TSANANI CHAPTER 16

TSANANI







CHAPTER 16




Cikin Wata irin rikicewa da d’imaucewa tare da rawar baki nake faɗin sunansa
“Izuddeen dina ashe baka manta da ni ba, dama ina da rabon yin tozali da kyakkyawar fuskar ka, gaskiya ka cika ɗan halak, ka cika masoyi na gaskiya, ban taba ganin mutum irinka ba wanda ya san girman mai son shi tsakani da Allah ba”

ina maganar ina murza idanuwana don na ƙara tabbatar wa da kaina shi ne ko kuma mafarki nake yi.
Idanuna ne suka fara zubar da hawaye.
Cikin Wata sassanyar murya yace
“ki ƙara so mana Sa’adatuna, kin dade da xama jinin jikina soyayyar ki da kaunar ki a xuciyata take, baxa ta taɓa gushewa ba, kuma baxan taɓa mantawa da ke ba har karshen rayuwata, kin so ni tun lokacin da ba ni da komai, kinga kuwa babu abinda xai sa na guje ki har abada”

Yana faɗin haka ya buɗe min hannayen sa cikin sassarfa na ƙarasa wajansa hannu yasa ya rungume ni ban san lokacin da wani irin kuka ya sake ‘kwace min ba.
Cikin sigar rarrashi yace
“Sorry my life ba kuka zaki yi ba, godewa Allah ya kamata kiyi da ya sake haɗa fuskokin mu a matsayin masoya kuma ma’aurata nan bada dadewa ba, ban taɓa tsammanin xan sake ganinki ba a rayuwata duk a xatona an rabu mu, sai kuma ga shi mahalicci sarkin jin kai ya sake haɗa fuskokin mu”

Nan ya shiga rarrashina cikin wani irin salo mai wuyar fassarawa.

Mu’allim yana gefe wani irin tuƙuƙin baƙin ciki yaji ya rufe shi, nan da nan yaji garin yana jujjuya masa, baƙin kishi ya turnuke zuciyar sa, wai Sa’adatunsa ce wacce ya bawa dukkan kauna da soyayyah ita ce a rungume jikin wani da namiji me hakan ke nufi? wane ne wannan da har ya fi shi matsayi? me yake takama da shi da har ya janye hankalinta da wuri??

Tafin da Ruqayyah tayi ne ya fara dawo wa da su hankalin su, ita ma tayi ne sbd yadda taga masoyan sun shagala da junansu sun manta da kowa a gurin.

Cikin matsananciyar kunya Sa’adatu ta fara zamewa daga jikin izuddeen, amma shi gogan naka yaƙi sakinta, cikin muryan da take ƙara dulmiyar da ita cikin kaunar sa taji yana cewa.

“Pls my life kada ki bari a ƙara raba mu a karo na biyu, baxan iya rayuwa babu ke ba idan aka kuma raba mu mutuwa xan yi”

Cikin shagwaba
na narkar da idanu nace masa.
“Pls my man ka cika ni haka baka ganin mutane sai kallon mu suke”

Matse min hannu yayi yana cewa “Ruqayyah ce bakuwata bana jin kunyar kowa indai a kanki ne”

Cike da shagwaba na sake maimaita masa.
“baka ganin akwai bako a wajen”
Da sauri ya cika ni a dai-dai lokacin Mu’allim ya d’ago kansa, da yake masa barazanar fashewa cike da mamaki, idanunsa sun yi jawur sbd baƙin kishin da ya addabi zuciyarsa.

“Wai yau shi Sa’adatu take kira da baƙo me hakan ke nufi”

Izuddeen ne ya katse masa tunanin da yake yi, yana tuhumar Ruqayyah wane irin baƙo Sa’adatu tayi da zata fito a haka da wannan kayan masu kyau a jikinta.

Ɗan turo baki nayi tare da cewa
“Ni fa ba kwalliya nayi ba malamina ne yazo ya duba ni sbd ba ni da lafiya”

Ruqayyah da ke gefena kallona tayi tana rufe baki, sbd dariyar da take shirin kwace mata, saurin cewa tayi.
“Eh malamin su ne yaxo dubata”Ok” izuddeen ya faɗa yana mi’kawa mu’allim hannu ba don ya san muhimmancin gaisuwa a musulunci ba, da bazai miƙa masa hannun su gaisa ba, wani kallo ya bi Sa’adatu da shi, wata muguwar tsanarta ce ta kama shi ji yake kamar ya kashe kansa sbd baƙin ciki.
Neman hanyar fita daga soran ya fara yi sbd xuciyarsa baxa ta iya jure kallon abinda ta gani ba yanxu.

Yana tafiya yana haɗa hanya sbd takaici, ji yake ya tsani duniya gaba ɗaya da kyar yake jan kafa a haka har yaje gida.

Cikin soron muka koma muka fara hirar mu ta masoya cike da farin ciki sai a lokacin na lura da mu’allim baya nan, ban wani damu zuciyata ba sbd na san dama ya xama dole yaji haushi, nima tasirin da soyyyar izuddeen tayi min ne yasa ni mantawa da kowa.

Har cikin gida ya shiga ya gaida Adda ita tayi mamakin ganinsa a wajena duk da arxiki mai yawa da ya samu bai sa ya manta da soyayyata ba, wrapper din yan dari biyar ya miƙa mata, sannan ya ƙara jaddada mata soyyyar da yake min ya faɗa mata nan bada dadewa ba yake sa ran aurena.

Sai da muka yi sallar magariba muka yi sallama, tare da Rukayya suka tafi ya sauketa a gidansu shi kuma ya wuce wajen Innah.

A soro suka ci karo da salim, cikin sakin fuska ya miƙa masa hannu suka gaisa, sa shi yayi ya kira masa innah, ba tare da bata lokaci ba ta fito.

Ita ma tayi matuƙar mamakin ganin izuddeen, da yadda Allah yayi masa arziki dare ɗaya, nan ma ya ƙara jaddada mata cewar yana son Sa’adatunsa kuma baxai dade ba xai aureta, kuɗaɗe masu yawa ya dakko ya bata.

A Hanyar fitar shi kofar gida ya haɗu da Baba cike da ladabi ya tsugunna ya gaida shi, da farko bai gane shi ba sai da ya sake haska shi da touch light, sai a nan yaga izuddeen ne, cikin sakin fuska yace.

“Tashi tashi ɗan nan, kaine yau a gidan namu”

Mamaki izuddeen yayi sbd irin karɓar da mahaifin Sa’adatu yayi masa.
Jan hannunsa yayi zuwa soro na biyu

“Ai bai kamata ka tsaya a nan ba ka shigo daga ciki kai ai ɗan gida ne, dakin Innah Salamatu yaje ya dakko masa shimfida tare da xaunar da shi a kanta”

Cike da ladabi ya sake gaida shi, a lokacin ya sake faɗa masa shi fa yana nan a kan bakansa na kaunar Sa’adatu.

Cikin sakin fuska mahaifin Sa’adatu ya dube shi.

“Ya za a yi kace kana son baxawara izuddeen ga yan mata nan kala-kala a gidan nan sai ka zaba ka darje, ka kyale wannan yarinyar ba yarinyar kirki bace yanzu haka ma na koreta daga gidana”

Shafa fuskarsa yayi
“Na riga na san komai Baba, Yanxu ma daga wajenta nake, duk na san ,wannan labarin idan da hali ni dai ina sonta a haka”

Ransa bai masa daɗi ba haka dai ya amsa masa da “shikenan tunda ka kafe a kan abinda kake so na kyale ka, amma Hausawa sun ce wanda yaƙi ji ba yaƙi gani ba”

Shi ma dubu ɗari ya bashi, nan da nan ya sake gigicewa kamar xai goya izuddeen sbd murna har bakin motar shi ya raka shi sannan ya dawo.

Jikinsa na rawa ya shiga dakin Innah Salamatu ya faɗa mata zuwan izuddeen da irin abin arzikin da yayi masa, nan fa baƙin cikinta ya motsa taji kamar ta mutu sbd haushi.

“Yanxu shi Wannan mayen sai da ya ƙara dawowa dole ne yana saurayi sai ya auri baxawara ga yan mata nan kala-kala yaxo ya zaba amma ya nacewa wannan guxumar, yarinyar nan ba haka ta kyale shi ba wlh asiri tayi masa, ya xama dole naje gidan su yaron nan na ƙara ankarar da su”

Da sauri mahaifin Sa’adatu ya dakatar da ita.
“Bana son mugun hali da sharri, kinga Allah xai rufawa yarinya asiri shi ne xaki je ki kashe mata aure, to wlh idan kika je a bakin naki auren”

Yana gama faɗa ya fita ya kyale ta.

Banda ciwo babu abinda zuciyarta ke yi sbd takaicin za a saketa.Kwance nake kan cinyar Adda tana min tsifa, ta lura da ni yau ina cikin farin ciki sosai, don gaba ɗaya bakina yaƙi rufuwa ina tuna yadda na kasance da izuddeen dina, da irin farin cikin da ya bani, ɗaga kaina nayi ina kallonta
“Adda kin san kuwa abinda nake tunani?”
Kallona tayi tare da bayar da hankalinta gare ni
“Sai kin faɗa Sa’adatu”

Gyara kwanciya nayi, cike da damuwa nace.
“Ban san ta inda xan fara miki ba Adda, xuciyata tana cikin damuwa sosai, kaina ya kulle na rasa me xan ce miki ki fahimci irin yadda nake ji a xuciyata, tunanin abinda xan faɗawa doctor nake yi, kin ga yana sona ya gama bani amanar xuciyarsa da soyyyar sa gare ni, yanxu da wane ido xan dube shi na faɗa masa cewa izuddeen ya dawo”

Mayar da numfashi tayi tare da ajiye kibiyar da ke hannunta.
“Wlh nima tunanin da nake yi kenan Sa’adatu tunda nake ban taɓa tunanin izuddeen xai dawo gare ki ba, duk a tunanina yayi miki nisa tunda Allah ya arxuta shi ya kai ga babban mataki ya xama wani a rayuwa, amma sai ya bani mamaki ya dawo, da na san haka xata faru da ban bari doctor yayi xurfi a sonki ba, ina tausayin ki Sa’adatu domin kin haɗawa kanki kulli mai wuyar warwarewa, ina fatan dai tun farkon haɗuwar ku kin bashi labarin rayuwar ki gaba ɗaya, don a nan ne kaɗai xai san da xaman izuddeen?”

Tashi nayi daga kwanciyar da nake
“Iya labarin malam Jibo kawai ya sani Adda”

Girgiza kai tayi
“Kin yi kuskure da kin sani kin faɗa masa, amma nasan baxa ki samu matsala da shi ba insha Allah, sbd doctor mutum ne mai fahimta da zurfin hankali, sai dai babu daɗi mutum ya rabu da abinda yake so”

Wayana naji yana ƙara, Adda ta sakar min kaina na shiga daki don amsa kiran, ɗan halak yaƙi ambato na faɗa tare da daga wayar, number doctor na gani.

Cikin siririyar murya nayi masa sallama.

Marairaice wa yayi
“Babyna shi ne yau ko ki kira mijinki ki ji ya ya kwana, kin san xuciyata bata iya jure rashin ki amma yau gaba ɗaya kin manta da ni”

Ajiyar xuciya na saki cike da marairaice wa nace
“Kayi hakuri doctorna, ba mantawa nayi da kai ba kuma kana raina nima tun daxu nake tunaninka, tunda naji shiru na san ka wuce asibiti, tunda jiya ka faɗa min kana da tarin aiyuka, bana so na kiraka ne na hana ka yin aikinka, amma xuciyata ta faɗa min kana cikin koshin lafiya”

Shafa fuskarsa yayi gami da mirgina kanshi gefe guda har ga Allah yana jin daɗin kalamanta, zuciyar shi tana faɗa masa yadda zai samu kulawa matuƙar ya mallake ta.

Cikin rikitacciyar muryar shi yace
“To babyna na gode kuma na gamsu da kalaman ki, idan shirya ki fito gani nan a kofar gida ina jiranki”

To nace tare da mi’kewa, daure gashina nayi na shiga gyara fuskata, hijabina na sanya sannan na fita.

Ina sako kaina kofar gida da fuskarsa na fara yin tozali, yana sakar min wani kasalallen murmushi, a da idan yayi min wannan murmushin ba ƙaramin narkar min da xuciyata yake yi ba, amma yau sai ban ji komai ba, a sanyaye na ƙarasa wajen shi.

Sannu da zuwa na masa d’ago fuskata yayi yana kallona, “

“Sa’adah ya nake ganin damuwa a cikin idanuwanki?? Ko yau ma nayi laifi ne na tsugunna na kama kunne na batawa sarauniya ranta”

” uhmm” nace ina gyara tsayuwata

“Ba komai ai kai autan maza ne baka laifi” na ƙarasa maganar ina kawar da fuskata.Nuna min hanya yayi
“Bisimillah mu shiga daga ciki babyna”
A hankali na ja kafa nayi gaba shi kuma ya biyo ni a baya.

Gaisawa muka ƙara yi, zaulayata ya fara yi.

“Ni fa kwanan nan wani kyau kike yi, tun kafin a fara maganar auren mu har kin fara kyallin amarci ko dai kin kosa ne?”

Narai-Narai nayi da ido kamar xan yi kuka. Ban iya bashi amsa ba sbd abinda ya tsaya min a wuyana.

Cike da tashin hankali ya sake dubana tare da sakkowa daga shimfidar da nayi masa.
“Me yake damun ki Sa’adatu ko wani abin aka yi miki, ki faɗa min damuwar ki ni mijinki ne, ni nafi cancanta nayi miki maganin matsalar ki”

Idanuwana ne suka ƙara ciccikowa na fara magana a hankali.
“Daman daman wata magana nake so mu yi ni da kai, amma ina so ka yiwa maganar kyakkyawar fahimta, dan Allah kada ta xama sanadin samun matsala ta da kai”

Cike da kulawa ta dube ni
“Ina jin ki Sa’adatu ki fadi komai ni naki ne Insha Allah baxa ki samu matsala da ni ba”

Saita nutsuwata nayi tare da sunkuyar da kaina sbd baxan iya hada ido da shi ba.

“Allah ya sani ina Kaunar ka kuma ina kwadayin kyawawan halayenka masu kyau, amma duk abinda zan faɗa maka ina so kai min kyakkyawar fahimta, kai mutum ne mai hakuri da kawaici tare ɗaukan kaddara mai kyau da mara kyau” nan na dora masa da tarihin rayuwar mu da izuddeen tun daga daga farko haɗuwar mu har ƙarshe.

Sake kallon shi nayi
“Dan Allah kayi hakuri ka bar masa ni ya aure ni, ya faɗa min idan ya rasa ni mutuwa xai yi”

Na ƙarasa maganar tare da zamowa daga kan kujerar da nake zaune, zuba gwiwoyina nayi a ƙasa ina d’aga masa hannu.

Kayi hakuri kada ka rika min kallon wacce ta yaudare ka, wlh ban yaudare ka ba doctorna, na ceci ran izuddeen ne sbd bak’ar wuyar da ya sha a kaina har kulle shi Babana yayi, idan ya rasa ni xai iya rasa rayuwarsa”

Kafin na karasa maganar kuka mai tsanani ya kama ni, duk maganar nan da nake idanunsa na kaina yana min kallo mai cike da tausayawa, sai da na samu nutsuwa na sake kallon sa.

“Ina neman alfarma a gurin ka dan Allah ka auri yar uwata Ruqayyah, zata xama sanyin idaniyarka, xata riƙe maka yayanka amana, zata baka kulawa fiye da ni, kayi min wannan alfarmar dan Allah
doctor, bana son mu yi asararka a cikin dangin mu don kai mutum ne na gari”

Hannayen sa ya saka ya d’ago ni daga durkusan da nayi, ya matso daf da ni numfashin sa na dukan fuskata, cikin wani salo ya fara min magana.

“Naji dukkan abinda kika fada min sa’ar mata, na kuma yarda da ke na san baxa ki yaudare ni ba, baxa ki cuce ni ba, kuma baxa kiyi abinda xaki wulakanta soyayyar da nayi miki ba, kin nuna min kauna kin so ni iya so, kin so abinda na haifa, yanzu ma na san lalura da kaddara ke neman raba ni da ke, amma ki sani har abada baxan iya cire soyayyar ki a xuciyata ba, sai dai xan yi hakuri na barki ki auri wanda kike so sbd ina sonki, soyayyar ki tasa ni son duk abinda kike so, ni mai ceton rai ne ba mai kashe rai ba, don haka na amince na yarda ki so izuddeen ko don mu ceto rayuwar shi daga halaka, sbd shi masoyinki ne na gaskiya ya can-canci ki so shi har karshen rayuwar ki, sbd ya nuna miki kauna tun lokacin da baki san kanki ba har zuwa yanxu bai manta da ke ba, na yarda har ga Allah ki aure shi”Ban san lokacin da wani farin ciki ya lullube ni ba, dubansa nayi ina murmushin farin ciki
“Na gode doctor gaskiya ka cika masoyi na gaskiya ka cika ɗan halak, ka amsa sunanka na namijin duniya, yadda ka tseratar da zuciyar wani daga halaka kaima Allah ya kula da kai, Allah ya duba bayanka”

Amsa min yayi da ameen, sake jefo min tambaya yayi.

“Amma kina nufin ita Rukayyan, ba tada wata matsala xata so ni, kuma ba tada wanda take so, sbd bana so na shiga tsakanin masoya?”

Ya faɗa tare da marairaicewa cikin wani salo mai ban tausayi.

A sanyaye nace
“Rukayya ba tada matsala yadda halina yake haka nata yake, shi yasa abotar mu tayi ‘karko har muka kawo wannan lokacin, sannan iyayenta sun fi nawa hali ta fini kyau ta fini ilimi, ina tabbatar da cewa ba tada kowa a halin yanzu don haka ka tsarkake xuciyarka ka faɗa son Rukayya Ina tabbatar maka da cewa baxa ka samu matsala ba”

Daga min hannu yayi tare da dakatar da ni
“Wannan ni duk ba damuwata bace Sa’adatu nafi buƙatar kyan hali fiye da kyan fuska, amma na san baxa ki min xaben tumun dare ba, Allah ya tabbatar mana da alkhairi”

Amsawa nayi da ameen

Sake duba na yayi
“Kin faɗawa Rukayya wannan tunani da kika yi?”

A sanyaye nace
“Ban faɗa mata ba ina so dama naji ta bakinka ne kafin nayi mata magana, na san baxa tayi min musu ba”

Murmushin ƙarfin hali yayi
“To shikenan bani numberta yau xamu yi magana kuma baxan baki kunya ba Sa’adatu”

A hankali na fara laluben number Rukayya na bashi, cike da girmamawa muka yi sallama ya tafi.

A hankali ya yi wa motar shi key ya bar kofar gidansu. Jikinsa na rawa yake driving din ya rasa me ke yi masa daɗi a duniya, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un kawai yake nanata wa a fili, tare da addu’ar Allah ya bashi nutsuwa da juriya a kan wannan babbar jarrabawar da ya shiga.
Yana xuwa gidansa yayi parking fitowa yayi, masu yi masa hidima sai sannu da zuwa suke masa amma ya share su sbd baya cikin hayyacinsa. Banɗaki ya shiga ya sakarwa kansa ruwa sai da ya fara dai-daita nutsuwar sa sannan ya daura alwala ya fito.

Sallah yayi raka’a biyu ta neman zabin Allah tare da addu’ar Allah yasa zabin da Sa’adatunsa tayi masa ya xama alkhairi a rayuwarsa, don yasan baxa ta bashi abu mara kyau ba.

Tabbas yaji xafi da ciwon rabuwa da ita, amma babu yadda zai yi izuddeen ya fi shi cancanta da ya auri Sa’adatu, kuma a yadda alamu suka nuna xai riketa tsakani da Allah, tunda gashi ya yi kuɗi amma bai manta da ita ba, kuma shi ne wanda ya fara sonta tun farko, idan har ya raba su bai yi musu adalci ba.

Tashi yayi ya kwanta a kan gado yana ta juyi yana tuna irin madarar soyayyar da ya kwasa a wajen Sa’adatu, amma yau mai rabawa ta raba su, rintse idonsa yayi tare da matse pillow a kirjinsa. Yana ta ambaton Allah.Ko da na koma gida sai da na faɗawa Adda yadda muka yi da doctor, tayi farin ciki sosai da karɓar Rukayya da yayi, ita kanta sai da ta jinina masa sbd namijin ƙoƙarin da yayi wajen karɓar ƙaddara, komawa daki nayi na cire hijabin da ke jikina, mayar da kallona nayi ga Hanan da ke faman sharar bacci bisa katifata, tausayin yarinyar ne ya kama ni, na so a ce ni xan maye mata gurbin mahaifiyarta amma ƙaddara ta riga fata, matsawa nayi ina cigaba da kallonta tare da sumbatar goshinta, har cikin zuciyata ina jin kaunar Hanan naso a ce a kafaduna xata cigaba da kasancewa.

Yau tsabar tashin hankali doctor ya mance da yar diyar tasa gaba ɗaya, don ko tambayar lafiyata bai yi ba.

Tsakar gida na fito don na sha iska kasancewar yau ana xafi, sallamar yaro naji a hankalina na d’ago ina kallon shi.

A ladabce yace
“Wai ina Sa’adatu?”
Gaba ɗaya na bayar da hankalina gare shi, tare da cewa “gani”

Wata takarda ya miko min
“Wani ne a kofar gida yace na kawo miki”
Gabana ne ya fadi sbd ina jin tsoro ko malam Jibo ne ya aiko shi, da har na yanke shawarar baxan karba ba, sai kuma na miƙa masa hannu ya bani.
Cikin kosawa da ganin abinda ke jikin takardar na shiga budewa don ganin abinda ke ciki, sunan mu’allim na gani a zane jikin takardar.

A kasalance nace
“Na gode kace ina gaida shi”
Tsintar kaina nayi cikin fargaba da tashin hankali, nasan tabbas ba abin arxiki mu’allim ya rubuta min ba, muddin na karanta wasikar ba lallai ne na iya bacci ba.

Tashi nayi na shiga daki, sai da na dai-daita a kan katifata sannan na fara buɗewa.

*_Assalamu alaikum masoyiyata a da amma kuma sanadin kukana a yanxu, na shiga d’inbin damuwa tun bayan rabuwata da ke, amma ke na san ba haka abin yake ba a cikin zuciyar ki, tunda masu kuɗi sun hure miki kunne har sun kai ga raba ki da masoyinki na gaskiya, tun bayan da kika kyale ni kika sa na shiga zargin kaina ko ina da wani mugun hali ne da har ya sanya ki guduna. Dan Allah ki taimake ni kada ki sa zuciyata ta koma kallon so a matsayin wani abu mara daraja, abin gujewa da rashin can-canta ga rayuwa ta zahiri. linzamin farin-cikina na a hannuwanki a halin yanzu. Ina son ki, kuma xan cigaba da sonki har abada duk da cewa ke kin guje ni, amma ko kaɗan ban ji tsanar ki a xuciyata ba, ina miki fatan alkhairi ke da sabon mijinki Allah ya bar ku tare, nima ina so ki ci-gaba da taya ni addu’a Allah ya zaba min mace ta gari, wacce baxa ta guje ni ba a daidai lokacin da nake da tsananin bukatar ta_*

*_Bissalam_*

Ban san lokacin da na kwanta ba tausayin mu’allim ya kama ni, tabbas ina son shi amma ba kamar yadda nake son izuddeen ba shi ma kanshi ya sani, amma halin da na jefa shi ne babban abinda yake damuna a yanzu.

Haka na kwana cikin damuwa, wayar da muka kwana muna yi da izuddeen ne ya ɗebe min kewa.

***********

Kwance nake kan sallayata ina karatun Alkur’ani tare da addu’ar Allah ya tabbatar mana da alkhairi tare da zaman lafiya a aurena da izuddeen, ‘karar da wayata tayi ne yasa ni saurin kai hannuna wajen dakko ta, murmushi na sauke a kan wayar saboda ganin sunan masoyina a jikin screen din.

A hankali na d’aga tare da karata a kunnena.
“Barka da asuba my man”

Ɗan murmushi yayi tare da tashi daga kwanciyar da yayi.
“Barkanki mu wife, Ina fatan kin tashi lafiya kuma babu abinda yake damunki”

Kara saita wayar nayi cikin shagwaba nace.
“Babu abinda ke damuna illa rashinka”

Ɗan siririn murmushi ya saki “Indai ni ne yanzu ma sai nazo wajenki, kin san burin kowane masoyi ne ganin murmushi a fuskar wadda yake kauna, ko da a ce wani ya saka ki cikin damuwa, ni kuma zan yi iya kokarina wajen bayyanar da murmushi a saman fuskarki”

Murmushin farin ciki nayi
“Ina godia my man, wannan kalma na dade ina jinta a wajenka, kuma na amince da ita ɗari bisa ɗari”

Ƙasa yayi da murya cikin sigar rad’a yace.
“Da gaske my wife?”

Cikin wani salo nace.
“Kwarai kuwa, shi yasa na baka sarautar xuciyata domin ka shimfida mulki a cikinta yadda kake so, a kullum burina ka zamo nawa, ta yadda zamu kasance tare tamkar jini da tsoka. kaine jarumi guda ɗaya tilo da zuciyata ta aminta da shi. Ina son ka, fiye da yadda nake son kaina”

Cikin tsantsar farin ciki ya saki wani mutum
“Yanzu wannan matsayin duk ni kaɗai Sa’adatu?”

Kamar yana ganina na girgixa kai alamar eh.

Cikin sigar rarrashi ya fara min Magana.
“Kiyi hakuri Sa’adatu yau baxan samu zuwa ba kamar yadda nayi miki alƙawari, sbd xan je na gano ginin gidan mu inda xamu shimfida rayuwa da soyayya mai kyau tare da ke da yayanmu”

A shagwabe nace
“Ni Allah nafi buƙatar ganinka, kawai kaxo idan ba haka ba kuma nayi fushi da kai”

Rarrashina ya shiga yi har sai da na hakura ya tafi ganin ginin namu.

Da misalin ƙarfe hudu na yamma na shirya tare da tambayar Adda don xuwa waje Rukayya, kama hanyar tafiya gidan su nayi, hannuna janye da Hanan.

Sallama nayi muka shiga cikin dakin su cikin farin ciki ta karɓe mu tambayarta nayi ina ummansu sanar min da tayi bata nan taje unguwa.

Abinci ta zubo mana muna cikin ci ta dube ni.
“Tunda izuddeen ya dawo wani kyau kike yi wato hankali ya kwanta ko?”
Ta ƙarasa maganar tana murmushi tare da ajiye cokalin abincin.

Cike da zaulaya nace
“Ke kuwa ba dole na canja ba mai bani farin ciki ya dawo”

Miko min hannu tayi muka tafa, sai a lokacin idanunta suka kai kan Hanan.

“Wannan babyn kuma a ina kika samo ta na dai san ba yar Adda bace, don ba tada yarinya kamar wannan”

Rausayar da kaina nayi
“Yar ki ce fa, ina fatan ma rainon yarinyar nan da kulawarta su dawo hannunki idan kika auri mahaifinta”

Cikin rashin fahimtar abinda nake nufi ta dube ni.
“Ban fahimce ki ba Sa’adatu, me kike nufi da hakan?

Nan na bata labarin nagartar doctor, da kyawun halinsa da irin yadda ya kula da ni tun xuwana asibitinsa.

Mayar da ajiyar zuciya tayi.
“Na gode Sa’adatu na san baxa ki haɗa ni da mutumin da kika san ba shi da nagarta ba, amma kina ganin zai karbi soyayyata?”

Girgiza kai nayi
“Kwarai kuwa don shi ne ma ya nemi na samo masa macen aure da kaina, na faɗa masa nagartar ki kuma ya yaba da komai naki, kada ki damu ke dai kiyi addu’a kawai kawata, Allah ya tabbatar da alkhairi”

Da ameen ta amsa min, hira muka cigaba da yi muna maganar ne doctor ya kirata, da zaulayarta ya fara har sai da ta saki jiki da shi suka fara sabawa, ita kanta ta yaba da halin shi da yadda yake da saukin kai da barkwanci, a lokacin take fada masa muna tare, karbar wayar yayi muka yi magana inda ya faɗa min yau da daddare xai xo ya dauki Hanan.Da ummansu ta dawo muka faɗa mata halin da ake ciki, ita ma tayi farin ciki sosai tare da addu’ar Allah ya dai-daita su.

Sai wajen isha muka koma gida, a kofar gida naci karo da shi har yaxo yana jirana, gaisawa muka yi sannan na shiga gida na dakko masa kayanta, da abubuwan da Adda ta bata.

Da kyar muka rabu da yarinyar muna ta kukan shakuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *