THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 10 BY NIMCYLUV
Faɗin “Ya salam”
sai kuma ya ƙara runtsa idanunsa da ƙarfi fiye dana baya,yayinda ya kejin wani sanyi na ratsa saman fatar jikinsa zuwa cikin namansa jikinsa,baki yatsa ya datse teeths ɗinsa da suka ɗan soma ƙara suna bada wani ƙaramin sauti.
wani irin girma yaji kansa yay masa tare dajin laɓɓansa sun masa nauyi fiye da ko wanne lkc,a hankali yaji nutsuwa na ratsa cikin zuciyarsa zuwa gangar jikinsa,wata izza da gadarace yaji ta saukar masa lkc guda har yana jin sam bazai iya buɗe idanunsa bare da buɗe bakinsa harya samu damar faɗin wani abu.
dukkan yadda ya kejin kansa a wannan lkcn ya huce tunanin dukkan wanda yake wajan,sosai yake jin kansa yay masa girman gaske tamkar wanda aka ɗurawa dutsen dala.
tabbas a wannan lkcn babu abinda yake tunani cikin ransa sai iyayensa,lallai ya tabbatar kuma ya amince Ubangijine kaɗai zai iya tsare bawansa a ko wanne hali,shine kaɗai zai bashi kulawa da kuma kariya,koda wasa kuma ko amafarki mai taɓa tunanin ya haɗa jinin da wata aba sarauta ba,bare harya saka ran zai sama sarki.
Allah buwayi gagara misali kenan,maiyin komai a kuma lkcn dayaso,komai na rayuwa yana da iyaka kuma yana da ƙarshe kamar yadda ƙaddara take da nata lkc’n.
qaddara ta juya rayuwar zuwa baƙin ciki,damuwa,takaici ta kuma sanyashi a halin daya san babu wani ɗan adam daya isa ya fiddashi sai Ubangijin daya nufa abin zai sameshi.
rayuwa kenan kana taka Allah yana tashi kuma ta sane gsky,yasu ace koda sau ɗaya yaga fuskar iyayen nasa,yasu ace ya rayu dasu irin rayuwa ta har abada ɗinnan amma babu yadda zaiyi,zaita ƙoƙarin ganin ya nema masu gafarar Ubangiji.
numfashi yaja a hankali kana kuma ya taune jajayen red lips ɗinsa.
wacce hanya mahaifinsa yabi ya gudanar da mulkinsa har jama’a suke sonsa?tayaya ya iya sauke haƙƙin al’umar da suke kansa?shi sam bayajin zai iya wannan abun kula da al’umma wanda baka isa kasan adadinsu ba ƙaramar masifa bace.
a zahirance sun haifeshi ne kawai amma a yanzu bashi da wani mahaifi kuma jigonsa sama da Abbunsa,shine komai masa haka kuma shine jin daɗinsa da kuma farin cikinsa a koda yaushe.
a hankali kuma cikin nutsuwa ya fara ɗaga lashes ɗin da suke ƙwance samar idanunsa harya samu nasarar ware manyan idanunsa wanda sukai jaa har wani ruwa-ruwa suke sabida damuwar da yake ciki.
kallonsa ya sauke zuwa ga Abbu,inda shima Abbun shi yake kallo aka samu sa’a suka haɗa idanun cikin son ƙarfafa masa quiwa ya jinjjina masa hannu tare dayi masa murmushi.
ƙwaɓe fuska yay tare da langwaɓar dakai,tunawa da yay basu kaɗaine a wajan ba yay saurin dai-dai ta nutsuwarsa tare da haɗe ransa a dole bai son abinda ake ƙoƙarin ɗura masa nauyinsa.
hakan ya ƙara masa kyau sabida wasu bai yanar manyan beauty points ɗinsa,a hankali ya sanya hannunsa ya shafi ƙwantaccen baƙin beard ɗin da yaywa ƙyaƙƙyawar fuskar ƙawanya.
daimond ring ɗinsa ya zuba idanu ganin yana haske pouting lips ɗinsa yay sabida jin zuciyarsa ta buga da ƙarfi wanda yay dai-dai da buɗewar baƙinsa cikin ƙasa da murya yace.
“My Rinaaa whare are you,i was looking for you but i can’t found you”
ya faɗa yana mai ƙara taune laɓɓansa wanda ya kejin sun ɗan jige sabida yawon bakinsa daya sauka kan lips ɗin.
Sarkin fada,da sarkin sakar gida ne suka ƙarasu inda yake zaune suna zuwa suka fara ƙoƙarin sanya masa wata lafiyayyiyar alƙyabba.
Mai martana Khalid mai murabus ne yace.
“kafin ai ƙoƙarin ɗurashi bisa wannan kujerar yana da ƙyau shima ya kawo shaidun da zasu sanya ai masa wannan naɗin,kamar yadda aka buƙaci sauran suyi”
“mene kakeci na baka na zuba yanzu nake ƙoƙarin kawo kayan sai kuma kayi saurin tarar numfashina”
cewar Abbu wanda ya faɗa yana ɗan tafa hannayensa guda biyu nan take wasu mutane guda biyu suka shigo ɗaya mace ɗaya namiji,cikin sauri da kuma ɗaga murya haɗi da gigicewa Lil prince yace.
“Meyrah!!”
wani shu’umin murmushi tayi masa haɗe da juya ƙwayan idanunta akan fuskarsa,sosai yay farin cikin ganinta da sauri ya ƙarasu inda take tsaye yace.
“Meyrah bani wannan ring ɗin ko mene kikeso zan maki amma ki bani wannan zoben shine farin cikina da kuma jin daɗina gsky am happy to see kin dawo akan lkcn kafin komai ya ƙaremin”
far tayi da idanunta kana ta sanya hannu ta zaro zoben daga jikin hannunta kamar zata miƙa masa zoben sai kuma tayi saurin baya da hannunta.
da mamaki ya kalleta tare da faɗin.
“bani mana saiki faɗi kuɗin da kikeso na maki matsayin bansar zoben”
dariya tayi kaɗan tace.
“what the think ahaa kana tunanin na dawo ne sabida na baka zoben ai dana baka gwamma nayar a bola”
baki ya saki yace.
“amma mene ya saka hakan bayan kinsan wanene ni da kuma tarayyar dake tsakaninmu”
tako ɗaya biyu tayi zuwa gabansa kana tace.
“ba kayi tunanin yadda na shigo rayuwarka lkc guda ba,shin ba kayi tunanin yadda nasan komai a kanka ba?bakai tunanin yadda ina zuwa nace ina son wannan zoben ba? lallai ƙaramar ƙwaƙwalwa gareka da kuma ƙarancin tunani,nai mamaki yadda koda wasa baka taɓa tuhuma ta da wani abunba,sannan bakai tunanin tunda muke ban taɓa yadda ka kusancan ba? na baka dama a wannan karan ka tambayi dalili”
gaba ɗaya launin idanun sane suka sauya kala wani sabon tashin hankali ya ƙara shigarsa ga kuma baƙin cikin rashin kujerar daya daɗe yana muradi da kuma son mallakarta.
tun yana ƙarami aka sanya masa son mulki cikin zuciyarsa.
cikin wata iriyar murya wacce take nuna zallar damuwar da yake ciki yace.
“why mene ya sanya kika aikata hakan wacece ke?”
“I’m Senat’s sister!!”
da sauri yay baya tare da sanya hannu ya dafe kansa sabida da sara masa da yaji yayi lkc guda.
cikin ruɗewa da kuma tashin hankali yace.
“mene yasa kikaimin haka me yasa kika rabi da abinda zai zamemin garkuwa a rayuwata?”
dariya tayi masa.
“tabbas na shigo rayuwarka da niyar ɗaukan fansa,idan nace fansa ina nufin fansar ran ƴar uwata,bana da ƙarfi ko kuma ikon da zan kaika court hakan tasa na hqr bawai dan abin baya damuna ba,aa kuma ina ƙwana ina kuma tashi da tunanin yaya zanyi na ɗauki fansar ran ƴar uwata,haka na tattara komai a gefe harna samu nasarar zuwa Cameroon da niyar karatu,satina guda kenan na ziyarci super market a nan na haɗu da da wannan mutumin..”
ta nuna Abbu kana taci gaba da faɗin.
“nan naji yana waya kuma a ciki naji yana faɗin masarautar bilhas,sosai mai mamaki banyi ƙasa a quiwa ba naje na tambayesa ko yasan wani a masarautar anace masa Lil prince,da mamaki ya kallan yace meme haɗinki dashi,nan na gaya masa komai sabida a ranar da Senat tabar gida ta ajjiye wasiƙa kuma ta rubuta inda zata hakan tasa koda maga gawarta babu wanda nai tunani sai Lil prince,nai yagamin komai na masarautar bayan na gaya masa qudirina,nan shima ya bani labari Yarima Maleek sosai naji tausayinsa hakan tasa na ɗauki niyar taimakonsa,dan haka da niyar abu guda biyu nazo wannan masarautar,wata rana idan baka manta ba kaje kasha giya kazo kana bani labarin irin tsanar da kaiwa Saifu wanda baka san cewa shine Maleek ba,kuma tun kafin nan daman nasa matsayin zobe hannunka domin a sanda naga zoben nasan akwai babban abu a tattare dashi hakan tasa na nemi kabani kai tsaye,yawwa yadda akai nasan inda kake a wannan lkcn shime wannan mutuminne ya faɗamin”
tsayawa tayi da maganar tana ƙara wani murmushi wanda yake ɗauke da mugunta tace.
“nasan zakasu kasan tayaya akai Yarima Maleek ya tsallake tarkon daka kafa masa?,a wannan daren naji komai da kake faɗa sabida a make kake,sosai na shiga tashin hankali bayan bacci ya ɗauke na tashi da sauri na nufi part ɗinsa cikin tsoro sabida babu kowa a lkcn sai masu tsaron ƙofa,a haka harna samu ma ƙarasa part ɗin cikin tashin hankali na shiga parlour’n sabida ganin ƙofar a buɗe tunanina sun riga da sun aikata abinda ka turosu,saidai ina zuwa na same zaune akan dadduma da alama salla ya idar,nan na shaida masa abinda yake faruwa kuma na roƙi alfarmar kada ya ƙwanta a ɗakin,kasan cewar bai son yawan surutu da hayaniya ya sanya ya jinjjina min kansa tare da nunamin hanyar fita daga nan bansa yaya akai ya tseratar da kansa ba”.
lumshe idanu Maleek yay lkcn da Meyrah ta gama bada labarin,kana ya waresu akan fuskarta haɗe ta taɓe baki can cikin ransa yace.
“parrot”
a zahiri kuma gyara zama yay tare daya mutsa fuska domin ya fara gajiya da zamansa a kan kujerar,ware red lips ɗinsa yay yace.
“kina fita nima na miƙe kai tsaye bedroom ɗin na nufa na kera manyan pillow kana na lulluba masu barko,ina cikin haka naji ana taɓa ƙofar cikin sauri na shige cikin toilet tare da rufewa na sanya key,a haka naji tafiyarsu har cikin bedroom ɗin nan na leƙa kaina domin har yanzu ban wani tabbatar da abinda kika faɗa,cikin mamaki kam naga wasu manyan mutane gaba ɗaya sun rufe fuskarsa,ina nan tsaye ina leƙesunta ta cc tv camera har suka fiddo da wannan injection ɗin,a tunaninsu sun ɗauka nine hakan ta sanya suka caka allurar kai tsaye suna gamawa sukai waje ba tare da tunanin duba wanda yake ƙwance ba,dana tabbatar sun tafo saina fito a nan naga sirinjin allura cikin sauri na ɗauka kasan cewata babba likita mai zaman kansa ban wani sha wahala gane wacce allura bace,sunsu haukatani irin haukan da wahala mutum ya dawo hayyacinsa,nan na ɗauki sirinjin na adana cikin box ɗita sabida ta zama evedance gareni,washe gari da sassafe ko salla banyi ba nayi wanka tare da al’wala na fice daga cikin masarautar gaba ɗaya,direct Bristol place hotel na shige na kama ɗaki a nan nayi salla,bayan na idar nayi wanka na sauya kayana zuwa dark blue ɗin gezna sabida sanya ƙananun kaya baya tsarina,ina kammalawa naji wayata na ringing nan naga number Abbu a nan ya shaidamin alrdy ya sauka a bilhaa bayan yabi ta Kogi,nan na faɗa masa inda nake harnan hotel ɗin ya saman,yana zuwa shine wannan tazo”
wata ajjiyar zuciya mai ƙarfin gaske sabida jin numfashinsa na fisga dalilin dugun maganar da yayi,kana kuma ya lumshe idanunsa har yanzu itace a ransa yana nanne kawai amma zuciyarsa tana gareta.
baya jin zai iya jure rashinta kusa dashi a koda yaushe a kuma ko wanne lkc yana jin kansa kamar bashi ba,kewarta sa kuma rashin inda zai sameta ya addabi zuciyarsa da kuma gaggar jikinsa.
shuru Lil prince yay saima sunkuyar da kansa yay yayinda yaji wata matsananciyar kunya ta kamashi.
Mai martaba kam mamakine ya kamashi ganin har yanzu babu abinsa ya sami Yarima Maleek duk daya shafe wajan 30minutes zaune akai.
mutumin daya shigo tare da Meyrah ne ya yaye abinda ya rufe fuskarsa dashi,da sauri Mai martaba ya zare idanunsa cikin ɗaga murya yace.
“Dauwas!!”
murmushi Dauwas yay yace “kana mamaki da ganina ko,a zahiri ni yaron bokanka Gilmas ne,amma a baɗini Wannan mutumin na kewa aiki..”ya nuna Abbu kana kuma yace”ka kawo wata yarinyar masarautar nan,kuma ka buƙaci Gilmas ya juyar maka da tunaninta ta yadda zata manta wacece ita,nayi amfani da wannan damarne nima nayi aiki da abinda na koya wajan Gilmas na tura wani aljani jikinta wanda zai bata kariya,a wannan lkcn’ne kuma aljanin ya fara aiki ta hanyar ƙwashe takobi da kuma hular masarautar dukkan abinda take ina ganinta ta cikin allon tsafina,kuna hatta faɗuwar da Yarima Maleek yay a hawan kilishi Gilmas shine sanadi,kuma rashin sanin an bawa Yarima Maleek dokin da mahaifinsa Sudais yafi ƙyauna sama da sauran,muna zuwa bilhas yanzu haka babu inda na tsaya sai lambun da kayan suke barima kaga shaida”yana faɗin hakan ya fita waje babu jimawa ya dawo hannunsa ɗauke sa tsuhuwar aƙwatin..
girgiza kai kawai Abbu yay yace “toya kaji wannan tarkon? bana jaa da mutum idan nasan ban shirya ba,kamar yadda ka hana idanuna bacci na ɗauki alƙwarin nima saina hanaka farin ciki da muradin rai da zuciyarka kuma..”
“dakata malam baka da hurumin da zakazo gaban mahaifina kana faɗin wannan shirman kuma nayi alƙwarin ɗaukan fansa akan abinda kayi mana zaka ganw cewa shayi ruwa ne idan harni ɗan halak ne wlh sai naga bayanku gaba ɗayanku”
Lil prince ya katse Abbu ta hanyar faɗin hakan,cikin tsawa da kuma ƙarani Abbu yace.
“da kata haka nan kada ka fusatani na faɗi abinda banyi niya ba”
tsaki Lil prince yay tare da ficewa daga fadar gaba ɗaya,shuru ne ya biyo baya a fadar ganin duk maza ne a cikin fadar ya sanya Meyrah fita daga ciki,direct kuma part ɗin Mai babban ɗaki ta nufa.
cikin nutsuwa aka zurawa Yarima Maleek lafiyayyiyar alƙyabbar kana aka ɗura masa wata ƙwatacciyar hula ra zallar azurfa sai sheƙi take,cikin nutsuwa da kuma kamala aka fara naɗata masa wani ƙyaƙƙyawan farin rawani mai zaiba,sosai aka ɓata lkc wajan naɗanin rawanin wanda ya kasance mai kunnuwa biyu irin na sarakuna,baya nan aka ɗauki wata takalmin fata mai ƙyau na aka sanya masa a ƙafarsa,sandan girma na azurfa aka danƙa masa a cikin hannunsa,shidai kawai da idanu yake binsu domin jin abin yake tamkar amafarki yana jin kamar bashi ba.
sarkin fada ne yace “masha Allah zan faɗi abu saika mai-mai ta”
i danunsa a lumshe yake yana sauraron abinda sarikin fadar yake faɗa,ware manyan gajiyayyun idanunsa yayi cikin wata zazzaƙar muryaraa mai fidda wani cool sound voice yace.
“NI SARKI MALEEK SUDAIS SUFRAK BILHAS NA AMINCE KUMA NA YARDA ZAN KULA DA TALAKAWA BISA DUKKAN GASKIYATA DA KUMA AMANA,NAYARDA ZAN KULA DA LAFIYARSU,DUKIYOYINSU,KUMA ZAN GIRMAMA RA’YINSU ZAN ZAMA JAJIRTACCE TAKO WANNE FANNI WANNAN RASUWA DA AL’KURANI MAI GIRMA”
gaba ɗaya wajan aka ɗauki kabbara cikin girmamwa aka fara zubewa gabansa ana ƙwasar gaisuwa da kuma jinjina,dake sarautar a jinin cikinsa yake hakan ya sanya baya iya amsa gaisuwar saidai kawai ya jijjina kai ko kuma ya lumshe idanunsa,sai sarkin kirari dake faɗin “an gaisheku sarkim sarakuna mai adalci na gdy”
“Allhamdulillah” Abbu ya faɗa lkcn da wasu hawaye masu zafi suka sauka daga cikin idanunsa zuwa kan fuskarsa,sosai yake farin ciki da sauke haƙƙin daya ɗurawa kansa.
wajan SARKI MALEEK ya ƙarasu tare da ƙoƙarin zubewa gabansa,da sauri SARKI MALEEK (SAIFU) ya zabu daga kan kujerar mulki ya durƙoshe gaban Abbun nasa tare da ɗura kansa bisa cinyar cikin murya mai raunin gaske yace.
“idan kowa zai zube gabana na hqr banda kai Abbu kai rayuwatace kaine mahaifina gaba da baya dan Allah kada ka sake nine nake da ikon kaisheka bakai ba,idan kace zakai haka babu shakka zan hqr da wannan mulkin”
girgiza kai Abbu yay ba tare da yace komai ba sai bubbuga bayan SARKI MALEEK yake sabisa jin yana sauke ajjiyar zuciya hakan kuma ya nuna masa cewa rauninsa ke son bai yana.
ciki ƙasa da murya yace.
“shikenan my love ban ƙarawa Ubangiji ya tayaka riƙo kuma ya baka ikon sauke haƙƙin al’ummar daya rataya a wuyanka”
pouting lips ɗinsa yay tare da zame jikinsa daga na Abbunsa,nan ƴan jarida suka fara ɗaukan sabbin labarai da kuma tare photona tun a cikin masarautar aka fara sakin labarai na naɗin *THE NEW EMIR* da akai.
miƙewa Sarki Maleek yay tare da gyara zaman alƙyabbar jikinsa cikin isa da kuma gadara haɗi zallae izza wacce ta gama ratsa jinin jikinsa ya fara tafiya zuwa waje,ganin haka ya sanya fadawa mara masa tare da rufesa ta gama da kuma baya,tsayawa yay tare da ɗaga masu hannunsu kana kuma ya girgiza kansa alamar baiso,haka suka tsaya shi kuma yaci gaba da tafiya zuwa part ɗin Mai babban ɗaki a hankali ya kewa Abbunsa bayani da kuma mitar shifa an takurasa aka nemi matsa masa za’a nemesa a rasa a garin gaba ɗaya.
shidai Abbu dry kawai yake domin yasan yaron nasa da mifa idan baiso abuba.
a haka suka ƙarasa sashin Mai babban ɗaki da sauri hadimi Kamis kuma mai tsaron ƙofar Mai babban ɗaki ya ƙarasu gaban Abbu yana zuwa ya rungome mahaifinsa wanda ya kasance uba a garesa,cikin farin ciki shima Abbu ya rungomesu.
sosai suka bawa Sariki Maleek tausayi ta dalilinsa wannan soyayyar ta rabo,dalilin kula da rayuwarsa ya banzatar da rayuwar tilon ɗansa,lallai wannan sadaukarwa ba kowa zai iya yinta ba.
ganin kallon da yake masu ne ya sanya Abbu ya raba jikinsa dana ɗan nasa,shima Kamis wajan Sarki Maleek ya ƙarasu zai durƙosa da sauri Maleek ɗin ya riƙe hannunsa kana ya jawoshi jikinsa cikin ƙasa da murya yace.
“you are my bro no nees kayi hakan kaji”
jijjina kai Hadimi Kamis yay kana ya sanya remote ya buɗe masu ƙofar hannunsa Maleek ya riƙe a tare suka shiga cikin parlour.
a zaune suka sami Meyrah da kuma kuyanga Kulsum sai kuma Hadima Kaltume.
ɗan juya idanunsa yay ganin baiga wacce yake son gani ba.
daga bayansa yaji an rungomesa lumshe idanunsa yay sabida wani sanyi da yaji ya saukar masa a zuciyar.
cikin farin ciki tace.
‘lale marhabika jikana farin cikina taurarona abin alfaharina,wai duhun dake cikin rayuwar yakau yayinda haske ya maye wanann gurbin”
da mamaki yake kallonta ganin yadda idanunta suke a buɗe tamkar bata taɓa makanta ba.
“ka daina mamaki daman haka tsarin sihirin yake sai lkcn da jininta ya amshi sarauta sannan idanunta zai buɗe”
sosai Sarki Maleek yaji daɗin hakan jikinta ya shige yana Allah tasbihi cikin ransa shi kaɗai yasan farin cikin da yaji da ganin Ammin tasa,ashe yana da rabon ganin jininsa a duniya.
hannunsa ta kama tare sa zaunar dashi akan wata lafiyayyiyar kujera cikin ƙaramin lkc aka cika gabansa da kayan marmari.
bayan sun ɗan gaisane Abbu yaja numfashi kana ya kalli Sarki Maleek yace .
“sai maganar auranka”
kallonsa kawai yayi ba tare da yayi magana ba,can ƙasan ransa yana mamaki abinda ya sanya Abbun yace haka bayan yafi kowa sanin halin da yake ciki da kuma wacce yake so.
abinda ya jine a yanzu ya sanya shi saurin ɗago kansa domin tabbatar daga ina maganar ta fito.
gyara zama Abbu yay yace.
“babu ruwana daka shirya ko baka shirya ba aldy na zaɓa maka Meyrah matsayin mata saika shirya zama ango nan da ƙwana uku…
*_(Yadaa mutum ya keso ba hakan ke kasan cewa ba,kamar yadda qaddara bata shawara damu yayin shiga rayuwarmu,naso na ida labarinan kafin ramadan amma ubangiji bai nufa ba,sai dai duk da hakan yaci gaba da posting a ramadan tunda raguwar pages ya rage mana masu comment ina gdy marasa comment dan Allah ko babu yawa kunayi hakan yana faranta raina,kullum ina ƙwashe 3hours zaune ina typing a hakanma idan ban tashi ba,gaba ɗaya comment ɗin baiyi 5minutes ba,wlh nayi busy fiye da tunaninku a kullum sai dare nake samun damar typing banda wajan aiki da nake zuwa ga wajan yarana na NGO so abun duk sai hqr🙌🏼🤝🏻)_*
Saukar maganar yaji tamkar ruwan sama wanda ba’a shirya saukarsa ba,kallon Abbun yay kawai ba tare daya samu nasarar faɗa masa wani abunba,tabbas bazai taɓa ja da maganar wansa yake ganin bashi da kamarsa ba,domin hakan kamar butulcine washi ɗin.
ya kula dashi tun yana ƙarami ya basa ci da kuma sha,tayaya zai iya bijirewa buƙatarsa ta son ya auri wata muradin zuciyarsa ba,tabbas bazai iya jure rashinta kusa dashi ba,yana jinta tamkar jinin dake guduna a cikin jijiyoyinsa.
hakan na nufin tasa ƙaddarar soyayyarce tazu masa a haka ba tare daya sani ba.
ƙwarai da gaske bazai taɓa iya sauke nauyinta garesa ba,hakan kuma kamar ya cutar da itane musamman idan akai duba da yadda abun yazo masa ba tare daya shirya ba,babban abun kuma rashin soyayyarta da babu cikin zuciyarsa.
numfashi yaja mai ƙarfi tare da sauke ajjiyar zuciya hannu yasa ya gyara zama alƙyabbar jikinsa,cikin wata ƙasaitacciyar murya mai sauti da kuma daɗin sauraro yace.
“Auran Meyrah matsayin mata gareni na nufin buɗewar wasu sabbin qaddarori a cikin rayuwata,zanzo ace Abbu ka fahimci yadda zuciya a koda yaushe take bugawa a dalilin soyayarta,zanso ka fahimci ƙunci da kuma raɗaɗin da zuciyata take a dalilin rashin mahaɗinta,Abbu ina son ka fahimci sauyawar ruhi da kuma ganggar jiki da suke dalilin rashin abokiyarsu,ina sonta inaji kuma bazan iya zama da wata ƴar mace ba saɓaninta,Abbu ka fahimci zuƙatan zuciyoyi guda biyu kada ka rabasu ta hanyar tirsasani na auri wata ba Rinaaa ba,wlh bazan iya sauke dukkan nauyinta dake wuyana ba,kuma dalilin hakan haƙƙinta zan ɗauka domin itama macace kuma tasan menene aure Abbu dan Allah ka fahimceni ka janye maganar wannan auran banso”
shafa hannunsa Mai babban ɗaki ta kama tare da riƙesu gam cikin nata hannun,wata soyayyar jikan natane ta soma ratsa dukkan wata gaɓa da kuma sassan jikinta haɗi da kuma zuciyarta,tana jinsa tamkar ɗan data haifa a cikinta wato Sudais.
gefe guda wani tausayinsa ta keji domin tasan ba zata iya sama masa abinda ya keso ba,komai hqr da kuma juriyar mutum indai yana ɗauke da zazzafar soyayya a cikin zuciyarsa za kuga komai nasa nada banne yana yinsa tamkar ba sauran mutane ba,zai zamana juriya da kuzarinsa nayin ƙasa yayinda zai kasance vry weak.
numfashi ta sauke tare da murza tafin hannunsa cikin ƙasa da murya kasan cewar tasan bai son haniya da kuma surutu ya sata faɗin.
“Hausawa sunce abarwa rai abinda ya keso sai komai yazo da sauƙi,amma anayin hakanne idan aka tabbatar da cewa wannan rai ɗin tabbas zai samu abinta yake muradi da ƙauna,shin tayayane za’a iya zuba ruwa a cikin rariya harya zauna?tayaya mutum zai rayu babu iskar shaƙa?tayaya zuciya zatai aiki bayan numfashi da take amfani dashi a yanzu babu?…”shuru tayi na ɗan wani lkc sai kuma ta ɗura da faɗin.
“tayane MALEEK zaici gaba da takon son abinda yasan bazai sameshi ba?,wacece ita? ina take? ina zaka sameta duk baka sani ba?to kana tunanin zamu barka cikin ƙunci da kuma haɗi da kaɗaicinta,ka sani kakai matakin da zaka ajjiye iyali kamar kowa kuma wannan yarinyar da kake magana koda ka sameta zai wahala su amince su baka aureta domin tayi ƙanƙant….”
ka tseta yayi ta hanyar ware narkakkun idanunsa a saman fuskar Abbu kana kuma ya juya ƙwayar idanunsa zuwa ga Mai babban ɗaki,pouting lips ɗinsa yay yana jin zuciyarsa na breating kamar zata fiddo waje cikin wani cool sound yace.
“Rainonta zanyi”
gaba ɗaya suka zuba masa idanu musamman Abbu da yafi kowa sanin wanene Maleek da kuma abinda yake so,kuma da lalurar dake tare dashi.
shi kansa zaiso ace ya samu wacce ya keso,amma yasan hakan ba mai yiwowa bane domin a yadda Mai babban ɗaki ke magana ya tabbatar ba zata iya ɗauke buƙatar gwarzon namiji maiji da ishasshiyar lafiya kamar Maleek ba,ya tabbatar dukkan wacce Maleek zai amshi virgin nata ba ƙaramar wahala ake sha ba,ga yarinya mai ƙaranci shekaru irinta ai sai yayyon fitsari ya kamata ta dalilin hakan.
numfashi ya sauke wannan shine karan farko da bazai iya samu ya bawa Maleek ɗin abinda ya keso ba,yana jin hakan kuma a matsayin babban lamari ya san cewa a yadda Maleek ya ɗaukeshi ko Mai babban ɗaki bazai iya sharing damuwarsa da ita sai shi ɗin daya zame masa GARKUWA.
Danne abinda yake ransa yay kana kuma ya gyara zama yace.
“Eh zaka iya ranonta kowa ya san da hakan,amma shinkai baka tunanin kanka da kuma abinda kakeso?kana buƙatar samu lafiya mai inganci kuma wannan yarinyar ba zata iya sama maka ita,kuma muna buƙatar ganin yaranka kamae yadda muke ganinka a gabanmu,ka ɗauka mun amince tayaya zaka sameta? shine abin tunanin alfarma guda zan iya yi maka Maleek zaka auri Meyrah idan yaso kaci gaba da nemanta ita yarinyar idanka sameta mun amince kayi aure da ita a karo na biyu”
tunda Abbun ya fara magana idanunsa a lumshe yake har kawo yanzu daya gama,ware laɓɓansa yay ba kuma tare daya ce wani abu.
a sanyaye kuma a kasalance ya miƙe ya nufi part ɗin da Mai babban ɗaki ta kaisa ƙwanaki.
cikin nutsuwa da kuma kamala yake tafiya harya kusa zuwa part ɗin sai kuma ya tsaya cak kamar wanda yaga wani abu,mai makon ya amsa masu waccan maganar sai yace.
“bana iya zama a part ɗin da wasu ƙazama suka gudanar da mulkinsu,itama fadar dan babu yadda na iyane,ina son nan da gobe a gyara part ɗin…”fesar da numfashi ta hanci mahaifinsa zaice amma yana jin kunyar idan Abbu kana kuma baison da wanne suna zai kira shi mahaifin nasa dashi ba.
gyara tsaiwa yay tare da covering jikinsa da alƙyabbar yace.
“part ɗin Daddy sannan fadar a sauya mata tsari ta hanyar zuba sabbin abu a sanarwa da sarkin fada haka,bro kuma daga yau yabar tsaron ƙofa shima ai ɗan uwane mai ƴanci”
yana faɗin hakan ya shige cikim part ɗin ba tare daya jira abinda zasu faɗa ba.
wani ƙayataccen murmushi Mai babban ɗaki ta sauke yau jinta take wani fresh kamar babu abinda yake damunta.
“Abbun Maleek sai a fara shirye-shiryen bikin nan da 3days ko,za’a haɗa da bikin naɗinsa idan babu takura”
kaiya jinjina mata ta hanyar girmamawa kana ya miƙe tsaye yace.
“Allah ya ƙara maki lafiya yanzu kam domin dama shirye-shirye sunyi nisa da kuma irin event da kuma al’adun da za’ai a bikin domin dole duniya tasan da zaman bikin tun a safiyar yau na buga invitation tare da manyan photonansa wanda na tura yanzu da akai masa na naɗi,na tabbatar zuwa yanzu labarin bikin SARKI MALEEK SUDAID SUFRAK BILHAS,ita kuma yarinyar yau za’a mai data gidansu saidai tazo matsayin fulanin bilhas”
murmushi jin daɗi Mai babban ɗaki tayi kana tai masa gdy shi kuma yay waje domin samun Sarkin fada da kuma Drever ya maida Meyrah gida..
Fulani kilishi ce tsaye a tsakiyan tirakarta sai kaiwa da kawowa take tare da haɗe hannayenta tana bugasu a jikin na juna.
bata taɓa tunanin irin wannan ranar zata riskesu ba,ta gama yarda da kuma yaƙinin cewa zuwa yanzu tilon ɗan nata wato Lil prince ya gama zama Sarki.
sai kuma abin yazo mata a ba zata domin yadda take tunanin abin ba haka yazo mata ba,bata taɓa kawowa ranta cewa Maleek ɗin yana raye ba.
bare kuma harya nemi dawowa kujerar mahaifin nasa.
lallai basu da wata dabara domin duk yadda sukai da haɗa wani mugun saiya wargatse.
“Uhmm yanzu dole muyi hqr mu riƙi abinda yazo mana dashi,sai dai dole nayi abu guda yana da kyau kaje wajan mahaifinka kace kana buƙatar kuɗi kimanin 20m domin barin ƙasar kai ba zaka iya zama kana ganin baƙin ciki ba,kaga kana amsa saika sanya wasu su katse Sarki Maleek kai kuma kabi jirgi kamar gari dole ba za’a taɓa cewa kai bane idan aka ɗauki watanni saika dawo a naɗaka sarki a karo na biyu”
shuru yay yana auna maganganunta daka bisani kuma ya miƙe tsaye tare da soma tafiya yace.
“idan har jinin mahaifina ke gudana a jikina babu shakka sai naga bayan Sarki Maleek tabbaa nina zan kawo ƙarshe mulkin zan nuna masa cewa tawa ZARRAH gaba take da tasa,babu shakka zan nuna masa kalan nawa ƙarfin iko lallai daga yanzu zai fara irga raguwar awannin da suka rage masa a duniya”
yana faɗin hakan ya saka kai ya fice daga cikin part ɗin nata baki.
direct part ɗinsa ya nufa yana zuwa ya fara gyara kayansa cikin aƙwati sai daya gama komai sannan ya miƙe ya nufi tirakar tsuhun sarki mai murabu wato Khalid.
A hankali Sarki Maleek ya zare alƙyabbar jikinsa tare da saƙaleta a gefen bedside,kana kuma ya sanya hannu ya zare rawanin da aka naɗa masa a kansa,wanda ya kejin yay masa nauyi gaske komai yake dauriya yake badan yana so ba.
shi kaɗai yasan abinda yake damun zuciyarsa amma ya fahimci ba kowa zan gane zafi da kuma raɗaɗin daya keji akan rashinta ba.
ta zame masa rayuwarsa yana jin komai nata a tattare da ita babu shakka saya sameta dan bai taɓa kakowa ransa cewa a wannan karan zai zama mara nasara ba.
hannunsa dake manne a jikin handle ya mura nan take ƙofar bathroom ɗin ta buɗe cikin nutsuwa ya tura duka gangar jikinsa zuwa bathroom ɗin.
a gaban makeken madubin dake manne a jikin bangon bathroom ɗin ya tsaya.
idanunsa ya ɗan lumshe kana kuma ya ƙara buɗesu a jikin mirrow’n ƙwantacciyar sumar dake ƙwance a ƙirjinsa ya tsorawa idanu ganin yadda ta ƙara yawa tare da baƙi sai sheƙi take.
taune lips ɗinsa yay dai-dai lkcn da yaji mararsa ta harba da ƙarfi har saida ya saki ƴar ƙaramar ƙara,tare da sanya hannu ya dafe saman marar tasa wanda yaji yana dripping haka nan.
sosai yay mamakin hakan cikin son kawar da hakan ya sanya hannu ya zame wandon shadar dake jikinsa ya saƙale a hanger.
a kasalance ya ƙarasa gaban shower’n tare da sakarwa kansa ruwa.
duka hannayensa ya sanya ya dafe jikin bangon kana ya ɗaga fuskarsa sama.
ruwan shower’n ya fara dukan saman beauty face ɗinsa wacce ta ƙawatu da zagayayyiyar saje da kuma gemu.
jin ruwan na shirin yi masa illa ya sanya yay saurin ɗauke kansa tare da gyara tsaiwarsa.
sosai ruwan ke dukan jikinsa saida yay wanka ya gyara jikinsa tare dayin brush ya ɗaura al’wala ganin dab da magrib ake.
wani long blue black ɗin towel ya ɗauka ya ɗaura saman waist ɗinsa.
kana ya fito daga cikin bathroom ɗin jin garin na ɗan kaɗawa alamar yanayin damuwa ya soma bai yana ya sanyashi lumshe idanunsa tare da ƙara sawa gaban window’n dake bedroom ɗin ya ɗan buɗe kaɗan.
ƙyaƙyawar ƙoramar dake gudana ya zobawa idanu inda gefe da gefenta ya kasance da wasu kurayen jiyayi masu ƙyau da kuma tsari.
banda kukan tsuntsaye babu abinda ke tashi a wajan.
saurin lumshe idanu yay tare da harɗe hannayensa a saman ƙirjinsa sabida wani ƙamshin furannin daya kawowa hancinsa ziyara.
wata daddaɗar iska mai ratsa jikin mutane ce ta fara kaɗawa hakan ya bawa sumar kansa damar kaɗawa yana sauka a saman idanunsa.
a wannan lkcn shi kaɗai yasan abin yake tunani,lallai wanda ya ja da ikon Allah shine sa taɓewa,kamar yadda bai taɓa tunanin ko amafarki zai zama sarki ba,haka kuma bai cire ransa da samun abinda zuciyarsa keso ba.
a wannan zaibi abinda zuciyarsa keso ne,zai kuma tabbatar da kasan cewarsu tare *ABADAN DA’IMA* wannan shine buri da kuma fatansa,bayan ya tsallake *TUGGU BIYU* da maƙiyansa suka ƙulla masa.
da zarar kuma ya samu abinda yake ƙauna zai bar masu garin zaije ya zauna da ita tamkar *TAGWAYEN ASALI* wannan shine kawai muradinsa.
sakin labulan window’n yay kana ya juya zuwa gaban dressing mirrow bisa dole ya zauna kan wani stool kana ya zubawa mayukan wajan idanu.
daga ƙarshe ya ɗauki wani lotion mai ƙamshi wanda ya san bazai masa illa a saman fatarsa ba.
a hankali yake murza lotion ɗin a saman fresh chocolate skin ɗinsa,yana gamawa ya ɗauki comp ya fara gyara sumar kansa.
kana ya shafa wasu lafiyayyun mayuka masu ƙyan gske.
wani parfume ya fesa wanda ya kasance body spray.
yana gamawa ya ƙarasa gefen mamakin royal bed ɗin mamaki yay ganin wata red ɗin jallabiya mai taushin gaske a saman bed ɗin.
ɗauka yay ya warwareta taɓe baki yay yana mamakin komai sai an sanya abunda zai nuna na sarauta ne,sosai jallabiyar tayi masa ƙyau kasan cewarfa red saita haska chocolate skin ɗinsa.
lumshe idanu yay sabisa ƙamshi jallabiyar da kuma taushinta,hannayensa ya zura cikin aljihun jallabiyar kana ya sunkuyar da kansa ƙasa kamar yana tunanin wani abu.
yana nan tsaye yaji ana knoking door ɗin bedroom wajan 3minutes kenan ana buga ƙofar cikin ɗan hasala yace.
“in”
A tsorace Meyrah ta shigo cikin bedroom ɗin,kasa kallonsa tayi sabida wani ƙwarjini da yay mata ga kuma wani sahihin ƙamshi da take fita jikinsa.
zama yay a gefen ɗin tare da jawo wayarsa,cikin nutsuwa ya fara danna password ɗin dake wayar cikin manyan ha rufar ya rubuta RUHINA yana rubutawa wayarta buɗe take makeken photonta ya bai yana cikin wata orange ɗin abaya da alama lkcn azumi ne,domin ta ɗan faɗa haka kuma ya ƙarawa fuskarta ƙyau.
pink lips ɗinta ya zubawa idanu gani sai sharning suke gaba ɗaya ta jiƙasu da yawo.
lumshe idanu yay sabida tsigar jikinsa da yaji yana tashi.
sosai ta shagala da kallonsa,mamakin girman kai da kuma miskilancinsa take,duk da cewa sarauta ba ƙarya bace amma shi nasa na dabanne.
komai cikin shanƙamshi yake yinsa.
numfashi ta sauke tace.
“Allah ya taimake ya ƙara maka lafiya daman Abbune yace nazo nai maka sallama zani gida”
saukar muryarta ya sanyashi ware fitinannun idanunsa wanda suka soma janye sabida wani hurt feeling da yaji yana kamasa.
ɗan ware manyan fararan idanunsa yay a kanta tare da juya eyes ball ɗinsa.
shi yama manta da cewa an shigo cikin bedroom.
taɓe yay ganin tana sunne kai a ƙasa.
kamar mara lafiya haka ya buɗe bakinsa yace.
“your accout details”
ya faɗa tamkar wanda akaiwa dolen magana,wata farar paper ya ta ɗauko a jaka ta rubuta masa,kana ta miƙa masa.
bashi da alamar karɓa hakan ya sanya tace.
“gashi”
ya tsuna fuska yay still kuma bai amsa taba,yana ta danne danne a waya tana zaunw taji notification a wayarsa dubawa tayi nan taka alart ɗin kuɗi na kusan 1.5m a accout ɗinta tana duba sunan wanda ya turo taga ansa MALEEK BILYAM BILHAS.
kanta a ƙasa tace.
“Wannan kuɗinfa? kuma yay yawa ai”
ƙwaciya yay akan bed ɗin hakan ya sanya ƙafafunaa bai yana,ƙaurinsa ta zubawa idanu gani ko ina gashi ne ƙwance sai sheƙi suke gwanin sha’awa a karo na uku kenan daya ƙara shiga ranta fiye dako wanne lkc,wajan 5minute yana ƙwance yana latsa waya harya manna wayar saman kunansa kana yace.
“kee mene kike kije kiyi using dashi na weeding”
da mamaki rashin ko in kula ɗinsa take kallonsa.
murya na ɗan rawa tace.
“Allah yaja da ranka ya ƙara lafiya ina gdy”
da hannu yay mata alama tace tana takurasa,tana fita yace.
“eyee ango ne kai ashe”
ya faɗa can ƙasan maƙoshi,shuru yay yana sauraran wanda suke maganar sai kuma ya mirgina tsakiyar gadon tare da rungomw pillow yace.
“eyee Abbune ya zaɓa,amma dole zangi attending bikinsa,wace take maka shagwaɓa gefe ko amaryarce?”
haka dai suke wayar wacce Maleek yaji daɗinta sosai kuma ya tabbatarwa da abokin nasa cewa gobe yana tafe tunda jibi bikin nasa,daga nan sukai sallama.
jin ana kiran salla ne ya sanyashi miƙewa tare da ɗaukar alƙyabba ya sanya a jikinsa tare da rawanin wanda yay masifar yi masa ƙyau ya fito a cikakken sarkinsa mai taƙama da iko,kuɗi,mulki,ilimi,uwa uba izza a haka ya ƙarasa babban parlou’n.
Cikin ɓacin rai Mai martaba Khalid ya kalli Lil prince yace.
“ka haukace ne,ni kake tunanin zan baka wannan kuɗaɗan masu yawa,nima wacce take ban kuɗin ta daina sabisa tsafin ya karye”
Kallonsa Lil prince yay cikin mamaki yace.
“Ba zaka banba ko? to shikenan wallahi saina ƙarar da kuɗinka gaba ɗaya”
hannu ya ɗaga sai sauke masa mari yay sauri riƙe hannun nasa tare da faɗin.
“tab nine zaka mara? haba Daddy nifa uhmmm”
“idan na mareka zaka ramane ne,niba matsayin uba nake gareka ba…?”
wani dake shiguwa cikin parlour yay saurin faɗin.
“Eh tabbas bakai ne asalin mahaifin Najeyb ba…