TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 4
Kamar saukar aradu haka maganar Dee ya sauka kunnen Hajiya, wacce ta yi ƙaryan zagawa bayi amma ta ɓige da zuwa soro domin ganin wannan saurayi da Baba Anas ke ta zuzutawa, wato wanda aka zaɓa akan Saifullah. “Sanadiyyar abin da ya sami mahaifiya ta, Ni da ke Amatullah kowannan mu za mu iya yin addinin mu, Wallahi babu abin da zai hana ki musuluncinki, ki dubi girman Allah ki amince da aurena… ” Kalaman da ke mata yawo cikin kwakwalwar ta kenan, musammam jin Dee ya ce “Wallahi babu abin da zai hana ki musuluncinki”4 “kenan shi ɗin ba musulmi bane” ta faɗi tana mai toshe bakinta kamar ba ta son wani ya jiyota. Matsar da kunnenta tayi tana so ta jiyo wani abin da zai tabbatar da zarginta. Babu abin da ta jiyo sai shesshekar kukan Amatullah, ta tsaya kusan mintuna uku tana jiran jin abin da za ta ce amma shiru sai kukan da take yi. Hakan ya sa ta juya don ta koma cikin gida jikin ta na rawa tsabagen daukan gulma.5 Amatullah kuwa kuka ne ya ci karfin ta har ta kasa magana. Tausayin kan ta da shi Dee ta ke ji domin kuwa ta san Dee haramtacce ne a gare ta duk kiyayyar ta da Saifullahi. “Amatullah ki bar kuka ki amsa min, za ki aure ni?” Amatullah ta girgiza ma sa kai alamar ah ah. Komawa yayi ya sake zaman dirshen a kasa. Kamar mai rada ya furta “Why?”2 “Saboda TAZARAR DA KE TSAKANINMU” Ta mayar masa cikin yanayin muryar da ya tambaye ta, ba ta gushe ba ta cigaba “Babu aure a tsakanin mu, haramun ne a musulunci, mahaifin ka na da daman auren mahaifiyar ka ko da kuwa ba ta canza addini ba, domin kuwa shi namiji ne, ni kuwa ban da wannan damar, ba zan iya auren ka ba…”3 “Saboda me ya sa? Why? Me ya sa mace ba ta da wannan damar sai namiji?” Ya sake katse ta cikin nuna rashin gamsuwa. “Haka shari”a ta ce, Saboda ita mace rauni gare ta, ba kamar namiji ba…”2 “Ba zan cutar da ke ba Amatullah, ba zan bari a cuce ki ba, na daukar mi ki alkawarin zan kare duk wani hakki na ki a matsayin ki na ƴa mace kuma mata ta…” “Hakkin ubangiji fa? Za ka taya ni kare shi?” Amatullah ce ta katse shi a karo na farko. Shiru yayi yana kallon ta na wasu yan mintina kafin daga bisani ya furta “Har da hakkin ubangiji….”4 Tashi ta yi tsaye ta na mai share hawaye, shima din tashi yayi idanun sa bisa fuskar ta. Kallonsa ta ke cikin yanayinda kwayar idanun ta su ka kasa ɓoye tsananin soyayyar da ta ke ma sa, haka shima haka na shi soyayyar ke bayyane cikin kwayar idanun shi. Cikin sassanyar murya ta ce “Ina so ka fara daga yanzu, ka taya ni kare hakkin ubangiji ta hanyar fita daga cikin rayuwa ta”2 “Amatullah!!! ” Ya furta a hankali amma cikin tashin hankali. Hannu ta daga ma sa “Please…….. don’t make it more difficult for me, addini na ya fiye min duk wata soyayya da na ke ma ka ko ka ke min, idan har yanda ka ce gaskiya ne, stay away from me”2 “Idan kuma na karbi addinin na ki fa?” Baki bude ta tsaya ta na kallon shi domin kuwa tabbas tambayar na sa ya mata bazata, nisawa ta yi, kana ta ce “Idan za ka karɓi addinin ba dan ni ba, ba dan soyayya ta ba, domin soyayyar dan adam abu ne mara tabbas, idan za ka karɓa domin soyayyar Allah da manzon sa, Ni ma na ɗaukar maka alkawari ba zan cuce ka ba, ba zan bari a cuce ka ba, Zan kare duk wani hakki na ka a matsayin ka na miji na….”4 Ta na gama fadin haka ta juya ta fice da sauri. Nan ta bar Dee tsaye kamar mutum mutumi, yayinda zuciyar sa ke radadi, cikin ran sa kuwa fadi ya ke lalle Allah ya jarabce shi da soyayya mafi zafi a rayuwar shi. Hajiya kuwa ko da ta koma kasa zama tayi, magana na cin ta, ko da ta tuna da Karin maganar na da bahaushe kan ce zafi-zafi a kan daki ƙarfe tuni ta aje tsintar shinkafa sai ga ta cikin dakin Baban Sasa “Baba Ka yi min rai ka hakura da haɗin nan” ta ce cikin shesshekar kuka har da majina. Ba Baban Sasa kaɗai ba har Baba Anas da Baba Mahmud da ke zaune tare da mahaifin su sai da su ka kaɗu. “Sadiya na daɗe da sanin kina da hannu a rashin hankalin Saifu, ki fita ido na, yarinyar da bakwa so ai ta samu kamilallan miji mai tarbiyya” Baba Anas ya tare ta. Kallon matarsa yake zuciyar sa na kimtsa masa abubuwa da zai yi amfani wajen yin maganinta da ɗanta. “Baba ka ji wai kamilalle, ina kamala a jikin bamaguje, ni dai Baba ka yi min rai kar ka aura ma ɗana sauran maguzawa ka san zina ce kalar ta su soyayyar” tace tana ƙara sakin kuka mai tsuma rai, gaba ɗaya ta birkita tunaninsu, kallon ta su ke yi don babu wanda yayi tunanin abin da za ta ce kenan. Ganin an tsaya kallonta ne ta sake faɗin “Rantse mata fa yake in sun yi aure za ta cigaba da musuluncinta…”6 STORY CONTINUES BELOW “su da ke falon waje ke da ke madafi ta ina kika jiyo, labe ki ka koma Sadiya? wallahi Sadiya ki fita ido na” Baba Anas ya sake katse ta ji yake kamar ya rufe ta da duka.2 “Mahmuda je ka shigo min da yaron” Baban Sasa ya faɗi zuciyarsa na zubar jini, tare da jin haushin Amatullah a karo na farko, don shi yayi yaƙini Hajiya Sadiya ba za ta taɓa zuwa gabansa tana kuka in ba ta tabbatar da zancen da ta zo da shi ba. Zaman jugum su ka yi kowanne da abin da ke yawo a ransa. Can sai ga Baba Mahmuda ya dawo shi da Baba Salihu mahaifin Amatullah da shigowar sa kenan daga Abuja. Har ƙasa ya tsuguna ya gaida mahaifinsa kafin ya gaida yayansa da matarsa. Yayi mamakin yanayin fuskokinsu amma ya bar ma kansa. “Mahmuda ina yaron?” Baban Sasa ya tambaye shi. “ina fita motar sa na barin layin nan” yace kai tsaye. “wai matashin da na gani a mota? Ina tsayawa yana shiga mota da na ga kamar kuka yake na tsaida shi, mun gaisa a mutunce na ƙara da fadi masa Rayuwa ɗan hakuri ne, kuma bawa baya wuce kaddararsa” Baba Salihu ya faɗi yana gyara zama. “Suriki nane, mijin Amatu da yardan Allah, yan bakin ciki sai dai su mutu” Baba Anas ya faɗi yana hararar matarsa. “Anas!!!” Baban Sasa ya kira da zumar gargaɗi. Shiru ya sake biyo baya kafin ya sanya Hajiya ta shiga ta kirawo Amatullah. Tashi tayi ta fice rana fita ta gyara fuskarta a famfon da ke wajen ta ɗaura alwala sannan ta isa wajen da sauran mata su ke. “Ahayyyeee Allah mun gode maka, ina ka fito islamiyya ina zaki da’awa amma ki rasa masoyi sai bamaguje, ai Auzubillahi ashe duk salon da’awa ne” ta faɗi tana mai kyalkyata dariya. Tun da ta fara magana Amatullah wacce tun shigowar ta ke kokarin ɓoye fuskarta cikin hijabi gudun kar a gane halin da ta ke ciki ta dada shiga cikin tashin hankali, dama fitowarta kenan ganin tunanin da ta ke yi a ɗaki zai iya tarwatsa zuciyarta fara maganar Hajiya ya sa ta ji ina ma bata fito ba. “Amarsu ki je Baba na kira” ta ce tana kallon Amatullah wacce ke tsure kamar wacce ta yi wa sarki ƙarya. Haka ta tashi sumsum ta wuce hawaye na rigarigen saukowa kuncinta. Tana juya baya Hajiya ta shiga bada labarin abin da ta jiyo, nan yan gidan aka shiga tsine ma boko da abin da ke ciki acewarsu bokon da ta zurfafa ne ya sa ta kula bamaguje a matsayin masoyi. Goggo Mairo ta rasa in da za ta sa kanta yadda ta ga hajiya da ta kawo labarin ko wurin ba ta bari ba amma an fara canza labari da ƙara masa gishiri da Magi.3 *** Da Sallama Amatullah ta shiga ɗakin, hawayen da ke zubo mata bai fasa zubowa ba tashin hankalinta ya ƙaru ganin mahaifinta zaune a wajen. “Baba gani” tace bayan ta bi su ɗaya-ɗaya tana gaida su. “Yauwa! Amaryas, ko da yake an ce wannan da zai min kwace ya zo ko” ya faɗi cikin sigar tsokana. Girgiza kai ta shiga yi tana so ta yi magana amma halshenta ya mata nauyi. “Baban Sasa wallahi ban karya alkawarin mu ba, zaɓinka shine zaɓina” ta kokarta ta fadi nan ta saki sabon kuka a wajen, wanda ya taɓa zukatan baban Sasa da baba Anas kaɗai. Mahaifinta da ke wajen ji yayi kamar ya mauje ta yanda take kuka. Su baba zubairu kuwa da su ka shigo bayan fitan Hajiya ma duk takaici ta basu. “Toh shi wancan da ya zo wanene shi?” Baban Sasa ya tambaya a dake. Baya son tausayin ta ya ci galaba akansa. “Dee Yusuf ne” ta ce a can kasan muryarta. “Ba shi ne Saifullahi ke magana ba” cewar Baba zubairu a harzuke. Shiru tayi ta kara sinne kanta. “Wanene shi Dee Yusuf din? Me nene ma’ana Dee ɗin” Mahaifinta ya tambaya cike da addu’ar amsar ta ya karyata Hajiya Sadiya. Don duk yadda ya so ya duba bai hango dalilin da zai sa yarsa mai ilimin addini da kokarin kiyaye dokokin Allah ce da soyayya da wanda ba musulmi ba. “Sec Gen din SRC ne, shi ke mana tutorials din chemistry, past question papers ya kawo min” ta samu kanta da fadi, amma sanin da su ka yi ita ba mai karya bace take su ka ɗago ta. “Dauda yake ko Dahiru” Baba Mahmuda ya faɗi ganin ta kife su akan asalin sunansa.5 “David Yusuf” ta fadi a hankali. Take ɗakin ya kaure da salati, baba hamza ya taso zai kai mata hannu take Baba Anas ya tare shi. “Fisabilillahi karya kuke so ta muku? Bata ɓoye alakar su ba, koyar da su karatu yake, sannan ina ce Saifullahi ya fara kawo zancen Dee din sannan innarsa ce ta fara kawo zancen shi din ba musulmi bane. Haba ku duba mana” Baba Anas ya ce yana kare ta, sauran in banda masifa babu abin da su ke tare da aibata ta. “Babanmu ka duba lamarin nan da kyau, tun kafin a haifi Amatu babu macen da ke daraja ku kamar Mairo, tun da ka ba da ita ga Saifullah ba a taɓa ganin ta da waninsa ba duk da ba a ganta da shi ɗin ba. Duk zamanta a jami’a bincike na ya tabbatar min ba ta fita zancen da wasu ɗalibai ke yi, Babanmu Amatullah ba ta saɓa alkawarin ku ba, kar ka yi mata hukunci akan laifin da ba ta aikata ba” yace yana mai gurfanawa gaban Baban Sasa, hakan ya kara tsinka zuciyar Amatullah tare da ganin rashin kamatan abin da zuciyarta ta aikata na son Dee. “Kai Anas in an yi magana ka dinga kare Mairo da iyalinta kenan, ni ban san me su ka baka ka sha ba, Salihu ka yi magana mana ka yi shiru kana kallon mu” Baba Idris ya faɗi a harzuke. “ni kuwa mai zan ce bayan ku ne iyayenta” Baba Salihu ya ce yana mai mikewa da barin falon. Nan su ka haɗu su na ta masifa tare da aibata karatun ƴa mace da nuna laifin Baba Salihu da ya gagara nuna fushinsa akan abin da yarsa ta aikata. “Baba ba ka ce komi ba” Baba Anas ya ce da Baban Sasa yana mai sunkuyar da kansa. “Amatullah kin ce Alkawarin mu na nan ko” yace yana mai kallon ta cikin tausayawa, kuka take bilhaqqi kamar ranta zai fita. “Ehhhh!” tace tana mai jan majina. “Anas ka amince da bamu ƴarka a matsayin mata” Baban Sasa ya sake fadi yana mai kallon Baba Anas, hakan ya dawo da hankalin sauran da ke falon garesu. “Baba Zaɓinka shine namu ko ƴar Albarka” yace yana kallon Amatullah. Gyaɗa kanta sama tayi, tana mai share hawaye. “Toh ku kawo kawo sadakin Dan ku, gobe bayan sallahn Asuba za’a ɗaura aure, sati mai zuwa kamar yadda nayi alkawari zan sanya ranar tariya a maimakon ranar aure” Baban Sasa yace yana kallon sashin da su Baba Zubairu ke zaune. Da haka ya sallame Amatullah. Cikin sanyin jiki ta ƙarasa ɗakin su, a falo ta zauna amma tana jiyo muryar mahaifinta da goggonta abin da ba ta taɓa ji ba. “me ya sa kike mahaifiya in ƴar ki ba za ta samu Rahma daga gare ki ba? Kin bincike ta kin ji gaskiyar lamarin ko dokin zuciya kawai kika hau? Amanar da na baki kenan” Yace, yana fitowa, ganin da ya mata cikin hawaye ne ya sa ya riko hannunta su ka fita, ko da su ka iso tsakar gida kallon ta yayi ya ga hawaye kawai take yi hakan ya sanya shi sa hannu tare da share hawayen da su ka zubo ma Amatullah. Chan gefen gidan su ka je inda ɗakin kannen Amatullah maza yake, ciro makulli yayi ya bude su ka shiga. Gefen katifa su ka zauna, ya ciro hankici ya bata ta share hawayen da ya take yi sannan ya ce “Amatullah!!!” Ba Ta amsa ba sai ɗago idanunta tayi ta kalle shi. “Faɗa min gaskiyar abin da ke faruwa, na yarda dake, na san ba zaki taɓa manta inda kika fito ba, faɗa min and I will give you 100% support” yace yana riko hannayenta biyu. Nan ta samu ƙwarin gwuiwa ta faɗi masa duk abin da ya faru tun daga farkon haɗuwarta da Dee Yusuf zuwa abin da ya faru zuwan shi.16 “Wani amsa kika bashi bayan ya faɗi miki uzurin sa?” “Idan za ka karbi addinin ba dan ni ba, ba dan soyayya ta ba, domin soyayyar dan adam abu ne mara tabbas, idan za ka karba domin soyayyar Allah da manzon sa, Ni ma na daukar maka alkawari ba zan cuce ka ba, ba zan bari a cuce ka ba, Zan kare duk wani hikki na ka a matsayin ka na miji na….” Amatullah ta maimaitawa mahaifin ta. Kai ya ke girgizawa cike da dana sani “kin san da na shigo aka faɗi min, na ji tsoro a raina saboda ina tsoron kar ace hakkin Binta Sule ne ya kamani” Ya ce cikin sanyin jiki. Kallon sa tayi cikin neman ƙarin haske. Be gushe ba ya cigaba “Ajin mu ɗaya da Binta Sule, duk mun shaida soyayyarta da Yusuf Haɗeja. Muna cikin wainda ke mata kallon tubabbiya, muna da hannu a komawarta Christianity. Amatullah Al’ummar musulmi Hausawa na da wannan nakasun, ni ma a lokacin ina da ita. Kwanakin baya mun haɗu a taron yan jarida, na yi kokarin neman gafaranta amma tace min abin da mu ka Aikata ya zama mata gobarar titi a jos” Numfashi ya sha cikin dana sani ya cigaba da fadin “Ta so MSS su kula da ita, ta so zama cikin musulunci amma alakar da muka nuna mata mai rauni ce, da shi wannan David din na ki zai karbi musulunci ko shakka babu ni mahaifin ki zan ba ku kowacce gudunmawa, duk da dai zan fi so ki auri dan uwan ki wanda ya ke tsatson ki…” Shigowa ya yi don amsar abincin dare duk da hakan ba al’adarsa bace amma yanayin da yake ciki ya isa ya hana masa cin abin da yafi soyuwa a gare shi da dare. Har yayi hanyar ɗakin gwaggo Mairo kamar yadda ya saba sai ya canza don baya fatan abin da zai haɗa shi da bagidajiyar yarinyar nan, ya ayyana a ransa.2 “Amma dai an yi sakarai wahalalle ya rasa wacce zai ci burin sakawa a motar nan sai bagidajiyar yarinyar nan” ya fadi ya na mai dafa bango jin wani abu ya tokare shi a ƙirji. “2008 Suzuki SX4 ce fa” ya faɗi tunawa da cewa a ƙarshen shekarar da ta gabata a ka fitar da motar, yayi maitan mallakar ta amma shi a karan kanshi ya san motar ta girmi duk wani ahlin gidan Jamoh a wannan lokacin, sai gashi wacce ya fi gani a kaskantaciya da bai yi tunanin mamallakin keke zai kalle ta da soyayya ba mamallakin dream car dinsa ya zo afujajajan idanunsa dauke da tsantsan soyayya gareta.10 Sai da ya kwashe kusan mintuna goma sha biyar yana maida numfarfashi da tattaro natsuwa kafin ya karasa cikin ɗakin mahaifiyar sa . “Ku tashi ku bamu wuri” hajiya ta faɗi ma kannensa ganin suna zaune ba mai shirin fita duk da ba wai don sun saba fita bane in ya shigo ɗakin. “Saki Ranka yayansu, ashe yaron nan da Amatullah ke so arne ne, in faɗa maka ina ji na yi wuf na iske baban Sasa na faɗa masa” tace cikin raɗa, fuskar ta cike da annuri, rasa me zai ce mata yayi, ya rasa yanayin da ya tsinci kansa haka yake kallonta sheƙeƙe bai ga ta in da tayi gwaninta ba balle ta birge shi.3 “Kin ga matsalar shegiyar al’adar nan taku ta banza wai kunyar ɗan fari ko, ni na ce miki ina son Amatullah da har za ki taya ni kishi” ya ce yana kokarin saita fushi da ya ji yana taso masa da ga kasan zuciya. ‘watau ba ma musulmi bane balle a ce shima ustaz ne yana son ustaziyya’ zuciyar sa ta dinga nanata masa. “Na ga dai duk gidan nan babu wacce ta kamo kafafunta ne a haɗuwa boko da islamiyya, in ka aureta zan tabbata na zarce duk wata mace a gidan nan” ta katse masa tunani, magana take ƙasa-ƙasa gudun fitar da wani gun, duk da ta san ana faɗin bango na da kunnuwa. “A tunanin ki hajja zan auri wacce ta taso a cikin manyan biranen ƙasar nan ne balle kuma wacce ta taso a cikin zaria, matan da ba su san komi ba sai lulluɓe jiki kamar sauran kuturta. Hajja ki min jagora kar a aura min bagidajiyar can, zan auro miki wacce ta haɗu, wacce duk ta wuce sai an saki baki an bi ta da idanu, ki amince min Hajja” ya ƙarasa rauni cike da muryarsa, shiru ta yi ta lula mafarkin ido biyu, babu abin da ta ke hangowa sai surukar da sanadin ta za ta dinga zuwa haji duk shekara.11 “Amma kuma mahaifin ka fa? Ɗazu fa kiris ya kwaɗe ni gaban su Baban Sasa” tace sa’ilin da ta tuna babu wanda zai kawo masu cikas sama da shi.2 “Hajja matarsa fa kike, kiyi amfani da damar nan” yace mata kai tsaye. Tunawa da tayi da Madina, kanwar mijinta kuma aminiyarta wacce ba ta san wa yafi tsanar Goggo Mairo ba cikin su biyun. “Zan nemi madina gobe inshaAllah, duk abin da ake ciki za ka ji” da haka su ka yi sallama, ya wuce ɗakin sa ya rufe, baya ko fatan abin da zai sa ya haɗu da mahaifinsu hakan ya sa ya kuduri niyyar ba zai fita sallan asuba ba.6 *** Kwance ya ke bisa gadon sa, duk yadda ya so ya cire tunanin Amatullah da maganganun da su ka yi abin ya gagara. Hamza yayi kokarin jan shi su fita amma hakan ya ci tura, rokan sa yayi da dan Allah ya rabu da shi sam ba ya jin dadi dan haka ba ya san damuwa. Sanye ya ke cikin farin singileti da gajeran wando. Tun yana juye-juye har ya tashi yana mai lalubar wayar shi da tun dawowar shi daga wajan Amatullah ta ke kashe. Kunna wayar yayi, idanun sa kan fuskar wayar in da agogon kan wayar ya nuna karfe goma sha daya da rabi na dare, lalle ya daɗe kwance domin kuwa Allah kaɗai ya san awanni nawa ya ɗauka nan kwance. Ba tare da ta san abin da ya ke ba ya tsinci kan sa ya na mai danna number Amatullah, ta yi ringing har ta katse ba ta ɗaga ba. Ajiyar zuciya ya saki, yayin da ya furta STORY CONTINUES BELOW “Oh lord I’m so confused I’m going crazy!!” Number Mahaifiyar shi ya shiga kira ba tare da yayi la’akari da lokaci ba, har sai da wayar ta kusa tsinkewa sai gashi ta daga a tsorace ta furta “Dan albarka lafiya kuwa ka kira cikin dare haka?”2 “Mummy……….” Dee ya amsa mata yayin da ya nemi abincewa ya rasa. Jin haka Mahaifiyar shi wacce wayar Dee din ne ya tashe ta daga bacci, tashi ta yi gudun kar ta tayar da mijin ta daga bacci. Sai da ta koma falo ta sami waje ta zauna sannan ta ce “Owk David, yanzu ina jin ka, me ke faruwa? Ba ka da lafiya ne?” “Lafiya lau Mommy, kawai dama na kasa bacci ne…..” “No David, na san ka kamar yunwar ciki na, hakan nan dan ka kasa bacci ba zai sa ka kira ni cikin dare haka ba, me ya faru my baby?”2 Ta katse shi ta na maganar ne cikin nuna damuwa. Numfashi ya sauke sannan ya furta “Mommy idan har addinin musulunci ya yarda namiji musulmi ya auri mace Christain ko da kuwa ba ta musulunta ba, me ya sa kika musulunta?” Shiru ne ya biyo baya, domin kuwa tambayar da Dee ya mata ya zo mata a bazata, har yayi tunanin wayar ya katse, ya sake furta “Hello Mummy? Hello?” “Yes Son, I can hear you….well kyawawan halin mahaifin ka da kaunar da na ke ma sa ya sanya na ga hasken da ke cikin addinin sa, ya sa min kwaɗayin shiga addidnin, duk da ya ce zan iya addini na ba tare da mun bari dangin sa sun sani ba. Your Father was very kind, da haka duka musulmai su ke da har yanzu ban bar musulunci ba” Ta amsa masa ta na mai jin dacin rashin mahaifin Dee da har yanzu be bar zuciyar ta ba. Jin Dee yayi shiru ta kara fadin2 “Oya it’s your time to answer me now, me ya sa ka ke min wannan tambayar? Na san hakan nan baza ka kira ni cikin dare ka na min wannan tambayar ba tare da wani dalili ba, so tell me what is going on, I mean tell me everything kar ka ɓoye min komi” Shiru Dee yayi yana mai muhawara cikin zuciyar shi na fada mata ko rashin fada mata. “David……” “Na’am Mummy” “Start talking, your Mommy is here for you” Cikin sassanyar murya ya furta “Mummy Amatullah ce……” Sai kuma yayi shiru, ya kasa cigabawa. Cikin bashi karfin gwiwa ta ce “Ina Jin ka, wacece Amatullah? A ina ta ke? Wani irin dangantaka ce a tsakanin ku? Me ya faru?” Tambayar da Mahaifiyar ta jero ma sa ne ya sanya Dee bude mata cikin sa, tun daga haduwar shi da Amatullah har izuwa ranar yau in da ya je gidan su Amatullah. Ya kare maganar ne da “Wallahi Mummy ina kaunar Amatullah, babu abin da ba zan iya yi ba a dalilin ta, ko da kuwa hakan na nufin zuwa Hadejia ne….ki taimaka min Mummy…..” “David ka san me ka ke faɗi kuwa? Ka na tunanin dangin mahaifin ka za su karɓe ka ne after all this years? Ka na jinjiri, innocent child ba su karɓe ka ba sai yanzun da ka zama saurayi ka tashi cikin addinin da ba na su ba? Ka na tunanin za su karbe ka ne ka na Christain? “2 Cewar Mummy cikin nuna bacin rai Jin Dee na zancen zuwa Hadejia, dan kuwa idan akwai wainda ta tsana su na bayan dangin mahaifin Dee. Ga mamakin ta sai ji ta yi ya ce “Mummy in dai zuwa Haɗeja gun dangin baba na shi zai sa su yarda su nema min auren Amatullah, Mummy zan yi, ko da kuwa za su min korar kare……” Shiru Mummy ta yi na ɗan wani lokaci, daga bisani ta furta ” Oh Lord Jesus! This is history repeating itself!!!” “Mummy please understand me, Ina son Amatullah, ban taba son kowace ɗiya mace ba kamar yanda na ke son Amatullah…” STORY CONTINUES BELOW “Ita Amatullah ta na son ka ne? Ya za ka yi da tazarar da ke tsakanin ku? Shin kana tunanin iyayen ta za su yarda su aura ma ka ita ka na Christain? Ko ba ka san addidinin su ya hana ba?” Mummy ce ke maganar cikin faɗa -faɗa. Shi kuwa Dee daɗa sassauta murya yayi kamar ya na gaban ta ya ce ” Mummy na sani, I mean ta fada min a addidinin su haramun ne mace Musulma ta auri Christain, Amma idan na musulunta shikenan…….” “Za ka musulunta ne David saboda yarinya da soyayya? Shin rayuwata ba zai zame ma ka makaranta ba David?” “Mummy….. please try to understand me, please!” Ya faɗa cikin rauni. Shirun da Mummy ta yi ba karamin tayar ma sa da hankali yayi ba. Idanunsa na fitar da hawaye ya furta “It’s not just about Amatullah kawai, har da mahaifina wanda ki ke kauna har gobe, da kyawawan halin sa da ya kwaɗaita mi ki son shiga musulunci, Mummy ina laifi idan ɗa yana so ya gaji uban sa? Ina laifi dan ina son kasancewa kamar mahaifi na……..?”2 “David…….” Mummy ta yi kokarin katse shi, Dee wanda ke gudun jin abin da za ta ce ya tari numfashin ta “Mummy kasancewa na musulmi zai zama abin alfahari ga mahaifina, abin kaunar ki…..kar ki manta addinin musulunci addidinin shi ne, please Mummy understand me….” ” I understand David, na fihimce ka, you have my blessings son today and always addini ba zai taba zama tazara a tsakanin mu ba, a Musulmi ko Christain you will always be my blood and flesh”6 Cike da murna wanda ya ke bayyane cikin muryar sa ya ce ” Na gode Mummy, na gode, I love you so much” Tana murmushi ta amsa da “I love you more son, but David?” “Na’am Mummy” “Shin ka faɗa mata za ka musulunta? Ita Amatullah ɗin ta ka? Ka ga ka ce ana shirin ɗaura mata ɗan uwan ta nan da one week, kar fa ka makara”2 Nan gaban shi ya faɗi, yana ɗan sosa kyeya ya ce “Ah ah Mummy ban faɗa mata ba, dama I wanted to tell you first, bari in je faɗa mata yanzu…..” “Toh Alhaji ɗan gidan Yusuf, ka duba agogo ka ga lokaci kuwa? Sha biyu ya wuce fa, gidan mutane za ka je mu su da wannan daren?” Cewar Mummy ta cike da fara’a. Shi ma ɗin dariya ya ke, har ran sa da zai samu dama babu abinda zai hana shi zuwa gun Amatullah domin yi mata wannan kyakkyawan albishir ɗin. A zahiri kuwa cewa yayi “Toh da asuba kuwa zan je, ana buɗe kofar gidan su Amatullah za su ganni bakin kofa domin ta san cewa I mean business, I love her Mummy”5 “I know right, I hope she loves you too son, Allah ya mu ku albarka ka ji dan albarka?” “Ameeen, you’re best, thank you”2 Da wannan su ka yi sallama. Ciwon rashin masoyin ta ne ya tashi, Nan ta zauna ta na mai zubda hawaye domin kuwa mahaifin Dee ya so ta, soyayyar da har yau ba ta sami irin shi ba, ya tararraye ya ta kuma ya kare hakkin ta, ya kance da ita yana yi mata hakan ne domin cika hakkokin ubangiji, haka addinin shi ya koyar. Ina ma ace mutuwa ba ta raba su ba. Dee kuwa yanda ya ga rana haka ya ga dare dan kuwa ya nemi bacci ya rasa, Allah Allah ya ke Allah ya wayi gari ya ga Amatullah. Haka ita ma Amatullah wacce tun rabuwar ta da mahaifin ta ta shiga yanayi mai wuyar fasaltuwa, ta nemi bacci ta rasa akan dalilin da ita kan ta ba ta sani ba. Kawai dai gaban ta na faduwa da wani tashin hankali da tsinci kan ta ciki, haka har aka fara kiraye kirayen Sallar asuba sannan bacci ya fara sace ta. *** A cikin masallaci bayan an idar da sallar asubahi, Baban Sasa wanda tunda su Baba Anas su ka ga ya fito sallar asuba su ka san ta faru ta kare ramamme ya zagi maye, ya matsa kusa da liman ya ce da shi “Allah gafarta Malam akwai auren da mu ke so a daura a yau, tsakanin jikoki na biyu, dan wajan Anas da diyar Salihu….kai Ina Saifullahin ma ya ke?” Ya tambaya ya na mai wage wage.5 “Ina ga fa yau be sami damar fitowa ba ko kuma masallacin bayan layi da ya fara zuwa ya je” Baba Anas ne ya bashi amsa, shi kuwa Baba Salihu da ya san halin da ƴar sa ke ciki na game da auren Saifullahi ne ya sa jikin sa yin sanyi dan kuwa dai be yi tunanin Baba Sasa da gaske ya ke zai daura auren a yau ba sai yanzu da ya ga zahiri. “Ah toh madallah, ai sai a ɗaura me za a jira in dai akwai waliyai, shedu da sadaki?” Cewar liman yana mai baza babbar riga. Ba tare da ya damu da rashin Saifullahi a wajan ba sai ga Baban Sasa ya fito da kudi daga aljihun rigar sa, ka na ya mika ma Baba Zubairu ya ce “Amshi nan Zubairu, kudi ne dubu hamsin sadakin dan ka ne, kai na umurta ka zama wakilin Saifullah, Ni kuma ni zan kasance waliyi ga Amatullah, kai yaro yaka nan shiga gida, ɗaki na za ka ga alawa da goro maza kwaso su nan….” Da saurin yaron da aka aika ya tashi ya fita, nan aka fara shirin daurin aure, inda Baba Anas da Baba Salihu su ka zama yan kallo.2 ***** Tun kafin a idar da sallar asuba Dee ya shiga wanka. Ana idarwa shi ma din yana fitowa daga wanka a gurguje ya shirya cikin shadda brown dinkin jamfa. Alkawarin doka sammako zuwa gidan su Amatullah din da ya dauka na gaske ne. Domin kuwa yau da shi za a bude gidan. Kasancewar Hamza baya nan tun jiya da ya fita be dawowa ba, yaci sa’ar fita ba tare da ya sha tambayoyi ba, yanda ya sha hula da turare kai ka ce ango haka ya shiga motar sa cike da nishadi ya nufi gidan su Amatullah.7 **** An ɗaura aure an shafa fatiha in da Amatullah ta tabbata matar Saifullahi. Cikin wanda su ka shaida ɗaurin auren, In aka dauke Mahaifan ma’auratan biyu wato Baba Anas da Baba Salihu babu wanda abin bai masa dadi ba, musamman Baban Sasa wanda zama yayi dirshen cikin masallacin ya na raba alewa da goro cike da jin dadi. Lokacin da Dee ya sami isowa gari yayi haske, haka kuma yayi mamakin ganin kofar gidan su Amatullah a bude. Ya na mai tunanin kila sammako su ke yi wajen buɗe gidan ya sami gefe ya faka, sannan ya fito ya tsaya kofar gidan ya na shawarar kiran Amatullah ko kuwa dai ya jira gari ya daɗa wayewa. Ganin fitowar Baban Sasa daga masallaci hannun sa rike da sauran alawa da goran da ya rage, tare da su Baba Anas sun nufo gidan yayinda jama’a wanda su ka shaida auren da kuma wanda su ka ji labari daga baya ya sanya Dee ɗan ja da baya ya koma jikin motar shi. Kamar yanda ya kula da su haka suma su ka lura da shi, musammam Baba Anas wanda ko cikin bacci zai gane shi, shi kuwa Mahaifin Amatullah kallon sa ya ke ya na mai mamakin kamannin sa da marigayi wato Mahaifin Dee Yusuf Haɗeja. Ko da su ka isa kofar gidan sai Baban Sasa ya tsaya yana mai tsurawa Dee ido, ganin haka suma kawun nan nata tsayawa su ka yi, su ma din Idanun su kan Dee din ya ke. Cike da fargaba Dee ya ƙarasa gaban su har kasa ya durkusa cikin girmamawa ya shiga gaishe su.2 “Yaro daga ina? ” Baban Sasa ya tambaya. Cike da jin nauyi Dee ya ce “Dama na zo ne….” Sai kuma yayi shiru, ya kasa magana. “Ka zo me?” Baban Sasa ya sake tambaya. Jin shirun yayi yawa Dee ya kasa magana Baba Anas ya ce “Shi ne wanda ya zo neman Amatullah jiya” “Auho kai ne Dee Yusuf din da na ke ji gurin jikata?” Jin Baban Sasa ya kira sunan sa ya sanya Dee jin dadi har cikin ran sa, wato har iyaye da kakannin Amatullah sun san da zaman shi. Ya na mai murmushi ya ce “Eh ni ne Dee Yusuf” “Kai ne kirista da ke kokarin hurewa jikata kunne, ka ke kokarin ruguza tarbiyar da mu ka bata ta hanyar sauya mata addini da dabi’a ko? “2 Tambayar Baban Sasa ba karamin tayar da hankali Dee ya yi ba, in da ya dago kai da sauri ya na mai fadin “Wa’iyazubillah!!! Afuwan Baba, amma dai ina ga an sami rashin fahimta ne, ko kusa ban taba tunanin aiwata haka ba, na zo ne a yau domin shaidawa Amatullah zan karbi addinin musulunci, ta kuma shige min gaba domin shaidawa iyayen ta, ina mai neman izinin turo iyaye na neman auren ta…….”4 “Kai tafi can rufewa mutane baki!!!” Cewar Baban Sasa cikin tsawa da tsangwama, yayinda Baba Salihu ya runtse idanun sa cike da tausayin Dee da ya rufe shi. Baban Sasa be gushe ba ya cigaba da fadin8 “Ku ji fa dan Allah yana kirista shekara da shekaru kawai an wayi gari wai ya zo wajan mu karbar musulunci da ke ka mayar da mu shashashe irin ka! Mu za ka zo ka yaudara? Toh ka ruke tubar ka ka kai can ba dai gare mu ba! Ahir din ka! Jika ta dai na aurar da ita ga jika na musulmi dan musulmai!!”7 Jin maganar ya ke tana shigar sa kamar kibiya tsabagen ciwo, hawayen da shi kan sa bai san da zubar su ba ke gangarowa daga idanun sa yayinda ya dukar da kan sa kasa. Baba Anas wanda shi kan shi maganar Baban Sasa ya masa tsauri girgiza kai ya shiga yi, Jan hannun Baban Sasa cikin dabara tare da faɗin+ “Baba ai ina ga zai fi kyau ka ɗan shiga ciki ka huta, ka jima a waje” Cikin cijewa yayin da Baba Anas ke jan sa be fasa faɗin “Ai to ka bari Anas na yi masa wankin babban riga, ɗan tselan uwa, ta Allah ba taka ba, jika ta dai na maka katangar karfe da ita…..” “Baba faɗa ba naka bane tun da TAZARAR da ke tsaƙaninsu ya ƙara ƙarfafa” Baba Anas ya ce yana jan Baban Sasa zuwa cikin gida. Su Baba Zubairu ma baya su ka rufawa Baban Sasa, mahaifin Amatullah ne kaɗai ya rage tsaye gaban Dee wanda ya sunkuyar da kai kamar an ajiye dutse.6 Cikin sassanyar murya Baba Salihu ya “Ban san da wani ido zan kalle ka ba, ban san da wani baki zan baka hakuri ba, ni mahaifin Amatullah na so ka da ɗiyata, ko ba don komai ba ko don kuskuren da na aikata dangane da Mahaifiyar ka a baya…..” Yanda yaga Dee ya ɗago kanshi a karo na farko su ka haɗa idanu, da yanda ya ga idanun sa sun kaɗa sun yi jajur ya sanya Baba Salihu shanye maganar sa, kana daga bisani ya furta “Allahu akbar Allah ya jikan Yusuf da rahama, babu shakka kai jinin sa ne, ina mai fatan za ka yafe mana a karo na biyu Yusuf” Yana gama faɗin haka shima ciki ya shige cike da danasani, dan kuwa da ya taimakawa Mahaifiyar Dee da ya girma cikin musulunci. Allah kaɗai ya san tsahon mintocin da yayi nan tsugunne, har sai da jama’a su ka fara taruwa suna tambayar lafiya? Sannan ya tashi da kyar ya na mai goge hawayen da suka rufe fuskar shi. Har ya karasa ga motar shi kafin ya juya ya kalli kofar gidan su Amatullah, gani ya ke kamar za ta fito ta ce duk ba gaske ba ne, ganin babu ita babu alamar ta ya sanya shi buɗe motar, ya shiga ya zauna, Amma kunna motar ya gagare shi5 “Amatullah shikenan yanzu na rasa ki?”3 Cewar Dee ya na mai kifa kan sa bisa sitiyari yayin da maganganun Baban Sasa ke masa yawo cikin kwakwalwar kan sa. “Amatullah….. Amatullah………” Amatullah kuwa tana cikin tilawa saƙon ɗaurin aurenta ya isa kunnuwanta, ba ta yanke da karatun ba cigaba ta yi tana mai godiya ga Allah ba don tana son auren ba amma don ta san aure wata dama ce da Allah ya ke ba wanda ya so, ba wayon mutum ba dabararsa ke sanya ya yi aure a duniya ba, sannan matukar lokacin mutum yayi to babu shakka za a ɗaura ga kuma mijin da Allah ya riga ya tsara. Shigowar Mahaifinta ne ya sanya ta kasa kunne Jin ya na magana da Gwaggo, ya na mai rokan Allah kariya daga dukkan sharri a gidan auren Amatullah. “Mairo na so a ce yaron nan ya iso kafin a ɗaura auren nan, wallahi sai dai a yi duk abin da za ayi shi zan ba Amatullah.” Amatullah ta tsinkayo mahaifinta na faɗi, ajiye Qur’anin tayi don jin wani yaro babanta ke magana akai. “Wa kenan baban Hafiz?” ta tambaya a sanyaye don za ta iya rantsuwa ta dade ba ta ga mijinta cikin tashin hankalin nan ba. “Wancan da Amatullah ke so” ya faɗi kai tsaye. “Wanda Hajiya tace bamaguje ne?” ta ce a ɗan firgice. “Ahlil kitaab ne, ya zo da shahadar sa a zuci so kawai yake a sanya masa a laɓɓansa amma ya zo an riga da an ɗaura auren Amatullah.” Amatullah tana jiyo tausayi da buri a cikin muryar mahaifinta. ‘Dee Yusuf ya zo don ya musulunta’ ta faɗi a cikin zuciyarta tana mai jin wasu zafafen hawaye suna gangarowa kuncinta. ” Baban Hafiz mu kaddara hakan ne Alkhairi, ka manta duk wani abin dai auku a rubuce yake, Allah da kansa ya faɗi a zancensa mafi gaskiya LIKULLI AJALIN KITAAB” tace muryarta a sanyaye, Amatullah ba ta iya jin sauran zantuttukan iyayenta ba ta tashi ta jiki na rawa ta fice waje, jama’ar gidan na amarya amarya amma ina hankalin ta yayi waje domin kuwa ba ta da buri da ya wuce kanin Dee Yusuf ko da kuwa shine gani na karshe da za ta ma sa a rayuwar ta. Sai da ta ganin motar ya dauke ma ta, sannan ta juya a hankali kamar wacce kwai ya fashewa ta shige gida. Dakin ta ta koma tana mai kuka kamar ranta zai fita, shike nan Tazarar da ke tsakanin su ya tabbata, shike nan za ta rayu da wanda ya fi kowa ganin ta a matsayin kaskantaciyar halitta. Tunanin da su ka dinga tunzura kokenta kenan. Fadi ta ke “Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun, Ni Amatullah na rasa masoyi!!!” ***2 STORY CONTINUES BELOW Baban Sasa kuwa ɗakinsa Baba Anas ya wuce da shi, nan ɗin ma baki ya dinga bashi yana mai koɗa haɗin da yayi wanda hakan ya zama ruwan da ya dinga wanke zuciyar Baban Sasa da ganin Dee yusuf ya sanya shi cunkushewa kamar tuƙuƙin hayaƙi. “Anas a ce Arne har ya ga fuskar da zai ce yana son ta, shi yasa na tsani bokon ƴa mace” Baban Sasa ya nisa ya faɗi, sai da baba Anas ya ɗauki wasu yan daƙiƙai kafin ya ce “Ka san Arne da tsaurin ido, dama an ce su kan janye yayanmu cikin hilla da kyautatawa. Amma ni ban shakkar Amatullah ko da na daƙiƙa ne, Allah ya albarkaci Auren nan nasu, Baba ba zan iya kwatanta farin cikin da nake ciki ba. Allah ya saka da Alkhairi” murmushi Baban Sasa ya yi cike da farin ciki da alfahari da abin da ya yi. Nan Baba Anas ya zauna su baba Zubairu su ka shigo su ka dasa hira, ba su suka bar ɗakin ba sai da baban Sasa ya fara gyangyaɗi bayan ya sha maganinsa na safe. Ba su yi mamakin ganin yanda mata su ka cika gidan ba saboda mafi akasarin su na yan tsakankanin Amaru ne.2 Farin cikin da ke tattare da muryar Baba Anas yayin da yayi sallama a ɗakin matarsa ƙadai ya isa ya fassara tarin farin cikin da yake ciki. “Wai ni kam Alhaji Anas wannan farin ciki duk akan samun kwancen surika ne” Madina ta tambaya tana wani yamutsa fuska. “aikuwa ke ma kya faɗi a ce mutum Sam bai san abin da ya kamata ba” Hajiya ta amshe tana ƙarasawa da ƙaramin tsaki. “Ohhh toh ni ban fahimci in da kuka sa gaba ba, ke madina abin kunya ne ma a ji zancen nan daga bakinki, in ita sadiya karere ce a gidan nan ke kuma fa? Nono ɗaya kuka sha fa da mahaifin yarinyar nan” yace yana gimtse fuska. “Toh ni dai ban ga mai Mairo ta tsinana a gidan nan ba in banda raba tsakaninmu da iyayenmu, sannan shi Salihun da kake magana sai naga ɗan uba ne a gareka, har wani cancanta yayi ka sayar da farin cikin ɗanka akan tashi ɗiyar, wacce Allah kaɗai ya san abin da ta shuka a jami’a” Madina ta faɗi cike da bakin ciki da takaicin yayanta, shirun da yayi ya sanya su tunanin cin galaba akan tunaninsa, na hajiya ta ɗaura ” ai in za a ci kwaɗo ai gara a ci me mai. Shi yayan nasu ma ya riga ya shirya da wata tun a can Turan. Yar babban gida wacce ko ba komi mun san ba hayen boko ta yi ba” tace, cike da alfahari don tun jiya ta kwana da mafarkin suruka yar baban gida da za ta zama silar komawar ta haji ba ma sau ɗaya ba duk shekara. Shiru yayi yana kallon sa suna magana wanda duk akan kushe Amatullah ne da mahaifiyarta da kuma ƙawata masa zaɓin Saifullah. “Madina ki zama shaida, Duk abin da ya sami auren Amatullah kwatankwacin sa ne akan Sadiya. In kun ga dama ku sanya shi ya yaƙice auren” yace bayan ya gaji da jin kalamansu, bai jira sun farfaɗo daga kaɗuwar da su ka yi ba ya sa kai ya fice daga ɗakin. 9 *** “Wai ko yau baban Sasa ya rasu zai rasu da cikar burinsa, aure da subahi sai kace ana neman kai” maganar da ya daki kunnen Saifullah kenan ya yi saurin tashi daga kwance ya zauna don tabbas in ba ƙarya kunnensa ke masa ba muryar Shahid ne Dan wajen baba Mahmouda. “Kai dai bari, ai Saifullah yayi mugun dace, ina ma ni ne aka ma wannan alkawarin, kana ji murya kamar ana busa sarewa, wani abin ma hmmmn ba a ko magana wallahi Amatullah ne ake kira da wife material” abokin hirar Shahid ya faɗi wanda muryar sa ta faɗi ma Saifullah Yasir ne ɗan Baba Zubairu. “Yaya Yasir bari anty Amina ta jiyo ka, kasan kishin ta babu part 2” Shahid ya faɗi cike da shaƙiyanci. Saifullah bai ji amsar da Yasir din ya bada ba saboda yawo da kalamansu na fari ke yi a kwakwalwarsa. Bai san lokacin da ya miƙe ya ja jikinsa zuwa ɗakin Baban Sasa ba, yana isa ya iske shi yana bacci bai tuna da halin da yake ciki na ciwo da tsufa ba ya fara magana yana jijjiga shi. “Why Baban Sasa, me yasa za ka min haka, ka aura min wanda duk duniya na tsana, bagidajiya, baƙauyiya wacce ba ta san kanta ba, why Baban Sasa” yace yana kuka shaɓe-shaɓe kamar ransa zai fita. Kamar a mafarki Baban Sasa ya ji kalaman nan, a hankali ya bude idonu ya ke kallan Saifullahi. “Baba ko mace an hana a mata auren dole balle ni namiji, auren dolen ma ga bagidajiya irin Amatullah” ya sake faɗi yana girgiza kanshi alamun shi kanshi bai yarda ba. Kallo mai cike da firgici Baban Sasa ke masa, shi bai taɓa tunanin Saifullahi baya so ba duk kuwa da a lokacin ya dinga taro duk abubuwan da su ka gudana. Take tausayin Amatullah ya cika shi, yana mai tuna tsantsan soyayyar da ya gani a idanun Dee Yusuf yana mai jin haushin abin da ya aikata masa. “Bagidajiya ce bana sonta, aurenta abin kunya ne a gare ni Baba, ka taimaka min” saifu ya faɗi yayin da ya hango ta cikin hijabinta da safa a ƙafa da hannu. Faɗin irin mamakin da Baban Sasa ya shiga ba zai misaltu ba, zufa yake yi yana kallon jikan da yake masa kallon gudaliya wajen kauna, wanda duk inda ya zauna zai ba da shedar irin biyayyar Saifullah gare shi amma shi ne zaune yana masa ɗibar albarka akan abin da bacci ya ɗauke shi yana mai alfaharin aikatawa. Shirun baban Sasa ne ya sanya Saif ɗaga ido ya kalle shi, sai a lokacin ya dawo cikin hankalinsa ya tuna gaban wanda ya ke, ya tuna duk wani shirin sa ba zai yi tasiri ba matukar bai goge abin da ya aikata ba. “April Fool!!!” ya samu kansa da faɗi yana mai kirkiro murmushi da kuma rungumar Baban Sasa da ya zauna kamar mutum-mutumin da aka danka. “Baba Nagode da wannan kyauta, cikin bacci na ji su Shahid na maganar baka ji farin cikin da na shiga ba, amma na ce bari in dan ɗanaka duk da dannen kirji yaci in maka” ya faɗi yana mai rike hannun baban Sasa kamar wanda ke tsantsan farin ciki. Shi dai baban Sasa zaune yake yana mai cike da waswasi don in ba ƙarya idanunsa ke masa ba toh tabbas Saifullah a haukace ya shigo ɗakin babu wani zancen wanawa. “Ka san halin da na shiga da tace min wani Danliti ta ke so, Nagode Allah mai kyauta mai ƙari, na gode Baban Sasa ina mai farin cikin kasancewa tsatsonka. Na maka alkawari zan riƙe maka Amatullah fiye da yanda kake tsammani” ya faɗi cikin farin ciki tsantsa wanda gaba ɗaya na abin da zuciyar sa ta raɗa masa ne akan zai iya aikatawa ga Amatullah. Baban Sasa bai iya cewa komi ba don kaɗuwar da yayi tun farko, shafa kan Saifullah ya shiga yi yana murmushi da addu’ar Allah ya kauda idon makiya da shaiɗanu a auren su.