THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 9 BY NIMCYLUV

 THE NEW EMIR (SARAUTA) CHAPTER 9 BY NIMCYLUV

Da kata a nan Captain Saifudeen.

Mai martaba ya faɗa cikin isa da kuma iko yay maganar ne bisa bada umarni,hakan na nuni da dukkan wanda akaiwa ita dole ne yabi maganar ko yaƙi ko yasu.

Tsayawa Saifu yay ba tare da yay magana ko kuma ya juyo ba,daga can ɓan garan cike da mamaki Abbu ya ɗan miƙe tsaye  tare da sakin numfashi yace.

“Saifudeen kaida waye haka?”

da yake indai magana mai muhimmanci ce Abbu bai fiye ɓoyewa Saifu sunansa ba.

tsaiwarsa ya gyara tare da lumshe gajiyayyun idanunsa wanda suke cike da bacci,kana ya sanya hannu ya shafi ɗan lafaffan cikinsa,daimond ring ɗin hannunsa ya zubawa idanu ganin yadda yake ta haske.

“Are you with me? Yarona meke faruwa ne?” kayi magana mana kasan yadda na keji a raina,kaga idan aikin da kake a nan da matsala kawai ka ajjiye aikin bawai kuɗin da zan kula dakai ne bana dashi ba maza ka fara shiri daga yanzu zuwa ko wanne lkc jet zai sauka gareka”

maganar Abbu ce ta dawo dashi daga tunanin daya tafi,wanda rabin tunanin na Zarinansa ne,wacce a kullum yake cikin tunaninta,har yanzu ya kasa yadda cewa bata garesa,kuma ya kasa yadda bata cikin masarautar,yaya zaiyi yana jin zuciyarsa na zafi da raɗaɗin,ji yake kamar ya buɗe baki yayta ƙwarara ihu sabida zallar damuwar da yay masa yawa a zuciya,amma taurin ransa da jajircewarsa ya sanya da wahala ka gane abinda yake damunsa a rai,baya son bai yana rauninsa ta dalilin hakan baya son akan mace ya gaza.

numfashi mai ɗan ƙarfi sabida maganar Abbun daya kuma yi a karo na biyu da yake faɗin.

“abokina ba zaka faɗamin what is going on ba?,ok good ka jirani”

yana faɗin hakan ya katse wayar cikin ɓacin rai,ɗan juya manyan fararan ƙwayar idanunsa yay tare dabin wayar da kallo.

“what should i do?”

ya tambaya cikin zuciyarsa,domin yasan Abbunsa kaifi ɗayane idan yace zai abu babu shakka sai yayi kuma babu wanda ya isa yay masa musu bare ya tankasa,yana dq zafin zuciya idan ransa ya ɓaci,shiyasa koda Saifune yay abu yakan masa uzuri domin yasan cewa kaɗan ya ƙwace daga cikin halayyar mahaifin nasa.

ƙara rolling eyes ɗinsa yay zuciyar fal tsoron abinda Abbun nasa zaiyi,to mezaizo yay a bilhas? shin kodai yaji abinda Mai martaba ya faɗane?.

ganin bashi da wata mafita akan hakan ya sanya ya cilla wayar cikin aljihu,a hankali kuma a nutse ya juya ya fuskanci Mai martaba wanda yake tsaye gefensa kuma su Tiraki ne,Chiroma,Waziri,Sarkin fada,da Fadawa sune sukaiwa Mai martaba ƙawanya suka sanyashi tsakiyarsu.

lumshe idanunsa yay few minutes kuma ya ƙara saukesu a fuskar Mai martaba daya kafeshi da idanu.

wani murmushi takaici Mai martaba yay ya tabbatar Saifu he never say anything,sosai yake mamakin jinkai da isar yaron,Numfashi ya sauke tare da ɗan matsuwa kusan Saifu ya gyara zaman alkyabbar jikinsa yace.

“Wanene kai?”

waro manyan fitinannun idanunsa waje yay,dan baiyi tunanin abinda ya kawo Mai martaban ba kenan,kallonsa kawai yake ba tare daya amsa tambayar da yake masa,bashi da amsar tambayar gaba ɗayanta,bawai dan shiɗin bashi da gata ko kuma a sali ba,a’a sabida rainin hankalin da yake cikin tambayar ne ya sanya bazai iya cewa komai ba.

 wani huci Mai martaba ya sauke a fuskar Saifu,cikin tsananin ɓacin rai haɗi da tsawa yace.

“do i look like idiot to you?haaa harni ina maka magana kana ƙin amsani,kasan waye ni kowa?dukkan mutanan da suke garin bilhas iko nane kuma mallakina ne daga ciki kuma harda kai,domin a bilhas yanzu kake rayuwa,ya zama dole kabi umarnina and ina da ikon da kuma ƙarfin mulkin da zanyi ko mene nakeso babu abinda zai faro kuma babu wanda ya isa yay magana akai sabida ina sauraranka waye kai?

  pouting lips ɗinsa yay yana jin tsawar da Mai martaba yay masa na hautsina kansa,bawai danga shigesa ba aa sabida azabar da ciwon kansa yake masa,ga kuma zallar damuwar rashin abokiyar rayuwa,tsaiwarsa ya gyara tare da sanya hannu ya shafi ƙwantaccen gashin dake manne gefe da gefen fuskarshi wanda suka ƙwanta lub lub abinda sai ƙyalli suke.

cikin wata cool and serious talk voice yace.

 “Wow!! mai Saifudeen  Bilyam ya tarewa Mai martaba Khalid Wazeer bilhas ne a rayuwa?”

(kada ku manta Wazeer ya haifi KHALID da SUFRAK,SUFRAK KUMA YA HAIFI SUDAIS).

yay tambayar yana mai ɗauke kansa daga kallon Mai martaba.

“hattara dai ɗan talakawa ƙarya kake”

cewar fadawan.

Mai martaba wani murmushi yay sosai maganar ta daki kansa,yau shine wani,waninma wanda ba ɗan garinsa ba yazu har gabansa yana kiran sunansa without respect,cikin dakiya yace.

“bana da matsala da talaka na,koda akwai zanyi amfani da ƙarfin mulkina wajan ganin na tarwatsata,matsalar kaine kakeso kunnuta da kanka ba tare daka sani ba,amma gayamin wanene kai shine zai tabbatar da abinda nake tunani gsky ne ko kuma akasin hakanne”

“Kaga yaro duk babu sa’anka a nan zaka faɗa cikin ruwan sanyine ko kuma saika koma ɗakin duhu”

Chiroma ya faɗin magnar yana me nuna Saifu daya tsa,

hannu Saifu ya saka a saman kansa tare da murza forehead ɗinsa wanda yake fidda gumi kaɗan².

kasa ce masu komai ba,dan gaba ɗaya bashi da lkcnsu gaba ɗaya hankalinsa ya koma indai ya fito tabbas a yau basai gobe ba,zai barmasu wannan masarauta barin da bazai taɓa dawowa cikinsa ba,sai dai idan a zanan qaddararsa aƙwai dawowa ɗin wannan ya san babu yadda zaiyi domin mutum baya taɓa gujewa qaddararsa.

cikin ɓacin rai da kuma gajiyawa da maganar da suke masa,hannu ya ɗaga masu tare dayi masu wata gigitacciyar tsawa wacce ta sanya gaba ɗayansu yin baya,girman tsawar da yayi ne ya sanya Mai martaba saurin runtsa idanunsa.

cikin wata kakkauciyar murya mai amoo ta sauti yace.

“Mene matsalata daku ne ayeee?aiki ya kawoni nan bawai neman magana ba,da nasu gaba ɗayanku ina da hanyar da zan sanya a ɗaureku cikin sauƙi,ina da sanin cewa ka tura har part ɗin dana sauka domin a ɗauko maka system ɗin,wow this is wonderful,baka samu wannan ba,ka sanyani abinda tunda nake a rayuwata ban taɓa yi ba,ahaaa burinka ya cika ka tuzar tani cikin mutane,hakan baiyi maka saida ka sanyani cikin ɗakin duhu na wajan watanni huɗu,tunaninka hakan zai zama ajalina baka san cewa Ubangiji shike kula da bawansa ba,shine mai iko da dukkan wani numfashi da ɗan adam yake shaƙa,bayan nafito wancan mahaukacin ɗan naka ya tsareni da shirmansa,wlh wlh idan kuka sake fushina ya kufce a kanki za kuyi bayani,hakan duk bai isheku ba saida  kuka san yadda kukai kuka rabani da farin cikina kuma muradin rai da zuciyata,sabida kunsan cewa itane raunina,aikine daga yau na daina sai….”

“Ohhh shiiit pls dear”

Maganar mai babban ɗaki da katseshi daga abinda ya keson ƙara faɗa,huci kawai yake sabida tsananin ɓacin rai da kuma damuwa idanunsa har wani jan ruwa suke kawowa,gaba ɗaya jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗaɗa.

jikin Mai babban ɗaki ya faɗa yana maida numfashi gaba ɗaya jikinsa rawa yake,ƙara shigewa jikinta yay,lkc guda kuma wani zazzafan zazzaɓi ya shiga ratsa nama da ɓarkon jikinsa,sun haɗu da ciwon da kansa yake ba.

cikin azaba da kuma sauyawar yanayi ya soma fidda wani numfashi hqransa suka shiga haɗewa suna bada wani sauti na ƙasss ƙasss.

jansa tayi zuwa wani ƙawataccen bedroom yayinda shine ya zame mata jagora sabida ba gani take ba,suna take tana lalubar hanya,har suka ƙarasa cikin tsaftaccen bedroom wanda aka cika da kayam mure rayuwa na musamman,komai na ɗakin green ne,kana ganin ɗakin kasan mamallakin ɗaki ba ma’abocin fita bane sabida dukkan abinda ake buƙata komai aƙwaishi.

  a gefen bed suka zauna gaba ɗayansu still kuma yana jikinta bai bar rawar sanyin da yake ba,rungometa yay sosai a jikinsa sai a lkcn wani wahalallan kuka mara sauti ya ƙwace masa sai ajjiyar zuciya yake saki.

shuru tayi masa domin tasan kukanne kawai zai masa maganin abinda ke damunsa a cikin ransa,bayansa kawai take bubbugawa tare da hautsina masa gashin kansa.

Mai martaba wata zufa ya sauke tare da kallon sarkin fada yace.

“aje a fara shirye-shiryen naɗa magaji sarauta a yau basai gobe ba zanyi murabus”

gaba ɗaya suka juyo suna kallonsa da makaki,tabbas dukkan abinda zai sanya Mai martaba ya faɗi hakan ba ƙaramin abu bane.

“Allah ya taimakeka ya ƙara maka lpa ya saka kafi haka zai a matsu da kayan naɗin kusa kasan sai dasi za’a ɗanashi, dole sai an kawo TAKUBIN NISFU,DA HULAR GARKA,DA ZOBEN GIRMA sannan za’a ɗura Magaji akan kujerar sarauta”

Sarkin fada ya faɗa yana mai ƙurawa Mai martaba idanu,wani shegen murmushi Chiroma yay kana yaja bakinsu yay shuru.

jinjina kai Mai martaba yayi tare da faɗin.

“Wannan duk suna wajan   Chiroma da anzo naɗin zai kawosu,zoben kuma yana wajan magaji kaga babu abinda damuwa duka a ciki”

yana faɗin hakan ya juyawa domin fita gaba ɗaya suka rufa masa baya har zuwa ƙofar tirakarsa yana shiga suma duka suka nufi sashinsu zaman fada ya ƙare sai jiran zuwan gobe ai naɗi.

  Lil prince kam bai san abinda ke faruwa hankalinsa gaba ɗaya yana kan Zarina,bashi da wani tunani sai nata,dukkan inda yake saka ran ganinta babu ita.

ƙwalbar giyar data zama wajan ta biyar ya sauke daga cikin bakinsa,a hankali ya ɗaga jajayen idanunsa ya kalli jama’ar da suke cikin makeken club ɗin wanda ya zama mallakinsa.

wata iska ya fesar kana ya kalli Yazeed dake gefensa yace.

“ina sonta,ina sonta yaya zanyi Yazeed?wlh dukkan namijin dana ganshi tare da ita nine ajalinsa zanci gaba da nemanta,zuwa gobe zanje inda muka sameta may be nayi sa’ar samunta,a wannan karan zance mata da yarda da kuma amana zannuna mata zallar so da ƙauna da kuma ƙyautatawa”

 sosai yay bawa Yazeed tausayi lallai dukkan macen da Prince yace ya naso abinda dubawa ne,domin da ace dan sha’awa yake sonta aƙwai mata da yawa wanda suka fita,numfashi ya sauke yace.

“amma mai zai hana ka hqr da ita?ina ganin kamar tafi ƙarfinka ni a ganina kawai ka hqr ka auri Meyrah tunda kana jin daɗin taryya da ita amma banjin zaka samu farin cikinka Zarina am…”

   shaƙar da Lil prince yay masace ta kasa bashi damar ƙarasa sauran maganar da yay niya.

da hannu ya nuna yana mai jijjiga kansa sai kuma ya sakeshi yay waje,yana zuwa ya faɗa cikin motarsa tare dayi mata key yaja da gudu yabar club ɗin.

a wani waje yay parking yana gama parking wasu ƙarti mutane sukazo wajansa,magana sukai kana ya nuna masu wani abu a waya,da dukkan alamar pic ɗin Zarina ne,kana ya ɗauki kuɗi da yawan gaske ya basu.

cikin sauri yaja motar ya nufi cikin Masarauta.

Saifu

sosai yay kukan daya ishesa,kana ya soma sakin ajjiyar zuwa,jajayen idanunsa ya ɗaga ya kalli Mai babban ɗaki ciki wata kasalalliyar murya yace.

“Ammi yaushe zan huta ne?yaushe farin ciki zai dauwama cikin zuciyata,mene ya saka babu wanda ya damu da damuwa sai mahaifina?mene ya saka matar dana amince da ita ta zaɓi da gujeni akan ta zauna dani?mene ya saka wannan mutanan suka sanyani a gaba nemai masu maina tare masu?…”hannunta ya kama ya ɗura saman ƙirjinsa wajan zuciyarsa yace.

“zuciyana ciwo Ammi dan Allah ki nemo Rinaaa itane maganin damuwata itace zata ɗaukemin ciwon da nakeji a cikin zuciyata ina sontaaa…”

kansa ya kifa saman cinyarta yana sauke numfashi,jiya yay gaba ɗaya zaman masarautar ya damesa gefe guda kuma yana jin faɗuwar gaba da kuma tsoro  na ratsa zuciyarka gaba ɗaya hankalinsa yaƙi ƙwanciya yana jin kamar wani abu na shirin faruwa dashiii.

Mai babban ɗaki kasa magana tayi domin ita kaɗai tasan abinda yake mata zafi a rai,tana jin kamar ta fishi shiga damuwa.

Hadima Kaltume ce ta shigo bakinta ɗauke da sallama.

Mai babban ɗaki ta amsa kana ta zame kan Saifu dake cinyarta ta shafi sumar kansa tace.

“maza jeka part ɗinka ka ƙwanta kaga dare yayi da safe kazu ka saman”

kai kawai ya ɗaga mata yana ƙara lafewa jikin luntsumemiyar katifar.

hannunta Kaltume ta kama suka nufi part ɗinta domin lkcn dare yayi sosai wajan sha biyu da arba’in.

Misalin ƙarfe biyu da rabi na dare wasu ƙartin mutane majiya ƙarfine suke shiga part ɗin hannunsu ɗauke da manyan bindigo masu girman gaske,dukkansu sun rufe fuskarsu da baƙin yadi.

kimanin so goma suka shiga part basu tsaya ba saida suka shiga har cikin bedroom ɗin ƙwance suka sameta kan mamaken gadon yana bacci ya rufe jikinsa da duvet.

da idanu wani yay magana cikin sauri wani ya zaro wata injection daga cikin aljihunsa kana ganin allurar kasan aƙwai wani mugun abu cikinta.

wani yay murmushi yace.

“finally Captain Saifudeen Bilyam zai zama mahaukaci”

a kuma dai² lkcnne mutumin ya nufi wajan da yake a ƙwance yana zuwa ya saita baƙin allurar ya caka masa a bayansa…..

injection ɗin da sukai masa irin mai ƙarfin gaske nance,wacce lkc guda take shiga cikin brain ɗin mutum ta hautsina tunaninsa,yadda allurar take da dafi ya sanya ba ko wanne asibiti ake ajjiyeta ba,wasu ma sai dai suyi oder nata daga ƙasar waje.
sau biyu suka samu nasarar saka masa allurar a kuma dai² inda ake buƙatar aiwa mutum ita,ba tare sunyi magana ko kuma sun ɗauki wani abu a part ɗin ba suka juya a hankali suka fice daga part ɗin gaba ɗaya.
suna fita suka nemi wata hanya ta baya ina a nan suka riski Lil prince yay masu jagora har suka fice daga masarautar baki ɗanya,domin ace da ɗan gari akanci gari.
kiraye kirayen sallar asubane ya farkar da Mai babban ɗaki daga baccin daya ɗauketa,sallati tayi tare da addu’ar tashi daga bacci,a hankali ta fara laluban hanya kana ta sakko da ƙafafuwanta zuwa ƙasa,hakan yay dai² da shiguwar Kaltume.
da sauri ta ƙarasa wajan ta taimaka mata tare dayi mata jagora har zuwa toilet,al’wala tayi kana ta bubbugawa ƙofar alamar ta gama hakan ya sanya Kaltume ta shigo ta kama hannunta tare da nufar cikin bedroom da ita 
ladduma ta shimfiɗa mata kana ta sanya mata hijab ta ajjiye mata casbawa a gefenta.
cikin ƙasa da murya Mai babban ɗaki tace.
“jeki part ɗin dana kai Saifudeen ki ganemin ya tafi sashinsa,idan yana nan saiki tashesa”
da “to” ta amsata kana ta nufi part ɗin,shuru taji babu kowa tun daga ƙaramin ɗakin har zuwa ƙofar bedroom,ƙofar ta tura tare da sanya kanta cikin bedroom ɗin.
ganin ɗakin duhu ya sanya ta lalubi bedside inda lamp yake ta kunna wani blue light,ɗan waro idanu tayi cike da mamaki tace.
“he already left”
cike da rashin gamsuwa ta tura kanta cikin bathroom ɗin nanma shuru ne babu kowa ciki,hakan ya tabbatar mata da cewa tun jiya ya fice daga cikin ɗakin,cike da addu’ar sama masa nasara a rayuwa ta juya zuwa bedroom ɗin Mai babban ɗaki.
samunta tayi zaune harta iddar da sallar tana lazimi,cikin girmamawa tace.
“Allah ya taimaki Mai babban ɗaki aina lura tun jiya yabar part ɗinan gaba ɗaya domin baya nan”
jinjina kai Mai babban ɗaki tayi cike da gamsuwa,ba tare da ta kuma cewa komai ba ta sunkuyar da kanta ƙasa tare da lumshe idanunta,wannan lkcn casbahar kawai take jaa,amma a cikin zuciyarta ita kaɗai tasan abinda yake damunta a rai,wani tsoro da fargaba ne ya shigeta wanda bata san dalilin hakan ba.
Kaltume kitchen ta nufa domin haɗawa Mai babban ɗaki dafaffiyar madarar shano,duk safiya da ita take fara breakfast.
bayan fitarta Mai babban ɗaki kishin giɗewa tayi zaune a ladduma wani sabon baccin ya ɗauketa.
Misalin ƙarfe 11 na safe da sassarfa Lil prince yake tafiya domin amsa kiran Mai martaba,a kuma yau yake saka ran tafiya neman Zarina,wacce ya ɗauki al’washin aurenta a lkcn da yay arba da ita koda a court ne ya amince ya ɗaura masu aure.
gefensa kuma Meyrah ce sanya ta fararan kaya irin na kuyangu,hannunta riƙe da jakar Lil prince wacce ya sanya kayasan kusan kala uku ciki 
yana tafe yana danna waya harya samu nasarar kammala transfer ɗin da yake na kuɗi kallonta yay yace.
“Be happy na maki transfer kuɗi na kimanin 2.m sai ai shagalin biki lafiya,tunda ba’a samu damar yin shagalin babbar salla ba ko?”
dry tayi kana ta riƙe hannunsa tace.
“thanks nima yau nake son tafiya gida,tunda kaga daman dominka nake zaune a nan,so kuma babu kai dole tasa zan tafi duk da zanyi kewanka cikin raina…”
“naso kin tsaya kinga yadda uban girman kancan zai dinga timamin hauka just imagine ace Captain Saifudeen  Bilyam yana yawo naked babu kaya sabida zallar hauka,amma babu damuwa as soon as na dawo kema zaki dawo mu ɗura daga inda muka tsaya”
lil prince ya tari numfashinta ta hanyar faɗin hakan,a kuma lkcn suka kawo hanyar shiga Fada,jakar hannunta ta miƙa masa kana ta juya ta koma part ɗinsa ba tare da tace ƙala ba.
cikin fadar ya shiga yana zuwa ya zauna gaban Mai martaba tare da gaidashi.
gyaran murya Mai martaba yay tare da gyara zaman alƙyabbar jikinsa ya kalli Lil prince yace.
“Magaji ka shirya a yau da yamma za’a na ɗaka Sarkin garin  bilhas,bayan nan za’ai bikin naɗi a kuma lkcn za haɗaka aure da wacce na zaɓa maka”
jinjina kai yay zuciyar fal farin ciki,domin burinsa a yanzu guda biyune,ga kuma guda ɗaya zai cika,shi kaɗai yasan irin zallar ikon dazai kafa a mulkinsa wanda ko mahaifinsa bai isa yay irin wannan ikon da kuma gadarar ba.
lallai kasan cewaraa Sarkin bilhas shizai bashi damar girmama night club ɗinsa ba tare da tsoro ko kuma shakka ba.
hatta aure da zaiyi dan yana son yarinyar ne banda haka babu abinda zaisa yay wani aure matan garima sun ishesa.
wannan rana ita yake jira domin samun damar amshe makarantar islamiyar dake ƙauyen bilhas domin gina event senter.
gyaran Mai martaba yayi a karo na biyu ya kuma faɗin.
“Ni Mai martaba Khalid Wazeer  bilhas nayi Murabus daga kan kujerar sarautar a rana ta Litinin wanda yay dai² da 5/4/2021 inda ɗana Prince Najeyb Khalid Wazeer  bilhas zai maye gurbina”
gaba ɗaya wajan ya ɗauki kabbara,sai a lkcn Lil prince ya fahimci jama’ar dake wajan kamarsu Hakiman bilhas,da kuma dagatai,haɗi masu unguwanni,sai kuma manya daga gida  Gwamnati da kuma ƴan ɗaukan rahoto wato ƴan jarida,da kuma ƴan gidan t.v.
dukkan wani wanda yake da iko a ɗanin sarautar yana wajan.
a hankali Mai martaba ya zare rawanin dake kansa tare da ajjiyeshi gefe,kana kuma ya miƙe daga kan kujerar karaga.
idanunsa ya ɗaga ya kalli Lil prince ya sakar masa murmushi tare da ɗaga masa hannu alamar jinjina.
Chiroma ne ya kama Prince ya miƙar dasbi tsaye tare da nufar kujerar mulkin dashi yana  ƙoƙarin ajjiyeshi Sarkin fada yace.
“Dagata  Chiroma kasan babu wanda ya isa ya hau wannan kujerar sai an kawo shaidun dazai nuna cewa mutum ya gaji sarautar kamarsu Takobi,Hula,da kuma Zobe”
murmushi Chiroma yay yace.
“eh ƙwarai hakane Kai lil Prince saika kawosu”
sai a lkcn Mai martaba ya ɗaga kai ya kalli  Chiroma cike da tuhuma yace.
“Kamar bayan kayan yana wajanka,bakai na bawa ajjiya ba?”
gyara tsaiwa Chiroma yay yace.
“ƙwarai ni kamawa ajjiya amma ka sani kamar yadda kake da iko da wannan kujera nima ina da ita,na daɗe ina neman hanyar da zanbi na samu wannan mulkin amma wannan lkcn shine yay dai² da ra’ayina,kada ka manta dukkan wanda ya kawo wannan kayan shine da mulki”
gaba ɗaya Mai martaba da Lil prince da kuma Waziri suka ɗago kai suna kallonsa,hatta galadima saida ya kalleshi.
wata wahalliyar zuface ta fara karyowa Mai martaba wani takaici da kumq ladamar bawa Chiroma amana ya ɗarsu cikin zuciyarsa.
wata kam wannan daliline ya sanya boka Gilmas cewa ya hanzarta ɗura Lil prince a kujerar mulki aƙwai guguwar da take shirin tunka rusa,wato Chiroma shine guguwar?.
“Chiroma jeka kawo kayan mudai babu ruwanmu wanda yake da shaidun zama sarki shi zamu naɗa,kuma mulki baya jira saidai a jirasa”.
cewar Sarkin Fada.
cikin sauri Chiroma ya fice daga cikin fada ya nufi wani keɓantaccen waje a gidan sarautar.
yana zuwa ya ɗauki wayarsa ya danna wata number ringing ɗin farko aka ɗauki wayar cikin sauri yace.
“lkc yayi ina jira”
yana faɗin hakan ya kashe wayar,wajan 5minutes ta shigo wajan cike da yauƙi hannunta ɗauke da kayanta,tana tafe tana taunar cimgun jikinta duka rawa yake sabida yadda kayan ya matseta.
tana zuwa ta zare ring ɗin hannunta ta miƙa masa tace.
“harka ta kuɗi bana wasa da ita kamar yadda kaban 5.2m akan wannan ring ɗin dole na baka shi,a kuma yanzu zan bar masarautar bilhas”
tana faɗin hakan ta juya da saurin tabar wajan bayan ta bashi zoben.
a can Fada kowa wani murmushin jin daɗi Mai martaba yay tare da kallon Lil prince yace.
“ina zoben dana baka tun shekarun baya..?
 zaro idanu Lil prince yay tare da duba yatsun hannunsa,runtsa idanunta yay Allah ya sani shi sham ya manta da amfanin zoben,soyayya ta gigitashi ya bada ƙyautarsa.
cikin ƙasa da murya yace.
“bari na amso na bawa wata kuyanta ajjiya nasan zuwa yanzu bata tafi ba..
*_Kogi_*
numfashi ta kuma saukewa a karo na biyu tana mai ƙara shigar da pillow’n dake kusa da ita.
lumshe idanunta tayi kamar yadda tayi tunanin hakance ta kasance,domin ƙyaƙƙyawar fuskarshi ta fara yi bata gizo a cikin idanunta,sai dai a wannan karan tana mamakin yadda fuskar tashi ta cika kamala,ƙwarjininsa ya ƙara fito fiye da ko yaushe.
ga wani sihirhataccen haske daya kewaye duka sassan jikinsa,babu abinda yake bata mamaki yadda fuskarsa gaba ɗaya babu ɗigun fara’a haɗe rai tamkar zai fasa ihu.
ƙyawawan jajayen laɓɓansa ta zubawa idanu ganin yadda suke sharning su kaɗai tamkar ya shafa lipstic.
ajjiyar zuciya ta sauke tare da ware manyan idanunta wanda suke a rufe,ƙwarai yana da ƙwarjinin da bata isa ta haɗa idanu dashi ba.
sosai yake da haiba da kuma cikar zati,yaushe zata ganshi?yaushe zatai arba da aljaninta?yaushe ne damuwae dake cikin zuciyarta zata kau?tana jin sosai wanda ya zame mata jini da tsokar jikinta,tana jin sonsa yana ratsa dukkan wata gaɓa ta jikinta.
shiɗin gwarzona duk da cewa a mafarki take ganin amma tayi imanin cewa ƙyansa yafi yadda take ganinshi a cikin mafarkinta da ƙwayar idanunta.
a sanyaye ta ɗaga kanta tare da sauke ganinta a kan ƙofar da taji ana turowa,ƙwaɓe fuska tayi tare da lafewa jikin pillow’n.
da sauri Sufyan ya ƙarasu inda take ƙwance yana zuwa ya zauna gefen bed ɗin tare da kama hannunta yace.
“Little tunani ko,yauma heart beat ɗin naki ne,may be wani ƙatun aljanin ke buɗe maki ido”
turo baki tayi tare daya mutsa fuska tace.
“Yaya ko aljanine shi ɗin ina sonsa,ya zama jini da tsokan jikina,yaya zuciyata bugawa yake sabida sonsa,dan Allah yay ka taimaki sister ɗinka ka nemomin shi”
shuru yayi a ransa yana girmama irin son da takewa mutumin da bata san dashi ba,tayaya zai tayata neman mutumin dako a mafarki bai taɓa ganin fuskarshi ba.
tayaya zai nemo wanda babu tabbacin aƙwaishi a wannan duniya may be ba jinsin mutane bane.
“Little shikenan zan tayaki amma ki daina wannan tunanin,jibi yadda soyayya ya ramarki a haka zaizo ya ganki jiki duk ƙashi,maza zo muje *_UNCLE NE..!!_* yazo daga Cameroon daga nan zai huce wani garin,yace yana son ganinki yay maki jajen saceki da akai”
ɗan washe baki tayi hakan ya haddasa bai yanar hqrin makkanta da kuma lumawad beauty points ɗinta,zaman vail ɗin abayarta ta gyara tare da zura bedroom shoe ta miƙe tsaye,hannunta ya kama zuwa cikin babban parlour’n nasu.
a zaune ta samesu Mom,Mamu,Tupic,Abba,Abbu,hannunta ta zame ta nufi inda Abba ke zaune kusa da Abbu tana zuwa ta faɗa jikinsa ta lumshe idanunta tana jin zuciyarta na bugawa da ƙarfi,kanta Abba  ya shafa tare da faɗin.
“Dear wannan mutumin yana wahalar dake ni yaya zanyi na samaki farin cikinki haka ne?”
Murmushi Abbu yay tare gyara zama yace.
“To wanene kuma har haka yarinya take damuwa dashi haka?”
“Wallahi Uncle mu duka babu wanda ya sanshi,a mafarki kawai suka haɗu shine gaba ɗaya tasa damuwa a ranta,na rasa yaya zanyi na sama mata farin cikinta”
cikin zallar mamaki Abbu ya kalli Zarina wacce take ƙwance jikin Abba yace.
“To mene zai hana a haɗata aure da wani ina ganin hakan zai sanya ta daina da damuwa da mutumin da bata tabbacin aƙwaishi a wannan duniyar”
shuru Abba yay yana tunanin maganar Abbu,tabbas idan aka haɗata aure da wani babu shakka hakan zai sanya ta daina tunanin wani daban,kuma auren da zatai zai ɗebe mata kewa harta manta abinda ake ranta da zuciyarta.
numfashi Abba yaja yace.
“ina ganin wannan shawarar taka itane zamubi,daman aƙwai wani ɗan abokina da yake sonta naƙi bashi dama,amma dole yanzu zan amince masa,idan yasu sai a haɗa bikinta dana Tupic tunda Sufyan yaƙi”
Mamu dake gefensu tayi saurin faɗin.
“Babu uban dazai sanya Sufyan ya zauna babu aure,wannan masifar ciwon cikin da yake shi kaɗai bai isa ya sanyashi yay aure ba”
Abbu dake murmushi ya kalli mamu,can cikin ransa yace.
“Ayya har kinsa na fara tausayin yarinyar da Saifudeen zai aura”
a fili kuma ya miƙe tsaye tare da faɗin.
“Nizan tafi daman nazu ganin lafiyar Saifudeen ne,shiyasa nace bari na leƙo nan ɗin,sai kuma munzo ɗaurin auren ƴan uku,kafin nan insha shima Saifu zan tilasta masa yin aure wajan shekara 36 amma babu niya”
gaba ɗaya wajan suka sanya dry banda Zarina data kafe Abbu da idanu,sosai take jin sunan daya faɗa na SAIFUDEEN nayi mata yawo cikin ƙwaƙwalwarta,amma ta kasa fahimtar inda ta taɓa sanin inda taji sunan,idanunta taja ta lumshe tare da janye jikinta daga jikin Abba ta lafe a jikin sofa ta shiga sauke numfashi.
tayayane zata iya rayuwar aure da wanda bata sani ba? tayaya zuciyarta zata iya mantawa da mutumin da take jinsa a jinin cikinta?
tayaya zata iya yiwa wani biyayar aure ba aljaninta ba?
wasu zafaffun hawayene suka fara fita daga cikin idanunta ita kaɗai tasan zafi da raɗaɗin da take ji cikin zuciyarta,lafewa ta ƙarayi a jikin sofar ta shiga sauke numfashi.
Sufyan kam kasa cewa komai yayi ya cika yay fam sabida zallar takaicin abinda Mamu tayi masa,gefe guda kuma Tupic ne yake tayi masa dry,Mom kam shuru tayi tana tunanin yadda za’a aurar mata da yarinyar da ƙarancin shekaru.
Abba da Abbu ne suka fita suna tafe suna yin maganar auran da kuma yadda zai kasance nanda sati biyu masu zuwa,da wannan maganar Abbu ya shiga mota Yahaya drever ya jashi.
Bilhas
Dukkan inda yake tunanin ganin Meyrah yaje babu ita babu labarinta.
haƙiƙa rashin ganinta ba ƙaramin tayar masa da hankali yayi ba.
cikin wani sabon tashin hankalin ya dawo cikin Fadar ya shaida masa abinda yake faruwa.
sabida tashin tsoro da fargaba yasa ya kasa faɗin komai sai kallon Lil prince da yake.
wajan 20minutes Chiroma ya dawo hannunsa ɗauke da Zoben bilhas,yana zuwa yace.
“ga zoben bari naje kawo sauran kayan”
da sauri sarkin fada ya dakatar dashi da faɗin.
“A’a hujja gudama ya isa ina tunanin sai a fara shirin naɗaka kawo zoben”
cikin farin ciki Chiroma ya nufi wajan da kujerar karagar da sauri sarkin fada yace “stop it’s fake ring…
Da sauri Chiroma ya ɗago kansa da zallar mamakin yadda zoben ya zama fake,bayan yana tabbacin wannan shine asalin zoben da ake takama dashi a gidan sarautar,zoben da ko wanne sarki yake fata da kuma burin ganin ya samesa domin shine zai maka damar samun kujerar mulkin,tabbas idan akace wannan zoben fake ne babu shakka shima Mai martaba Khalida tsuhun sarki shime kawai an naɗashi ne kawai amma ba’a tabbatar da ingancin zoben ba,bare a ɗauki mataki akai.
idan har wannan ring ɗin fake ne abin tambayar a nan shine ina Real ring ɗin yake?ina ya shiga?.
ko kuma Meyrah ta yaudaresa ne bawai na gskyr ta bashi ba? kai hakanma bamai yiwuwa bane dole tabbas wannan shine ring ɗin da ake buƙata,kuma ya zamana dole a ɗurashi kan karagar mulki shima ya fara gudunar da kalan nashi tsagwaran zaluncin mulki wanda ya buɗi idanu yaga tsuhun Sarki Khalid wazeer bilhas ya nayi.
Mai martaba kam wani shu’umin murmushi ya saki wanda shine kaɗai yasan ma’anarsa,cikin dakiya da rashin nuna jin daɗinsa ya miƙe tsaye tare dayin waje.
yana fita harabar Masarautar ya zaro wayarsa a cikin aljihu ya dailing wata number ringing biyu akai picking call,cikin ƙasa da murya ya fara magana yana magana yana tafiya zuwa sashin lambun daya daɗe bai shiga ba.
babu inda ya tsaya sai ƙasan bishiyar fasadabir cikin zallar makirci yace.
“Na fahimci Saifudeen ba shine matsalarmu ba,daman ance makashinka yana tare dakai,a kullum a kuma koda yaushe nunamin yake yana sona bai damu da mulki ba,dalilin hakan yasa na bashi yarda fiye dasu Galadima,Waziri,Tiraki,sai gashi shida nayarda dashi shine yaymin zagwan ƙasa,ina son duk yadda za’ai kada ka kuskura ya samu damar dazai hau wannan kujerar mulkin tabbas idan yahau zai jawa kansa masifa wacce bai taɓa sanin da akwai irinta a wannan duniyar nan ba”
yakai ƙarshen maganar yana sauke idanunsa akan wani tudun ƙasa,ci gaba da tafiya yayi harya tsaya kan ƙasar da haka kurum yaji hankalinsa bai ƙwanta da wajan ba.
daga can ɓangaren boka Gilmas yay dry mai yawan gske wacce take fidda wani sauti mara daɗin gaske,tabbas wannan ranar yake jin tsoron zuwanta ranar daya san babu wani sauran raguwar wani abu da Chiroma zai ya daɗe yana son fahimtar da Mai martaba wannan abun amma ya gagara fahimta ko kaɗan,amma gashi yau da kansa ya fahimci abinda yake faruwa tsakaninsa da Chiroma,yau ɓoyayyan sirrin da yake ɓoye ya tuna kansa ba tare da wani tsananin bin cike ko kuma tada hankali ba.
a karo na biyu ya ƙara ware hangamemen bakinsa ya ƙwarara wani uban ihun daya haddasa fitowar Dauwas daga cikin wani surƙoƙin ɗaki.
gaba ɗaya yankin ya ɗauki sautin ƙatuwar muryarsa wacce take fidda sauti mara daɗin ji.
dukkan ɗakin girgiza yake har wani ɗan ƙaramin haƙine ke fitowa daga cikin bakinsa.
lkcn kaɗan wani surƙomemen baƙin aljani mai kawona wajan biyar ya bai yana gaban boka Gilmas,banda huci da kumbura hanci babu abinda aljanin yake.
sai dalalo da dugun harshensa waje yake yayinda wani baƙin yawo ke biyo bayan harshen nasa,dukkan yadda kakai kaga inda tsayinsa ya tsaya ka faɗi ƙarya,shi kansa Dauwas saida ya firgita da ganin wannan mummunar halittar mara fasali.
tsaigai tawa yayi da dry kana ya shiga faɗin wasu  kalmomin siddabaru haɗi dana tsafi,wani jan ruwa ya ɗauko ya zuba a wata ƙwarya kana ya yafa wani baƙin ƙyalle nan take kujerar masarautar bilhas ta bai yana cikin ƙwarya,sai haske take tamkar yanzu aka gama ƙerata.
haka ya dinga tsubbace-tsubbacensa daga ƙarshe ya daki kan aljanin tare da faɗin.
“Tashi wannan aikin na kane kaine kaɗai zaka iya,ina son ka zama aljanin dukkan wanda ya kuskura yahau wannan ƙawataccen kujerar muddin ba Magajin Mai martaba ne,idan kasa wani abu ya gagareka ko kuma kayimin kuskure cikin aikina babu shakka nine ajalinka kasan kuma  zan iya,dukkan abinda kake buƙata an baka saida kashanye jinin jarirai guda 10 kafin ka amince da hakan maza jeka”
wata girgiza Aljanin yay sai gashi ya ƙwala wani ihu tare da ware fuka-fuskansa ya ƙara wata girgizar a karo na biyu,ɓat ya ɓace daga wajan.
wata dry Boka gilmas yay kafin ya daki ruwan dake cikin ƙwaryar saiga Aljani    Gumfak akan kujerar mulkin garin bilhas..
Wani murmushin gefe baki Mai martaba Khalid tsuhun sarkin bilhas ya saki tare da sakin wata dry a lkc guda,gyara tsaiwarsa yay lkcn da yaji boka na faɗin.
“Duk wanda ya sake yahau wannan kujerar saidai uwarsa ta haifi wani badai shi ba,dan haka ka ƙwantar da hankalinka dole ne magaji yahau wannan kujerar mulkin dole ne ya gudanar da mulki kamar yadda kaima kayi babu shakka Magaji zai zama sarki”
Cikin farin ciki da kuma jin daɗin Mai martaba ya kashe wayar ba tare daya kuma cewa komai ba,lambun ya shiga ƙarewa kallo kamar mai neman wani abu kamar ance kalli gefenka yana juyawa yay tozali da.
a can fada kowa cikin son kawar da abinda yake ransa,ya saki murmushi tare da kallon sarkin fada yace.
“fake ring? but how can that happen? bayan ga tambarin masarauta nan ajikin zoben kuma idan fake ne babu yadda za’ai aga zanan tambarin masarautar a jiki”
kallonsa sarkin fada yay tare da sakin murmushi yace.
“congrat Chiroma am just joking is not take ring is real finally are the Emir of Masarautar bilhas”
wata wahalalliyar ajjiyar zuciya Chiroma ya saki tare da faɗaɗa fuskarshi da murmushi,daman ya sani da wahala ya zama jabo yana da tabbacin akan zoben da kuma wanda ya bashi zaben,cikin jin daɗi da kuma tsananin farin ciki ya isa inda haɗaɗɗiyar kujerar mulkin take ajjiye,gaba ɗaya mutanan wajan suka miƙe tsaye domin girmamawa,cikin issar daya keji tazo masa ya nufi zama akan kujerar runtsa idanunsa yay tare sa sakin ƴar ƙamar ƙara sabida abinda yaji wani irin..
Cikin jin daɗi Mai martaba ya nufi wajan daya hangi wani lafiyayyen nunannan fasadabir daya faɗo ƙasa sabida tsananin nunar da yayi,wajan ya ƙarasa tare da sanya hannu ya ɗauki fasadabir tare da nufar hanyar fita,yana fita harabar masarautar yanu wajan wani fanfu dake kusan masallacin bilhas,wankewa yayi kana ya juya ya nufi fada cikin tafiyar issarshi wacce take tare dashi duk da cewa mulkin ya riga ya tafi.
yana zuwa cikin fadar yaga gaba ɗaya an miƙe tsaye dan haka bai nuna alamun wani abuba shima ya tsaya domin ganin abinda zai faro dan yana da tabbacin a yau  Chiroma saidai wani bashi ba.
Tun kafin ya zauna akan kujerar wani zazzafan zafi da huci ya daki jikinsa,ga kuma wani abu tamkar allurar da yaji sun dira cikin tsakiyar kansa.
cikin fitar hayyaci da kuma tsananin azabar daya keji ya matsa daga kusan kujerar wacce bai riga ya zauna ba,a ƙasan lafiyayyiyar daddumar dake shimfiɗe a fadar ya faɗi ya zauna yana maida numfashi.
cikin takaici da kuma baƙin cikin abinda ya sameshi ya ɗaga jajayen idanunsa ya sauke a fuskar Mai martaba Khalid,wani murmushi Mai martaba yayi tare da ɗauke idanunsa daga gareshi ya kalli Lil prince wanda yake tsaye ya harɗe hannayensa.
a zahiri idan kaganshi zaka ɗauka hankalinsa yana ga abinda yake faruwa a cikin fadar ne,amma a cikin zuciyarsa tsananin damuwa da kuma zallar tunanine yay masa yawa,a yanzu bawai mulkin yake buƙata ba gaba ɗaya tunaninsa yana ga yadda zai ya samu farin cikinsa Zarina.
a wannan karan ita kawai yake muradi da kuma fatan gani,sosai zuciyarsa ta azabtu da rashin ganinta.
saukar muryar sarkin fada ce ta sanya saki numfashi tare da ɗaga idanunsa ya kalli sarkin fada.
hakan da yayne ya tabbatarwa sarkin fada cewa lil prince baiji abinda yace ba,cikin farin ciki Mai martaba ya mai²ta abinda sarkin fada ya faɗi ta hanyar faɗin.
“Magaji matso kusa lkcnka yayi a wannan karan ababu abinda zai hana ka zama sarkin bilhas..
*_Kogi_*
Hannu tasa ta murɗa handle ɗin ƙofar tare da buɗewa ta fito daga cikin bathroom ɗin,a kasalance kuma a sanyaye ta ƙarasa gaban dressing mirrow inda kayan shafanta yake ajjiye.
stool ta jawo ta zauna kana ta ƙurawa makeken mirrow’n dake manne a bango ɗakin,wasu zafaffun hawaye masu zafin gaske ne suka zamu nasarar fita daga cikin idanunta,wayarta dake side ɗin mirrow’nce ta ɗauki ƙara alamar kira ya shigo,a hankali ta miƙa hannunta tare da ɗaukan wayar idanunta ta lumshe hakan ya ƙara bawa hawayen da manne cikin ƙwayar idanunta damar gangarowa,a jin wani sabon kiran ya shigone ya sanya ta ware manyan idanunta wanda suka ƙanƙance sabida yawan kukan da take da kuma zallar tunanin rashin mafita akan lukutar masifar dake shirin tunkarota,sam koda wasa bata taɓa tunanin cewa maganar da Abba ya faɗa na cewar zai mata aure da gaske ba,tayaya zataiwa Aljaninta kishiya a cikin zuciyarta?bata jin koda wasa zata iya zaman aure da waninsa,shi kaɗai take muradi da kuma fatan kasan cewa dashi,kasan cewa kuma irinta har abada ɗinnan, babu abinda zuciyarta ke muradi sama dashi a wannan lkcn,sosai kunnuwanta keson jin daddaɗar muryarsa,idanunta na ƙwaɗai tuwa dason ganin ƙyaƙƙyawar fuskarsa mai cike da gwarjini da kuma haiba,babu abinda gangar jikinta ke murada sama dajin ɗumin jikinsa,sosai sonsa da kuma zallar qaunarsa keson zautar da tunaninta,ba tajin komai haka kuma bata ganin komai sai tsaftatacciyar soyayyarsa wacce a kullum take ƙara yawan a cikin zuciyarta.
a hankali ta janye idanunta daga kan makeken screen ɗin wayarta,wayar wacce ta kasan ƙirar iphone11 max pro ita ta ajjiye akan dressing mirrow.
cikin kasalan data gama zama a jikinta ta ɗauki wata lafiyayyan body lotion na carrot cikin nutsuwa ta fara shafa man a saman soft fresh skin ɗinta,sosai ta shafe ko’ina na jikinta,cikin ƙaramin lkcn skin ɗinta ya fara sharning musamman santala-santalan cinyoyinta.
bayan ta kammalane ta ɗauki body spray ta fesa a saman fatar jikinta,cikin nutsuwa ta miƙe ta nufi wajan wardrobe wata lafiyayyiyar arabian abayar ta ɗauka tare da vail ɗinta.
bayan ta kammala sanya unders ta zura abayar a jikinta tare da rolling kanta da vail ɗin abayar hakan ta haddasa bai yanar long hair ɗinta wanda yake ƙwance har bayanta.
ɗan ya mutsa fuska tayi tare da sanya hannu ta danne saitin zuciyarta haɗi da murzawa kaɗan,cikin siririyar muryarta wacce take fita a hankali ta ware laɓɓanta tace.
“Ya rabbi ka baiyarmin abinda yake alkairi a gareni,ubangiji ka bai yanamin aljanina koda shiɗin da gaske aljanina ba mutum ba,ina sonsa a yadda yake na kuma amincewa rayuwa dashi a duk yadda na sameshi,wannan aure idan shine silar yayewar damuwata Allah kabani ikon jure hakan,amma nasan dukkan wanda na aura bazai taɓa jin daɗin zama dani ba,bazan iya bashi kulawar daya dace ba amatsayinta na mijina ba,Ya see this innonce Zarina helf her ya rabbi”
lumshe idanunta ta kumayi kana ta waresu a karo na wajan biyar kenan taji wayarta ta fara ringing,bedroom flat shoe ta sanya a ƙafarta tare da sanya hannu ta ɗauki wayar ganin sunan Mom na yawo saman screen ɗin ya sanya tayi pic tare da ƙwaɓe fuska.
gyara zama Mom tayi jin tayi picking call ɗin ta kalli Sufyan dake gefenta tace.
“my luv you have a guest tun ɗazu ya kira wayanki baki picking ba,kiyi sauri ki fito haka”
Zarina ji tayi gabanta ya faɗi zare wayar tayi daga kunnanta tare dabin wayar da idanu,cikin rashin fahimtar zancen na Mom ta riƙe wayar tare da nufar hanyar babban parlour.
a zaune ta samesu suna kallon wani tafsir a tashar sunna t.v, tsawaya tayi ba tare da tayi magana ba,su duka kallonta suke musamman Mom ganin yadda ta rame idanunta suka ɗan fito sai fari data ƙarayi tamkar jini zai fito a jikinta.
kasa cewa komai Mom tayi saima miƙewa da tayi ta nufi part ɗinta,sam ba zata iya jure ganin halinda autarta ta take ciki ba,sosai take jin matsanancin tausayinta.
Sufyanne yay ƙoƙarin faɗin.
“yana parlour’n baƙi yana jiranki can”
lumshe idanunta tayi tare da saurin ɗauke kanta tace.
“yaya banso zuciyana ciwo please a barni bana da auran nan”
wani tausayinta yaji ya kamasa hakan tasa yace mata “sorry sweet sisi sabida nema maki mafita akai hakan am sure idan kikai auren zaki daina tunanin gaimu domin nika a film ban taɓa ganin mafarki yazo ma mutum a haka ba,kawai kiyi addu’a everting will be fine dear”
jikinta ta faɗa ta sakar masa kuka saida tayi mai isarta sannan ta zare jikinta ta daga nashi tare da goge idanuta ta nufi parlour’n,baki ɗauke da sallama wacce iya karta laɓɓanta a zaune ta sameshi akan sofa yasha shadda sai murmushi yake,kanta a sunkuye da kuma raguwar sanyin jikin daya rage mata ta nemi waje can nesa dashi ta zauna.
yanayinta ba ƙaramin birgesa yayi ba,cikin son janyota da shira yace.
“beauty ykk na sameki lpa?”
kaita jinjina masa tare da saurin tanne lips ɗinta sabida yadda taji zuciyarta nayi mata wani breating.
da ƙyar ta samu ta gai dashi haka ya dinga janta da surutu bata cewa komai sai uhmm ko ɗaga kai domin ko full face ɗinta ba,numfashi ya sauke tare da miƙewa tsaye yazu inda take zaune ɗan durƙoshewa yay gabanta tare da sanya duka hannayensa ya tallafo haɓarta.
lumshe idanu yay sabida tuzali da beauty full face ɗinta da yayi cikin sanyin murya yace.
“will you marry please beauty i love you so soo much..
*_Bilhas-*
Sarkin fada ne ya bawa Lil prince umarnin zama akan kujerar karagar,yana ƙoƙarin zama sukaji an fara tafi a bayansu gaba suka juyo da kallonsu zuwa ƙofa da sauri Mai martaba khalid ya miƙe tsaye domin wanda ya gani ba ƙaramin bashi mamaki yay ba,yana ƙyautata zonta wannan bashi bane sai dai kurwarsa.
Galadima ne yay dauriyar faɗin “wanene kai mene kakeso da zaka katsewa mutane daga abinda suke”.
Murmushi daddijon mutumin yay kana yace.
“a lkcn da zalunci yaga gsky a kuma lkcn da duhu yaga haske a wannan lkcn gaba ɗaya tunanin mutum goshewa yake dan haka nai maka uzurin rashin ganene da kayi dan nasan ruɗewa ce ta sanya hakan,amma idan kai baka ganene niba ai nasan Khalid wazeee bilhas bazai taɓa manta fuskata ba haka ne?”
innalillahi gaba ɗaya jikin  Mai martaba Khalid ne ya ɗauki rawa dan yana tabbacin zuwa yanzu tabbas mutumin da yake tunanine bawai kurwaraa bace.
murmushi Waziri yay mai cike da jin daɗi yace.
“bawan Allah meke tafe dakai har haka baka ganin ɗanin sarauta za’ai?”
gyara tsaiwarsa mutumin yay cikin fara’ar data zama jikinsa yace.
“wacce sarautar wanene ya gaji sarautar da za’a naɗashi?”
cikin rashin fahimta sarkin fada yace.
“Malam meke tafe dakai ne haka?”
kallon sarkin fada yayi yace.
“nazo kawo wanda ya dace da kujerar mulkin masarautar bilhas,gsky ce ta dawo yayinda ƙarya zata tattara kayanta tabar wannan wajan ba tare da an kureta ba,Nayjeb bashi shine ya dace daya zama sarki ba,domin a wannan karan wanda ya gaji sarauta gaba da bayanta shine yazo amsar abarsa”
ruɗani kenan gaba ɗaya wajan sun gama ruɗewa da zancen mutumin yayinda Lil prince ya zare idanunsa tare da faɗin.
“Malam banson surutun banza shin har aƙwai wanda ya dace ya gaji wannan kujerar bayanni?”
dry mutumin yayi yace 
“ƙwarai da gaske ya fika komai hankali,nutsuwa,ilimi,tausayi,jinƙai,haiba,ƙwarjini ya dawo karɓar kujerar gadonsa a lkcn da bai son cewa shiɗin jinin sarauta bane,ya dawo a lkcm daya dace ya ɗauki fansaaa”
ya ƙare maganar yana kallon Mai martaba,cikin rashin fahimta Lil prince yace.
“shirmen banza idan har bai san ya haɗa jini da sarauta ba tayaya kuma zai zama sarkin bilhas bayan bashi da wata alaƙa da masarautar,shin wai akanwa kake magana?”
wani banzan kallo mutumin ya watsawa lil prince kana yace.
“Sweetheart come in”
tun kafin ya shigo wani sihirhitaccen ƙamshi mai tafiya da tunanin mutum ya cika cikin fadar yayinda wata ƙyaƙƙyawar iska ta fara kaɗawa,wata iskace mai ƙarfi ta fara kaɗawa yayinda garin yay dubu alamun tabbas hadarin dake ƙasane yake yunƙorin zubda ruwa.
sosai yanayin garin yay daɗi iskar kuma ta fara ratsa jikin mutuane zuwa cikin hancinsu,yayinda take tahowa da ƙamshin furannin dake masarautar.
a kasalance ya lumshe daradaran fitinannun idanunsa wanda suke farar tas har wani ruwa suke kawowa sabida haske,yanayin iskar yay dai² da yadda sumar ƙasan wuyansa dake kaɗawa a hankali,cikin nutsuwa haɗi isa da izzar data gama zama a jinin jikinsa yake tafiya harya ƙarasu cikin fadar,cikin kaɗuwa da kuma zallar tashin hankali wanda suka gani gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin…
MALEEK!! wani ƙawataccen murmushi mutumin yay wanda ya bai yanar da zallar farin cikin da yake ciki,babu shakka a yau yazu masu da abu mafi farin ciki a yayinda wasu kuma yake abu mafi muni cikin rayuwarsu,tabbas bai yanarsa babbar nasarace ita kuma take nuni da cewa dukkan wata taƙaddama da ake akan kujerar mulkin yazu ƙarshe,basu taɓa wane shiba ko kuma mene matsayinsa,tsoro wani abunne kaɗai zai sanya suce sun manta matsayinsa,wanda a yanzu shima tsoron yakau domin wanda ake dominsa ya zama tahiri.
hannu ya sanya ya sharce zufar dake neman jiƙa masa kayan dake sanye a jikinsa,yayinda wani jiri ke neman ɗibansa ba tare daya shirya hakanma,har yanzu gani yake abu tamkar a mafarki,mafarkinma irinna shirme da shiririta,ƙara murza ƙwayan idanunsa yayi domin tabbatarwa kansa abinda yake gani a gabansa.
tashin hankali tabbas da ace mutum na iya sauya yau ta koma jibi ko kuma ya sauya jibi ta koma gata babu shakka da yayi hakan kodan samun cikar burinsa,amma ina banda Allah babu mai yin haka,wannan hukuncin lillahi wahidul qahhar ne.
lallai shine bashi da wani babbanci da photocopy ɗinsa,mekennan hakan?kenan ya kashe majine ba tare daya sare kansa ba?shin ya cire shukane ba tare daya cire nijiyar dake ƙasan shukar ba?koko ya manta da cewa shuka bata taɓa yiwowa saida iri shi yake da ƙoƙarin yaga tasa shukar ta fidda tsuro.
wannan wanne irin gagarimin artaban masiface keman zuwar masa ba tare daya shiryata ba.
jikinsa dake rawa ya kama ya riƙe a ƙoƙarinsa nason daina shi rawan.
a karo na biyu ya ƙara ɗaga kansa ya kalli MALEEK wanda ke tsaye yana ɗan juya ƙwayar idanunsa wa al’umar wajan.
da sauri ya janye idanunsa sabida ganin MALEEK ɗin da yayi tamkar zanan SUDAIS SUFRAK WAZEER BILHAS.
Mutanan Fadar kam kowa ya kasa ƙwaƙƙwaran motsi sabida ƙaɗuwa da kuma ganin abin al-ajabi,yayinda Lil prince ya zubawa Maleek ɗin idanu sabida ganin cikar hallitarsa,kyau,zati,haiba,ƙwarjini,da kuma zallar annorin daya haske fuskarsa,duk da dry ba ɗabi’arsa bace amma yadda fuskarshi ke haske  saika ɗauka murmushi yake,musamman yadda beauty point ɗinsa ke lumawa sabida mutsawar fuskarsa.
Gyara tsaiwa mutumin yay tare da kallon Maleek sai kuma yay murmushi,ɗauke idanunsa yayi kana ya ɗan tafa hannayensa yace.
“Oska”
wani ƙatun mutum ne ya shigo kana ganinsa kasan shiɗin ba rainon nan bane,hannu ya miƙa masa yace.
“bani fake face ɗinan”
babu musu Oska ya miƙa masa fuskar dake hannunsa,amsa yayi tare da ƙarasawa inda Maleek yake a tsaye yana zuwa ya saida fuska a dai-dai tasa fuskar ya saka masa,tabba wanda baya wajan yabar kallo.
nan take fuskar SAIFUDEEN BILYAM ta bai yana.
cikin wani sabon tashin hankalin daya shiga Mai martaba,yaci gaba da ƙarewa Saifudeen kallo,cikin rikicewa haɗi da daburcewa yace.
“Captain Saifudeen how zai zama Maleek,wannan maganar aƙwai munafurci a cikinta,kuma bayan kowa yasan cewa Maleek he is no more shine za kaje kayi wani siddabarun naka kazo kace wannan Maleek ne sabida kana son ka mallaki kujerar bilhas ko?”
sai a lkcn Saifudeen wanda yake matsayin Maleek ya ɗaga gajiyayyun idanunsa ya sauke akan fuskar Mai martaba tare da kafeshi da idanunsa masu kaifin gaske.
da sauri Mai martaba ya janye idanunsa sabida wani mugun ƙwarjininsa daya dirar masa,Sarkin fada ne ya kada baki yace.
“a saninmu dai Saifudeen  yazo masarautarnan sabida ya bawa Mai martaba tsaro ya kuma kula da shige da fice na wannan masarautar amma yayane zai zama sarki a masarautar bilhas bayan bashi da wani alaƙa da ita?”
gyara tsaiwa mutumin yay kana ya bawa Oska umarnin ya cirewa Saifudeen rigar jikinsa.
dan sauri Saifu ya ɗago kansa ya kalleshi sai kuma ya shagwabe fuska cikin wata tautashasshiyar murya mai sauti da amo da kuma daɗin saurare yace.
“My love”
jijjina kai mutumin yay ba tare daya tanka Saifu ba,hakan ya tabbatarwa da Saifu ba shawararsa yake nema ba wannan umarnine,manyan wayoyinsa masu ƙirar iphone 12 max pro,ya miƙawa Oska ya amsa ya zuba a jikin aljihunsa,kana ya ware hannayensa tare da ɗagasu sama kaɗan.
Cikin nutsuwa Oska ya fara ɓalle ma ɓalli rigar jikinsa kana ya fara ƙoƙarin zare masa rigar zuwa sama,shidai yana tsaye kamar sitatue komai masa ya kunce yayinsa zuciyaraa keyi masa tsalle tamkar zata faso waje haka ya keji,abubuwa da yawan gske ne suka haɗe masa a wannan karon,banda kallon mutumin daya kira da my love babu abinda yake.
abinda ya keso ya fahimta shine shin mayafin masa jinin sarautane bai taɓa sani ba sai yanzu?all this da yake faruwa na mene?meye haɗinsa da wata sarauta a bar da bai taɓa sha’awa ba koda wasa,bayan yana kallon yadda shuwagabannin sukewa talakawansu,shin dama wannan dalilin ya sanyashi dawowa yau ba tare daya sani ba.
numfashi ya fesar mai zafin gaske lkcn da yaji an cire masa rigar jikinsa ya rage daga shi sai marar singlet wacce ta kama jikinsa,hakan ya  bai yanar da ƙwantaccen baƙin gashin dake ƙirjinsa wanda yake ƙwance lub lub dashi.
ware manyan idanunsa wanda suke a lumshe yay sabida jin an taɓa hannunsa,idanun sane ya saukan akan Lil prince wanda yake tsaye gabansa yana taɓa guron dake damtsen Saifu.
“wannan kaɗai ya isa ya tabbatar maku da waye shi domin kowa yasan babu yadda za’ai guron masarautar bilhas hannun Saifu,ku cire duk wani tunani dake son ruɗa maku ƙwaƙwalwa dan haka Maleek jinin bilhas ne kun gane”
Waziri ne ya gyara tsaiwa wanda tun ɗazu baice komai ba,sai idanu daya zubawa Saifu yana ayana abubuwa masu yawan gaske cikin ransa.
cikin nutsuwa yace.
“Ba wannan muke da muƙatar jiba,yaya akai Saifu yazo masarautar bilhas da niyar kula da Mai martaba ba tare daya san koshi wanene ba?sannan gaba ɗayanmu kowa yasan cewa Maleek baya raye mene shaidar da zai tabbatar mana da cewa shiɗin jinin bilhas ne kamar yadda ka faɗa?”
Numfashi Lil prince ya sauke shi gaba ɗaya tunaninsa yaya akai Saifu ya tsallake tarkon daya haɗa masa?lallai a wannan masarautar aƙwai masu yi masa zagwan ƙasa banda haka tayayane Saifu zai tsallake wannan lukatar masifar daya sanya shi?
Gefe guda kuma Saifu ne ya yage fake face ɗin da aka sanya masa ya koma Maleek ɗinsa zam,a hankali yake tafiya harya ƙarasa gaban mutumin daya kira da sunan my love,lumshe idanunsa yay sabida wani bugun gaske da yaji zuciyarsa tayi masa,a wannan lkcn itace ta faɗu masa domin daman duk wani numfashi da yake fitarwa baya fita saida tunaninta.
ware idanun nasa yay tare da watsasu akan fuskar Mutumin cikin wata sabuwar murya wacce ta bai yana kanta a yanzu yace.
“why all this happen?kasani cikin juyayi ka hautsinamin tunina dan ALLAH ka gayamin waneni?nasan bana da mahaifin daya huce kai,kaine mahaɗin rayuwata kaine mutumin dana buɗi ido dashi,haka kuma kaine farin cikina kaine komai na Maleek,amma yanzu mene ya sanya kake haɗani da abinda ban haɗa jini dashi ba,bayan kaima nasan baka haɗa jini dashi ba,ka sani abubuwa da yawa wanda kawai yinsu nake ba tare dana san dalilin hakan ba,na aiwatar da dukkan wani umarninka sabida nayi maka biyayya duk mene ya sanya kayimin hakan,ka sanya nayi aiki da banawa ba,ban taɓa sanin yaya ake riƙe wata aba bindiga ba sai daka sanyani,ina tsaka dayin tiater a asibiti kace na shirya domin zuwa garin bilhas kuma cikin masarautar,kasa na sauya sunan da banawa sai nayi da gaske nake gane cewa dani ake magana sabida nayi amfani da sunan da yake ba mallakina ba,duk hakan na menene?”
Tafiya Abbu ya fara harya isa gaban ƙawatacciyar kujerar mulkin da ake taƙaddama a kanta,cikin ɗaga murya yace.
“Sabida ƙwato maka ƴan cikinka,nayi hakanne kuma sabida ka tsira da ranka,sabida nayi imani da Allah dukkan wanda ya kashe ahalinka da zarar yasan kana raye kaima sai yabi diddiginka yaga bayanka,nayi hakanne sabida ka kai lkcn da zaka ɗauki fansar jinin iyayenka,nayi hakane kuma sabida ka girma ka zama sarki kamar yadda mahaifinka yayi dukkan abinda kaga nayi wanda kake ganin ba dai-dai ba gaba ɗaya nayi shine sabida dakai MALEEK!!”
ya ƙare maganar yana ɗaga murya,cikin toshewar ƙwaƙwalwa da kuma juyayin daya shiga ya fara girgiza kansa tare dayin baya,cikin takoshewar murya yace.
“No!! Abbu kada ka gayamin cewa bakai ne mahaifina ba,kada ka rusamin farin cikin da nake ciki idan ina tare dakai,kada kace zaka raba zuƙatanmu ta hanyar faɗin wata kalma wacce zatai dai-dai da bugawar zuciyata,na roƙeka Abbu koda abinda zaka faɗa gsky ne kada ka faɗeshi bana buƙatar komai sai kai dan Allah kazo mu koma inda muka fito please”
kansa ya kisa a wuyan Abbu a kuma dai-dai lkcn wace zafaffun hawaye suka shiga fita ta cikin idanunta,yayi hakanne kuma sabida kada jama’ar wajan suga rauninsa akan Abbun nasa.
wani murmushin takaici Abbu yay cikin ƙasa da murya yace.
“am so sorry sweetheart banyi hakan dan nai hurtting ɗinka ba,amma ya zama dole na faɗi abinda yake ɓoye na tsawon shekaru masu yawan gaske,kayimin afuwa amma dole ne susan sun kashe macijine ba tare dasun sare kansa ba”
Galadima ne yay gyaran murya yace.
“itafa kujera bata jira saidai a jirata idan baku da wata hujja muna iya ɗura Lil prince domin shine ɗan gado gaba da baya kuma…”
da sauri Lil prince ya katseshi ta hanyar faɗin.
“ohhh koda wata shaida ya bayar ai babu wani wanda ya dace da wannan kujerar saini domin nine magajin wanda yay murabus akan kujerar dan haka bamu buƙatar jin wannan ƙanzon kuregen kun gane”
Dariya Abbu yayi yace.
“a yanzu zan faɗa maku hawaye Maleek da kuma yadda akai ya zama magajin wannan kujerar da  asalin labarin shine..
*_Kogi_*
kasa ce masa komai tayi sai jajayen idanunta da suke ɗigar ruwa ta zuba masa,duk yadda taso ta ware laɓɓanta domin ta faɗa masa wata maganar kasawa tayi.
hannunsa ya janye daga jikin fuskarta cikin farin ciki yace.
“i’m happy sosai nai farin ciki wannan shurun naki ya tabbatarmin kin amsheni matsayin mijinki nanda sati biyu masu zuwa,nagode Allah ni Yusuf dana samu wannan beauty gril ɗin matsayin matar aure thank you”
ɗan ware manyan idanunta tayi tare da juyashi a saman fuskarsa wacce sai lkcn da samu damar ganinta.
sosai yake da kyau dukkan abinda wata ƴar mace zata buƙata wajan ɗa namiji yana dashi amma yaya zatai?zuciyarta ta riga data bawa wani tuntuni bata jin zata iya yi masa kishi domin hakan kamar cin amana tayi.
janye idanunta tayi daga kansa,daimond ring ɗin hannunta ta shiga murza wanda ƙwana biyu yay ɗan duhu amma yau cikin ikon Allah sai haske yake.
miƙewa yay yace.
“beauty zan tafi sai gani na biyu wanda daga shi kuma saidai ki ganni as ur husband”
samun kanta tayi ta jinjina kai cikin shauƙinta da ƙaunarta ya fice daga cikin parlour’n.
hawayen da take ta maƙalewa tun ɗazu suka samu damar sauka cikin idanunta.
lallai idan ba mutuwa yay ba to ba’a gama jarabtarsa da wasu abubuwan ba,ita dai wannan abubuwan da suke faruwa sunyiwa tunanin yawa sun girmi brain ɗinta,shin yaya zatai da soyayyarsa wacce tayi mata muguwar kamo tun ƙuruciyarta.
ta amince koda soyayyarsa itace ajalinsa bazata taɓa haɗashi da wani a kuma zuciya ɗaya ba.
a kasalance ta miƙe ta nufi hanyar babban parlour nanta tarar da Abba shida Mom suna duba wasu saitin kayan ɗaki a cikin waya da alama kuma odersu za suyi,ba tare data kulasu ba ta nufi bedroom ɗinta kai tsaye kan bed ta faɗa tare da zame vail ɗin da tayi rolling kanta dashi.
hannunta ta rungume a ƙirji ta soma shassheƙar kuka.
sosai tayi kuka mai tsuma zuciya a haka wani wahalallan bacci ya ɗauketa.
a can parlour kuma Mom ce ta kalli Abba tace.
“a tunanina ba wannan hanyar ya kamata kabi ba,zaifi kyau abar yarinyar nan ta auri wanda takeso”
kallonta yayi yace.”ohh kema shashancin nata za kibi?wanda takeso nasan ba zata sameshi ba,da alama aljanu suka buɗe mata idanu banda haka ba tayaya mutum dan yay mafarki da wani zaice shiya keso,nafa masa auri sati biyu nan da kwana uku xuwa biyar za’ai bikin shima Tupic ya fito da wacce ya keso gaba ɗaya zan haɗasu kima gaya mata aure ita da Yusuf babu fashi..
*_Bilhas_*
Rana mafi muni da baƙin ciki ranar da dukkan wani  dake cikin garin bilhas bazai manta da ita ba,wato ranar da aka wayi gari da mutuwar SARKI SUDAIS.
a cikin daren da zasu riski ajalinsu naje tirakarsa domin yin wata muhimmiyar magana,bayan mungama  ɗansa wanda bai huce shekara guda biyu da haihuwa ba ya maƙalemin duk yadda nasu yaje ga mahaifinsa ƙi yayi.
hakan tasa Sarki Sudais yace naje dashi zuwa safiya a kawoshi,babu musu na ɗaukesa muka shige sashina.
da farin ciki matata ta amshe ta haɗa da yaron wajanta.
a tare muka ƙwanta gaba ɗaya asuba nayi Maleek ya tashi ya fara kukan Abbi Ummi,cikin sauri nai al’wala shima ya nuna yana so haka nayi masa na fita zuwa masallaci ba tare dana tafi dashi ba.
tun kafin na isa masallaci naci karo da jama’ar masarautar sun cika harabar masarautar,da sauri na ƙarasa wajan mutanan nace lafiya.
cikin kuka Galadima yace.
“a daren jiya Sarki Sudais ya haɗu da ajalinsa shida matarsa tare da ɗansa Yarima Maleek”
tashin hankali kenan wanda ba’a saka masa rana sabida tsabar tashi hankali kallonsa kawai nake ba tare da nace ƙala ba,banda sauke ajjiyar zuciya babu abinda nake,nidai kawai na jishine amma ban yarda da abinda yake faɗa ba,a wannan lkcn dan salla ta zama dole ne ya sanya naje masalaci na gabatar.
ban tabbatar da abinba saida naganni tsaye a gaban gawar Sarki Sudais shida matarsa Omeshi sai kuma gawar ƙaramin yaro a tsakiya,sosai na shiga wani tashin hankalin sabida a sanina Yarima yana wajena ga kuma wata gawa dana gani.
haka aka buga tambarin masarauta tare da shela cikin abinda baifi awa guda ba,garin bilhas ya ɗauki kuke-kuke mutane jama’a koda ina zuwa ake manyan mutane da kuma Sarakuna da gari daban-daban.
haka akai masu wanka aka kaisu yaron kuma a cikin gida mata sukai masa shida mahaifiyarsa hakan tasa babu wanda ya gansa sai a cikin makara.
a ranar da akai sadakar baƙwai a wannan ranar aka naɗa Mai martaba Khalid a matsayin sarki,Mai martaba Khalid kuma ya kasance wa ga mahaifin Sarki Sudais ma’ana yayane wajan Sufrak wanda suka haɗa uba,uwa kuma kowa da tasa.
sosai nai mamakin yadda akai Mai martaba ya samu kayan ɗanin sarki domin babu wanda yasan inda yake sai Sarki Sudais.
tunda wannan abun ya faro da idanuna banga Mai babban ɗaki ba,ashe itama da wata lukutar qaddararce ta sameta ta makanta.
gaba ɗaya dai na rasa mene yakemin daɗi.
a wannan daren rananne kuma kunnuwana suka jiyemin wata babbar magana wacce ta sanya na gigice cikin gaggawa naje na ɗauki Yarima Maleek na goyashi a cikin darenne kuma nabar masarautar bilhas.
daga nan kuma ban sake sani mene yake faruwa ba,saidai a zuciyata na ɗauki niyar bawa Yarima kulawa da kuma gata haɗi ilimi bayan ya gama samun wananne kuma zam dawo dashi a matsayin garkuwar iyayensa wanda zai ɗaukar masu fansar abinda ya sanya nabar masarautar.
sosai na shiga duniya da Yarima nayi dako nayi zubda shara haka kuma nayi aikatau duk danna kula da Yarima,ina ƙwana banci domin naga na inganta rayuwarsa.
daga nan na sanyashi makaranta islamiya da buko,sosai yake karatu wanda ya bawa kowa mamaki.
shakarunsa goma cif a duniya ya haddace al’kurani cikin farin ciki hukumar makarantar suka bashi kyautar kuɗi masu yawan gaske.
haka na fara juya kuɗin ina business ubangiji kuma ya sanyamin albarka.
shekara na dawowa na zama mai kuɗin gaske a kuma wannan shekarar jama’ar unguwa suka fara zargin Yarima shegena hakan tasa nai mana ticket muka koma Cameroon da zama.
ƙwanci tashi Yarima ya girma ya zama cikakken likita mai zaman gaske ɓangaren Gani wato likitan mata.
sosai ya zama mai kuɗin gaske harya takeni a kuɗi domin har dry yakemin yana ban iya business ba,na kanyi dry domin nasan duk kuɗin hanuna mallakin sane.
Nasan kuna son kuji yaya akai Yarima Maleek yazo masarautar   Bilhas a zummar soja? bayan barinmu daga bilhas wajan shekara biyu na dawo a wannan lkcn nayi ɓadda kama na gana da matata wacce ta kasance Jakadiya a wannan lkcn,ita kaɗai na gayawa dukkan abinda yake faruwa kuma na bata number wayata duk yadda tasu na tsaya naga ɗana ƙi nayi.
A wata rana ina zaune a parlour ina duba wasu files naji kiran waya da sauri na ɗaga ciki mamaki dajin muryar matata.
nan ta shaidamin cewa ka sanya a nema maka soja mai kula dakai,sosai nai farin ciki dajin hakan,babu ɓata lkcn naje wajan shugaban sojojin domin na sanshi aiki ya taɓa haɗamu a Cameroon,nan na bai yana masa ƙudirina da ƙyar ya amince,haka na amshi uniform da komai wanda zai nuna shaidar shi cikakken soja ne.
Yarima yana cikin yiwa wata baiwar Allah aikin domin ciro mata baby na sanya a kiramin shi,saida ya gama aikin yazo yana zuwa na shaida masa buƙatata ba tare da tambaya ko kuma musu ba,ya amshi kayan gari na wayewa ya sanya kayan har airport nai masa rakiya domin zuwa bilhas.
idan kun lura tun zuwansa bai taɓa sanya complt uniform ɗin ba,da yawan lkcn kuma idan kun kira sunansa bai fiya amsawa ba sabida yana jin wani iri kasan cewar sunan ba nasa bane.
Maganar fake face kuma bayan na gama shirya komai na tafiya,na samu Oska na shaida masa komai sannan nace ya bani fuskar robar da zatai dai-dai data Yarima Maleek haka ya kawomin na bashi kuɗinsa.
Tsagaitawa yay da maganar kana yay murmushi yace.
“kun girgiza ko? hatta sanya Yarima Maleek a ɗakin duhu da kukai ina sane dashi duk da cewa shiɗin bai gayamin ba,ba kuyi mamakin yadda yake shiga wajan Mai babban ɗaki kai tsaye ba duk da matakan tsaron da yake sashin,dalilin shine wanda yake gadin wajan shine ɗana kuma a wannan lkcn ya riga ya gama sanin komai akan Maleek ɗin ya kukaji wannan bayanin?aƙwai wanda zai girgizako sai nan gama yanzu dai kamar yadda kukace kujera bata jira saidai a jirata toga Yarima Maleek nan yazu domin hawa kujerarsa ta gado”
gaba ɗaya wajan yay shuru wasu kuma hawaye suke gogewa sabida mutuwar Sarki Sudais ta dawo masu sabuwa.
Sarkin fadane ya numfasa yace.
“Allah ya taimaki Sarki Sarakuna ɗan nagada gaba da baya Allah ya ƙara maka lafita da nisan  ƙwana matsu a fara ɗani domin lkc naja”
Yarima Maleek dake durƙoshe dafe da kansa yana sauke ajjiyar zuciya,yana jin abun tamkar a mafarki mai yasa rayuwa take masa haka ne?mai yasa qaddara take juyashi ne har haka?mene laifinsa da wannan mafisun suke bibiyar rayuwar mai mene ya sanya za’a ɗura masa mulkin da baya buƙata,mene ya sanya za’a ɗura masa nauyin jama’ar da mazai iya basu haƙƙinsu ba,tayaya zai san wani yaci ko bai ciba.
shikam bazai iya sam baya so baya kuma muradin wannan kujerar ya hqr da ita.
jajayen idanunsa ya ɗaga ya kalli Abbu cikin wata iriyar murya yace.
“Abbuna banso bana buƙata”
cikin sauri Abbu yace.
“bakai kakeso ba,ita Sarautarce take sonka dan haka ko kanaso ko bakaso dolene ka zama Sarkin garin bilhas”
jin abinda Abbun yace ya sanya ya miƙe tsaye jiki a sanyaye ya fara tafiya zuwa wajan kujerar,wani shu’umin murmushi Mai martaba yayi domin yasan babu yadda za’ai Maleek ya zauna a wannan kujerar ba tare da wani abu ya samesa ba,dan haka sam mai dabu da ɗanin nasa ba,dan yasan cewa Lil prince shine magajin wannan kujerar.
a hankali Maleek ya ƙarasa inda kujerar take haka kawai yaji wata faɗuwar gaba tare da tsoran zama akan kujerar ya ɗarsu cikin ransa.
wajan 5minutes yana tsaye shibai zauna ba haka kuma bai juya ba,numfashi mai ƙarfi ya sauke tare da lumshe idanunsa a kuma dai-dai lkcn ya samu nasarar zama akan kujerar.
runtsa idanunsa yay da ƙarfin sabida abinda yaji,gaba ɗaya jikinsane ya fara rawa gargasar jikinsa ta mimmiƙe jijiyoyin kansa suka fito raɗa-raɗa azabar daya kejine ya sanya yay saurin..⁷¹,⁷²

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *