TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 6 BY AUFANA
Zama tai anan bakin k’ofar tana kuka maiban tausayi tana zubda kwallah zuciyarta sai zafi take mata,,,….+
Ganin kuka bashine mafita agaretaba yasa ta tashi tacire mayafinta tarufe hancinta dashi sannan tafara kwashe kwalaben giyar tawuce toilet tazube sauran giyardake cikinsu sannan tadawo dak’in tafara tsabtaceshi sai k’ara toshe hancinta take saboda ji take kamar tai amai saboda tsananin warin giyar,,,”…..
Bayan ta tsabtace dak’in sannan tawuce d’akinta tad’akko tirarukan d’aki masu k’amshin gaske irin na mutan kebbi tadawo d’akinsa tafesheshi da tirarukan nantake dak’in yad’auki k’amshi, bayan tagama saitai tsaye tana kallonsa yana kwance tarasa yanda zatayi dashi saikawai tad’auki jakarta da phone d’inta tafita ta janyomasa k’ofa tarufe,,”….
D’akinta takoma tacire kayanta tawuce toilet tai wanka sannan tad’auro alwala tafito, bayan tafito tai sallah tasaka kayanta sannan tafito parlor, kitchen tawuce tadafa indomie da kwai sannan tafito parlor tazauna ta kunna TV tana kallon news,,,, tana zaune saigashi yafito sanye da jallabiya kallo d’aya tamasa tad’auke fuskarta, kamar mara gaskiya haka yak’araso yazauna a kujerardake kusa da wacca take zaune,,,…
Kallonta yai cikin sakin fuska yace “am MUFIDA dan Allah kiyi hak’uri akan abunda kikagani d’azu wallahi kuskure ne kuma insha Allah hakan bazata sake faruwa ba” saida tahadiye abincinda tasaka a bakinta sannan tai murmushi batareda ta kallesa ba tace “hmm ka d’auka hala yanzune nasan kana shan giya” kobata kalli fuskarsaba tasan mamaki ya bayyana a gareta, waigowa tai tana murmushi ta kallesa tace “idan ma bakasaniba to yanzu kasani nadad’e dasanin kai cikakken d’an giya ne a wannan gidan maka kakezowa tareda abokananka ku b’oye kusha abunku saboda wayonka yasa kakeyin hakan hakankuma yasaka dady da abban ammar harma da Abbu dik basusan kanashaba saini da munira kawai, hmm faruk kenan wannan duniyar taishe kowa riga da wando kuma dik wanda yagyara yasani hakama dik wanda yabata yasani” tana gama fad’ar haka ta tashi tawuce tabarsa anan yana cike da tsintar mamaki,,,…..
Kitchen tawuce takai kayan sannan tafito tawuce bedroom d’inta tarufo k’ofar da key sannan takashe fitilar d’akin ta kwanta,,,”…..
Washe gari tin 6am ta tashi tai sallah tai wanka tashirya sannan tafito, koda tafito kuwa tini su harira sungama had’a breakfast suna ganinta suka durk’usa suka kwashi gaisuwa ta amsa sannan tawuce dining domin yin break,,, tana cikin yin break saiga faruk yafito shima cikin shirin fita aikin, batareda ta kallesaba tamasa barka da safiya ya amsa cikin fara’a tareda tambayarta takwana lafiya saidai tinda ta masa barka da kwana bata sake cemasa uffan ba hakan kuma baidamesaba nan yazauna shima yafara yin break d’in,,”….
Tana gamawa tamik’e tsaye tad’auki carkey d’inta da phone nata tareda jakarta tawuce abunta,,,”….
Yaukam suna tashi daga aiki kai tsaye tayo gida saboda yau taci aiki sosai a office tagaji tana buk’atar hutu danhaka tana tashi tayo gida, tana isowa tai wanka takwanta domin tad’an hutu,, bacci b’arawo bata ankaraba ya kwasheta, can acikin bacci saitaji kamar ana murzata, dasauri ta tafarka tabud’e idanuwanta saitagansa akanta yana kissing d’inta harya rabata da rigardake jikinta,,”….
K’ok’arin hanasa tai amma saita kasa nan yacigaba da bata hot kisses masu zafin gaske tako’ina najikinta, d’agowa yai yafara shinshinar wuyanta tareda saka harshensa acikin kunnayenta yana lasa,,, zafafan kwallah ne ke zuba daga idanuwanta zuciyarta cike da k’unci da takaici a zuciyarta tana fad’in “inama ace MUJAHID ne ke morata inama ace MUJAHID danabashi dikkanin zumata saboda nasakasa acikin farinciki sannan yasan irin tsintsar k’aunarsa danai k’auna mai tsabta ba irin wacca faruk kemanba ta sha’awa” tana fad’ar haka tak’ara fashewa da kukan takaici zuciyarta namata zafi,,”….
Bata ankaraba tajisa kasanta yana lasar cinyoyinta hanunsa kuma yana shafar kan HQ d’inta cikin salon yaudara, wani irin nishi tai tareda zubda kwallah takai hanunta tarik’e hanunsa saiya kufce yacigaba da shafarsa yana kissing d’in cinyoyinta tareda shafasu da hanunsa d’aya, d’agowa yai yad’ora bakinsa kan nipples d’inta yafara tsotsa nan tai mik’a ta gantsara taredayin nishi mai sauti sosai takai hannayenta tacusasu acikin sumarsa saboda wani irin bakon al’amarinda taji ya ziyarceta,,”…..
Shigaba yai da tsotsar kan nipples d’inta cikin salonsa na yaudara itakuma sai nishi take da k’arfi da k’arfi tana k’ara gantsaromasa bobbs d’inta, hanunsa yakai yadinga matsasu da k’arfi hakan yasa tarikice kwallah sukacigaba da zubarmata saboda wani irin zafinda takeji mara misaltuwa,,”….
Yariga ya haukace ya rikice burinsa kawai yaji yashigeta bai ankaraba yana cikin shafar surarta yana tsotsar kan nipples d’inta saiyaji tazame jikinta tamirgina gefe d’aya tana kuka, matsowa yai kusa da’ita yakai hanunsa bayanta yafara mata magana cikin disasshiyar murya “haba MUFIDA dan Allah ki taimakeni kada kujeni MUFIDA wallahi zan iya mutuwa marana zafi takeman MUFIDA ki taimakeni” kwallah take zubarwa ta tashi zaune dakyar tafara masa magana “faruk kai mayaudarine faruk kai maci amanane faruk natsaneka faruk bana k’aunarka faruk na tsaneka bazan tab’a amincewa dakaiba” tana gama fad’ar haka ta tashi jiki ba kwari tashige toilet tabarsa anan kwance,,”….
Ganin batada niyar dawowa yasa yatashi jiki ba kwari yafita yawuce izuwa nasa dak’in,,,…..
Wanka tai ta tsalkake jikinta sannan tad’auro alwala tafito, bayan tafito tai sallar magrib da isha sannan saka kayanta na bacci tafita parlor, kitchen taje tadibo abinci tafito tadawo d’akinta taci bayan tagama sannan takwanta bacci,,”….
***** *****
Rayuwa tacigaba da tafiyar musu acikin wannan halin har izuwa yanzu babu wani sauyi acikin rayuwar aurensu MUFIDA dikta rame tai bak’i kamar wacca tai ciwon wata tara,,,,…..
Yau takasance Sunday weekend danhaka tashirya tafita, gidan hajiyar dady taje tawuni acan sai 4pm sannan tawuce gidansu, saidai kash koda kaje dadyn ta bayanan yayi tafiya k’asar Italy danhaka batawani jimaba 5pm takamo hanyar gida,,”….
Tin akan hanya takejin gabanta na fad’uwa kirjinta sai bugawa yake, acikin wannan yanayin harta iso gida, bayan tai parking saitafito takama hanyar shiga parlor, tana isa ciki saitaga parlon kasha kasha dikya baci ya rikice kamar bakowa acikinsa, can gefe d’aya tahango muciya da takalman harira da zanenta,, dasauri takama hanyar d’akinsu harira cikin fargaba da tsoro tana isa saita hango luba zaune tana matsanancin kuka tana ganin MUFIDA tasake fashewa da wani sabon kukan,,,….
Cikin kid’imewa MUFIDA tafara tambayarta “luba ina harira meke faruwa ne kike kuka ina harira?” kasa magana lubar tai sai kawai tarika hanun MUFIDA suka fita,,,,….
Ganin sunkama hanyar dak’in faruk yasa gaban MUFIDA tadinga fad’uwa yana dukan uku uku, suna isa MUFIDA tazaro daran daran idanuwanta ta firfito dasu waje nantake
kwallah suka zubomata, dagudu taje tasaka mayafinta tarufe mata jikinta tana zubda kwallah bakinta har rawa yake, cikin tashin hankali ta tallafo kanta tana jijjiga ta tana kiran sunanta “harira harira harira kitashi dan Allah” sadai ina yarinyar tasuma saboda azabarda tasha a hanun faruk k’afafuwanta dik jinine hanunta da fuskarta ta yanke har jini yafito kamar wacca akasaka wuk’a aka yanketa alamar tai k’ok’arin kwatar kanta ta k’arfi yamata,,”….
Tasowa tai tayo kan faruk wanda yake zaune akasa cikin maye sai waige waige yake ga kwalbar giya a gefensa jikinsa bako kaya dagashi sai d’an kamfai jikinsa dikya baci da jini, kyawawan marika ta sauke masa har biyu tafashe da kuka tana fad’in “ka cuceni faruk ka cuci rayuwar wannan yarinyar kuma wallahi sai Allah yafitarmata da hak’k’inta k’arshenka bazai tab’a yin kyau ba wallahi faruk na tsaneka na tsani dik mai hali irin naka kuma Allah wadan da masu halayya irin taka” cikin maye yakai hanunsa ya rikata taisaurin kaucewa saiyafad’i k’asa,,,….
Cikin maye yake fad’ar “wallaiii…Niiii…Banni bannee….Allah banni….Bannee……” wani marin tasake watsa masa sannan ta tofa masa yawu a fuska tareda fad’in “Allah wadaranka” tashi tai tafita tad’akko wayarta tai dialing number na dadyn ta……………Ringin d’aya a na biyu yad’aga saboda dady ko acikin meeting yake indai MUFIDA takirasa saiya nemi excuse yad’aga idan suka gama sannan yadawo,, yana d’agawa cikin kuka take fad’amasa abunda faruk ya aikata, tsintsar mamaki ne ya bayyana a fuskar dady sannan yacemata “ok baby yanzu nadawo ina gida jirani ganin zuwa” tace toh sannan takashe wayar,,”….+
Wardrobe d’inta tabud’e tad’akko zani takoma tarufewa harirar jiki ta zauna nan akasa ta tallafota tad’ora kan cinyarta tana kukan takaici da bak’in ciki,,….
Suna acikin wannan yanayi saiga dady da momy da mubina sun iso da gudu taje tarungume dady tana kuka nan yafara rarrashinta sannan suka k’arasa acikin dak’in, momy ce taisa da mubina tana bud’e jikin harira tai saurin juya fuskarta tareda fad’in “subhanallah” dady kuwa gaba d’aya hankalinsa yatashi saboda tinda yake baitab’a sanin faruk yana shan giya ba hadda zina sai yau, k’arasawa yai gunsa ya tallafosa cikin tsintsar b’acin rai yawanka masa mari sannan yajefasa kan gado yad’auki phone d’insa yakira abban ammar yashaidamasa abunda ke faruwa,,,”….
Cikin k’ank’ane lokaci abban ammar da momyn faruk suka isa, abban ammar na isowa yaje yadamk’o faruk yadinga dukansa yana kuka yana fad’in “ka cuci rayuwarka faruk ka cuci rayuwar wannan yarinyar faruk nai danasanin haihuwarka faruk Allah wadaran da masu hali irin naka” haka yaita fad’a yana dukansa dakyar dady yakwacesa yafita dashi yasaka mota sannan yacewa su momy a d’auki yarinyar awuce hospital da’ita,,,….
Daga MUFIDA har momyn faruk da luba dik kuka suke nan mubina da MUFIDA da luba suka d’auki harira suka fita da’ita suka sakata acikin mota momy da MUFIDA da mubina suka shiga mubina taja motar itakuma momyn faruk da luba da abban ammar suka shiga d’ayar,,,”…..
Kai tsaye FMC hospital suka nufa suna isa kuwa cikin gaggawa aka karb’i yarinyar akashiga da’ita wani dak’in, saida likitoci suka duddubata sannan suka fito suka fad’awa abban ammar yanzu zasushiga dak’in theater da’ita saboda yajijjimata ciwo sosai sai anmata operation an gyara wurin nan abban ammar yace bakomai sukaje office yasaka hanu wato ( signing ) sannan yafito,,,,….
9pm dot akashiga da harira operation lokacin kuma dik dady ya’iso, har izuwa yanzu MUFIDA bata daina kukaba saboda ji take kamar k’anwarta munira ko mubina ce faruk yayiwa wannan cin amanar, saida aka fito da harira sannan su dady suka koma gida akabar luba da baba mai tuwa y’ar aikin hajiyarsu dady da MUFIDA saboda itakam tace bazata iya tafiyaba harsaitaga harira tasami sauk’i,,,”…..
Dik yanda su baba mai tuwo sukaso MUFIDA ta tafi gida ta kwana k’in tafiya tai dataji ma sundameta da tafi saitamasu fad’a tana fad’in “ni da ku dika d’aya ne banason kuna nuna bambamci a tsakaninmu ai mai kud’i da talaka dik Allah ne yayimu sannan Allah yace ba wanda yafi wani acikinmu sai wanda yafi tsorona saboda haka banason kuna nuna bambamci a tsakaninmu ku d’auki harira tamkar mubina ko munira aguna zan iya mata komai musamman idan kukayi duba da cin zarafinda akamata ni ma macece dole naji ba dad’i” baba tace “hakane kam bawanda yafi wani agun Allah sai wanda yafi tsoronsa Allah yakarama tsoron ubangiji” suka amsa da ameen,,,”…..
Abban ammar ne tsaye acikin parlon hajiyarsa yana magana acikin zafin nama ransa abace yace “wallahi nayi nadamar haihuwarka faruk nayi nadamar kasancewarta babban d’a na dana fara haifa ashe bansaniba kana nan kana nema ka b’ata man suna aciki gari to wallahi bara kaji kayi kad’an ba’ahaifeka bare harka girma kuma insha Allah saika girbi abunda ka shuka tinda ka b’ataman rai kaima sainaka ya baci kuma yarinyar saika aureta tinda ka lallata mata rayuwa saboda bazan iya tinkarar iyayenta da wannan maganar marar dad’i ba, kai…..!!! Faruk” yanunasa da yatsa kasancewar ya dawo hayyacinsa,,,”….
STORY CONTINUES BELOW
Ja da baya yai cikin tsoro hawaye saibin fuskarsa suke yacigaba “ka kiyayeni wallahi kuma daga yau nacireka amatsayin manager na AHMAD SHITU….N.L.T COMPANY kai nama koreka kar insake ganin kafarka acikinsa sannan rabaka aurenka da MUFIDA saboda sam baka dace dakazama mijinta ba” yana gama fad’ar haka yajuya zai tafi, dasauri yarike k’afarsa yana kuka yace “dan Allah abba kayafeni kamun rai wallahi natuba bazan sakeba daga yau” hanunsa yasaka yaturesa yafad’i yawuce abunsa,,,”….
Gun hajiya yadawo yana kuka yarike k’afafuwanta yace “dan Allah hajiya kitaimakeni wallahi na tuba” ko kallonsa hajiya bataiba ta tashi tashige bedroom d’inta Abbu dama bayanan yai tafiya BAGDAAZ gun d’an’uwansa,, haka yagaji da kukansa yatashi yafita,,,….
Dik zamanda akai a asibiti tareda MUFIDA acan take kwana wuni ne batayi saboda aiki datake zuwa hakan kuwa bak’aramin dad’i yayiwa dady ba saboda akodayaushe yana alfahari da kyawawan halayen MUFIDA musamman yanzu data sauya,, hhhh nikwa nace sab’anin da datake kyamatar talaka,,,…..
***** *****
Yau kimanin sati biyu kenan dafaruwar wannan al’amarin kuma har izuwa yanzu su dady basu yanke hukunci akan abunda faruk ya’aikata ba, tinda abun yafaru MUFIDA tadawo gida abunta,,,….
A b’angaren faruk kuwa nadama da tsinewa giya shine abun yinsa kullum kansa yai zafi komai ya jagulemasa lissafinsa ya jagule gashi abban ammar yasaukesa daga matsayinsa na manager of AHMAD SHITU….N.L.T COMPANY hakan kuwa bak’aramin k’ara dagamasa hankali yaiba dakuma k’ara sakasa acikin tashin hankali,,,”…..
Suhail ne da Nazir zaune a gefensa shikuma yana kwance akan kujera idanuwansa sunyi jajir saboda tsintsar b’acin rai, kamar zautacce kawai sukaga ya d’ago tareda fad’ar “kai ina sam giya batayiba wallahi Allah i tsinewa giya dama dik wanda yake shukata” dariya suka kyalkyale da’ita har suna rik’e ciki, saida suka tsagaita suhail yace “amma wallahi faruk kabamu kunya yanzu amatsayinka na babban yaro wanda ke ji da kansa zaka bari wannan y’ar k’aramar matsalar ta gagareka magancewa haba” Nazir kuwa cikin tsokana yakaimasa d’an duka a baya tareda fad’in “ohhh….No boss Come on be a man mana” tashi yai yashige toilet batareda yasake cemasu komaiba,,,…
Harira taji sauk’i harma ansallamota daga hospital sun dawo gida nan baba mai tuwa tace abarmata ita hanunta tacigaba da kula da’ita har ta warke gaba d’aya,,,”…
Yau takasance Sunday weekend danhaka yau MUFIDA ana gida ana hutawa, kwance akan kujera tana karanta wani hausa novel *NI DA MIJIN YAYATA* na marubutan zamani ( maryam momyn Afrah da Amina meena Abba ), musty ne yazo da gudu yana wasa da motar yara a hanunsa, yana zuwa yace “Aunt
y dady yace kizo yana parlon sa” hararansa tai yai murmushi tace “inkamun k’arya saina fasa bakinka” yace “eh na yarda” saita tashi tasaka takalmanta tawuce,,,”….
Cikin sallama taisa parlon dady dake zaune kan kujera yana duba wasu file’s ya karb’a mata sallamar momy da mubina suna gefensa, k’arasawa tai tazauna kusa da dady sannan tace “dady mustapha ne yace nazo kana nemana” d’agowa yai cikin murmushi yace “eh MUFIDA nike nemanki”,,,…..
Saida yakammala abunda yake sannan yadawo da hankalinsa izuwa garesu, wasu takardu sukaga ya d’akko masu d’an yawa yajuyo yakalli MUFIDA yai murmushi sannan yabata, cikin rashin fahimta takarb’a har zatayi magana sai yace “nasan bakusan abunda yasa nataraku ananba to yanzu zan fad’a maku” saiya juya ya kalli momy sannan yacigaba “Naraba dikkanin dukiyata gida biyu rabin na mallakawa MUFIDA ina fatar bazaku d’auki wannan abun dawata manufa b….” ai baiko k’arasaba momy ta taryeshi da fad’ar,,,,,
“Tabdijam kai kansa kasan abunda bazai tab’a yiwuwa bane kafad’a dan Allah bazan tab’a yarda da wannan shirmen banzan ba, taya zaka yanke wannan d’anyen hukuncin batareda neman shawarar kowa ba naga ai MUFIDA ba’itakadai nace ka haifa ko kana mufin kanunamana cewa kafi son ta fiye da sauran y’ay’an naka to indai hakane meyasa ka haifesu”,,,,
Murmushi yai sannan yace “hajiya fatima kenan momyn yara uwar gida sarautar mata, kekinfi kowa sanin ko waye ni matuk’ar nayanke hukunci ba wanda ya’isa yatadasa acikin gidannan, naga dukiyar nan tawace inada damar nai dik yanda naga dama da’ita sannan MUFIDA y’ata ce ina ikon yimata komai amatsayina na mahaifinta innaga dama saina mallaka mata dukiyar baki d’aya kuma ba wanda ya’isa yahana”,,,,,,
Mubina ce tamik’e tsaye tareda fashewa da matsananci kuka tafita, itadai MUFIDA kallonsu kawai take batace uffan ba,,,,”…..
Momy ma mik’ewa tai tafita tana huci, juyowa tai ta kalli dady tace “dady meyasa kai hak….” bata k’arasaba yarufe mata baki yana murmushi tareda fad’ar “shiiiitttt….!!!banason naji komai yafito daga bakinki tashi kije Allah yamaki albarka” badan taso hakan ba ta tashi tawuce,,,”….
Iya nadama faruk yayita yanzu har tausayi yake bama abban ammar saidai har yanzu baidaina fushi dashiba gashi yayi har yagaji amma abban ammar yace baza’amayarda MUFIDA ba,,”….
Yauma kamar kullum zaune take acikin parlor tana kallon tashar zeeworld suna wani series film twist of fate saiga faruk yashigo, kallo d’aya tamasa tajuya fuskarta tacigaba da kallonta, k’arasowa yai batareda yacemata komaiba yawuce parlon dady…………Cikin sallama ya’isa cikin parlon dady na zaune yana shan coffee yakarb’a masa sallama, ahankali yak’arasa ya durk’usa har k’asa yagida dady, cikin fara’a dady yakarb’a yace “a,a son kaine a gidan yau” sinne kai alamar mara gaskiya yana sosa keya baya yace “eh wallahi dady nine” dady yai murmushi saboda yasan kwanan zancen nan yazauna,,,”….+
Shuru yad’an ratsa parlon can dady yad’ago yadubesa sannan yace “son inafatar dai lafiya ko akwai abunda kake so ne…?” ya jefamasa tambayar, shafa keyarsa yai sannan yad’ago cikin yanayin kunya yafara magana “am…dady…dama…dama” saikuma yafara in ina, murmushi dady yai sannan yace “relaxes my son kwantarda hankalinka kayi magana ina sauraronka” dakyar yasamu nutsuwa sannan yafara magana “dama dady nazone nabaka hak’uri akan abunda yafaru wallahi nai nadama dady dan Allah kai hak’uri kuma kabama abban ammar da momy hak’uri sunyi fushi sosai dani yanzu haka yakoreni daga Company yace karya sake ganina acikinsa kuma yace harira zai auramun sannan yaraba aurena da MUFIDA kuma wallahi ni dady inason matata dan Allah kabashi hak’uri please;;” yai maganar cikin yanayin tausayi,,”…..
Hmmm….!!! dady yasauke nannauyan numfashi sannan yafara magana “hak’ik’a faruk ka aikata babban laifi wanda ni kaina saida rai na yab’aci sosai amma bakomai komai ya wuce kadaina kuka gobe insha Allah za’adawo maka da matarka kuma zaka koma aikinka tashi kaje” wani irin dad’i yaji ya mamayesa nan yarungume dady kamar k’aramin yaro yana fad’ar “thanks my dad i love u so so much am very proud of u my dad” yasakesa yafita yana murna dady kuwa banda dariya ba abunda yake,,”….
Da dare bayan ya kammala komai yaje yasami abban ammar da hajiyarsu da momyn su faruk yabasu hak’uri, da farko abban ammar k’in hak’uri yai saida dady yaitamasa nasihohi yana janyo masa ayoyi da hadisai akan irin tanadinda Allah yayiwa masu yafiya da gara sannan yahak’ura,,,……
Bayan yadawo yakira MUFIDA yamata nasiha sosai akan lada da falalar dake cikin ribar zaman aure dakuma biyayya ga miji sannan yabata hak’uri akan abunda yafaru yakuma nemi ta yafewa faruk sannan gobe tashirya takoma gidan mijinta, badan tasoba saidan biyayya ta amince gobe zata koma nan dady yasanya mata albarka tareda kyakkywar addu’a dakuma fatan alkhairi acikin rayuwar aurensu sannan ta tashi tawuce, tana isa d’akinsu tafad’a kan gado tafara rera kukan bak’in ciki tana fad’ar “wato dai har yanzu wannan azzalimin baifita acikin rayuwataba wallahi faruk banasonka na tsaneka meyasa kaketa dawowa acikin rayuwata kai ya Allah kai gaggawar raba wannan auren kashiga tsakananina da wannan mugu azzalimin macuci kuma mayaudari” haka taita sambatu tana kuka mai taintsar ban tausayi mai raunana zuciyar wanda yajisa,,,…..
Zaune take acikin parlor bayan tagama kuka idanuwanta dik sun sauya launi izuwa ja, mubina ce tashigo tana ganin MUFIDA zaune tana kallon saitazo tad’auki remote tacanja Chanel d’inda MUFIDA ke kalla sannan tazauna kan kujera tad’ora kafa d’aya kan d’aya tai tamkar batasan da mutum zaune acikin parlon ba, cikin mamaki MUFIDA ta kalleta sannan tace “ke meyasa zaki sauya man Chanel d’inda nake kalla ko bakiga kallo nakeyiba” wani watsassten kallo tabi MUFIDA dashi tana taunar cwingom batareda tasake kallon inda takeba tabata amsa “bana buk’atar kallon wannan chanel d’in wannan nake buk’atar kalla”,,,…..
Tasowa MUFIDA tai daga gunda take zaune dama yau dik jin rayuwarta take ba dad’i b’acin rai takeji bare kuma yanzu antabota dama masifar tasaukane saboda wani dalili a baya yanzukuma dole tad’an dawo tinda antabota,,”….
Gunta tazo tai tsaye tace “bani remote d’in kona sauya maki kamanni wallahi yanzinnan” itama mik’ewa tai tsaye tarik’e kugu sannan tace “bazan badaba saboda ubana ya siya idan har kinason kema ki kalla kokiyi iko akai to kije naki uban dabamusan ko waye ba tsohon najadu kije yasiyamak…” bata k’arasaba MUFIDA tawanketa da kyakkawan mari sannan tanunata da ysata cikin tsintsar b’acin rai tace “idan kinacin k’asa ki kiyayi ta shuru saboda rijiya ba wurin wasan makaho bace karki sake kice zaki zagarman uba idan ke bakisan darajarsa ba toni nasani kuma remote dakike fad’ar ubanki yasiya naga nima ubanane kuma narigaki zama a parlon nan saboda haka dole kibarni nakalli tasharda nakeso”,,,….
STORY CONTINUES BELOW
Wata iriyar dariya mubina ta kyalkyale da’ita saida ta tsagaita sannan tasha kunu takalleta tace “hmm to idanma bakisaniba yanzu kisani dady bashine ubanki ba mundade da zuwa gana kuma mun gano gwandama tin wuri kije zuwa neman tsohon najadunki mai siyarda goro da sigari a bakin titi” saita sake kyalkyalewa da wata dariyar mugunta sannan tacigaba “kuma wallahi dik wani abu dakikasan dady yabaki kiyi gaggawar mayardashi saboda babu hak’k’inki aciki mtssssss……..!!!! *TSINTACCIYAR MAGE* kaw……” bata k’arasaba taji ansauke mata wasu kyawawan marika har biyu,,,”….
Ita MUFIDA gabad’aya ta dazkare a nan tsaye banda kwallah babu abunda take zubarwa, atare suka juya domin ganin wanda yai marin, dady suka gani a tsaye fuskarsa babu alamun fara’a yasha kunu tamkar baitab’a dariya ba, damk’o mubina yai yafara dukanta cikin tsintsar b’acin rai da bak’in ciki kankace me bakinta haryafashe yana zubda jini, kuka take tana ihun neman d’auki,,,”….
Momy ce t
afito cikin tsintsar b’acin rai takwace mubina daga hanun dady sannan tafaramasa magana cikin b’acin rai “wato akan wannan *TSINTACCIYAR MAGE* ne zaka dakarman ‘ya to wallahi bara kaji ban daukaba kuma bazan amince da hakanba idan har kai bakasonsu toni ina son abune ko kaso afada ko karkaso dik sai anfada ko a gabanka kokuma a bayanka komai daren dad’ewa kuwa” tajuyo tawatsawa MUFIDA datai tsaye tana kuka harara sannan taja hanun mubina sukai ciki,, dagudu tawuce izuwa d’akinsu tana matsanancin kuka dady kuwa gaba d’aya yarikice brain d’insa tai zafi sosai yarasa ya zaiyi, binbayanta yai domin ya rarrasheta sannan yak’aryata abunda su momy suka fad’a sadai koda yaje tarufe dak’in da key dole yajuya yawuce izuwa nasa d’akin,,”….
Daren ranar dakuma wunin safiyar data waye dik a cikin k’unci MUFIDA tayisa har izuwa yanzu cin abinci kawai ke fito da’ita taci kuka harta godewa ubangiji idanuwanta sunyi jajir kamar barkono, da dare ma da hajiya tazo zata d’auketa domin amaida gidanta saida aka saka key aka bud’e k’ofa sannan tafito, saida dady yasake mata wasu nasihohi masu ratsa zuciya dakuma gangar jiki sannan aka d’auketa suka wuce,,,”…..
Har suka isa gidan shuru shuru take batada wani kuzari saboda har izuwa yanzu takasa gasgata abunda su momy suka fad’a zuciyarta takasa gasgatawa tana kokonto amma to kodai da gaske suke ne dady da momy basune iyayentaba toma idan hakane ina ainihin iyayenta suke kuma waye su, waennan tambayoyin sune sukamata zarya acikin brain waenda kuma takasa samun amsarsu, bilkis da k’annen momyn faruk guda uku sune sukamata rakiya sai 9pm sannan suka dawo suka barota itakad’ai dan yanzu babusu harira,,,,,…..
Wanka tai sannan tai sallar isha da shaf’i da witiri sannan tai shirin kwanciya bacci, saida tarufe k’ofar da key sannan takashe fitilun dak’in ta kwanta, koda yadawo saiya tarar hartai bacci shikam yanzu yama saba sadai har yanzu zuciyarsa namasa kuna akan rashin amincewarda MUFIDA batamasa ba amatsayinsa na mijinta tak’i ta mallaka masa kanta gashi yau yazomata da shiri na musamman saboda su raya rayuwar aurensu ma’ana sushiga sahun ma’aurata amma kash yanzu ya tarar tarufe d’akin gashi key d’in d’akinta dayane kuma shine a hanunta,,,…..
Badan yasoba dole yajuya da tarkacen kayanda yazo dasu yawuce d’akinsa,,,”….
Washe gari tana farkawa daga bacci tai sallah sannan tafito tawuce kitchen, had’adden breakfast tahad’a masu naji da gani bayan takammala sannan tad’auka takai dining, d’akinta takoma tai wanka tashirya cikin doguwar rigar abaya bak’a mai ratsin ja tai rolling da veal ja sannan tasaka takalmanta suma ja da jakarta ja tafeshe jikinta da tirare sannan tad’auki phone d’inta tafita,, tana fita shikuma yana dawowa daga masallaci sanye da jallabiyya, cikin sakin fuska tamasa barka da kwana tamkar zautacce haka ya amsa mata saboda tsabar farinciki yau MUFIDA tasakarmasa fuska,,,….
Takula dahaka danhaka tasharesa tace “ga breakfast can akan dining idan katashi ci” aibatako k’arasaba yai saurin fad’ar “to to muje kawai” yanda yai maganar saida d’an murmushi ya kub’ucemata nan suka wuce dining atare, dasuka jema itace tai saving nasa sannan tasakawa kanta tazauna suka fara ci,,,….
Sunacin abincin sai satar kallonta yake itakuwa baisan wani irin bak’inciki takejin yana tasomata da takaicinsa kawai sharewa ne take domin yin biyayya, batawani ci sosaiba ta tashi tad’auki kayanta tawuce, har saida tabace masa sannan yadaina kallonta yana murmushi,,,”….
Around 6pm bayan suntashi daga aiki saita kamo hanyar gida saboda yau agajiye take sosai tana buk’atar hutu bazata iya zuwa gidan hajiya ba, tana isowa tai horn gateman yabud’e mata tashigo tai parking sannan tafito ganin motorsu suhail da nazir yasa nantake ranta yab’aci kai tsayi tawuce izuwa cikin gidan,,,….
Abunda dai take tinani shine yafaru faruk ne dasu nazir zaune acikin parlor suna kwankwadar giyarsu san ransu, wasu zafafan kwallah ne suka zubomata saita juyo tadawo tashiga motarta tasake fita,,,….
Kai tsaye gida tawuce ranta a b’ace tamkar wacca akayiwa sakon mutuwa, tana isowa gida kai tsaye tawuce d’akin dady tana isa tafadamasa har yanzu faruk baidaina halinsaba, hak’uri yabata yace tajuya takoma gashinan zuwa badan tasoba dole saboda biyayya tajuya tafita,, tana fita saida taje d’akinsu tad’akko wani abu data manta sannan tafito,,,”….
Tana kawowa dai dai k’ofar side d’in daday saiga momy zataje dak’in dady nan ta gaidata kanta k’asa batajira ta karb’a ba tawuce ranta a b’ace zuciyarta namata tafasa,, harta shiga motarta gateman yabud’e mata tafita kenan saiga momy tafito dagudu tana fad’in “habu karka bari tafita tsayardaita tsayardaita” saidai ina koda habu yaje ya tsaidata tariga tawuce, cikin tsintsar tashin hankali momy tafara kiran “security’s security’s security’s kuna inane kuzo takashe Ahj takasheshi habu kiraman security’s” habu kuwa sam baifahimci abunda momy ke nufiba danhaka yai tsaye yana tambayarta “hajiya lafiya meke faruwane” batace dashi uffan ba saitawuce cikin gida dagudu,,,….
A b’angaren MUFIDA kuwa cikin tsintsar b’acin rai ta’iso gida tana isowa tai parking tafito tawuce izuwa cikin gida,, tana shiga cikin parlon abunda taganine yasa tai mutuwar tsaye, dagudu taje ta tallafosa yana d’aukan rai ga wuk’a ancafka masa a ciki jini sai zuba yake tamkar abud’e famfo, cikin tsananin tashin hankali tafara masa magana “faruk waya aikatama wannan mummunar muguntar faruk waya kasheka” tana maganar tana k’ok’arin cire wuk’ar daga cikinsa, dakyar ta’iya cireta aikuwa sai jikinta gaba d’aya yawanke da jini nan yaja numfashi baisake ja ba rai yai halinsa,,,”….
Kuka tafashe dashi cikin tsananin tashin hankali tana bubbugasa tana fad’in “hamma karka mutu karka mutu dan Allah katashi kafad’aman wanda yamaka wannan muguntar namaka alk’awarin zan d’aukar maka fansa dan Allah hamma karka mutu” tanacikin fad’ar haka saitaji anfasa kuka a bayanta mai kukan tana fad’in “lahaula wala kuwwata shima faruk d’in takasheshi takashesa innalillahi wainna ilaihi raji’un wannan yarinya memuka maki kika sakamana da wannan *MUGUWAR SAKAYYA* bayan mun maki komai a duniya” waigowa tai saitaga police bayanta tareda momy da mubina da gateman…………..
Hmm…!!! Lallai MUFIDA kinacikin tashin hankali Allah yafitardake kawai zan iyacewa