TSANANI
CHAPTER 5
Yau kusan satina ɗaya a gidan Adda saratu rayuwa nake mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali babu wani abu da ke damun xuciyata, sbd Adda saratu mace ce mai kirki babu wani abu mara daɗi da take min ta ɗauke ni tamkar yar da ta haifa a cikinta, sai dai abu ɗaya da ke damuna shi ne yawan tunanin innata da nake yi a halin yanzu, sbd ban san halin da take ciki ba, tunda Adda saratu da kanta taje gidan namu don shaida mata cewa ina wajenta, sai aka ce mata an koreta daga gidan, ga rashin masoyina da aminiyata wanda ban san halin da suka kasance ba bayan tafiyata, ban san lokacin da zan daina kewarsu ba
Tsaye nake a kitchen ina mayar da kwanukan da na wanke, Adda saratu ce ta shigo “Sa’adatu anya kina so mu yi tafiyar nan kuwa, ki kalli agogo har ƙarfe ɗaya saura tayi” da sauri na duba agogon da ke nanne a kitchen din “ayya ban kula lokaci ya tafi haka ba bari nayi sauri na ƙarasa abinda nake tunda nayi wanka baxa mu bata lokaci ba” sauri nayi kammala abinda nake yi, har ga xuciyata bana son tafiyar nan saboda kada wani daga cikin ahalin gidanmu ya ganni ya fadawa Babana inda nake, amma tunda ta nuna min muhimmancin tafiyar sai na yarda , saboda xamu je ne mu duba inda inna take da kuma yanayin da take ciki, na san duk inda take hankalin ta na kaina.
Khadija da zainab muka bari a gidan kasancewar su yara masu nutsuwa, har mu dawo baxa a samu wata matsala ba.
Kai tsaye gidan kanwar mahaifiyar su innah muka nufa gwaggo Balaraba amma da gwaggo suke kiranta, saboda mun san shi kaɗai ne gidan da xata iya zuwa ta xauna, kasancewar ita kadai ta rage musu duk iyayensu sun ƙare, kuma duk wata matsala ita ce take kashe musu ita.
Da ƙarfin gwiwa nake tafiya na san yau xan ga innata farin cikin rayuwata, da sauri muka faɗa cikin gidan, gidan bangare-bangare ne, kusan duk ƴaƴanta idan sun tashi aure a gidan suke zama kaɗan ne suke fita waje su yi gini. bangaren gwaggo Balaraba muka nufa sai dai kash!!! Kofarta a kulle, don haka muka shiga wajen danta Abbas, tun daga nesa matarsa ta ganmu ta tarbe mu da farin cikinta, daki ta kaimu ta bamu lemo da abinci lemon kadai muka sha saboda mun ci abinci a gida, sai da muka ɗan taɓa hira take faɗa mana cewa gwaggo sun tafi kauye tare da innata, tambayarta Adda saratu tayi dalilin tafiyar tasu, a nan ta shaida mata cewa sun tafi ne a kan abinda yake faruwa da ni, kasancewar kusan kullum sai Babana ya zo yayi xage-xage a kan innah ta fito masa da ni ko kuma ya kaita ƙara, hakan yasa su tafiya don shaidawa magabatanta.
Tunani da tausayin innah ne ya kamani duk wannan abin ana yi mata ne saboda ni, don haka ya dace na nemo hanyar da zata rabu da wannan baƙin cikin na har abada, sbd tunda innah take a gidanmu lokaci kaɗan take farin ciki ragowar duk bakin ciki take yi, jikinmu babu ƙarfi muka koma gida.
Tunda na koma na shiga daki ina tunani da kuka, wane irin uba Allah ya bani da yake yi min wulakanci yake ƙoƙarin wulakanta mahaifiyata, yana iƙrarin yana sona amma ko kadan babu kaunata a xuciyarsa, tunda ga shi yana neman jefa rayuwata a halaka, gaba daya sha’awar zaman gidanmu ta fita a raina gara naje ko’ina nayi rayuwa a kan na xauna a gidanmu, amma kuma ina tunanin irin cin mutuncin da Babana xai yiwa innata a duk lokacin da ya duba yaga bana tare da shi, ko ina so ko bana so dole na koma indai ina son na samarwa mahaifiyata farin ciki.
Ban san lokacin da hawaye suka riƙa gangarowa daga idanuna ba, ina a wannan halin Adda saratu taxo ta same ni, cikin kulawa take min magana tare da bani hakuri a kan irin jarrabawar da nake fuskanta, ta kuma yi min alkawarin duk rintsi duk wuya baxa ta bari na koma gidanmu ba sai dai duk abinda xai faru ya faru.
*************
Baban Izuddeen ne a zaune gaban yan sanda suna tattaunawa dangane da abinda ake xargin Izuddeen din da shi, saboda yau har yayi sati daya babu wata kwakkwarar magana a kan xa a sake shi ko za a bada belinshi, shi yasa yau ya taso da kansa yaxo don jin inda aka kwana.
Yana zaune Baban Sa’adatu yaxo, da izza da rashin mutunci ya shigo wajen bayan sun gaisa da yan sanda ya mayar da kallonsa ga mahaifin Izuddeen, wani kwarjini da kimarsa ne suka kama shi bai san lokacin da ya zube kasa yana gaishe shi ba, su kansu yan sandan sai da suka yi mamakin hakan, mutumin da ya dau xafi a kan abinda ya faru amma yau shi ne da xubewa kasa yana gaishe da mahaifin wanda ake zargi.
Ba tare da bata lokaci ba aka fara magana daga ƙarshe aka cimma matsaya a kan xa a bada belin Izuddeen amma da sharadin nan da sati biyu idan ba a ga Sa’adatu ba za a sake cafke shi, fito da shi aka yi suka tafi gida tare da mahaifinsa.
Yan uwa da abokan Izuddeen ne suka taru don tabarsa kowa na tofa albarkacin bakinsa wasu su ce ya rabu da Sa’adatu tunda ba yar gwal bace, wasu su ce ya cigaba da sonta tunda ita ma tana kaunarsa, sai da ya shiga wanka ya fito sannan ya ci abinci ya shiga wajen iyayensa don ganawa da su.
A cike gidan su Sa’adatu yake da mutanen kauyen bankaura da kuma mutanen jarumawa, duk sun taho ne don jaje da kuma daura auren Sa’adatu wanda mahaifinta ya shaida musu za a daura shi da misalin karfe hudu na rana.
Baka jin komai sai tofin ala tsine da yiwa Sa’adatu habaici, wasu su ce bakin mahaifinta ne ya kamata wasu kuma su ce yawon bariki ta tafi.
Wasu daga cikin matan gidansu ne da waɗanda suka zo daga ƙauye, suka tafi gano dakin amarya don kai mata katifa da kuma shimfida mata leda.
Gida ne karami mai ɗauke da dakuna guda hudu falle d’ai-d’ai ragowar dakuna uku na sauran matansa ne, sai kuma daki daya wanda ya barwa Sa’adatu, kyan gidan zaman mace daya a hakan ma zata takura musamman idan tana da ya’ya, amma mata uku ne da kusan yaya ashirin da biyar suke rayuwa a cikin gidan kowane yaro a dakin mahaifiyarsa yake kwana, shi hoton naka ma ba shi da daki sai rabe-rabe da yake a dakin matansa, duk matar da take da kwana sai dai yaranta su kwana a shago shi kuma ya kwana a dakin, gaba ɗaya gidan yayi musu kaɗan rayuwar takura kawai suke yi, shi yasa gidan ba tsafta duk a jike ga tarin tsummokaran yara.
Sallama suka yi tare da tambayar matan gidan dakin amarya a yatsine suka amsa tare da mika musu mukullin dakin, daga gefe dakin Sa’adatu yake, sai kuma kitchen na langa-langa da yayi mata, shi kaɗai ne dakin da aka yiwa farar kasa sai faman jirwaye take alamar dakin ya dade bai ga fenti ba, kyauran dakin da tagar duk na katako ne, sai ka xura kafarka sosai sannan xaka iya shiga dakin idan baka yi da gaske ba xaka iya fasa baki, duk flastar da ke dakin ta cinye haka dai aka samu aka yi farar kasar ba tsiya ba arziki, ceiling din dakin ma na kwali ne banda uban duhu babu komai, kasancewar dakin tsohon daki ne ya dade a gine kuma daga lungu yake. A gaggauce suka shimfida ledar tare da jingine tsohuwar katifar da aka siya mata a gidan wata dillaliya, fitowa suka yi ko arxikin labule daki bai samu ba. Sai rike baki suke suna mamakin irin wannan gida, duk macewar gidansu ya fi wannan kyau. +
Tunda suka dawo suke dariya an yi wa Sa’adatu auren mugunta, sai maganganu marasa dad’i suke fada.
A fusace salim ya fito daga daki yana masifa, wajen yan uwan mahaifin nasu ya nufa “indai kuna ganin mugunta ku ka yiwa Sa’adatu insha Allah kanku xai koma, kuma ko ni kadai na ishi auren nan indai ina doron kasa Sa’adatu baxa ta auri almajiri ba” yana cikin wannan maganar malam Salisu ya fito daga dakinsa, dukansa ya fara yi kamar ya samu karamin yaro, hakan yasa salim ya bar cikin gidan tare da alƙawarin baxai sake dawowa ba indai wannan xaluncin za a cigaba da yi.
Ƙarfe hudu dai-dai aka taru don daura auren Sa’adatu da malam Jibo ango ya sha tsohuwar farar shaddarsa wacce ta ji jiki kamar an kwatota daga bakin kura, sanye yake da jar Dara takalmin kafarsa baƙi ya saka, duk inda ya bi sai zundensa ake yi wai tsabar son xuciya shi xai auri Sa’adatu, mutane da yawa sun san auren cuta za a yi mata kuma laifin mahaifinta suke gani, a kan tabarmar da aka baxa a kofar gidan su ya xauna yana jiran fitowar sauran waliyyan Sa’adatu, don bashi aurenta.Su innah basu dawo daga ƙauyen da suka je a ranar ba, sai da suka yi kusan kwanaki uku a can, suna tattauna a kan yadda za a bullowa al’amarin Baban Sa’adatu, wasu daga cikin iyayenta har sun yanke shawarar a kashe auren tunda babu kwanciyar hankali a ciki ga zaluntarta da ake yi, wani kakan innar ne ya hana a kashe auren sbd shi mutum ne mai saukin kai da hangen nesa, yana duba yadda Sa’adatu zata kasance a bayan babu mahaifiyar ta a gidan, saboda a duk lokacin da suka kashe auren, tamkar sun kashe rayuwar Sa’adatun ne, a dalilin hakan xata iya fadawa cikin kunci da wahala saboda mahaifinta baxai taɓa bari ta zauna a hannun wani ba idan ba gidan shi ba, don haka dole a yi hakuri a zauna a haka don duba maslahar rayuwar yarinyar.
************
Zaune Malam Jibo yake ya zuba uban tagumi yana jiran dawowar Baban Sa’adatu, don tunda yace masa xai je ya dawo har yanzu shiru babu labarinsa, sai duba hanya yake ko zai ganshi ya bullo, yayi zama ya fi na awa biyu da rabi babu labarin malam Salisu, kuma babu labarin waliyyanta, hakan yasa ya fusata ya tashi ya bar kofar gidan yana tafe yana masifa kawai don yaga ba shi da kudi ne kuma bai bashi komai ba shi yasa yayi masa wannan wulakancin amma zai ganar da shi kuskurensa, bude shagon gidansa yayi ya shiga ya zauna yana cigaba da ban-bamin faɗa.
Ko da Baban Sa’adatu yaxo bai ganshi ba hankalinsa ne ya tashi, ya san halin malam Jibo da fushi da zuciya watakila haushi yaji yayi tafiyarsa, a sanyaye ya zauna a kan tabarmar da ya shimfida yana jiran dawowarsa, har wajen sallar magariba bai dawo ba, wannan dalilin ya sanya shi nade tabarmar tare da xuwa gidan malam Jibo da kansa, a Kofar gida ya tsaya yana kwala masa kira, yana jinsa yayi banza da shi, yaro ya sake aikawa a fada masa cewa yazo yana kiransa, ko da yaron ya fada masa sai yace a koma a ce masa baxai samu fitowa ba, duk yadda ya so ya haɗu da shi yayi masa bayanin abinda ya tsare shi hakan ya garara don haka shi ma yayi fushi ya tafi gida.
A fusace ya shiga gida yana masifa “shi wannan mutumin ya san bai shirya auren yarinyar nan ba yasa nayi asarar kudin katifata da ledata, haka na tatike aljihuna ban bar ko sisi ba, gaskiya malam Jibo ba mutum bane na bashi yar tawa kyauta ya wulakanta ni, nima kuwa sai na wukakanta shi duk da abinda yake takama sai nayi maganinsa”
Da rawar jiki innah salamatu ta karaso wajen sa “me kuma ya faru malam naga kana fada haka kai kaɗai” dafe kanshi yayi tare da hadiye wani ɓacin rai da ya tare masa a makogoro
“wane ne kuwa banda malam Jibo mun kulla magana za a daura aure ƙarfe hudu ga shi har magariba tayi Babu shi babu dalilinsa naje gida na kira shi yaƙi fitowa ya san bai shirya auren ba yasa na fadawa yan uwana”
Jinjina kai innah salamatu tayi “Gaskiya malam kaine da laifi tun kafin lokacin malam jibo yazo kaine ka Kad’a kai kayi tafiyarka, neman duniyar nam an yi maka ba a samu inda kake ba” ajiyar zuciya yayi “to ai ba wani waje naje ba, naje ne na ƙarasa karbo gudunmawar da abokaina xasu bani sbd naga alama idan ban je da kaina ba, babu mai bani taimakon kwandala, don naga alama yarinyar nan ba tada goshi, ko sisi ban samu ba sai asara da nayi, gashi auren ma yana neman lalacewa”
Tabe baki innah salamatu tayi “aure yana nan daram babu inda xa shi don baxa mu yi jeran mu a banxa ba, kaje ka samu malam Jibo ku sasanta a sake saka ranar daura auren, tunda yau dai ta wuce Allah bai yarda an daura ba, ta sai a sake lale, ni a ganina ma fa uwar yarinyar nan ita ke bata abin sbd ba so take ba shi yasa ta tsaya tsayin daka take bin abin ta ƙarƙashin kasa don haka ku dage sai an yi ko bata so, idan bata auri jibon ba uban wa xata aura? yarinya irin wannan mummuna kamar a yanka a boye wukar ga uwa uba bakin hali, jibon ne maganinta shi xai saita ta”
Guri ya samu ya xauna ya haɗa kai da gwiwa duk wani shirinsa an rushe masa, amma xai yi kokari ya gyara komai, kafin sati mai kamawa.A ɓangaren malam jibo shi ma a damuwar yake bai ji daɗin abinda malam Salisu yayi masa ba, yau ya shirya tsaf don tarbar amaryarsa amma ya watsa masa ƙasa a ido, babban abinda ya fi damunsa habaicin da matansa ke yi masa a kan rashin daura auren, har dai yayi xuciya ya hakura da Sa’adatun gaba ɗaya, amma dole ya daure yaje ya bawa mahaifinta hakuri a kan a dawo a daura auren ko don ya huta da gori.
Bayan dawowar su innah bai fi da kwana biyu ba aka aiko daga gidan gwaggo Balaraba ana nemana, jikina har rawa yake sbd shaukin son ganin innata, tare da yaron da aka aiko muka tafi, tun daga soro nake jin tashin muryar Babana da alama wata tijarar ya ƙara xuwa yayi musu, da sand’a na shiga cikin dakin a hankali cikin siririyar muryata da ta dashe sbd fargabar da ta cikata nayi sallama, gaba ɗaya kallo ya dawo kaina.
Su ma a sanyaye suka amsa min ina ganin innata bata dago ta kalleni ba, wanda na kasa fahimtar dalilin hakan, gefenta na samu na zauna duk na takure kamar mai jin sanyi, bi nayi na gaida kowa har da Baba Amma bai amsa min ba.
Dakin ne yayi shiru ana jiran a ji wanda zai fara magana amma babu wanda yace wani abu har sai da aka ɗauki wasu mintuna masu tsayi, gwaggo Balaraba ce ta fara bashi hakuri a kan abinda nayi masa tare da rokon ya mayar da innata dakinta kuma ya janye dukkan takurar da yayi mana.
Na lura da fuskarsa yaji dadin kiran sulhun da aka yi masa, fuskarsa bayyane da murmushi ya fara magana.
“Ba komai gwaggo komai ya wuce dama sharrin shaidan ne haka baxai sake faruwa ba, kuma a ja musu kunne duk su biyun sbd gaskiya basa jin maganata”
Nasiha su gwaggo suka yi min tare da innah a kan yin biyayya a bisa dukkan abinda ya umarce mu, tunda gaba dayanmu a karkashin sa muke kuma yardarsa muke nema.
Har aka yi maganar aka gama innah bata ce komai ba da alamu bata ji daɗin sulhun ba, kawai don an fi karfin ta ne shi yasa tayi shiru, don ta san ba canja xani xata yi ba ko ta koma ci-gaba xa a yi daga inda aka tsaya.
A lokacin ya nemi mu tafi tare da shi, gaba daya muka nuna kin amincewa da hakan, kyale mu yayi ya tafi tare da faɗa mana cewa lallai gobe mu taho gida.
Da farin ciki ya shiga gida a xuciyarsa yake fada duk burikan da yake son cika su a yanzu ne lokacin da zai cimma su tunda sun amince xasu dawo.
Yana fita na faɗa jikin innah ina kuka “me yasa kika amince mu koma hannun shi innah wlh baxa su canja ba watakila ma yanxun wani tuggun aka hado mana…… Dan Allah kice baxa mu koma ba innah”
Tun safiyar ranar da zamu koma gida Baba yake ta aike mu taho ya aiko yara sun kai biyar, don mu bamu yi niyyar dawowa a kan lokaci ba, sai mun ƙara hutawa sosai takurar da yayi mana ne yasa ko karyawa bamu yi ba muka tafi, a kofar gida kan benci muka same shi sallama muka yi masa tare da gaishe shi a sanyaye ya amsa babu wani walwala ko farin cikin ganinmu a fuskar sa. Cikin gida muka shiga ya bi bayanmu, kamar jama’ar gidan sun san da zuwanmu duk suna tsakar gida sun jere suna kallon kofar da zamu shigo, da sallama muka shiga cikin gidan abinda ya bani mamaki yau sun ɗan canja kaɗan da fara’a suka tarbe mu, abinda na kasa ganewa shi ne anya ba wani tuggun ake shirin haɗa mana ba kuwa ni da innah. Don na lura da su suna cikin farin ciki sosai har wata yar dariya naga innah salamatu na yi min.
Mukullin dakinmu muka karba a hannun Baba, ni na ajiye kayan da ke hannuna na shiga buɗe kofar, abin mamaki muna shiga muka tarar da komai namu na dakin an kwashe mana, sai yar katifar da muke kwana kawai aka bari hatta kayanmu na sawa da yan kwanukan da muke amfani da su duk babu.
Kallon juna muka yi ni da innah, zan yi Magana kenan naga ta sa yatsanta a bakinta alamun nayi shiru. rausayar da kaina nayi xuciyata cike da damuwa kallonta na sake yi tare da son ta bani damar yin magana amma ta nuna kin amincewar hakan, wajen xama muka samu muka zauna, baka jin motsin komai a cikin gidan duk an yi shiru ana sauraren jin abinda xamu ce.
Mu ma shirun muka yi kasancewar dukkanmu muna cikin damuwa, gaba ɗayan mu duniyar tunani muka tafi, sallamar Baba ce ta dawo da mu daga dogon tunanin da muka tafi.
Gefen katifa ya samu ya zauna tare da yin gyaran murya “Abinda nake so da ku shi ne ku kasance masu bin doka da odar da na saka muku, sbd hakan ne kaɗai xai baku damar cigaba da xama a wannan gida da rayuwa a cikinsa kamar kowa” nuna innah yayi “ke kece sarkin bawa Sa’adatu goyon bayan yin duk wata lalatar da take yi a gidan nan, to ki shiga hanlinki ki, ki nisanci dukkan abinda xai kawo mana sabani saboda ke ba wajibi ne na cigaba da zama da ke ba, amma ita Sa’adatu dolena ce, don haka ki kula da kyau kuma na hana Sa’adatu fita daga rana irin ta yau, ta zauna ta jira ni har zuwa lokacin da zan yanke mata hukunci”
Mayar da kallonsa gare ni yayi “kema ki gyara halinki ki zauna da yan uwanki lafiya duk abinda salamatu ta umarceki, kiyi kokari ki rika cikawa idan aka kawo min ƙararki kin yi wani abu da ya saɓa ka’ida ranki ne zai ɓaci sannan na hana ki fita, makarantar ma na soke ki bari kya ƙarasa a dakinki tunda dama gidan ilimi na kai ki, sannan kada na sake jin kin yi zancen saurayinki na raba ki da shi har abada saboda baxan bari ya gurɓata miki rayuwa ba”
Juyawa yayi zai fita “Au na manta ban fada muku ba, kada ku ga babu kayanku na kwashe ne na siyar na siyawa Sa’adatu kayan aure, don yanzu haka ma an jera wasu daga ciki lokaci kawai muke jira”.Shiru muka yi gaba ɗaya mun rasa bakin magana sai bin sa da ido kawai muke yi, nice nayi karfin halin yin magana “Yanzu innah haka xamu zuba ido ana yi mana cin kashi a gidan nan baxa mu yi magana ba, haka zamu rika rayuwar rashin yanci kamar wasu bayi?” Mayar da numfashi tayi “uhmm me kike so nace Sa’adatu so kike nayi magana mu riƙa tashin hankali ana jin kanmu da shi, duk abinda yake min da Allah na bar shi, sakayyar aure tun kafin a mutu Allah yake nuna ishara, to ni baxan daka ta tasa mu lalace ba” jin ana motsi a kofar dakinmu ne yasa muka yi shiru. +
Innah salamatu ce ta tsaya a bakin kofar tare da kirana naxo na karbar mana abin karyawa, cikin nutsuwa na karasa wajenta, murmushi take min mai cike da ayoyin tambaya tare da cewa
“Sannu Amaryar malam har naga kin fara kyallin amarci, amarya kenan bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida”
kallon mamaki nake mata don ban fahimci abinda take nufi ba, ban amsa mata ba na karbi kwanon na koma wajen innah a gabanta na ajiye ina fuskantar ta
“innah kin ji zaton da nake yi yana son zama gaskiya ko, dama nace miki ba a banxa suke wannan fara’ar ba, tabbas akwai abinda ake shirin kulla mana a gidan nan, tunda ga abinda innah salamatu ta faɗa shi ma kuma Baba ya bamu satar amsa, shi yasa nace miki kada mu dawo takurar da ake mana dai ita za a cigaba da yi, baxa su taɓa sonmu ba kuma baxa su daina musguna mana ba tunda dama ba burinsu mu yi farin ciki ba, sun fi son kullum mu dawwama a bakin ciki”
murmushin takaici innah tayi “Har yanzu bakya fahimtar rayuwa Sa’adatu wani abin ko kana da ikon ramawa dole kayi hakuri saboda magabatanka sun shiga maganar, banda su gwaggo sun sa baki babu abinda xai dawo da ni, wallahi na fiki takaicin dawowata gidan nan, amma maslahar rayuwarki na duba, idan bana nan zaki shiga cikin matsala ne, wata rana ma zasu iya cewa baxa ki kwana a gidansu ba ko kuma duk wanda suka ga dama su aura miki duk munin halinsa, tun a gabana ana wulakanta ki ina kuma ga bana nan, duk abinda xan fuskanta nafi son mu yi rayuwa tare da ke, saboda na baki kariya irinta uwa”
Har Cikin ƙwaƙwalwata nake jin kalaman innah tausayinta ne ya kama ni, gaskiya soyayyar uwa ta musamman ce ga ƴaƴanta babu wanda zaka samu a duniya yayi maka irin son da mahaifiyarka take maka, ta zaɓi mu sha wahala tare a kan ta tafi ta bar ni, Allah sarki innata, Allah ya bani abinda zan saka mata da shi.
Da yamma nayi wanka na nemi iznin innah ina son zuwa wajen Rukayya saboda ina cike da kewarta, amma ta hanani saboda ta faɗa min hakan zai iya janyo mana wata matsalar, wannan dalilin yasa na hakura na zauna a cikin damuwa.
Bayan sallar isha har mun yi shirin kwanciya bacci Baba ya shigo da kansa ya kira ni, a ladabce na tsugunna tare da cewa “gani Baba” fuskarsa a daure ya dube ni
“Yi maza ki canja zani mijinki ya zo zaku yi magana ta fahimta da shi, idan naji kin faɗa masa wani abu wanda ya bata masa rai ni da ke ne”
Zan bude baki na tambaye shi wanene mijina ya dakatar da ni
“kada ki min wata tambaya ina da halin zaba miki duk mijin da naga dama saboda ni ne mahaifinki ina da ikon yi miki duk abinda naga dama matuƙar bai saɓa ka’idar Shari’a ba”
Idanuna ne suka cika da hawaye “Baba wannan kayan ne kaɗai suka suka rage min ba ni da wasu” shiru yayi na wani ɗan lokaci “to naji kije a haka idan kika ci Sa’a ma kafin auren naku zai iya yi miki dinki, ni da nace na yafe masa saboda sadaka na bada ke”
A sanye na dube shi
“sadaka fa kace Baba” Idanunsa a zare yace “kwarai kuwa sadaka na bayar da ke ko ban isa bane?” Ban iya bashi amsa ba sai kuka da nake yi kawai, nuna min hanyar soro yayi alamar na fita.
Idanuna a rufe na lalubi takalmi na saka sai da naje soron farko na ɗan goge hawayen da ke idona sai a lokacin na lura da takalmin da ke kafata wari da wari ne.
Tarar wa nayi har an yi masa shimfida a xuciyata nace da alama an shirya cutata don naga wannan baƙo ne mai matukar muhimmanci ga Baba sallama nayi don ina son naji muryar bakon kafin na karasa inda yake, don nasan ko wanene kasancewar ssoron da ɗan duhu kuma babu hasken fitila.
Bai amsa min ba sai da na matso daf da tabarmar da aka shimfida masa sannan ya zaro touch light ya kunna, haske soron da tayi ne yasa naga ashe malam Jibo ne ya sha uban rawani.
Jajayen hakoransa wanda suka sha goro ya shiga buɗe min a yatsine na dube shi “lafiya malam na ganka a wannan lokacin, dama kaine kake kirana”?
Murmushi yayi “nine Sa’adatu samu guri ki zauna xamu yi magana ne ta fahimtar juna ni da ke” ban yi masa musu ba na samu kan wani ɗan dutse na zauna
“ina jinka kayi sauri ka faɗa min don bacci nake aka taso ni”
Wani kallo yake bi na da shi kamar xai cinye ni
“Ba ki da labarin xuwan bikinmu ne naga kamar baki san komai dangane da hakan ba”
A firgice na dube shi “Bikinku da wa?? kai zan aura malam ni bana sonka kuma baxan aureka ba, domin a matsayin ubana kuma malamina na ɗauke ka baxan iya zaman aure da kai ba, kuma ni gaskiya bana sonka kayi min girma ina da wanda nake so kuma har an gama magana da shi” +
Murmushi yayi “Haba Sa’adatu kenan idan an gama magana da shi me yasa mahaifinki yaxo ya same ni yace ya bani ke, ki daina rudar rayuwarki da wannan shashan saurayinki naki mayaudari wanda ya lalata miki rayuwa, da kike ganin na tsufa, tsufan iya fuska ne kawai, amma duk namiji namiji ne babu yaro babu tsoho, abinda nake so ki gane yanxu shi ne, ki kwantar da hankalinki mu yi magana ta fahimta don wannan auren wallahi babu fashi sai an yi shi matuƙar muna numfashi ni da ke, idan kinga an fasa sai dai idan na mutu ko kin mutu, don haka ki bawa xuciyarki hakuri ki tsaya mu tsara bakinmu da yadda zai kasance. Kece baki san abinda ke faruwa ba har kike wannan maganar ba don tsutsayi ya gifta ba da tuni an daura auren nan, yanxu haka ma kina gidana, kuma ko jiya mun tattauna da mahaifinki a kan a sake daurawa nace a bari mu dai-daita junanmu, sbd bana son takura miki, amma naga har kina taurin kai kina wata fiffi’ka ko? To mahaifinki ma yaso bani ke, sbd ya faɗa min cewa ke bazawara ce a rigar yan mata tsohon saurayinki ya gama da ke, sbd na rufa miki asiri yasa xan miki lefe ko kala biyun ne saboda kada mutane su gane halin da ake ciki, amma tunda haka kika zaba bari na tashi na tafi, aure za a kaura ko ta halin kaka kuma gidana ya zama dole kixo”
Yana gama magana ya miƙe ya tafi a fusace, dama malam Jibo mutum ne mai fushi da zuciya, a tsugunne ya barni ina kuka.
Ni Sa’adatu naga ta kaina dama Baba yawo yake da ni yana kwance min zani, yanxu mutane duk kallon lalatacciya suke min, wayyo Allah ina xan sa rayuwata, yanxu ko Malam Jibon da nake rainawa na aura wane irin kallo zai rika min, a yanzu dai na zaɓi na mutu a kan na cigaba da wannan muguwar rayuwar da nake yi, baxan iya auren malam jibo ba wlh sosai nake faɗa.
Kwanciyar nayi ina kuka mai cike da ban tausayi.A hasale malam Jibo ya shiga shagon da ke cikin gidansa, zaunawa yayi ya haɗa kai da gwiwa yana tunanin
kalaman Sa’adatu da irin yadda ta nuna bata kaunarsa, har ga Allah a yanxu xuciyarsa ba tada wani tunani wanda ya wuce ya mallaka ta, sbd ya san idan ya sameta ya gama samun farin cikin duniya, ko kaɗan kalamanta basu kashe masa gwiwa ba sai ma ƙarfi da suka ƙara masa, kuma ya yiwa kansa alƙawari duk wuya sai ya aureta ko tana so ko bata so, gobe da shirinsa xai je gidan su a daura auren don kada ma wani abin ya gifta a daga.
Nafi minti goma kwance ina kukan baƙin ciki, banda zalunci an hana ni wanda nake so Yanzu kuma a haɗa ni da wannan tsohon wanda ko tsaftar kirki bata isheshi ba.
Baba ne ya fito yana haska soron don ganawa da malam jibo tare da tambayarsa yadda suka yi da ni.
A wannan halin ya same ni Ina ta rusa ihu dago kaina yayi tare da tambayata “ke lafiyanki ba ki da hankali ne kike faman kuka haka, wani abin yayi miki, ko kuma dai rashin kirki kika yi masa,menene dalilin da xai sa ki riƙa kuka a wannan lokacin da ya kamata na ganki cikin farin ciki, a wajen wannan mutumin farin cikin rayuwarki yake kada kiyi wasa da wannan damar taki domin taimaka miki xai yi, buɗe bakinki ki fada min gaskiyar abinda ya haɗa ku, kuma idan naje na tambaye shi naji akasin abinda kika fada min ni da ke ne” idona a rufe na bashi amsa da “wallahi bana son shi baba” .
dauke ni yayi da mari Yana faɗin “haka kika fada masa ko Sa’adatu shi yasa ya fita a fusace mun yi da shi kafin ya tafi xai nemeni amma bakar maganar da kika fada masa ne yasa ya tafi to wlh xaki haɗu da ni ne”
Takalmansa ya shura ya fita a hasale bai xame ko ina ba sai gidan malam Jibo kai tsaye ya shiga shagon gidan don ya san yana can, yana ganin Baban Sa’adatu ya miƙe yana cewa
“yarka ta wulakanta ni ta tozarta ni, tace bata sona nayi mata tsufa, ta ci min mutunci da maganganun da bai kamata su fito daga bakinta ba, dama taimaka maka xan yi na aureta don haka na fasa kaje ka bata ɗan iskan da take so, dama jihadi xan yi tunda ta nuna bata so na kyaleta da tsiyarta, ka tashi ka fita ka bar min gida kafin na huce takaicina a kanka”
jikinsa ne ya dau rawa bakinsa yana karkarwa yake magana “baxa a yi haka ba malam ka yiwa Sa’adatu uxuri har yanzu yarinya ce bata san rayuwa ba, baxa ta gane muhimmancin ka ba sai nan gaba, idan kace ka kyaleta akwai matsala kayi hakuri xata dai-daita halinta xuwa gaba”
shiru yayi yana sauraren baban Sa’adatu, mayar da ajiyar zuciya yayi “shikenan nan naji kaje ka ja mata kunne idan ta cigaba da abinda take yi xata yi asarar aurenmu kuma kayi mata albishir lefen da nayi niyya na fasa, yanzu kuma shawara ya rage naka kayi kokarin da xaka yi a daura auren nan da wuri kada wani dan iskan ya sake hure mata kunne”
Miƙa masa hannu Baban Sa’adatu yayi amma sai ya ƙi karba
“insha Allah malam xan yi wannan kokarin na gode sosai Allah ya kara girma” fitowa yayi da sauri xuciyarsa tana ta sake saken irin cin mutuncin da zai yiwa Sa’adatu idan ya koma gida.
A fusace ya nufi dakinsu cikin rashin Sa’a ya tarar sun kulle da alama yau da wuri suka kwanta.
Tunda na shiga daki ban rintsa ba gaba daya na nemi bacci a idona na rasa kawai tunanin yadda xan tsara rayuwarta da malam Jibo nake yi, na san tunda Baba ya kafe xai yi wuya abin nan bai tabbata ba. Tashi nayi na bude kofa a hankali na daura alwala na koma daki sallah nake yi ina addu’a Allah ya nisanta ni da malam Jibo Allah ya kawo min sanadin da xa a fasa auren gaba ɗaya.