TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 2 BY AUFANA
Tana isa tak’ara murtuk’e fuska cikin tsintsar masifa tace “hallooo gyaizz ina buk’atar kubani aron hankulanku α nan” dasauri suka juyo suna kallonta tacigaba da tauna cwingom d’inta sannan tace “wane d’an rainin wayou ne yai parking yagaggiyar motarsa a inda nake parking motana” shuru sukai suna kallon juna hakan kuwa bak’aramin k’ara b’ata mata rai yaiya tak’ara jin haushi da takaici tasake cewa,,….+
“Waiko bakuji abunda nace bane” wanine can daga nesa yace “bawanda yai parking motarsa anan danma yau ko mota bamuzo da’ita ba watakil dai awaje ne” rantane yak’ara baci kamar tai kuka sai kawai tawuce fuuu kamar zata tashi sama,,,….
Tana fita sai yafito daga mab’oyarsa suka tafa da wanda yai maganar ashe friend d’insane cosmate d’insane sannan suka kyalkyale da dariya ashe dik plan ne suka had’amata, MUJAHID yace “tin yanzu harkinfara b’ata rai kina damuwa tin wasan batai nisaba hhh don’t worry smolle baby wasan yanzu aka fara” abokinsa yai dariya sannan yace “nidai friend inajimaku tsoron kada wannan game d’in naku yajuye yakoma love saboda irin haka tasha faruwa wallahi daga k’arshe saikaga abun yasauya” wani mugun kallo yamasa cikin b’acin rai yace,,,….
“haba Rayyan meyasa kakeman wannan muguwar fatar kai a tinaninka zan iya auren wannan yarinyar to idan ma kana tinanin haka kai gaggawar cire wannan tinanin daga zuciyarka dan ni wallahi ko soyayya bazan iyayi da itaba bare har na aureta” cikin b’acin rai yake maganar yana gama fad’ar haka yajuya cikin b’ata fuska yawuce, Rayyan kuwa dariya yai sannan yabi bayansa,,,….
Tana fita kai tsaye gunda suka saba had’uwa da k’awayenta tawuce, tinda tatinkarosu suka fahimci akwai damuwa a fuskarta tana isowa Nusy tai murmushi tabata hanu suka gaisa sannan tace “yadai feedom naga fuskarki kamar ba walwala what’s happened” glass d’in dake idanunta tacire sannan tace “nazo zanyi parking kawai sainatarar wani banza yazo yai parking a gunda nake parking d’in motana kuma inada tabbacin wannan sha sha shanne” cikin mamaki Amira tace “lallai kuwa akwai wata a k’asa kodai yana nufin yanzune yafara nasa game” Nusy tace “of course hakane yanzu yafara” wani murmushin gefen lebe tai sannan tace “ku kwantarda hankalinku ladies idan yasan wata ai bai san wataba just follow me” tasaka glass d’inta tawuce suma sukabi bayanta,,,…
Gun masu aikin restaurant d’in school d’in taje tace su’aramata wuk’a ko karamace, dafarko k’in bata sukai saboda tsoro dakuma rashin sanin mezata aikata da’ita saida tamasu barazana sannan suka bata takarb’a tana murmushin gefen lebe, bayan takarb’o tafito tacimmasu a waje,,,….
Gun motar takoma saita durk’usa ahankali sannan tacafka wuk’ar a tayar motar nantake iskan tayar yadinga fita,, tana ganin haka tai murmushi suma k’awayen nata sukai dariya, saida iskan yakusa fita gaba d’aya sannan tamik’e tsaye tamayarda glass d’inta tace “so now ladies tinda mungama aikin saimuje class ko” tajuya sukabi bayanta suna takon k’asaita mai d’aukan hankalin mai kallo,,….
Har suka shiga class tanajin zuciyarta cike famm da farinciki sai wasa take jan su Nusy suna dariya, suna zaune har lecturer d’insu yashigo sunfara d’aukan lecture sai aka aiko kiran MUFIDA, gabantane yafad’i rass kan taji wanda ya’aiko kiran nata wani lecturer d’insu ne daya manne mata shi adole santa yake itakuma sai wasashi take kamar wuk’a tana jansa kamar rak’umi da akala,,….
Wannan farinjinin nata shine yakesakata take k’ara jin girmankai saboda har PC d’in school d’in sonta yake kasancewar musulmi ne kuma Allah yajarabceshi da son mata idan yaga mace kamar yadamkota yakeji, hakama sauran lecturers da dama sun nuna suna sonta dakuma wasu students saboda MUFIDA macece mai sha’awa tanada k’irar mata sosai bayan kyanda take dashi gakuma farinjini wanda shine yakemata rumfa,,….
Wannan damarce take amfani da’ita wajen yin abunda takeso kuma taga dama acikin school d’in saboda taga tanada opportunity, saidai MUFIDA tanada kamun kai bata yarda ta sakemasu fuskaba hakan yasa wasunsu dole suke cemata aurenta sukeso suyi kad’an ne suke nunamata life kawai sukeso suyi da’ita daka fad’a mata kuwa anan take zata cimaka mutunci ta yayyagamaka rigar arziki sannan tahad’aka da PC ko hamma faruk suci ubanka kuma akoreka daga School,,,….
Ahankali tamik’e tsaye tafita cikin tsintsar b’acin rai tasha kunu ta tamke fuska, kai tsaye tashiga office d’insa tana shiga ta taddashi zaune akan kujerarsa cikin masifa tafara masa magana “haba Mr adam wannan wane irin wulak’anci ne nagayamaka kada ka k’ara kirana idan muna lecture wallahi banasan haka natsani haka karatunnan fa danshine nazo k’asar nan dan nayisane nazo School dinnan so why kake takurawa rayuwata plss and plss narok’eka ka kyaleni kafita daga harkana if not kuma wallahi yanda nasa akayiwa mr abbas kaima zansaka amaka haka” kallonta yake harta gama abunda takeyi, tana gamawa batajira komaiba tafita abunta fuu kamar zata tashi sama,,,…
Class takoma tacigaba da d’aukan lecture, yau 4pm suka tashi koda suka fito tanajin yunwa sosai danhaka suka wuce wani restaurant dake cikin School d’in domin suci abinci,,,….
Bayan sungama ci suka wuce wajen shan iska dake kusa da restaurant d’in, suna zaune sai Nusy tahango MUJAHID yanata fama da motarsa yana k’ok’arin yatadata, dasauri ta tabo MUFIDA tanunamata shi tana dariya itama dariyar ta kyalkyale da’ita har tana rik’e cikinta,,,…
Tashi sukai sukaje kusa dashi MUFIDA na kyalkyala dariya tacemasa “eyyah Allah sarki sannu mr man Nusy kozaki taimakasa da k’udi ne kokuma ki aramasa motanki yaje gida kar amasa fad’a baikoma da wuriba” itakuma Nusy tace “a,a nikam feedom miye had’in kifi da kaska kumama ni ai kinsan bancikasan bama kowa aron motana ba bankuma cika d’aukan kowa a motana ba barekuma kazamin talaka kamar wannan” tana fad’ar haka suka kyalkyale da dariya suka tafa shidai kallonsu kawai yake yana murmushi saboda yama rasa mezai cemasu,,…
Juyawa sukai suka wuce sunata dariya, suna wucewa yafiddo wayarsa yai dialing nmbr na mubashir ringing d’aya yad’aga cikin sauri tareda fad’in “Allah yak’ara maka nasara ur Highness” cikin isa da k’asaita yace “kad’akko man wata mota ka kawoman sannan kazo da mai gyaran mota a d’auki wannan ta lallace” cikin girmamawa yace “angama ur Highness”,,,….
Baifi 30mnts dayin wayarba saikuwa gashi yazo dawata dank’areriyar mota sabuwa gall yakarb’i key yashiga yabarshi atare da masu gyaran motar idan an gyara shi zaitafi da’ita,,,…
Kai tsaye gidansa yanufa yana isa yai parking yafito sannan yawuce ciki, wani dank’areren parlor ne naga yashiga ciki yakunna fitilu sannan yazauna akan kujera 2seater ya kwantarda kansa akan hanun kujerar, ransa yakejin yana masa suya yarasa wane hukunci zaiyiwa yarinyar nan saboda shifa a ganinsa batafa isheshi fad’a ba amma yaga tana k’ok’arin ta rainasa saboda haka dolene yad’auki mataki akanta dolene yamata hukuncinda ko sunansa taji saita tsorata bare kuma taga fuskarsa,,,….
Haka yaita tinanin irin hukuncinda zai mata daga k’arshe yatashi yashiga kitchen yad’akko girkinda mubashir yamasa sannan yadawo parlor yazauna,,,….
Zama yai yafara cin abincin yanaci yana tinanin MUFIDA rashin tsoro irin nata da tsiwa irin tata, mamakinta yake sosai saboda baitab’a ganin mace k’aramar yarinya mai irin shekarunta tana irin abunda takeba, yamatuk’ar mamaki rana ta farko data d’aga hanu tamaresa abunda ko amafarki baitab’a tinanin wata y’a mace zata iya masaba,,….
Shi yakasance namiji miskili sosai bamai yawan magana ba hatta k’anensa tsoronsa suke mahaifiyarsa kullum cikin yimasa fad’a take akan miskilancinsa wasu har cewa suke wai mugun raine dashi ko dariya bayayi gashi kuma baya d’aukan raini agun kowa k’anensa dasun masa laifi yake bulalesu hakan yasa suke mugun tsoronsa amma wai yau shine wannan k’aramar yarinyar takeyiwa haka kuma batareda ya hukuntataba to wai meyasa haka ne why….? yatambayi kansa,,,…
Da wannan tinanin yagama cin abincin sannan yawuce bedroom d’insa, kayansa yacire yawuce bathroom yai wanka sannan yafito yasauya kaya,,,….
A b’angarenta kuwa suna wucewa suka shiga motocinsu suka wuce izuwa gida saboda yau agajiye suke bazasu fita yawoba gakuma exam data matso saboda haka yanzu dole surage yawo sufara karatu……