THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 1 BY NIMCYLUV
Anties a kakkaɓe zani banso na saki ba,domin ban shirya hakan yanzu ba,amma naga kamar kun fini damuwa dashi dole nai ƙwanan zaune domin yi maku typing hope zaku amshesa kamar yadda yazu da zafinsa,ni bana da wani warning a kan book ɗin nan,abinda kullum nake faɗa kada kayi karatu danjin daɗinka ko shauƙinka,kayi karatu dan wasu muhimman abubuwa da suke cikin labarin domin zaisa ka amfana da hakan,so
dayawa wasu basu gane hakan sun ɗaukan luv ɗin ciki whatever dai ga THE NEW EMIR nan ya taɓa ko ina kada a fara karatu zai an wanke hannu kuma ansa face mars😂 ok Nimcy taku tana maku sahihiyar ƙauna
_Britol place hotel_
“for God sake” ya ƙarasa magana cikin muryarsa da bata fita sosai sabida ƙarfin mulki da kuma jinin sarauta dake yawo cikin jikinsa.
Cikin kuka da kuma takaicin rayuwarta Seenat ta kalle shi na wani lkc kafin a hankali ta janye idanunta daga gareshi,sbd sam taba jure kallo cikin idanunsa sosai suke mata kaifi tare da cika mata idanu,Allah yay masa baiwar hallitta ƙyau tsari ga kuma izza irin tasu ta masu sarauta,tabbas idan ta sameshi matsayin miji ta gama jin daɗin rayuwa tayi duk wata ɗiya mace nisa,nisa kuma mai tsayi,idan mafalkinta ya tabba tasa she move “Yes” move ɗin da babu wanda zai tadda ta,but how can that happen,bai sonta bai son ta raɓesa why ƙaddarar soyayya yaci gaba da haɗasu a wajan da masuyi tunani ba,saukar muryarsa a kanta yasa tayi saurin jan idanunta tare da mannasu a kanshi,kasa control kanta tayi hakan yasa ta faɗa jikinsa ba tare data san hakan ba,cikin kuka tace.
“zuciyana ciwo Lil Prince,sai yaushe ne zaka barni haka? Sai yaushe zaka amshe ni as ur luv i luv u,soyayyarka ƙaddarata ce dan Allah ka amshi jaririyar zuciyana pls”
Dryar mugunta yay wacce ta fitu da ɗan ƙaramin sauti,Alkabbar jikinsa ya gyara tare da murza daimond ring ɗinsa,numfashi yaja kafin ya cireta jikinsa yace.
“look Haseenatu put ur eyes ball to me, am not stupid ni ba age mate ɗinki bane daza kina yimin rubish,bazan iya sanya ki a zuciyana ba saina amshi virgin ɗinki idan kin amince da hakan fny nima a shirye nake domin kuɗi masu yawa nasa na kama wannan ɗakin,idan baki amince ba saiki shamin lpa”ya ƙare zancen yana jan numfashi mai ƙarfi.
Da mamaki Seenat take kallonsa ace mutumin da mutane suke ganin dararja yana matsayin babba ɗan sarki amma shike lalata al’ummarsa wannan wacce irin rayuwace? Mai yasa a koda yaushe manyan gari sune suke aikata zunubai a ban ƙasa kuma zunubai mafi muni,Tayaya za’a samu ƙwanciyar hankali,Mai kuɗi ya hulaƙanta talaka,masu mulki su wulaƙanta talakawansu,shugabanni su tauye haƙƙin na ƙasa dasu,mazaje su tauye haƙƙin matansu,malamai suci zarafin ɗalibansu,ƴan siyasa su lalata yaran mutane ta hanyar basu manyan drug,ya rabbi wannan wacce kalan lukutan masiface,wannan giremamman abun yafi tunanin dukkan mai tunani,yaushe za’a samu sauyi a gari yaushe ƙasa zata dai²ta a samu nutsuwa,ya rabbil izzatu ka kawo mana mafita,Ina sonshi ina ƙaunarsa ina jin zan iya amincewa da buƙatarsa Ubangiji kada ka kamani da laifin aikata Zina,ina da rauni a zuciya ban iya hqr da abinda raina sa ruhina ke buƙata…’
“Damn it” Lil prince ya faɗa yana ƙoƙarin ficewa daga cikin ɗakin,Sauri miƙewa Seenat tayi tare da kama hannunsa cikin sanyin murya tace.
“na amince indai zan samu luv and care naka”takai ƙarshen mgnar,Killer smile yay tare da murza hannuta dake cikin nasa yace “good gril” yana faɗin hakan yay sauri haɗe bakinsu waje guda ya suma ya mutsata Haseenatu kam dukkan jikinta rawa yake yayinda zuciyarta ke bada wani sauti mai tafiya da numfashinta,yayinda da take jin wani baƙin ciki yana sauka a cikin zuciyarta,sosai Lil prince ya samu nasarar rabata da kayan jikinta kana ya jefata saman makeken gadon take mamallakin hotel ɗin,babu kunyar cewa shiɗin mutum ne mai ƙima da kuma dajara a idanun mutane ya shiga aikata ta’asarsa son ransa,sosai ya muri jikin Seenat hakan yay masa daɗi,Seenat kam faɗin wahalar data sha ba’a magana,sai da yay wajan1hour sannan ya samu nutsuwa ya zare jikinsa a nata,wani mugun murmushi yay cike da mugunta yace.
_Masarautar Kano_
Gida ne na sarauta wanda ni ban isa na fasalta maku tsarin gidan ba,sai da dukkan wanda ya karanta yay tunanin tsarin gidan,sbd dukkan wani da akace sarauta ya fita daban sa sauran,kuɗi,iko,mulki,izza,da sauran abubuwa najin daɗin rayuwa,gida ne wanda idan baki bai isa yafi adadin kuɗi da aka tsareshi ba,tabbas sarkin wannan masarautar yana ji da kuɗi da iko haɗi da zunzurutun mulki wanda ya gajesa,a tarihi musan cewa babu wani wanda ya isa ya gani ya hau mulkin wannan masarauta indai ba gada yay wajan mahaifi ko kuma kaka ba,alaƙa dai mai ƙarfin gske itake sawa a gaji mulki,shin wannan Sarki gada yay ko kuma taka haye yayi? Wannan sarki mai adalci ne ko kuma azzalumi ne mai cin zarafin al’ummarsa da tauye masu haƙƙinsu kamar yadda Haseenatu ta faɗa? Shin wannan sarki halinsu ɗaya da Lil prince ko kuma aƙwai banbanci?.
Baka ganin komai cikin makeken gidan Sarautar sai barori da kuyangi haɗi da fadawa da kuma maharba haɗi da masu tsaron ƙofa,ko wanne tawaga da nau’in uniform ɗin jikinsu Farin yadi na Kuyangi,Jaa da green na Fahadawa,blue na Barori,yayinda baƙi yake na masu tsaron ƙofa.
Fituwarsa kenan daga cikin Fada wanda yanzu ne lkcn wutawarsa a gida da kuma kaɗai cewa da iyalinsa,Sanye yake cikin wata duguwar Alƙabba da kuma wanda tsarinsa daman idan yana gida bai fiya zama da babbar Alƙabba ba,shigace sosai ta alfarma mai kaɗan milk da ash,hannayensa sunji ring ɗin daimond da glod gefe guda sandar girmansa ce,ta azurfa sai ƙyalli yake,komai na turakarsa an tsara sa ne da azurfa,manyan amintattun Kuyangin sane a gefe suna masa firfita,yayinda Gilishi ke gefensa tana yanka masa Apple da kayan fruit,cikin girmamawa tace.
“Allah yana da ƙwana ya baka tsawon rai,ina ganin lkcn da za’a zaɓawa Lil prince mata yayi hakan zai ƙara maka girma idanun mutane,kafin kayi murabus na tabbas Prince lkcn ya tara zuri’a kaga dole ya gajeka ko ana so ko ba’a so,balle maganarka tamkar umarni ne a wajan talakawanka sai da baka faɗa ba,ranka shi daɗe a yafan idan nayi kuskure”ta ƙare mgnar tana ƙasa da kanta.
Murmushi yay wanda bai kai ga bayyanar haƙwaransa ba,cikin muryarsa mai amo waccw bata fita saisa gargaɗi a cikinta yace.
Uhm muna gdy Kilishi kunyi tunani mai kyau,amma bamu takurawa Prince coz abinda yakeso shi nakeso uhm farin cikinsa shine namu,amma zamuyi tunani a hakan yaka”
Jinjina kai tayi cike da gamsuwa,ciki ƙaunar mijin nata ta miƙa masa Apple ɗin data yanka,dakatar da ita yay ta hanya girgiza kai alamar bai so,kiɗan sarewa ne ya fara tashi cikin tafkekiyar wayarsa,da hannu yaywa Kilishi nuni datai picking kuma tasa a handfree,kirari aka shigayi masa wanda yake jin daɗinsa har cikin ransa kafin mai kiran yace.
“Kaga sarkin da babu kamarsa sarkin sarakuna faɗe taka cikawa tamu dukkan wanda yay ja dakai shizai ƙwana,Allah ya ƙara girma da ɗaukaka aƙwai matsala fa,idan babu damuwa a yau ina son ganinka a garinmu na Kogi domin bakina bai isa ya furta wani abu gareka ba,amma zuwanka shizai warware mana komai,nida a sanina babu wanda ya tsira a ahalin Yayanka Sarki Sufwan Sufrak dukkansu mun kashesu hatta Yarima Bilyamin bamu barshi ba,amma abinda nagani yau yay matuƙar tsoratani domin nasan allon sihirina bayan gayan ƙarya dasai nace yaymin ƙarya idan nayi laifi aga farceni ya shugabana”
Sosai Mai martaba ya shiga tashin hankali amma sbd tsaurin rai irin nasa baka isa ka fahimci komai a garesa ba,cikin murya da mulki ya gama ratsata yace “On mah way”.
*** ***
“i can’t loving u bby gril” cewar Lil Prince,zuba masa idanu Seenat tayi tana jin zuciyarta na zafi haɗi da turiri zafi baƙin cikin rabata da budurcinta da Lil prince yay,da amince dashi yaci amana kuma ya yaudareta mene makomarta wajan Ubangijinta me zata gayawa Allah idan ya tambayeta laifin data aikata garesa,tasan cewa ba komai mene Ƙaddara ba wani abun ana fakewa da itane alhalin ba ita bane,amma tasan soyayyar data ƙewa Lil prince ƙaddarace tabbas tata ƙaddarar kenan,bata da ikon hana zuciyarta abinda ta tsara,zuciya bata mutum ba,ba ƙashi kuma bata da girma,ba mutum ne ke faɗawa soyayya ba,soyayya ce ke faɗawa mutum kamar ta faɗa mata,to meye laifinta dan zuciyarta taso shi? Cikin muryar kuka tace “ka cuceni” ganshin kansa ya shafa lkcn harya gama sanya kayansa yace “i know” yawo ta haɗiye mai ɗaci tace “Allah bazai barka ba”ta faɗa lkcn numfashinta ya fara sama,nanma murmushi yay yace “i know,idan kin tashi ga kuɗi nan ƙyayi using dashi idan ƙwai buƙatan ganinki zai kiga ɗan aike”
Girgiza kai tayi cikin fitar hayyaci yace “nasan sonka shine ajalina dan Allah kaji tausayin jaririyar zuciyata,idan kabarni mutuwa zanyi” ga faɗa ya ɗaga kana yace “wahatever ba kanki farau ba,and pls kada kiyi tunanin ne mana idan bani na nemeki ba that all”yan faɗin hakan ya fice daga cikin ɗakin.
Cikin ƙaraji da fitar hayyaci irina wanda suka samu heart attack lkcn guda ɗinan ta shiga faɗin “la’ilaha ilallahu Muhammadun rasulillahi S.A.W” shine abinda yazu bakinta kafin taja wata shaƙuwa mai ƙafin gske sai kuma numfashinta ya ɗauke cak a nan jini ya shiga fita ta hancinta rest in peace Seenat😭.
Jerryna Heroine Jakadiyan tunan silili a masarautar Bilhas,My luv Autar manyan shugaban masu iya kirari a masarautar Bilhas, this page dedicated to u my guys thank you once again✋🏼😂.
*ASSALAM MY REAL FANS*
_Duba da yadda labarina na the new emir yake ƙagagge kuma ƙirƙirarre wanda banyisa dancin zarafin wani ko wataba yasa na sauya sunan masauratar cikin labarin wanda ada na saka masarautar kano ne amman duba da yadda labarin nawa yake ƙagagge yasa na juya sunan masarautar sabida ina son yadda labarin yake ƙagagge to yazama sunan masarautar ma ya zama ƙagaggene yanzu ya koma MASARAUTAR BILHAS dafatan kun fahimceni nagode_
Lil Prince na fita ya tarar da best friend ɗinsa wanda suka tasu tun ƙuruciya,Murmushi Yazeed yay kafin yace “barka da fitowa Lil Prince”gyara zaman Alƙyabbarsa yay kana ya dubi Yazeed yace “sai ina” kallon room ɗin da Lil ya fito Yazeed yayi kana ya dubesa yace “friend where is she?”taɓe baki Lil yay kafin ya fara tafiya cikin isa da gadara haɗi izza,wajan 2minutes Lil bai amsa Yazeed ba,dan haka Yazeed ya ƙara nanata masa tambayar cikin girmamawa,a ɗan fusace Lil yace”Fuck you Yazeed”girgiza kai Yazeed yay domin yasan halin abokin nasa cikin ɗan fusata shima yace”you mumu i’m care about ur life ne,coz duk macen dakai mu’amala da ita mutuwa take,koda bata mutu ba muna sawa a kasheta domin shi zaisa ka tsira da mutuncinka,and kasan yana ɗaya daga cikin sharuɗan boka idan har aka samu wata tai rar ba zaka taɓa zama SARKI ba harka ƙare rayuwanka,kuma kasan wannan shine burin mai martaba a duk lokacin da yayi murabus,so nazu ina tambayarka kana min rubish i’m not stupid da zan maka questions mara amfani amma think about that”Yazeed yakai ƙarshen maganar yana kallon Prince.
Shi Lil Prince abinma dariya ya basa,sai yanzu ya tabbatar aƙwai wanda kome ka zama a rayuwa bazai taɓa yi maka biyayya ba,jibi dai yadda Yazeed ya dage yana faɗin magana son ransa,shuru yay yana auna maganar Yazeed a ransa,dan yasan gsky ya faɗa babu batun ƙarya zuwa yanzu yay amfani da sama da mata goma kuma duk ƙarshensu mutuwa suke,yana da tabbacin Seenat ma yanzu bata raye da wannan yana ɗaya daga cikin ƙarfin ikonsa da kuma girman mulkinsa,suna suwa zuwa compound na hotel ɗin suka shiga cikin wata lafiyayyiyar mota wacce aka rubuta Lil prince 3,side ɗin baya suka shiga shida Yazeed sannan drever yaja suka bar hotel ɗin.
Sama da 1hour ba’a kawo key ɗin room 267 kuma sunga fitar Lil Prince,dan haka wata ma’aikaciyar ɗakin ta nufi cikin room ɗin domin gyarawa,mamakin ganin ƙofar abuɗe tayi tana shiga tayi saurin sakin abin hannunta sbd hango Seenat da tayi jini na zuba ta hanci da bakinta,a kiɗime ta juya zata bar ɗakin domin sanarwa da securities sai kuma ta tsaya domin bata da ikon faɗin wanda ya aikata hakan ga Seenat,ganin bata da wani mafita wanda ya huce ta taimaki Seenat yasa tayi saurin ɗauko ruwa mai sanyi ta shiga zuba mata,tare da danna ƙirjinta tana shafa tafin hannunta zuwa na ƙafarta,wajan 5minutes Seenat ta saki ajjiyar zuciya tare da sakin kuka mai ciwo,tausayinta ne ya kamata ma’aikaciyar duk da kasance warta ƙabila amma sosai take da zuciyar imani,cikin harshen nasara tace “what’s wrong with you?”Seenat tsayawa da kuka tayi kafin taja numfashi tace “Ubangiji ka isarmi,Allah ka sakawa ruhina da gangar jikina,Allah ka azabtar dashi da soyayya mai zafi kamar yadda ya azabtar da zuciyarta,Allah ka hanashi jin daɗin rayuwa kamar yadda ya tarwatsa farin cikina,Allah ka hanashi ƙwanciyar hankali kamar yadda zai hana iyayena ƙwanciyar hankali,ya Ubangiji ka tarwatsa wannan Sarautar zalunci ubangiji kada ka basu abinda sukeso,Ya hayyu ya ƙayyumu ka kawo *The New Emir* mai jinƙan talakawansa,Allah ka ɗurama Prince son abinda iƙonsa bai isa ya bashi ba,Ubangiji kaya femin kaji ƙaina kaga fartamin,zuciyana ciwo babu daɗi,Ummina kiya femin inajin kunyarki amma nafi jin kunyar mahaliccina”ta ƙarashe magana tana sakin wani kukan,Hawayena ya shiga zuba cikin idanun Emeka sbd tausayin halin da Seenat ke ciki,da ƙyar ta lallaɓata tayi wanka tare da ɗaura alwalar la’asar,ta gabatar da sallah ta roƙi Ubangiji ya fiya,tana idarwa ta saka hijab ɗinta,ta nufi wata court dake kusa da ita,tana zuwa ta basu labarin abinda ta aikata amma ta cire sunan Lil prince ciki,sanan tace tana son afidda haƙƙin Allah jikinta,sosai tabawa mutane tausayi dan haka aka yanke shawarar za’ai mata bulala tunda matsayin budurwa take,tace ta amince babu ɓata lkc aka shiga yanke mata hukunci tunda aka fara take murmushi tare da kiran Ya Gaffaru,ana gamawa ta faɗi a wajan tare da kiran sunan Allah,ruwa mai sanyi aka kawo mata ta girgiza kai alamar sam bata so,bakin tane ya shiga rawa alamar tana son faɗin wani abun,dan haka suka ƙasa kunne cikin rawar murya ta shiga faɗin “Li..li..li..,” kasa ƙara sawa tayi sbd wani abu da taji ya daki kanta cikin fitar hayyaci ta shiga faɗin kallamar shahada mutanan wajan suna tayata,tana kammalawa rai yay halinsa ya salam😭.
N.S University
A nan motarsu Lil Prince tai parking bashi da wani abu da zaiyi cikin makarantar abokinsa Yazeed shine lecture na makarantar yana ɗaukan ɗalibai sama da 100 a fannin seicology, yan zuma ya shigo sbd yana sa lecture 4 zuwa 5,direct office ɗinsa suka huce yana zuwa aka fara shiguwa bada Assignment,ana haka wata ƙyaƙƙyawar yarinya ta shigo tare da faɗin “Sir jiya banzo makaranta ba,so bansan ka bada wani Assignment ba,kuma naji kace shine matsayin exam ɗinka,ina neman afuwa a bani nayi yanzu” taɓe baki yay yace “tunda ga ɗan iska ko? Kina gida kina hutawa sai yanzu ki kaga damar zuwa kice wani na baki Assignment ko?” raurau tayi da idanu tace “No sir i’m telling u the true ne,wlh bana da lafiya kasan sanyi ya busa mu sai a hankali”jin jina kai yay tare da ƙoƙarin ɗauko wata peper gyaran muryar da Lil prince yayi ne yasa ya dakata,haɗe rai Yazeed yay yace “wannan shine year ɗinki na kammala makaranta right?”kaita ɗaga alamar eh “good, zan baki amma idan kinyarda da abinda zan faɗa”cikin murna tace “i agree sir kawai faɗi domin bazan ɓata shekaru masu yawa ba,kuma wannan exam ɗin ya rusamin plan” murmushi yay yace “zaki kasance a bed ɗina a wannan daren,so idan kin amince na yafe Assgnment ɗin zan baki mark mafi yawa cikin nasauran” a kiɗime Meema ta zare idanu cikin faɗuwar gaba tace “what sir saɓon Ubangiji fa?” haɗe rai yay yace “out! ba surutu na nema ba,amma ki tabbatar ƙin amincewarki dai² yake ta lalacewar shekara guda a karatunki is not my business is urs,dan haka the choices is urs” kuka ta fara tare da durƙushewa a wajan tace “dan Allah sir idan kuɗi kakeso zan baka,amma kada ka nemi lalata rayuwata ta abinda nafiso,karatuna shine burina kuma mafalkina,kaji tausayina kaima Ubangiji saiya dafa maka” zaro idanu yay yace “ohh nai maki kala da mayan kuɗi ko,kina son nunawa duniya ke mai kuɗi ce ko?get out from my offoce idiot!” ya ƙare cikin ɗaga murya,da gudu Meema ta fice daga cikin Office ɗin tana kuka,Murnushi Lil prince yay yace “weldone Man aƙwai kaya a wannan makarantar fa,nizan huci gida ina son ganawa da mai martaba yau kafin ya shiga tirakarsa,sallama sukai da juna kana Prince ya shige mota drever yaja da gudu suka fice daga cikin makarantar.
_Masarautar Bilhas_
Cikin sauri mai martaba ya gama shirinsa,cikin shiga ta alfarka ya sanya Alƙyabba mai ruwan ƙwai,tare da murza takalminsa na Fata irin nasu na masu sarauta komai ƙyalli yake jikinsa musamman sandar girmansa ta Azurfa,sai kuma ring ɗin gold da daimond wanda suke sanye a hannunsa na hago da kuma dama,wani ƙaramin Guro ya ɗauka wanda shine shaidar duk wani ɗan gidan sarautar,kuma dashi ake gane cewa kai jinin masarautar ne,kuma jinin BILHAS yara da manya babu wanda baya dashi indai jinin sarautar na yawo a jikinsa,indai ka ɗauke Barori da kuyangu haɗi da sauran hadiman gidan sune kawai basu da ita,yana gama shirin ya dubi Kilishi cikin muryar girma yace “ina Prince inaso muje dashi domin a ƙara yimin aiki a kansa” ya faɗa yana jan numfashi,sadda kanta ƙasa tayi alamar girmamawa tace “Ya mijina kuma sarki sarakuna mai taƙama da ƙarfin mulkinsa ka sani Lil prince kai kawai yake jira ya jima da dawowa” murmushi jin daɗi yay yace “Godiya muke Kilishi” yana gama sanya Guron ya miƙe tare dayin gaba nan Kuyangunsa suka mara masa baya,cikin nutsuwa yake tafiya a flat ɗin nasa wanda yake da nisa da fada,wani ɓangare ya ƙarasu mai shegen ƙyau wanda akayi shi da zallar azurfa,har yau yana jin baƙin cikin wannan sashin yana ƙarasuwa,wani amintaccen Sarki na ƙarnin daya huce ya tasu fuska babu yabu babu fallasa ya shiga yiwa sarki kirari,kafin yasa Remote ya buɗe tangamemiyar ƙofar flat ɗin,cikin sa’a ta buɗe nan Sarki ya umarci Kuyangunsa dasu jirasa a nan,kana ya shige ciki.
Zaune ya sameta kan wani tattausar ladduma mai ƙyau da tsari hannunta riƙe da casbaha,da sallama ya shiga yana zuwa masu kula da ita suka basu waje,cikin girmamawa yace “barka da huta Mai babban ɗaki ya ƙarfin jikin”ya ƙare yana jefa mata harara.
Hajiya mai babban ɗaki da kasance uwa ga sarkin baya sarki Sufrak Bilhas kenan,yayinda take matsayin kishiga ga Mai martaba Khalid sarki maici a yanzu kenan,Ya rasa mahaifiyarsa tun yana ƙarami shine ya ɗauki baƙi hali da son zuciya ya ɗurama kansa,tun yana shekara 15 da mahaifinsu yay murabus saiya bawa yayensa Sufrak Mulki,shi kuma baƙin cikin hakan yasa yabar garin gaba ɗaya bai dawo ba sai ranar da yayensa yay murabus ya bawa ɗansa Yarima Sudais Sufrak Bilhas,a wannan yanar kuma akayi sunan ɗan Yarima Sudais a kuma wannan ranar sarki Sufrak yabar duniya ta hanyar ciwon ciki,Satin Sudais 6 akan mulki cikin dare aka shiga aka kashesu dashi da matarsa Omehi da kuma ɗansa MALEEK(sorry da za kuji nace Bilyamin am sorry Maleek ne) wannan baƙin cikin yasa Hajia mai babban ɗaki tayi kuka kamar zata rasa rai cikin hukunci Ubangiji kuma a wannan lkcn ta samu makanta ta hanyar rasa ganinta wanda shime ba’asan dalili ba.
Mutum ɗaya ta aminta dashi kuma yasan sirrinta wato Waziri na zamanin sarki Sudais wanda aka nema sama da ƙasa aka rasa,daga ƙarshe aka sami gawarsa saman ruwa,shine ɗansa Kamal ya gaji Mulkinsa amma fa ba waziri ba,ta ɓangaren aminta dashi da Mai babban ɗaki da tayi,wannan kenan a taƙaice.
Murmushi tayi tace “A’a Khalid ne da wannan yammacin?”taɓe baki yay dan yana mamakin yadda wani tym ɗin take fahimtar yanayi,shurun da yayi ne yasa ta cewa “kana mamaki da hukunci ubangiji ko?”ɗan zaro idanu yay tare da saurin faɗin “Kamarya kenan mai babban ɗaki?” nisawa tayi tace “munata ta tunanin sanyi ya huce amma naga antashi da hunturo yau” hamdala yay kana yace “daman na leƙo do baki ne,gashi har yau kinƙi bari a kawo maki mai kula da dake sosai” fuskarta cike da haiba tace “ayya Khalid yau nake tsoro nikam na yafe domin gaba ɗaya rayuwar tawa mene yay saura” jinjina kai yay tare da ƙasa da murya yace” hakane mai babban ɗaki domin ance makashinka yana tare dakai,amma idan kasa Allah a ranka sai kaga komai yay dai²,kullum muna addu’ar Allah ya bamu ikon kula da Al’ummar mu” cikin farin ciki tace “Ameen ya samadu Allah ya kare ya kiyaye”sallama yay mata kana ya bar flat ɗin gaba ɗaya.
Yana zuwa ya ƙwashi amintatunsa na Fada tare da Lil prince aka aka kira pilot ya ƙarasu da jet domin tafiyan gaggawa sukesu zuwa gobe da safe sazu dawo,ba’a fi 5mins ba jet ya sauka suka shiga jiki cikin,da sauri pilto ya data jet suka ɗaga zuwa garin KOGI.
*** ***
Kogi state
Zaune yake gaban Boka daga shi zai bantee ana ƙwara masa jini a jikinsa tare da faɗin wasu kalmomi marasa ma’ana,sun daɗe cikin hakan faɗin a ɗauko wata ƙwarya,sosai na tsorata gani tsotsotsi cikin ƙwaryar sai mutsi suke,ɗan zare idanu nai ganin mai martaba Khalid ya ɗauki guda ɗaya ya zura jikin bakinsa tare da taunewa,kana ya ɗauki guda ya tura cikin sumar kansa,nan take wani baƙin hayaƙi ya fita cikin farin ciki Boka yace, “komai ya kammala amma sosai na tsorata ganin yadda,wani mutum kebinka kaida Lil prince hannunsa riƙe da wata matashiryar yarinya,koda na matsa bincike cikin madubina sai ya tarwatse hakan yasa ban samu damar ganin fuskar matashin ba,amma ga wani aiki zanma indai har yayi to babu wanda ya isa ya gaji mulki idan ba jininka ba,koya hau saiya mutu”cikin farin ciki mai martaba Khalid yace “mun baka dama” gyara zama Boka yay sannan ya haɗa wani garin magani yace “za’a samu ƙaramar yarinyar mai shekaru 17 zuwa 18 amma ta kasance ƙyaƙƙyawace ajin farko kuma mai tsarin halitta kuma wacce magana bata dameta ba,idan aka samu yarinyar zaka bata kulawa na kimanin sati 2 kana saika ƙwanta da ita,amma kafin jikinka ya shiga nata dole ka cusa mata wannan maganin a ƙasanta.
*_Kun shirya nima na shirya tsaf idan baku shirya ba ya kamata a kakkaɓe zani a gyara zama,magana ake da ƙarfin mulki,magana ake ta matsalolin makarantun university,magana ake akan kuɗi,magana ake ta abinda ke faruwa a wannan zamanin😟😍ku biyoni domin jin yadda allura zata tuno garma,duguwar tafiya ce inji AUTAR MANYA,kada a baki labari kada a baka labari,wanda na kewa ba dai² ba yay hqr bayin kaina bane aikine yazu da hakan,dan nasan zan farantawa wasu kuma zan baƙanta ransu buy i don’t care ina tsaya akan ra’ayina banyi dancin zarafin wani ko wata ba,SARAUTA kaifi ɗaya ce👌🏻idan nai gaba bana baya da yardar Lillahi wahidul ƙahhar,afuwa😂idan na fara surutu ban iya tsayawa ne yasin kusan san magana ta masu Sarauta amma Allah ba wasa aƙwai ƙalubale babba🙁😒_*