THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 5 BY NIMCYLUV
Wani mugun murmushin aljanin yayi wanda a yanzu ya zama kamilallan mutum mai siffar Saifudeen,ƙara kallon bokan yayi domin ya duba abinda baiyi masa kana yace.
“jeka maza jeka garesu yanzun lkc’n kaɗai ne,lokacin da zaka shaƙƙu da koƙwanto cikin zuƙatansu yayi,lokacin da zaka rusa ɗan ƙaramin farin cikin da suke dashi yayi,wannan shine lkc’n ɗauka fansa,ehh! tabbas fansa zauka ɗauka jekaa!”ya ƙarasa maganar cikin ɗaga murya,ba tare da wani dugun tunani ba,Aljanin najin hakan ya ƙurma ihu tare dayin wani juyi haɗi da katantanwa izuw sama,saiga asalin halittarsa ta bayyana,halitta mai cike da tsoro halittar da dukkan wani ɗan adam yayi tuzali da ita zai iya rasa ransa sabida tsoro da firgici,a hankali yanayin ya soma juyewa jikinsa ya fara shaƙwanyewa zuwa ƙasa,saida ya zagwanye gaba ɗaya kana ya zama wani baƙin haƙi cikin abinda baifi sa’a ɗaya hayaƙin ya tashi zuwa sama.
Bokan naganin aikinsa yaci kuma ɓuƙatarsa zata biya ya saki wani mahaukacin ihu tare da dukan ƙirjinsa iya ƙarfinsa,kafin ya zame ya soma zane jikin wata farar ƙasa wanda akafi sani da duba
**** ****
Zaune suke a babban parlour’n da aka ƙawatashi da kayan alatu na mure rayuwa dajin daɗin,sosai gidan suke cikin ƙwanciyar hankali dajin daɗi kafin ƙaddara tazu ta gilma cikin rayuwarsu,ƙaddara mafi muni domin rashin ɗan mutum a wannan zamanin ba ƙaramin tashin hankali bane.
Ɓatan ZARINA ya zame masu wani miƙe da bazai taɓa goguwa cikin rai da zuciyarsu,hatta gangar jikinsu kewan rashinta suke,sabida sabo da ƙwanciya da tayi a jikinsu,Zarina kenan ƴar gata mai jida dangi gaba da baya ko ina soyayya ake nuna mata,bata tama kuka ba da sunan ɓacin rai saina shagwaɓa,kukanta ɗaya idan tayi mafarkin Heart dream ɗinta,ko kuma ta nemi ring ɗinta ta ɓata wannan dalilai sune kaɗai kesa hawaye fita a idanun Zarina.
Kallonta Abba yayi cike da tausayawa yace “sai yaushe ne hawaye zai daina fita a idanun mace mai juriya,sai yaushe ne damuwa zata bar zuciyar mace mai taƙama da ikon Allah,sai yaushe ne matana zata yarda da ƙaddara?”ya ƙarasa maganar cikin sanyin murya da kuma danne abinda yake ransa.
Kallonsa Mom tayi kana ta saki murmushi tace “ba ina kuka bane dan banyarda da ƙaddara ba,ina kukane sabida tunanin halin da Zarina ke ciki,ina tsoro halinda zata samu kanta,nasanta taƙin cin abinci ko a gida,to ina tunanin inda take aƙwai abincin ko babu,ina take ƙwana ina take dashi ban sabi ba,wannan dalilin shike sani zubar da hawaye”ta ƙare maganar tana goge hawayen idanunta.
Mamu dake gefe tana lissafin mutanan da za’a fiddawa zakka tace “ato Audu faɗa mata dai may be idan kaine zata amince da cewa Allah ɗaya ne,banda sakalci ina damuwa ta taɓa zama magani,bakai kaɗai kikejin zafin rashinta ba,nasan dole zaki fimu jin zafi da raɗaɗi sabida ke uwace,amma dole muyi hqr mu fauwalawa Allah komai”.
Abdallahi wanda yake matsayin Abba kamar yadda iyalansa suke faɗa masa,yana numfashi kana yace “Insha Allah ubangiji zai kareta kullum cikin addu’a muke kuma na tabbatar ba zata faɗi banza ba”Mom da tayi shuru tun ɗazu sai yanzu ta samu damar magana tace “insha Allah”
“Mumu ya maganar abincin sadaƙa na almajirai da za’a dingayi da azumi,ina son fitar da duk wani abu da za’ai na azumi bansan ajjiye nauyi a kaina”jinjina kai Mom tayi kafin ta tace.
“Munyi yanke shawarar ɗiban masu aiki domin yin ƙosai da kunu ana rabawa almajirar,sbd idan mukace mune zamuyi abin zaiyi yawa aƙwai aikin gida ko Mamu?”ta ƙarasa maganar tana kallon Mamu wacce take nesa dasu,ajjiye abin hannunta Mamu tayi kafin ta gyara zama ta fuskancesu gaba ɗaya tace.
“Eh Sultanerh kinyi tunani mai ƙyau domin aikin azumi wahala garesa,sabida ƙishi da kowa keji,zuwa anjima sai a fara neman ma’aikan sannan aje kasuwa asiyo sauran kayan da babu” da “to”Mom ta amsa sabida yanayin damuwa da kuma tunanin ƴarta da take wanda ya kasa mantuwa cikin zuciyarsa,rufe idanunta tayi tana jin yadda zuciyanta ke mata zafi da raɗaɗi na rashin ƴarta ta,Abba ne ya katse masu shurun ta hanyar faɗin.
“nida yanzu ga A.t.m ɗina dukkan abinda kuke buƙata saiku cira,yafi a tsaya lissafin kuɗin,insha Allah zuwa gobe ko jibi zan fitar da zanbayar sabida banson a fara azumi ban bayar ba,haka kuma….”ringing ɗin wayarsa ce ta tsayar dashi daga maganar da yake,wayar ya ɗauko daga cikin aljihunsa,farin ciki fal fuskarsa ya dubi Mom yace.
“A’a Sufyan ke kira da alama sun samu kansu a dajin”yakai zancan yana picking call ɗin tare da sata a speaker.
Sufyan dake can ɓangaren ya jingina da jikin wata bishiyar darbejiya acikin jejin illori,ya lumshe idanunsa lkcn da yaji anyi picking call ɗin nasa,kana ya saki murmushi yana matse hannun Tupic dake kusana,cikin ƙasa da murya da kuma salon shagwaɓ Safyan yace.
“Abbana munshiga damuwa sosai na rashin jin muryarku,munyi kewanku sosai fa har bama iya aiki”ya ƙare maganar yana kallon Tupic wanda ya matsu yaji yaya lafiyan little sis ɗinsu.
Daga can ɓangaren Abbu ya saki wani murmushin jin daɗin muryar ɗan nasa yace.
“ina tabbacin munfiko kewanku komai namu da muke baya tafiya saida tunaninku,kullum cikin zullumi da fargaba muke sabida rashin sanin halin da kuke,Mom ɗinku kullum cikin damuwa take gaba ɗaya ta rabe kamar ba ƙatuwar matana ba”Abba ya ƙare zancan yana jan hancin Mom wacce ta ƙwaɓe fuska alamar taji haushin maganar Abba.
Sufyan ya saki dariya a karo na biyu tare cije leɓensa na ƙasa yace.
“Abba ƴar ƴan Mom zasuci tararnka,ko gaisawa ba muyi ba zaka fara tsukana”Mom dake gefe tayi saurin dawowa kusan Abba tare da ƙwace wayan tace.
“sweetheart yakuke hope komai nrml yaya aikin naku yaushene zaku dawo,muna buƙatarku kusa damu,na gaji da rashinku kusanmu”ta ƙare maganar hawaye na sakko mata,Abba ganin Mamu ta shiga bedroom tun ɗazu ya saka hannu ya jawo Mom jikinsa tare da soma rarrashinta ba tare da yayi magana ba.
Tupic dake tsaye kusan da ɗan uwansa ya turo baki gaba yace. “Mom kuka ko? Har yanzun bakki daina kuka a kanmu,soon zamu dawo gida zuwa goma ga azumi ko biyar,tun ɗazu muna magana banji muryar little ba,where is she?”ya ƙare maganar yana kallon Sufyan wanda yake riƙe da wata ƙatuwar bindiga mai jigida.
“Ayya Tupic daɗin jin muryarku kaɗai zai sani kuka,dan Allah kuyi ƙoƙarin dawowa da wuri,little kuma na ɗaki tana bacci ta tashi da ciwon kai”
Gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin “what little babu lafiya tun yaushe ne,wayyo our luv get well soon pls Mom ki kula mana da ƴar ƙaramar ƙanwarmu kice muna sonta da ƙaunarta,bye zamuci gaba da aiki yanzu”yana faɗin haƙan ya ƙatse wayan ya soma harɓi sabida ganin kilmawar ƴan ƙonar baƙin wake da yayi,shima Tupic ya mara masa baya suka fara sakin wutar harɓi,ƙaran harbinsu ya ankarar da sauran sojojin,kafin wani lkcn dajin ya cika da ƙarar bindigo babu abunda kake gani sai wuta da hayaƙi dake tashi zuwa sama.
Shuru Mom tayi jinsun kashe wayan,lamo tayi jikin Abba ta soma shassheƙar kuka,sosai take kewan yaranta gaba ɗaya sam ta gaji da wannan aikin nasu,sukenan cikin jeji babu wani jin daɗi daga shan ruwan tirɓaya da cin ganye”.
Ta ƙare zancan idanunta na kawo ruwan hawaye,Abbane ya shiga bata baki tare da ƙwantar mata da hankali kana shima ya miƙe tare da nufar waje,yana zuwa ya faɗa cikin motarsa tare dayi mata key ya harbata zuwa bakin get,yana zuwa aka buɗe masa ƙofar a hankali ya cilla kan motar waje.
*_Masarautar bilhas_*
Ƙwanci tashi babu wahala wajan ubangiji,tun muna irga ƙwana kinmu zamu koma irga watanni daga watanni zamu koma irga shekarau.
A kullum ƙwanakin ƙara hucewa suke kamar yarda numfashin mutum kullum ƙara ƙarewa yake,ƙwanakinsa suna ƙara tafiya girma na zuwar masa,babba kuma tsofa ya ziyarcesa.
Ranakunmu na ƙarewa ba tare da mun ankare ba,haka nan kullum zunubinmu ƙara yawa yake ba tare da mun ƙyautata ƙarshanmu ba.
Yau ya kama ranar da ake saka ran ganin watan Ramadan watan dake saka mutane da yawa ruɗu wajan nemansa.
Cike Fada take da manyan mutame irinsu hakimar dagatai da kuma sauran manyan,wanda suka amsa kiran Mai martaba,sannu a hankali suke zuwa tare da ƙwasar gaisuwa wajan Mai martaba,saida kowa ya gama ƙwasar gaisuwa sannan Mai martaba ya gyara zama tare dayin gyaran murya yace.
“Kamar yadda kuka sabisa ga al’ada da kuma tsari irin na wannan masarauta kusan cewa idan watan azumi yayi Hakimai na kawo buhun shinkafa da babban buhu na yatsi guda ashirin-ashirin,sannan Dagatai suna kawo guda goma-goma,sannan masu Unguwanni zasu kawo guda biyar-biyar,haka nan masu Unguwanni suna gayawa Al’ummarsu su kawo gudan ɗai-ɗai,wannan shine tunatarwar dana taraku a nan domin nayi maku,zuwa nan da goma ga wata Ramadan ko wanne mai Unguwa ya tabbatar ya haɗa kayan al’ummarsa ya miƙa ga Dagaci,Dagaci ya bawa Hakimi,Hakimi ya kawo masarauta,wannan shine kawai zaku iya tafiya”.
A hankali Saifu ya ɗaga manyan gajiyayyun idanunsa ya mannasu akan fuskar Mai martaba,domin tabbatar da abinda yake,sam ya kasa yadda cewa aƙwai wani shugaba dazai iya aikata hakan wa al’ummarsa,banda haka ace kana matsayin shugaba amma awajan al’ummarka kake neman abu,kuma a lkcn da kowa yake buƙatar lada domin samun da cewa rana gobe ƙiyama,to wai duk yawan abincin da yake buƙata ina zai kaisu? Mene zaiyi dasu har haka?.
Wani huci mai zafi ya fesar da wani zazzafan huci ta hancinsa,lkci guda idanunsa suka rufe tare dayin jaa sbd ɓacin rai,idanunsa ya ɗauke daga kan Mai martaba kana yaja idanunsa ya rufe,sam bazai jure wannan adalcin ba,ya zama dole yabar wannan masarautar da zarar an kammala azumi,cije lips ɗinsa yayi lkcn daya tuna da Mai babban ɗaki idan ya tafi yaya matsayin rayuwarta yake,yasan cewa kowa rayuwansa a hannun ubangiji yake,amma aƙwai sanadi ai,hannu yasa ya shafi sajen fuskarsa.
“Allah yaja da ranka ya ƙara maka lafiya amma adubi talakawanmu yanzu ana hali na rashin wada taccen abinci ga rashin kuɗi da ake,tabbas akace za’a karɓi wani abu wajansu za’a takurasu sbd da yawancinsu abinci ci wahala yake masu,a yafemi idan na faɗi ba dai²” Hakimin Kantagari ya ƙarasa maganar yana sadda kansa ƙasa alamar girmamawa.
“karya kake ɗan talakawa ahir ɗinka,har Mai martaba ne zaiyi magana wani ya tanka?cewar sarki fada,Hannu Mai martaba ya ɗagawa Sarkin fada tare da faɗin”basshi bana magana biyi gaba ɗaya ko ɓacen da gani”.
Gaba ɗaya suka miƙe tare dayiwa Mai martaba sallah suka tafi.
Bayan fitarsu Mai martaba ya dubi Saifu dake tsaye bayansa yace.
“yanayin zamanka zai sauya zaka koma da safe,da yamma kuma kana hutawa”jinjina kai Saifu yayi ba tare da yace komai ba.
Suna zaune a fada Lil prince ya shigo cikin shigarsa ta alƙyabba yayi ƙyau sosai,yana shiga ya zabgawa Saifu harara kana ya ɗauke kansa ya zube gaban mahaifin nasa kana ya ƙwashi gaisuwa,Waziri ne ya dubi Prince yace.
“Magaji ka yini lafiya?”ya ƙare maganar yana sakin murmushi domin a duniya yana ƙaunar Prince,wannan dalilin yasa Mai martaba ƙaunar Waziri tare da yadda dashi.
Shuru Lil prince yayi ba tare daya amsa gaisuwar da Waziri yake masa ba,kallon Mai martaba yayi kana ya sunkuyar da kansa ƙasa yace.
“Dan Allah kaji tausayina kabarni na samu farin cikina,ina sonta sosai bana sonta yayimin illah,kai shaidane ban taɓa ganin wata ƴar mace nace ina sonta da aure ba,dan Allah ka yar jemin kai shedane inayin dukkan abinda kakeso kuma ka umarceni akai,Allah da gaske nake son ZARINA”
Wani ɗan ƙaramin tsaki Saifu yaka jin yadda Lil prince ya cika kunnansa da surutu,jiyayi zaman fadar ya ishesa kuma daman lkcn tashi yayi dan haka kawai ya fice daga cikin Fadar gaba ɗaya ya nufi lambu.
Idanun Waziri ne yayi jaa kana ya ɗauke kansa tare da maidashi wajan Mai martaba domin yaji abinda zaice,wani Murmushi Mai martaba yayi kafin ya kalli Prince yace.
“Komai kakeso a nan duniya inayi maka,baka taɓa kukan babu ba,a wannan karan tunda kaji nace A’a saika samamin lafiya tun kafin fushina ya kufce a kanka,kaine ka kawota gidan ko ni?shin daman na kawota ne domin ka ganta kace kana so,kaje ka nemi duk wacce tayima ni kuma a gobe zan ɗaura aurenka da ita,bana son dugun zance tashi a gabana”wani ɓacin raine ya sauka a zuciyar Lil prince,cikin fushi da kuma ɓacin rai ya fice daga fadar.
Zaune ya sameta akan sofa tana yanke farce,wata duguwar sofa ya samu ya zaune,ɗan lumshe idanunsa yayi wanda suka janye sbd ɓacin rai,a hankali ya buɗe idanunsa ya mannasu akan ƙafarta wacce take fara tas baƙi gashi yayi ƙwance luff sai ƙyalli yake,haka nan ya samu kansa da kasa ɗauke idanunsa daga kan yatsun ƙafarta wanda suke jere abin sha’awa,ɗan juya eyes ball ɗinsa ya juya haka nan ya samu kansa dajin haushinta wanda bai san dalilin hakan ba,yadda tsigar jikinta ke tashi ya tabbatar mata cewa idanunsa na kanta,wani sanyi taji a ranta da kuma wata nutsuwa ta musamman na shigarta,cikin yanayi na shauƙi da kuma so,ta ɗago idanunta tare da saukesu a kansa,ajjiyar zuciya ta sauke mai ɗan ƙarfi lkcn da ƙyaƙƙyawar fuskarsa ta bai yana cikin ƙwayar idanunta,saurin janye idanunsa yayi ya rufe tare dajan ƙaramin tsaki kaɗan.
Wasu hawayene suka cicciko cikin idanunta wani tsanar zuciyarta ya kamata sabida a kullum ita ke sanyawa aci mutuncinta,amma yaya zatayi da hukuncin ubangiji tasan cewa dukkan abinda ta keji game tashi itane ta ɗurawa kanta ba,kuma bata da ikon hana faruwar hakan,
A hankali hawayen dake cikin idanunta ya samu damar saukan a kan innoncet face ɗinta,cije lips tayi jij rezar ta ƙwace ta yanki gefen yatsanta,ƙwaɓe fuska tayi kukan da take ɓoye ya kufce mata,cikin tsoro da kiɗima ta kalli yatsanta inda jini ke zoba,babu abinda ta tsana irin taga jini balle ta ganshi a jikinta,ƙwaciya tayi ƙasan carpert ɗin ta soma birgima tare da fasa wani kukan.
Ɗan waro manyan idanunsa yayi tare ƙunshe dariyan da yazo masa,sosai ya tsora mata idanu ganin yadda take birgima tare da kuka tamkar yarinyar baya.
“wayyo Mom wayyo Abbana zan mutu jini ƙafa shikenan jinina zai ƙare,yayana Safyan Yaya Tupic kuzo kuka yadda jinin ke zoba”
Ta ƙarasa maganar tana sakin wani sabon kukan,duk yadda yasu danne dariyan dake cinsa ya saki wani shegen murmushi wanda iya gefen bakinsa ya tsaya.
A kasalance ya miƙe tare da shigewa bedroom ɗinsa.
Sosai tane kuka tare da kiran sunan ƴan gidansu,a haka ta shiga sauke numfashi alamar bacci yayi gaba da ita.
Yana shiga bedroom ya zare rigan dake jikinsa tare da zame long carzy jeans ɗinsa mai kalan dark blue,cikin datti clothes ya sanyasu kana ya nufi fridge yana zuwa ya sunkuya tare da ɗauko ƙwaryar Furar daya amsa ɗazu wajan Mai babban ɗaki,
Miƙewa yayi yare da komawa tsakiyan bedroom ɗin ya zauna tare da lanƙwashe ƙafafunsa,a hankali ya ɗauki lodayin dake cikin ƙwaryar tare da ɗiban furar yakai bakinsa,daɗin furar da sanyinta ya sanyashi lumshe idanunsa tare dasa hannu ya shafi ƙwantaccen gashin dake ƙirjinsa,sosai furar tayi masa daɗi da garɗi saman harshensa,ware idanunsa yayi tare dakai wani lodayin bakinsa,sosai yake injoying na lkcn harya shanye furar bai sani ba,murmushi yayi tare da taune laɓɓansa,cikin ƙayatacciyar muryarsa mai amo yace.
“ya rabbi ashe na shanye”ya ƙare maganar yana pouying lips ɗinsa tare da shafa cikinsa wanda yaji yaɗan tasa,sosai yayi mamakin yadda ya saki jiki yasha furar har haka,rabon da yaci abinci harya ƙoshi ya manta daman mutum guda ke sanyashi yaci abu kuma baya kusa dashi.
Jin kasala na saukar masa ya sanyashi tashi ya maida ƙwaryar inda take,toilet ya nufa yana zuwa ya zare boxer’n dake jikinsa ya sakarwa kansa shower.
Sanyin ruwan da ya jine ya sanyashi lumshe idanunsa,few minutes ya buɗesu tare da saukesu a saman mararsa,sosai yake mamakin yadda mararsa ke yawan yi masa ciwo,hannu ya miƙa tare da ɗurashi saman ƙwantaccen gashin dake ƙwance a saman marar tasa,a hankali ya murza mararsa,ɗan runtsa idanu yayi jin wani zafi da raɗaɗi na ratsashi,zare hannunsa yay daga marartasa kana yaci gaba da wankan.
Brush yayi tare da ɗaura al’wala haka nan ya fito ba tare da wani towel ba.
A ɗan gaggauce ya shirya cikin wata buɗaɗdiyar riga ash colour kana ya sanya dugun wandonsa na uniform ɗinsa na sojoji,wani sihirtaccen parfume ya fesa,kana ya sauke hulan dake manna da jikin rigarsa tare da ɗanyin ƙasa da zip ɗin rigarsa wanda ya haddasa bai yanar faffaɗan ƙirjinsa wanda ɗauke da ƙwantaccen baƙin gashi.
Cikin nutsuwa yasa kai ya fice daga cikin bedroom ɗin tare da nufar parlour’n,direct hanyar dazai sadashi da ƙofar da zata fiddashi waje yayi,yana ƙoƙarin ficewa daga cikin parlour’n yaji saukar shassheƙar ajjiyar zuciyarta a cikin kunansa.
Tsayawa yayi cak tare da lumshe idanunsa a hankali ya juyo tare da ware idanunsa a kanta,tana ƙwance ƙasan carpert tana sauke ajjiyar zuciya tana sauke numfashi,a hankali ya maida idanunsa zuwa kan yatsanta da har yanzun ke fidda jini,ƙara lumshe idanunsa yayi ba tare daya buɗe ba ya ƙarasa inda take ƙwance,cikin nutsuwa ya sanya hannunsa duka biyun ya ɗagota zuwa jikinsa,ƙara lafewa tayi jikinsa tare sa sauke ajjiyar zuciya.
Zama yayi da ita a jikinsa,yana jin yadda zuciyoyinsu ke bugawa a tare,a hankali ya miƙa tattausan hannunsa ya ɗurashi bisa ƙafarta.Saukar hannunsa ƙan yatsan ƙafarta ya sanyata sakin wata nauyayyiyar ajjiyar zuciya,Narkakkun idanunsa wanda suke a ɗan lumshe ya tsorawa yatsan ƙafar nata,wanda har yanzun yake fidda jini,lumshe idanu yayi yana jin tsigar jininsa na tashi,tabbas shima ya tsani jini baison ganinsa,amma sabo da yanayin aiki yasanya dan dole yake jurewa idan ya ganshi,cikin yanayin kasa ya ɗura hannunsa dai² inda jinin ke zoba,nan yaga ashe da gaske yankewan tayi ba sakalci bane.
Ganin jinin yaƙi tsayawa yasa a hankali ya ranƙwafa kansa zuwa wajan ƙafan nata,cije laɓɓansa yayi kana cikin dauriya da jarumta ya ɗura laɓɓansa bisa inda jinin ke zoba.
Sanyin laɓɓansa da taushinsu da taji saman skin ɗinta,ya tsanya ta ƙara tura kanta bisa faffaɗan ƙirjinsa,cikin rashin sa’a ta ɗura jajayen laɓɓanta bisa tsinin nipples ɗinsa wanda suke a baiyyane,kasan cewa buɗaɗdiyar riga ya saka.
Wani irin abune yaji ya kama jikimsa tamkar wutar nefa ya jashi,a hankali gargasar dake ƙwance bisa jikinsa suka soma mimmiƙewa sabida wani baƙon yanayi daya samesu,domin wannan shine karo na farko daya taɓa sanya wata ƴar mace a jikinsa,har suka samu kusanci haka.
Pouting lips ɗinsa yayi kafin ya buɗe manyan gajiyayyun idanunsa ya sauke bisa ƙyaƙƙyawar fuskarta mai ƙyau da kuma tsari,tabe baki yayi kafin a hankali kuma cikin nutsuwa ya sanya tattausun laɓɓansa akan yatsanta,wata nauyayyiyar ajjiyar zuciya ta sauke,cikin nutsuwa ya shiga zuge raguwar jinin dake ɗiga ta wajan yankan,saida ya tabbatar babu abinda yayi saura sannan ya ɗauke laɓɓansa tare da fesar da wani zazzafan huci ta hanci,dariya ta kusa bashi amma ya shanye sabida bata daga cikin halinsa yawan dariya,gaba ɗaya ta shige jikinsa ko kanta ba’a gani sabida yadda ta turashi cikin ƙirjinsa,gaba ɗaya ta kanainayeshi,miƙewa yayi da ita a jikinsa,cikin nutsuwa ya nufi bedroom ɗin da take ƙwana,yana zuwa ya shimfiɗeta tare da lulluɓeta da duvet,remote ya ɗauka ya rage mata gudun A.c’n,juyawa yayi tare da tsora mata idanunsa kamar me neman wani abu a jikinta,wani tattusan murmushi ya saki ganin yadda ta tura yasanta cikin baki tana tsotsa tamkar ta samu sweet,lumshe idanunsa yayi cikin kasala ya saka kai yabar bedroom ɗin nata.
Yana fita direct sashin Mai babban ɗaki yayi,cikin tafiyarsa mai kamala da kuma nutsuwa yaɗi isa da kamala,sannu a hankali yake tafiya daddaɗar iskar da ake tana ratsa sassan jikinsa,tsayawa yayi cak lkcn daya ƙarasu gaban ƙawatacciyar ƙofar,numfashi yaja kana ya juya kaɗan ya kalli Batade kamal wanda shima shi yake kallo,da sauri Kamal ya ɗauke kansa tare da ɗaukan remote ya buɗe ƙofar,a hankali ƙofan ya buɗe cikin nutsuwa ya sanya kansa cikin babban parlour’nta wanda tafi yawan zama cikinsa,tunaninsa kam ya bashi dai²,tana kishin giɗe saman wata dadduma mai taushi da laushi,hannunta riƙe da casbawa tana jaa,gabanta kuma fruit ne kala² sai damammiyar fura wacce taji zuma,wani ƙawataccen murmushi ya saki tare da lumshe idanunsa,cikin nutsuwa ya ƙarasa inda take zaune tare da zubewa gabanta.
Murmushin jin daɗi tayi tare da faɗin “ohh na ɗauka ganina kawai kazu shine kaƙi ƙarasuwa”ta ƙare maganar tana ajjiye casbawar hannunta.
Baice komai ba sai kansa daya ɗura bisa cinyoyinta yana sauke ajjiyar zuciya,hannu tasa ta shiga shafa sumar kansa,tana lura dashi a duk sanda ya raɓo da jikinta,saiya daɗe yana fidda ajjiyar zuciya da numfashi kafin ya ɗago yayi mata magana.
Sun ɗau lkc a haka kafin ya ɗago kansa,cikin kamilalliyar murya mai daɗi yace.
“Kinyini lafiya ya ƙarfin jikin?”ya ƙare maganar yana pouting lips ɗinsa wanda sukai jaa sbd yawan taunesu da yake.
“lafiya Allhamdulillah Yarona,ina ita Zarinan?”..”Ammi bacci take fa”jinjina kai tayi sannan tayi masa nuni da ƙwaryar dake gabanta,babu musu ya ɗauki ƙwaryar tare da langwasa ƙafunsa ya fuskanceta sosai,furar ya soma sha,saida ya kammala sha itama ya bata tasha sosai, tissue ya ɗauka ya goge mata bakinta shima ya goge nasa,gyara zama yayi tare da riga hannunta duka biyun ya zuba mata narkakkun idanunsa,hannu tasa ta shafi fuskarsa jin abu mai ɗumi nabin fuskar tasa yasa tayi saurin faɗi.
“why?”ta faɗa cikin ƙasa dayin murya.
Sunkuyar dakai ƙasa yayi tare da ƙara matse hannunta dake cikin nasa,can ƙasan maƙoshi wanda ita kaɗai zata iya jin abinda yake faɗa,ya soma yi mata magana mai kama da raɗa.
“ohh shine abin kuka kamar ba soja ba?”ta ƙare maganar tana ja masa hanci,langwaɓar dakai gefe yayi tare da faɗin.
“Ayya Ammi ya haka?”hannunta ta zame daga nasa kafin tace.
“Zarina zata dawo nan da zama idan Ansha ruwa sai kazo nan muyi buɗe baki gaba ɗaya”shuru yayi mata yana jinjina girman abinda take faɗa,lumshe idanu yayi tare da taune laɓɓansa da ƙarfi tamkar zai rabasu gida biyu,cikin dauriya da kuma jarumta yace.
“ok to”
Shira suka shigayi a tsakaninsu yau Saifu hadda yin dry tamkar bashi ba,hakan kuma ba ƙaramin ƙyau yayi masa,sai haibarsa da ƙwarjininsa suka ƙara bayyana a fili fiye da da,kiraye-kirayen sallah Isha’i ne ya sanyashi tayi dare da kiran Hadima Kaltume yace.
“ohh ya maza ɗaura mata al’wala”yana faɗin hakan yasa kai ya fice daga sashin gaba ɗaya.
Yana fita sukaci karo da Mai martaba yana gyara Alƙyabba zai shiga sashin Mai babban ɗaki,tsayawa sukai gaba ɗaya suna kallonsa zuciyar Mai martaba cike da mamakin ganin Saifu zuciyarsa cike da tambayoyin yadda akai yasan flat ɗin harya fara shiga cikin sashin nata ba tare daya sani ba,Saifu kuma kallo ɗaya yayi masu yayo ƙasa da kansa,sosai yake kokawa da laɓɓansa da sukai masa nauyin gaske a ƙoƙarinsa nason faɗin.
“barka da fitowa Mai martaba”wannan kalmar ita yake son faɗi amma laɓɓansa sunyi masa nauyin da bazai iya buɗesu ba bare har yayi tunanin faɗin abunda ke ransa.
Waziri dake kusa da Mai martaba shine ya dakawa Saifu tsawa tare da faɗin “hattara yaro Sarkin sarakunane gabanka sunkuya ka ƙwashi gaisuwa”
Shuru yayi masu sabida baya tunani zai duƙawa wani bawai sabida bai isa ba,dalilin tsawar da Wasiri yayi masa itane tasa bazai aikata hakan ba,saidai su sallamesa a aikin da ace ya aikata abinda sukeso,Mai martaba dake tsaye yana kallon ikon Allah ya saki murmushi tare da faɗin.
“Saifudeen kenan yau gaisuwa aka kawai Mai babban ɗaki kenan?amma zaifi ƙyau ka tsaya iya matsayinka”yana faɗin hakan yaja jiki suka ƙarasa sashin Mai babban ɗakin.
Wani murmushin gefen baki Saifu yayi ba tare da tunanin komai ba yaci gaba da tafiya harya ƙarasa cikin masjid ɗin da aka fara yin sawo domin gabatar da sallan issha’i.
*** ***
Sannu a hankali yake tafiya cikin nutsuwa da kamala,yana tafe yana lumshe idanunsa tare da shaƙar daddaɗar iskar dake kaɗawa mai daɗi da kuma sanyi,hannu yasa ya murda handle ɗin ƙofar tare da tura kansa ciki,yana nan parlour’n yadda ya barshi babu abinda ya sauya saima wani daddaɗan ƙamshi dake fitarwa.
Direct bedroom ɗinta ya nufa,a ƙwance ya sameta kamar yadda ya barta,wani ƙawataccen murmushi ya saki ganin yadda gashinta yayi ɗai-ɗai bisa pillow’n da take kai sai ƙyalli da sheƙi yake fiddawa.
Ƙarasawa gefen bed ɗin yayi ya zauna tare da kafeta da sexcy eyes ɗinsa,wani yawo mai ɗacin gaske ya haɗiya yana jin yadda mararsa keyi masa ciwo tare da murɗawa,hannu yasanya tare da jawota zuwa jikinsa,cikin wani irin yanayi mai kama da feelings ya tura kansa tsakiyan wuyanta,ya shiga shaƙar daddaɗan ƙamshin dake fiddawa ta cikin wuyanta,ƙara tura kansa yayi tsakiyan wuyanta,tare da sanya hannu ya tura cikin yalwataccen dugun baƙin gashin kanta,wani zazzafan numfashi ya sauke yana jin daɗin yanayin da yake ciki,jin yana samun sauƙi daga jikinta ya sanya ya ƙara matseta cikin jikinsa,a hankali ya shiga sauko da kansa zuwa tsakiyar ƙirjinsa,numfashin sane ya tsaya cak jin abinda bai taɓa jiba,laɓɓansa yasanya a wajan tare da sakar mata wani lafiyayyan kiss mai tsayawa a rai da zuci musamman ga sabbin balaga irinsu Zarina.
Jinta a sabon yanayi ya sanya ta ƙara shige cikin jikinsa ta shiga fidda wani wani numfashi,a hankali kuma ta soma buɗe manyan idanunta wanda suke cike da bacci,ƙara lumshe idanunta tayi sabida wani dishi-dishi da take gani,few minutes ta ware idanunta tar a kansa,cike da tsoro tayi saurin jan jikinta gefe guda,gaba ɗaya jikinta ya soma rawa,bakinta na rawa tace.
“Saifu kaine why? Haka kake daman,ashe gwamma Lil prince dakai,mene yasa zuciyata ta amince da fasiƙin mutum mazinaci irinka,wlh Saifu na tsaneka,ko abinda na keji a zuciyata zaimin illah bazan taba kasan cewa dakai ba,nagode Allah daya nunamin gskyan halinka tirr dame fuska biyu,nazu na kasance dakai *ABADAN DA’IMAN* amma halinka yajamin rugujewar burina tabbas kaiba alkairi bane”ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kuka mai taɓa zuciya.
Wani lafiyayyan murmushi ya saki tare da miƙewa ya shafi sajen dake ƙwance saman fuskarsa,cikin nutsuwa ya ƙara sanya hannu ya riƙota,tare da zura hannunsa saman lafaffan cikinta tare da sanya ƙaraimin yatsa ya shafi ramin cibiyanta,wani kukan ta ƙara saki tare da koƙarin ƙwance kanta,ƙara matseta jikinsa yayi tare da ɗura bakinsa cikin kunanta,cikin daddaɗar muryarsa yace.
“baki mamakin ba lkcn dana zaɓeki as my maid,kiyi tunani hakan ƴan mata,nina matane mata kuma nawane”ya ƙare maganar yana sakar mata hucin cikin bakinsa.
Daimond ring ɗin dake manne jikin hannunta ya soma fidda wani sihirtaccen haske wanda ya cika ɗakin,a hankali ya saketa tare da saurin saka hannu ya dafe forehead ɗinsa sake sara masa,miƙewa yayi tare da saurin barin bedroom ɗin.
Wani kuka ta fashe dashi,tare da ɗaukan pillow ta rungome ta soma sakin ajjiyar zuciya zuwa yanzu kukanma yayi ƙaura daga cikin idanunta,wani ƙunci da baƙin cikine kwance cikin zuciyarta,yayinda da take jin wani zafi da raɗaɗi a cikin ranta,hawayen dake maƙale cikin idanunta ya samu damar saukkowa sabida lumshe idanunta da tayi,zuciyarta batai mata adalci ba,abinda takeso yaushi ke ƙoƙarin rabata da mutuncinta,tabbas ta tsanesa tsana kuma mai yawan gaske tsanar da bata taɓa yiwa wani ɗan adam,tayi al’ƙawarin ko zata rasa ranta baza ta taɓa amincewa dashi ba,daman ance zato zunubine,wanda take tunanin yana bin mata ashe ba shi bane,taune lips ɗinta na ƙasa tayi cikin muryar kuka tace.
“ka yafemin,lallai na ɗauki haƙƙinka,ka yafemin Lil prince”ta ƙare maganar tare da saurin dirowa daka kan bed ɗin tayi waje da gudu sabida ƙofar toilet da taga tana buɗewa.
*** ***
Yana durƙoshe gaban Fulani Kilishi yana sauraran abinda take faɗa masa,ɗago kai yayi tare da zuba mata jajayen idanunsa,kafin yace.
“wai mene yasa Mai martaba bazai tayani yaƙi akan neman Farin cikina ba,zuciyata babu daɗi ina sonta Fulani”ya ƙare maganar idanunsa na kawo ruwa.
Jinjina kai Kilishi tayi kafin tace “Magaji baka iyacin riba zama da mutane ba sam,ina ruwanka da Mai martaba ni Mahaifiyarka nayi maka al’ƙawarin samun Zarina kota halin ƙaƙane”
“amma sai yaushe ne?bana son aikata wani abu da ita nafison mallakarta matsayin mata,ina jin wani abu game da ita ina hqr ne kawai”ya ƙare maganar yana kallon Mahaifiyar tasa.
“kai mene zai dameka kana da kuɗi mulki iko,kana da ikon da zaka aikata komai a duk lkc’n da kaso,kana da ikon da zakai mu’amula da dukkan macen da kakeso babu wanda ya isa yayi komai,ballatana Zarina da take matsayin Kuyanga kuma baiwa a masarautar bilhas,maza jeka gareta hakan shine zai baka ikon mallakanta cikin sauƙi”
Wani murmushin jin daɗi yayi domin samun ƙarfin quiwa da yayi wajan Mahaifiyar tasa,yana tunanin wannan hanyarce kawai zata mallaka masa Zarina kuma ya shirya yin hakan indai zai samu Farin cikinsa,domin sosai yake sonta hakan kuma bai sauya komai daga cikin halinsa ba,cikin farin ciki ya miƙe tare da yiwa Fulani kilishi saida safe.
Yana fita ya shiga sashinsa tare dayin wanka ya shirya cikin wasu ƙananun kaya daibai taɓa sawa ba,a gaggauce ya fice daga ɗakin ya nufi sashin Saifu domin a nan yake tunanin ganinta,yana cikin tafiya yaji ance.
“Allah ya taimaki Magaji mai jiran gado wajanka nazo”
Juyowa yayi domin yaga mai Maganar,wani dugun tsaki yaja ganin Waziri ne,wanda a ƙalla zai iya zama age mate ɗin Mai martaba,cikin faɗa-faɗa yace.
“meye?”
“daman shawara nazu baka yadda zakai ka samu auren KUYANGA ZARINA” wata dryar rainin hankali Lil prince yayi kana yace “ohh kai har kana da wani power da zaisa na auri Zarina,ds shawarar da rashinta duk ɗaya domin aurenta gareni babu fashi,ɓacemin da gani!”ya ƙare maganar yana sakar masa tsawa,cikin rawar jiki Waziri ya miƙe tare da maida ƙwallan idanunsa ganin yaro ƙarami yana gaya masa magana,da sassarfa ya bar wajan,Lil prince shima hucewa yayi tare da shigewa cikin sashin Saifu,hannu yasa ya murɗa handle ɗin ƙofar tare da tura kansa cikin ɗakin.
A tsaye ya samu Saifu wanda shigowarsa kenan,yana tsaye a wajanne sabida kukanta da kunnuwansa suke jiyo masa.
Zarina kam kasa buɗe ƙofar tayi sbd tsoran daya gama ratsa zuciyarta,cikin sa’a ta samu nasarar buɗe ƙofar tare da ruguwa da gudu tayi parlour,bata duba wake kusanta ta faɗa jikinsa tare da rungomesa ta saki kuka mai tsuma zuciya.
Lumshe idanunsa yayi yana jin yadda kukanta ke sauka cikin kunnuwansa,a hankali Saifu ya buɗe idanunsa tare mannasu a kanta,ganin yadda jikinta gaba ɗaya ke rawa ya tabbatar masa bata cikin nutsuwarta ya sanyashi ɗagota daga jikinsa tare da tallafo haɓarta cikin zazzaƙar muryarsa mai daɗi yace.
“kee! Kedawa?”ya tambayeta tare da ɗan buga kumatunta kaɗan.
Idanunta ta buɗe tare da saukeso akansa,cikin tsoro da firgici taja baya tare da nunasa da yatsa👉🏼kamar za tace wani abu sai kuma tayi shuru tare da durƙoshewa wajan tace.
“dan Allah idan wani abu nai maka kayi hqr ka barni haka,kada ka lalatamin rayuwata kada ka rabani da mutuncina”
Ɗan waro idanunsa yayi alamar mamaki,domin baisan mene ya aikata mata har haka ba,taɓe baki yayi tare da ɗag kafaɗa yaja ƙafa yabar wajan ya shige cikin bedroom ɗinsa.
Baƙin ciki da takai cine ya sanya Lil prince saurin ficewa daga cikin parlour’n yayi waje.
Kuka Zarina ta fashe dashi tana jin duniyar gaba ɗaya na juya mata,ta kurewa waje guda tayi tana sauke numfashi,a haka bacci yayi gaba da ita.
Kasa bacci yayi sai juyi yake saman bed,miƙewa yayi tare da saka bedroo slippers ya nufi parlour,ƙwance ya ganta tana bacci yatsanta a hannu sai sauke ajjiyar zuciya take,idanu ya ƙura mata yana tuna irin maganganun ta faɗa masa ɗazun,lumshe idanunsa yayi tare da lafewa jikin luntsumemiyar kujerar da yake kai.
Saukar wata ƙarar bindiga a kununwata ya sanya ta farka daga baccin wahalan daya ɗauketa,a firgice ta faɗa kansa sbd tsananin firgicin data shiga,duk da yana cikin damuwa bai hana shi sakin murmushi ba,wannan ƙaran bidigar kuma ya tabbatar masa da cewa shaidar anga watan RAMADANNE kowa ya ɗauki niya,lumshe idanu yayi yana jin yadda ta lafe jikinsa tana sauke numfashi..
Saifu na fitowa daga ɗakin Zarina bayan hasken dake fita ta cikin daimond ring ɗinta,a bakin ƙofa ya tsaya tare dayin wata girgiza saiga wata iska mai ƙarfi ta bayyana cikin abinda bai huce ƙiftawar idanu ba,halittarsa ta rikiɗe ta koma wani zabgegen baƙin dodo👹mara fasali wara kururuwa yayi saika wani hayaƙi na fita ta cikin bakinsa,a hankali jikinsa ya fara zagwanyewa yana ƙasa harya koma tulin wani baƙin yaƙi,wata ƙara aka saki sai kuma yahaƙin yayi sama,a dai² wannan lkc’n kuma Saifudeen ya dawo daga masallaci.