TSANGAYAR MATI
CHAPTER 5
Inna ta d’aga hanci sama taja iska, sai kuma ta furzar ta baki tana hararar kwanukan da Nene ta aje gabanta. “Uhm ni wai da mushe kikai miyar ne Nene?” “Me kika gani Inna?” Nene ta fada tana so sa kai. “A‘a gani nayi tunda kika doso gurinnan ya cika da tsami da k’arni tamkar wacce ke aiki a kwata k0 mutuware.“ ‘Ai fa, komai na yi ban burge ba, to ai sai dai ki mutu, aikin na Mati ne, mallaka kuma tawa ce, sai shegen kinibibi da wani bakinta kamar na bakar Akuya…‘ Ta fada da gunguni “Me kike cewa ne?” “A’a cewa na yi Binta Sudan ne na balbala ajikina saboda kiji kamshin.” “Ko kuma Binta Maliya ba? To wanann dai karni yake sai a sake lale, ki kwashe kwanukan nan daga gabana, anjima zansa Mati ya karbomin Abincin daga gidan Larai.” “Uhm gaba ta kaini, dama kena tsamewa kai da kafar kazar.” Ta fada da ‘kun’kuni tana tattara kwanukan. “Bakiji ba” Inna ta fada “Inaji Inna” Ta fad’a tana gabda barin d’akin. “Idan gyaran zaki yi ki fara gyara can cikin, shi ne ko da kinsa turaren zamuji dadinsa, amman wanann in gayamiki gaskiya yau sai an turaramin dakin nan da miski zan iya zamansa. Yanzu haka sai nasha kanwa sabida kumburin ciki.” “To masharranciya.” Nene ta fadi a hankali tana barin dakin a fusace. Abule dake make a gefe tana sauraro ta kyakyace da dariya tana juyawa Nene mazaunai. Nene tayi kwafa tana gyada kai, kafin kuma ta yi dakinta tana mai sauke kaba.
Gab da Magriba Abule na tsakar gida tayi daurin kirji, da zabira a hannunta tana tsifar kai. Can daga k’ofa kuma Nene ce zaune tana gyaran Tafasa tana yi tana sakin habaici a wake.
“Munafuncin dodo dai mai shi yakan ci, yau bajumma’a ba idi ba, ba kuma kwanan mutum ba ya d’au niyyar wanka harda tazar kai na asara.” Nene ta fadi da karfi”: tana hararar Abule.”
“Oh ni Abu? Lalle idan ta karewa kare barin haushi yake ya koma tunkuyi, na ga dai abin rabo ne auran Mace da ciki. Ki gwada naki salon mana mu gani, ai wani asirin baya ci da turaren hayaki sai an had’a da yan dabaru.”
“Uban wa ke asiri da turare?” Nene ta fadi a fusace tana ture fai-fain tafasa gefe.”
“A’a ai kinji matsalarki baki cin ribar magana, yanzu mene na sakin na maguzawa a wannan hirar? Ni kinga wucewata yin abinda zai fisshe Ni. Ta fada tana mai sunkutar bokitinta ta fada Makewayi.
Nene ta ciji yatsa tana mai tura baki gaba, sai kuma idanuwanta suka sauka kan kayan da Abule ke d’orawa saman yar katangar bandakin ta langa-langa. Abin mamaki harda wani tsohon dankwalin wata atamfarta me fanteka da mati yasa mata tun a toshi. Har dai ta juya zata wuce, sai kuma dai ta sakejuyowa tana kallon katangar zuciyarta na kiyastamata abinda Abulle keyi da kaya haka. Nan fa idanuwanta suka sake sauka kan wata tsummar rigar Mati da tun yana Saurayi ta sanshi da ita. Wani makirin murmushi ta saki da ta gama hasaso abinda take zato. Ai sai tayi gun ‘yar katangar a hankali ta janye kayan bata bar
mata komai ba sai zanin da zata yanejikinta.
Da sauri tayi daki gurin Inna dake gyangyadin shaidan na gabda Magriba. Itama lnnan sai data firgita na ganin yarda Nene ta fado Mata bako gafara dai.
“Lafiya Nene kika katsemin barci haka dan rashin mutunta Uwar Miji?”
“Bari dai Inna, ai abinda na gani yau idan ban sanar miki dana cika maci Amana, na rantse miki da izifI sittin Abule cikin zani gare ta. Idan baki yarda da batunnan ba biyoni kofar Makewayin ki gani.”
Inna ta watsa mata wani kallo she’ke’ke, sai kuma ta mi’ke tana tura d’aurin kallabinta gaba “Muje na gani.” Ta fada tana yin gaba.
Abule data gama jika-jikan tamike zata mai da zannuwanta ta d’aure yanda ta saba, ai sai ta tarar babu, ta dauka ko baya suka fada dan haka ta fice a sadade tana Addu’ar Allah ya kau da idon Nene harta kwashe. Sai dai fa turus! Tayi ganin Inna da Nene tsaye ana sakar mata dariyar Mugunta. Jiki na tsuma ta sunkuyar da kanta ‘kasa.
“Shegiya guntuwa me bakin hali, abinda ban zata gare ba sai gashi ya tabbata gunki. Uwar wa ta koyamiki wannan kinibibin k0 dan ganin yar uwarki nada cikin? Inna ta fadi tana mai kai mata rankwashi a jikakken kanta.
“A’a Inna lafiya kike bugarmin Abule” Mati ya fada da shigowarsa kenan.
“Zaka rama mata ne? Sha-sha-sha kawai, Matarka na cikin Zani dan sakarci ka kasa ganewa.
Ya kwalalo ido yana dubanta, sai kuma ya hau sosa kai yana nokewa. “A’a Inna ya za,ai na sani, abinda rabon da ayi abu tun watan shekaran jiya.
Ai sai Inna ta hau tafa hannu da Sallallami.
“Haka Auren ya mayarmin kai Mati sai abinda Mace take so?Menene amfanin auren idan ba zaka taki mace tamkar gona ba? Ke kuma bakar Munafuka sai kin fadimin abinda kike bawa dana da har kikejuyashi haka ko kuma ki tafi gidan Ubanki wallahi.”
Ta fada tana jawo gashin Abule. Da sauri Mati ya shiga tsakani yana fadin “Sakarta Inna.”
Da dai Abule ta fito daga hannun Inna ai sai tayi kan Nene dake ta sheka dariya a fusace tana fadin ” Bazan fita Ni kadai ba sai dake bakar mujiya muga naki cikin mana in gaske ne.” Ta kai mata wawura.
Nene ta kankame jikinta tana ture Abule, ta daga hannu zatai naushi, Abule tayi nasarar bankare hannun ta kuwa gatsa mata cizo a hammatar da dazunnan ta barbadawa hammatar toka danta rage tsami, ai kuwa bata daga bakinta gurin nan ba sai data cisge gashin hammatar Nene harjini yayi tsartuwa.
Nene ta saki ihu tana dafe hammatarta. Abule kuwa tayi wuf! Ta fisgo zanin Nene sai ga tullin tsummokara daure a ciki. Wani abin mamakin har da wani koren Gajeran Wandon
Mati daya gaje shi tun gurin kakansa wanda yasha doyin jakai da warin fitsari, da Mati ya shafe shekara yana nemansa, yau sai gashi a cikin Nene daure…
Hmmm😁😁😁😁