TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 14 KARSHE BY AUFANA
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_+
*******Haka sukacigaba da kula daita da abunda ke cikinta doctur Aysha ma tana kokari sosai wajen duba abundake cikinta akai akai saboda sanin lafiyarsa,,,….
Zaune take agefen gadonta tanashan iska, daure take da towel kasancewar fitowarta kenan daga wanka, dan k’aramin towel ne ahanunta tana tsattsafe jikinta, ji take towel din ya’isheta dikya dameta donhaka ta saukesa k’asanta kawai tarufe k’aton cikinta tabar bobbs dinta a fili tana shan iska saboda suma yanzu sunk’ara cika suna damunta,, so take tad’aga tad’akko man shafawa amma kuma ganda takeji,,,….
Kwanciyarta tai tanashan iska saiga MUJAHID yashigo, ganinta a kwance saiyai dariya tareda k’arasowa kusa daita yazauna yana mata murmushi sannan yace “my only na yadai kodai jikin ne” murmushi tai sannan tace “a,a lafiya na kalau wanka nai shine kuma nakejin kiwar tashi nad’akko mai nashafa” dariya yai sannan yatashi yadakko mata man yana fadin “kai my only ai nafada maki idan bakyajin k’arfi kifada mana baganiba sainazo namaki abunda kike bukata idan kuma bana nan ai su Nasmat suna nan, kinfasan banason kina wahalar man da baby na ko” hararansa tai sannan tace “au watoma nice ke wahalardashi bashine ke wahalardani ba ko” dariya yai sannan yace “Allah yahuci zuciyar Princess Allah yajima da ranki bahaka nake nufiba kema nasan ai kina kokari sosai” sai itama tai murmushi sannan takarbi man tafara shafawa,,,,….
Shima tayata yai yana fadin “only ona kinga yanda bobbs dinnan nawa keta k’ara cika suna batsewa kuwa” murmushi tai sannan tace “eh nagani” saiya kashemata ido d’aya yace “kamar kodayaushe karnai missing nasu” dariya tai tareda rufe fuskanta da tafukan hannayenta tana fadin “kai habiby bakada dama wallahi to yanzu dai ai dole kabarwa baby ko” hararanta yai sosai sannan yace “naki din naki wayon ai nima baby ne, kai my only nafaga halamar idan kika haihu watsi zakiyi dani saboda gashi yanzu tinkan ki haihu kinfara wani gujeman to kisani bazamike gun jaddati jego ba anan zakiyi jegon ehi”,,,,……
Zaro daran daran idanuwanta tai tafirfito dasu waje saiyace “Eh ba’inda zakije anan zakiyi jegon” shagwabe fuska tai kamar zatai kuka tace “please habiby kada kahanani tafiya jego dan Allah” sake hararanta yai yace “bafa inda zakije ehi jakadiya zan d’akkomaki tamata jegon anan” ai baiko k’arasaba saiga kwallah sunfara bin kuncenta tamkar anbude famfamo haka sukafara zubowa,,”….
Cikin magiya tariko hannayensa tace “dan Allah habiby kayi hakuri kabarni naje can nai jegon dan Allah” takarasa maganar cikin magiya, sumbatar hannayenta yai har zaiyi magana saisukaji karar waya donhaka suka duba saisukaga wayar MUFIDA ce, duba kan screen din wayar tai saitaga my Lil Sis M danhaka tad’aga tareda karawa a kunne, magana sukai takusan 30mnts shidai MUJAHID kallonta kawai yake yanda take magana cikin faraa da dariya dakuma girma irinna yaya da kanwarta, saida tagama sannan tahuramasa iska a fuskarsa saiya rufe idanuwansa sannan yabude, cikin murmushi tace “kak’uraman idanuwa kamar yau kafara ganina” murmushi yai sannan yace “ai kullum sabuwa fuskarki ke dawoman koda yaushe idan nakalleta tamkar yau nafara ganinta sainaji banason d’auke idanuwana daga kallonta” murmushi tai sannan tabashi hot kiss a lips tace “to banda kai habiby da abunka ai da kai da kaya dik mallakar wuyane, da fuskana da gangar jikina da ni kaina aidik mallakinkace shiyasa nafison kasamcewa a gida saboda a koda yaushe nakasance atare da kai kaita kallona kaita kallona har karka gaji” dariya yai sannan yarungumeta ya sumbaceta a goshi yace ‘ana hubbiki ya habibty” tai murmushi itama tace “ana hubbika ya habiby” kasancewar yanzu MUFIDA fa anfara koyon larabci hhhh Lol,,,….
STORY CONTINUES BELOW
Can tadago tacemasa “munira ce takirani wai jibi zasuwuce madina angama gyaran gidan sarki inda zasu zauna maaruf yasamu lecturing a school dinsu Nasmat” murmushi yai sannan yace “Eh dama inataso mafadamaki ai tin last week ne suka bashi offer to shine sai sarki yace dayaita wahalan zirga zirga yana yawon hanya baya madina baya BAGDAAZ bara yasaka agyaramasu gidansa dakecan saisu zauna anan kinga yafi sauki ai yanzu mudasu saidai idan munje Umrah ko munkaimasu ziyara” MUFIDA tai dariya tace “lallaikam yanzu zasu mana nisa” sai yace “Rayyan ma yakirani yafad’aman yakammala aikin gidansa na habuja karshen month dinnan zasu tare” cikin dariya tace “a,a kai masha Allah, ubangiji yasanya alkhairi gaskiya kafada masa dole yamana walima” MUJAHID yai dariya yace “gaskiya kam yakamata saidai fa kinsan yanzu bashida kudi bikinnan dikya talautashi” MUFIDA tai dariya tace “kai bawani Rayyan mai kudinefa Allah”,,,….
Haka sukacigaba da shan firarsu har izuwa wani lokaci sannan suka ta tashi yatayata tashirya suka fito atare,,”….
****** *****
Yau kimanin wata biyu kenan da bikin su Rayyan, maaruf da munira sunkoma madina Rayyan da Amira suma suntare agidansu na habuja yanzukam rayuwar aure kawai suka saka agaba,,,….
Wata ranar Monday ce MUFIDA ta tashi batajin dad’in jikinta amma ganin abun bawani mai yawa bane yasa batadamuba tasha magani tacigaba da harkan gabanta, abun kamar wasa amma sai k’ara cigaba yake maranta na ciwo gakuma bayanta shima yana ciwo sosai, tintana juriya tana hakuri abun haryafi karfinta donhaka tadauki wayarta takira MUJAHID dake office, aikuwa yanajin haka baitsayaba dasauri yad’auki excuse yadawo gida, ganin halinda take ciki yasa yai saurin kiran doctur Aysha tazo taduba, koda taduba saitace nak’uda ce amma haihuwa fa dasaura donhaka suka zauna zaman jiran haihuwa,,,….
Har dare ba haihuwa ba alamunta ganin dare yayi sosai gashi kuma doctur Aysha tanada iyali da miji yasa dole MUJAHID yamaidata gidanta amma tace ko zuwa 1am ne yaga haihuwar taiso to yakirata kawai mijinta zai kawota, daga haka yamaidata yadawo gun MUFIDA anata abu d’aya,,,….
Har washe gari amma haihuwa batazoba sai fama ake da abu d’aya, ganin dai wahalar tai yawa yasa yaje gida yafad’amasu halinda ake ciki, aikuwa yana fada jaddati tahausa da masifa tayazaibar yarinya haihuwan fari itakadai, nan cikin gaugawa akaje aka d’akko MUFIDA aka dawo daita gida, koda jaddati taduba saitace “eh nak’udace amma nak’udan tsaye ce kuma itace mafi wahala saboda sai angama nak’udan tsaye nak’uda ta haihuwa ke zowa,,,…
Haka kuwa akayi MUFIDA tawahala sosai tasha wuya, washe gari ganin abun har yanzu yaki zowa gashi sai wahala takesha donhaka sarki yace ad’auketa aje asibiti,, haka kuwa akayi saidai suma can din drip suka sakamata na tada nak’uda sannan suka kyaleta anan kan gadon haihuwa,,,”….
Dikda drip dinda suka sakamata baisa haihuwar tazoba saima wata azaba wuya da wahalarda suka taso mata daita dan saboda tsabar wahala tini MUFIDA tacire tsammanin zatacigaba da rayuwa a duniya saboda tsintsar wahala, tawahala wuce tinanin mai karatu saboda tsabar wahala hartafara neman yafiyar mutane tana fadar akiramata MUJAHID tanemesa gafara akiramata hajiyar dady akiramata munira tazo, haka taketa fama da wannan bakar wahalar amma shuru kakeji b
a haihuwa ba labarin zuwanta,,,….
Saida takwashe kimanin kwana shida tana nak’uda sai anje hospital kuma adawo gida, ganin irin wahalanda takesha yasa MUJAHID yace kawai aje ai operation acire babyn wannan wahalan yayiwa MUFIDA yawa tintana nak’uda da karfinta har karfin yakare amma har yanzu haihuwa batazoba, kowa ya goyi bayan haka saboda kowa MUFIDA tabasa tausayi yana tausayamata sosai danhaka nantake akafara cike ciken file’s da signing,,….
Cikin ikon Allah har anshiga theater room daita anajiran isowar doctur kwatsam saiga haihuwa taiso batareda karfin jikintaba da ikon Allah, abun mamaki abu kamar saiga baby yafara fitowa MUFIDA na wani’irin nishi tana juya kanta saboda wahala, kanakce me saiga baby yafito aikuwa murna da farinciki baya misaltuwa agun nurse’s din, koda doctur yashigo saiya tadda MUFIDA ta haihu, har anfara shafewa babyn jiki saikuma ga dayan babyn yafara fitowa donhaka suka sake dawowa suka taimakata har dayan yafito,,,….
Saida suka shafewa baby’s din jikinsu sannan suka fito domin sanardasu MUJAHID, nurse’s din suna fitowa dasauri MUJAHID da mai martaba da maaruf sukayo kansu domin jin inda aka kwana cikin tsintsar damuwa dikkaninsu fuskokinsu ba walwala, saida suka jamasu aji sannan sukace “to dafarko dai kamun mucemaku komai kufara bamu tukuici ” cikin harshen larabci suke magana, kallon kallo MUJAHID da ma’aruf suka fara cikin rashin fahimtar abunda nurse’s din suke fada, ganin haka nurse’s din sukai dariya sannan dayar tace “to ALHMDLLH batareda anyanketa anfitarda abunda ke cikintaba Allah yasauketa lafiya tahaifi twin’s namiji da mace” ai saboda tsabar farinciki MUJAHID durk’usawa yai anan yayi ( sujudul shukhru ) wato sujadar godiya ga Allah wacca baayiwa kowa sai ubangiji sannan yamike tsaye kudindake cikin aljihunsa waenda shi kansa baisan adadinsuba kawai yacirosu yabama nurse’s din amatsayin tukuici sannan yace “zan iya shiga nagansu” sai nurse din tace “a,a kujira har afito dasu izuwa dakin hutu tukuna yanzu ana shiryasu ne” danhaka suka wuce domin sanardasu munira da jaddati,,,”…
Saida aka tsabtacesu aka sakawa yaran kaya itama suka taimakata tagyara jikinta sannan akawuce daita izuwa dakin hutu, saida suka doramata drip da jini sukamata wasu injection domin tasami karfin jiki dakuma wasu na bacci domin tahuta sosai saboda jininta yahau sosai, nantake bacci yai awon gaba daita saboda wahalarda tasha dakuma gajiya, baby’s din kuwa ana fitowa dasu akabama su MUJAHID, hmm MUJAHID ji yake kamar yamayardasu ciki dan farinciki sai baccinsu suke abunsu, saidaifa shi har yanzu hankalinsa bai kwantaba saboda baiga only dinsa ba,,….
Koda suka shiga dakinda take tini tai bacci munira na a gefenta tanamata tausa a kafafuwanta, MUJAHID na kallonta yaji wani irin tausayinta yakara shiga zuciyarsa nan yatako yazo dab daita yaduko yasumbaceta tareda shafa sumarta cikin tsintsar tausayinta da kaunarta,,,, koda tafarka kuwa d’akin acike yake da mutane munira da jakadiya jaddati dasu Nasmat da matan Abbanta tajudeen su biyu da wasu hadimai mata hudu, tana farkawa nankowa yamata sannu da tambayarta karfin jiki tace ALHMDLLH,,,….
Tana farkawa kuwa MUJAHID bako kunya yazo ya rungumeta yanamata sannu itakuwa gaba d’aya kunya tagama mamayeta gasu jaddati ga matan abbanta kowa yana gani amma shikam wallah baruwansa, haka yaita nan nan daita dakansa yabata abinci tashi sannan yazauna yanamata tausa a kafafuwanta baby’s din kuwa dikya tattara yarike abunsa yahana kowa ya daukesu saboda bai ajiyeba bare a dauka, saida jaddati tashiga rigar arzikinsa da masifa sannanfa ya’ajiye yaran takoresa yafita su munira sai dariya suke,,,”….
Saida tai 1hour da haihuwa sannan suka dubata sukaga bawata matsala donhaka suka sallameta suka koma gida, a gida ma bayan tai wanka taci abinci sake komawa bacci tai jaddati tace abarta tai baccin tahuta sosai donhaka aka kyaleta taita baccinta baby’s din kuma suna waje a hanun mutane ana ganinsu………
ai kwana biyu da biki sannan suka wuce hakama su munira ranarda su Amira suka wuce suma da maraice suka hau jirgi suka koma madina sukabar su jawahir da kewarsu,,,….
nada shekara biyu da wata bakwai Amira tasake samun wani cikin, wannan cikin kam ALHMDLLH batasha wani wahala ba kamar cikin Afza, haka suka sake haifar yayansu MUFIDA tahaifi da namiji amma saidai wannan haihuwar kam da matsala don saida akamata operation aka cire babyn, tasha wahala sosai ganin haka yasa MUJAHID yace adaure mahaifarta saboda wahalan yai yawa yana tsoro kar watarana yarasata gaba d’aya, Amira kuma tasake haifan baby boy wanda yaci sunan abban Rayyan sukamasa inkiya da Affan, dan MUFIDA kuma yaci sunan sarki Abdussamad suka masa inkiya da Anwar,,,,…..
ashigo, zaune take akan gado tai shuu sai suka karaso suka zauna, kallonsu tai tace “dan Allah MUFIDA narokeki ki yafeman abunda namaki natabbata abunda na aikata maki da dadyn MUFIDA shine yake bibiyar rayuwata, narasa komai nawa dik tarin dukiyarda na mallaka ta halak data haram dikta kare komai yakare ga mubina tamutu yayana dik sun gujeni hatta mustapha danaje gunsa guduna yai” saita kalli munira tace “munira kiyiman magana ko sanyi naji dan Allah” daga munira har MUFIDA kuka suke sosai, dakyar MUFIDA tadago takalli momy sannan tace “shikenan momy yaisa haka kidaina kuka dan Allah nayafemaki dik abunda kikaman ni dama can wallahi ban rikeki azuci ba kinemi yafiyar ubangijinki saboda shine babban wanda kikayiwa laifi saikuma dady wanda shi ba’abunda zamu iyacewa akansa saboda datin farko kunkarbi hukuncin Court dadik wannan matsalar batafaruba” hmm….!!! Momy tasauke nannauyan numfashi sannan tashare kwallanda suka zubomata tace “hakane sai a yanzu ne nake girban abunda nashuka bankarbi hukuncin Allah ba yanzu gashi yana hukuntani dakansa tinkan naje gunsa wannan kadai yaisa yazama *EZNAH* gasauran masu halayya irin tamu, mubina anyi mutuwar wulakanci” saita fashe da kuka MUFIDA da munira ma kukan suke sosai,,,,……