TSANGAYAR MATI COMPLETE

TSANGAYAR MATI 





CHAPTER 7




“Maigidan Randar Zuciyata, Idan ka fita kaje shagon Bakari Mai Ashana kace a baka Makilin da Burushi.” Mati ya washe baki yana kallon kwalelen kanta da yasha zanen shuku yana ta kamshin Karkar. 
“Wani sabon Abinci ne muka samu Amarya Timah?” Tayi far! Da ido “a’a kai dai jeka kawo za kaga abinda zan maka da shi.” “To shi kenan, bari nayi wanka sai na fita na siyomiki, kinsan tunda na sameki bana iya fita banyi wanka ba. Tayi murmushi “Yauwa kama tunamin abinda nace zan nuna maka rannan, muje Makewayin na maka kaga sai na cudamaka baya ma.” Ta fada tanajawo hannunsa Fisgewa yayi yana nuna mata waje da baki, sai kuma a hankali yace “Ki rufan asiri safiya ce fa? Kinsan su Nene sun tashi kar ya zama abinda zan kasa cin abinci yau.” “Haba Maigida Ni wallahi kanamin irin wannan sai in dinga ganinka ragon maza, ranar kwana nane fa, kuma baka shiga hakkin kowa ba dan ka shiga Makewayi dani, Matarka ce ni, bata aro ba, ko ta titi,
kuma kosu ka shiga Makewayi da su ba abinda zai dameni tunda na san aikin lada ne. Ya zare ido yana dubanta “Da gaske aikin lada ne?” “Kwarai kuwa, ai zaman Aure indai ba cuta lada gare shi.” “Au to muje, amman dan Allah sadaf-sadaf bana so Nene k0 Abule su tsinkayi motsi na. “To shi kenan muje” Ta fada tana me yin gaba. Ruwa ta tuttula daga tulu a dan kwatashin wankan na su, ta sunkuto tayi Bandakin da shi, shi kuma Mati ya hau kewaye tsakar gidan, da dai yaji kamar babu motsi ko daga dakunansu, ai sai yayi wuf! Ya fada Makewayin. 
Abule ta yi mika ba salati ba rufe baki, ta mike tana mai rike mararta sakamakon fitsarin 
da ya rike mata ita. A hankali ta fito waje, ganin ba kowa yasa ta tsugunna nan gefen kwatamin tsakar gidan ta tsiyaya abinta, ta wawwatsa ruwa bako cudawa ta mike, za ta koma daki ta jiyo kamar kacaniya a Bandaki, a zatonta Kajin makotane ke kacaniya, sanin da tayi sunsha fadawa wawakeken masansu azo ayi ta hayaniya yasa ta zari sanda da sauri tayi makewayin. 
Sai dai fa turus! Tayi tana sakin wani razanannen Ihu ganin Mati zaune a dutse daga shi sai gajeran wando, Amarya Timah kuma duke saitin hammatar Mati da wani dan karfe a hannunta tana ta kwasar gashin hammatar tana hura masa iska, shi kuma yana dariya gami da fadin “Wai, ci gaba,da dadi wallah.” A firgice Fadi ta yada dan karfen saboda yadda ihun Abule ya kidimata, Abule kuwa da kyar ta jawo sauran numfashinta tana son daidai ta kanta, sai kuma ta daga sanda ba tai wata‘ wata ba ta saukewa Fadi ita a kafadarta. 
“Sai na nakasaki bakar mujiya me salon karuwai kawai, dan Ubanki ce miki akai nan bariki ne da zaki shiga wanka da Mijina, ko kuwa ce miki akai ni din zan yarda.” 
Ta sake dagawa zata rafka mata Mati ya rike sandanjiki na bari, “Karki kuma dukanta, zan fa rama mata, ke Abule kifa futa idona da wanann jahilcin naki, baki san aikin lada bane take yi? Bana son sakarci fa.” Ai sai tayi baya tana kallon Mati sama da kasa, kafin kuma ta rangwada guda. 
“Ahl lalle Mati yanzu na san ka dauru tamau a Minjaye, yanzu saboda wannan me zubin botoramin kake cewa zaka dake ni, Ni Abu? Daka ce aikin Lada na ga dai kwanana ya shiga daga sanda aka kira assalatu.” 
“To na ji, yanzu dai wuce ki tafi haka ba zai kara faruwa ba.” 
“Bazan tafi ba, Nifa idan bajini na fidda mata ba bazan ji daidai ba.“ “Haba Abu tawa, nace kije dai, da daddare zaki ji sako.” 
Ta ballawa Fadime harara dake dafe da kafadarta, ki sake gwadamana karuwanci gidan nan ki gani, wallahi na lahira sai ya fiki jin dadi, shegiya da wani idonki kamar tsaka ta saka kwai.” 
Af! Abu mai sauki, wai kura ta zo gidan Maharbi, idan karuwancin ne ki gwada naki mana mu gani, ai wallahi babu wata me siffar Fanteka data isa ta hanani kula da Mijina. Aikin lada ne yanzu na fara, wanann sandar kuma bashi kikaci.” Fadi ta fada tana murguda baki. 
Sanin Mati ba zai barta ta sake taba Fadi ba, ya sata juya dakinta takaici fal ranta. 
Tun bayan da akayi cacar baki tsakanin Abule da Fad’ime gidan ya kara kacamewa. Tsakanin Abule da Nene sai ka rantse tun da can kansu a hade yake tsabar amincin da suka kulla na munafunci. Koda suna cikin habaice-habaicen su ne Fad’ime ta fito tsakar gidan nan zasu bige da shewa suna watsamata bakaken magana a fakaice. Ko kallon inda suke Fadime ba tayi balle su saka ran zata tankamusu. 
Ranar wata laraba wanda ya yi daidai da cikar Inna kwanaki goma sha shida a birni, Abule da Nene suna zaune a gaban dakin Abulen suna kus-kus tare da Shafa makwafciyarsu. Shafa keyi musu tallar magungunan gyara na mata kala-kala. Ta daga wani kullin gari tana fad’in. 
Kun ga wannan? Na rantse da daren farkona dajikan Lamido yana da masifar kyau. Ke wannan da kuke gani sunansa ‘Saki Matar Uba’.” 
Nene dake soshe-soshenta ta dubi Abule suka yi wata iriyar shewa gami da cafkewa. 
“lnda ranka ka sha kallo! Yo Allah na tuba idan kura na magani ta yiwa kanta mana!” Fadin Abule. “Atoh, taya ni gani! Wai Matar kwarto da tallar maganin mata.” Nene ta cafke. 
Jin haka ya sanya Shafa kallonsu a fusace kafin ta dan kalli dakin Fadime, ga dukkan alamu batasan ma me suke yiba. Ta maido dubanta gare su cike da borin kunya ta ce. 
“Oho dai, gwara ni akan ku, haka zaku karata a borori.” 
Ta hau tattara komatsanta a sadda suka yo mata ca! kowannensu da bakar maganar da yake yarfamata. A daidai nan kuma Fadi ta futo daga daki da gudu zuwa bakin makwararar tsakar gida ta hau sheka amai kamar ba gobe. Nene ta mike ido waje tana tafa hannu, yayin da Abule ta dafe kirji tana duban Fadi dake duke. “Duka-Duka yau kwana nawane da Auren ni Nene? Taya ni lissaf’ Abule. Abule ta hau kasafta yatsun hannunta, sai kuma ta zare ido waje. “Duka-duka kwana goma sha bakwai kenan, kar dai da rubabban kwai aka shigo?” “Oh ni Nene, wannan wace irin hadama ce haka, ranarfarko da rabon ciki kamar marainiyar Karya? Ke kuma makaryaciya kika cemin ba ai komai ba ranar jikin tagarsu kika kwana?” Abule ta balla mata harara, “tuna dai, ke kika cemin ranar da aka kawo ta jini take, koma dai menene ni ban yarda da wannan Salon ba, ban tabajin cikin dake bayyana kansa daidai 
da lissafln zuwan Amarya ba. Sai dai idan da shi aka shi…” Nene tayi Wuf! Ta rufemata baki jin sallama kamar ta Inna. 
“Barta ta karasa mana manyan Akuyoyi, ai na dade tsaye ina sauraronku, wanda ya gani dai shi yaji kunya wai kallon fitsarin makaho. Idan baku da kuke cikin kauye, haihuwar kauye, renon kauye, auren kauye ba, ina na taba ganin ana labewa sabuwar Amarya? Kunyi asara wallahi Nene, matsa ni na duba ‘yar mutane, shashashai masu wankin kai da ruwan daddawa, idan ma da cikin ta shigo sai me? Nace sai kaka? Irin kune a jahannamar ma can kasan wailun kuke. Sannu ‘yarnan, sannu.” 
Inna ta karashe tana mai karasawa ga Fadime wacce aman ya dan lafawa. 
Gefe guda ta ajiye akwatin kayanta, ta yaye gyalenta ta dora saman akwatin kafin ta tattare zaninta dinkin rafa siket. Ruwa ta zubo a buta gami da mikomata. 
“Tayani duba Abule, toh wallahi ba zata sabu ba bari Matin yazo, ni ban yarda wannan cikin nasa bane, ga dukkan alamu dai mutum da abinsa yazo, ai daman ni nasan za’a rina, angama yawon ta zubar an kuntso..” 
“Kika kara magana a wajennan sai na nunamaki nice nan na isa da Mijinki don kuwa yana zuwa zan sanya ya sallamaki ga tsohonki.” 
Nene tayi dif taja hannun Abule wacce ranta ke kuna suka fada daka. Shafa kuma dake gefe kunne waje, tayi sadada ta fice daga gidan. ’ 
“Mun shiga uku Abule, yanzu idan ta tabbata matarnan juna biyu gareta ya zamu yi?” Fadin Nene kenan yayinda gumi ke tsirfomata. Abule wacce ta rasa bakin magana tsabar bakin ciki da tashin hankali, sai a lokacin ta iya bude bakinta tace. “Hum, ni na rasa ma abin cewa wallahi.” 
Sallamar Mati ce a gidan ta katse su, suka yi shiru suna sauraron yanda Inna ke gayamasa rashin Iafiyar Fadime da kuma cewar Fadimen ma tunda tazo bata ga Al’adarta ba. 

Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *