Tarihin  Kannywood (masana’antar film na Hausa)

Tarihin  Kannywood (masana’antar film na Hausa)

Kannywood Takasance Shahararriya kuma fitacciyar masana’antar shirya fina finan Hausa. Ta kasance babbar masana’antace wacce ke gogawa da masana’antar shirya fim ta nollywood

Sunan Kannywood yasamo asaline daga Kano da kuma Hollywood ( wato cibiyar shirya fina finan kasar amurka) la’akari da sunan Hollywood ne dakuma kano yasanya wa masana’antar suna Kannywood.

Tarihin  Kannywood (masana'antar film na Hausa)
Adam A Zango, Ahmad S Nuhu dakuma Alin Nuhu

An kafa masana’antar ne a shekarar alib 1990, makirkirin sunan Kannywood kuwa shine Sunusi shehu dake mujallar tauraruwa a shekarar alib 1999, shekaru uku kafin akafa masana’antar Bollywood.

Shirye shirye harshen Hausa yafara yaduwa ne a hankali a shekaru 70 zuwa 80 dasuka gabata da shirin da gidan rediyon RTV Kaduna ta Samar a shekarar 1960 a shirin da Dalhatu Bawa da Kasimu Yaro suka fara shiyawa daga bisani Usman Baba Pategi da kuma Mamman Ladan suka fara shirya wa an barkwancin Hausa domin nishadantar da masu ji dakuma sauraron arewa

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN ALI NUHU

Tsarin shirya fina finan Hausa yasamu sauyi a domin Jan hankali masu kallon shirye shiryen a shekarun 1990 zuwa sama.

Sarin yahada da salon Fina finan Bollywood dake India dakuma shirye shiryen al’adun Hausa hakan yasa Kannywood takara sanuwa a kasashen hausawa kasancewar tasirin da fina finan India sukai a wancan lokacin.

Shiri daya fara Karbuwa a masana’antar kannywood kuwa shine shirinnan mai suna “TURMIN DANYA” wadda sake a shekarar 1990, Gimbiya, fatima, in da so da kauna, munkar, badakala dakuma ki yarda dani. Inda kuma aka samu bayyanar jarumai da suka shahara irinsu Ibrahim Mandawari dakuma Hauwa Ali Dodo

Karanta: CIKAKKEN TARIHIN ADAM A ZANGO

Daga bisani a shekakarun dubu biyu zuwa sama an samu Shikowar Jarumai mata dadama masana’antar hakan yakara habaka shirye shiryen Hausa a kasashen Africa.

Zuwa shekarar 2012, kamfanin shirya fina finai sama da 100 sukai regista da kamfanin shirya fina finan Hausa dake jihar kano state wato Kannywood.
Karamar kwamitin tace fina finan Hausa wadda masu shirya fina finan Hausa suka kafa an Kara Saura masa Salo, Girma dakuma karfi inda mai girma gonna Rabi’u Kwankwaso yasa mata suna izuwa “HUKUMAR TACE FINA FINAI TA JIHAR KANO” a shekarar 2001. Sannan Dahitu beli ya kasance a matsayin babban sakataren zartarwa na hukumar.

 

Tarihin  Kannywood (masana'antar film na Hausa)

TASIRIN ADDININ MUSULUNCI GA MASANA’ANTAR

A shekarar 2013, lokacin fitowar kungiyar musulunci ta izala dakuma zuwa mai girma Gomnan kano Mal Ibrahim Shekarau kan karagar mulki kwamitin musulunci ta kaddamar da tsarin yaki da Kannywood. Inda aka dakatar da fina finai dadama da akaga basuyi dadai da tsarin addinin musulunci ba kuma aka tsare wasu daga cikin yan masana’antar dadama a gida yari. Hakan ya kifarda nasarori da dama na masana’antar inda itako masana’antar shirya fina finan kudu wato Nollywood tasamu damar tsere wa Kannywood.

YAN KANNYWOOD

Kawo yanzu masana’antar tanada Sama da Mawaka 1000, jarumai 3000, masu bada umarni samada 200, produsosi 400 dasauransu.

KASASHE

Sama da kasashe koma na kallon fina finan Hausa ciki hadda

-Nigeria
-Niger
-Ghana
-Gabon
-chadi
-Cameroon
-libiya
-dasauransu

Tarihin Kannywood

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *