TSINTACCIYA CHAPTER 4 BY NIMCY LUV

TSINTACCIYA CHAPTER 4 BY NIMCY LUV

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ƙamshin haɗaɗɗan turarensa ne ya daki hancinta wanda ya sanyata saurin janye shanyayyun idanunta tare mai dasu ta rufe,

Wani irin harbawa Zuciyarta keyi tana jin wani matsananci tsoro na shigarta, gata dai male male a jikin mutum amma ta kasa wani ƙwaƙƙwarar motsi bare tayi tunanin zame jikinta.

Yana zaune saman kujera 1 seater yana sanye cikin wani tattausan wando 3gauter sai farar singlet wacce ta kama jikinsa sosai ta fito da 6pack na jikinsa idanunsa a lumshe yana sauke numfashi, yayinda gudun da zuciyarsa ya ƙaro fiye da baya,

Idanunsa dake a Lumshe ya buɗe a hankali ɗan taune bakinsa yay jin yadda take masa sukur sukur a jiki kamar wata macijiya.

Hannunsa ya miƙa ta gefen lafaffan cikinta yana jin yadda take sauke ajjiyar zuciya cup of coffee ɗin sa ya ɗauka, gently kuma yay baya tare da kwanciya a jikin kujerar.

A hankali yake spending coffee ɗin a bakinsa ya ɗauki wajan 10minute kafin ya shanye coffee ɗin domin daman ƙa’ida ne sai ya sha Wannan coffee ɗin na Subhi da cikin dare kamar wani buzu ko labarabe.

Ajjiye cup ɗin yay cikin nutsuwa kuma ya sanya tafin hannunsa duk biyun tare da zurasu ta tsakiyar hammatar ta caraf ya ɗaga ta tsaye yana yatsuna fuskarsa.

Tsaye Akeela tayi kanta a ƙasa, kunya duk ya kamata through ba taga fuskar wanda ta zauna a cinyarsa ba, amma dadɗan ƙamshin parfume ɗinsa ya sanya tasan cewa shi ɗin daban yake ko a cikin maza.

Musamman yadda taji Physique chest ɗinsa dake cike da ƙwantaccen gashi lub! lub!!..

A razane ta sauke ajjiyar zuciya tare ƙanƙame Jikinta waje guda, naman jikinta ya wani irin rawa da ɓari dalilin saukar wani masifafan ruwan sanyi da taji tun daga tsakiyar kanta har ƙasan ƙafafuwanta, da alama ma ruwan daga cikin fridge aka ɗauko shi.

Idanunta da sukai wani irin juyewa suka ja ta buɗe da niyyar ganin wanda ya zuba mata ruwan.

Amma kamar walƙiya tuni Akeem ya haura upstairs babu mai cewa Shine yay punishing ɗin ta da wannan ruwan sanyin domin babu wani sign daya bari a wajan.

Abinka da mai ciwon ciki wanda jininta yake double SS tuni jininta yay wani daskarewa, tare da tsaya mata waje guda, a hankali kuma wata ƙwaya ta tsaya a tsakiyar jijiyar ƙafarta tare da lanƙwashewa kamar laushe.

Cikin ƙaramin lokaci ƙafarta ta fara wani irin matsanancin ciwo kamar ana sanya gatari ana datsa ɓargo da ƙashin ƙafarta haka ta keji.

Tsananin azabar da yay mata yawa ne yasa ko kuka ta kasa sai wani irin fitinannan numfashi da take gumi na yanko mata.

A hankali ta sulale tare zubewa a saman carpet ɗin parlon cikin wani irin wahalallan sabon yanayi ta kwanta tare da ɗura ƙafarta a saman kujera ta shiga jujjuya kanta tana sakin wani gigitaccen kuka iya zuci mai bala’in cin rai.

Gashi babu Folic acid da paludrine a kusa da ita bare tasha ko taji sauƙin abin.

Dukkan hannunta ta sanya a ƙafarta ta riƙe gam “ɗib! ɗib!! ɗib!!” Haka jijiyoyin ƙafarta suke harbawa alamar ciwo yayi ciwo a hankali kuma ciwo ya fara yawo a jikinta daga ƙafa zuwa kwankwasonta bata samu bacci ba sai wajan kiran sallar farko na Subhi.

A hankali yake sakkowa daga strains ɗin benen part ɗinsa, yana sanye da Embrodiery Islamic jallabiya white colour, wacce ta kasance mai santsi da taushi tana da half hand daga gaban ƙirjin kuma a ɗan tsage take..

A hankali yake tafiya kamar bai so cikin nutsuwa bakinsa ke motsawa alamar tasbihi yake ga Ubangiji.

Hannunsa a goyo da bayansa yana taka ƙafafuwansa dake sanye cikin Mon mule slippers masu kyau..

A tsakiyar parlon ya tsaya idanunsa a rufe  babu jimawa Abbu ya fito daga part ɗinsa shima sanye da jallabiya milk irinta Akeem.

Babu wanda yay magana a haka suka jera zuwa masallacin dake cikin estate ɗin nasu.

Rutse idanunsa yay da tuni su uku ne suke tafiya amma waccan shigiyar Yarinyar mai siffa da aljanun ruwa taja masa a rasa mafi muni a rayuwarsa.

Bayan an idar ya zauna zaman azkar ƙarfe 6 dai-dai suka fito daga cikin masjid ɗin zuwa gida.

Kai tsaye Akeem kitchen ya nufa yana zuwa ya samu Ummi a ciki sanye da ƙaton hijab har ƙasa, kallonsa tayi tana Murmushi, a sanyaye murya can ƙasa yace.

“Sabahul khair Ummina”

Mug ɗin hannunta dake cike da coffee ta ajjiye a hankali ta ƙarasu wajansa yana ganinta ya ɗan zube a ƙasan gwiwoyinsa tare da zame wular kansa, hannunta ta ɗura a saman sumar kansa kafin tace.

”Sabahul khair Hero”

Murmushi Yay irin Murmushin nan da idan ba ita ba ko Abbu babu mai ganinsa sai Md Adnan.

Addu’a ta shiga yi masa kafin gently ya miƙe, ganin yadda take kallonsa yasa ya ɗan kwaɓe fuska yana lumshe idanunsa cikin narkakkiyar murya yace.

“Ummi”

Hannu tasa ta ja dugun hancinsa tace “Allah ya kyauta maka, ƴarka tayi taɓara kai ma kayi”

Shi dai bai ce komai ba, maimakon ya fita daga kitchen ɗin sai yay zamansa akan kujera yay hakanne kuma saboda bai son fita yaga Akeela.

Fita Ummi tayi sam bata kula da Akeela ba kai tsaye part ɗinta ta shige.

Abbu da ya tsaya da Bala driver yana bashi hqr ne ya shigo cikin parlon kai tsaye kuma idanunsa ya sauka akan Akeela wacce take baccin wahala a saman carpet..

Da sauri ya nufi inda take  yana faɗin.

“Ya Salam Babyna bacci a Parlo a ƙasan carpet why?”

Ya faɗa yana tsugunawa tare da sanya hannunsa gaba ɗaya ya ɗauke ta zuwa jikinsa, Ajjiyar zuciya ya sauke yana ƙara kallon fuskarsa wacce tai jajirr idanunta ya kumbura sosai.

Cikin tausayinta da kuma masifafan sonta dake ƙara zautar da Abbu a hankali ya manna bakinsa a saman goshinta tare da sumbatar wajan karaf a idanun Akeem taɓe baki yay da kuma sauri ya juya tare da komawa kitchen ɗin.

“Sorry nine ko, sorry Babyn Abbu muje na goyaki kiyi bacci sosai, i promise to you cewa ba zaki kuma kuka ba, I’ll be your side kinji Babyn Abbu na” ya faɗa yana ƙara shafa fuskarta tare dayin part ɗin yaransa da ita.

  http://wa.me/+2348119237616

*_wannan book ɗin na kuɗi ne biya 500 a saki a vip ko kuma 300 a nrml grp_*

Abbu na shigewa Akeem ya fito fuska kamar hadari babu walwala baki ɗaya, kai tsaye wani room ya shiga yana shiga ya kunna hasken ciki, ɗakin karatu ne yana shiga wajan kujera yaje ya zauna tare da lumshe idanunsa yana sauke numfashi.

Not too long da zamansa a buɗe ƙofar a hankali aka shigo, Amani ce ƙyakkyawar Yarinya mai fuskar Akeem.

Washe bakinta tayi da gudu ta nufi wajan Akeem tana faɗin “Hero na” ware gajiyayyun idanunsa yay tare da mai da idanunsa kan Amani kallon da yay mata yasa ta tsaya tare da juyawa da sauri ta fita tana dawowa tace “Salamu Alaika” wani fitinan Murmushi Yay mata yana jin wani sanyi a ransa yace “Wasalamu alaiki Amani Abdul-hakeem Bukar Bello” ya faɗa yana lumshe idanunsa tare da ware mata hannayensa cikin jin daɗi ta faɗa jikin Mahaifin nata tace.

“Azunnu annaka bikhair?”

Shafa bayanta yay tare da sumbatar goshinta yace.

“Lafiya lou and you”

Murmushi tayi tana sumbatar goshinsa tace “Ana bikhair”

Lumshe idanunsa yay yana ƙara rungome ta a jikins
a yana jin wani so da ƙaunar Yarinyar nasa na shiga zuciyarsa, zameta yay a jikinsa yace “sit” Zama tayi tana kallonsa sosai kamar bazai magana ba sai kuma yace “biya haddarki” a hankali tai rufe idanunta kamar yadda taga yanayi kafin ta fara karanta masa inda yay mata, tana cin karatun ne Afaf da Aleema suka shigo sanye da manyan hijabai, nan da nan walwalar fuskarsa ya ɗauke zubewa sukai bakinsu na rawa suka fara gaida shi.

Suna tsaye ko Kallon su bai ba yaci gaba dayiwa Amani karatu.

Bayan ya gama ya kallesu har zai magana sai kuma ya fasa.

Hadda suka bashi kana ya ɗura masu da karatu.

Suna cikin karatun ne Aka buɗe ƙofar Abbu ne ya shigo cikin tashin hankali ganin hakan yasa duk yaran nasa suka kallesa a kiɗime yace.

“Dr Saboda Allah ba danni ba kazo ka duba Yarinyar nan she’s in critical condition ciwonta ya tashi bana son yay worse da yawa”

Shiru Akeem yay tare da ƙara haɗe fuska ganin hakan yasa Abbu faɗin “saboda Allah, saboda matsayina na mahaifi please Abdul-hakeem Bukar Bello” Miƙewa tsaye yay ba tare da yace komai ba ganin hakan yasa Abbu yabi bayansa, Akeem kam ji yake kamar ya zunduma hannu aka yay ihu dan baƙin ciki.

A bakin ƙofar ya tsaya Murya a can ciki yace “Kaje Abbu I’ll check her” yana faɗin hakan ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga tare da rufewa girgiza kai kawai Abbu yay ya juya.

Tana kwance saman bed ɗin sai juyi take domin a yanzu bata iya tantance inda yake mata ciwo a sanadin ruwan da Akeem ya sheƙa mata..

Hannunsa ya harɗe a ƙirjinsa cike kuma da tsanarta ya ƙarasa inda take tsaye yana jin kansa na wani irine sara masa zuciyarsa na harbawa sosai.

Ganin bata hayyacinta gaba ɗaya yasa gently ya zaune a gefen gadon tare da sanya hannunsa ya wani irin fincikar ƙafarta wata razananiyyar ƙara ta saka jikinta na kyarma da sauri ta tashi zaune tana cije bakinta tare da yarfar da hannayenta Jikinta sai ɓari Yake gaba ɗaya rigar jikinta ya zame gashinta ya hargitsa sosai..

A karo na farko ya ƙara Kallonta kafin ya daka mata wata gigitacciyyar tsawa ƙarfin tsawar da kuma rashin sabon jinta ga halin ciwo da kuma matsanancin tsoron daya shigi Akeela yasa gaba ɗaya tai wani irin juyi tare da faɗawa jikinsa ta wani irin cusa fuskarta a tsakiyar ƙirjinsa jikinta duk rawa yake domin dam bata saba da kind of this abubuwan ba.

Tsaki Akeem yaja yana taune bakinsa kafin a hankali yasa hannunsa yay cilli da ita daga jikinsa, kanta ya daki frame ɗin gadon wani irin runtse idanunta tayi azaba biyu ta haɗe mata.

Bayan ya fita daga bedroom ɗin ne Akeela ta fashe da wani irin kuka, gashi ita magana sam bata tsarinta bai dame ta ba, wani irin zafi da ciwo ta keji a ranta, wanne irin mutum ta haɗu da shine? Me tayi masa da har zai dinga cin mutuncin ta har haka? She don’t even know him balle tai wani abu na rashin dai-dai amma yana nuna ko ina kula infact ma shine yaja mata wannan masifar na tashin ciwon nata.

A yanzu ba ciwon ke sanyata kuka ba, domin idan da ana sabawa da zafi da kuma raɗaɗin ciwo da yaci ace ta saba dashi, amma a kullum idan ya tashi a sabo ta kejinsa, ciwon sikila ya wuce tunanin dukkan mai tunani ko mai haihuwa ba lallai taji azabar da suke ji ba.

Kifa kanta tayi a tsakiyar cinyoyinta tana wani irin kuka mai cin zuciya.

Akeem na fita derect wani side ya shiga ashe ƙaramin clinic ne, wata injection ya haɗa guda biyu fuskar nan nashi babu walwala sam.

A haka ya gama haɗawa ya fito yana fitowa ya tsaya idanunsa akan Didi wacce ta ciko plate da farfesun naman cow head.

tsareta yay da idanu domin mamakin naman data kwasa yake amma fuskarsa sam bata bayyana yanayinsa ba, harara ta maka masa tace “to ba sai dai kaci kanka ba, ai dai lalura ce bata shige kan kuwa, jiya jiyan na dakta ya gama gayawa Bukari naci nama na ƙoshi, to wallahi nidai li’ilafi ƙurash kaci kanka nama na kurr aniya bil aniya ato”

Girgiza kai kawai yay tare da nufar part ɗin su Aleema.

“Ɗan banza fuska kamar karas in sha Allah sai Ubanka yay maka auran dole, masifa sai cin yaro take shi kenan shan lemun tsami” 

_(shan lemon tsami baya rage sha’awa sai ma amfani da yake wajan inganta Mani, more impormation kiyi attending class ɗin we are all Women wanda zan gabatar da grp na Vip ɗin Tsintacciya 500 kacal)_

Parlo ta koma lokacin Abbu ya fito cikin wata dakakkiyar shampoo dark blue anyi masa ɗinkin jamper da babbar riga.

Ya haɗu sai ƙamshi yake zubawa, Didi na ganinsa ta fashe da kuka tana faɗin.

“Sai a gaya min cewa bani na haifi Bukari na kawosa duniya ba, da za’a dinga yi min gori a gidan ɗan dana haifa”

Kallonta yay yana zama dai-dai nan Mami ta fito cikin wata milk ɗin valisco sai ƙamshi take zama Abbu yay yace “Gori kuma Didi?”

Bakin zani ta cire ta face majina tace “A’a to ba dole nace gori ba gashi nan Audil yana cemin kura bani da aiki sai cin nama, kuma dai ai naga lalura ce ko ba gaskiya ba? Babu ruwana fisabilillahi nidai na basshi da Allah bance ka faɗa masa masifar sa ta ƙare masa akai wallahi” 

Akeem a hankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga tana cure waje guda lokacin su Aleema sun gama shiryawa tuni Drive ya tafi kaisu makaranta su da Amani.

A ɗan fakaice ya kalleta dugun gashinta wanda yake zube har saman bed ɗin ya kalla taɓe baki yay aransa yana faɗin “har ƴan ƙauye sun iya ƙarin gashi mtwss”

Gently ya ƙarasa inda take zaune tana sauke ajjiyar zuciya har yanzu jikinta ɓari yake.

Baya jin zai ɓata lokacin da wajan yiwa Wannan stupid gal ɗin magana yay mata wata iriyar muguwar tsana wacce bai taɓa yiwa kuwa ba.

Yana daga tsaye ya ajjiye injection ɗin a gefensa cikin wani ɓacin rai ya sanya hannunsa tare fisgota daga kan gadon har sai da ƙashin ta yay ƙara.

Cije bakinta tayi bata son yin wani motsi saboda ciwon da jikinta yake mata, Nightgown ɗin tabi jikinta ta wani manne dukkan Jikinta ana gani ga fure fresh skin ɗinta sai glowing take.

Hannunsa ya miƙa dai-dai lokacin daya ɗauko allurar ta buɗe shanyayyun idanunsa wani irin zare ido tayi domin ba’a taɓa yi mata allura ba wata mugun jin tsoran allura take.

A sanyaye a hankali kuma ta shiga girgiza kanta har lokacin kuma bata kalli fuskarsa ba, jikinta na rawa ta ɗaga ƙafarta zata gudu da wani saurin ya sanya hannunsa ya fisgota ta zuwa jikinsa….

Idanunta tayi saurin kullewa tana jin yadda haɗaɗɗan Baccarat rouge (Maison Francis) parfume ɗin sa ya wani daki hancinta, al’amarin daya haddasa mata lumshewar idanunta, jikinta na wani irin rawa domin this is the best time a tsayin rayuwata da  wani ya riƙe ta har ya sanyata a jikinsa so close to him, abin sai ya zama wani Extraordinary to her.

Ajjiyar zuciya ta sauke a hankali ta ɗaga hannunta da suka sauka a saman ƙirjinsa tana wani motsawa saboda zafi da zugin da ƙafarta ke mata yasa sam ba zata iya jure tsaiwar ba, a hankali ta fara yin ƙasa zata zille naman jikinta na wani irin motsi gaba ɗaya jijiyoyin ƙafarta har bawa suke saboda tsananin ciwo..

A karo na biyu Akeem ya ƙara ware gajiyayyun Maraitattun idanunsa tare da sauke su akan Akeela, wani irin lumshe idanunsa yay yana taune bakinsa ji yake kamar ya shaƙe ta ya wuta dama ganinta baki ɗaya a gidan.

Buɗe idanunsa yay yana jan wani mugun tsaki shi dai Abbunsa ya gama dashi, ganin yadda take ƙoƙarin zillewa daga jikinsa ya gently ya gyara tsaiwarsa, tare da ɗaga left hand ɗinsa ya wani manna shi a saman waist ɗinta slowly kuma ya haɗa ta da lafiyayyan jikinsa a hakan yana jin yadda naman jikinta ke rawa na tsananin azaba, cikin nutsuwa kuma ya fara murza Nightgown ɗin dake jikinta da sauri ta buɗe lumshasshun idanunta for the frist time ta sauke idanunta akan kamilalliyar fuskarsa.

Wani irin ƙyakƙyawan bugawa Zuciyarta tayi, zata iya cewa bata taɓa ganin Mutum mai mugun kyau kamar Abdul-hakeem Bukar Bello ba,  ƙwayar idanunsa kaɗai zata zautar da mace dalilin daya sanya koshi karan kansa ba kowa yake kalla da idanunsa ba, fuskar nan kamar tai tsartuwar jini s
aboda wani irin fari da yake da shi, ga wani haɗaɗɗan kewayayyan ƙwantaccen sajansa wanda ya taho da sumar kansa ya ke waye fuskarsa dashi da wani gashin baki amma akwai gemu da saje mai ɗaukan hankali.

Ga bakinsa kamar na mace Ƙarami laɓɓansa masu kauri jajaye wani yirrrrr dasu very cute and softness.

Da sauri ta rufe idanunta domin ba zata iya ci gaba da kallonsa ba wani mugun tsoransa ta keji, laɓɓanta ne suka shiga rawa gaba ɗaya suka jiƙe da yawo a karo na farko ta fisgi kalmar “Uhm..dan Allah kada kayi min zan mutu uhm” ta faɗa tana runtse idanunta sosai bugun Zuciyarta na ƙaruwa.

Taɓe bakinsa yay irin ko a jikinsa ɗin nan kima mutu waye yay asara, gumi ne ya shiga tsastsafo mata a tsakiyar goshinta tsakaninta da Allah take gudun allura, jin yaci gaba da murza rigar jikinta yana son fito da ass ɗinta waje yasa ta matse jikinta domin bata taɓa ganin sabon iskanci irin haka ba sai yanzu ko hannu ba’a taɓa riƙe mata ba, da sauri ta sanya tattausan tafin hannunta wanda ya jiƙe da gumi ga wani irin ɗumi da yake da shi ta riƙe hannunsa tana girgiza masa kanta kamar wacce take shirin shiɗewa tace.

“Dan Allah banso, kaji…uhm kada ka kalli jikina”

Wani zaro idanu waje yay wato saboda jikinta take wannan abin jikinta ɗin banza yay uwar me dashi, village gal like her ma harta san wani ɓoye jiki.

Wani cije lips ɗinsa yay yana ƙara haɗata ta  da jikinsa domin bai zo nan dan kallan wani part of her body ba, banda ɗoyi Meye ma jikin yake yanzu ma sai yaje yay wanka ysin.

Wata Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya ta sauke tare da ware dukkan hannayenta ta wani zura su ta tsakanin hammatar sa ta wani irin ƙanƙamesa sosai lokacin daya caka mata allurar cike da zallar mugunta.

Cije bakinta tayi jikinta na rawa kafin ta wani fashe da maraitaccen kuka mai ratsa zuciya tare da kifa kanta a ƙirjinsa, ba taɓa sanin akwai mugunta irin haka ba, ana faɗin zafin allura bata taɓa sanin haka allura keda mafifaffan zafi ba sai yanzu, ji tayi ta ƙara jin haushinsa bata sanshi ba amma daga jiya zuwa yanzu yay mata abinda ko maƙiyinta ba lallai yay mata shi ba.

Ajjiye emtyn injection ɗin yay tare da sauke fuskarsa a tsakanin wuyanta cikin wata kasalalliyyar murya mai ratsa zuciya yace.

 _“I would rather waltz with the devil of loneliness than tango with a devil like you. I hate you.”_ ya faɗa yana wani jan numfashi tare ƙara sauke kansa a wuyanta cikin wata husky voice idanunsa na wani ruwa ruwa yace.

_“Do you know the real meaning of the world Selfish? Take a look into the mirror and you will find out. I hate you_, ke selfish ce kin kashe min ƙani ke gaki nan You still alive kina shaƙar iskar duniya, _You killed my brother_ wallahi na tsane ki bana son ko buɗe idanu na ganki _I hate you.. I hate you, I hate you! You stupid gal witch!!!_

Ya faɗa yana wani cilli da ita tare da hankaɗata baya Allah yasa da bed kusa da ita gaba ɗaya tai bed ɗin ta faɗa saman sa “Auchhhiiii!!” Ta faɗa tana tura ƙaramin bakinta gaba saboda zafin burgewar da tayi, abinda bai sani ba tunda yay mata allurar bacci yay gaba da ita, gyara kwanciya tayi wani nauyayyan bacci ya ɗauke ta.

Cike da zallar ɓacin rai yake taka ƙafafuwansa a nan Parlo ya samu Abbu da Ummi da Mami harda Didi wacce bacci ya ɗauke ta a saman carpet bakinta ɗauke da ƙashi tana tsotsa.

Kai tsaye upstairs yay yana wani irin fitinannan taku kamar wani ɗawisu,  kai tsaye bathroom yay tare da  zame jallabiyar jikinsa akan wannan Village girl ɗin yay late a wajan aiki.

Wanka yay ya fito ɗaure da towel kafin yay ɗauki handrayer ya fara gyara sumar kansa, lotion mai ƙamshi ya shafa a saman fatarsa kana ya ɗauki body spray ya fesa, nan da nan sumar kansa ta kwanta luff har wuya jan laɓɓan nan suka ƙara yin yirrrrr dasu.

Wajan closet ɗinsa ya nufa ya ɗauki Sunset Suit Nevy blue ya sanya kana ya ɗura jacket a sama kafin ya sanya white necktie.

Wani half cover shoe ya sanya black kafin ya ɗauki briefcase ɗin sa, wayoyinsa ya ɗauka ya sanya a aljihu gently ya fita daga part ɗin yana tafe yana duba Rolex ɗinsa na Companyn Patek philippe.

Lokacin daya fita bai samu kowa ba sai Didi wacce take bacci kai tsaye fita waje yay dai-dai lokacin da P.a ya shigo bai tsaya amsa gaisuwar P.a yau da kansa ya buɗe ƙofa ya shiga back seat ganin hakan yasa P.a yiwa motar key ya fita da gudu.

Kai tsaye Audi baƙo way suka nufa inda *AKEEM BETTER FARMING INSTITUTE A.B.F.I* Babban waje ne babba  babu mai iya ganin girmansa domin makaranta ce guda ta kuyar da aikin noma, da kuma taimakon mutane, kai tsaye sashin ma’aikata yay tun daga reception aka fara gyarawa ga Hero nan, ga Hero nan hannu kawai yake ɗaga masu har ya isa Elevator yana tsaye kafin ta buɗe ya shiga lift ɗin ya danna 8floor a dai-dai 8floor ɗin ta tsaya ya fito ta office ɗin Md Adnan ya fara shigewa yana wani irin runtse idanunsa sosai.

Kafin ya nufi office ɗinsa wanda aka rubuta Ceo haɗaɗɗan office ne mai kyau da tsari domin hadda ƙaramar cineme da deep frizer ga wasu a.c masu kyau.

Kujera yaja ya zauna a hankali ya buɗe System ya fara aiki.

Ya jima yana dannawa kafin ya ɗauki telephone line ya danna wasu Numbers ɗagawa akai cikin girmamawa akace.

“Mun ɗaga kira daga sashin karɓar ƙorafi Tayaya zamu iya taimakawa maka Dr Abdul-hakeem Bukar Bello Ceo? Lumshe idanunsa yay yana sauke numfashi kamar bazai magana ba sai kuma yace “Uhm Something new?” Cikin nutsuwa matar tace “Yes sir! Mun ƙara samun takardar ƙorafi daga Ƙauyen Wudil  akan matsalar ƙwace masu gona, zuwa yanzu Mutanan sun fara yi masu ta ƙarfi”

Tsayawa yay daga danna keyboard ɗin ɗin tare da sauke hannunsa a fuska yana shafa gemunsa cikin ƙasa da Murya yace.

“Uhm! Su waye ne?” “Binciken da mukai ya tabbatar da cewa wasu Manyan shugabannin ƙasa ne suke sun yin kwacan Wannan gonakin domin su kafa wani company kuma an tabbatar da cewa Wannan company na magani za suyi kuma irin haramtattun Drugs ɗin nan masu kashe mutane, suna son yi a Wudil saboda ruwan dake wajan zai hana aji wari da kuma shaƙar hayaƙin maganin”

Miƙewa yay tsaye ba tare da yace komai ba ya kashe wayar baki ɗaya.

Daga 8floor ya sakko zuwa reception a nan ya samu p.a fita yay daga cikin sashin gaba ɗaya ya nufi ɓangaren koyar da ilimin noman.

Tafiya yay mai ɗan nisa kafin yazo ƙarshen wajan wani ƙaton fili ne a ƙalla za’a iya gida sama da ashirin ga wasu ƙanan kurayen ganye sun fara fitowa alamar shukar ta fara huda.

ga yara a wajan da manya hadda ƴan primary school, cikin nutsuwa ya zare takalman ƙafarsa tare da naɗe hannun rigarsa cikin gonar ya shiga tare da ɗaukan Adda ya fara yanke ciyawar da tai tsayi ganin hakan yasa gaba ɗaya yaran suka fara yin aikin da yake.

  *_littafi na paid book ne, 500 for vip 300 for nrml grp idan zaki siya dan ki fitar na yafe😂🤷🏾‍♀️_*

Http://wa.me/+2348119237616

A can gida kuwa Didi ce ta fito daga cikin gidan zuwan compound da sauri Bala driver ya ƙarasu tana ganinsa tace “Bala maza buɗe min mota” buɗe bayan motar yayta shiga kafin ya tayar da motar gatekeeper ya buɗe masu da sauri suka fita suna fita motar Abbu na shigowa.

A hankali Driven sa yay parking ajjiye jaridar daily trust ɗin hannunsa yay ya fito yana gyara zaman babbar rigarsa kai tsaye cikin babban parlo ya shiga da sauri Amani dake zaune ta riga da wando tana shan chocolate da ice cream ta miƙe tana faɗin “Oyoyo Grandfa”

Ɗaukan ta yay yana faɗin “eyee matar mai kama da Hero” Murmushi tai masa kafin yace “how was your school?” Tana sauka jikinsa tace “Allahamdulillah Grandfa” ganin babu kowa a Parlo ya san kuma su Aleema basu dawo ba kai tsaye ya nufi part ɗin yaran nasa yana sakin wani irin Murmushi domin ya azabtu da rashin ganin Akeela sosai.

Didi na cikin motar Bala driver yace “Hajiya Didi ina zan kaiki?” Kyaɓe fuska tayi tace “ofishin hisba” jinjina kai yay babu
jimawa suka ƙarasa da sauri har tana ƙoƙarin faɗuwa ta shiga ciki tana shiga wajan mutane uku suka miƙe da sauri tace “A’a yaya..nace yaya haka kamar dai ana yaƙi bana son gantali babu ruwana wajan ogan ku nazo” ɗaya daga cikin su yace “Hajiya gani” wani kallo tai masa tace “Malam ogan ku nace yaya zakai min tsaye kamar sandar rake” wani ne yace “shine ogan” haɓa ta riƙe tace “Muhammadur Rasulullah S.a.w a’a babu ruwana akace hisbar malamai ne anya Wannan ya iya fataha ma, Tuf astagafirullah ai karatu kuma dai azuci yake Malam ƙara na kawo” Kallonta yay sosai kafin yace “ok Hajiya tame” fashewa tayi da kuka tace “Ubangiji dai ya haɗani da gantalallan jika abin yay masa yawa ga sata ga maita”

Cikin nutsuwa Abbu ya tura ƙofar ɗakin tun daga door way ya fara jiyo sautin shassheƙar kukan ta, da sauri ya rufe ƙofar tare da shiga ciki.

Tana zaune tayi wanka sanye take da Black Silk short robe sai wata Halter top data ɗura a sama, ta rufke gashin kan nan nata da ribbon ya sauka har baya sai ƙamshi take, wani irin harbawa zuciyar Abbu tayi kamar wanda ake ja da mayan ƙarfe haka ya nufi inda take ba tare da zato ba Akeela ta jita akan….

Me Abbu yake nufi ne😂😂 na kusa gama free pages tabbas daɗi na neman yi maku yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *