THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 6 BY NIMCYLUV

 THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 6 BY NIMCYLUV


Lumshe idanunsa yay tare da fesa mata hucin hancinsa akan fuskarta,mai makon yay kissing lips ɗinta kamar yadda yay niyya sai kawai ya zare laɓɓansa daga cikin nata.

Zarina kam numfashin tane ya kusa ɗaukewa,sabida yadda taji saukar laɓɓansa cikin bakinta ba ƙaramin sauya mata lissafi yay ba.

Sosai take sauraran ɗumin cikin bakinsa dake ratsa cikin ƙaramin bakinta,gaba ɗaya ta sare ta sallama tana jiran taji abinda zai biyo baya,hakan kuma da yay mata ya ƙara tabbatar mata da zargin da take masa na lalata ƴar ƴan mutane,wani ƙunci da baƙin cikine suka cika zuciyarta ladamar saninsa ta ɗarsu cikin zuciyarta,shuru kawai tayi tana sauke ajjiyar zuciya sabida kukan da tayi dalilin marukan daya sauke mata.

Ga mamakinta mai makon ya sumbaci leɓenta na ƙasa daya sanya cikin bakinsa,sai taji ya zare bakinsa gaba ɗaya daga cikin nata.

A hankali ta sauke ajjiyar zuciya tare da buɗe idanunta da sukai mata nauyi sabida kumburar da sukai,idanunta ta tsura masa kamar yadda ya kafeta da nasa fitannun idanun wanda suka sauya kala zuwa jaa tare da ɗan janyewa sabida ɓacin ran dake ƙwance cikin zuciyarsa.

Juna zuka zubawa idanu yayinda ƙwayar idanunsu ke yawo cikin na ko wannansu,yaya zaiyi da soyayyarta wacce ta shigesa lokaci guda?,mene makomar zuciyarsa data faɗa soyayyar da ƙaramar yarinya wacce ya kewa kallon “ƙwaila?”,meyasa take masa kallo nada ban?,shin ya taɓa aikata mata wani abune wanda ba dai² ba?,ta jefesa da maganganu marasa daɗi wanda suke dai² da tarwa tsewar zuciyarsa.

Taje fesa da abu mafi mune,ta haɗasa ta kallma mai munin gaske,kallamar dako da wasa baison jinta,hasalima ya tsani duk wani mutum mai aikata ta.

Kallamar “Zina”data haɗashi da ita ba ƙaramin ɗaci da muni taiwa zuciyarsa ba,yana jin wani ɗaci da baƙin ciki a ransa,zuciyarsa nayi masa zafi da raɗaɗi fiye da tunanin dukkan mai karatu.

Yana daurewa tare da ƙoƙarin danne damuwarsa bai son taga rauninsa ko kaɗan bai shirya hakan ba.

Cike da kuzari da kuma jarumtar daya arowa kansa ya ƙwantar da kansa bisa kafadarta tare da sanya hannunsa ya rumgeme waist ɗinta dashi.

Numfashi ya sauke mata tsakanin wuyanta,sosai yay hugging ɗinta a jikinsa yana sauraran yadda bugun zuciyarta ke tafiya,Zaiyi fata ace numfashinta da bugun zuciyarta baya tafiya saida tunaninsa,soyayya sam ba tai masa adalci ba data haɗa shi da ƙaramar yarinya wacce sam baiga abin ɗauka a jikinta ba.

  Yadda yake sauraran bugun zuciyarta haka itama take sauraran tasa bugun zuciyarsa wacce take gudu very past,tana fata ace bugun zuciyarsa da tunaninsa baya fita saida tsanarta,kamar yadda nata numfashin baya taɓa fita saida tsanarsa,tayi masa tsana mafi muni,tayi masa tsanar da bata taɓa tunanin za taiwa wani ɗan adam shi ba.

  Hawayen dake maƙale cikin ƙwayan idanunta suka samu damar silalowa tare da sauka bisa ƙafaɗarsa,taune laɓɓanta tayi tana jin yadda zuciyarta keyi mata zafi da kuma raɗaɗi.

Saukar hawayenta saman kafaɗarsa yay dai² da yadda Zuciyarsa ta ƙara gudu da ƙarfin gaske,a hankali ya zare jikinsa daga nata tare da zuba mata gajiyayyun idanunsa masu kaifi,a sanyaye ya kama hannunta tare da ɗurashi  bisa saitin zuciyarsa.

Runtsa idanunta tayi sabida yadda taji ƙirjinsa na bugu kamar zuciyarsa zata fasu waje.

Pouting lips ɗinsa yay tare da lumshe idanunsa some minutes ya buɗe a hankali tare da saukeso bisa ƙyaƙƙyawar fuskarta,matso da fuskarsa yay dab da tata,can ƙasa maƙoshi yay amfani da muryarsa wacce tayi ƙasa da yawa yace.

“RINA..”shuru yay kafin yaja da numfashi ya ɗora da “kinji yadda zuciyana ke gudu a kanki,ohh wow thank you babyluv kinyi nasarar tafiya da zuciyata,kinsa na shiga halin damuwa da kaɗaici duk akan ke ɗaya,zan iya ninka shekarunki guda uku amma na buɗe baki nace ina sonki..”numfashi ya sauke tare da taune laɓɓansa kana yaci gaba da faɗin “see you kene zaki dubeni da idanunki da kuma bakinga kice baki sona for what reason ma?ohh ya rabbi zuciyana ciwo babu daɗi duk a kanki”.

    Shuru tayi masa tana jin tsanarsa na ƙara nunkuwa cikin zuciyarta,da ace zai iya ganewa babu shakka daya batta taji abinda yake damunta,tabbas da ace zai iya ganin yadda tsanarsa tayiwa zuciyarta ƙawanya daya rabu da ita.

   Miƙewa yay tare da sanya hannunsa bisa kafaɗarta ya miƙar da ita tsaye,hannayensa ya sanya ya tallafo haɓarta tare ƙurawa lips ɗinta idanu wanda sukai red sabida tsabar taunesu da take,duk yadda yasu tace masa wani abu ƙi tayi saima haɗe fuska da tayi tare da ɗauke fuskarta zuwa wani wajan.

   Matsuwa yay kusanta tare haɗe jikinsu waje guda yana jin ɗumin jikinta na ratsashi,hawayen fuskarta ya sanya hannu ya share mata,bakinsa ya ɗora bisa nata kana ya ware laɓɓansa hakan ya bawa lips ɗinta na ƙasa damar faɗawa cikin bakinsa.

A karo na biyu ya haɗe laɓɓansa waje guda tare da lumshe idanunsa kana yaywa lips ɗinta wani mahaukacin tsotsa.

Wani numfashi suka sauke a tare kana yaɗan ƙara shigewa jikinta sabida yadda jikinta ya fara rawa.

Zare bakinsa yay a hankali tare da ɗorasa bisa tsinin hancinta nanma ya sauke mata sumba,haka idanunta da kuma kuncinta.

Kansa ya ɗora bisa wuyanta tare da sanya bakinsa cikin kunanta ya sakar mata da wani zazzafan huci ta cikin bakinta,da wata murya mai sanyi yay amfani wajan faɗin.

“Just wait for me,i will come back,komai nisa komai daɗewa zan dawo WAIT FOR ME BABYLUV”.

Hawayen dake manne cikin idanunsa ne suke ƙoƙarin fallasa kansu ta hanyar sakkowa,murya mara sauti yay saurin faɗin.

“Goodbye”kana ya sakar mata wata lafiyayyiyar sumba tare sanya mata wata envelope  a hannunta,da sauri ya juya tare da fice daga sashin gaba ɗaya.

Zubewa tayi akan sofa tare da sakin kuka,sosai take kuka mai taɓa zuciya,ta nayi tana sauke ajjiyar zuciya,wani baƙin ciki da takaicine yay ƙwance cikin zuciyarta,yayinda wutar tsanarsa ke ƙara ruruwa cikin rai da zuciyarta,runtsa idanunta tayi tare dajan pillow ta rungome ta soma sakin ajjiyar zuciya a jajjere.

  Lil prince dake baƙin ƙofar shigowa sashin na Mai babban ɗaki,yay saurin sakin wani shu’umin murmushi lokacin daya gama jin abinda Saifu ke faɗawa Zarina,da kuma abinda Zarinan ke faɗa masa,da sassarfa yabar wajan sabida alamun tafiya da yaji anayi za’a fito waje.

  A hankali ya fita daga cikin sashin Mai babban ɗaki,yana tafe yana bada ɗan faɗin,cikin da juriya da isa yake tafiya,time to time yakan lumshe idanunsa tare da sakin ajjiyar zuciya shikaɗai yasan me ya keji mene kuma yake damunsa,tabbas soyayyarta halittace a zuciyarsa,bawai a sanin da yay mata na yanzu ya fara jin sonta ba,ya sota a lokacin da baisan mene shikansa so ɗin ba,yay dakon sonta tun baisan zai ganta a nan duniya ba,domin tunaninsa ya gama bashi ita ɗin ba mutum bace sabida yawan mafarkin da yake da ita,a ranar daya sauka Masarautar bilhas a ranar ya san cewa soyayyarta ta riga da tayi masa illah,taune lips ɗinsa yay tare da son kawar da abunda yake ransa,sam bai son rauninsa ya bai yana ta dalilinta bai shirya hakan ba sam.

Agogon dake manne a tsintsiyar hannunsa ya kalla ganin har shaɗaya ta kusa.

Da ɗan sassafar ya ƙarasa sashin Mai martaba kamar yadda ya umarci shi akan ya sameshi a tirakarsa.

Yana zuwa bakin ƙofar ya ɗan tsaya haka nan ya samu kansa da samun faɗuwar gaba,addu’ar neman tsari yay kana ya sanya kansa cikin tirakar tare dayin sallama cikin muryarsa mara fita.

   Daga can cikin tirakar Mai martaba yay gyaran murya tare da bawa Saifu damar shigowa daga ciki.

  A hankali ya sanya kasan bakinsa ɗauke da wata addu’ar,kana ya ƙarasa shiga cikin ƙawataccen parlour’n na Mai martaba wanda yaji kayan mure rayuwa.

Zaune ya samesa bisa wani cosin mai ƙyau da kuma laushi,gabansa ciki yake da kayan marmari kala²,danginsu pineapple,mango,orange,inibi,apple,gauva,fasadabir.

Gefe guda kuma al’kakine,dubulan,makilawa,sai kilishi wanda yaji kayan haɗi.

Zama yay tare da langwashe ƙafafunsa ya fuskanci mai Mai martaba,kamar zaice wani abu sai kuma ya share kawai ya sunkuyar da kansa ƙasa tare da zubawa wani zobe dake hannun Mai martaba idanu.

   Tun shiguwarsa Mai martaba ya zuba masa idanu yana mai gasgata zancen Ciroma da sukai ɗazu,shi sam bai kula da hakan ba sai yanzu,wani murmushin gefen baki yay cike da izzah yace.

    “A’a kace harka fito yau sai ganin Abbunka daya ƙwace mana kai”

  Kallonsa Saifu yay na wani lkc kana ya ware laɓɓansa yace.

    “Eh! Nayi missed nashi ne fa”

“ok ka gaishesa,amma yana da kyau ka dawo kafin sallah,sabida aƙwai shagalin ƙaramar sallah da ake bisa tsari kuma a al’adance,hakan tasa dole muke neman tsaro mai kyau bisa taimakonka kuma”ya ƙare maganar yana ciro bandir ɗin ƴan 1k sabbi fil kusan bandir goma ya ajjiye gaban Saifu sannan yace “ga wannan aiwa mutun gida abin buɗe baki”

   Girgiza kai Saifu yay cike da kuzari da izzah yace “No! Thank you gwamnati na biyana,ban amsar naka”

  “nikam Saifu zanzo insan wanene kai,idan na kalleka sai kayimin kama da Fulanin daji masu kiwo da manyan shanu”

  “uhmm idan wannane tunaninka to basshi a hakan”yana faɗin hakan ya miƙe tare da nufar hanyar da zata sadashi da waje,yana gaf da fice yaji Mai martaba yace.

   “ka rage wannan izzar taka,kabar wanda suka gajeta suyi ta ƙama da ita ba talakawan ƙasa irinku ba”

  Tsayawa Saifu yay cak,tare da sauke wani numfashi ɗan cizon leɓensa yay kana ya juya ya kalli Mai martaba,a hankali yace.

   “wasu izza a jininsu take wacce ta zame masu halayya,wasu kuma mulki ke saso,idan kuma kana ta ƙama da mulkin kane babu shakka munga FIR’AUNA yana ina yanzu?babu wani mulki dake tabbata idan bana ALLAH ba,dan haka izza a jini da tsokar SAIFUDEEN take na barka lafiya”

   Yana faɗin hakan ya sakai ya fice daga sashin gaba ɗaya,da idanu Mai martaba ya bisa yana ƙara mai-mai ta maganganun da Saifu’n ya faɗa masa,wani murmushi ya ƙarayi mai cike da ma’anoni,wayarsa ya ɗauka tare da kiran wata number,yana kira akai picking.

Daga can ɓan garen akace.

    “Allah ya ƙarawa Mai martaba lafiya,Allah ya taimaki sarkin sarakuna barka sa shan ruwa”

  Ba tare daya amsa maganar da yay masa ba,cike da ƙasaita yace.

  “abi bayansa yanzu har zuwa inda zashi”yana faɗin hakan ya kashe wayar,tare da miƙewa ya nufi ɗakin da shigarsa ya zame masa kamar al’ada a watan azumin da kowa yake neman rabauta da rahamar ubangiji.

  Lil Prince cike da farin ciki ya shige sashinsa,yana mai jinjina abinda zai aikata akan tafiyar Saifu’n,tabbas zai dawo ya samu mummunan labari,domin zai dawo yaga Zarinan dake neman zaucewa a kanta ta zama mallakinsa ta zama matarsa ƙarƙashin inuwarsa,zai mallaketa kamar yadda suka mallaki masarautar bilhas gaba ɗayanta.

   Zarina kam kanta ne ya shiga sarawa tare dayi mata wani mahaukacin ciwo,a hankali kuma wani zazzafan zazzaɓi ya fara ratsa cikin gaɓoɓinta,hakan ya haddasa mata jin wani tsayi na musamman na shigarta,curewa waje guda tayi dan ba tajin zata iya miƙewa tsaye bare harta nufi ɗaki ta ƙwanta,zafin zazzaɓinne ya tsananta a jikinta cikin fitar numfashi da wahala ta soma sauke wata sabuwar ajiyar zuciya,yadda jikinta ke tsumane ya haddasa gazawar numfashi wanda ya fara fisga  kamar wacce ake shirin zarewa rai.

Wasu tawagwan hawaye ne masu zafi suka soma sauka bisa kuncinta,duk yadda kake tunanin zaka fassara halinda take ciki yafi ƙarfin hakan.

Kuka ta fashe dashi jin ciwon nata ya sake tsananta ga babu wani kusa mai taimakonta,a haka tai ta zama tana rera kuka har bacci yay  nasarar ɗauketa.

A hankali saifu yake taka steps ɗin jet wanda ya daɗe da sauka a babbar harabar masarautar bilhas,sai da yaje steps ɗin ƙarshe ya tsaya tare da juyawa ya zaubawa masarautar idanu,zuwa wasu minutes ya ɗauke idanunsa tare da ƙarasa shigewa cikin jet ɗin.

Wata lafiyayyiyar kujera ya nema ya zauna akai,kana ya kashe wayoyyinsa ya ajjiyesu bisa side ɗinsa,lumshe idanunsa yay yana sauraran gudun zuciyarsa wacce take fita da ƙarfin gaske.

“ya rabbi ka karesu na danƙa amanarsu bisa hannunka”

Yana faɗin hakan ya ƙara lumshe idanunsa,yana jin yadda jet ɗin ya fara kewaya masarautar a hankali kuma ya luula zuwa sama.

A hankali jet ɗin ke luulawa saman gajimare harya ɓacewa ganin Ciroma.

Numfashi Ciroma ya sauke tare da ɗauko waya ya kira number Mai martaba,wajan ringing uku ya ɗaga,Ciroma najin ya ɗaga wayan yace.

“Allah ya ƙara maka lpa yaron nan ya shammace mu,har Masatautar bilhas jet ɗinsa ya sauka yanzu haka sun jima kaɗan da barin wajan”.

Daga can ɓarin Mai martaba yace.

“Ohh zai san da Sarki Khalid Bilhas yake magana,jeka abinka kawai”yana faɗin hakan ya ƙatse wayar tare da wurgi da ita,saman bed ya faɗa ya cukokuye jikinsa,bai jima bacci yay gaba dashi.

   Cike da farin ciki Ciroma ya nufi sashin dan shima burinsa bai huce ya cimma tasa buƙatar ta zama Sarkin Masarautar  Bilhas na 5.

  Yana ƙoƙarin shigewa sashin domin wunin yau curr baiga iyalinsa ba,yaji muryar Waziri a bayansa.

 “Mene kukeson aikatawa wa Saifudeen,mene yasa duk wani bakirci da za’a haɗa a wannan masarautar sai ansami hannunka ciki,Mulki fa ba hauka bane,wanda ubangiji ya ƙaddara zai zama Sarki bayan Mai martaba yay burabus dole ne ayi masa biyayya,amma ka zauna kana cin ƙafar wanda ya amince maka,koda yake sam bana ganin laifinka wlh,sabida Shima Mai martaba ba’a bisa ƙa’ida yake aiwatar da mulkin saba,nida fatana Ubanji ya kawo *Saɓon sarkin* dazai wakilcemu bisa gsky da kuma amana”ya ƙare yana kallon Ciroma.

 “Daka tamin nan Waziri waikai wanne irin mutum ne mai sa idon masifa,ina sane da cewa kaima fa mulkin nan kakeso,kuma nasan komai akan ɓoyayyen sirrin da kake ɓoyewa shekara da shekaru,da nasu da tuni nayi hanyar da zata saka a kulleka a ɗakin duhu na iya tsawon shekarunka,kayi gaggawar ɗauke idanunka daga kaina na faɗa maka”

  Kafin Waziri yay magana lil prince ya ƙarasu wajan,domin hanyarsa ce ta zuwa lambu,kallonsu yay gaba ɗaya kana ya buɗe baki yace.

“mene Wazirin ke ɓoyewa tsawon wasu shekarun maza faɗamin?”

  Da sauri Ciroma yace.

“Allah ya taimaki magaji mai jiran gado,ba wani abu bane kawai na faɗane don rantsa ya ɓaci,haka nan yazu yake gayamin magana ciki wannan daren a kuma wata mai falala”Ciroma ya ƙare maganar yana matso ƙwalla daga cikin idanunsa.

Lil prince ne ya kalli waziri yace “Kai baka taɓa tunani magana kafin ka faɗeta,mai yasa baka da tunani ne,ni sam banga abinda yasa Mai martaba yake zaune dakai ba,tunda Mahaifiyar ta sheƙa kasan dai mulki ba samunsa zakai ba,dan haka ka yayeni”yana faɗin hakan ya shige cikin lambun.

Da idanu Waziri yabi Prince Najeeb dashi,ganin hawaye dake ɓoyewa na neman bayyana kansu yay saurin barin wajan tare da shigewa ɓangarensa,daman tunda matansa ya mutu bai kuma wani auren ba.

“daga kai har Mai martaba ɗin dai² nake da ƙugunku,bare wani Magaji”Ciroma na faɗin hakan ya shige sashinsa.

Lil prince,

Da sauri ya shige cikin lambun tare da soma kewayesa yana son ya laluɓo inda Mai martaba yace masa aƙwai wata tsuhuwar aƙwati amma ya kasa gane inda take.

Haka yay duba shuru harya huce inda Zarina ta haƙa ta cilla aƙwatin ciki.

Apple guda biyu ya tsinka kana ya fice daga cikin lambun.

*_Washe gari_*

 Ya kama uku ga azumi,sosai jama’ar masarauta dama ƴan unguwa su kaji babu daɗi da tafiyar SAIFU wacce tazu masu a bazata.

Misalin 5 na yamma,Sarkin sakar gida ya fito da sauri sabida gaba ɗaya ya manta ance yaje ya fito da Kulsum daga ɗakin duhu.

Da sauri yake ratsawa cikin gidan sarautar sabida yana da girman gaske,saida yaje ƙarshe kana ya tsaya a wani ƙaramin ɗaki mai ginin bilan ƙasa,yana zuwa ya sanya masu tsaron ƙofa sauri buɗewa tare da bashi waje 

Girgiza gansa yay tare da faɗin.

“fito da ita”

Ya faɗa a taƙaice,juyawa Mai tsaron ƙofar yay tare shigewa cikin ɗakin mai duhun gaske ga zafi.

Tana ƙwance tamkar mara rai sai fidda numfashi take,rabonta da cin abinci mai ƙyau kuma isshesshe harta manta.

“kee! Maza fice”ya faɗa yana saurin fice sabida zafin daya fara damunsa.

Jan numfashi tayi tare da rarafawa ta fito daga cikin ɗakin,wata ajjiyar zuciya ta sauke tare da zubewa a wajan sabida wata daddaɗar iska data ratsata.

“maza tashi kiyi naki waje”cewar Sarkin tsakar gida.

Kulsum kam jiki a bace ta miƙe gabq ɗaya jikinta rawa yake sabida tsananin yunwa da kuma ƙishirwa mai yawa.

Tana zuwa sashin dazai sa data da ɗakinsu ta yanke jiki ta faɗi tare da soma ƙwarara amai tamkar wacce kayan cikinta zai fito.

Zarina da fitowarta kenan neman bushasshen zoɓo domin yau lemon zoɓo suke sha’awa ta hangi kulsum ƙwance a wajan aman da tayi.

Da ɗan sauri ta ƙarsa  wajanta duk da itama bawai lafiyanne da ita ba.

Tana zuwa ta kamota tare da sona jera mata sannu,idanunta cike da ƙwalla,haka ta taimaka mata zuwa ɗaki tare da haɗa mata ruwan wanka,bayan tayi wankan ta shirya ta kalleta tace.

“kina azumi ne”ta ƙarasa maganar da murya irinta masu azumi.

Kai Kulsum ta ɗaga alamar.

“eh”jinjina kai Zarina tayi domin ita kaɗai ne tasan abinda yake damunta.

“Kulsum dan Allah kiya femin a kaina akai maki wannan cin mutuncin,wlh aci zarafin wani akaina gwara banzo duniyar ba”ta ƙare maganar hawaye na zubuwa daga cikin idanunta.

“ke Alkairi ce garemu Zarina,kiyi amfani da damarki domin ki taimaki jama’ar garin Bilhas,aƙwai mutanan da aka ƙwace masu filayansu Zarina aka siyarwa gwamnati,aƙwai iyayen da aka karɓe ƴar ƴar yansu aka aka sai dasu ga wata masarautar,kamar yadda nima aka ɗaukoni daga garinmu na KOGI aka kawoni”

Ambarta sunan garin KOGI da tayi ya sanya Zarina saurin dafe kanta daya shiga juya mata lkc guda,cikin siririyar muryarta tace.

“Ya salam,kogi?”

Ta tambaya tana runtsa idanunta wanda sukai mata jaa sabida ciwon da kanta yake mata.

“Kamar na taɓa jin sunan fa,amma bansan ina ba?”

Wani murmushin takaici Kulsum tayi,cikin tausayawa Zarinan tace.

“ba zaki iya tuna komai na rayuwanki ba,sai wanda Allah ya nufeki sabida sun riga sun hargitsa tunaninki gaba ɗaya,kada kisare domin wannan zoɓen naki ya ɗauke da hanyar da za’a kuɓutar da masarautar bilhas”

Shuru Zarina tayi gaba ɗaya bata fahimtar Kulsum ta tafi tunanin inda ta taɓa jin sunan garin Kogi,ganin kanta na neman tarwatse ya sanya ta ɗauke tunanin daga ranta.

Domin bata fiye ajjiye ɓacin rai ba,tana da sauƙin kai tana kuma da saurin yafiya,amma tana da kafiya da kuma naci akan abinda ta sanya gabanta babu wanda ya isa ya sauya mata shi,ko kuma ya sanya tayi abinda ba tayi niya ba.

Miƙewa tayi ba tare data tanka kulsum ba tayi ficewarta daga ɗakin,ta koma sashin Mai babban ɗaki.

Tana zuwa ta samu Hadima Kaltume harta gama shirya kayan buɗe baki lkc kawai take jira.

Tana shiga ta nufi wani ɗaki inda yanzun a nan take ƙwana.

Direct bathroom ta nufa ta sakarwa kanta shower,ajjiyar zuciya ta shiga saukewa sabida sanyin ruwan daya gama ratsa jikinta.

Ƙirjinta tsurawa idanu ganin yadda tagwayenta suka ƙara girma  nipples ɗinsu sunyi red,turo baki tayi tare da sanya hannu ta matsesu sosai,Ita sam  Allah ya sani bata son wannan abun kunya suke mata,ko brazia bata sakawa sabida sunyi mata kaɗan.

Jin masallacin Bilhas na kira da alamun lkcn buɗe baki yayi.

Ya sanya ta ƙarasa wankan cikin sauri tare dayin brush ta ɗaura al’wala.

Handrayer ta ɗauka tare da junawa ta tsane ruwan kanta dashi.

Bayan ta gama ta ɗaura towel a ƙirjinta kana ta fito daga cikin bathroom ɗin.

Wata blue ɗin abaya ta sanya wacce take ɗauke da pech ɗin flowers masu ƙyau.

Wani pech ɗin vail ta ɗauka ta yane kanta dashi tare da ɗan fesa turare,ko lotion bata shafa ba.

Ta sanya flat shoe wanda Mai babban ɗaki ta bata jiya.

A hankali ta fito daga bedroom ɗin nata,direct wajan daining area ta nufa nan taga Mai babban ɗaki da kuma Kulsum sai Hadima Kaltume suna zaune saman kujera.

Sosai taji daɗin ganinsu sabida suna ɗeɓe mata kewa.

Kejera taja daga cikin jerin kujerun da sukaiwa daining ɗin ƙawanya,cikin ƙaramar muryarta mai cike da rauni tace.

“Ammi barka da shan ruwa”

“yawwa barka ɗiyata yaya kewa?”ta ƙare maganar tana sakin murmushi.

Turo baki Zarina tayi gaba hawayen da take ɓoyewa suka samu damar sakkowa daga cikin idanunta.

“eyee kewanne hadda kuka bayan kuma tijarar da kikai masa”Hadima Kaltume ta faɗa tana sakin dry.

“ohh wai kuka ne?”Mai babban ɗaki ta faɗa lkcn tana sanya yam balls wanda aka haɗashi da naman kaza.

“wai wane ake kewa hakan nifa duk ban gane ba?”Kulsum tayi mgnar tana miƙewa tsaye.

Dariya Hadima Kaltume tayi cike da zolaya tace.

“masoyin ƙwarai mana,kuma na gartaccen namiji mai baiwar ƙyau da Cikar zati,uwa uba ilimi daya gama ratasa jini da tsokar jikinsa,wlh ba kowa ke samun irinsu Captain Saifudeen yay wasa da damarsu ba”Hadima kaltume ta ƙare maganar tana wurgawa Zarina harara tare da gyatsina hanci gefe guda alamar dai haka🤥.

“wai fa irin jan ajin nan na ƙwailaye take masa but am sure komai nisa zata gane Allah ɗaya ne”cewar mai Babban ɗaki.

Kuka Zarina ta fashe dashi tare da faɗawa saman carpet ta fara birgima kamar ƙaramar yarinya,ko da yake ai ita ɗince domin haryan zun bata huce 17years ba.

  Lil prince dake bakin ƙofa tun ɗazu yana kuma jin abinda suke faɗi,yay saurin ƙarasuwa cikin babban parlour’n fuska a haɗe ya kalli su Hadima Kaltume da kuma Kuyanga Kulsum yace.

“kai dalla ku ficewa mutane tun bansa anyi maku ɗan banzan doka ba”

Da sauri suka fice daga sashin jikinsu ma rawa sabida wani mugun tsoransa suke musamman Kulsum.

Wajanta ya ƙarasu tare da durƙu sawa daf da ita yace.

“Maza miƙe ki share hawayenki,kada ki damu da abinda suke faɗe ninan zan zama gatanki koda yaushe ko mene kike ɓuƙata ki gayamin”

Ajjiyar zuciya ta soma saukewa a jajjire,kallonta yay yace.

“kinci abinci?”girgiza kai alamar “a’a”

Wajan daining ɗin ya ƙarasa tare taɓe baki yace.

“barka da hutawa mai babban ɗaki ya azumin?”

“Allhmdllah”tace a taƙaice.

Bai ƙara kallon inda take ba ya ƙwashi abin buɗe bakin da Hadima batul tayi a plate tare da gorar ruwa mai sanyi.

Yana zuwa ya sanya hannu ya miƙar da ita tsaye,yana jin yadda take ƙoƙarin ƙwace jikinta tana zabewa.

Cije laɓɓansa yay yana jin yadda wutar sonta sa kuma sha’awarta suna ƙara ƙaruwa fiye da koda yaushe anya bazai aikata abinda Yazeed yace ba kuwa?kai “no”banyi hakan zan watsar da damata,domin na fahimta bata ƙaunar ZINA ko makamancin hakan dalilin hakan ta tsani Saifu tsana mai yawan gaske,zanci gama da kula da ita daga nan harna samu damar da zan mallaketa matsayin matar aure,duk ina da ƙarfin ikon da zan aureta ko tana so ko bata so”.

Ya ƙare maganar zucin yana sanya mata soyayyiyar yam a baki,guda ɗaya taci kana tasha ruwa mai yawa,tana gama sha ta miƙe tsaye tare da cewa.

“kana ciwo bacci zanyi”

Idanu ya zuba mata yana jin kamar yaje ya rungometa yay kissing pink lips ɗinta koya samu sauƙi.

A zahiri kuma ya sakar mata murmushi tare da faɗin.

“ok dear i love you”

“thanks”tace a taƙaice.

Girgiza kai yay yace.

“you can say you love me too? Mene yasa ba zakice kina sona ba,bayan nasan cewa aƙwai soyayyata a zuciyarki,matan hausawa ba sam baku iya soyayya ba,da yawanku idan ance maku i love you ba kusan cewa i love you too,wlh na ƙarace maki i love you kika cemin wani thanks saina fasa baki”ya ƙare maganar rai ɓace kana ya fice daga cikin sashin gaba ɗaya.

Da gudu ta faɗa jikin Mai babban ɗaki tana sakin kuka.

“uhm duniya kenan ai,kinƙi mai lallaɓaki yanzun ai zaki so mai takuraki kuma bana da ikon magana,kin ni bani sandana naje ɗaki na gabatar da salla”

“Ammi zuciyana ciwo bana jin daɗi rayuwar nan,wai wacece ni?nina gaji babu wanda zanji daɗi wajansa,kema yanzun kina fushi dani”ta ƙare maganar tana sakin wani kukan.

Kanta Mai babban ɗaki ta shafa tare da bubbuga bayanta alamar rarrashi.

“Zarina”

Wannan shine karon farko da Mai babban ɗaki ta kira real name ɗinta,lafewa tayi jikinta tana sauke numfashi.

“bansan yaya SAIFUDEEN yake a fuska ba,amma nasan cewa girman addininsa da kuma tsoran Allah da yake dashi bazai taɓa sawa ya aikata abinda kike zarginsa dashi ba,za kiji kunya kuma zaki dana sanin lkc’n da kika fahimci wanene shi ɗin,dake dashi babu wanda na sani,ko duka ƙaddara ne ya haɗani daku,kamar yadda ƙaddara ke bibiyana haka kuma ke bibiyarki,kici gaba da addu’a domin ki samu damar tuna asalinki,kici gaba da addu’a domin neman zaɓin ubangiji,kici gaba da addu’a domin neman kariya daga sharrin wannan masarautar”

Kai Zarina ta ɗaga tare da zubawa Mai babban ɗaki idanu,a ranta tace wata kam duk wani abunda ake aikataw a wannan masarautar tana sane dashi,tana jin tausayin kanta amma a wannan lkc’n tafi tausayin Mai babban ɗakin fiye da kanta.

Hawayen fuskarta ta goge tare da kama Mai babban ɗaki ta kaita ɗaki tare da shimfiɗa mata dadduma domin sallah.

  Itama ɗaki bedroom ɗinta ta huce,tana zuwa ta shimfiɗa dadduma tare da gabatar sa salla,tana gamawa ta fara tilawan alkur’ani saida tayi wajan izu uku kana ta gabatar da sallar issha’i da kuma ashan sannan ta cire kayan jikinta tare da sanya wata farar rigar bacci,bed ta faɗa tare dajan pillow ta rumgometa tana jin wani ƙamshi na musamman na dukam hancinta.

Tabbas wannan ƙamshin sane shi kaɗai ta sani mai irin wannan parfume ɗin.

Sai a lkc’n ta tuna rigar tana ɗaya daga cikin kayan daya siya mata.

Lumshe idanu ta ƙarayi tana jin wani irin abu na musamman na ratsa zuciyarta da kuma gangar jikinsa,amma sakalcinta ya hana ta fahimci a salin dake ranta.

A haka bacci yay gaba da ita.

*_kogi_*

Sannu a hankali yake taka steps ɗin benen jirgin cike da kuzari da kuma jarumta,yana zuwa step ɗin ƙarshe ya ware manyan gajiyayyun idanunsa da suke a lumshe.

Babban filin tashi da jirgin ya zubawa idanu kamar mai son ganin wani abu.

Yana nan tsaye wani mutum yazu cikin sauri ya miƙa mata wani ɗan ƙaramin abu kana ya juya da azamarsa.

Abin ya zure cikin aljihun wandonsa kana ya ƙarasa sauka daga cikin kan step ɗin.

Ɗan ƙaramin tsaki yaja ALLAH ya gani bai son jira shiyasa yace Abbunsa ya bashi address na gidan da yake ciki yaƙi.

Ya san cewa Abbun nasa bashi da wani gida a nan garin,hasalima mamakin yake da yace yana KOGI yake,basu da wani ƴan uwa a kogi,a cameroon suke kamar yadda shima aka ɗaukosa daga cameroon zuwa illori sabida su ƙwantar da tarzuma,daga illorin kuma ya samu sanarwar an sauya masa aiki zuwa garin bilhas,kuma cikin masarautar bilhas ɗinma  gaba ɗaya domin kula da lafiyan Mai bartaba.

  A karo na biyu ya ƙara jan wani tsakin musamman ƴan mantan da yaga sun zuba masa idanu tamkar zasu cinyesa ɗanye.

Agogon dake manne saman tsintsiyar hannunsa ya ɗan shafa kasan cewar agogon apple ne.

Nan take ya kawo haske,ɗan juya idanunsa yay ganin har sha biyu na dare ya gota.

Da sauri wani mutum ya ƙarasu wajansa tare da duƙawa yace.

“Captain Saifudeen Bilyan hakane?”

Jinjina kai kawai Saifu yay ba tare daya tankasa ba.

Jakar hannunsa ya karɓa tare da faɗin.

“am Kamis yahya ur father’s drever les go”yana faɗin hakan yay gaba tare da buɗe boot ya sanya jakar Saifu ciki.

Taɓe baki Saifu yay tare da faɗin.

“Talkative”

Hannayensa ya tura cikin aljihun wandonsa kana ya mara masa baya cike da nutsuwa da kuma izza.

Cike da ladabi Kamis drever ya buɗewa Saifu side ɗin baya.

Sai a lkcn Saifu ya cire kai ya kallesa murya can ƙasa mai ɗan sauti yace.

“jaa jikinka,ni bana da hannu ne halan,ko kuma ni ɗin Sariki ne da motar ma sai an buɗe min”

Murmushi kawai Kamis yay cikin girmamawa yace.

“tuba nake”

Kafaɗa sabi ya ɗaga alamar ko a jikinsa.

A hankali ya zura jikinsa cikin motar kana ya zauna tare da ɗan kishin giɗewa.

Hannunsa ya santa saitin zuciyarsa da har yanzun bai daina har bawa ba,ya ɗan murya tare da dannewa.

Lumshe sleepyn eyes ɗinsa yay tare da lumshe idanunsa cikin zuciyarsa yace.

“rayuwa kenan aduk lkc’n da kaso kare kanka daga wani abun a kuma dai² lkc’nne wani abun ke ƙara shigowa rayuwanka ba tare daka shirya hakan ba,bai san daɗin soyayyar ba,haka kuma bai san jin daɗi ba,yasha wahala sosai a rayuwarka,ka sancewarsa mutum mai ƙarfin guiwa shine ya sanya baya taɓa sarewa da daga rahamar ubangiji,ya sani kuma ya yarda hakan akan cewa komai lkcne,tun yana ƙwana saman ciyawa yaci ganye da ruwan ƙorama,daga nan ya dawo ƙwanciya saman simiti yasha kuma ruwan rijiya,rayuwa na tafiya kuma ƙaddararsa na ƙara sauyawa,daga nan ya koma ƙwanciya saman tabarma yasha ruwan buhal,haka nan ya koma ƙwanciya saman katifa yasha ruwan fanfo,yau shine yakai wani mataki da zai ƙwana saman gado kuma yasha dukkan kalan ruwan daya keso da kuɗinsa da gominsa saɓanin da”

Wani murmushin takaici yay a lkcn baya da aka goranta masa wai bashi da mahaifi shi ɗin shege ne….

Kallamar shege da aka haɗashi dashi ba ƙaramin dakula masa lissafi akai ba,amma kasan cewarsa mutum mara sanya damuwa a zuciya ya tattara kallmar yay watsi da ita,sabida yasan koda shi shegene aiba shine ya haddasa faruwar hakan ba.

Bare yay imani da Allah Abbunsa bazai taɓa aikata wani abu ga wata ƴar mace ba har ace ta samu ciki da haifesa.

Ƙara taune lips ɗinsa yay yana jin kamar ƴanzu abin ke faruwa.

Jin drever’n ya tsaya da dreving ya sanyashi buɗe gajiyayyun idanunsa wanda sukai masa nauyi.

Idanunsa ya zubawa gidan sabida yadda ginin gidan ya birgesa.

Jin drever ya buɗe masa ƙofane ya sanyashi ƙwaɓe fuska kana cikin nutsuwa ya zuro da ƙyawawan ƙafafunsa masu ƙyau.

Hannunsa ya sanya duka cikin aljihun wandonsa kana ya ɗan jin gina da motar yaci gaba da ƙarewar gidan kallo.

Kamis drever bayan ya buɗewa Saifu ƙofa ya zagaya wajan boot tare da ɗauko jakar kayansa.

Wayarsa ya ɗauko jikin Aljihu kana ya kira wata number.

Daga can ɓangaren akai picking call ɗin cikin murya mai daɗi akace.

  “tun kafin kace komai naji ƙamshin Sweethert kusa dakai,baza kawomin shi”yana faɗin hakan ya katse wayar.

  Dry Kamis yay tare da jinjina soyayyar dake tsakanin Alhji Bilyamin da yaronsa Saifudeen.

Koda yake ba abin mamaki bane,domin ƙarfin soyayar uba da ɗa tafi haka.

Jakar kayan Saifu ya ɗauka kana yay gaba yana faɗin.

  “Ƙaramin Alhji biyoni nai maka iso”taɓe baki Saifu yay tare da ɗauke kansa gefe guda.

Cikin nutsuwa da kamala yake bin bayan Kamis har suka isa wani babban parlour dake gidan.

Sosai parlour’n ya birgesa ba kajin komai sai ƙarar Ac’n dake bada iska cikin parlour’n.

Parlour’n yana da part kusan guda huɗu da dukkan alamu ko wanne na aiki sabida yanayin wani ɗan duhun haske kaɗan dake fitowa ta cikinsa,guda ɗaya ne a rufe hakan na nuna shiɗin emty ne.

Wani part yabi a hankali ganin Kamis yabi hanyar yana zuwa bakin ƙofa yaga harya kai jakar ya fito,sai da safe yay masa kana yay hanyar ficewa daga cikin gidan baki ɗaya.

Hannunsa ya ɗura bisa handle ɗin ƙofar kana ya ɗan tura a hankali.

Yana shiga ya jingina da jikin ƙofar tare da zubawa Abbunsa nasa dake zaune bisa kan duguwar sofa yana shan coffee idanu.

Ganin Abbun nasa ya sanya yaji zuciyarsa tayi masa sanyi,raunin dake ɓoyewa ya bayyana a fili sabida idanunsa daya sauya kala tare da ɗan janye kaɗan.

  A hankali Abbu ya ajjiye glass cup ɗin hannunsa bisa senter table take gabansa,ajjiyar da yaji ana saukewa da kuma yanayin kallon da yaji ana binsa dashi ya tabbatar masa cewa sanyin idaniyarsa ya ƙarasu gareshi.

Murmushi yay mai ɗan sauti dan yashan halin Saifu sam ko kaɗan bai gajiya da kallonsa tun yana ƙarami haka yake.

Shi yar mamaki yake idan yaga yana binsa da kallon ƙurilla sai yaga kamar wani abune a jikinsa.

Kansa ya ɗaga tare da sauke ganinsa bisa ƙyaƙƙyawar fuskar ɗan nasa,shima ƙuri yay masa da idanu ganin zallar damuwa da rauni sun bai yana saman fuskar Saifu’n.

Sai yanzu yasan dalilinsa nason zuwa yaga gansa,ya tabbar yaje gejin da bazai iya danne damuwarsa ba,haka kuma baison wani yaga rauninsa idan ba shi ɗin daya saba gani ba.

Ɗan juya masa idanunsa yay tare da ware hannayensa alamar yazu garesa.

Da sauri Saifu ya zare picap ɗin kasan tare da cilli da ita kana ya ƙarasa wajan Abbun nasa da raguwar kuzarinsa.

Yana zuwa ya faɗa jikin Abbu tare da sakin wata nauyayiyar ajjiyar zuciya,sai a lkcn hawayen da suke ƙwance cikin idanunsa suka samu damar silaluwa daga cikin idanunsa.

Shuru Abbu yay yana sauraron ajjiyar zuciyar da Saifu yake saukewa ajajjere,a hankali ya sanya hannunsa cikin ƙwantacciyar sumar kansa ya soma shafa masa ita tare da hargisata haɗi da ɗan bubbuga bayansa.

Wajan 10minutes suna haka jin ya ɗan lafa da sauke ajjiyar zuciyar ya sanya Abbu faɗin.

  “bata amince ba halan?”ya faɗa yana ƙara shigar da Saifu cikin jikimsa sabida jikinsa da yaji ya saki.

A hankali Saifu ya ɗaga jajayen idanunsa tare da saukeso fuskar Abbu.

Yayinda shima Abbun shi yake kallo.

Runtsa idanunsa yay da ƙarfi yana yawon bakinsa nayi masa ɗaci,murya can ƙasa wacce iya Abbunne kaɗai zai iya jin abinda Saifu’n ke faɗa yace.

 “Abbu zargina take”ya ƙare maganar yana pouting lips ɗinsa.

 “zargi?to for what reason?”

Lumshe idanunsa Saifu yay yana jin maganar nayi masa nauyi a laɓɓansa,cikin dakiya da jarumta ya riƙe hannun Abbun tare da faɗin.

“Abbu waini ɗan iska ne fa tace,wallahi Abbu ni babu macen data taɓa birgeni bare nayi tunanin aikata wani Abun,akanta kawai na saɓawa Ubangina wanda yanzu haka na kejin kunyarsa matuƙa”

“mene ka aikata na saɓun Ubangijin Sweetheart?”

Turo baki Saifu yay tare daya mutsa fuska,kamar bazai magana ba sai kuma yace.

 “Abbuna i kissed her kuma na rungometa bansa menesa na aikata hakan ba,amma Abbuna ina sonta i want to marry her”ya ƙare maganar yana ƙwantar da kansa bisa ƙirjin Mahaifin nasa.

  Murmushi kawai Abbu irin nasu na manya masu sanin me suke,nisawa yay yace.

“ka sani mana,soyayyane ya ruɗamin tunanin yaro,tun yaushane nake cewa kasanar da ita?nasan halinka idan ka nuna kana son Abu baka yi masa ta sauƙi,kana sonsa da dukkan zuciyarka,lafiyarka,dukiyarka,iliminka,kana iya sallama komai a kasan,gashi yarinya ƙarama nasn zautar da tunaninka kamar ba soldier  ba”ya ƙare maganar yana dry.

Ƙwaɓe fuska Saifu yay tare faɗin.

“Abbu..!!”

Shafa kansa Abbu yay yana danne dryar dake ransa yace.

“karka damu baby,ƙuruciyar ke damunsa amma as soon as tasan abinda yake mata ciwo a zuciya zata gane Allah ɗaya ne,yanzu dai yaya Mai babban ɗaki daka daman da zancenta kullum?”

Shuru Saifu yay masa ba tare daya tanka saba,sosai ya kejin nutsuwa na saukar masa.

Damuwarsa n raguwa fiye da da.

Shima Abbun shuru yay masa domin ya fahimci ya gaji da magana,shi hakanma yaga ƙoƙarinsa domin yafi kowa sanin waye Saifu da kuma tarin miskilancinsa.

Hannu yasa zai zareshi daga jikinsa,Saifu yay saurin ƙanƙameshi tare da girgiza kansa murya can ƙasa yace.

“No! Abbu barni pls”

Jinjina kai Abbu yay ba tare da yace komai ba,babu jimawa yaji saukar numfashinsa alamun bacci yay gaba dashi,a hankali ya zareshi daga jikinsa tare cire masa rigar jikinsa da sojoji,murmushi ya saki kana ya sunkuya ya sumbaci ƙoshinsa.

Remote ya ɗauka tare da ƙaro gudun Ac’n.

Duvet ya ɗauka ya lulluɓesa kana shima ya ƙwanta bisa ƙasan ƙujerar saman carpet a haka bacci ya ɗaukesa cike da soyayyar ɗan nasa.

Ƙarfe uku dai² ya soma buɗe gajiyayyun idanunsa wanda suke cike da bacci,cikin gajiya da kasala ya ware laɓɓansa tare da faɗin.

“ALLAHAMDULILLAHIL LAAZI AHYAANA BAA’ADAMA AMATAANA WAA’ILAIHIL NUSHUUR”

Sakkowa yay daga duguwar sofar tare dayin miƙa yay salati wa Annabi.

Ɗagukunan dake jere a parlour yaɓi ɗaya bayan ɗaya.

Daga nan yaga ɗakin da aka kai masa kayansa,shiga yay tare da nufar wata ƙofa,tunaninsa ya bashi dai² domin bathroom ne.

Kayansa ya cire ya saƙale saman hanger kana ya haɗa ruwan zafi cikin jakuzie.

Sosai ruwan yay masa daɗi yana jin yadda yake ratsa jikinsa.

Tunawa da ita da yay ya sanya mararsa ta halba tare da ɗan miƙewa kaɗan.

Idanu ya zuba mata yana kallon yadda take huci ita ɗaya,shi abin har mamaki yake basa bai tana tsintar kansa cikin wannan halin ba sai akanta.

Cikin saɓon yanayin daya samu kansa aciki yasa hannu ya ɗura bisa mararsa wacce ya kejin tana dripping.

Ƙasa yay da ita yana jin yadda take kokawa da hannunsa tana son yin sama,murmushi yay kaɗan wanda ya fidda zallan ƙyansa da ƙwarjininsa.

Hakan da take ya tabbatar masa shi cikakken me lafiya ne.

Tunanin mace kaɗai ya sanyashi yin hakan inaga ace ya kasance da ita,uhm sorry for her yana jin tausayin dukkan wacce zata shigo hannunsa.

Da ƙarfi ya dannata tsakakin laps ɗinsa kana ya haɗe cinyoyinsa wace guda.

Ya mutsa fuska yay jin yadda take huci ita ɗaya.

Saida ruwan ya gama ratsa jikinsa sosai kana ya miƙe daga cikin jakuzzie’n.

Wajan shower ya nufa ya sakarwa kansa yana jin yadda tsigar jikinsa ta mimmiƙe hakan ya bawa fatar jikinsa shigar masa da wani sahihin sanyi cikinta.

A kasalance ya gama wankan tare dayin brush ya ɗaura al’wala.

Yana fitowa yaje wajan kayansa ya sanya wata farar jallabiya mai sulɓi da kuma gajeran hannu hakan ya bawa murɗaɗɗan hannunsa damar bai yana a waje.

Yana jin kansa na ɗigar ruwa ya share cump ya ɗauka ya taje sajen fuskarsa tare ma tsagaicin gemunsa yay ƙwance lib lib abin sha’awa.

Wani sanyayyen parfume ya ɗauka tare da fesawa a jikinsa kana ya ɗauki laddauma ya shimfiɗa ya tadda salla raka’a biyu.

Cikin sujjadarsa ta ƙarshe ya shigar da buƙatarsa ta neman zaɓin Allah kamar haka.

“اللهم إني أ ستخيرك بعلمك،وأستقدرك بقدرتك،وأسأالك من فضلك العظيم ،فإنك تقدر ولا أقدر،و تعلم ولا أعلم،وأنت علام الغيوب ،اللهم إن كنت تعلم أن هذا آلامر (Allah ka mallakamin Zarina matsayin mata)خير لي في ديني ومعاشي وعا قبة أمري،عا جله فا قدره لي و يسره لي ثم بارك لي فيه، وإن كانت تعلم أن هذا آلامر شر لي في ديني و معاشي وعا قبة أمري،فاصر فه واصر فني عنه واقدرلي الخير حيث كان ثم أرضني به.

(YA ALLAH INA NEMAN ZAƁINKA DOMIN ILIMINKA,KUMA INA NEMAN KA BA NI IKO,KUMA INA ROƘONKA DAGA FALALARIKA MAI GIRMA,DOMIN KAI NE MAI IKO NI KUMA BA NI DA IKO.KUMA KAI NE MASANI,NI KUWA BAN SANI BA,KUMA KAI NE MASANIN ABUBUWA FAKE.YA ALLAH IDAN KA SAN WANNAN AL’AMARIN (NA MALLAKAMIN ZARINA MATSAYIN MATA) ALHERI NE GARE NI A CIKIN ADDININA,DA RAYUWATA,DA KUMA ƘARSHEN AL’AMARINA-A WATA RAYUWAR,DA MAGAGGAUCIN AL’AMARINA DA MAJINKIRCINSA-KA ƘADDARA MINI SHI,KUMA KA SAUƘAƘE MINI SHI,SANNAN KA ALBARKANCE NI A CIKIN ADDININA,DA RAYUWATA,DA ƘARSHEN AL-AMARINA-A WATA RIWAYAR,DA MAGAGGAUCIN AL-AMARINA DA MAJINKIRCINSA-KA KAWAR DASHI DAGA GARE NI,KUMA KA KAWAR DANI DAGA GARE SHI,KUMA KA ƘADDARA MINI ALHERI, A DUƘ INDA YAKE KUMA KA SANYA NI IN YARDA DA SHI).

Ya ƙare addu’ar ISTIHARAR idanunsa na fidda ƙwallar tausayin kansa,bai taɓa jin son wani abu ya shigesa farat ɗaya irinta ba,sosai ya kesonta da dukkan zuciyar.

Bayan ya gama addu’ar ya ɗago da kansa tare da ƙara yiwa Allah kirari yana kammalawa ya fara tilawan alkur’ani mai girma da ɗaukaka,na yaji zuciyansa nayi masa sanyi wata nutsuwa na saukar masa,ƙarfi da hikimar alkur’ani kenan maganin duk wasu masifun duniya.

Agogon dake saƙale a tsintsiyar hannunsa ya duba yaga har wajan huɗu da wani abu.

Miƙewa yay tare da naɗe laddumar ya ajjiyeta a gefe,kana ya ɗauki alkur’anin ya ajjiye a muhallinsa.

Cikin nutsuwa da kuzari haɗi izza da nuna shiɗin namijine ya soma tafiya yana mai lumshe idanunsa tare da fesar da iska ta cikin bakin,duk yadda yake da damuwa a zuciya a wannan karon idan ka ganshi baza ka taɓa cewa yasan wata aba wai ita damuwa da ƙuncin zuciya ba.

Sosai haiba da hasken addini suka wanzu cikin ƙyaƙƙyawar fuskarsa.

Ƙwarjininsa ya ƙaro fiye da ko yaushe.

A parlour ya samu Abbunsa zaune shida wani magidancin mutum suna shira ƙasa².

Gabansu shaƙe da kayan sahur domin ɗaukan azumi na biyar acikin azumin 29/30 da za’ai bisa tsarin irin na addini,wanda yake ɗauke bisa calender musulunci.

Mutumin dake gaban Abbunsa ya zubawa idanu,ganin yana shirin ɗago kansa ya sanya yay saurin janye idanunsa daga garesa.

Bakinsa ɗauke da sallah

Ya shiga cikin parlon.

Murmushi fal fuskar Alhji Bilyam ganin ɗan masa kuma gudan jininsa ya fito cikin ƙoshin lafiya.

A hankali ya ƙarasu tare da zama bisa carpert ɗin kana ya saci kallon mutmin da Abbunsa ya kira da Alhji ABDALLAH.

Cikin murya mai sanyi da kuma daɗi wacce nutsuwa ta gama cikata yace.

“Barkanku da Asuba”

A tare suka amsa masa da

“barkai dai”

Kafin su ƙara magana ya ɗauki gorar ruwa mai sanyi ya ɓalle murfinta ya manna bakin gorar bisa laɓɓansa.

Sanyin daya ratsa cikin maƙoshinsa ne ya sashi ajjiyar zuciya mai ɗan ƙarfi.

Abbune ya matsu masa da kayan sahur ɗin tare da faɗin.

“oyyya lkc na ƙurewa”

Ya mutsa fuska yay tare da kallon Abbun nasa cikin muryar sangarta da kuma shagwaɓa yace.

“Abbu..”

Murmushi Abbu yay daman yasan za’a rina.

Plate ɗin da aka soyayya cips wanda yaji zallar ƙwai ya ɗauko kana ya sanya yatsunsa ya ɗauko tare da faɗin.

“haa to ko buɗe bakinma sai nayi maka?”

Girgiza ka Saifu yay cike da jin daɗi ya buɗe bakinsa Abbu ya saka masa cips ɗin cikin bakinsa.

A hankali ya lumshe idanunsa tare da soma tauna cips ɗin a hankali.

Alhji Abdallah kam tsayawa idanu yake binsu dashi cike da birgewa.

Runtsa idanunsa yay sabida mikin dake neman dawo masa ɗanye cikin ransa.

Haka Abbu yayta bawa Saifu cips ɗin yana ci.

Kai ya ɗauke lkc’n daya miƙo masa fried indomie.

Bayar da ita yay kana ya ɗauki dabino mai ƙyau guda baƙwai ya fara sanya masa cikin bakinsa.

Lumshe idanu yay tare da ɗura kansa saman cinyar Abbun sabida daɗi da garɗin dabinon daya gama ratsa kunansa.

Bayan gama ne ya ƙara bashi ruwa mai sanyi yana sha ana kiran Assalatu.

Hannu yasa ya ɗan gemun dake ƙwance saman haɓarsa cikin ƙasa da murya yace.

“Allahamdulillah”

Miƙewa sukai gaba ɗaya suka jera tare da nufar masallacin dage wajan gidan.

Saifu yana tsakiyarsu yayinda su koma suke gefe da gefensa.

Suna tafe suna magana akan shawarar da suka yanke kafin tafiyar Alhji Bilyamin Umara.

Bayan an idar da sallar asuba suka zauna domin yin lazimi sai wajan baƙwai na safe suka baro masallacin kowa ya shige part ɗin.

Abbu harya ƙwanta saman makeken gadon dake ɗakin yaji an turo ƙofar ɗakin.

Buɗe idanunsa yay ganin Saifu tsaye bakin ƙofa ya sashi sakin murmushi.

Hannu ya miƙa masa alamar “yazu”

A hankali Saifu ya ƙarasa jikin bed ɗin tare da ƙwanciya ya shige cikin duvet ɗin da Abbunsa ya lulluɓa.

Rumgomesa Abbu yay tare da shafa kansa yace.

“oyyya bacci”

Kai ya ɗagawa Abbu kana ya ƙara shigewa cikinsa lkc guda bacci yay gaba dasu.

Washe gari

Misalin biyar da rabi Saifu ya farka daga baccin daya ɗaukesa bayan yayi sallar la’asar.

Bakinsa ɗauke da addu’a ya sauko daga kan bed ɗin,yana miƙewa ya nufi toilet tare da cire boxer’n dake jikinsa ya wanke tas kana ya ɗan zauna akan toilet domin rage cikinsa,bayan ya kammala ne ya ƙarasa wajan shower ya sakarwa kansa ruwa.

Yana gamawa yay brush kana ya ƙara ɗaura wata sabuwar al’wala.

Towel ya ɗauka tare da ɗaurawa bisa waist ɗinsa.

Jikinsa na ɗigar da ruwa ya fito daga toilet ɗin,a gaban dressing mirrow ya zauna.

Wani lotion ya ɗauka mai ƙamshi da kuma sauƙin zafi a fata,ya fara shafawa jikinsa,yana gamawa ya fesa wani sihirtaccen parfume Ohudmood mai daɗin ƙamshi da kuma sanya zuciya sanyi.

Wajan wardrupe ya ƙarasa inda jiya ya ajjiye kayansa ciki.

Wani long blue crzy jeans ya sanya tare da wata ash ɗin t.shirt wacce akai mata rubutu da manyan baƙi aka rubuta.

“HAPPINESS”

Sanya t.shirt ɗin yay kana ya taje ƙwantaccciyar sumar kansa wace tayi ƙwance har wuyansa sai ƙyalli yake.

Lumshe idanunsa yay tare da taune jajayen laɓɓansa.

Wayarsa dake yashe saman bed ce ta soma ƙara alamar kira ya shigo.

Wayar ya ɗauka tare da katse kiran sabida ganin number Abbunsa ce.

Da ɗan sauri ya cilla wayan cikin aljihu kana ya sanya half shoe na maza yay waje.

A tsaye yaga Abbun nasa shida mutumin jiya Alhji Abdallah.

Kallonsu kawai yay tare da kawar da kansa gefe yana mamakin yawan maganar da suke wacce bata ƙarewa.

Alhji Abdallah ne ya kalli Saifu tare da faɗin.

“Captain muje part ɗina a can yau zakai buɗe baki”jinjina kai kawai yay kana ya mara masu baya.

A nutse suke tafiya yana binsu a baya har suka iya wani babban parlour da sallama suka shiga cikin direct wajan danning area suka nufa inda suka hangi mutane zaune.

Suna zuwa kowa yaja kujera ya zauna wajan ya ƙarewa kallo kana ya yaja kujera ya zauna tare dayin ƙasa da kansa ya soma latsa wayars.

Alhaji Abdallah shine ya kalli Sultaner yace.

“Mom Za…”sai kuma ya shiru tare da ƙara cewa “Wannan Saifudeen kenan ɗan *UNCLE NE* Captain wannan itace matana ga kuma mahaifiyata Mamu”sai a lokacin ya ɗaga kai ya kalli Mom wacce take farcing ɗinsa,kafeta yay da idanu haka nan ya samu kanta da ƙara ganin fuskarta.

Ganin ya kasa gane abinda yake son gani ya ɗauke kansa tare da saukesu kan Mamu cikin sassayyar murya yace.

“barkanku da yammaci ya azumi fa?”

Mamu ce tai murmushi tare ta shafa kansa cikin jin daɗi tace.

“Allahamdulillah ya naka”kai kawai ya jinjina mata suna cikin haka aka ƙwala kiran salla.

Cikin nutsuwa suka fara buɗe baki tare dacin Ƙosai da Kunu wanda yaji kayan ƙamshi,sai haɗin lemon Abarba mai sanyi.

Saifu dabino kawai ya sanyawa bakinsa tare da shan ruwa mai sanyi.

Gaba ɗaya suka miƙe tsaye tare da nufar masallaci.

Har sunje ƙofa Saifu ya tsaya tare da kallon wajan danning area ɗin yace.

“Ayya Mamu lkc fa”yana faɗin hakan yabi bayansu Abbunsu da ɗan sauri suka nufi masallaci.

Bayan sunyi salla sun dawo sun ɗanci abinci Saifu ya shige bedroom ɗinsa yabar su Abbu suna magana.

Yana shiga ya faɗa toilet ya sakarwa kansa shower.

Bayan ya fito ya sanya three gauter ya zauna bisa wata haɗaɗdiyar kujera tare da ɗaukan system ɗinsa ya fara dannawa.

Wajan 10minutes Abbu ya shigo hannunsa ɗauke da tablet da glass cup yana zuwa ya janye system ɗin tare da sanyawa Saifu maganin cikin bakinsa ya kafa masa glass cup ɗin.

Runtsa idanunsa yay sabida ɗacin maganin daya sauka saman halshensa.

Ƙwaɓe fuska yay tare da kallon Abbu yace.

“Abbu am tried magani zaimin illa haka nan fa”

Shafa kansa Abbu yay tare da faɗin.

“am sorry sweetheart haka ƙaddararka yake wata rana sai labari,na rasa yaya zan maka Saifudeen ace mutum shekara 35 amma ka kasa gane matsalarka ka nemi matan aure halan sai ciwon yaci ƙarfinka tukun?”

Turo baki yay tare da miƙewa ya faɗa jikin Abbun ya rungomesa yace.

“am so sorry Abbu”

Hannunsa yaja ya ƙwantar dashi bisa bed kana yaja masa duvet tare da ƙaro gudun ac’n,sunkuyawa yay wajan fuskarsa tare da faɗin.

“am sorry mah luv kaine haskena kuma kaine burina dake nake taƙama,banson takuraka Allah yay maka Albarka ya baka wacce zata kula da kai ta ɗebe maka damuwar da kake tare ita”sumbatar ƙoshinsa yay kana ya fice a ɗakin.

Shuru Saifu yay yana mai jin tausayin Mahaifin nasa a haka bacci ya ɗaukesa.

_Masarautar bilhas_

Ƙwance tashi babu wahala wajan Ubangiji da kuma dukkan wanda yake raye a doran ƙasa.

Cikin ikon Allah da hukuncinsa yau ankai azumi na ashirin cif.

A kuma yau kuma aka fara sallar TAHAJJI bisa al’ada kuma wasu suke tashe da kuma kiɗan gwauro.

Zaune take bisa duguwar kujera lkc zuwa lkc ta kan kuke ƙwallar dake fita ta cikin idanunta.

Sosai take jin wani abu mai kama da kewa a zahiri kuma bata san kewan mene ba.

Ko dan Lil prince yaje Dubai ne?

Shine tambayar da taiwa zuciyarta.

Hannu tasa ta ƙara goge hawayen dake sauka cikin idanunta zuwa kan fuskarta.

“uhmm wanda yace zai haɗiyi gatari ai saika sakar masa ƙota,Kulsum maza ɗauki kayan can kikai a ɗinka maku kinga Salla ya kusa,da lace da atamfar da kuma shaddar na wancan sakalyarne,sauran kuma naki”

Cikin girmamawa Kulsum ta ƙwashi kayan kana ta fice.

Ita dai Zarina na jinsu tai masu shuru sabida tasan babu wanda zai iya sanin abinda yake damunta bare kuma ya fahimceta.

Wayar Mai babban ɗaki dake saman senter table ce ta fara ringing.

Wajan kira na biyar kenan  hakan tasa Zarina miƙewa a hankali tare da kallon Mai babban ɗaki ashe sallar lafila ta tayar.

A hankali ta fara tafiya zuwa wajan wayar.

Tana ɗauka kiran na tsinkewa.

Taɓe baki tayi tace.

“wannan koma waya aƙwai naci ɗan masifar tsiya”wani kiranne ya ƙara shigowa.

Number ta zubawa idanu.

“ɗauki mana”cewar Mai babban ɗaki.

A sanyaye tayi picking tare da mannata saman kunnanta cikin siriyar murya tace.

“Assalamu Alaika/ki”

Ajjiyar zuciya mai ƙarfi Saifu ya sauke,ƙara rungome pillow’n dake ƙirjinsa yay,yana jin wata nutsuwa na saukar masa.

Shuru yay tare da lumshe idanunsa yana sauraran yadda take ƙunƙoni ƙasa².

“idan ba’a da niyar magana a kashe wayar mana”

A karan farko bayan rabuwarsa da ita ya saki wani tattausan murmushi tare da fesa mata hucin bakinsa ta cikin wayar.

Saurin lumshe idanunta tayi sabida tsigar jikinta da taji yana tashi.

Mirginawa Saifu yay tare da sanya hannusa ya ɗora bisa mararsa cikin wata murya mai amo da kuma sauri kaɗan yace way…

Wayyo zaki fasamin kunne”ya ƙare maganar yana ƙara sakar mata numfashinsa.
Zaro idanu tayi tare da saurin sanya hannu ta danne ƙirjinta sabida wani bugawa da ƙirjinta yay da ƙarfi.
Sam ko a mafarki ba tayi tunanin za taji muryarsa ba.
Balle cikin kunneta,lumshe idanu tayi tana sauraron yadda yake fidda numfashi a hankali.
Ƙara mirginawa ya ƙarayi yana ware idanunsa ya ɗagasu saman silin ɗin dake bedroom ɗin.
Jin tayi shuru taƙi magana ya sashin faɗin.
“who i am speaking with?”
Murguɗa baki tayi kana cikin tsiwa tace.
“ohuuu”
Zaro idanu yay cike da mamaki dan  baiyi tunanin tana da tsiwa har haka ba,ɗan murmushi yay sabida gaba ɗayanta iya ƙirjinsa ta tsaya.
“Ammi salla take idan ta idda ka kirarta”
Ɗan tsaki yaja kaɗan mara sauti kana yace.
“uhmm ba ita na kira ba nima,na kira rayuwar Saifudeen ne kuma Thank God she pic my call”
 “wace rayuwar raka?”
Ɗan runtsa idanunsa yay kaɗai yana jin yadda cikinsa ya fara yi masa ciwo,domin wajan wata huɗu kenan baiyi ba.
“tana nan wata ƙwailan yarinya”
Ƙwaɓe fuska tayi kamar zatai kuka sai kuma ta fara ƙoƙarin kashe wayar.
Cikin sauri yace.
“katinki ko nawa?wlh kika kashen waya sai halbeki da bindiga”
Saurin zare idanu tayi cike da fargaba,sai kuma ta murmuguɗa baki.
“laaaa nine kike murguɗawa baki,uhmm lallai wlh kin ɗauki bashi you don have to worry”
Ƙwaɓe fuska tayi kana tace.
“ni..ni yaushe nayi hakan”
Jinjina kai yay kana ya kiba kansa bisa kan pillow yace.
“RINAAAA..”
Yadda ya kira Rinaa tare da jan a ɗin ƙarshe ya sanya tsigar jikin miƙewa,cikin sanyin jiki tace.
“Na’am”
Taune lips ɗinsa yay kana ya ware manyan idanunsa yay cike da wani sabun shauƙi yace.
“mekike yanzu har haka?”
Jin motsi a bayanta ya sanya ta juya sauke numfashi tayi ganin Hadima Kaltume ce take riƙe da ita zuwa ɗakinta.
Shurun da ya jine ya sashi faɗin.
“uhmmm”
“bacci zanyii”
Taɓe baki yay kana yace.
“bacci bako wanka ohyaa maza jeki bedroom Allah yasa naji kin kashen waya”
Juya idanunta tayi cike da mamaki ta soma juya kanta tana ƙarewar parlour’n kallo.
“keee dilla ni Aljanine aka ce maki maza shigee”
Ba tare da tayi magana ba,ta shige cikin bedroom tana zuwa tace.
“gani bedroom”
“shiga bathroom 20minutes na baki kada ki manta da al’wala”
Turo baki gaba tayi tace 
“to ai bana Salla”
Wani ƙawataccen murmushi yay domin har ransa yaji daɗin maganarta,a zahiri kuma yace.
“meysa”
Wata kunyace ta kamata domin bata san ta faɗin hakan ba,turo baki tayi tacem
“uhmmm uhmmm”
Kaiya langwaɓar gefe guda cikin can ƙasa da murya mai cike da zalla shauƙi haɗi da so da ƙauna yace.
“eyee ƴar ƙwailar ta girma saura kaɗan”
Da sauri ta ajjiye wayar bisa kan bed ta faɗa cikin bathroom,ruwan zafi ta haɗa tare da zoba turaren miski ta shiga cikin ruwa lumshe idanunta tayi sabida ruwan daɗin ruwan da taji.
Ƙare ware cinyoyinta tayi ruwan yaci gaba da ratsa cikin jikinta,haka ƙamshin turaren miskin yana bin jikinta.
Tana gabawa tayi tsarki da sabulun miskin kana tayi brush ta ɗaura al’wala.
Handrayer ta juna tare da busar da gashin kanta.
Cikin sauri ta fito ta nufi wardrope tana zuwa ta ɗauki wasu kayan bacci riga da wando masu kalan pech.
Gashin ta cure waje guda kana ta fesa turare mai daɗin ƙamshi.
Harta zauna ta tuna da wayar still kiran bai tsinke ba.
Tsaki taja tace.
“nana tacce ɗan anaci”tana faɗin hakan ta manna wayar a kunnanta.
Numfashi ya sauke tare da kallon Abbunsa wanda ya shigo yanzu bashi magani.
“Abbuna wai nine ɗan a naci fa”murmushi Abbu ya shafa kansa cikin raɗa yace.
“sorry boy”
Sai yanzu ta ƙara gasgata rashin kunyarsa waya da budurwa a gaban Dad ɗinsa.
Dariya suka saki gaba ɗayansu,domin sunji abinda tace,gyara zamansa yay yana amsar maganin da Abbu ya bashi yace.
“waye budurwan,nine na taɓa cewa ina sonki ne?”ya faɗi maganar mai cike da ɗan gwaranci,domin har yanzu zallan hausa bai gaba zama bakin saba,tun yana 10years suka koma cameroon da zama.
Shuru tayi ba tare data kulasa ba,shima shuru yay yana fakar idanun Abbu kana ya wasa maganin ƙasa bed.
Sam Allah  bai haɗa jininsa da magani ba.
“yi addu’a bana baki san aljanin dazai kawo maki ziyara ba,sauƙinta ɗaya a Ramadan muke”
Cike da tsoro ta farayin addu’ar kana ta shafa a jikinta.
“nayi fa”
Numfashi ya sauke a hankali lokacin Abbu tuni ya fita da yaga yasha maganin,wata murya mai sanyi da kuma daɗin sauraro yace.
“I luv you Rina”
Idanu ta runtse da ƙarfi da ace tana da iƙon son sanya zuciyarta ta soshi babu shakka da tayi hakan,amma a kullum tsarsa take fiye da ko wanne lokaci.
Shuru kawai tayi masa domin idan tace zatai magana babu shakka baza ta faɗi mai daɗi ba.
Dai² ta bakinsa yay a speaker’n wayar kana ya sakar mata wani gigitaccen kiss wanda ya banda sautin.
“mu’ahhhh 💋”yana faɗin hakan ya kashe wayar tare da cilli da ita gefe,sabida wani irin raɗaɗi daya keji cikin zuciyarsa.
Lumshe idanun yay tare taune laɓɓansa tamkar ya rabasu gida biyi sabida turirin azabar daya kejin cikin ransa.
Wayar tabi da idanun sabida wani sabon yanayi daya saukar mata,kanta ta cura cikin pillow tare dakin wani wahalallan kuka mara sauti.
Ita ɗaya tasan abinda yake damunta,ita kaɗai tasan abinda zuciyarta keso,ita kaɗai tasan abinda gangar jikinta ke muradi,ita kaɗai tasan kewan abinda kunnuwanta sukai.
Cikin shassheƙar kuka bacci yay gaba da ita.
Abbu na fita ya miƙawa Alhaji Abdallah bandir ɗin 1k kusan bandir biyu,haka ya Alhji Abdallah ya amsa badan ransa yasu ba,sabida matsan tawar Alhaji Bilyamin.
Saifu kowa bacci ɓaro da bai san lkc’n daya saceshi ba,ya hadda masa katsewar tunanin da yake.
A haka yay bacci zuciyarsa cike da ɓacin rai.
Washe gari
Ta tashi jiki babu kuzari haka dai tayi wunin rana ko surutun da take yiwa Mai babban ɗaki bata samu damar yi ba.
Hadima Kaltume da kuyanga Kulsum ne kaɗai ke shirya abinda za’ai buɗe baki.
Sabida Zarina ba azumin take ba,ga kuma wani ciwon mara daya sanyata gaba kamar zai kata lahira,da aduk wata wannan abin take fargaba sabida ciwon cikin da take.
Yana ƙwance saman carpert sa juyi take gaba ɗaya jikinta rawa yake,ga wani a zababban zazzaɓi dake shirin saukar mata.
Zufa ce kawai ke karyo mata duk da sanyin A.c’n dake kaɗawa da kuma yalwatacciyar iskar dake kaɗawa a hankali tana ratsa jikin ɗan adam.
Amma baisa ta daina jin zufar da ƙwaranyo mata ba.
Mai babban ɗaki dake kishin giɗe bisa tattausan cosin ta numfasa tare da faɗin.
“Ke kinci baki son magani an taɓa ciwo babu magani,kai wannan abuba da zamani mu ina mukasan wani ciwon ciki,gaki da shegen son zaƙi kamar jikar shazomamu ba dole ciki yay ciwo ba”
Kuka Zarina ta sanya sabida azabar daya isheta zuwa yanzu kam ko kuzari babu jikinta sabida tsananin ciwo,a hankali ta soma birgima tare ƙara sautin kukanta.
Wayar Mai babban ɗaki dake bisa kujera ta fara ringing a hankali tace.
“kulsum pic the call”
Hannu Kulsum ta sanya tare da ɗaukan wayar,screen ɗin wayar tabi da kallo tace.
“Vedio call ne Ammi”cewar kulsum sabida itama bakinta yabi na Zarina na faɗin Ammi.
“ɗauki man”Mai babban ɗaki ta ƙarasa faɗa tana maida kanta saman pillow.
Da mamaki tabi wayar da kallo ganin number babu suna.
Cikin far nutsuta ta sanya wannan tare da connectiny na vedio.
Ƙyaƙƙyawar fuskarsa ta bai yana mai ciki da haiba da kuma hasken muslunci
Da hanzari Kulsum ta sunkuyar da kanta sabida wani ƙwarjini da yay mata.
Zubewa tayi har ƙasa tace.
“barka da yammaci ya azumin?”
Lumshe idanunsa yay ba tare daya amsata ba yace.
“wake kuka kuma?”
Da saurin ta jingine wayar saman sofa inda zai iya ganin Zarina dake ƙwance ƙasan carpet tana rera kuka.
Lumshe idanunsa yay tare da fesar da wani zazzafan numfashi ta cikin bakinsa,a taushashe yace.
“cikinne halan?”
Da sauri Kulsum tace “eh”gaba ɗaya haibarsa sun cikata.
Jinjina kai yay yace “Uhmm Kulsum zamu ruwan zafi a bowl da ƙarfin towel”
Da sauri ta ƙara miƙewa ta nufi kitchen domin samo ruwan zafi kana ta huce bathroom ta ɗauki ƙaramin beby towel mara nauyi.
Numfashi Saifu ya sauke yana kallo yadda ta ɗura hannunta bisa cikinta sai kuka take gaba ɗaya fuskarta ya haɗe da majina da hawaye haɗi da yawo.
A hankali ya gyara zama murya can ƙasa yace.
“sorry Rina sorry pls”
Ina sam Zarina bata san mene yake faɗi ba,sabida ciwo ya riga dayaci ƙarfinta.
Bowl ta towel ta ajjiya kusa da Zarina duk abinda suke yana kallonsu.
“maza ɗaya rigarta kiɗan jaaa siket ɗin ƙasa kaɗan maranta ya bai yana”ya faɗi hakan yana haɗe rai tamau sabida kallon mamakin da kulsum tayi masa.
Yadda ya faɗa haka tayi tana gamayin hakan yace.
“ohyaa sanya towel ɗin cikin ruwan zafi saiki ɗan fara murza mata saman cikinta zuwa mararta”
Da “to”ta amsa masa kana ta farayin abinda yace.
Wata ajjiyar zuciya Zarina ta sauke sabida yadda taji daɗin saukar ruwan zafin saman mararta.
Ajjiyar zuciya ta fara saukewa jikinta yay laƙwas ta tsaya da kuka sai shassheƙa kamar ta haɗiyi zuciya.
Bayan ta gama yace.
“ɗauki wayar ki ɗura bisa kunnanta”duk yadda yace haka tayi a hankali ya gyara zama cikin zazzaƙar muryarsa yace.
” Bisimillah”
Saida ya faɗa sau uku kana ya fara yi mata addu’ar samun sauƙi wajan ubangiji.
Saukar numfashinta yaji sosai tana yi tana sauke ajjiyar zuciya alamun bacci ya ɗauketa.
Numfashi ya sauke sabida soya da maƙoshinsa ke masa,a sanyaye yace.
“ɗauke wayar idan ta farka ki haɗa mata tea mai zafi da kauri ki mata”yana faɗin haka ya disconnecting na kira.
Cike da mamaki Kulsum take kallon Zarina inda tayi luff saman carpet tana sauke numfashi.
Miƙewa ta ajjiye wayar kana taci gaba da aikinta.
Wajan Saifu shima ficewa yay daga parlour ya samu Abbunsa shi ɗaya yana kallon tafsir,key ɗin Abbu ya amsa kana yay waje domin zaga gari.
A hankali yake dreving cike da nutsuwa da kamala,yana tafe yana sauraran daddaɗar ƙira’ar dake tashi a cikin mutarsa cikin suratul Ahzaaab,a hankali laɓɓansa ke motsawa alamin bin karatun yake tym to tym yana lumshe idanunsa sabida daɗin ƙaratun da yake,can ƙasar zuciyarsa kuma fal yake da tausayin Zarina,sosai yake jin ciwonta a jikinsa domin yafi kowa sanin zafi da raɗaɗin ciwon ciki.
Taune laɓɓansa yay kana ya sanya hannu yaja ma dai² cin gemun dake manne bisa haɓarsa.
A haka yake dreving cike da nitsuwa harya isa wani babban gida wanda kana ganinsa kasan yaji kayan mure rayuwa ko ina matakan tsaro ne a wajan.
Wanda sukaiwa kadangar gidan ƙawanya.
Ɗan kansa yay saman gidan inda aka rubuta *Disable and Opanage house* lumshe idanunsa yay tare da murza kan motar ya ɗan danna horn a hankali.
Tun kafin ya ƙarasu get ɗin getman ya hangame masa ƙofar get ɗin,cikin ƙwarewa y cilla hancin motar cikin harsbar gidan nakasassun da marayun.
Yana fitowa wani mutum ya ƙarasu wajan tare faɗin.
“sir how can i helf you?”
Murmushi Saifu yay kana yace.
“daman shiga zanyi wajan manager’n wajan,but tunda kaga fine”hannunsa ya saka cikin aljihu kana ya zaro bank Tyler  tare da ɗauko pen ya cike masu komai hadda sa hanunsa kana ya saka sauran tyler cikin aljihunsa ya miƙawa mutum takaddar hannunsa.
Cike da mamaki mutum ya zaro idanu tare da faɗin.
“what sir 2million na mene?”
Mota Saifu ya faɗa tare dayi mata key kana ya zuro kansa ta ƙofar motar yace.
“aci gaba da kula da marayu da nakasassun fisabilillah”
Cikin farin cikin mutumin yace “sir sunanka address naka pls”.
Murmushi kawai Saifu yay tare dajan motar da gudu ya fice daga cikin gidan.
Da kallo mutumin yabisa tare da mamaki irinna Saifu yay sadaka but baison asan shine yay.
Hannunsa ya ɗaga sama yace.
“Allah kada fawa wannan mutumin Ubangiji yay masa albarka fiye da tubansa,ya jiƙansa fiye da tunaninsa,Ubangiji ya sanya haske cikin rayuwarsa,Allah ka bashi abinda ya keso duniya da lahira”yana faɗin hakan ya juya da sauri ya nufi office ɗin manager yana shiga yay masa bayanin komai.
Cike da farin ciki shima yay masa addu’a domin daman kuɗinsu yay ƙasa suna buƙatar abubuwa da yawa musamman yadda salla yazu.
Kai tsaye Saifu gidan da yake zaune ya nufa yana shiga ana kiran sallar magrib.
Lumshe gajiyayyun idanunsa yay tare da furta.
“Allahamdulillah”
Yana fitowa daga cikin motar su Abbu na fitowa daga cikin gida zasu masallaci.
A hankali ya rufe motar tare da murza key,bayansu yabi da ɗan sassarfa ya shige masallacin lkc’n har anta da kabbara.
Bayan sun idar sunyi azkar kana suka fito tare da nufar cikin gida.
Gaba ɗaya danning area suka nufa suna zuwa kowa yaja kujera tare da zama.
A hankali Saifu yaja kujera ya zauna shima kana ya ɗan siyayi coffee a glass cup ya manna bisa bakinsa.
Lumshe idaninsa yay yaci gaba da shan tea ɗin.
Bayan ya gama yaja fruit gabansa tare da ɗaukan dabino ya sanya cikin bakinsa.
Daɗi da zagin dabinon haɗi da garɗinsa suka ratsa cikin kunnuwansa,wanda suka haddasa masa rufewar idanunsa.
Sosai dabinon yay masa daɗi cikin bakinsa.
Saida yaci guda baƙwai kana ya ɓalli inibi bayan ya shanye,yana gamawa ya ɗauki Apple ya saka cikin bakinsa.
Yana gama shan apple ɗin yaja ƙujerar baya tare dayin ƙyasa a hankali ya ware laɓɓansa yace.
“ZAAHBAZZAM’U WATALATUL URUUF WASABBATIL AJJIRAA INNSHA ALLAH”
murmushi Alhji Bilya yay tare da zubawa ɗan nasa idanu,sosai ya kejin soyayarsa a zuciyarsa,tunane² kala a ransa,yana son faɗa masa abinda ke ransa amma yana tsoro dan haka kawai yake shareshi domin yafi son yay komai cikin sirri,yasan har abada bazai taɓa kuka akan abinda yay masa komai daɗewa komai jimawa aƙwai randa zai masa godiya akan hakan.
“Abinci fa naga duk tar kacan ruwa kasha”
Shuru Saifu yay kana kuma ya buɗe idanunsa tare da zubasu bisa fuskar Mom wacce take sanya cips cikin bakinta,ganin tana ƙoƙarin ɗago kai yay saurin janye idanunsa.
Kana ya kalli Abbu yace.
“Abbu zuma nakeso ko dakakkiyar fura”ya faɗa yana pouting lips
Gaba ɗaya suka ɗago kai suka kallesa,Mom,Mamu,Abba ankai azumi kowa yana son sanya abu mai ɗan nauyi cikinsa shi kuma yana neman wani abu ikon Allah.
Shikam Abbu baiyi wani mamaki ba domin yasan hakan zai iya kasancewa wajan Saifu neman Abinda ya zama halayyarsa wanda yabi jini da tsokar jikinsa.
“ok anjima za’a kawo maka”cewa mom jinjina kai yay tare da faɗin.
“uhmmm nagode”yana faɗin hakan ya shige part ɗinsu tare da faɗawa bathroom yay wanka.
Haka dai ya ƙarasa sauran sallolin kana yay shirin bacci bayan yasha furar da aka kawo masa.
Number Mai babban ɗaki ya kira amma swcith up  haka ya ƙwanta zuciyarsa fal tunaninta sabida yasan bata da lafiya.
_Dubai_
Hankali ƙwance lil prince ke aiwatar da rayuwarsa ba tare data kura ba.
Azumi ne idan yay guda biyar sai yasha guda 1 acewarsa wai bazai iya zama babu mace ba.
A haka ya haɗu da wata yarinya mai suna Meera,haɗaɗɗiyace ajin farko,tun ganin farko da yay mata yaji mararsa ta halba da sauri kana cikin dauriya yace.
“heyy”
Juyowa tayi tare daci gaba da tuna cimgom ɗin bakinta kana tace.
“ohh hello”
Murmushi yay kana yace.
“basai nayi maki maganar abinda ke raina ba,domin ganinki hakan ya tabbatarmin ke ƴar hannu ce,so ina buƙatar haɗin kanki”
Wani shu’umin murmushi  tayi kana ta ciro wani card a wayarta ta miƙa masa cike da yauƙi.
Ganin accout number ta da sunanta da kuma bank name ɗinta yasan abinda take nufi.
“wow smart gal”yan faɗin hakan ya ciro wayarsa yay mata transfer  ɗin dubu ɗari biyar cif.
Gyara zama tayi haɗin da ɗan banƙaru ƙirjinta kana ta zare glass ɗin idanunta tace.
“Lil prince cikikakken sunan kuma NAJEEB KHALIS BILHAS ɗaga sarkin bilhas maici a yanzu,kana da aboki Yazeed shine best friend ɗinka ya kasance kuma lecture a N.S University,kana da gidan giya a ɓoye wanda ko mahaifinka bai san dashi ba,well kana ɗauke da zoɓen da idan babu shi babu wanda ya isa ya gaji sarauta,kana son Kuyangarka mai suna Zarina yayinda take maka kallon nagari bata san kaiɗin kumurcin macijine sara zai kaiga duniya,ka sadu da ƴan mata da yawa wanda ƙarfin tsafi da shirin jikinka yake sanyawa su mutu,yarinyar daka kashe ta ƙarshe Haseenatu ana kiranta da suna Seenat,number wayanka itane 0903333777 ba wannan ba aƙwai ɓoyayyan abu game dakai wanda ake ɓoye maka wanda dana su zan iya gaya maka”
Saurin miƙewa yay tsaya zuciyarsa cike da mamaki haɗi da tsoro yake kallonta tare da faɗin.
“wacece ke?mene kike nema dani?yaya akai kika san da abinda ko Mai martaba bai sani ba”
Miƙewa Meera tayi kana tayi sama kallon sama da ƙasa tace.
“bana buƙatar komai wajan sai ƙuruciyarka duk ta riga ta watse wajan wasu matan,amma hakan bai daman ba,kai infact ma dankai nazu Dubai kuma tun a kafin kazu nan na sanya ayimin bincike a kanka kuma na samu,ka sameni a gida kana duk ranar da zaka koma bilhas tare zamu tafi kada ka damu bazan takuraka ba,zanje matsayin baiwa duk sanda kake buƙatar ne ɗauke maka kewa ina maraba da kai”
Tana faɗin hakan tasanya kai ta fice da cikin gidan tana kaɗa masa manyan bom bom ɗinta.
Bai wani tunanin komai a kanta,burinsa kawai ya jisa cikin jikinta dan haka ya shirya zuwa after 10:30.
Tun daga wannan ranar suka ɗinke shida Meera kullum suna tare,yayinda basa haɗuwa sai bayan ansha ruwa.
Sun yanke shawarar ranar sallah zasu dawo bilhad inda Meera zata shiga matsayin Kuyanga..
**** *****
Kamar yaune ake faɗin saura ƙwana ashirin Ramadan yau gashi ankai azumi na shirin da tara.
Kuma a yau ake sanya ganin watan zul ƙiida.
Sosai fuskar Alhaji bilya ta cika sa farin ciki har bata iya rufe bakinsa.
Sa ɗan sauri ya shigo part ɗinsa tare da faɗin.
“My boy..my boy kana ta inane oyyaaa fito maza”yana faɗin hakan ya zauna bisa duguwar sofa.
Saifu kam yana cikin ɗakinsa suna waya da best friend ɗinsa yana tsoka narsa akan zama jeni da suke.
Haka dai sukai shirarsu cike da farin ciki inda yace shima Biyar ga sallah zai dawo.
Yana tsaka da wayar yace Sufy..sai kuma yay shuru kana yace “i will call u lrt”.
Yana faɗin hakan ya miƙe tsaye tare da nufar parlour inda Abbun nasa yake yana zuwa ya gansa zaune bisa sofa.
Ƙarasawa yay tare da zama kusan Abbu yace.
“Ayya Abbu ka bani tsora fa what is going on?ya ƙara maganar yana kallon Abbun wanda har yanzu fuskarsa take ɗauke da farin ciki mara misaltuwa..
Rungome Saifu yay tare da shafa ƙwantacciyar sumar kansa yace.
“Allah yay maka albarka yau ranace mafi muhimmanci cikin sauran ranakunsa,sai kuma wanda zasu riskeka nan gaba”
Da mamaki Saifu ya kalli Abbu cike da son jin abinda ya faru yace.
“uhmm menene wai har haka?”
Murmushi Abbu yay yace
“kada ka damu aƙwai lkc’n da zaka san komai,gobe zan huci Cameroon kaima ka shirya komawa wajan aikinka,tunda kayi nasarar hanani zuwa Umara amma nayi farin ciki ma da hakan domin wannan abin farin cikin dana tafi da tuni bai sameka ba”
Zamewa yay tare da ƙwantar da kansa bisa cinyar Abbu yace.
“Abbu ina tsoro bansan yaya zan fuskanceta harta gane abinda yake gaskiya akaina,duk lkc’n dana kansa ina loosing brain ɗina hakan tasa nake nesa da ita,ina kasa control kaina a kanta”
Shafa kansa Abbu yay yace.
“wai wacece wannan ban taɓa jin sunanta ba kullum labarinta na keji”
Ajjiyar numfashi Saifu ya sauke kana yace.
“Sunanta Za….”bai ƙarasa maganar ba Alhaji Abdallah ya shigo cikin parlour’n hakan tasa yay shuru sai kuma daga baya ya gaisar dashi kana ya miƙe ya shige cikin bedroom ɗinsa.
_Masarautar Bilhas_
Tun asuba kowa ya miƙe cike da farin ciki da murnar zagayowar watan ƙaramar sallah.
Kowa na masarautar wankan tafiya sallar idi yay kana kuma kowa bakinsa ɗauke da kabbara.
“ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR LA’ILAHAILLAHU ALLAHU AKBAR WALILAHIL HAMM”
Haka masallacim Marautar bilhas cike da Mutane yara da manya maza da mata kowa yaci sabbin kayan sallah.
Sahun farko Mai martaba ne sai,Hakimin bilhas,Chiroma,Waziri,Sarin fada,Tiraki,Sarkin dawakai,Sarkin cikin gida,baya kuma fadawa ne da sauran ƴan Masarautar kana kuma al’ummar gari.
Salla kai raka’a biyu aka sallamewa aka shiga gaishe².
Cikin girmamawa Fadawa suka baza rigunansu aka lulluɓe sarki.
Yana zuwa ya shiga wata ƙaramar mota wacce yake amfani da ita a cikin gidan sarautar.
Bangaren Fulanin sura tasha sabuwar alƙyabbar irinta mata mai ƙyan gaske.
Cikin nutsuwa kuyangunta da barorinta suka take mata baya har zuwa sashin Mai babban ɗaki.
Zaune ta sameta kan wata sabuwar ladduma mai ɗan tudu irinta masu sarauta.
Tasha ado cikin wata dakakkiyar lafaya orange sai green flowers masu ƙyau.
Kana ta sanya farar alƙyabba sosai ƙyanta ya baiyana a fili,gabanta cike da girke-girken da akai na sallah.
Cikin ladabi tace.
“Barka da buɗe baki Mai babban ɗaki fatan anyi sallah lafiya”
Murmushi mai Babban ɗaki tayi cike da jin daɗin ganin Fulanin sura tace.
“lafiya Allahamdulillah baƙo yazu ya tafi daman komai lkcne”
“hakane fa,Allah yasa munyi karɓaɓɓe”
“Ameen ina Khalid ɗin?”
Shuru Fulanin sura tayi sai kuma tace”bai dawo daga sallar idi ba”idanu ta zubawa wata ƙofa ganin wata ƙyaƙƙyawar yarinya mai ƙarancin shekaru ta fito.
Sanya take da lace sky blue wanda yaji stone masu ƙyau sai sheƙi suke.
Anyi mata ɗikin buba wanda ya zauna faffaɗan jikinta mai tsari.
Ta sai light blue na vail ta yane sumar kanta dashi.
Gashinta ya sauka har ƙasan vail ɗin sai sheƙi yake.
Kamar sanya cikin wani flat shoe wanda yake da blue ɗin igiya.
Sai zamga ƙamshi take fuskarta aya mutse sabida ciwon da cikinta yake.
Daman farko da ƙarshen period  sai tayi ciwon ciki,yanzu ma duk da tayi wankan tsarki amma bai hana cikinta ciwo ba.
Sosai Fulanin sura ke ƙare mata kallo far gabarta ɗaya idan ya kasance ita lil prince ya keso.
Domin yarinyar tayi mata musamman nutsuwarta.
Ita kam Zarina sam bata kula da Fulanin sura ba sabida idanunta a lumshe yake.
Tana zuwa ta zauna kusa da Mai babban ɗaki tare da shigewa jikinta tace.
“Ammi ciwon ya dawo pls ayimin irin wancan”
Shafa kanta Mai babban ɗakin tayi kana tace.
“Ɗiyata ciwonne dai,wacce tayi maki bata kusa,amma zan kirashi Saifu’n naji yaya ake”
Kaita jinjina mata kana ta ƙwantar dakan bisa cinyarta.
Da idanu kawai Fulanin sura take kallonsu ita dai harga Allah yarinyar ta birgeta,Hadima batul kam sai ware idanu take tana ɗaukan rahotu.
Sallah Fulani tayiwa Mai babban ɗakin tare fice ta nufi sashin Fulani kilishi domin sauke haƙƙin Allah.
Jin ciwon na tsanata ya sanya Zarina miƙewa tare da faɗin.
“bari kawai na duba Kulsum ciwon ya takurani Ammi”
Kai Mai babban ɗaki ta jinjina mata alamar “to”
Miƙewa tayi cikin nutsuwa hannunta bisa cikinta tana matsewa.
Flat shoe ɗin ta sanya bisa ƙafarta wacce taji jan lalle na salatif da Hadima kaltume tai mata.
Cikin nutsuwa ta fara tafiya zuwa waje tana yadda zuciyarta ta tsananta bugawa ga wani tsoro da far gaba daya kama cikata.
Sosai jikinta yake very weak.
A haka ta isa bakin ƙofar da zata fiddata waje.
Tana sanya kai zata fita shima yana sanya kai zai shigo,cikin rashi sani sukai karo da juna lumshe idanunta tayi sabida wani daddaɗan turare daya daki hancinta.
Ba tare data buɗe idanunta ba ta fara ƙoƙarin ficewa ta gefensa sabida gaba ɗaya ciwo cikin ya fara galabaitar da ita.
Ganin kamar bata cikin hayyacin tane ya sanshi sanya tattausan hannunsa ya kama nata tare da murzashi a hankali.
Cikin ƙasa da murya dai² kunanta yace.
“keee!!!”
Ya faɗa yana ɗan ɗaga muryarsa kaɗan.
Saukar muryarsa cikin kunnanta ya hadda bugawar zuciyarta da ƙarfi.
Dan bata jin zata manta wannan muryar a ko’ina.
A hankali ta fara buɗe idanunta saman ƙyaƙƙyawar fuskarsa.
Sanya yake cikin wani tissue  ɗin boyal fari tas,ɗikin dogun wando da rigar ciki sai babbar riga,kansa sanya da light blue ɗin hula jaddara.
Kunnansa maƙale da farin bluetooth,hannunsa riƙe da casbawa da kuma key ɗin part ɗinsa daya amsa yanzu wajan Sarkin tsakar gida.
Wani masifaffan ƙyau yay mata zata iya cewa bata taɓa ganin baƙar mata mai sihirtaccen ƙyau irin nasa ba.
Fuskarsa ta ƙara haske da haiba da kuma annuri.
Haka sajen dake fuskarsa ya ƙara yawa fiye da ko yaushe.
Ammincin Allah su tabbata ga mamallakin wannan halittar.
Komai na jikinsa haske musulunci yake fiddawa chocolate skin ɗinta tamkar ta ƴan itofia.
Shima kallon yake a ƙwana goma sha taran da yay bai ganta ba sai yaga tamkar shekara goma yay.
Ta kara ƙyau fresh skin ɗinta ya ƙara fitowa haka faffaɗan wait ɗinta sun ƙara faɗi,haka kuma ƙirjinta shima ya ƙara cika tamkar zai fasa cikin riga ya fito.
Pech lips ɗinta ya zubawa idanu sabida yadda yaga sun jiƙe da silva sabida taunasu da take.
A hankali kuma numfashinta ya fara fisga ta soma fidda dashi da sauri,idanunta ya fara lumshewa.
A zaba da raɗaɗin ciwon cikin da take wanda period ya haddasa mata ya sanya tayi saurin kama damtsen hannunta.
Da ɗauri ya sanya key ɗin cikin aljihun babbar rigarka a hankali ya sanya hannu ya fara dokan kumatunta haɗi da faɗin.
“Rinaa….Rinaaa ke Rinaaa”
Ƙara ta saki lkc’n da cikinta yay wata kartawa mai ƙarfin hakan ya haddasa ɗaukewar numfashinta ta faɗa jikinsa babu numfashi.
Ɗan rolling ƙwayar fararen ƙwayar idanunsa yay hakan ya ƙarama fuskarsa ƙyau.
Ganin yadda jikinta ya saki baki ɗaya ne ya sanya shi ɗaukanta tsam ya mannata da ƙirjinta,jajayen laɓɓansa ya ɗura bisa kunnanta ya fara sakar mata wani zazzafan numfashi.
Murya mai cike da juriya jarumta izza yace.
“No! Pls open ur eyes pls babyluv”
Sai kuma yay saurin cire bakinsa tare da sanya shi cikin ƙaramin bakinsa lumshe idanunya yay cikin wani sabom mood daya samu kansa ya tura  tongue  ɗinsa cikin bakinta tare da kamo…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *