TSANANI
CHAPTER 19
Cikin gida na shige tare da ajiye ledar da ya bani a gaban Adda, buɗewa tayi muka fara duba invitation card din don ganin ranakun da xa a gabatar da bikin namu, daurin aure ne a farko wanda ya kama za a yi ranar juma’a a babban masallacin juma’a na unguwar mu, sai dinner daga baya kuma sauran shirye-shirye suka biyo baya, yinin Innah ne a ƙarshe.
Ware invitation din ta shiga yi, ta ware nata da na innah, tare da miko min na kawayena, miƙa mata nayi ta rage kasancewar ba ni da wasu kawaye na a zo a gani, sai dai ban sani ba ko Rukayya xata gayyato nata kawayen, naira dubu ɗari izuddeen ya bani, nayi abubuwan walimata gaba ɗaya na dam’kawa Adda kuɗaɗen.
***********
A ɓangaren Innah Salamatu kuwa tuni ta gama rud’ewa, hankalinta gaba ɗaya baya jikinta ganin lokacin bikin Sa’adatu na ta matsowa ita babu labarin na ƴaƴanta, wajen salele ta koma yau a soron gidansa ta tarar da shi ya shimfida tabarma yana fito da hotunan yan matan da suka bashi ya samo musu mijin aure. Sallamar da tayi ne ya dawo dashi hankalin shi.
Da farin ciki ya karbeta gami da bata gurin da xata xauna.
Cike da damuwa ta dube shi.
“Salele har yanzu naji shiru babu wani labari lafiya dai ko”?
Murmushi yayi gami da kallonta
“Akwai labari mana Hajiya salamatu, tunda gashi Alhaji yau yace xai zo yaga A’isha da fatan dai kun shirya, kin san shi yana zuwa sai magana baya jira shi haka halinsa yake baya yin abu da wasa”
Murmushi tayi
“Ni kuwa na shirya salele, ni da na matsu na kawar da su, ji nake kamar yaran nan gaba ɗaya a kaina suke, bana samun nutsuwa idan na gansu a gabana,. musamman ma zaliha yanzu da ta tsiri fitina kullum ba tada aiki banda yawon shakatawa ita da samari, na kosa na kawar da ita kada ta dakko min magana, ita ma da xaka taimaka ai da ka samo mata ko tsoho ne a samu dai a rufawa juna asiri”
Gyara xama yayi ai wannan ba matsala bace, tunda kina da ni a hannu, fatana dai ki cika min aljihu da kuɗi, yadda xan rika tuntubar manyan mutane don a samo mata mai dan tsoka”
Murmushi tayi
“Ni ba nida matsala indai a bayar da kuɗi ne, ga wannan ka karba kafin buƙatar mu ta biya”
Yau ma naira dubu biyu ta bashi tare da yi mata alƙawarin a yau ɗin nan Alhaji yawale xai zo a gama komai a wuce wajen.
Da rawar jiki ta tafi gida tana zuwa ta faɗawa ƴaƴanta halin da ake ciki, ba ƙaramin murna zaliha tayi ba, ita kuwa A’isha haushi ne ya cika ta sbd yanzu babu namijin da take so sama da malam Jibo, kawai don an fi ƙarfin ta ne shi yasa ta hakura, share tsakar gida innah ta shiga yi tana sharar tana wa’ka tare da yi wa innar Sa’adatu habaici, ita dai tana d’aki bata tanka musu ba sbd tasan ba komai ke damun su ba sama da ciwon hassada.
Karfe hudu dai-dai Alhaji yawale ya iso kofar gidan su, tare yake da salele shi ke rike masa jaka, ya sha shadda kamar gaske, a hankali yake taku d’ai-d’ai har ya iso soron, a tsaye ya tsaya yana karewa gidan kallo gaba ɗaya gidan bai masa ba don ba sosai yake son haɗa harka da talaka ba, cike da iyayi A’isha ta fito tana juyi ita a dole ta samu saurayi mai kuɗi..
gaishe shi tayi cike da izza ya amsa, dama shi haka dabi’ar sa take, akwai jin kai da girman kai musamman ga talaka, duk iyayin da tayi bata burge shi ba, haka nan dai suka yi hirar ba yabo ba fallasa, sai tayi magana goma da kyar zai bata amsa ɗaya. umartar yawale yayi ya duba bayan motarsa ya dakko masa lemukan da ya kawo mata, da rawar jiki tasa hannu ta karba, kallonta yayi yana wata irin dariyar mugunta, cikin zuciyarsa yace
“Ki karbi wannan iya rabon ki kenan, kwadayayyar banxa kina shigowa hannuna kin gama shan irin wannan don ya san kwadayi ne yasa ta aure shi, tunda duk garin nan babu wanda bai san halinsa ba da auri sakin da yake yi, sake murmusawa yayi wannan shi ne lemo na ƙarshe da zaki sha indai daga hannuna zai fito.
A gadarance yasa ta kira masa innarta, tana zuwa ta tsugunna kamar xata yi masa sujjada, shi kuwa yana tsaye a kanta babu girmamawa yake mata magana.
“Gobe nake so na aiko da komai na aure idan kun shirya” cikin rawar jiki tace
“A shirye nake mana Alhaji”
Shafa gemunsa yayi
“Shikenan haka nake son ji, gobe xa a kawo kayan lefe da kuɗin aure gaba ɗaya, amma fa ni ba karya xan yi ba, xan yi komai dai-dai ruwa dai-dai kurji, ba a harkar karya da ni”
Ya ƙarasa yana mata wani kallo, sam A’isha bata yi masa ba, idan yaxo neman aure yana kashewa mace kudi don ya mallaketa, amma wannan baya jin xai iya dukan jikinsa da d’anyen kara yayi mata hidima kamar yadda yake yi wa sauran matansa.
Duniyar tunani Innah Salamatu ta shiga.
“Yanzu abinda mutumin nan xai min kenan, amma bari na amince ban sani ba ko irin abun su ne na masu hannu da shuni, watakila mamaki xai bani shi yasa bai bayyana min abinda xai mata ba”
Katse mata tunani yayi da
“Kin amince”
Da sauri tace
“Sosai ma kuwa Alhaji ai mu albarkar muke nema”
Haka ya karkad’e rigarsa ya tafi ba tare da ya bata ko sisi ba banda wannan lemo katan biyu da ya kawo, ita kanta abin yayi matuƙar bata mamaki.
A tsakar gida suka ajiye lemukan, kowane d’aki sai da suka kai, amma banda na innah sai murna suke yi suna habaici wai A’isha ta samu miji mai arziki, Babansu yana dawowa aka faɗa masa, shi dai Allah ya sanya alkhairi yace, yayi ƙoƙarin ya nuna mata muhimmacin bincike kafin aure amma ta nuna ‘kin amincewa dole ya kyaleta ba don ya so ba.
Washe gari da safe aka yi sallama da shi wai an zo kawo kayan lefen A’isha, gaba ɗaya ya manta da xancen sbd bai ɗauki maganar da muhimmanci ba, makocinsa ya kira suka xauna tare suka karbi kayan.
Dubu hamsin ya biya na aure, sai akwatuna biyar da yayi mata, kana ganinsu xaka san tsofaffi ne duk sun ji jiki sun goge sun lalace, ‘yan kayan ciki kuwa babu tsiya babu arxiki, bra ma guda biyar kaɗai ya sako sai pant rabin dozen, atamfa kuwa ba a magana don duk kusan a leda ne, less da material kuwa ba a zancen su, don ko daya bai sako ba, shi dai tunda yake karbar kayan lefe bai taɓa karbar irin wannan ba, haka dai ya karba aka yi addu’a aka sanya biki dai-dai da ranar Sa’adatu sannan suka tashi suka tafi.
Innah Salamatu ta kame a daki tana jiran a kawo mata lefe ta gani, tunda aka fara shigowa da shi ta makale tana gud’a gami da yiwa yarta kirari wai yarinya tayi goshi, gadan-gadan aka yo dakinta da kayan a firgice ta buɗe ido tana salati gumi kuwa yanko mata yake yi ko ta ina, da sauri ta dubi baban Sa’adatu tace.
“Shi kuwa wannan mutum an yi matsiyaci ya rasa mai zai kawo mana sai waɗannan yan iskan kayan kamar mun roƙe shi dole”
Kallonta yayi ya tabe baki
“Ke dai kika gayyato shi, ba ni nace yaxo ya auri yarki ba don haka ba ruwana ku kare lafiya”
Yana gama faɗa ya juya ya kyaleta, jiki a sanyaye ta riƙa shiga da kayan d’akinta, cike da takaici ta riƙa budewa babu wani abin arxiki a ciki sai tarin tsiya, babu wanda ta iya nunawa kayan a gidan sbd kada a yi mata dariya.
Shiryawa tayi ta nufi wajen yawale, a fusace take tafiya kamar xata tashi sama.
Da sauri ta kama hanyar xuwa gidan salele sai dai cikin rashin sa’a bata tarar da shi ba baya nan, don haka ta barwa matarsa sallahun cewa yana dawo wa yaje gida ya sameta, hankali a tashe ta kama hanyar gidanta.
Tarar da zaliha tayi ta baje kayan a tsakar gida ana ta kallo, ranta bai mata dad’i ba ta shige daki tana sa’ka irin cin mutuncin da xata yi mata tunda ta tona mata asirin da take rufewa.
Waya ta ɗauka ta kira salele take shaida masa yaje ya faɗawa Alhaji ta fasa bashi auren A’isha tunda tsiyar da yayi mata kenan bushewa yayi da dariya.
“Lallai kina so ki taro faɗan da ya fi karfinki Hajiya Salamatu ai yanxu idan
Kika ce a fasa auren nan, jefa kanki xaki yi cikin matsala na san halin Alhaji sarai, cewa xai yi sai kin biya shi dukkan abinda ya kashe, kinga dai ba wasu kuidade masu yawa ya kashe ba, abinda ya kashe muku gaba ɗaya baxa su wuce dubu dari ba, amma xaki ji sharrin da zai miki don haka ki rufawa kanki asiri ki bar wannan maganar.”
Shiru tayi tana saurarensa.
“Mafita ɗaya ce ki hakura a yi ina tunanin gwada ta yake yi amma xai sakar mata kuɗi xuwa nan gaba, sbd duk garin nan an san Alhaji mai bautawa iyalansa ne, kika sani ko sanadin xuwanki umara ne yayi”
sauke ajiyar xuciya tayi
Ita dai xuciyarta bata yarda da maganar salele ba, amma ba tada wani zaɓi dole ta bari a yi auren ta huta.
Kusan kullum Alhaji yana kan hanyar xuwa xance kullum akwai abinda xai ce a girka masa kuma haka nan zai karkad’e rigarsa ya tashi ya tafi, ba tare da ya bada ko sisi ba, hakan ba ƙaramin batawa Innah Salamatu rai yake ba sbd ta gama kwallafa rai a kansa xata samu kuɗi, ga lokacin biki na ta matsowa har yanzu bai nuna gurin da xata xauna ba, ga shi har an fara yi wa Sa’adatu jere ita kuwa bata san matsayin da diyarta ke ciki ba.
********
A kullum lokacin biki ƙara matsowa yake, yau ya rage saura kwana uku daurin aurena da izuddeen tunda dama shi ne abu na farko da xa a fara, duk wanda ya kamata a gayyata mun gayyato shi, har gida aka kira mai ƙunshi tayi min ni da kawayena, komai na al’amarin bikin mu na tafiya cikin nasara babu wata matsala, gudunmawa kuwa tun daga kan yan uwa da abokan arziki babu wanda bai yi rawar gani ba, dukan su sun yi iya bakin kokarin su a kaina.
Yan uwa daga sassa daban-daban duk sun zo wasu a gidan Innah suka sauka wasu kuma muna tare da su a gidan Adda ko ta ina an nuna min gata.
A tsakanin wannan kwanakin izuddeen ya samu aka bar shi ya taho daga wajen aikinsa, tare da abokansa guda biyu ya taho ragowar kuma sai ana i gobe daurin aure xasu taho.
Yau a gidan mu ya fara tsayawa sbd mun yi magana da shi ina buƙatar ya kawo min lemon walima, ina ganin kiran wayar shi na tashi, hannun Rukayya naja muka fita tare da ita.
A kofar gida muka tarar da shi tare da abokan sa sun jingina jikinsu da motar da suka zo da ita, shi kuma izuddeen na tsakiya yana bi na da mayataccen kallon da ya saba bi na da shi, yau ya ƙara kyau sai dai ya ɗan rame kaɗan wanda ban san dalilin ramewar tasa ba.
Zuba min ido yayi kamar bai taɓa ganina ba har ina ƙoƙarin yin tuntube.
Kaina a sunkuye har na ƙarasa wajen da suke tsaye, gaisawa muka yi da su, cikin barkwanci suka yi magana.
“Gaskiya izuddeen ka iya zaɓe ka dace da kyakkyawar amarya, to kada fa ku kwashe kyawawan kafin mu zo namu auren” suka faɗa tare da kallon idanunshi suna dariya, saurin sunkuyar da kaina nayi sbd na lura su ma yan yi ne.
Har yanzu idon izuddeen na kaina, lumshe kyawawan Idanunsa yayi gami da yin tasbihi tsarki ya tabbata ga Allah, a hankali cike da sanda ya ƙaraso inda nake.
Cikin kasalalliyar murya yace
“Sa’ar mata kinga haɗuwar da kika yi kuwa, ko dai nasa a matso da lokacin daurin auren nan ne ya dawo yau, gaba ɗaya kin kwance min tunanina”
Ya faɗa tare da lumshe idonsa, ɗaya daga cikin abokan nasa ne ya dafa kafadunsa.
“Haba malam saurin me kake yi, me kake ci na baka na zuba ne mutumina yau fa saura kwana uku kamar yanzu ne xaka ga lokaci yayi, wata shekarar kuma mu zo suna”
Ya faɗa tare da kanne idonshi yana dubansa.
Murmushi izuddeen yayi
“Ai ka san xan iya, namiji kamata ka san xai yi abinda yafi haka ma, don ma ba a haihuwa a wata ɗaya ne da sai nace wani watan xaku zo suna”
Daga ni har Rukayya kunyace ta kama mu, muka rasa inda xamu sa kanmu su kuwa maganar su suke yi ba kunya, na kosa ya bani sakona na wuce gida don kunnena baxai juri sauraren wadannan maganganun nasu ba.
Mayar da kallon shi yayi gare ni
“Amarya kinga mara kunyar angonki ko, sai kin yi hakuri da shi?’
Ya faɗa tare da kallon izuddeen
Harar shi yayi, cike da xaulaya uace
“To ina ruwanka ni gara ma ina da wacce xan yiwa rashin kunyar kai kuwa fa?”
Murmushi yayi
“To ai nima kamar yau ne xaka ga na samo tawa, ka sani ma ko a wajen Bikinku xan haɗu da rabona”
gaba ɗaya muka kwashe da dariya, sake kallona yayi.
“Yauwa akwai abinda xan faɗa miki amarya, kinga tunda lokacin bikin nan ya taho gaba ɗaya ya daina ci ya daina sha, sai dai kawai ya sha fresh yo, Amma duk faman da xamu yi da shi a kan yaci abinci baxai ci ba”
Wani kallo izuddeen yayi masa.
“Kai dadina da kai gulma baka gani kayi shiru”
Dage gira yayi
“Indai wannan ce gulma nayi, dole na faɗa mata gaskiya, dama nace sai na faɗa”
Rausayar da kai nayi kamar xan yi kuka
“Haka kake yi ko babyna?”
Na fadi maganar cikin sigar shagwaba
Kwantar da kanshi yayi jikin motar da yake tsaye, yana kallon fuskata.
“Ba haka bane babyna tunaninki ke hana ni ci abinci, idan na tuna da ke sai kawai naji na koshi”
Gaba ɗaya abokan nasa suka sa dariya tare da dukan kafadarsa.
“Sannu Romeo to ai ko shi baban soyayyar yana cin abinci”
Kallon su yayi kawai bai iya mayar musu da martani ba
Sake duban shi nayi, cikin siririyar muryata da ke ƙara narkar da zuciyar izuddeen nace.
“Ni dai ka taimake ni ka riƙa cin abinci ko so kake yi ina xuwa na fara da jinya”
Girgiza min kai yayi alamar a’a
Mun dade muna barkwanci da su, da suka tashi tafiya suka ajiye mana lemuka masu yawa, tare da faɗa mana duk abinda muke buƙata xamu iya kiransu su kawo mana.
Rana bata ‘karya sai dai uwar d’iya taji kunya, duk abinda aka sakawa rana tabbas sai yazo duk daren dad’ewa a yau juma’a 3/4/2020 ya kama ranar d’aurin aurena tare da yar uwata A’isha, wanda aka d’aura a babban masallacin juma’a na unguwa uku da misalin karfe biyu na rana a kan sadaki dubu ɗari, ita kuma A’isha Alhaji yawale ya bata sadakin dubu ɗari biyu da hamsin, murna a wajen Innah Salamatu bata misaltuwa a lokacin take ƙara tabbatar da maganar salele na cewa Alhaji yawale mai kuɗi ne, karya ce kawai bai son yayi musu.
Tun safiyar ranar aka ci-gaba da gyara ni gami da sanya min turaruka masu matuƙar daɗi, komai nawa turare ne, duk abinda na taɓa sai yayi kamshi sbd gyaran da aka yi min ba na wasa bane, sanye nake cikin wani farin less mai matuƙar tsada, kayan da nayi ado da su duk masu launin gold ne tun daga kan sarka har zuwa takalmin da na sanya, duk wanda ya ganni sai ya yaba kyawun da nayi, a gida na zauna tare da kawayena har zuwa lokacin da aka dawo daga d’aurin auren, mutane ne cike da gidan suna taya ni murna, ita ma Innah tana gidanmu tare da nata jama’ar.
Da misalin ƙarfe uku izuddeen ya iso tare da abokansa, yayi matuƙar kyau tsadaddiyar farar shadda ya sanya, dinkin ya karbi jikin shi, kana ganin shi ba sai an ce maka ango bane, sbd yadda yake barin kamshi na hadaddun turaruka, bayan mun yi hotuna mun gama, ya kira ni a waya yana jirana a bakin motar shi, sauran abokansa kuma tuni yace su wuce su tafi zai taho daga baya.
A hankali nake takawa cikin nutsuwa har na isa wajensa, a tsaye na tarar da shi ya harde hannun shi a kirjin shi, ya xubawa hanyar da nake taho wa ido, a kunyace na ƙarasa wajensa tare da yin sallama.
Lumshe idanunshi yayi tare da buɗe murfin motar shi “shigo yau a ciki nake so mu yi magana”
Ma’kale kafad’a nayi
“Allah a’a mu yi maganar mu a nan ya fi sauki”
‘Dage kafad’a yayi
“Shikenan tunda baki ji maganata ba nima baxan fasa yin abinda nayi niyya ba”
Tsayawa nayi ina fuskantar shi
Cikin sigar shagwaba nace
“Ya na ganka kai kaɗai ina ragowar abokan naka suke?”
Gyara tsayuwa yayi yana murmushi
“Na kyalesu su d’an huta ne kin san har yanxu akwai gajiyar tafiya a tare da su”
Matsowa yayi daf da ni, yana lumshe idanunshi da sauri ya kai hannu ya rungume ni, duk yadda nayi ƙoƙarin na kwace sai na kasa sbd irin rikon da yayi min, wani irin nunfashi yake sauke wa mai cike da rikitarwa, cikin rad’a yace
“ya za a yi naxo da wasu wajen matata, alhalin ina so mu yi ganawa ta musamman da ita”
Da sauri na d’ago baki xan masa magana kafin nace wani abu, ya haɗa bakina da nashi yana kissing dina cikin wani salo mai wuyar fassarawa.
A hankali nake ƙoƙarin zame jikina daga nashi, ƙara riko ni yayi sosai yana aika min da wasu sakonni, ajiyar zuciya ya sauke gami da haɗa goshina da nashi, kallona yayi yana sakin wani murmushi.
“Kin yi matuƙar kyau amaryata, kullum kyawun ki ƙara bayyana yake yi, kinga abinda nake faɗa miki ko Sa’adatu ina matukar bukatar ki a kusa da ni baxan iya jure rashinki a tare da ni ba, naji daɗi da yau ta kasance ranar da kika xama mallakina da ban san yadda xan yi da rayuwata ba”
A kasalance na buɗe baki nace
“Kayi hakuri ka kyale ni, kaga a gida muke kada kayi abinda bai kamata ba”
Lumshe idanunshi yayi wanda suka canja suka koma kamar na mai jin bacci, babu komai a cikinsu sai tarin kaunata da soyayyata, a hankali ya sake ni tare da mayar da wani wahalallen numfashi.
“Shikenan na hakura amma akwai lokacin da ko kin bani hakuri baxan ji ki ba, ni kaɗai na san irin hakurin da nake yi da kuma irin yadda nake jin ki a cikin raina”
Komawa yayi gefe ya tsaya yana mayar da numfashi, ni kuwa ji nayi kamar kafafunsa baxa su dauke ni ba sbd halin da na tsinci kaina, komawa kusa da shi nayi na lafe kamar wacce za a kama, babu abinda ke raina banda fargaba.
A hankali ya sake takowa ya dawo kusa da ni, hannuna ya rike.
“Me yasa xaki matsa daga gare ni my wife, yau naga wani tsorona kike ji sai kace an faɗa miki ni ɗin dodo ne” ya faɗa cikin sigar tsokana.
Tabe baki nayi cike da shagwaba nace
“Wai me ma kaxo yi ne yanzu, tunda an baka ni ba sai ka hakura a kawo ni gidanka ba indai nice har sai ka gaji da ganina”
Hannun shi ya ɗora kan lips din shi alamar nayi shiru
“Shhhhh kada na sake jin kince xan gaji da ke, har abada baxan taɓa gajiya da kasancewa da ke ba, ke jinin jikina ce”
Girgiza masa kai nayi alamar baxan sake ba
Kwanto dani yayi na faɗa kirjin shi cikin kunnena yake faɗa min.
“Naji kina tambayar me naxo yi wajen ki ko?”
Da sauri na d’ago ido tare da cewa “eh”
Murmushi yayi tare da shafa gefen fuskata
“Kina so na nuna miki abinda naxo yi din ne”
Ya faɗa tare da riƙe hannuna sosai ta yadda baxan iya kwacewa ba.
Kamar idanuna xasu kawo hawaye, cikin rawar murya nace
“A’a”
Siririyar dariya ya saki
“Dadina da ke tsoro ban san me yasa kike tsoron mijinki ba”
Ni dai shiru nayi masa ban iya cewa da shi komai ba, ina jin shi yana ta xuba rashin kunyar shi ban tanka masa ba.
Motar shi ya buɗe ya fito min da wata leda.
“Karbi wannan naki ne ya kamata na fara ciyar da matata tun yanzu, don na san hayaniyar mutane bata bari kin ci abinci ba”
Lagwabar da kafada nayi
“A’a ka bar shi ni a koshe nake”
Tsuke fuska yayi babu alamar wasa a fuskar shi
“Ki karba ko kuma yanxu nayi abinda bakya so”
Da sauri nasa hannu na karba sbd na san wannan kankani ne a cikin aikinsa..
Bai tafi ba har sai da aka kusa kiran sallar la’asar.
Ina komawa gida dakin Adda na faɗa tana ganina ta hau ni da faɗa, wai tun daxu ake nemana naxo na shirya mu tafi wajen waleema bata ganni ba, da yake ba a gidan za a yi ba.
Ɗan turo baƙi nayi cike da shagwaba nace
“Ina wajen mijina fa Adda”
Kallon mamaki ta bi ni da shi tare da sakin baki
“Inye sannu Sa’adatu wato kina wajen mijinki, wannan abu ya fi karfina”
Mutanen da ke dakin ma salati suke yi
“Lallai yaran yanzu sai dai a bar su” ina jin su suna ta surutansu ni kuwa ko a jikina.
Wucewa nayi na bawa Rukayya ledar da ya bani sannan na dawo wajen Adda
Ruwan wanka ta haɗa min tare da zuba turaruka masu kamshi a cikin ruwan, shiga nayi na kammala wankana na fito, mai kwalliya ce ta xauna ta nutsu ta tsara min fuskata nayi matuƙar kyau kamar ba ni ba.
Wata tsadaddiyar doguwar riga na sanya (wedding gown) maroon colour, aka min nad’i da tie maroon colour, na saka takalmi high heel shi ma maroon, sai yar kamar jaka ta amare da na riƙe ita ma maroon colour, tsayawa bada labarin kyawun da nayi ma bata lokaci ne.
Wadatattun motoci izuddeen ya kawo aka ɗauki kowa xuwa wajen biki, shi dai bai halarci wajen ba sbd mata xallah ne, an ci an sha abinci da lemo har ragowa yayi.
Kawaye da abokan arziki sun fita sun yi rawa, nima da kyar Adda ta ya’ke ni na fita na taka kaɗan, nan fa aka riƙa yi min ruwan naira, yan uwa da abokan arziki sun nuna min kauna sosai, sai da na gaji da rawar sannan na dawo na xauna.
An dade ana cashewa sannan aka tashi, a motar abokin izuddeen na dawo ni da Rukayya.
Ita ma A’isha ana can ana shagali, Alhaji yawale ya sakar musu kuɗi sosai, Innah Salamatu sai alfahari take yi tana yada magana Allah ya bawa diyarta mai kuɗi.A ranar a gajiye muka koma gida sbd hidimar da muka sha, amma duk da haka sai da muka sha waya da izuddeen yana ƙara jaddada soyayyar sa a gare ni, sai bayan mun gama waya sannan na kwanta.
Washe gari da wuri me kwalliya taxo ta fara shirya kwayena, sannan ta shirya ni yau ma wani tsadaddiyar farar doguwar riga na sanya, dukkan kayan da aka yi min ado da su farare ne tas, na fito nayi kyau tamkar yar tsana, ana gama yi min kwalliyar na turawa izuddeen photona ta WhatsApp, ba ƙaramin yaba kyauna yayi ba, sai santi yake gaba ɗaya duk ya bi ya rude, har kofar gidan mu yazo da mota ya ɗauke ni, muna gidan baya ni da shi sbd abokin shi ke yin driving din.
Muna tafe yana kallona ƙasa-ƙasa, hannuna cikin nashi har muka isa wajen, sai da aka sanar da shigowar mu sannan aka buɗe mana murfin mota muka fito, har yanzu hannunmu rike yake da juna, taku muke mai cike da burgewa, kawayena da abokan shi ke tafiya a bayan mu, suna take mana baya har muka shiga cikin hall din.
Ba ƙaramin haɗuwa wajen yayi ba, kallo ɗaya xaka yi masa ka san ba da ƙaramin kuɗi aka kama shi ba, komai a tsare yake wajen xaman mu kuwa an ‘kawata shi da fitilu masu ɗaukar hankali, haka ma wajen da ‘yan bikin ke xaune, muna takowa wajen aka sanya mana wakar amare, gaba ɗaya mutanen wajen suka miƙe suna yi mana tafi, cikin tsari muka isa wajen zaman mu muka xauna.
Abinci kala-kala aka riƙa ajiyewa kowa a gabansa, tun daga kan snacks har zuwa lemuka, babu wanda yaje ya dawo da yunwa an yi komai cikin tsari abin ya burge kowa, sai kusan sha biyu na dare sannan aka tashi, amma ba don an gaji da bikin ba.
A kofar gida ya ajiye ni, yanzu ma da kyar muka rabu sai da ya gama kissing dina ta ko’ina sannan ya kyale ni na tafi, duk jikina ya mutunta sbd ya gama jagwalgwala ni.
Gari na wayewa aka tafi da ni gidan innah tunda a nan ne za a yi wuni daga nan kuma a kai amarya, kafin na tafi ma sai da mai gyara min jiki taxo ta gyara ni ta ko’ina, sannan Adda ta bani magunguna kala-kala, har sai da naji kamar xan yi amai sbd irin abubuwan da aka harhad’a min, sai da aka yi min kwalliya sannan muka tafi.
Muna zuwa aka fara sha’ani Innah Salamatu na yin nata mu ma muna yin namu, masu kidan ƙwarya ne suka xo suka taya ni murna,ba ƙaramin kuɗi aka xubar musu ba, sai wajen ƙarfe biyar sannan suka tafi, ina dakin innah ni da kawayena muna hutawa Adda tazo ta kira ni.
Kallona tayi.
“Ki shirya masu ɗaukan ki sun zo”
Xuba mata ido nayi jikina duk yayi sanyi kamar wacce aka zarewa laka gaba ɗaya na kasa magana, ji nayi kamar nace baxan tafi ba na fasa auren, jan hannuna tayi muka fita sai faman bin ta nake kamar raƙumi da akala.
Banɗaki ta kai ni ta shiga xuba min kala-kalar turare kamar yadda ta saba yi min, sannan ta umarce ni nayi wanka da ruwan, na dad’e ina tunani kafin na fara wankan har sai da ta gaji ta le’ko tayi min magana, sannan na cigaba da wankan, ina fitowa ta fara gyara ni.
Duk ilahirin jikina sai da ta shafe shi da turare ga kuma humra mai daɗin kamshi da aka kawo min ita daga sudan, komai nawa kamshi yake, wata super Holland ta d’akko min mai launin blue, a hankali na d’akko na saka, ci-gaba da gyara min jikina tayi sai da nayi tsaf na fito a sunana na amarya, sannan ta ƙara feshe min jiki da turaren feshe, hannunta rike da nawa muka fito wajen innah.
Tana ganina ta taso ta rungume ni, ina jinta a jikina na saki wani kuka mai cike da ban tausayi, bubbuga bayana ta shiga yi cikin shigar rarrashi, sannan ta kamani ta xaunar da ni kusa da ita, nasihohi masu ratsa xuciya take min game da xaman aure da irin kalubalen da ke cikin shi, ni kuwa sai kuka nake na kasa magana ina ji a raina xan yi kewar innata.
Adda ce ta janyo ni “kiyi shiru Sa’adatu kada ki bata kwalliyar ki, wannan ranar tana da matuƙar muhimmanci a rayuwar ki, ba kuka zaki yi ba godewa Allah xaki yi, goge min hawaye ta shiga yi sannan ta ƙara min powder a fuskata sbd hawayen da ya bata min kwalliyata, duk da wannan abin da tayi min bai sai hawayen ya tsaya ba, sai da Innah ta gama min faɗa sannan aka kaini wajen Babana.
A dakinsa muka same shi, duk jikinsa yayi sanyi da dukkan alamu akwai abubuwan da yake tunawa game da ni, kamar xai yi kuka ya fara min nasiha.
“Allah ya baki xaman lafiya ke da mijinki Sa’adatu, Allah yasa kin shiga a Sa’a, hakika ke ya ta gari ce, kin yi min biyayya Sa’adatu kin so dukkan abinda nake so, Allah ya albarkaci rayuwar ki ya baki dukkan abinda kike so a duniya, na umarce ki, da ki yiwa mijinki biyayya ki so dukkan abinda yake so, ki so danginsa da iyayensa, na san kina da halin kwari ko kaɗan bana jin mijinki xai samu matsala da ke, ke ta daban ce a cikin yayana Allah ya baki hakuri da juriyar zama da mijinki lafiya, na yafe miki Sa’adatu Allah ya bada Sa’a”
Ya ƙarasa maganar Muryar shi na sarkewa.
Gaba ɗaya wajen aka amsa da ameen, muna tafe mutane na take min baya abun gwanin burgewa.
Idanuna a rufe suke ina ta faman rusa kuka har muka isa bakin motar da aka kawo domin a ɗauke ni, mota ce kirar G-wagon mai launin baƙi bude min aka yi, Adda saratu ce ta tura ni da kyar na shiga, sai kannen Babana guda biyu da suka biyo bayan mu.
Gidan su izuddeen aka fara kai ni, ɗakin mama aka ajiye ni ita ma nasiha tayi min sannan ta dakko kuɗi da kayan kwalliya ta bawa Adda ta bani, kai tsaye wajen mahaifinsa aka wuce da ni, shi ma dai faɗa yayi min a kan zaman aure sai da aka yi addu’a aka shafa sannan muka tashi muka tafi, na samu kyautuka masu yawa a gidan su izuddeen, sun yi min karba mai kyau wannan ya nuna min cewa suna sona.
Kai tsaye hanyar gidan da izuddeen ya gina mana muka kama, wanda yake unguwar hotoro G.R.A muna tafe ina ci-gaba da kukana.
Muna isowa aka bude mana gate muka shiga, gida ne flat dai-dai xaman amarya, gidan yayi matuƙar kyau an tsara shi yadda ya kamata, babban falo ne sai d’akuna guda huɗu kowane d’aki da toilet, sai dining area sai kuma kitchen daga gefe, kowane d’aki sai da aka yi min jere gaskiya ba ƙaramin kokari aka yi min ba.
Har yanzu hannuna na cikin na Adda umarni ta bani nayi Bismillah sannan nayi addu’a kafin na shiga cikin dakin, bisimillah nayi kamar yadda tace sannan na shiga, yaye lullubin da ke kaina nayi na fara kallon yadda aka kawata min dakina, komai ya xauna a muhallinsa, a zahiri na furta Masha Allah.
Kayan gadon Royal bed ne launin gold, labule ma golding color ne, daga ɓangaren gabas aka saka min wardrobe
Sai kuma madubi da ke dama da ita, sai labule da carpet din dakin duk golding color ne, an jere min kala-kalar turare a saman dressing mirror din.
Adda ce ta dube ni.
“Ki tashi kije kiyi Sallah ki dawo na sake shirya ki” da yake ban yi sallar magariba ba da isha.
Jikina babu ƙarfi na tashi na shiga toilet na kunna ruwa na fara alwala, ba ƙaramin haɗuwa banɗakin yayi ba, shi ma an ‘kawata shi da kayan ado kala-kala, fitowa ta kenan su Rukayya suka iso, gefen gado suka samu suka xauna suna yaba irin kyan da gidana yayi tare da yi min fatan alkhairi.
Sai da na idar da Sallah sannan Adda ta sake gyara min fuskata tare da sanya min turare, sai dai suka yi min nasiha sosai sannan suka tafi suka bar ni.
Suna fita naji wani sabon kuka yaxo min, ji nayi kamar na bi su mu tafi tare amma baxan iya ba sbd soyyar mijina ta mamaye zuciyata.
Bayan tafiyar su Adda bai fi da minti goma ba izuddeen ya iso wanda ya samu rakiyar abokansa, zaune nake a gefen gado na lullube fuskanta ina ta faman sharar kuka, sallama suka yi min cikin muryata wacce ta sirance sbd kuka na amsa, a kusa da ni suka zaunar da shi bayan sun gama abinda xasu yi, aka yi addu’a tare da yi mana fatan zaman lafiya suka wuce suka kyale mu, tashi yayi ya raka su gami da kulle mana kofar gidan mu.
Da sallama ya shigo dakina sai na samu kaina cikin rashin iya bude baki na amsa masa sbd tsabar fargabar da ya cika zuciyata, samun kusa da ni yayi ya xauna jikinsa na gogar nawa, yaye rufin mayafin da ke fuskata yayi a hankali na fara buɗe idanuna tare da kai hannu zan share hawayen da ya bata min fuskata.
Da sauri ya riƙe hannun nawa ya shiga lashe hawayen nawa da harshensa sai da ya goge hawayen gaba ɗaya, sannan ya haɗa goshina da nashi ya sumbace ni, cikin raunanniyar murya ya fara min magana.
“Ki daina kuka sa’ar mata ko kadyan bana son ganin zubar hawayenki, ni ne mutumin da ya fi cancanta ya kula da ke a rayuwar ki, kuma yau Allah ya haɗa mu a Matsayin ma’aurata murna xaki yi ba kuka ba kin ji farin cikina, Insha Allah ni zan maye miki gurbin su innah ki rayu da ni cikin farin ciki”
Ya ƙarasa maganar tare da kwanto da ni kirjinsa, yana shafa bayana.
A sanyaye na girgiza kaina alamar “eh”
Har yanzu kaina a ƙasa yake ina wasa da yatsuna na kasa haɗa idanu da shi, a tsora ce nake sosai na kasa sakin jikina.
kama hannuna yayi tare da ɗora lips din shi a kansu ya ƙara sakar musu kiss, kunshin hannuna yake shafawa, yana yaba irin yadda mai ƙunshi tayi ƙoƙari a kaina, hira yake min gami da bani labaran yadda bikin mu ya gudana, duk don na saki raina amma na kasa yau ya koma min kamar Wani baƙo, cikin wata irin rikitacciyar wacce ban saba jin irinta ba yace
“Komai naki mai kyau ne Sa’adatu shi yasa nake ji da ke da matuƙar kaunar ki, na godewa Allah da ya mallaka min ke a matsayin iyalina”
Har yanzu kaina na ƙasa na kasa magana, jan hancina yayi cikin sigar tsokana yace “naji kin yi shiru ko ba gaskiya na fada bane?”
Ya faɗi maganar tare da tashi tsaye, Ni dai ban iya bashi amsa ba. ledar da ya shigo da ita ya d’akko tare da ajiyeta a gabana, gasashshiyar kaxa ce da fresh milk, tashi yayi ya shiga kitchen ya dakko cups guda biyu da plats, janyo ni jikinsa yayi ya shiga bani kaza da madarar har sai da na sha na koshi sannan ya kyale ni, tattara kayan yayi ya sake mayar da su kitchen sannan ya dawo.
Umarni ya bani mu je mu yi alwala, bayan shi na bi, tare muka shiga bathroom muka yi alwala, muna fitowa ya ja mu jam’i sai da muka yi addu’o’i muka gama sannan na sake komawa na rakabe a gefen gado kamar wacce za a kama, fita yayi daga dakin, mintuna kaɗan ya dawo sanye da pyjamas farare kal, wannan ya nuna min cewa wanka ya fita yayi, nima umarni ya bani na shiga nayi wankan, a sanyaye na tashi na shiga bathroom, na jima ina nazari kafin fara wankan, ina fitowa na tsaya gaban mudubi na ƙara feshe jikina da kala-kalar turare da humra, gefena na duba sai naga har ya dakko min wata hadaddiyar riga wannan ya nuna min ita yake so na saka, rigar doguwa ce mai launin fari, iyakar ta gwiwata tayi min matuƙar kyau, kallon kaina nayi a madubi naga yadda rigar ta bayyana duk wani sirri na jikina, har na kammala shiryawa bai dawo dakin b, samun mayafina nayi na yafa na dawo na dun’kule zuciyata na min sake-saken abubuwa daban-daban.
A dai-dai lokacin ya shigo, yana ganina ya sakar min wani kyakkyawan murmushi, a hankali ya fara takowa har wajen da nake zaune, gefena ya samu ya zauna kamshin turaren shi ne ya daki hancina, cike da salo yasa hannu ya sabule mayafin da na saka.
Cikin rawar murya na fara magana
“Ka barni da mayafina dan Allah”
Dan murmushi yayi gami da kwanto da ni jikin kafadunsa.
“Yau dai mayafi ba shi da amfani a gare ki sbd kina tare da mijinki mai son ganin kin faranta masa”
Marairaice fuska nayi kamar xan yi kuka, cikin salon iya rikita ya mace ya shiga shafa kaina tare da manna ni a kirjinsa yana sakar min kiss ta ko’ina, wani irin nunfashi yake saukewa wanda ya tabbatar min da cewa hankalinsa ya fara gushewa daga jikinsa.
A hankali yasa ya hannu ya shiga zuge xif ɗin da ke jikin rigar, da sauri na riƙe hannun shi cikin kasalalliyar murya nace.
“Kayi hakuri babyna”
Lumshe idanunshi yayi.
“Na fada miki dama sa’ar mata akwai lokacin da baxan ji hakurin ki ba, to wannan ranar nake nufi”
Bai tsaya jin me xan faɗa ba, ya cigaba da xuge xif din har sai da ya kaishi ƙasa, a haka har sai da rigar ta sauka daga jikina, ban san lokacin da hawaye ke xuba daga fuskata ba ko kaɗan ban yi tsammanin ganin hakan daga wajen izuddeen ba.
Bakin shi yake kan wuyana yana ta sumbatata ko ta ina, gami da rikita ni da salo salo na soyayyar shi, tabbas izuddeen gwani ne wajen iya rikita ‘ya mace duk taurin kanta, haka yayi ta jagwalgwala ni ta ko’ina, babu abinda nake yi banda kuka mai tsanani, gaba ɗaya na kasa fahimtar duniyar da yake ƙoƙarin aika ni,sai sautin kukana kawai da ke tashi, wata ƙara naji na saki, sbd wata sabuwar duniya da kuma sabuwar rayuwa da izuddeen ya jefa ni a cikinta.
Sai da ya dawo cikin natsuwar shi sannan ya gane irin barnar da yayi min, rungumo ni jikinshi yayi yana rarrashina, gami da yi min tausasan kalamai masu kwantar da xuciya, Cikin wani irin salo ya sake rugumo ni.
“I love You sa’ar mata, na gode sosai da kika iya riƙe min kanki wannan azzalumin bai samu damar shiga hurumin da ba nasa ba, na gode miki sosai babyna”
Bubbuga bayana ya shiga yi cike da soyayya yana mayar da wani wahalallen numfashi, rufe ni yayi da bargo, ya ci-gaba da lallaba ni tamkar jaririya.
“Kiyi bacci mai daɗi babyna”
A hankali na lumshe idanu tare da gyara kwanciyata
Haka ya cigaba da tarairayata har bacci yayi awon gaba da ni, amma duk da haka ina jin zafi da radadin abinda ya shiga tsakanin mu.
Ban farka ba sai Asubah, tattausan hannun shi naji yana shafa bayana a hankali na fara buɗe idanuna cikin rad’a yace min
“Tashi mu yi sallah babyna”
A hankali na fara yunkurin mi’kewa sai na kasa, ɗaukana yayi cak ya kaini banɗaki yayi min wanka sannan ya fito da ni ya dire ni a kan gado ya fara shirya ni, wata tsadaddiyar riga ya d’akko ya saka min tare da d’aure min gashina nayi kyau sosai, hijabi na saka sannan ya ja mu jim’i muka yi sallar asuba.