THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 3 BY NIMCYLUV
Gaba ɗaya Fadawanne suka tsaya suna kallonsa cike da mamakin tsawar da yay masu,tsawar dako Lil prince bai taɓa yi masu ita ba,tsawaya Prince yay tare da harɗe hannayensa yana jiran ƙarasuwar Saifu,Cikin taƙama da izza Saifu yake takawa zuwa gabansa,wata irin tafiya yake tamƙar ɗawisu ya zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa,yana ƙarasawa wajansu yaja ya tsaya kana yaja numfashi tare da lumshe idanunsa kana ya ware saman fuskar Kulsum wacce ke zube gabansu tana kuka tamkar ranta zai fita,taɓe baki yay tare da ɗauke kai daga kallonta,gyara tsaiwarsa yay tare dajan ma dai²cin gemunsa yace.
“Wannan fa?”ta tambaya yana mai ƙawar da kansa daga kallonsu tamkar bashine yay magana ba,daga bayansa yaji ance “nine ya kamata ka tambaya basu ba”juyawa yay ya kalli Lil prince wanda ya ƙarasa maganar cikin ɓacin rai,wani shegen murmushin gefen baki Saifu yay wanda ya haddasa lumawar beauty points ɗinsa tare da bayyanar gav teeth ɗinsa wacce take siririya,ɗauke kansa yay daga kallon Prince ba tare daya tankasa ba,gaba ɗaya hankalinsa ya mayar kan Fadawan yana jiran jin abinda zasu faɗa masa.
Wani ƙwarjinsa ne ya ninku a idanun Fadawan jikinsu na rawa suka faɗi ƙasa tare da faɗin “Umarnine daga magajin Mai martaba,ya nemi ta fito da *Kuyanga Zarina* amma taƙi kuma an tabbatar da itane ta ɓoyeta”suka ƙare maganar suna kallon Kulsum,cikin kuka Kuslum ta shiga faɗin.
“tabbas ɗazu naga Zarina lkcn dana fitowa daga sashin wannan mutumin daga nan taje ɓangaren Zaitun a nan na fita na barsu”ta faɗa tana sharce majinar data silalo ta cikin hancin sbd tsabar kuka.
Waro manyan idanunsa Saifu yay tare da juyasu kaɗan wanda hakan ba ƙaramin ƙyau suka ƙarawa fuskarsa ba,cikin zazzaƙar muryarsa mai ɗauke da nutsuwa yace “Ni!?”ya faɗa yana mai ɗan ɗaga muryarsa,domin bai fahimci yarinyar sa suke magana akanta ba,jinjina kai Kulsum tayi tace.
“eh! kai domin tun jiya muke nemanta bamu ganta ba,sbd ita baƙuwace a masarautar bilhas ba ko’ina ta sani ba,bayan gari ya waye nazu shiga sashinka domin kaima breakfast na haɗu da ita a hanya haka ya tabbatarmin da a wajanka ta ƙwana”
Wani baƙin cikine ya kama Lil prince,babu abinda ya ɗaga masa hankali wai a wajansa ta ƙwana,gaba ɗaya ya ruɗe tsantsar kishinta ya bayyana a kan fuskarsa,tabbas sai yanzu ya tabbatar ba ƙaramin so ya kewa yarinyar ba,son da baiyi tunanin zaiwa wata ƴar mace irinsa ba,son daya kejin zai iyayin komai a kanta haka nan zai iya hqr da komai a kan ya mallaketa,kasa cewa komai sai numfashi daya shiga saukewa,Saifu kam sai yanzu ya fahimci yarinyar da suke magana a kai,to ina taje ina ta sani a wajan,mai yasa ma ya barta ta fita tana cikin hali na neman taimako,mai yasa ya kasa tausayinta bare har yayi tunanin taimakonta kamar yadda ta buƙata,shurun da yayine,yasa Fadawan ci gaba da jan Kulsum suka bar wajan.
Taune laɓɓansa yay yana jin babu daɗi cikin ransa,tabbas bai nunata mata tausayi ba,kuma dukkan abinda ya sameta yana dasa hannu a ciki,dafashin da akai yasa ya buɗe sexcy eyes ɗinsa ya saukesu a kan fuskar Lil prince wanda yake tsaye gabansa yana fitar da numfashi,zame kafaɗarsa yay kana ya kalli Prince yace.
“Ka tsaya matsayinka na ɗan Sarkin Masarautar bilhas,shoulderna ba tsaranka bace gane ko?”ya faɗa yana ɗaga masa girarsa ta hango,baki Prince ya saki domin tunda yake babu wanda ya taɓa yi masa irin wannan maganar bare har yay tunanin muzuntashi gaban mutane,amma yau an wayi gare a cikin garinsa kuma masarautarsa wacce yake ta ƙama da ita,kuma a gabansa wani ƙato ya tsaya ya gaya masa magana ba tare daya ɗauki mataki ba,yana kallon Saifu yayi gaba yabarsa a wajan ba tare daya tanka saba.
Wani baƙin ciki ne da kuma tsanar Saifu ne ya sauka cikin zuciyansa,kuma ya ɗauki alƙwari baƙanta ransa kamar yadda ya baƙanta masa nasa ran,sai yasa yayi ladamar abinda ya aiƙata masa a yanzu,saiya wulaƙantasa gaban jama’a haka nan saiya tuzartashi,sai ƙulla masa sharrin da bai iya ya shallaƙesa ba,da wannan tunanin ya juya ya nufi Fada ya ƙira wasu Fadawa a kansu suje su bincika masa ɗakin Zaitun ko Zarina na ciki,cikin rawar jiki suka kama hanya domin aiwarta da aiken na Lil prince,suna zuwa su kaga ƙofar a rufe nan suka shiga ƙoƙarin buɗewa abu ya gagara,abu kamar da wasa harya zama babba,saida Prince ya gaji da kansa yazu yana zuwa yasa aka kunce ƙofar,ana kunce ƙofar ya faɗa ciki,da sauri yaja da baya tare da juyawa waje yana fidda numfashi ya shiga nuna ɗakin da hannu ganin hakan yasa gaba ɗaya Fadawan suka shige cikin ɗakin,salatin suka shigayi ganin.
Ganinta yashe a ƙasa bakinta ya fashe jini na zuba ta jikinsa,da sauri suka ƙarasa cikin jarumta wani Bafade yaji ya taɓata tare da jijjigata yana kiran sunanta,amma shuru babu amsa nan suka tabbatar babu numfashi a jikinta domin harta fara kumbura,da hanzari suka fito da ita waje tare da rufeta da wani mayafinta,Lil prince gaba ɗaya brain ɗinsa tsayawa yayi da aiki yana tunanin abinda ya sameta daga jiya zuwa yau wanda yayi sanadiyar rasa ranta,juyawa yayi yabar wajan yana tunanin inda zaiga Zarina domin shi yanzu itane damuwarsa ba mutuwar Zaitun ba.
Mai martaba yana zaune a Fada jikin shigarsa ta alfarma wacce take nuni da shiɗin tabbas Sarkine,sanye yake cikin Alƙyabba mai ruwan ƙwai,Kuyangunsa sai fifita suke masa tare dayi masa kirari wanda yake ƙarasashi girmankai da kuma jin shiɗin wanine,gefe guda kuma Captain Saifu tsaye a kansa yana danna waya daman duk sanda ya shigo harya fita ƙala baya cewa sai abu ya zama mai muhimmanci yake magana,cikin kiɗima Fadawan suka shigo cikin Fadar tare da zubewa a ƙasa suna yiwa Mai martaba kirari,Sarkin Fadane yace “gaisheku bayi Mai martaba na godiya meke tafe daku?”ya ƙare maganar yana kallonsu,Numfashi suka sauke a tare kana ɗaya daga cikinsu yayi jarumtar faɗin “Tuba muke Mai martaba idan abinda zamu faɗa zai ɓata ranku,amma tabbas matsala ta fara faruwa cikin masarautar bilhas,wacce a tarihi ba’a taɓa samun irinta ba” ya ƙare maganar yana sadda kansa ƙasa alamar jinjina, Mai martaba jiyayi zuciyarsa ta bada sauti dam,domin baya burin ace a lkcn mulkinsa wani abu ya faru wanda ba’a saba ganinsa a cikin gidan Sarautar ba,Zubawa Fadawan idanu yayi ƙafin ya gyara zama yace “Eheem”hakan da yayi ya tabbatar masu yana buƙatar jin abinda ya faru,da Sauri Sarkin Fada yace “Ƙarya kuke ƴar ƴan talakawa babu wani abu dazai faru a wannan masarautar mai’adalci bada sanin Mai martaba,idan kuma aƙwai ku faɗa munajinku” cikin rawar murya da kuma tsoro wani bafade yace “munje sashin kuyangi domin neman Kuyanga Zarina,sai akace tana ɗakin Kugayan Zaitun,ba muyi ƙasa a guiwa ba,mu kaje ɗakin amma abinda muka gani ha bamu tsoro domin gawar..”tarin da Saifu yayi ne ya dakatar dashi daga ƙarasa maganar.
Gaba ɗaya suka zuba masa idanu ganin da gske tarin yake,cikin sauri wani ya ɗauko gorar ruwa ya miƙa masa,bai amshi ruwan ba,kana baice masu komai ba yasa kai ya fice daga cikin Fadar,gaba ɗaya sukabi bayansa da kallo hatta Mai martaba suna mamakin abinda yasa mood ɗinsa ya sauya lkc guda.
Saifu jiyayi zuciyarsa ta cunkushe gabansa ya faɗi ƙirjinsa ya bada wani sauti mai ɗauke da fargaba,jiyayi gaba ɗaya ya zama wani vry weak duk wani kuzari na jikinsa ya kau,babu a sannu tunaninta ya fara sauka cikin ƙwaƙwalwarsa,ina take ma yasa Prince yake nemanta,maita aikata garesa har haka,hannu yasa ya dafe kansa wanda ya soma juya masa,gawarwa suka gani wanda ya sasu tsorata,baidai ita bace domin yasan tabbas bata da lpa,wani zafi zuciyarsa tayi masa a karo na farko ya kasa taimako mace wanda hakan ba halinsa bane,bai san mene yasa ya kasa taimakonta ba,aduk lkcn da yayi tunanin zuwa gareta yana jin zuciyarsa na tsananta bugu fuskarta nayi masa ƙwarjini,yayi rayuwa a ƙasashe daban-daban amma bai taɓa cin ƙaro da macen data tsaya masa arai harya kejin fargabar zuwa gareta,sau biyu ya ganta amma yadda zuciyarsa ke matsa mata da tunaninsa saika ɗauka yayi shekara guda da saninta,ɗan ware manyan idanunsa yay wanda suka soma ƙanƙancewa sbd ciwon da kansa ke masa,a hankali gargasar jikinsa ta soma miƙewa wani sanyi ya fara ratsa ƙofofin jikinsa,ba tare daya san inda yake ɗura ƙafafunsa ba,a haka yake tafiya harya ƙarasu cikin kata faren lambun dake masarautar wanda ba kowa ne yake shigarsa ba,yana zuwa ya sami wata farar kujerar mai ƙyau da tsari wacce akaiwa ado da tambarin gidan sarautar,a ƙafe take ƙasan wata bishiyar guava,zama yayi tare tura duka hannayensa cikin ƙwantacciyar sumar kansa tare da hargitsata ya shiga fesar da wani zazzafan numfashi ta cikin bakinsa,cikin tattausar muryarsa wacce ta soma sauya kala yace “YES! I know her in my dream”.
Gaba ɗaya suka ɗauke kansu daga kallonsa kana sarkin fada yace “muna jinka waziri me kake cewa gawarwa kuka gani har kuka gigice?”numfashi Waziri ya sauke yace “ba gawar kowa bace face kuyanga Zaitun”da sauri Mai martaba ya ɗago kansa a rikice yace “What! Mene kuke faɗa Zaitun fa? Ko daren jiya mu….”sai kuma yay shuru mai ƙarasa abinda zaice,wani murmushi yayi mai ɗauke da ma’anoni mutuwarta shike tabbatar masa da aikinsa ya amso wajan boka,ƙara gyara zama yayi ya shafi cikinsa,cikin ransa yace “nasan dole daki mutu”a zahiri kuma ya kalli waziri da sarkin fada yace “aje a nemi Fulanin sora da Kilishi da jakadiya suyi mata suttura”Waziri da sarkin fada suka miƙe tare da nufar sashin Fulanin sora.
A kishin giɗe suka zameta sai fita kuyangunta suke mata,tasha Alƙyabba tasu ta mata,gabanta kayan cimane kala² irinsu Dubulan,Alkaki,Bakilawa,Zuma,sai kuma dan ginsu fruit,suna zuwa suka zube gabanta tare da miƙa gaisuwarsu da kuma jinjinar ban girma,nan suka faɗa mata saƙon Mai martaba saurin miƙewa tsaye tayi tare da rafka salati tace “ikon Allah jiya ta daɗe a nan gaba ɗayanta a rikice take ashe yarinyar nan alhine Ubangiji ya nuna mata mutuwarta,ikon Allah ya jiƙanta maza ka ɗauko gawarta zuwa nan sashin kana kuje ko faɗawa su Kilishi da jakadiya kada kuje wajan mai babban ɗakin itama ba lafiya gareta ba”
Cikin gaggawa aka yiwa Zaitun wanka tare da shirya cikin likkafani,sannan akai waje da ita akai mata sallah kamar yadda addini ya kuyar,kana aka nufi da ita wata maƙabarta dake bayan gidan sarautar,abin mamaki dukkan kabarin da aka haƙa zai aga ruwa a cikinsa,daga ƙarshe aka sakata wani abin mamakin ana sakata acikin kabarin wani irin baƙin hayaƙi ya fito ta gabanta yay sama,gaba ɗaya wajan suka ɗauki salati,haka aka binneta sukai mata addu’a suka koma cikin masarauta.
Kamar a mafarki haka ta keji ana bugun ƙofar tamkar za’a ɓallata,a hankali ta shiga buɗe idanunta da sukai mata nauyin gske ga wani irin ciwo da kanta yake mata,miƙewa tayi zaune ta takure waje guda ta shiga rera kuka tare da kiran sunan Mom da sauran ƴan gidansu,tsagaitawa tayi da kukan jin bugun ƙofar ya ƙaro,a hankali ta lumshe idanunta cikin wata ajjiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi kana ta saki wata tattausan murmushi a lkcn da hawaye suka gangaro da cikin idanunta,sosai ta rungome pillow ɗin dake kusanta,a hankali ƙyaƙƙyawar fuskarsa taci gaba da bayyana cikin eyes ball ɗinta,babu abinda yake ɗaukan hankali ya tafi da nutsuwarta ya dagula lissafinta irin faffaɗan ƙirjinsa wanda ya kasance a murɗe,a karo na biyu ta ƙara sakin murmushi,ƙara ta saki sabida fisgar da taji anyi mata,a kiɗime ta ɗaga jan idanunta ta sauke cikin na Lil prince,saurin ja baya tayi ganin idanunsa ya sauya jikinsa sai rawa yake,wani mugun murmushi yayi tare dayi mata rumfa,runtsa idanunta tayi sbd wani abu daya daki hancinta,ƙasa tayi sata gudu yayi saurin sanya mafa ya ta ɗeta ta faɗi ƙasa,kamar zautacce wanda ya rasa ƙwaƙwalwarsa ya nufi inda take tare da sanya hannunsa ya tura cikin..