TSANANI CHAPTER 6

TSANANI






CHAPTER 6






Tun bayan fitowar Izuddeen daga police station bai sake samun sukuni ba, kullum cikin damuwa da tunanin halin da Sa’adatunsa take ciki yake yi, yana ji a ransa baxai taɓa barinta ba har abada ko ana muzuru ana shaho, gaba ɗaya ya daina fita harkokinsa komai nasa ya tsaya cak saboda tunani, kullum cikin kuka yake duk ya rame yayi baƙi, ko abinci baya ci sai idan mama ta bashi shi ma sai ta rarrashe shi sannan zai ci. +

Yau ma kamar kullum kwanon abincin yasa a gabansa, hannunsa rike yake da wayarsa ya kurawa wayar ido yana hawaye, hoton Sa’adatu yake kallo zuciyarsa sai radadi take masa, ji yake kamar yaje ya shaqi Baban Sa’adatu ya fito masa da ita, saboda idan akwai abinda yake da muradin gani yanzu bai wuce Sa’adatunsa ba. Sallamar mama ce ta katse masa dogon tunanin da ya tafi, tare take da abokinsa Kabir karasowa daf da shi tayi fuskarta a bayyane da damuwa.

“Wato har yanzu dai kana nan kana wannan tunanin naka ko Izuddeen, yaushe xaka cire yarinyar nan a ranka ne, tunda mahaifinta ya nuna baya sonka baya son tarayyarka da yarsa ya kamata indai da zuciya aka halicceka kayi hakuri ka kyale masa ‘yarsa gudun kada a sake samun matsala, kana ganin dai irin cin mutuncin da yayi mana, aure indai yaxo da haka kamata yayi a hakura a canja she’ka sai Allah ya canja da mafi alkhairi. amma kai kaxo kana tunanin wacce bata damu da kai ba bata ma san kana yi ba, tana can tana rayuwarta cikin farin ciki”
muryar Izuddeen a sha’ke ya fara magana “wlh mama ta damu da ni,duk inda Sa’adatu take yanxu ina cikin ranta ita ma ba a cikin nutsuwarta take ba, ki fahimci yarinyar nan mama tana matuƙar sona bakin ciki ake so a yi mana kawai a raba mu, dan Allah idan kina da hali ki taimake ni ki haɗa Ni da ita
ya karasa maganar yana kuka.

Ba ƙaramin tausayawa ɗan nata tayi ba saboda ta san yadda zafin ciwon so yake da ciwon rabuwa da abinda mutum yake so, cikin nutsuwa suka samu guri suka zauna ita da kabir, dago fuskarsa tayi “kayi hakuri d’ana ka karbi kaddara ka sanya a ranka wannan ita ce kaddararka idan kayi hakuri Allah xai canja maka da mafi alkhairi, na san abin da ciwo amma kayi hakuri wata rana zai wuce ya xamto kamar bai faru ba”

Shi ma kabir hakuri ya riƙa bashi a kan ya cire damuwa a ransa ya manta da komai kuma ya daure ya ci abincin da ke gabansa, kuka Izuddeen kawai yake sbd ko ya sa abincin a bakinsa baxai iya samun damar hadiye shi ba, duk magiyar da suka yi masa haka suka rabu da shi bai ci abincin ba. Duk ya xama wani iri ya fita a kamaninsa ba shi da aikin da ya wuce kuka kamar yaron da yayi rashin mahaifansa.

Hankalin mama a tashe ta tashi ta shiga wajen Mahaifinsa da sallama ta shiga tare da karasawa inda yake, xaunawa tayi da niyyar ta faɗa masa abinda ke damun ɗan nasu, amma sai ta kasa sai hawaye da ke fita a idonta, tashi mahaifin Izuddeen yayi daga kishingidar da yayi cikin kulawa yake tambayarta

“Lafiya Hajiya me ke faruwa naga kina kuka haka” gefen mayafinta tasa ta share hawayen da ya cika idonta
“A kan maganar yaron nan ne Izuddeen wlh Alhaji yana cikin wani hali tun bayan rabuwarsu da yarinyar nan ya daina ci ya daina sha, kullum cikin kuka wai dan Allah baka lura da yadda ya koma ba ne, duk yayi baƙi ya lalace, dan Allah dan Annabi idan da ɗan kokarin da xaka yi masa, ka taimaka kayi masa ka shawo kan mahaifin yarinyar nan saboda mu ceto rayuwar ɗanmu”
Da kuka ta ƙarasa maganar.

Sauke ajiyar zuciya yayi “Hmmm Hajiya kenan dan Allah ki kyale maganar mutumin nan ki manta da su, mu taya shi da addu’a Allah ya canja masa da wacce ta fi ta, wai dan Allah duk kin manta da abubuwan da suka faru da mu ne? Kin manta irin cin mutuncin da mahaifin yarinyar nan yayi mana, ɗaukan ɗanmu yayi fa ya kulle sai da ya shafe wasu adadin kwanaki sannan ya fito, duk fa yayi haka ne da niyyar tozarta mu Allah ne ya kiyaye ya takaita abin, a tunaninki da Allah bai yayyafawa abin ruwa ba me kike tsammanin zai faru? Indai gidan wannan mutumin zan je nemar masa aure sai dai idan baxai yi ba gaba daya, saboda ni bana shiga harkar mumutumin da baya ganin ‘kima da mutuncin na gaba da shi, kije ki cigaba da bashi hakuri Allah ya canja masa da wacce ta fi ta alkhairi”
komawa yayi ya kishingida yana sauraren amsar da xata faɗa masa.

Magiya ta cigaba da yi masa “Ba halin mahaifinta xamu duba ba, nagartar yarinyar xamu duba da yadda mutane suke yabon kyawawan halayenta, idan ka lura da wani abu ita kanta yarinyar ba jin daɗin mahaifin nata take yi ba, kawai don ya zama dole a kira shi da mahaifinta ne amma da tuni ta canja wani uban, don Allah ka duba rokona ka taimaka ka samowa yaron nan mafita, ko baka je da kanka ba ka daure ka aika yayyensa tare da abokanka su nemar maka alfarma a bamu dama mu fito a yi biki”
Har yanxu dai kalamanta ba wani ratsa shi suka yi ba kawai yana bin ta da kallo ne, ɗan murmushi yayi wanda ya ƙara bayyanar masa da kamalarsa

“Dadina da ke kafiya idan kina son abu, mutumin da bai duba mutuncin Musulunci da ma’kotaka ya ɗagawa ɗan da na haifa ƙafa ba, shi ne xan je wajensa na nemi alfarma yayi min? kawai wannan bata lokaci ne ki tashi kiyi hakuri”

Magiya take yi masa sosai amma har yanxu yaƙi sauka, umarni ya bata taje ta kira Izuddeen yana son magana da shi, da sauri ta tashi ta nufi ɗakin nasa faɗa masa tayi cewa mahaifinsa na son magana da shi, jikinsa babu karfi ya tashi ya bi bayanta.

Cike da ladabi ya shiga dakin tare da yi masa barka da rana, cikin sakin fuska mahaifin nasa ya amsa.
“Yanzu duk a kan soyayya ka xama haka Izuddeen, ka manta da dukkan abinda suka faru a baya? Me yasa kake son jefa rayuwarka cikin wani hali, kaifa malami ne bai kamata ka manta da kaddara ba ka jefa kanka a damuwar da xata iya kai ka ga halaka, bana so na cigaba da ganinka a wannan halin kayi hakuri xan nemar maka wani auren da kaina, kuma baxa a ɗauki lokaci ba za a daura shi”

Kan Izuddeen a sunkuye ya fara magana “Dan Allah Babana mai tausayina kayi hakuri ka taimaka min ka aika gidan su Sa’adatu ka nemar min aurenta wlh Baba ita nake so da ita na tsara rayuwata, baxan iya xaman aure da wata ba idan ba ita ba” da kyar ya iya ƙarasa Maganar sbd kukan da ya ci karfinsa.

Cike da tausayawa mahaifinsa ya dube shi, “shikenan kaje magana ta ƙare xan aika gobe da kuɗin aure idan sun amince sati mai zuwa ma za a sa muku rana a daura aure tunda haka kake so amma duk abinda ya biyo baya babu ruwana”
Wani farin ciki ne ya bayyana a fuskar Izuddeen bai san lokacin da ya saki murmushi ba.

“Na gode na gode Baba Allah ya kara girma Allah yasa kafi haka”

Amsa masa yayi da ameen ya tashi ya tafi, a ranar da farin ciki ya wuni sbd dadin albishir din da aka yi masa, ita ma mama tayi farin ciki sosai sbd ɗanta zai samu abinda yake so.Yau tsayin wuni a daki nake ko tsakar gida ban leko ba, sbd ciwon kai mai tsanani da zazzaɓin da ke damuna, maganar da malam Jibo ya fada min ke min yawo a ƙwaƙwalwata duk da cewa ina addu’a amma ina tsoron sharrinsa, na lura da shi sosai akwai manufar da yake son cimmawa a kaina, ba alkhairi ne ya kawo shi wajena ba, duk kulle-kullen da ake yi a gidanmu ina ji, amma sai naki fitowa sbd kada na haɗu da Baba, sai da na tabbatar ya fita kasuwa Sannan na fito na ɗan yi abinda zan yi na koma. kwanciya nayi da niyyar na huta sallamar Rukayya ce ta katse min baccin da nake yi, da sauri na tashi na rungumeta fuskata cike da farin cikin ganinta, muryarta a ƙasa take min magana sbd bata son su innah salamatu su san da xuwanta su haɗa mana tuggu a wajen Baba, gurin zama ta samu ta xauna. Tambaya ta jefo min
“Yaushe kika dawo Sa’adatu nayi kewarki sosai kuma na shiga tashin hankali da naji ance kin gudu tunanina kada ki faɗa hannun azzalumai kinga duniyar nan ba amana, tun lokacin ban sake samun nutsuwa ba sai da naji an ce kin dawo, naso naxo tun lokacin da kika dawo amma sbd matsalar gidan nan yasa nayi xamana kada na sa kiyi laifi”
Murmushi nayi wanda ya tsaya a iya hakorana, takaici da baƙin cikin da ke tattare da ni baxai bari nayi murmushi sosai ba.

“Ba fa guduwa nayi ba Rukayya ina gidan Adda saratu can na koma sbd naga cutata ake shirin yi, ya za a yi ina rayuwar birni na koma ƙauye ai ba a yi min adalci ba

“Ni kaina naji dadin gudun da kika yi, amma daga baya da nayi tunani sai naga rashin dacewar hakan, sbd kada makiya su samu kofar da xasu yi miki sharri, kinga dai irin rayuwar da kike yi, yau zaƙi gobe maɗaci”

Rausayar da kaina nayi idanuna kamar zasu kawo hawaye “indai sharri ne ban ga ranar da xasu daina min ba har sai ranar da Allah ya raba ni da su, yanxu haka ma a tarkonsu nake suna son haɗa ni da malam Jibo kuma ina ganin alamun da wuya ne abin bai tabbata” A razane Rukayya ta miƙe “wannan wane irin zalunci ne da mugun hali, me yasa ake miki haka ne Sa’adatu?? Sai kace ba Baba ne ya haifeki ba innalillahi wa inna ilaihi raji’un Allah ya canja miki da mafi alkhairi Allah ya kawo miki mafita, shi ne kaɗai abinda xan iya cewa dan al’amarin ya wuce lissafina” komawa tayi ta xauna tana min kallo mai cike da tausayawa “wlh sosai nake jin tausayin ki Sa’adatu amma ba komai rayuwa ce duk abinda suka yi dan kansu, ke dai kiyi hakuri kuma ki riƙe Allah dukkan tsanani yana tare da sauki” mun ɗan taɓa hira sosai amma hankalina gaba ɗaya ba a kanta yake ba, yana wani wajen daban kawai tunanina ya zan yi da Malam Jibo, idan nayi tunanin na gudu sai naga hakan ba mafita bace saboda innah xan jefa a wani hali, sannan kuma har ga Allah bana son bijirewa umarni Baba, sbd bana so a zargi innata da laifin da ba nata ba, haka na kasance ina ta sakawa ina kwancewa har lokacin tafiyar Rukayya yayi, iya soro kaɗai na iya rakata sbd dokar da aka kafa min.

Bayan na koma daki Baba ya dawo daga kasuwa ya neme ni xai min faɗa a kan abinda ya faru jiya, duk kiran da yayi min ban amsa ba sai na nuna bacci nake yi, hakan yasa bai samu ganina ba. Ya zauna zai ci abinci kenan naji an aiko wani yaro cewa ana kiransa a waje, ba tare da bata lokaci ba ya hau wanke hannu ya fita don ganin masu nemansa.

A kofar gida ya tarar da mutanen da ke nemansa, mutane ne dattijai masu kamala da mutunci kowannen su sanye yake da Babbar riga da hula, cikin karamci suka yi masa sallama, fuskarsa a ɗan d’aure ya amsa musu tare da tambayar su dalilin zuwansu ɗaya daga cikinsu ne yayi magana
“Allah ya gafarta malam magana ce mai muhimmanci ta kawo mu, idan so samu ne mu shiga daga ciki xai ɗan fi sirri saboda idanun mutane”
bai yi musu ba ya kwalawa A’isha kira ta kawo musu babbar tabarma ta baxa musu suka zauna.

Bayan sun gama gaishe gaishen da xasu yi, wani dattijo ya fara masa bayani “mun zo wajenka ne neman wata alfarma dangane da ɗanmu da yaga yar wajenka Sa’adatu yana so, idan da hali muna so a bamu dama mu fito, yaron bai zo da wasa ba kuma mu ma haka, don da shirinmu muka zo” +

Kamar bai fahimci abinda suka faɗa masa ba yace “Ban gane Sa’adatun da kuke nufi ba, ni dai nasan ina da ‘ya Sa’adatu amma kuma har aurenta an daura”
kallon kallo suka shiga yi tare da mamakin jin abinda yake faɗa musu.
“Ikon Allah amma nayi mamakin wannan maganar don mu gidan nan aka kwatanta mana kuma tare da yaron da yake neman auren ma muka zo shi yayi mana rakiya, kaga batun a ce ba nan bane bai taso b”

Murmushin mugunta yayi “Na gane yaron da ku ke magana a kai na sanshi farin sani, na kuma san yana son ‘yata Sa’adatu sai dai a gaskiya baxan iya bashi aurenta ba sbd na riga da nayi mata miji tun da dadewa, da tuni ma an daura auren yar matsala aka samu shi ne ya kawo jinkirin abin”

Girgiza kai suka yi tare da mikewa “shikenan mun gode Allah ya sanya alheri shi kuma Allah ya bashi ta gari”
Ameen yace tare da bin su da wani matsiyacin kallo.
fita suka yi daga gidan suna ta tunanin abinda mahaifin Sa’adatu ya faɗa musu.

Izudeen na tsaye a bakin kofar gidan yana jiran ganinsu da amsar da xasu ba shi, yana ganin fitowar su ya taho da sauri tare da tambayarsu “An dace kuwa??
Wani dattijo ne ya hau shi da faɗa “kai da kasan an bada ita har an kusa aure zaka sa mu nemi aure a kan aure, gaskiya baka kyauta mana ba da kimar mu da mutuncin mu”
Yayan izuddeen ne ya dafa dattijon yana yi masa magana “wlh bai sani ba Alhaji kawai dai baxai bamu auren bane amma ko mutanen unguwa sun tabbatar babu wani aure a kanta”

Mayar da kallonsa yayi ga izuddeen cike da tausasawa ya fara yi masa magana “kana so na baka shawarar da zata amfaneka?” da sauri ya amsa masa da “eh”

“Tabbas zaka ji zafi idan ka rasa abinda kake so amma kuma xaka ji dadi idan ka tuna Allah zai canja maka da wanda ya fi shi alkhairi idan kayi hakuri, kowane dan adam da kake gani da irin ƙaddara ko jarrabawar da take samunsa sai dai na wani ya fi na wani, ka ɗauka wannan shi ne ƙaddararka kuma zaka yi hakuri don ganin ka cinye
Dan Allah dan kaunarka da Annabi ina yi maka magiya saboda Allah, ka kyale yarinyar nan ka cire soyayyarta a ranka, tunda iyayenta sun nuna basa sonka basa son kayi tarayya da yarsu kuma baxa su baka ba aurenta ba, ka bawa zuciyarka hakuri tun kafin ciwo ya kamaka, yanxu haka maganar da nake maka an kusa daura mata aure, dan haka ka rabu da ita Allah xai canja maka da wacce ta fita”

Wani baƙin ciki ne ya kama izuddeen kamar ya fashe da kuka, amma sai ya nemi hawaye gaba ɗaya ya rasa a idonsa sbd bacin rai, bin bayansu yayi suka tafi, ji yayi kamar kafafunsa baxa su iya daukansa ba ga jiri da ciwon kai da zazzaɓi mai xafi da yake ƙoƙarin rufe shi, gaba ɗaya baya ganin hanya duhu kawai yake gani sbd bacin rai.

**********

Da bacin rai Baban Sa’adatu ya shiga cikin gidan yaji ciwon maganar da dangin izuddeen suka xo masa da ita, kuma bai ga laifinsu ba illa laifin Sa’adatu da har ta basu damar xuwa su tunkare shi da maganar, don haka kai tsaye dakin su Sa’adatu ya nufa yana ta surfa mata kira da yaga ba tada niyyar fitowa zata bata masa lokaci, shiga dakin yayi a fusace yana fadin

“Fito nan munafukar banxa ni xaki je ki haɗawa tuggu da munafunci, har wasu mutane su tutsiye ni a dole sai sun sa nayi abinda ban niyya ba, ke wai a dole sai na aura miki wanda kike so ko, kin kyauta kuma xaki ga sakamakon abinda kika yi nan bada dadewa ba, za kiyi nadamar tozartanin da kika yi”

Cikin rashin fahimtar abinda yake faɗa min na dube shi “Baba me nayi wlh ban turo kowa ba, kuma ban sa wani mutum ya tozarta ka ba”
Ture ni yayi yana nuna ni da ɗan yatsansq, wlh idan kika sake magana sai nayi ƙasa-kasa da ke a gidan nan karya xan miki? dole ne sai na aure miki wannan ɗan iskan yaron da kika kawo wanda bai san mutunci ba mai ƙoƙarin keta alfarmarki ta ya mace, to wlh ki sani a daren nan xan daura aurenki zan ga wanda ya isa ya hana ni, tunda kin nuna ke ba yar mutunci bace xan nuna miki ba kida wayo
Fita yayi ya bar ni ina ta sharar kuka ita kuwa innah bin shi tayi da kallo, bayan ya fita ta jawo ni jikinta tana rarrashina “kiyi kiyi hakuri Sa’adatu Allah baxai wulakanta mu ba, suna ganin sun yi mugunta sun hada ki da Malam Jibo ko, da yardar Allah karshe sai ya xama alkhairi a gareki, tunda muka riƙe Allah baxa mu yi da na sani ba, ki daina wannan kukan baxai mana maganin komai ba addu’a ita ta kamace mu” +

Yana fita bai zarce ko ina ba sai gidan malam Jibo, a zaure ya tarar da shi tare da wani abokinsa suna tattaunawa, yadda yaga Baban Sa’adatu a birkice ne yasa ya tambaye shi “lafiya malam Salisu me kuma ya faru haka Allah yasa dai kalau??”

Cikin zafin rai ya fara magana “ka shirya yau xan daura maka aure da Sa’adatu da misalin ƙarfe bakwai na daren yau ka fadawa mutanen da zaka fadawa, ni na riga na gama yanke hukuncina yanxu xan kira abokina Alhaji Lamma yaxo shi ma ya shiga cikin shedu”

Wani farin ciki gami da daɗi ne ya saukarwa malam jibo, ji yayi a ransa kamar yayi ihu dan dadi, cikin girmamawa yace “to shikenan Allah ya kaimu ni dama a shirye nake ko yanzu a kawo amarya”

Wajen abokinsa ya wuce ya sanar da shi daurin auren Sa’adatu yau, duk wanda yaji labarin auren sai yayi Allah wadai, dukkan mutanen unguwar sun san auren mugunta aka shirya yi mata, babu wanda yake cewa Allah ya sanya alkhairi sai dai Allah ya sakawa Sa’adatu.

Da misalin ƙarfe bakwai malam jibo da abokinsa suka hallara a Kofar gidansu su Sa’adatu dukkan mutanen da suka halarci daurin basu wuce mutum bakwai ba, ba tare da bata lokaci ba aka daura aure, dubu goma Malam Jibo ya biya na sadaki sun ɗan zo da goransu da alewa wanda bai taka kara ya karya ba, bayan an kammala aka gabatar da addu’a tare da fatan Allah ya bawa ma’auratan zaman lafiya.

Cikin gida mahaifin Sa’adatu ya shiga hannunsa riƙe da kullin dabino da goro da alewa, dakin salamatu ya shiga tare da mika mata kayan, cikin kissa da makirci take tambayarsa “wannan kuma na menene malam?” kawar da kansa gefe yayi yana magana “Na daurin auren Sa’adatu ne da malam Jibo yanzun nan aka kammala shi” wani gud’a ta saki
“Alhamdulillah yau dai Allah ya nuna min auren bazawarar yata mai baƙin jini ashe dama ina da rabon ganin aurenta, oh!!! ALLAH da iko yake” shewa tare da ihu suka rika yi ita da ƴaƴanta.

Daga nesa na riƙa jiyo karad’insu, a xuciyata nace yau kuma me ke faruwa a gidan namu naji innah na murna Allah yasa dai ba ni abin ya shafa ba, kafin na rufe bakina har sun fado dakinmu jefo mana dabino Baba yayi gami da mayar da kallonsa gare ni

“Ki daina daukan dukkan abinda nake fada miki da wasa idan nace xan yi abu la shakka sai na aikata don haka ki kiyaye ni, aure an daura shi kuma ya dauru ga sadaki dubu goma ya bayar amma baxan baki ba sbd ni sadaka na bayar da ke, don haka xan mayar masa da kudinsa ke kuma idan na samu xan biyaki” yana gama faɗa ya juya, hawaye kawai na gani a idanuna na sauka, ji nake kamar xuciyata xata faso kirjina ta fito, na kasa cewa komai sbd bakin ciki.
Innah salamatu ce ta karaso cikin dakin da mu ke zaune ni da innah “Sa’adatu ina taya ki murna yau dai nauyin ‘kashi ya ƙare Allah yayi xaki tafi gidan aure kema ki samu irin falalar da ake samu, wannan ranar na dade ina jiran xuwanta ashe a kusa take, kuma wani ikon Allah ashe ma mijin anan kusa yake bai fito ba sai da lokaci yayi, gaskiya na yarda da karin maganar Bahaushe da yace komai da lokacinsa wai mahaukaci yayi girbi a watan bakwai, fatana a gare ki shi ne kiyi hakuri gidan mata uku Allah ya kai ki kece cikon ta huɗun, duk wani girman kai da jiji da sai kin cire su kin ajiye su gefe guda, wannan nu’kufurcin naki kiyi watsi da shi da wannan mugun halin don baxai kai ki ga tafarkin tsira ba, sannan ki kama ƴaƴan mijinki ki rike su tsakani da Allah banda rowa da sharri da makircin don nasan duk kin………” Kafin ta ƙarasa innah ta dakatar da ita “ya isa haka ya ishe ki salamatu, na gaji hakurina ya ƙare baxan juri wannan bakaken maganganun da kike fada mata ba da me xata ji, da bakin ciki da hassadar da kuke mata da sharrin da kike kulla mata ko kuma da maganar da kike mata yanxu, duk abinda ya faru da Sa’adatu wace ce sanadi idan ba ke ba, ina da labarin dukkan sharrin da kike kullawa Sa’adatu kawai shiru nayi na barki da Allah tunda ba a duniya za a dauwama ba, ke idan ana maganar bakin hali da mugun hali har kya yi magana da cin amana da ha’intar ya’yan miji har kya yi magana, wanda bai san halinki ba xaki fadawa wannan amma wane irin makirci ne baki iya ba, tun daga kan karfar baka har yawon malamai wanne ne a ciki bakya yi, ki je na barki da fitowar rana da faduwarta na san dukkan abinda kika shuka wata rana sai kin girbi irinsa, kema kina da ya’ya xaki gani a kansu, auren nan kuma insha Allah alkhairi xai xamewa Sa’adatu ba sharri ba, da yardar Allah abinda kike da burin ya same ta baxai sameta ba har abada muguwar banxa wahalalliya” +

Fashewa innah salamatu tayi da kuka wai innah ta xageta, aikawa tayi aka kira Baba shi ma yaxo ya riƙa faɗa da xage xage, a ranar dai gidanmu a rikice ya kasance sai can dare abin ya lafa, daga ni har innah bamu samu mun rintsa ba sbd tunani wannan dalilin ya bamu damar yin Sallah da fadawa Allah muguntar da ake shirin yi mana.

Washe gari da yamma su Rukayya da ummansu suka zo don jajanta mana abinda ya same mu, don ko su Adda saratu basu san da daurin auren ba sai a yau din innah ta aika ta faɗa mata, sbd takaici cewa tayi baxata xo ba.

Sallama mahaifiyar saleem tayi tare da shigowa dakinmu yau fuskarta a sake sbd tana farin ciki da abinda aka yi mana, gaisawa suka yi da innah tare da fada mata cewa Baba yace a fito da ni za a kaini dakina, ban san lokacin da na rusa wani ihu ba wanda sai da ya gigita mutanen gidanmu gaba daya, fitowa suka yi suna sallallami tare da tambayar abinda ya faru da ni, a lokacin ne Baba yaxo ya daka min wata tsawa yace na d’akko mayafina a kai ni, amarya babu kunshi ballantana fulawa, ba wani kamshi da nake yi a matsayina na amarya, duk wanda ya ganni ya san auren dole aka yi min, saukinta ɗaya nayi wanka amma ko mai ban shafa ba, sutturar jikina ma ba wata mai kyau ba ce, haka aka ɗauke ni muka tafi ina tafe ina kuka saukin da na ji ɗaya ne na samu rakiyar Rukayya da mahaifiyarta sai kuma ya’yan gidanmu da suke son xuwa su ga kwakwaf.*Wannan shafin gaba ɗaya naki ne halak malak na bar miki shi kiyi yadda kike so da shi, kawata aminiyata maxumunciyata abokiyar shawara abokiyar faɗa AISHA SABO ABDULLAHI (mrs khamis) Allah ya bar min ke ko ba kai ba ƙafa ko dan naci dariya🤣🤣🤣*
+

Muna isa bakin kofar gidan umman Rukayya ta umarce ni da yin Bismillah tare da shiga da kafar dama don neman sa’a, ban yi gardama ba nayi abinda ta umarce ni, daga saka kafata a soron gidan na fara cin karo duwatsu da kawazzabai saura kiris na fadi, haka na daure na buɗe idona don gudun kada na fada wani ramin sai da muka isa tsakar gida na rufe fuskata, hayaniyar da ake yi a gidan ne ya daki kunnena yara ne ƙanana waɗanda baxa su wuce shekara biyar ba xuwa shida suke ta wasanni da tsalle-tsalle, ilahirin tsakar gidan a jike yake baka jin komai na tashi banda warin banɗaki, gidan dai babu sha’awar gani saboda tsafta bata wadaci mazauna gidan ba, yaran gidan na ganinmu suka hau ihu suna ga amarya har da masu kokarin kama mayafin jikina sai da Rukayya ta kai musu duka sannan suka tarwatse.

kai tsaye dakin uwar gida aka shigar da ni, tare suke a dakin ita da ragowar matan nasa biyu, gefen gadonta aka samu aka xaunar da ni ragowar yan rakiyata kuma suka tsaya daga waje, kasancewar dakin baxai dauke mu gaba ɗaya ba, gaisawa suka yi da su umma sama sama saboda uwar gidan ba sosai take da kirki ba, ragowar kishiyoyin nata sun ɗan fi ta sakin fuska, sun fi karɓar mu hannu biyu-biyi. umma ce ta fara magana “To ga kanwarku kuma amaryarku mun kawo dan Allah ku riketa amana, duk abinda ya dace na gyara ku rika yi mata, kuma ku riƙa hakuri da gazawarta”
Duk bayanin da umma tayi basu ce komai ba ƙaramar cikinsu ce tayi ƙarfin halin yin magana “to xamu riketa amana Allah ya bamu ikon zama lafiya da junanmu”
Gaba daya aka amsa mata da “ameen”

Tashi muka yi muka nufi ɗakin da xan xauna tunda na hango kofar dakin wani baƙin ciki ya daki xuciyata, ilahirin bangon dakin duk yayi jirwaye, ita kanta farar ƙasar ba mai kyau ya siya ba, duk macewar gidan mu ya rufawa na Malam jibo asiri, mukulli Rukayya ta karba ta bude kofar dakin, a hankali na saka kafata na shiga babu komai a dakin sai uban duhu, wayar Rukayya aka kunna don ganin hanya, duba dakin na shiga yi naga bangon duk ya lalace, wani ƙarin abin takaici ko labule ba a saka min ba, ledar ma bata shimfidu dai-dai ba saboda ramukan da ke dakin, kukana ne ya tsananta yanzu nake kara tabbatar da irin cutar da aka yi min.

Kama hannuna umma tayi ta zaunar da ni kan tamulalliyar katifar da aka shimfida min wacce ko arxikin zanin gado bata samu ba, kusa da ni ta xauna hannunta cikin nawa a hankali take min rada a cikin kunnena”kiyi hakuri Sa’adatu kinga dai yadda Allah yayi da mu, ba yadda xamu yi tsarin Allah shi ne tsari kuma duk yadda ya tsara haka xa a yi, a kullum addu’ar alkhairi muke yi kuma muna nan insha Allah xai tabbatar mana da alkhairin, kiyi hakuri ki daina kuka wata rana komai xai xamo tarihi, ki yiwa mijinki biyayya ki xauna da kowa da xuciya daya, insha Allah xaki cinye wannan jarrabawar cikin sauki kuma baxa ki tabe ba har abada fatana a gareki shi ne ki riƙa Allah tare da addu’a duk rintsi kada ki manta da karatun Alkur’ani da kiyamullaili ki kuma saka a ranki DUKKAN TSANANI yana tare da sauki”
rungume ni tayi muna ta kuka tare, ita kuwa Rukayya tun shigowar mu take ta kuka kamar iya ce Amaryar babu abinda take iya faɗa banda Allah ya saka miki Sa’adatu.Sun ɗan yi zama na yan awowi don sai da aka kira sallar isha muka yi sallah tare da su sannan suka tashi don tafiya gida, kana kallon fuskokin ya’yan gidan mu xaka tabbatar da cewa suna cikin farin cikin abinda aka yi min banda fara’a babu abinda suke yi, ganin idon ummansu Rukayya ne ma ya hana su magana amma da babu ita da sai na gudu don habaicin da xasu yi min. +

Har bakin dakina na ɗan taka musu ina ta kuka “yanzu umma tafiya xaku yi ku bar ni a wannan gidan dan Allah kada ku tafi ku kyale ni ban san yadda xan yi rayuwa a cikin gidan nan ba, na rabu da ku na rabu da innata na shiga uku”

Rungume ni Rukayya tayi tana kuka ita ma umma kukan take sosai aka rasa mai rarrashin wani a tsakaninmu, sai da muka yi kukan da ya ishe mu sannan muka saki junanmu, riko hannuna Rukayya tayi gaba ɗaya ta kasa sakina, kuma ta kasa magana ji take kamar ita aka saka a wannan kurkukun, cikin ƙarfin hali na fara yi mata magana.
“Dan Allah Rukayya ki nemi izuddeen duk inda yake ki bashi hakuri ki fada masa dukkan abinda ya faru ba a son raina ya faru ba, kuma dan Allah idan da hali kice na bashi dama ya aureki ko xai samu sassaucin xafin da yake ji” ina karasa maganar na fashe da matsanancin kuka ban san lokacin da suka wuce suka barni ba, sbd idan suka daka ta tawa baxan bari su tafi ba gashi dare ya ɗan fara yi. 2

Sai da nayi kukan da ya ishe ni sannan duba jakata na dakko wata tsohuwar touch light din innah da na sakata a jakata, haska dakin na fara yi ina ƙare masa kallo, baka ganin komai sai ramukan kiyashi da cinnaku, daki kamar ba na amarya ba a xahiri nake furta Allah ya isa Allah ya bi min hakkina, gyaran muryar da naji an yi ne ya dawo da ni cikin tunanina.

Malam Jibo na gani hannun shi rike da touch light sallama yayi min tare da isowa wajen da nake, ko dagowa na kalle shi ban yi ba ballantana ya samu arxikin amsa masa sallamarsa. samun guri yayi ya xauna daf da ni da sauri na janye jikina na sauka daga kan katifar ma gaba ɗaya, ledar da ke hannun shi ya ajiye tare tare da budeta, murmushi yake yana min magana.

“Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida, ga Gurasa nan da balangu na siyo musamman sbd ke kizo mu ci, daga nan mu yi sallah mu godewa Allah a bisa baiwar samun juna da yayi mana” A fusace na dube shi Allah ya kiyaye na ci abinci da kaxamin Mutum irinka wanda bai san hakkin kowa a kansa ba sai kansa, azzalumi wanda ya raba ni da farin ciki a rayuwata, ka sani yadda ka zama sanadin sanya ni cikin baƙin ciki kaima baxa ka taɓa samun farin ciki Daga gare ni ba” gaba ɗaya na nemi tsoronsa da kimarsa da nake gani na rasa, ji nake kamar na tashi na xane shi komai nashi haushi yake bani.

Murmushi yayi tare da shafa cukurkudadden gemunsa “Kanki kalau kike fadin haka Sa’adatu anya kina cikin hankalinki kuwa, ba wani abu kika sha ba Sa’adatu ni ne fa malam Jibo malaminku ko kin manta ne?, ki kwantar da hankalinki ki min biyayya duk abinda wata mace take samu a gidan mijinta kema xaki samu, ki sani duk cikin matana nafi sonki kuma sai kin fi samun soyayya fiye da kowace mace da ke gidan nan”

Gefe na koma na sunkuyar da kaina nayi gami da toshe kunnena, ina ta sharar kuka baxan iya jure sauraren kalamansa ba idan na cigaba da ji xan iya faɗa masa abinda ya fi haka ma.

Numfashinsa naji na dukan kunnena da sauri na miƙe, wani kallon ban haushi yake bina da shi, cikin fushi nace
“Bana son rashin jan girma me kuma ya kawo ka nan, tun wuri kaja mutuncinka kafin nayi maka abinda xaka yi nadama, abinda ka siyo nace baxan ci ba kaci kai kaɗai talauci na bai kai naci abinda ya fito daga hannunka ba”
Shafa kansa yayi
“Tunda baxa ki ci abinda na siyo ba tashi mu je wajen yan uwanki na gabatar da ke na kuma faɗa miki dokokin gidana”.Fita yayi na bi bayan shi a tsakar gida na tarar da su an yi shimfida ana jiran karasowar mu, wajen xama suka bani amma sai naki xama a kan shimfidar tasu, ajiye takalmina nayi na xauna a kansa ina sauraren abinda xai faɗa min.

Gaishe shi naga matan nayi a yadda na fahimta suna matukar jin tsoron sa, a murtuke ya amsa musu kamar baya son yin maganar, gabatar da ni yayi a gurinsu ya kuma faɗa musu irin yadda yake ji na a ransa.
Albarka suka shiga sakawa auren tare da yi mana fatan alkhairi, Ni kuwa duk abinda suka faɗa sai nace ba Amin ba don har sai da maganar tawa tayi kokarin fitowa.

Mayar da kallonsa gare ni yayi yana murmushi “malama Sa’adatu kinga dai yanxu kin shigo cikin wata sabuwar rayuwa wacce baki saba da ita ba, kuma na san ko a mafarki baki taɓa tsammanin xaki yi ta ba, dan haka ki xamto mai hakuri da kawar da kai, kuma ki xama mai biyayya a gare ni, duk abinda na umarce ki ko yayyen nan naki suka ce kiyi, ki riƙa kokari kina yi, sbd ni gidana yana da tsari da kuma doka, dole ne karami ya yiwa babba biyayya ta haka ne xamu samu xaman lafiya da cigaba. Sannan kuma ina da sharadi ba a fita unguwa sai dai da kyakkyawan dalili kamar mutuwa ko rashin lafiya, shi ma sai dai idan a gidanku abin ya faru, sannan kuma ba a xuwa asibiti ina da kokarin da nake yiwa iyalina idan suna rashin lafiya, yayana ashirin da bakwai amma dukkansu babu wanda aka taba kaiwa asibiti, kuma babu wanda aka haifa a asibiti, sannan kuma magana ta biyu bana so baƙi su rika zuwa kowane lokaci, sai lokacin da ya dace za a rika zuwa xan fada miki lokacin idan buƙatar hakan ya taso”

Mayar da kallonsa yayi ga ragowar matan “Rabon kwana fa ya canja kowace mace zan rika yin kwana biyu a dakinta sabanin kwana ukun da nake yi a da, amma yanzu tunda ga Sa’adatu amarya an kawo xan fara yi mata kwana bakwai kamar yadda Musulunci ya yarda a yiwa budurwa idan an aureta, daga nan kuma xamu koma kamar yadda muka tsara, tsarin girki zai zo daga baya idan Sa’adatu ta huta”

Da sauri na tashi “Bana so ka rike kwananka bana buƙatar ganinka a dakina sbd ba sonka nake yi ba, kayi harkar gabanka nima nayi nawa kada kayi tsammanin xaka same ni a matsayin matarka ta aure, ka ƙaddara ajiya aka kawo ni gidan nan kuma yadda na shigo lafiya haka xan fita, sannan kana maganar girki babu ɗan matar da ya isa na dafa masa abinci idan xasu dafa da kansu su dafa idan ba haka ba kowa ya kwana da yunwa, kana da zabin sakina ko cigaba da xama da ni wannan duk matsalarka ce”

Sakin baki matan suka yi suna kallona, mamakin yadda babu shakka nake fadar abinda na ga dama, ji nayi suna magana ƙasa- ƙasa “Dama ba sonsa take yi ba ya aurota, lallai ya siyo tsaye”

A fusace ya mike yana nuna ni da hannu “Za kiyi nadamar abinda kika fada min, kada kiyi xaton ko sonki nake yi, nima ba kaunarki nake ba kamar yadda bakya kaunata taimakawa ubanki nayi na aureki, ganin kina kokarin lalacewa, ko kin manta sadakar ki ya bani, ina baki shawara ki taka a hankali indai ni ne da sannu xan yi maganinki”

Kallon kallo matan ke yi suna mamakin jin wannan kalaman daga bakinsa ni kuwa ko a jikina ban damu ba, da zai sallame ni ma haka nafi so a fusace ya tashi ya bar wajen nima dakina na koma.

Duba kyauran dakin na shiga yi ko xan ga sakata na saka amma ban ganta ba, tura kofar nayi na koma na kwanta.

Can cikin dare naji an bude kofar dakin a razane na tashi don ganin ko wane ne, malam jibo na gani sanye da…………Sanye yake da wasu kaya marasa fasali, su dai baxa a kira su da manyan kaya ba haka ma baxa a kira su da ƙanana ba, amma kusan surar jikinsa a bayyane yake sbd kayan ba masu kauri bane, kuma da dukkan alamu sun dade basu ga ruwan wanki ba, babu abinda kayan suka yi masa sai ƙara bayyanar masa da asiritaccen muninsa, sai a lokacin na ƙare masa kallo naga ilahirin gashin sa babu baki sai kaɗan amma majority din gashin ya xama furfura. +

ina ganin shi nayi karfin halin miƙewa duk da cewa akwai bacci a idona amma hakan bai sa naji kasalar miƙewa ba, a fusace na dube shi.

“lafiya ka shigo min daki a wannan daren, me ya kawo ka me kake nufi da xuwanka a dai-dai wannan lokacin, tun wuri ka fita kafin nayi maka abinda ranka xai ɓaci, na riga da na faɗa maka baxa ka taɓa samuna a matsayin matarka ba ka ƙaddara cewa rainona aka kawo maka, insha Allah sai na kai budurcina gidan izuddeen”

Gyara wuyan rigarsa yayi tare da matsowa inda nake warin jikinsa ne ya daki hancina miƙa hannu yayi xai riko ni, da sauri na bar wajen sbd idan na tsaya xan iya yin amai, cikin tausasa murya ya fara min magana “ki tsaya ki saurare ni Sa’adatu na lura har yanxu kuruciya na damunki, wanda ya samu miji kamata me yasa xaki tafi hangen wani saurayi daban wanda ba shi da niyyar aurenki sai niyyar lalata miki rayuwa, abinda ya kawo ni yanxu naxo ne mu yi sulhu da junanmu, mu kuma bawa juna kulawa da haqqin auratayayya, ina ganin wannan hanyar da muka dakko baxa ta bulle da mu xuwa alkhairi ba, ni da ke ma’aurata ne masu fatan ganin sun zama ɗaya har abada ki bani dama na nuna miki irin yadda nake sonki, da yadda nake jinki a cikin xuciyata”
Wani kallon raini na bi shi da shi “Allah ya kiyaye nayi rayuwar ma’aurata da mutum irinka ina neman tsarin Allah, ka manta irin maganganun da ka fada min a gaban matanka, kai fa ka kira ni da yar iska karuwa wacce aka baka sadakarta, me yasa kuma yanxu ka shigo dakin karuwa baka tsoron na shafa maka cutar HIV ne tunda duk kace na gama bin maxa kafin a haɗa ni da kai, wlh da xaka burge ni da ka sake ni yanxu, don xamana da kai ba mai dorewa bane, duk son da kake min haka wata rana zaka kyale ni na auri wanda nake so”

Kafin na ankara ya dako tsalle ya dawo inda nake, ji nayi ya rungume ni yana sumbatata kokarin dauke numfashi nayi sbd muddin na shaki warin jikinsa xan iya amayar da abinda ke cikina, cikin kalmomi masu taushi ya fara min magana “ki tsaya ki fahimce ni Sa’adatu duk abubuwan da na faɗa miki na faɗa ne a cikin ɓacin rai amma ba don na wukakanta ki na fada ba, na san baxa ki gane girmanki da matsayinki gare ni ba sai a wannan lokacin da xan dandana miki dadin soyayyata, ki bani haqqina kada ki shiga sahun matan da Mala’ikun Allah suke tsinewa”

kokawa muka riƙa yi sosai yana kokarin sai ya zame mayafin da ke jikina da karfin hali na tunkude shi ya faɗa baya, na fita da gudu tsakar gida ina mayar da numfashi.

A gigice ya biyo ni, kallo ɗaya xaka yi masa ka gane yana cikin matsananciyar jaraba komai nasa ya canja, hanyar kofar gida na kama ina ƙoƙarin zare sakata, biyo bayana yayi yana min magana.Sa’adatu ina xaki je a wannan tsohon daren yanzu fa karfe biyu da rabi ina hankalinki yake tafiya ne, so kike ki fita kiyi gamo da aljanu” +

Kuka na fara yi “ka sake ni wlh bana sonka bana kaunarka ka kyale ni na tafi duk inda naga dama, hakan ne ya fi dacewa da rayuwata, a kan na xauna a wannan kurkukun wlh gara na fita ko duniyar aljanun ne na koma na xauna”
Ina gama faɗa na juya baya ina ta rusa kuka, a yadda nake ji ban ki na fita ba duk abinda zai same ni ya sameni.

Jin shi nayi ya jingina jikinshi a nawa ya hade ni da bangon soron yana sake sumbatata a fusace na juyo na ture shi na wuce dakina da gudu na turo kofa, a daren haka na sha gwagwarmaya da shi duk yadda ya so yaga ya keta alfarmarta ta “ya mace Allah bai bashi dama ba, haka muka sha kokawa a ranar gaba ɗaya ban samu na runtsa ba.

Washe gari da safe da misalin ƙarfe goma sha daya Rukayya taxo min, yan kayan aiki da labule umma ta bata ta kawo min, ina ganinta na rungumeta ina rusa kuka abinda ta fara tambayata shi ne babu abinda malam Jibo yayi min ko da na fada mata yadda muka yi da shi ba ƙaramin dadi taji ba.

Daya daga cikin yaran gidan ne ya shigo hannun shi rike da kwanon abinci sallama yayi tare da ajiye kwanon a gabanmu, abincin karyawa ya kawo min ko da na bude kwanon ido huɗu nayi da tuwon dawa miyar kuka, a take nace ya mayar musu da abincinsu bana ci.

Ina jin matan na yan maganganu a kan rashin cin abincin da ban yi ba ni kuwa hakan bai dame ni ba don ni neman dukkan abinda xai raba ni da gidan nake yi a yanzu ko na huta da jarabawar wannan mugun tsohon.Kai tsaye gidan innah Rukayya ta wuce, tun a hanya take ji a ranta kamar ta fashe da kuka saboda halin da ta bar kawarta a ciki, don ba tada ikon kashe auren Sa’adatu ne amma da tuni wani labarin ake yi ba wannan ba, da sallama ta shiga cikin gidan a tsakar gida ta tarar da Baba da innah salamatu suna hira yadda taji salon zancen nasu a kan Sa’adatu suke magana, a ladabce ta gaishe su haka dai suka amsa mata ba yabo ba fallasa, har ta kama hanyar shiga dakin innar Sa’adatu Baba ya kirata, cike da ladabi ta dawo tsugunnawa tayi a gabansa gami da cewa “gani Baba”.
Wani kallon tuhuma ya bi ta da shi “To an yi bikin Sa’adatu dai Allah ya nufa, yadda ku ka so ba haka Allah yayi ba, kuma an yi komai lafiya an gama lafiya, kada naji kada na gani, kuma kada ki kuskura na fara ganin kafarki a gidanta, don baxa ki je ki kashe mata aure ba, an samu tayi auren da kyar ki je ki xuge min yarinya ta bujirewa umarnina da na mijinta, dama duk sha’kiyancin da ta riƙa yi kwanakin baya ke kike sakata a hanya, ban hana ki xuwa nan gidan ba amma gidan Sa’adatu dai bana so na sake ganinki a can, xumuncin da aka yi a baya ya isa idan ita taxo kwa gaisa”

Jikinta a sanyaye ta tashi ba tare da tace masa komai ba, dakin innah ta shiga, shigarta ke da wuya sai ta tarar da innar ba irin yadda ta saba ganinta ba, da dukkan alamu ita ma tana cikin kewar yarta da tausayin irin rayuwar da ta shiga, har tayi sallama bata san ta shigo ba sai da taje ta dafa kafadarta sannan ta dago tana murmushi.
Jefa mata tambaya tayi.
“Lafiya innah, Allah yasa dai ba wani abu ke damunki ba”?
ƙoƙarin hadiye kwallar dake shirin zuba daga cikin idanunta tayi duk don kada Rukayyah ta fahimci halin da take ciki, gajeran murmushi ta saki gami da gyara zamanta. “Babu abinda yake damuna Rukayya illa dai kewar Sa’adatu amma tunda na ganki yanxu tamkar na ganta ne, har naji sanyi a raina kuma kewarta ta tafi a xuciyata ina fatan xaki riƙa xuwa sa’i da lokaci kina ɗebe min kewa”
Murmushi Rukayya tayi tare da ajiye abinda ke hannunta “insha Allahu innah indai wannan ne ki daina saka damuwa a ranki, kullum xan zo na ganki mu yi hirar mu ta ‘ya da uwa, nima bana so ki xauna ke kaɗai ba, kaɗaici xai iya cutar da ke”
Abincin da ke gefenta ta jawo ajiye shi tayi a gaban Rukayya “buɗe kici abinci nan tun daxu aka gama amma na kasa ci”

Girgiza kai Rukayya tayi “nima wlh a koshe nake innah na ci abinci amma ki daure ki ci zama da yunwa ba daɗi” sun ɗan yi hirar duniya kaɗan sannan Rukayya ta dubeta.

“Inna naje gidan sa’adatu yanzu ma daga can nake”
Cike da kulawa ta amsa da “ya kika barota da fatan dai babu abinda ke damunta”

Idanun Rukayya ne suka ciko da kwalla a hankali tasa hannu ta share ba tare da innah ta gane ba
“Lafiya lau take amma ta……….” shiru tayi ta ƙasa karasawa.
“Me tace miki Rukayya kada kiyi shakkar faɗa min komai”
Rausayar da kanta tayi sannan ta cigaba da magana
“Ta bani labarin dukkan halin da take ciki da irin ka’idojin da Malam ya kafa mata bayan tafiyarmu”
Cikin nutsuwa innah ta dubeta “Dokoki kuma Rukayya dokokin menene haka?”
Girgiza kai Rukayya tayi “yace baya son a rika yawan zuwa kuma ita ma baxa ta riƙa fita ba sai da babban dalili, kuma dole ta fito ta girkawa matansa da ya’yansa abinci”
Hawayen da innah ke boyewa ne suka yi nasarar zuba daga idanunta jin an fama mata tabon dake cikin zuciyarta, a ranta take faɗa dama ta san za a yi haka amma baxa ta gushe ba tana yi wa diyarta addu’a har sai Allah ya sassauta mata halin da take ciki.Hankalin Rukayya ne ya tashi ganin yadda kamar innah take xubar da hawaye, wanda tunda suke basu taɓa ganin ta bayyana damuwarta ba ballantana har tayi kuka, fuskarta bayyane da damuwa ta riƙe hannunta.
“Haba innarmu bai kamata wannan maganar ta saki kuka ba na faɗa miki ne don ki xage damtse wajen taya Sa’adatu da addu’a, ki kuma yi kokarin jawota a jiki da kai mata ziyara don a wannan lokacin tana da tsananin buƙatarki, dan Allah ki daina kuka innah, kukanki zai zama ƙarin damuwa a gare mu, a yanzu tafi buƙatar addu’a da kwantar da hankali fiye da wannan kukan” +

Numfasawa Inna tayi tare da cewa “Shikenan na daina diyata” murmushi Rukayya tayi
“Yauwa innata Allah ya ƙara miki hakuri da juriya” amsawa tayi da “ameen”.
Cigaba da magana Rukayya tayi “innah idan kina da zanin gado ko tsoho ne ki kawo a kaiwa Sa’adatu katifarta haka take tsura ba shimfida, daxu umma ta bani labule da yan kayan aiki na kai mata, amma baxa su isheta ba sbd ba masu yawa ba”

“Kai!!! Amma mun gode Allah ya ƙara zumunci Allah ya saka mata da alkhairi kice ina godiya da kulawarta gare mu, Insha Allah ina kokari xan samo mata ko a wajen saratu ne, fita ne ban samu ba shi yasa, duk ranar da na fita xan je na karbo na baki ki kai mata”

Har Rukayya ta tashi xata tafi ta juyo tana dubanta idanunta kamar zasu kawo hawaye “Akwai abinda nake son faɗa miki innah amma dan Allah kada ki sa damuwa a ranki, xan fada miki ne kawai idan kina da taimakon da xaki iya bawa Sa’adatu”
Fuskarta a sake tace ina jinki ‘yata.

“Cikin irin dokokin  da malam ya kafa mata har da na rashin zuwa asibiti duk irin tsananin cutar da ke damunta, yace shi gargajiya ake yi a gidansa baxai ta taɓa bari matarsa taje asibiti ba, dan Allah ki faɗawa Baba ko xai tsawatar masa a kan haka, duk cikin dokokin da ya saka mata babu wacce ta fi daga min hankali sama da wannan”

Har ga Allah innah taji ciwo a ranta sbd babu uwar da xata so ta aurar da yarta ga irin wannan mijin, kuma ya kafa mata wadannan zafafan dokokin, kawai don ba tada yadda zata yi ne amma da sai ta rushe wannan dokar, cikin jarumta innah ta fara magana.

“Haba Rukayya don wannan kika tashi hankalinki kowane ɗan Adam fa da irin ƙaddararsa, kika sani ko hakan ya zama silar samun aljannarta idan tayi hakuri ta jure tayi ibada ta yiwa mijinta biyayya, kije ki faɗawa sa’adatu  ta karbi wannan kaddarar hannu biyu kuma ta godewa Allah,idan ta duba tata ma da kyau a kan ta wasu, kada ta manta komai yayi zafi maganinsa Allah, kuma DUKKAN TSANANI yana tare da sauki, kija hankalin ta a kan muhimmancin yiwa miji biyayya da hadarin saɓa umarninsa, ki faɗa mata yanzu Malam Jibo a matsayin mijinta yake ta danne zuciyarta tayi masa dukkan abinda ya umarceta kuma ta gujewa saɓa umarninsa domin aljannarta tana ƙarƙashin kafafunsa sai ya daga mata zata wuce, duk rintsi duk wuya kada ta yarda ta danne hakkinsa ko yaya yake sbd sakayyar aure tun a duniya Allah yake nuna ishara, kuma kice mata ta fito cikin matansa ta kama girki kamar yadda suke yi, kuma tayi ƙoƙarin taka rawar da matan aure ke yi a gidajen mazajensu, ina rokonki kema ki ƙara nusar da ita girman miji, kuma ki koma yanxu dan Allah ki faɗa mata sakona, nasan xai yi tasiri a zuciyarta kuma xata ji saukin damuwar da take ciki a yanxu”
Jikin Rukayya ne yayi sanyi sbd jin nasihohin innah gaskiya innah uwace wacce ta amsa sunanta uwa, dukkan wanda ya samu kamarta a duniya ya dace tana da xurfin hankali da tawakkali gami da yarda da dukkan abinda Allah ya tsara mata a rayuwa. Ita kanta zuciyarta tayi sanyi da taji kalamanta tashi tayi tare da yi mata sallama ta nufi gidan sa’adatu kamar yadda Innah ta umarce ta.

Fitar Rukayya ke da wuya ta kifa kanta  ta cigaba da zubda  hawaye masu zafi, tashi tayi ta dauro alwala ta ɗauki Kur’ani ta fara karantawa don ta san shi kaɗai ne abinda zai saukaka mata damuwarta.

**********

A ƙarshen katifa nake zaune na haɗa  kai da gwiwa, babu komai a raina banda kewar Rukayya da innah na riga na saba a dai-dai wannan lokacin muna tare muna hira, idan bana gidanmu ina wajen Rukayya, sallamarta ce ta dawo da ni hankalina ba ƙaramin farin cikin sake ganin Rukayya nayi ba a karo na biyu, fuskata bayyane da farin ciki nake mata magana “kamar kin san tunaninki nake yi babu komai a raina banda kewarki, daxu sai naji kamar na biyo ki mu tafi gida, da fatan dai kwana xa kiyi ko?”
Cike da zaulaya Rukayya ta dube ni “ya za a yi na kwana so kike malam ya koro ni xan hana shi cin amarci”
Duka na kai mata “Allah ki daina wannan maganar ko mu yi faɗa”
Kama hannun juna muka yi muka ƙarasa wajen da xamu xauna. Kallona Rukayya tayi “yanzu fa daga wajen innarmu nake” cikin murna nake tambayarta lafiyar innata da halin da ta barta a ciki. +

“Lafiyar innah kalau tana cikin farin ciki amma dai tana ɗan kewarki kaɗan” harararta nayi “da yawa take kewata ai ni aminiyar innah ce ba tada kawar da ta wuce ni” ture ni tayi “Ni din kuma fa a ina kika ajiye ni?” 
Toshe baki nayi “Au na manta kiyi hakuri ban miki kara ba”.

Mayar da kallonta tayi gare ni “Inna ta bani sakonni masu yawa kuma masu muhimmanci, haka tace min lallai na isar da su gare ki a yau ba sai gobe ba, don har nayi niyyar wucewa gida ta sake jaddada min cewa lallai naxo na faɗa miki”.

Bata hankalina nayi sbd na san dukkan sakon da innah xata bayar mai muhimmanci ne gare ni, kuma mai tasiri ga xuciyata sannan kuma xai taimaka wajen sassauta damuwata cikin nutsuwa nace ina jinta

Faɗa min nasihohin  innah tayi, Sannan ita ma taja hankalina a kan na bi dukkan abinda ta faɗa min sbd innah ita ce wacce tafi sona a duniya baxa ta faɗa min abinda zai cutar da ni ba.

Kafin ta tafi sai da ta sanyaya min xuciyata da kalmomi masu kwantar da hankali kasancewar Rukayya yarinya ce mai tunanin manya da xurfin ƙwaƙwalwa, sai na nemi dukkan damuwata na rasa, bata tafi ba sai da muka yi sallar magariba, ko da ta tafi ban yi sakaci ba tashi nayi na dauki Kur’ani na fara karatu ina addu’ar Allah ya bani ikon bin abinda Innata ta umarce ni, da kaucewa sabawa malam Jibo a haka na kasance har nayi sallar isha.


Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *