannah har agarin haka ta bige mata ciki. “Amal kinason kijiwa Hanan naki ciwo ne?” “A’a Ya Fannah barin k’ara ba its just that I missed you wallahi gashi munyi hutu ba gun zuwa Ya Shettima kullum na cikin bullying d’ina.” duk maganganun nan datake bata kalli Ummimin da tayi mutuwan tsaye tana kallonta ba ko kyaftawan ido ba. “Aiko ga Ya Anas naki ya dawo seki kai masa k’orafi.” “Haha! Ai kibari Ya Anas yace ze rama min ko Ya Anas?” Tayi maganar tana k’ok’arin maida kallonta kan Anas a garin haka idanunta suka sauk’a kan Ummimi da idanunta suka ciko dam da hawaye ganin ‘yar data bari a cikin tsumma ne ta girma haka tazama babbar budurwa kuma kyakkyawa. Kallon cikin ido suka tsaya sunayi wa juna na kusan minti biyu, wani erin yanayin da Amal bata tab’a tsintan kanta ciki ba tasoma yau. Aina na santa? tambayar data ke tayi wa kanta kenan. “Amal” cewar Ummimi tana mata murmushin daya zame mata dole. Ta bud’e baki zata mata magana kenan seta tuna abinda Anas yace mata sekuma tayi shiru. “Amal barakiyi mata magana bane? Bakiji ta kira sunan kiba?” Cewar Fannah. “Baruwanki, bata santa ba taya zata mata magana zo Angel d’ina na siya miki iphone 7s ma taho kinji?” “Dagaske Ya Anas yeyy!” Taje tayi hugging nasa. “Ina yake Ya Anas?” “Nachan gida tare zamu koma yau zaki kwana mana ba?” “Yeyyy!!! Mushiga ciki toh” dake hankalin ta har a yanzu na yara ne anan ta mance da chapter’n Ummimi taja hannun Anas suka shige ciki. “Ummimi please karkiyi kuka dan Allah, nasan da akwai k’wararren dalilin dayasa Amal tak’i miki magana Anas ne ya hanata kuma jin maganansa take har fiye da yadda takejin na Abuu, duk abinda yace mata yi take but karki damu with time zaku saba she is fun to be with mushiga daga ciki.” Da k’yar tayi convincing Ummimi data kariya da reaction na Amal tabita suka shige ciki bakowa a parlourn illa Anas dake a dining space yana shan ruwa bayan ta zaunar da Ummimi kan kujera ta nufa inda Anas yake. K’asa k’asa take maganar ta yadda Ummimi barata jisu ba. “Habeebi yanzu abinda kayi ka kyauta kenan?” “Menayi kuma yanzu?” ya bud’e goran ruwan ze kai baki tasa hannu ta k’wace. “Ma tambaya na kake ko? Mena hana Amal yima mahaifiyarta magana?” “Haka Amal tace miki ni na hanata? Ma in ni na hanatan toh ina ruwanki? Tsakaninsu su biyu bata santa ba taya zata mata magana bani ruwana insha.” “Barin bayar ba.” “Ki riqe akwai wani cikin fridge d’in ai” daidai zebud’e kenan tasa hannu ta taresa. Murmushi ya saki “I will excuse you Flower saboda dama mata masu ciki sunada taurin kai.” pecking nata yayi a goshi wanda tuni ta tunkud’esa, killer smile nasa ya kashe mata “Shettima! Shettima!” Yau hau k’wala masa kira. Daidai nan Ummie da Abuu suke fitowa har Amal taje ta sanar dasu dawowan su Anas dawata mata me kama da ita da Anas harma da Shettima kad’an kad’an. “Oyoyo! Mutanen New York ne a gidan namu, maraba lale!” cewar Ummie alokacin data ga Fannah, hugging nata tayi ahankali gudun karta jimata ciwo anan sukayi exchanging greetings. Ummimi dake a parlour ba abinda take se kallonsu hawaye na bin k’uncinta. “Me kuke tsaye anan?” Abuu ya tambayesu. “Uhm ruwa nazo d’aukawa Anas” Fannah tamai qarya “gashi Anas” murmushi ya saki sannan ya karb’a. “Toh mu k’arasa parl-” be samu daman k’arisa maganan ba kasancewan ido hud’u da sukayi da Ummimi kwata kwata ya kasa amincewa da abinda idanunsa ke gane masa cewa ma yayi ko imagination nasa ne kawai, Ummie ma was at shock alokacin data ga Ummimi she couldn’t believe it either. Cike da rashin yarda Abuu ya juyo yana kallon Anas fuskarsa d’auke da son k’arin bayani har b’ari bakinsa ke. “A.. An.. Annas wac..wacce wancan?” yana nuna Ummimi da yatsa, shida Ummie suka kasa kunne suna jiran amsar sa. Daidai nan Amal ta falfalo da gudu, Shettima na biye da ita yana huci sanadin d’aukar masa cookies dayayi niyyan kaiwa Afrah da tayi. “Ai wallahi yau se jikinki yayi tsami, sa’an kine ni da zan ajiye abu ki d’auka har kichi?!”” Yayi maganar se binta yake a yayinda take ta gudu tana kiran sunan Anas “Ya Anas! Ya Anas! Shettima ze min duka.” Suna isowa dining area’n duka suka sa full stop tuni Amal tayi bayan Anas. Ganin Abuu Shettima ya dakata kaman ance ka juya ya juya idanunsa se akan crying Ummimi. Idanunsa ya zaro sosai kamar ze ciresu sam shima ya kasa yarda da abinda idanun nasa ke gane masa. “Abuu wace wancan?” Abinda ya iya tambaya kenan. “Ya Anas meke faruwa haka? Ya naga su Abuu sunyi shiru.” Amal ta tambaya. “Anas magana nake maka wacece wancan?” cewar Abuu. “Abuu Nima bansanta ba Flower keda kika kawo ta seki musu bayani” anan duk suka maido da kallonsu kan Fannah suna jiran amsarta seda ta kalli Ummimi sannan ta kallesu bakinta ya bud’u “Abuu wancan Ummimi ce, Ummimin ku.” © MIEMIEBEE
TANA TARE DA NI… TANA TARE DA NI… PAGE 94 BY MIEMIEBEE “Um… Waye?!”Abuu yayi maganar cike da k’in yardan abinda Fannah tace. “Eh Abuu Ummimi ce” ta sake tabbatar masa, juyawa yayi ya miyar da kallonsa a gareta “Aysha?” Yayi questioning nata hawaye ne ke ambaliya kan fuskarta “nn..na’am Ya Ibraheem” “Ummimi?” Cewar Shettima disebelievingly. “Na’am Shettima.” “Noo this can’t be wannan ba Aysha bace ko Nafeesa?” Abuu yayi maganar har yanzu be yarda ba. “Ya Ibraheem ka kwantar da hankalinka please ba shakka zahiri wannan Aysha ce.” “Meta kemin a gida? kice mata ta tashi tabar min gida tun kafin nakira mata securities banida wani alaqa da ita” yana kaiwa nan yayi ciki. “Ya Ibraheem ka tsaya please” Ummie tabi bayansa. Wani erin matsanancin kuka Ummimi ketayi abin tausayi ayayinda su Shettima suke kallonta kamar TV har a yanzu yakasa motsawa dan yadda mamaki ya ziyarce sa gabad’aya ashe dama ze sake sa mahaifiyarsa a ido? “Ya Anas wace ita? Dagaske kake she is a bad person shiyasa Abuu yace tafita mana daga gida?” “Yes Angel mushiga ciki in ta tafi se mu fito” Fannah ce ta dakatar dasu. “Anas baka gani is about time Amal tasan gaskia itama?” “Flower don’t you ever tell her a thing about it, am not asking you am ordering you banason kifad’a mata wani abu I hope am clear” yana kaiwa nan suka fice. “Shettima” Fannah ta kira sunansa a nitse. “Shettima nasanka kai kam I know baraka yi shunning Ummimi ba dan Allah ka mata magana kama mahaifiyarka magana” kai kawai ya girgiza sannan shima ya koma d’akinsa. Wajenta Fannah ta nufa tana bubbuga bayanta tana bata hak’uri tana me tabbatar mata da cewa evrything will be okay. ** A d’akin Abuu. Zaune yake a bakin gado ya had’a uwa uba tagumi yayi shiru ko kad’an yakasa comprehending abinda ke faruwa gani yake wane a mafarki wai Aysha ce ta dawo matar da har a ayau yakasa son wata mace bayan ita, matar da har a yau yakasa maye gurbin ta da wata, Aysha his first and last love, toh me tazo yi? Ina mijinta dakuma ‘ya‘yanta? shekara goma shabiyar dole ace ta haihu. “Ya Ibraheem bekamata ba kace ta fita maka daga gida nasan yadda abin yake da ciwo da zafi amman hak’uri yazama dole, dole kayi hak’uri kaje kaji dame ta taho meya kawota? Dakuma me takeso” “No Nafeesa kije ki sameta kice mata ta fita min daga gida, banason sake ganin fuskarta.” “A’a Ya Ibraheem nasan you don’t mean what you said, Aysha cefah matarka daka fiso fiye da komai, cool down kaje ka sameta muji dame take tafe please.” Tana kaiwa nan ta fice zuwa d’akin Shettima inda ta samesa miqe kan gado yayi jugum se hawaye yake zubarwa. “Ahhhh namiji dakai kake wannan hawaye Shettima gaskia ka badani yanzu in Afrah taganka haka me makeso tace? Saurayinta rago ne saboda yaga mahaifiyarsa yake wannan kuka?” Tashi yayi a lokaci d’aya yayi hugging Ummie gagam yana fad’in “kece mahaifiyata Ummie, ke kika raineni ke nasani ba itaba, she gave birth to me but you played the role as my mother, ta tafi ta barmu alokacin da muke tsantsan buqatar ta kece mahaifiyata ba itaba Ummie.” Bayansa ta hau bubbugawa a hankali “shhh! is okay Shettima inhar kamar yadda kace nice mahaifiyarka inaso kamin wannan abu guda d’aya yau kaje ka zauna a parlour ka jirani, kamata yayi kabawa Ummimi chance ko explaining kanta ne tayi muji menene amfanin dawowanta kaji son?” “Noo Ummie I don’t want to banason sake ganinta, Ummimi bata sonmu bata tab’a sonmu ba ta tafi kawai.” Breaking hug d’in tayi ta riqo fuskarsa “banason suratan banza kaji ko? Man up! Haba na Afrah ba haka fa na sanka ba tashi kaje parlour kajirani kaji? Don’t say no tashi! Tashi! ina ganinka” ba gardama ya share hawayensa sannan yafice izuwa parlon inda ya tarar da Ummimi se kuka take da Fannah a agefenta ba tare da yace dasu komai ba yanemi waje ya zauna. ** “Anas ka bud’en k’ofan nan kaji koh?” Ummie tayi maganar tana buga k’ofan d’akin Anas dayasa lock ya rufesu da Amal ciki. “Amal tashi ki bud’e.” Ido yamata nufin karta tashi aiko ta maqe tayi shiru. “Anas wai baraka bud’e ba? Sa’arka ceni nace ka bud’e!” “Toh Ummie ki fad’i me kikeso inhar maganan Ummimi zaki mana save it bamuwa so.” “Anas abinda kake be dace ba ka bud’en please.” Badan yana so ba ya tashi ya bud’e tashigo. A kan gado a gefen Amal dake kusa da Anas ta zauna tare da riqo hannayen Amal cikin nata tana mirzawa a hankali. “Amal d’ita.” “Na’am Ummie.” Kafin Ummie ta sake magana Anas ya dakatar da ita “Ummie please don’t tell her karki fad’a mata komai banason wannan yazamo silan lalacewar rayuwar Amal I can’t afford it.” “Ya Anas meke faruwa ne please ku sanar dani, meneh Ummie?” “Amal sweetie kinga matan data shigon nan ko wacce Abuu yakira da Aysha?” “Eh naganta.” “Ummie please don’t” Anas yayi pleading. “Bakiga kuna kama da ita ba? Dukanku da Ya Anas naki harma da Shettima?” “Nagani Ummie wacece ita?” “Ummiminku ce.” “Ummimin mu? Meaning?” Juyo da ita Anas yayi “listen to me carefully kinji Angel?” Kai ta gyad’a. “Good kinga Ummie nan ko?” Nan ma ta gyad’a kai “who is she to you?” “My mother mana Ya Anas, she is all our mother, Ummie mamanmu ne dukan mu koba hakaba Ummie?” Shiru Ummie tayi takasa amsa Amal tsantsan tausayi yau shekarun ta goma shabiyar amman ace batasan wace asalin mahaifiyarta ba, batasan ta ina zata fara mata bayani ba. Kanta ya karkato zuwa direction nasa. “I’m sorry Amal.” abinda ta iya cewa kenan. “Ummie ba mahaifiyarmu bace Angel, ba ita ta haifemu ba she just played the role as our mother amman ba ita bace asalin mahaifiyar mu Ummie is our foster mother Ummimi wanda Abuu yakira da Aysha a while ago itace mahaifiyarmu ita ta haifemu kingane?” Hawaye tasoma zubarwa alokaci d’aya sam k’wak’walwarta yakasa comprehending abinda ke faruwa kamar ya Ummie ba mahaifiyar ta bace. “Ya Anas bangane ba, bangane me kake nufi ba? Taya zakace Ummie ba mahaifiyata bace, ba mahaifiyarmu bace duka? Taya zakace wancan matan datazo wanda ban tab’a ganinta ba se yau itace mahaifiyata? Why Ya Anas?” Hannu yasa ya share mata hawayen. “Angel banason ganinki kina kuka.” “Then tell me you are not telling the truth” cike da tashin hankali ta juyo tayi hugging Ummie. “Ummie you are my real mother right? Kece mahaifiyata bawata daban ba Ummie you are my mother please say yes, Ya Anas be gane bane you are my mother and no one else” itama Ummien kuka take sosai na sosai da k’yar ta d’aga Amal daga jikinta tasa hannu ta share mata hawayen. “Amal I’m so sorry kinji? Ban tab’a sanar dake gaskiya ba, na tauye miki hak’k’inki na sanin asalin mahaifiyarki amman kisani nayi hakan ne for your sake, wanki Anas ne yahana a fad’a miki gaskia sabida yadda yakeson ki bayanson abinda ze lalata miki rayuwa, bani bace mahaifiyarki Amal Ummimi ce ta haifeki itace mamanki na asali.” “Noo Ummie ni kece mahaifiyata and no one else kece ba ita ba she is a bad person banasonta ban santaba.” Ta rushe da kuka, hugging nata Anas yayi yana bubbuga bayanta har seda tayi shiru. “Ya Anas inhar ba Ummie ce mahaifiyata ba then wacece ita? Mesa take zama damu kullum?” “Ummie sister’n Abuu ne bakiji Abuu na kiranta Nafeesa ba? Asalin sunanta kenan but ana cemata Ummie shiyasa time da ta dawo zama damu tun kafin a haifeki muke kiranta Ummie, dalilin daya sa ta dawo zama damu kuwa shine sanadin barin mu da Ummimi tayi” “Toh in haka ne mesa ban tab’a sanin Ummimi ce mahaifiyata ba? Inhar dagaske kai da Ummie kuke wancan matar itace mamanmu mesa bata zaune damu?” “Kinason kisan dalilin Angel?” Ta gyad’a mai kai. “Saboda batada imani Angel, bata da tausayi bata sonmu.” “Anas don’t talk about your mother like that” Ummie ta katsesa “uwa uwa ce komin rashin dad’inta.” “No Ummie kibari in sanar da ita dukkannin abinda Ummimi tayi mana sabida kar ta tausaya mata.” “Anas I said no.” “I’m sorry Ummie amman ya kamata Amal tasan abinda mahaifiyarta ta mata” nan ya cigaba “Amal Ummimi bata tab’a sonmu ba zaki iya tuna ciwon dake a hannu na wanda nace miki agarin ball aka jimin?” Nanma ta gyad’a kai. “Its a lie kinga matar dake parlourn, Ummimi ita tajimin ciwon, she left us for another man 15 years ago…” nan ya kwashe labarin komai yabata ba tare da yabar komi a baya ba. Kuka sosai Amal take Ummie takwantar da ita a jikinta. “Ummie mena mata? Mesa ta tsaneni? Mesa bata bari naji d’uminta ba?” “Shhh! is okay sweetheart ya isa kinji? Bar kukan haka, duk abinda ta miki she is still your mother-” katseta Amal tayi tare da d’agowa daga jikinta “No Ummie you are wrong Ummimi ba mahaifiyata bace, ita ta haifeni amman ke nasani as mahaifiyata saboda haka you are my mother right Ya Anas?” “Yes Angel come here” nan ta matso jikinsa yayi hugging nata “is okay bar kuka kinji?” “Ya Anas promise me Ummimi batazo dan tafiya dani bae, bana sonta kamar yadda tak’i ni tun ina baby, Ya Anas karka barta ta tafi dani please.” “That will never happen Angel.” “Anas ya isa please be kamata kasawa Amal tsanan mahaifiyar ta haka ba koda meh Ummimi tayi she is still your mother yanzu ku tashi muje mu sameta a parlour banason jin no ku tashi.” ** A parlour. “Shettima, Shettima d’ana dan Allah kamin magana I’m sorry for what I did to you dan Allah kayi hak’uri.” Anan ta miqe ta nufo inda yake zaune ta dafe kafad’ansa, hannunsa yasa yacire nata shima yana hawaye “Shettima please kayi hak’uri.” “Ummimi why? Mesa zaki dawo bayan mun mance dake? Why do you have to mess up our lives always? Why Ummimi?” Ya rushe da kuka tsugunawa tayi gabansa tare da hugging nasa sam be hanata ba sede beyi hugging nata back ba, yana kuka tanayi Fannah na kallonsu sun kusan minti biyu a haka sannan ya raba jikinsa daga nata. “Shettima wallahi ba’a son raina na tafi na barku ba I love you guys so much” ta yi maganan hannunta dafe akan fuskarsa tana shafawa a hankali. “Sharrin shaid’an ne ba komai ba Shettima dan Allah don’t stop me from being a mother to you kabani dama in biya wannan shekaru goma shabiyar da mukayi ba’a tare ba please this is all I ask nasan barin iya tambayan gafarar ka ba saboda ban cancanci hakan ba ni kawai kabani dama in zame maka mahaifiya again please Shettima.” Shiru yayi bece komai ba. “Shettima kayi shiru” Fannah tayi maganar tana d’ago Ummimi daga k’asa. Daidai nan Abuu yafito idanunsa sun mugun kad’awa bayanshi Ummie ne da Amal sekuma Anas. Bayan sun zazzauna Abuu yayi gyaran murya; “Aysha meke tafe dake? Me kika zo yimin a gida? Ko ban tambaya ba nasan sharri ne tattare dake saboda haka in kinayi wa Allah kitashi kifita min daga gida, nida yarana bamu k’aunan ganinki, bak’in cikin da kika bamu da abaya kad’ai ya ishemu basekin k’ara mana.” “Ya Ibraheem please ya isa kayi hak’uri” cewar Ummie. “Amal taho nan” Abuu yakirata seda ta kalli Anas yabata nod tukuna taje tasamu Abuu, a gefe dashi ya zaunar da ita. “Zaki iya tuna wannan?” Ya tambayi Ummimi da tuni kuka yafi k’arfinta. “Zaki iya tuna ‘yar da kika k’yamata kika turo ta kamar shegiyar da batada uba acikin basket? Zaki iya tunawa?” Har k’asa ta sauqa kan guiwanta tana roqan Abuu. “Ya Ibraheem dan darajan ubangiji kayi hak’uri, kayi hak’uri dan Allah wallahi baroku danayi shine babban kuskuren dana tafka a rayuwa na, d’an Adam ajizi ne we all make mistakes nasani kuskuren danayi babba ne wanda se me imani da tausayi ze iya yafemin, Ya Ibraheem wallahi nayi nadaman abinda na muku musamman ma abinda nayi ma Amal.” Nan ta dawo da kallonta kan Amal. “Amal dan Allah kiyi hak’uri kiyafewa mahaifiyarki I’m so sorry Amal please forgive me, give me the chance to hold you in my arms Amal tunda na haifeki ko k’are miki kallo banba nasa aka nad’eki cikin tsumma aka turoki ban tab’a riqeki ba Amal wannan abu har a yau yana damuna barin tab’a samin sukuni ba a rayuwa na har se in na riqeki as mothers do dan Allah karki hanani please my Amal.” Hannu Amal tasa ta share hawayenta sannan ta miyar da kallonta kan Abuu. “Abuu mena tab’a mata ta tsaneni haka? Mesa baka tab’a fad’amin inada wata mahaifiya ba bayan Ummie? ” “Amal kiyi hak’uri kinji? Nasan mun miki laifi wanda yake babba na hanaki sanin asalin ki, kisani nayi hakan ne saboda ina sonki Amal banason ki tashi kina kewar mahaifiyarki, I’m sorry kinji? Bar kuka” yasa hannu ya share mata hawaye. “Angel zo abinki” Anas ya kirata ba gardama taje ta samesa. “Abuu nida Angel zamu d’an fita in kun gama abinda kukeyi call me se in d’au Fannah.” “Anas dan Allah karka tafi kabari in nemi gafarar Amal please.” “Amal zaki iya yafe mata tauye miki hak’k’in datayi? Zaki iya yafe mata wulak’antaki da tayi since you were a baby?” Kafin Amal ta amsa yacigaba “no that the answer daga ni har Amal bame yafe miki sede ko Abuu da Shettima kina iya hak’uri in maganganun dana fad’a miki are a bit harsh to your ears, hakan na nuni da tsantsan tsanan da nake miki ne Ummimi dukda cewa kina mahaifiyata.” “Anas enough!” Ummie ta daka masa tsawa “kai bakasan wannan mahaifiyarka bace kake gasa mata bak’k’en kalamu haka iya son ranka? Ya Ibraheem kamishi fad’a.” “Anas yayi laifi Nafeesa, amman kuma in kika lura Aysha itace sila da ace bata aikata abinda tayi 15 years back ba da Anas bare tab’a gaya mata munanan kalamu haka ba, I’m not saying Anas is right what am saying is he has a point mukad’ai muka san kalan hell da mukayi witnessing da wannan marar imanin ta tafi ta barmu. Aysha me muka tab’a miki? Talaucin da kika tafi kika barmu danshi kisani bamu muka d’aura wa kanmu ba, gashi nan kinzo kin gani da idanunki Allah ya yaye mana shi saboda haka me kika zo min a gida?” “Tabbas ba k’arya ko kuskure a magananka Ya Ibraheem Allah shike azritawa aduk sanda yaga dama, inda zan iya bayyana muku how sorry I am da nayi, inda kunsan kalan tashin hankalin dana shiga bayan barinku danayi, wallahi tun a duniya anan naga sakayyan butulcin dana muku shiyasa nake barar gafararku Ya Ibraheem inhar baku yafemin ba bansan a’ina zan sa kaina ba bansan ya zaman kabari ze zame min ba ku agaza please. Ya Ibraheem inhar kai baka yafemin ba ba yadda yaran nan zasu yafemin please ka taimaka, Ummie dan Allah kisa baki ko zejeki.” “Ya Ibraheem kayi magana please godiya yakamata muyi tunda har Aysha tagano kuskurenta kuma tayi repenting se ku kuma kuyi hak’uri ku tausaya ku yafe mata, Aysha ko zaki bamu labarin ya rayuwarki ta kasance cikin wannan shekaru goma shabiyar dasuka shud’e ba tare da kowa yaji ko ya ganki ba? Ko ban tambaya ba nasan kina cikin babban tashin hankali jikinki kad’ai amsa ce game tambaya in shaa Allah, in family’nki sukaji labarinki zuqatansu zasu kariya su yafe miki.” “Nagode Ummie” tayi maganan tare da komawa kan kujera ta zauna. “LABARI NA bashida dad’in sauraro, ba komai bane aciki banda k’uncin rayuwa wanda ni dakaina na d’aura wa kaina saboda kwad’ayin kayan duniya dana sa a gaba, kwad’ayi ya kasance halin mata dayawa a rayuwarmu na yau. A gaskia duk wacce tad’au kwad’ayi abinyi toh wallahi tana tattare da gwagwarmayar rayuwa saboda kwad’ayi ba abar yi bace. Labari na wanda yasamu asali tun daga ranan dana bar gidan Ya Ibraheem nabi Alhajin Yola shine mafi mumunan labarin da na jima banji ban kuma gani a real life ba sede a labarai.” Taja numfashi sannan ta cigaba… © MIEMIEBEE
 “A yinin ranan da nabar gidan Ya Ibraheem nabar yarana abin muradina Anas da Shettima badan komai ba sedan bak’in talaucin daya addabemu sau dayawa muna tashi ba abinchi bayan gashi a waje Alhajin Yola ya nuna yana sona yana kashe min kud’i ba tare da na kawo wani tunani a raina ba na tattara kayakina nabar gidan Ya Ibraheem dukda erin kuka da roqana dasu Anas suka rik’ayi hakan be hanani tafiya ba saboda alokacin kwad’ayi ya riga ya rufemin ido”. “Bayan nabi Alhajin Yola yawuce danu Yola a ranan inda muka sauk’a awani had’ad’d’en hotel, seperate d’aki yakama mana acewarsa bamuyi aure ba tukuna be dace mu had’a d’aki ba washegari ya tinkareni ya fad’amin abinda ke zuciyarsa na aurena dayakeson yi dukda nasan haramun ne aure akan aure hakan be hanani amincewa da k’udirinsa ba, achan Yola aka d’aura mana aure acikin sati yamana processing visa inda muka wuce tsarkacacciyar k’asa Saudi yin honey moon sede wani gudu ba hanzari ba tun isar mu chan nake fama da zazzab’i, zuwan mu asibiti aka tabbatar mana juna biyu ne d’auke dani cikin Amal kenan, barin b’oye muku amman a lokacin cewa ma nayi azubar da cikin kasancewar chan gari ne me tsarki basu aikata haramun aka k’i biya min buk’ata koda muka dawo gida hankalina a tashe yake tsoro na kar Alhajin Yola yace ya fasa zama dani tunda na taho masa da cikin wani gidansa, alokacin banida wata burin data fi in kasance dashi saboda yadda yake kashe min kud’i. Shi ya kwantar min da hankali yakuma tabbatar min da cewa in kwantar da hankalina inyi rainon cikin kar na zubar yaso in na haife se na dawo muku da abunku, without a second thought na amince da hakan, haka nata rainon cikin Amal daya bani wuya har fiye da na Anas cikin fari dalilin haka yasa natsani abinda ke cikin ko ante-natal d’ina ba regularly nake zuwa ba fata na Allah rabani da abinda ke cikin nawa lafiya.” “Munyi tsawon watanni 7 a Saudi ba tare da mun samu sab’ani da Alhajlin Yola ba tarerayata yake kamar ‘yar baby abinda nakeso shi yakemin alokaci d’aya na mulmule tunda nafita daga first trimester. A wannan watan ne muka dawo Nigeria inda muka sauk’a a Maiduguri nacigaba da rainon cikina dana tsanesa fiye da mutuwa, kwatsam da daren wata rana nak’uda ya taho min wanda nad’au mutuwa zanyi bayan kusan awa shida danayi a labour room nasamu Amal ko k’are mata kallo banyi ba, in tambayi nurse d’in mace ce ko na miji ma banba saboda jin dad’in da nake na rabani da ita ko shi da Allah yayi, naso barin ta ta kwana a asibiti amman sunka k’i dole na taho da ita gida anan ne na gano mace ce na haifa duk erin kukan da Amal take a lokacin dan yunwa besa na shayar da ita ba yaron dake mana d’an hidima ne yabata ruwa ta rik’a sha kafin garin Allah ya waye Alhajin Yola yasa sa a mota da Amal tare da letter dana rubuta aka kawo muku ita”. d’ago kai tayi ta kalli Amal dake ta kuka jikin Anas kamar ba gobe taji ta k’ara tsanan kanta na wulaqanta wannan kyauta da Allah yayi mata. “Se a wannan lokaci nakai Alhajin Yola gun iyayena basu ko damu taya nayi auren ba tambayar da suka min d’aya ne shin yanada kud’i? siyayyan da Alhajin Yola ya musu ne yazame masu amsa, k’arya namusu nace ka saken ne Ya Ibraheem shiyasa na sake aure, please kayi hak’uri ka yafemin na sharrin dana maka”… “Ko kad’an baki min sharri ba Aysha saboda aranan da kikayi stepping foot kika bar gidana a ranan na miki saki d’aya saboda nasan duk inda zakije aure zakiyi nikuma ina sonki barin iya jure fushin Allah akanki ba shiyasa na sauwak’e miki kinga ko bakiyi aure akan aure ba.” wani sabon kukan ya sake rufe Ummimi she can’t ever forgive herself. “Tabbas babu kaman ka acikin mazaje Ya Ibraheem nagode k’warai Allah yima sakayya. “Daga nan muka wuce New York kamar yadda yamin alk’awari, rayuwa bata tab’amin dad’i kamar a wannan lokaci ba sede abin mamaki koda na tambayi Alhajin Yola wani aiki yake seyace min he is self employed niko da dama kud’insa ne ya damen ban kawo wani abu a raina ba haka muka d’au tsawon shekara muna soyayya dashi ba tare da mun samu wani matsala ba iyayena kuwa kullum yana cikin musu alkhairi daban daban a shekara na biyu da aurenmu ne nasamu cikin Barrah da Basmah wanda suka kasance twins kyawawa wane Amal shekarunsu uku nasamu Yusuf wanda yake sak Anas shi kuma, harta blue eyes nasu iri d’aya” ta d’ago kai tana kallon Anas da take ya kawar da kallonsa daga gareta, hawayen ta ta share sannan ta cigaba; “Alhajin Yola ya kasance yana matuqar son ‘ya‘yansa becika tsawata masu ba koda sunyi laifi ne, haka rayuwa ta cigaba da kasance mana cikin jin dad’i alokaci kad’an ne nake tunawa dasu Anas da Shettima amman kuwa in na tuna da talaucin daya fitini gidan Ya Ibraheem sema inji na tsanesu tun daga kan Yusuf haihuwa ya tsaya min. Su Barrah suna da 12 years aduniya nasoma fuskantan chanji daga mahaifinsu mutumin da baida magana baida masifa yamiyar da masifa abinyi abu kad’an kayi seya tsigale ka, akwai lokacinda har mari na yayi saboda yana ma Yusuf fad’a nashiga toh tun daga wannan lokaci ban sake gane kan mahaifinsu ba, yadena sonmu kullum cikin k’untata mana yake school fees na makaranta ma seya ga dama yake biya musu nayi nayi ya gayamin inhar laifi na masa ya fad’a mani in basa hak’uri amman ina inya watsa min wani mugun kallo ni dakaina nake tashi masa agun a 13th birthday’n su Barrah yayi suprising namu duka, birthday cakes biyu ya siyo musu mukayi celebrating birthday nasu washegari yasa duka yaran cikin mota cewa ze kaisu park su shaqata yatambayeni ko zani nace mai a’a bansani ba ashe wannan rana shine rana na k’arshe da zan sake sa yara na a idanu na ba. Kuka ne yafi k’arfinta hankalin kowa ya tashi wajen banda Anas, duk sun k’osa suji meya faru, Ummie da Fannah ne ke bata hak’uri. Picture’n taciro ta miqa ma Ummie “yau watanni bakwai kenan da rasuwansu.” Salati kukeji a d’akin bayan Ummie tagani ta miqa wa Abuu se Shettima lastly Amal then back to Ummimi again, anan duk sukayi mata ta’aziya shima Anas badan yanaso ba yayi mata. “Tun safe ya fita min da yara har La’asr basu dawo ba kodana kira wayansa kuwa har ta tsinke be d’aga ba wayoyin su Barrah kuwa switched off yake cemin, anan fa hankalina ya tashi daman tun tafiyarsu nake ji ajikina something bad will happen to them nakasa zama gu d’aya fatana Allah dawo min dasu lafiya se bayan Isha’i naji k’aran bud’ewan gate a guje na fita waje bayan yayi parking na tsaya gun ina jiran fitowan farin cikina yara na, sede basu ba alamansu, mahaifinsu kad’ai nagani cike da tashin hankali na tambayesa ina yaran suke kallo na yayi a raunane sannan yace min wai an sacesu, bansan a lokacin dana sume wajen ba next abinda nasani shine gani na danayi kwance akan gadon asibiti se a washegari muka dawo gida ba kalan tambayan duniyan da banma Alhaji Isma’il ba ya fad’amin ina ‘ya‘yana, amsar nasa d’aya ne an sacesu jiya a park cike da tashin hankali na d’ago mayafina zan kai report station ganin haka munafikin ya dakatar dani yamin qaryan wai tun jiya yakai report yanzu haka police sunakan investigation haka har wani sati ya zagayo ba labarin yarana, ban sake sanin meke min dad’i ba akullum ina sa ran za’a samu su Barrah amman inaa adaren wata rana na fito daga d’akina zan wuce dining space dan shan ruwa naji Alhaji Isma’il akan waya har na wuce se wani abu ya dawo dani baya nakasa kunne ina sauraron meyake fad’i a wayan. Hankalina ya matuqar tashi jin da bakinsa yake fad’in “ran yara na uku dana baku be isheku ba yanzu na mata ta kukeso?” Innalillahi wa’ina ilaihi raji’un” “Mutuwan tsaye nayi a wajen totally speechless ban hankara ba naga Alhaji tsaye a gabana fuska nakad’ai ya zame masa amsa ga tambayan daya s min. Ina kuka na mai maganar, “Alhaji? Dagaske ne?” Na tambayesa. Kame kame yasoma bansan a lokacin dana fara kai masa bugi ba, ba kalan zagin da ban masa ba a daren nace zan kai k’aransa station nan ya kukkule duka k’ofofin gidan da dambe da fad’a yakaini wani d’aki ya rufeni, ina jinsa yayi waya da d’aya daga cikin ‘yan k’ungiyan nasu yana cemai ya yarda ze sihar dani nima acewarsa tunda nasan sirrinsa yanzu ba amfani na again, ba waya akusani dani koda akwai ma bansan wa zan kira ba kwana nayi ina Sallah Allah ya kub’utar dani daga sharrin sa, washegari nasome neman abinda ze taimaka min in b’alla lock na k’ofan, da cokalin da nasamu na b’ab’alle screws d’in k’ofan na fito a lokacin bayi gida yafita, kayaki kad’an na d’auko da sauran essential things da zan buk’ata, na nemi wayana sama da k’asa na rasa, a gurguje nabar gidan nakai report police station ko ya akayi maganan yaje kunnensa oho next abinda naji shine wai yagudu yabar k’asan kwata kwata tun daga wannan rana ban sake sa shi a idanu na ba 3 months ago na ganshi awani super market tundaga wannan lokaci na shiga b’uya saboda nasan aduk lokacin da ya ganni tabbas nima siyar danayi zeyi, aiki na samu awani restaurant as a cleaner dashi na dogara har izuwa lokacin dana had’u da Anas da Fannah, kunji takaicaccen labari na.” Tausayinta ne yakama kowa a d’akin harta Anas, seda Ummie ta zubar da hawaye. “A gaskia kinsha gwagwarmaya a rayuwanki Aysha ba abinda zamuce se Allah ya kare aukuwan na gaba ya tsaremu daga sharrin mutane da aljanu gabad’aya…” dadda’d’un kalamu Ummie tariga gaya wa Ummimi shi kansa Abuu ya mugun tausaya mata yasani alhak’in sune yakama ta tunda har a duniya taga sakayya yaci ace sun yafe mata suma. “Aysha ni na yafe miki na yafe miki har abada abinda ya faru dake kuma Allah takaita” cewar Abuu. “Ya Ibraheem nagode, Allah ya saka da alkhairi, Shettima, Shettima dan Allah ka yafemin abinda na maka.” Shiru yayi bece komai ba ba irin rok’an da bata mai ba seya bud’e baki zece ya yafe mata seya kasa haka ta dawo kan Amal ma duk ba wanda ya iya ya yafe mata Anas kam ba magana Abuu be sa baki ba saboda yasan ba’a shiga tsakanin uwa da yara yasani with time duk zasu yafe mata. * Abuu ne tsaye da Ummie a dining ayayinda Ummimi ke zaune da Fannah a parlour su kad’ai Anas da qannensa duka sunyi d’aki. “Ya Ibraheem yanzu ya zakayi da Aysha?” “Ni kaina bansani ba Nafeesa, bansan me zanyi da ita ba.” “Agani na mubarta ta zauna damu anan tunda ba inda zata iya zuwa batada kowa banda mu.” “Me kike nufi Nafeesa?” “Ina nufin ka dawo da ita d’akinta ai akwai aure a tsakaninku.” “Barin iya dawowa da Aysha ba ina sonta amman barin iya dawo da ita ba.” “Zaka iya Ya Ibraheem kayi hak’uri mukoma parlon.” Bayan sun dawo suka zauna Ummie tayi gyaran murya “Aysha kinje kinga iyayenki kuwa?” “Banje ba tukuna bansani ko iyayen nawa ma suna raye ba.” “Kinada masauk’i yanzu?” “Banida Nafeesa.” “Toh yanzu wani mataki kika d’aukar?” “Ba abinda nakeso kaman in kasance da ‘ya‘yana Ya Ibraheem dan Allah kayi hak’uri ka dawo dani d’aki na badan halina ba dan Allah.” “Aysha na soki kuma zan cigaba da sonki amman ban tsammanin zan iya dawo dake.” “Ya Ibraheem please karka min haka dan Allah karka hanani daman kasancewa da yarana again nayi kuskure amman wallahi na tuba barin sake aikata abinda nayi da a baya ba, ka taimaka please” “Aysha kiyi hak’uri amman barin iya dawo dake ba” yana kaiwa nan ya miqe. Hak’uri sosai su Fannah suka rik’a bata. Da k’yar Ummie ta samu tayi convincing Abuu ya yarda aka bawa Ummimi d’aki d’aya a gidan Anas najin haka yasa Amal ta had’a akwatinta suka koma gida tare yasan muddin Amal tacigaba da zama da Ummimi toh eventually Amal zata yafe mata abinda baiso kenan. ** Tun isar su Fannah gida bata ma Anas magana ba a d’akinta Amal ta sauqa daidai da Azahar Anas yatura Amal dataje ta kira Fannah suyi Sallah a d’akin Hanan ta tarar da ita bayan tayi sallama tace, “Ya Fannah wai kifio muyi Sallah inji Ya Anas.” “Kice masa yajaku ku biyu zanyi nawa da kaina” da “toh” Amal taje ta isar wa Anas da saqon Fannah, daman yau yasan da akwai drama shida kansa ya miqe yaje yasamu Fannar, agefenta ya zauna “Flower tashi muje muyi Sallah.” “Bakaji meh Amal tace maka bane? Nace kajaku zanyi nawa ni kad’ai.” “Mesa toh?” kafin yakai hannunsa kan cikinta taja da baya. “Mara na namin ciwo se anjima zanyi.” “Toh zamu jiraki.” “Ni ina ma ace yadda kakemin haka kake ma Ummimi wallahi Habeebi ko kad’an banji dad’in abinda kama Ummimi ba yau, uwa uwa ce fa you are not being just inhar kai baraka yafe mata ba then don’t drag Amal into it, I know ba tsakani da Allah kasa Amal had’a akwati ta biyomu ba gudun kar ka barta achan eventually tayi forgiving Ummimi ne koba haka ba?” “Ke kikaji wajen zaki tashi muyi Sallah ne kokuwa?” “Bansani ba nima” tana kaiwa nan tabar masa d’akin binta yayi da kallo yana cizen lips nasa, d’akinsa takoma haka tak’i binsu Sallah ita kad’anta tayi nata bayan nan suka soma jin yunwa sarai zata iya musu girki tace barata iya ba Amal ‘yar gata kam dama ba abinda ta iya yi koda Anas yace ze musu girkin Fannah ta b’ullo da dabara tace ita yau tuwo takeson chi tasan sarai ba iyawa yayi ba. “Flower tuwo kuma yau?” “Eh tuwo nakeso.” “Toh Mom Hanan Amal jeki d’au mayafinki muje musiyo mata.” “A’a Amal is staying with me akwai aikin danakeson ta tayani bayan tafiyan mu cleaners d’in ba kullum suke zuwa aiki ba d’akina duk yayi k’ura zamuyi dusting.” “Flower bakida lafiya kibari gobe sukazo se suyi.” “Don’t worry ai bawani aiki bane zaki tayani koh Amal?” “Why not Ya Fannah.” “Good muna jiranka kefa barakichi tuwon ba asiyo dake?” “A’a banachi banaso.” “Ya muku kyau keda wannan yayan naki wato bakiya chin tuwo kema? Seku nemi abinda zakuchi nide aje asiyo min tuwo da miyan yakuwa I’m hungry.” “Toh Mom Hanan” yayi maganan tare da rufe gab dake tsakaninsu daidai zeyi pecking goshinta kenan taja baya sakamakon haka Amal ta k’yalk’yale da dariya “wai! Wai! Su Ya Anas ansha boncy, an kwashi shoki” itama Fannar bata san lokacinda ta qyalqyale da dariya ba. “Wato ni kikayi shunning a idan Amal ko Flower?” “Ni kaje ka siyo min abinci abeg yunwa nakeji.” “Kin kyauta kekuma Amal ina dariya kikemin nafasa bada iphone 7 d’in ma Shettima zan bada.” “A’a Ya Anas please I’m sorry”*** Bayan tafiyan Anas Amal ta d’auko bucket da towel dan fara goge-gogen da Fannah tace zasuyi sede ta tarar da Fannah zaune a parlour. “Ya Fannah kince akwai goge-gogen da zamuyi.” “Wasa nake babu zo nan ki zauna” tayi mata nuni da space dake gefenta “zamuyi wata magana” ba gardama taje ta zauna. “Amal ke ba yarinya bace yanzu you are 15 years old kinsan whats right and wrong koba haka ba?” Ta gyad’a kai “good” Fannah ta cigaba “inason ki saurari abinda nakeson fad’a miki da kunnen masu hankali ki ajiye duk wani abinda Ya Anas naki ya fad’a miki a gefe do you get me?” “Yes Ya Fannah.” “Mesa kika k’i ma Ummimi magana? Baki tausaya mata ne she lost 3 of her children, three fa Amal how does it feels ke lokacin da classmate naki nema yarasu ya kikaji balle ace ‘yan daka haifa har guda uku kana ji kana gani aka siyar dasu, just how bad does that feels?” shiru Amal tayi bata iya tace komai ba. “Magana nake miki Amal.” “It feels bad.” “Good then meya kamata kiyi dan sata feeling better kuma?” “Inyi condoling nata in bata hak’uri.” “Exactly amman mesa bakiyi ba?” “Ya Fannah ni kin manta abinda tamin ne danake baby? She hated me batare dana mata komai ba ko shayar dani batayi ba, to cut the crap har cewa tayi zata zubar da cikina kuma ga ciwon dataji ma Ya Anas nifa bana sonta.” “Kai kai ya isa haka ya isa karki sake fad’in bakiya son Ummimi, kema Anas ya koya miki wannan banzan halin nasa ko? Ya cusa maki tsanan mahaifiyarki, waya gaya miki ana k’in uwa ne?” “Ya Fannah nifa ba k’inta nayi ba ita ta k’ini, ita mesa baraki mata magana ba.” “Ai na mata Amal we humans we are prone to make mistakes ko ke nan akwai mistakes da kikayi kuma akwai dayawan da zakiyi a gaba haka Allah ya hallice mu we aiint perfect amman kuma the best amongst us shine wanda yayi laifi yayi realising yakuma tuba kamar yadda Ummimi tayi kiga kukan data tayi mana d’azu akan yaran data haifa kinsan da zata bud’e baki ayau tace ta tsine muku gabad’aya bameyin albarka cikin ku kin sani?” Amal ta kad’a kai. “Kinga shiyasa, Amal duk abinda zakiyi ma Ummimi aduniyan inma duniya zaki siya mata wallahi barekai kwatankwacin d’aukan cikin ki datayi ta reneshi har ta haifeki ba, kinsan azaban haihuwa kuwa? Ba zafin daya fishi se mutuwa fah shiyasa akace duk wacce ta mutu ta hanyan mutuwa ‘yar aljanna ce tayi mutuwan shahada, uwa uwa ce komin rashin dad’inta koda cikin shege tayi ta haifeku wallahi shima abu ne our mothers are priceless ba abinda zamu iya musu in return of abinda suka mana.” © MIEMIEBEE
TANA TARE DA NI… PAGE 96 BY MIEMIEBEE “Toh ni yanzu me kikeso in mata Ya Fannah?” “Kema ai kinsani Amal kidena biyewa Ya Anas kibata chance da take nema to hold you and be your mother bawai nace kiyafe mata bane amman kibata wannan chance da takeso dakanki zaki yafe mata in kikaji dad’inta ke bakison kisan mamanki ne?” “Ai nasan Ummie.” “Ummie ba itace mahaifiyarki ba Ummimi ce mahaifiyarki…” haka Fannah tariga ma Amal nasiha seda ta kashe mata jiki. Dawowan Anas ya taho ma Fannah da tuwonta nan tasamu ta kora yunwa shikuma da Amal suka wuce kitchen dan dafa nasu kamar Anas yasani ya tambayi Amal ko Fannah tamata maganan Ummimi bayan fitansa, bata b’oye masa ba ta fad’a masa zahirin gaskia. “Ya Anas don’t you think is about time mu bawa Ummimi chance to be our mother? Wallahi wa’azin da Ya Fannah tamin ya mugun tsorata ni.” “Ai dama nasani, nasan hakan ze faru kinaji na ba bawani chance da zakibawa Ummimi am I clear?” Baki na rawa tace “yy.. Yes.” Washegari… Da sassafe Ummimi ta tashi tayi wanka sannan ta rok’i Ummie data rakata kitchen dan nuna mata inda postions na plates da sauran utensils suke hakan kuwa akayi breakfast me rai da lafiya favorite na Abuu ta had’a wato doya me k’wai a jiki bayan tagama ta had’a kan dining. 8:30AM Abuu yafito daga d’akinsa cike da ladabi da biyayya ta sauk’a har k’asa ta gaishesa ba yabo ba fallasa ya amsa. “Ya Ibraheem ga breakfast chan na had’a maka dan Allah kar kace bara kaci ba kayi hak’uri please” kai ya gyad’a mata sannan yabita dining d’in taja masa kujera ya zauna sannan tasoma serving nasa tana bud’e flask d’in k’amshin girkinta wanda he can’t tell how he missed it ya buga masa hanci bayan tayi serving nasa ta had’a masa tea sannan ta koma gefe tana kallonsa a hankali yasoma chin abincin har ya k’are. “In k’ara maka ne?” Ya gyad’a mata kai dad’i sosai taji a ranta “ashe har a yanzu baka dena son doya me k’wai ba.” “Mesa zan dena so bayan kin riga kin saba min dashi, kefa barakiyi breakfast d’inba?” “Zanyi amman nafison duk ku karya tukuna, Shettima fah? Har yanzu yana kai goman safe kafin ya tashi kokuwa ya rage bacci?” “Keda d’anki kuma kina iya zuwa kiduba d’akin sa ai shine first room by your right.” “Toh nagode sosai Ya Ibraheem.” Seda yagama chi ta masa Allah kare ya fice office sannan ta dawo ta d’iba wa Shettima nasa a plate da tea nasa ta nufa d’akinsa a hankali tayi knocking. “Waye ne” ya tambaya. Da k’yar bakinta ya iya cewa “Ummimi ce Shettima.” Daga nan be sake cewa komai ba. “Shettima yi hak’uri ka bud’en kaji? Yi hak’uri please.” Nanma shiru “Shettima barin bar nan ba har se in ka bud’en k’ofan nan.” Tafi minti goma tsaye a wajen sannan Shettima ya tashi ya bud’e mata ba tare da yace mata komai ba, bayansa tabi ta ajiye masa breakfast d’in akan centre table dake d’akin. “Ina kwana Shettima?” Nanma be amsata ba gefensa ta nufa ta zauna kan gado. “Shettima barin iya forcing naka kayimin magana ba saboda na kasance me laifi amman kayi hak’uri ka tashi ka karya kaji Babana?” “Ummimi why are you doing this?” “Saboda inason ka Shettima, ina sonka fiye da yadda nakeson kaina.” “Shine kika tafi kika barmu alokacin da muke buk’atanki?” “Barin ku danayi shine babban kuskuren dana tafka kuwa Baba na shiyasa nakeson inyi making up for the last 15years da mukayi ba a tare ba, yi hak’uri ka karya kaji?” Hannunsa taja ta zaunar dashi sannan da kansa ta soma basa abincin yana karb’a har yagama chi. “Thank you so much Shettima na wannan dama da kabani Allah ya saka maka da alheri yakuma maka albarka.” “Ameen” ya amsa. Daidai nan wayarsa yasoma ringing kasancewar wayar na kusa da Ummimi tasamu daman ganin wake kira ‘honey boo’ taga rubuce kan screen d’in. Da sauri ya d’aga wayar daga dubanta sede yakasa amsawa ganin Afrah ke kira, d’an murmushi ta saki “haka Baban nawa ya girma? D’aga wayar mana to ko se surikar tawa tayi zuciya ne?” Besan alokacinda ya murmusa ba. “Ko kunyan Ummiminsa yake ne?” “Ummimi fa ba budurwa ta bace.” “Awww shine akayi saving lambarta da honey boo, d’aga mana kose ya tsinke ne.” “Zan kirata anjima.” “Toh wace ita? Wata lucky girl d’in ne ta sace min zuciyan one in town son d’ina?” Murmushi sosai Shettima ke “sunanta Afrah k’anwar Fannah.” “Wow aiko ina da tabbacin itama tana da hankali kamar Fannah, Allah tabbatar mana da alkhairi yabar ku tare.” “Ameen Ummimi” “I will love to know you better Shettima” “Don’t worry” yayi maganar yanasa shirt nasa. “Toh Babana ya naga kamar kana shirin fita?” “Eh makaranta zani inada lectures.” “Oh okay me kakeso kaci da rana?” “Babu ba sekin dafamin komai ba zan siya a school.” “A’a mahaifiyarka na raye bara ka chi abincin waje ba fad’a min meh kakeso.” “Ina irin macronin da kike dafa mana? Irinshi nakeso.” “Toh angama son Allah kiyaye kaji? I love you.” So yake yace mata he loves her too amman kuma yakasa dan haka ya gyad’a mata kai zallah. Bayan tafiyan Shettima ta share masa d’aki tayi mopping tsatsaf haka d’akin Abuu ma sannan tasake yin sabon breakfast masu Anas tare da Ummie suka fita dankai musu sede Ummie tak’i shiga tabar Ummimi ita kad’ai, securities suna ganin Ummie suka bar Ummimi tashiga door bell ta danna alokacin Anas na aka kitchen shida Amal suna had’a musu breakfast ita ya tura da taje ta bud’e ganin Ummimi ce ta bud’e tare da gaisheta kamar yadda Fannah ta buk’ace ta. Dad’i sosai Ummimi taji “Amal my princess ya kike?” “Lafiya.” “In shigo?” Daidai nan Anas yafito “waye ne Angel?” “Ummimi ce Ya Anas” apron d’in jikinsa yacire sannan ya k’ariso “ina kwana Anas” kamar wanda bare amsaba ya amsa “lafiya” tare da sake tare k’ofan dan kar ta samu daman shiga “wani abu ne?” “Breakfast na kawo muku.” “Ai da baki b’ata lokacinki ba we are making breakfast already zaki iya tafiya.” Hannu tasa ta taresa daga rufe k’ofan “Anas please karka min haka dan Allah” tayi maganan hawaye na ciko mata a ido daidai nan Fannah tafito daga d’akin sanye take da kayan bacci iya guiwarta, ganin alaman baquwa bakin k’ofan yasa takoma ta sanya hijabi sannan tafito “Habeebi meke faruwa anan?” “Ya Fannah Ummimi ce tazo.” Amal ta amsata. “Shine baku shigo da ita ba?” tayi maganan alokacin datake tsaye gefen Anas. “Ummimi please kishigo” wani kallo ta watsa wa Anas sannan tashigo da Ummimi ciki anan suka gaisa. “Waya miki kwatancen gidan namu?” “Tare da Ummie muka taho tana waje tana kuma gaisheku duka, dama breakfast na kawo muku.” “Allah sarki Ummimi da gajiya haka ai da baki wahalar da kanki haka ba, Anas d’an karb’i mana” yi yayi kaman be jita ba “Amal karb’i flask d’in kinji?” Ba gardama ta amsa takai kitchen hira kad’an suka tab’a wanda ciki ko uffan Anas be furta ba haka Amal ma kasancewar taga idon Anas daga k’arshe ma kitchen ya koma ya cigaba da abinda ke gabansa da Ummimi tazo tafiya takira Amal tare da miqa mata wasu hada’d’d’en porches na iphone 7s. “Gashi Habibti wannan naki ne naji Ya Anas ya siya miki iphone 7 koh?” Ta gyad’a kai “toh gashi bansani ba ko kinason maroon and red colour? best colorn Basmah da Barrah kenan I was thinking ko kema haka kinaso” amsa Amal tayi tana k’are musu kallo “sosai inason red and maroon colour Ummimi thank you.” “Always Habibti” ta bud’e mata hannu da nufin hug ba gardama Amal taje tayi hugging nata wani erin yanayin da bata tab’a tsintan kanta ciki ba tayi yau, tunda take bata tab’a jin dad’in hug ba kamar na yau gaskiyan Fannah our mothers are priceless sunjima a haka se kallonsu Fannah ke cike da jin dad’i ina ma Anas zebawa Ummimi chance d’innan ta zame masa uwa kamar yadda take buqata. “Toh zan tafi seko gobe in dawo kinji?” Amal ta gyad’a kai. “In na dawo gobe zaki bani labarin ki, kinga yanzu nasan favorite colors naki inason insan komai about you zaki min?” Shiru tayi chan ta gyad’a kai “thank you so much Amal Allah miki albarka yamuku albarka gabad’aya zan tafi” ahaka sukayi sallama. Dawowan Amal ta wuce kitchen “Ya Anas kalli porches da Ummimi ta kawo min na wayan daka sayamin amazing how tasan favorite colors d’ina koda shike tace favorite colors na step sisters namu Allah jik’an rai Barrah da Basmah ma kenan, Ya Anas Ummimi isn’t bad.” “Mesa kika karb’a?” “Ya Anas I’m sorry.” “Bance karki mata magana ba?” “Ya Anas she is our mother.” “Naji zan karb’i iphone d’ina se muga aina zaki sa porche d’in.” “Ya Anas I’m sorry.”*** ★★★★ Haka nan tun daga ranan Ummimi tacigaba da musu girki, da sauran ayyukan gida dukda abinda Anas ke mata hakan be hanata ja da baya ba saboda tasan dalilin dayake hakan alokacin data tafi shine me wayon chan dole abin yafi affecting nasa, addu’arta a kullum baifin Allah kawo ranan da Anas zeyi accepting nata as his mother ba, duk yadda yayi dan hana Amal alak’a da Ummimi yakasa as the saying goes ba a shiga tsakanin uwa da d’a, shak’uwa me k’arfi ne yashiga tsakanin Ummimi da Amal har fiye da nata da Shettima koda Amal takoma gida d’akin Ummimi ta tare, atare suke kwana da Ummimi, tamata tsifa tamata kitso har wanki haka ma Shettima tuni suka daidaita a tsakaninsu daman Abuu abinda yake jira kenan bayan ya tabbata everything is cool tsakanin Ummimi da yaranta ya dawo da ita d’akinta dad’i sosai Ummimi taji harda kukan murna her biggest dream is now a reality su Ummie da Fannah duk sunji dad’in wannan re union d’in har small party suka had’a inda Fannah tayi introducing Ummimi wa Maminta anan Ummimi taga Afrah in-law to be nata abinde se wanda yagani they turn out into a one big happy family banda Anas da duk wannan abubuwa da akeyi baima zuwa bale yaga kayan bak’in ciki har a yau bayajin ze iya yafewa Ummimi yariga ya dawo daga rakiyarta gabad’aya sede hakan be hana Ummimi fita daga harkansa ba ita ba. Musamman Abuu ya kira Fannah yamata godiya in person in da badan ita ba yasani da bare sake had’uwa da Ayshan sa ba, dabadan Fannah ba da Amal won’t get the chance to see her mother again, da badan Fannah ba da Ummimi won’t get the chance to see her family ever again har ta nemi gafararsu dan haka yayi mata godiya sosai tare sanya mata albarka ba iyaka. Shak’uwa na haqiqa ne ya cigaba da shigewa tsakanin Fannah da Ummimi, yadda Ummimi tad’au Amal haka tad’au Fannah tamkar ‘yar data haifa saboda irin ladabi da biyayyan da Fannah ke mata itama sekace wa Mami. Ummimi da Abuu dasu Shettima ne duk sukaje gidan iyayenta, alhamdulillah iyayen nata na nan da rai dakuma lafiya anan duk suka nemi gafarar Abuu akan abinda suka yi masa shekaru da dama da suka shud’e. Tun daga wannan rana rayuwa tayi turing perfect ma wannan family kan Ummimi da Ummie a had’e sekace ba in laws ba sosai Ummie kebawa Ummimi girma bata kuma dena yiwa Anas wa’azi ba itama fatanta Allah kawo ranan da Anas zeyi accepting Ummimi. Cikin Fannah se girma yake masha Allah a yanzu haka cikin nata ya tsufa yanada 8 months da sati d’aya, sosai cikin nata yayi girma yazamo ko k’wararren motsi zatayi setayi dagaske, ga wani erin tsoron haihuwan datake cikin yi a kullum ko asibiti bata son zuwa, Anas, Mami da Ummimi ke cikin kula da ita kullum, Amal tadawo zama dasu ma tak’i dan yadda batason rabuwa da Ummiminta bata tab’a sanin dad’in uwa ba se a yanzu. ** Yau ranar ta kasance Saturday zaune Fannah ke a garden tana d’an ciye ciyenta, gefenta Anas ne da laptop a gabansa yayi focusing sosai yana aiki akai. “Habeebi” takira sunansa. “Nagaji” “Yes Mom Hanan, Hanan na damunki ne?” Kai ta gyad’a a shagwab’ance. Laptop nasan ya rufe tare da ajiyewa kan table sannan ya matso kusa da ita yana shafa gashin kanta a hankali, “hak’uri kad’an zaki k’ara Sweetheart nan da 3 weeks in shaa Allah Hanan namu zata fito tadena damun min Flower” yayi pecking goshinta. “Yau zaki iya fita walk?” Kai ta girgiza mai da wuri “banajin zan iya fita yau Habeebi.” “Flower haka jiya mafa kika k’i fita kin tuna me Dr tace? Yi hak’uri kinji?” A hankali ya miqar da ita suka fita walk tafiya kad’an Fannah tayi tace ita su dawo gida hakan kuwa akayi.*** 3 weeks later 2 days later, exactly 9:43AM… Kamar yadda suka saba kwanciya manne da juna haka ma suke a yau sede Fannah ta kasa bacci tun bayan Sallan Asuba da sukayi, da k’yar ta miqe ta zauna dan girman cikin nata. Bayanta ke mata wani erin zafin azaba kamar tacire ta ajiye a gefe da na bayan ya lafa sekuma cikinta yahau juyi ta k’asa k’asa tun tana iya jure zafin takasa ta k’wala wa Anas kira a firgice ya tashi ganinta yayi miqe a k’asa tana hawaye tana juyi. “Omg! Flower what is happening?” kafin tayi magana ruwanta yayi breaking. “Anas I’m in labour please do something arrggh!” Ta saki k’ara hannunta na a k’asan mararta bayi yashige yayi brushing yafito da wuri da k’yar ya iya d’agata yakaita mota sannan ya d’ago maternity bag nata se asibiti, hankalinsa ya matuqar tashi ganin yadda Fannah ke kuka kamar ba gobe da k’yar ya iya tattara hankalinsa gu d’aya ya kira Mami ya sanar da ita, Mami ce ta sanar dasu Ummimi kusan a lokaci d’aya suka iso asibitin duka. Alokacin Anas na a d’akin da Fannah ke ya riqe hannunta gagam cikin nasa yana kissing kanta assuring her _YANA TARE DA ITA_ sede sam its not helping sekaceba Flowersa ba gabad’aya tafita daga hayyacinta tana kuka tana ihu abin tausayi wane mutuwa zatayi, tana zufa yana share mata shima besan a lokacinda ya soma kukan ba sunfi minti talatin ana abu d’aya tun yana iya jure kukan nata har yakasa besan a lokacinda yafito ba he can’t take it anymore, bare iya jure pain da wahalan da Fannah ke fuskanta ba. Ummie, Ummimi da Mami ya tarar tsaye bakin k’ofan da gudu yayi kan Ummimi yayi hugging nata batayi tammanin hakan ba tsabagen yadda mamaki ya rufeta kasa hugging nasa back ma tayi. Kuka yake wane d’an yaro ya matseta gagam ajikinsa. “Ummimi I’m sorry, I’m so sorry please dan Allah kiyi hak’uri, please forgive me I never knew you went through this kafin kika haifeni nima dan Allah kiyi hak’uri for all that I’ve done to you, forgive me please mother.” © MIEMIEBEE
 *THE END* “Little Fauzi kinsan in Mammy taganki zata zane kikoh?” “Daddy hide me” tasake matse mai k’afa, hannu yasa ya d’agota sama yana k’are wa jan bakin dake fuskarta kallo kawai seya hau dariya, hannu tasa cikin dimple nasa tana matsewa itama se ta gwada tab’a nata. “Makeup artist indeed why are you being stubborn kinason mu fara fad’a dake?” Ta girgiza mai kai “toh karki sake tab’a kayan Mammy kinji? Duk wanda yake sa Mami magana fa ojuju zasu kama shi irin na cikin story books naki.” “O’o Daddy nadena.” “Who is a good girl?” “Aysha Hanan Fauzi!!” “Great! High five!” Suka tafa hannu a sama “low five” suka yi a k’asa “then friendly punch” sukayi punching juna a hannu, kayanta ya cire mata ya nufa bayi da ita ya mata wanka da k’yar ta yarda yafito da ita dan shegen son wasa da ruwa ne da ita, kayakin Fannah ya hau tattarawa ya ninke ya miyar cikin wardrobe d’in da sauran accessories nata. “Ina Mammy?” “She is sleeping” ta basa amsa tana k’ok’arin ciro d’aya daga cikin hand bags na Fannah dake rataye a hanger. “A’a little Fauzi banda b’arna zo na saya miki chocolate” da gudu tayi wajensa bekaita ko ina ba se wajen data yi rubutu “Little Fauzi what is this?” “Wannan?” ta nuna mishi da yatsa. Kai ya gyad’a mata. “Daddy bakasan capital letter A and small letter a ba? Aahhh! Shame on you” Tasa hannu tana tare kumatunta. “I mean mesa kikayi rubutu ajikin k’ofa da nan?” “Aunty said we should practice everywhere.” “Hanan what she meant is that kuyi practicing a books ko papers ba jikin walls, floors da k’ofa ba, ba’a rubutu ajikin bango kinji? A book kad’ai akeyi.” “O’o nafison anan my book is too small.” Da k’yar yayi convincing nata ta yarda barata sake rubutu ba se cikin littafi dukda kuwa yasan baji zatayi ba. A 2 seater ya zaunar da ita ya kunna cinema yasa mata Cartoon network wai a tunaninshi cartoon ze d’auke mata hankali baratyi b’arna ba dan ze shiga bayi watsa ruwa, “Behave yourself kinji little Fauzi? Banda tab’e tab’e.” “Yes Daddy” tayi maganan tare da sake riqe teddy bear nata tana mai murmushi yana b’acewa daga kallonta ta sauk’o kan kujeran ta d’au remote tasoma bin buttons d’in one by one tanaci seda ta cinye kap sannan ta miyar ta ajiye ta nufa dining ita wai a dole yunwa takeji zata d’iba abinci. Flask d’in ta bud’e taga spaghetti seta sakar da murmushi ta fara bin kan naman ciki one by one tana chi kad’an ta rage agarin rufe flask d’in tayi b’arin abincin duka ya zube a k’asa. “Oh no! Mammy will beat me today, Aunty said learn to tell your parents sorry when you are at fault” cute smile nata ta sakar sannan ta ja teddy bear nata ta nufa d’akinsu Fannah a hankali ta bud’e k’ofar ko noticing nata su Fannah da suka zurfafa suna kissing juna basuyi ba, baki wangalau Hanan ta sake, a nitse ta dosa cikin d’akin taje ta zauna kan couch opposite them tana kallonsu, har a ynzu basu san da shigowarta ba seda Anas ya juya Fannah, Fannah taga Hanan ko kad’an shi Anas ma be ganta ba. “Habeebi wait! Ka tsaya Hanan is here” firgit ya miqe zaune yana k’ure wa Hanan data sa hands nata a both side of her cheeks tana kallonsu ko kyafta ido babu. Dukansu were at shock bawanda ya iya mata magana gawani kallonsu da take har yanzu. “Little Fauzi why didn’t you knock before you came in?” “Because the door was open, Mammy what are you doing with Daddy?” Cike da kunya Fannah tace, “nothing sweetie jeki d’auko min princess gown naki mu nuna wa Daddy.” “Saboda in na fita ku sake kama junanku ba, hmm bad girl” “Little Fauzi don’t say that kinga Mammy batada lafiya ne nake dubata.” “Are you a doctor? Toh aima you may kill her kayi nauyi ka zauna akanta.” “Ya Salam Hanan dan Allah kiyi shiru kuma karki sake magana haka, we are sorry kinji?” Cewar Fannah. “Perfect! Dama nima nazo ince miki sorry kuma kin fad’a min thank you Mammy’ tayi tsalle ta sauqa daga couch d’in. “A’a wait Hanan what did you do?” “Nothing Mammy, Daddy ka cigaba da duba Mammy bye” taja musu k’ofan. **** Chan dare around 7:30PM su Fannah suna zaune a parlour, Anas is busy with work itakuma tana taya Hanan homework sede sam Hanan tak’i concentrating. “Daddy Mammy our teacher has a veryyy biiggg nose.” “Ikon Allah Hanan me ruwanki da hancin teacher’nku kuma.” “Mammy baki gani bane? Ai seda na gwada sa 5 fingers d’ina aciki kuma duk suka shiga kuma setacmin wai you this Aysha you’re so stubborn you are lucky your dad is… Is.. Billo oho ni na manta haka de tacemin.” Dariya sosai Anas ya tsaya yi. “Habeebi Allah kadena mata dariya the more kana mata dariya the more take sake rashin ji.” “Flower I can’t help it.” “Flower??” Hanan tayi maganan tare da tab’e baki “Daddy mesa kake cewa Mammy Flower? Flowers fa acikin story books suke” shiru kawai yamata dan kuwa Hanan tafi k’arfinsa bayan sun gama mata home work d’in da k’yar, Anas yace, “Hanan baby miqo min remote” “Daddy gashi” daidai ze danna power button kenan yaga wuyam! Hannu ya aza kan bakinsa in shock. “Hanan Fauzi! What is this? Ina kika kaimin buttons d’in? “Daddy bani bane.” ”You are lying ko? Then waye ne?” “Mammy ne naganta d’azu tana ci but don’t tell her” aiki Fannah dake fitowa da towel na Hanan ta jiyota. “Hanan nice nachi remote?” “Eh kece.” “Oh Allah shiryeki Hanan.” “Ameen Mammy kema Allah shiryaki.” “Ai ka soma gani da kanka ni wuce muje mu miki wanka ki kwanta gobe akwai school.” “O’o ni barin sake zuwa ba hancin teacher’n mu is too biggg.” “Oh ni Maman Hanan da ana siyar da mutane dana siyar dake Hanan in huta.” “Kema Mammy da ana siyar da mutane dana siyar dake.” Hanan ta kwaikwayeta. Anas na tashi shiga d’aki dan d’auko wani abu Hanan ta kewaya taga ba Fannah tuni ta nufa gun dataga papers na Anas “aha! Daddy said we only write in books and on papers” biron dake kusa da wajen ta d’au tahau zana ‘Aa ’ masu desings akai, fitowan Anas yayi daidai da lokacin data ke danne danne cikin laptop nasa. “Daddy does like this and like th-” “Omg! Little Fauzi Allah yasa baki fitamin daga inda nake ba saboda banyi sav-” aiko be k’are maganan ba yaga tayi shut down na system d’in gabad’aya. “Hanan” ya juyo yana kallonta cute smile nata ta sakar masa da innocent baby face nata. “Daddy!” Kafin yamata magana ta d’au files na F&C enterprises da suka basa dan signing meze gani akai? ‘Aa’ na Hanan akai kota ina baki yasake totally speechless “Flower!” Ya danna wa Fannah kira ”yes Habeebi” tayi maganan tana fitowa daga kitchen. “Kizo ki d’auki wannan b’eran kisata baccin dole please.” “Yau kuma kanku akeji da little Fauzi da bata laifi? Hanan me kikayi wa Daddy?” “Be iya rubuta A bane na mishi kuma d’azu yace I should stop writing on doors and walls I should write on on papers and in books shine nayi.” ★★★★ _6 months later…_ Tsaye Fannah ke a kitchen tana girki da k’atoton cikinta wanda yake nan kaman na twins na 5 months, aiko Hanan ta tabbatarmin da eh cikin ‘yan biyun ne da Mammynta. 12:30PM driver yadawo da Hanan gida bayan ta yi wulli da takalamanta dakuma jakan makarantan ta a parlour ta dosa kitchen inda taji motsin Mammy. “Mammy I’m home.” Shiru Fannah tayi bata tanka taba “Mammy I said I’m home” nanma shiru. “Mammy I’m sorry.” “Ai ba ruwa na dake Hanan tunda bakiya jin magana kinga in na haifi baby twins d’ina barin sake shiga harkanki ba, saboda su basu gagara in akace musu stop zasu bari not like you.” “Mammy I’m sorry.” “Aini ba ruwa na dake kicigaba da biye wa Daddy, Airah da Aidah (baby twins nata) kawai nasani ina haifansu zamu bar miki gidan nam sekita rashin jinki me kad’an ki.” “Mammy no please karki tafi min da sisters d’ina.” “Toh mesa zan bar miki su? Dan ki koya musu rashin ji suma?” “No Mammy I’m sorry I won’t do it again” ta riqe kunnuwanta. “Are you sure?” “Yes Mammy” “Oya come here” ta wanke hannunta a sink da gudu Hanan tayo kanta Fannah ta d’agata sama “daga yau bara ki sake min b’arna ba?” “Yes Mammy.” “Thats my girl zaki tab’a sisters naki?” Cike da jin dad’i ta gyad’a kai nan Fannah ta ajiye ta sannan ta aza hannunta kan cikinta aikuwa tayi having kick. “Mami najisu Airah da Aidah koh?” Fannah ta gyad’a mata kai. “Mammy se yaushe zasu fito?” “In 3 weeks time in shaa Allah” “Yeyy! Zan zama Ya Hanan koh? Yawwa Mammy zanje wajen Ummimi yin weekends Ya Amal tace zamuyi wasa kuma zata kaini wajen Ya Aiman.” “Wallahi data kyauta min kona samu sakat bari zuwa anjima zan shirya miki akwatinki oya jeki cire uniform naki sauran kuma kice zaki wanke kinji ni ba?” Daidai nan wayan Fannah dake kan counter yasoma ruri ganin Afrah ke kira ta d’aga da wuri. “Mata a gidan Shettima.” “Hehe Mom Hanan maman ‘ya biyu ya jiki?” “Wallahi alhamdulillah ya hidima?” “Se godiya, nikam gown da zansa a bridal shower d’innan nakeso ki rakani store inje in duba anjima.” “Aww ba d’inkawa zakiba?” “Baby yaban enough kud’i siyan na kanti kawai zanyi.” “Toh fa Afran Shettima Allah nuna mana bikin nan naku, zuwa anjima in Amal tazo ta d’au Hanan se in taho muje mu duba miki.” “Yauwa ina wannan meh blue eyes nakin?” “Wai Hanan?” “Eh mana kai! Yarinya ko jaraba?! ai wallahi banson ta sake zuwa mana yin weekends waya na fa ta d’auka ta tsoma cikin miyan kukan Mami, tad’au shampoo tana wanke wa bebinta gashi, farin jallabiyan Baba ta d’auka tana gogawa a k’asa wannan Hanan seku.” “Toh naji karki zagar min ‘ya ahakan Amal keson d’aukanta yau har ina rowa, zanso kema Allah baki ‘ya kaman Hanan.” “Chab! Allah raba I’ve got to go zani booking makeup artist bye!” Ta katse wayar murmushi Fannah ke “su Afrah amarya oh! Wataran kuma na Aiman.” 4:25PM Anas yadawo from office, alokacin har Amal ta tafi da Hanan. Fannah kad’ai ke zaune a parlour tana shan tuwon madara “welcome home Habeebi yau ka k’ariso da kanka barin iya tashi ba.” Murmushi ya sakar mata sannan ya ajiye jakansa ya nufo inda take ya zauna light kiss yamata brushing. “The queen of my princesses I love you.” “I love you too king of my princesses.” “Ina little Fauzi?” “Amal tazo ta d’auketa d’azu wai zatayi weekends achan.” “Flower mesa kika barta haka last weekend ma Hanan batayi a gida ba.” “Toh wake neman ‘yar jaraban chan? Kasan yadda ta buga min ciki kuwa d’azu da safe?” “Ta tab’a mana Airah da Aidah koh?” Ta gyad’a mai kai. “Kinsan Hanan she got no worries se hak’uri we love you much.” “Wallahi nagaji Habeebi daga wannan I’m not getting pregnant again tunda nasamu two in one” “Haba the queen of princesses sauran two bayan wannan.” “In kai zaka haifesu kam ai ba matsala amman bani ba.” Pecking nata yayi a goshi “muje mu wanke miki kan.” “Banaso ai tun jiya nace kamin kak’i.” “Jiya ai nayi wa Hanan ne yi hak’uri Flower” arms nata tayi cycling a wuyansa tare da kissing nasa passionately na ‘yan mintuna “I love you Mr. Fauzi.” “I love you too Mrs. Fauzi tashi muje toh” a hankali ya miqar da ita suka wuce d’aki. ______________________________ *ALHAMDULILLAH!!!* Anan ni MIEMIEBEE na kawo k’arshen wannan littafi nawa me taken *_TANA TARE DA NI_* inda nayi kuskure ko na fad’i ba daidai ba Allah yafemin, kamar yadda kuka sani wannan labari k’irk’ira na ne (fiction) saboda haka adena kwatanta min shi da real life nayi littafin ne dan nishad’i sekuma dan fad’akarwan dake ciki. I will first of al like to thank *you* for reading my novel and supporting me through out, thank you so much as we keep loving each other haters wanda basuda zuciya bayan nace subar karantamin littafi amman sun kasa dan dad’i should keep on hating, mutum in baida maqiya to be kaiba abinda Fans ke cemin kenan kullum, alhamdulillah tunda ina dasu dan haka nake godiya wa haters d’ina keep on hating I got the f*ck finger up for yah! Godiya me tarin yawa ga *Aunty Sis* my sweet mom I love you Allah bar zumunci yacigaba da kare min ke, to *Lubiee (finest)* thank you for your support I’ll love you always like you do ME. To my co writers that have been supporting me through out thank you. Fatima malumfashi Hanefah usman Queen Meemiluv Anee Futha lurv Pherty Lilmeerahcute Munaysat Bebeelo Miss Hafsy Rash kardam Sahaf Miss xoxo Xybab Yusuf Ummi Aysha S.A Azeez Pharty B~B Nafee anker Ummee Adnan Hafsy Rano Xarah B~B Qurratul ayn da sauran wanda sunan su ya kwanta min kusani duk kuna raina. Special thanks to all of my group members *(MIEMIEBEE NOVELS GROUP)* yours support is different I Love you guys so much, Allah cigaba da had’a kawukan mu (OneLove) To my Fans club *(MIEMIEBEE FANS)* thank you for your love and care. From the buttom of my heart nas lisafo duka names na true fans na wannan littafi nawa butbthe prblem is Allah yayi wa wannan littafi masoya dayawa, na rubuta kusan 50 na goge saboda naga fans d’in basu k’arewa kuma banason in rubuta wasu in bar wasu, wai wannan ma wanda nasani kenan ina ga wad’anda bansan su bafah? Thank you so much guys for making my novel talk of the town. *MIEMEIBEE LOVES YOU SO MUCH WOLLAH* akwai lokacinda na fita naje kasuwa wasu ‘yan mata tsaye a gefe na suna hirar Tana Tare Da Ni wata ke cewa Allah had’ata da marubuciyar koda na fad’a musu nice writer’n they couldn’t believe it dan dad’i so dayawa ana bani labarin yadda Fans ke tad’in novel d’ina abinda nakeso kusani shine kamar yadda kukeso na kuke kuma *_TARE DANI_* nima haka nakeson ku nake kuma *_TARE DA KU_* I’m nothing without you guys (fans) kusani comments naku da wanda na gani da wanda ake ban labari akai ke keeping d’ina moving, forward ever backward never in shaa Allah haters will keep on hating till they die munyi gaba bame dawo damu baya. Allah had’a fuskokinmu agidan Aljannah, AMEEN. BISSALAM!❤

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *