TSANANI CHAPTER 3

TSANANI






CHAPTER 3





Hawaye na gani ya cika idonta da sauri na fara tambayarta “menene ya sa ki kuka Rukayya? Kiyi hakuri insha Allah alkhairi ne xai same ni, ki daina damuwa da halin da na shiga a yanzu wata rana sai labari” ƙarfin halin mikewa tayi tare da riƙe hannuna “tashi mu je wajen innah hankalina baxai kwanta ba har sai mun samu amsar abinda malam ya fada miki, to ni me ma yake nufi da Maganar nan ni fa na fara tsoron al’amarin sa,, saboda tunda yake tare da mu bai taɓa kiranki ya faɗa miki wani abu makamancin wannan ba, gaskiya idan wani abu ya faru Baba ya cuce mu” tashi nayi ba tare da nayi mata gardama ba muka riƙe hannun juna muka tafi gida
Izuddeen muka hanga tun daga nesa yake mana murmushi babu wacce ta iya mayar masa da martanin murmushin da yake mana saboda dukkanmu muna cikin damuwa, ya lura da yanayin da muke ciki, sauri ya riƙa yi har yana tuntube don yazo ya tarar da mu.
Sallama yayi mana gaba daya muka amsa Rukayya ce tayi ƙarfin halin yi masa magana “Izuddeen ya kake ya gida” amsa mata yayi da “lafiya” mayar da kallonsa yayi gare ni “nasan rashin ganina ne yasa kike fushi da ni to kiyi hakuri ba ni da lafiya ne shi yasa ban zo ba, sai yau na samu kaina”
Kawar da damuwar da ke xuciyata nayi “Ai dole naji haushi kwana ɗai-ɗai har uku ban ganka ba kaima kasan dole na damu, kuma a ce kayi rashin lafiya baka faɗa min ba ai da naxo na duba ka, ko ban zo ba nasan Rukayya xata wakilce ni gaskiya kayi babban laifi kuma baxan hakura ba” +

Tsugunnawa yayi”ranki dade na san nayi laifi a yi hakuri kada a hukunta ni” murmushi nayi wanda bai kai zuci ba “baxan hakura ba har sai kayi min tsallen kwado” dariya muka saka gaba daya Rukayya ce tace “baza a yi haka ba tunda ya fadi uzurinsa shikenan” mun ɗan yi barkwanci sosai da shi kasancewar sa mutum mai saukin kai, kuma yana da nishadi da sakin fuska. Ya jiki muka yi masa, sannan na faɗa masa yadda nayi kewarsa amsa min yayi da “Na warware, nima nayi kewarki sosai ba don uzurin rashin lafiya ba da kullum sau biyu xaki ganni.
Murmushi nayi “kada kasa a ce tun yanzu ka xama tace” rausayar da kansa yayi “Ai dama na xama ni kan kice ne ma ba tace ba, indai a wajen kyautata miki ne na yarda a kirani da kowane suna, idan kina da lokaci yau zan shigo”

Gabana ne ya fadi saboda bana so yaxo Baba ya yanke mana hukunci karshe ya raba ni da shi ya janyo min asara, shirun da yaji nayi ne ya sanya jikinsa sanyi, cikin Siririyar muryarsa yake min magana “ko dai bakya so naxo ne Sa’adatu, idan akwai wata matsalar ki fada min, don na san yadda zan yi na shawo kanta”

Gargixa masa kai nayi alamar babu komai, sauke ajiyar xuciya yayi tare da furzar da numfashi mai zafi “shikenan Allah yasa abinda kika fada min haka ne” eh nace ai kasan baxan faɗa maka abinda yake ba dai-dai ba
sallama muka yi da shi sai da ya rako mu daf da layinmu sannan ya juya.
Ko da muka koma gida innah bata dawo ba, rashin dawowar innah ba ƙaramin damuwa ya jefa ni ba, muna cikin wannan halin naji maganar Baba sai a lokacin na san yana gidan, cike da fargaba da rashin sanin yadda xan tunkare shi da abinda malam Jibo ya fada min na tashi jikina babu ƙarfi, tunda na fito naga su A’isha da zaliha suna ta tuntsura dariya, wacce ni kaina na kasa gane fassararta wucewa nayi na kyale su suna ta haukansu.
A dakinsa na tarar da shi yana cin abinci, da sallama na shiga ina ganin haka na juya saboda na san indai yana cin abinci baya saurarar duk wanda yazo wajensa.

Juyawar da nayi ne yasa shi kwala min kira, jikina na rawa na koma “gani Baba” cikin ɓaci rai ya fara min magana
“Lafiya naga kin zo kuma kin juya wane munafuncin ne kuma ya kawo ki da har yasa kika juya?”

Kaina a ƙasa na fara magana “Dama malam Jibo ne ya kira ni daxu da naje makaranta yace idan naxo gida na tambaye ka maganar da ku ka yi”
Ajiyar zuciya yayi “ina da dama da ikon da zan yi duk abinda naga dama a kanki, bana buƙatar shawara da ke ko wani abu da yayi kama da haka, kije idan da rai da lafiya zaki ga amsar tambayar ki a aikace

Ji nayi kafafuna sun kasa ɗaukana jiri jiri na shirin dibana ya fadar da ni a kasa, don haka na nemi guri na tsaya. Tsawar da ya daka min ce ta dawo min da ni hankalina jikina “fice min daga daki munafukar banxa munafukar wofi kin tsaya kina sand’a kamar mutuniyar kirki” +

Da sauri na fita na bar masa dakin, abinda na kasa ganewa shi ne mai baba yake nufi da xan ga abinda yake nufi da idona idan muna da rai da lafiya??????Da kyar na ja kafa na shiga daki, ina zuwa na zube a ƙasa, mikewa Rukayya tayi tare da tambayata “ya faɗa miki abinda maganar malam ke nufi”? Cike da damuwa na yi mata bayanin yadda muka yi da shi, haɗa kai muka yi muna kuka mai cike da ban tausayi ni ina tausayawa kaina ban san ma’anar abinda Baba yake nufi ba, Rukayya na tausaya min halin da xan tsinci kaina a ciki. Har yamma innah bata dawo ba wannan dalilin ne ya ƙara saka ni a tashin hankali sbd tunda nake da ita ban taɓa ganin taje unguwar ta kai yammaci ba iyakar dadewarta la’asar, hankalina ne ya ƙara tashi ga damuwar Baba ga damuwar tafiyar innah, ga shi babu waya a hannuna ballantana na kira gidan da taje. Mayar da kallona nayi ga Rukayya “Ni fa na fara damuwa dadewar nan ta innah tayi yawa” cike da kulawa take min magana “Nima haka wlh magana ne kawai ban yi ba kada na sake ji miki wani ciwo a xuciyarki, amma tashi mu je gidanmu ki xauna zuwa anjima sai mu dawo mu duba ko ta dawo” tashi nayi na dakko hijabi na saka muka tafi.
A cikin damuwa ummansu ta ganmu tambayar mu halin da muke ciki tayi, ban iya yi mata magana ba saboda na san ina farawa xan iya fashewa da kuka sai Rukayya ce ta faɗa mata abinda ke shirin faruwa da ni. Kwantar min da xuciya tayi da kalamai masu ratsa jiki da sanyaya ruhin ɗan Adam musamman idan yana cikin damuwa, abinci ta xuba mana bai fi cokali uku nayi ba na ajiye saboda damuwa ta cika cikina.
Sai da muka yi sallar magariba sannan muka dawo gida, abin mamaki a kulle na sake ganin dakin innah tashin hankali ne ya bayyana a fuskata sai naji kamar na fashe da kuka amma sai na daure saboda bana so su A’isha su gane halin da nake ciki, jan hannun Rukayya nayi muka koma soro saboda baxan iya jure xama a dakin innah ba, ba tare da tana cikin dakin ba. Zama muka yi shiru babu mai cewa kowa komai sai dai tunani da kukan zuci da nake yi.
Sallamar ya salim ce ta dawo da ni hayyacina, haska mu yayi da wayarsa “Au dama ku ne a zaune ai na zaci aljanu ne” dariya muka saka gaba daya nice nayi ƙarfin halin yin magana “Haba ya Salim aljanu xaka gani a haka” murmushi yayi “Eh mana idan ba aljani ba waye xai xauna a duhu shi kadai”
“Akwai abinda muke jira shi yasa ka ganmu a nan” kallona yayi yana murmushi “ko dai mutumin ne zai dawo” girgiza kaina nayi “ba shi bane innah nake jira ta tafi unguwa tun safe bata dawo ba” ɗan hararata yayi ” ka ji ta da wani zance wai innah kike jira banda abinki innah xata bata ne, xata dawo duk inda ta tafi watakila ma tana kan hanya, ke dai naga yadda xaki yi idan aurenki yaxo lokacin da xaki rabu da innah”
Kwalla naji na ƙoƙarin fito min da sauri na mayar da ita “Ba don aure sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam bane da nace baxan yi ba saboda rabuwa da innah a rayuwata ba ƙaramin tashin hankali bane” ji nayi mahaifiyarsa ta kwala masa kira, bai amsa ba sai da muka gama magana sannan ya amsa mata da yana zuwa.
Duk da cewa muna ɗan nesa da juna amma sai da na jiyo sautin muryarta tana yi masa faɗa “kai wane irin yaro ne mara jin magana, ba na raba ka da Sa’a ba, me kuma kaje kana ce mata? tun wuri ka daina kula yarinyar nan kafin nayi maka baki” shi dai shiru naji yayi mata bai ce komai ba ni kuwa a xuciyata nace “yau na janyowa ya salim faɗa” Ni kaina ina so na daina saurar shi idan ya kula ni, sai dai baxan iya yin hakan ba saboda yadda yake bani kulawa da yadda yake damuwa da dukkan abinda ya dame ni.
Muna a wannan halin muka ji sallamar innah da sauri na tashi na rungume ta ina yi mata oyoyo ita ma Rukayya sannu da zuwa tayi mata, sai dai abinda ya bani mamaki tare da kakarta gwaggo Abu suke tafe, da alama ita ce ta rakota gaisheta muka yi da sakin fuska ta amsa mana, bin su muka yi gaba daya muka shiga ciki, ƙoƙarin bude dakin nake yi xamu shiga, muna gama buɗe musu dakin gwaggo Abu ta dakatar da mu “ku tsaya a nan na fito sai ku shiga” bin umarninta muka yi muka zauna a bakin kofa, abinda na fahimta akwai maganar da zasu yi wacce basa so mu ji.Cikin siririyar murya take yiwa innah magana “kiyi hakuri mero, wannan dakin shi ne sutturar ki duk abinda za a yi miki ki kawar da kai kiyi hakuri, idan kika ce kin yi fushi kin tafi kin bar gidan nan wane hali kike so ‘yarki ta samu kanta, kin san dai halin malam Salisu sarai baxai bari ki tafar masa da ‘ya ba, dan Allah kiyi hakuri da dukkan abinda zaki ji ko ki gani wata rana sai labari, basu isa su yi muku abinda Allah bai muku ba, komai kika ga ya samu bawa mukaddari ne sannan ki manta da Maganar mutumin nan zamu yi iya bakin kokarinmu wajen hana abin sai dai idan kuma ya fi karfinmu”
+

Godiya innah tayi mata, sai da ta raka gwaggo Abu har bakin kofa sannan ta dawo, abinda na fahimta a Maganar da suke yi kamar yaji innah tayi aka dawo da ita.
Daki muka shiga tambayarta na fara yi “Innah ina kika tafi kika barni ina ta tunani duk duniya tayi min zafi” ƙoƙarin mayar da damuwarta tayi don kada na gane halin da take ciki amma hakan ya gagara don kallo daya xaka yi mata ka gane akwai damuwa mai yawa a tattare da ita. “Yau na sha yawo ne a garin nan Sa’adatu shi yasa na dade ban dawo ba, kin san na dade ban fita ba to akwai gaishe-gaishen marasa lafiya da naje da gaisuwar mutuwa da yan barke-barke shi yasa na dade”
Sannu da zuwa muka yi mata, har na bude baki xan tambayeta dalilin rakiyar da gwaggo Abu tayi mata sai kuma na fasa, saboda bana so na ƙara tayar mata da wani tabo a xuciyarta, sai bayan sallar isha’i Rukayya ta tafi gida yau da wuri muka kwanta bacci saboda mu yi yaƙi da damuwar da ta addabe mu.

Yau ya kama Alhamis ba makaranta don haka ban tashi da wuri ba sai da rana ta ɗaga sosai kasancewar garin akwai dan sanyi, ita ma Innah baccinta take yi, daga gidansu Rukayya aka aiko mana da abin karin kumallo sai da muka watstsake sosai muka karya. Muna cikin cin abincin na jefawa innah tambaya “innah wai me Baba yake nufi dani? naje makaranta ne jiya sai malam jibo yace naxo na tambayi Baba a kan maganar da yaje masa da ita, da na dawo na tambaye shi ya nuna min cewa duk hukuncin da ya yanke a kaina ya yanku sai dai nayi hakuri dan Allah me yake nufi da hakan, na tambayi kaina na kasa gane amsar abinda suke nufi, na san duk abinda yake faruwa zaki iya sani kuma baxa ki boye min ba”?
Ina kallon idanun innah kamar xasu xubar da hawaye, hadiye miyan takaici tayi gami da cewa “Babu komai Sa’adatu kawai xance ne irin nasa so yake ya tayar mana da hankali”

Kuka na fara yi “Allah innah da gaske yake, lokacin da yake Maganar babu wasa a fuskar shi, shima malam din haka sannan malam Jibo yana magana yana murmushi, a jiyan kuma naji innah salamatu tana habaici maganganunta sun yi kama da abinda malam da Baba suka fada min kada fa a ce shi Baba xai aura min”
Saurin dakatar da ni tayi ” ya kike irin wannan maganar Sa’adatu bana so na sake jin irin wannan daga gare ki, kin san haka baxai faru ba insha Allah”Sosai nake kuka “wlh Innah indai shi aka ce za a aura min baxan xauna ba kuma sai yaga salo salo na rashin mutunci, saboda an raina mu duk ya’yan gidan nan ni kadai aka tsana wa aka taɓa yiwa irin abinda ake mana, wannan karon baxan iya yiwa Baba biyayya ba sai dai idan a kore mu”
Shiru Innah tayi tana saurarona nasan bata taba tunanin fitowar wadannan xantukan daga gare ni ba. Rarrashina ta shiga yi har sai da xuciyata tayi sanyi. +

Yau muka yi da Izuddeen xai kawo min ziyara tun yamma na fara shiryawa saboda na kosa yazo a yi duk wacce za a yi yanxu tsoron kowa ya fita a xuciyata, Bayan sallar magariba na cigaba da jira shiru bai zo ba, sai daf da isha’i aka aiko yaro ana kirana, ban ja lokaci ba na fita shimfida nayi masa a inda ya xauna ran nan, gaisawa muka yi muka fara hirar mu ta masoya, cike da nishadi muke maganar mu kamar babu wata damuwa a raina, sai da hirar mu tayi nisa sannan ya miko min wata leda, “karbi wannan Sa’adatu” makale kafada nayi alamar baxan karba ba sake miko min yayi “ki karba kiga abinda ke ciki” ban yi masa gardama ba na karba ina budewa waya na gani sabuwa fil a kwalinta kirar infinex, da sauri na bude ido ” wannan wayar ta min girma ka barta idan kana da karama ka bani” a xuciyata nace idan ka bani wannan ai sai a ce karuwancin nake yi da gaske, muna cikin duba wayar muka ji mutum a kanmu

Daga idon da zamu yi naga Baba yana mana wani kallo, cike da ladabi Izuddeen ya gaishe shi, harara ya kwada masa bai kuma amsa gaisuwar ba.

Cikin fushi ya nuna Izuddeen da hannu “Dan ubanka dama kaina kake zuwa har gida kana lalata min yarinya”
Kallon mamaki Izuddeen ya bi shi da shi saboda bai san me yake nufi da abinda yake fada ba, cikin ladabi ya sunkuya “wlh Baba ba da niyyar yaudarar Sa’adatu naxo ba naxo ne don na aureta” nuna shi yayi da hannu aurenta xaka yi amma kaxo kana lalata ta da Abin duniya salon ta bijirewa iyayenta ko? Irinku ne masu hurewa yaran Mutane kunne har gida, tashi ka fita ka bar min gida kafin ranka ya ɓaci kada na sake ganinka a nan, ke kuma xaki zo ki same ni”

Wucewa yayi ya barni a tsugunne ina sharar hawaye har Izuddeen ya fita yana waiwaye na.A bakin tebur ɗin mai shayin da ke saitin gidanmu ya tsaya yana hangena, kallo mai cike da soyayya da tausayawa yake min idanunsa sun yi jawur kamar zai fashe da kuka, sai da ya gama kallona tsaf sannan ya juya cikin tsananin ɓacin rai da damuwa.
Bai wuce gida ba saboda zafin da yake ji a ransa kai tsaye wajen abokinsa Kabir ya wuce, a Kofar gida ya same shi yana yana karkade machine dinsa da alama shirin tafiya wani wajen yake yi, yana ganinsa ya saki fuska “mutumina yau kuma kaine a dai-dai wannan lokacin, ai kuwa kaxo a dai-dai sai kayi min rakiya wajen madam don yau zuwa na musamman zan yi mata” shirun da yaga Izuddeen yayi masa ne ya tabbatar masa da ba lafiya ce ta kawo shi ba yanayinsa ya canja lokaci daya idonsa ya faɗa gashi yayi ja. Matsawa yayi kusa da shi yana tambayarsa “lafiya kuwa mutumina na ganka a haka, Allah yasa dai ba mutuniyar ce ta haɗa maka xafi ba” ya karasa magana yana dariya tunda dama Kabir gwanin zaulaya ne sun saba tsokanarka juna ya tsokane shi, shima ya tsokane shi haka suke yi.
Shiru yayi ya kasa magana saboda abinda ya cika masa zuciya.
Ganin yadda yake ne yasa yayi saurin gane ba lafiya ba saboda babu yadda za a yi ya tsokani Izuddeen ba tare da ya rama ba, amma yau sai bin sa kawai yake yi da ido.
Zaunar da shi yayi “me yake damunka Izuddeen ni fa ban saba ganinka a irin wannan yanayin ba faɗa min damuwarka mana”
Wani daci yaji ya taso masa daga kasan makoshinsa a hankali ya hadiye miyan takaici, a gintse ya amsa da “ina cikin tashin hankali Kabir mu shiga daga ciki na faɗa maka”
Tashi suka yi suka shiga soro wanda a nan dakin Kabir yake.
Furzar da numfashi yayi mai cike da takaici “ka san yarinyar da nake baka labarin na haɗu da ita kwanaki?” Cikin kulawa Kabir ya amsa masa da “Eh”
Shiru yayi na wasu yan mintuna sannan ya cigaba da magana.
“Tun kafin na furta ina sonta nake ganinta a hanyar xuwanta makaranta, na yaba da hankali da nutsuwar yarinyar wannan dalilin yasa nake matukar sonta har na fara zuwa wajenta hira mun fara fahimtar juna, sai kuma babanta ya bijiro min da wasu abubuwa wanda na kasa gane inda ya dosa, yanzu ma kokarin da yake yi shi ne neman ya raba ni da ita, yanzu haka ma wajenta naje shi ne yayi min korar kare, ban sani ba ko bai shirya aurar da ita bane nayi masa katsalandan”
Cikin nuna damuwa da halin da abokinsa yake ciki ya fara magana.
“Subhanallahi to me yake nufi, Ni dai nasan gaba da baya ba kada wani abin kunya ko makusa abokina, kuma dai-dai gwargwado kana da rufin asirin da xaka iya riƙe yarinyar, sannan iyayenmu mutanen kirki ne ba su da wata matsala, ka cancanci a soka na san duk wani uban da kaje neman auren yarsa xai yi alfahari da hakan, amma bamu sani ba ko kuma miji yayi mata shi yasa ya dakatar da kai”

Saurin girgiza kai Izuddeen yayi, “gaskiya bana zaton an yi mata miji don tun farkon haduwa ta da ita bata faɗa min cewa akwai wata magana a kanta ba, nafi tsammanin akwai abinda yarinyar take boye min”
“Ok ba mamaki amma shawarar da zan baka, ka fadawa Baba kana sonta a aika a nemar maka izinin zuwa zance, ina ganin wannan rashin aikawar ne ya ɗan baka matsala”
Girgiza masa kai kawai Izuddeen yayi sbd yanxu Maganar ma wahala take masa tunanin yadda za a ce an raba shi da Sa’adatu yake yi, ya san har abada baxai taɓa jurewa ba, Kabir ne yake ta yi masa hira don hankalinsa ya kwanta shi dai jin shi kawai yake amma zuciyar shi da hankalinsa yana wani wajen daban, har gida Kabir ya kai shi a machine sbd baxai iya tafiya da kanshi ba kasancewar baya jin karfin jikinshi.

*************
Na fi rabin hour a zaune ina zulumi, ni ban shiga gida ba ni kuma ban tashi daga inda nake ba, tunanin inda zan ajiye wayar da ya bani nake yi saboda bana so a kwace masa wayarsa karshe nasan ba nice xan mora ba, a gabana xa a yi wa su A’isha kyautarta ni kuma a bar ni da kunar zuciya. A bayan kaure na ajiyeta da niyyar idan kowa ya shiga daki na dawo na ɗauka.
Tunda na doso kai bakin kofa naji an cika tsakar gida ana ta maganganu da dukkan alamu zuwana ake jira, komawa soro nayi na zauna a raina nace “sai kun gaji da xama xan shigo dan baxan xo a kusan cinye namana danye ba” komawa nayi na xauna abuna, shirun da suka ji yayi yawa ne yasa Baba xuwa da kansa kirana. +

“Kina nufin baxa ki shigo bane Sa’a ko kuma binsa xaki yi ku tafi, ina nan ina jiranki kixo ko kuma ranki ya ɓaci”
Daurewa nayi na miƙe idanuna suna ƙasa na kasa dagowa a hankali nake jan ƙafa har na shiga ciki, idanun kowa ne ya dawo kaina ana yi min wani kallo mai ɗauke da fassarori masu yawa, cikin kakkausar murya Baba ya fara yi min magana.
“Tsugunna nan zan tsaga miki sharudda a gaban yan uwanki saboda ina so su zama shaida ko zuwa gaba” ban yi gardama ba na xauna tare da sunkuyar da kaina ina wasa da yatsun kafata, addu’a na shiga yi Allah ya bani damar daurewa kada makiyana su ga kukana.
“Wannan shi ne maganata ta ƙarshe da ke kada na sake ganin wannan yaron a gidan nan idan ba haka ba kuma zaki haɗu da fushina daga ke har mahaifiyar ki, kin ji abinda na fada miki ko” gyada kaina nayi alamar eh.

Innah salamatu ce ta amsa da “kai kake bata bakinka malam amma ba saurara abinda take yi xata yi ba, sau nawa kasa doka aka karya maka, shawara daya xan baka kaje ka dakatar da yaron nan har gida, ko kuma ka bani dama ni naje da kaina tunda kai naga bori kake yi da sanyin jiki”

Maganar innah ba ƙaramin tokare min xuciyata tayi ba, na san matuƙar taje gidan su Izuddeen Maganar aurenmu ta gama lalacewa har abada, har na gwammace zuwan Baba a kan nata saboda shi idan suka gyara zancen xai iya amincewa da aurenmu.
Cikin gamsuwa da abinda ta faɗa ya jinjina kai
“Kwarai kuwa xuwan naki ma ya fi muhimmanci tunda kin san gidan, kuma ke xaki samu mahaifiyarsa kai tsaye ki fada mata kudurinsa na son lalata mana yarmu. Ni kuwa ba lallai ne na samu babansa ba, don haka gobe da safe kije ki fada musu su katange dansu ni ma zan bawa yata kariya duk abinda ya biyo baya kuma kada su zarge ni su zargi kansu”

Farin ciki ne ya bayyana a fuskarta taji dadin hukuncin da aka yanke min, cikin kissa take magana “Amma malam ina ganin har da rashin abincin nan da ba a bata, shi ne yasa take so ta jefa kanta a rayuwar da ba tata ba, ina roko a dawo musu da kwanon su ita da borar uwarta ko sa ji sassauci, idan aka tsare mata cikinta za a toshe wata kafar barnar tunda dama da yunwa ake fakewa ake wata lalatar”

Shiru yayi na dan lokaci sannan yayi magana “to shikenan tunda kin amince ki cigaba da basu amma ki tabbatar sai kowa ya koshi”

Amsa masa tayi da “To” har ya juya xai tafi ta kira shi.
“Au malam baka ji ba” da rawar jiki ya dawo “Da akwai abinda kika manta ne baki fada ba?”

Cike da makirci tace “Maganar bawan Allahn nan ya kamata a taso da ita tunda da kanka kaje ka same shi ka faɗa masa damuwarka, kuma ya yarda ya amince, amma kuma har yanzu baka sake cewa komai ba kamar wanda aka daurewa baki, kaga wannan ma wata hanya ce da xata sa a toshe kafar barna tunda dai ta nuna aure take so, kuma hakkinka ne dama ka aurar da ita don haka tunda akwai miji a kasa me ake jira sai magana kawai”
Sauke ajiyar zuciya yayi “ina sane da wannan maganar akwai abinda nake jira ne shi yasa kika ji nayi shiru amma ba mantawa nayi ba”

Juyowa yayi kaina “Au dama tun daxu kina nan munafuka, kin sa mutane a gaba kina zare mana ido wato duk maganar da za a yi sai kin ji ko, tashi maza ki bace min da gani kafin na karya munafukar kafar taki”Tashi nayi na shiga daki a xaune na tarar da innah tana karanta littafin addu’o’i babu wani alamar damuwa a tare da ita, duk da cewa na san duk abinda aka taji tattauna a kunnenta, sannan ta san da dukkan abinda ake kulla min, gefenta na samu na zauna nima ƙoƙarin kin nuna mata damuwata nayi, sai da naga alamar ba tada niyyar ce min komai sannan nayi magana. +

“Innah wai duk abin nan da ya faru baki ji bane naga kina ta karatu kamar baki san anyi wani abu ba, naga ma kamar baki damu ba”.
Fuskarta mai cike da kamala ta dago “to me zan ce Sa’adatu, wanda yake da Allah me xai dame shi, ina ganin addu’a ce kawai maganin abinda yake faruwa a gidan nan, ni da Allah na dogara kuma nasan xai isar min, duk abinda suke yi na barsu da Allah idan ba yau akwai gobe, kema abin ya daina damunki idan mijinki ne duk makircin da zasu shirya sai ya rushe kin aure shi, shi yasa abin nasu ma ya daina damuna”

Tawakkali da nutsuwar innata da yadda take samun nutsuwa a duk lokacin da masifa ta same ta ba ƙaramin karfafa min gwiwa yake yi ba, wannan Dalilin ya sanya na daina saka kaina a damuwa, kallon duk abinda suke mana nake yi a matsayin film wata rana dole zai kare.

Ban sake yin magana ba sai da naga ta idar da addu’ar da take yi saboda bana so na katse mata abinda take yi, cike da ladabi nace “innah waya fa ya bani shi ne abinda ya janyo wannan kace nace din, wai Baba da kansa yake cewa lalatani yayi sannan ya bani” Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, rarrashina innah take yi
“Duk naji abinda suke faɗa Allah ya fi mu sanin halinmu, kuma zai mana hisabi a kan abinda suke fada shi yasa ban fito na kare ki ba, saboda nasan ko na faɗa a banxa ba yarda xasu yi ba, cewa zasu yi ni na yarda kiyi, don haka ki kyale su Allah baya bacci, yanzu ina wayar”
Cikin kukan na amsa mata da tana bayan kyauren soro.

Da sauri ta dube ni, “kika ajiye masa waya a soro salon a je a sace, yi maza kije ki dakko” tashi nayi na tafi naje na bude bayan kyauren abin mamaki banga waya ba, hankalina ne ya tashi na rika duba lungu da sako amma babu waya babu dalilinta

Da gudu na shigo gida na karbi touch light na haska ko idona ne bai ga dai-dai ba nan ma dai shiru babu waya, da kuka naxo nake sanarwa innah ban ga waya ba.
Ita ma hankalinta ne ya tashi sosai saboda kada mu je Izuddeen yace bai san xance ba sai mun biya shi waya, ga shi ba wani na bawa ajiya ba ballantana na tunkare shi nace ya bani.

Mun fi 2hours muna neman waya ba labarinta, mu ba abin mu yiwa jama’ar gida cigiya ba mu janyowa kanmu gori.

Bayan Asubah ma sai da na sake dubawa ban ganta ba, kuka sosai na riƙa yi ina addu’ar Allah ya bayyana wanda ya sace ta, innah ma taya ni ta riƙa yi.Gari na wayewa na tafi gidan su Rukayya tunda ta ganni da sassafe haka ta san ba kalau ba, tana ganina ta miƙe tana tambayata “kada dai kice wani abin ne ya sake faruwa Sa’adatu”
cikin kuka nake bata labarin zuwan Izuddeen da labarin batan wayar da ya bani, tayi bakin cikin batar wayar sosai, ummansu ce ta bani kudi muka siyo alewa tace mu kai makaranta a yi sadaka a roki Allah ya bayyanata, malamin ƙananan yara na samu na bawa na fada masa a kan bukatar da nake so a yi min addu’a Allah ya bayyana barawon da ya saci wayar, tun kafin na bar gurin aka sa yaran suka fara hasbunallahu abinka da yara sun ga alawa sai ƙara bada himma suke sosai.

Mun juya xamu tafi kenan naji an kirani ban amsa ba sai da na juya don naga mai kirana, malam Jibo ne ya leko da kansa daga rumfar da yake karatu, nuni yayi min da hannu naxo, kallon Rukayya nayi tare da cewa “kixo ki raka ni” kafewa tayi a kan baxa tayi min rakiya ba, kuma nima baxan je ba, ganin yadda ya kafe ta da ido ne yasa ta sake ni naje kiran.

Raina a haɗe naje yau ba irin tsugunnon da na saba nayi masa ba, a takaice nace ina “kwana”
Yana murmushinsa mai cike da ban haushi ya amsa.
Ina gama gaishe shi na miƙe na juya baya zan tafi ya kira sunana “sauri kike haka ne Sa’adatu daga gaisuwa sai tafiya, me yasa yau baku zo makaranta ba, naga kwana biyun nan kuna wasa da hadda bakwa bada himma irin da” a gintse nace “ina da abin yi ne shi yasa”
Ina gama magana na fita ina ji yana kirana nayi banxa da shi na tafi.

Ko da na dawo babu Rukayya babu dalilinta da alama fushi tayi shi yasa ta tafi ta kyale ni, a hanya naci karo da ita ta rabe jikin wani gini tana jirana, bi na tayi da harara duk maganar da nayi mata bata amsa ba sai can tayi min magana cikin fada “wlh duk kece kike bawa mutumin nan kofar da zai raina ki me xai hada ki magana da shi, kawai don ya kiraki sai ki bi shi kamar wata jela, idan bakya saurarsa ko shi ne shugaban marasa zuciya dole ya hakura ya kyale ki, wannan sanyin naki idan baki daina shi ba bazai haifar miki da ɗa mai ido ba, idan baki ɗauki mataki ba ke zai zo addaba ba ni ba, shawara nake baki tun wuri kiyi maganinsa don naga ke kamar ta ruwan sanyi kike binsa”
Mayar da ajiyar zuciya nayi ina nazarin maganganunta wanda suke da tasiri a gare ni, shiru nayi har muka kusan zuwa gida tana min faɗa. komawa gidansu muka yi muka sanar da umma cewa mun bayar har an fara addu’a.

**************

Yau Izuddeen a makare ya tashi tun bayan da yayi sallar asuba ya kwanta ba shi ya farka ba sai wajen sha biyu saura. Saboda jikinsa ba ƙarfi zafin abinda Baban Sa’adatu yayi masa ne yake taɓa xuciyarsa, shi yasa ya zabi yayi ta bacci ko xuciyarsa xata yi sanyi, a hankali ya mike daga shimfidarsa banɗaki ya shiga yayi brush ya dan watsa ruwa, bayan ya fito ya fesa turare kala-kala masu daɗin kamshi saboda shi ma’abocin tsafta ne da son kamshi shi yasa bai fiye fesa turare kala ɗaya ba, sanya farar jallabiya yayi, sai da ya kulle dakinsa sannan ya nufi hanyar shiga gida don ya gaisa da mahaifansa, tunda yau tun safe basu ji motsinsa ba zasu iya shiga damuwa idan basu ganshi ba musamman Mama da yake dan lelenta.

A bakin kofa ya ci karo da wata mata wacce baxai iya tantance ko wace ce ita ba, sai dai abinda ya bashi mamaki ganin kwalin wayar da ya kaiwa Sa’adatu jiya a hannunta, tambayar kansa ya shiga yi “me kuma ya haɗa wannan matar da kwalin wayar Sa’adatu, ko dai ita ce mahaifiyarta, idan kuwa haka ne ya san duk shirinsa sai an tarwatsa masa, don ya fuskanci kamar iyayen Sa’adatun basa son alakar shi da ita”kai tsaye yaga ta shiga cikin gidansu wannan ya tabbatar masa da cewa tuntuni dama ta san gidan, don bata tsaya tambayarsa hanyar da xata sadata da wajen iyayensu ba, kasancewar gidan su Izuddeen babban gida ne ɓangaren kowa daban. +

Ɓangaren mama yaga ta nufa, dalilin da yaja hankalinsa kenan ya bi bayanta saboda ya san kowace ce daga gidan su Sa’adatu aka turo ta.
Ganin ta shiga dakin mama ne yasa ya dawo da baya tunda ko menene indai maganar ta shafe shi sai yaji, dakinsa ya koma ya zauna ya cigaba da latsa wayarsa yana Game kamar yadda ya saba
Da sallama ta shiga dakin a zaune ta tarar da mama saboda a lokacin ta idar da sallar walha tana addu’a, sai da ta shafa sannan ta juyo gareta da karamci ta karɓe ta gami da yi mata sannu da zuwa, cikin farin ciki ta amsa.
Bayan sun gama gaisawa mama ta mayar da kallonta gareta da cewa “kiyi hakuri Hajiya ban wanye da ke ba, da yake jama’ar tamu da yawa”
Sunkuyar da kai kasa tayi sannan ta fara magana “La ba komai Hajiya ai komai sai da dalili, Ni sunana Hajiya salamatu a nan makotanku muke, nice matar malam Salisu”
Murmushi Mama tayi “Ayya sai kuma da kika yi bayani na gane ki, kin san an dade ba a hadu ba”

“Wlh kam haduwa tayi wuya kin san da yake komai sai Allah ya nufa” Bayan sun gama gaisuwar yaushe gamo ta kalli mama
jin daɗin yadda tace ta gane ta ne yasa ta saki jikinta ta fara bayani.
“Dama na zo ne a kan Maganar danku Izuddeen da yaje neman auran yarmu” cikin farin ciki tace “Oh Allah sarki kwarai kuwa ya faɗa min da har muna shirin aikowa ma kwanan nan tunda ya gama karatu me ake jira sai aure kawai”
Rausayar da kai innah salamatu tayi “Hmm da kin san Abinda Ya kawo ni da baki fadi haka ba”
Cikin rashin fahimtar abinda take faɗa ta dubeta, “Ban fahince ki ba Hajiya wani abin ne ya faru” jinjina kai tayi kwarai kuwa hakan ne ma yasa mahaifinta yace na taso da kaina na faɗa muku abinda ke faruwa don ku kula”
Gyara xama mama tayi, a zuciyarta addu’a take Allah yasa dai ba wata maganar Izuddeen ya dakko musu ba, duk da cewa ta san ɗan nata kamili ne ba a taɓa kama shi da wani laifi ba, amma ta san sharrin zuciya ba tada Kashi ko ita ce, ta ja shi ya aikata laifi, jefa mata tambaya mama tayi “wani abin Izuddeen dina yayi”
Jinjina kai innah salamatu tayi “A’a babu abinda yayi amma mun zo mu ankarar da ku ne, yarinyar da yake nema ‘yata ce amma ba ni ce mahaifiyarta ba, amma ni nake rukonta duk halinta na sani yarinyar ba tada dabi’u masu kyau, an zubar mata da ciki ya kai sau biyar, jiya yaron yazo xance mahaifinta da kansa ya kamata tana ƙoƙarin lalata shi, kinga fitina tun tana karama ake maganinta shi yasa Babanta da kansa yace naxo na faɗa muku ku katange danku ku raba ta da shi tun kafin ta lalata masa kuruciya, saboda bai kamata a ce gida kamar wannan da ku ka yi shuhura a arxiki da ilimi a ce an auro muku mara tarbiyya ba, kinga abu bai yi kyau ba kenan” tunda ta fara fada mata wannan maganar mama ta kasa magana duk hankalinta ya tashi, yanxu a ce duk tarbiyyar da suka bawa Izuddeen sakayyar da xai musu kenan.
Miƙa mata ledar wayar da ya bawa Sa’adatu jiya tayi ” kinga Babbar shaida ko, don kada ma ki zaci ko sharri aka yi musu, jin dadin abinda tayi masa ne yasa yake bata kyautuka daban-daban, amma kada kiga laifin danki domin janye hankalinsa tayi har ya biye mata kuma kin san dai yadda mace take da tasiri ga da namiji, duk girmansa duk iliminsa duk abinda yake ji da shi cikin ƙananan mintuna zata gama da tunaninsa, shawara ki jawo danki a jiki ki nema masa yarinya ta mutunci ,ko mu a nan gidan namu idan yana so akwai yan mata kyawawa masu tarbiyya sai yaxo ya nemi wata” tana gama fadin Abinda Ya kawota ta mike.
Duk gwiwoyin mama sun yi sanyi ta kasa magana ji take kamar ƙasa baxa ta dauke ta ba, tunda suke neman aure basu taɓa cin karo da matsala irin wannan ba sai a kan Izuddeen, sun aurar da yaya sama da sha Biyar amma babu wadda aka taɓa zuwa har gida aka fadi aibunta sai ta Izuddeen.Sallama innah salamatu tayi mata, cike da farin ciki ta bar gidan, har mama ta kama hanyar shiga dakin Izuddeen ta fasa saboda maganganun da aka faɗa mata suna buƙatar nazari
dakinta ta koma ta kwanta rigingine idanunta sun yi ja saboda ɓacin rai, ta fahimci a maganganun innah salamatu akwai karya amma kuma wani abin gaskiya ta faɗa, tunda ga shaidar waya ta nuna, sai dai abinda ya bata tsoro a maganarta da tace idan yana bukatar aure yaje ya nema a gidan su, ta fuskanci kamar wata manakisar ake shirin kullawa yarinyar, sai dai har Yanzu ta kasa amincewa ɗari bisa ɗari cewa ba lalata suke da Izuddeen ba duk da cewa ta san halin danta amma ba a shedar dan yau.
Tunani ta rika yi a kan ta samu mahaifinsa ta faɗa masa ko kuma ta fara tunkarar Izuddeen da maganar saboda bata so ta bata masa suna a idon yan uwansa. +

*******
A Hanyar mu ta komawa gida muka ci karo da innah Salamatu bin mu tayi da wani matsiyacin kallo, sannu da zuwa muka yi mata amma ko yan kallo bamu isheta ba, a soro suka ci karo da Baba shi ma sannu da zuwa yayi mata tare da cewa “Har kin dawo da wuri haka kin mayar musu da wayar su dai ko” kallon kallo muka rika yi ni da Rukayya dama su suka ɗauki wayar?
Cikin kissa tace “naje mun gama magana da su sun yarda da dukkan abinda na fada musu kuma sun ce xasu katange dansu” tana gama faɗa ta juyo kaina tana bi na da kallo mai cike da tsana.

Da gudu na shiga gida na fada dakin innah ina kuka “innah tashi kiji ashe innah salamatu ce ta sace min wayar nan mayar gidan su Izuddeen, sannan ta fadi karya da gaskiya a kaina, na shiga uku innah me matar nan take nufi da ni” A gigice innah ta tashi sai a lokacin na lura da bacci take, innalillahi wa inna ilaihi raji’un naji tana maimaitawa “ALLAH kayi mana maganin abinda ya fi karfinmu” kuka mai cin rai nake yi ita ma Rukayya haka, innah sai faman rarrashi take yi tana janyo mana hadisai da ayoyi masu magana a kan hakuri da yarda da kaddara da kyar ta samu kanmu muka yi shiru.





Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *