TSANANI
CHAPTER 2
A makaranta ma dai ban wani mayar da hankali nayi karatu ba saboda yawan tunane-tunanen da na riƙa yi har malam sai da ya fuskanci ina cikin damuwa. Tare da Rukayya muka dawo muna tafe muna hirar mu irin ta kawaye, gidanmu tace zata je saboda kawai tana so ta ɗebe min kewa na manta da dukkan damuwa ta, sannan kuma ummansu bata nan ko ta koma gidan babu abinda zata yi sai zaman kaɗaici
+
+
Sallama muka ji a bayanmu gaba ɗaya muka waiwaya ba tare da mun amsa sallamar ba, wani kyakkyawan saurayi ne mai cikakkiyar kamala sanye yake da shadda fara ƙall wacce aka yiwa aiki da brown din zare, takalminsa ma brown ne, kansa babu hula wanda Hakan ne ya bani damar ganin kyakkyawan kwantaccen gashin sa, bai gajiya ba wajen sake yi mana sallama wucewa muka yi muka kyale shi ba tare da mun amsa masa ba, biyo bayan mu yayi. “Haba bayin Allah bai kamata ku ƙi amsa min sallama ba, ga alamu sun nuna min ku malamai ne baxa ku wulakanta ni ba wannan dalilin ne ma ya ja ni har nayi kwadayin yi muku sallama nasan baxan samu matsala ba ya kamata ku amsa min kada ku watsa min ƙasa a ido” kanmu a ƙasa muka amsa masa da “wa alaikumussalam” muna gama amsawa muka juya don cigaba da tafiya, saboda idan da abinda na tsana na tsaya ina magana a hanya ko da yar uwata mace ne ban so ballantana kuma da namiji
Ganin yadda muka wuce muka kyale shi bai sa yayi zuciya ba sake bin bayanmu yayi, ku yi hakuri na tsayar da ku a hanya ko, na san kuma hakan ba dai-dai bane amma na kasa hakuri ne sbd daya daga cikin ku ce tayi min sata”
Gaba daya muka juya muna yi masa kallon mamaki Rukayya ce tayi ƙarfin halin yin magana sbd ta fi ni baki, gaba ɗaya na kasa cewa komai sbd mamakin jin fitowar kalmar sata daga bakinsa “sata fa kace bawan Allah?? Sake wani zancen dai ba wannan ba, mu bama sata kuma bamu taɓa satarwa wani dan adam komai ba, muna bakin kokari wajen dogaro da abinda Allah ya wadata mu da shi
Murmushi yayi wanda sai da fararen hakoransa suka bayyana sannan ya dan sha kunu “ba ke nace kin min sata ba kawarki ce, amma ita ma bata san ta min satar ba” A razane na dube shi kirjina na dukan uku-uku sbd bana so na sake dakkowa innah abinda xai xame mana abin gori da bak’ar Magana, cikin rawar murya na fara magana “ban taɓa yiwa wani sata ba tunda nake malam watakila mai kama da ni ka gani” ban jira amsar da zai bani ba na ja hannun Rukayya muka cigaba da tafiya.
Sake shiga gabanmu yayi “ku tsaya mu warware matsalar mana ko su ku ke yi sai Maganar ta je gaba? Idan haka ku ka zaba shikenan, amma ni shi ne abinda bana so. Tsayawa muka yi cak muna sauraron shi, gyara tsayuwa yayi tare da tambayata kin san satar da kika yi min. Da sauri na amsa masa da ban sani ba, rausayar da kansa yayi
“To zuciyata kika sata”
Gabana ne ya fadi mamaki ya mamaye ni wai yau ni wani da namiji yake cewa na sace masa zuciya abinda ban taɓa ji ba kenan, sbd tunda nake babu wanda ya taɓa tunkarata da sunan na burge shi ballantana har ya furta yana sona.
Ganin dogon tunanin da na tafi ya sanya shi yi min magana “lafiya naji kin yi shiru ko ba gaskiya bane abinda na fada?” Ban bashi amsa ba na juya na tafi tare da Rukayya na bar shi suna Magana ban san me take fada masa ba.
Sai da na shiga gida da kusan minti biyar sannan na ganta, sallama tayi na amsa mata duk jikina yayi sanyi.
Masifa ta fara yi min “ke shikenan daga fara magana sai ki wani tafi ki kyale mutane sai ni nayi masa bayani, na fada masa sunanki da kwatancen gidan nan dan haka ki shirya yau kina da babban bako”
Fito da ido nayi “Haba ya xaki min haka ban so kika bashi kwatancena ba” hararata tayi “ok so kike ki xauna a cigaba da miki gori ba mai tayawa ko, ai ko ba aurenki xai yi ba yana da kyau kema a ga kina xance kin huta gori” dakatar da ita nayi “Kinga ni duk wannan bai dame ni ba sama da yadda idan nayi aure xan tafi na bar innah a wannan gidan shi ne abinda ya fi tayar min da hankali”Wannan duk na Allah ne Sa’adatu baki san alkhairin da ke tattare da wannan bawan Allahn ba, watakila ya zama silar farin cikinki ke da innah” a takaice na bata amsa da haka ne yar uwata.
Aiki ta taya ni muka gyara ko ina sannan muka yi wanke-wanke muna aikin, mutanen gidanmu na hararmu duk wanda Rukayya ta gaisar babu wanda ya amsa mata, ita ma baƙin jinina ya shafeta.
Har yamma muna tare da ita sai da aka kusa sallar magariba sannan na rakata hanya ta tafi gida. Ina dawowa bayan nayi sallah ban dade ba na dan ji hayaniya a tsakar gida, ban mayar da hankalin sauraren abinda ake yi ba sbd nasan alkhairi bai fiye fitowa daga bakinsu ba, muryar yan matan gidan mu naji suna cewa ” sam baxai yiwu a ce da Sa’adatu ake sallama ba sbd tunda take ba a taba xuwa ana sallama da ita ba, me xa a yi da mummunar yarinyar nan ga baƙi ga baƙin hali ai farare irinmu ake yayi, kai koma ka sake tambayarsa ya faɗa maka wa ake nema”
Ajiye littafin da nake karantawa nayi nasan mutumin da muka gamu da shi daxu ne yaxo, sallamar yaron ce ta katse min tunanina.
“yace Sa’adatu yake nema wacce suka haɗu tare a hanyar makaranta”
Jikinsu ne yayi sanyi saboda sun san duk cikin ya’yan gidanmu ni kadai nake xuwa makaranta ragowar basu san komai ba sai yawon gidajen makota. Umma ce tace da yaron “je ka fada masa bamu san da zaman wata Sa’adatu a gidan nan ba”
Hawaye naji na ƙoƙarin fito min yanzu a ce na samu mai son nawa ma sai an yi min bakin ciki, ban samu ba kuma ana min gori. ni kuma baxan iya fita na fada musu Ni ake nema ba ballantana na cewa yaron ya faɗa wa mai nemana ina zuwa ba, saboda na san duk rintsi duk wuya rabona baxai taba wuce ni ba, mayar da idona nayi kan innah tana ta sharar bacci abinta, da nayi ƙoƙarin tashinta na fada mata sai kuma na fasa kasancewar yau bata jin daɗin jikinta.
Ina cikin wannan halin naji sallamar ya salim ta window ya leko da kanshi “Sa’adatu kina ina, yi sauri ki leko xan yi magana da ke”
Sauri nayi na janyo hijabi na saka, nima lekawa nayi ta window nayi masa magana sbd bana so Mahaifiyarsa ta san ina kula mata danta.
“Ya salim gani” nace masa. Karasowa yayi wajena
“Ba kece kika yi baƙo ba Sa’adatu kin barshi tsaye yana jiranki tun daxu, ga sanyi ana yi, baki kyauta ba wlh, abinda muke nema Allah ya kawo mana xaki mana asara”
Ban fada masa abinda ya faru ba illa kawai murmushi da nayi “na zaci wajen su A’isha yaxo shi yasa ban fita ba
Hararata ya dan yi “menene alaƙa tsakanin sunan A’isha da Sa’adatu ke dai kawai kice kina jin kunya, tashi ki shirya yana can yana jiranki”
Har ya juya ya tafi ya dawo “Au na manta ba ni tabarma na je na shimfida masa”
Ɗan bata rai nayi “Haba ya salim daga xuwa sai a fara ba shi tabarma ka bari mu tsaya a tsaye, ni baxan dade ba minti biyu na dawo”
Riƙe baki yayi yana kallona lallai Sa’adatu har yanzu ba ki san rayuwa ba, wanda yaxo wajenka abin girmamawa ne ya cancanci kayi masa dukkan abinda xai sa yayi farin ciki. Saboda Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da kansa ya fada mana cewa wanda ya bada gaskiya da Allah da ranar lahira ya girmama bakonsa, ke malama ce amma kuma kina mantawa, maza miko min na tafi”
Ban tanka Masa ba na miƙa masa tabarmar, hijabin da naje makaranta da shi na sake sakawa na fita.
A soro na biyu ya salim yayi mana shimfida, zaune na tarar da shi ya tankwashe ƙafarsa, kansa a sama kamar mai tunani har na iso gare shi bai san naxo ba sallamar da nayi masa ne ya dawo da shi hankalinsa, da fara’a ya amsa min tare da gyara xaman sa.A ladabce na gaishe shi tare da yi masa barka da zuwa, gefen tabarmar na samu na zauna, sai na samu kaina a jin kunya na kasa haɗa ido da shi tunda wannan shi ne karo na farko da na taɓa fitowa zance da saurayi.
Gyara zama yayi yana kallona, wato Malama Sa’adatu sai an ja min rai za a fito ko, ko da yake ban ga laifinki ba ke din mai tsada ce don kin ja aji ba komai girmanki ne ranki ya dade.
Murmushi akwai nayi ba tare da na bashi amsar maganar sa ba.
Gabatar min da kansa ya shiga yi ” nasan dai baki yi mamakin ganina ba, tunda kin san da xuwana kuma kawarki ta fada miki komai game da ni” girgiza kai nayi alamar bata fada min ba
Murmushi yayi tare da gyara zama “tunda bata wakilce ni ta fada miki ba to ni bari na fada miki da kaina don waka a bakin mai ita tafi dadi. Sunana Izuddeen Muhammad iyayena mu maxauna wannan unguwar ne gidan malam Muhammad mai yan makaranta , na san baxa ki kasa sanin gidanmu ba, sai a lokacin da yayi min wannan bayanin na gane a gidan da yake (mahaifinsa babban malamin addini ne, yana da rufin asiri sosai, sannan mafi yawan ya’yan gidan manyan ma’aikata ne) nayi karatuna a jami’ar Ahmadu Bello da ke zaria na karanci bangaren engineering, Amma ban samu aiki ba sai dai ina ragewa a wani Company kafin babban aiki ya samu. A gaskiya nayi matuƙar farin ciki da Allah ya bani damar yi miki magana, domin na dade ina sonki amma na kasa fitowa na furta miki, kullum sai na tsaya jiranki a hanyar zuwanki makaranta da dawowarki ko xan samu damar fada miki abinda ke raina sai yau Allah ya bani wannan dama kuma nayi farin ciki da yadda kika karɓe ni, Allah yasa na xama silar farin cikinki na har abada, ki miƙa min godiyar ki wajen kawarki domin da taimakonta na samu wannan damar mai tsada”
Har yanzu kaina na ƙasa na kasa cewa komai “baki ce min komai ba Sa’adatu, ko dai ban yi miki bane?”
A hankali na dago kaina “Na gode da kulawarka gare ni” ita ce kawai kalmar da na iya furtawa.
Bamu fi minti sha biyar muna tattaunawa ba ya mike tsaye ya fara nade tabarmar da na shimfida masa.
Da sauri nace “ka bari na nade da kaina”
A’a ki bari ai baxan so na fara sa ki aiki ba.
“to ni zan tafi Sa’adatu sai yaushe kenan?”
Murmushi na dan yi “sai bayan sati daya”
Da sauri ya dube ni “sai bayan sati daya fa kika ce, kema kin san baxan iya ba, ki bani dama gobe na dawo”
“Gobe ina da unguwa ka bari ka dawo jibi” amsa min yayi da Allah ya kaimu.
Sallama muka yi ya juya ya tafi, sai a lokacin na tsaya na kalle shi sosai, kyakkyawa ne mai matsakaicin tsawo baxa ka kira shi dogo ba haka kuma baxa ka kira shi gajere ba, wankan tarwada ne idanunansu masu kyawun gani Musamman idan ya daga ido xai yi kallo xamu iya kiransu da sexy eyes, bakinsa ma madai-daici ne ga kuma kyakkyawan saje da ya xayyana fuskarsa.Har ga Allah ban yi tsammanin wannan kyakkyawan saurayin zai furta yana sona ba, kasancewar ba wani kyau ne da ni ba, haka nake ba yabo ba fallasa. +
A tsoro na biyu na ci karo da A’isha da innah salamatu da da dukkan yan matan gidanmu, Maryam saliha da bilkisu sun kasa kunne suna sauraren tattaunawar da muka yi da Izuddeen abinda ya bani mamaki ganina bai sa sun ji kunya sun matsa ba, sai ma magana da naji suna yi “lallai abu ya ci-gaba ɗan iska har cikin soro Allah ya kawo Baba yau za a yita ta ƙare
Ji nayi kafafuna sun yi sanyi addu’a na fara yi Allah yasa kada su hada min tuggu a wajen Baba, don yanzu baya jin maganar kowa sai tasu, daki na wuce na bar su har yanzu dai innah bacci take bata farka ba don haka ban tashe ta ba na kyaleta.
Maganar su na rika ji “Ai wlh baxa mu bari yarinyar nan tayi aure ba sai mun hada mata makircin da sai an koreta daga gidan nan sai yayanmu sun yi aure tsaf sannan xata yi, haka kawai ku fi ta komai sannan Izuddeen yaro nutsatstse yace yana sonta yaron da kowa ya san yayi fice a ilimin boko da dana addini, da ku ya dace ba ita don haka kamar mun sa an kore shi ne”
Washe gari da safe na tambayi innah ina son xuwa gidan kanwarta Adda saratu sbd a nan kusa da mu take kuma na dade ban ziyarce ta ba, kasancewar Baba baya barina na fita, maganganun su innah salamatu sun fara yi masa tasiri, wannan yasa yake saka min takunkumi sai wajen da ya yarda nake zuwa. +
Sai da na gama shiryawa tsaf na fito tsakar gida, tarar da innah nayi zaune a kofar daki tana gyara shinkafa, a ladabce nace “innah na fito ko kina da sakon da zaki bayar a kai mata?” Murmushi innah tayi. “Ba ni da wani sako Sa’adatu abinda zan ce miki kawai ki kula da kanki kuma kada kiyi dare, kinga dai irin rayuwar da muke yi ki gaishe min da ita da kyau, alewar kwakwa ta miko min, karbi wannan ki kaiwa yaran nawa.
Sallama muka yi na fita a soro naci karo da zaliha wani kallon wulakanci tayi min a haka dai za a ƙare kullum a tafe an rasa mashinshini, ban saurareta ba sbd baxa tayi min haushi na rama ba.
Cikin nutsuwa nake tafiyata, har na isa gidan Adda saratu sallama nayi na shiga gidan, yaran ta na tarar suna wasa a tsakar gida suna jin muryata suka taho da gudu suka rungume ni, “sannu da zuwa Aunty Sa’adatu, kin manta da mu” karɓar kayan da ke hannuna suka yi muka shiga cikin dakin Adda saratu, bamu tarar da ita a ciki ba kasancewar ta shiga wanka.
Ruwa da lemo suka dakko min sannan muka fara hirar zumunci tare da su duk da cewa ƙanan yara ne amma suna da hankali da nutsuwa basu fiye shirme irin na yara ba, sbd Adda saratu mace ce mai nutsuwa da iya tarbiyya shi yasa ya’yanta suka fita daban a cikin yara.
“Wata sabon gani yau kece a gidan namu” da sauri na waiwaya Adda saratu ce ta fito daga wanka, da sauri na ƙarasa muka rungume juna muna farin cikin haduwa da junanmu, waje ta samu ta zauna “yau kece a gidan namu, nayi mamakin ganinki don kin jima rabonki da mu, shi yasa nima nayi fushi na daina zuwa babu ke babu innah”
Murmushi nayi wlh Adda makaranta ce ta boye ni, kin san na kusa haɗa haddata shi yasa bana samun lokacin ziyara”
“Ayya shi yasa bana ganinki to Allah ya taimaka Allah yasa ta tsoron Allah ce, ai kuwa nima sai na hada miki walima ‘ya guda ta haddace Alkur’ani ai dole mu nuna godiya ga Allah” tambaya ta jefo min.
“Sa’adatu har Yanzu ba wani labari ne?”
Murmushi nayi da akwai Adda amma Akwai yan matsalolin da ba a rasa ba, labarin Izuddeen na bata da irin matsalar da nake fuskanta a gidanmu addu’a ta yi min kan Allah ya kare ni daga sharrinsu.
Haka muka cigaba da hira har zuwa yammaci sannan na tashi don tafiya gida, kayanta ta hado min kowanne da mayafinsa, saboda ta lura da irin kayan da suke jikina duk sun mutu, kusan kala goma ta bani, godiya nayi mata sannan na tashi na tafi.
A kofar gida naci karo da Baba, wani kallo yake min wanda ya sanya gabana faduwa a cikin xuciyata na fada “Allah yasa dai ba wani laifin aka ce nayi ba”
A sanyaye na tsugunna na gaishe shi amma sai naga ya kawar da kansa gefe, sake maimaita gaisuwar nayi a zatona ko ji ne bai yi ba, sai naga ya wuce ya barni a tsugunne.Jikina babu ƙarfi na tashi na shiga gida a tsakar gida na tarar da innah tana alwalar sallar magariba.
A damuwar da ta ganni yasa ta saurin tambayata. “Lafiya Sa’adatu me ya same ki na ganki a haka”
Ban fada mata ba Saboda bana so ta shiga damuwa ga shi ita kanta ba wani koshin lafiya gareta ba, “bana jin dadi ne innah ji nake kamar marata xata yi ciwo” cikin tausaya wa ta dube ni “Allah ya baki lafiya amma yana da kyau kije daki ki dauki maganinki sbd bana so ciwon nan ya tasar miki da ƙarfi” to nace na wuce daki.
Shigowa tayi ta same ni, na hada kai da gwiwa “kin dai sha maganin ko, wai ni anya ma kuwa ciwon nan kike yi ba wani abu ne ya same ki ba?” amsa mata nayi da “shi ne innah babu wani abu da ke damuna”
Kayan da aka bani na mika mata “innah kinga kayan da Adda saratu ta bani” cikin farin ciki ta fara bude kayan “kai madalla mun godewa sarai ita dai bata gajiya da yiwa zumunci hidima Allah ya saka mata da alheri”
Cikin shagwaba nace
“Kema ki duba ki zabi wanda xai miki dai-dai innah”
“A’a Sa’adatu ki saka ai kece budurwa kin fini buƙatar kayan kwalliya, kuma ni wannan ɗinkin na yara ne ya xan yi da shi, ke dai ki saka ita kuma Allah ya biyata da aljannah”
Muna cikin maganar naga Baba ya leko kwalawa innah kira ya fara yi, ita kanta tayi mamakin kiran da yake mata don rabon da ya kirata har ta manta, da sauri ta tashi ta fita. Ni kuwa xuciyata kamar ta tsaga kirjina ta fito saboda fargaba nasan da kyar ne idan kiran ba nawa bane.
“Gani malam”
A yatsine ya dube ta “ina Sa’adatu?”
Ina ji kafin ta kirani naje tsugunna sbd bana so wani abin ya biyo baya “gani Baba”
“Ina kika je yanxu don naga kwana biyu dabi’un ki sun fara canjawa ba irin yadda na sanki da kike ba”
Kafin nayi magana har na fara kuka wannan yasa na kasa yin magana saboda baƙin ciki, wato dai ta tabbata zargina Baba yake yi.
Kafin nayi magana ya wanke ni da mari “baxa ki fada min inda kika je ba sai na ci mutuncinki ko? Innah ce ta bashi amsa “Ba wani guri taje ba malam gidan sarai taje, sbd ta dade bata ziyarce ta ba”
Dakatar da innah yayi “kada na sake jin kin min magana sbd kece munafukar da kike goya mata bayan duk abinda take yi, sbd ana shigo miki da leda ko, duk abinda yake faruwa ina ji kuma labari yana zuwar min, an fada min har yaron da yake lalata ta har gidan nan yake xuwa, to wlh duk randa na sake ganinsa sai ransa ya baci Allah yasa na sake ganin ƙafarsa a gidan nan”
Dakawa innah tsawa yayi. “Maza dakko min ledar da ta shigo da ita haramiyarku” da sauri innah ta shiga daki ta kawo masa ledar kayan da Adda saratu ta bani, kiran innah salamatu yayi, cikin hanzari ta fito tana dariyar mugunta.
“Gani malam”
“Ina su zaliha” cikin kissa da makirci irin nata ta amsa da “suna daki”
Kirasu su zo su kwashe kayan nan, da murnarta ta kwala musu kira kamar jiran a kirasu suke yi suka fito a guje, kayana baba ya miƙa musu ku karba ku je ku saka, ke kuma xaki gamu da ni.
Ficewa yayi ya barmu a tsaye ni da innah, su innah salamatu da ƴaƴanta sai dariya suke mana tare da yi mana habaici.A salube muka shiga daki gaba ɗaya na kasa daina kuka, sbd na gaza gane irin wannan kiyayar da Baba yake mana, wani lokacin shi da kansa yake bada kofar da xa a ci min mutunci, nasihohi innah ta rika yi min tare da kwantar min da hankali cewa komai mai wucewa ne.
Washe gari Baba bai fita ko ina ba sbd yana ta dakon xuwan Izuddeen, tunda dama sun riga da sun fada masa yau xai dawo, cikin ikon Allah sai kuma ranar bai zo ba, ban san uzurin da ya tsare shi ba kasancewar ba ni da waya, addu’a na riƙa yi Allah yasa dai ba su ne suka hargitsa min shirina ba don yanzu zuciyata ta fara kaunarsa Musamman da naga yadda yan gidanmu suka so su ya nema ba ni ba.Washe gari ma shiru bai zo ba, tun daga lokacin hankalina ya tashi kewarshi nake yi sosai kamar mun dade da shi, tambayar kaina na shiga yi, anya ba baba ne yaje ya dakatar da shi ba kuwa, tunda mutanen gidan mu sun fada masa karya da gaskiya kuma sun san gidan da yake, ko kuma wani abu aka je aka fada masa a kaina, tambayoyin da na riƙa yi wa kaina kenan wanda na kasa samun amsar su, kasa hakuri nayi na tambayi innah ina son zuwa wajen Rukayya saboda nasan a wajenta ne kadai xan samu amsar tambayoyina.
Gidansu Rukayya na nufa amma cikin rashin Sa’a sai na tarar da gidan a kulle basa nan. Raina bai min dad’i ba naso samunta mun tattauna a kan matsalar dawowa gida nayi da sauri kafin Baba ya fuskanci bana nan, addu’a na shiga yi Allah yasa alkhairi ne ya boye shi ba akasinsa ba. +
*WACECE SA’ADATU*
Malam Salisu Abubakar shi ne sunan Mahaifina, muna zaune ne a garin kano cikin unguwa uku da ke kano, mahaifina ɗan kasuwa ne sai dai ba wani babban ɗan kasuwa ba, yana da rufin asiri dai-dai gwargwado, mun fi karfin ci da sha. Gidanmu irin babban gida ne family house kasancewar kakanmu malam Abubakar shi ne mai unguwar unguwa uku don haka duk yayansa shi yake yanka musu fili, wannan yasa muka kasance a dunkule a gida daya, mahaifina shi ne babban dansa, sai kannensa guda shida biyu maza huɗu mata dukkan matan suna aure a Kano, ragowar mazan ne muke gida ɗaya da su. Mahaifina yana da mata biyu, innah salamatu ita ce uwar gida tana da ya’ya takwas biyar maza uku mata, salisu, Hamza, Yusuf, Ibrahim, Musa, Aisha, zaliha, zainab. Ta aurar da ya’ya mazanta gaba daya sai kuma zainab wacce tun kafin mu yi wayo aka aurar da ita, wato A’isha da zaliha ne suka rage bata aurar da su ba wanda suka kasance kanne a gare ni.
Innata Maryam ita ce amarya wacce na kasance yarta daya tilo kasancewar duk ya’yan da innah take haifa mutuwa suke yi ni kadaice na tsaya, shikenan kuma tun daga kaina bata sake haihuwa ba.
Tare muke da kannen Babana da matayensu amma ɓangaren kowa daban, Baba Sani shi yake bin mahaifina wanda kuma shi ne mahaifin ya salim yana da ya’ya biyar biyu maxa uku mata an aurar da mata biyu saliha ce kaɗai ta rage ba a aurar da ita ba. Sai kuma Baba Umar wanda ya kasance dan autansu shi ma ya’yansa biyar shi kuma duka maza ne.
A farkon zamantakewar gidanmu kan su innah da ragowar matan a haɗe yake babu wata matsala da ke tsakanin su, daga baya innah salamatu ta canja rayuwar gidan gaba daya da gulma da munafunci, aka hadewa innata kai muka zama abin tsangwama, babu laifin tsaye babu na zaune.
Back to story
A ɓangaren Izuddeen kuwa tunda ya koma gida yake fama da matsanancin ciwon kai, yayi ƙoƙarin zuwa yaga Sa’adatunsa amma hakan ya gagara sbd ko kofar gida baya iya fitowa sai dai abokansa su shigo su taya shi hira, ba karamin damuwa ya shiga na rashin ganin abin kaunarsa ba, ga shi ko waya bai bata ba ballantana ya kira yaji muryarta.
Yau dai ya ɗan ji ƙarfi a jikinsa wanka yayi ya sanya farin yadinsa mai kyau, kayan ya karbi jikinsa kasancewar Izuddeen mutum ne ma’abocin son fararen kaya, cikin gidan su ya shiga don gaida mahaifansa, kai tsaye dakin Hajiya Amina (mama) ya shiga kishiyar mahaifiyarsa wadda ta kasance ita ce amarya kuma uwar dakinsa, tun lokacin da taxo gidan Izuddeen ya zamto dan dakinta, komai nasa a wajenta yake baxa ka taɓa cewa ba ita ta haife shi ba, Kasancewar kan iyayensu a haɗe yake komai tare suke yi baka gane tsakanin su.Da farin ciki ta karɓe shi “sannu da xuwa dana na kaina lallai jiki yayi sauki” guri ya nema ya zauna cikin ladabi ya gaisheta, amsa masa tayi tana mai tashi ta kawo masa kayan karin kumallo, bayan ya gama ci sun ɗan taɓa yar hira, sannan ya gyara zama “mama ina da magana da ke” da yake da sunan da yake kiranta kenan, hankalinta ta bashi ina “jinka dana na kaina”
Sunkuyar da kansa yayi “Dama mama fada miki zan yi na samo miki suruka” farin ciki ne ya bayyana a fuskar ta “Alhamdulillah Allah ya nufa nima xan ɗauki jikokina a hannu, ya sunan surukar tamu kuma a ina take”
Kansa a sunkuye yake magana “sunanta Sa’adatu a nan kusa da mu take”
Mamaki ne ya kamata “Izuddeen dama a nan kusa akwai yarinyar da zata burgeka gaskiya nayi matuƙar mamaki”
Murmushi yayi “Dama lokacina ne bai yi ba mama shi yasa kika riƙa fama da ni a kan na samo mata to yanzu dai na samo na huta” murmushi suka yi gaba daya, fatan alkhairi tayi, “insha Allah yau xan gayawa malam, na san ba ƙaramin dadi xai ji ba” kujera ya nema ya kwanta.
****************
Innah salamatu ce zaune a bakin Kofar dakinmu yau saboda tsabar raini da tsokana yau a Kofar dakinmu take bushe masara, tana busar tana habaici abinda na lura da shi a habaicin nata, da akwai abinda yake shirin faruwa da ni, ni dai addu’a nake Allah ya kare mu daga dukkan sharrinsu ni da innata.
Sallamar Rukayya ce ta katse min tunanina da sauri na amsa mata lekowa nayi sbd baxan iya wucewa ba tunda innah salamatu ta tare bakin kofar da kayanta. gaisheta tayi amma bata amsa mata ba, sai ma bin ta da tayi da wani matsiyacin kallo, bata kula da ita ba ta cigaba da magana da ni. “ina innarmu??” amsa mata nayi tare da harararta “Ba a sani ba jiya ina ta nemanki kika kulle gida kika tafi” murmushi tayi “unguwa muka je ni da umma shi yasa baki ganni ba, ina innarmu nace miki?” “Bata nan taje unguwa”
Hijabi na dakko tare da mika mata allona nace ta riƙe min kasancewar idan na fito da shi da kaina xan iya buge innah salamatu, ko samun kulle dakin ban yi ba sbd tare kofar da tayi.
Wucewa muka yi muka makaranta. Muna barin kofar gidan mu abinda na fara tambayar Rukayya shi ne “ina Izuddeen kin ji wani labari daga gare shi” kallon saroro tayi min “ban gane ina Izuddeen ba ke da masoyinki ke xan tambaya inda yake”
Rausayar da kaina nayi kamar xan yi kuka “tunda ya tafi bai sake dawowa ba dalilin da yasa naje gidanku nemanki kenan sbd hankalina ya tashi kwarai da gaske, kinga ranar da yaxo na tarar da su innah salamatu da yayanta har yayan wajensu ya salim sun kasa kunne suna jin tattaunawar da muka yi da shi, da Baba ya dawo sai suka juya min zance suka ce wai ɗan iskana na kawo shi ne Baba yace zai je ya dakatar da shi kada ya sake zuwar masa gida”
Cikin tausayawa ta dube ni “kai amma mutanen nan an yi munafukai azzalumai, ta Allah ba tasu ba idan ina jin matsalolin gidanku sai na riƙa ji kamar a film, me yasa su innah salamatu suke haka na rasa dalilin wannan kiyayyar, ki kwantar da hankalin ki idan Izuddeen rabonki ne duk rintsi duk wuya sai ya aureki, matar Mutum kabarinsa wannan hassadar da suke miki baxa tasa kiyi ƙasa ba da yardar Allah sai kin fi ƴaƴansu komai”Har muka isa makaranta tattaunawar da muke yi kenan, don ko damar karatu bamu samu ba muna ta kullawa muna kwancewa, wani yaro na gani tsaye a kaina ɗaya daga cikin almajiran makarantar mu, “kixo inji malam jibo” kallon mamaki na hau yi masa a zuciyata na riƙa cewa kiran me malam jibo yake min, Rukayya ce tayi saurin cewa kace “Bata nan” dakatar da ita nayi “ki bari naje naji kiran kika sani ko maganar haddata ce” har na miƙe ta zaunar da ni “wlh ba inda zaki je idan hadda ce ai da kansa yake xuwa, kika sani ko kararki Baba ya kawo, haka kawai ki kai kanki inda za a rika jibgarki kamar jaka”
Komawa nayi na zauna ‘Haka ne kuma Rukayya ni na manta da hakan ma sai da kika tuna min, ban san sharrin da aka kulla min ba” sake dawowa yaron yayi “Yace idan baki zo ba zai zo da kansa”
Jikina na rawa na tashi na tafi, a cikin rumfar da yake karatu na tarar da shi zaune a kan buzunsa yana karanta Kur’ani, ga dogon carbi a gabansa, sallama nayi da fara’a ya amsa min, nayi mamakin karbar da yayi min kasancewar shi mutum ne ba mai yawan sakin fuska ba musamman ga dalibansa.
Cikin ladabi nace “Gani malam”
Murmushi yayi “Babanki bai fada miki komai ba?” kaina a sunkuye nace bai fada min ba, a xuciyata nace me Baba xai fada min haka? Katse min tunanina yayi da gyaran muryar da yayi, kallonsa nayi yana min murmushi tare da gyara hularsa. “to!! to!! to!! Tashi zai faɗa miki don jiya yazo nan ya same ni da wata magana ina fatan xaki bani hadin kai, amma nafi so dai kiji komai daga bakinsa”
Jikina a sanyaye na tashi har na fita yana bi na da wani kallo da ni kaina ban san fassararsa ba.
Wajen Rukayya na koma hankalina a tashe, tana ganina ta miƙe dafa kafadata tayi “lafiya naga walwalarki ta canja kawata faɗa min abinda ke damunki”
Kwashe labarin yadda muka yi da malam Jibo nayi na fada mata, tunda Rukayya ta sunkuya bata dago ba ban san me ya hana ta dago bata kalleni ba.