TSANANI
CHAPTER 8
Bayan tafiyar su Baba da kaɗan, ‘ya’yan Malam Jibo suka riƙa shigowa dakina sahu-sahu suna tsokanata, haka na kasance a daki babu damar na fita tsakar gida sai uwar gidan ta riƙa yada min da magana, ko nayi niyyar ramawa sai na fasa sbd duk abinda aka min mahaifina ne ya fara zubar min da mutunci don haka ko me suka faɗa bana ganin laifinsu. +
Bayan na dawo ɗaki komawa nayi na kwanta sbd jirin da ke dibana, ina kwanciya na tashi sbd kwanciyar naji ba daɗi, duk na takura ina ta fama ciwon da ke jikina, don haka na fara ƙoƙarin tashi zaune amma na kasa, duba jikina na shiga yi sai naga duk jini ya bata min kayana, ina so na tashi na canja wani amma na kasa, kukana ne ya ƙara tsananta, addu’ar Allah ya duba halin da nake ciki ya kawo min mafita na riƙa yi
A ranar wuni nayi ban fito ba ko alwala a daki na riƙa yi sbd bana son na fita a faɗa min abinda zai sosa min raina, a zaune na riƙa sallah sbd zazzaɓi mai tsanani da ya kamani, shi kuwa malam Jibo tunda ya fita ban sake ganinsa ba, har zuwa wayewar gari kasancewar ba a dakina yake ba, ko shigowa ya duba halin da nake ciki bai yi ba, sai dai naji muryarsa a tsakar gida yana wasa da dariya da matansa.
Haka na kasance cikin kunci da damuwa musamman idan na tuna innata da yadda aka raba ni da ita, aka kawo ni wannan kurkukun, ga rashin abinci mai kyau uwa uba kuma ba kulawa, kullum ƙoƙarinsa ya za a yi ya sanya ni cikin halin baƙin ciki da damuwa.
************
Ko da Baban Sa’adatu ya koma gida bai samu ganin Salim ba, kafin ya koma ya tarar da shi har ya gudu sbd yana jin tsoron karansu da malam Salisu, duk jiransa da yayi don ganin ya same shi ya ci masa mutunci Allah bai yarda ba.
Salim bai sake dawowa ba sai washe gari, cikin sand’a yake shiga cikin gidansu, kai tsaye bangaren su ya nufa, a tsakar gida ya ci karo da mahaifinsa yana alwala, Sallama yayi tare da tsugunnawa ya gaida shi, wani kallo ya bi shi da shi tare da kiran sunansa.
“Salim jiya a ana ka kwana don na duba dakinka jiya, ban ganka a cikin yan uwanka ba, faɗa min inda kaje ka kwana”
Motsa baki ya shiga yi kamar yana son yin magana amma ya kasa sbd bai san abinda xai ce da mahaifin nasa ba.
Tsare shi yayi da ido ya sake tambayarsa “Ba magana nake maka ba, ka faɗa min inda kaje don baxan amince ka riƙa kwana a wani waje daban ba?”
Kansa a sunkuye ya amsa “A gida na kwana Baba amma ban shigo da wuri bane shi yasa baka ganni ba” a fusace yace “Ni xaka rainawa hankali, ka riga ka sani bana son karya, ya zaka ce a gida ka kwana alhalin na leka dakin da kike kwana ba adadi naga baka nan, ka faɗa min gaskiya tun kafin na saukar maka da fushina
Shafa fuskarsa yayi “A dakin abokina na kwana”
Ajiye butar da ke hannun shi yayi ya matso kusa da shi “yanzu kuma irin lalacewar da kake son yi kenan, banda laifin da kayi jiya yanxu kuma kana ƙoƙarin sake yin wani, me kake son xama ne Salim ka tuna kai fa ba ƙaramin yaro bane da za a ce kullum sai an fada maka abinda ya dace a kayi, ya kamata ka shiga hankalinka wannan ba rayuwa bace”
Kansa na ƙasa ya fara magana “kayi hakuri Baba insha Allah baxan sake yi maka irin wannan ba”
Girgiza kai yayi “zancen kenan kullum baxa ka ƙara ba amma gobe ma sai ka sake yi Allah yasa dai ka gyara halinka don bana so ka riƙa dakko min magana kullum”
Tashi yayi zai shiga daki ya gaida mahaifiyarsa kafin ya shiga har ta fito tana faɗin “Hmm sannu Salim sannu da aika-aikar da kayi, ka janyo min xagi da abin faɗa a tsakar gida, yanxu abinda kayi ya dace kenan ka daka ta wannan yar iskar yarinyar xata lalataka, tunda ita ta kwashe kayanta daga gaban Annabi menene na zuwa inda take..”
Saurin dakatar da ita Baban salim yayi “ke me yasa kullum bakinki baya son furta alheri ne, Sa’adatu ‘yata ce duniya da lahira kamar yadda salim yake ɗana don haka ki guji furta munanan kalamai a kanta”
Shiru tayi ta kasa cewa komai sbd tana tsoron mijin nata duk gutsuri tsomar da suke yi ita da innah salamatu bai sani ba, amma da ya sani da tuni ya dade da taka mata burki.
Nuna salim yayi “tashi kaje wajen wajen yaya yana son yi magana da kai, kuma ka bashi hakuri don ka fusata shi sosai” +
Tashi yayi ya fita bai bi ta kan kiran da Baban Sa’adatu yake yi masa ba ya wuce wajen harkokinsa
************
Kwance nake ina ta juyi yau da wani matsanancin ciwon ciki na tashi ga zazzaɓi da ke damuna, tun bayan da Baba ya dake ni ban ƙara samun sauki ba kullum ciwon gaba-gaba yake yi gashi ban sha magani ba ballantana nasa ran warkewa, shi kansa malam jibon tun daga wannan lokacin ban ƙara sa shi a idona ba, yau kusan kwana uku kenan, sautin nishin da nake yi ne ya fita har tsakar gida, shi ne dalilin da yasa ɗaya daga cikin matan nasa ta shigo dakina don ganewa idonta halin da nake ciki.
cike da tashin hankali ta dube ni “lafiya Amaryarmu?” da yake da wannan sunan take kirana, ban iya buɗe baki na faɗa mata abinda yake damuna ba sbd ni kaɗai na san irin radadin da nake ji, nuna mata cikina na shiga yi.
Cike da kulawa tace min “Sannu Allah ya baki lafiya watakila karuwa muka samu, Allah ya inganta”
Ganin yadda nake ƙoƙarin fita daga hayyacina ne yasa ta fita a gigice, kai tsaye soro ta nufa tare da shiga cikin shagon da yake zama, lekawa tayi tare da faɗa masa cewa ba ni d lafiya, kuma ina cikin mawuyacin hali, rokonsa tayi ya bata dama zata kaini asibiti.
A kaikaice ya dubeta “me yasa wani lokacin ba ki da lissafi ne Talatu? Kina so ki riƙa yi min shishshigi a harkar gidana, sai kace kin fi ni sanin dai-dai, shekarar ki nawa a gidan nan baki taɓa ganin an kai wani asibiti ba, kin san dai halina kin san tsarina ba zuwa wajen likita duk ciwon da xai kama mutum, tunda ina da maganina a gida babu wanda ya isa ya canja min tsari, amma ke kullum ƙoƙarinki shi ne kiyi min gyara a al’amurana sai kace ke kike aurena, ita yar gwal ce da baxa ta sha irin abinda nake haɗa muku ba, ko kuma zane ta fi ku a fuska, kije ki ƙara jaddada mata ba a taɓa zuwa asibiti a gidana ba kuma baxa a fara ta kanta ba”.
Wani kofi ya dakko ya barbaɗa garin magani sannan ya kafa kansa a bakin kofin, babu wani abu da yake karantawa banda tofa uban miyau da yake yi, miƙa mata yayi cike da ladabi tasa hannu ta karba tare da cewa “mun gode malam Allah ya ƙara hasken makaranta” cike da ƙasaita ya amsa da “Ameen”
Jikinta na rawa ta shigo dakina kafin tazo har na suma, da gudu ta sake fita ta kira ragowar matan gidan, ruwa suka shiga yayyafa min tare da jijjigani amma kamar dutse na kasa farfaɗo wa, sake komawa wajen Malam Jibo tayi ta sanar da shi cewa na suma a yatsine ya kalleta.
“Wai ke me yayi miki zafi da yarinyar nan ne, ke kika kawota gidan nan ko ni na kawota, naga kina xakewa da yawa a kan al’amuranta ko kina so ki nuna min cewa kema halinku ɗaya da ita?? Tun wuri ki fita daga idona ni na kawota kuma ni na san irin hukuncin da zan mata”
Hawaye ne suka fara xuba a idanunta cikin kuka take masa magana “ba ina nufin na fika sonta bane sai dai hakkinmu ne mu kula da ita da dukkan abinda ya sameta, sbd kaine a haqqu da ka kula da lafiyarta tunda har ka barota da wajen iyayenta”
Tsawa ya daka mata “ki kama bakinki ki kuma san me xaki riƙa faɗa min idan ba haka ba kema xaki shiga irin tarkon da ta shiga” jikinta a sanyaye ta kyale shi ta shiga cikin gida, tambayarta suka shiga yi ina malam, labarin yadda suka yi da shi ta kwashe ta faɗa musu.
Uwar gidan ce ta fita da kanta ta masa magana, sai da yaja lokaci sannan ya shigo, yana tafe yana baza babbar riga buɗe labulen ɗakin yayi ya shiga.
Xama yayi a ƙasa yana tofa mata miyau duk dakin ya rikice da warin bakinsa, babu abinda yake karantawa sai tofa miyau.Yau tunda innah ta tashi taji jikinta babu daɗi babu komai a zuciyarta sai tunanin Sa’adatu, ji take kamar ta tashi ta tafi gidan nata don taga halin da take ciki, amma kuma sai taji bata son xuwa sbd kada ta janyowa kanta abinda za a zo ana maganganu a kansa, har ta daure ta hakura sai taji baxa ta iya ba, tashi tayi ta nufi ɗakin mahaifin Sa’adatu don ta faɗa masa abinda take ji a ranta, har tasa Ƙafa ta shiga ciki ta juyo sbd ta ganshi tare da innah salamatu suna magana, don haka ta juya don bata son tayi magana a gabanta, juyawarta ke da wuya ya kirata a sanyaye ta dawo ta tsaya tana dubansa, fuskarsa a d’aure yace
“Ya naga kin shigo kuma kin juya lafiya dai ko?” A takaice ta bashi amsa
“Dama magana nake so mu yi kuma naga ba kai kaɗai bane shi yasa na koma”
Bin ta yayi da wani irin kallo “Ban gane ba ni kaɗai bane kina nufin ita Salamatu wata ce daban??”
Kanta a sunkuye tace “Ba haka nake nufi ba, naga ita ma tana magana da kai ne, kaga bai dace na katse muku hirarku ba”
Wani kallo innah salamatu ta watsa mata, mayar da kallonsa yayi ga innah
“Ba wani nan ke dai kawai akwai abinda kike son kullawa don kin ganta ne xaki canja magana, ke dai ki riƙa jin tsoron Allah wlh wannan halin da kika dakko ba halin kirki bane, gashi nan kin koyawa yarki baƙin hali bata kaunar yan uwanta gaba ɗaya, to ni baxan juri wannan abin ba ni bana son gulma da munafunci da raba ɗaya biyu, abinda ya yi ni shi yayi Salamatu duk abinda xaki fada min xaki iya faɗa a gabanta, ke ko baki faɗa ba ma sai na faɗa mata don tana da hakkin da xata san halin da kike ciki ke da yarki, tunda ita ce gaba da ke”
Mayar da ajiyar zuciya innah tayi tare da kallonsu gaba ɗaya, ba tare da tace wani abu ba ta juya ta kyale su suna mayar da maganar, tana fita aka saka faifan gulamarta cike da makirci innah salamatu ta dube shi kamar xata yi kuka.
“Na rasa me na yiwa matar nan ta tsane ni, kullum burinta taga bayana ni kuwa xama a gidan nan daram don ni taxo ta tarar, mugun halin da yake kunshe a ranta ya fi karfin cikinta, Allah ne yaga niyyarta ya barta a haka, yanxu banda tsabar masifa maganar ce baxa ta faɗa a gabana ba sbd ga munafuka ko, kada na kwasa na gayawa duniya, tunda bata son naji ni kuma wlh sai na san halin da ake ciki, tashi ka bi ta daki kaji me ke tafe da ita”
Da sauri ya miƙe ya shiga dakin innah , yadda taga ya shigo yana tambayarta abinda ya kawota ne ya bata mamaki, hakan ne ya nuna mata cewa ba yin kansa bane aiko shi aka yi, don haka ita ma a takaice take bashi amsar duk abinda ya tambayeta ba tare da ta wani sakar masa fuska sosai ba.
A hankali ta fara yi masa magana “Dama a kan maganar Sa’adatu ne yau na tashi duk jikina ba daɗi banda tunaninta babu abinda nake yi ko aiki na kasa yi, shi ne naga ya dace na tambayeka ina so xan je na ganta, kaga tunda aka yi aurenta ban taɓa zuwa naga muhallin ta ba ballantana na san halin da take ciki”
wani kallo ya bi ta da shi gami da gyara tsayuwa “kinga dakata bana son kinibibi da son iyawa, sai kace a kanki aka fara aurar da ‘ya xa kice xaki je ki ganta, duk yan uwanta da suke xuwa su ganta basu wadatar ba sai kin je da kanki dole kin ganta, wato salon kiga wani abin da bai miki ba ki kashe mata aure ko?? To ban yarda ba, kuma idan har kika je ban yafe miki ba, duk abinda kike so a yi mata ki faɗawa Salamatu xata yi miki, don ta fi ki kyakkyawar zuciya kece ma kike nuna mata baƙin hali amma duk abinda kake so xata yi miki”
Sai da ta bari ya kammala magana, cikin nutsuwa ta dube shi “Haba dan Allah malam idan aka yi min haka sam ba a yi min adalci ba, ya zaka yi min Allah ya isa a kan xanje naga halin ‘yata ɗaya tilo da na mallaka a duniya, duk abinda Salamatu xata yi min ai ba kamar wanda xan yi da kaina ba, gaskiya ka janye maganar Allah ya isan nan sbd idan aka yi min haka an shiga hakkina tunda kowace mace a gidan nan kana bari tana xuwa gidan yarta ni me yasa zaka yi min haka?”Yana gyara Babbar riga yake mata magana “sbd ke kin nuna kina ‘kin auren tun farko, shi yasa baxa ki taɓa zuwa gidan ba sai dai idan ita taxo miki, wannan dalilin ne yasa na saka miki wannan dokar kuma dole ki bi ta, matuƙar kika fara xuwa gidan Sa’adatu nasan xaman lafiya ya ƙare, kuma baxa ki bari yarinya tayi xaman aure ta xauna lafiya da mijinta ba” +
yana gama faɗa ya fita, duk abin duniya ne ya damu innah ta rasa abinda yake mata daɗi, wannan karfa karfar da ake mata ba ƙaramin mamaki take bata ba.
Tana cikin wannan halin ne taji sallamar Adda saratu, wani sanyi taji a zuciyarta taji kamar an yi mata gafara da murna ta fita tsakar gida tana yi mata sannu da zuwa kama hannunta tayi suka shiga daki tare da yi mata shimfida.
Tambayar farko da tayi mata shi ne ina Sa’adatu?? nan da nan fuskar innah ta canja daga farin ciki zuwa akasin haka, cikin rawar murya ta amsa mata da “tana gidanta” girgixa kai Adda saratu tayi “wallahi ina jin xafi a raina duk lokacin da na tuna Sa’adatu malam Jibo ta aura, wannan auren cuta har ina, shi yasa ma kika ga wlh ban taɓa karambanin xuwa gidanta ba, sbd bana son naje naga abinda xai bata min raina”
Murmushin takaici innah tayi “Ganin abinda zai bata miki rai ai ya zama dole saratu, don yadda naji labarin gidan abin ba dadi, nayi ƙoƙarin zuwa amma malam ya hana wai baxan bari ta xauna lafiya da mijinta ba, ko yanxu ma kafin kixo sai da nayi masa maganar yace Allah ya isa idan naje wai kashe mata aure xan yi”
A firgice Adda saratu ta dubeta “kan malam kalau kuwa? Ya za a yi ke da gidan yarki yayi miki Allah ya isa don kin je, gaskiya rayuwar gidan nan naku ba adalci, to ke yanxu kin hakura da xuwa kenan?”
Dagowa tayi “to ya xan yi saratu, na kyale shi tunda ina da ke na san ba nida matsala, idan kin je duk abinda xan yi kema xaki iya yi” girgixa kai tayi “Haka ne yaya insha Allah duk abinda ya kama xan yi miki”
Bayan sun ɗan yi hira sai ta kwatanta mata gidan Sa’adatu don xuwa ta ganta, ba tare da bata lokaci ba ta tashi ta nufi gidan, da farko da taje bata gane kwatancen ba sai da ta sake tambaya aka nuna mata, tun daga kofar gidan take jinjina irin wannan gida da ya kawo Sa’adatu gida kamar a ƙauye, ko fulasta babu a kofar gidan, ko’ina na cikin gidan ƙasa ne ga uwar kazanta, a soro taci karo da malam jibo ya sa benci yana zaune yana jan carbi, ya kasa ya tsare kamar mai gadi, sallama tayi masa, fuskarsa babu walwala ya amsa, neman hanyar wucewa ta shiga yi.
Tsareta yayi da ido yana tambayarta, “Baiwar Allah ba a shiga gidan nan sai da izni, naga kina kokarin wucewa ciki ba tare da kin tambaya ba da alama dai baki san dokar gidan ba ko”
Mamaki ne ya kama Adda saratu yanxu a wannan mataccen gidan za a ce sai an tambaya idan za a shiga, kallon mamaki ta bi shi da shi sannan ta fara magana.
“Au Yi hakuri malam ban sani ba ai”
Kallonta ya cigaba da yi “to ba matsala wajen wa xaki je”
Cike da nutsuwa ta bashi amsa da cewa.
“wajen Sa’adatu naxo” kamar ta yafa masa ruwan xafi yaji, don haka a fusace ya amsa da “Bata nan taje ganin gida, sbd tunda aka yi aurenta bata fita ba sai yau ta fara fita”
A kaikaice ta dube shi.
“Haba malam da girmanka bai kamata ka riƙa karya ba, yanxu haka daga gidan nasu nake ban ganta a can ba”
Fuskarsa a daure ya dubeta
“Nace miki tana can kije ki duba mana ya xaki saka ni a gaba ki riƙa tuhumata kamar wani yaron gidanki, matarki ce ko tawa?”
Ita ma gyara fuskarta tayi tare da haɗe rai
“Yau naga ikon Allah, me kuma yayi zafi haka daga tambaya sai faɗa, kai dai kace kawai baka son naje wajen Sa’adatu amma tabbas tana nan”
Ɗaya daga cikin ya’yansa ne yayi sauri yace da malam Jibo ” Baba Aunty amarya tana nan, ka manta tana can a kwance ba lafiya”
A firgice ta dubu yaron “Ba tada lafiya kuma??” Cikin zuciyarta ta rika addu’a Allah yasa dai ba ciki ne da ita ba.
Duka ya kaiwa yaron “ban hana ka wannan shegiyar maganar taka ta banxa ba nasa da kai ne, da xaka sa min baki, wlh idan kana mun haka ranka xai riƙa ɓaci”
Yana Cikin wannan maganar ta kewaye ta bayan shi ta wuce, bai lura ba sai da ta kusa kaiwa cikin gidan, da sauri ya bita bayanta yana masifa, shan gabanta yayi +
“Ba ki da hankali ne,ban baki dama ba zaki shigo min gida, idan bakya so na xubar miki da mutunci tun wuri ki fita ki bar min gida tun kafin ranki ya ɓaci”
Mamaki ne ya kamata “me kuma ya kawo maganar xubar da mutunci wajen yata naxo ina da hakkin da xan ganta don haka baka isa ka hana ni ba” A fusace ta wuce da sauri ya sake bin ta tare da tare kofar shiga bangaren Sa’adatu
Gardama ce ta tufke a tsakaninsu yana cewa baxa ta shiga ba, ita kuma tana cewa sai ta shiga, a fusace ya sake dubanta, “ke wace irin mace ce da bata san mutuncin aure ba tun farko na fada miki cewa bana bari a ga Sa’adatu ko mahaifinta ne yaxo a wannan halin bai isa ya ganta ba don haka ki kama hanya ki bar min gida tun kafin kiga abinda xai faru”
Kallon shi kawai take yi, don ita yanxu a shirye take duk abinda xai faru ya faru indai a kan Sa’adatu ne.
Musu ne ya kaure tsakanin su, baka jin komai sai tashin hayaniya, gaba ɗaya matan nasa sun bi gefe suna ganin rashin dacewar hakan da yake yi, amma kuma ba su da ikon yin magana sbd gudun kada ya huce a kansu, haka suka koma dakunan su suka barta da shi suna bugawa, yana cews baxa ta shiga ba ita, kuma tana sai ta shiga ko ta halin ƙaƙa, ganin ba tada niyyar fita daga gidan ne yasa ya fita wani kallo mai cike da tsana yake bin ta da shi yana tafe yana jan wani tsaki, babu wanda ya san inda ya tafi da abinda yake shirin yi, ganin hakan ne yasa matan suka taho da sauri wajenta suna mata magana, “ke kuwa baiwar Allah ki rufawa kanki asiri ki wuce ki bar gidan nan don ba a jayayya da malam, idan yace baza a yi abu ba ta xauna, sai dai kowa yayi hakuri, mu ma nan da kike ganinmu biyayya muke yi amma kaf cikinmu babu wacce ta isa tayi jayayya da shi” +
Murmushi Adda saratu tayi “To ai gara da ku ka ce ku, ni ai ba a cikinku nake ba, kuma ni ba yarinyarsa bace da zan ji tsoronsa ko na bi umarninsa hakkina ne naxo naga ‘yata kuma dole ya kyale ni na shiga, banda ya san akwai abinda yake boyewa menene na hana ni ganinta”
tana gama faɗa ta wuce ta kyale su a tsaye.
Saka kanta tayi tare da bude kofar ɓangaren Sa’adatu, tarar kofar dakin tayi an turo kamar bata nan, don haka tasa kafa ta tura kofar ta buɗe, a kwance ta tarar da ita cikin mawuyacin hali banda numfarfashi babu abinda take yi duk ta galabaita ta fita daga cikin hankalinta, cike da gigita ta ƙarasa wajenta tare da dago kanta tana kuka, kiran sunanta ta shiga yi amma ga mamakinta sai taga ko ɗan yatsanta baya motsawa, sai ta sarrafata sannan take sarrafuwa.
A gigice ta fara jijjiga jikinta amma sai taji shiru duk iya kiran da tayi mata bata amsa ba, ihu ta fara yi tana neman taimakon matan gidan, da sauri suka taho suna tambayarta ko lafiya cikin kuka take ce musu “Yanxu kuna ganin halin da Sa’adatu take ciki amma ku ka kyaleta a wannan yanayin, kuma naxo wajenta tsabar wulakanci mijinku yana ƙoƙarin hana ni ganinta, ashe ya san zaluntarta yake yi shi yasa xai hana naga halin da take ciki, sbd kada na tona masa asiri”
Dafa kafadarta daya daga cikin matan tayi “wlh ba laifinmu bane baiwar Allah mu ma hakuri muke yi da shi, haka tsarinsa yake duk tsananin ciwon da mutum zai yi, da halin da xaka shiga baxai bari a kai shi asibiti ba, sai dai a rika yi masa yan jike-jike, ita ma Sa’adatun tana da laifi duk abinda ya bata bata sha sai sai ta xubar shi yasa kika ganta a wannan yanayin da tana sha da tuni ta warke”
Wani kallo Adda saratu ta bi ta da shi “ya za a yi a ce mara lafiya da iya jikon magani kaɗai xai warke, ai ko ana shan jiko dole sai an kai mutum asibiti an san me yake damunsa, amma yanxu don wulakanci ya jibgeta a daki dubi yanxu ko hannunta bata motsawa bata cikin hayyacinta gaba ɗaya, kuma alamu sun nuna yunwa ta shigeta dubi hannunta a bushe ba jini, to wlh ko xai mutu yau sai na kai Sa’adatu asibiti, sai dai idan tsafi ne da shi ya karye”
Da sauri ta fita ta kira mai a dai-daita sahu, taimako ta nema daga wajen matan a kan su taimaka mata a saka Sa’adatu a dai-daita sahun, amma gaba ɗaya sai suka riƙa komawa gefe suka ki taya ta, cike da ƙarfin hali ta dube su kamar xata yi kuka sbd takaici.
“Haba bayin Allah ina neman taimako amma gaba dayanku sai dai ku bi ni da ido, babu mai taimaka min na sakata a mota, ko baku san yarinyar nan ba ai ya kamata ku tausaya mata, ballantana kuma yar uwa ce a gare ku”
A sanyaye suka dubeta “kiyi hakuri baiwar Allah, ba kin taimaka miki muka yi ba, akwai abinda muke gudu ne shi yasa indai yaji da hannunmu wajen taimakawa a kaita asibiti mu kaɗai muka san irin tashin hankalin da xamu fuskanta, dan Allah kiyi hakuri da fatan kuma baxa ki damu ba kin ji uzurinmu”
Girgiza kai tayi kawai ba tare da tace wani abu ba.
Cike da jarumta tayi kokari ta daga Sa’adatu ta ɗora ta a dai-daita suka nufi asibiti, tun a hanya Adda saratu take ta kuka tana tausayawa halin da yarta ke ciki, kai tsaye privet hospital tace ya kaita sbd idan suka je na gwamnati sai an kai ruwa rana kafin a karɓe ta.
Suna zuwa aka fara bata taimakon gaggawa, daga baya likita yaxo yayi mata bayanin cewa, tsananin yunwa ke damunta don tana da barazanar kamuwa da cutar olsar sannan kuma malaria na damunta, lissafin kudade masu yawa aka yi mata har wanda xata siya magani, ganin kudin hannunta baxai isheta bane yasa ta kira mijinta ta sanar da shi halin da ake ciki, yayi ƙoƙarin kiran innah ya sanar da ita amma ta dakatar da shi, sbd bata san kowa ya san abinda ake ciki har sai Sa’adatu ta samu kanta.
*******************
Shi kuwa malam Jibo yana fita bai xame ko ina ba sai gidan su Sa’adatu yau ko bari a kira Babanta bai yi ba da kansa ya danna kai cikin gidan, Inna Salamatu ce sunkuye tana shara, tana ganinshi ta xube a ƙasa da sauri tana yi masa sannu da xuwa.
“Malam yau ya na ganka a wannan halin ban saba ganinka a haka ba, kamar dai ba a hayyacinka kake ba, lafiya dai ko, ko yar tamu ce tayi laifi na santa da taurin kai da rashin jin magana?”
Yana huci ya fara magana “ina malam din yake wajensa naxo, shi ne yace wata mata taxo ta shigar min gida bada ixnina ba, idan shi ya turota yaxo yayi min bayani don baxan yarda da irin wannan abin ba, a rika keta min alfarma na saka doka a karya, idan kuma aurena ne da yarsa baya so sai na saketa ta cigaba da yawon iskancin tunda haka ya zaɓa”
Cikin rashin fahimtar abinda yake faɗa ta dube shi “wani abin aka yi maka ne malam ban gane abinda kake nufi ba? Mu dai daga nan babu wanda yaje gidanka da niyyar kashe maka aure, don malam baya barin kowa yaje sbd gudun fitina, sai dai kuma idan ita ta tura yan iskanta su yi maka haka, amma dai bari naje na sanar da shi halin da ake ciki, dan yayi maka bayanin yadda aka yi aka haihu a ragaya”
Da sauri ta yar da tsintsiyar da ke hannunta ta faɗa dakinsa, ganin yadda ya ganta ba nutsuwa ne yasa yayi saurin mikewa tare da tambayarta “lafiya na ganki a haka salamatu wani abin ne ya biyo ki?”
Jikinta har rawa yake sbd ita a duniya tana farin ciki taji an fadi aibun Sa’adatu ko kuma wani abin sharrin ya sameta, cikin rawar murya tace “kaxo an kunno maka wuta daga wajen Malam Jibo, waccan munafukar ta daki ta kunna maka masifa, sai kayi ƙoƙarin zuwa ka kasheta da kanka tunda xamanka take yi a gidan”
tana gama faɗa ta fita, kiran sunanta ya shiga yi a hankali ta waigo.
“Malam ɗin yana ina??”
Hanya ta nuna masa
“Kaje yana soro yana jiranka amma dai tabbas kayi kokarin yin maganin abin, ka yiwa tufkar nan hanci idan ba haka ba kuma za a bata tsakaninku da shi”
Jikinsa har rawa yake, ji yake kamar yayi fiffike yaje ya tarar da malam Jibo ko takalmi bai samu damar sakawa ba ya fita, a tsaye ya tarar da shi ya goya hannunsa a bayansa, miƙa masa hannu yayi suka gaisa sannan daga bisani ya tambaye shi abinda ke tafe da shi, bayanin xuwan Adda saratu yayi masa, da dukkan abinda ya shiga tsakanin su da ita.
Wani bakin ciki ne ya tokare wuyan baban Sa’adatu don haka ko komawa gida ya saka takalmi bai yi ba suka rankaya suka tafi gidan malam jibo don ganewa idonsa abinda ke faruwa.
Kai tsaye dakin Sa’adatu suka nufa duk a tunaninsu xasu ganta a ciki amma abin mamaki babu komai sai filin wajen, ba ƙaramin tashin hankali malam Jibo da mahaifin Sa’adatu suka shiga ba, a gigice ya fito daga dakin yana tambayar matansa ko sun ga Sa’adatu da matar da taxo.Jikinsu na tsuma suka bashi labarin tafiyarsu asibiti, nan fa hankalinsa ya tashi ya san matukar aka kai Sa’adatu asibiti xai yi wuya likitoci su bari ta dawo gidansa. Juyawa yayi ya dubi mahaifinta. +
“Kaga irin abinda matar nan tayi min ko? masifa take shirin jawo min, dama tunda na ganta na san ba alheri ne ya kawota ba, watakila ma yar yankan kai ce ba a sani ba, amma kuma tace min wai ita yar uwar mahaifiyar Sa’adatu ce wanda ni hankalina sam bai kwanta da hakan ba, shi ne dalilin ma da ya hana na bari ta ganta”
Girgiza kai baban Sa’adatu yayi tare da cewa malam Jibo ya kwatanta masa kamannin matar, yana gama faɗa masa ya dube shi.
“tabbas ba karya take yi ba kanwar mahaifiyar ta ce, don yanxun ma daga gidana ta fita, da hadin bakin mahaifiyar Sa’a aka yi komai duk wannan tsiyar ita ta kulla, ai kuwa sai ta gane kurenta sai
ta faɗa min inda ta kai min ‘yata idan bata yi wasa ba a bakin igiyar aurenta, shi yasa ai tun farko na faɗa maka na haramtawa kowa zuwa gidan nan har mahaifiyar tata amma baka ji ba ka kyaleta ta shigar maka gida, gashi nan ai ta samu damar karya maka doka, watakila ma tayi kutungwilar da auren zai lalace”
Shiru malam Jibo yayi yana naxarin maganar sa sannan ya bashi amsa “wlh xaka yi mamakin gwagwarmayar da muka yi a kan baxa ta shiga ba amma ta kafe, gudun kada a yi abin kunya ne yasa na tafi na kyaleta”
Cikin fushi baban Sa’adatu ya dube shi
“Kai da gidanka xata zo tayi maka gadara me yasa baka sheme ta ba”
Malam Jibo ne ya dafa shi “a’a dakata malam ai ba a yi haka ba, gara dai da na kyaleta din taci arzikin igiyar aurenta, yanxu abinda za a yi mu fara xuwa gidan matar ko sun dawo daga asibitin, kuma mu faɗawa mijinta irin aika-aikar da tayi mana, shikenan xai fi sauki sai ya san irin matakin da xai ɗauka a kan matarsa”
Fita suka yi gaba ɗaya suna huci, bin su matan gidan suka yi da ido don kuwa su kansu idan ya dawo sai ya sauke musu kwandon tijara, gidan Adda saratu suka nufa a kulle suka tarar da kofar gidan don haka suka xauna don jiran ganin dawowarsu.