TAZARAR DAKE TSAKANINMU CHAPTER 9
Cikin iko na Ubangiji da taimakon wata malamarsu Dr. Mu’azatu Usman El-Yakub ta samu tayi differing semester ɗin nata, hakan ya sanya ta daina fita makaranta.3 Cikinta kullum girma ya ke ƙarawa yayin da motsinsa ta zama mata abokin hira abokin ɗebe kewa. Idan ya motsa har shafo shi take cike da ƙauna ta ce “Ubangiji Allah ya nisanta ka da mummunar halin mahaifin ka” wani lokaci kuma ta shagala wajen ba shi labarin duniya.4 “ka ga rayuwar duniya da daɗi amma cike yake da ƙalubale, kar ka damu ina son ka, ba zan taɓa juya maka baya ba, come sun come rain” ire-iren hirarrakin da ta ke yi da ɗan Cikinta kenan. Wani lokaci ta bashi jinsin mace wani lokaci na namiji.4 Banda pad, zaitun, sai riga ƙwaya ɗaya bata ta siya komi ba, su ɗin ma da kyar ta iya fitar da kudin su saboda gaba ɗaya ba ta da hanyar samu.5 Saifullahi kuwa sashin da aka tura shi aiki babu wani tsauri, ya kan yi sati biyu bai je Abuja ba in ya je kuma baya wuce kwana biyu zuwa uku. Ko da cikin ta ya cika wata tara babu abin da ta ke sai addu’a, sosai ta rike YAA HAYYU YAA QAYYUM BI RAHMATIKA ASTAGITHU saboda samun sauƙin haihuwa. Yanda Saifullahi ya maida hankali wajen kammala gininsa a cewarsa nan Ayush za ta tare har mamaki ya ke ba Amatullah, ganin gaba ɗaya bai wani hoɓɓasa ba wajen tanadar mata abin haihuwa tun daga kanta har zuwa na jaririn ya sanya ta sadakar da cewa tabbas Saifullah ba ƙaunar ta yake ba.8 Duk halin da take ciki baya dubawa yake kwasan romon sadakinsa. Bata taɓa hana masa ba, ta yanke ƙauna daga sake samun jin dadin aure, ta kaddara a ranta kila cikin ya zama ajali a gareta. “Ki dage da Addu’ar sulhu da ƙulla soyayya tsakanin mutane” shine shawarar da goggonta ke bata a duk lokacin da ta kai mata kokenta ya sanya ta ke barin ma cikin ta. Hakan bai hana mata yawaita faɗin ALLAHUMMA ALLIF BAYNA ƘULUBINA, WA ASLIH ZATA BAYNINA WAHDINAL SUBULA-S-SALAM. ALLAHUMMA ALLIF BAYNA ZAUJIE WA IYAYYA BI SHAFAQATIN WA RIDAAN WAL WI’AAM.7 Tana yi don samun salama da soyayya a gidan aure, ta san Alƙalamin kaddararta ya riga da ya bushe amma wani sa’in ta kan ji ni’ima da rahman Ubangiji ya lulluɓe ta.4 *** Ana saura sati uku su koma makaranta sabon shekara ta fara naƙuda. Da farko ba ta ɗauka da gaske ba sai da ta fara jin ba za ta iya jure zafin ba. A hankali ta isa ga Saifullah wanda ya zauna ya tasa kallo a gaba yana yi yana kyakyata dariya shi kaɗai yana jefa ci cin ɗin da ta masa a baki. “Ya Saifullah taimaka ka kai ni asibiti, inaga haihuwar ce ta zo” tace cikin cije leɓe. Kallonta yayi a sheƙe wanda hakan yayi daidai da ƙarar wayar sa, bai kula da ya bata amsa ba ya ɗaga wayar. “Babe how far” ya faɗi wanda hakan ya tabbatar ma Amatullah Ayush ce ta kira. Nan ta ji wani murɗawan ciki da bata san lokacin da ta tsuguna tana mai ambatan “Wash!” ba. Maimakon ya kula ta sai tsallake ta yayi ya fice daga gidan.4 Hawaye mai zafi ya zubo ma Amatullah, gaba ɗaya ta sadakar a wajen za ta cika don ba ta da mai taimakon ta sai Allah. Tana cikin mukurkusun ta jiyo sallama, hamdala ta yi don ta san in ba Allah ba babu wanda ya turo mata ɗauki. Makociyarta ce ta shigo sa charji, nan ta ganta cikin naƙuda. “Subhanallah! Pharm kashe kanki za ki yi?” tace tana tallafo ta zuwa kujera. “bari na ma Baban Huda magana ya kaimu Layin sarki” tace tana mai ficewa. Ba tare da ɓata lokaci ba ta dawo ta kamo Amatullah ta taimaka mata zuwa cikin mota, sannan ta koma ɗauko kayan da Amatullah ta faɗi mata in da ta ajiye. Asibitin primary health care da ke Layin sarki su ka nufa, da kyar aka amince da ta haihu a wajen saboda ƙaida ba sa karɓa haihuwar fari da na wacce ta yi fiye da biyar. STORY CONTINUES BELOW Bayan doguwar naƙuda na kusan awa uku Amatullah ta sambaɗo ɗanta da daga faɗowarsa ya karaɗe asibitin da kuka. Nan aka kimtsa ta, aka ɗinke ƙarin da ta samu, sannan aka kai ta ɗakin hutu.3 *** Saifullah kuwa fitan da yayi saƙo ya amso na wani leshi da Ayush ta sanya ya siya mata don sawa a akwati, leshin yayarta ke siyar da shi Dubu ɗari da hamsin. Saman gadan ɗanmagaji yaje ya same su in da za su wuce Abuja daga Kano su ka tsaya su ka bashi. Tun a hanyar dawowa halin da ya bar Amatullah ke masa gizo, nan ya tuna da zancen “mai naƙuda ƙafarta ɗaya na duniya ɗaya na lahira ne” Hakan ya ƙara masa matsanancin tsoro ya ƙara gudun motarsa zuwa gida. Kamar yadda ya sa rai tana ciki, ya zata ganin gate ɗin gidan kamar yanda ya barshi. Cikin sassarfa ya isa cikin gida amma babu ita a falo da ya barta tana muƙurƙusu, ya shiga ɗakuna babu ita, ya duba bayan kitchen babu ita, take ya ji wasu zufa su ka fara keto masa. “Inna lillaahi wa inna ilaihi raji’un” yace yana mai kai komo a cikin gidan ko tana wani lungu ne cikin rashin hayyaci. Wayar sa ya ɗauko ya kirata sai jin ƙarar wayarta yayi a ɗaki. Addu’a yake ba kakkautawa don baya son abin da zai haɗa shi da Baba Anas a wannan Marra. A haka ya fito zuciyarsa na bugu da niyyar zuwa Amaru don yana da yaƙinin can ta nufa. Ya fito kenan ya iske makocinsa na shirin shiga motarsa. “Engineer ashe kana gari” ya ce masa bayan sun yi musabaha. “Eh wallahi amma shigowata gidan kenan, na fita da safe” ya faɗi yana mai saurin tada motar. “Can Layin sarkin zan je dama, amma tun da can kayi ga wannan ka kai musu na san za su buƙata” yace yana mai miƙa masa filas ɗin ruwan zafi da kulan abincin da ya riga ya sanya a motar. “Ai inshaAllah yaci ta sauka yanzu, Allah ya buɗe idanunsu lafiya” Baban Huda ya sake faɗi ma Saifullah da gaba ɗayansa yayi mutuwar tsaye. Godiya ya shiga yi ma Baban Huda ganin da gaske ba Amaru ta nufa ba. “Nagode fa, Allah ya saka maku da Aljanna” ya sake faɗi har da yar duƙawarsa. “Haba Engineer wannan godiya haka, ai yi ma kai ne. Ka yi sauri ka isa na san yanzu kila suna bukatar sa, it’s over 3 hrs fa da muka isa, don ma da kyar su ka amsheta ne” yace yana taɓo kafaɗun Saif. Jiki na ɓari Saifullah ya isa tudun wadan, ko da ya isa Amatullah na barci, wani sabon ni’ima ya ji ya saukar masa ganin bai ga kowa daga Amaru ba. Har ƙasa ya durƙusa ya gaida maman Huda duk da a shekaru ba zata girme shi ba, amma har cikin ransa yake jin rufin asirin da su ka masa a matsayin gagarumi. “Ga Danlami fa, ka ji murya da ya saki kukan maraba da duniya” tace tana miƙa masa jariri naɗe cikin zani babu ko rigar sanyi sai wata yar shalaushalon riga. Tunanin in da Amatullah ta samo rigar yayi don shi dai ya san bai saya ba. Hannu ya sa ya karɓe shi yana kallo, tsantsan kamar da yaron yayi da su ya sanya shi jin wani iri, bai sani ba ko hakan ne soyayyar ɗa da mahaifi da ake faɗi ko kuma kiyayyar da yake ma cikin ne ya shafi yaron. “Allah ya raya mana Muhammad Jamoh” yace yana mai miƙa ma maman Huda. A wajen ya sanya waya ya kira Baban Sasa. “Muhammad Jamoh ya iso fa Baban Sasa” yace cikin shaƙiyanci bayan sun gaisa. “In yi guɗa ne Saifullah” yace cike da murna “Ka taso kawai ka tare shi, amma kuma kar ka shafa masa tsufa. Wallahi bana tunanin za a samu wani tsatsonka da zai yi kama da kai kamar shi” yace yana ƙara leƙen yaron. Baban Sasa ya kasa ɓoye murnar sa, a haka su ka yi sallama ya tashi yana mai dogara sanda zuwa cikin gida. Abin da yafi shekaru rabon da ya taka, nan ya faɗi masu haihuwa gida ya karaɗe da murna. Saifullahi kuwa sallama yayi ma maman Huda ya shiga kasuwar tudunwada ya siyo kayan maza, da shawul da kayan sanyi. Ko da ya koma asibiti Amatullah ta farka har ana shirin sallamarsu. *** Ko da su ka isa gida, maman Huda taimakawa tayi ta wanke Jamoh tas, ta sa masa kaya masu kyau cikin wanda Saifullah ya siyo, jariri ya shiga bacci cikin kwanciyar hankali. A lokacin ne yan Amaru su ka shiga tururuwa, suna shiga da fice, ga lafiyayyen tuwo da Goggo mairo ta bayar a kawo mata, taci ta hantse. “ku haɗa mata kayan amfaninta, mu samu mu wuce bayan la’asar” kawai yaji Inna Hafsatu ta faɗi. Bai ɓata lokaci ba ya kalle su yace “Babu fa inda za ta je, anan za ta zauna, na riga da na tanadi wacce za ta zo ta mata wanka, mun yi ciniki har na biya rabi” yace yana cijewa.4 “An taɓa haka ne Saifullahi. Haihuwar fari fa, kuma kwatakwata Amatullah sha tara take fa bana. Don Allah ka duba dai” inna Hafsatu ta sake fadi cikin magiya. “Gaskiya mun gama magana da iyayenmu maza, kuma sun amince da tsarin” ganin saurin da yake amfani da shi ya sa tayi shiru kafin ya kai ga zagin ta.3 A haka suka yini cur suka tafi ba tare da Amatullah ba, ko da suka koma ma Goggo Mairo da yanda aka yi, har cikin ranta taji babu daɗi amma sanin mahimmancin bin umurnin miji ya sa ta ce a bar zancen dawowarta.Gaba ɗaya Saifullah ba zai ce ga halin da ya shiga ba, ya kan ji wani irin zugi tun daga tafin ƙafarsa har saman kansa in ya tuna da wai shi aka haifa wa ɗa. 2 Ƙanwarsa Asiya ya nema ya bata kuɗi naira dubu talatin ta shiga kasuwar sabon gari ta haɗo duk wani abin buƙata na jariri. Sannan ya ware wasu kudaden ya ba da aka siyo Rago aka yanka ma Amatullah na ƙauri. Bai gushe ba sai da ya ɗauko Ƙanwar Hajiyarsa Inna Jamila don ta zauna da Amatullah. Ranar a gajiye ya kwanta cikin wani annashuwa dan ko ba komai ya san yayi bajin ta gurin Baban Sasa, ya samu ya dan wanke kan shi daga bakin cikin da Amatulah ta ku kuntsa masa. Amatullah kuwa ko da aka watse aka barta da inna Jamila mamaki komai ya dinga ba ta, wai itace yau da ɗa, ɗan ma ita tayi nakudarsa ta haifa. In ta fakaici idon inna Jamila sai ta tsura ma yaron idon cikin so da ƙauna. Tayi godiya ga Allah ya fi sau a ƙirga, ta ga mugun wautarta na amincewa cire cikin da farko. “Ashe dai haihuwa kyauta ce da bawa bai isa ya siyo ma kansa ba” tace a ranta tana mai istigfari na kusan butulce ma Allah a farko. 4 Cikin kwana biyu Saifullah ya shayar da ita mamaki, kula sosai yake ba ta da yaron ta, duk ya fita sai ya shigo mata da tsaraba, wani irin rawan jiki ya ke musamman idan Inna Jamila na kusa ba, ita dai na ta ido, na ciki na cikin, dan kuwa ta tabbatar komai ya yi na ganin ido ne, Saifullahi ba kaunar ta ya ke ba bare ɗan da ta haifa, ba za ta taɓa mance yanda ya tsallake ya barta ta na tsaka da nakuda ba. 5 Zirga-zirga da yake wajen tabbatar da komi ya zo cikin sauki ya sanya gaba ɗaya baya ba Ayush wani kulawa, da ita yake kwana ya tashi cikin begenta da kidayan kwanakin da yayi saura na bikin su. Kullum ya ƙirga ya ga saura fiye da kwana ɗari sai ya ji inama ana fast-forward a rayuwa. *** Bayan kwana uku, Amatullah zaune bakin gado ta ci ado cikin atamfa. Sun gama rigima da Inna Jamila wacce ta ke yiwa jariri wanka ya na mai tsallar kuka, akan Amatullah ba ta san ɗaure cikin ta, ita kuwa azabar ciwon da ta ke ji saboda dinkin da aka mata ga wani ciwon ciki da take fama da shi ya sa sam ɗaure cikin baya gaban ta. Saifullahi ne ya shigo gaishe da Inna da Jamila kamar yanda ya saba, kallo ɗaya Amatullah ta ma sa ta kawar da kai. Ganin ana yiwa jaririn wanka ba karamin dadi ya ji ba, ya na mai godewa Allah yau ba sai Inna Jamila ta masa gwalegwalen ɗaukar jinjirin ba, ya durkusa har kasa ya gaishe ta. Ita ma Amatullah a dake ta gaishe shi duka gudun kar Inna Jamila ta dago jirgin ta. 4 Bayan sun gama gaisawa Saifullahi ya tashi ya na shirin fita Inna Jamila ta tsayar da shi ta hanyar faɗin “Ni kuwa Saifullahi sai na ga zai fi idan ka mayar da Amatulah gida, ka ga dai haihuwar fari ne, gashi an mata dinki yanda ta ke da raki ba na ji za ta iya kula da kan ta” Saifullahi na mai sosa kyeya ya ce “Ai Inna Jamila kar ki damu, Zan kasance mai kula da ita da kai na, ba na so su yi nisa da ni ko kadan…..” 2 Ya karasa maganar ya na mai ƙasa da kan sa, cike da takaici Amatullah ke kallon sa, a sanin ta ba dan komai ya ke gudun komawar ta gida ba sai dan gudun kar asirin shi ya tonu. Ita kuwa Inna Jamila kai ta jinjina ta na mai faɗin “Yaran zamani, toh ai shikenan” Sinsin ya fice gudun kar Inna Jamila ta sake furta wani abu. STORY CONTINUES BELOW “Yanzu Inna haka za ku bar ni da shi? Wallahi babu abin da zai yi min, Yaya Saifullahi macijin sari ka noke ne…..” “Kul!” Inna Jamila ta katse ta cikin tsawatarwa, ta kara da “Kar na sake ji, ku yaran zamani sam ba ku da godiyar Allah, ki duba yanda yaron nan ke mi ki hidama Amatullah, tsabagen rashin godiyar Allah ki kira shi macijin sari ka noke?” 2 “Duk wannan hidimar da ki ga yanayi na ganin ido ne. …” “Lahaila!” Cewar Inna Jamila ta na mai jinjina kai, ba ta gushe ba ta kara da “Ba ki da godiyar Allah ƴar nan! To kuwa duk wanda bai godewa Allah ba ya ƙi godewa azabar shi ba!” Shiru Amatullah ta ma ta, cikin ran ta kuwa faɗi ta ke ai shikenan, duk randa ya kashe ni kwa gane. Haka Inna Jamila ta kare wankan jinjira ta na mita har sai da Amatulah ta yi danasanin lafazin ta tsabagen mitar Inna Jamila. **** Zaune suke suna kallo, hankalinsu ya ɗauku ga series ɗin Korea da suke kallo, Zainab, Sa’adah da Farida sun natsu gaba ɗaya. Ayush rike da waya tana mai jan tsaki, hakan bai sanya sun waigo sun kalle ta ba, wani dogon tsaki ta sake ja wanda yayi daidai da shigowar Antyn ta mahaifiyar su zainab Anty Ruqayya wacce aka fi sani da Hajiya Haske. Gidanta Ayush ta wuce a Abuja lokacin da ta ajiye ma Saifu leshi. Tun rabuwar su ta lura gaba ɗaya hankalinsa ba shi a kanta, ita da kanta ta neme shi ta sanar masa da isarsu, tun ranar kuwa ba su sake wayar minti ɗaya ba, free call din sha biyu da rabin da su ke yi ma ko ta kira sai ta iske wayarsa a kashe. “Baby Ish lafiya kuwa, don dai hankalinki baya kan talabijin balle na ce kallo kike” Hajiya Haske tace tana zama gefenta. Ita kanta Ayush ta san Anty Ruqayya na cikin wainda ke shagwaɓa ta, kanwar mahaifiyarta ce da ke sonta kamar ƴar da ta haifa. In dai ka ji su a rana toh akan rashi suturta jiki ne, don Hajiya haske irin matan nan da kuɗi bai sanya su canza shigarsu ba. “Maami Saif ne fa, yau kwana biyar kenan sai share ni yake, yanzu ina shiga Facebook na iske an ɗaura hoton jariri har ana tagging dinsa, the baby looks so much like him” tace cikin shagwaɓa “Common baby, ba yana da aure ba, menene in matarsa ce ta haihu” Hajiya Haske ta faɗi tana rungumar Ayush. “Maami Alkawari ya min fa, cewa yayi ni zan fara haifar masa yara”. Tace tana dakin kukan da ta makale shi a makoshi. Rarrashinta Hajiya Haske ta dinga yi tana bata baki yayin da su zainab su ka zo su ka tsaya cirko cirko cikin tausayin yar uwar su. 6 “Common Ayush, we are in 21st century fa, 2011 muke ba 90s ba, har namiji zai ce miki haka ki yarda, ni wallahi shi ya sa na so ki amince ma Baba Hashim ɗinmu, ga kyau ga ilimi ga naira, amma kin nace ma baƙauyen zaria” zainab da suke sa’anni da Ayush ta faɗi cikin jin zafi. “Ba Baba Hashim kaɗai ba, shin wa ya kira ku nan ma” hajiya haske ta ce tana janye Ayush cikin ɗaki. Nasiha sosai ta ke mata akan haihuwan Saif ba komi ba ne in har da gaske yaron da ta gani ɗansa ne. Kuma tun da su duka sun shaida son da yake ma Ayush sun san tabbas tana shiga ragamar gidan zai koma hannunta. “Ki yarda da kanki, sannan kada ki ce zaki dinga soloɓiyanci, ba a taɓa aurenmu mun zama bora ba, tabbas sai dai mu mulki gida” hajiya Haske ta ƙarasa da faɗin haka. Wanda hakan ya fi komi kwantar da hankalin Ayush, ta san iyayenta tsaye su ke akanta. 5 Komawa wajen yan uwanta tayi su ka cigaba da kallo, da ga baya kuma su ka fara hira inda Sa’adah ce ta buɗe musu ƙofa da faɗin “Wai ni Ayush me kika shirya ma Saif dinnan ne, makaho fa bai san ana kallonsa ba sai ka zungure shi” ta ce tana mai sassauta muryarta. STORY CONTINUES BELOW “Kuma fa wallahi haka ne, shi wai ga munafuki ba, yana can suna soyewa da matarsa ke yana bin ki da daɗin baki, watau shi ya san daɗin haihuwa ko” Farida ta ce tana mai jan tsaki. Hankalin Ayush yayi matukar tashi ta maida hankalinta gaba ɗaya gare su tana son jin me suke nufi. Su kuma ganin haka ya sanya su fadi kamar haɗin baki “Comment on the pic” sai a lokacin taji wani daɗi, take ta ɗauko wayarta ta shiga Facebook tare da neman hoton don tayi sharhi akai. “Me zan sa?” tace kamar za ta yi kuka. “Welcome to the world darling. May Allah bless your parents with much love and harmony” zainab ta amshi wayar ta rubuta tare da karanta musu. Shewa su ka yi gaba ɗaya suna tafawa. 2 “Kin san yana gani dole ya shiga tsilla-tsilla” zainab ta fadi cikin dariya. Da haka su ka cigaba da kallo suna sharhi zukatansu fal da murna. *** Saifullah na zaune bayan isha’i, ya dawo gidan da balango in da ya miƙa ma Amatullah nata kamar yanda yake mata tun bayan haihuwarta. Sam ba ta mamakin kyautata mata da ya ke kokarin nunawa Inna Jamila ya na yi, ta san kaɗan daga aikin Saifullahi. Tun da ya dawo ya ɗauki wayarsa ya shiga Facebook, nan ya iske sanarwan sharhin Ayush a kan hoton da bai san da zaman sa ba. ” Hasbunallah” yace yana mai miƙewa tsaye. Shi dai ya san bai faɗi mata komi dangane da cikin ba balle a je zuwa haihuwa. ‘in ta fasa fa’ sashin zuciyarsa ta faɗi masa hakan ya sa ya ƙara firgicewa. Wani takaicin Amatullah da abin da ta haifa ya tokare masa ƙirji, cikin rawan hannu ya lalubo lambar Ayush ya kira. 2 “He is calling” tace cikin murna ta na nuna ma yan uwanta. Dama ta faɗa musu zai kira daga gani don son da yake mata bata da haufi akai. “Ki ɗauka, kar ki nuna ɓacin rai ki ce ya haɗa ki da matar za ki mata barka, make sure you leave him in suspense” zainab tace yayin da sa’adah da farida su ka amince da shawarar. “how far babe” yace bayan ta ɗauki wayar. Danne zuciyarta ta yi kar ta ƙunduma masa Ashar. “maimakon ka sanyo ni muyi jegon tare sai a yi min wariyar launin skin” tace cikin dariya. Shiru yayi kamar ruwa ya ci shi, sai da ta sake faɗin “Hello” sannan yayi gyarar murya ya ce “Kiyi haƙuri, ni mai laifi ne, wallahi ba yanda kike zato bane, duk yadda na so a zubar da cikin nan ta ƙi amincewa. I did all I could wallahi” yace kamar zai yi kuka. 2 Dariya ta yi sosai, zuciyar ta fal da murna ta ce “Subhanallah! Saboda so na zaka saɓa ma Allah, ai tun da dai aka yi kuskuren shiga inda ba muhalli ba ai hakuri ake da duk abin da ya biyo baya. Yanzu dai bani maman Babyn na mata barka” tace muryarta sarai ba alamun ɓacin rai. 2 “Bana gida ai, rabon da na sa su a ido tun washegarin haihuwan. I’ve been busy ne a kammala gidan ki, jiya na ga wani gu da ba’a yi da kyau ba, gaba ɗaya can na yini har yau. Ni gaba ɗaya auren mu ne gaba na” ya samu kansa da shirgo ƙarya. “Amma ai ba zai hana ka kashe kudin suna ba ko, don duk son mu da yin classy biki, taron sunan nan ma is very important” tace tana mai addu’ar haƙanta ya cimma ruwa. “Suna kuma, ai in kin ga nayi recognizing wani ɗa a gidan nan toh Queen Ayush ce ta haihu, kin san Allah ɗaya tun ranar da ta haihu na faɗi suna but yanzu ba sai gobe ba zan kira na ce ba suna kar ma su da rai” yace cikin rudewa. Bai kashe wayar ba ya kira Baban Sasa yana mai haɗa conference call. STORY CONTINUES BELOW “Baban Jamoh jikan Jamoh” baban Sasa ya faɗi cikin raha. Gaishe shi Saifullah yayi suka dan yi raha sannan yace. “ni dai Baban Sasa ban son taron sunan nan, taron gulma ne kawai, ka ga a ɗan zuwa barka ana neman zuga yarinyar nan. Don Allah ka tsawatar, kowa yayi zamansa ya mana addu’a daga can” yace cikin muryar magiya. Shiru Baban Sasa yayi ya ce “Ayi haka Saifullah, kar mu tauye ma yarinyar nan fa da yawa” “Baban Sasa ni duba zaman lafiyar mu nake, nan jiya na shigo na ji ana mata kirarin jinin Jamoh ba su zaman kishi, Baban Sasa in ba dai fasa auren nan zan yi ba” ya ce sanin da yayi baban Sasa ba zai taɓa yarda da fasa auren ba. 2 “mu kuma ka maida mu mutanen banza ko, iyayenku ne matsorata amma ni cikakken bazazzage ne, cikin zage-zagin ma Bamalle, sai da na yi huɗu ras” yace cikin dariya, shima Saifullah dariya yayi. “Zan faɗa masu, Allah ya raya mana Muhammad Jamoh” Baban Sasa yace nan su ka yi sallama Saifullah cike da farin ciki. “Babe believe me, wallahi ba abin da ba zan iya yi don farin cikinki ba” yace bayan ya ajiye wayar baban Sasa. 3 Tsaki ta ja cikin nuna takaici ta ce “Toh wai ka birge ne nan, ku yi sunanku lafiya ni bacci zan yi” bata jira amsarsa ba ta kashe wayar. 4 Kansa ya rike gaba ɗaya ya rasa me zai yi ya wanke kansa wajen Ayush, ya san ta sarai a haukarta ma sai ta iya fasa auren. Kwata kwata bai yarda da amincewarta ba yafi ganin sa a shigo shigo ba zurfi ta masa. *** Kamar yadda ya tsara ilai kuwa hakan ya faru, Amatullah na ji tana gani baban Sasa ya sanya dokar rashin bikin suna tare da tsawatar ma yaya da jikokinsa akan zuwa gidan Amatullah akai akai. Mamaki sosai ya cika ahlin gidan don shi bai furta cewa ga yanda su ka yi da Saifullah ba balle wani ya zarge shi. “Aure mijinta zai ƙara, yarinyar nan ta amince ta yi tawakalli na zan laminta ba a fake da taron suna a zuga ta” shine hujjar da ya bayar wanda sosai yaransa maza su ka yi na’am da hakan. Har gida Baba Salihu ya je ya samu Amatullah ya mata nasiha sosai, ya nuna mata rayuwar ma gaba ɗayansa guda nawa ne, da suna ko babu suna abin da ya ke rabon ta ba zai wuce ta ba. 2 “Baabaa!!!” tace tana mai son fadi masa halin da ta shiga lokacin rainon cikin ta da halin da suke ciki a yanzu. Damuwar da ta hango a kwayar idanunsa ya sanya ta faɗin. “Next week za mu koma makaranta, ina jin tsoro kar na kasa making result ɗina” kallon ta yayi a matsayinsa na ɗan jarida yana son ya fassara ma’anar abin da ta ce. Saifullah da ke maƙe bakin ƙofa ma saukar da ajiyar zuciya yayi da ya ji abin da ta faɗi, kafin Baba Salihu ya kai ga cewa komi ya shiga falon haɗi da sallama. Sai da su ka gaisa da Baba Salihu sannan ya kalli Amatullah ya ce “Baba yarinyar nan da ita ce auta ban san ya za ta yi ba, kin wani tasa Baba kina hawaye” Dariya Baba Salihu yayi ya ce “Wai tsoron boko take yi kuma sai kace kanta farau boko da goyo. Ni dai abin da zan ce miki shine ki sani gatanki ne bokon nan, kar ki ji tsoro ki dage ki fauwala ma Allah komi sannan ki yi addu’a. In an buɗe portal ki cire transaction ID zan sa a ƙarasa miki registration, Allah barshi sai ki koma in an fara lectures.” yace zuciyar sa cike da tausayin ƴarsa. 2 Nan dai su ka cigaba da hira su ukun, kafin da ga bisani Baba Salihu ya tashi ya tafi ba don ya so ba. *** STORY CONTINUES BELOW Tun bayan da aka yi kwana bakwai, Saifullah ya sallami innarsa Amatullah ke yin komi, tun daga yi ma jariri wanka har zuwa yin nata wankan. Ga shi dinkin ta sam ko hanyar warkewa bai dauka ba, ko da ta yiwa Gwaggo korafi sai cewa ta yi tsabagen raki ne irin na Amatullah, dama Inna Jamila ta ce ba ta san shiga ruwan zafi to ina kuwa din ki zai warke? Lalle ta dage da shiga ruwan zafi. Ana cikin haka wayarta ta lalace, gaba ɗaya sai ta koma kurma, ba ta jin kowa babu mai jin ta, ga zamansu ba laifi yau lafiya gobe akasin haka. Kamar yadda baba Salihu yayi alkawari shi ya tsaya ta kammala registration sannan ya ɗauki dubu goma yace ta rike ko za ta bukaci wani abu. Sai kwana uku da fara lectures ta koma makaranta, duk dai har lokacin ta kan ji dinkin da aka mata ya na sukar ta, idan ya tashi mata ciwo har kwakwalwar kan ta take ji, ga wani dan hamami hamami da ta kan ji ya na tashi duk sanda ta ɗan bude wajen. 12 Ranar da ta fara zuwa ranar lectures din Dr. Muhammad Zayyad ne ta shiga kusan a makare ga goyo kuma. 4 Kujerar da ke kusa da ita ta zauna inda wacce ke zaune ta matsa mata cikin fara’a. Karatu yake musu cikin gwaninta da iya koyarwa a fannin clinical pharmacy. Sosai ta ke jin daɗin karatun, cikin rahamar Allah har ya gama awa biyunsa Emjay bai tashi ba. Bayan fitarsa ne su ka gaisa da wacce ke kusa da ita. “Great pharmacist ce yau a ajinmu” tace cikin fara’a “suna na Hannah Dawud ana ce min mimi, tun da nazo 100level nake son zama da ke, like sosai kike birge ni, ba ruwanki da gayu always in hijab kuma first class student” tace cikin tsantsan farin ciki. “mimi kenan, to tell you nothing is permanent in life yau gani repeating 300lvl. Anyway it’s nice meeting you” tace tana miƙa mata hannu. Nan Amatullah ta faɗi mata courses din da za ta yi, mimi ta bata update akan su. “in ba za ki damu ba, let’s be friends please, na san circumstances su ka yi leading to carry over ɗinki, Kinga ni Christian ce daga Adamawa, amma family ɗinmu duk mix ne, I hope ba zaki damu ba” ta ce cikin fara’a, yayinda ta ji mummunar faduwan gaba jin ta ambaci ita christain ce, kuma daga Adamawa. Dee Yusuf ne ya faɗo mata, yayinda ta ke kallonta tana mamakin kyanta da gayunta haɗe kuma da surutun Mimi, amma ace christain ce, wannan asara har ina. Tun daga ranar gaba ɗaya harkan karatu tare su ke yi, su na ba juna assignment su na ma juna bayani. Mimi ta bata shawaran samun cikin masu shara da zata kula mata da Emjay( sunan da take kiran babyn ta kenan) sai dai in sun samu sarari ta je ta bashi nono. Duk wanda ya san Mimi a gidansu da hostel ya san Maman Emjay ko a labari ko a fuska. Haka Amatullah bata kyashin kiranta da mummyn Emjay saboda kulawar da mimi ke bashi. Abin da ta lura da shi shi ne shakuwar da ke tsakanin Mimi da cousin ɗin ta, wanda kullum ba ta da magana sai na shi, bini bini ta kira shi, ko kuma ta ce da Amatulah ta raka ta office din shi nan bayansu a faculty of medicine da yake ta ce da ita assistant lecturer ne, wannan session din ya fara koyarwa. Amma hakan nan Amatulah ta ji ba ta son raka ta, har Mimi ta gaji ta daina mata tayi, a cewar ta kila Oga ya hana ki zuwa office din lecturers, ciki har cousin din kawar ki, ita kuwa ta bi ta eh ba tare da ta taɓa tunanin jin sunan cousin din na Mami ba, ta kan tsoka ne ta da Mimi cousin. Tsakanin ta da su Zulaikha kuwa sai dai idan ta shiga hostel ko sun haɗu wajen sallah dan kuwa yanzu sun zama seniors din ta. **** STORY CONTINUES BELOW Dinki ta ba karamin damun ta ya ke ba, Amma duk sanda ta tunkari Saifullahi da maganar sai ya ce tsabagen gudun kar ya koma mata ne, ta kwantar da hankalin ta shi kan shi ba ta bashi sha’awa yanzu, dan kuwa ba dan ba dan ba sai ya ce ya kan ji dan wari wari na fita daga jikin ta, in dai haka ake jego Allah wadar jego irin na ta. Ranar haka ta sha kuka har ta yi mai isar ta, duk tsafta da kula irin na ta Saifullahi ya ce ta na ɗan wari wari, duk da dai ita kan ta ta san ba daidai ta ke ba. Washagari ya kama satin da za tafi mid semester, Amatullah na zaune da Mimi suna bitar wani course dinsu na pharmacology da za su yi test ranar Juma’a da za a tafi midsemester. “Maman Emjay me ke faruwa ne? Na ganki kwana biyu wata iri, yau idanun ki a kumbure” Mimi ta tambaya cike da damuwa. “wallahi mummyn Emjay, ina fama da ciwo sosai a ƙasa na, tun bayan haihuwa da aka min dinki ban sake jin dadin gurin ba, har ruwa yake yi, I think I got infected, idan ya tashi min ciwo har tsakiyar kai na, yau har jiri na ke ji” tace cikin hawayen da kamar dama suna jiran izinin fitowa. “kin kula yana wari kuwa, tun last week na ji, amma ina ta neman hanyar faɗa miki, me Dadyn Emjay yace” mimi ta faɗi cikin kulawa. “Mimi me zai ce, aurensa saura wata biyu, gaba ɗaya hankalinsa na wajen ne, labari na mai tsawo ne wata rana zan baki” tace tana murmushin takaici. “tashi mu tafi asibiti, ki na ɗiya mace be kamata ki yi wasa da abu irin haka ba, darajar ki ne fa, yanzu haka za ki zauna har a kawo mi ki kishiya jikin ki da wannan ciwo haka? Ai ya zama ciwo Maman Emjay, tashi mu tafi gaskiya……” 2 Duk da Amatulah ta ɗan girme mata, yau sai Mimi ta zama kamar ita ce Yaya gurin ta. Amatullah na mai raunana idanu ta ce4 “Ki na gani za su karɓe mu? Har biyu fa Mimi?” “Kar ki da mu, ai nan shika za mu ce, akwai wata Anty na da ke aiki wajan, na san za ta iya taimaka mana” Cikin jin dadin yanda Mimi ta damu ya sanya Amatullah jin dadi, ga ta dai ahlil kitab amma sai zuciya mai kyau kamar ‘Dee Yusuf…’ Karo na hudu da ya kara faɗowa cikin ran ta kenan, ta na mai kokarin cire shi daga cikin zuciyar ta, tare da kwabar zuciyar na ta ta tashi, su ka ɗauki hanyar fita daga ajin ta na mai yiwa Mimi godiya. Wata coursemeta din su ce su ka samu ta rage mu su hanya. Kamar yanda Mimi ta faɗa Anty din ta ce ta taimaka su ka ga wata Gynecologist. Ko da Amatulah ta bude mata ga halin da ta ke ciki kuka ne kawai ba ta yi ba in da ta rufe Amatullah da faɗa sosai. Ya ta na ƴa mace za ta bari ta lalace haka? Shin ina iyayan ta su ke? Kuka Amatullah ta saka mata dan kuwa dai rasa da mai za ta ji ta yi, ciwon da ta ke ji ko kuwa masifar gynecologist da ake kira Dr Hajara. Sai ta karaci masifar ta har ita kan ta Antyn Mimi da ba ta ji daɗin halin da Amatulah ke ciki ba ta saka baki, dan kuwa Dr Hajara cewa ta yi ba za ta iya taba Amatullah ba. Dr Hajara na mai kallan dinkin Amatullah da har kore kore yayi tsabagen rashin kula ta ja tsaki a karo na uku kafin ta ce “I’m doing everything a fresh, kankare shi zan yi na sake buda ta, a sake mata wani dinkin, wajan is infected, Allah ya sa bai zama sepsis ba, fatana dai shi ne ace iya ka dinkin infection din ya tsaya!” Ta na gama faɗin haka ta tashi ta fice daga office din. Antyn Mimi na mai taɓa hannun Amatullah cikin bata karfin gwiwa dan kuwa gaba daya hankalin ta tashe ya ke. Mimi wacce ke rike da babyn Amatullah Antyn ta kira, in da ta ke shaida mata halin da ake. Mimi na mai duban Amatullah wacce idanun ta ya cika da hawaye ta ce STORY CONTINUES BELOW “You will be fine Amatullah, don’t worry, ga waya ta ki kira Dadyn Emjay ki fada ma sa halin da ake ciki” Hannun ta na rawa ta karbi wayar a hannun Mimi, ta kira number Saifullahi har sau wajan biyar amma bai ɗaga ba. Murya sanyaye ta ce “Mimi ya ki dagawa….” “Toh ko Momcy za ki kira?” Cewar Mimi cike da damuwa. Amatullah na mai girgiza kai te ce “Ah ah, kar na ɗagawa Gwaggo hankali, dama shi din dai zan iya faɗa ma, amma tunda bai daga ba, a yi min kawai na huta da wannan masifar” Da wannan Mimi ta shaidawa Antyn na ta, da izinin Amatullah tare da ƙwarin gwiwar Mimi da Antyn ta, wajan karfe uku aka shigar da Amatulah daki na musamman da aka ware domin aiki da ya shafi mata. Allurar kashe wajan da kuma girman dakin bai hana Mimi jiyo ihun salatin Amatullah ba, tun ta na iya jurewa har ta kasa, tashi ta yi tana da jijjiga Emjay da ya ɗan fara koke koken yunwa, su ka fice can waje. Sai wajan biyar da rabi aka gama Antyn Mimi ce ta kira ta in da ta ke shaida mata an ci sa’a infection din be shiga cikin tsokar ta ba. Cike da fargaba Mimi ta tambaya ko za ta iya ganin Amatullah. 1 “Sosai ma kuwa, Nan da one hour ma da ta ji dan dama dama za ta iya tafiya, Amma gaskiya ki jawa kawar ki kunne ta bi duk dokokin da Dr Hajara ta ba ta in dai ta na so ta sami sauki” Da wannan Mimi ta sami ganin Amatullah da har lokacin ba ta dawo cikin hayyacin ta ba. Mimi ce ta kara kiran number Saifullahi amma har lokacin bai dauka ba, sai kawai ta tura ma sa sako kamar haka “Hello Dady Emjay, his mom, your wife Amatullah is very sick and in the hospital, kindly call me back it’s urgent” Ta tura ma sa, har tsahon minti 30 shiru, dan haka kawai sai ta kira cousin din ta, ta roke shi alfarmar ya zo ya same ta hospital. Da ya ke ya ji batun asibiti sai yayi tunanin Mimi ce ba lafiya, dan haka ba tare da bata lokaci ba ya garzaya asibitin. Mimi ce ta taro shi daga in da yayi parking, dauke da Emjay wanda ya sha kuka ya gaji har bacci ya sace shi kwance bisa kafadar ta, suna tafe ta ke shaida masa halin da Amatulah ke ciki, ta kare da “Har yanzu dai mijin na ta bai kira ko ya min reply ba, shi ya sa ma na kira ka ko za ka taimaka ka bani 15k dan biya kudin asibitin, sai mu kai ta gida I take God beg you…” Bakin kofar ɗakin da Amatulah ke kwance su ka tsaya, ya na mai kallan ta ya ce “Mimi rigima, like how can you get your self involved in something like this? Mijin ta ba ya daga waya ba sai ta hakura ta je gida ta faɗa ma sa…” “Believe me, it was an emergency, please ka taimaka…..” Ta fada ta na mai marairace masa Cikin dariya ya lakace hanci ta tare da fadin “As usual dole na yi yanda ki ke so Mimi, you always have that power over me, wanna shi ne babyn na ta ke nan” Ya na maganar ne yayinda ya ke kai duban sa ga fuskar yaran a karo na farko, wani iri mummanar faduwar gaba yaji yayinda yayi ido hudu da Emjay. “Eh Emjay kenan, yayi kuka ya gaji ya fara bacci” Hannu ya sa ya shafi fuskar Emjay, yayinda kamanin ta ke dawowa zuciyar sa “Ya sunan ta ne? Maman Emjay?” Zuciya daya Mimi ta ce “Sunan ta…….” “David dantawaye idanun ka kenan?” Antyn Mimi ce ta katseta, yayinda Dee Yusuf ya ja ajiyar zuciya ya na mai duban Antyn ta su ya ke murmushi, ya ba ta amsa da STORY CONTINUES BELOW “Ni na isa Anty, ai tuwo tuwo ne ba a sake ma sa suna Mama na” “Ka dai yi bayani, yaushe rabon da na saka ka a ido na? Ko ka dena iyayen da mu ne?” “Kai na bisa wuya na Anty, ai ban isa ba, aikin ne sai a hankali” Nan ya gaishe ta cike da girmamawa, kafin ta shedawa Mimi kawar ta fa ta dan sami dama dama, za su iya tafiya gida. Dee Yusuf da tun ganin Emjay gaban sa ke faduwa tuni yayi gaba, ya ce da Mimi su same shi a mota bayan ya ciri kudin da Mimi ta tambaye shi, naira duba goma shabiyar ya bata. Sai da ta yi biya komai sannan ta koma gun Amatulah wacce ta tabbatar mata ta na cikin hayyacin ta, za ta iya gane hanyar gida sannan ta sheda mata cousin din ta na mota ya na jiran su. Hannun Mimi ɗauke da magunguna Amatullah, Daf da magarib, Amatullah na godiya babu adadi, ta na tafiya kamar mai koyan tatata har su ka isa motar Dee Yusuf. Ya na daga zaune bai damu da ya fito daga motar ba su ka yi sallama da Antyn su, bayan mota Mimi ta budewa Amatullah ya zauna sannan ta zaga dauke da Emjay ta zauna gaban mota. Sai da ta zauna ta ce “Maman Emjay yau dai ga cousin dina da ki ke min tsaya akan shi, Dee meet Maman Emjay” Duk radadin da ta ke ji bai hana gaban ta faduwa ba jin Mimi ta furta ‘Dee’ shi kuwa zuciyar shi daya ya juyo ya na fadin “Sannu Maman Emjey…….” Nan ya tsaya cak yayinda yayi ido biyu da fuskar da ya kasa mancewa a rayuwar sa “Amatullah” Ya tsinci bakin sa na furta sunan ta cikin numfashi, Amatullah kuwa gaba ɗaya rudewa ta yi, ba ta taɓa zaton za ta karasa shi a Ido ba, haka kuma ba ta so a ce cikin halin nan da ta ke za ta gan shi ba, ba ta yi shirin sake ganin shi ba. Shirun da ta ga sun yi suna duban junan su ya sanya Mimi faɗin “I’m missing something here? Dee dama ka san ta ne?” Dee na mai jinjina kai, ya juyo ya tada motar, ya ce “Na san ta sanda ina under graduate, Amatullah……” Ya fadi sunan ta yayinda ya tada motar su ka fara tafiya, cikin ran sa ya na jin ciwon da ke kasan zuciyar sa da Mimi ta fama masa. Mimi kuwa gyada kai ta ce “Oh yes guru dole ya san guru duk da dai akwai tazara a tsakanin ku, idan na yi lissafi daidai su na hundred level ka yi graduating ko?” Kai kawai ya gyada mata, daga nan bai sake furta komai ba domin kuwa gaba ɗaya rasa abin da ke ma sa daɗi, ashe Amatullah ce Maman Emjay din Mimi? Ashe duk wannan azabar da Mimi ta ba shi labarin Maman Emjay ta sha wajan dinki ashe Amatullah ce? To ina mijin ta? Wani irin soko Amatullah ke aure? Zance da ya ke yi cikin ransa kenan har su ka isa bakin gate din asibitin. Amatullah kuwa mutuwar zaune ta yi, sai da Mimi ta tambaye ta sau uku sannan ta fahimci da ita Mimi ta ke magana, ta faɗa ma su sunan unguwar da su ke zaune. Cike da tausayawa Mimi ta ce2 “Maman Emjay please ki rage damuwa, Allah zai ba ki lafiya kin ji?” Kai Amatullah ta jinjina mata ba tare da ta iya furta komai ba, Allah Allah ta ke su isa gida ta fita daga motar Dee, ba dan halin da ta ke ciki ba da tuni ta sauka ta gwammaci ko machine ne ta hau, fatan ta Allah ya sa har su ajiye ta kar su hadu da Saifullahi, duk da dai ba ta da tabbacin ya san Dee, ko ya san shi ba lalle ya gane shi ba. Ganin yanayin Dee ya canza sam Mimi ba ta kawo komai cikin ran ta ba, duk a tunanin ta tsabagen haushin involving kan ta da ta yi cikin lamarin Amatullah da ta yi ne. Dan haka duk surutun ta sai ta sami kan ta da kame bakin ta. Haka su ka yi tafiyar kurame har su ka isa unguwar su Amatullah. Mimi na tambayar ta kwanar da za a shiga ta na fada mata shi kuma Dee na karya kan motar shi har su ka isa kofar gidan Amatullah, nan su ka yi kacibus da Saifullahi, ya fito daga gidan kenan ya ga wata hadaddiyar mota ta faka kofar gidan sa. Tuni ya shagala da kallon motor ya ma manta ya fito ne domin ya je gida ya shedawa Baban Sasa Amatullah fa ba ta dawo daga makaranta ba, gashi yayi neman duniya cikin makaranta har department din su amma be gan ta ba. Hasken farin wata da kuma hasken fitar layin ne ya haske fuskar Dee da ke hakince gaban mota shi sam bai lura da Saifullahi ba, wanda ko a mafarki aka nuna masa Dee zai gane shi. Ran Saifullahi bai baci sai da ya ga Mimi ta fito dauke da Emjay bisa kafadar ta, ta zo gidan baya ta budewa Amatullah wacce ta fito da kyar ta na faɗin “Na gode sosai, madallah” Dee wanda ya tabbatar da shi ta ke kai ya jinjina mata ta na mai sakar mata murmushin nan na sa mai kayatarwa. Duk abunda ke faruwa a kan idanun Saifullahi wanda ya cika yayi fal tsabagen wani bakin kishin da tun da ya ke a rayuwar sa be taba zatan ya na da shi ba. 2 Ita kan ta Amatullah sai a sannan ta lura da shi, ganin yanda ya hade girar sama da na kasa ya na huci kamar macici ya sanya Amatullah kokarin karbar Emjay daga hannun Mimi, ita kuwa ta ce 2 “Ah ah mana Maman Emjay bari na shigar mi ki da shi ai” Amatullah na mai tasbihi da neman tsarin Allah daga halin Saifullahi wanda Sam bai lura da yanayin tafiyar da Amatullah ta ke yi ba tsabagen masifa ya rufe ma sa idanu su ka iso daf da shi, cikin sanyin murya ta ce “Ya Saifullahi yi hakuri daga asibiti……!” “Ke dallah yiwa mutane shiru!” Saifullahi ya daka mata tsawar da ita kan ta Mimi sai da ta ja baya da sauri har ta na tuntube, Emjay tuni ya razana ya fashe da kuka, hakan ne ya ja hankalin Dee Yusuf, har ya sauke gilashin motar shi cike da mamakin abun da ke faruwa. Saifullahi wanda bai yi la’akari da ba su kadai ba ne ba, kuma a kofar gida su ke ya cigaba da bambami, ya na mai zargin Amatullah ta hanyar furta munana kalamai gare ta, fadi ya ke “Macuciya! Azzaluma! Ashe da auren ki ba ki rabi da wancan arnan ba? Da auran ki kina bin namijin da ba na ki ba! Kin yi asara Amatullah……!” “Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun, Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun, Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun!” Iya ka abin da Amatullah ke iya furtawa kenan. Ita kuwa Mimi hankalin ta ne ya tashi, Ganin Dee ya fito daga mota a fusace ya tabbatar mata Dee Yusuf din ne arne kuma tsohon saurayin Amatullah da Saifullahi ya ke nufi, da sauri ta sha gaban shi ta na mai girgiza ma sa kai, idanun ta cike da magiya ta ce “Dee I beg of you..Kar ka yi haka, kar ku tara mata mutane, she is ill for goodness sake! please ka koma mota, bari na kai ta ciki” 2 Saifullahi kuwa ya na huci ya ke fadin “Ki bar shi ya karaso mana, me zai iya min kwartan banza kwartan hofi, ko da yake ku kwartanci a addinin ku ba komai ba ne, ita dai da ta ke musulma ita ta yi abin kunya…..” A fusace Dee ya furta “Mimi!” Mimi da idanun ta su ka cika da kwalla ta ce “You’re better than this, you can do better, please Dee” Ya na mai jinjina kai ya koma mota, Mimi ta ja hannun Amatullah da tashin hankali ya sa dishi dishi ta ke gani. Allah ya so Saifullahi bai kai ga datse gidan ba su ka karaso, dan haka Mimi ce ta tura kofar gidan, hannun ta cikin na Amatullah su ka shige ciki suka bar Saifullahi tsaye ya na huci ya ke duban Dee da ya shige motar shi ya na mai dage gilashin mota. Har ga Allah ya so yiwa Saifullahi dukan kawo wuka, Amma halin da Amatullah ke ciki, da kuma Mimi ya sanya shi zama cikin mota zuciyar shi na tafasa. Ganin Dee Yusuf yayi banza da shi, ya sa ya shige ciki a fusace. A falo ya tadda Amatullah zaune, rike da Emjay da ke ta kuka amma ta kasa ko kallan sa bare ta kai ga rarrashi ko ba shi nono. Mimi da ke Allah Allah ta koma wajan Dee kar ya biyewa Saifullahi ta yi mata sallama, tare da bata hakuri sannan ta juya, ba ta kai ga fita ba ta ji Saifullahi ya ce “Wannan yaron da ki ke rike da shi, ina kyautata zaton ba dana ba ne shi ya sa ki ka dage ba za a zubar da cikin ba, dan wancan kwartan na ki na waje ne…!!!” 9 Ba Amatullah ba ita kan ta Mimi a razane ta juyo ta na duban Saifullahi, Amatullah kuwa neman hawaye ta yi ta rasa, salatin ma ya kafe a bakin ta, duban shi kawai ta ke da idanun ta da su ka su ka yi jajur. Bai gushe ba ya kara da “Ki hade na ki ya na na ki ki bar min gida, Ni Saifullahi na sake ki Amatullah, na sake ki! Na sake ki!” kafin su samu farfaɗowa daga suman zaunen da su ka yi su ka tsikayo shi yana faɗin “Sannan wallahi kar ki bari na dawo na isko ki a gidan nan, banza fasiƙa”+ Wani irin abu ya tokare ma Mimi a wuya, ta na jin ana faɗin maza ba su da kirki ba ta taɓa yarda ba sai yau da ta ga zahiri.4 Yanda Saifullahi ya gifta ta a fusace ya sanya Mimi jan gefe gudun kar ya buge ta. Ta koma wajen Amatullah ta na kokarin karɓan Emjay daga hannun ta ta ce “Yi hakuri Amatullah, I don’t even know what to say, da na san zuwa asibiti da zuwan mu gidan nan abin da zamu jawo mi ki kenan wallahi da ba mu zo ba, kin ce cousin din ki ne ko? Tashi mu kai ki gida kafin ya riga mu” Maimakon ta sakar mata Emjay, sai daɗa riƙe shi ta yi gam. Ta na mai duban Amatullah da idanun ta da suka riga su kafe ta ce “No Mimi, ba zan bi ku ba, ki tafi kawai” “Why? Saboda me?” Mimi ta tambaya cike da mamaki. Amatullah ta ɗaura Emjay kafadar ta, ta na mai jijjaga shi, cikin wani irin yanayi mai wuyan fassarawa, yanayi na tsantsan kunar zuciya ta ce “Ya kira ni fasiƙa, ya shegentar da ɗan sa, duk dan a dalilin na shiga motar Dee, kuskuren shiga motar ɗan uwan ki ya janyo wannan kazafin a gare ni Mimi, yanzu sai na ƙara shiga ku kai ni gida? iyayen mu su gan na fito daga motar ɗan uwan ki? Ta Yaya zan wanke kai na?” “Iyayen ki sun san wacece ke Maman Emjay, they know what their daughter is capable of doing saboda sun san sun bawa diyar su tarbiya mai kyau…” “Hakan ya sa ba zan bari daidai da second ɗaya zargi irin wannan ya gifta a zukatan su ba, na gode Mimi…..I will find my way”2 “Maman Emjay a wannan lokacin har kina tuna wani bayan ke, ba ki tunanin halin da ki ke ciki? you have to wake up and start loving your self” mimi tace tana mai danne takaicin da ya taso mata. Ba ta san me yasa mata da dama basu damuwa da ƙaunar kansu ba, a dai barsu da son zuciya (selfishness) amma sam ba su san wani abu wai shi self love ba balle self esteem. Amatullah na mai runtse idanu, murya can kasa ta ce “Go …… just go Mimi” “I’m so sorry Amatullah” Cewar Mimi kafin ta juya ta fita jiki a sanyaye. Sai bayan fitar ta Amatullah ta sami damar bawa Emjay nono, gaba ɗaya kwakwalwar ta ce ta daskare yayin da idanun ta ke kan Emjay wanda yana shan shanono ya na mai sakin ajiyar zuciya. *** Yanda ya ga Mimi ta shiga motar ta zauna jiki sanyaye ya sanya shi faɗin “How is she?” “Very hurt…..” Cewar Mimi, kafin ta juya ta na kallon Dee, cikin neman bayani ta ce “Menene dangantakar ku? What was she to you? Me ya sa mijin ta zai zarge ka da neman matar shi na aure? What is happening Dee?” Ajiyar zuciya ya saki, ya na mai wasa da sitiyarin motar ya ce “It’s a long story Mimi, Zan ba ki labari. Amma zancen neman matar shi wallahi sharri ne irin na namijin da bai san ciwon kan sa ba, Amatullah is the most decent person I know in my life, please mu tafi kafin wannan jahilin mijin na ta ya dawo, wallahi zan iya bugun shi….” “Ya sake ta!” Cewar Mimi ba tare da ta kalli Dee Yusuf ba. Ji yayi kamar kunnen sa ne ke masa gizo. STORY CONTINUES BELOW “I beg your pardon!” Cewar Dee cikin kaɗuwa. Mimi na mai jinjina kai yayin da hawaye ke zuba daga idanun ta “Ka ji ni da kyau, an saki Amatullah, that useless person accused her of sleeping with you, kuma hatta Emjay ya ce ba ɗan sa ba ne, ɗan ka ne……” “Waiyazubillah!”4 Cewar Dee ya na mai doka hannu kan sitiyari. Mimi ba ta gushe ba ta kara da “Ya ce kar ya dawo ya same ta, Amma ta ki yarda mu kai ta gida, Ni damuwa ta a yi clearing wannan misunderstanding ɗin kar ya je ya maimaitawa iyayen su abin da ya furta mata, I’m feeling very bad Dee, Ni na jawo mata, da na sani da ban ce mu je asibiti ba, da mu ka kira wayar shi bai ɗaga ba da mun hakura ta koma gida, da ban kira ka ba…..” Ta karasa maganar cikin shashshekar kuka. Motar ya kunna ba tare da ya tankawa Mimi ba, zuciyar shi ke tafasa yayinda ya ke Jin duk duniya babu jahili mara ilimi kamar Saifullahi ba. Motar ya ja, Mimi na tambayar shi ina za su je bayan sun bar Amatullah cikin halin haula’i, ya mata shiru. Tun ta na tambaya har ta gaji ta ma sa shiru ta zubawa sarautar Allah ido. *** Saifullah kuwa ko da ya fice Amaru ya wuce, zuciyar sa in ban da ƙuna babu abin da take yi, hango Amatullah da Dee ya ke a shimfiɗa, tiryan tiryan idanunsa ke masa gizo da abin da kwakwalwarsa ke sauwara masa. Da haka ya isa gidan Jamoh. Kamar yadda yake al’adar su yau ɗin ma zaune suke, su takwas ciki har da mahaifin sa da mahaifin Amatu. Bai tsaya rufe ƙofar motar sa ba ya isa garesu a firgice. “Lafiya? Me ya samu Amatullah?” Baba Anas ya tarye shi cikin matsanancin tashin hankali. “Baba Amatullah ta cuce ni, shege ta kawo min… ” wawan marin da ya sauka a fuskar sa ya sa ya kasa ƙarasawa. “Ko mutuwa na kunyan idon mahaifa balle kai sakarai gaja, kalli nan mahaifinta ne, kalle mu nan mu bakwai duk ba wanda zai yarda a ci zarafin Amatullah” Baba Anas yace cikin Dana sanin tambayarsa. “Baba wallahi bata rabu da Arnen nan ba, yau a kan ido na ya sauke ta a ƙofar gidan aurenmu” yace yana sunkuyar da kai, nan gaba ɗaya su ka ɗauki salati. “Saifullahi shin wani laifi Amatullah ta yi ma ka da za ka jefe ta wannan mugun zargi haka? Idan mai magana wawa ne ai majiyinta ba wawa ba ne” Cewar Baba Zubairu cikin adduar Allah ya sa dai Saifullahi bai san abin da ya ke fada ma. Shi kuwa mahaifin Amatullah mutuwar zaune yayi duk da kuwa ko duka jikin shi kunne ne ba zai taɓa yarda da wannan maganar ba. “Allah ya wadar na ka ya lalace! Saifullahi sakayyar da za ka yiwa zumunci kenan?” Cewar Baba Anas wanda kunyar mahaifin Amatullah ya rufe shi, ji ya ke kamar kasa ta tsage ya shige. Motar Dee da ya faka daga gefen su ne ya ja hankalin su, kallan motan su ke cikin jiran tsammani. Shi kuwa Saifullahi da ya san motar Dee ne, tsabagen idanun sa sun rufe be ma iya gane daga Dee sai Mimi ne tafe cikin motar ba, cikin farin cikin Allah ya kawo ma sa sheda har gida ya ce tsaya, “Kun ga ni ko Baba, ga shi dai kun ga zahiri ya kawo ta har gida dan rashin daraja!” Duka motar su ke kallo, da ya ke fitilar kofar gidan Baba Sasa ba ta da haske sosai dan haka ba su iya tantace wacce ke zaune gaban motar ba, shin Amatullah din ce kamar yanda Saifullahi ya ke jaddawa? Tambayar da ke yawo cikin kwakwalwar Baba Anas kenan. Shi kuwa mahaifin Amatullah adduar neman tsari daga abin da ke shirin faruwa ya ke, dan kuwa idan ya kasance Amatullah ce da tsohon saurayin ta zaune cikin motar nan, to lalle diyar shi ba ta ma sa adalci ba. Mimi da tun isar su ta ke duban Dee ta ce “Dee ina ne?” “Gidan su Amatullah…” STORY CONTINUES BELOW Ya amsa mata a takaice, kai Mimi ta jinjin kafin ta ce “Da gaske ne kenan you guys had a relationship? Oh Lord Jesus!” Cewar Mimi ta na mai dafe kai, ba ta gushe ba ta kara da ” Ohh She is the one! That Muslim girl that made you……” “Mimi babu lokaci, please za mu yi magana, for now you have to this for Amatullah, you call her a friend, da ke aka yi komai, kin ga wannan mutanen da ke zaune?” Ya nuna in da su Baba Anas ke zaune “I’m very sure uncles din ta ne, or maybe da Baban ta, ina wayar ki? Jiki sanyaye ta ce “Ga shi nan” “Ina receipt din hospital bill da ki ka biya?” Ta na mai dafe kai ta ce ya na jakar Maman Emjay. “Na so ya na gun ki, but wannan ma zai yi, I know you’re smart, I trust you, only you can clear Amatullah, please go and explain everything to them!” Cikin karfin hali Mimi ta girgiza kai, kana ta ce “Tare za mu?” Dee ya girgiza kai tare da faɗin “I don’t need to be there, you can do it” Kai ta girgiza alamar toh, kana tayi yunkurin buɗe motar. ” kun gani ko, har yanzu ta kasa fitowa tsabagen borin kunya” Saifullahi ya faɗi yana tashi kamar wani sabon hauka ya dumfari motar Dee. “Idan ka ƙara taku ɗaya Allah ya tsine maka Saifullah” Baba Anas ya ce, wanda hakan yayi daidai da fitowar Mimi. Nan Saifullahi ya tsaya ya na raba idanu domin ganin Amatullah ta fito bayan Mimi, amma babu ita babu alamar ta. Baba Anas kuwa da Mahaifin Amatullah ajiyar zuciya su ka saki a lokaci ɗaya, su na mai godewa Allah ganin watan Amatullah ce ta fito daga motar, maimakon Amatullah da Saifullahi ya ce. “Haba Anas, wai duk gaskiyan nan da ke bayyane, me ze sa makamashin nan dawowa kofar gidan nan in ba dai akwai kamshin gaskiya a maganar Saifullahi ba? Ku duba da kyau ku gani wannan arnan nan ne dai cikin motar can” Baba Mahmuda ya faɗi cikin hasala. Sallama Mimi ta musu duk da kuwa gaban ta na dukan uku uku, cikin girmamawa ta gaida su, su ka amsa suna kallon ta a kyamace. “Yarinya ke kuma daga ina?” Ba ta kai ga amsawa Baban Sasa ya aiko Hafiz da ya kai masa rahoton abin da ke faruwa da duk su shiga ciki. Dan haka duka su ka garzaya, Baban Anas ne kafin ya tashi ya dubi yarinya ya ce “Za ki iya jiran mu yarinya?” Mimi ta ce “Eh Baba, dama na zo ne kan batun Amatullah ta nan can gida yanzu haka ba lafiya…..” “Amatullah ki ka ce?” Mahaifin Amatullah wanda shi ma ɗin tsayawa yayi dan sauraron Mimi. “Ai ina ga zai fi ita ma din ta biyo mu” Cewar Baba Anas, ya na mai kallon Mimi ya ce za ki iya shigowa daga ciki. Baba Anas da Mahaifin Amatullah tafe, Mimi na biye da su haka su ka shiga ciki gurin Baban Sasa. Nan su ka tadda su Baba Zubairu zaune, Baba Anas yayiwa Mimi wacce tun shigowar su Baban Sasa ya bi ta da kallan tuhuma, wuri da setin in da Saifullahi ke zaune taje ta ɗan raɓe. Su ma din waje su ka samu su ka zauna. Baba Mahmuda da Baba Idris ji suka yi kamar su hau mimi da duka saboda kafiɗirinta. “Me ke faruwa da kuke min tallan martaba a idon duniya, a’a kai!” Baban Sasa ya ce cike da takaici yana mai bin su da kallon tuhuma. “Baban Sasa, ashe ɗan can ba nawa bane, ashe Amatullah ta daɗe tana cin amanar aure na Ban tashi sani ba sai yau, ashe shi ya sa lokacin da na ce a zubar da cikin ta ƙi amincewa saboda riban soyayya ne” ya faɗi ba tare da tunanin abin da yake faɗi ba sai da ya ga kallon da baba Anas ke watsa masa, bai gushe ba ya cigaba da fadin. STORY CONTINUES BELOW “Tun la’asar nake makarantar su don ɗauko su aka ce min ta tafi, wasu suka ce ba ta ma zo ba, na dawo gida shiru shiru kawai na fito na sanar da ku sai na ga wannan tsinannen tsohon saurayin ta kawo ta, yau dubun su ya cika” ya karasa maganar ne cikin dacin kishi. Salati Baban Sasa ya saka, ya na mai dafe kirji ya ke faɗin2 “Kai Amatullah ta ba ni kunya, Amatullah ta cuce mu ta ci mutuncin aure!” Mahaifin Amatullah ya sunkyar da kai cike da kunya da takaici. Ita kuwa Mimi jikin ta har rawa ya ke tsabagen yanda ta ke so a bata dama ta yi magana. “Baba ban tari numfashin ka ba, zai fi kyau a bi wannan lamari daki daki a yi bincike kafin yanke hukunci! Ga wannan yarinya ta zo mana da batun rashin lafiyar Amatullah, ya na da kyau a saurare ta” “Shin yaushe mu ka fara sauraran magana daga bakin bare?” Cewar Baban Sasa ya na mai kallan Mimi a wulakance. Haka ma Saifullahi wani mugun harara ya jefi Mimi da shi, cikin jandadin furucin Baban Sasa ya yi saurin fadin “Yo to wannan ai bakin su daya ma, ai dai ku na gani tare da arnen ta zo, da ita su ke bugewa suna aikata masha’an su” “Aw ku na nufin ya zo har gidan nan!” Cewar Baban Sasa cike da nuna bacin rai. Ita kuwa Mimi da ran ta ya fara baci ganin yanda su ke kyamar su kiri kiri, ba tare da jiran izini ba ta fara jawabi kamar haka “Sunana Hanna Dauda, resiting 300lvl da Amatullah ke yi ya sa na zama kawarta don na dade da saninta a matsayin mai ƙoƙari. Handout, abinci, duk Amatullah bata san su ba, duk rana duk sanyi a motar haya take zuwa duk da ɗanyen jego…….” “Dakata yarinya, wannan wani irin zancen banza ki ke faɗa mana! Ita Amatullah din ce ta fada mi ki haka? Kai Saifullahi ina gaskiyar maganar nan” Baban Sasa ne ya katse Mimi, in da duka dakin kallon Saifullahi da ya fara zufa har ta kan hanci su ke. Ya na mai girgiza kai ya shiga karyata Mimi, faɗi ya ke “Karya ta ke! Wallahi karya ta ke min babu abin da ban ɗaukewa Amatullah ba!” Mahaifin Amatullah wanda idanun sa suka cika da kwalla ne ya furta, ke mu ke sauraro yarinya. Mimi ta nisa sannan ta cigaba kamar haka “Tun last week na lura da tana wari kaɗan kaɗan duk da kasancewarta mai tsafta, Amma na kasa faɗa mata, sai ɗazu da kan ta tazo min da maganar, cewar dinkin da aka mata tun na haihuwa ya nan ya zame mata ciwo, shi ne ya ke fitar da ɗan wari……” “Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun” Cewar Mahaifin Amatullah. Baban Sasa ya kara da “Amatullah mai tsafta ce ta ke da ciwo a jiki har ya na fitar da wari? Saifullahi ka na da masaniya akan haka?” Saifullahi na mai share zufa da bayan hannun sa, shirun da yayi ya tabbatarwa ya san da wannan lalurar. Hakan ya bawa Mimi damar cigaba da faɗin “ko da mu ka je asibiti, likita ta duba Amatullah ta mana bayanin cewa ta na cikin tsaka mai wuya, muddin ba a yi mata aikin gaggawa ba, Baba a duba wayar Saifullah Amatullah ta kira shi, kusan sau biyar ta kira shi tun kan a shiga da ita tiyata, bai daga ba, da aka fito da ita na sake kiran shi, be daga ba, shi ne na tura ma sa sakon text……” “Wa ki ka kira? Wa ku ka kira? Wa ki ka turawa sakon text? Ga dai waya ta nan tun safe ta ke hannuna! Kuma in banda sharri da wata wayar Amatullah zata kira ni ita da wayar ta ta lalace kusan wata ɗaya ta wuce?” Saifullahi ne ya katse ta cikin rashin sukuni, dan kuwa dai idanun sa sun fara raina fata. Maimakon ta bashi amsa, sai ta budi na ta wayar ta ce “Malam Saifullahi halan wanna number din ta ka ce 080********” “Kwarai kuwa numbarsa ce kuwa” Baba Anas ya amsa mata, shi kuwa Saifullahi wani gumi ne ya shiga keto masa dan jin ta karanto numbar shi na karamin waya, Dan kuwa dai wannan wayar ta shi a silent ta ke tun shigar sa masallaci da ya saka ya manta bai cire ba. STORY CONTINUES BELOW “Ba ni wayoyin ka Saifullahi!” Baba Anas ya faɗa cikin umarni. Jiki sanyaye Ya mika ma sa wayoyin. “Wanne daga ciki numbar da ta kira yanzun nan ta ke?” Yayi nuni ga ɗan karamar wayan cikin ran sa ya na adduar Allah ya sa ba wuka ya dabawa kan sa ba. Baba Anas na dubawa sai ga missed calls ba adadi, ya umarci Mimi ta karanto numbar ta, ta karanto. Nan maganar Mimi ya tabbata, missed calls dai gasu nan reras, haka zalika sakon da ta turawa Saifullahi, wanda shi kan shi bai san da shi ba. Baban Sasa kallon Saifullahi kawai ya ke. Mahaifin Amatullah ne ya ce da Mimi “Yarinya dan Allah karasa jawabin ki ko ma san halin da yarinyar nan ta ke ciki” Mimi na mai gyada kai ta cigaba da magana kamar haka ” Wallahi ban san cousin ɗina ya san Amatullah ba, kiran sa kawai nayi ya zo ya cece mu don Bill dinmu 15, 000 wanda an mata aikin ne don emergency mu ka je. Baba lokacin da Amatullah ta ga Dee wallahi ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta biyo mu don ni na san da lafiyar ta lau ba za ta ko kalle shi ba, haka mu ka kai ta gida, Nan kofar gidan mu ka ga Saifullahi in da ya shiga aibantata tare da faɗi mata kalamin zargi tare da shegenta ɗan sa na cikin sa” Mimi ta karasa maganar ba tare da furta sakin da Saifullahi yayiwa Amatullah ba, tsabagen nauyin da kalmar ta yi mata. Zufa ne ya rufe Saifullahi, shi kuwa Baban Sasa hawaye ne ke fita daga idanun sa wiwi, Mahaifin Amatullah kuwa wani sanyi ne ya ratsa zuciyar sa an wanke diyar sa akan zargin da mijin ta ya ke mata. “Allah ya isa, Saifullahi Allah ya isa tsakanina da kai, ka zalinci Amatullah, ka haince ni, da ka fada min ba ka san yarinyar nan da ba mu cuce ta mun aurar da ita ga kai ba!” Cewar Baban Sasa hannu bisa kirjin sa da ke harbawa tsabagen ciwo da ya ke ma sa.4 “Saifullahi za ka gama da duniya lafiya kuwa?” Cewar Baba Anas. Baba Zubairu na mai girgiza kai ya “Ah ah kar ku masa baki, kuskure ne da aikin shedan……” “Akwai shedanin da ya wuce shi kan shi Saifullahi? Ya azabtar da ƴa, ya kuma saka mata da zargi, kazafi fa? Allah ya wadar na ka ya lalace, na dai faɗa ma ka yanda ka kuntata mata haka zan kuntatawa ita uwar ta ka mai zuga ka!” Nan fa gaban Saifullahi ya fadi, dan kuwa dai ya saki Amatullah, gashi Baba Anas na maganar ramuwar gayya. Cike da nadamar abin da ya aikata, dan kuwa be taba tunanin abin zai juye ma sa haka ba “A yi hakuri Baba, wallahilazim na rantse da Allah ban san ta je asibiti ba, ban ga kiran su da sakon wayar na su ba, wayar tawa a shiru ta ke ” Cewar Saifullahi ya na mai share zufa. “Ba ka san tana asibiti ba? Ba ka san ta na da ciwo ba har ya kai da fitar da wari? Saifullahi ai ko babu dangantaka na aure ai Amatullah kanwar ce Saifullahi” Cewar Mahaifin Amatullah cikin nuna rashin jin dadi, in da su Baba Zubairu su ka shiga tofa albarkacin bakin su. Cikin jin daɗin yanda ta wanke Amatullah, ya na duban Mimi ya ce “Yarinya ba mu san da wani baki za mu gode mu ku ba, ba mu san yanda za mu gode mu ku ba” Cikin jin dadi da gamsuwa Mimi ta bashi amsa da “Ba sai kun gode min ba ai yiwa kai ne, ni dai fata na a duba lamarin Amatullah, Allah kaɗai ya san halin da ta ke ciki….” “Bari na koma gidan yanzu!” Saifullahi ya katse Mimi yayin da ya tashi zumbul ya na kokarin sanya takalmi. “Ka koma wani gida? Mahmuda je ka dauko min yarinyar nan kafin ya je ya karasa mana ita, nan za ka zauna har sai an kawo ta babu in da za ka!” Cewar Baba Anas. Saifullahi da ya so komawa gida domin ya san yanda zai yi ya shawo kan Amatullah, dole ya dawo ya zauna. Nan Mimi ta musu sallama zuciyar ta cike da annushawa. Ganin Mahaifin Amatullah ya rakota har kofar gida ya tabbatarwa Dee haƙan su ya cimma ruwa, ko shakka babu Mimi ta wanke Amatullah, wani farin ciki ne ya mamaye zuciyar sa, wanda har sai da Mimi ta gane yayin da su ka hau hanya. Ta na mai jinjina kai ganin yanda Dee ke murmushi, baki har kunne ta ce ” By the way ka ke murmushi na san ka gane mun yi nasara, but ina bin ka bashin bayani ka sani ko?” Cike da jin dadi ya figi motar yayinda su ka hau bisa kwalta ya na mai maimaita “Na sani Mama na, na sani Mama na!” Ita ma din murmushin ta ke cike da annushawa. **** Amatullah kuwa kamar yanda Baba Anas ya ce, Baba Mahmuda ne ya je gidan, ya tadda ta zaune dai in da su Mimi su ka bar ta. Ganin shi ta san Saifullahi ya je ya faɗa mu su ita mazinaciya ce, dan haka ko da ya ce ya zo ne su tafi, ba ta tambaye shi dalili ba, tashi ta yi tana tafiya da kyar. Ba karamin tausaya mata yayi ba, ya na mai mamakin rashin imani irin na Saifullahi, yana dana sanin kiyayyar da ya ke mata ita da mahaifiyar ta, a sanyaye ya ɗaukar mata Emjay, da sannu a hankali, ya na mata sannu har su ka isa motar, ya bude mata gidan baya ta zauna. Sai da ya bata Emjay sannan ya karbi mukullin gidan ya rufe ba su zame ko ina ba sai gidan Baban Sasa. Ganin Amatullah babu wanda bai tausaya mata ba, hatta Saifullahi sai shigowar ta ya lura da yanayin tafiyar ta, wani kunya da nauyin iyayen su ne ya rufe shi, ina ma zai iya mayar da hannun agogo baya, da bai aikiata abin da ya aikata ba. “Sannu, sannu Amatullah” Kalaman da ta ke ji daga bakin iyayen ta kenan wanda shi ya ba ta ɗan kwanciyar hankali, ko babu komai sun san ba ta da lafiya. Kan katifa kusa da shi Baban Sasa ya umarci Amatullah ta zauna. Burin ta kar ta hada idanu da Mahaifin ta, bayan kazafin da Saifullahi ya mata, kuma ta tabbatar ya faɗa mu su ba ta san da wani ido za ta iya kallan sa ba. “Sannu Amatullah” Cewar Saifullahi wanda ke kallan Amatullah idanun sa cike da magiyar neman rufin asiri. Amatullah kuwa ko kallan sa ba ta yi ba bare ta san ya na wajan. Maimakon ta ji tsinuwa da la’antar da ta ke tsammani, sai ji ta yi Baban Sasa ya ce “Amatullah ashe haka mu ka cutar da ke ba mu sani ba? Mu ka aurar da ke ga mara kaunar ki? Amatullah za ki iya yafe mana kuwa?” Cike da mamaki ta daga iduna ta dubi Baban Sasa, wanda kallo ɗaya za ka masa ka tabbatar da tashin hankalin da ya ke ciki, cikin awa biyu kacal ya kara tsufa, numfashi na neman harde ma sa. Sai a sannan ta iya kallon mahaifin na ta, wanda idanun sa ke cike da kwalla. Kan ta ta sunkuyar, dan kuwa dai ba ta da ta cewa, ta faru ta kare an yiwa mai dami daya sata. Baban Sasa bai gushe ba ya cigaba da faɗin “Nan gidan za ki zauna har ki gama jinya, ba dan saki babu kyau ba da na umarci ja’irin nan ya sake ki a yau Amatullah…” Cike da mamaki Amatullah ta ɗago kai ta na mai duban Saifullahi wanda ya shiga girgiza mata kai, alamar ta yi shiru. Cikin taikaci ta ce “Baban Sasa ana yin wani saki ne bayan saki ukun da Allah ya halatta ma da namiji? In dai kuwa ba a yi ina mai tabbatar muku Saifullahi ya sake ni, ya sake ni saki uku!”4 “Innalillahi wainnailaihi ilaihi rajiun” Cewar dukkan wanda ke cikin ɗakin har da uwa uba Saifullahi, in da wani ni’ima da farin ciki ya saukarwa mahaifin Amatullah, ya na mai hamadala cikin ransa. Saifullahi kuwa na shi salatin ba na komai ba ne sai na tsoran masifar da kalaman Amatullah za ta haifa masa. Hannu bisa kirji sai ga Baban Sasa na zubda hawaye, fadi ya ke2 “Saifullahi ka shayar da ni bakin ciki, bakin cikin da tun da na zo duniya babu wanda ya shayar da ni kwatankwacin shi, Saifullahi ka cuceni ka cuci zumunci!” “Ah ah Amatullah kada ki min haka, kar da ki sanya tazara a tsakanin mu ba zan iya jurewa ba! na yi kuskuran furta saki gare ki, Amma ban fadi iya adadin sakin ba, har ga Allah saki daya na mi ki ba uku ba, Allah ya ga zuciya ta! Dan Allah Baba ku duba lamarin nan