TAURA BIYU CHAPTER B KARSHE

 TAURA BIYU CHAPTER B KARSHE

*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *21*

Tsayawa Finn yayi akansu Yana kallonsu cikin wulaqanci ganin har lokacin da sauransu ya juyo ya kalli tiger yayi Masa alama da ido…

Kallon yaransa tiger yayi Sai aka Kuma ‘debo ruwan qanqanra a qaton bucket aka Kuma jiqasu tareda cigaba da dukansu..

Iya dakuwa Kam sun daku bama kamarsu Yaya abbakar dasuke samari anfi dukansu duk da dai Suma su baban ba a raga musu ba…

+

Sake kallonsu Finn yayi yaga sun bugu yasaki murmushin qeta tareda fiddo wayarsa ya ‘daukesu yaturawa mum kafin yakirata yace ta duba..

Dariyar Jin da’di tayi lokacinda taga hoton takira tace a kaisu inda aka ‘daukosu a watsar..

Zamewa tayi daga rumfar dayayi Mata takoma bakin gado ta zauna kanta a qasa tana kallon dogayen fingers dinta..

Dawowa yayi kusada ita ya zauna shima ya qurawa hannun nata ido..

Ayshah please lets get married before informing our families about us…

‘dagowa tayi ahankali takallesa ta kawar da idonta kafin ahankali tace,

No Nik…I can’t marry you without my family’s approval.. besides that I’m Muslim you’re Chris…..

Katseta yayi da cewa,

I’m ready to convert my love….I want to become Muslim too…

Kallonsa tayi idonta na cikowa da hawaye sabuwar soyayyarsa na qara shigarta sbd ganin yanda idonsa ya rufe bayako tuna masifar dake gabansu ta dukkanin 6angaren biyu…Dan tasan gidansu sun gwammace ta mutu dasu barta dashi..

I love you ayeeshah…

Juyarda Kai tayi tareda sakin 6oyayyen murmushi..

Fira yafara yi mata ahankali Yana Bata lbarinsa saidai tayi murmushi kawai batareda tayi maganaba.

Mantawa suka da komai da kowa Saida sukaji knocking tayi saurin miqewa tsaye gabanta na fa’duwa jikinta na rawa..

Kallonta yayi tareda sakin qaramin murmushin daya bayyana white teeths ‘dinsa qasa qasa yace,

Wait hia…

Qofar ya 6ude ahankali saiyaga nurse ce yasaki ajiyar zuciya ahankali tareda juyowa ya kalli yanda ayshan tayi zuru duk saiyaji tabasa tausayi ya matso kusada ita yakai bakinsa saitin kunnenta zaiyi magana tayi saurin zillewa ta Fice ‘dakin da sauri tana Jin farin ciki na shigarta tako ina.

Shafa kansa yayi tareda kwantawa a gado Yana Jin farin ciki Mara misaltuwa.

Tundaga nesa ta hango qofar gidansu da kamar mutane gabanta yayi fa’duwa ta qarasa a darare..

Su Yaya sani dasu babanta ne ke qoqarin shigardasu baba alhaji cikin gida dukkaninsu ba kyan gani kawunansu da fuskokinsu a kumbure da jini a kayansu..1

Yawu ta ha’diye daqyar tashigo gidan Nan ta tararda kowa hankalinsa a tashe su husna ma harda kuka ganin mummunar aika aikar da akayiwa su baban.

Sosai itama hankalinta ya tashi Dan koba’a fa’daba tasan wannan aikin mum ne..

Har dare gidan ba da’di Dan kowa na cikin jimami da baqin ciki..itadai Bata kosanyin wani qwaqwaran motsi sbd tsoron Mai zai biyo baya.

Har akai kwana biyu ba’ai zancen komaiba kan al’amarin Kuma tun ranar Bata fitaba sbd tsoro da fargabar abinda zai biyo baya duk da ba qaramin tausar zuciyarta takeyiba akan son sanin ya jikinsa yakeba..

STORY CONTINUES BELOW

Yau kwana hudu da afkuwar tsautsayin su baba..

Matuqar zafi gidan kusan kowa ya ‘dauka musamman matasan gidan wannan karon ko baba malam ya ‘dau zafi matuqa….

Shiyasa ya tarasu yau kowada kowa..

Gyara Zama yayi tareda kallon ayshah murya a karsashe yace,

Ayshah Kinga abinda wa’innan mutanen sukayi Mana ko?

Shiru tayi gabanta na bubbugawa da sauri..

Cigaba yayi da cewa,

Duk bazanyi wani tashin zanceba ko dogon zance auren Umar da ayshah nasaka Nanda wata biyu kowa yaje yafara shiryawa Kuma nijar zasu koma bayan auren nagama magana kowa zai iya tafiya.

Takaici ne ya turniqe Yaya Umar Dan so yayi ace Nanda sati ‘daya a ‘daura auren..

Iyayensu da sauran ‘yan gidan kaf sunyi na’am da hukuncin baba malam ‘din Dan tsoron abinda zai iya biyowa baya.

Ayshah kuwa jitayi hankalinta yayi mummunan tashi hawaye yaciko idanuwanta jikinta har rawa yake ta miqe ko gani batayi sosai tabar palon.

Kuka take sosai cikin qaramin sauti zuciyarta na tsananta shiga qunci..

Kamar munafuka takoma cikin gidan ko fitowa Bata cikayiba..hakama zuciyarta a matse take dason ganinsa.

Zaune take akan carpet ‘din sallah kaman kullum tayi shiru idanuwanta a lumshe..

Zama kusada ita taji anyi ta bu’de idanuwanta ahankali ta sauke kan nuratu…

Qasa qasa da murya nuratu tace,

Anty ayshah jiya Da ina dawowa daga makaranta nagansa acikin anguwar Nan..yauma Dana dawo nagansa.

Qurawa nuratu jajayen idanuwanta tayi gabanta na duka da qarfi….

Muryarta na rawa tace,

Kinfa’dawa wani kingansa?

Girgixa Kai tayi tana kallon ayshahn tace,

Anty ayshah kina sonsane?

Hawayen dasuka gangaro Mata ta goge da bayan hannu tace,

Ina sonsa nuratu..

Dafata nuratun tayi cikin danne mamakin da tausayawa tace,

Anty ayshah karki Bari zuciya da shai’dan suyi galaba akan tarbiyar da iyayenmu sukai shekaru suna bamu.

Cusa kanta tayi tsakiyar qafafunta ta bawa hawayen datake dannewa Daman kwarara..

Washe gari shiryawa tayi a sanyaye Dan batada tabbacin za’a barta cigaba da karatun duk da tuni ya fara wargajewa.

Cikin ikon Allah ba’a hanata tafiyaba saidai tana fitowa titin anguwarsu taga motarsa ajiye gefen titi nanta ha’diye wani yawun tashin hankali Dan tabaro su Yaya Umar dasu ya Ahmad qofar gida suna Shirin fitowa…

Tabbas idan haryana cikin anguwar akwai yiyuwar su gansa Kuma tasan wannan karon bazasui Masa Mai kyauba.

Juyawa tayi da sauri taking cikin layin saigasu sukuma sun fito layin tayi saurin shigewa soron wani qaramin gida..

Jitayi hayaniya ta kaure da sauri ta leqo saita hangosa tafe izuwa gurinsu batareda ya ankare dasuba.

Ya sani yafara ganinsa ya zabura tareda nunawasu Umar shi…

Qatuwar spanner dake hannun ya abbakar dazai gyara mashin ‘dinsa ya saitashi ya jefa Masa Sai a goshinsa ba zato yaji saukar qarfe Nan take goshinsa ya fashe ya ‘dago lazy eyes ‘dinsa dasukai jan azaba yakallesu duk da yaji tsoron ganinsu bayajin zai iya guduwa ko tafiya batareda yau ya gano gidansuba.

Tsayawa yayi jini na fita a goshinsa ya kalli sani daya shaqo kwalar rigarsa Yana huci.

Azafafe yace,

STORY CONTINUES BELOW

Uban me kakeyi anan?

Kallo yabisa dashi sbd baisan meyake fa’daba..

Mari  Umar ya wanka Masa akan kyakkyawar fuskarsa dayakejin kamar ya zuba Mata batir..

Yace,

He said wat are you doing hia you monkey fool.

Kallon Umar ‘din yayi akaro na farko dashima yaji tsanar wani ‘dan Adam Kai tsaye yace,

I came hia to see my love.

Ture sani Umar yayi da qarfi ya shaqo wuyan Nik ‘din yace,

Wh…wh..who is your love?

Ayeeshah””””ya fa’da Kai tsaye ba tsoro a idanuwansa.

Hannu ya dunqule yakaiwa Nik wani mugun duka Saida bakinsa ya fashe.

Wani dattijo ayshah tagani zai wuce tayi saurin Shan gabansa tana hawaye tace,

Baba Dan Allah kaga wasu can suna fa’da Dan Allah ka hanasu karka Bari ayi fitina.

Juyawa yayi ya kalli gurin daidai sun nanna’de rigunansu zasu cire takaicin dukan daakayiwa iyayensu dattijon yayi saurin tarewa tareda matsarda Nik dake tsaye baida alamar motsawa gefe yace,

Haba Kuna ‘yayan musulmai ‘yayan manyan malamai zakuyi Abu irin na jahilai…

Meyayi zafi haka dabazaku Kira hukuma ba Zaku ‘dauki mataki da hannunku…

Fa’da yahau yi musu sosai suka basa hkr tareda barin gurin sbd duk zafin ransu sunada tarbiyar girmama babba sosai Koda basusanshiba.

Juyowa yayi ya kalli Nik yace,

Kaima ka wuce tunda Suma sun tafi..

Juyawa yayi ahankali yabi bayansu duk da baisan abinda mutumin yafadaba…shidai yau alqawarine yayiwa zuciyarsa saiyaganta Dan haka zaibi bayansu saiyaga gidansu..

Daf dazai shiga kwanar yaji anriqo rigarsa ta baya yayi saurin juyowa sukai Ido biyu ta juya yabiyota da sauri Yana Kiran sunanta Amma taqi tsayawa.

Saida takai bakin motarsa ta tsaya tareda juyowa ta kallesa taga yanda goshinsa da bakinsa ke jini ta ‘dauke Kai tareda ‘daure fuska ta nuna Masa motarsa tace,

Leave…

Da sauri ya kalleta zaiyi magana tace,

Go… please..

Idanuwansa ne suka ciko da hawaye ya kalleta kaman zaiyi kuka yace,

Ayeeshah please don’t ask me to leave because I can’t….

Rintse ido tayi cikin ra’dadin ganin jininsa na zuba ta sake juyar dakai tace,

Please Nik go…

I don’t want to lie to myself again..

I don’t want to continue believing in a fake dream…

My parents fixed date for my marriage with someone…..

Wani mugun jiri ya ‘dibesa dama jurewa kawai yake Dan tuni yakejin jirin jinin dayake fita a goshinsa…

Hawaye taga sun 6alle Masa yayi ya ‘dago lazy eyes ‘dinsa taga sun canza launi tayi baya ka’dan ba zato taji ya damqo hannunta tana fixge da qarfi yakuma damqota tafara qoqarin qwacewa Amma takasa Dan mugun riqo yayi Mata ita batama ta6a tunanin yanada qarfin dazaiyi Mata wani riqo takasa qwacewa saigashi yabata mamaki..

Da gudu wani Dan sauri dake bakin titin ya isa yafadawasu Umar dake qofar gida suka dungumo a guje daidai lokacinda ya turata mota tana tirjewa yabar gurin da mugun gudu da ita.

iska Umar ya daka da qarfi Yana cewa,

Wlh duk yayi kuskuren ta6ata ko sauke haushi akanta saina nayi ajalinsa.

STORY CONTINUES BELOW

Gida suka koma suka sanar da iyayensu Nan hankula suka qara tashi suka ‘dunguma station don Kai report.

Gudu yake sosai har lokacin idanuwansa basudaina hawayeba jiyake kozai rasa ransa bazai ta6a Bari arabasa da ayshah ba…

Kuka take sosai itama ahankali batareda takalli gefensa.

Fita gari yayi ya qarawa motar gudu tayi saurin kallonsa tareda fashewa da wani sabon kuka zuciyarta na karyewa gabanta na tsananta fa’duwa.

Awa ‘daya da rabi saigasu a wani babban gari dabazata iya cewa inane ba.

Anguwar dasuka shiga tasata ‘dan sararawa da kukanta Dan lurada kamar anguwar duk malamai ne da almajirai tareda masu ‘daukar karatu.

Kallonsa tayi taga fuskarsa tayi jajir sbd azaban ciwon dayakeji akansa hakama jinin dake goshinsa duk ya bushe a fuskarsa…

Wani mugun tausayin kansune yakamata Dan Sai a lokacin ta lurada muguwar ramar dayayi..

Parking yayi tareda juyowa ya kalleta tsowon minti goma murya a sanyaye yace,

Ayeeshah can you please come inside with me..

Goge jajayen idanuwanta dasuka kumbura tayi tareda kallon qofar gidan ta ‘daga Masa Kai.

Bu’de motar yayi yafito ya zagayo ya bu’de Mata ta fito jiki ba qwari ga idanuwanta da Bata gani sosai dasu sbd kuka.

Babban palon dake zauren gidan yashiga ga mamakinta saitaji yayi sallama duk da kusan a birkice yayita Saida takusan fa’duwa sbd mamaki…

Babban mutum tagani zaune cikin shigar babban malami Yana karatun wani littafin larabci Yana ganinsa yasaki murmushi tareda amsa masa sallamarsa Yana qara gyara Masa yanda take daidai.

Zama yayi a qasa kusada qafafun malamin tareda fashewa da kuka ahankali….

Subhanallah…..sheik abdallah yace da sauri Yana kallon Nik ‘din cikin kulawa yace,

Wat is the matter Muhammad?

Kuka taji itama taji ya qwace Mata sbd sunan dataji ankirasa dashi na Muhammad.

Shiru shaikh abdallah yayi Yana sauraran kukansu na tsawon mintuna kafin Nik ya ‘dago manyan lazy eyes ‘dinsa ya kalli Ayshah cikin sanyin murya yace,

Ayeeshah….

Bata ‘dagoba haka zalika Bata amsa ba har lokacin kuka take..

Ayshah please let get married today…

Sabon kuka tasaki tareda miqewa da sauri zata bar gurin yayi saurin Shan gabanta tareda zubewa qasa ya riqe qafafuwanta..

Gyara murya shaikh yayi tareda Kiran sunanta cikin nutsuwa yace tadawo ta zauna.

Ba musu tadawo a sanyaye tazauna hawayenta na tsananta gudu..

Ayshah ke musulma ce Kuma ‘yar malamai Masana addini kamar yanda yanda Muhammad yayimin bayani..

Muhammad yazo Nan kwana biyu dasuka wuce ya bayyanamin komai akan qaunar dakukewa juna Kuma aranar ya kar6i musulunci ya kar6i kalmar shahada Kuma daga ranar kullum saiyazo Nan garin koyan abinda ya danganci addinin musulunci…

Amma bai za6i sunaba yace kece Zaki za6a Masa suna Kuma ya tabbarminda qalubalen da fitinar dake gudanuwa a tsakanin gidajenku Dan haka ya bayyana buqatarsa tason a na ‘daura muku aure Dan shika’dai ne zai kawo qarshen fitinar dake tasowa..

2

Girgixa Kai tahau yi tana cigaba da kuka duk da zuciyarta cike take da muguwar soyayarsa musamman yanzu dataji ya musulunta…Amma bazata yarda suyi aure yanxu ba Saida yardar iyayensu.

STORY CONTINUES BELOW

Matsowa yayi gabanta a susuce yace,

Please ayeeshah say yes,,,I promise I won’t do anything to you until everything is right… please ayeeshah I beg you in the name of Allah…

Rintse idanuwa tayi hawaye nacigaba da xubo Mata ta miqe tsaye tareda juya Masa baya dan matuqar taci gaba da sauraransa zuciyarta na daf da karyewa…

Sake zubewa qasa yay ya riqe qafafuwanta Yana fidda sautin kuka ahankali jikinsa har rawa yake sbd wani mugun zazza6ine ke cin jikinsa Amma bayaji alokacin.

Jin kuka yake sosai zuciyarta takasa controlling kanta ta durqusa da sauri gabansa itama tana tsananta kukanta.

‘dagowa yayi fuska jajir ya bu’de baki daqyar yace,

Ayeeshah please…..

‘daga Masa Kai tayi da sauri cikin tsananin sonsa da tausayinsa..

Thank you… thank you…yafada cikin farin ciki tareda juyowa gefen shaikh saiyaga baya palon…fita yayi da sauri kaman zai Fadi yakirowosa Yana kallon tsakiyar idanuwanta yace,

Shaikh she accepted… please get us married today…

Kallon ayshah shaikh yayi ta sunkuyar dakai yace,

Allah yabaki ladar wannan jahadin ayshah,,Kuma Allah ya kawo haske a rayuwar aurenku yakuma shirya iyayenku sanadin wannan auren..

Amin tace axuciyar na bugawa very fast..

Kallon Nik dake faman murmushi yayi yace,

I will send her inside now you’ll see her after the fatiha…

Ok…yace Yana kallonta cikin farin ciki..

Wait shaikh let her choose a name for me..

Kallonta sukayi su duka Dan sauraron sunanda zata fa’da ahankali cikin sanyin murya tace,

*_DEEN_*….._*NURADEEN*_….

wani lazy smiling ya aiketa dashi yanabin bayanta databi shaikh cikin gida da sauri.

*_ZUCIYA MUGUN NAMA_*……

Cikin qanqanin lokaci layin ya ‘dan cika da malamai da ‘dalibai tareda masu zuwa ‘daukar karatu aka shaida ‘daurin auren _NURADEEN DA AYSHAH_…Akan sadaki naira dubu hamsin Wanda shaikh ne yabiya sbd qaunar NURADEEN da Allah yasaka Masa aransa tun ranar daya fara zuwa gurinsa..

Tunda babban ‘dan shaikh yashigo ya sanarda an ‘daura auren taji hankalinta ya tsananta tashi wani sabon kuka yazo Mata ta sake cusa kanta cikin qafafunta tana yi.

Uwar gidan shaikh ‘dince ta ringa rarrashinta tana jero Mata nasihu akan tabbas Bata kyautawa iyayentaba Amma tunda jahadine tayi Allah bazai Bari ta wulaqantaba insha allah…Dan ba’asan iya Wanda zai musulunta ba sanadiyar auren.

Awa ‘daya da gama ‘daurin auren shaikh ya Aiko kiranta tashiga pilonsa da sallama a qasan maqoshi sbd muryarta data shaqe sbd kuka..

Nasiha yayi Mata sosai Mai matuqar shiga jiki kafin yace taje Deen na waje yana jiranta zai maidata gida.

Tana fitowa idanuwansu suka ha’du Nan take taji jikinta yakuma sanyi gefe ‘daya wahalalliyar soyayarsa na ‘dawainiya da ita.

Shikuwa ji yake tabbas Babu abinda yakai musulunci da’di tunda ya mallaka Masa ayeeshansa.

Ya zagayo Yana rintse ido sbd mugun zazza6i da rawar sanyi da jikinsa keyi…

Bu’de Mata motar yayi tashiga asanyaye kafin shima yashiga suka bar gurin…

Ko anguwar Basu fitaba yaji jikinsa na neman rikicewa ya ‘dan saci kallon gefenta yaga kanta a sunkuye ya tattaro ‘dan kuzarinsa Dan yasamu yakaita gida  kafin ciwon ya kwantardashi..

Dashi dishi yafara gani saura qiris yadaki wata babbar mota yayi saurin take burki….

‘dagowa tayi a ‘dan tsorace saitaga jikinsa na rawa sosai idanuwansa sunyi jajir jijiyoyin kansa duk sun yanko…

A rikice takira sunansa hawaye na gangaro Mata…

Kallonta yayi kaman zaiyi kuka yace,

Ayeeshah my head….I can’t see properly…

Shaking yake sosai ta juyo takalli waje taga hadarine sosai a garin Dan kowa Sai hanxarin guduwa gida yakeyi..

Maido kallonta kansa tayi taga yayi mugun laushi ta ‘daga hannunta ahankali Yana rawa ta dafa goshinsa taji zafi sosai cikin hawaye tace,

Deen let’s go back to shaikh house..

Daqyar ya iya ‘dagowa yace,

My love I can’t drive that far..

Idonsa ne ya sauka kan wani qatoton babban hotel and suites dake bakin babban titin dasuke..

Juyarda kan motar yayi daqyar daidai lokacinda ruwan sama masu qarfi suka 6arke..

Tunda yashiga yayi parking yafita jikinta ya’dau rawa sabbin hawaye suka 6alle mata harya dawo kaman zai zube sbd jiri ga ruwa na sake dukansa ganin Yana tsaye ruwa na dukansa ta kasa yi Masa musu ta fito suka shige tareda shigewa lift zuwa floor ‘din sama gaba ‘daya.

Suna shiga ko Kaya ban iya cirewaba ya zube a doguwar sofa jikinsa na tsananta shaking a wahalce yace,1

Ayeeshah please cover me.

Mamuh💋*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

_Viawattpad@mamuhgee_

              *22*

Qarfe Tara da kusan rabi baccin wahallalen zazza6in da yayi ya farka tareda bu’de idanuwansa ahankali ya saukesu akanta,

Take yaji wani sabon sonta da tsananin tausayinta na qara shigarsa sbd ganinta zaune gabansa bacci ya ‘dauketa fuskarta jajir Kuma a kumbure sbd kukan datasha kafin baccin ya ‘dauketa.+

Ahankali ya saki wani lazy smile kafin ya miqe ya nufi qofar toilet yashige.

Wanka yayi cikin kwanciyar hankali farin ciki da nutsuwa na shigarsa…,

Alwala ya ‘dauro kaman yanda shaikh ya koyar dashi kafin yafito ‘daure da farin towel qal ‘daure a qugunsa.

Har time ‘din bacci take a zaune inda ya barta Kuma Sam bayason tayarda ita sbd ganinsa ahaka zai iya sa ta tsorata dashi besides that tana buqatan bacci da hutu sosai.

Telephone ‘din dake cikin room ‘din yayi amfani dashi yakira boutique ‘din dake cikin hotel ‘din yayi ordern kayan bacci nasa da nata tareda dogayen rigunan dazasu iya sakawa suyi sallah harmada designer perfumes masu sanyayan qamshi nasa da nata.

Bayan yakashe restaurant dinsu yakira yakuma ordern abinci kafin ya dawo gabanta ya zauna tareda qura Mata lazy eyes ‘dinsa Yana murmushin farin cikin kasancewarta tasa.

Ahankali ta bu’de idanuwanta tana ganinsa tayi saurin miqewa tareda sunkuyar dakai gabanta na fa’duwa Dan kallo ‘daya tayiwa lafiyayyan jikinsa dake bayyane ta ‘duqar da Kai.

Murmushi yasaki harsaida sautinsa yafito ya matsota sosai hartanajin qamshin sabulun da yayi wanka dashi na papaya.

Hannunsa ya Kai ahankali ya ‘dago da fuskarta ya qura Mata ido tayi saurin rintse idanuwanta hawaye na gangarowa daga cikinsu.

Fuskarsa ya matsa daf da Tata zaiyi magana akayi knocking qofar room ‘din.

Rintse ido yayi tareda sakin ajiyar zuciya kafin ya juya ya nufi qofar…

Orders ‘din dayayine aka kawo lokaci ‘daya..

Kar6a yayi tareda ‘dauko credit card ‘dinsa ya miqa  musu suka wuce.

Bu’de kayan yayi tareda ‘daukar farar jallabiya Mai santsi da kyau yasaka sannan ya fesa wani cool turaren signature na oriflame  kafin ya juyo ya kalleta tananan tsaye still kanta a qasa..

Matsowa yayi gabanta ya riqo hannuwanta duka biyi tareda ‘dan duqawa ya leqa fuskarta yace,

My love am going to pray now,,, you should take a shower too then come and pray…

Ba musu ta zame hannayenta ta nufi toilet tashige ta rufo.

Wanka tayi tareda ‘dauro alwala saikuma takasa fitowa sbd towel ‘din yayi qarami sosai Sai kawai ta goge ruwan jikinta dashi ta maido kayanta ta fito..

Zaune yake kan sallaya Yana qoqarin karanto azkar da salatin da shaikh ya koyar dashi ta kallesa duk saitaji ya sake Kama zuciyarta ta qaraso ahankali ta tsaya kusadashi ta tayarda Tata sallar.

Tana idarwa tafara karanto azkar ‘dinta a fili cikin sanyin murya Nan ya juyo ya fuskanceta Yana qara gyaggyara inda yayi kurakurai.

Sun ‘dau tsawon mintuna ahaka kafin suka kammala Ya zauna kan sofa tareda jawota ba zata ya zaunar a cinyarsa Sai kuma yasaki ‘yar qara ahankali da a rikice ta kallesa cikin tashin hankali saiya saki qayataccen murmushi Yana kallon fuskanta cikin tsokana yace,

Oh my God you broke my legs..

Ajiyar zuciya tasake tareda harararsa batareda tasaniba

Baisan sanda yasaki qaramar dariyaba Yana kallon bby face ‘dinta  cikin wasa yakuma cewa,

Oh my God sweetheart you’re eyeing me…

Sunkuyar dakai tayi da sauri tareda miqewa yayi saurin dawo da ita amma saita zille tazauna gefensa maimakon jikinsa.

Abincin da aka kawo ya bu’de tareda kallonta yace taci…

Daqyar yasami ya takurata taci ka’dan ta miqe tashige toilet kafin shikuma yasamu yaci slice ‘din pizza ‘daya da milkshake.

Wanko bakinta tayi ta fito ta tsaya tareda kallonsa a ‘dan daburce tace Masa,

Deen let’s go home please it’s already late.

Tasowa yayi ya tsaya gabanta yace,

Baby it’s already late and I don’t drive at nights I’m scared of dark.

‘daure fuska tayi tana qoqarin danne hawayenta tace,

Ok I will go myself.

Hanya takama ta nufi qofar fita tajita a rufe Gam tasake mur’dawa tajita Gam tajuyo a tsorace zata kallesa taji mutum a kusada ita tayi saurin matsawa ya kalleta yaga yanda duk takasa nutsuwa ya matsa nesa da ita yace,

Ayeeshah please don’t get me wrong but….

Kuka tasakar Masa tun bai qarasaba yayi saurin matsowa a ru’de yace,

Please don’t cry I will take you home now…

Keys ‘din motarsa ya ‘dauka tareda kamo hannunta ya bu’de qofar suka fito.

Har lokacin ruwa ake sosai Amma haka ya ‘daure ya tada motar suka baro hotel ‘din.

Tafiyar minti shida sukayi yafara sakin hanya Yana qure kallonsa a hanya sbd komai baya gani sbd qarfin ruwan ga qarin darene Kuma Daman shi baya tuqin dare sbd tsoron fitama yake da daddare.

Ba zato sukaji sun daki wani Abu sun fa’da qatuwar gota…

A tsorace ya kashe motan ya juyo ya kalleta yaga idanuwanta a waje cikin fargaba da tsoro qarara yawu ya ha’diye tareda tattaro qarfi da jarumta sbd Kar tagane tsoronsa da yawa ya bu’de motar ya fita.

Qatuwar gotace suka fa’da Kuma ya tabbatarda bazasu iya fitaba Saida taimako gashi ba mutane.

Komawa cikin motan yayi ya fa’da Mata dole ta fito tana matsar hawaye suka fara takawa cikin ruwan suka koma hotel ‘din..

Saidai kafin su Isa kowannensu ya daku da ruwan musamman mashi da ko Yaya ruwa ya ta6asa ba 6ata lokaci zai fara zazza6i..

Itadai Kam zazza6in ne Mai qarfi ya kamata tun kafin su Isa room ‘dinsu tafara Jin kamar zata zube.

Suna shiga yayi saurin kashe ac tareda zaunar da ita a kujera ya zare Mata hijab ‘dinta dake jiqe tareda saurin ‘dauko kayan baccin dayayi order ‘dazu yafara qoqarin cire Mata doguwar rigar atampar dake jikin tayi saurin riqe hannunsa ya kalleta kaman zaiyi kuka yace,

Ayeeshah please don’t do this to yourself you’re completely wet and…

Kar6ar kayan baccin tayi tareda miqewa da qyar ta fa’da toilet Dan itama kayan a matse take dason ciresu Dan har ‘digar ruwa suke.

Doguwar rigar bacci ce cotton fara qal mai ‘dan kauri Amma batada wani tsawo Dan duka fararen  cinyoyinta a waje suke hakama hannuwanta Dan hannun shimi ne da ita gashi har bra ‘dinta tacire Dan itama a jiqe take.

Kasa fitowa tayi ta zauna  gaban mirron ciki tareda qanqame jikinta dake tsananta rawar sanyi.

Tu6ewa yayi shima tareda saka kayan bacci shima masu kauri ka’dan ya zauna jiran fitiwarta Amma shiru.

Matsawa yayi bakin qofa yakira sunanta Amma shiru..

Da sauri ya bu’de qofar cikin fargabar ko wani Abu yasameta aciki.

Qarasawa yayi da sauri a ru’de tareda tallafota jikinsa Yana cewa,

Oh my God baby you’re burning.,

‘daukanta yayi da sauri ya fito ya kwantarda ita a gado tareda rufeta da blanket Mai laushi ya hau shima tareda jawota jikinsa ya rungume ahankali.

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

_Viawattpad@mamuhgee_

              *23*

Rawa jikinta yake sosai duk ta qara rikice Masa Nan hankalinsa ya tashi ya qara shigarda ita jikinsa cikin tsananin damuwa sbd baisan Mai zaiyi Mata ba duk da shima yanajin zazza6in sosai Amma ganinta cikin wannan yanayin yasashi daurewa tareda mamakin kansa yanda yanajin zazza6in nacin jikinsa Amma ya share shida a gida ko ‘dan yatsansa ke ciwo kwantawa yake su mum suhau jinyarsa ana tarairaysrsa.

Sannu ahankali saiga zazza6in yafara sauka tafara tsatsafo zufa ahankali duk da tuni bacci yayi gaba da ita.+

Kallon face ‘dinta yayi yaga yanda ta ha’da zufa ya zura hannu ya’dau remote ya kunna aircon.

Sanyin Aircon ‘din yaji na qara rura wutar nasa zazza6in ya gyara kwanciyarsa tareda shigewa cikin bangon gaba ‘daya Nan shima bacci ya ‘daukesa.

Kiran sallar asubar masallacin hotel ‘din ne ya tayardasu Amma ita tafara tashi sbd sabon tashi datake dashi na sallar asuba.

Maqalqale yake da ita yashige cikin jikinta sosai Yana baccinsa cikin kwanciyar hankali…

Face ‘dinsa ta kalla duk da ba haske hasken dim light ne kawai Amma tana iya ganin baiwar kyau da Allah yayi masa.,

Lumshe idanu tayi tareda addua cikin ranta,

Ya Allah ka sanyaya rayuwar iyayenmu ka kawo sauqi cikin wannan alamarin.

Qoqarin zame jikinta Take ta tashi saitaga ya bu’de lazy eyes ‘dinsa cikin bacci ya kalleta.

Cikin kunnensa dake daf da bakinta murya qasa qasa tace,

It’s time for salat.

Wata mummunan fa’duwa gabansa yayi sbd numfashinta da yanda muryarta suka shiga kunnensa sun sakar Masa da wani irin yanayi Kuma Nan take idanuwansa suka nuna ya ‘dago yakuma kallonta  sai lokacin ya lurada yanda take tun jiya da dare..

Dogon gashinta daya sauko saman kafa’darta ya kalla kafin ya maida idonsa kan rigarta Mai qaramin hannu data bayyana kafa’dunta da dogayen hannunwanta har zuwa qirjinta daya zaunu ya tsaya daidai acikin rigar.. lumshe idanu yayi tareda ‘dauke kansa ya tashi zaune a kasalance yakai hannunsa goshinta ya ta6a yaji ba wani zafi ko alaman zazza6i ya sauko gadon ya fa’da toilet yayo brush da alwala yazo yafice ya nufi masallacin.

Saukowa itama tayi tareda ‘dauro alwala tazo tayi sallah.

Har gari ya fara haske bai dawoba tana gama azkar ‘dinta zame ta kwanta agun Nan take bacci yakuma ‘daukarta.

Qarfe bakwai saura yashigo yaga tana bacci ya shiga toilet ya ‘dauko kayansu na jiya tareda ‘dagata ahankali ya zame  hijab ‘dinta ya miqawa laundry man na hotel ‘din dake tsaye bakin qofa kafin ya rufe dakin.

Duqawa yayi ahankali ya dauketa ya ‘dora saman gado ya kwantar shima jallabiyarsa ya cire ya haye gadon ya kwanta cikin jikinta.

Bacci sukayi sosai na tsawon lokaci kafin suka tashi..

Wannan karon shiya fara tashi ya qurawa fuskanta Ido musamman bakinta dayake jajir kaman tasa lipstick.

Shafa fuskanta yayi ahankali tareda Kai bakinsa saitin kunnenta cikin wata irin kasala yace,

my love..

Tsikar jikinta ce ta tashi gabaki ‘daya lokacin da muryar dayayi amfani da ita tashige ta ta bu’de idanuwanta ahankali ta sauke su Akan face ‘dinsa dake daf da Tata har dogayen hancinansu na gugan juna.

STORY CONTINUES BELOW

Matsowa bakinsa yayi daf da nata idonsa na kallon qwayar idanunta a wahalce yace,

Gud morning sweetheart..

Daqyar ta tattaro ‘dan kuzari ta bu’de baki zata amsa masa ya toshe bakin da nasa Yana kallon idanuwanta.

Rintse idanuwan tayi da sauri jikinta na fara rawa..

Passionate kiss yake Mata cikin nutsuwa tareda sake shigewa jikinta Yana lumshe idanuwa yanayin buqatar mace na shigarsa sosai sbd Koda yake Chris bai ta6a neman mataba sbd yanada tsananin qyama.

Mutuwa jikinta yayi batayi wani qwaqwaran motsi ba saidai hawaye dage bin fuskarta da gudu.

Lokacinda yakai hannuwansa kan qirjinta kusan atare suka saki ajiyan zuciya kaman wa’inda aka watsawa ruwan qanqara.

Yanda yake kissing ‘din bakinta cikin so da kulawa yasa buqatarsa ta ida tasowa gabaki ‘daya ya zame rigar jikinta yafara wasa da qirjinta Nan kuka ta yafara sautin fitowa ahankali Amma tuni yafara Nisa shi.

Sosai ya gigita yafice hayyacinsa sbd jinsa a inda baitaba zuwaba..

Kuka tasake Mai qarfi Wanda yashiga har cikin zuciyarsa Nan take ya dakata da abinda yake Shirin yi ya mirgina gefe jikinsa na saki.

Jin kukanta na tsananta ya juyo a hankali ya jawota jikinsa ya rungume jikinsa na tsananta saki.

Saidayaji ta daina kukan ya zareta daga jikinsa tareda saukowa ya shige toilet.

Wanka yayo yafito ‘daure da towel ya kalleta yaga duk a firgice take ya qaraso ya zauna bakin gadon tareda jawota jikinsa cikin sanyin murya yace,

I’m sorry ayeeshah..

‘dagowa tayi takalli idanuwansa taga har time ‘din jajir suke ta sunkuyar dakai tace,

Please take me home Deen.

Kallonta yayi yaji muguwar desire takuma taso Masa sbd yanda tayi maganar kaman a shagwa6e.

Sakinta yayi tareda miqewa Yana tsayawa gaban mirror yace,

I’ve called a mechanic he’ll soon be there to see the car.

Turare ya fesa tareda saka wata jallabiyar Nan yafito kaman wani balarabe ya juyo ya kalleta yace,

My love lemme go and order breakfast for us.

Ficewa yayi sbd son matsawa daga ganinta Dan jiyake kaman zai iya loosing control.

Saukowa tayi jiki a mace ta ida zame rigarta dayabari bakin qafafuwanta ta fa’da toilet.

Wanka tayo ta ‘dauro towel ta fito.

Gashinta dake sake duk baki bakinsa ya jiqe sbd tsawonsa saiya kwakwanta a kafa’dunta da wuyanta.

Tunda ta fito ya qura Mata ido Sam batayi tunanin yadawoba.,,

‘dauke Kai yayi tareda maida hankalinsa kan black tea ‘din dayake kur6awa ahankali.

Kasa qarasowa tayi ta tsaya gabanta na fa’duwa ga tsananin kunyarsa datakeji.

Jin Bata motsaba yasa ya ‘dan juyo ahankali yaga Sai kakkama jiki take tanajan towel ‘din dake ‘daure a jikinta baisan sanda yasaki murmushin qarfin haliba tareda aje cup ‘din hannunsa ya taso yazo gabanta ya riqo hannunta har zuwa gaban mirror ya tsaya bayanta Yana kallonta ta cikin mirror.

Daqyar ta iya shafa Mai ka’dan tareda fesa turare ta juyo kanta na kallon qasa.

Kallonta yake Yana qoqarin controlling kansa ya riqota ya zaunar tareda fara Bata breakfast cikin nutsuwa tana ci.

STORY CONTINUES BELOW

Ba wani sosai taciba ta ture hannunsa tareda girgixa Kai alamar ta qoshi.

Kallonsa tayi kaman zatayi kuka tace,

My clothes..

Kallon farar fatarta yayi kafin ya miqe ya ‘dauko kayan daya siya jiya ya miqa Mata ta kar6a tana bu’dewa taga doguwar rigace har qasa Amma batada hannu tai saurin kallonsa yace,

Manage..

Kar6a tayi tashiga toilet tasako ta fito ta zauna nesa dashi sbd Jin kanta datake uncomfortable cikin rigar.

Dawowa kusada ita yayi tareda kamo hannunta Yana cewa,

Come and teach me some duas.

Tsakiyar gado ya zaunar da ita shikuma ya kwanta tareda ‘dora kanshi saman cinyarta Yana kallon face ‘dinta.

A takure ta bu’de baki saita kasa magana ta maida bakin ta rufe tana numfashinta na fita da qarfi.

Kallon yanda qirjinta ke bugawa yayi ya ‘daga hannu ya sunkuyo da kanta ya ha’de bakinsu.

Wannan karon jikinsa ya kar6u sosai ya kwantarda ita tareda zura hannu ya rage hasken ‘dakin ya zame handless rigarta yaja bargo ya rufesu.

Duk yanda yaso controlling kansa kasawa yayi Saida ya mayarda ita cikakkiyar mace duk da shima yaji jiki Dan ba qaramin gigicewa yayiba da sabon alamarin daya tsinci kansa aciki…5

Ayshah kuwa Banda kuka Babu abinda take Dan kuwa ko hannunta Bata iya ‘dagawa.

Daqyar yasamu ya daidaito numfashinsa ya jawota jikinsa ya rungume cikin wani mugun sonta dake qara hudasa yafara lallashinta.

Wahallalen bacci da zazza6ine suka dauketa ya sauko gadon ahankali tareda kunna wayarsa yakira shaikh yayi masa bayanin yanda zaiyi wankan janaba ya fa’da toilet yayo wanka yadawo bakin gadon yazauna gadinta sonta da tausayinta na shigarsa.

Lokacinda ta farka bacci ya ‘daukesa a gurin ta saki wani sabon kuka zuciyarta na karyewa ga mugun zazza6in datakeji.

Kukantane ya tadashi ya tashi da sauri ya zauna kusada ita tareda juwota yafara lallashinta kaman zaiyi kukan shima.

Daqyar yasamu tayi wanka ya dawo da ita sukayi sallar azahar da ake Kira.

Abu kaman wasa saigasu da kwana uku a gurin Dan tuni soyayya tayi tasirin shagaltar dasu suka Sha amarcinsu ba damuwar komai.

Yau tunda ta tashi gabanta ke fa’duwa sbd motarsu da aka gama gyarawa Kuma ayau ‘din zasu koma gida.

Tsaye take gaban mirror ‘daure da towel tayi zuru cikin tunani ya duqo tareda rungumota ta baya ya ‘dora kanshi saman wuyanta a kasalance yace,

My love..

Juyowa tayi ta kallesa ya hure Mata ido tareda kissing idon bayan ta lumshe yace,

Baby let’s stay here I don’t want to go back.

Shigewa jikinsa tayi ta kwantarda Kai a sanyaye tace,

No Deen let’s go home.

Kanta dake jiqe da ruwan wankan tsarkin datayi ya shafa Yana cewa,

Ok but I will take you to a saloon to dry this hair first.

Bata basa amsaba sbd bakinta daya cafke da nasa Yana kallon eyes dinta data lumshe…Nan yaqara shagaltar dasu Saida suka Kuma making love kafin sukai wanka a gaggauce suka fito.

Driving yake Amma hannunsa ‘daya na riqeda nata harsuka iso cikin gari..

Tana ganin ya Kama hanyar anguwarsu hawayen datake riqewa suka 6alle Mata yayi saurin yin parking ya jawota jikinsa.

STORY CONTINUES BELOW

Sun ‘dan Jima ahaka kafin tayi qarfin halin janyewa tace,

Yatafi zata qarasa da qafa Dan batason yashiga anguwar Dan koba’a fa’daba tasan fitina nacan qasa tana jiransu musamman mashi da komai zai iya faruwa dashi idan yashiga anguwar Yan gidansu suka ganshi.

Kallonta yayi cikin damuwa yace,

No ayeeshah I will drop you home.

Riqe hannunsa tayi cikin karyar da kai tace,

Please deen don’t be stubborn now.

Badan yasoba ya yarda ta yabarta ta tafi bayan ya miqa Mata wayarsa ‘daya Dan yariqa waya da ita Amma taqi karba.

Saida yaga tashige konar layin gidansu ya iya barin gurin ya nufi gida.

Tun kafin ta qaraso abbakar dake zaune qofar gida tareda Ahmad ya hangota yayi saurin sake kallawa yaga ita ‘dince ya Kira sunanta da ‘dan qarfi nansu Ahmad suka lura da ita.

Umar dake taredasu baba a Palo Yana yimusu bayanin haryanzu ba wani bayani daga ‘yan sanda Sai sukaji ankira sunanta bai qarashe abinda yake fa’daba ya fito da sauri daidai lokacinda tashigo gidan Nan kowa yafito cikeda fargabar yanayin dazasu ganta Amma ga mamakinsu Sai sukaganta lafiya qalau dansu a tunaninsu tanacan suna azabtarda ita kaman yanda akayiwa su baba.

Durqushe tayi gabansu baba malam Banda kuka babu abinda takeyi musamman yanda taga duk sun yamutse sbd tunani da fargabar halinda take ciki.

Saidata sukaga kukan yaqi tsayawa baba malam ya kalleta murya a karye yace,

Ayshah kidaina kukan haka ya Isa kije ciki abata abinci ta huta anjima zanyi magana da ita Kuma Kar Wanda ya tambayeta komai.

Kamata su husna sukayi suka nufi ciki da ita kowa da abinda yake saqawa arai.

Da daddare baba malam ya Tara kowa yakirata cikin ‘daure fuska yace,

Ayshah,,

Na’am”’tace muryarta Bata fita sosai.

Ayshah kina saneda yau kwana hudu kenan da 6atanki Kuma ‘yan uwanki da sauran mutane sunga lokacin da wannan yaron ya ‘daukeki?

Eh ”””tace hawaye na gangaro Mata.

To yanxu inason sanin abinda yafaru bayan nan Dan ‘daukar mataki.

Fa’duwa gabanta yahau yi cikin rawar murya zufa na keto Mata tace,

Wani guri yakaini yace su ajeni Kuma bansake ganinsa ba Sai yau Yana zuwa ya daukoni ya dawo dani.

Kallon tsaf yayi Mata yace,

Inane inda yakaiki?

Share zufa tayi tace,

Bansan ko inaneba sbd ‘daure idona akayi.

Mata ne yakaiki gurinsu ko maza?

Mata ne””””ta fa’da da sauri.

Kintabbarda gaskiya Kika fa’damin ayshah.

‘daga kai tayi hawayen baqin cikin qaryarda tayi suna gangaro mata.

Cikin zafin zuciya da takaici baba alhaji yace,

Wlh Daman ni nasan sunanmu sukeson 6atawa shiyasa ya ‘dauketa yakai ya boye yanxu yadawo da ita Dan mutane suyi tunanin anbata Mata rayuwa.

Tabbas hakane baba malam yafada Yana jinjina alamarin cikin ransa Nan kowa zuciyarsa ta yarda da hakan ne suka hau tofa Masa mugayen adduoi.

Umminta da ya Umar kuwa hakanan zuciyarsu takasa aminta da hakan musamman yanda suka lurada yanda fatarta tayi wani fresh Sai glowing take.

Bayan komai ya lafa ummi takira ‘dakinta takuma tambayarta harta bu’de baki zata fa’da Mata saiga babanta yashigo ta ha’diye zancen tareda sunkuyar da Kai Nan suka hau yimata nasihar data matuqar sanyaya jikinta ta koma ‘dakinsu tana matsar hawaye.

Da daddare ya Umar ya Aiko kiranta Nan taji gabanta ya Fadi sbd tuno yanxu tanada auren wani akanta.

Hakanan ta miqe jiki ba qwari ta tafi.

Polon mama sakina Daman suke fira can ta nufa mamar na ‘daki ta shika’dai ne zaune a palon Yana kallon ‘yar qaramar tv ‘dinta dake kunne ana tafseer.

A darare ta zauna a qasa kaman yanda tasaba saitaga yadawo kusada ita ya zauna suna fuskantar juna.

Da mamaki ta ‘dan ‘dago ta kallesa ta ‘dauke Kai tareda gaidashi a sanyaye.

Amsawa yayi Yana kallon  hannuwanta datake wasa dasu yanajin sonta na shigarsa Dan baigane mahimmancinta a rayuwarsaba saidata 6atan Nan yagane samunta shine kwanciyar hankali da cikar burinsa.

Cikin son nuna canzawarsa ya ringa janta da fira Amma saidai ta ‘daga ko girgixa Masa Kai.

Hakadai harsuka Dan dauki Time tukuna yabarta ta tafi yanabin bayanta da kallo.

********

Bai Isa gidaba saidaya tsaya wani masallaci yayi sallar magriba da Isha,,

Tunda yayi horn Mai gadi ya bu’de Masa gate yashigo ya hango mum ‘dinsa tafe cikin farin ciki da murnar ganinsa sbd tun sunacan yayi wayada ita ya sanarda ita cewan yayi tafiya da friends ‘dinsa motansu ta lalace.

Rungumesa tayi cikin Jin dadi tareda cewa,

I missed you so very late my boy.

Cikin kulawa yace,

I love you mum.

I love you too my sweet boy.

Suna shiga Palo Davina ta taso da gudu ta rungume shi tana cewa,

Wow Nik you look fresh.

Dariya mum tayi tareda cewa,

My boy is slowly becoming a big man right?

Murmushi yasaki fuskarsa na bayyanarda annashuwa yace,

Yes mum your boy has finally become a man.

Batareda ta fahimci zancensaba takama hannunsa suka nufi dinning.

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

_Viawattpad@mamuhgee_

              *24*

   

Da daddare dukkaninsu kasa bacci sukayi musamman mashi Sai juyi yake kewar matarsa na shigarsa,

itama anata 6angaren lafewa tayi Dan Kar juyin yayi yawa ayi zargin wani Abu.

+

Washe da asuba cikin ‘dakinsa yayi sallarsa Yakoma ya kwanta gari na waye saiga mum da Bible ‘dinta tafara jero Masa adduointa yanaji ya lafe kamar maiyin bacci sbd jiyake kaman tana watsa Masa ruwan zafi a kunnuwa.

Tana gamawa ta tadashi tareda kallonsa cikin kulawa tace yatashi ya shirya lokacin zuwa makaranta nayi.

Lumshe fararen lazy eyes ‘dinsa yayi yanajin tsananin buqatar son ganin ayshah ya sauko daga gadon ahankali tareda miqewa ya fa’da toilet.

Duk iya zagayen dazaiyi yayi a makaranta da anguwar Amma baiga ko alamar ganinta ba haka ya lalla6a Yakoma gida a wahalce zuciyarsa ba da’di.

Itama dai Kam sukuku ta wuni ba wata walwala gashi ko maganar zuwa makaranta ba Wanda yayi Mata.

Abu kamar wasa saigasu har tsawon sati Basu ga junaba ita Sam anhata fita yanzu shikuma Yayi yawon yayi neman Amma Babu alamarta.

Sati na biyu kenan da yanxu Kuma zuwa lokacin daga shi har ita kowa danginsa sun gano Yana cikin damuwa ita tayi wata irin Rama shikuma rigis ya kwanta ciwo.

Zaune take tana kallon yanda su husna ke Shirin fita zuwa gidan anty Amina a sanyaye ta bu’de baki tace,

Wai sauri da ‘dokin me kukeyi na zuwa gida musamman make husna.

Asma’u dake saka hijab tace,

Fa’da Mata zamuyi tazo taga kayan lefen da ya Umar ya ha’da miki.

Duk da batada wani kuzari a jikinta batasan sanda ta tashi zaune ba ta kalli asma’un da kyar tana ha’diye yawu tace,

Lefen me?

Kallon rainin wayo asma’un ta jefeta dashi kafin tace,

Na aurenku Wanda za’ayi Nanda sati biyu.

Hawayen datake dannewa ne suka 6alle Mata tayi saurin juya musu baya kuka na qwace Mata.

Binta da kallo sukayi basuce Kuma cemata komaiba suka fice.

Bayan gadonsu tashige tafara rero kuka cikin tashin hankali tareda rashin sanin abinyi.

Kamar daga sama saiga nuratu tashigo ‘dakin tana ganin halinda take ciki ta qaraso gurinta da sauri tana kallon yanda idanuwanta sukai mugun kumburi.

Kasa tambayarta dalilin kukan tayi cikin sanyin murya tace,

Anty ayshah ummi ce tace nazo nace Miki ki shirya mutafi gidan anty Amina muma sbd duk yau zasuso ganin kayan aurenki gwara ki ‘dan fita.

Kallon nuratu tayi da jajayen idanuwanta kamar zatace Bata son fita Koda tsakar gidan ne saita tuna tana tsananin buqatar ganinsa Dan sanin abinyi.

Wanke fuskarta tayi tareda canxa hijab tafito..

Gidan nasu Ashe tuni yafara cika da ‘yan uwansu dake garin Sai murna da farin ciki suke.

Kanta a sunkuye tayita gaidasu harsuka fito gidan.

Tunda suka fito take tunanin hanyarda zatabi tagansa suyi magana.

Daf dazasu Isa unguwarsu anty amina kamar daga sama saita hango Davina sun fito wani qaton mall itada mum da Finn..

STORY CONTINUES BELOW

Rarraba idanu tahauyi kozata gansa Amma Bata gansa ba.

Dakatarda Mai napep ‘din dasuke ciki tayi tareda cewa yabi bayan motarsu mum ‘din.

A gate suka tsaya tareda miqawa Mai gadi ledojin dasuka siyo suka Kuma  barin layin gurin batareda sun shiga gidaba.

Fitowa napep tayi ta matso kusada maigadi dake qoqarin shiga ciki yakai saqon ta qaraso da ‘dan sauri tace,

Please is Deen inside…. sorry I mean Nik.

Kallonta up and down yayi Yana mamakin dagon hijabinta dake Jan qasa Amma wai nik take nema.

Yes,,,yace Mata Yana jiran Mai zata Kuma cewa tace,

Please I wanna see him… I’m his school mate.

‘dan nazari yayi Amma gudun laifi gurin oga Nik ‘din saiya ce tashigo yakaita.

Matsawa tayi jikin napep ‘din ta kalli nuratu dake kallon ikon Allah tace,

Nuratu kije gidan anty zainab karkije gidan anty amina zan same acan Zan fa’dawa wata qawatane maganar aurena Dan taje.

Badan ta yardaba ta ‘daga kai sukabar gurin da Mai napep itakuma da sauri tabi bayan Mai gadin Dan tasamu tayi magana da wuri ta fito kafin su mum su dawo.

Qaton qyataccen palon gidan yashiga da ita tareda nuna Mata kujera ya qwalawa Deborah Mai aikin gidan Kira ta fito da sauri ya miqa Mata ledojin hannunsa tareda cemata taje sama tafadawa Nik yanada baquwa.

Kallon ayshah tayi cikeda mamakin ganin Mai hijab a gidansu.

Sama ta hau tayita knocking can qasan maqoshi yace,

What?

Murya na rawa tace,

Sir one lady is here to see you.

Tsaki yasaki sbd baita6a kawowa arai ayshah zata iya zuwa gidanba yanxu.

Korota yayi ta sauko takalli ayshan tace yace bayason adamesa.

Kallon Deborah ayshah tayi idonta na cikowa da hawaye tace,

Please go and tell him it’s ayshah.

Kamar bazata komaba saita koma ai tana ta6a qofar ya daka Mata wata gigitacciyar tsawa a rikice ta juyo saitaga ayshan bayanta.

Tura qofar ‘dakin ayshah tayi tashiga ya Ciro kansa a fusace zai fara zuba masifa idanuwansa suka sauka cikin nata baisan sanda ya zaburo da qarfi ba yayo gurinta yayi Mata wata kyakkyawar runguma itama sake shigewa jikinsa tayi tana qara qanqamesa.

Deborah na ganin haka tayi saurin barin gurin zuciyarta na mamakin ayshan.

Sun Jima ahaka kafin ya jata suka zauna bakin gado ya riqo hannuwanta Yana kallon face ‘dinta a kasalance yace,

I missed you so badly my love.. please don’t ignore me like this again.

Kasa magana tayi ta lafe cikin jikinsa tanajin nutsuwa na da farin ciki na shigarta na ganinsa.

‘dagowa yayi ya kalli face ‘dinta Yana shafowa yace,

You look so pale my love..

Fuskarsa ta kalla tace,

You don’t look good too.

Matsoda fuskarta yayi kusada tasa Yana kallon cikin idonta yace,

What do you expect to see my love,,,,I’m nothing without you ayeeshah.,

I can’t imagine my life without you in it…

Sake shigewa jikinsa tayi hawaye na taruwa cikin idanuwanta na tausayin kansu Dan ko ita tasan Rashi agunta babban qalubalene ga rayuwarta.

‘dago fuskarta yayi cikin kulawa yace,

My love is everything ok?… I mean you here..

Gabanta ne ya Fadi da abinda zata fa’da Masa ta zame jikinta tareda miqewa tsaye kanta a qasa tace,

Deen…Sai kuma tayi shiru.

Miqewa yayi ya Kuma kamota ya zaunar da ita kan cinyarsa tareda zare dogon hijabinta ya aje ya kalleta da kyau yaga ta qara wani irin fresh fatarta Sai glowing take Sai ‘yar ramar datayi..

shafo wuyanta yayi har zuwa qirjinta ta riqe hannunsa ya kalleta da lazy eyes ‘dinsa tareda kallon red lips ‘dinta Yana Kai bakinsa kansu.

Kissing dinta yake cikin tsananin buqatarta..

Rigarta ya zame yana Kai hannunsa kan qirjinta yayi saurin zare bakinsa anata yakallesu sbd cikar dayaji sun qara da laushi.

Rintse idanuwa tayi cikin kunya yasaki murmushi tareda kwantarda ita a gadon yabita.

Saida komai ya lafa ya ‘dauketa yakaita toilet sukayo wanka suka fito tana gyara zaman hijab ‘dinta tace,

Deen there’s a problem..

Saurin aje turaren dayake fesawa yayi ya riqota yace,

What is it my love.

Idonta na kawo ruwa tace,

It’s about the wedding they’ve fixed for me and ya Umar,, the preparation for the wedding has started.

Jikinsa taga ya’dau rawa idanuwansa na canxa launi ya kalleta cikeda baqin ciki da takaicin zancen yace,

I’m sorry my love but I can’t hide this anymore I will go and talk to them right away.

Riqosa tayi tana hawaye tace,

Deen please don’t go let’s find a solution first this is not gonna work.

Zama yayi tareda rintse idanuwansa Yana karanto adduar da shaikh ya koya Masa ta idan Rai ya 6aci.

Saida ya share kusan minti goma ahaka kafin yaji zuciyarsa ta rage quna suka fito Yana riqeda hannunta suka shiga mota sukabar gidan.

Shopping yakaita Amma Sam taqi yarda ta fita motar dole yashiga yayo Mata siyayya yakaita gidan anty zainab.

daqyar ya iya rabuwa da ita tashiga shikuma ya wuce.

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

                 *25*

Tun ranar Ba’a Kuma barinsu fitaba har tsawon kwana hudu duk inda hankalinta yake yayi mugun tashi musamman yanda taga shirye shiryen biki Sai da’da kankama suke Dan yanxu sati ‘daya ne yarage kullum tana quryar ‘daki a takure batada aiki Sai kuka ga wani mugun zazza6i da kullum dashi take kwana..

Duk hanyarda tabi danta samu ta fita batayi aikiba  ga Yaya Umar da yanxu wata soyayya yakeji saima hakan yakuma sakata cikin babban tashin hankali..

A 6angaren Deen ma kusan haukacewa su mum yayi ya ‘daga musu hankali yaqi ci yaqi Sha ga ciwon damuwa da yunwa daya bayyana qarara a tattare dashi Nan hankalin mum yayi mummunan tashi takasa zaune takasa tsaye Amma yaqi fa’da Mata damuwarsa.

Yau Kam daqyar yaga safiya yanayin sallar asuba ko wanka baiyiba ya zari mukullin mota ya fice.

Direct anguwarsu ayshah ya nufa yanayin parking ya fito ya doshi gidansu Kai tsaye ba tsoro ba fargaba.

Kasancewar da safe ne Babu kowa a qofar gidan dai Sai qarfe goma ake fara karatu.

Qofar gidan a bu’de take Kuma Yana jiyo sautin karatun alqur’ani da wani yakeyi a ‘dakin dake kusa daga ciki.

Sallama yayi ahankali ba’ajiba ya ‘dan ‘daga murya yakumayi Yana cusa Kai cikin babban soron gidan.

Ya Ahmad dake ‘dakinsa Yana karatun Qur’an ya aje ahankali tareda tasowa yafito Dan ganin wake sallama da sassafe haka.

Murza idonsa yayi yakuma kallon Wanda ke tsaye cikin doguwar farar jallabiya ya matso a zafafe zai cakumosa Deen ya riqe hannunsa tareda ‘dago lazy eyes ‘dinsa dasukai ja Kai tsaye yace,

I’m not here for this…I came to see my ayeeshah.

Uwarka zaka gani ba ayshah ba””’sukaji anfa’da daga bayan Ahmad…

Umar ne tareda sani da baba alhaji..

Fixge hannun Ahmad baba alhaji yayi daga hannun Deen bai tsaya komaiba ya wankeshi da lafiyayyan Mari.

Rintse ido yayi da qarfi sbd Marin yashigesa Amma bayajin yau zai ja baya.

Nunasa da yatsa baba alhaji yayi cikin 6acin Rai yace,

Wannan Marin qoqarin 6ata Mana suna dakayine ta hanyar sace  Mana ‘ya dan sunanmu ya 6aci.,,Kuma inason maza tun kafin mutane su taru kabar Mana gida.

‘dagowa yayi da fuskarsa datayi ja sbd Marin ya kalli baban yace,

Ayshah is my wife and….

Naushi Umar yakai Masa a baki kafin ya cakumo wuyansa cikin zafin Rai Yana huci yace,

Idan kakuma fa’dar ko sunanta a wannan qazantaccen bakin naka saina fasa makashi da kwalba.

Sakinsa yayi tareda turasa baya da qarfi yana nuna Masa qofa da Ido yace,

Maza bar Nan tun kafin hakurina ya qare.

Gyara tsayuwa sukaga yayi yakuma kallon baba alhaji danko kallon Umar bayasonyi danji yake zuciyarsa zata iya bugawa idan Yana kallonsa…yace,

Baba please let me see her we have something to tell you all….

Ta baya Umar ya fixgosa jiyayi zuciyarsa ta ‘dau zafi a hasale ya juyo ba zato ya saukewa Umar gigitaccen marinda Saida hancinsa bakinsa ya fashe..

STORY CONTINUES BELOW

Ahmad da sani na ganin haka suka rufesa da duka tako ina Nan hayaniya ta tashi kan kace me gabaki ‘daya ‘yan gidan sun fito Nansu abbakar suka da’du sukayi Masa mummunan duka.

Da qarfi nuratu tashigo ‘dakin tana kallon qofa kamar munafuka tace,

Anty ayshah zasu kashesa gashican su Yaya na dukansa yaqi ko motsawa….

Tafi kwana biyu batada lpia ko qwaqwaran motsi batayi idanuwanta sun ko’de sbd kuka tanajin abinda nuratu ta fa’da Bata tsaya Jin sauran ba ta tashi tabar ‘dakin da gudu..

Tundaga nesa Umar ya hangota yayi saurin cewa su anty su riqeta.

Riqeta sukayi ta qwace da qarfi ganin wani mugun dukan da Umar yakaiwa Deen ‘din a baki.

Zubewa tayi gabansu tareda riqe qafafun baba malam cikin tsananin kukan fitar hankali tace,

Dan allah baba kace su daina,zasu kashesa wlh ya musulunta shima musulmi ne yanxu,,,,Ina tsananin sonsa Kuma da aurensa a…..

Wani lafiyayyan Mari taji ya sauka a fuskarta tana ‘dagowa taga babanta tsaye ransa a matuqar 6ace

Umminta kuwa cikin gida ta koma da sauri sbd jiri da qirjinta dataji na neman bugawa.

Cikin wani irin yanayi na 6acin Rai baba malam ya juya baya yace,

Abbakar ku ‘daukesa ku fitar dashi daga gidan Nan yanxu banason sake ganinsa.

Jansa sukayi sukayi suka Kai har bakin motarsa daidai Finn yabiyo ta anguwar yaga motar Nik ya tsaya saikuwa yagansa yashe cikin jini a rikice yafito yakira mum kafin ya ‘daukesa yabar gurin da mugun speed.

Suna Isa asibitin akayi gaggawar kar6arsa kayi cikin emergency dashi sbd numfashinsa dayake qoqarin barin jikinta.

Ko ka’dan wannan karon ba sauqi cikin alamarin Dan kallo ‘daya zakayi musu kasan Bata wani tashin hankali sukeba ta lapiyar ‘dansu suke.

Zaune suke jigum jigum idanuwansu a ko’de da tsantsar damuwa da tashin hankali musamman mum da duk tayi wani mugun laushi Dan a yanda taga ‘dan nata tasan yanada wuya yayi surviving..

Kuka takuma fashewa dashi tana fa’dawa jikin Finn.

Ba’a samu shawo kan matsalarba sai maraice sosai Kuma Yana farfadowa yafara qoqarin tashi mum da Finn sukayi saurin taresa yakalli mum da kumburarun idanuwansa saikuma ya fashe da kuka ahankali,

Jikinsu ne yayi sanyi gabaki ‘dayansu ganin yanda yake kuka gashirban cikin tsuma zuciya.

Dafasa mum tayi tana tsiyayar hawayen tausayinsa Finn ma matsowa yayi ya dafasa shima zuciyarsa na karyewa.. Davina ma jikin Nik ‘din ta kwanta tana kuka ahankali sbd Basu ta6a ganinsa cikin irin wannan yanayin ba.

Washe gari jikin nasa ya’dan samu sauqi ya tashi zaune dai dai shigowarsu mum ‘dauke da breakfast cikin qaton  basket.

Kallonsu yayi ‘daya bayan ‘daya da kumburarun idanuwansa kafin ya miqe ya tsaya gaban mum cikin shaqaqiyar murya yace,

Mum,,,

Kallonsa tayi tareda bashi duka nutsuwarta dan itama yau so take suyita ta qare Dan saiya fa’da Mata damuwarsa sbd tariga ta yanke shawarar barin qasar zasuyi zasu koma can Paris da Zama tareda dadynsu.

Kansa a qasa yace,

Mum I,,,I I’ve converted to Islam…

Jirine yayi mugun ‘dibarta Finn yayi saurin tarota..

Bai ‘dagoba yaci gaba da fa’din,

And I’ve got married to ayeeshah,,the Ninja lady….

Wani gigitaccen mari tasakar Masa dayayi sanadiyar fashewar gefen bakinsa ya zube gabanta tareda riqe qafafuwanta yasaki kuka Mai tsima zuciya.

Zanye qafafuwanta tayi tareda fashewa da kuka Mai tsanani yakuma rarrafowa cikin kuka zai sake riqota tayi saurin janyewa idanuwanta na zuboda hawaye cikin kakkausar murya da tsantsar baqin ciki tace,

Finn take me away from here I’m feeling surfucated,,,,

Da sauri ya riqeta Yana qara fashewa da kuka yace,

Mum please let me explain…

Wani gigitaccen marin takuma sakar Masa tareda kallonsa a zafafe kamar zuciyarta zata qone tace,

you are on your own Nik…i disown you,,

I don’t want to see your face ever…

I regret my love for you…

Go and don’t ever show your face to me…

You no longer belong to this family…

I…I.. numfashinta ne yafara qoqarin ‘daukewa Finn yayi saurin tarota yafice da ita.

Bin bayansu Davina tayi tana waiwayen ‘dan uwanta cikin qaunarsa da tausayinsa.

Sunkuyar dakansa yayi Yana kuka cikin tsananin damuwa da tashin hankali tareda rashin sanin abinyi.

Koda sukaje gida rufe kanta a’daki mum tayi tareda fashewa da kuka hartana shaqewa sbd duk duniya ba abinda take matuqar so da qauna kamar Nik ‘dinta Dan tarigada tasan bazata ta6a iya rayuwa babushi ba.

Dukkanin familyn gidan aranar Babu Wanda yayi bacci saima kwanan qunci da kuka dasukayi musamman shi da mum.. Davina ma Bata rintsa ba kuka takwanayi itama.

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

                 *26*

Babban alamarin tashin hankalin ba qaramin Dakar zuciyarsu malam babba yayi ba Dan iya ,’daukar zafi sun ‘dauka da ayshah shiyasa malam ya ‘dau babban mataki cikin 6acin Rai na hanata fitowa Koda tsakar gidan bare harta fita.

Tayi kuka har qarfin jikinta ya qare saidai na zuci,

Fuskarta kuwa ta ko’de tayi wani haske kamar Mara jini.

Nuratu ce kawai mai tausayinta tana qoqarin tausauta Dan ganin ta rage damuwa Amma Sam kullum alamari qara gaba yake Dan ba abinda ke ‘daga Mata hankali kamar yanayinda aka fitardashi batada tabbacin Yana Raye….

Hakan take tunanowa taji kamar zata haukace wani sa’in Sai nuratu ta ririqeta…

Kamar lokuta da dama yauma kwance take ta takure qarshen qatuwar katifarsu zazza6i takeji sosai Amma batajin ko motsawa zata iya yi sbd raunin dake zuciyarta yayi nasarar karya dukkanin garkuwar jikinta.

Qarasowa nuratu tayi ta zauna gabanta tareda kallon yanda hawaye suka bushe Mata a fuska ta dafa qafafuwanta cikin sanyin murya tace,+

Anty ki misalta min inda yake zance nadubo mikishi Dan hankalinki ya ‘dan kwanta..

Da sauri ta ‘dago idanuwanta dasuka koma qanana sbd kuka ta kalli nuratu batasan sanda ta rungumetaba cikin farin ciki.

Gidan anty zainab tayi qaryar zuwa aka barta tana fita daga gidan saita fara zuwa gidan anty zainab ‘din Sai yamma sosai ta fito ta nufi asibitin da ayshah ta misalta Mata

Bata Sha wata wahalar gano room ‘din dayakeba tana shiga Nan ta tarar da wani tashin hankali.

Zaune yake kan daddumar sallah kansa a qasa kuka yake kashir6an kamar ransa zai fita..

A darare ta qaraso gabansa takira sunansa cikin hawaye Dan baqaramin karyewa zuciyarta tayiba da ganin shima halinda yake ciki.

‘dagowa yayi Yana ganinta yasan nuratu ce qanwar ayshansa datake fa’da Masa ya kalleta cikin dashashiyar murya yace,

Ayeeshahna tana…

Katsesa tayi cikin hawaye da fa’din,

Ita tasani nazo Naga halinda kake ciki…

Rintse idanu yayi cikin Jin sabuwar soyayyar ayshansa ya bu’dese ya sauke akan nuratu tareda zubewa gabanta tayi saurin ja da baya jikinta rawa cikin kuka tace,

Me kakeyi haka??

Murya a shaqe yace,

Please take me to her,,,,I want to see her before I die coz I can feel my life is about to end…

I want to see and tell her how much she means to my miserable life because I’m the couse of all her pains…

Please please ple…..kuka yaso kwace Masa batasan sanda tayi saurin durqusawaba itama tace zata kaisa.

Ana Kiran magriba suka Isa anguwar..

Dayake duhu ya’dan fara Babu Wanda ya lura dasu suna,

Saidata leqa taga gabaki ‘daya mazan gidansu sun shige masallaci matan kuwa duk sunshiga ‘dakuna sallah tayi saurin kiransa yashigo takaisa ‘dakin da aka maida ayshan aka hanata fitowa.

Yana shiga tasaki ajiyar zuciya tareda barin gurin.2

Duhu ne a ‘dakin Amma Yana iya ganinta zaune kan sallaya ta cusa kanta cikin qafafuwanta tayi Nisa acikin tunani.

Jikinsa ne yayi matuqar saki ya qaraso ahankali ya zauna gabanta tareda Kiran sunanta can qasan maqoshi.

Kamar a mafarki taji muryarsa tana ‘dagowa sukai Ido biyu da qarfi ta fa’da jikinsa tareda fashewa da kuka tana qanqamesa.

Shima hawayen yake Yana qara shigarda ita jikinsa.

STORY CONTINUES BELOW

Daqyar suka lallashi kansu sukayi shiru suna sauke ajiyar zuciya…

A sanyaye yace,

Ayeeshah….I’m really sorry ayeeshah..

I’m sorry I was so blinded by love and  force you into marrying me and now you’re suffering it’s all because of me…

I’m nothing but a pain,,,a sorrow,,,a…..

Toshe Masa baki tayi kuka na qwace Mata tace,

I love you Deen,,,

I love you because I choose to…

I love you because my heart want to…

You change my life,,,,

you bring happiness in it…Deen I can’t live without you so please don’t leave me here I want to live with you…

Qanqameta yayi cikin kuka yace,

I love you ayeeshah,,,

I love you and I want you to know that will never change even I’m here or somewhere else….

‘dago da fuskarta yayi ya kalla cikin hawaye yace,

Promise me you’ll always  remember that I nuraddeen Aiden only love you ayeeshah,,,, you alone my ayeeshah,, promise me you’ll never forget that…

‘daga kai tayi hawaye na bin fuskarta da gudu…

Ya qara shigarda ita jikinsa shima Yana hawayen.

Mantawa sukayi da yanayin rashin kwanciyar hankali dasuke ciki suka Sha soyayyarsu kamar ranar suka fara ha’duwa da juna Dan kuwa soyayya Mai sanyi da shiga Rai ya nuna Mata Wanda tashiga ranta ta tsaya.,,

Kwance take cikin jikinsa lullu6e sbd dukkaninsu ba Kaya ajikinsu ta kwantar da kanta a qirjinsa tana Jin bugun zuciyarsa ta lumshe idanu tareda ‘dago Kai takalli raunikansa dake na’de da bandage takai hannu ahankali idonta na Tara hawaye ta ta6a yayi saurin rintse ido ta janye hannu da sauri sbd har cikin ranta tanajin ra’dadin ciwonsa cikin zuciyarta ta kwantarda kanta tareda qara lafewa cikin jikinsa..3

shafo kanta yayi yana rufe idonsa yanajin wani yanayi na shigarsa na qarason kasancewa da ita.

Qara ‘dago kanta yayi ya ha’de bakinsu Yana kallon face ‘dinta ba musu taqara bashi hadin Kai suka Kuma making love hankali kwance.1

Washe gari dukkanin familyn gidan suna babban palo gurin karatu adaidai wannan lokacin yafita yabar gidan batareda kowa ya gansaba…da Shirin gobe zaije yazo da shaikh ayiwasu baba bayanin aurensu.1

Ba laifi a Daren kwanan farin ciki sukayi dukkaninsu musamman mashi daya matsu gari ya waye yaje yazo da shaikh.

Washe gari gidansu yacika maqil da ‘yan uwansu na nesa Dana kusa sbd ranar ne za’a fara bikinta da ya Umar…

Hidima ake anata kaida kawo da hayaniyar biki itadai tana ‘daki kwance wani mugun zazza6i ke cin jikinta danko hannunta Bata iya ‘dagawa sbd kukan datasha…1

Nuratu ma nakusa da ita zaune cikin damuwa..

Ummi kuwa tun ranar da alamarin yafaru lafiya tafara yi Mata qaranci Dan baqaramin Dakar zuciyarta abin yayiba sbd Allah yagani tana tsananin qaunar ‘yarta bazataso ace tayi wani abin tir ba.

Kallon nuratu tayi daqyar ta iya bu’de baki murya a shaqe tace,

Nuratu kije kifa’da Masa an jawo ‘daurin auren gobe…

To nuratu tace asanyaye tareda ficewa,,,

Umar dake tsaye bakin qofa yazo magana da ita yanajin abinda tace yayi saurin barin gurin zuciyarsa na tafasa.

Yana bakin titi yaga shigar nuratu napep yatari mashin yabi bayanta.

Har ‘dakin dayake cikin asibiti saidaya bita yagani tana fitowa ya lafe bayan bishiya saidata bar asibitin ya fito Yana kallon qofar ‘dakin cikin wani mugun tunani.

Gaf da magriba Dr yazo ya sallamesa sbd takurawar dayayi a sallamesa ‘din…

Sallar magriba yafarayi kafin yafito cikin hanzari zuciyarsa na tsananta bugawa.

Amenity word yake Daman Kuma akwai qaranci mutane sosai a word ‘din…

Tafiya ka’dan yayi daga ‘dakin yaji saukar wani mummunan duka a tsakiyar kansa da qaton qarfen dayafi Kama da guduma…3

Baya yayi fuskarsa na rufewa da jini cikin mummunan yanayi ya yanke jiki ya fa’din jini nabin qasa.

Murmushin mugunta yasaki tareda barin gurin cikin Jin da’din samun nasara.

Cikin tashin hankali nurse datazo tagansa taje ta kirawo Dr Nan hankalinsu yayi mummunan tashi sbd jinin dake zuba sosai ga ba alamun Rai ajikinsa..

Waya Dr yafitar jikinsa na matuqar rawa yakira mum har kusan so biyar Sai ana shida ta ‘dauka cikin tashin hankali yayi Mata bayanin halinda Nik ‘din yake ciki.

Cikin mintuna qalilan ta suka iso hankali tashe

Suna ganin halinda yake ciki mum tace ayi musu Shirin komai subar qasar zuwa gobe.1

Duk inda hankalinta yake yayi mummunan tashi sbd har dare bashi ba shaikh…

Koda gari ya waye ko gani batayi sbd kuka gashi da ko Zama Bata iya yi sbd ciwo gashi Sai shirye shiryen ‘daurin aure ake bayan sallar juma’a..

Su anty amina ne suka shigo ‘dakin tareda kamota ta tashi suka kaita har cikin toilet daqyar ta iya ‘daga bucket ‘din tajuyewa jikinta har cikin Kai tafito suka miqa Mata Kaya ta zura aka fito da ita sbd Mai qunshi da’aka Kira.

Tana fitowa tsakar gidan wani mummunan jiri ya ‘dibeta sbd rashin qarfin jiki da zafin zuciyar daya yunquro Mata Nan take ta zube gurin asume…

Agigice sukayi kanta suna Kiran sunanta Amma ba alamar numfashi atareda ita.

Da sauri aka zuba Mata ruwa amma ba alamar zata motsa ba Nan hankali ya Kuma tashi su baba alhaji da ya Umar da mama sakina aka kwasheta Sai asibiti.

Cikin gaggawa aka kar6eta akai cikin emergency da ita.

Zama su mama sakina sukayi jiran tsammani har kusan awa ‘daya saiga Dr yafito ya nufi office ‘dinsa su baba da ya Umar suka bisa.

Zama yayi Yana warware tie ‘dinsa ya kafin ya kalli su baba dake raba idanun jiran bayani.

Alhaji maganar gaskiya yarinyar Nan tana fama da damuwa tareda yunwa Kuma hakan babban barazanace ga lafiyarta da abinda ke cikinta,,,,ma’ana juna biyun dake cikinta na wata ‘daya da kwanaki….5

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *27*

*_godiya Mai tarin yawa ga masoyan TAURA BIYU aduk inda suke.._*💋

Babbar Riga baba alhaji ya gyara Yana qara gyara Zama sbd shi Sam bai fahimci zancenba ya kalli Dr yace,

Aa wannan dakake magana ba itace Wadda muka kawoba,,

Wadda muka kawo itama tanan cikin ‘dakin sunanta ayshah Kuma budurwace Bata ta6a aure ba…yauma ne dai za’a ‘daura auren nata kaga mijin Nan a tsaye.

Takaici ne ya ‘dan Kama Dr Amma fahimtar dayayi da Rashin sanin komai dasukayi akan ‘yarsu saiya gyara Zama Dan sake musu bayani dalla dalla..

Alhaji maganar danake fa’da muku anan bayanine akan ‘yarku da kuka kawo..’yarku ayshah tana ‘dauke da ciki na haihuwa ‘dan wata ‘daya da satittika…

+

Sharce zufa baba alhaji yayi ya juyo ya kalli baba qarami dashima tuni babbar rigarsa ta Shirin ‘daurin aure ta jiqe sbd zufa…

Atare suka juyo suna aikawa Umar da zuciya tagama kashesa Banda mazari ba abinda jikinsa keyi idanuwansa kuwa ko gani sosai bayayi dasu sbd baqin ciki da tafasar zuciya…

Juyawa yayi a fusace zai fita baba qarami yayi saurin Shan gabansa tareda sharara Masa lafiyayyan Mari…

Ji yayi kansa na neman bugawa ya ‘dago da jajayen idanuwansa yakalli su baban yaga irin kallon dasuke Masa ya daki bango da qarfi kamar zautacce yace,

Karma kufara wannan tunanin,, tunda nake a rayuwata ko hannun ayshah banta6a riqewa bare har ni nayi Mata…..

To idan bakai bane wane?””””” Baba alhaji yafada da qarfi cikin zafin zuciya da 6acin Rai.1

Jiki sanyaye baba qarami ya kalli baba alhaji yace,

Muje gida mayi komai acan gaban malam babba.

Fitowa sukayi kowanne daqyar babbar rigarsa ke ‘daukarsa sbd kunya da baqin ciki..

Kallonsu mama sakina tayi cikeda damuwa tace,

Lpia kuwa?

Meke damunta likitan yace?

Fuskarsa na kallon wani gurin yace,

Ayshah cikine da ita Dan haka kitashi maza yanzu muje gida ayi komai can gaban kowa.

Yawu ta ha’diye daqyar jikinta itama Yana ‘daukar rawa sbd gabaki ‘daya ta nemi nutsuwarta ta rasa dajin wannan mummunan zance daga bakin baba alhaji.

‘dakin tashiga ta tararda ayshan ta tashi saurin ‘dauke Kai tayi cikin tashin hankalinta daya kasa 6oyuwa tace,

Taso maza gida zamu yanxu..

Ba musu ta sauko gadon ahankali jikinta na tsananta sanyi hakama fa’duwar gabanta na tsananta..

Koda suka fito su baba harsun samu mota sun shiga suna fitowa Umar yabar gurin yaje yahau mashin Dan bayajin zai iya shaqar numfashinda jinin Deen dake cikin ayshah yake shaqa.

Tunda suka shiga motar Babu Mai ko qwaqwaran motsi sbd kowada tunanin dayake ransa.

Umar ya rigasu isowa shiyasa koda suka iso ya Tara kowa a palon ana jiran isowarsu Dan ko magana baya iyayi bare yafa’di abinda yake faruwa..

Suna shigowa palon kowa yabisu da idanuwa sbd fargabar Jin koma menene Dan tun a yanayin Umar ‘din suka tabbatarda koma meyene bamai da’di bane.

STORY CONTINUES BELOW

Gyara Zama malam babba yayi ya fuskanci baba qarami yace,

Shehu lafiya dai Naga fuskokinku ba da’din kallo..

Gumi na qara yanko Masa yace,

Ba lafiya ba…

Wani ‘daci malam babban ya ha’diye tareda maida kallonsa ga baba alhaji dashima har lokacin zufa yake yace,

Bello yimin bayanin komai yanxu Ina sauraronka.

Yaya muna cikin gagarumin tashin hankali sbd mutunci da sunan wannan gidan ya gama lalacewa daga yau…

Ayshah gatanan zaune cikine da ita na haihuwa ma’ana dai cikin banxa..

Ba kowa daya ki’dima dajin zancenba ita kanta zabura tayi cikin masifaffen tashin hankali umminta dake kusada ita ta mayarda ita zaune tareda rufe Ido ta saukar Mata da kyakkyawan mari tareda fashewa da kuka numfashinta na qoqarin ‘daukewa da sauri nuratu da salma sukayo kanta duk da dukkaninsu jikinsu rawa yake sbd tashin hankalin dasuke ciki.

Malam babba kuwa qoqarin fita hayyacinsa yake sbd hawan jininsa daya Haye gabaki ‘daya Nan take zufa ta jiqasa yafara gani dishi dishi..

Hankali tashe su baba qarami dasu abbakar sukayi kansa ana Masa firfita hankali a matuqar tashe..

Rarrafowa tayi da sauri gaban malam babba ‘din tana kuka sosai zatayi magana babanta da zuciya tagama kashesa ya rufeta da duka tako ina Nan hankali ya Kuma tashi sbd ganin baban nata ya zube qasa Yana kuka sosai…

Ba qaramin duka baban yayi Mata ba Amma haka ta miqe baki na jini ta qara rarrafowa gaban malam babba cikin tsananin kuka tace,

Wallahi baba banyi watsi da tarbiyar da kuka bani ba wannan al’amarin qaddarace daga Allah wlh baba na yarda danayi babban kuskuren barin soyayya ta rufemin Ido nayi aure batareda saninku ba….

Shaqota Umar yayi ahasale yace,

Da wa Kika ‘daura auren?

Cikin tsananin kuka tace,

Niklaus..

Wurgi yayi da ita da qarfi cikin 6acin saida kanta ya daki dutsin da aka tare qofa dashi Nan take goshinta ya fashe duk da haka Bata tsayaba saima kukanta daya tsananta ta rarrafa taqara zuwa gaban malam babba da har lokacin numfashinsa bai daidaita ba ta riqo qafafunsa cikin tsananin kukan dayake jijjiga jikinta tace,

Baba wlh da gaske nake ban aikata zinaba na samu wannan ciki wlh aure…..

Hannu ya ‘daga ba zato kowa yaji kukan Marin daya sakar Mata.

Tsit sukayi cikin mamaki da tsoro sbd malam babba bai ta6a ‘daga hannunsa akan kowaba Sai yau.

Miqewa yayi su abbakar na riqe dashi numfashinsa na sama sama ya rintse Ido cikin kakkausar murya da bai ta6a magana  da itaba yace,

Daga yau nacire ayshah daga cikin zuri’ata,,,

Daga yau ayshah Bata cikin zuri’ar gidan Nan,,,

Daga yau na Kori ayshah daga cikin gidan Nan har abada bana buqatar sake ganin fuskarta,,,

Daga yau ko sunan ayshah karna kumajin wani ya furta acikin gidan Nan,,,

Kuma ban yafe ta ra6i ko ‘daya daga cikin zuri’ar gidan Nan ba haka Kuma ban yafe taje gida nijar ba da wannan mummunan abin kunyar…..

Cikeda tsoro da fargaba baba qarami ya matso zaiyiwa malam magana akan Kar akoreta ayimata duk wani hukuncin cikin gida…

Malam ya ‘daga Masa hannu idanuwansa na qarasa rufewa Nan hankalinsu Yakuma tashi…

Kasa motsawa tayi sbd babban tashin hankalin dataji…

Cikin zafi da ‘daga murya  babanta yace,

STORY CONTINUES BELOW

Umar fitar Mana da ita daga gidannan Kuma koni duk ranar data Kuma waiwayar gidannan ban yafe haihuwar danayi mataba…

Hannu ta ‘dora akai tareda fashewa da wani sabon kukan tashin hankali ta rarrafo gurinsa da sauri tana want irin kuka hartana shaqewa ya janye qafafuwansa tareda barin palon jininsa na hayewa danshima daqyar yake gani.

Gurin baba alhaji ta rarrfa tana kuka Mai ban tausayi da tsananin nadama shima yabar palon ta koma gurin baba qarami kukanta ya ta6a zuciyarsa matuqa sbd kukan datake ya wuce tunani dan komai na jikinta rawa yake…

Cikin tsananin tsawa baba yace,

Ka fitar da ita Umar…

Matsowa yayi jikinsa a sanyaye idanuwansa jajir Dan tun ‘dazu shima kukan yake kamar ransa zai fita sbd yasan ya rasa ayshah kenan tabbas daya sani tun farko zaice cikin nasane kodan ya sameta.

Idanuwansa a rufe yake janta,

Kuka take tana kiran sunayen su baba tana bayyana tubarta da Basu hakuri amma Saida Umar yakaita waje ya kalli cikinta wani baqin ciki ya taso Masa ya jefata da qarfi kan qaton dutsen dake qofar gidan cikinta yayi mummunan buguwa Nan ta dafe ciki cikin wata mummunar azaba sabbin hawaye na bin fuskarta…

Jitayi wani sanyi nabin cinyoyinta tasa hannu ta shafo saitaga jini…1

Rintse ido tayi cikin tsananin azaba da kuka ta miqe da qyar goshinta da bakinta na jini ga Wanda yake bin qafafunta ta tsaya ta kalli gidan sabon kuka na zuwar Mata ta juya jiri na ‘dibarta tayi titi.

Napep ta tsayar ko gani sosai Bata iyayi sbd jini daya daketa ga kukan datasha kamar na hauka Kuma har lokacin Bata daina kukanba.

Qofar gidansu Deen aka ajeta ta fito a dudduqe ta nufi gate maigadi na ganinta ya bu’de Mata sbd tun wancan zuwan datayi Deen yayi Masa kashedin datazo ya bu’de Mata kofa.

Aharabar gidan ta tarardasu mum sun rufe ko’ina zasu shiga mota Sai ganinta sukayi.

Tana zuwa gaban mum ta zube tana wani irin kuka Mai tsima Rai Dan nantake ya ta6a zuciyar Davina Da tsananin qaunar datakewa ‘dan uwanta tasa tafara qaunar ayshah ‘din.

Bu’de mota mum tayi zata shige tayi saurin riqe qafarta cikin tsananin kuka tace,

Mum pls I need to see him..I want to talk to him,,,I was thrown out of my house,my family,,,,

I have no one now,,,he is my only hope now….

Fusge qafarta tayi tareda damqarta tafara janta cikin masifa takai wajen gate ta watsar tareda nunata da yatsa cikin tsananin baqin ciki tace,

I’ve never hated something or someone so badly the way I hate you,,,

I hate you to the last core that I can strangle you to death…

My son Nik will never see you or be with you again because he’s already in somewhere else,,,

You’ll never set your eyes on him for the rest of your miserable existence…

So go, leave,stay out of our lives….

Cikin karaya da tashin hankalin Jin  zancen mum ‘din hawaye nabin  fuskarta tace,

Mum please don’t do this to me,,,if not for me please let me see him for sake of his unborn child…..

Cikin tashin hankali dukkaninsu suka zaro idanuwa musamman ma Davina da wani irin da’din zancen ya kasheta kafin tayi magana mum ta tura ayshan baya da qarfi ta fa’di kife Nan tasaki qara tareda dafe cikin Nan sauran jinin daya tsaya ya qara 6alle Mata ta kalli qafafuwanta da sauri taga yanda jinin ke gudu kafin tayi want motsi ruwan sama suka 6alle mum takalli su Davina ta nuna musu mota da Ido kafin ta bu’de jaka ta Ciro bundle ‘din one one thousand ta jefawa ayshah ta fa’da mota sukabar gidan aguje Sai airport suna Isa ko minti ashirin basuyiba jirginsu ya tashi sukayi bankwana da Nigeria..

STORY CONTINUES BELOW

Qurawa jinin cikinta dake bin ruwan sama Yana gudu tayi zuciyarta na Mata wani irin nauyi,,,,

Jinin tacigaba da kallo har ruwa yagama wankesa yatafi dashi ta rintse ido tareda sakin wani ihu tareda kuka…

Har aka gama ruwan saman tana duqe gurin tana kuka irin Wanda Bata ta6a yinsa arayuwaba.

Rarrafawa tayi qoafar gidan ta ra6e jikin gate tana rawar sanyi da wani zazzafan zazza6i har haqoranta na ha’duwa.

Da safe Mai gadi na fitowa yaganta kwance a gurin kamar batada Rai yayi saurin komawa ciki ya ‘debo ruwa ya antaya Mata tasaki ajiyar zuciya ahankali tareda bu’de Ido daqyar.

Durqusawa yayi gabanta cikin tausayi yace,

Kiyi hkr ki koma gida ko kitafi wani guri Dan maganar gaskiya itace Nik yatafi,anvar qasar dashi Kuma bazai ta6a dawowaba.

Kamar wawiya take kallonsa zuciyarta na wata irin tafasa tabbas tayi ganganci tareda babban kuskuren barin soyayya ta rufe Mata ido tayi aure bada sanin iyayenta ba gashi yanxu yasamu abinda yake so ya gudu ya barta da ciki gashi gidansu ankoreta….

Wani mummunan nauyi taji zuciyarta tayi Mata idanuwanta sukai wani mugun ja ahankali taji tsanar kowa da qiyayyar kowa na shiga dukkanin ga6obin jikinta ta miqe tsaye tareda durqusawa ta ‘dau ku’din da mum ta jefo Mata cikin wani irin yanayi tace,

Zanbawa kowa mamaki,,,

Gidanmu sun rufe idanu sun koreni batareda bani damar gyara laifina ba ko bani uzuri amatsayina na mace,,,

Sunan dasuke gudun ya lalace har suka koreni saina lalata musu wannan sunan ta yanda ko qofar gida Babu Mai sha’awar fitowa….

Ku’din da mum ta jefo Mata takalla da jajayen idanuwanta tace,

You’ll pay for this queen…

I promise to make all your lives a living hell….

I hate you all..

You’ll all pay for my poor unborn childs blood..

Kuka tasaki tanajin zuciyarta na karyewa ahankali tace,

Meyasa duk zaku gujeni adaidai lokacinda nake tsananin buqatarku,,,meyasa Zaku barni rayuwata ta lalace akan titi….

Wata qatuwar lafiyayyar black Jeep ce tashigo kwanar layin da gudu daga gani matuqin motar ransa a matuqar 6ace yake kafin tayi wani motsin arxiki motar tayi sama da ita ta watsar.

A rikice kyakkyawar budurwar dake tuqin ta fito Mai gadi yakama Mata ita suka saka mota tayi asibiti da ita Dan ita batacika son 6ata lokaciba akomai afterall tanada gurin zuwa..

Cikin qanqanin lokaci akayi gama treatments din komai sbd ba wani ciwo tajiba kawai buguwace a hannu Sai maganin qarin jini Dana masu 6ari daya rubuta musu.

Kallonta fannah tayi cikin yanayin ‘dan tausaya tace,

Ya sunanki?

Ayshah”””””tafada ataqaice sbd lurada datayi da fannan idanuwanta a bu’de suke matuqa duk da tanada ‘dan banxan kyan ‘daukar hankali.

Ayshah Ina ne gidanku nakaiki sbd ni Nan tafiya zanyi zankoma inda nake Dan ni baqunta nazo Kuma yau zankoma.

Banida gida Kuma banida gurin zuwa.,kitafi kibarni anan.

Batayi mamaki ba dantaga alamar korarriyace kamar ita awancen lokaco Dan haka kai tsaye tace,

Korarki akayi daga gida?

‘dagowa tayi ta kalli fannan idonta na qoqarin 6oye hawayenta..

Murmushi Mai ciwo fannah tasaki Dan itama ta ‘dandani irin wannan ciwon na korar iyaye Kuma haryau Tanakan ‘dandanar ciwon..

Kallon ayshan tayi tareda cewa ta tashi sutafi.

Motarta suka shiga suka baro asibitin tana Hawa titi takalli agogo tareda juyowa ta kalli Ayshah tace,

To ayshah ni Zan tafi Zaki bini ne ko kuwa kinada gurin zuwa..

Danne karayar zuciyarta tayi tareda sauke idanuwanta Kar kan titi tace,

Muje ni 6arnar suna nafito yiwa zuriata tareda 6ata rayuwar Deen da zuriarsa.

Wata dariyar farin ciki da samun ‘yar uwa fannah tayi tareda bawa motarta wuta suka Kama hanyar barin gari.

*Nasiha,,,,,,iyaye da abokan zaman rayuwa akoda yaushe yiwa dan Adam uzuri abune Mai mahimmanci sbd rashin bada dama da uzuri shike qarasa ta6ar6arar da alamari qarshe ayi aikin jahilci da Dana sani ta biyo baya Wanda hakan baida kyawu kwata kwata a addini…*

*Iyaye komai girman laifin da ‘yaya zasu yimuku Kar ku kasance masu rufe Ido ku aikata abinda zai dawo ya zame muku abin Dana sani Don kuwa qeya ce.*

*Allah ya tsare yakuma Kare zuri’ar mu gabaki ‘daya*…

_masu cewa wannan yayi, wannan baiyiba wannan yakamata ayi, wannan bai kamata ba kokuma ga abinda sukeso ace anyi to duk wannan bashine ba idan kun nutsu kunbi labarin ahankali to ahankali  Zaku fahimci yanda labarin yake dakuma darussa tareda alajabin dayake cikinsa._

*Nagode da qauna*💋

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *28*

_*A zahirin gskia banajin da’din yanda wasu da dama suka dameni da zancen wani bai kamataba ace ayshah tayi karuwanci da aurenta  ba,,*_

*_kusani nimafa musulmace Kuma gwargwado inada ilimi da sani akan addina nakumasan me nakeyi Kuma ni nasan abinda nake rubutawa amma ku masu karantawa Sai ku kasa hakuri kuga yanda labarin zai kasance wasuma harda zagi da munanan kalamai to Wanda hakan ba tunani bane Dan haka please and please for god sake idan Kunga abinda bakwa iya karantawa to ku barshi ba dole bare zagi da cin fuska yashigo._*😠

 5

Tsakar dare suka shiga garin Abuja Kuma zuwa Time ‘din ayshah gaf take da ficewa hayyacinta sbd mugun zazza6i da ciwon marar datakeji.

Sannu fannah ke Mata cikin tausayawa da damuwa tareda tsoron Kar ‘yar mutane ta mutu a hannunta.

Wata ‘yar babbar private hospital dake kusada anguwarsu ta nufa Kai tsaye batareda sun Isa gidaba Nan aka kar6eta tareda qoqarin fara Bata treatment ‘din gaggawa sbd tashin farko suka gano cikin dake jikinta ne ke qoqarin qarasa zubewa Nan suka fara qoqarin tsayar da jinin.+

Tun fannah na ‘daukar abin da sauqi saigasu da kwana asibitin.,,

Koda ayshah ta farka abun farko da fannah tace Mata shine azubar da cikin.

Kallon mamaki ta aiketa dashi fuskarta na qoqarin bayyana farin cikinta tace,

Cikina yananan bai zubeba?

Cikeda mamakinta fannah tace,

Yana Nan amma banga amfanin barinsa ba gwara ki zubar tunda shege n….

Cikin tsawa ta dakatarda ita hawaye suka gangaro Mata tace,

Cikina ba shege bane ‘dan halak ne,

‘dan sunna Kuma Koda shegen ne ta bazan ta6a zubarwaba sbd shika’dai ne abinda Zan riqa gani naji sanyi arayuwata zuwa Nan gaba,,,,

Bansakaki Zama Dani doleba idan kinajin bazaki iya Zama Dani Dan inada cikiba to ko anan Zaki iya tafiya kibarni ahakanma nagode..3

Ajiyar zuciya fannah tasaki tareda miqewa tsaye cikin kulawa tace,

Ayshah bance lallai saikin zubarba shawarace nabayar a tunanina ba cikin aure bane Kuma kince bazaki zubarba ba shikenanma ki daina kukan ya Isa haka…Bari naje na kar6o Mana sallama muje gida Dan gskia nagaji da zaman asibitin.

Tana fita ayshah tabi bayanta da kallo cikin mamakin sanyin halinta sbd yanda ta gasa Mata maganganu Amma bataji haushiba..

Fannah ta girmeta zaikai kamar da shekaru biyar,,

Fannah kyakkyawar chocolate mace Mai kyan jiki,,Sam batada zafi  tanada hakuri da tausayi Amma a gurin maza labarin bambam ne don kuwa Bata raga musu Bata ‘daga musu qafa hakama batajin wuyar ci musu mutunci sbd namiji ne sanadin qorar da iyayenta sukayi Mata,,

Ahankali tariqota suka fito tashigarda ita mota suka bar asibitin.

A wata anguwar masu Hali gaban wani qaton flat Mai kyau da tsari taga sunyi horn Mai gadi yazo da saurinsa ya bu’de musu gate suka shiga harabar gidan sukayi parking..

Kallonta gidan tayi zuciyarta na karyewa idanuwanta na qoqarin kawo hawaye sbd tunanin iyayenta daya fa’do Mata Dan tabbas tafi sha’awar Zama taredasu Koda acikin ruga suke akan irin wannan daular da aka Tara ta hanyar 6arna.

Qofar shiga babban palon sukayi fannah ta fiddo keys ta bu’de suka shiga.

Zaunar da ita fannah tayi  tareda Zama kusada ita cikin sanyin murya tace,

STORY CONTINUES BELOW

Ayshah Kinga gidana Kuma nikadaice nake rayuwa acikinsa shiyasa ban cika zamaba kullum ina gurin tafiye tafiye Amma ayshah nayi Miki alqawarin ‘dage duk wasu tafiye tafiye na na zauna na kula dake har lokacinda Zaki haihu Insha allah.

Kallon palon ayshah tayi taga ya ha’du matuqa Dan komai najin da’din rayuwa an zuba Masa  kafin ta maida kallonta ga fannah cikin hawaye batareda tace komaiba sbd ita duk ba wannan takeso iyayenta da Deen takeso..kuka tasaki ahankali tana shesheka.

Dafata fannah tayi cikin son danne Tata damuwar da kullum take dannewa tace,

Ayshah dole hakuri zakiyi for now har lokacin da Allah zai kawo qarshen damuwar.

Kukanta Tasha Mai isarta kafin fannah ta riqo hannunta takaita bedroom ‘daya daga cikin two bedrooms ‘din dake palon..

Qaton ‘dakine Mai ‘dauke da lafiyayyan makeken gado da wrdrope ‘dinsa da qaton mirror Sai lafiyayyan toilet.,komai na room ‘din is blue and white shiyasa ‘dakin yayi masifar ha’duwa.

Zaunar da ita bakin gado fannah tayi tareda cewa,

Ayshah ga room Nan kishiga kiyi wanka kifito kici abinci saiki kwanta ki huta zuwa anjima idan na huta Zan fita nasiyo Miki ‘yan kayanda Zaki riqa sawa..

Bedroom ‘dinta takoma Wanda ya’danfi na ayshan tsaruwa sbd tsadaddun designers perfumes da kayan kwalliya masu tsada da mayukan dake jere gaban mirronta hakama.

Ayshah kuwa saidata shaqi sabon kuka kafin ta lallashi zuciyarta ta shiga toilet ‘din tayo wanka..

Doguwar riga Mara nauyi ta tarar a kan gado data fito saita ‘dauka ta saka Dan tasan fannah ce takawo Mata.

Abinci fannah tashigo dashi cikin plate ta aje Mata agabanta tareda ruwan faro da magaungunanta.

Dafa cikinta tayi cikin yanayin sonyin kuka tace,

Sbd Kai ko ke zanci abinci Nasha magani…

Murmushi fannah tayi cikin nutsuwa tace,

Na tabbatarda sonda kikewa wannan cikin ba qaramin so kikewa ubansa ba.

Hawayen datake tarewa ne suka gangaro tace,

Ada kenan,,7

Miqewa fannah tayi tareda tattara kayan ta Fice dasu batareda tasake mgnba.

Da daddare fannah taje tayowa ayshah siyayyar kayan sakawa Mai ‘dan yawa.

**********

Sannu ahankali tafara sakewa sbd yanda fannah ke kulada it’s sosai gashi itama ta ‘dauki son duniya ta ‘dorawa cikin kaman yanda ayshah ke matuqar son abinta,,

Lafiya tasamu gareta sosai Dan tuni fatarta ta canxa sbd hutu daya ratsata danko fita Bata ta6ayiba harsaida cikinta yafara tsufa kullum Sai sun fita shopping kayan baby..

So da dama ayshah najin matuqar tausayin fannah na irin rayuwar data jefa kanta aciki musamman yanxu datake jinta kamar Yar uwarta ta jini.,

Duk wani Jin da’di da kulawa Babu Wanda fannah Bata Bata hakama duk sati take kaita awo asibiti.

Zaune take a Palo ta miqarda qafafuwanta dasuka matuqar kumbura sbd tsufan da cikinta yayi tanacin guava da fannah tasiyo mata tana kallon wani shirin larabci a tasar salamtv.

Fannah ce tashigo palon riqeda handbag wata yarinya kimanin shekara goma Sha bakwai tana bayanta riqeda ‘yar Viva bag.

Kallon fannah tayi cikin murmushi tace,

Anty baquwa Kika kawo Mana.

Zama tayi kusada ita tareda ‘daukar yankan guava ‘daya taci tana cewa,

STORY CONTINUES BELOW

Eh ‘yar aiki ce nasamo sbd abubuwa sunyi yawa gashi kina gaf dashiga watan edd ‘dinki so Dole muna buqaran helper.. she’ll be the one gyaran gida da girki so that I will be able to take good care of our prince or princess…

Murmushi tasaki tareda kallon cikin tana danne ‘dacin zuciyarta da haryau takejinsa kullum kamar sabo Amma ta koyi danne abinta tun kafin ta haihu abin yashafi ‘danta.

‘dakin dake gaf da kicin fannah ta nunawa yarinyar Mai suna Nana bayan tayi Mata bayanin aikinda zata riqayi.

Tunda Nana tazo gidan ayyuka sukayi ma fannah sauqi Dan tuni takoma aikinta na office Dana harkokinta da mazanta.,

Yau Kam kwance take zuciyarta a dagule sbd kukan data kwana tanayi Wanda kusan kullum saitayisa kafin ta kwanta…

Shiru tayi tana tunanin rashin adalci irin na zuciyarta data kasa cire Deen aranta duk da yaudararta dayayi tareda cin amanarta ya gudu yabarta cikin mummunan Hali.1

Fannah ce tashigo ‘dakin cikin shirinta na zuwa office ta kalleta cikin sanyin jiki sbd itama kwanakin hakanan takejin ranta ba da’di.

Ina kwana anty””””tace murya a sanyaye.

Lpia klau ayshah ya jikinki hope dai bakyajin komai?

Kai ta ‘daga tareda tashi zaune ta sauko gadon tana Shirin miqewa tsaye taji takasa yunqurawa sbd riqewar da bayanta yayi tayi saurin kallon fannah cikeda tsoro tace,

Anty bayana nakasa miqewa..

Wat””fannah tace da sauri tareda aje handbag da keys ‘din hannunta ta matso tana riqota….

Ya salam” anty bayana da cikina….

A ki’dime fannah tace,

Ayshah bansani ba ko haihuwace Bari muje asibiti kawai idanma ba itabace Sai muji meyene.

Nana ta qwalawa Kira da qarfi saigata ta iso Nan suka kamota suka saka mota Sai asibiti…

Tashin farko nurses na karbarta sukace haihuwace Nan aka Kira doctors suka shige labour room da ita aka barsu anty fannah cikin fargaba Dan Koda suka iso asibitin ciwon yayi mugun tsanani.

Abu kamar wasa haihuwa taqi zuwa ga azabar datake ciki tayi yawa Suma doctors ‘din dakansu suna tausaya Mata Amma sunyi iya yinsu haihuwar taqi zuwa Sai naqudar wahala takeyi..

Ganin ana neman rasa uwar da babyn yasa suka yanke shawarar yimata aiki cikin qanqanin lokaci fannah tasa hannu tabiya komai aka shiga tiyata da ita.

Alhamdulillah cikin ikon Allah ansamu nasarar aikin anciro Mata qaton lafiyayyan balaraben ‘danta daya ‘dauko komai na ubansa.1

Tunda aka miqowa fannah shi takallesa cikin  showel na jarirai taji wani mugun so da qaunar yaron tashigeta ta rungumesa tana Jin hawayen tausayinsa na gangaro Mata.

Ayshah Bata farkaba Sai gab da asuba Kuma tana farkowa babynta tafara tambaya fannah ta miqo matashi tana kar6arsa taji wani farin cikinda rabonta dashi harta manta,

Cikin tsananin sonsa idanuwanta suka ciko da hawaye cikin farin ciki tace,

My junior Deen,

My love,

My happiness,

My mistake,, you’re my everything now my sweet boy…

Murmushi fannah tayi tareda matsowa ta shafo  fuskarsa cikin so tace,

Ayshah is now a mother…

Dariya tayi tana kallon face dinsa tace,

Yes I’m a mother now but not only me,, you’re his mother too.

Nana daketa faman murna ta matso ta kar6esa cikin tsananin farin ciki tace,

Anty ayshah babyn Nan yanada kyau sosai Amma dai ni Zan ringa goyashi ko?

STORY CONTINUES BELOW

Eh Nana harsai kin gaji da goyo sbd ayshah makaranta zata koma da zaran yafara wayo.

Cikin tsananin farin ciki ayshah takalli fannah tareda cewa,

Anty da gaske?

Yes ayshah coz already admission letter ‘dinki is in hand.

Thank you””””tace tareda kar6ar ruwa da brush ‘dinta take miqo Mata.

Kwanansu uku a asibiti aka sallamesu suka koma gida..

Koda suka koma gida ayshah tayi mamakin ganin maqwaftansu na shigowa barka harda friends ‘din fannah duk da wasu daga cikinsu ba masu kimtsi bane Amma hakan ya sanyata farin ciki koba komai sun nuna farin cikinsu sa6anin iyayenta da uban ‘dan dasuka gujesu.

Koda suna yazo ba wani taro dasukayi andai yanka raguna tareda ra’da Masa suna _Mahmud_,.

Tun bayan haihuwar Mahmud komai na rayuwarta ya canxa ta ‘dauki dangana da hakuri tabawa zuciyarta duk sbd farin cikin ‘danta,,

Tsananin son datake yiwa Mahmud yayi yawa Dan ko kukan ciwo ciki ko wani Abu yake itama zaunawa take ta darza kukanta.

Gata soyayya da tsantsar kulawa yaron kesamu daga ayshah har fannah Dan kullum cikin yimasa shopping take,,,ko Nana ba laifi tana tsananin qaunar yaron sbd kyansa kamar yanda tace,.

Ganin irin yanda fannah ke kashe musu ku’di ba sauqi yasa tayi tunanin fara zuwa makarantar da fannah ta nemar Mata sbd kotayi saurin gamawa ta samu aiki Dan ragewa fannah lalura.

Mahmud nada shekara ‘daya da wata biyar ta yayesa tafara zuwa makaranta bayan uwar siyayyar Kaya da ‘dinkuna da fannah tayi mata ciki harda Bata motarta ‘daya.

Shigarta makaranta ya qara canza rayuwarta kwata kwata Dan kuwa Sam Babu Wanda zai ganta yace ayshan gidansu malam babba ce sbd wayewar datayi da wani mugun Jan class daya shigeta uwa uba ayshah Bata ‘daukar reni ko ka’dan yanxu,,

Duk wani kyanta da kyawun fatarta ya da’du Dan bazaka ta6a cewa ta ta6a haihuwaba kullum ka ganta cikin gayu take danko fannah yanxu Sara Mata take a fannin gayu da qwalisa.

Duk wannan abin da’ake maza tsoron tunkararta suke sbd tsoro da fargabar kwarjininta da cika idonta dakuma fuska dabasu ganiba.

Qawarta ‘daya a school ‘din Mai suna Aisha itama Amma shanty ake kiranta,,

Shanty ‘yar tsohon ministern ku’di ce kuma ita ka’dai iyayenta suka Haifa Wanda gata da ku’di suka lalatata ta hanyar shaye shaye da yawon club duk da dai Bata ta6a iskanciba a taqaicema batada saurayi ko ‘daya Dan Bata kulasu shiyasa ayshah ke matuqar qawance da ita batareda tasan tana shaye shayeba.

Fannah zuwa lokacin girma ya’dan fara zuwar Mata ta aje komai ta rungumi aikinta dasu ayshah amatsayin iyalinta da nauyinsu ya rataya kanta musamman ma Mahmud da yanxu yafi Zama da ita sbd rashin zaman ita ayshan.

Yau batada Lectures ko ‘daya Dan haka tana gida sunata nisha’di a palon itada anty fannah suna fira Nana nata wasa da Mahmud Sai tsalle yake Yana dariya.

Kallon fannah tayi tace,

Anty fannah Dan Allah kibawa Yaya Ibrahim dama Mana Kinga Yana tsananin sonki after all Mahmud fa Yana son yaje agolanci”””””ta qarashe zancen cikin tsokana.

Dariya tayi tana kallon Mahmud ‘din tace,

Yaron mummy zonan,,

Da gudu yazo gurinta tareda fadawa jikinta tace,

Anty ce tace Wai zakaje agolanci?

Batareda yasan metake nufiba da agolanci yace,

No I don’t want to go..

Kamosa ayshah tayi jikinta tace,

Amma ai kanason dady ko?

Eh”””yace Yana tsalle tareda yiwa Nana gwalo…

STORY CONTINUES BELOW

Qaran doorbell yasa Nana miqewa taje tabude saiga shanty tashigo taci kwalliya tayi kyau harta gaji Dan itama ba laifi kyakkyawace farin ayshah ne kawai batayiba.

Da gudu Mahmud yaje yafada jikinta Dan yasaba da it’s sosai sbd itama tana tsananin qaunar yaron ta ‘daga qatuwar ledar hannunta sama tace,

Guess wat it s.,,,

Cheese””yace Yana tsalle.

Girgixa Kai tayi tace,

No.

Ice cream ayshah tace tana kallon ledar.

You failed too”'””shanty tafada Mata tana hararanta.

Mangwaro da yalo”””””Nana tafada tana wage bakinta cikin murna..

Dariya suka sake dukkansu shanty kuwa cemata tayi,

Comon keep quiet ai bakinki ne magoes ‘din.

Chocolates and shortbreads..anty fannah tafada Masa qasa qasa.

This is cheating anty fannah””””shanty tafada tana miqa Masa ledar tareda Zama kusada ayshah dake miqe a three seater sanyeda black pencil jins da farar armless top ‘din shaking material gashinta a ‘daure tsakiyar Kai.

Anty ina wuni?

Lpia qlau Aisha ya gida da mum.

Fine anty please zamuje kar6an ‘dinki a wuse market.

Kallon ayshah tayi ayshah tayi saurin cewa,

Allah is not a plan Nima yanxu nakeji abakinta.

No ayshah ba Ina hanaki fita bane you know wat is in your head Ina tayaki Kare wannan martabar ne sbd gujewa mummunan alamari Nan gaba.

‘dan ‘daure fuska tayi zuciyarta na zafi sbd koda wasa batason tuno duk wani alamari daya shafi Deen.1

Bedroom suka shiga da shanty ta canxa Kaya zuwa doguwar rigar wata red atampa Mai adon blue ta zaro blue Vail ta yafa batareda ‘dankwaliba ta ‘dau wayarta suka fito Mahmud yataso yace saiya bisu hakanan taji gabanta yayi mummunan fa’duwa tace,

Sweetie kazauna gida gurin mummy Mana idan zamu dawo I promise to buy ice cream for you my boy.3

Maqe kafa’da yayi Yana Shirin yin kuka tajuyo takalli anty fannah sbd baita6a cewa saiya bitaba idan zata fita yafi yiwa anty fannah haka.

Riqosa anty fannah tayi ya fashe da kuka tareda fa’duwa qasa Yana Shure Shure.

Kamo hannunsa shanty tayi tareda tayardashi ta ‘daukesa takalli Nana tace,

Jeki ‘dauko hijab dinki muje ki riqesa.

Da gudu Nana ta ‘dauko Dan akwaita dason yawa da wasa Dan akwai sauran ‘dabi’un qauye atareda ita.

Tunda suka fito tayi tsit gabanta na fa’duwa hakanan taji hankalinta na tashi

Shanty dake driving ta juyo ta’dan kalleta tace,

Whats wrong eshaah?…sunan datafi kiranta dashi kenan.

I just don’t know but I’m having some strange feelings.

Ba komai eshaah just relax okay.

Wata qatuwar shopping complex suka Parker suka fito tareda shiga.

Mahmud dake hannun Nana riqe Yana hango 6angaren kayan wasa yayi can da gudu Yana cewa Nana,, yeeyyyy catch me if you can.,

Binsa tayida gudu dai lokacinda idanuwan ayshah suka sauka kan qatuwar plasma tv dake gurin,,,

Fuskar Deen ce bayyane jikin tv ‘din cikin taron dubban jama’a fatarsa kawai ta Isa ta nuna tsananin hutu da kwanciyar hankinda yake ciki tareda farin ciki.,

Bodyguards taga sunata faman kakkaresa masu ‘daukar hoto da Yan jarida Sai rige rige suke yaci wani irin ado cikin dark blue shadda da maiqonta kawai ya bayyana tsananin tsadarta….

Kai Amma wlh yau nataya shaikh nuraddeen auren dayayi Dan kuwa Yana matuqar tausayi da taimakon addini Dan kuwa shika’dai ne matashin babban shaikh damuke taqama dashi a qasashen qetare..1

Hmmmnn kaidai jabir Bari wlh ni Yana matuqar burgeni daya za6i zamowa babban masani akan addini maimakon wani aikin Kuma qarin abin burgewa shine dayazo gida Nigeria ya za6i Mata ya aura…..

‘dauke Kai tayi tana qoqarin danne abinda yake taso Mata Amma tuni wani wawan jiri ya ‘dibeta shanty tayi saurin tareta kafin tayi magana saiga Nana a guje hankali tashe kamar zautacciya tace,

Anty anty wasu sun ‘dauke Mahmud sun gudu dashi a mota.

Wat'”shanty tace da qarfi tareda sakin ayshah da itama tuni ta girgije ta kwasa waje da gudu suka bita tareda sauran ma’aikatan Amma Ina suna fita motar na barin gurin.

Kawai Sai ganin sukayi ayshah ta yanke jiki ta fa’di.

Mamuh💋1

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *29*

 

  Arikice shanty takamota tana girgixata da qarfi cikin tashin hankali Amma ba alamar ko numfashi atareda ita bare tasakaran zata motsa.,,

Kallon Nana dake risgar kuka cikin tashin hankali tayi tace,

Kamomin ita maza,

Mota suka sakata cikin mota aguje ta Isa specialist da ita kafin takira anty fannah tafa’da Mata abinda ke faruwa.+

Sumane kawai anty fannah batayiba Jin mummunan zancen cikin qoqarin danne kukanta tace gatanan qarasowa asibitin,

Tana kashe wayar tasaki kuka ahankali jikinta na matuqar rawa Dan tasan rashin ganin Mahmud barazanace ga kwanciyar hankali da dadda’dar rayuwarsu musamman ayshah datasan zaucewama zatayi.

Kodata isa asibitin ayshahn ta farko Banda hauka Babu abinda take musu Sai ririqeta akeyi tana ganin anty fannah tasaki wani irin kuka Mai qarfi tareda fadawa jikinta tana cewa,

Anty fannah Mahmud ‘dina,,,,I can’t live without my son,,,,, Mahmud is my life,,,my Mahmud…..

Kukane yaci qarfinta ta rintse idanuwa tana rerosa da qarfi..

Anty fannah da shanty ma duk kukan suke Nana kuwa ita ko magana ba’ayi.

Police sukaje suka bada report tareda zube maqudan ku’di Nan da Nan suka ‘dau bayanai suka fara nemansa cikin gaggawa.

Gida suka koma Amma ayshah ko Zama kasayi tayi ta zari mukullin mota ta Fice da sauri suka bita Nan suka fara yawo cikin gari lungu da saqo suna nemansa ganin dare yafarayi ba alamar ganinsa yasa ayshah qara rikicewa Banda kukan tashin hankali Babu abinda takeyi,,

Daqyar suka samu suka tirsasata suka dawo gida  cikin dare..

Washe gari ma hakance takuma faruwa tun safe suna yawo Amma ba alamar nasara suna dawowa gida wani mugun zazza6i ya rufeta sbd kuka da rashin cin abinci danko ruwa su anty sunyi sunyi Amma Sam ko kallon abinci tason yi Banda kuka ba abinda take iyayi.

Police sunyi iya yinsu har tsawon sati biyu ba wani bayani Sai kawai suka aje case ‘din gefe,,,

Duk inda hankalin anty fannah da shanty yake ya matuqar tashi sbd halinda ayshah ke ciki Dan kuwa sosai ciwo ya kwantar da ita tayi wata irin muguwar Rama ta yamutse ta Fice hayyacinta sbd komaima sabo yadawo Mata ciwon rabuwa da iyayenta Dana 6atan ‘danta da yanda rayuwarta ta ta6ar6are duk komai ya taru ya zautata.

Anty fannah ma tuni kwanciyar hankali yayi Mata qaura duk ta rame sbd ganin yanda ayshan takoma kamar Wadda tayi shekaru cikin ciwo,,

Sunyi yawon asibitota harsun gaji Amma Babu wani sauqi..

Wata biyu da 6atan mahmud ciwo ya kwantar da ayshah suka kwanta asibiti jinya..

Zaune take bakin gadon ‘dakin datake cikin mummunan yanayi Dan ko gani sosai batayi yanzu sbd kuka dayafara cinye Mata lafiyar Ido.

Daqyar shanty dake zaune ta lalla6ata takamota suka fito wajen ‘dakin kota ‘dan sake maimakon ciki Banda ajiyar zuciyan kuka ba abinda take Dan yanxuma kukan bai zuwa saidai na zuci dayafi ciwo.

Wata kyakkyawar lady ce ta nufo aminity word ‘din cikin shiga ta alfarma ta dogon hijab maroon har qasa daya matuqar qayata kalar fatarta hannuwanta sunci adon Jan lalle hakama qafafuwanta wasu matsiyatan heels ne duk da hijab ne ajikinta,

Murmushi fuskarta ke bayyanawa har haqoranta na ‘dan bayyana ta qaraso gurin wasu Mata dake zaune kan qatuwar dadduma suna fira daganinsu kasan gidan masu tsananin arxiki suka fito.

 

Cikin farin ciki suka tarbeta tareda ‘yan rakiyanta guda biyu dake bayanta,

Kujera aka ‘dauko Mata da sauri aka aje Mata ta zauna cikin sakewar fuska takalli dattijuwar ciki tace,

STORY CONTINUES BELOW

Haj babba Ina wuni,,

Lpia klau *_siyama_* ya gida ya nuraddeen da jama’a.

Murmushi tasaki cikin Jin da’din tambayar mijinta da akayi tace,

Alhamdulillah hajiya ya mama da jiki?

Taji sauqi Dan muna sakaran sallama yau ko gobe insha Allah.

Allah yasa su sallameku yau Dan inason nayi fira da mama kafin gobe mu wuce sbd yanada wani taron manyan malamai dazasuyi a Madina insha Allah.

Ok Allah ya taimaka ai gskia nuraddeen Yana qoqari Dan wlh samun irinsa acikin sa’anninsa zaiyi wuya ta yanda yake yiwa addini yaqi da hidima duk da dai ba acikinsa yatasoba mudai saidai muce Allah yasakawa Wanda yayi jahadin musuluntar dashi,ke Kuma Allah yabaku Zama lpia da zuria Mai albarka.

Amin””””tace cikin farin ciki da Jin da’din anyabi farin cikinta ma’ana mijinta.

Ayshah datun zuwan matar taji zuciyarta na Mata nauyin ganinta ta rintse ido Amma Jin abinda suka fa’da yatabbar Mata dako matar wace,.

Jitayi tana qoqarin ha’diye wani Abu daya tsaya maqoshinta Yana neman danne numfashinta ta miqe da qyar tabar gurin zuciyarta na gaf da bugawa..

Ganin yanayinta yasa shanty saurin Kiran nurses tareda Dr Nan suka fara qoqarin dubata sbd numfashinta dake sama sama kaman zai fita…

Wani qarfine da mummunan 6acin Rai suka taso Mata ta fusge hannunta da ake qaqarin zubawa ruwan allura ta cannula.

Riqota shanty tayi cikin tsoron sabon yanayin data ganta ta girgixa Sai kawai ta fashe da wani irin kuka Mai tafasa zuciya.

Sanyi jikin shanty yayi ta zauna kusada ita tareda dafata cikin sanyin murya tace,

Ayshah Dan Allah kiyi hkr ki rungumi qaddarar Allah har zuwa lokacinda Allah zai iyakance miki..

Tsananta kukanta tayi ta ‘dago cikin kuka tace,

Shanty na rasa komai duk sbd soyayyar Wanda ba Sona yakeba amfani yakeso kawai yayi Dani,

Shanty rayuwata ta lalace sbd mugun mutumin da yake Kiran kansa da shaikh yanxu,,

Na rasa komai na rasa kowa Banda abinda zan dogara dashi naji qarfin gwiwar qarasa rayuwata.,

Shanty I’m nothing but a loose…

Inama ace zan manta komai nakoma rayuwata ta da,,,inama ace Zan iya ciresa a Raina kwata kwata batareda na tunosa Koda na second ‘daya bane,,,,,

Shanty I can’t bear this pain anymore,,, it is really hurting…I can’t bear it.,,,ji nake gwaramin mutuwa sbd kowa bayasona,,,,

Basa Sona basa buqatana sbd laifi qalilan Kuma naso subani dama na gyara babban kuskuren Dana tafka…

Gashi mahmud ‘dina baya taredani duk nasarasa mutanen danake tsananin so da qauna a rayuwa so what is the point of living in misery….

Rufe Mata baki shanty tayi cikin tsananin tausayinta cikin hawaye tace,

You’re my best my only friend I can’t see you suffering like this I promise you won’t feel this pain again,,,you’ll be happy again my eshaaa insha Allah..

Bu’de hanbag ‘dinta tayi ta ‘dauko wasu qwayoyi ta miqawa ayshah tace,1

Take this now and I promise you won’t feel a thing again…

Kallonta ayshah tayi da jajayen idanuwanta ta kawai da Kai saikuma wata zuciyar ta ingizata ta kar6a Tasha batareda dogon tunaniba sbd kawai buqatarta ta dainajin ra’dadin da ciwon datakeji cikin zuciyarta..1

Kanta taji yafara ‘dan juyawa ta ‘dago takalli shanty saitaga biyu biyu take ganinta Nan ta tashi tana bin ‘dakin da kallo Yana juya Mata saitaji abin namata nisha’di Dan  kamar a sama take jinta…..

STORY CONTINUES BELOW

_mugun mafari_,,,

Sannu ahankali saiga ayshah ta warware Ras kamar ba itaba tuni aka sallamesu suka dawo gida duk da anty fannah tayi mamakin ganin sauyin gaggawa daga ayshan Amma saita dangana hakan da adduar datake kwana tanayi Mata.

Ayshah kuwa sabuwar duniyar sha aka shiga Dan kuwa tuni takoma school duk wata mashaya yanxu tare suke zuwa da shanty Wanda Nan take idanuwanta suka qara bu’dewa ta qara zanzarewa Dan yanxu ko Zama gida Basu cika ba kullum suna club suyi nis su lalla6o gida su kwanta,,,,,1

Lokuta da dama tana idan tana cikin hayyacinta zaunawa take tayi kuka kamar ranta zai fita sbd ganin mummunar rayuwar data tsinci kanta sanadiyar iyayenta da Deen,,,

Tanason dainawa Amma abin yayi matuqar shiga jikinta Bata iyawa Dan yanxu shiga kowace iri taga dama yitake ta fita sbd abin ba qaramin fara shiga cikin kanta yayiba Dan ita Shan hauka takeyi harsaida shanty tafara Dana sanin sata aharkar.

Anty fannah alamarin duniya ya taru yasata gaba tayi kukan harta gaji Amma ayshah ta zare ko maganarta ba wani jitakeyiba saidai idan abin yasaketa tazo tana kuka tana Bata hakuri.,,,

Tun anty fannah na ‘daukar abin da sauqi harta gaji tafara tsanantawa ayshah Amma maimakon sauqi saima ayshah ta qara zarewa danko gida Bata dawowa wataran idan sukayi dare saidai takwana gidansu shanty.

Rama da ciwo yafarasaka anty fannah gaba danko fita office Bata iyayi tayi kuka tayi addua tayi fa’da Amma ba wani sauqi Sai kawai ta tattara kayanta tabar gidan bayan ta rubutawa ayshah wasiqa.

Yau da wuri tadawo Qarfe bakwai parking tayi taga ba motar anty fannah gabanta taji ya’dan fa’di sbd tasan anty fannah batada lpia Bata fita ko’ina tunda da’dewa,

Fitowa tayi riqeda handbag dinta cikin shigar doguwar straight gown ta English wear black Sai blue Vail ‘daure akanta da blue designer  takalmi masu tudu sosai.,,,

Tayi haske saidai Rama dake tattare da ita dakaga idanuwanta zakayi zargin tana kora qwayoyi sbd a wani lumshe suke.

Palon tashigo Kai tsaye cikin sanyin jiki Sai ganin Nana tayi rakube tanata darzar kuka…

Rass gabanta ya buga cikin tsawa tace,

Can you please keep quiet,,,ke kullum bakida aiki Sai kuka..

Sharce hawaye Nana tayi tareda miqewa ta miqa Mata doguwar letter.

Kallon Nana tayi ta kalli lettern ta kar6a tana yamutsa fuska ta bude tafara karantawa…

Jikintane yayi mugun saki ta zube gurin jikinta na rawa Sai kawai tasaki kuka cikin mummunan yanayi na tashin hankali…

I’ve lost another part of my life today,,,

Once again rayuwa ta nunamin I will never be happy in my life again..,,

Kuka takeyi cikin mummunan yanayi Dan har wani qanqamewa take..

Sunanta taji Nana takira ahankali ta ‘dago da jajayen idanuwanta saitaganta tsaye da kayanta ta rintse ido cikin ra’dadi da quncin zuciya tace,

Kema tafiya zakiyi bazaki iya rayuwa daniba…

Dama wazai iya rayuwa Dani iyayen dasuka haifenima sun gujeni mijin danake tsananin so ya gujeni,

Mahmud ya tafi,,anty fannah ta tafi kema kitafi dama ni nasan bani ba farin ciki arayuwa sbd rayuwata tagama lalacewa bamai iya tolerating din mugayen halayen danake dasu yanxu,,,.

Tana gurin zaune tana kuka Nana ta wuceta tabar gidan cikin tsananin kuka da damuwar halinda tabar ayshah aciki Dan tasan ayshah ada Mai sanyin Hali da hkr tareda nutsuwa Amma yanxu takoma Banda tsiwa da masifa tareda rashin mutunci ba abinda ta iya.

Tunda Nana ta tafi takasa tashi agurin har tsakar dare da shanty tazo suje mashaya ta tararda ita cikin tashin hankali tayi kuka har kukan ya daina fita…

STORY CONTINUES BELOW

Acikin Daren shanty ta kwashe Mata kayanta suka koma gidansu shanty ‘din sbd iyayenta basa qasar zaune ita kadaice Sai tsohuwar dake tayata Zama sbd karatunta.

Duk iya wani farin ciki tarigada tasan ya qare Mata damuwa da baqin cikin rayuwa sun rigada sun yiwa zuciyarta mummunan kamu sai rayuwa ta qara lalace Mata sbd rugujewar da rayuwar ta ida yi.

_Years back_…..

Lokacinda manyan doctors suka gama iya bincike da nuna qwarewarsu akan matsalarsa sun gano yasamu shafewar qwaqwalwa,,

Sunyiwasu mum bayanin komai maimakon nuna damuwa Sai mum ta nuna farin cikinta akan hakan Dan ko ba komai she’ll get her son back yanda takesonsa…

Davina kuwa hakanan taji hankalinta yatashi zuciyarta taqi yarda da amincewa da karsu fa’dawa Nik komai akan abinda yasamesa dakuma auren dayayi,,,

Sam bazata iya 6oyewa ‘dan uwanta yanada Mata da ciki ba Dan gwara yasani yaje ya ceci matarsa da ‘dansa daga baqar wuya.

Tunda ya warke yakomawa normal life ‘dinsa as a Christian Davina takasa zama saidata fa’da Masa komai da farko bai yardaba harsaida yaga nacinta da dagewarta yayi yawa qarshema wayarsa dake ‘daukeda hotunan ayshah dashi ta nuna Masa Nan yaji jikinsa yayi sanyi amma ackin zuciyarsa bayajin tsananin sonta kaman yanda Davina tace yana tsananin yi..

Saidai tausayinta daya mugun shigarsa na yanda tayi sacrificing komai kan sonsa shiyasa yayi alqawarin nemota ya inganta soyayyarta garesa.

Cikin sirri suka shirya tafiya Nigeria shida Davina ta hanyar yiwa mum qaryar Mexico zasu  auren wani friend ‘dinsa.

Ba musu mum ta amince  suka taho Nigeria tashin farko gidansu ayshah suka nufa Kai tsaye.

Su baba alhaji suka fara cin karo dasu a qofar gida.

Gaidasu yayi cikin mutuntawa Dan Koda yake cikin yanayi na shafewar qwaqwalwa wannan mutunci da tsarkin musulunci har lokacin suna taredashi.

Kallo ‘daya sukayi masa jiki duk a sanyaye suka amsa Nan yaso fara yi musu bayanin abinda ke tafe dashi suka dakatar dashi tareda kallonsa dakyau sukace yabar gidan idan ayshah yazo nema batanan sun koreta basusan inda takeba.

Kallonsu yayi cikeda mamakin yanda suka iya rufe Ido suka Kori yarsu batareda Duba yanayinta na ‘ya mace ba Kuma harda juna biyu ajikinta.

Gida suka koma cikin ikon Allah da zallar mamaki saisuka tararda Murphy a qofar gidan cikin shiga ta alfarma ta cikakken musulmi.

Davina ita tayiwa Nik bayanin waye Murphy agurinsa Nan dai suka tattauna ya sanardasu shi yanxu musulmi ne sunansa muh’d nandai suka ha’da Kai suka duqufa gurin bincike akanta Amma ba wani lbr.,

Mum kuwa tuni hankalinta yatashi sbd antabbatar Mata dasu Nik ‘din basa Mexico.

Davina tun dawowar Murphy taji duk duniya ba abinda takeso kamarsa Dan nutsuwa da tuninta tuni suka qwace Mata Wanda Sai alokacin take qara jinjinawa ayshah Dan yanxune takejin abinda taji Kuma itama a shirye takeda ta kar6i musulunci akan soyayyar datakewa muh’d.

Tun mum na ‘daukar abin wasa saigasu sun shafe kusan wata hudu a Nigeria wanda tuni sukayi Nisa tareda maida hankali gurin koyan karatu da sani gameda addinin musulunci Dan kuwa tuni Davina ta musulunta.

Ganin sunyi neman Amma ba lbari yasa suka koma Amma batareda muh’d ba daya koma Abuja bakin aikinsa.

Lokacinda suka fuskanci mum haukace kawai batayiba ganin ‘yayanta datafi so cikin inuwa da arzikin musulunci..,,

Rufe idanuwanta tayi ta koresu fata fata a rayuwarta dadynsu kuwa bai tauyesuba yabasu damar bin addinin dasuke ra’ayin bi.

Ba 6ata lokaci Deen ya Nemo musu admission a makarantar Madina shida Davina cikin ikon Allah suka samu suka koma Madina suka maida hankali kan karatunsu batareda wata damuwa ba.

Lokacinda suka kammala karatun Davina takoma gida shikuwa zurfafa karatun nasa yayi Sai gashi allah yayi Masa baiwar sanin addini Nan take yayi fice yazamo matashi lamba ‘daya daya haddace alqur’ani da littafai da dama akan addini Dan kuwa duk wani taron musulunci da da’awa Yana cikin manyan baqi da musulunci keji dasu ayanxu,,

Hutu, kwanciyar hankali da arziki Mai tarin yawa sun samu Zama sosai arayuwarsa shiyasa Mata da dama ke sha’awarsa musamman kyawunsa da class ‘dinsa dake fuzgar duk wata mace Mai sauraron fatawarsa.

Siyama salees shine cikakken sunan yarinyar data maqale Masa tun ranar farko data fara ganinsa a wani taro dayazo  Nigeria a Abuja tun Yana share Mata hardai ya amince akayi aurensu Wanda ranar ‘daurin aurensu a ranar mahaifinsa ya musulunta Kuma a ranar mum tagano ayshah hartasa aka sato Mata Mahmud takaisa qofar gidan Deen ta aje tareda doguwar wasiqar cewa ayshah ce takawosa akan Bata buqatar sake ganinsa ga dansa Nan yariqe…

Sosai yaji zafin hakan datayi Sai kawai ya ‘dauke yaron ya bar qasar dashi bayan yayi dna ya tabbatarda dansa ne,

Murmushi mum tayi cikin farin cikin ganin tasamu hanyar fara cusa tsanar ayshah cikin zuciyar Deen kamar yanda tasan ayshah ta tsanesa yanzu danso take ko kallon juna karsuyi da mutunci duk ranar dasuka ha’du1

Muh’d kuwa duk wani tunaninsa ya karkatasa ga binciken inda zai gano ayshah Dan kuwa lokaci yayi da zai kar6i abarsa kamar yanda ya qudurta.

11

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *30*

 

  *_gskia I really appreciate_*😍

*_masoyan taura biyu_*💋

Zaune take gaban mum Banda tsayayar hawaye ba abinda take sbd duk duniya batajin zata iya abinda mum ‘din tace na cewar ta cire muh’d cikin ranta sbd tasan ba abune Mai yiyuwa ba,

Cikin baqin ciki da damuwa mum ‘din tace,

I will never forgive that horrible ninja lady for wat she has done to my family,,

The family I build with so much love,

She distroy everything for me,,,,

Cikin hawaye Khadija (Davina) tace,

Mum please stop blaming ayshah sbd mu muka dama muka za6i rayuwar datafi, rayuwa Mai ‘dorewa ta gobe a qiyama,,

Tashi mum ‘din tayi jiki a sanyaye sbd gabaki ‘daya yanxu Bata iya zaman mintuna da ‘yayanta sbd zancen addininsu dasuke yimata akoda yaushe.

Cikin sallama yashigo qayataccen palon Yana tashin qamshin turaren Arabian oud cikin farar tsadaddiyar jallabiya fara blue Sai Kyau da hasken fatarsa ya da’da bayyana.

Kallo ‘daya mum tayi Masa ta ‘dauke Kai ta nufi hanyar bedroom ‘dinta yayi saurin Shan gabanta tareda riqo hannunta fuskarsa ‘dauke da wani lallausan murmushi yace,

My sweet mum please don’t stop ignoring me like this,,

I love you so very much mum so will you please stop ignoring me mum,,

Kallonsa tayi tayi son ‘danta da kewarsa na ‘dawainiya da ita ta rintse ido tareda juyawa zatabar gurin..

Granny,,,,

Cak ta tsaya tareda sakin  tareda juyowa Nan take tasaki fuska kamar ba itaba da gudu ya qaraso gurinta ta ‘daukesa sama duk da yaqara girma sosai tace,

I miss you so much my beautiful boy..

Kumatunta yaja cikin dariya kamar yanda taja nasa yace,

I miss you too granny but I won’t stay with you today since you’re angry with my daddy.

Bedroom ‘dinta ta nufa dashi tana cewa,

Your daddy is a stubborn man he doesn’t care for me now….

Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka ‘dan bayyana sbd yasan mum ta sauko sosai sbd tsananin sonda takewa mahmud Amma yakasa gane meyasa ta tsani ko sunan uwar Mahmud ‘din afada.

Juyowa yayi gefen Khadija dayar kolacin take zaune tana kuka ahankali ya zauna a sofa Yana kallonta yace,

Menene Kuma Khadija?

Ahankali tace,

Shaikh just pray for me sbd naji ajikina nice Zan biya dukkanin haqqin ayshah da aka zalunta Dan kuwa tun yanxu nafara ganin ishara Kuma na tabbatarda duk inda ayshah take Bata cikin kwanciyar hankali tunda Bata tareda iyayenta da ‘danta duk sbd soyayya.,,,,

Katseta yayi cikin ‘dan yamutse fuska yace,

Karki ha’da kanki da ita sbd ita itace ta za6i kawo ‘danta dantayi rayuwar dataga dama afterall tasan inda nake tunda harta kawomin ‘dana so inda tanada niyyar Zama Dani da tuni ta bayyana kanta Amma she chooses to stay away and wani gefen zuciyana is telling me we are better without each other…..

Kallonsa tayi da jajayen idanuwanta tana girgixa Kai cikin kuka tace,

Shaikh kaiba butulu bane karkayi butulci da raharamarda Allah yayi maka ta musulunci ta dalilinta,

Shaikh kome ayshah tazama arayuwa Kaine sanadi,

Koda yake basai nafada ba Zaku gani akaina duk da banjiba banganiba Amma haqqi zai sauka akaina.

STORY CONTINUES BELOW

Miqewa yayi batareda yakuma tanka zancentaba yace,

Maganar zuwana Nigeria ne yataso sbd gobe Zan wuce insha Allah if you’re still interested in coming with us ki shirya.

Wucewa yayi yabarta farin ciki na ratsa zuciyarta najin maganar zuwansu Nigeria zataje taga muh’d dinta.

Washe gari shida matarsa siyama da ‘dansu mahmud tareda Khadija suka diro Nigeria suka baro mum cikin ‘dibbin damuwar ganin gabaki ‘daya yayanta yanxu kamar ba nataba nantafara tunanin mezai Hana tabi nasu addinin matuqar familynsu zai qara Zama Happy family kamar da.

A qaton lafiyayyan gidansa dake asokoro suka sauka Wanda Nan aka qaro securities agidan

Siyama hankalinta ya qara kwantawa Dan dama tafison zamansu a Nigeria akan can Paris ‘din,,

Babbar damuwa da tashin hankalinda take ciki shine rashin haihuwarta har yanxu,,

Tayita yimasa compain akan hakan Amma bai damu ba sbd ganin mahmud dayake jinsa cikin jinin jikinsa Dan ba qaramin so yakewa yaronba.

Hakan yasa gabaki ‘daya hankalinta ya tashi dason haihuwa sbd batason Koda wasa yayi tunanin maido karuwarsa  tada Dan ita Bata ‘dauketa matarsaba saidai karuwa Dan bataga dalilin ha’da shimfida da kafiriba tunda alokacin yanada sauran dabiar kafirai ataredashi.

2

********

Wani qaton babban hotel daya amsa sunansa na manyan mutane,

Acikinsa akwai manyan halls na alfarma dan meetings ko taron manyan mutane.,

Hakama akwai club na ‘yayan manya dake cikin gurin Wanda ya tsaru ya ha’du ba kadanba.,,

Zaune take cikin club ‘din tayi crossing legs tana sanye da wata designer English gown red datayi masifar yimata kyau sbd kwantawar datayi ajikinta  Sai wani siririn black scarf Mai adon red data ‘daure gashinta gefe  dashi Wanda duk Rabin gashinta a waje yake sbd tsawonsa Sai hakan ya qara Mata kyau,,

Abuge take banda lumshe idanu ba abinda take shanty dake zaune gefenta waya take tana kur6a ruwan qwayoyi ahankali tana lumshe ido,,,

Wani kyakkyawan saurayine ya qaraso gurinsu cikin qasaita na kasancewarsa ‘dan senator ya kalli Ayshah dako kallo bai ishetaba yace,

Eshaah my love look at me please,,,,look wat your love has done to m..

Banza tayi dashi tareda ‘daka cup ‘din dake gabanta ta shanye zuciyarta na tafasa taji Bata dainajin qunar zuciyarba ta ‘daga wani cup ‘din takai bakinta yayi saurin Kai hannunsa zai riqe cup ‘din ta miqe tsaye ta ‘daga hannu ta sharara Masa wani lafiyayyan Mari Nan take ‘yan koransa sukayo kanta kafin suyi wani yunqurin takuma yanka Masa wani Marin Nan take guri ya kaure da hayaniyar fa’da sbd wani ‘dan governor dayake matuqar son ayshan ya shiga fadan dama yanajin haushin Abbas ‘din sbd yanason ayshah Nan suka hau fa’da harda fasa kwalabe.

Shanty datafi ayshah qarfin jini Dan yanada wuya ta bugu duk abinda Tasha kuwa,

Kamo hannun ayshar tayi suka fito harabar hotel ‘din inda Nan take gurin yacika sbd fadan Nan yadawo.

Fixge hannunta tayi cikin maye tace,

Let go of me shanty,,,I’m not done,,,let me teach the bastard a lesson…

Fitowarsa kenan daga meeting ‘din dasukayi agurin yayi mamakin ganin mutane agurin tunda ko hayaniya ba’ayi sosai agurin.

Kamar a mafarki idanuwanta suka sauka akansa ta lumshesu tasake bu’dewa sai kawai tasaki dariya Mai qarfi cikin tsananin maye  tareda nunasa tace,

There he is,,,,the one and only Niklaus Aiden,

The greatest cheat so far…

Kanta securities dinsa sukayo sbd tuni gurin yayi tsit kallo Yakoma kansu ganin tana qoqarin  6atawa shaikh suna cikin bainar jama’a Amma Abbas yayi saurin Shan gabansu cikin rashin mutunci yace,,,,.

STORY CONTINUES BELOW

Karku fara ta6amin babe okay…

Dariya takuma saki tareda nunasa cikin maye tareda kallon shanty da juyayun idanuwanta tace,

Look at him shanty my sweet friend,,,

He is the father of my poor son Mahmud…

He is nothing but a cheat,,,,he uses me and run away like a,,,,, like a,,,

Yesssss like a mosquito..hahhhhhhh

Rintse idanuwansa yayi zuciyarsa na mugun tafasa gashi tuni yafara ganin hasken cameras na tashi ana ‘dauka koba’a fa’daba ya tabbatarda itace ayshah uwar ‘dansa,,,

Kanta securities sukayo tayi saurin zillewa tana dariya ta isa gabansa takallesa from head cikin dariya ta ta6a Masa tana cewa,

Wow Mama’s boy yatara muscles bayan yasha duka agunsu ummmmnnn Yama sunansa,,,,,yesss ya Umar the great heartless parson of the universe,,,,look shanty everyone look”””””tafada tana qoqarin Kai hannunta kan damutsansa cikin tsananin 6acin Rai da baqin ciki ya watsa Mata Marin dayasa Rabin mayen dake tareda ita sakinta ya fa’da mota da qarfi driver yaja sukabar gurin wasu na tir da halinsa na 6oye da yau tsohuwar karuwarsa ta tona..2

Ita kuwa baqin ciki takaici da danasani ne suka shigeta na abinda tayi cikin mayen shanty tajata sukabar gurin..

Koda ya Isa gida Zama yayi a kujera zuciyarsa na tsananin tafasa he can’t believe he once fall for that shameless crazy lady,,,no I can’t love that thing”’yafada da qarfi Yana miqewa tareda fadawa toilet yasakarwa kansa ruwa Dan ji yake kaman zaiyi bindiga sbd baqin ciki da takaicin ganin Wadda ake cewa yaso abaya.

Qin fadawa Khadija yayi yaga ayshah sbd bayajin zai iya cigaba da Zama da mace kamarta,,,

Koda yafadawa muh’d kuwa ganin yayi hankalinsa yatashi Nan yaqara labarta Masa halayen ayshar nada shidai shiru yayi Dan baiga duk wasu gud qualities dake cewa tanadasu ba atareda ita.

Kwana biyu da faruwar hakan sukaje shopping a wata qatuwar sabuwar mall da’aka bu’de itada shanty duk da har lokacin ranta da zuciyarta kullum qara qonewa suke da baqin ciki da tsanarsa akan gagarumar qiyayyar daya nuna Mata ta hanyar marinta Dan abin ya daki zuciyarta matuqa Dan kwana tayi ta wuni tana kuka bayan mayen yasaketa ace mutumin dataso harta jefa  kanta cikin wannan mummunan rayuwar shine ya ‘daga hannu ya mareta.

Doguwar gown ce ajikinta Ash kamar ta maza Amma tanada shape da aljihu na gaba Dana gefe gefe tayi matuqar yimata kyau sbd kaskenta da kyawunta daya fito duk da tuni ta manta wata kwalliya,,,

Facing cap tasaka akanta red duk da gashinta ba duka yashigeba Amma ko ajikinta sbd yanxu ba komai take gane shine daidaiba.

Wayartace kawai ahannunta

Shanty ma dai goduwar rigarce Amma ita normal Arabian gown baqa Sai qaramin scarf yellow ‘daure akanta.

Shanty ke ‘daukar komai itadai Banda tunani ba abinda take duk da Tasha ka’dan kafin tafito abin dai yau da ‘dan sauki bazakace Tasha komaiba matuqar ba magana tafara ba.

Daf da zasu fita taji gabanta yayi mummunan fa’duwa sbd muryar dataji har abada bazata mantataba…

Da sauri ta juyo tare jikinta har rawa yake tace,

Mahmud,,,,

Wat””””tafa’da da qarfi sbd ganin waye yake riqeda mahmud ‘din…

Riqe yake hannun siyama tana tareda Khadija suna shopping cikin nisha’di hankali kwance…

Rantane yayi mummunan 6aci zuciyarta ta rufe ta qarasa gabansu batayi wata wata ba yankawa siyama wani gigitaccen mari,

Arazane suka kallota Khadija ta zaro Ido zatayi  magana a qule ta ‘daga Mata hannu tareda Kai hannu zata jawo ‘danta taji anriqe Mata hannu tareda tureta baya cikin tsananin 6acin Rai ya kalli siyama dake dafe da kumatu ya maida kallonsa kanta yace,

STORY CONTINUES BELOW

Don’t you dare touch him with these dirty hands dasuke aikata sa6on Allah,,,just leave here quitly sbd I won’t tolerate your nonsense again so just leave..

Kallonsa tayi ido cikin Ido idanuwanta na cikowa da ruwa tace,

I hate you,,I hate you so very much,,I’ve never regretted anything the way I regret knowing you in my life,,

You  take away my son from me you cheat….1

Riqeta shanty tayi da sauri sbd tuni tafara jawo  musu attention ‘din mutane..

Kallon Khadija dake kukan ganin mummunar rayuwar da ayshah ta tsinci kanta aciki yayi cikin 6acin Rai da takaici ya nuna ayshah yace,

See,,, see the woman you’ve been praising and talking about.,,

Girgixa Kai tayi cikin kuka tace,

Shaikh ayshah is a decent and…..

Will you please keep quiet,

If this is the kind of girl I once loved then I must say mum is right she’s not the kind of girl I should loved or married,,,,,

Kallonsa ayshah tayi da sauri idanuwanta na 6arewa da hawaye ta kalli Khadija tace,

I will never forgive your family for this,,,,

Juyawa yayi a fusace tareda riqo hannun siyama da Mahmud yabar gurin.

Duk yanda taso daurewa kasawa tayi ta durqushe a gurin tareda fashewa da kuka cikin qunar zuciya.

Tabbas ba itaba ko shanty yau zuciyarta ta ta6u da abinda yayiwa ayshah..

Koda suka koma gida gabaki ‘daya kukanta sabo yadawo Dan kuwa saiyau ta qara gane kuskuran data tafka.

Kwana biyu duk yarasa gane kansa Dan duk yatuno abinda yafaru saiyaji ransa yayi mummunan 6aci sbd hakanan wani gefe na zuciyarsa ke cewa bai kyautaba koba komai bai kamata ace da aurensa akanta yabarta tacigaba da gantali agari Dole dai ya kawota gidansa ya killace ko kuwa ya sauwaqe mata.

Siyama Kam duk inda hankalinta yake ya tashi sbd ba qaramin ka’duwa tayi da ganin ayshah ba Dan kuwa Bata ta6a tsammanin tanada kyau ko ma’ana ba sbd Jin cewar kullum cikin hijab take,,,indai har tana cikin hijab Deen yakamu da mugun sonta to kuwa yanxu ma data zare hakan bazaiyi wuyaba itakuwa bazata ta6a yarda ko Bari ayshah tadawo rayuwar mijintaba Dan tasan itace da rabon barinsa.

Khadija kuwa rayuwa tayi Mata zafi sbd muh’d daya fito fili ya nuna rashin sha’awar sonta gareshi,

Nan komai ya dagule Mata ta rasa Ina zata saka kanta Dan har ciwo ta kwanta Amma qememe yaqi ko zuwa dubota sbd har cikin ransa yakejin zafin abinda mum tayiwa ayshansa.

Su shanty tafara bi batareda sanin shaikh ba tun suna wulaqantata har shanty ta ‘dorata akan network ita kuwa ayshah cewa tayi ba ruwanta kowa tasa ta fishshesa….

Tun Abu na wasa saigashi zance ya bayyana har cikin jaridu cewar matar babban matashi shaikh nuraddeen da qanwarsa sun kar6i number ‘daya a fannen shaye shaye..

Ranar da jaridar ta fito kasa bacci yayi tuni ciwo yafara qoqarin kamasa sbd baqin ciki da takaici,

Mum lokacinda taga abinda ke faruwa zubewa zaune tayi tana tsiyayar hawaye sbd inda qaddarar Khadijar tafi muni ita harda maza sha’aninta takeyi.

Tun ranarda jaridar ta fito Bata dawo gidaba sbd tasan mummunan hukuncinsa dazata tarar Sai kawai suka cigaba da sha’aninsu duk wannan sha’anin dasukeyi ayshah Bata ko kallon Khadija bare Bata cika ko amsa maganartaba Dan duk wani Wanda ya danganci Deen ta tsanesa.

Yau zaune suke a garden din gidan suna shaqatawa su duka ukun,,

Shanty da khadeee Sai annashuwarsu suke ita kuwa wayarta take daddanawa duk da kallo ‘daya zakayiwa ayshah kasan Sam ta manta da ya farin ciki yake,

Dogon pencil jeans blue ne ajikinta da Pink armless top ta ‘daure gashinta tsakiyar kanta Yana lilo…

Gate sukaga anbude hankinsu Yakoma can Banda ayshah dako ‘dagowa batayiba taci gaba da kallon wayarta.

Motar Deen khadee tagani ta miqe da sauri tareda Kiran sunansa.

Itadai ayshah banxa tayi dasu duk da taji abinda Khadijar tafada tacigaba da abinda takeyi.

Cikin takun qasaita da burgewa yake takowa fuskarnan a ‘daure Amma kyawun fuskar ya Hana aga mummunan 6acin Randa ke tattareda ita bayyana,

Tsayawa yayi gabansu tareda kallon Khadija Rai amatuqar 6ace ya nuna Mata mota.

Turo baki tayi cikin qunquni tayi cikin gida Dan dauko kayanta.

Har ya juya ya tsaya cak tareda juyowa ya kalli gefenta ahankali yaga Sam ko kallo duk Basu ishetaba saima game ‘dinta datakeyi…

Kayan dake jikinta ya kalla yaji ransa ya 6aci a qule yace,

You’re also coming  so just stop that rubbish and get up….

Rintse idanuwa tayi tana qoqarin danne hawayenta zuciyarta na karyewa tace,,,, why is he doing this to me ya Allah,,i loved him more than anything is this the punishment for the mistake I’ve done,,,he is  always the reason for my tears…

Hawayen datake dannewa ne suka gangaro Mata ta miqe zuciya karye zatabar gurin baisan sanda ya riqo hannunta ba sbd yaga hawayen dasuka gangaro Mata Kuma sunyi matuqar tasiri a zuciyarsa ta yanda bazai iya tafiya yabarta ba.

Juyowa tayi ta kallesa da  idanuwanta dasuka ka’da  cikin karyewar zuciya tace,

I’m not coming Deen,

Nida Kai yanxu akwai matuqar banbanci duk da ko awancen lokacin akwai banbancin Amma so yarufemin Ido nakasa gani I don’t want to repeat dsame mistake now,,

Kaci gaba naci baya so let’s just end this now sbd bamai Sona yanxu bamai iya Zama Dani Dan nazama abin kunya,abin gudu abin kyama…

Fixge hannunta tayi ta juya da sauri tabar gurin sbd kukan daya qwace Mata Dan kuwa tabbas tana tausawa kanta duk ranar da shanty ta tattara takoma gurin iyayenta.

Harya shiga mota yaji bazai iya tafiyaba gwara ya ‘dauketa ko gidan uwayenta yamayarda ita maimakon wannan mummunar rayuwar datakeyi.

Kuka take ahankali zuciyarta na qara karyewa taji anriqo hannunta a hasale ta ‘dago tareda fixgewa Amma ba qaramin riqo yayi Mata ba yafara janta tana tirjewa harya saka mota ya rufe yashiga yabar gidan da shanty tsaye tana hawaye..

Koda ya Isa gidansa dama part biyu ne Sai nasa atsakiya ya bu’de part ‘din datun farko akayi da sunanta sbd baisan haka halinta yakomaba ya jefata ciki tareda koma gate yabawa securities gargadin karsu kuskura subarta fita Koda wasa tukuna ya juyo ya nufi part ‘dinsa inda anan ya tararda siyama zaune cikin ado tana kallo Mahmud kuwa dama Yana school.

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *31*

 

Tunda tazo gidan kwananta biyu Bata Kuma sakashi a Ido Bata damu ba Dan dama bashine a gabanta ba hasalima iskancinta ta tsulawa a gidan son ranta sbd ganin take taken siyama data ‘dauki tsana da kishi ta saka Mata,,

Abu ‘daya ke damunta shine yanda tun ranar data dawo gidan ya ‘dauke ‘danta yamaida gurin mum sbd wai karyaga munanan ‘dabi’unta,,,,

Khadija ce kawai abokiyar firarta wani lokacin musamman yanda suke cikin tsananin kewar kayan mayensu hardai ita ayshah Dan jitake kamar ta zare sbd rashinsu shiyasa kowa ya ta6ata a gidan Bata raga Masa sbd takaicin rashin kayan caza kwakwalwa,..

Tunda ayshah tadawo gidan siyama take cikin baqin ciki da takaici tayi mitar harta gaji Amma Yama qi sauraronta sbd idan har ayshah tabar gidan to gurin iyayenta zai maidata Amma ba yanxu ba saita dawo cikakkiyar nutsuwarta sbd yasan suka ganta ahaka zuciyarsu bazatayi dadiba,,,,

+

Kwance take cikin tsararen palonta ta qurawa tv Ido Amma ba kallon takeba tunani take ta yanda zata samu ganin shanty Dan tayi kewarta da Kuma kayan korawa.,

Gajeran wando ne black ajikinta da vest itama black da ‘dan adon white ajiki.,

Qofar palon taji anbude anshigo da qarfi tareda jeho Mata Kaya akai.

‘dagowa tayi taga siyama tsaye Rai a6ace kamar zata fashe tace,

Ga kayanki Nan idan bazaki iya wankewa da kankiba to saiki hkr Amma Mai Mana aiki bazata wanke wa’innan kayanba masu najasar giya da wama yasaniba ko harda najasar….

Wawan Mari ayshah tasakar Bata batareda tayi tsammaniba takuma tureta tareda fitowa daga palon ta qwala Kiran Mai aikin dakeda suna Fatima.

1

Da sauri fatimar ta iso jikinta na rawa ayshah ta kalleta fuska a ‘daure tace,

Wuce maza ki kwaso kayan Nan ki aje duk aikin dakike Kona waye ki wankemin su now..

Fitowa siyama tayi cikin zafin Rai da zafin Marin datasha ta kalli fatima ta daka Mata tsawa tuni jikin yarinyar ya’dau rawa sbd ganin tana tsaka…

Kallon siyama ayshah tayi cikin takaici kafin ta juyo takalli Fatima Sai kawai takama hannun fatimar tajata zuwa part ‘din Deen.

Da sauri siyama tabi bayansu tana Kiran sunan fatimar a fusace,

Zaune yake a palon Yana waya sanye yakeda qananan Kaya sai wani qyallin kyau fatarsa take Sai ganinta yayi gabansa ba zato,.

Kayan dake jikinta yafara kallo tunda sama har qasa ya dan tsuke fuska sbd fa’duwar da gabansa yayi,,,1

Maida kallonsa kan siyama dake cika tana batsewa yayi hankali kwance yace,

Ya akayi ne?

Cikin ‘dage gira ayshah tace,

Nizaka kalla Dan nice zanyi magana,

Kan tv ya maida fuskarsa Yana cewa,

Then speak.

Cikin takaici tace,

Wannan me aikin waye yake biyanta agidan Nan?

Kallonta yayi cikin mamaki da takaici yace,

Idan baniba kece kike biyanta?

Just answer the question bance ka fadamin maganaba.

Yana kuma maida kallonsa ga tv yace,

STORY CONTINUES BELOW

Nine nake biyanta,.

Nikuma menene sunan matsayina agidan Nan?

Mata”””””yafada Kai tsaye batareda ya juyo ya kalletaba sbd yagano Sarai masifa takeji shikuma bazai iyaba yanxu.

To hakan ne gud for nothing matarka takasa ganewa sbd she’s insane so just tell her karta Kuma shiga harkana daga yau sbd next time I won’t be nice like this…ok..

Juyawa tayi tabar gurin yabita da kallon mamaki baki asake harta fice kafin yamaido kallonsa kan siyama cikin ‘daure fuska yace,

karki Kuma tsokanota Cox she’s nothing but trouble so idan bazaki iya tsayawa gurinki ba harsaikin je neman fa’da to karkiga laifina akan irin hukuncin dazan riqayi.

Miqewa yayi yashige bedroom dinsa yabarta tsaye kamar zatayi bindiga sbd baqin ciki da takaici.

Itakuwa tana komawa fatima ta kwashi kayan tafice dasu jiki na rawa ita kuwa kasa Zama tayi a palon ma tashige bedroom ‘dinta ta kwanta.

Bayan two days da faruwar haka ta fito part ‘dinta tana Shan waqar single ladies ta Beyonce a wayarta ta nufi ‘dakin Khadija dake kusada part ‘din siyama.

Siyama dake zaune balcony ‘dinta tana gyaran farce tahangota Nan take taji duk annurin zuciyarta ya gushe sbd ganin baiwar kyawu da diri da ayshan takedashi,,

Gefen Deen takalla taga Yana zaune shima a balcony ‘dinsa Yana karatu ga dukkan alama shibaima lurada itaba hankalinsa nakan abinda yake karantawa,

Saurin tasowa tayi sbd Sam batason mijinta yaga ayshan ahaka,

Gabanta Tasha tareda jifanta da wani wulaqantancen kallo tundaga sama har qasa kafin tace,

Kindaisan Nan ba gidan gala bane dazaki ringa shigarda kikaga dama idanma kina tunanin ‘daukar hankalin mijina ne then you’re wasting your time sbd mijina bashida sha’awa akan matan bariki hasalima kallon maza yake musu ba Mata ba so just go back inside and change kafin ki Kuma fitowa.

Kashe wayarta tayi tareda sakata cikin aljihun jins ‘din dake jikinta ta kalli siyamar taga kishi qarara bayyane cikin idanuwanta cikin ranta tace,

Lallai ma wannan matar tacika Yar rainin wayo nida nakeda mijin tun farko na danne abinda nakeji shine zata kawo min rainin hankali lallai kuwa Zan daidaita Mata sahu na koya Mata hankali.

Murmushi tasaki na rainin wayo tace,

Kina tunanin inada abinda zanyi da wancan mijin naki?

Banda abinyi dashi Amma Zan nuna Miki Koda na lalace ahaka shi yanada abinyi Dani idanma bayada Zan nuna Miki mijinki baida tabbas.

Kallon kanta tayi taga dogon pencil jeans ne blue daya matse ‘yan cinyoyinta sosai red top Mara hannu Sai ‘yar jacket Mara nauyi data ‘dora akai ko ‘dankwali Babu akanta,

Murmushin mugunta tasaki tareda kashe Mata ido ‘days ta nuna Deen da idanu tace,

Just wait and watch…

Jacket ‘din jikinta ta zare tabar taciki ta nufi gurinsa tana zare ribbon ‘din data ‘daure kanta dashi.

Saidata Kusa Isa gurinsa ta tasaki qara tareda qarasawa gurinsa da sauri tana ihu…

‘dagowa yayi da sauri tareda miqewa tsaye kafin yayi wani motsi ta shige jikinsa ta cukuikuye tana ihun Kiran scorpion.

A tsorace ya ‘dago da ita daga jikinsa Amma Sai qara shigewa jikinsa take tana ihun kuka kamar da gaske….

Rintse idanuwansa yayi kansa na sarawa sbd hoton ranar da irin haka tafaru a tsakaninsu can baya ya dawo masa.

Girgixasa tana sakin kukan qarya yayi saurin ‘dagota cikin kasala Yana kallon cikin idanuwanta wasu abubuwa na qoqarin dawo masa yace,

Calm down ayshah ba wani scorpion anan.,,,

‘dagowa tayi ta kallesa sbd Jin kasalalliyar muryar dayayi magana da ita tace,

Akwai scorpion anan”'””” ta fa’da cikin shagwa6a  tana nuna cikin rigarta,.

Hannuwansa dake riqe da ita ya ‘daga ‘daya ya nufi cikin rigar ahankali jikinsa na tsananta mutuwa.

Gefen siyama dake daskare cikin tsananin mamaki da takaici tareda baqin ciki ta kalla tasakar Mata wani mugun murmushin mugunta Jin hannunsa ya sauka cikin rigarta yasa tayi saurin zamewa tana ha’de fuska  Amma ganin siyama ta nufosu a zuciye saitayi saurin komawa jikinsa tana cewa,

Ba anan yakamata acire scorpion ‘dinba we need some privacy.

Hakanan yakasa Musa Mata ta jasa suka shige part ‘dinsa ta turo qoafar da qafarta sukabar siyama tsaye sake da baki jiri na neman zubarda ita.4

Suna shiga ta fixge jikinta tareda harararsa tana qarasawa tsakiyar palon ta kwanta a ‘daya daga royal kushins dake palon ta canxa Tasha zuwa boomtv.

6

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *32*   

Qarasowa yayi tsakiyar palon ahankali sbd jikinsa daduk ya mutu Dan ba qaramin yamutsa tunaninsa tayiba musamman yanda yaji kansa na sarawa da alamun dawowar tunaninsa,,,

Har cikinta ransa baya qaunar bu’de idanuwa yakallleta badan komaiba Sai Dan halayenta na yanxu musamman mashi dayaga kamar tafi rainasa sbd haushinsa datakeji.

Bedroom ‘dinsa ya wuce yaje ya zauna bakin gado Yana qara tunano ‘dan tunaninsa na baya daya ‘dan shigo kansa adazun.,,

A ‘dazun da tunanin ke shigarsa ji yayi kamar numfashinsa zai fuzge ya bar jikinsa sbd wani zazzafan sonta daya shigesa acikin tunanin,,,

Kenan shima akwai lokacinda scorpion ta shige Masa Riga…oh Allah please help me remember komai da komai coz I want to feel that love,the happiness and possession Dana shiga duka akanta koba komai I can see in her eyes she’s completely broken and lonely she’s just trying to endure the pain ne batareda ta nunaba but he can see it all around her kawai she’s fighting it ne sbd taci gaba da rayuwarta koba kowa,..+

Miqewa yayi ya dawo palon for the first time yanason yaji everything daga bakinta,,,

Cak ya tsaya akanta sbd bacci daya tarar tayi abinta hankali akwance,

Zama yayi kusada ita tareda qurawa face ‘dinta Ido Yana kallon natural beauty da kuma yanda fatarta ke kyalli saidai tayi wata irin Rama duk da yamanta yanda take ada Amma yasan tabbas wannan ramace,

Wayarta dake aljihun wandonta tafara haske alamar shigowar Kira ahankali yakai hannu yazaro ya Duba dakyau saiyaga shanty ce ke kiranta Sai kawai yayi rejecting tareda blocking ‘dinta ya shiga contact ‘dinta yayi wiping komai sbd karma tasamu damar Kiran wani akawo Mata kayan mayen.

Miqewa yayi ya fice daga palon ya nufi motarsa yashiga yabar gidan.

Siyama kuwa tunda tashiga palonta takasa zama takasa tsayi Jin zuciyarta take kamar zata bindige ta watse sbd baqin ciki da takaicin dake cinta.

Tabbas Dole tayi gaggawar ‘daukarwa isakancin ayshah mataki tun kafin mijinta yafara son ayshan ko yanxu Dan hakan na gaf da faruwa matuqar ayshah nacikin gidan,,,,Dole ne ayshah tabar gidan Nan da gaggawa.,,,,,,tafada tana Zama kan kujera ranta na Dan saki sbd tunanin daya fa’do Mata.

1

Baidawo gidanba Sai dare Koda yadawo tuni tabar ‘dakin takoma part dinta tacigaba da sha’anin gabanta.

Haryayi Shirin kwanciya ya kwanta siyama Bata shigoba tanacan tana fushi,

Fitowa yayi cikin kayan bacci na maza Ash color ya nufi part ‘dinta.

Kwance take itama cikin kayan bacci tana ganinsa ta ‘dan ‘daure fuska ya lura Amma ya share ya tsaya bakin gadon tareda zura hannunwansa cikin aljihun wandonsa yace,

Are you ok?

Yes”””””tace Masa Kai tsaye batareda ta saki fuska ba.

‘daga kafada yayi yace,

Ok Saida safe.

Ya juya ya wucewarsa.

Sabon takaici ne yataso Mata ganin ya tafiyarsa da gske kenan bazai iya rarrashinta ba.

Qasa hakuri tayi ta sauko gadon tabi bayansa.

Shikuwa kasa komawa part ‘dinsa yayi yasamu kansa dason zuwa yayiwa ayshah Saida safe itama.

Cikin nutsuwa yashigo bu’de qofar yashiga,

Bata palon saidai kayan kallon palon a kunne suke musamman ma qararsu datayi yawa ya girgixa Kai Yana cewa,

STORY CONTINUES BELOW

Problem queen.

Kashe kayan yayi harzai fice yaji sheahekar kuka na fito daga bedroom ‘dinta.

Shiru yayi kamar ta tafiyarsa saikuma zuciyarsa takasa nutsuwa ya nufi bedroom ‘din ahankali ya shiga.

Zaune take qasa can qarshen gado ta cusa kanta tsakiyar qafafunta kuka take sosai kamar ranta zai fita Wanda tunda rayuwarta ta ta6ar6are kullum komin dare saitayisa da hakan ne take ‘dan rage nauyi da qunar zuciyarta.

Tsayawa yayi daga bakin qofar kansa na fara sarawa sbd qarar sautin kukan dake shiga kunnuwansa na dawo Masa da sautin kukanta adah,

Rintse idanuwansa yayi da qarfi sbd kukan namatuqar motsa qwaqwalwarsa musamman yanda abubuwa keson dawowa qwaqwalwansa da qarfi Nan take kansa yafara juyawa ya dafe kan da qarfi Nan ‘dakin yafara juyawa dashi Sai kawai ya yanke jiki agurin ya zube.

Qarar fa’duwarsa tasata ‘dagowa ahankali saita gansa zube qasa kamar ba Rai ajikinsa.

Fa’duwa gabanta yayi mummunan yi ta taso jikinta na 6ari ta zube gabansa tareda Kiran sunan Amma ba motsi

Yawu ta ha’diye cikin tsananin tashin hankali ta jijjigasa iya qarfinta bai motsaba da gudu ta ‘debo ruwa toilet cikeda roba ta zuba Masa Dan tuni ta manta da yayyafa ruwan ake.

Wurgi tayi da robar ta zube qasa tareda kamosa jiki na rawa ta qara Kiran sunansa kuka na su6uce Mata Nan tafara rera kuka ahankali Mai tattareda kashe jiki sbd Bata ta6a tunanin sonda takewa Deen ‘dinba haryanzu yananan kamarma kullum qaruwa yake,.

Ahankali ya bu’de idanuwansa tareda ‘daga hannu da qyar ya dafe kansa saiyaji jikinsa yayi tsananin mutuwa na wani mugun tausayinta sbd kukan dayaga tanayi sosai sbd ganin halinda yashiga,

Murya qasan maqoshi yakira sunanta kawai saita miqe da gudu tabar gurin sabon kuka na zuwar Mata na yanda ko yaushe dai sonsa keyiwa zuciyarta galaba Wanda Kuma taga illar hakan yakamata ace takoyi darasi Amma gashinan cikin mintuna qalilan ta manta halinda take ciki duk akansa ta rikice ganin halinda yashiga yanxu.

Kasa barin ‘dakin yayi ya zauna bakin gadonta jikinsa na rawar sanyin ruwan data jiqasa tsaf dasu ga sanyin ac.,

Lafewa yayi jikinsa amatuqar mace Dan tabbas kukanta ya ta6a zuciyarsa.

Har tsakiyar dare tana Palo rakube tana kuka saidataji shiru ta miqe jiki a sanyaye ta nufi bedroom ‘din,

Kwance yake bacci ya ‘daukesa ya takure guri ‘daya alamar sanyi.

Qarasowa tayi bakin gadon ta zauna tana kallon face ‘dinsa hawaye nacigaba da gangaro Mata tajawo bargo ta rufa Masa cikin sanyin muryar kuka tace,

Deen na yarda da soyayyarka itace qaddata,

Banta6a tunanin zuciyata zata so wani Abu duniya kamar yanda take sonkaba,

Duk wata tarbiyata da alada ta iyayena da kakanni na asuli na zubar na za6i soyayyarka sbd Kaine farin ciki Ashe bansaniba Kuma Kaine baqin cikina,

Tabbas Dana tankwara zuciyata nabi za6in iyayena na auri ya Umar da duk wahalarda zansha arayuwa inada ladar hakurinta sbd iyayena nakewa biyayya,

Deen banyi Dana saninkaba arayuwa sbd har yanxu zuciyata takasa yimin adalcin cireka acikinta musamman ma yanxu danake ganin qiyayyata qarara a idanuwanka Wanda hakan ba qaramin karya zuciyata yayiba Dan kuwa na tabbata hasararriyar data rasa komai.,

Mahmud ‘dina danake ganin shine ‘dan farin cikin daya saura arayuwata shima karabani dashi sbd kaima kana gudun ‘danka yayi irin halina sbd na Zama abar gudu ga kowa,

Ka rabani da iyayena,

karabani da farin cikina,

Ka tarwatse rayuwata,

Qarshe ka rabani da kanka but still zuciyata kaitake so why deen.?

Kukane yaci qarfinta tayi shiru zuciyarta na tsananin zafi da qunar halinda take ciki…

Da sauri ta miqe sbd kukanta daya fara sauti Dan karta tadashi Wanda ita Bata saniba duk abinda take fa’da yanaji

Jikinsa yayi matuqar sanyi Dan baita6a tunanin haka take sonsaba Sai yanxu,

After what all happened she really wants to give his love a chance…

Rintse idanuwansa yayi jijiyoyin kansa na tashi tausayinta da sonta na shigarsa lokaci ‘daya musamman yanda yakejin ‘dacin rabata ‘da ‘danta da akayi lokaci ‘daya kenan wanine ya ‘dauke mahmud yakawo Masa ba itace takaisa da kantaba.

I’m the reason for all her pains and sorrows,

I’ve been acting to harsh towards her,

I’ve insulted her for no reason,

Rintse idanu yayi zafin abubuwan na shigarsa kamar yayi kuka,

Ayshah kukanki yazo qarshe insha Allah..

From tomorrow i will give you your full right as a lovely respected first wife.

Har akayi asuba idonsa biyu cikin tsananin tunani Nan take Sai kansa yafara wani mummunan ciwo Wanda baita6a irinsa ba musamman yanda kaman tunaninsa ke neman dawowa da qarfi out of control.

Da qayar ya iya fitowa yaje masallacin gidansa sallar asuba.

Akan idon siyama ya fito hawayen datake dannewa suka silalo Mata kenan dai agurin ayshar ya kwana.

Daga masallaci part ‘dinsa ya wuce Kai tsaye ya kwanta sbd har time ‘din jiyake kaman kansa zai buga Dan har wani jiri ya ke gani.

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *33*   

Qarfe bakwai na safe motar muh’d tashigo harabar gidan badan yasoba sbd tun ranarda Deen yamaido ayshah gidan ya yafe gidan gabaki sbd zuciyarsa bazata ta6a iya ‘daukar ganin ayshah da waninsa ba.,

Amma yau dolece sbd tun jiya mum ke Kiran Deen Bata samunsa shine takirashi ta sanardashi mutuwar Finn   cikin tsananin kuka da tashin hankali gashi daddynsu tuni Yakoma Madina da Zama saidai yakan ziyarceta time to time.,

Ga Deen da Khadija basanan tayi kuka harta gaji shine ta yanke shawara ta sallami duka masu aikinta da zarah Mai kulada mahmud tayo Nigeria gurin ‘yayanta danta gaji da muguwar rayuwar ka’daicin datake ciki tana buqatar ‘yayanta atareda ita Koda hakan na nufin saita musulunta infact she’s ready to become Muslim kamar mijinta da yaranta musamman ma Mahmud shiyasa tana dirowa qasar takira muh’d yazo ya ‘dauketa.

Bu’de qofa yayi yafito riqeda mahmud ya zagayo ya bu’de Mata qofar ta fito tun anan jikinta yayi mugun sanyi sbd ganin baiwa da ‘daukakar da Allah yayiwa ‘danta ta hanyar musulunci.

Tundaga nesa Khadija ta hango mum ‘din da gudu ta fito ta rungume mahaifiyarta tareda sakin kuka ahankali sbd tana tsananin tausayin kanta da mum ‘dinsu sbd suna cikin tsananin ka’daicin rayuwa musamman yanxu da iyakacinta cikin daki ko gate Deen ya hanata kaiwa bare ta fita.

Lafiyayyen ‘dakin Khadija mum tasauka shikuwa muh’d palon Deen yaje ya zauna Yana cigaba da kiransa a waya sbd ko alamar siyama baiganiba bare tafadowa Deen ‘din.

Mahmud kuwa da gudu ya nufi bedroom ‘din daddynsa Yana kwala Kiran sunansa cikin farin ciki.

‘dago Kai yayi daqyar yana ganin Mahmud ‘din ya saki murmushin qarfin hali da farin cikin ganin ‘dansa ya tashi zaune ya rungumesa.

Assalamualaikum daddy””””yafada Yana tashi daga jikin daddyn nasa tareda miqa Masa ‘dan qaramin hannunsa.

Wa’alaikm Salam my boy'””””yafada Yana miqa Masa hannu kafin ya miqe tsaye ya fito dashi Palo Yana ganin muh’d a zaune ya qara sakin fuska tareda miqa Masa hannu suka gaisa ya zauna nan muh’d yafada Masa abinda ke faruwa.

Shiru yayi Yana maimaita innalillahi cikeda tausayin ‘dan uwansa sbd ya mutu bai samu arzikin musuluntaba.

Miqewa yayi suka fito suka nufi gurin mum ‘din muh’d kuwa noqewa yayi ya tafiyarsa sbd ko ganin Khadija ko ayshah baya son yayi.

Mum na ganinsa ta taso da sauri ta rungumesa tareda sakin kuka ahankali.

Bubbuga bayanta yariqa yi Yana cewa it’s ok mum, everything will be fine insha Allah.

Zaunar da ita yayi bakin gado tareda riqo hannayenta biyu yace,

Mum ayshah is here and….

Da sauri ta ‘dago ta kallesa yayi shiru taredayin qasa da Kai.

Murmushi tasaki tareda ‘dago fuskarsa tace,

I’m happy to hear that sweetheart,,

Your happiness is always my happiness, she won’t face anything from me I promise afterall she’s my sweet little Mahmud’s mother,,,and I’m really sorry for….

Girgixa Mata Kai yayi tareda cewa,

Mother’s don’t apologise to their children.

I love you my sweet boy.

I love you too mum.

Wayarsa ya fitar ya Danna Kiran siyama don ayi gaggawar shiryawa mum ‘din abinci.

STORY CONTINUES BELOW

Saidata Kusa katsewa ta ‘dauka a daqile tayi sallama,,

Shima a qasan maqoshi ya amsa tareda cewa tazo ta gaida mum yanzu a 6angaren Khadija.

Fuska ka ‘daure sosai kamar zatayi kuka cikin baqin ciki tace,

Another problem has arrived mitswww.

Abinda Bata saniba shine  yaji abinda tafada ransa yayi mummunan 6aci Amma saiya qyale kawai.

Saidata share kusan rabin awa kafin ta iso tashigo fuska ba walwala ta gaida mum ‘din.

Baki mum tasaki ganin irin gaisuwar rainin wayo da siyamar tayi Mata Nan take ta ‘daure fuska zata yiwa siyamar kaca kaca saita tunoda tayi alqawarin Kama girmanta sbd Deen ‘din ta amsa tana qaqalo murmushi Amma cikin zuciyarta tsana da takaicin siyamar ne fal.

Qoqarin juyawa take cikin ‘daurewar fuska yace,

Prepare something for mum to eat yanxu.

Danne takaicinta tayi takallesa cikin Ido tace,

Inaga wannan ba aikina bane sbd banice da girki ba idan ka manta jiya agurin tsintacciyar matarka ka kwana.

Murmushi yasaki harsaida haqoransa suka ‘dan bayyana yace,

Yes you’re right na mantane you can leave Zan kirata ita tayi.

Haushinsa ne ya qara turnuqeta ta Fice cikin takaici kamar zata daki iska.

Daqyar ta tashi tayi wanka fuskarta duk a kumbure sbd kukan data kwanayi wannan karon doguwar rigace ajikinta Mara hannu ta jawo qaramar hula tasaka duk gashinta a waje sbd Bata kamasaba Kai tsaye ‘dakin Khadija ta nufa sbd number shanty takeso ta duba wayarta taga komai ya goge.

Dai dai kusan qofar Khadija Nan sukaci karo da siyama ta fito afusace.,

‘dauke Kai tayi zata wucewarta siyama tace,

I will never live peacefully with these three around,the great madam queen,the mental so called first wife and the stubborn son of great time mitswww…

Kasa qyaleta tayi ta kalleta a wulaqance tace,

And who are you calling mental?

You””””tafada Kai tsaye tana gyara tsayuwa.

Murmushi ayshah tasaki tareda kallonta up and down tace,

Do you know you’re completely crazy and foolish?

Qara hasala siyama tayi zuciyarta ta rufe ta ‘daga hannu zata sakarwa ayshar Mari taji anriqe hannunta ta baya.

Atared suka juyo Dan ganin waye dukkaninsu idanuwansu suka sauka kan mum.

Wurgar da hannun siyama tayi ta ‘daga nata hannun zata Mari siyamar ayshah da idanuwanta suka ka’da Nan take sbd ganin mum ‘din ta riqe hannun mum ‘din idanuwanta na bayyana tsantsar qiyayyarta da mum cikin ‘daga murya tace,

And who are you to interfere in this.?

A razane dukkaninsu suka kalli Ayshan sbd ba qaramin bazata zancenta yayi musuba.

‘daure fuska ta sakeyi tareda ‘dage gira ‘daya tace,

This is between me and her and I can fight for myself I don’t ask or need anyone’s interference coz I don’t tolerate crazy old ladies now…..

A matuqar zuciye ya ‘daga hannu zai Mari ayshar mum tayi saurin riqeshi tana girgixa Masa Kai idanuwanta na kawo ruwa sbd ta tabbatarda abinda tayiwa ayshar Dole ta fuskanci haka.

Cikin 6acin Rai ya kallesu fuska a ‘daure tareda daka musu tsawa yace su bar gurin.

Wani kallo ayshah ta watsa musu kafin tabar gurin tana cewa,

STORY CONTINUES BELOW

Dama me mutum ze tsayayi tunda masifa ta iso gidan.

Kasa kallon mum da jikinta yayi matuqar sanyi yayi yawuce part ‘dinsa direct zuciyarsa na quna dan kuwa mummunan mataki zai ‘dauka akansu duka indai akan mum ne.

Daf da zata shiga palonta taji anrungumeta ta baya da sauri ta juyo tana ganin Mahmud ‘dinta ta ‘daukesa da sauri tareda qanqamesa tana hawayen farin ciki koba komai ta yanke shawarar tafiya sbd har abada bazata iya Zama gida ‘daya da mum ba ‘dauke ‘danta zatayi ta tafiyarta inda bamai Kuma jinsu bare yagansu.

Ranar da ‘danta takwana cikin farin ciki da Jin ‘dadin data Jima batayiba.,

Shikansa mahmud yayi kewar mummynsa sosai shiyasa Sai lafe Mata yake Yan shagwa6a.

Acikin Daren ta ha’da kayanta tsaf asuba nayi tayi sallah ta fa’da wanka jiki na rawa.

Daga masallaci direct part ‘dinta ya nufo daf dazai shiga yaga fitowar wani qaton namiji da gudu riqeda rigarsa a hannu yayi bayan part ‘din nata..

Mummunar fa’duwa gabansa yayi kansa ya Sara harsaida wani mugun jiri ya ‘dibesa yayi saurin dafa bango.

What namiji cikin gidana?

Wani qarfi ne yazo Masa tareda 6acin Rai sa zafin zuciya yabi bayan mutumin Amma bai ganshiba gate yakoma da sauri yacewa securities karsu Bari kowa yafita Koda matansa ne kafin yadawo zuciyarsa na tafasa a zafafe ya banka qofar bedroom ‘dinta dai dai fitowarta wanka ‘daureda ‘dan wani munafikin towel dayayi Mata ka’dan danko hadewa bayayi sosai.

Fa’duwa gabanta yayi jikinta ya’dan fara rawa Amma tafara qoqarin dakewa Dan ita tunaninta yagano guduwar dazatayi.

Duk wani alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da ita

Ya rintse idanuwansa cikin zafi da karyewar zuciya ya damqota tareda matseta ya jijjigata da qarfi yace,

Why,why ayshah?

Duk abinda kikayi baya da aurena is not enough saikin kawomin cikin gidana,,,

Cikeda mamaki da tsoro take kallonsa tana qoqarin kwacewa sbd zafin riqon dayayi Mata,.

Tureta yayi da qarfi harsaida ta fa’di har kanta ya bugu goshinta ya fashe a zafafe zuciya na tafasa yace,

Ayshah Nima ayau na tabbatarda kece qaddarata,

Nasoki abaya so Mai tsanani,

Yanxuma Dana manta komai still zuciyata saidata kamu da sabon sonki nakuma tabbatarda dazan Kuma samun wani memory loss ‘din I will still fall for you but wannan shine sakayyar….

Rintse idanuwansa yayi ga mamakinsa saiga hawaye na tsiyayo Masa ya girgixa Kai zuciyarsa na qara ‘daci yace,

Ayshah go, leave, I don’t want to see you again.

Tashi tsaye tayi cikin tsananin zafi da qunar Rai tana kallon tsakiyar idanuwansa hawaye na qoqarin sauko mata tace,

Deen me kake zargi dashi?

‘dauke Kai yayi yace,

Just leave,.

Juyosa tayi da qarfi cikin kuka tace,

Deen ni kake zargi da wani?

Ni ayshah kana tunanin Zan iya rayuwa da wani namijin bayan kai.?

Deen do you really hate me that much da har kakemin wannan zargin after all the years danayi batareda kaiba Amma na tsare mutunci aurenka.?

Wannan shine nawa sakamakon?

Deen when will you stop hurting me and ruining my life?

Girgixa Kai tayi cikin hawaye idanuwanta na kadawa jajir sbd wannan shine Abu mafi Muni dayayi Mata arayuwa and this mark the end of their relationship.

Share hawayenta tayi tace,

Bazan ta6a manta wannan ranarba sbd itace ranarda na datse duk wani sauran hope na tsakanina dakai,

Nagama dakai Deen.

Juyawa yayi ya fice a fusace hawayensa na qara 6allewa.

Zubewa tayi bakin gado tareda sakin kuka ahankali zuciyarta na Kara karyewa tace,

Baba kuyi hkr gida Zan dawo wlh zuciyata fashewa zatayi Ina cikin tsananin rayuwa Ina buqatarku ku yafemin.

Har time ‘din mahmud bai tashi bacci ba hakanan ta tadashi ta saka Masa Kaya ko wanka batayi masaba suka fito.

Mum da Khadija tagani bakin qofar palonta jiki asanyaye Khadija kuwa kuka takeyi sosai.

Kallon Khadija tayi itama idanuwanta na sake 6arewa da hawaye tace,

Khadija mum yau ta qara tabbatarminda Bata qaunata and she will never do sbd nasan she’s behind all this,,, anyways dama I should be ready for even more of these since she’s here Amma komai yariga ya qare…

Hawaye ne suka ganagarowa mum ta bu’de baki da zatayi magana ayshar tayi wucewarta riqeda hannun ‘danta.

Ayshah na fita gidan kamar daga sama Khadija taga mutum bayan flowers ‘din bayan windon ‘dakin ayshah ta zaro idanuwa tayi cikin tsoro harzata gudu ‘daki Sai tafasa ta nufi part ‘dinsa da sauri jiki na rawa tafada Masa

A zafafe ya qaraso gurin tareda cakumosa siyama dake bayansu ta lalla6o da ta6aryarsu ta aiki ta ‘daga da qarfi ta kwalawa Deen akai Nan take ya zube agurin Khadija ma na juyowa ta qwala Mata tasaki qara Mai qarfi itama ta zube qasa.

Hanya ta nuna Masa tareda basa kudin aikinsa da sauri ya fice haryana tuntu6e bayan ya maida uniform ‘dinsa na aikin security agidan.

Ta6aryar ta maida kicin da sauri kafin tadawo gurin tareda daka kururuwa tana Kiran mum na mum ta qaraso tana ganin ‘yayanta biyu zube qasa hankalinta yayi mumman tashi suka kwashesu Sai asibiti.

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

                   *34*

Tafiya ka’dan tayi bayan tabar gidan taji takasa riqe kukan dake son fito Mata ta durqushe agurin tasaki kukan cikin qaramin sauti zuciyarta na neman tarwatsewa..

Zama kusada ita Mahmud yayi tareda 6ata fuska zai fashe da kukan shima yace,

Mummy who beat you?

Sake sakin Wani kukan tayi tana jawo ‘danta jikinta.

Saida tayi iya Wanda zuciyarta ta ‘dan rage nauyi kafin tafara qoqarin tashi taji ankira sunanta cikin sanyayar murya Mai taushi.

‘dagowa tayi tareda miqewa tana juyowa idanuwanta suka sauka kan muh’d dake tsaye akansu yayi folding ‘din hannuwansa a qirjinsa Yana kallonsu cikin tsananin sonta da tausayinta sbd mum takirasa tafada Masa Amma bayajin zaifara zuwa asibiti gurinsu Deen batareda yafara sanin inda ayshan da ‘danta sukeba.

Sabbin Hawaye ne suka gangaro Mata cikin karyewar zuciya tace,

Murphy..

Lumshe idanu yayi zuciyarsa na tsananta tafasa da ganin yanda ayshan takoma.

Cikin kukan da baya fita sosai take kallonsa tace,

Where were you Murphy?

Deen has destroyed my life,,

I’m not dsame ayshah you used to know,,

I’m a shame now…… kukane ya qwace Mata ahankali tayi shiru tana rerowa zuciyarta na qara kaririyewa.

Matsowa yayi gabanta ya tsaya murya a karye yace,

Ayshah insha Allah wahalanki da kukanki ya qare,,

Girgixa Masa Kai tayi cikin kuka tana cewa,

I have no one to see or call my own..,I’m all alone..

Karki cire Kai daga rahamar ubangiji ayshah,

Have faith in Allah insha Allah everything will be alright again.

Kamo hannun Mahmud yayi tareda Jan akwatinta ya kalleta yace,

Let’s go.

Kallonsa tayi saikuma ta sunkuyar dakai tabi bayansa ya bu’de musu motarsa suka shiga ya tada suka tafi.

Tunda taga sun fita garin Abuja ya gyara Zama tareda qarawa motar gudu sosai suka ‘dau hanya ta rintse idanuwanta hawaye suka gangaro zuciyarta ta karye Dan kuwa kobai fa’daba tasan gida zai kaita.

********

Zaune suke suna sauraron abinda shaikh abdallah yake fa’da zuciyarsa ba da’di..

Tabbas malam babba kun Bari shai’dan dason zuciya sunyi galaba akan sani da kukedashi na addini,

Meye al’ada?

Al’ada fa ba musulunci bace hasalima gurarare da dama tayi hannun Riga da abinda musulunci yace ayi.,

Malam babba wannan al’ada da kuka ‘dabbaqa gatanan Kuna gani tayi sanadin rushewar mutumci da girmanku a idon masu mutuntaku sbd yanzu meye amfanin wanna?””””yafada Yana ‘daga jaridar hannunsa ta ayshah da aka bugo.

Gyara Zama yayi ransa na qara ‘daci yace,

Wlh nayi baqin cikin rayuwar data samu ayshah sbd nida ban haifetaba nafi Jin zafin mummunar qaddarar data sameta,

Shi Wanda kuka wulaqanta ‘yartaku akansa gashinan Kuna gani a tv da jaridu irin kyakkyawar rayuwar dayake yi duk sanadin ‘yarku data Zama silar musuluntarsa.,

Maimakon da kuka gane komai ku gadewa Allah da aure sukayi ba zaman sa6on Allah ba saiku aje wata al’ada ku rufawa kanku asiri kubarsu.,

Idanma har hakan bazata yiyuba ku binciki ‘yarku Mana ku gano ta inda Zaku warware matsalar cikin ilimi,

STORY CONTINUES BELOW

Cikin tsananin sanyin jiki baba qarami yace,

 

Tabbas ayshah taso bayani Amma sharrin zuciya da 6acin ran laifin datayi ya Hana a saurareta…

Wannan shine babban kuskuren da kuka tafka amatsayinku na masana addini,

Wlh Koda yaushe aikin zuciya Babu komai atareda dashi Sai nadama da kuka.,

Yanxu gashi duk masu zuwa ‘daukar karatu da da’ira sun daina sbd ganin bakuyi aiki da alimin da kuke dashiba to maizasu cigaba da zuwa koya.?,

Da bahaushe,da yoruba,da kanuri,da buzu da Fulani da kowane yare ‘daya agurin Allah matuqar musulmaine,

Gskia wannan hukuncin da kuka ‘daukarwa ‘yarku yayi Muni ko a al’adar bare a musulunci,

Yanxu gashi Nan atsakanin ‘yayanku dakuka aurarma Sai sa6ani ake samu sbd yawancinsu bason juna sukeba tauyesu kuke sbd al’ada,

Ayshah tayi kuskure Amma Kuma tayi jahadi babba sbd yau musulmai da dama suna alfahari da shaikh nuraddeen hakama zuri’arsa kaf sun musulunta duk ta dalilin ‘yarku shin wannan bai isheku alfahariba?

Nine na ‘daura auren ayshah da nuraddeen akan sadaki naira dubu hamsin,

Ciro bundle ‘din 500 yayi ya aje gabansu yace,

Wannan shine sadakin ayshah danaketa ajiya Ina jiran ranarda komai zai daidaita namiqawa iyayenta Amma kun rigada kun tarwatse rayuwarta banga amfanin cigaba da ajewarba.

Abban ayshan ya kalla yaga ga dukkanin alamu lafiyama ta gujesa sbd rashin ‘yarsa cikin tausayawa yace,

Mal Yusuf Kai da mahaifiyar ayshah kunfi kowa haqqi akanta haka itama tafi kowa haqqi akanku Dan haka ina roqar Mata yafiya

Dukkaninku ku yafe Mata, Allah ma muna Masa laifin dayafi wannan ya yafe mana bare mu ‘dan Adam da ba’abin ha’dawa bane da Allah.

Miqewa yayi tareda yi musu sallama ya fito ya tafiyarsa baba alhaji da baba qaramine suka rakosa har bakin mota suna Masa godiya jiki amace.

Koda suka koma kuka reras suka tarar da abban ayshan nayi Nan jikinsu ya qara mugun sanyi sbd sunsan anshiga haqqinsa matuqa Amma yayi biyayya baice komaiba.

Jiki a mace malam babba da tsufa ya zuwarma ya fara rarrashinsa tareda Tara dukkanin zuri’ar gidan ya sanar dasu ya janye al’ada ko wace iri matuqar Bata addini bace.

Nan uwayensu suka ga abin mamaki Dan kuwa kowa murna da farin ciki yake sbd kowa nada wa’inda sukeso awaje Amma sun kasa bayyanawa,

Cikin Jin da’di suka fara sawa ayshah albarka data qwato musu ‘yancin soyayya da wa’inda sukeso awaje.

Allah sarki Umar kuwa ranar aka fama Masa tsohon ciwon son ayshan Dan kuwa kwana yayi kuka Dan kuwa yasan har abada ya rasa ayshansa.

******

Tunda suka iso asibitin hankalin siyama yafara tashi sbd ganin kowannensu bai tashiba

Nan take tsoro yashigeta musamman Deen ‘din datakeji kamar ta cire ranta tabashi sbd so.

Sam batayi tunanin abin zaikai hakaba tayi tunanin bugesu ne harta samu Musa ya wuce batareda yafa’di sunantaba.

Mum kuwa tuni takira daddynsu ta sanardashi komai hankalinta amatuqar tashe sbd Khadija ta farfado amma Sai wani fusge fusge takeyi tuni doctors sukayi ‘dakin hoton qwaqwalwa da ita sbd tunanin wani Abu dasuke zargi.

Ana gurin hoton Deen ya farko,

Kansane yayi Masa mugun nauyi ya rintse Iumshe idanuwansa ya bu’de ahankali.

Ayshah yafa’da cikin wani irin yanayi tareda miqewa tsaye,

Ahankali komai yafara dawo Masa tun wayonsa har ranar farko daya fara ha’duwa da ayshah da duk sauran abinda yabiyo baya har korar dayayi mata.

Sulalewa qasa yayi ahankali tareda sakin Wani irin kuka dabai ta6ayi arayuwarsaba,,,,kukane na soyayyar ayshah dake yawo cikin jinin jikinsa,,,,

Kukane na abubuwan dayayi Mata,,,,

Kukane na azaba tareda qanqancin rayuwa datayi sbd shi…

Sosai yake kukan kamar ransa zai fita,,,

Ya tsani kansa,ya tsani rayuwarsa..

Mum ce tashigo da sauri siyama na bayanta sbd kiransu da akayi cewar y farfado.1

Cak ta tsaya cikin tsananin tsoro da tashin hankalin ganin kukan dayake Dan Bata ta6a ganinsa acikin wannan yanayinba.

Qarasowa tayi ahankali ta dafasa ya sake fashewa da kuka haryana jijjiga yace,

Mum I remember everything…

Wani farin ciki ne ya rufeta ta rungumesa da sauri tareda sakin kuka ahankali.

Wani mummunar yawu siyama ta ha’diye jiri ya ‘dibeta tayi saurin dafa bango hawayen baqin ciki da danasanin buge Masa Kai suka gangaro Mata.

1

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

                    *35*

Nurse ce tashigo ta tsaya tareda kallon mum cikin yanayi na damuwa tace,

Ma’am doctor wants to see you in his office.

Fa’duwa gaban mum yayi takalli Deen da idanuwansa da fuskarsa tuni sukayi jajir sakancewarsa fari sbd kuka jijiyoyin kansama tuni suka firfito shika’dai yasan mummnan halinda zuciyarsa take ciki.+

Danne damuwarsa yayi tareda miqewa tsaye riqeda hannun mum ‘din suka nufi office and Dr ko kallon gefen siyama baiyiba Dan baimasan da wanxuwarta a ‘dakinba.

Kallo ‘daya Dr yayi musu yasan suna cikin tsananin damuwa Amma Dole ya sanar dasu halinda ‘yarsu take ciki.

Shaikh ya jikin naka Kai?

‘daga Masa Kai yayi Yana lumshe idanu sbd bayajin zai iya magana.

Well gskia a irin yanayin da Khadija ta farfado dashi yabamu tsoro da mamaki Amma bamu tabbatarda abinda muke zargiba Saida mukayi iya binciken mu….

Tsakanin buguwa ko duka days shiga sosai cikin kanta yayi sanadin ta6uwar qwaqwalwanta,,,,, ataqaice dai tasamu ta6in qwaqwalwa..1

Kuka qarfi mum tasaki Deen yayi saurin rungumeta Yana Kiran innalillahi……

Duk wani kukan Dana sanin shuka mugun Abu yau mum tayishi sbd ganin mummunan halinda ‘yayanta suka shiga,,

Finn ya mutu,

Deen baya cikin kwanciyar hankali,

Ga Khadija ta samu tabin Kai..

Kuka tayishi iyakar yinta harya daina fita saidai tunani.

Gida aka sallamosu suka dawo mum na riqeda khadijar daketa faman kalle kalle tana Sosa Kai tana ketar dariya.

Shikuwa ko magana baya iyayi suna dawowao ko Zama baiyiba ya kalli mum jiki amace yace,

Mum Zanje gurin ayshah.

Hawayen tausayinsa Dana kanta ne suka gangaro Mata ta miqe tareda shigewa bedroom ta hado kayanta Dana khadijar a akwati biyu tace,

Itama zata koma gomben sbd bazata iya Zama ananba tafison gidansu na can where it all started.

Bai hanataba ya fito kamar zai wuce saiya tsaya zuciyarsa na nauyi da qunci ya nufi part ‘din siyama daidai lokacinda take waya da qawarta tana fa’da Mata abinda ta aikata..

Yaji abinda duk tafada saiya aje Mata kudi tareda ficewa batareda ta gansaba.

Airport driver yakaisu mintuna qalilan aka Kira jirginsu suka tashi Sai gombe.

**********

Tunda suka shigo garin gombe jikinta yayi mummunan sanyi tayi zuru rayuwarta tada na dawo Mata musamman dasuka kawo daidai makarantarsu Nan komai yadawo Mata tasaki kuka ahankali zuciyarta na qara karyewa.1

Shiru muh’d yayi kukanta na ta6a zuciyarsa Dan shima ganin makarantar ya dawo Masa dakomai na lokacin suna cikin Jin da’di da duhu na kafirci.

Yana parking bakin kwanar layin gidansu zuciyarta ta tsinke akaro na farko rabonta da gida da tsananin tsoro yashigeta.

Kallonta yayi tareda ‘daga Mata Kai murya a sarqe yace,

You can do this,, Allah na tareda ke.

Share hawaye tayi jikinta na rawa sbd tsoro cikin sanyi tace,

Thank you murph….

Katseta yayi da cewa,

Muh’d.

STORY CONTINUES BELOW

Sorry tace tana fitowa motar.

Shike riqeda mahmud Kuma janyeda akwatinta.

Ita kuwa kamar zata Fadi sbd daqyar take ‘daga qafafuwanta.

Mutane da dama Basu ganetaba wasu kuwa basuma lura dasuba har suka Isa qofar gidan saita tsaya cak takasa shiga sbd Babu kowa a qofar gidan kamar dah.

Kallonta muh’d yayi tareda sauke mahmud cikin kulawa da tausayawa yace,

Ayshah you’ll have to do this ke ka’dai,,,

Komai zasuyi Miki karki Kuma barinsu,

Ba’a fushi da iyaye komai zasuyi maka,

I will come back tomorrow insha Allah.

Juyawa yayi ya wuce yabarta tsaye riqeda hannun Mahmud daya gaji da tsayuwa jikinta ba inda baya rawa,

Shekaru biyar ba wasa bane batasan yazata fuskanci iyayenta da ‘yan uwantaba musamman umminta data Bari cikin tsananin damuwa.

Ayshahhh””””””””taji ankira sunanta da qarfi a tsorace ta ‘dago taga ya abbakar cikin shigar kayan soja zai fita.

Umar dake bayansa ne yayi saurin qarasa fitowa Jin sunanda abbakar ‘din yakira.

Qoqarin ja baya take taji mutum a bayanta da sauri ta juya zuwa lokacin har qafafunta rawa suke sbd fargaba da tsoro.

Abbanta tagani abayanta tsaye yayi wata muguwar Rama duk manyanci da tsufa sun fara bayyanar Masa sbd damuwa.

Kallonta abbanta yayi sama zuwa qasa yaga suturar dake jikinta Nan take tausayin ‘yarsa da baqin cikin sakata a wannan halin yataso Masa sbd dogon wandon  pencil jeans ne ajikinta blue da yellow top Mai  dogon hannu ka’dan Sai blue hijab qarami iya wuya qafafunta kuwa lopas ne black.

Zubewa qasa tayi da sauri jikinta na wani irin 6ari cikin kuka takira sunansa…

Ga tarin mamakinta hannu yakai yatada ita tsaye tareda janta zuwa cikin gida hannunsa ‘daya na riqeda mahmud daya qanqame uwarsa cikin tsananin tsoro.

Palon malam babba ya nufa da ita su abbakar na bayansa jiki duk amace da ganin canjin yanayin rayuwarta qarara afili Wanda Suma sunsan sun taka muhimmiyar rawa matuqa gurin jagula komai.

Duk Wanda ya ‘dago Kai yakalli ayshah saiyaji hawayen tausayinta sun ciko idanuwansa sbd ayshah Mai kunya da sanyi tareda kawaici Amma yau gata tsaye cikin mummunan shiga batareda hijab.

Tabbas duk Wanda baiyi tunaniba gurin yanke hukunci zai qarashe cikin kuka da Dana sani tareda babbar kunya.

Kukan farin ciki kawai takeyi ganin har malam babba dakansa Yana neman yafiyarta Nan tasake sakin kuka tana qara Basu hkr….

Kodata isa dakin umminta ta tarar da ita zaune nuratu na miqata Mata magani da ruwa

Ta rame ciwo ya zurfi ajikinta suna ha’da Ido ummin ta ‘dauke kanta da gudu ayshah ta qasaro ta rungumeta tana kuka sosai.

Kasa daurewa ummin tayi ta rungume yarta cikin farin cikin ganinta.

Nuratu mahmud dake riqe da rigar ayshah tajawo jikinta tana cewa,

Zo Nan my sweet boy..

Zuwa yayi a Dan tsorace sbd shi duk gidanma tsoro komai ke basa.

Kasa sakin ummin tayi Banda kuka ba abinda take harsaida abin yafara bawa ummin da abbanta tsoro abban yakira sunanta ta girgixa Kai cikin tsananin kuka tace,

Abba nayi qunci na zuciya Dana rayuwa,

Ummi nayi rayuwa cikin tsanani,

Ummi nika’dai nasan zafi da qunar da zuciyata tekeyi kowace Rana….

Sanyi jikinsu yayi Abba yace,

STORY CONTINUES BELOW

Kiyi hkr ki godewa Allah dawa daidaita Mana komai ki danne abinda yararu ki gyara tarenki da ubangijinki kiyita istigifari.

Daqyar ta tsagaita kukanta ta tashi tayo alwala tadawo kusada ummi tayi sallah tafara addua tana tsiyayar hawaye.

Su husna duk anyi musu aure Dan haka yanxu ‘yan matan gidan su nuratu ne dasu kausar shiyasa koyaushe tana zaune gurin umminta sbd batada abokanan fira yanxu.

Su Yaya abbakar da sauran samarin gidan suna matuqar son mahmud sbd akwai shiga Rai ga shegen wayo duk da ba sosai yakejin hausaba ba,

Ta 6angarensu baba ma sunaji dashi Dan mahmud ‘din akwai qiriniya da rashin son Zama guri ‘daya.

Tunda tadawo kullum da saitaje kowane sashe ta gaida uwayensu kafin ta yada zango gurin malam babba acan take zamanta yayita yimata nasiha sbd yanzu tsananin qaunarta da tausayinta yake musamman ma data Fadi yanda tayi rayuwa.

Ya Umar duk abin duniya ya damesa Sai ramewa yakeyi sbd har lokacin qaunar ayshah nanan kwance cikin ransa gashi yanxu kallonsa batayi iyakacinta dashi gaisuwa.

Ranarda Muhd yadawo har cikin palon malam babba aka shigo dashi akai Masa tarba ta musamman Nan suka sake gode Masa.

Bai bar gidanba Sai yamma sosai bayan yasha fira dasu malam.

Dazai tafi har mota qofar gida ayshah ta rakosa tana qara fa’da Masa yanda hankinta ke kwance yanxu.

Kallonta yayi yaga yanda harta fara canzawa fuskarta na fidda wani kyakkyawan murmushi.

Murmushi yasaki tareda kallon agogo yace,

Bari naje ayshah Zan ‘daukosu mum daga airport Zan dawo gobe.

Fa’duwa gabanta yayi ta qaqalo murmushi tana cewa,

Ok bye.

Kodata koma gida cigaba da harkokinta tayi Tama manta da zancen da muh’d ‘din yafada Dan ita mum da duk wani tarkacenta basa gabanta yanxu.

Washe gari tunda ta tashi tayi Shirin zuwa gidajen su husna datayi musu alqawarin zuwa.

Akwatinta ta bu’de ta fiddo duk kayan ciki hakanan dai ta daure tasaka wata doguwar Riga Mara hannu sbd ba kayan arziki acikin kayanta.

Daure gashinta tayi ta Ari hijab ‘din nuratu dogo maroon tasaka ummi tabasu kudin mota suka fito.

Polon malam babba suka shiga da sallama.

Mummunar fa’duwa gabanta yayi ganin Deen da daddynsa harda mum da muh’d taredasu malam babba.

Yawu ta ha’diye tareda ‘dauke kayi tafadawa malam babba zasu tafi.

Mahmud dake riqe a hannun nuratu ya qwace cikin farin ciki da ihun murna ya nufi dadynsa.

Rungumesa yayi lazy eyes ‘dinsa nakan ayshah da baqin cikin ganinsu ya bayyana qarara afuskarta.

Gurin mum Yakoma Yana cewa,

Yeeeh granny you’re wearing a hijab like my mum she’s wearing a hijab too now.

Juyawa tayi zata fice malam babba yace,

Ayshah dawo zonan ki zauna.

Dawowa tayi ba musu ta zauna qasa ba annuri ko ‘daya a fuskarta.

Ayshah so nake ki shirya ki koma ‘dakinki.

Murmushi tasaki ahankali Dan ita yanxu ta daina cutar kanta cikin girmamawa tace,

Baba idan kunaso nayi aure zanyi Amma bada Deen ba…

Shiru sukayi dukkaninsu Babu Wanda baiyi mamakin zancentaba.

Shidai Deen shiru yayi har lokacin lazy eyes ‘dinsa nakanta Dan yasan fiyeda hakama zatayi ayanda ranta yake 6ace akansa.

Tashi kije”””””baba malam yace Mata.

STORY CONTINUES BELOW

Tashi tayi ta ficewarta.

Dawo da kallonsa gurinsu dady yace,

Ahalinda ayshah take ciki yanxu ba’ayi Mata adalciba idan aka tilas Tata…

Cikin sauri da mutuwar jiki Deen yace,

Baba please Kar a tilas Tata Zan iya jira harta huce banason ranta ya 6aci pls ko magana na Kar akuma yimata ranta xai 6aci and I don’t want that…

Dafasa muh’d yayi zuciya a karye sbd alamu sun Kuma nuna ayshah dai ba tasa bace..

Sai yamma sosai suka dawo tana shawo kwanar layin gidansu shita fara hangowa zaune bakin gidan Yana waya mahmud nakan jikinsa yanacin Pringles.

Nuratu na ganinsa ta saki fuska ta gaidasa ya amsa idonsa nakan ayshah data wuce tana waya ko kallo bai ishetaba.

Murmushi tasaki tana kallon duk yanda ya susuce Yakoma Nik ‘dinsa sbd yanda yayi laushi kalar tausayi hakama halayensa nada da dama sundawo musamman sanyinsa.

Wucewa tayi tabi bayan ayshah tana adduar Allah yabata Mai sonta kamar yanda Deen ‘din keson ayshah.

Anan yayi sallar magriba da Isha taredasu malam kafin ya wuce gida.

Kullum Yana gidan har dare Amma tun lokacin bai sake sakata a idoba sbd tuni ta yafe fita Dan har cikin ranta batason ko ganin fuskarsa yanxu.

6angaren mum kuwa ta maida hankali gurin koyan addini da Kuma hidimar kulada khadija duk da dai akwai Mai kulada ita dasuka ‘dauko.

Ayshah hankali ya kwanta tayi fresh fatarta ta sake gogewa ga uwa uba wani kyau data qara.

Hijab ta jawo tasaka ta nufi 6angaren mama sakina suna cikin fira ya Umar yashigo ta miqe ta fito saita wuce palon malam babba Kai tsaye.

Da sallama tashiga ba zato sukaci karo da juna.

Dagowa tayi hannunta dafe da goshinta idonta ya sauka cikin lazy eyes ‘dinsa tayi saurin ja baya gabanta na fa’duwa sbd muguwar ramar data gani ataredashi.

Juyawa take qoqarin yi yayi saurin riqota ta fixge da qarfi zuciyarta na tafasa yayi saurin Shan gabanta tareda rungumeta yasaki wani lazy kuka cikin kunnuwanta Wanda ita kadaice meji.,

Yanda kukan ke shiga kunnenta directly tareda rungumar da yayi Mata yasa jikinta mutuwa sonsa nason motsa Mata hawaye na gangaro Mata.

Sosai yake Mata kukan cikin kunne Yana cewa,

I love you my ayeeshah,

I’m really sorry please forgive me I can’t live without you..

You’re my life,my happiness my everything please forgive me….

Gyaran murya sukaji daga bayansu arikice ta qwace jikinta tana sunkuyar dakai tareda juyawa da gudu tayi cikin gida.

Kallonsa abbanta yayi yaga yanda har lokacin bai daina hawaye ba take tausayinsa ya kamasa Kuma yasan itama ayshan haryanzu tana sonsa kawai zafin abinda  yayi Mata ne ya kasa sakinta…

Kallonsa yayi tareda Kiran sunansa yace,

Nura kaje ka shirya Nanda sati biyu ayshah zata dawo gidanka insha Allah.

‘dagowa yayi cikin farin ciki saikuma ya sunkuyar dakai cikin karyewar zuciya yace,

Aa Abba banason a takura ayshah, zatayi kuka and I hate to see her tears…

Murmushi abban yasaki tareda wucewa yabarsa.

Palon malam babba abban yashiga Nan ya tararda malam ‘din suka Kai qarshen magana sati Mai zuwa zata tare.

Koda suka fa’da Mata kasa Musa musu tayi saidai kwana tayi tana kuka kamar ranta zai fita sbd ita ka’dai tasan yanda takeji akan siyama ko acan da daurewa kawai takeyi Sam bazata iya Zama dashiba a yanxu.

Duk yanda yaso ya ganta taqi yarda sbd wani sabon haushinsa takeji.

Gyara na musamman su mama sakina dasu anty Amina suke Mata itadai ta qyalesu ne kawai Dan nuna biyayya ga iyayenta Dan nuna canxawarta da tubanta.

Kayan lefe na ban mamaki da tsoro mum takawo tareda wasu qannenta dasukazo guda biyu duk da ba musulmai bane ba’a nuna musu qyama ba suma Basu nunaba,

Tunda sukazo kowa saidaya tausayawa Khadija halinda take ciki musamman ma ita ayshan Dan Saida tayi hawayen ganinta a wannan halin,

Ya Umar da tunda yaga khadijar yaji zuciyarsa ta kamu da qaunarta akaro na farko daya kalli wata mace da sunan so bayan ayshah..

Lokacinda yasanarda su baba maganar sun tausaya Masa matuqa sbd ganin dai a qarshe ya Kare da auren mai ta6in qwaqwalwa Wanda ba komai cikin auren Sai lalura Amma hakanan tunda yanaso Kuma su mum sunyi na’am sai aka ce anbasa.

Ana gobe za’a kaita aka shirya walima a gidan inda dukkanin dangi da abokanan arziki suka taru akayi taro sosai..

Amarya ayshah Banda kyalli da wani haske ba abinda take ga Jan lalle da aka tsara Mata a farar fatarta.

Washe gari da yamma aka kaita gidansu Deen ‘din dake garin bayan Tasha kukan sake rabuwa da gida kamar me.

Koda kowa ya watse ta yaye lullu6inta ahankali ta qarewa ‘dakin kallo tana tunano ranar farko data fara zuwa gidan harta shigo room ‘din.

Lumshe idanu tayi son Deen ‘din na taso Mata qasan maqoshi tace,

I can’t stop loving you nuraddeen Niklaus, you’re my love my life _(mi’amor mi vida)_..1

Toilet tashiga tayo alwala tafito tana yaba tsafta da son gayu da kayan qamshi irin na Deen ‘din kamar mace,..

Saukowa qasa tayi ba kowa a palon Sai sabuwar Mai aikinsu ruqayya tana jera abinci a dining ta wuce bedroom ‘din mum Kai tsaye.

Sallah ta tararda mum ‘din nayi itama ta tsaya gefenta ta tayarda tata..

Kusan atare suka gama Nan mum ‘din ta sake roqon gafararta.

Girgixa Mata Kai tayi tace,

Mum please don’t apologise to me you’re disgracing me after all you’re my mother and mother’s don’t apologise to their children..

Rungumeta mum tayi cikin farin ciki kafin suka fito Palo daidai lokacinda yashigo palon hannunsa riqedana mahmud.

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

          _Mi amor-mi vida…._

 

_Viawattpad@mamuhgee_

        

                   *36*

Da gudu Mahmud yayi gurin mum data nufi dinning Yana nuna Mata sabon chocolates ‘dinsa.

Sanye yakeda farar Australian shadda dataci uban nerori ya qara wani irin haske da kyau sbd ‘yar ramar dayayi ta rashin ganinta.

‘dauke Kai tayi tareda ‘daure fuska zata wuce yayi saurin riqo hannunta Yana marairaice fuska yace,

Baby please don’t…

Wani kallo ta watsa Masa yayi saurin sakin hannunta jiki asanyaye sbd ya tsani ganin fushi ko 6acin a fuskarta.+

Kasa tsayawama palon tayi ta juya takoma bedroom ‘din mum yabi bayanta da kallo shauqin sonta na qara shiga jininsa ahankali ya nufi gurinsu mum Yana cewa,

Ya Allah I love this girl so very very much..

Zama yayi kusada mum ta kallesa tana zaunarda mahmud kusada khadija da ruqayya ke bawa abinci Tana dawo da rabi.

Ina ayshan ita?

Lumshe lazy eyes ‘dinsa yayi tareda bu’dewa ahankali yace,

Mum she’s still angry with me.

Murmushi tasaki tareda miqa Masa cup ‘din milkshake da kullum saiyasha tace,

Be more patien my sweet boy.

Karban cup ‘din yayi Yana cewa,

I love her morethan…

Katsesa tayi da cewa,

Yes I know my son but ka qara Bata time kasan she’s deeply hurt.

Har suka gama having dinner tana ‘dakin mum tana game a sabuwar wayarta da mum ‘din tasiya Mata.

Daga dining toilet ruqayya tayo da mahmud tamasa wanka tana qoqarin shiryasa ayshan ta kar6esa tacigaba da shiryasa cikin kayan bacci ya haye gadon mum ‘din ya kwanta Nan take bacci ya ‘daukesa.

A ‘dakin mum tayi sallarta ta Isha tana idarwa itama tafara qoqarin Haye gadon saiga mum baki sake take kallonta tace,

Ayshah mekikeyi anan haryanxu?

Hamma ta’dan saki tace,

Mum inajin bacci ne.

Zama mum ‘din tayi bakin gadon tareda kallonta dakyau tace,

Ayshah nasan an cutatar dake anzalunceki but please ki yafewa mijinki.

Sunkuyar dakai tayi cikin sanyin murya tace,

Mum na yafe Masa tuntuni.

Thank you ayshah and may God bless you my child tashi maza kije your husband is waiting for you upstairs.

Saukowa gadon tayi ba musu ta fito tana fitowa tashigewarta bedroom ‘din khadija ta tararda ita tayi bacci kan lafiyayyan gadonta Sai itama tayi kwanciyarta agadon hardasu Jan bargo ta lullu6e.

Tun Yana jira harya cire ran zatazo ya kwanta jiki a sanyaye bayan ya kashe wayoyinsa Dan gudun damuwar da siyama ke Masa da yawan Kira.

Bata baro ‘dakin Khadija ba Saida Tasha barcinta har kusan ten kafin ta fito ta nufi stairs ta Haye sama tashige room ‘din.

Tsaye yake gaban mirror ‘daure da towel iya qugunsa lafiyayyar fatar jikinsa Sai glowing take sbd hutu.

Ta cikin mirror yaga yanda ta ha’de fuska Taki kallon ko gefen dayake.

STORY CONTINUES BELOW

Juyowa yayi ya tsaya gabanta tareda riqo hannunta yace,

Gud morning luv..

Qwace hannunta tayi tareda fa’dawa toilet ta rufo qofar da qarfi tabarsa tsaye jiki duk a mace.

Daqyar ya iya saka kayansa ya sauko qasa daidai fitowar mum a shirye tsaf itada mahmud.

Da gudu mahmud ya fa’do jikinsa Yana cewa,

Gud morning Daddy.

Morning my boy,,gud morning mum.

Morning sweetheart,,,ya ayshah take?

She’s getting dressed.

Dinning suka nufa daidai lokacinda ruqayya tafito da khadija bayan ta shiryota..

Tundaga nesa qamshinta ya daki zuciyarsa ya lumshe idanu tareda budesu tsaf akanta taci wani irin ado da kwalliya cikin skirt and blouse na wani black lace Mai adon red dayaci uwar nera gurin siya yakuma zauna cif cif ajikinta kyakkyawan figure ‘dinta yafito.

‘yar qaramar sarqar white diamond ce a wuyanta da earrings ‘dinta Sai ‘dan qaramin bracelet…

Baki ya saki Yana kallonta sbd baita6a ganin ayshah Koda powder ba Amma yau wani fitinannen hot red lipstick ne a lips ‘dinta dayayi mugun kwa’daita Masa Shan lips ‘din.

Rufe Masa baki mahmud yayi ta hanyar saka Masa  chips a baki Yana cewa,2

Daddy kaima kanason granny tabaka abinci abakine?

Tauna chips ‘din yayi still idonsa na kanta ahankali yace,

Oh my God she’s looking damn hot.

Harararsa tayi tareda Zama kusada khadija tana gaida mum.

Cikin farin ciki mum ta amsa tana hararar Deen ‘din yanda ya kafe ayshan da Ido cikin shauqi.

Hankali kwance taci breakfast ‘dinta itadasu mum shikuwa tuni yayi loosing control kawai dannewa yake sbd agaban mum ne da Mahmud da saiyayi kissing wa’innan red lips ‘din nata.

Suna gamawa muh’d da ya Umar sukazo kaisu airport Nan hankalinta yayi mummunan tashi zuciyarta tayi mugun nauyi hawaye suka zuwar Mata tayi saurin maidasu,

Idan akwai abinda ta tsana ayanxu to shine komawa Abuja ta zauna gida ‘daya da matar deen.

Sarai ya lurada canxawarta duk saiyaji tabasa tausayi ya riqo hannunta ahankali zaiyi magana ta zame tareda hayewa sama.

Shigowa yayi ya zauna kusada ita tareda Kiran sunanta ahankali tayi banxa dashi.

Cikin sanyin murya yace,

I’m really sorry ayeeshah you….

Katsesa tayi ta hanyar miqewa tsaye ta jawo handbag ‘dinta da hijabinta tasaka ta sauko qasa tabarosa.

Shida kansa yafito Mata da kayanta suka fito aka kaisu airport ‘din.

Koda zasu tafi ya Umar kallon Khadija yayi Yana murmushi tareda Mata sweets nanta kar6a harda tsalle kaman yanda Mahmud keyi duk saiyaji yaqara sonta,,

Su muh’d kuwa duk tausayi suka Basu mum dai Sai hawaye.

Tunda suka shiga jirgi zuciyarta ke bugawa da qarfi harsuka Isa driver yazo ya ‘daukesu suka iso gidan.

Part ‘dinta tashige batareda tajira fitowar siyama ba danko fuskarta Bata qaunar gani.

Goge komai da ko’ina tayi ta share tayi mopping ta kunna ac ac da fridge tareda kunna burner Nan take ko’ina ya’dau sanyi da qamshi

Ta nufi bedroom ta tu6e tafa’da toilet tayo wankanta tana fitowa tasaka doguwar rigar roba Mai hannun vest ta ‘daura scarf tareda saka hijab tayi sallar azahar da la’asar kafin ta’dan kwanta danta huta.

STORY CONTINUES BELOW

Su mum ma ruqayya ce ta gyara musu part ‘dinsu tsaf ta kunna ac tareda feshe ko’ina da room freshener Mai da’di kafin sukayi wanka da salloli.

Tunda suka shigo gidan taga shigowarsu tayi shigewarta bedroom ta kwanta zuciyarta na tafasa da dawowar ayshah harda ma mum ‘din.

Part dinsa yashiga duk saiyaji bazai iya komaiba sbd ya’danyi qura Yana buqatan gyara saiya fito Kai tsaye ya nufi gurin ayshah.

Yana bu’de qofar palonta wani sanyi da qamshi ya tarbesa ya lumshe ido tareda qarasowa ciki bayan ya rufe qofar.

Bedroom ‘dinta ya nufa ya tararda ita kwance tana bacci hankali kwance murmushi yasaki tareda duqawa yayi kissing ‘din lips dinta ya tu6e yashige toilet.

Wanka yayo yana fitowa ya tsaya gaban mirror ya fesa body spray tareda juyowa ya haye gadon ahankali tareda jawota jikinsa ya lumshe idanu sbd shima baccin yakeson yayi.

Saida marairaice sosai suka farka kusan atare tana ganinta ajikinsa ta ‘daure fuska tana qoqarin tashi yayi saurin riqeta cikin jikinsa Yana kallon cikin idonta.

Mutuwa jikinta yayi ta kalli lazy eyes ‘dinsa dake kashe jikinta ako yaushe murya qasan maqoshi tace,

Sakeni Mana.

Kallon idonta tayayi laushi yayi ya qara shigarda ita jikinsa yakai bakinsa saitin kunnenta cikin wani irin salo yace,

Har abada bazan sakekiba.1

Lumshe fararen idanuwanta tayi tana narkewa ajikinsa tace,

Naji but please let go of me…

Saikince kin yafemin.

Kallonsa tayi cikin tsakiyar Ido jikinta na qara saki cikin yanayin sanyi tace,

Do you think I can be angry with you for long…

Sonka yariga yayimin mummunan shiga Deen I can’t be angry wit you or hate you for long,,, believe it or not you’re my life,my happiness my love…. hawaye ne suka gangaro Mata yayi saurin girgixa Mata Kai Yana lashesu da harshensa.

Bakinta yake qoqarin kamawa tayi saurin zillewa ta sauko gadon batako waiwayesaba ta shige toilet.

Daqyar ya tattaro nutsuwa da ‘yar kamewa ya nufi masallaci sallar magriba.

Tana gama sallah gurinsu mum ta nufa ta tararda sun gama sallah suna qoqarin cin abinci da ruqayya tayi musu.

Tuwon semo ne da miyar ku6ewa dataji naman rago da kifi.

Zama tayi tana cewa,

Mum da gani this food will taste very sweet harna matsu inci.

Mahmud dake na’de ‘yar qaramar daddumar sallarsa yace,

Mummy please don’t eat it all bamu ciba fa.

Dariya yabasu sbd yanda yayi zancen ya nuna yunwa yakeji.

Zaunawa sukayi tsakiyar palon sukaci suka qoshi Nan suka fara fira har akayi Isha sukayi ayshah taqara koyawa mum wasu abubuwa dangane da ibada.

Part ‘din siyama ya nufa Kai tsaye daga masallaci ya tararda ita a zaune tana kallon tashar national geographic.

Kallo ‘daya tayi Masa ta ‘dauke Kai shikuwa ko kallon nata baiyiba sbd Sam baimasan yazai kalli wata maceba bayan ayshansa.

Yana ta6a wayarsa fuska a ha’de yace,

Are you fine,,,I mean is everything ok?

Banxa tayi dashi ya ‘dago ya kalleta Nan take ransa yakuma 6aci a hasale yace,

Badake nake magana bane?

Zuciya datazo Mata wuya saura qiris ta qunduma Masa Zaki Amma saita danne tajuyo takallesa tace,

Lapiya qalau.

Juyawa yayi ya ficewarsa tayi saurin tasowa tabiyosa tareda riqo hannunsa ya tsaya cak tareda rintse ido zuciyarsa na ‘daci sbd riqon datayi Masa jiyake kamar wutace ke qona jikinsa.

Zagayowa gabansa tayi tareda rungumesa tana cewa,

I Miss you my shaikh.

Ayshah data fito daga gurinsu mum idonta yayi Mata mummunan gani wani mugun jiri ya ‘dibeta saura qiris ta zube tayi saurin dafa bango tareda barin gurin da sauri ko ganin gabanta batayi.

Zare jikinsa yayi da qarfi tareda ‘daure fuska sosai ya ra6ata ya wuce sbd yaga wucewar ayshah da sauri Kuma ya tabbatarda tagansu.

Qofar palonta yayita qwanqwasawa Amma taqi bu’dewa qarshema yanaji ta kunna qarar tv dankarma takumajin qaran qwanqwasan.

Gurinsu mum Yakoma yaci abinci daqyar kafin Yakoma yakuma ta6a qofar arufe ya juya jiki amace zuciya a jagule ya nufi part ‘dinsa.

Washe gari Bata fitoba Sai guraren azahar lokacin baya gida Yana gurin aiki asanyaye tagaida mum tazauna dining tayi breakfast Rai a jagule.

Tana gamawa ‘daki takoma ta kwanta saitaji sabon kuka na sake zuwar Mata ta fashe dashi zuciyarta na qara nauyi.

Dafata taji anyi ta ‘dago da jajayen idanuwanta ta ganshi tsaye lazy eyes ‘dinsa na qoqarin saukoda hawaye ta miqe  tareda wucesa ya dawo da ita tareda Bata kyakkyawar runguma cikin jikinsa da sauri ta qanqamesa tareda sakin Wani sabon kukan.

Saidatayi Mai isarta Yana rungume da ita kafin ya ‘dagota tareda share Mata hawaye ya kamo hannunta suka fito.

Tana ganin sun Kama hanyar part ‘din siyama ta tsaya tareda zame hannunta tana ‘daure fuska.

Kallonta yayi yace,

Please come with me.

Girgixa Masa Kai tayi idanta na kawo ruwa.

Sakinta yayi ta nufi part ‘din su mum tashige da sauri.

Mamuh💋

_dont forget to follow, vote and comment_*_MAMUH GEEE_*

_*TAURA BIYU….*_🍒

_Mi amor-mi vida…._

_Viawattpad@mamuhgee_

*37*

Zaune take tana cika tana batsewa Dan yau jitake Sai anyita ta qare Dan wlh tagaji da wulaqancin Deen saidai ko ita ko ayshah wani yabar gidan sbd bazata yarda karuwa tafita matsayi acikin gidantaba.

Da sallama yashigo fuskarsa ba yabo ba fallasa.

Ko sallamarsa Bata amsaba ta taso tazo gabansa ta tsaya cikin zafin Rai tace,

Yau inason sanin matsayina a gidan Nan.+

Kallonta yayi cikin baqin cikin Yama ya iya zaman aure da wannan for almost two years Kai wlh na cutu nida ayshana da yawa.

Cikin masifa tace,

Fadamin meye matsayina acikin gidan Nan Dan kuwa yau inason sanin nida tsintacciyar matarka waye Mai….

‘daga Mata hannu yayi da sauri sbd ransa daya fara 6aci yaciro envelope daga aljihunsa ya miqa Mata.

A wulaqance ta kar6a kafin ta bu’de yabar gurin.

Cheque na kudi tagani kafin taga muguwar takarda daga baya ma’ana takardar sallama.

Hannu ta ‘dora akai zata zunduma ihu saita fasa tana cewa,

Wlh ma bazanyi ihunba saidai Kuma wlh bazan yardaba.

A zuciye ta banko qofar palon mum tashigo ba zato tasakarwa ayshah wani mummunan mari kafin ta sauke hannunta mum tasakar Mata tana juyowa Deen ya ‘daga hannu ayshan ta riqe hannunsa tasakar Mata Wanda yafi na mum qara ranta a6ace.

Riqo ayshan yayi da sauri Yana shafo fuskarta kaman zaiyi kuka ya juyo Rai a6ace yace,

Get out.

Kururuwa ta saki tana cewa,

Wlh bazan tafi koina ban kar6i wannan sakinba indai akan wannan tsintacciyar karuw…

Marin dai dabata samu a farkoba saidata shasa a gigice ta ‘dago Dan Marin ba qaramin shigarta yayiba ya kalleta Rai amatuqar 6ace yace,

Foolish woman,idan baki yarda da sakin akan ayshah ba kije ki yarda da sakin akan abinda kikayi yazama sanadin rushewar lafiyar khadija.

Wat””””mum tafada da qarfi tana kallon Deen ‘din ya ‘dauke Kai Dan baiso fidda maganarba Amma ita taja.

Azuciye mum takalleta zuciyarta na ‘daukar zafi ayshah tayi saurin dafa mum ‘din tana cewa,

Don’t weste your energy mum let hand her to police let them deal with this crazy mentality.

Kai tsaye yace,

She’s not going to any police let her go zata ga daidai abinda tayi Nan gaba.

Kuka tafashe dashi tareda zubewa qasa cikin nadama tana basa hakuri ya fice riqeda hannun ayshah Yana kallon face ‘dinta inda siyamar ta mareta.

Part dinsa suka shiga ya zaunar da ita kan kujera tareda durqusawa gabanta yakai hannu ya shafo fuskarta kaman zaiyi kuka.

Riqe hannunsa tayi tana kallon face ‘dinsa hawaye naciko idanuwanta tace,

Deen idan har saboda ni ka saki siyama then please ka maida ita nizan koma gombe ita ta zauna anan…

Shihhhhhh””yace Mata Yana ‘dora yatsansa kan lips ‘dinta ahankali yace,

Ayshah kece rayuwata farin cikina,,

Ayshah matuqar kina taredani bazan ta6a yiwa ko wace mace adalciba bare siyama da Bata ganin girmana Dan mum ‘dina,

Banason ranar lahira natashi da shanyayen Rabin jiki sbd rashin kwatanta adalcina.

STORY CONTINUES BELOW

Rungumesa tayi ahankali tareda cewa _i love you deen_ ahankali.

I love you more baby.

Da daddare suna gama cin abinci ta miqe takoma part dinta tayi wanka tareda zaunawa gaban mirror tayiwa turare 6arna kafin tashafa hot red lipstick ‘dinta data fahimci Deen na mutuwar so.

Wardrobe ta bu’de ta ‘dauko rigar bacci tasaka pant tana qoqarin saka rigar yashigo bedroom ‘din Yana ganin jambakinta ya zaro Ido kamar qaramin yaro yace,

Oh my God I love that red lips.

Qarasowa yayi tareda jawota jikinsa Yana kallon lips din yanda jambakin ya zauna daidai akansu ya lumshe ido cikin kunnenta ya ra’da Mata _i love this_.

Lumshe fararen idanuwanta tayi ya nunasu Suma yace,

And i love these too.

Shafo gashinta dayaji gyara yayi Yana lumshe ido yace,

And this too.

Hannu ya zura cikin ‘yar fingilar rigar ya lalabo qirjinta kusan atare numfashinsu yakusa ‘daukewa murya Bata fita yace,

And these too..

Sake shafarsu yayi tareda matsawa ta ja wani irin numfashi kafin ta bu’de idanuwanta dasukai ja Nan take ta kallesa.

Launin da idanuwanta suka koma yaqara tado dukkanin wata sha’awarsa ya Kai bakinsa ahankali kan lips ‘dinta yana lumshe ido sbd wani laushi da da’dinsu daya shigesa.

Numfashi takuma ja sbd kissing ‘din ba qaramin shiga kwanyarta yayiba.

‘dagata cak yayi ya kwantar kan gado tareda zame ‘daya da babun rigarta yakaimata wani lafiyayyan kiss a Mara daidai inda akai Mata aiki lokacinda ta haifi mahmud.

Numfashi taja da qarfi tareda riqe qansa shikuwa jikinta yacigaba dabi da kiss harya Isa qirjinta Nan take su duka suka ida rikicewa Nan yafara nuna jarumtakarsa suka Lula birnin ma’aurata.

Koda gari ya waye daqyar ta iya tashi ta lalla6a tayi wanka tazo tayi sallah tana idarwa Yana dawowa daga masallaci,

Zama yayi kusada ita tareda jawota jikinsa cikin kunnenta ya ra’da Mata _i love you my ayeeshah_..

Murmushi tasaki tareda ‘dan ‘dagowa ta kallesa tace,

I love you too my man.

Bacci suka koma inda ya hanata sakewa da soyayyarsa Saida suka qara soyewa kafin baccin ya ‘daukesu.

Qarfe Tara da rabi suka tashi suka shiga wanka.,

Kallonta yayi Yana riqeda hannayenta ya shafo lips ‘dinta tareda kissing ‘dinsu kafin ya shafo wuyanta shima yakai baki ahankali yayi kissing ‘dinshi qoqarin Kai baki kan qirjinta yake ta riqo fuskarta tareda ha’de bakinsu tana lumshe ido.

Da shiririta sukayo wankan suka fito Nan suka shirya suka fito tsaf cikin adansu na sabbin amare dake cikin tsananin farin ciki.

Cikin qanqanin lokaci dukkaninsu suka canxa Sai wani qyalli da haske suke qarawa sbd kwanciyar hankali gefe ‘daya ga shirye shiryen auren ya Umar da khadija dakuma na muh’d da nuratu dasukeyi Dan gaf ake da farawa Sai angama zasu koma Paris sbd makarantar mahmud dakuma likita da khadija zata fara gani.

Tunda suka fara shirye shiryen tafiya gombe take cikin farin ciki Dan tana matuqar son ganin umminta da abbanta tareda malam babba tayi kewarsu matuqa.

Zaune take tana waya da nuratu tana sanarda ita gobe zasu iso yashigo palon riqeda green apples yankake daya yanko Mata sbd abincinta kenan yanxu.

Zama yayi tareda jawota jikinsa ya ‘dauki ‘daya saidayayi kissing bakinta kafin ya saka mata.

STORY CONTINUES BELOW

Na biyu ma Saida yayi kissing bakin yasaka Mata,

Ana uku daya Kama bakin yafara kissing Yana lumshe ido ta zame tana kallon idonsa tace,

Deen you know this is cheating right?

Kamota yayi Yana kallon bakinta idanuwansa na qanqancewa yace,

This is our deal,,,you want apples,I want kiss so….

Maida bakinsa yayi cikin nata batareda yakarasaba sbd amatse dacigaba dashan bakin nata itama ba 6ata lokaci ta fara mayar Masa suka cigaba da soyewarsu.

Koda suka iso ba qaramin farin cikin ganinta hankali kwance iyayenta sukayiba Nan aka hau hidimar biki ranar asabar da qarfe goma dubban jama’a suka shaida auren Umar da khadija saina muh’d da nuratu.

Ranar da daddare aka Kai nuratu gidan muh’d dake gomben kafin yatashi komawa aiki su koma tare.

Khadija ma a ranar aka kaiwa ya Umar ita a gidan da mum ta Gina musu tabashi halak malak.

Bayan kwana biyu da ‘daurin aure suka tattaro suka dawo sbd zazza6i da jirin da ayshah ke fama dashi Wanda Deen ya ‘daga hankalinsa Saida suka dawo.

Koda suka dawo jikin baiyi wani sauqiba sati na zagayowa suka wuce Paris inda acan sukaga Dr aka sanardasu cikine ajikinta.

Tun kafin su mum suzo yabuga ya sanar dasu Nan aka tayasa farin ciki.

Tunda cikin ya tabbata yahata sakat kullum Yana maqale da ita idan ya ‘dan matsa daga jikinta to mahmud is at home duk da dai mahmud ‘din shima duk da Yana yaro yasan daddynsa loves his mummy so much.

Saida aurensu Umar yayi wata biyu kafin suka iso Paris inda nanma part ‘daya aka ware Masa shida Khadijarsa.

Lokacinda cikinta ya tsufa lokacin ba laifi khadija tafara samun lafiya Dan tuni ta daina wani hauka saidai can ba’a rasaba.

Wannan karon batasha wuyaba kaman na Mahmud ta haifi baby girl ‘dinta Deen Zak tana ganinta ta turo baki tareda harararsa tace,

Deen Allah kana qwaruwana fa bayan mahmud and now my sweet princess too.

Dariya yayi tareda jawota jikinsa Yana kashe Mata one eye yace,

Karki damu dakinyi 40days Zan baki wani….

Bai qarasaba tace,

Mum kinjisa ko?ko fita asibiti daga haihuwa banyiba yanamin maganar new b….

Toshe Mata baki yayi Yana qunshe dariya sbd ganin ta manta zata fa’dawa mum…

Murmushi mum tayi tana girgixa Kai tareda miqawa Umar babyn ya kar6a Yana murmushi.

Mahmud dayaga babyn da sauri yadawo kusada dadynsa yace,

Daddy mummy karta koma gida yau tabari gobe tasake bamu wani new baby like this one ko daddy.

Hannu yabasa cikin dariya yace,

Yes my boy you’re right.

Harara tabisu da ita tareda kallon mum a shagwa6e tace,

Mum kingani ko?

Cup ‘din thick tea mum ta miqa Mata tana cewa,

Just forget them sweetheart and drink your tea muje gida.

Ana saura kwana biyu suna muh’d da nuratu tareda baba alhaji da mama sakina suka iso farin ciki kamar yayi Mata me hakanan tayita kallon nuratu da ‘dan cikinta tana Jin da’di.

Sunan mum yarinyar taci wato _maryam_ suna kiranta da ummi.

Bayan suna kowa ya watse suka cigaba da jegonsu hankali kwance har tsawon wata ha’du kafin ta shirya kar6an mijinta.

Wanka tayi bayan tayiwa ummi wankan ta shiryata,

Turaruka ta fesa na ‘daukar attention kafin ta ‘daure kanta ta sa6a ummi a kafa’da ta nufi bedroom ‘dinsa daga ita Sai towel.

Yana toilet Yana wanka ta kwantarda ummi a gadonta tana tasowa Yana fitowa ya tsaya kallonta harzuwa kan lips ‘dinta dasuka zanu da hot red lipstick ‘din dayakeso.

Murmushi yasaki Yana ‘dauke gira ‘daya.

Zare ribbon ‘din kanta tayi gashinta ya sauko ta kashe Masa Ido ‘daya tareda sakin towel ‘din jikinta.

This girl will kill me””””yafada Yana fixgota jikinsa tareda kaiwa lips ‘dinta da nonuwanta damqar dambu.,,taja numfashi da qarfi cikin Jin da’di kafin suka fa’da gado gaba ‘daya.

*Alhamdulillah*

*Alhamdulillah*

_godiya sosai ga masoyana a duk inda suke_

_godiya sosai ga Kuma masoyan taura biyu aduk inda suke sbd fa’dosu bazai yiyuba hakama Ina godewa group da dama Ina miqa godiyata kuyimin uxuri bazan iya zayyanokuba sbd gajiyar danayi da typing Amma kusani Kuna raina_💋💋💋💋

*Darasin dake ciki Allah yabamu ikon aiki dashi*,

*Kura kuran ciki Allah ya gafarta Mana nida na rubuta daku da kuka karanta*,

*Mugayen ‘dabi’un dake ciki Allah yayi Mana tsari da kariya dasu tareda muguwar qaddara*,3

*Amin*..

Mamuh💋1

_dont forget to follow, vote and comment_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *