TSANANI CHAPTER 1

TSANANI 







CHAPTER 1




Yunwa da ƙishirwar da suka addabe ni ne suka sanya ni kasa bacci ina yi ina farkawa sbd yunwa ta riga da tayi min illah, haka ma innata baccin kawai take yi amma na fahimci ita ma tana jin irin radadin da nake ji, don na lura sosai tunda ta kwanta take juyi.

Agogon da ke manne a dakin mu na duba ƙarfe goma dai-dai na dare, har na share na hakura saboda na san matukar na fito diban abinci xan iya samun matsala da innah salamatu, har na hakura naji abin ba mai yiwuwa bane matuƙar muka wayi gari a haka zamu iya samun matsala. daurewa nayi na tashi na don samo mana abinda zamu kai bakin salati, ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar korar mu daga gidan gaba daya. A hankali na lallabo na fito daga dakin innata saboda bana so ita kanta tasan zan fita, indai ta sani sai ta dakatar da ni saboda bata son abinda zai bata mata rai. Kasancewar innata mace ce mai saukin kai bata fiye son abinda zai kawo tashin hankali ba, wannan dalilin ya sanya aka mayar da ita bora saboda hakuri da kawar da kai irin nata. Inna salamatu da yayanta su suke juya gidan duk a abinda suke so shi ake yi.

Bakin murhu na nufa a hankali na bude tukunya, tuwo miyar kuka na gani, ba karamin dad’i naji ba saboda rabon da na sanya wani abu a bakina tun abincin safe. tsugunnawa nayi tare da yin bismillah na fara cin tuwon, kafin kace me tuni naci rabinsa, daga nesa na hango ana haskani da fitila a raxane na mike tare da boye hannuna a bayana, sai da ta karaso daf da ni sannan na ga ashe innah salamatu ce, wani kallo ta sakar min wanda ya sanya jikina rawar ɗari, kafin tace min wani abu tuni hawaye sun cika idona, don na san na taro kwai tara tsinana, na janyo wa kaina da innata masifar da Allah ne ya san ƙarshen ta, tsungunawa nayi tare da rokonta ta yafe min.

Cike da takama da kasaita ta matso daf da ni janyo wuyana tayi tare da ɗauke ni da marin da sai da network din kaina ya dauke gaba daya.
“Munafuka annamimiya irin mugun hali, wato ragowar tuwon da na bari zamu dumama da safe shi ne kika biyo dare zaki cinye shi ko? Dama na dade da fadawa Malam kin fara sata amma ya nuna min kamar nayi miki kaxafi” kafin kace wani abu tuni jama’ar gidan mu sun taru kasancewar gidanmu gidan yawa ne, shi yasa duk motsin da zaka yi a kunnen mutane zaka yi shi, tofa albarkacin bakinsu suka shiga yi dukkan su babu wanda ya tsawatar a kan abinda aka yi min sai ma zuga inna salamatu da suke yi, babu wata kalma da ke fitowa daga bakinsu banda ta aibatawa da muzantawa

Dakin babana inna salamatu ta shiga, tarar da shi tayi yana bacci abinsa, sababin da ta rika yi masa a kansa ne ya farkar da shi, tashi yayi ya biyota suka taho wajena, tsaye na ganshi a kaina, wani irin kallo yake min mai cike da tsana, babu abinda ya fito daga bakinsa sai “tabbas abinda ake zargin ki da shi ya tabbata Sa’adatu, wannan shi ne sakamakon tarbiyyar da nayi miki, sakayyar da xaki min kenan a ajiye abu ki sata ko? abin boye ya fito sarari abinda ake zargin ki da shi ya tabbata yau na gani da idona, da a zatona sharri ake miki amma yau naga zahiri” baƙin ciki ne ya tokare min xuciyata naji kukan ya tafi gaba ɗaya saboda ba wannan ne karo na farko da na fara gamuwa da irin wannan kalubalen ba idan da sabo na saba, indai wannan rayuwar ce mun saba da ita ni da mahaifiyata, an mayar da mu tamkar gumaka marasa amfani a cikin gidan.

Maganar baba ce ta katse min tunanina “Sa’adatu ba ki da labarin na hana a rika baki abincina ne, ba ki da labari nace? amsa min!!!
Kaina a kasa na amsa masa da
“Eh”
“To daga yau na haramta miki abincina ke da uwarki don baxan zauna ina ciyar da ƙatuwar banxa mara amfani ba, shekara sha tara babu abokin tashi duk yan uwanki an gabatar da su ke kadai kika rage, mugun halin uwarki ya hana ki samun miji, to ki sani baxan cigaba da ciyar da ke ba, saboda duk abinda ke faruwa uwarki tana sane ta kyaleki kara zube ta saka miki ido kiyi abinda kika ga dama to sai dai kuwa ta ɗauki nauyin ki, hidimar ma da nayi a baya ta isa Allah ya bada lada”
Wucewa yayi dakinsa yana huci
Tuntsurewa Inna salamatu tayi da dariya. +

“Oh Allah ya taimake mu yayanmu suna da farin jini, tun suna yan sha shida ake kwashe mana su, to kin ji dai abinda tsohonki yace da kansa ba sako ba, sai a yi kokari a fito da miji ko kuma a tsufa a gida”

Haka ragowar matan gidan da yayansu suka rika min dariya gami da goranta min a kan rashin samun mijin aure, jikina babu wani karfi kamar an xare min laka na kasa tashi daga wajen da nake sbd takaici nafi minti goma ina xubar da hawayen bakin ciki, yanxu idan Baba ya hana mu abinci wane hali yake so na tsinci kaina.

Tabbas idan rayuwata ta cigaba da kasancewa a haka ban san ina xan sa kaina ba.

Ya Salim na hango daga kofar ɓangaren su yana dago min hannu, alamar na biyo shi. salim dan kanin mahaifina ne kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda basa goyon bayan abinda ake yi mana ni da mahaifiyata, har wasu daga ya’yan gidanmu suna tunanin ko sona yake yi, wannan dalilin yasa mahaifiyarsa take ta fadi tashi dan ganin ta raba ni da shi. Bin bayan shi nayi muka fito soro, cikin nutsuwa ya kira sunana “Sa’ar mata!!” Da yake da wannan sunan yake kiran a.
Dago fuskata nayi tare da share kwallar da ta cika idona na amsa masa da na’am ya salim.

“Kiyi hakuri a kan abubuwan da suke faruwa a gidan nan, ina daki ina jin irin abinda suke miki kasa jurewa nayi na fita, saboda xuciyata baxa ta jure jin mugwayen kalaman da suke fada miki ba, ki daurewa zuciyarki ki rika kulawa da dukkan abinda xai sa a rika yi miki irin wannan cin mutuncin, indai matsalar abinci ce tasa aka yi miki insha Allah na ɗauki nauyi kullum zan rika kawo muku abincin da xaku ci ke da innah. Ki kara hakuri komai na Allah yana da iyaka kuma dukkan tsananin yana tare da sauki, wannan rashin auren ki ɗauke shi a matsayin jarrabawa, duk wadannan abubuwan da suke faruwa wata rana sai sun zama tarihi a gareku ke da innah, kiyi hakuri ki jure a kan dukkan kalubalen da xaki fuskanta a gidan nan, lokacin ki na yi xaki tashi, da aure da mutuwa duk lokaci ne da su kuma mijinki na nan xuwa ya ɗauke ki, ya samar miki kyakkyawar rayuwa

Wadannan kalaman na ya salim ba karamin kwantar min da hankali suka yi ba, sai naji dukkan damuwata tayi sauki, farin ciki ya saukar min.

Leda ya miki min, karbi wannan sa’ar mata. Girgiza kai nayi ka bar shi yaya wannan kyautar sai ta jawo maka matsala.
Bata rai yayi ki karba kowace irin matsala xata jawo ba ruwanki.
Tsugunnawa nayi na karba tare da yi masa godiya, wucewa daki nayi na barshi tsaye yana min kallo mai cike da tausayawa.Ko da na shiga daki a zaune na tarar da innah mamaki tare da fargaba ne suka cika zuciyata saboda yadda na ganta a zaune ga kuma damuwa bayyane a fuskar ta, da sauri na ƙarasa wajenta, tsugunnawa nayi tare da dafa kafarta “lafiya na ganki a zaune innah?” Kawar da kanta gefe tayi da alama bata so na fahimci halin da take ciki ba,  sake tambayarta nayi. “Dan Allah innah ki fada min damuwarki ni kadai na rage miki dan Allah ki fada min abinda ya sa ki kuka” share hawayen da ya cika idonta tayi “Babu komai Sa’adatu, amma tabbas ban ji dadin abinda kika janyo mana ba, da kin hakura Allah zai kawo mana hanyar da zamu samu abinci, bakin dan Allah ya tsaga baya hana shi abinci, da baki taɓa musu kayansu ba da duk haka bata faru ba, duk rashin mutuncin mutum bai isa ya keta alfarmarka ba matuƙar baka shiga gonarsa ba, haka zai ganka ya kyaleka, amma sanadin wannan kin janyo abinda za a yi ta goranta mana, shikenan sun samu topic din da zasu rika maimaita wa kullum, dan Allah ki xama mai gudun xuciya da yarda da ƙaddara Sa’adatu, duk halin da muke ciki Allah ya fi mu sani”

Ji nayi kwalla na shirin fito min daga idona a takaice nace “Haka ne innah insha Allah xan kiyaye dukkan abinda zai kawo matsala a tsakanin mu” ledar da ya salim ya bani na miƙa mata, ga wannan ya salim ne ya bani, kuma yace zai riƙa kawo mana abinci kullum mu riƙa hakura da na gidan nan.
Shiru innah tayi sannan tace “Ni fa bana son irin wannan Sa’adatu kin san halin uwar yaron nan sarai bata ƙi taci mana mutunci ba gaba ɗaya, ki dakatar da shi bana so ina zaman zamana a xo a daga min hankali

“Insha Allah babu abinda xai faru innah ai shi ba shi da matsala kuma tsakaninsa da Allah yake taimakon mu”
bude ledar tayi gurasa ce da nama, godiya ta yiwa yaya salim tare da fatan Allah ya albarkaci rayuwarsa, sai da muka ci muka koshi sannan muka kwanta, amma abin mamaki sai bacci ya kauracewa idanuna maganganun da aka riƙa fada min ne suka rika dawo min cikin kunnuwana, tashi nayi na dauro alwala na fara jero nafilfili, bayan na idar na dauki Alkur’ani na karanta, sannan nayi addu’a Allah ya saukaka mana halin da muke ciki, daga lokacin naji nutsuwa ta lallube zuciyata bakina bai gushe da ambaton Allah ba, ban san lokacin da bacci yayi awon gaba da ni ba.

Kiran sallar asuba ne ya tashe ni, da sauri na dauro alwala tashin innah nayi muka tada Sallah, azkhar muka rika yi har zuwa fitowar rana.

Ina daki ina shara naji ana kwala min kira, jikina na rawa na leka ta window don ganin mai kirana, umma ce mahaifiyarsa salim, a ladabce na amsa mata da “na’am umma”
Wani matsiyacin kallo ta bi ni da shi, “kada ki sake ce min umma domin ni ban haifi mai baƙin jini irinki ba, wato an rasa mai tayawa an ga dana kyakkyawa zaki makale masa ko to sam bazai yiwu ba, yanzu ma gargadi na karshe naxo yi miki babu ke babu salim, na yanke duk wata alaƙa da ke tsakaninku, ki fita daga rayuwar dana idan ba haka ba kuma baxa tayi miki kyau ba, don baxa ki lalata min shi ba ki gurbata min rayuwarsa, kin shiga  kin fita har sai da yaron nan ya nace miki, gashi yanxu har hidima yake miki, to baxan lamunta ba saboda shi ba ubanki bane ba a kansa nauyin ki yake ba, uban naki ma ya kasa saboda mugun halinki da na uwarki, tun wuri ki kyale shi kafin na fito bainar jama’a na yaye miki rigar arziki”.Duk maganar nan da take kaina na ƙasa na kasa dagowa sbd bakin ciki, haka ta gama ban-bamin masifarta ta koma ɓangaren su, taimakon da Allah yayi min ragowar matan gidan basu fito sun tayata ba amma nasan duk abinda ya faru da sa hannunsu.

A sanyaye na zame na xauna, cikin jimamin abinda ya faru dani naji innah na min magana “kiyi hakuri Sa’adatu ki daina damuwa Allah muke gayawa matsalolin mu shi muke fatan ya kawo mana dauki, tashi ki kintsa ki tafi makaranta Allah ya baki dukkan abinda kike nema”

Maganganun innah suna ratsa ni kuma suna da matukar tasiri ga rayuwata, ko naji abinda ake min ya dameni idan na tuna da nasihohin da take min sai zuciyata tayi sanyi, sbd innah mace ce mai tawakkali da yarda da dukkan abinda ya sameta na rayuwa, sannan bata yarda taje ta fadawa yan uwanta halin da take ciki ba,  wani lokacin ko tambayarta suka yi dangane da matsalolin gidanmu bata fada musu sai dai kawai tayi murmushi waɗannan dabi’un nata su suka sanya dukkan makota suke sonta. Kintsa kaina nayi na sanya kayana dai-dai na talaka Kasancewar duk kayan nawa sun mutu don rabon da baba yayi min dinki har na manta sai dai makota su tausaya min su bani kwance, allona na dauka na fita tare da yiwa innah sallama.

A soro na ci karo da matan gidanmu sun saka faifan gulamata suna ta tattauna abinda ya faru jiya suna ganina suka kara bada himma wajen zagina kawai dan naji raina ya ɓaci, ban kula da su ba na ratsa ta cikinsu na wuce, daya daga cikinsu naji na cewa “aikin kenan kullum a ɗauki uban allo a tafi makaranta kamar gaske, Allah yasa dai ana ganewa” umma ce ta karbi zancen “ina fa ake ganewa a yi sha’ani dai wai na birni ya cuci na ƙauye, da ana ganewa a rika sata gashi ana so a lalata min yaro” 
Muryar A’isha kanwar salim naji “mu mun san inda ake xuwa ba wata makaranta ku ake rainawa hankali”
Ba karamin zafin kalmar da A’isha ta jefe ni da shi naji ba, wato kallon ma yar iska suke yi min

Gidan su Rukayya na wuce don biya mata makaranta sbd na saba kullum tare da ita muke tafiya, dukkan mutane sun saba ganinmu tare idan ma ban biya mata ba duk wanda ya ganni sai ya tambayi inda take. Rukayya kawata ce tun muna kanana, duk da cewa ta dan girme ni amma mun yi matukar shakuwa da juna babu wanda yake jin tsakanin mu, babu wani abu da nake iya boye mata ita ma kuma haka, lokuta da dama idan aka bata min rai wajenta nake xuwa ta kwantar min da hankali, mutanen gidan mu sun yi iya bakin kokari wajen ganin sun zuga mahaifiyarta a kan ta raba mu, amma taki karbar kudirin su saboda ba yabon kai ba ina da nutsuwa da kamun kai kuma ba ni da yawan surutu sannan ban fiye shiga abinda bai shafe ni ba, wannan dalilin yasa mutane suke sona kuma suke son abota da ni.
Saka kaina nayi cikin gidan tare da sallama ban tarar da kowa a tsakar gida ba don haka kai tsaye na wuce daki, a kan gado na tarar da Rukayya tana ƙarasa haddarta don haka ban yi mata magana ba har sai da ta kammala karatunta sannan ta kula ni. “Sa’adatu lafiya yau na ganki a haka da alama ma kamar kuka kika yi” yaƙe nayi kawai saboda bana son na sake maimaita maganar, kawar da tambayar da tayi min nayi da “ina umma ban ji motsin ta ba lafiya?” 
“Yau da sassafe ta fita an kwantar da yar kanwarta a asibiti shi yasa baki ganta ba”

“Ayya Allah ya bata lafiya” amsa min tayi da “ameen”
Sake jefo min tambayar dazu tayi “ki fada min abinda yake damunki Sa’adatu na sanki da zurfin ciki abu yana damunki baxa ki fada ba,kuma ga damuwa nan a idonki Ina gani, ki fada min komai kin san dai babu boye-boye a tsakanin mu”
Sai da ta yi min magiya sosai na fada mata sbd ban fiye son bude cikina ba musamman ma idan mutum baxai iya yi min maganin abinda yake damuna ba.
Kafin na fara faɗa mata har kwalla ta cika idona, rarrashina ta shiga yi har sai da hankalina ya kwanta na fada mata dukkan abinda ke faruwa da ni, tayi matuƙar tausaya min kasancewata yarinya mai kananun shekaru amma har na fara cin karo da matsalar masu yi min gorin aure, nasihohi tayi min tare da bani misalan da xasu kara min nutsuwa
Sai da ta gama
shiryawa sannan muka tafi makaranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *