THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 4 BY NIMCYLUV
..Kasan cewarsa Namiji mai juriya da kuma haɗiye ɓacin rai yasa gaba ɗaya ya fita hayya cinsa,yadda jikinsa yake rawa tamkar mazari zai tabbatar maka ba ƙaraƙin ciwo ya keji a cikin zuciyarsa ba,bai san mene rauni ba,haka nan bai san mene karyewar zuciya ba,amma kasan cewa da ita a ƴan ƙwanakin nan zuciyarsa na son
karaya,rauninsa na son bayyana wanda kuma hakan ba shine burinsa ba,gaba ɗaya ta hana zuciyarsa sukuni,tunaninta na son tarwatsa masa zuciya,cikin zafin nama yasa hannu ya kaiwa bangon toilet ɗin doka,ƙarfin bangon da kuma girman naushin da yayiwa bango ya haddasa fashewar hannunsa jini ya soma zoba,ganin shower’n na neman bashi haushi ga yadda zuciyarsa keyi masa zafi da raɗaɗi ya sanyashi faɗawa cikin jakuzzie wanda yake cike da ruwan tamkar ƙaramin kogi,a hankali ya fara shigewa jikin jakuzzie’n yayinda numfashinsa ya fara ɗaukewa sbd yadda ruwa’n ya shanye saman fuskarsa,a hankali numfashinsa ya tsaya yawan ruwan da kuma girman jakuzzie’n ga kuma yadda jikinsa ya saki ya sanya gangar jikinsa tayo sama kansa kuma ya nutse jikin ruwa’n haka ya fara yawo saman ruwan tamkar gawa.
Lil Prince na barin wajan Zarina ya ƙarasa flat ɗin Fulani kilishi wacce ta kasance mahaifiyarsa,fuskarsa a ɗaure ya faɗa ɗakin yana zuwa ya sameta kishin giɗe akan cousion,Gefenta Hadimanta da Kuyangunta wasu nayi mata fita,wasu kuma na matsa mata ƙarfa,yana shiga yayi gyaran murya gaba ɗaya Hadiman da Kuyangun suka fice daga cikin ɗakin sukayi waje,da ɗan sassarfa ya ƙarasa wajan Kilishi tare da zubewa gabanta ya sauke ajjiyar zuciyar mai ƙarfi kafin ya dubi Kilishi yace.
“Yanzu ni shikenan Mai martaba bazai ta yani samun cikar burina ba,ina Sonta kilishi so bana wasa ba,ina mata son da basan zan iya yiwa wani ɗan adam ba aduniya,Fulani wlh ina sonta da gsky bazan iya hqr da ita ba,kuma inaji a raina bazan iya bin umarnin Mai martaba idan akanta ne,dan Allah ki tayani samunta zuciyata ciwo”
Ya ƙare maganar cikin ƙwantar da murya tare da zubawa mahaifiyar tasa idanu,Numfashi kilishi taja na wani lkcn kafinta gyara murya tace.
“Ba abin mamaki bane dan Mai martaba yaƙi amince da wannan burin naka sabida shima yana buri akan yarinyar,bayan haka kasan cewa a tarihin masarautar bilhas jinin sarauta bai taɓa auren baiwarsa ba,amma ace so sone sonkai yakai yafi,yana da burin akanta ga farin cikina kuma yana sonta,wanne kake ganin zai yihu daga cikin biyun nan,CIKAR BURI KO FARIN CIKIN RAI?”ta ƙare maganar tana yin wani murmushi wanda yake da ma’anoni kala².
Lil prince ne ya dubeta da idanunsa da suka soma sauya kala sabida damuwa kana ya janye idanunsa daga gareta yace.
“CIKAR BURI bai zama lallai ba domin ko babu shi mutum zai iya rayuwa kuma ya samu ƙwanciyar hankali,somin ko burinsa bai cika ba aƙwai wani abun da yafi wannan burin muhimmanci wanda zai sanya ya manta da wannan CIKAR BURIN,
Amma FARIN CIKIN RAI wani abune mai girman gaske wanda idan babu shi zuciya da gangar jiki zai iya samun matasala,farin ciki zaiyi ƙwara daga zuciyar mutum kana baƙin ciki ya maye gurbin farin cikin,samuwar FARIN CIKIN RAI ne kawai zai ɗauke wanda zafi da raɗaɗi da zuciya take ciki,haka shine zai shafe ƙunci da baƙin cikin da zuciya dake cikin idan aka auna wannan abu biyu babu shakka zance FARIN CIKIN RAI GABA YAKE DA CIKAR BURI”ya ƙarasa maganar yana kama hannayenta tare da zuba mata idanu yana son yaji abinda zata faɗa.
Jinjina kai Kilishi tayi alamar gamsuwa da maganar Prince,hannayenta ta zame daga cikin nata kanata ta shafi kansa ciki isa da gadara haɗi da tabbatar da abinda take faɗa tace.
“Na rantse da sarkin dake busamin numfashi harna shaƙa na fesar,saina mallaka maka farin cikin ranka,idan har banyi haka ba tabbas ban cika ƴar wacce ta haifu wajan iyayenta ba,kaine magajin Mai martaba haka kuma kaine Sarkin gobe,jeka abinka ka ɗauka cewa ka samu farin cikin ranka,sannan kayiwa Mai martaba akan idanunsa kada ka bijirewa umarnisa ka barshi shima yayi fafutukar samun cikar burinsa,keja ɗan nagada wanda aka haifa ga daular mai ciki a yanzu a wannan nahiya tamu ta Bilhas”
Wani farin ciki ne ya cika zuciya Lil prince cikin zumuɗi ya ɗura kansa bisa cinyar Kilishi yace.
“nasan kina raye bazan taɓa kuka ba,tabbas kinamin sahihiyar ƙauna fiye da Mai martaba shiyasa nake ƙaunarki fiye dashi”
Kunnansa ta murɗa da ƙarfi wanda ya sashi sakin ƙara kaɗan,sakina tayi tace “ɗan nema dukkanmu iyayenka ne ya zama dole kayi biyaya wa abinda mukeso,maza jeka nema zan saka ayimin iso wajan Mai martaba”
Miƙewa yayi tare da shafa kansa yace “zandai bar maki ɗakinki amma ban iya bacci yanzu sai naje na rage zafi da ita”ya ƙare maganar yana fice daga cikin ɗakin.
Dariya tayi kana ta ɗauki Apple guda ta sanya abakinta,tana jin soyayyar Prince na ƙara shiga zuciyarta musamman idan ta hangesa saman karagar mulki idan Mai martaba yayi murabus,tana zaune Hadimanta da kuyangunta suka shigo,da kallo ta bisu kafin tace.
“ina Kuyanta Kulsum ne?”
Da sauri Hadima Batul tace “Ai ranki ya daɗe Lil prince magaji mai jiran gado ya sanya akaita ɗakin duhu”ta ƙare maganar tana sunkuyar da kanta ƙasa.
Jinjina kai Kilishi tayi kafin tace “da kyau halan laifi tayi masa naga ta fiya rawar kai”ta faɗi maganar tana taɓe baki alamar ko ajikinta,nan ta sanya akayi mata kiran jakadiya tana zuwa tace tayi mata iso wajan Mai martaba,babu daɗewa Jakadiya ta dawo tare da faɗin “Mai martaba ya riga daya ƙwanta sai dai a tara zuwa gobe”.
Wata tsawa Fulani kilishi ta watsawa Jakadiya tare da nunata da hannu tace.
“wannan shirmen na gaji dajinsa bana da ikon ganin mijina yau ace Fulanin sora bata bada umarni ba,gobe ace kaza haba bafa baiwa ce ni ba,kisan duk yadda kikai gobe na samu ganin Mai martaba”tana faɗin hakan ta miƙe tare da tattare Alƙyabbar jikinta nufi bedroom ɗinta.
Lil prince na zuwa sashinsa ya huce bedroom kana ya cire kayan jikinsa ya nufi bathroom,wanka yayi sannan ya sanya wasu kayan bacci masu ƙyau,kana ya zaune gefe guda yana jiran zuwa Zarina,sama da 2hours yana zaune babu ita hakan kuma ya tabbatar masa da baza tasu ba,kuma yasan babu wanda ya hanata sai wannan wawan cike da takaici ya ɗauko wata ƙwalbar giza ya fara zubawa cikinsa,saida yayi tatil sannan ya faɗa bed yana surutai a haka bacci yayi gaba dashi.
Saifu’s pov
Cikin fitar hayyaci da kuma goshewar tunani yayi saurin ɗago kansa sama daga cikin jakuzzie ɗin,wata nauyyiyar ajjiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi tare fesar da wani zazzafan huci ta cikin bakinsa,a hankali ya ɗaga lashes ɗin idanusa wanda suka jiƙe da ruwa sukai zara-zara,cikin abinda baifi 3seconds ba ya buɗe gajiyayyun idanunsa wanda sukai jaa,sabida ruwan daya shigesu,luff yayi cikin jakuzzie’n ya shiga sauke numfashi,mene hakan ke nufi akan hakan ya kasa control kansa? Dalilin hakan ya kasa danne bacin rai da damuwan dake ransa? Mene yasa yake abu kamar zautacce ba tare da yayi tunanin hakan zai faru ba,mekenan all this na mene? A hankali ya sanya hannunsa saman goshinsa tare da murzawa,cikin wata ƙasalalliyar murya yace “ya rabbi meke shirin faruwa,ohh God save me”ya faɗa yana taune laɓɓansa wanda sukayi jaa sabida taunesu da yayi,yasan dukkan lkc’n da yayi hakan there’s something big gonna happen to him..
A kasalance ya miƙe daga cinin jakuzzie’n kana ya ƙarasa gaban shower’n ya ɗauraye jikinsa tare dayin brush ya ɗaura alwala..
Batherope ya sanya a jikinsa yana fitowa ya ƙarasa wajan wardrope ɗin da kayansa suke ciki,wani ƙaramin wando troser ya ɗauka ya sanya kana ya saka wata ƙaramar singlet.
Wata farar jallabiya ya ɗauka ya sanya a jikinsa kana ya fesa wani parfume wanda yake sawa idan zaiyi sallah,paryer mat ya shimfiɗa kana ya tada da sallah cike da nutsuwa,yana kammalawa ya fara tilawan alkur’ani cikin ransa,bai ƙwanta ba sai wajan 2 shima ya daɗe yana juyi akan bed kafin wani wahalallan bacci ya samu nasarar yin gaba dashi.
*_Washe gari_*
A hankali ta buɗe idanunta sosai tayi mamakin ganinta ƙwance a ƙasa,kai ta ɗaga domin ganin lkc da ɗan sauri ta miƙe tsaye ganin shida ta kusa,da ɗan sassarfa ta zura flat ɗin shoe ɗinta ta nufi toilet,alwala tayi kana tayi brush tana fitowa ta tada sallah akan abinda ta ƙwanta,bayan ta idar tayi lazumi ta miƙe domin shiga kicthen nan idanunta ya sauka kan table ɗin data jera food warmers ɗin akai,wajan ta ƙarasa ganin kamar ba’a taɓa abincin ba,amma domin ta tabbatar da abinda take tunani,wani baƙin ciki taji a zuciyarta ganin babu abinda ya taɓa,wasu ruwan hawaye taji ya sauka daga cikin idanunta,wata kam duk irin abinda tayi masa bai taɓa ba,lallai ta ƙara yarda ya maidata baiwa,share hawayen fuskarta tayi kana ta ƙwashe kayan ta nufi kicthen,tana zuwa ta juye abincin cikin wani babban flast kana ta wanke dukka flast ɗin..
Tsayawa tayi tana tunanin tayi masa girkin ko kar tayi,daga ƙarshe ta yanke shawararyi masa,cikin sauri ta haɗa masa kunun gyaɗa da kuma masa,kana tayi masa farfesun zallan kayan ciki wanda yaji kayan ƙamshibayan ta kammala ta haɗa masa fruit salad,tana kammalawa ta jera masa komai kamar jiya..
Fruit salad ta ɗiba tasha dan bata fiya cin abinci ba,wani jug mai kyau ta ɗauka ta zuba kunun gyaɗan sannan ta ɗibi farfesun kayan cikin ta zoba cikin wani flast,ma dai² cin basket ta ɗauka ta zoba kayan ciki ta rufe da wani ƙyalle,cikin ɗan saurin da take dashi ta ɗauki basket ɗin tayi waje.
A hankali ta dinga satar hanya tana fakar idanun mutanen waje,harta ƙarasu wani haɗaɗɗan sashi dake cikin gidan sarautar mai ƙyan gaske,wani numfashi ta sauke na wahala kana ta zobawa wajan idanu musamman ƙofar glass ɗin tana tunanin ta yadda za’ai ta shiga ciki ba tare da kowa ya ganta ba,numfashi ta sauke kana cikin siririyar muryarta tace “Ya rabbi help me”tana faɗin ta soma ɗaga ƙafanta tun daga nesa daimond ring ɗin hannunta ya fara wani irin haske,babu inda kuma hasken ke tsayawa sai jikin ƙofar,tun kafin ta isa taga ƙofar ta fara buɗe tamkar magic,tana ƙarasuwa wajan ƙofar na buɗewa gaba ɗayanta,a dai² lkc’n hasken zoben ya ɗauke..