TSANANI
CHAPTER 7
Bayan na gama karatun Alkur’ani kishingida nayi sbd ina so na ɗan huta amma duk da haka bakina bai bar ambaton Allah ba, tashi nayi na karkade katifata na shimfida zanin gadon da innah ta aiko min da shi.
Sallama malam Jibo yayi tare da dage labulen dakina, ina ganin shi na tashi zaune tare da amsa masa sallamar, tsaye yake a bakin kofa bai karaso inda nake ba ya fara min magana “Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida” haɗe fuska nayi ban amsa masa ba, murmushi yayi “wai sai yaushe xaki daina fushi da ni Sa’adatu na zaci komai ya wuce a tsakanin mu, dan Allah ki saki ranki ki min murmushi ko zan ji daɗi, wai kin ci abinci ma kuwa naga tsakanin jiya da yau kin ɗan rame, ko sai naxo na dura miki ne” duk maganar da yake min idanuna na ƙasa ban dago na kalle shi ba ballantana na bashi amsa. Sako kafarsa yayi cikin dakin ya cigaba da yi min magana.
“Sa’adatu ina so ki dafa min ruwan wanka xan ɗan watsa a jikina ko xan ji dadi, yau kin san a dakinki xan kwana ina so na faranta miki ranki sosai, shi yasa zan yi wankan nan amma banda haka babu abinda zai sa na watsa ruwa a jikina da wannan uban sanyin, da fatan kema xaki tanadi abinda zai faranta min raina sosai don na san ke ɗin ba ta wasa bace” ya karasa maganar yana wata irin dariya.
Kallon shi nayi tare da mayar da kaina gefe idan yana magana a wasu lokutan kamar ba babba ba, da farko naji kamar kada na dafa masa ruwan amma sai na tuna da nasihar innah hakan yasa na tashi, duba gefena nayi tare da miƙa hannu na dakko tukunyata yar madaidaiciya hanyar fita na nufa tare da cewa
“Bani hanya na wuce” murmushi yayi “Haba Amaryar malam zaki iya wucewa ai babu wani abu don jikinki ya gogi na mijinki, ni da ke duk abu ɗaya ne don an riga da an bamu junanmu, zamu iya cin karenmu babu babbaka babu abinda zamu samu sai lada”
komawa gefe nayi sbd bana son kusantar inda yake a lokacin da yake min magana kasancewar shi mutum ne da bai damu da tsaftar hakoransa ba, ganin na ja da baya ne ya bashi damar sake matsowa inda nake tare da cafkoni ya mannani a kirjinsa yana sumbatar goshina ƙoƙarin kwatar kaina na shiga yi ina faɗin ya sake ni, sai kace na ƙara masa kaimi ya cigaba da shafa gashin kaina da sumbatata, cikin wata irin murya yake min magana. “Me yasa kike min haka Sa’adatu ya kike so nayi da raina idan kina min rowar jikinki, ki faɗa min dukkan abinda kike so na canja wanda zai sa ki soni, ki kuma riƙa bani kulawarki sbd ni dai ina sonki kuma har abada baxan taɓa rabuwa da ke ba duk irin wulakancin da xaki yi min”
Muryata na rawa na amsa masa “ka sake ni na dawo daga ɗora maka ruwan wankan sai mu yi magana” sai da ya gama mammatsani sannan ya sake ni, numfashi na shiga mayarwa ban san lokacin da hawayen takaici ke zuba daga idona ba, taɓa min jikin da yayi ba ƙaramin bata min rai yayi ba, takalmi na saka na fita wajen da matansa ke yin girki, ɗaya daga cikin matan na tambaya wajen da itacen girki yake, fuskarta a sake ta amsa min sannan ta miko min sai da ta taya ni kunna wuta sannan ta dawo wajena ta zauna, hira ta fara min tare da bani labarin halayen mijinsu da abubuwan da yake so da wanda baya so, kaɗan-kaɗan nake bata amsa sbd bana so ma na saba da kowa a gidan fatana kawai na fita na bar musu gidansu na huta.
Sai da na tabbatar da ruwan ya tafasa na surka masa sannan na wuce daki, makalewa nayi a bakin kofa tare da cewa “na surka maka ruwan wankan kaje ka kai shi banɗaki kada ya huce” ina gama faɗa na koma bakin dakin na zauna.
A tsaye yake a kaina da cewa “tashi mu shiga ciki akwai abinda nake son faɗa miki” dagowa nayi na kalle shi “ka fadi dukkan abinda xaka faɗa a nan ina saurarenka”
Ganin ba nida niyyar tashi ne yasa ya ɗauke ni cak ya shigar dani cikin dakin, cike da mamaki na dube shi.
“Bana son irin abin nan da kake min, na faɗa maka bana so nayi maka abinda zan shiga hakkinka, amma kai kullum kokarinka kayi min abinda zaka tunxurani, ka saka ni aiki yanzu nayi abinda ka umarce ni, menene dalilin da yasa yanxu kuma zaka dakkoni, na fada maka baxan iya tafiya da kaina bane??”
Kallo ya bi ni da shi, sannan ya bude baki ya fara magana “naga ba ki da niyyar shigowa ne shi yasa na dakko ki kuma ai ba haramci na aikata ba tunda jikin matata na taɓa, kuma don naga yau kamar sarauta kike ji ne shi yasa na dakko ki, kuma ma dai bana so kiyi wahalar tafiya da kanki shi yasa na aikata hakan”
Shiru nayi ban bashi amsa ba, gabana ya dawo yana fuskantata, “kince xaki fada min abinda kike so na gyara wanda zai sa ki daina guduna ko?”
Gyada kai nayi alamar “eh” +
Gyaran murya yayi to faɗa min don ina so na faranta miki, kuma ina so na samu farin ciki daga gare ki, don ki daina guduna.
Baƙin cikin jin kalamar samun farin ciki daga gare ni ne yasa naƙi faɗa masa abinda nake son ya gyara, don ni gyaransa da rashin gyaransa bai dameni ba, duk yadda yaso yaji daga gare ni bai samu ba.
Ganin ruwansa na neman salamcewa ne yasa ya miƙe, tare da cire kayansa gefe nayi da kaina tare da ƙoƙarin kawar da numfashina sbd warin da ke tashi daga jikinsa, babbar riga ya mayar ya fita, bar min boxes dinsa yayi a cikin dakin wanda shi ne ya ƙara taimakawa wajen ƙaruwar wari a dakin, Allah Allah na riƙa yi ya dawo ya ɗauke kayansa don ni ko taɓa shi baxan iya yi ba.
Bai fi minti biyar da tafiya ba ya dawo, wasu matattaun kaya ya sanya komawa kan katifata yayi ya kwanta, ni kuma kasa na samu can kusa da kofa na zauna sai da nayi sallar isha sannan na kwanta ban farka ba sai Asuba.
Fita nayi na daura alwala na dawo daki na fara tashinsa, duk maganar da nayi masa sai ya nuna bai fahimci abinda nake nufi ba, har sai da na fita waje na samu ruwa na ɗan shafa masa sannan ya bude ido, cikin nutsuwa nace masa “lokacin sallah yayi”
Amma ga mamakina sai naga ya mayar da kansa ya cigaba da bacci abinsa, duk ƙoƙarin da nayi wajen ganin ya farka yayi sallar Asuba bai tashi ba sai wajen bakwai na safe yayi sallar Asubah.
‘Dansa ya aiko ya kawo min koko da kosai bayan yaron ya fita ya shigo, fuskarsa a d’aure yake min magana “kada ki kuskura ki sake yi min katsalandan a cikin lamarina, daga yau sai yau kada ki sake tashina idan ina bacci, kece xaki faɗa min abinda ya dace da ni, hankali kika fi ni ko girmata kika yi?? naga dai duk karatun da kike takama da shi a wajena kika same shi, to nayi miki kashedi na karshe idan kika sake min haka xaki ga ɓacin raina” yana gama faɗa ya fita don ko abincin karyawar sa bai tsaya ya karba ba.
Ban yi mamakin jin hakan daga gare shi ba, don dama tun muna makaranta idan lokacin sallah yayi baya bata muhimmanci sai dai ragowar malamansa su yi shi kuwa ko a jikinsa.
***************
Zaune Rukayya take tana nazarin irin rayuwar da kawarta ta tsinci kanta a ciki, tana cikin tunanin ta tuna alkawarin da ta yiwa Sa’adatu na samun izuddeen ta bashi hakuri dangane da abinda ya faru, wayarta ta ɗauka ta shiga neman numbersa ta fara kira.
A xaune yake yana kallo yaji shigowar kiran Rukayya, yana dubawa yaga bakuwar number da har baxai ɗauka ba, sbd baya ɗaga number da bai sani ba, shahada yayi ya karata a kunnensa tare da yin sallama.
Da farko bai gane ita bace sai da tayi masa bayani ita ce, kasancewar wayarsa ta fadi tun bayan fitowarsa daga police station, bayan sun gama gaisawa ne ta fara yi masa magana cikin murya mai taushi.
“Sa’adatu ta bani sako na fada maka”
Jin an ambaci Sa’adatu yasa ya gyara zama tare da bata hankalinsa dari bisa dari don jin sakon da ya fito daga wajen Sa’adatunsa.
Fuskarsa a sake ya amsa mata da “ina saurarenki kawarmu”
“Na san kai Musulmi ne izuddeen kuma ka yarda da ƙaddara ka yarda da cewa Allah shi ke bayarwa kuma shi ke hanawa, kuma dukkan abinda bai zo hannunka ba to ba naka bane, kuma dukkan abinda yaxo hannunka rabonka ne duk rintsi duk wuya babu dan Adam din da ya isa ya kwace maka” amsa mata yayi “da haka ne Rukayya ina jinki”.Wani abu taji ya taso mata na baƙin ciki amma sai tayi ƙoƙarin mayar da shi sbd bata so ta fiye saka damuwa a ranta.
“Na san ba lallai ne kana da labarin abinda ya faru ba ko?”
Da sauri ya amsa mata da “Eh” yana da labarin dukkan abinda ya samu Sa’adatu sbd har gida aka xo aka faɗa masa labarin, ya nuna mata bai sani bane sbd bai sani ba ko wani sabon abin ne ya taso.
A hankali ta cigaba da magana.
“Bayan zuwan nan da yan uwanka suka yi a kan maganar aurenka da Sa’adatu, a ranar mahaifinta ya daura mata aure da Malam Jibo, don har an kaita ma yau kwananta biyu a gidan, shi ne tace na sameka na faɗa maka kayi hakuri ba da son ranta hakan ya faru ba, kuma idan ka samu mace kayi aure, tace ka kasance mai yawan yi mata addu’a kuma kada ka manta da ita da irin soyayyar da take maka” +
Numfashi mai xafi ya furzar muryarsa na rawa kamar xai yi kuka yake magana.
“ki faɗa mata baxan manta da ita ba har abada, duk inda na kasance a rayuwata, ki mata albishir ina sonta kuma xan jirata baxan taɓa aure ba har sai ta fito ko ‘ya’ya nawa ta aura, kuma ki faɗa mata ta kasance mai biyayya ga mijinta insha Allah sai mun mallaki junanmu”
Kuka ya fara yi sosai, wani ciwo sabo Rukayya ta tabo masa, haka Rukayya ta kashe wayar ita ma xuciyarta cike da tausayin masoyan guda biyu.Yau kusan satina biyu a gidan malam Jibo har na fara canjawa daga kamannina na Sa’adatu xuwa wani sunan daban, saboda tsabar wahalar da nake girba na girki da aiyukan gida, kusan girkin mutum talatin nake yi a duk ranar girkina, sannan kuma babu mai taya ni ko iza wuta duk da cewa gidan akwai yan matan da xasu iya taimaka min da wani abun, gani ba gwanar iya tuka tuwo ba haka dai na daure na koya, wata rana yayi kyau wani kokacin kuma ba yabo ba fallasa, ko xan mutu da aiki babu mai taimaka min sai dai idan na gama a xo ci karshe ma yaran gidan su yi min rashin kunya haka nake kyale su ba tare da na tanka musu ba, abinda yasa bana damuwa da abinda suke min sbd nasan insha Allah xamana ba mai tabbata bane a gida.
Taimako ɗaya Allah yayi min duk tsayin satukan da na shafe a gidan malam Jibo, Allah bai bashi damar cimma burinsa na sanina a ‘ya mace ba, sai dai mu sha kokawa ya gaji ya kyale ni.
Da yake yau ba a dakina yake ba shi yasa bani damar samun isasshen bacci, don matuƙar yana dakina ba ni da kwanciyar hankalin kwantawa nayi bacci kamar kowa, sbd fargabar kada ya min illa ina bacci, tun bayan da nayi sallar asuba ban farka ba sai wajen sha biyu don ko karyawa ban yi ba, tashi nayi a hankali na nufi banɗaki ina isa wajen naji wani wari na tasowa a daddafe na kwara ruwa na ɗan wanke shi sbd baxan iya amfani da shi a haka.
Zan shiga kenan naji ana min magana waiwayar da xan yi naga uwar gidan Malam Jibo ce a tsaye tana ƙare min kallo, nima kallonta nayi tare da sauraren jin abinda xai fito daga bakinta, sai da ta gama ƙare min kallo tsaf sannan tayi magana.
“Na fuskanci tunda kika shigo gidan nan kike mana gani-gani kin wi fitowa cikinmu ki sake tamkar wacce kike ƙyamar mu da yayanmu, yanxu kin xo shiga banɗaki kin hau toshe hanci kamar waɗanda xamu shafa miki cuta, alhalin mun san gidanku mun san tarihinki gaba ɗaya ke ba yar kowan kowa bace, kamar yadda labari ya tabbatar mana mannawa mijinmu aka yi, idan kinga baxa ki iya hakuri da yadda muke ba, xaki iya tafiya dama mu ba a son ranmu aka dakko mana ragowar karuwanci aka kawo mana gida ba”
Kallonta nayi zuciyata cike da mamakin jin waɗannan kalaman daga gareta, har nayi niyyar mayar mata da martani sai kuma na fasa, sbd bai kamata karya tayi min haushi ba ni kuma rama, kuma ko ba komai akwai banbanci mai yawa tsakanina da ita, wannan yasa na kyaleta na cigaba da abinda nake yi.
Daya daga cikin matan nasa ce ta taso tana mata magana.
“Haba maman biyu wannan abinda kika yi bai kamata ba, kuma zubar da kima ne da mutunci, kuma ko yanxu kin xubar da girmanki a idonta wanda hakan bai dace da ke ba, tunda yarinyar nan ta shigo gidan nan bata yiwa kowa abinda xata bata masa rai ba kullum kokarin kyautata mana take yi, kuma tsakani da Allah ko mu idan xamu shiga banɗakin nan sai mun wanke sbd mutane ne daban daban suke shigarsa laifi ne don mutum ya tsaftace wajen da xai biya bukatarsa, gaskiya bai kamata ba kuma hakan da kika yi xai bawa yaran mu damar rainata, ko me tayi a baya bai kamata ki goranta mata ba tunda dai Allah ta yiwa ba ke ba kuma idan yaga dama dai yafe mata” jikinta ne yayi sanyi da jin kalaman yar uwar tata na lura duk kunya sai da ta kamata, shiga banɗakin nayi na kyale su tana ci-gaba da yi mata faɗa ni kuwa ko kadan abin bai bata min rai ba sbd na san ban aikata abinda ake zargina da shi ba.A tsantsame nayi wankan duk ina jin kyankyami, kasancewar masan gidan a cike yake fal da kashi gashi ko murfi basu saka masa ba, ga iyayen kyakyasai da suka mamaye shi abin dai sai wanda ya gani, don kawai bana son kazanta ne amma da baxan iya wanka a wannan banɗakin ba ko don kada na kwashi wata cutar.
Ina gamawa na shiga daki na saka kayana har da hijab kamar dai mai shirin zuwa unguwa, fitowa nayi tsakar gida na shimfida sallayata na zauna kasancewar garin ana ɗan zafi.
Daga soro na jiyo murya kamar ta ya salim, tsayar da hankalina nayi don sauraren muryar mai maganar, a karo na biyu kuwa naji ya ambaci sunana da sauri na tashi na nufi soron
Ina ganin shi wasu hawaye masu xafi suka riƙa xubo min sai naga kamar innata na gani sbd ya salim yana cikin mutanen da suka gwada min so, sai na rasa kukan me nake yi kukan murna ne ko na baƙin cikin halin da nake ciki.
Hankalin shi a tashe ya dube ni “ki daina kuka sa’ar mata kada kisa hankalina ya tashi ziyara na kawo miki domin kiyi farin ciki ba na xama silar sanyaki a damuwa ba, sai da nayi kukana sosai duk lallabanin da yayi bai sa nayi shiru ba sai da nayi mai isata sannan na hakura.
Cikin gida na shiga na dakko masa tabarma kasancewar Malam Jibo baya bari namiji ya shigar masa gida duk kankantarsa, wannan yasa na dakko masa tabarma na shinfida masa.
Waje ya samu zauna muna fuskantar junanmu, tambayar farko da ya fara min shi ne babu abinda yake damuna kuma babu abinda malam Jibo yake min wanda yake kuntata min.?
Nan da nan naji idanuna xasu kawo hawaye amma sai nayi ƙoƙarin shanyewa sbd bana son na d’aga masa hankali girgixa kai nayi alamar babu komai.
Tsare ni yayi da ido yana sake tambayata “ki fada min gaskiya sa’ar mata wane ne zai kalle ki yace babu abinda yake damunki, ko makaho idan ya dube ki zai fahimci akwai damuwa a tattare da ke, dubi fa yadda kika yi baƙi kika rame, sati biyu kacal da aurenki amma duk yanayinki ya canja, kin xama kalar tausayi”
Share guntun hawayen da ke shirin fito min nayi “babu abinda yake damuna sai kewarka kai da innah, sai kuma aikin da nake yawan yi wanda ya fi karfina shi yasa kaga na rame”
A xubure ya dube ni “aikin me kike yi da har yake shirin yi miki illa haka?”
Rausayar da kaina nayi “aikin girki ne na kusan mutum talatin shi yasa kaga na rame”
Kallon tausayawa yake bi na da shi “kiyi hakuri Sa’adatu komai mai wucewa ne wata rana xaki ji dadi har ki bada labarin irin wannan halin da kika shiga”
Sake jefo min tambaya yayi “amma kina samun abinda kike so kina ci ko? dan na sanki sari ba gwanar cin abinci bace kin fi son kiyi ta xama da yunwa, wai ke kada kiyi kiba”
Har sai da ya bani yar dariya.
A takaice na bashi amsa da “bana iya ci” kallon mamaki yake bi na da shi bakya iya ci kuma to sbd me, kinga irin halin naki ko” +
Kaina a sunkuye nace “Abincin da aka dafa da daddare shi ake ci safe da rana sai wani daren ake sake yin sabon girki shi yasa bana iya ci”
Na lura da ya salim kamar kuka yake son yi amma ya daure, a hankali ya fara min magana “Allah sarki sa’ar mata Allah yana tare da ke kuma zai kawo miki mafita”
Hannu yasa a aljihu ya miko min “karbi wannan duk lokacin da aka yi abinda bakya so ki siya abinci ki ci wannan zaman baxai yiwu a haka ba, sbd Allah ne kaɗai yasan ranar fitar ki daga gidan nan tunda aure rai ne da shi, sai lokacin da Allah ya ƙare shi xai mutu, ki cigaba da hakuri da kuma jajircewa da ibada da addu’a nima xan taya ki”
Gabana ne ya fadi jin yana kiran Allah ne ya san ranar fitata daga gidan Malam Jibo, sai da na ɗan yi nazarin maganar na wasu lokaci sannan naga gaskiya ya faɗa min.
Cike da ladabi nasa hannu na karbi kuɗin tare da cewa “na gode ya salim Allah saka da alkhairi Allah ya bude maka hanyoyin samu, amma fa kaima ba kudi ne da kai ba me yasa ka bani kuɗi masu yawa haka, kada ka karar da yan canjin naka”
Cike da kulawa yake min magana
“duk abinda nayi miki wajibina ne kuma ban yi asara ba Sa’adatu fatana dai Allah ya kawo miki ƙarshen wannan matsalar da kike ciki, insha Allah kuma sai kin ji dadi a rayuwarki, kuma ki kwantar da hankalinki da yardar Allah kin kusa fita daga wannan kurkukun da aka kawo ki”
Wannan kalmar da ya faɗa karaf ta shiga kunnen malam jibo ashe ya dawo ma basu sani ba sai kawai ganinsa suka yi a kansu yana musu masifa.
“Dama kaine munafukin da kake xuwa har gida kana hure mata kunne kada tayi zaman aure da ni ko, shi yasa na rasa duk wani farin ciki daga gareta, take wulakanta ni tare da tozartar da son da nake mata duk gwanintar da xan yiwa yarinyar nan baxan taɓa burgeta ba, to wallahi yau Allah ne kaɗai xai raba ni da kai, har gidanku xan kai ka naji idan kwangila ma ka karbo daga hannun wannan ɗan iskan yaron don kayi sanadin raba aurena da Sa’adatu”
Kafin ya salim yayi magana har ya sheke shi ya fara ƙoƙarin dukansa,
Kokawa suka shiga yi da ya salim, wuyan rigarsa ya kama yana xaginsa shi dai ya salim bai tanka Masa ba sbd yasan mutuncin na gaba da shi, duk abinda ya faɗa masa sai dai ya bi shi da kallo kawai.
Gidan su Sa’adatu suka nufa don gayawa mahaifinta abinda salim din yayi masa.A soron nake tsaye kamar wacce aka kafe na kasa komawa cikin gida, duk fargaba da tsoro sun mamaye zuciyata addu’a ɗaya nake yi Allah yasa kada malam Jibo yaje ya fadi karya da gaskiya ya kunno min wani shirrin a wajen Baba, ban iya komawa cikin gida ba a soron na tsaya don jin abinda zai dawo min da shi, fatan da nake yi Allah yasa wannan zargin da yayi mana ya zama silar rabuwar auren gaba ɗaya.
Jan salim ya riƙa yi tamkar ya kamo barawo shi kuwa bin sa kawai yake kamar raƙumi da akala.
Cikin soron gidan su suka shiga, sallama malam jibo ya shiga yi, jin muryarsa da Baban Sa’adatu yayi shi ne dalilin da yasa ya fito da sauri don duk lokacin da yaji malam Jibo yana irin wannan sallamar yasan ba lafiya.
Ganin shi riƙe da kwalar rigar salim ne ya bashi mamaki gami da tambayarsa ko lafiya, yana huci ya fara bashi amsa. +
“Wlh yaron nan naku ɗan kwangilar kwartanci ne, masifa yake ƙoƙarin kunna min a gidana, shi ne yake ƙoƙarin kashe min aure, yanzun nan daga wajen Sa’adatu yake yaje yana xugata, a kan ta rabu da ni ban dace da rayuwarta ba, har faɗa yake idan tana son guduwa xai bata mafakar inda zata buya, kuma zai bata kuɗin motar da zata tafi”
Wani kallo Baban Sa’adatu ya bi salim da shi tare da girgiza kai. “tabbas duk abinda aka zargi yaron nan da shi baxan yi musu ba Malam, sbd tun tana gida shi ne mai shige mata gaba ta rika yin shashanci”
Cikin fushi ya shiga nuna Salim da yatsa “Wannan ita ce tarbiyyar da muka baka ko salim? dama duk abinda Sa’adatu take yi kaine kake goya mata baya ko, cin amanar da xaka yi min kenan me nayi maka kake bina da sharri haka? Allah ya isa tsakanina da kai”
yana ƙarasa fadar haka ya shige cikin gida.
Bangaren su salim ya shiga inda ya kira mahaifinsa, ganinsa a gigice ne yasa ya fara tambayarsa amma bai saurare shi ba ballantana ya bashi amsa.
Hankalinsa a tashe ya sake dubansa “lafiya yaya na ganka a hargitse haka Allah yasa dai ba wani abin ne ya taso ba, don naga kamar baka cikin nutsuwarka”
Kofar fita ya shiga nuna masa “mu je soro kaga irin maganar da salim yake shirin dakko mana muna zaman mu lafiya” jin ya ambaci salim ne ya sa ya fita da sauri hankalinsa a tashe ko takalmi bai saka ba ya fita.
Har yanxu dai malam Jibo rike yake da wuyan salim yaƙi sakinsa, ba don bazai iya kwacewa bane yasa ya kyale shi kawai don yana gani mutuncin wanda ya girme shi ne.
Cike da mamaki mahaifinsa yake magana “Lafiya malam Jibo wani abu salim yayi maka haka naga ka riƙe masa wuyan riga, Allah yasa dai ba aika-aika yayi maka ba”
Gyara tsayuwa yayi fuskarsa a murtuke ya fara magana
“Na Kama su suna lalata shi da Sa’adatu, kaga abinda yayi yafi ƙarfin mu kira shi da aika-aika sai dai lalata”
Cike da tashin hankali salim ya dubi malam Jibo “ka rantse da Allah abinda ka kama mu muna yi kenan, da girmanka ka rika karya kaji tsoron Allah duk abinda ka faɗa yana kallonka kuma Mala’iku suna rubutawa, kuma zaka tsaya ranar shaida” Daka masa tsawa mahaifinsa yayi “yi min shiru mutumin kawai kada na sake jin bakinka, na shiga ban dauka ba ai bata fidda barawo, me yasa kaje masa gida? da baka je ba zai ce kayi masa haka ne, ko kai kaɗai ne ɗa a cikin gidan nan, duk abinda ya faɗa dole mu yarda tunda daga gidansa ya kamo ka”
Sauke ajiyar zuciya Baban Sa’adatu yayi “gaskiya yarinyar nan ta cika lalatacciya, dama abinda take yi kafin aure shi ne bayan tayi auren ma baxa ta sallata ba sai ta ɗora daga inda ta tsaya, amma kuwa yarinyar nan bata ji daɗin halinta ba, malam Jibo kada kaga laifin salim ka fara ganin laifin Sa’adatu sbd ita ce ta gayyato shi yazo mata, da bata kira shi ba baxai zo ba, idan kayi aiki da hankali xaka ga cewa sai da ta lura baka nan sannan ta kira shi, ya zama dole na ɗauki mummunan mataki a kan yarinyar nan sbd idan nayi sake ƙarshe ni xata jawowa abin kunya
Cikin nutsuwa mahaifin salim ya dube shi
“A’a yaya ba haka za a yi ba a bi abin nan a hankali, sbd abu ne da yake buƙatar bincike ka bar min komai a hannuna zan san yadda za a yi” kallon salim yayi tare da cewa “tashi ka shiga shiga ciki ka jira mu da irin hukuncin da zamu yanke maka” +
STORY CONTINUES BELOW
Waje suka samu suka tsugunna gaba ko nutsuwar dakko tabarma basu samu ba, a hankali mahaifin salim ya fara tambayar malam Jibo “Naji dukkan abinda ka faɗa kuma bana goyon bayan yayana a kan abin nan da ya faru, tabbas basu kyauta maka ba, kuma ya keta maka haddi duk da kasancewarsa ɗan uwanta, bai kamata ya shigar maka gida kai tsaye ba tare da ya nemi izninka ba, tunda dai ba muharraminta bane, Amma ina mai baka hakuri zamu ɗauki matakin da ya dace a kansu”
Girgiza kai malam Jibo ya shiga yi “Babu wani mataki da zaka ɗauka ni xan ɗauki mataki da kaina sbd ni aka ciwa zarafin kuma ni aka zalunta”
A tsorace mahaifin Sa’adatu ya kalle shi “Dan Allah kayi hakuri malam kada ka sakar min ‘yata, idan ta dawo gida abinda zata yi sai ya fi haka, duk matakin da ka ɗauka a kanta xan amince kuma xamu yi biyayya, amma dan Allah banda na saki kayi mata hakuri tunda wannan shi ne karo na farko”
A wulakance ya dube su “shikenan naji amma abinda yake tayar min hankali shi ne, kada ta riƙa fita yawon banxarta ƙarshe ta kawo min cikin da ba nawa ba gida, tunda dai ni tunda nake da ita ko hannunta bata taɓa bari na taba ba, ballantana a kai ga auratayya”
Kallon kallo suka shiga yi shi da mahaifin salim, a sanyaye mahaifin nata yace “ya aka yi ka kyaleta tana wannan shashancin, dama akwai abinda take nufi dole ta hanaka hakkinka, yau din nan xan je har gidan na bata kashi sbd naga kamar akwai abinda yake mata yawo a hankalinta”
Sai da suka gama tsara yadda za a yi wa Sa’adatu hukunci, sannan suka rankaya gidan tare da shi da malam Jibo shi kuma Baban salim ya shiga gida.
Yadda nake a soron dai ban matsa ba ina nan ina tunanin irin yadda salim zai fuskanci matsala daga wajen iyayenmu, ganin basu juyo bane yasa hankalina kwanciya tare da komawa daki, ina mai addu’ar Allah ya kare salim daga sharrin malam jibo.
Komawa ta daki ke da wuya naji sallamar malam mutan gidan ne suka riƙa xubewa suna gaishe shi, tare da yi masa sannu da dawowa, daga can kuma naji murya kamar ta Babana kafin na tashi na fito naga ko waye har sun iso cikin dakina.
Ina ganin shi na zube kasa ina masa sannu da zuwa, kallon da yake bi na da shi ne ya tabbatar min da cewa ba lafiya ce ta kawo shi ba, tashi nayi na koma gefe cikina duk ya ɗuri ruwa sbd ban san da abinda suka xo min ba.
Malam Jibo ne ya dubi Baba “To kaga dai abinda nake fada maka malam Salisu haka take shigo min da karti kala-kala cikin gida idan taga bana nan na fita harkokina, ko ‘ya’yana ka tambaya abinda xasu faɗa maka kenan, yau ma Allah ne ya toni asirinsu ta ajiye kwarton nata a soro”
A tsorace na dube shi xan fadi gaskiyar abinda ya faru har na bude baki xan yi magana Baba ya dakatar da ni alamar nayi shiru, haka naja bakina na kulle sai da ya gama jero masa karya da gaskiya sannan ya mayar da kallonsa gare ni.
“Wannan ita ce sakayyar da xaki min Sa’adatu, dama ashe na kashe miciji ne ban sare kansa ba ina ganin na aurar da ke xan samu kwanciyar ashe tsuguni bata ƙare ba, ke a duniya ba ki da wani buri wanda ya wuce ki dakko min magana, yau xaki gane kuskuren abinda kika yi min, indai ni na haifeki yau sai ranki ya ɓaci”
Kafin na ankara ya dakko sabuwar bulala ya hau dukana da ita, malam Jibo na ganin haka ya fita yana murmushi, dukana yake ko ta ina iya karfinsa, duk kukan da nake yi bai saurare ni ba sai da yayi min laga-laga kamar baxai bar ni da rai ba, sai da yaga komai na jikina ya daku har Ina kokarin suma sannan ya kyale ni”
Hango kishiyoyina nayi su da ƴaƴansu cike a kofar dakina, duk sun zo kallon abinda ke faruwa, duk wanda yaji ance Babana ne yaxo hukunta ni sai dai kaga ana kama baki ana mamaki, kowa tunanin girman laifin da nayi masa yake da har yaxo gidana cikin kishiyoyina yake dukana a gabansu.
Kiran malam Jibo cikin rawar jiki ya shigo yayi fuskarsa ɗauke da murmushi yake kallonsa, da alama yaji daɗin hukuncin da aka yi min.Fuskar Baba a daure ya dube ni “wannan shi ne karo na farko kuma na ƙarshe a gare ki, idan na sake jin wani abu ya bullo tsakaninki da wannan bawan Allahn ni da ke ne, kuma ki saka a ranki matuƙar kika kashe wannan auren babu ni babu ke, kada ma ki nuna kin sanni ballantana har ki kirani da mahaifinki”
Mayar da kallonsa yayi ga malam Jibo
“Gata nan ka kula da ita ka saka mata takunkumi kada ka sake bari ko soro ta leka kuma duk wanda yaxo wajenta na baka damar ka koreshi tunda ta nuna ita ba yar mutunci bace” +
Jinjina kai ya shiga “madalla na gode malam Allah ya kara girma” sake kallona Baba yayi “mijinki ya bani labarin har yanxu baki bashi hadin kai ba to wlh gobe nake so yaxo min da labari mai kyau, idan naji sabanin abinda nake tunanin xan sake dawowa na ƙara baki kashi, tunda naga alama kunnen kashi gare ki”
Duk maganar nan da suke ina sunkuye ina ta gunjin kuka hawayen ma sun ƙafe saboda tsabar xafi da axabar da nake ji, ilahirin jikina duk a fashe yake na rasa gane kan irin wannan rayuwar da nake yi, kamar Babana baya sona haka nake gani don babu uban da xai iya yiwa yarsa wannan toxarcin da yayi min a gaban
Ya’yan miji da kishiyoyi.
Fita suka yi tare suka barni cikin yanayi mara dadi
Masoya kada ku damu da halin da Sa’adatunku take ciki ku yi hakuri haka tsarin labarin yake shi yasa ma na kira shi da tsanani insha Allah saukin na nan xuwa na tabbatar da cewa xaku yi farin ciki nan gaba.