TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 7 BY AUFANA
Tasowa tai dasauri hanunta rik’e da wuk’ar idanuwanta na zubda kwallah tayo gun momy sai suka ja da baya da sauri momy nafadin “a,a wannan yarinyar nan anya tanacikin hayyacinta kuwa security’s kukamata mana kar muma tahad’a damu takashe” itakuwa kuka take tana fad’in “momy waya lashe hamma faruk momy waya kasheshi” cikin matsanancin kuka take maganar,,,…..
Security’s hud’u suka kamata suka rik’eta momy tazo ta wanketa da kyawawan marika sunfi a kirga tana fad’in “kin cucemu MUFIDA kin yaudaremu kin rabani da mijina abun k’aunata sannan kuma kin kashe faruk wallahi bazan barkiba saina kema saina kasheki” tana maganar tana marinta kuma tana dukanta, dakyar mubina da d’aya dagacikin security’s d’in suka jata,,,…..
Tsintsar mamakine ya bayyana a fuskar MUFIDA kwallah nazubarmata cikin mamaki tace “momy kina nufin kice dady na ma yamutu” mubina ce tai magana cikin kuka tace “to wazaki tambaya bayan kece da kanki kika kasheshi sannan kuma kikazo yanzu kika kashe hamma faruk kokina nufin kice rainama hankali zakiyi bayan ankamaki dumu dumu” cikin mamaki tace “ni kuma kina nufin kice nice nakashe dady da hamma” mubina tace “kece za’ayiwa wannan tambayar ba kece zakiyi tambayar ba saboda amsar tambayar tana gunk..” batako k’arasaba sukaga MUFIDA tazube k’asa somammiya, cikin tsintsar b’acin rai momy tace “kukira I.G da D.I.G da commissioner of police kufad’amasu sannan ku tsareta anan kamin su k’araso karku yarda tad’aga izuwa konan da toilet ne itakuma gawar za’aturo a d’auketa” suka amsa da “yes ma angama” saita juya ita da mubina suka wuce,,,,…..
Acikin y’an dak’ik’u kad’an zancen yakarad’e ko’ina da ko’ina acikin k’asar kebbi tini momy tasaka aje adakko munira school adawo da’ita, dika gidajen biyu banda koke koke da tsinuwa ga MUFIDA ba abunda akeyi momyn faruk kuka momy kuka su bilkis da mubina kowa kuka yakeyi gida dikya rikice sai koke akeyi, har and’akko gawarwakin sai Abbu yace ajira har gobe dai dai y’an uwa na nesa dana kusa sun iso sannan a sallacesu akaisu makwancinsu,,,”…
Haka kuwa akayi, washe gari around 10am kowa ya’iso kusan dik rabin familyn gaba d’aya sun iso sai waenda ke nesa sosai ne kad’ai suka rage suma kuma sunakan hanya, Governor da PA d’insa I.G da D.I.G da commissioner of police da sauran shuwagabannin gomnati dik sunzo,,,….
10:30am dot aka fito da gawansu, gidan sarki akamasu sallah sannan aka kira su momy sumasu addu’a sannan awuce akaisu makwancinsu na gaskiya, koda sukazo ma komai basu iyayiba banda kuka abban ammar ne kawai ya’iya tsayawa yamasu addu’oi shima sai zubda kwallah yake, Abbu da hajiya ma sunmasu addu’oi sannan akadaukesu akawuce mak’abarta aka binnesu,,”….
Allahu akbar kullu nafsin zaa’ikatul maut dady da hamma faruk anrigamu gidan gaskiya Allah yamaku rahama ya kyautata tamu idan tazo ameen,.
A b’angaren MUFIDA kuwa tini ta farfado sai kuka take matsananci idanuwanta dik sun sauya launi sunyi zajir sun kukkumburo saboda kuka ita bama kazafinda akamata yasa take kukaba a,a mutuwar dady saboda tasan yanzu tabbas tarasa gata har abada rayuwarta saidai wani iko na ubangiji,, gidan kuwa gaba d’aya ansakamasa tsaro gaba da baya ko’ina police ne da sojoji,,,….
Bayan andawo daga mak’abarta su governor suka shigo gida sukayiwa su hajiya dasu momy ta’aziyya sannan suka wuce, suna wucewa I.G yawuce gidan faruk suka d’auki MUFIDA suka wuce da’ita izuwa station d’insu,,,….
Suna isa kuwa yasa akashigar da’ita wani d’aki inda suke magana da mai laifi kan su hukuntashi, bayan anshiga da’ita tana zaune itakad’ai saiga I.G yashigo tareda wata police mace k’atuwa, zama yai a kujerardake fuskantarta sannan yad’ago jajayen idanuwansa masu ban tsoro yakalleta fuskarsa tamke yafara mata magana “ke meyasa kika kashe mahaifinki da mijinki…? wane laifi suka maki…?” haka yajeromata tambayoyin atare,, wasu zafafan kwallah ne suka zubomata bakinta na rawa tace “Wallahi wallahi Allah banina kashesuba shin wace riba zanci idan nakashe mahaifina haba kudinga tinani mana kan kuyi magana mahaifinane fa shi kuma wanda banida kamarsa a duniy…” bata k’arasaba yadaka mata tsawa saida ta razana cikin kakkausar murya yace “ba wannan na tambayekiba kifad’aman meyasa kika kashesu waya sakaki ki aikata hakan” cikin kuka tace “nafad’a maka wallahi Allah banina kashesuba ni ko kiyashi bantab’a kashewaba bare mutum kuma ko mutum ma dady na da yayana” wani kallo yamata sannan yace “ohhkk bazaki fad’aba kenan Good A.S.P hafsat” matar dasuka shigo atare tace “yes sir” yace “kishiga da’ita kumata dik yanda yadace har saitafad’i gaskiya tai magana sannan kufito da’ita” matar tace “ok sir angama, ke tashi muje sha sha wacca batasan ciwon kantaba barin irinku acikin al’umma bala’i nema wallahi” MUFIDA tamik’e tsaye jiki ba kwari suka fita atare,,,,….
STORY CONTINUES BELOW
Sai kusan 1pm sannan munira suka iso tin a k’ofar shigowa dataga y’an zaman makoki tafashe da kuka dakyar ta’iya k’arasawa cikin gidan, tana shiga tafad’a jikin momy tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu cike da tsintsar tausayi, da akafada mata wai MUFIDA ce takashe dady da faruk k’in yadda tai tace “kai ina wallahi k’aryane wannan sharri ne wanine kawai yakeson yasaka aunty MUFIDA acikin tashin hankali bayan wanda tashiga na rasa dady amma wallahi sam Anty MUFIDA bazata tab’a iya aikata wannan laifin ba” wata muguwar harara momy tawatsa mata batareda tace mata komaiba hakan yasa dole munira takama malamin bakinta,,”….
Wani d’aki mai duhu tashiga da’ita tana ganin cikinsa tagane gunda suke horasda masu laifine nantake k’irjinta yafara bugawa da k’arfi da k’arfi, wasu mata taga sunshigo su hud’u manya masu girma sosai kuma karfafa dan idan kagansu ma zakace maza ne kuma da’alamu dikansu ba musulmi bane A.S.P ce kawai musulma acikinsu, suna shigowa tacemasu “ku tub’eta kusakamata riga yanzu” nan suka kama MUFIDA tana kallonsu suka ciremata kaya suka maidata daga ita sai brez da pant saisuka sake d’akko wata y’ar best bak’a suka sakamata girmanta iya cinya sannan suka rufemata fuskarta da wani kyalle bak’i,,,…
Bayan sun rufe fuskarta sannan suka kamata suka d’ora akan wani abu suka d’aureta sannan suka d’akko wata bulala irin wacca ake dukan doki da’ita ba ice bace ita bulala ce nan suka fara dukanta su biyu suna zabgamata ita tako’ina na jikinta musamman cikin k’afafuwanta da tafukan hannayenta, kuka take tana k’ara mai sauti saboda azabarda takeji amma haka sukacigaba da dukanta tintana ihu tana k’ara har muryanta ya disashe, saida suka gaji sannan suka kyaleta suka kwanceta suka maidata zaune, A.S.P tace dai dai fuskarta tace “kifad’amana meyasa kika kashesu? waya sakaki?” cikin shesheka tana haki tace “wallahi banina kashesuba bani bace dan Allah kudaina cutardani banmaku komaiba bani bace” wani murmushin gefen leb’e tai sannan tace “ok da’alamu har yanzu baki shirya fad’ar gaskiya ba gyaiz zaku iya cigaba da aikinku”,,,….
Wasu karafa suka d’akko masu baki biyu sukazo suka kamo hanunta suka saka yatsunta bibbiyu acik
i suka matsesu sosai, wata iriyar k’ara tai mai sautin gaske tareda fad’in “dadyyyyyyyyy……!!!” saisuka kyalkyale da dariya sannan suka koma a kafafuwanta suka sake saka yatsunta na kafa suka matsesu sosai da iya karfinsu tasakeyin wata k’arar sai kawai tasome saboda bak’ar azaba,,,”…
D’aukanta sukai suka dora kan wani table wai fad’i sosai suka watsa mata ruwa a fuska dole ta farfado numfashinta yadawo tafara tari tana numfashi sama sama, kyaleta sukai saida takusan 30mnts tahuta amma har yanzu yatsunta basu daina mata zafiba gashi sai zubda jini suke,,,”…
A.S.P ce tazo tasaka hanunta tadamko bakinta cikin mugunta tace “kin shirya fad’ar gaskiya ko har yanzu” yanzukam tariga data galabaita ko magana bazata iyaba danhaka shesheka kawai take sai matar ta tashi tsaye, matan sukazo suka danneta anan kan table d’in sannan suka rufemata fuska da wani towel k’arami sai suka d’akko ruwa cike da bucket suka fara kwararamata a fuska, juyi take tana neman d’auki amma ina haka sukacigaba da kwararamata su saida sukaga numfashinta nanema ya dauke sannan suka kyaleta tafara tari tana jan numfashi da k’arfi tana fitarda ruwanda suka shiga a hancinta da bakinta, ganin ta galabaita yasa suka barta haka amma badan sun k’are mata ponishment d’inba,,,..
Haka sukacigaba da gana mata azaba kala kala amma har yanzu tak’i tace itace takashesu yanzuma ko magana bata iyayi saboda bakinta ya kumbura sosai saboda dukanda suke mata jikinta dik tabo ne jini kam ba’amagana gashi har yanzu y’ar wannan best d’in itace ajikinta gashi tanajin sanyi saboda zazzab’inda take fama dashi gakuma yunwa da k’ishi saboda yanzu sau d’aya suke bata abinci ruwa kuma sau biyu kawai tini tafita hayyacinta dan idan kaganta sam bazakace MUFIDA bace fuskarta dikta sauya,,,”…
***** *****
Yau kimanin kwana hud’u kenan da mutuwarsu dady angama zaman makoki kowa ya watse saidai har yanzu gidan cike yake saboda bak’inda ke zowa daga nesa,,,….
Around 3pm momy tace akaita gun MUFIDA nan munira tace itama zataje saisukaje atare, suna isa aka kaisu gun MUFIDA munira tafashe da kuka saboda ganin halinda MUFIDA take ciki, dakanta tad’auki key tabud’e k’ofar dagudu tashiga ta tallafo ta tarungume tana matsanancin, MUFIDA kuwa “ruwa ruwa” kawai take fad’a ganin alamun kishi takeji saboda bakinta dikya bushe yai fari alamar dai kishi takeji, tashi munira tai taje tabud’e wani k’aramin fridge tagani tad’akko ruwa acikin gora tazo ta dagata tafara bata ruwan aikuwa zokuga yanda take karb’an ruwa tana hadiyewa kamar wacca tai shekara d’aya batasha ruwaba saboda tsabar kishinda takeji,,,”…
Batako gama shan ruwanba saiga A.S.P tashigo ta karbe ruwan ta watsar sannan takama hanun munira tafitar da’ita tarufe k’ofar, cikin masifa munira tace “wai ke matarnan anya kuwa musulma ce saboda ina kokonto akan musulincinki, wane irin rashin imanine wannan zaki kama baiwar Allah kudinga azabtar da’ita bayan kuma tafad’a maku ba’itace ta aikata wannan abunb…” bata k’arasaba momy tawanketa da mari sannan tace “amma dai wallahi munira kinji kunya dumu dumu aka kamata da wuk’a ahanu tagama kashe faruk sannan tabbas itace takashe Alhj amma dikda haka wannan bai isheki ki tsinewa wannan muguwar ba wato kenan ke bakya bak’inciki akan kashe maki mahaifi datai” d’agowa munira tai tareda fad’in “to amma momy” sai momy tai saurin dakatar da’ita dacewa “dakata munira bana buk’atar sake jin komai daga bakinki tinda ke kin nuna bakiji zafin kashe maki mahaifi dataiba” tana fad’ar haka takalli I.G tace,,,….
“I.G tinda tak’i tafad’i gaskiya kukawo d’in nasaka hanu sai shigarda case d’in court inaga acan zaifi tafad’i gaskiya cikin sauk’i” I.G yace “ok madam” sai yaje yad’akko yakawo mata tai signing sannan tace “bana buk’atar kukai file d’in gunsu hajiya harsaikungama komai lokaci kawai ake jira nafara shiga court” I.G yace “dik yanda kikeso haka za’ayi ur Excellency” suna gama maganar tajuya suka wuce munira na kallon MUFIDA badan tasoba haka suka wuce sukabarta acikin wannan halin,,,,…..
Komai ya kammala nafara shiga court lokaci kawai ake jira sadai abunda yamasu matsala shine MUFIDA batada lawyer,,,….
24/3/2019 ~ 10:00am dot akafara gudanarda wannan shari’a a babbar cotun dake cikin k’asar KEBBI State, bayan lauyoyi sun gabatar kansu sai akafara sauraron k’ara, lauyan gomnatin shine yafara tambayoyi ga MUFIDA bayan yagama sai mai shari’a yace “idan lauyan wacca ake tuhuma yana kusa yazo yafara gabatarda shaidunsa domin kare wacca yake wakilta” nan aka shaidawa mai shari’a cewar batada lauya,,,….
Bayan mai shari’a yagama y’an rube rubensa sai yad’ago yace “duba da rashin lauya da wacca ake tuhuma batada andaga wannan shari’a har izuwa 27 ga wannan watan sannan tayi gaggawar samo lauyanta domin yakareta agaban kotu kan lokacinda aka d’iba yacika sannan acigaba da tsare wacca ake tuhuma” yana gama maganar yamik’e tsaye sai kowa yamik’e tsaye yafita,, police ne sukazo suka rik’e MUFIDA zasu fita, suna fitowa waje saiga y’an jarida kowanne sai jefowa MUFIDA tambayoyi yake itakuwa banda zubda kwallah ba abunda take takasa amsa kowa daga cikinsu tambayarsa, dakyar police suka samu suka wuce da MUFIDA,,,”….
Zaune take akan kujera tana kallon TV, wayartace a hanunta tana danne danne jin an ambaci sunan MUFIDA AHMAD SHITU wacca ta kashe mahaifinta da mijinta dasauri tad’ago kanta tamayarda hankalinta kan TV d’in, MUFIDA ce dai tagani an hasko tana kuka police sun rikota ‘yan jaridu sun rufeta sai tambayoyi suke mata, dasauri tafara kiran “ummi ummi ummi kizo mana” wacca takira da ummi tafito daga kitchen dasauri tazo tana fad’in “haba Amira wannan kiran mafarautan fa” tace “ummi zo kiga k’awata MUFIDA gatanan wai itace takashe mahaifinta da mijinta”,,,….
Zama tai ummin saida aka gama hasko abun sannan suka nannauyan numfashi atare Amira tace “wallahi insha Allah na tabba ummi wannan abun sharri ne saboda na tabbata MUFIDA bazata iya aikata wannan abunba” kallonta ummi tai sannan tace “Amira yanzu wani zamani yazo da ko iyayenka bazakayi shaidarsuba bare kuma aboki” cikin damuwa Amira tace “ummi nazauna da MUFIDA tsawon shekara hud’u nasan halayyarta mai kyau da mara kyau MUFIDA ko fad’a mukayi itace ke saurin sakkowa daga gadon fushi saboda bata iya gaba ko k’anwarta mubina data rainata wallahi kosunyi fad’a itace ke fara mata magana ummi na tabbata wannan sharri ne akamata kuma wallahi koma waye yamata wannan muguntar sai Allah ya toni asirinsa cikin gaugawa”,,,….
Numfashi ummin tasauke tace “to Allah yafitar da’ita yakuma toni asirin wanda ya’aikata kada a yankemata hukunci batareda itace ta aikataba” Amira tace “ameen ummi gobe dole nayi sammako k’asar KEBBI kuma dan Allah ummi kitayamu da addu’ah Allah yatoni asirin dik wanda ya aikata wannan abun” ummi tace “insha Allah Amira kuma zansaka a masallatai atayamu da addu’ah” nan Amira ta tashi tashige ciki,,,….
Washe gari tin 8am dot tashirya tai’sa airport 10am jirginsu yad’aga izuwa k’asar KEBBI…………..
ska sannan tafara mata magana “MUFIDA nazone naji dalilinda yasa kika kashemuna mahaifi da d’an uwa, MUFIDA meyasa kika kashe dady meya maki nawa aka baki danki kasheshi, hmm wallahi MUFIDA kinbani mamaki yanzu dik irin alkhairinda dady yamaki abunda zaki sakamashi dashi kenan ki d’auki wuk’a da hanunki ki kasheshi wallahi MUFIDA kinbani mamaki kuma kisani dik abunda kika shuka saikin girbesa nan bada jimawaba” zafafan kwallah ne suke zuba daga idanuwanta takasa ciwa uffan zuciyarta sai kuna take mata kalaman mubina sai k’ara tafarfasa mata zuciya suke, d’agowa kawai tai takalleta batareda tace mata k’ala ba,,,….
baitab’a kawo mata tinani akan camera’s d’indake cikin gidanba amma badamuwa zansan yanda nai, yanayinda yaga tashiga hakan yak’ara bashi kwarin guiwa, badan tasoba tace “O….K…Ok toh” yai murmushi sannan yatashi yafita jim kad’an yadawo tareda masu cirarsu nan suka hau suka kwancesu suka bashi sannan yayiwa momy godiya yawuce,,”…
“Barrister Rayyan kajira har Barrister sadiq yagama nasa tambayoyin” sai Barrister sadiq yace “nagama my lord zai iyayin nasa” saiya dawo ya zauna,,,….
in hanunki ne saboda haka kidaina wahalarda shari’a ki karb’i laifinki saboda tabbas kece kika aikatasa” cikin nutsuwa MUFIDA tace “wannan wallahi dik karyane ba gaskiya bane ni bani nakashesuba saboda haka bazan taba amsar laifinda bani na aikatasaba” dole ki karb’esa MUFIDA saboda kekika aikatasa. Barrister yafad’a dak’arfi tareda dukan kan table d’inda take tsaye harsaida ta tsorata,,,….