TSANTSAR BUDURCI COMPLETE

 TSANTSAR BUDURCI COMPLETE

A sanyaye matashiyar budurwar ta shiga dakin cikin yanayin damuwa, kayan jikinta sunyi wuluk saboda datti duk sun tsufa, kyakykyawar ja idan kayi musu zasu iya yagewa, kafarta kamar wacce ta shekara bata ga ruwa ba, hijabin jikinta kamar ankwato shi daga bakin kura, jingi a tayi da kyauren dakin nasu wanda tuni ya jima da karyewa, cikin karyewar zuciya mahaifiyarta take tambayarta.
        " farida yanxun ma ba'a dace ba ko"
Dan jim kadan tayi sannan tace, " wallahi inna naira biyar ban samo ba, duk gidan dana shiga neman taimako sai dai suce nayi hakuri, ga dai danyar taliya guda daya da naje wucewa ta wani layi na samu ana rabawa nima na  tsaya aka bani " ta karasa maganar tana mikawa mahaifiyarta taliyar.

    " to ay shikenan, Allah ya rufa mana asiri, dama malam nake ji kar ya tashi ba abinda zaisa abakinsa, amma hakan ma mun godewa Allah, zauna inje ingani ko zan samo mana abunda zamu dafa ko da mai muci " mahaifiyar tata ta fada.

     Farida zama tayi cen kusa da mahaifin nata, wanda yake kwance kan wata yaloluwar katifa wacce bata da maraba da tabar ma duk ta sid'e, har marmashewa take, tana kade masa kudaje, cikin zuciyarta tana tausaya musu irin 'kangin rayuwar da suke ciki.
Innar farida na fita rasa inda zataje tayi, saboda duk gidajen da zata je kowanne da kudin bashinsu akanta, gidan sahura ne ya fad'o mata, kai tsaye gidan ta nufa da sallama ta shiga cikin gidan, sahura najin sallamar innar farida tayi kicin-kicin ta tsuke fuska, ciki-ciki ta amsa mata sallamar kamar wacce akayiwa dole.

       Gefe innar farida ta samu ta zauna cikin sanyi jiki tana fadin, " sahura mun wuni lafiya ya yaran "
     " lafiya, yara kuma gasu " sahura ta fada tana dauke kai gefe.
          Innar farida tace, " Dan Allah sahura dama zuwa nayi ki taimaka dan girman Allah ki bani icce dauri daya wallahi zan hado miki da wadancen kudin "

     Kallan tsaf sahura tayi mata sannan tace, " haba sadiya yanxu bakiji kunyar zuwa karbar wani iccen ba, karki manta kudin da nake binki sun doshi wata uku fa, kullin sai dai akarawa barno dawaki, gaskiya na gaji wallahi wancen kudin ma naga alamar bazasu fito ba kije na yafe miki amma nida ke ciniki ya daina shiga tsakanin mu "
       Innar farida kamar zatayi kuka ta tsugunna tana rokon sahura, " dan Allah sahura ki taimaka mun wallahi bani da inda zanje da ya wuce nan, ki taimaka sahura kamar yanda Allah ya taimake ki " innar farida ta karasa maganar tana zubda kwallah.
      Sahura bata ce uffan ba fuuuuu ta tashi taje ta dauko wa innar farida icce  kullin hamsin ta shuro mata, tana hada mata da kananan maganganu alamar gunguni.
        Godiya innar farida ta shiga jerowa kamar wacce aka bawa kyautar gida, ta dauki itacen ta wuce gida.

       Kai tsaye gida ta wuce tana shiga inda tabar farida anan ta koma ta same ta, farida na ganin mahaifiyarta ta taso ta tarbe ta, wuta ta fara korarin hura, ledodi da yayi ya tadinga hadowa harta hura ta dora tukunyar girki.
      Mahaifin farida na kwance tari ya tirnike shi, ruwa innar farida ta dauko ta tallafo kanshi tana kokarin budewa ta bashi, da kyar yayi kurba daya ya kuma kwarewa sai bayan wani lokaci sannan tarin ya sake shi, shigowa dakin farida tayi cikin hadin baki suka fara jerawa mahaifinta sannu.

          Da ido ya bisu da kallo jikinsa na rawa bakinsa na karkarwa yace,
DOWNLOAD HERE👈

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *