TATTALINTA CHAPTER 9

TATTALINTA





CHAPTER 9







*A* yadda yaji ta fara magana yasan labarin auran shi yaje kunnanta domin yana d’agawa yaji tace,

“Sannu ango Sultan.”

Yayi fuska kamar beji abinda tace ba sai ma cewa yayi.

“Umma ina ta shirin bugo miki waya sai kuma gashi kin bugo min ya gida..?!”

“Ban sani ba, nace ban sani ba. yanzu Ahmad ni zaka yaudara sabida cimma wani kudiri naka? Karfa ka manta ni mahaifiyar kace nafi k’arfin duk wani abu da zaka yi na kashin kanka amma har kaje kayi aure ba tare da sani ba ko shawara dani ko? Toh ka kyauta kuma ina son gobe-goben nan na ganka a gida Nigeria ina matarka Nadiya take…?!”

Jikin shi ne yayi sanyi sosai ya kuma kasa bata amsar da ta tambaye shi domin shi kanshi ba zai ce ga inda Nadiya take ba dan yayiwa me gadinsu waya yace bata koma can ba. Muryar Umman yaji tana sake tambayar shi jiki a sanyaye yace mata,

“Umma Nadiya bata nan ta wuce O’Marah.”

Baki biyu kenan yayi be san abba ya gayawa Umma ba sai jiyayi tana cewa,

“Karya kake yi domin ni ba haka abbanka ya sanar min ba, cewa yayi min wai ta tafi had’o kayan lefe ina jin haka nasan karya ne domin babu macen da zataji katsam lokaci guda mijinta zai yi aure ta wani ce zata had’o lefe ba duk hakurinta duk kawar da kanta dole sai hallitar nan ta motsa. Sultan ka gaya min gaskiya ina Nadiya take?!”

Rasa abinda zai cewa Umman tashi yayi gashi Nadiya tace karyayi abinda za’a gano wani abun yayi kokarin kare mata martabarta ga Umma tasa shi a cell na dole sai ya fad’i gaskiya a hankali daya rasa mafita kawai sai yayi saurin yin stwice off d’in wayar yana bin screen d’in da kallo yana tunanin mafita don yana cikin tsaka mai wuya.

Juyawa yayi ya fita da saurin shi sabon sim card ya siya ya dawo ya d’ora akan wayar shi, layin Nadiya ya fara kira amma abin takaici stwice off Sultan yayi cilli da wayar a take ta tarwatse sai k’arar fashewa kawai yaji. Tafikan hannunshi ya sanya a saman goshinshi ya dafe da k’arfi sabida ji yayi kamar zai dare mai gida biyu, wata dabara ce ta fad’a mai ya k’arasa wajan wayar da sauri ya d’auka nan yaga screen d’in yayi wani daga-daga ya cire sim d’in ya kuma fita.

Sallah isha’i ya farayi sannan yaje ya kuma siyan wata k’aramar wayar, number’n mai gadin gidan hajiya kaka ya kira yace ya had’a su kasan cewar ita bata da waya a cewar ta duk wanda zai nemeta yazo da kafafuwanshi. Lokacin da mai gadi yaje tana zaune a parlour yayi mata bayani cewar Sultan ne ta k’ar6a cike da fara’a kamar a gabanshi take tace.

“Muhammadu d’an albarka, Muhammadu yaron kirki Allah yayi maka duk wani abu na alkairi a cikin rayuwarka ka gamamin komai yaron kirki ko yanzu na mutu wallahi an cika burina ya kuke?!”

Wai sai da ta gama fad’ar ta cikinta sannan zata bari a gaisa, murmushin jin dad’in addu’o’inta da tayi mai yayi kafin ya amsa mata,

“Lafiya ba Lafiya ba hajiya kakata.”

“Subhanallahi me kuma ya faru Muhammadu.?!”

Hajiya kaka ta tambaya tana dafe da k’irjinta, Sultan ya numfasa yace, 

“Hajiya ina cikin fushin Umma wallahi, kin san babu wanda ya san da auran nan, itama abba be gaya mata ba sai yau daya koma na rasa yadda zanyi wallahi hajiya Umma fushi take yi dani.” 

Story continues below


Ran hajiya kaka ya 6aci ta fara fad’a, 

“Aikin banza dana wofi kawai, wallahi Muhammadu wannan uwar taka bata kyautawa. Ina ruwanta toh? Ko ita za’a yiwa kishiyar ne? Naji ikon Allahh kasanta da jarababban kishi tsiya dan lokacin da mahaifinka zai k’aro aure haukan da ta dinga yi a gidanku ba zai fad’u ba sabida har…” 

Bai bari ta k’arasa ba ya k’atse ta sabida shi ba tarihi ko labari ya tambaye ta ba kuma ma ai ya sani dan yana da wayo aka yi shine zata taso mai da maganar, cikin halin damuwa yace mata. 

“Hajiya nifa bashi nake son ki gane ba, so nake yi ki kira Abba kuyi magana yaje ya taushi zuciyarta kafin na dawo, wallahi hajiya idan na dawo tana iya cewa sai na saki wata a cikin su, nasan Umma zata iya cewa sai na saki Nadiya akan cewar na yaudare ta ko nayi wani abun ko kuma tace na saki baby kuma ba zan iya ba please hajiya ki nunawa Abba yadda zaije ya lalla6ata ba tare da taga laifina ba gashi dama ba wani jituwa suke yi da babyn ba.” 

Hajiya kaka ta numfasa tare da fad’in. 

“Na gane ai Muhammadu, karka damu kai dai kuyi kokari ku dawo gida.” 

Ta fad’a cikin kwantar da hankali yace, 

“Toh hajiya insha Allah Umma tace gobe take son mu dawo shi kuma abba yace jibi so yanzu gobe zanje na samu nayi mana cuku-cukun tahowa idan be samu ba sai jibin dole.” 

“Allah ya nuna mana zan neme su karka damu.” 

Daga haka suka yi sallama wanda sai a lokacin Sultan yaji zuciyar sa tayi mai sauk’i tashin hankalin shi ya ragu. 

…… 

Tsaye yake a cikin d’aki sai faman buga hannu yake jikin d’ayan, shi kad’ai ne amma sai faman uban gumi yake yi ya k’arasa kan gadon da ya ta6a ajiye ta a kai yaje yana kallonshi a gyare yake tad’al-tad’al kamar ka lashe ya zauna a gefen gadon yana shafa saitin da take d’ora kanta yana shafa gurin a fili yace. 

“Balqees why (me yasa)..? Me yasa kikai min haka? kece kika yaudareni ko kuma wannan yaron da yake mafarkin ya aureki ah…?!” 

Kwanciya ya kuma yi a gurin tare da janyo pillow ya rungume yana cizon le6ansa idanunsa sunyi jawur ya kuma cewa, 

“Dama na san soyayya kuke yi Qees-Qees, amma kuka raina min hankali wajan nuna cewar ba haka bane. Ahmad me yasa kake son shiga gona ta ne? me yasa…?!” 

Ya fad’a da k’arfi tamkar wani zararre shi kad’ai a cikin d’akin. karaf idanunshi ya kai kan wani d’an medium picture d’inta da yayi mata enlargement dashi da bireziyar ta daya zakala a jiki kamar yadda India suke sagale follower’s jikin hotan wanda ya mutu shima haka yayi mata yaje ya zare bira d’in tare da d’aukar hotan yana kallo. Bacci take yi idanunta a rufe tayi masifar yin kyau kamar irin ‘ya’yan larabawan nan ‘yan kubul-kubul, ya lashi lips d’in sa tare da zaro ido tamkar wani kumurcin zaki da karfi ya cilla shi nan da nan glass d’in ya fashe a take sannan yayi cilli da bira d’in yana wani huci. 

Yusif kenan d’an gidan daddy, tun lokacin da daddy ya sanar dashi abinda yaje yaji shi kenan duk yabi ya damu kanshi zuciyar shi tak’i yin sukuni hankalin shi ya tashi yana zaune a office d’in shi ya dawo gidan cikin wata irin murya yace. 

“Balqees ina sonki, ina kaunarki me yasa kika fi son Ahmad a kaina? Me yake miki wanda ni kike ganin bazan yi miki shiba? Wallahi Zaku dawo zaku gane kuranku zaku gano kun yaudari Yusufa….!” 

Yana fad’in haka ya bar bedroom d’in, mota ya shiga ya wuce gida cikin 6acin rai. Irin kudun da yake yi kuwa tamkar ta6a66e shi bema san inda yake sanya motar ba. Yana ta tsula gudu yaje ya daki wata katuwar mota sai gashi a k’arkashinta, nan mutane suka taru ganin ta fara hayaki yasa aka zaro shi duk jini mutane suka d’auke shi sai asibiti. 

Gabaki d’aya hankalin ‘yan gidan su ya tashi lokacin da suka ji labari gashi daddyn baya k’asar yana dai hanyar dawowa, sannan basu sanar da kowa ba hakan yasa ko hajiya kaka bataji labari ba. Sai da suka gama waya da Sultan ta bawa mai gadi wayar shi tayi sallan magriba sannan Adda Aisha taje gidan bayan sun gaisa take sanar da ita abinda ya faru da Yusif d’in cikin tashin hankali suka tafi asibitin tare. 

….. 

Washe gari tunda asuba sultan ya fara cuku-cukun yadda zasu samu sukoma a ranar cikin ikon Allah kuma ya samu, gidan aunty Sa’adatu yaje har lolacin da mutane dankam a gidan yayi sallama da ita tare da sanar mata cewar zasu wuce gida k’arfe d’aya da rabi, taso ya bar Balqees d’in amma ya nuna mata rashin yiyuwar hakan domin shima ba yin kanshi bane umarnine tace shikenan zata shirya kafin lokacin. 

Janshi tayi har cikin gidan da kyar ya yadda sabida yawan mutane, kawai yaga ta kaishi d’akin da Balqees take kwance tana bacci. Kallonta yayi tana ta bacci hankali kwance sanye take cikin sleep dress riga da wando white (fari) da d’ishi-d’ishin pink & black (ruwan huda da bak’i) kayan dai-dai ita gashin kanta daya sha gyara duk ya fara tashi a hankali ba tare da ya ankara ba sai jinshi yayi yana matsawa kusa da ita har ya k’arasa bakin gadon. 

Gefen kuncinta ya shafa cikin baccin ita kuma ta sargafo shi tare da rungume hannun kamar za’a kwace dama haka take bacci mugun son jikina da ita hakan yasa ba’a kwanciya kusa da ita sabida d’ora kafa, shak’aro mutum ko nanikewa a jikinshi dan tasha matse humaira Allah yayi dai tana da tsawun kwana bata mutu ba. Shi abin ma dariya ya bashi hakan yasa ya d’an dara ya kuma sanya d’ayan hannun yana k’ok’arin zare d’ayan gabaki d’aya ta juyo tare da maida kanta kan cinyar shi ya zaro ido cikin sauri ya kalli kofa, da azama kuma ya zare mata kan ya mayar dashi kan pillow tare da mik’ewa tsaye yana kallonta. 

Wayarta ya gani a gefenta ya zura hannu ya d’auka ya bud’e nan ya hangi k’atan hotansu wanda yayi musu ranar da zasu je dinner d’in su Yaya Jamal sai dai da pattern a jiki wayar ya maida idonshi ya kalleta shi sai yanzu yake tuno wasu abubuwan da take yi a baya lallai na so ne amma shi duk ya kasa ganewa a tunanin shi kawai shakuwa ce. Ajiye wayan yayi sannan ya fita yana jin kaunar da yake mata ada tana canzawa zuwa wani sabon al’amari. 

Misalin k’arfe 12:00pm na k’asar ethopoeia Sultan ya dira a kofar gidan aunty Sa’adatu yana suka suka had’u da Afrah ta k’arasa wajan shi tana murmushi tace. 

“Angon mu! ashe yau zaku wuce, amma ai da an barma na ita sai mu kawo ta da kanmu.” 

Murmushi yayi tare da cewa, 

“A’ah da kune kuka kawo ta?!” 

Afrah tayi dariya sosai kafin tace. 

“Toh ai Yaya Sultan salon ne ya canza, please dan Allah kubarta ma kawota wani satin.” 

“Noh tare zamu tafi an kusa resuming gara mu tafi, shiga kice ina jiranta tazo mu wuce.” 

Wucewa tayi tana mai dariya wanda ya rasa ko ta meye ya d’aga kafad’a tare da komawa gefe yana jiran fitowarta mata sai kallonshi suke yi sabida ba karamin had’uwa yayi ba, ba wanda zai ganshi yace yana da aure bare ‘ya. Fito da ita akayi lullu6e kuma da alama kuka take yi dan tasha fad’a gurin ‘yan uwan Ummin ta aunty Sa’adatu ta kama hannunta tare da had’e su ana Sultan ta kalleshi tace. 

“Ahmad ga amanar marainiya a hannunka, mun san kayi kana kuma yi muna son ka k’ara Allah ya baku zaman lafiya sai munzo next week insha Allah.” 

Kanshi a k’as yace, 

“Thank you (na gode) aunty Sa’a Allah ya kawo ku lafiya.” 

Duk suka ce mai Amin sannan suka shiga mota sabuwar dal ta mijin aunty Sa’adatu Ahmad zai kaisu airport, duk baya suka zauna Afrah ta shiga gaba ita da Ahmad sannan suka ja motar suka bar gidan Balqees na jikin Sultan tana kuka mai ratsa zuciya…..

    
    Suna zuwa airport Sultan da Balqees suka fito, Balqees ta kankame Afrah kamar zata shige jikinta ganin suna 6ata lokaci yasa Sultan yi mata magana akan tazo su wuce, k’i tayi sai da yaje ya 6an6areta yaja hannunta sannan suka shiga ciki inda zasu wuce su shiga jirgi. 

Suna zuwa kuwa ba dad’e kasan cewar sun dad’e a gida yasa har lokacin yayi, gashi gata haka suka zauna still dai tana ta kuka har cikin zuciyar Sultan yake jinshi ya sak’alo hannunshi cikin nata ya matsar da kanshi kusa da kunnanta yana faman lallashi, da kyar ya samu tayi shiru ana fara tafiya tayi bacci shi kuma ya fara tunanin yadda zai tunkari Umman shi. 

Suna sauka a kano hankalin Sultan ya kuma tashi, taxi ya samar musu suka shiga yace a wuce dasu gidan hajiya kaka dan gara yakai Balqees can sannan shi kuma ya nufi gida gurin Umma yaji me zata ce, 

Suna zuwa suka tarar da ita tana bacci da alama kuma tana jin dad’in shi dan haka Sultan ya kalli Balqees da tayi sukuku ya kamo kafad’unta tare da rankwafawa saitin fuskarta yace. 

“Menene..?!” 

Kad’a mai kai tayi sannan yace, 

“Ki zauna anan kinga Nadiya bata gida sannan zanje gida gurin su Umma zan dawo anjima yanzu kiyi wanka ga abinci nan na gani kici idan hajiya ta farka kice mata zan dawo kinji ko…?!” 

Balqees ta kuma kad’a mai kai sannan ya d’auki small jakar kayanshi ya juya, sai da yaje bakin k’ofa sannan ya juyo ya kalleta itama tana tsaye inda ya barta tana kallonshi, murmushi ya sakar mata ta sunkuyar da kai sannan ya fita yanajin kamar karya tafi ya barta sabida tausayin ta da yaji ganin yadda auranta ya kasance bayan ba haka yake mafarkin yaga ya aurar da ita ba. 

Gidan su ya nufa yana shiga ya tarar da motar abba a compound da alamar yanzu shima ya shigo, shiga ciki yayi da sallama suka amsa domin su Yaya Jamal ma suna nan shida matar shi waheedah da boy d’insu. 

K’arasawa yayi ciki Jamal ya bashi hannu suka gaisa sannan waheedah ma ta gaida shi ya amsa yana d’aukar yaron da yake ta mik’o mai hannu, abba ya gaidar sannan ya gaida Umma ta amsa da kyar shima dan kar abba yayi magana ne da baxata amsa ba Jamal yace. 

“D’an uwa ina kuma amaryar ka barota?yanzu muka zo mukejin labari.” 

D’an murmushi Sultan yayi yanawa boy d’in wasa Umma kuma ta ware kunnuwa tana sauraran abinda zaice, kamar ya gano sai yace, 

“Lafiya lau bro me kuka zo yi ko hutu ka samu ne?!” 

Cikin rashin damuwa Jamal yace, 

“A’ah wallahi munzo dubiya ne ta Yusif.” 

Da mamaki sultan ya kalleshi cikin son jin k’arin bayani, ganin hakan yasa Jamal gane cewar beji labari ba dan haka yace mai. 

“Eh mana jiya ya samu accident wallahi yaji ciwo sosai goshinshi ya fashe sannan ya samu karaya a hannu da kafanshi yana cikin mawuyacin hali sosai.” 

“Innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un, Allah ya bashi lafiya ya kuma kare gaba bari zanje anjima insha Allahu.” 

Tashi abba yayi ya fita kamar jira Umma take yi yana fita ta maida hankalinta wajan Sultan wanda yak’i bari su had’a ido da ita take ta zabga mai harara tace. 

Story continues below


“Bazan fasa ce maka ina Nadiya ta tafi ba dan kuwa bayan amanace a gurinka muma muna da hakk’i muji inda take, ka gaya min ina ta tafi Ahmad..?!” 

Shiru yayi ya rasa me zaice Yaya Jamal ya kalleshi har zai yi magana sai yayi shiru ran Umma ya kuma 6aci ta fara fad’a ta inda take shiga ba tanan take fita ba amma still yayi shiru ta d’ora da cewa. 

“Karkaji hajiya kaka ta kirani d’azu harda cewa wani indai nace ka saki wata a cikin su a bakin aure na ka nemi ka k’ara 6atamin rai ka gaya min ina take…?!” 

“Umma wallahi ban sani ba nima sam tak’i sanar dani amma nasan ta dawo Nigeria kuma kamar yadda na gaya miki tace ita zata had’a kayan lefe sai ta had’o zata dawo gida.” 

“Naji amma Ahmad dan Allah ka gaya min gaskiya me yaja maka auran wannan yarinyar wadda idan auran kyauye kayi yaci ace ka haifeta yarinya ko kugunka bata kaiba amma wai ita ka aura..?” 

Shiru yayi babu amsa ran Umma ya kuma 6aci, waheedah na gefe dariya nasan kwace mata jin abinda Umma tace wai ko kugunshi bata kaiba Umma tace. 

“Toh ka tadani inda zaka saka ta ko kuma a gidan kakar taku zata zauna kai ka dinga zuwa can?!” 

“Umma…!” 

Ya kira sunanta cikin mamakin abinda tace, shafa kai yayi yana cizon le6anshi yayi shiri. ganin bashi da niyar cewa komai yasa ta mik’e ta shiga cikin d’aki, Jamal ya kalleshi cikin tausayi ganin duk ya rasa mafita yace. 

“Ahmad meye matsalar ne?!” 

Sultan ya mik’e tsaye tare da ajiye boy d’in yana cewa. 

“Babu matsalar kawai Umma ce ta damu sai tasan inda Nadiya take, ita kuma tace bata son kowa yasan inda take dan Allah ya zanyi? Nadiya nason tayi nisa dani ne badan komai ba sai dan kartaji zafin abinda ya faru ni na gano hakan, nafi Umma shiga damuwa akan Nadi ni nasanta na kuma son muhimmancin ta a gareni amma ya zanyi? Nima nabi abinda take sone dan karna takura mata tunda nasan ban kyauta mata ba nima abin ne yazo min lokaci d’aya.” 

“Allah sarki ai gaskiya ba’ayi mata halacci ba Yaya, kofa shekaru uku baku rufa ba amma wai har anyi mata kishiya, kuma ma da yarinyar da ta d’auketa tamkar ‘yar uwarta. Nifi wallahi shi yasa ko ‘yar aiki nak’i yadda akawo min gara almajiri haka kurum ayi maka sakiyar da ba ruwa.” 

Cewar Waheedah tana faman zak’alkalewa tamkar ita aka yiwa kishiyar, murmushin takaici Sultan yayi cikin 6acin rai da takaicin kalamanta ya kalleta yace. 

“Shi yasa nayi alk’awarin inda ta dawo gida babu wacce zata zomin sabida kar a sauya min halin mata daga sassanya zuwa zazzafa, ina son Nadi kuma hakan da tayi ya kara min soyayyarta a cikin zuciya ta, na bata wani katon fili a cikin zuciyata da rayuwata gaba d’aya.” 

Yayi maganar cikin nuna tabbacin abinda yake cikin zuciyarshi, Waheedah ta ta6e baki tare da cewa, 

“Allah ya huci zuciyarka Yaya Sultan.” 

Shareta yayi ya fita daga parlour’n, napep ya tara ya wuce can gidan shi ranshi duk babu dad’i yana zuwa bedroom d’in shi ya wuce yayi wanka sannan yayi sallan dake kanshi ya zaro waya, sim d’inshi yasa ya fara neman layin Nadiyan tana ta ringing amma ba’a d’aga ba sai kawai ya tura mata text message kamar haka. 

_”My Nadi dan Allah badan ni ba ko halina ba ki temaka ki dawo gida na rasa inda zan ra6a naji dad’i a cikin raina idan ba so kike kiji mummuanan labariba.”_ 

Nadiya kam bata gani ba sai da ta shigo d’akin kasan cewar tana parlour suna hira, tana shiga d’aki wayar ta d’auka dan ta kunna a tunaninta a kashe ta barta, miss call ta gani da yawa harda na Ummi d’in ta sai ta hango sms d’in Sultan ta bud’e ta karanta tare da ajiye wayan ta shiga bathroom, wanka tayi tayo alwala sannan tayi sallah har zuwa dare bata yi mai reply ba dan bata ma san abinda zata gaya mai ba. 

Ana yin sallan magrib sultan ya shirya suka je asibitin da aka kwantar da Yusif, kwance suka tarar dashi yana bacci kanshi yasha bandege su Mom suna zaune a waje sai Al-eemin dake ciki kusa dashi kasan cewar d’akin duk maza ne masu karaya. 

Sun jima sosai a asibitin kafin suyi musu sallama su tafi, Yaya Jamal ya sauke Sultan a gidan hajiya kaka shi kuma suna gaisawa ya tafi don d’aukar Matar shi su tafi gidan shi wanda dama ya gamashi sabida irin haka idan sunzo. 

Kallon shi hajiya kaka tayi cike da so ita kuma Balqees tana kwance kanta a saman cinyar hajiyan tace. 

“Wallahi Muhammadu so kake ka kasheni da farin ciki, sai gashi ina tashi naga baby a kusa dani duk na d’auka mafarki ne sai da ta ta6a sosai na yadda d’an albarka ashe kun dawo.” 

“Eh hajiya.” Sultan ya fad’a yana faman kallon Balqees wadda ke faman danna waya tamkar ma bata ganshi ba, hajiya kaka tayi ta sanya mishi albarka kafin su d’an ta6a hira. 

Har suka gama yayi wa kaka sallama Balqees batayi musu magana ba, kallonta yayi cikin mamakinta yace, 

“Baby ko sallama babu?!” 

“Sorry Yaya zulkallain sai da safe.” 

Tafad’a tana kallonshi daga kwance, wani kallo ya wurga mata sannan ya ta6e baki ya fita. 

Washe gari misalin k’arfe sha biyu na rana Sultan yana kwance a parlour’n gidan shi duk ya rasa abinda yake mai dad’i sai tunani yake da sake-sake. kukan da yaji daga bayan shi ne yasa shi saurin juyawa yana kallon k’ofar. Zumbur ya mik’e yana kallonta tana faman sakar mai murmushi humaira kuma sai so take a sauketa ta zauna a k’asa Sultan yayi saurin k’arasawa tare da yi musu wata wawar runguma yana sauke numfashi a hankali. 

“Abban humairah karmu fad’i fa.” 

“My Nadi barni..barni naji d’umin jikinku nasha wahala I miss you so much Allah ya gani nasha wahala my Nadi.” 

“Toh ya isa haka muje mu zauna ban maji duriyar  amarya ba ko bacci take?!” 

Suna manne a jikin shi haka suka je kan  kujera suka zauna, sauke humaira Nadiya tayi tana kallonshi ganin yadda ya manne mata kamar wani k’aramin yaro da alama yayi missing d’inta kuma babu abinda ya shiga tsakanin shi da Balqees, a hankali ta d’ago mai kai suka had’a ido tace.. 

“Wai lafiyar ka lau kuwa?!” 

Kwantar da ita yayi akan kujerar idanunshi sun k’ank’ance yana faman murza fuskarshi a jikinta yace. 

“Nadi ya za’ai nayi lafiya kin min yaji? Nadi kiyi min afuwa wallahi badan bana sanki na auri baby dan Allah karki tsaneni ko ki goge soyayyata a cikin zuciyarki please wallahi ina sonki.” 

Hawaye suka ziraro mata kanshi yana kan kirjinta, yadda take ajiyar zuciya ne ya nuna mai cewar kuka take gefe guda humaira sai wasanta take yi Sultan ya d’ago yana kallonta ta sakar mai murmushi sai yaji wani mugun tausayinta soyayyarta ta taso mai ya mik’e ya shiga d’akin da yake na Balqees ya kwaso kayan wasa lokacin da nepa yaje ya kunna carton sannan ya d’auki Nadiya ya wuce da ita bedroom d’inshi, kan gado ya kwantar da ita sai faman kallonshi take tana ganin ikon Allah. 

Wajan wardrobe d’in shi taga yayi ya bud’e ya d’akko wani d’an akwati na zobe ya k’arasa kan gadon ya kamo yatsanta na tsakiya ya sanya mata tare da cewa……

“My Nadi kece mace ta farko da bakina da zuciya suka fara furtawa kalmar SO, ni kaina nasan ina sonki ina kaunarki kice mace ta farko dana fara dank’awa duk wani sirrina ba kuma na iya 6oye miki komai daya shafi rayuwata kamar yadda kema kike min.” 

Yayi shiru yana share mata hawayen da suke ziraro mata a fuska wanda ita kanta ba’a son ranta take yin shi ba domin tun daga zuciyarta yake fitowa bawai iyakar shi cikin idanunta ba. Gefenta ya koma tare da janyota jikin shi ta lafe a kirjinsa shi kuma yana shafa dogwan gashinta daya sha kananun kitso fatar kannan tayi kal sai walwalin mai takeyi ya cigaba da cewa. 

“Tunda nake ban ta6a zaton zan kara aure ba domin babu abinda kika gaza yi min, kina da duk abinda nake so matata ta kasance Nadi, toh me zai sa nayi miki kishiya? Wallahi Nadi ki yarda dani tunda nake da baby ban ta6a kawowa ko a cikin zuciyata ba cewar zan aureta wallahi ban ta6a ba Allah shine shedata (sai kuma ku reader’s)lol.” 

Matsawa tayi ta kuma shigewa jikinshi shima ya sake mak’alota suna jin d’umin junansu na tsawon lokaci, Nadiya na k’ok’arin yin magana suka jiyo kukan Humaira cikin sauri Nadiya ta fara k’ok’arin zare jikinta ya rik’eta ta zaro mai ido tare da cewa. 

“Humaira zan d’akko.” 

Sumbatar lab6anta yayi yana kanne mata ido d’aya yace, 

“Gaskiya angel ta kwafsa min ina cikin jin d’umina wai yaushe zaki yaye tane Mu kaita gurin Umma?!” 

Yayi maganar yana yatsina fuska Nadiya ta jamai dogon hancin shi tare da sake janye jikin nata ta mik’e tana fad’in. 

“Lallai duka-duka nawa take da zan wani yaye ta gaskiya ba yanzu bama.” 

Koda ta fita bata dawo ba a parlour ta zauna tana bata nono yayin da ta kafawa yatsanta daya sanya mata wani had’add’an zo6en zinari mai d’an karan kyau da tsada, jin shiru ne yasa shi shima ya fito daga d’akin hannunshi rik’e da laptop dai-dai lokacin ita kuma Nadiya takai zo6en bakinta tana sumbatar shi dan kyautar ba karamin dad’i tayi mata ba. 

Murmushi yayi yana daga bayanta kafin ya fara gyaran murya ya k’arasa kusa da ita ya zauna kasan cewar tana zaune ne a two seater, ai kuwa humaira na ganinshi ta fara tsalle tare da komawa wajanshi tana dariya, kyakyawar yarinya ce dan duk ta d’ebo kyawun su gashi ne dai har lokacin sai an tattaro shi ake iya sa d’an soso d’in nan. 

Wayar Nadiya ce dake cikin jakarta ta fara ringing, mik’ewa tayi taje ta d’auka tana dubawa taga sunan Ummi cikin murna da zumud’i ta d’aga bayan ta koma ta zauna, tashi Sultan yayi zuwa d’aki zai d’akko abu Nadiya taji Ummi na cewa. 

“Kin dawo ko Nadi?toh ki gagauta zuwa gida ina son ganinki yanzun nan bana son ki k’ara sake koda awa d’aya a gidan Ahmad.” 

“Ummi lafiya dai ko?!” 

Nadiya ta tambaya cikin damuwa, a harzuk’e taji Ummi tace, 

“Ban sani ba idan kinzo kyaji za kuma ki gani shashasha kawai.” 

“Toh Ummi bari abban humairan yazo sai na tambaye shi.” 

Nadiya ta fad’a jikinta duk yayi sanyi kasan cewar bata gayawa kowa zancen auran Ahmad ba amma da yake zancen duniya baya 6uya ko kaika d’ai kayi zance sai kajishi a kunnan wani Ummi taji tana cewa. 

Story continues below


“Au har sai yazo kin gaya mai tukunna zaki zo kiran nawa Nadi?!” 

“A’ah wallahi Ummi ba haka nake nufi ba amma ai kinga bazan fito ba batare da na sanar mai ba kuma fa yana nan gida bari na gaya mai.” 

“Yanzu idan be barki ba kenan ba zaki zo bako Nadiya?!” 

“A’a Ummi wallahi ba haka nake nufi ba amma ai kinga tunda a kark….” 

Bata k’arasa ba Ummi ta katseta cikin fushi tace. 

“Kar Allah yasa kizo ki zauna kinji me miji..!” 

Dai-dai nan Sultan ya fito rik’e da humaira yaji Nadiyan na cewa, 

“Dan Allah Ummi kiyi hakuri ba haka…” 

Tuni ta kashe wayar Nadiya jiki ba kwari ta zare wayar tana bin ta da kallo, k’ara sawa Sultan yayi ya zauna kusa da ita tare da janyo ta jikin shi yana tambayar ta ganin yanayin da ta shiga. 

Kanta na kirjinshi ta sanya hannu tana shafar kirjinshi cikin sanyin murya tace, 

“Abban humaira Ummi ce take nema na yanzu, dan Allah ka barni naje yanzu zan dawo insha Allahu kaji?!” 

Nan da nan hankalin Sultan yayi mugun tashi ya ajiye humaira a k’asa ya kalli Nadiya da ta kasa kallonshi yace, 

“Lafiya dai ko Ummi take nemanki, gashi yanzu kika dawo ko wanka bakiyi ba bare kici abinci.” 

“Ban sani ba nima sai naje zanji karka damu banajin yinwa naci abinci a cikin jirgi, taho muje ka kaimu na gaji bazan iya tuk’i ba yanzu.” 

Cike da damuwa Sultan ya kalleta tare da d’ago kanta ya sanya idanunshi a cikin nata murya na rawa yace, 

“Dan Allah Nadi dan girman Allah karki bari a rabamu nasan kirin da take miki bazai wuce na aure na ba, please Nadi karki bari kinji?!” 

Hawaye ne suka zubu mata tana murmushi wanda ya kasa gane inda ta dosa, kallonshi tayi tare da cewa. 

“Toh naji yanzu dai ka amince min naje kiran da Ummi take yi min.” 

Jikinshi ya rungumu ta yana shafa kanta, baya son taje amma yasan idan ya hanata zata zarge shi da wani abun duk da ko hanata yayi baza tayi mai gaddama ba domin macace mai tsananin biyayya dajin maganar shi tamkar aya dan haka yace, 

“Na barki Nadi muje na kaiki idan yaso zuwa dare sai naje na d’auke ku.” 

D’agowa tayi daga k’irjin nashi tare da shafar kuncinshi tana d’an murmushi tace. 

“Nagode abban humaira bari na d’akko d’ankwali na.” 

Tashi tayi ta nufi hanyar bedroom d’in shi, bin bayanta yayi da kallo zuciyar shi na k’ara kaunarta sai dai hankalinshi a tashe yake akan zuwanta gidan su amma ba yadda zai yi ta fito tana d’aura d’ankwalin tare da yafa mayafinta shima yasa t.shit d’in shi suka fita. 

Har cikin get ya kaita Nadiya tayi tayi dashi akan su shiga tare amma fur yak’i yadda yace sai yazo d’aukarta, sai da yaga shigarta ciki sannan yaja motar ya tafi yayi gidan hajiya kaka dan yana son ganin Balqees. 

Tana shiga ta tarar dasu Ummi da yayanta Imran sai sai k’anwar babanta aunty Amina da Nabeela k’awarta babu wanda yayi mata oyoyo sallamarta kawai suka amsa a ciki-ciki sannan Nabeelah ta k’ar6i humairah, bata yi mamakin ganinsu ba da kuma rashin nuna jin dad’in zuwanta ko akas’in haka ba ta samu guri ta zauna tana musu yak’en murmushi. 

“Ummi ya gida? Yaya imran ya aiki ya shiga ruwa? Aunty Amcy ina su little Dad da ikram??!” 

Still babu wanda ya amsa mata gara ma imran yayi murmushi, ganin duk sunyi shiru ne yasa ta kuma yin magana. 

Story continues below


“Wai meyake faruwa ne duk sai magana nake kunyi shiru? Ina Papa?!” 

“Eh dole kiji munyi miki shiru, wai Nadiya yaushe zaki gane kanki har ki dinga sanin darajar kanki ne ah? Tun kafin kiyi aure kika mik’awa namiji yardarki da amincewarki, kika fallasa mishi duk wani sirri naki yau gashi namiji ya nuna miki irin halinsu ga da abinda Ahmad ya saka miki dashi nan ta hanyar auran yarinyar da kika rik’eta tamkar yazid, wannan shine hali na farko da d’a namiji ya fara nuna miki sabida amincewar da kika yi mishi…” 

Cewar aunty Amina cikin fad’a, nan da nan jikin Nadiya yayi mugun sanyi kwalla ta fara taruwa a cikin idanunta taji Ummi ta d’ora da cewar. 

“Nadiya kin riga kin bud’ewa mijinki cikin ki ya riga yaga komai na cikinsa shi yasa zai dinga yi miki abubuwa cikin nuna rashin shakarsa gareki, wallahi baki san halin maza ba shi yasa tun kafin auranku na dinga haska miki illar wannan alak’ar tashi da ta yarinyar nan amma kika kasa ganewa, yanzu baki ga komai ba sai ta tare a gidan, yanzu yana nuna miki babu tamkarki a zuciyar shi itama idan yaje gurinta haka zai gaya mata k’ila ma ya ninka kalamai na kwantar da hankali a wajanta akan wanda ya gaya miki. Nadi namiji hankaka ne gabanshi fari bayanshi bak’ikk’irin haka yake.” 

Ita dai Nadiya shiru tayi gabanta banda bugawa babu abinda yake yi, sosai ta dinga jin tsoran kalaman su sai dai ta fara addu’ar neman tsari a cikin zuciyarta kafin tayi karfin halin tattaro ‘yar guntuwar nutauwarta tace. 

“Toh ya kuke son nayi?so kuke na tattaro kayana na dawo gida sabida mijina zai yi aure? Wallahi Ummi Ahmad ba’a son ranshi hakan ya faru ba had’a su aka yi nasan kuma had’in Allah ne tayaya zanyi jayayya da hakan…?!” 

“Au haka ya kitsa miki? Me yasa da yasan baya so beyi gaddama ba ya yadda aka d’aura?ke Nadiya ki dena yadda da maganar namiji makarya ci ne wallahi.” 

Aunty Amina ta fad’a a kufule tana jin tamkar ta maketa, kallonta Ummi tayi itama ranta a 6ace ta d’ora da cewa. 

“Nadiya na rasa gane wani irin zuciya ce dake, na kasa gane wani irin so kike yiwa yaron nan, na rasa yadda zan nuna miki ki gane yadda halin maza yake wallahi tallahi..” 

“Wallahi Ummin imran yaron nan ya riga ya shanye ta, idan banda haka ba ta yadda za’ayi ace anyi miki kishiya amma kin gaza nuna bak’in cikin ki akai ya riga ya gama mallaketa.” 

Aunty Amina ta fad’a tana huci tamkar wadda tayi dambe, Nadiya ta jijiga kai tare da share hawayen fuskar ta, basu san tafiso jin zafin abinba amma tana kai zuciyarta nesa ne sabida k’arfin addu’a da kuma tuna cewar komai na duniya yin Allah ne cikin kuka tace. 

“Ashe ni duk abunda nake yi bashi da kyau a cikin idanuwan dangina, ashe duk iya kokarina na kare musu martaba da k’imar su hakan baya yi musu dad’i? Ummi a tunani na idan nayiwa mijina biyayya aka kalleni za’a ace Allah sarki wance yarinyar kirki ai zuriar gidan wane ce suna da mutunci da dattaku, ashe kunfi son nayi rashin d’a’a da nuna haukan kishi na rashin hankali a kalleni ace ai ‘yar gidan wane ce dama haka suke basu da tarbiya bare d’a’a, ace baku kaini islamiya ba, ace ina ja da ikon ubangijina..?” 

Ta kuma rushewa da kuka, da ace zasu iya bud’e zuciyar ta da zasu gano cewar basu kaita jin d’acin faruwar hakan ba amma ta danne aunty Amina tace, 

“Ya isa mu ba haka muke nufi ba karki yi mana wa’azi.” 

“Karya kuke yi Amina yarinya tafiku gaskiya….!” 

Gabaki d’aya suka juya suna kallon maigidan da ya shiga, ya dad’e tsaye a bakin k’ofar yana jin duk abinda suke fad’a daya ji zasu sauya mata zuciya ne yasa shi bayyana kanshi ya shigo ranshi a matukar 6ace, zama yayi a kusa da Nadiyan wadda ta kuna fashewa da kuka ya rungumota jikin shi yana lallashinta yana kallon su Ummi fuskarshi cike da 6acin rai. 

Kallon aunty Amina yayi cikin nuna ba wasa yace, 

“Ke! Amina tashi ki tafi gida yanzun nan.” 

“Yaya na tafifa kace?!” 

“Eh kije gidan ki nake nufi idan bazaki gane ba kai Imran tashi ka kaita.” 

Ran Amina ya 6aci tabi yayan nata da kallo gashi ba halin yin rashin kunya dan shine kamar uba yanzu a gurinsu kasan cewar shine babban su. Tashi tayi tare da zarar mayafinta fuuuuu tayi waje ko imran d’in bata jira ba tayi tafiyar ta. Kallon Ummi yayi tare da mik’ewa tsaye yayi hanyar bedroom d’in shi yana cewa. 

“Ina son ganinki Asma’u.” 

Tashi tayi tabi bayan shi yayin da imran ya koma kusa da Nadiya ya rik’o hannunta tare da cewa. 

“Sorry sister kinji share hawayen naki.” 

Nadiya ta share hawayen fuskarta tana murmushi wanda yafi kukan da take yi ciwo da rad’ad’i tace. 

“Yaya gani suke yi kamar ban damu ba ko?hmm da kuma damuwar na nuna Yaya imran da yanzu suna nan suna bani hakuri amma nayi hakurin sunga gaza wata ya suke so nayi?na dawo gida na zauna ko kuma nayiwa abban humaira rashin kunya ya dinga ganin rashin tarbiya ta?” 

“Shhhhhh Sister ya….
    
    “Shhhhhh! Sister ya isah haka kiyi shiru ki dena kuka, kinyi hankali a ciki wallahi domin ba kowace mace zata iya jarumtarki ba, Nadi zanyi alfahari idan har na samu mata mai irin halinki kiyi min addu’a Allah ya bani mata tagari kamarki nima kijin ko?!” 

Hawaye ta share da sauri tare da cewa, 

“Da gaske Yaya kana son ka auri wanda zata yi maka irin abinda nayi yanzu?!” 

Imran Yace “kwarai ma kuwa sister domin haukan mace baya hana k’ara aure, ki duba ki gani da idon basira hakuri be sa ank’i yi mak’i kishiya ba sai rashinsa?biyayya bata hana anyi ba sai tashin hankali? Bari na baki wani labarin wani friend d’ina ina jin ma kin sanshi wannan wanda muke zuwa dashi broader idan kunje min visiting kin gane shi ko?” 

Nadiya tayi shiru tana tunani tare da goge sauran kwallarta can ta numfasa tace, 

“Wannan Bilal A hydar d’in nan ko, shi kake nufi?!” 

“Exactly sister shi, kinsan dama yana da aure, to daya tashi yin ta biyu sai uwar gidan tace be isa ba ai babu abinda bata yi mai, wallahi ai kuwa aka dinga rigima mune masu zuwa sasantawa sabida har kusan dena kwana yayi a gidansa sabida tashin hankalinta. Yau itace yi mai habaici gobe shak’arsa jibi ma da abinda zata yi mai duk dan yace zai yi aure. Matar nan da mukane yi mata nasiha ta tashi munje mun gama bata hakuri ta tashi tace tana zuwa mun d’auka ta hakura har taje kawo mana juice ne, kawai sai gata da roba irin mai zurfin nan wallahi sister ina baku labari ashe manja ne a ciki jawur dashi tana zuwa ta watsa mana shi mu uku dani da jafar Munir da Mus’ab Muhd ta dinga zagin mu wai mu muka zugashi dan munafinci muda ko auran fari bamuyi ba Allah ya isa.” 

Nadiya da Nabeelah suka kyalkyale da dariya ganin yasa ta dariya yasa shi jin dad’i tare da cigaba da basu labari. 

“Dama Mus’ab ya fimu zuciya ya mik’e ya kalleta ya kalli red oil d’in dake jikinshi yace, wallahi wallahi indai aure ne kamar Bilal yayi shi ya gama ne idan anyi dan Allah ta mutu ko tazo ta kashemu, yana fad’a ya fita muma muka tashi muka bi bayanshi Bilal ya kalleta yace wallahi sai nayi nima Ummata zan ramamawa a’he tunda aka yi mata kishiya…muna jiyo su sai ga Bilal askwa ne har yana bige mu wai ashe biyo shi tayi da icce kuma wallahi sai da yayi auran ba’a fasa ba taje ta zage iyayan shi tatas shima ta hanashi kwanciyar hankali,kuma tunda ya furta zai yi aure suka dena mu’amular auratayya da ita ko ya nema sai tace yaje wajan kilakinshi k’arshe da abin ya isheshi sai ya sallameta yanzu yana nan da amaryar kuma ita uwar gidan yanzu so take ta koma yace a’a.” 

Gabaki d’ayan su suka kurawa imran ido cike da jimami, ya kalli Nadiya wacce ta rik’e ha6arta tare da cewa, 

“Yanzu dan bata da kunya mu take bi a waya tana neman mu sasanta su, ni tuni na sanyata a blacklist sabida haushi take bani ta d’auka kyawunta zai sa ak’i sakinta ko ak’i yi mata kishiya.” 

“Wallahi Yaya imran kamar kasan idan mace taga tana da kyau tafi rainawa namiji hankali, wawuya gashi nan ta 6ararwa da kanta mutunci, yanzu duk wanda zai aureta ai be zama lallai sai saurayi ba dole tayi gudun gara zata fad’a na zago.” 

Nabeelah ta fad’a cikin takaici yayin da Nadiya tayi shiru ta rasa ma me zata furta zuciyar ta sai sak’a mata take cewar Sultan yana can wajan Balqees ko me yake mata oho, saurin kawar da tunanin tayi ta hanyar cewa, 

Story continues below


“Allah ya kyauta mana yasa mufi k’arfin zuciyar mu” 

Suka ce “Amin.” 

A cikin d’aki kuwa mahaifin Nadiya ne a tsaye yayin da Ummi ta k’arasa ciki sai faman shan k’amshi take dan tasan fad’a zai yi, eye glasse d’in shi ya cire tare da kamo hannunta suka zauna a bakin gado ya kalleta yace. 

“Habba! Habba!! Hajiya me nakeji kuna magana akai keda yara? taya aka yi kika bari shaid’an yayi tasiri a cikin zuciyarki haka? Yau ace ‘yarki ta cikinki itace zata dinga nuna miki abubuwan da suka kamata ko suka dace da tayi kuma ke ya dace ki gaya mata su? Yanzu fa karki manta Nadiya ta tashi daga k’ark’ashin ikon mu ta koma k’ark’ashin mijinta, sai tabi mijinta sannan zata samu aljanna shi kuma sai ta taya shi  yin biyayya ga iyayanshi sannan zai samu tashi aljanna amma meye namu a cikin abunda zai yi?Babu ruwan mu matsawar ba cutar da ita yake yi ba, suna son junansu kina tunanin idan kika yi sanadiyar rushe auransu ko zaman lafiyar su zata dinga ganinki da k’ima ko mutunci?” 

“Amma dai kai kanka kasan wannan abun da yayi mata tsagwaran rashin mutunci ne, tayaya zaka auri yarinyar data d’auketa tamkar kanwarta uwa d’aya uba d’aya. Kuma ace dan zai aureta sai ya d’auki Nadiyan sunje can sannan zai nuna mata iyakar ta? Wannan duk salon a salwantar da rayuwarta ne da zuciyarta dan kawai aje a kashe min ‘ya ko a sa mata wani ciwon dan anga tana da hakuri….” 

“Asma’u me yake damunki ne?toh a hir d’inki akan maganar auran nan nasu babu abinda ya dameki a ciki kibarsu suyi abinsu.!” 

“Dama haka zaka ce mana tunda bakai aka yiwa ba..” 

Ummi ta fad’a tana kawar da kai, murmushin takaici yayi tare da mik’ewa ya cire kayanshi ya fad’a bathroom ba tare da ya kuma yin magana ba. Tashi itama tayi ta fita zuwa parlour, tarar dasu tayi sai faman hira suka suna dariya haushi ya kama Ummi ta wuce d’aki. Sai da aka kira magriba sannan suka tashi imran ya wuce side d’in shi Nabeela kuma ta wuce gida yayin da Nadiya ta koma ta d’auki humaira suka shiga cikin d’akin Ummi lokacin ita kuma ta koma d’akin mahaifin Nadiyan. 

Sallah tayi sannan ta kwanta sabida yadda kanta yake mata mugun ciwo humaira na gefenta tana wasa domin gidan ba yara. 

……. 

Sultan kuwa yana ajiye Nadiya gidan hajiya kaka ya wuce, shiga yayi ya tarar da Balqees a kwance saman kujera ta sanye eyepiece a kunnanta idanuwanta a lumshi bakinta sai faman motsi yake alamar tana bin wak’ar da takeji, hajiya kaka bata parlour’n ya k’arasa inda take ya tsugunna, kafeta yayi da idanuwan shi yana kallon k’irjinta sanye take da riga ‘yar 6ingila fara mai roba wadda ta fito da rabin k’irjinta da cikin ta, sai wani black d’in skirt wanda da kad’an ya wuce gwaiwarta ya kuma bin fuskarta da kallo tare da sanya yatsanshi k’aramin ya sanya shi cikin bakinta. 

Da sauri ta doke hannun still idanta a rufe yayi murmushi tare da k’ara sanya yatsan cikin k’ofar hancinta nan ma ta kuma buge hannun cikin nuna rashin son abinda yake shigar mata, Sultan yayi murmushi ya sake zura mata a cikin d’aya kofar hancin da sauri Balqees ta cafko hannun cikin takaici tare da bud’e ido da sauri tana kallon abinda ta rik’e d’in tana ganin hannu ta zaro ido zata kurma ihu yayi saurin rufe mata baki da d’ayan hannunshi. Murya k’asa-k’asa yace mata. 

“Matsoraciya…” 

Balqees ta kalleshi tare da turo mai baki cikin shagwa6a tace, 

“Kai Yaya dan Allah ka bani tsoro.” 

Hannu ya mik’a mata ta kalli tafin hannun nashi cikin rashin fahimtar abinda yake nufi ta sake turo baki tare da cewa. 

“Me zan baka?!” 

Yana kallon cikin idonta yace, 

“Tsoran  dana baki, tunda ba kya so bani kayana.” 

Dariya tayi kawai tare da tashi zaune ta cire warin earpiece d’in da yayi saura a kunnanta, mik’ewa yayi ya zauna akan kujera tare da d’ora k’afa d’aya kan d’aya yayin da Balqees ta bishi da kallo, wani farin ciki take ji duk lokacin da ta kalleshi ta kuma tuna cewar shine mijinta sai taji wani nishad’i da farin ciki ya wanzu cikin zuciyarta. 

Story continues below


“Yaya na kawo maka abinci zaka ci nice na dafa?!” 

Zaro ido yayi cike da mamaki dan be ta6ajin tayi girki ba, turo baki tayi ganin irin yadda yayi tana motsa baki kamar zata yi magana ya jijiga kai tare da cewa, 

“Baby dama kina girki ne?!” 

“A’ah Yaya na fara hajiya kaka tace ni zan dinga yin yanzu.” 

Sultan ya jinjina kai tare da kallonta ganin yadda tayi yasa shi cewa. 

“Zanci mana baby zubo min d’an kad’an.” 

Tashi tayi cike da murna ya bita da kallo zuciyar shi fal sak’e-sak’e, yana nan a zaune ta dawo rik’e da plate mai d’auke da jollop rice taje ta ajiye a gaban shi, komawa tayi kitchen ta d’akko mai zo6on da ta had’a sannan ta dawo ta zauna a inda ta tashi fuskarta cike da nishad’i, spoon ya d’auka kamshin abincin duk ya cika masa hanci ya kalleta cikin wani irin yanayi sannan yace, 

“Gaskiya baby kinyi k’ok’ari gashi abinci yayi amma ba kya yi? Allah yayi miki albarka.” 

Balqees cike da murna tayi murmushi tana cizon le6enta ta amsa da, 

“Amin Yaya zulkallain.” 

A hankali ya fara cin  abinci, yana sawa a baki ya rintsa ido tare da sanya hannu  a kanshi yana faman bubbuga kunnanshi sabida yadda yaji kanshi ya yayi zimmm tsabar gishiri yayi yawa, kallanshi tayi ganin ta shiga yanayin damuwa yasa shi yin murmushin yak’e da kyar yace, 

“Woww baby gaskiya kinyi k’ok’ari  yayi dad’i sosai.” 

Dariya tayi har kananun hakoranta farare suna bayyana Kansu, cikin jin dad’i cewa. 

“Nagode Yaya, amma kasan me hajiya kaka tace?!” 

Tayi maganar cikin yanayi na rashin kwarin jiki, Sultan ya tsiyayi zo6on yana kad’a mata domin bayajin zai kuma iya magana sabida yadda bakinshi da yakejin tamkar ba nashi ba kuma tundaga cokali d’ayan da yayi be sake yin wani ba ta 6ata fuska tare da cewa, 

“Wai wani cewa tayi gishiri yayi yawa zama a ita tsince shi kaji fa abinda tace.” 

Zo6on ya kur6a wayyo Allah da sauri ya had’iye shi idanunshi duk sun kawo kwalla sabida tsabar sugar yayi yawa ya rintsa idanuwa cikin ranshi cewa yake, 

_”Baby ai ba karya hajiya tayi ba ko shi aka barwa ya tsince gishirin ciki da sugar d’in cikin zo6on zan iya.”_ 

Amma fili sai yayi dariya yana kallonta yace, 

“Zonan baby.” 

Cikin rashin damuwa ta koma kusa da inda yake nuna mata wato gefenshi ya juya tare da riko hannunta yanajin wani abu na taso mai tun daga magudanar jininshi har kwakwalwarshi yace, 

“Hajiya kenan wasa take miki, da fatan dai kema kinci abincin…?!” 

“Naci sosai ma Yaya, gobe insha Allah wake da shinkafa zan dafa yau zansa asiyo mana barkono a daka yaji kanacin tafarnuwa a saka a ciki?” 

“Ina so baby.” 

Tace “toh shikenan.” 

Jikinshi ya janyo ta haka kurum yanzu yaji yana son jinta a jikinshi hakan yakan saukar mishi da wata kasala, matseta yayi sosai yana sauke ajiyar zuciya Balqees ta zaro ido gabanta ya fad’i jin yadda yake sakar mata numfashi a cikin kunne tayi saurin matsawa daga jikin nashi cike da jin nauyi da kunyar shi murya a sark’e tace. 

“Yaya kaci abincin mana.” 

Shafa kai yayi tare da kallon abincin yanajin kamar yayi amai yayi dariya yace, 

“Aikin san menene?so nake ki juye minshi na tafi dashi gida sai muci acan kinsan Nadi ta dawo yau kuma taje gidan su bamuda abuncin dare sai muci shi.” 

“Lahh Allah sarki aunty Nadiya ashe ta dawo, zanzo gobe ai sai ma na taho da Ummina.” 

Kad’a kai yayi sannan yace, 

“Kinje dubiyar Yusif kuwa baby?!” 

Yasina fuska tayi tare da gurgiza kai tace. 

“Hajiya kaka tace bazani ba sai na tambaye ka.” 

“Zonan toh.” 

Kasa zuwa tayi ganin haka yasa shi matsawa kusa da ita, shi kanshi ji yake tamkar matsar dashi ake yi gurinta. Hannu yasa ya kamo kugunta tare da janyota zuwa kan cinyar shi. 

“Yaya please ka bari dan Allah.” 

“Me yasa zan bari?!” 

Shiru tayi jikinta sai rawa yake yi shi kuwa Sultan ko mantawa yayi da cewar shi Papa d’inta ne, ya hau shafar gashinta bayan ya zare hulan kanta yana hura mata iskar bakin shi a cikin kunnanta. 

Motsin fitowar hajiya kaka ne yasa yayi saurin mekewa tsaye wuf ya fice daga parloru abinka da dogon mutum Balqees ta kwashe da dariya har hajiya ta fito taganta, mik’ewa tayi tabi bayanshi lokacin yana k’ok’arin tayar da motar shi yana kallon gurin ya ganta tana lekenshi tana dariya ya fice daga gidan zuciyar shi fal mamakin yadda yake jin sauyi akan Balqees abincin da be tafi dashi ba kenan dama haka yake so kawai ya kwantar mata da hankali ne dan baya son ganin damuwa cikin zuciyarta, da haka ya k’arasa asibiti. 

Sai da yayi sallan isha’i sannan yaje gidan su Nadiya, wadda farkawarta kenan daga baccin da tayi a gurin bayan tayi magrib. Mahaifinta na gidan yana sane yak’i fita sabida kar Ummi taje ta zuga mai yarinya akan d’abi’a marar kyau. 

Waya ya buga mata cewar gashi a k’ofar gida, mayafi kawai ta gyara tare da d’aukar humaira wadda itama taketa baccinta, har d’akin ta shiga tayi musu sallama mahaifinta ya dinga sanya mata albarka tare da yi Mata nasiha masu matukar ratsa jiki har kuka tayi sannan suka fito tare suka rakata iya k’ofa dan sunsan Sultan bazai so ganinsu ba sabida kunya…..

    
    Bayan sati d’aya sultan yana zaune a gidan hajiya kaka suna hira abban shi ya shigo, bayan sun gama gaisawa ne hajiya ta kalleshi sannan ta kalli sultan tace, 

“Yauwa gara Allah ya kawoka, kaga shekaran jiya yaran nan suka zo kowa yayi Allah ya sanya albarka amma sunce su sai sunyi biki kafin ta tare, shine nake son jin ya zai yi ina zai kai baby dan ni gaskiya gara akai ta d’akinta cikin mutunci kowa ya tabbatar da cewar anyi auran nan.” 

“Haka ne hajiya ai yin hakan shine mutunci kai Ahmad ya ka tsara zaka yi ne rabasu zaka yi ko kuma had’e su zaka yi duk yadda kaga yayi naka mu ba zamu takura maka ba domin duk matan kane.” 

Abba ya fad’a yana kallon Sultan wanda yake ta faman shafa keya, numfasawa yayi cikin rashin mafita sannan yace, 

“Abba wallahi ni ban yanke shawarar komai ba amma a k’aramin lokaci insha Allahu nan bada jimawa ba zan fad’a amma yanzu dai a k’aramin lokaci.” 

“Shi kenan Allah ya kaimu idan ka yanke shawara sai ka sanar mana, hajiya gobe za’a wuce da Yusif India sabida gaskiya jikin nashi sai dai addu’a kawai dan haka aka yanke shawarar kai shi can.” 

“Toh Allah yasa aje lafiya a dawo lafiya ai yana shan jiki kam.” 

‘Yar hira suka ta6a kafin su tashi su tafi Sultan duk ya damu kasan cewar bega babyn tashi ba tana ciki tana bacci tun kafin yaje kuma hajiya kaka tace mishi tana bacci, gida suka je gurin Umma wadda take ta faman harhad’e rai Sultan ya gaida ita ta amsa mai ciki-ciki ganin haka yasa be dad’e ba yayi tafiyarsa gida. 

….. 

Kwance suka akan gado duk yabi ya nanik’e mata a jikinta, Nadiya kam tunda taga haka tasan akwai abinda yake son ya gaya mata dan haka yake mata indai yana son yi mata magana mai muhimmanci, d’an zame shi tayi daga jikinta tare da d’ago da kanshi tana murmushi tace mai. 

“Abban humaira tashi kayi min magana ni ina mamakinka sai kace wani k’aramin wallahi.” 

Cike da kunya ya sake makalota jikinshi yana tura fuskarshi a k’irjinta, shiru tayi mai bata hanashi abinda yake yi ba har sai da yayi son ranshi, cikin kame-kame ya fara yi mata magana. 

“My Nadi ina cikin damuwa ne na rasa yadda zanyi gashi abba da hajiya kaka son kirani sunyi min magana akai.” 

Sai da k’irjinta ya buga dan tasan ba zai wuce zancen tarewar Balqees ba, da kyar ta samu zuciyarta ta tsaya guri d’aya sannan ta rungumoshi jikinta cikin dakiya ta fara magana. 

“Haba abban humaira your free to do what you want to do, gidan kanefa ni akark’ashin ka muke tayaya idan zaka yi abu kana son gaya min sai ka kama yin kame-kame? wallahi ina jin kunya a duk sanda kake yi min haka sai naji tamkar wata mara hankali ace mijina yanayin abu kamar yana shakkata please dan Allah ka dena kayi min magana a cikakken me gidan ka mana.” 

Sake matseta yayi a jikinshi kafin ya fara mata magana cikin tabbatarwa yace, 

“Tayaya kike tunanin zanyi yadda kike so Nadi? halinki na kawaici, biyayya, hakuri uwa uba yadda kike kula min da Umma na, ki gaya min tayaya zan iya zuwa miki daduk maganar danake son gaya miki?wallahi ina jin nauyinki ina jin kunyarki Nadi hakan yasa bana iya gaya miki duk maganar danaga dama, idan kuma ta zama dole toh nakanji nauyin fad’arta kai tsaye. Ina sonki Nadiya! Ina kaunarki ina fatan Allah ya bani ikon yi miki yadda kikeso a rayuwarki, ina fatan kar Allah ya nuna min ranar da zanyi miki butulci a rayuwata.” 

“Nagode yanzu dai menene?!” 

Sanar mata abinda su hajiya kaka suka gaya mishi yayi sannan suka yi shiru kowa yana sake-sake kafin ya numfasa cikin yanayin damuwa yace, 

“Na rasa ya zanyi tayaya ma zan 6ullowa al’amarin.” 

Numfasawa tayi duk da cewar zuciyarta na tsananin bugawa tare da cewa. 

“Toh kai ya kagani kana son ka had’a mune ko kuma kafi son kowacce gidanta daban?!” 

Shiru yayi yana shafar gashin kanta, jin yayi shiru ne yasa itama taja bakinta tayi shiru tana ta hailala a cikin zuciyarta. Ya dad’e beyi magana ba can kuma taji yace, 

“Ni gaskiya bana son abinda zai 6ata miki rai, so nake naji idan ked’in kina son a had’a kun idan kuma bakya so sai a samu wata mafutar.” 

Ta6e baki tayi ba tare da ya gani ba, numfasawa tayi tare da cewa, 

“Abban humaira kaine da gida kayi duk abinda kaga zaifi maka dad’i.” 

“Ke nake son ki gaya min Nadi.” 

“Toh ka barmu tare mana ina ganin hakan zai fi kaga basai mutane sun gane inda zaka kwana ba da ka shigo gida sai dai ka rufe babu wanda yasan a wajan wa kake.” 

“Toh Nadi ina zan sanya baby a gidan nan? A k’a’idar gidan nan na mace d’aya ne ya zanyi?!” 

Numfasawa Nadiya ta kuma yi sannan ta kamo hannunshi ya kalleta shima sannan tace, 

“Toh ga shawara abban humaira, me zai hana a fasa d’akin da take sai a had’eshi da corridor d’in wajan d’akin, kaga zai bullah ta BQ dama kuma ba kowa a ciki sai ka had’e mata shi a fitar mata da bedroom bathroom nasan zaiyi kuma sai yafi nawa girmama parlour kuma dama gashi nan amma idan hakan beyi maka ba kana da ikon yin yadda kakeso domin gidanka ne.” 

Rungumeta yayi sosai a jikinsa yana shafarta cikin tsananin so tayi mishi shiru tana jin duk abinda yake mata daga nan kuma alamra sukaci gaba da wakana soyayyar Nadiya na k’ara kwaranya a jini da tsokarshi. 

…… 

Sati d’aya dayin maganarsu Sultan ya turo ma’aikata kamar dama jira yaje aka fara rushe gurin da za’a had’e, Nadiya kama daga asubiti inda ta samu aiki zata wuce gida tayi wanka ta d’ora abinci sai ma’aikatan nan sunci sun koshi, idan aikin dare take dashi zata bawa mai gadi kud’u tace ya siyo musu abinci haka take yi kullum har ranar da suka kammala aikinsu inda za’a sanya Balqees ya kammalu tsab sai jere kawai da za’ayi. 

“Nagode my Nadi Allah ya baki aljanna.” 

“Amin abban humaira na gode da addu’arka.” 

Kwanciya yayi akan cinyarta ita kuma tana shafa kanshi yace, 

“My Nadi ya za’ayi wajan kayan lefe, na riga na sanar musu cewar kince zaki had’o ya kike ganin za’ayi?!” 

Wani kudum Nadiya taji a cikin zuciyarta tayi saurin rintsa ido still tana shafa mai kai, saurin numfasawa tayi dan karya ga rud’anin da ta shiga cikin dauriya tace. 

“Kajata kuje ta had’o mana ina ga hakan zaifi kaga ma baza’a zargeni dayin wani abunba kar ace na siyo mata ba irin wanda take so ba.” 

“No Nadi banak’i ta taki ba, kiyo d’in tunda na riga nace kina had’awa kinji kiyi min wannan alfarmar dan Allah.” 

Ba yadda zata yi dole ta amsa da toh,a ranar Sultan yayi mata transfer na kud’i cikin account d’inta haka ta daure ta gyagije ta fara had’a kayan akwatuna goma sha biyu haka ta had’o komai da komai wanda rasan anasawa a cikin kayan aure hatta kud’inta sai da tasa ba tare daya sani ba sai da ta kammala komai sannan ta fito dasu ta nuna mai. 

Sultan yayi matuk’ar mamaki dayaga kayan ya kuma san kud’in da ya bayar basu kai ace anyi wannan siyayyar ba k’imarta da darajarta suka sake ninkuwa a cikin zuciyar shi nan yasa su Jamila suka zo suka d’auki kayan aka kai gidan Umman shi nan mutane suka dinga zuwa suna gani kafin daga bisa ni akaisu gidan hajiya kaka. 

Su Balqees aka dinga murna ana farin ciki suna gama exam aka sanya ranar biki sati d’aya, Adda Aisha ce tasa aka yiwa Balqees gyaran jiki har anko suka yi wanda itama Nadiya tayi shi, ranar da za’a fara event na dare ne dama a wani katafaran hall……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *