TUNTUBEN HARSHE CHAPTER B
Washe gari After 2hrs open field lectures da mukayi daidaiku wayan da basu shiga hidimar competion din ne kawai suka nufi gida.. akan balcony Asad ya barni ni da zahra bugaje muna hiran lectures din da muka fito shi kuma ya nufi masallaci.+
“Sai Mukasame waje mai kyau muka tsaya fatimar ce Ta miko min wayarta da tuntuni yake hannun ta take famar latsawa..”
Tace Nadra,kar na manta ki saka min number ki..nasan Asad bazai yarda mu dame shi ba..ba yabo ba fallasa
Na karba fatima tabi hasken fatan hannu na da idanu in quick glance tana kallon jan kumshi dayaji yatsuna,cikin nitsuwa na shiga latsawa na saka digits zansa suna na nadrah,sai naga akwai match dayawa sai na juyo na dube ta dazinman na tambaye ta wani inkiya zansa mata tagane..kafin ta hankara sai naji an banke kafada ta da karfi sanda kasusuwan hannu na suka amsa
Na juyo da sauri
Sautin Qwas qwas na dogayen takalma shi ya cika mana kunne,fatima ta gyara tsayuwan ta da kyau, niko cike da mamaki Na dago kai dan naga waye charaf sai muka hade ido da wacce ake cewa carmila campbells…,tayi wani irin shiru ta kame hannun ta harde a hammata kamar bata san ta buge ni ba,take ma hade rai i looked at her well cikin nuna nima na san kaina cike da kallon sama da kasa babu kuma alamn sauki akan fuskta,”… just then na lura da ayarin ta wato molly da rico nasty agefe duka sunyi shiru sun tsura mana ido nayi tunanin nayi musu magana amma haka kawai naji araina carmilan bata burge nin da zaisa nayi musayar yawu na da su ba ..”yes tana da aji kam amma ko kadan kyaun ta be razana ni ba kamar yadda naga ta dauki kanta tana wani fixga cikin nuna ta isa tana wani hura min hanci,”
….mswww naja tsaki mai sauti juyowar can cikin dodon kunnen su sannan na dauke kai na..nace fatima ina jinki me zansa?
fatima ta karkta kai kamar me tunani chan tace emmm?kisa “pulchritude”..na mata kallon iyye?tayi dariya tace yes bazan manta cos its Asad’s favourite.. murmushi mai sauti ya kufce min nace ok,araina nace lallai asad ashe gulma na kawai yake iyayi in bana nan, batare da na bada hankali akan reaction din su ba muka share tashar su,since sun buge ni ba su ce komai ba muma ba sannu ba madalla muka yi banza da su mukayi kamar basa wajen,”
girman kan su budi baki suyi magana karara shi ya bayyana ayanayn su sai suka bimu da hararar gefen ido mai xafi still basu tanka manan ba carmilan ce ta gaji ta motsa tana gaba tana taku sauran suna biye da ita
Kallo daya nayi ma Bayan su nace”..mahaukata..fatima ashe kuwa baxamu shirya da yaran nan ba,wata acikin su ta sake min irin wannan rainin sai na barka wannan guntun skirt din”… cikin kasa daure abunda nakeji araina na fadi hakan,fati data lura da hakan ya ban haushi sai tayi kwafa salon tsokana tace oh oh no pulch,ta riko hannaye na ta juyo dani muna fuskantar juna,tace kar ki damu su…tell u what?nace what…tace ure so beautiful,..nace hmm na turo baki a shahance tuni na shiga kokarin zame hannu anata anma bata sake ba’tace..look am serious kullum ina fada miki ne amma baki yarda..,asad yazo da ilimi ke kinzo da kyau mai dauke idanu…dint u notice that haduwar ki ne yasaka dole azo ayi miki kallo na musamman?yadda taga ina yamutsa fuskan tasan kalaman tan a banza na dauke su,little did i knw that dagaske hakan ne,carmilla zuwa tayi taga kyaun nawa da ake fada..ashe dazun fitar mu daga lectures molly ta dauko chapter na a majalin su,tace guys have u noticed?gayen mu fa ya sako wata sabuwar teddy bear,’..carmilla ta daure tace “and she was holding his hand throut kamar wata makauniya
Molly tayi dariyar tsokana tana tarin karya… emm ehmmmm tuni carmila ta hade rai bata sake cewa uffan ba..wasu anan sunce ni blood sister Asad ne,rico tace sam bata yarda ba..ita kam ma haushi na ta keji
Cos bata ga alaman zanyi da’a ba8
Cin lunch ya fito da su,su ukun inda tun a step molly dake tana da far far ta dago kafadun carmila cike da tsokana tana nuna mata Asad daga can yana alwala,kallo daya ta masa ta dauke kau cikin rada molly tace umm uhmm carmilla kenan nidai am curoius,ashe ke kuma kama hannun sun shiya dame ki ba kyaun ta ba?
carmila ta tsaya cak cikin bugun xuciya amma bata iya cewa komi ba
..rico ta watsa ma molly harara alaman ta bari hakanan,molly ta dage kafadun ta tace ai bani na fada ba,ita tace hakan i just want to be sure..,carmilla kishi kenan? cikin roling eyes carmilla tayi gajiyayyen tsaki tace”..i hate u molly kin fiye maida gobe tmrw…wani kyau ne acan?a mean dube ta kamar karar tsana,siririn hanci da farar fatan ne ya raxana ki koko shamanmen nonowa da basuyi rabin nawa ba?molly ta wani fashe da dariya tace the babe is a model..babu abunda ta rasa.. Nan rico itama ta jona duka suna mata dariya tace kawata ashe baki kalle babe din da kyau ba.”she is nat bad persay..pls lets be truthful and shame the devil
Wani dauke wuta carmlla tayi ta kau da kai,nan molly ta taho ta dafa kafadun ta..sincerely speaking molly tace she is beauty to behold,and yes kuma ni bana so Ayi mana kishiya da ita..wani harara carmila watsa mata ta rasa mema xata ce musu duk dama tasan Allah ne kawai yasan meke zuciyar ta game dani tun ranar data fara ganin mu
Dazun ma Don ta tabbatar da maganan rico na cewa bata kalle ni da kyau ba ne yasa suka zo inda muke din su kare mana kallo..Saukar sun ke da wuya sai ga Asad,yace muje muyi lunch daga nan 2.00 dede za’afara competion dinsa da campbells this time a schl court room za’ayi.
Tare muka bar wajen Bayan mun kammala 3mint to time dede muka dawo court room already intrested students da members din brain box club duk an hallaro,ba a bar su carmila a baya ba su ukun a normal sitting position dinsu,Asad hanklin sa bai wajen amma na lura gaba daya mu suke kallo..na dada riko hannun sa cikin nawa kamar ban san da idanun su ba,tsaki na ja a raina yafi sau hamsin..
Can aka kira su wani daki su biyun,bayan minti 10 sai ga carmila sanye da kayan lawyoyi ta fito daga bisani sai asad shima ya fito cikin same dress.
Sunyi matukar kyau,altho ni nashi kawai nafi gani.
Nan Aka fara case zafi xafi akan mental slavery,”..
Bambancin bauta da biyayya..
Carmila tana karewa shikuma yana opposing
A cewar carmilla bauta da biyayya abu daya ne,dan biyayyar shine ginshikin bauta
Acewar asad kuwa ginshikin biyayya shine samun yancin kai,shikuma bauta kangi ne,basu da alaka da juna.
Suka shiga fafatawa kowa yana tsara basirar sa wajen yin magana da fayyace point dinsa inda wannan karon kusan dukan su akan dede suke tafiya,har aka gama aka tattara bayanan su duka aka watse akan washe gari za’ cigaba.
To washe garin da muka zo da safe akayi,dan haka aka bada carmilla dama ta kawo case file na one of the student acting as the victim of mental slavery a bainar jamaa tana masa tambayoyi masu ma’ana cike
Ilimi da basira..
Sai dai kash,Iya kokarin da carmila tayi wajen nuna cewa biyayya da bauta abu daya ne kuma yin su dukan su bazai shafe yanci ko lpyan kwalwan ba,but the more tana fadan dalilun ta the more asad yana bayyana ma client din cewa rayuwar bauta ko biyayya ma burin wani ko naka shine mataki na farko wajen ruguza rayuwar dan adam harda kwakwalwa.
“Karshe haka ta hakura tayi shiru,yace Rashin samun yancin kai shine mental slavery,,in ya fade hakan baya damun ta kamar in yace rashin samun yancin ruhi wanda shi tafi fama da shi musamman akan son sa dake damun ta wanda bata amince da shi ba..She knew shes getting affected amma sam taki bari hakan ya nuna a fuskn ta,rana na biyun asad sai ya fita bada bayanai gamsashu masu ma’ana.3
To arana na karshen munfito zamu schl sanda muka bar gida snn asad yake cemin shifa tunda ina nan nice zan zamo client dinsa agaban court dan haka na shirya amsa tambayoyin carmilla,”.. Naji fargaba but for mentioning her name sai naji himman tsayawa awajen kodan in kure ta.
Aikuwa fafatawar yau sai yafi na koyaushe xafi dan gani na ma kawai da carmila tayi ji tayi kamar zata sauke hawayen takaici,she was actually red with disgust,daurewa ma tayi tamin magana and her last question was:
“Tana so ta ji shin soyayya yakan kawo bauta da biyayya koko zallan tsana da bauta ke iya sa mutum ya shiga mental slavery
Nace mata soyayya baida alaka da irin wancan biyayyar dan ba dole bane kaso kuma asoka,sannan soyayya yanci ne shiyasa baida alaka
Bauta,in har yay alaka da bauta to tabbas mental slavery zai shigo.
Tayi kokri sosai wajen kwakwlo lotd of questions tana tambaya na amma sai dai bata samun saukin amsar su a baki na,karshe dan kar ta bada kanta kunya sai ta hakura tayi shiru
Aranta Sam bata so ace nima ina da ilimi sosai ba.4
Daga kan wannan amsar sai Asad ya kara da bayanan sa,inda yake fayyace mata matsayin biyayya,alamomin bautar da kai da kuma yancin dake cikin soyayya..
Duk da haka sam taki ta rusuna ta amince da hujjojin sa har ta soma bada mutane haushi Basu lura da yadda Tin kafin a gama ta rikice zuciyan ta ya cunkushe ba,bayan jin haushi na daya cika ta not even molly is with her today
Time na cika aka daga maker,kowa yay shiru ana jiran sakamakon gasa
Bisa ga tsarin kundin tsare tsaren su na lawyan ci da physoclogical facts da asad yayi ta amfani fa su shugaba dalibai sai ya ambaci asad xain matsayin wanda yaci nasarar gasar.4
Nikm Sosai nayi murna,duk dama sai yau na dada yadda da irin farin jinin da asad yake dashi wajen dalibai,na lura da kowa awajen ta kan mu yayo compelling carmila ta cika alkwarin ta na saka shi a brain box da kuma nuna yardan ta akan qudirin sa.
“Kukan xuci take kanyi idanun ta har sun kasa boye wutan su”…Badan taso ba tace he is welcome to brainbox…sai dai ita akwai girman kai baxa dai tace yafitan ba.
Mutane sai basu barta ta karasa speech din nata ba suka dada hura mata bakin ciki da kananan magana wasu nacewa lokacin ta ne ya kare…boldy wasu suke mata dariyar mugun ta
Rico nasty ce tayi kkri dan ta langwasa yanayin carmila kar suyi abun kunya awajen amma ina,..
Carmilla Sai tayi amfani da zuciya tace”tunda mutane sun zabe shi ita daga yau ma tabar club din…Hankli a tashe Molly da rico suka yi kanta suna tambayar ta why?tayi shiru kamar zata fashe da kuka tana bin kowa da ido,daga audience kuwa su fada ta amsa su Cece kucen da ba’a tabayi ba anan ya kaure. .
Abun da gaske sai ya dame Asad shi kadai yasan yadda carmila ta dauke brain box da muhimmaci arayuwar ta an for her to say she quit yasan ba karamin abu bane,…and i was like who bloody cares..tafi ruwa gudu mana..Ganin ta kore kowa ajikin ta tana cewa suje asad ne leader su yanzu ita a kyale da sauri asad ya sake hannu na ya iso gaban ta”..yace whats wrong with u..sai ta kauda kanta a masife,ya dan kamo arms din ta ya jawo ta da karfi,ta dada hade rai ta fincike kanta ta banka masa harara.
.duk wanyanda suke wajen haushin ta sukeji,asad yace look ke kika saka gasar,ai ba abun fada bane,if u want i wll leave,I dont want ur club,i want to. .sai tass ta wanka masa marin da sai da waje ya tsinke da silence,wani tsam nayi ayayin da na ji kaina na sarawa a zuciye na taho zan wanka mata marin nima sai naji fati ta riko hannun na dam dam cikin hana ni zuwa kusa dasu
A hatsale carmla ta juya ta bar wajen
Asad yay saurin jawo ta baya ya juyo da ita tana fuskntar sa ransa abace yace”U slp me?why…
Sai Ta kalle shi da Kamar baxata amsa ba chan cikin tsawa da ihu Tace yes,u ruined evrything..kaine munafukin..sai ta wani fashe da kuka “meye na maka?why did u want to ruin my effort cikin kukan ta dago ta kalle shi straight in d eys ta jefa masa wannan tanbayar jikin sa ne yay sanyi she is badly broken and defeated,ji yy ya kasa ce mata komi,ta cigaba cikin muryan kuka”kasan abunda yasa na tsane ka?sai ya dago kai suka locking idanu,tace u act like u care abt me har dacewa kana sona,bayan ba hakan bane,all ur stay, u do nothing less than destroy my dreams I seriously dont see u as a human being,makaryaci mayaudari kawai…
Abun sai ya mugun damun zuciyr sa sai yace Carmila pls listen..bata kula ba A mugun raunane ya dada matsowa, tayi sauri ta sauke idanun ta sauran hawayen ta ta share tace dont say a word,na baka brain box na baka fili kaida masoyan ka amma ka sani Bana tsoron ka,mummunan halin ka na yaudara da karya shi ya sa na dena ganin darajar karatu bawai na kasa ba.
Yace karyan me namiki?cikin fushi tace Meyasa bazaka fito fili ka nuna asalin tsanar da ke zciyar ka game dani ba
Sai ka dinga nuna sabanin sa?…u played ur game well
But im not scared,inka shirya cire mask din nima zan nuna maka ni wacece..but right now i cant fight a faked physcopath like u.. ure nothing less than a muderer who kill ppl nd act like a saint aftr.
Wajen sosai ya dauki shiru shikansa Asad baice komi ba,rico da molly ne suka karaso zasu taba ta hankln su atashe nan ma tsawa mai xafi ta daka musu,..
Tace Leave me alone,molly ta mata ihu tace composed urself carmilla..wani sabon hawayen ta sauke sai asad yace ma molly..”pls let me take her home..dake murynsa Dauke da courage ne sai suka matsa masa,yana kai hannu zai taba ta naga ta sake dagowa cikin hatsala zata mare shi,..bansan sanda na fincike hannu na cikin na fatima na iso gaban su ba
Cikin bacin rai da tsawa mai nuna baraxana afili nace ‘”..enough”Dont u dare…??a haukace carmilan ta maida hannun ta ta dago ta kalle ni sai Kyat ta dauke kukan data keyi ta tsura ma yan ytsuna dake pointing din cikin idanun ta ido,”…
Asad zaiyi magana molly da rico suka hayayyako suka tsaya mata kamar ba yanzu tagama korar su ba
Nima Na sha gaban asad na bata raina sosai ba alaman sauki tattare dani
Suna kallo dukan su
Ko asad din ma kasa taba ni yyi yaja bakin sa yy shiru daga baya na… Who is this?…Rico nasty dake tafi nuna bata kaunata tafada a walakance tana min wani irin kaxamin kallo,ko ajina Na maida mata kallon tara saura,na ja tsaki mai sauti..
Tuni ta hatsala…
“Hey dont hiss on me Molly ma ta hayyakoTsakin na kuma ja again and again na Na share su,ni marin da akayi ma asad ne yafi damuna harga Allah banjin zan yafe,jira nake suce zasu min wani abu na sauke haushin marin a fuskn daya daga cikin su amma sai sukayi shiru
Haka na wuce gaban su mollyn nayo ido da ido da carmila wacce alaman rikicewa ya gama zautar da ita slowly ta saka idon ta anawa ta kwaklo karfin gwiwan cigaba da kallo na,aikuwa ban fasa ba na cigaba cikin mita..nace who cares abt u?kin bi kin cika ma mutane kunne,kince baki yi rhen leave quietly why are creating a sin?.na nuna ta yar yatsa kamar ni na haife ta nace look
Ba damuwa irin taki ya kawo mu law schll ba…we need a break frm ur drama
Wani hadiye gullutun bakin ciki carmilla tayo tana kan kallon baki na nace”and one more thing u better stay away from my brother..na nuna sauran ma da yatsa cikin tsaki kafin na dawo kanta nace mata miss dumy kinjina..?i wll not have u disrespect him anymore,kikasake marin sa sai na miki blue black,in ba tsoro ba kiyi dani ni nan na isheki dan nasan na ko ni na fiki ilimin da kike buga kai akai..why im i not obessed with mine?wato kece wawiya ko..u have to let us be mungaji da yarantar ki..wani irin jan numfashi carmila tayi ts kau da kanta tana hawaye masu xafi alaman she is more than furious at me,Chan sai tayi zuciya ta goggoge hawayen tan take suka bushe tamkar wacce batayi kuka anan ba
Kalma daya dana furta na cewa”my brother”shi yake ringing a zuciyar ta
She was like Dama ita kanwar sa ne?that sound like a cool pool in a middle of hell”sanin haka ya sa taji dama dama aranta.
Se dai wani tunani ya mata dabai baiyi gaba daya sai tayi kyat cikin rasa tattaro kalma daya da zata cemin
Nikuwa Na kalle carmillan da kawayen ta a walakance,bayan su kan sun dade da wanko min harara ji suke kamar zasu kashe ni,harara na suke idanun su kamar xai fado kasa…tsakin da suka tsana na ja mai tsawo,nasan ba abunda mutum yafi tsana kamar ka dube tsakar idanun sa kayi magana ba fargaba ba tsoro nace..following a mean and stern voice na musu kallon raini da yarfawa na dubi zufa zufa da sauran damshin hawayen dake fuskn carmilla nace hmmmmm sai na sauke ajiyan zuciya nabi su da wata karin magana nace look…”Your faces is lame,maybe u shud drown urselves in foundation,ure a virtual pollution.
A Duk da yadda jikin kowa yay sanyi amma hakan da nace bai hana wajen kaurewa da wata irin Muguwar Dariya ba,.”..what a savage,da alama
Shashantar da maganan ma nayi
Rigimammen Dadin Sautin murya na kansa azaba ne bare yadda nayi maganan da sacarcism…tsaban bugun zuciya da wuri Carmilla ta rufe fuskan ta,sauran kawayen nata suka bude baki galala suna kallo na
Carmilla ta juya a fusace zata bar wajen,Asad bawai shima beyi dariyar bane amma sai ya juya adan dame zai je wajen su da wuri na kamo hannayen sa cikin harara nace da shi no u cant,sai ta juyo irin bari taga me zaiyi,aikuwa tana gani asad ya biye min ya batta ya dawo ya tsaya kusa dani.ta wani dauke numfashi da sauri ta karasa fita kawayen ta sukayi yuu suna bin ta abaya..
Bayan fitar su wajen ya dawo daga hm sai uhm wasu kuwa Har muka bar wajen basu dena maimaita zagin danayi ma su molly suna dariya ba,…
Nida asad Tare Muka raka fatima har gaban motar ta munata surutu Asad sai yyi shiru kamar bayajin zancen mu…
“Im so pissed,amma haka nake dannewa dk da haka duk abunda nakeji araina game da carmila shi nayi ta fada ma fatima..,alhmdull ko fatima bugaje ma bata musa min ko daya ba.”Nace neman ilimi hauka ne?wannan ai bakin ciki ne kawai da nuna hassada da rashin tawakalli irin nasu na tabbabu.2
I can understand in mutum yaji haushin kansa dan baisaba da xuwa na biu ba,amma meye dalilin ta na ta kurawa rayuwar Asad?nace mace ta sake haka tana marin namiji ai rainin yyi yawa,niko in har ina da rai tayi na karshe kenan..Kuma in har halin ta kenan baxamu taba shiryawa ba.2
Shidai Baice uffan ba har muka dawo gida duk ina lura da shi,So nake shi da kansa ya jawo maganan kafin inyi masa tas tas”i tot he said she is his friend?bayan ni banga wani kawance awajen ba sai tarin raina sa da tsanar sa datayi..all for what? cikin raina na furta ina ta bambami kallon sa nake har ya kammala shan ruwan sanyin daya dauko a fridge.
Bayabo ba fallasa shima ya kalle ni nima sai na masa shiru,shidai be nuna min bayajin haushin behaviours din carmila ba haka ma be nuna alaman yana bin bayana ko baibi ba..this has left me confused a bit cikin dauriiya nace da shi”..miye kake kallo na..Are u eating?…atake ya girgiza min kai alaman a’ah,sai yayi hamma kadan tare da sauke ajiyan zuciya..nadra?nace naam,a hnkli ya furta sai da safe…cikin wara ido na kalle shi nace what? baxaka fito ba ne?Yace ehn,i need ma time alone..kinji?..sai bance uffan ba na bishi da ido har ya juya ya barni anan ban motsa ba
“Huhhmm…na sake wata gajiyayyr ajiyan zuciya,Araina ina cewa Allah yasa asd ya fita a sabgar yarinyr nan da wuri,nidai bana jin na tsane ta but i really cant tolerate her,musamman in abunda nake matukar kauna zata rika walakntawa.
Yau Haka na wuni ina take masa wajen su kawu,gashi sai tanbaya na yake yi akan abubuqa daban daban،karshe nace musu ai dama da ciwon kai ya dawu yayi competition a schl kuma ya gaji sosai shiyasa yake ta barci.
Daga nan Kawu be sake kulawa ba ya cigaba da jin haushi aransa”how lazy can he be,in ya tuno da yadda azad yake da azama da son faranta ma iyayen sa rai sai yaji hankalin sa ya dada kwanciya…kawu ya runtse ido aranshi ya furta Allah ka taimake Dana Azad ka kare shi duk inda yake. .kullum dai aransa baya gajiya wajen furta hakan.
Nikuwa Har dare yyi nisa banyi barci ba,juyi nake akan gado na daga dungu zuwa dungu,tunanin Halin da asad yake ciki ya gama galabaita min xuciya,chan na tashi na zauna wani sasaaynr ajiyar zuciya ya kufce min…
What is Asad thinking?..i need to figure out..inda hali zan bashi shawara kawai ya dena competition din.
Cikin wannan tunanin nayi bacci,washe gari da safe bayan duk an karya banga asad ba sai na haura dan in shirya inje in same shi,to fitowa nan kenan najiyo muryan sa naji dadi sosai dana gansa a tsakar gida already yana sallama ma kawu zai fice,na dada lekowa naga mama ne agefen sa tana murmushi
,wow,its seems like today is gonna be a gud day,cikin sauri na karasa saukowa dan na ma kawu sallaman nima
Na rusuna a ladabce,nace a dawo lpya..kawu ya juyo ya kalle ni ya dan gyada kai da alaman saka min albarkan shi,”ya kuma tambaye mama ko ina da wata matsala a schl?da fuskan murmushi mama ta kalleni tace dashi babu matsala ai na tanbaye ta,yace to alhandulh in akwai kuyi tunani daga na dawo azo asame ni tace toh daga nan ya kada kafar sa yayi waje tana biye dashi ko kallon asad baiyi ba.”he care so much abt me,sumtimes much more than his kidz..hakan kuma na debe min kewar mutattun iyaye na arayuwata shiyasa nake mugun daraja kawu,har ya fita agidan kaina na kasa cikin yabon sa araina..dawowar mama daga rakiyan tace to zaku wace kenan?
“Nace eh,shikuma Asad yadan sauke boyayyen ajiyan zuciya ya gyada kai,” daga ni har mama bawan da ya lura da yadda ya dauke abubuwann aransa,tambaya yake meyasa duk wani so da gata kawu baya saukewa akansa?isit a crime to do what he want in life?da kawu yake tambya na…’he just tot ko anya ma tunda aka haife shi ya taba ce masa yay kake bare menene matsalan ka, .but who cares now..,ya ciza labbansa wishing that akwai cigarette a hannun sa yanzu to blow away the dust…Yau ko magana bamuyi ba while azuciyiyon mu daga ni harshi Allah Allah muke mu kama hanyar schl dan mu tattauna abunda ke ran mu.
Har mun fita a falo sai ga mama ta biyo mu da glass cup mai zurfi a hannun ta bansan me aciki ba amma da alama yayo sanyi sosai”…
Tana murmishi tace Kunga madara na aje muku jiya akan in kun dawo kusha Unfutonatley sai gashi na manta..
Duka muka juyo muna mata murmushi,just so that na bata damar nunawa danta kaunar data dade tana killacewa nayi flako na ce ni na koshi..،ai kuwa ta saka shi agaba ta tursasa shi sanda ya bude bakin sa ta bashi da hannun ta she look very happy doing that,daga yadda take kallon sa zaka san tana makutar kaunar sa2
Shikuwa daya gane hakan sai Yana sha yana wani sauke nishi dan yasa taji farincikin alaman Madarar tayi masa dadi sosai,”tce Allah ya maka albarka,yyi sauri ya dora mata kiss a goshi,maka ta kai masa tana murmusawa tace”..baka san ka girma ba ko,irin abunda kake yi kenan baban ka yake gani yana jin haushin ka,Asad yay kwafa yace “kai mama its just a peg,just to show u that i love u…nidai babu wanda zai hana ni kaunarki mama na.murmushi mama takeyi cikin rasa tacewa yace Take care of urself mum sai mun dawo mama tace ok bye,har muka shiga motar bata dena jin farincikin kalamann sa aranta ba..
A hankali yake tukin kamar baze min magana ba sai kuma naga ya juyo ya kalle ni?…da muka hade ido sai na dan murkuda mai baki,yace hmm ya tabe baki yace ohh tsaban an tsane ni ko gaishe yau baza’ayi ba?na kau da kai cikin tsimewa nace ni ban tsane ka ba… Why dint u open ur door?tunanin me haka ya ja lokaci?kasan su mama zasuyi ta tambaya ko?awar ka nawa a dakin?ya dan lumshe ido yy shiru can yace
Nady,…ban kula ba ya kyabe baki yace …baby nace tunani nakeyi fa..na ce toh ka gama tunanin so what?
Nady i think i have to see that girl once again
“Nace what?akan me?Ita bata zo ta nemeka ta baka hakuri ba sai kai zaka nemo ta wow now i got why,dole ashe tana marin ka….” A sanyaye yace pls enough babe..ki fahimce ni Ni bawai nace zan je na bata hakuri bane,nadra ki lura mana yarinyar tana da matsala..sannan kuma Akwai rashin fahimtar juna a tsakanin mu,.nifa cewa danayi ina son ta ba dagaske nake ba..hasalima bana tinanin hakan araina…jiya nayi tunani sosai akan maganganun da tace akaina…and i really wanna make things clear
Nace hmmmmm to anji, sai dole kaine zaka je ka same ta?dole ne sai ta fahimce ka?ita waye haka?
Cikin roling eyes Yace,Ohhh nady Baki gane ba,nasan dai wasa nakeyi tun farko ai nagaya maki kawai dama so nake in ga ta fadin,but right now i want to clear things up..wallhy har tausayi take ban duk ta wani susuce akaina Besides Ni ba karatun nakeyi ba,who cares in banci law schl ba?tunda tana so kawai zan bar ta ta samu,but i wanna make sure ta dena kira na da munafuki me fuska biyu..i want her to get it i meant no harm8
Jinshi kawai nake can kasan makoshi nace hmmmm…
yace noo,pls dont hmmm me naddy
Nasan kina jin haushin ta amma dan Allah ki fahimce ni,nace ok..2scnds ina shiru,can ya kalle ni da wutsiyar ido yace nady inje?..na gyada kai nace fine sai kaje ka same tan…yay murmushi ya harare ni.. Na maida masa nima na hade rai cikin wasa nace amma da sharadi..hannun shin daya ya bari akan stirn ya juyo da shi ya kalle ni a miskilance,”..asad in har kaje ta sake marin ka bazan kyale ta ba,i mean it….”‘dan dariya yayi ya kwalo idanun shi,yace inye?toh soryy mrs Asad,ba mai mara miki ni,sai yay dariyar sosai yana kallon turo bakin danayi yana mai kara gudun motar,sautin wakar “breathless”na shyne ward ya fara playing yana miming da sweet voice dinshi yana bina da wani dan iskan kallo yana murmushi”while he take it as nothing ..a fanni na kuma all this are confusing my heart,wani bin asad in yana min abu sai inji a duniya babu wani sai shi” ya cigaba da wakar sa..nidai bance da shi komai ba,a hankli dauke kai na ina kallon window blushing very shyly inajin kalaman nasa wanda kamar feelings dinsa ne yake bayyana min azahiri..2
Muna shiga harabar schl ya sauko ya bude min mota ya riko hannu na as usual,daga nan muka isa aji nan na lura kusan kowa ni yake kallo ana famar tuna abunda nayi jiya,..
Ban wani kula ba har aka tashi,yau carmilla batazo ba Haka shima Asad ya wuni neman ta bai ganta ba wasa wasa har tayi kwana uku batazo ba su molly ma sam basa son kulashi musamman in suka ganni awaje ko tsayawa basuyi, na lura hakan sosai ya so ya dame sa amma baison cika nunawa.
A rana na hudun,mun sauka kenan a mota zamuje schl market fare mu ci junks sai muka ga cunkuson mutane..
‘Get away from me..muryan carmilla ne ya fargan da shi da sauri yace min come lets go ban musa ba na bi bayan sa.
“Wani dalibin muka gani,wanda kwanan nan mukaji kishin kishin cewa ya bude nashi kungiyar and abun mamakin shine nashi kungiyar ma is strong kamar dai na carmilan.
Shine yasata agaba da tsokana bisa abunda tace nacewa xata bar ma asad brain box,gashi babu su molly anan ita kadai ce,sai kokarin tare hawaye takeyi amma ina…
” gayen Yace Yaga tun ranar data haukace bata zo ba ko lpya?taki ta kula shi,..dariya yayi ya fara maimaita mata zagin danayi musu in an embrassing way..iya dannewa tayi sai ta dada share shi..xata wuce ya jawo arms din ta tare da dangwala ta gabansa kamar xata fashe ta nunasa da dan yatsa amma tsaban fusata bata iya cewa uffan ba, sai yace mata shikenan ya fasa tanbayar tunda tanajin haushi anma ya maganan barin ta brain box club?..kau da kai tayi dan abun yana bata mata rai matuka,koda ta daure ta budi baki zata amsa sai ya tsare ta cikin kwaiwayon muryan kukan datayi ranan sai ya ke sake tsokanar ta,bata zubda hawayen ba amma Abun ya ci mata rai sosai har jikin ta ya shiga rawa bata sani ba
“Gayen is really anoying sunan sa noah scot,club din daya ke son budewar kuma shine “the law buccaners’..a wani tarihin ma ance shi dan cult ne dan kungiyar bucanners suna daya daga cikin the most dangerous cultist nd confranternity grop a kasar nigeria,dede zuwan mu wajen da asad mukaji yana ce mata tunda brain box ya fadi kasa shi zai bude club dinsa..me zafi..and he wont take her becos she is not invited…Asad yaji wani iri duk dama shima hakan tayi masa a farko
Sai ta kasa cewa komi duba da yadda mutane ke kallon su,koni taban tausayi shiyasa da ta wuce Asad ya fara bin bayan ta ban ko bishi ko na hana shi ba.
Basu tsaya ba sai bayan wajen pool din mu,babu kowa anan for now dan wajen akwai sanyi yanzu ne ma hasken rana yafara budewa,a gaban ruwan pool din carmila ta tsaya tsam kamar wacce bata gansa ba ta fashe da wani irin tsumayin kuka mai ban tausayi,yayi shiru yana kallon ta
For some moment He cant even believe that duk binta dayayi abaya har suka iso nan bata ma lura da shi ba,”wani irin kuka kawai takeyi tana rirrike jikin ta salon da zai bada duk wani mahalukin dake kallon ta tausayi,”hakan kuma sosai ya taba kwalwalar Asad,”..sun kai minti biyar ahakan sai can sai ya lunshe idon sa ya taho kusa tausayin ta ne ya cike masa kirji..a hankli ya matso ya miko hanayen sa ya jawo arms din ta tare da cewa carmilla?cikin shako tattausan muryan san ta rufe ido …Sai tayi tsit amma bata dai juyo ba,da kyar ya jawo ta yana rungumar ta ta dada fashe masa da kuka mai sauti “ya rasa meke masa dadi musamman yadda hannun ta yyi karfi jijiyon ta suka taso ,hakan ya dada daure masa kai sosai he felt like she is heartbroken nd sad bata ma cikin hayyacin ta,daurewa yyi da karfi dan ya dago ta amma sai yaga taki ta sake shi ta dada rungume shi sosai..
Kasa yin komi yy a sanyaye ya shiga cewa ..,”its ok,kidena kuka.. i wll talk to him if u want…ta cigaba da sheshekan ta batare da ta kwace jikin ta ana shi ba, a hankli ta shiga furta what did i do wrong?im just being serious here hakan laifi ne?babu wanda yasan meyasa na dage ma karatuna,why does my litle failure become a cursed kusan kowa yana min abunda yake so kamar dama jira na akeyi.! ..asad shiru yy,sanda ta maimaita hakan sau ba adadi cikin kuka sannan Ya taba ta dan ta farga ta ganshi ta san shine fa awajen,sai yasa hannu ya dago chin din ta da palms dinsa,cikin nitsuwa yace hey look at me..da kyar ta iya dago kai ai kuwa suna hade ido tayi saurin kau da kai ta ja wani karamin tsaki mai nuna tsana a hatsale ta juyo kamar xata bige shi,but da tazo xata wuce sai ya fizgota ta fado jikin sa..”get away from me… ta daka masa tsawa cikin kiciniyar kwace kanta..kirjin sa na diff diff sai bugawa yake cikin sauri amma haka yaki fir yaki ya sake ta,hawaye take tana kokowar kwace kanta but da taga ba sarki sai Allah sai tayo lamo ajikin sa idanun ta a rufe ta soma maganganu cikin sheshheka da nuna ta gaji da rayuwar ta..”voicing out how badly she need to be the best tace “i want this for father,nasan baxai barni ba in nayi wasa..i must win this..2
Tsaban tausayi muryn asad har yayi sanyi,yace Shushhhh…da kyar sai tayi shiru,
..batare da ya dago ta yace mata ta yi kkri ta cire hakan aranta in ba haka ba abubuwa da yawa baxata gane su ba.Yace pls Live for urself not for ur dad
A zuciye ta dago ta ture shi Tace who the hell are u to tell me that?.kamar me kenan baxan gane ba?i respect nd worship ma dad..duk abunda yace yana so dole ne xanyi..u have to get that too…4
Hmm kawai asad yace Kamar maraya ya matso kusa da ita,sincery speakng from his heart yace”.. Carmilla Ba rayuwa kike yi ba,ure in pain,ke baki jin tsoro ne?see, bcos of that biyayya makiyan ki kullum kuntata miki sukeyi And u wont get things now Kamar halayyar mutane,sai ya riko hannun ta yay ajiyan zuciya ya kuma dafa kafadun ta camly da kyar ta iya dagowa ta kalle cikin idanun sa ita kan ta tasan yaji tausain ta yau sosai araunane yce “am soryy for what happen,and even for yestade.. ok?ni bada nufi nake miki haka ba,i neva want to humiliate u duk dama niyya ta kenan a farko na karbi position dinki dan naji haushin mari na da kikayi bayan ni ban maki komi ba..asali na shiga gasar ki ne sabida friend dina fatima amma badan ke ba…u did embrassed her that day kuma banji dadi ba…sai Abunda kika fada jiya akaina shima naje nayi tunani,i admit na yaudare ki akan bana karatun jarabawa sorry again,..sai tayi shiru ta dan kau da kai bata tashi sake kallon sa ba sanda taji yace actually cewa danayi ina sonki da duk abunda nakeyi domin ki shima karya nake..,but i swear to u am not fake now i feel pity,banso inga mutum yana takura kanshi da rayuwar sa..i just want to get to know u please.2
Yana ta maganan amma Bai sani ba in shock take kallon bakin sa zuciyar ta na wani irin kuna da zafi..aranta tace ita koma yaya ne bata so ace Ya furta son daya ce yake mata a matsayin karya ba…so maimakon maganan san yana shigewa kunnen ta sai gaba daya taji bata ma son jin shi amma bai hakura sai zuba yake faman yi…2
Yace I respect u,kina da ilimi da basira and i know ure kind…in kinaso daga yanzu bazan sake zuwa brain box dinki ba..and u knw what?..ni nasan kinfi karfin wancan yaro….like a lost dog haka ta sake baki tana binshi da kallo tana ta fama da xfin dake damun ta azuciyar ta sosai jikin ta yay sanyi..duk dama asad ya bata mamaki sosai.
Har itace namiji zai basar?..duk kyanta fuk ilimin ta?So its all fake btwn them,while sumhow she felt sad in tana zagin sa dan harga Allah taso ace soyayyar daya firta ko baxai amfane su har abada da komai ba yadai kasance gaskiya….2
A hankli ta janye jikin ta kusa da nashi,tayi tsamm kamar zata ce wani abu daga bisani sai ta rungume hannayen ta akan chest din ta tayi shiru kamar me tunanin wani abu,.
Shima ya kure ta da kallo,wanda ita kadai tasan irin kokarin datakeyi sosai wajen kamewa da nuna kamar yanayin dake cikin kwayan idanun shi basu kafa tarihi a zuciyar ta.
Cikin dauriya,fuskn ta a murtuke tace are u done?..ya bita da kallo a marairaice yace yes…a hnkli tace ok,daga nan juyawa tayi cikin sauri xata bar wajen batare da wani response ba,”sai ya dada cewa pls am soryy..bata kula shi ba ta dada saka kai, jin bai ko motsa awajen ko yayi wani yunkurin biyo bayan ta ba sai ta tsaya chak batare da ta juyo ba tace naji…its ok…”amma zan yarda da kai ne in har ka fita a tsabga ta…and neva tell anyone about today pls act asif dani dakai bamuda wata alaka….i cant be ur friend,so u can’t get to knw me ..ni buri na nazo cikawa..
bana bukatar taimakon ka kona wani,in har kana daraja ni to kar ka sadaukar da komin ka akaina,just act asif we are normal student, kowa sai ya saka kansa kawai akan abunda ya kawo shi makarntan nan…cike da sanyin jiki mai ban tausayi ta sauke ajiyan zuciya ta lumshe ido tana budewa ta furta ..’yanzu da kasan menene burina,will u pls let me face it?Wani shiru ne ya gifta baice uffan ba sai ta juyo kalar tausayi ta dubi kwayan idanun sa muryan ta har na rawa tace
“…Am sorry…for being rude to u..
But Pls do not tell anyone abt today,by the way i am carmila campbells obasi it nice meeting you…
Cikin danne abunda yakeji na tausayin ta yayi murmushi me ciwo,Yace Asad zain Abduldshakur….
dan karamin murmushi kawai ta sakar masa daga nan ta juya ta barshi a tsaye bata sake juyowa ba.
#haaaaaaa let me see todays arquements…nidai nace gamu ga Allah
*TO GA tambaya ta daya ma fans,wai shin meyasa asad duk da asad yana nuna yadamu amma yayi saurin karyata kalman son daya furta wa carmilla agaban ta ya kuma jadadda amma bai iya fitowa fili yace ma nadra komi game da abunda ke tsakanin su ba duk dama ya san tana son sa sosai kuma yasan tasa aranta zasuyi aure…why is that pls?…why is it that ko a jokes matar sa yake kiran ta amma be furta mata a gaske ba?..,i want to knw the answer am curiously curioss😂
Har ta mule asad bai motsa ba Jiyayi ya Ya rasa abunda ke masa dadi a ransa,he felt so helpless daya ganta a hakan badon komai ba sai dan yana jiye mata nan gaba ..But why?meyasa iyaye ke sa buri me tsauri haka?nothing breaks his heart da ya tuna cikin kukan ta tace “im doing this for father..baban ta baxai so ba in ta yi wasa”.. Meyasa iyaye suke haka ne?ko ba akan karatu ba,mesa uba zai tursasa koya tsanan ta burin sa akan yarsa?
Anan sai ya tuno da rayuwar sa dana mahaifinsa kawu,..cikin kunci ya kada kansa ya kama hanyar barin wajen.
nikuma dake na dade awajen ina jiransa baixo ba sai da fatima tazo sai taja ni muka je aji amma zuciyata bewani kwanta ba,can na daga waya na tura masa tex for the scnd time’..na rubuta asad ina kake ne?pls com quickly.
Ko scnd biyar baiyi ba sai naga replay dinsa na bude na shiga karantawa
“Com bby..look tru the window nd follow me…now…
Cikin sauri na tashi na nufi windown fatima tana kallo na batace uffan ba,na leka sai naga hanya ne da yabi ta wajen da suka fito sai babban step da zai sada ka da can saman benen,..
Dada Lekowa nayi kadan daga idon da zanyi sai na hango sa acn kasa yana haurowa alamn yana so mu hade a can saman ne,banyi wata wata ba na ce wa fatyma ina zuwa.
Da sauri na dauko waya da jaka ta na fata bin steps din nikadai ina takowa sai naji shiru kamar babu kowa,har sanda na kusa kaiwa matakaln karshe na ji wani irin shewa da dariyar daya mugun bani mamaki da tsoro..da kamar zan shashan tar na wuce..Sai muryan carmilla campbells ya doke tsakan kunne ne,tsimewa nayi nayo kyat ina jin sautin su dariyar suke kamar an kunna musu comedy daga tvn aljanna
Molly tace Kawata ke muguwa ce…
Carmila da kyar ta gintse dariyar ta tace kinga molly bana son wannan sunan..Amma ai dole na ci uban noah,altho he is good…dariyar ne ya sake bule wajen sunayi suna tafawa su ukun su
Cike da mamaki Nace what dama wai carmilla tana shiri da noah ne haka?I was like Thank god fati taga yamin sunan sa dazu hala da baxan gane me suke cewa bama..
Maganan Rico nasty ne ya sake jan hanklina sai na leko dan nagan su da ido na, ita kadai ce me faman shan intoxicant sai ta dubi carmilla tace
“U have to be careful girl..
Carmilan sai Tace dont woryy girls,nice fa carmilla,adaora of obasi,the almighty campbells.
Dukan su Sukayi wata shewa..banjin yaren igbo dan haka banji me suka ce ba
Tamkar ba ita ke damuwa dazu ba naga Tana ta murmushin farinciki
….”Am santa am diabla,Ma’ana ita mala’ika ce kuma ita shedan ce.
Nidai ban fahinci maganganun ba,but for sure santa diabla is spain so na dan fahimci ma’anan wannan,su dai basu fito fili since wani abu ba amma haka kawai jiki na ya ban cewa wanan hirar tasu toh lallai akwai lauje cikin nadi,da wuri na bar wajen dan karma susan naji su.
Gudu gudu sauri sauri na haura na same shi agurguje nace Asad zoka ji wata magana?juyawa yyi adan firgit ya ce nadra please tsaya tukun kiji nawa,shawaran ki nake nema..Nace akan me?Yace akan carmilla… Kallo nabishi da shi,nace nima akanta nake magana..,yace oh what abt that?gaba gadi..nace Asad dama carmilla tana shiri da noah ne?yace mene?..nace yanzun nan nagan su akan balcony suna ta shewa da kawayen ta suna maganan sa’..mamaki yasa ya dan matso yace really?..”nace yes.. i dont realy get them anma naji tana cewa zataci uban noah but she still says he is good.
Asad yace and..
Nace naji dayan kawartan tace mata muguwa..ita kuma tace ma kanta santa diabla.
Yace Santa diabla?What does that mean Nace Angel devil…yace ohhh ..so what?u confused me bangane mekike fada ba..nace thats the point nima bangane me suke fada ba…Asad i feel sumthing fishy about them…noahn nan bashi ne dazu yake ci mata mutunci ba how comes shes being ironic about him?
Abun sai ya daure masa kai,but Tsaban ta ruda shi sai yaji ya rasa tacewa,kawar da zancen yyi yace I dont knw wat to think,hala kawai suna tadin shine,kinsan mata da gulma..nace no Asad wannan ba gulma bane..
yace ok..enough,koma miye ne zamu warware shi daga baya ..nace hmmm…”yace nadra bani da wanda zan fada ma damuwata sai ke,actually im worried…inaga bazan sake zuwa brain box ba carmilla needed this more than me tana cikin matsala sosai da mahaifin ta wallhy sanda na tausaya mata.
Sauke ajiyan zuciya nayi Nace hmmm wai Me tace maka ne?yyi shiru kamar be son cewa komai tsawon minti biyar nima ban tanka ba “..ok fine,tunda baxaka fada ba nidai shawarata shine kayi hankali da ita ni zan je class Na juya zan tafin dagaske sai ya jawo ni da karfi sanda na firgito sosai na bata rai irin ko kallansa banson yi….a hankli ya dube kwayar idanuna yace nadrah…na hade rai again nace meye ne?yce to ki kalle ni mana, Fuskar damuwar dake tattare da yanayin sa yasa nayi still bance da shi komi ba shikuwa sai kallo na yakeyi chan sai nace”..bazaka fada min ba?to ka sake ni ka cigaba da damun kanka akan carmilla Allah bada sa’a,wani dada jawo ni yyi sosai kamar zamu goge juna nace asad ka barni haka in tired nagaji da lamarin nan..just then i noticed he look nervous da kyar ya furta bawai baxan fada miki bane,tace na mata alkwarin baxan fade komi ba ne
Asad be taba tinanin boye min wani sirrin sa ba..cike da mamakin sa nace ok…cike da rasa gane ina y dosa a raunane na soma kkkrin fixge hannu daga nashi amma sai yyi sauri ya kamo hannayen duka biu ya dada makalewa cikin nashi cikin yanayi me tafe da sanyin jiki yace..nadra believe me ban taba boye miki komai ba kuma baran fara ba, i want to tell u this..maybe u cud help her too
Wani bin tausayi asad yake ban with much relieve nace ok just go ahead..
Sai Yy composing kansa kamar da wasa ya fara fayyace min yadda sukayi da ita be boye min ko jan numfashi ba
Nikuwa a lkcin wani irin lunshe ido nayi inajin saukar tsananin kishin sa da wani irin raxanan da baxan iya fassara shi ba..
Ya cigaba bao tsaya ba sanda ya kai aya..but Duba da yadda na dawo tin kan ya kammala yasa be tsaya yin sharhi ba da sauri ya dada riko hannyena,yasan ina mugun son shi so ba lallai na fahimci meya ce din ba.
“Nadra…pls understand this,..dama na fada miki bayin ta bane she even apologised for being rude,am just confused abt evryting tausayin ta ya kama min raina..ita mace ce fa?,but why?meyasa iyaye zasu na ma yayan su haka,all she want is to be the best not even for her self for dad …can u imagine.
Dannewa nayi Nace hmmm yea,but Asad ka kwantar da hankalin ka mana,pls relax,u cant even trust her did u?
Yace no,but i think i trust her now,i mean a’ah ban yarda da ita ba”. ,da chan ne nake mata kallon haka,amma yanzu kamar na fahimce abun sosai,tausayi take ban,rayuwar ta yakansa na tuno da namu,ashe rayuwa iri daya mukeyi?
rayuwar takuri da rashin yancin kai.
Nace ure confused Asad,rayuwar mu danata akwai banbamci sosai
Yace meyey ne banbancin?nace munada yanci sannan babu wanda yatakura mu yce sai mun zama na farko
Yace uhum cigaba da karyan..,nace asad ka kasa fahimtar yarinyar nan,she is just obsessed with being the best,damuwar ta kawai ta buge kowa
Yace haka ne Amma ai akwai dalili,nace kowa ma yana da dalilin yin abu aryuwar sa asad.
Yace ohh i see,kuma dalilin ne zaisa da ya kasa yin irin rayuwar da yake so
Sabida mahaifin sa?
Nadra Look at u look at my brother azaad..duk abunda yake yi sabida farincikin baba ne ba farincikin kansa ba.. why is that?huhn..cikin fushi ya karashe
Bata rai nima nayi sosai Nace,shi Axaad din ne ya fada maka haka?
Shin In tambayeka mana Why r complaining kai Meye bakayi asad?kana fita lokutan da kake so,duk wani abun da kawu ya hani kana aiktawa at ur will good or bad so?mekuma kake nema…yace still i dont have freedom abunda xakayi a boye?.
Ai Yanci har a zuciya yakamata ace ya na nan kema ya kamata ki yanta kanki nadra lets be free sai Na masa shiru.
Cike da damuwa ayanayin sa Yace Farin cikin ki kawai nake so,ina so inga ke da axad kuna aikata abun da ranku yake so bawai ki aje rayuwar ki sabida ra’ayin iyayen ku ba
Tsaki nayi kasan makoshi nace keeo confusinh urself… shiru yamin tsawon mint biu sannan na kklle shi..cike da nitsuwa nace haba Asad, ashe akwai wanda yakai iyayen mu son mu ne?God’s love is 70times close to mothers love babu wanda Allah ya kusanta son dayake mana da ita sai uwayen mu,shikuma uba shine mutumin nan daya ke dawwama arayuwar sa yana sadaukar da duk wani farinciki da jin dadin sa don kawai ya sama maka rayuwa mai kyau mai billewa,asad tunda aka haife ka kawu be huta ba,he gave up on all his comfort and satisfaction yay karatu yay aiki dare da da rana in pain and distress dan ya raya ka why must you not worship him againt ur silly desires?in iyayen mu basu cancanci mu sadaukar da wani abu domin su arayuwa ba to waya cancanta?itama carmilla so da daraja iyaye yasa ta take haka..baka sani ba halaa ma ita baxata taba iya yin butulci ma uban ta ba ne shiyaaa ta ke takura kanta,in ba haka ba shin ta taba gaya maka cewa tayi ma uban ta korafi akan abunda take so?i dnt expect u to judge her blindly sabida kai tsakanin ka da kawu akwai matsala nd then it might be ita ba haka bane tsakanin ta da dad din ta…who knows
Sai Yy min shiruu baice komi ba,can kuma yace ba haka bane nad,this is still wrong,is kind of destructive!
Axafafe Nace yes,ur freedom is desructive asad.
..kasan me?
Yancin da kake neman ma bai ma karbe ka ba,bcos all u do is harm self,party shan taba,yawon banza and u dont want to listen to anyone sai shegen ra’ayin ka
Wani furzan iska yayi alaman maganan ya sosa mai rai…yace”What if thats wht i want,nadra farinciki na baida wani muhimmacin kenan arayuwa dan iyaye suna da daraja?nasani nima ai,but atleast abari kayi biyayyar lokutan da kaima hankalin ka yake kwance…..if i dont party or smoke im not hapy,ni rayuwar da zai sani farinciki shine yanci na…Kaga ki nan kullum kina gida kina daki,u dont even knw waht u want,…and i hate that,kuma ynxu haka am also woried for that carmilla,baxata ma iya hutawa da karatun ba,kiga wahalan datake sha tana takura kanta and all she think abt is her dad..oh my god..yayi stressing words din a zafafe yana mai dafe goshinsa
Nayi shiru Na dade in kallon sa bance komai ba cahn Nace hmmmm toh
shikenan think wateva u want to think…but yakamata ka sani ko da carmilla na cikin matsala aganina ta amince da matsalar ne,”
beside meye naka ne aciki?..yarinyar nan bata bukatar ka cos she see u as a n obstacle to her success…amma tunda ka nace da tausayin toh abar maganan kawai,nidai nasan rayuwar mu dana carmilla bazai taba zamowa iri daya ba akwai bambamci kawu only want the best for us ba yancin mu yake neman tauye wa ba,kaima kuma zaka zo ka gane hakan.
Yamin shiru Baice komi ba,..nace ni mu tafi…this conversation is over
Ya kalle ni yaga na hade rai da kamar zaice wani abu sai ya kyabe baki ya juya kai cahn yace ‘lets go..a tare muka bar wajen muka sauko main hall kowa dai da abun da yake lailawa aransa.
Har aka tashi muka isa gida ba’mu sake dauko wata magana
Irin haka Sai dai yau ma tunda ya shiga daki yaki fir ya sauko…nasan tunanin halin da carmila take ciki yake yi and i dont wanna fight him nasan bazai wuce ya zauna yayi ta bushe bushen taba ba,to meye ne asad ya matsa da rayuwan yarinyar?,’..well nasan is in mens nature to go after macen da tafiye walakan ta su,and yes men dont go after strong women thy love to support emotionally helpless women againts all odds..
Carmilla kuma ta hada duka biyu hakan yasa ma na dena mamakin damuwar asad akan ta
Amma Ban taba sanin cewa asad bai fahinci komi game da son da kawu yake mana ba sai yau,ga kuma tausayin kanshi dake neman zautar da shi wanda yake dannewa.. dalilai dayawa wanda yasa na kaasa tantancewa.
Amma nasan ayanzu yazama min dole na tsayar da shi akan lamarin carmillan nan,im not againt him in ya temaka mata amma Asad yana bukatar ya fahimnce mahaifin sa kawu kafin yace zai taimaka ma wata na daban
.
Beside ni ban ji ina tausaya mata ba chan cahn ba,after wat i saw today da kuma abunda asad ya gaya min,toh ganin su suna dariyar yasa sai zuciyata taki ta amince da gaskiyar ta,and cud it be that itama kamar asad take basu fahimci son da iyaye suke musu in sun saka masu takunkumi ba?..ni na san dai babu yadda uba zai haife yarsa yace zai takura mata ta inda yasan xai cutar da ita,..maida kaina nayi akan pillow na runtse ido na sosai,”aiki ne mai yawa agaba na…i have to get up,dole ya zame min na bude masa ido yaga abunda yake dai dai ji nayi Bazan iya zama haka na cigaba da faruwa ba..asad shine rayuwata,he is the love of my life i just cant bear it.
Ko da na runtse ido banyi wani baccin kirki ba,da asubahin fari kiran sallar farkon na diro daga kan gado na,ina sauri ne amma be hana ni saka lallausan 100% coton bathrube din ba,ina matukar kaunar sa ko ba komi in nasa naga yamin das das kamar wata model hakan yana kara bayyana ma zcyta wani feeling din kasaita ayayin da shigar yake nuna min asalin baiwar da Allah yayi ma tsarin jikina.
Agurguje na hada ruwan wanka mai dumi na wanke kaina,har na fito sarari ina tsatsanewa qamshin sabulan wankan da nayi amfani da shi be dena cika min hanci ba,sallatul fajr na fara yi kafin na shafa cream sai na dawo na dora da sallar asubahi,bayan nan jawo stool nayi zama na a gaban mirror,ina kallon kyakyawan fuska ta ni kadai ina tantancewa.nace inyi kwalliya koko in bar shi hakan?u cant really diferntiate tsakanin asalin natural beauty na da na make up duk dama asali ban cika tsawwala wa ba…amma nikaina nasani ina da matukar kyau in banyi kwalliya ba fiye da yarda zaka ga na yi kwalliyar2
“Wani shegen ajiyan zuciya ya kufce min mentally nayi murmushi ayayin da kawalwata take rayamin wani abu,” blushing widely na ce makaina cut the crab,a ban shirya ba haka nayi kwalliya marar nauyi,just ligh pink powder mai haske na shafa wa fiskata sai na goga oily chappette mai qamshin strwberyy,na bude closet na jawo dan bingel din gown marar nauyi pus pink colour na sakaya black hoodie knited cap wanda ya maida suma kaina duka sukayi baya..
A hankli na bude kofa na leko ta waje all quiet nasan zai kai awa biu kafin zulai ta fito,Hanyar kitchen din na nufa na kunna gas,ruwan zafi na dora na saka medicinal lipton da aka saba dafa ma kawu,ginger da mint na kara akai na jira tafasa daya na juyr shi cup har sanda turirin ya dan sasauta,.
A Kitchen cabinet na dauki mop cup mai tsayi mai zurfi na daureye kafin na juye lipton din dake faman qamshi,pure honey na zuba amaimakon sugar na juya ban bata lokaci ba na nufi dakin asad da shi.
2mint ina knocking ba abude ba na tura kofar na shigo na same shi yana kwance ruf da ciki’..nayi Alhamdull daban ganshi wani yanayi ba,da kallo daya nabi ko ina kafin na matso ina takawa a hankli idanu na stll akan shi,sanda na iso daf na aje shayin a stoll na xauna gefe da shi kadan cikin sauke ajiyan nunfashi..nace Asad?nayi taping gefen gadon da palms dina naga yyi luf yyi shiru bai kuma juyo ba sai da nasake kai hannu na sai sannan na lura da earpice dake makale a kunnen sa
“…Sautin Hmmm kawai na sake a hnkli na zare kunne daya daga nashi nakai kunne na dan naji me ya saka shi nitsuwa haka har da lumshe idanu”a zato na wakar daya saba sawa acd player a tsakar daki shine yakeyji,ina kaiwa kunne na kuwa sautin muryan sheik abdlrasheed minshary alfasy ya doke kunne na,cikin daddan qira’ar sa cikin suratul ibrahim mai shegen dadin daya ke tabo kohon zuciya da qwalqwalwa,nayi murmushi again,wani shegen dadi naji araina..
well i dont blame Asad for swaying away now,dan ko ni babbar masoyiyar muryan minshary ne,banda haqqin karatun da zai sauke na kowani harafi abunda yafi burge ni dashi shine shi yakan karanta qur’ani ne kamar yana bayyana mana ma’anar sa a sarari..ga mai imani zai tsorata yyi kuka, game fahimta kuma dole ya dada gane cewa qur’ani littafin Allah ne kuma maganganun sa ne masu daraja cike da hikima da yantarwa,ga wanda ya iya gane ma’anan rubutun arabic da wanda be iya ba minshary ya saukake, somhow dole xaka gane wani abu a ayan qur’ani in har minshary ne yake karantawa,to top it all,his voice is highly mersmerizing dadin daxaisa ki sauke iya karatun qur’anin ki fiye da sau daya a rana..he is at normal speed shi baya hada ayoyi suyi tsayi sosai sai in dole ne,baya sauri sosai so u can easily catch ur breath with him(😉 my fans,he is ma favourite sheik nd Qur’an reciter dont mind me and dont miss out,check out his qur’anic visualiations videos and audios on youtube,im asuming u saying “thanks” already so “ure welcome☺)
Juyowar sa ke da wuya muka hade ido,sake lunshe nasa yayi da sauri kamar wanda kyun fuska nane yake maimaituwa a brain dinsa,’..nayi shiru nima ina jin karatun,dayaga hakan sai ya nitsu slowly ya shiga bude lunsashun idanun sa har ya ware su mai gaba daya ya sauke akaina,”na sake masa murmushi ya kashe min ido a akasale,a kunyace na sauke idanu na kasa motsi shikuma ya kure ni sosai da wani kallon da baxan iya fassara shi ba…har sanda sheik ya kammala qira’ar sannan Asad ya zare dayan earpice din,”..yayi mika bakin sa dauke da addua’..well wannan kam nasan yakanyi dan ko a egypr ma da muke kanana shiya koyamin duka aduaoin safe da na maraice,ina ta wannan tunanin sai charaf idanun sa ya sauka akan cup din dana zo dashi sai ya dage min gira..nikuwa cikin sanyin murya nace…”tea? Na dauko na mika masa,ayayin da ya tashi yaxauna akan gadon yana mai nade kafafun sa”..ba jira ya karbe tea din ya shiga sha da shike ya dan huce sai bai bata lokaci ba ya juye tas acikin sa yana min wani irin kallon gefe da idon sa guda daya,shidai bazai ce min ya gode ko ya yaba ba anma wani irin sace zuciya ya iya da salon sa na nuna yaji dadi sosai danayi masa hakan.
Forget abt the ginger and herbal lipton”tafashen mint da pure zuma maganin kara ilimi ne,many scholar have proven that mint da honey suna warware jijiyon dake kara kaifin tunani da iya rike karatu cikin sauri..
Asad yyi yunkuri kamar zai aje empty mop nikuwa har na sake jiki na xan gyara zama charaf sai naji ya wani finciko ni na fado kan kirjin sa, a dan firgit na dan tura shi na bata rai,shikuwa fuskan sa dauke take miskiliyar dariya yace wai kinyi mafarki na ne?..a shagwabe nace stop it da Allah..ya dada manna ni da jikn shi,nace Asad ka bari mana,ya tallafo waist dina a hankli yana matsowa da fuskan sa ta gefen kunne na,dede kan kafada ta ya ajiye kansa yana mai sake slight breath cikin sauri na runtse idanu na sosai,kirji na ne ya shiga bugu batare da na sani ba ma jiki na yafara kyarma sai naga nafi mayar da hnkli na akan zazzafan numfashin da dake saukar min da feeling din dake sakani sake asirtaccen goose bumps,”..zanje daki…yace akan me?ba mafarki na kikayi kikazo ba,oya tell me what happen?xan jnye jiki na naji ni dan dam kamar zanyi kuka nace toh ka sake ni..nifa tea na kawo maka”…yace and?na turo baki cike da shagwaba na matse bance uffan ba yy murmushi ya tabe baki”baxakiyi magana ba,ok to mucigaba da zama ahaka ,nace no pls,ai ai kaima kasan meya sa nazo ko?,dole ne in zo in duba lpyar ka,jiya baka ko ci abinci ba…jin haka ya sa naji Ya sake ni da dan sauri,nikuma sai na juyo cikin wara idanuna ina duban sa kamar bani ke gudun jikin san ba,”yace nadra kikace dole?
Na yi rau rau da ido sai ya girgiza kansa kawai yyi yana me kare min kallo,yace hmm fuska ba yabo ba fallasa sai yyi kwafa yace ko da shike ance wai zaki aure ni,i gues thats why na zama miki dole ko?… a baxata na galla masa harara..cikin sauri na dauke kaina na hade raina kasan makoshi nace ohhh maganan banza xaka fada min? banko karasa ba na sake kara a firgit zan mike…a mugun firgice na juyo sakamakon tsakura ta da yyi,Asad bana so,na fada cikin muryan da yayi kama da wanda zatai kuka.”
Yace baki so ko baki sona?..cike da turo baki nace both..nidai kadena .
Yay dariya mai sauti yace To kema ki dena,nace mene?yace takura kanki akaina mana,kamar zan cinye sa na hayayyko cikin harara nace wake takura kai akan ka?kai din wa
Hannu na ya capke abazata ya riko ya dora akan fuskan sa queit serious yace ga ki? mama cewa fa kawai tayi mun dace,hala hala in mun girma muyi aure,shikenan sai abu ya dawo official?4
Nace kuttt,waye ya dawo da shi official,yace ina wata?toh ni dai ba ruwa na,tsaban takaicin sa ji kawai yayi na maka masa pillow a krji,na fizge tsaye a masife,a duk dama ban yarda Asad baya so na ba amma nakanji fargaba sosai in yana cewa hakan akan tarayyar mu.3
Nace akace dakai dan haka nake zuwa wajen ka,ya boye fuskan sa a pillow cikin neman tsokana,na hade rai na kwace pilown na jefar,nace wayake rudin ka?ure not even the deal..ya wani fashe da dariya,..nace im serious da munin kan nan ma wazai aure ka?ure so so disquisting nd useless..,ya kure ni da ido dan yaga ko alaman wasa da dariya babu ayanayi na.. yace to shikenan bude cahn ki ban kwalin taba ta jiya dama ban shaba..,’nace inyeee?ka ma raina min hankli aikuwa nayi wuf na juya kan drwer na jijiga zan bude buri na nayi seizing tabar sai naji shi gam gam a kulle,..tsakin dana ja ya sa shi dariya yace taaaaaaah i gat u?1
Ai sai ki bar mumunan yaron yy kashe kansa why are u angry at my ciga..wato dan in na mutu ba wanda xaki aura ko?
“Nace really,to ka mutu man,inma me kammanin nake so i wll marry azad..ai shima dan mama ne ko?…daga cewa hakan sai naga yyi shiru bansan meyasa ya dena murmushin ba daga baya yace nadra just admit it na fiki gaskiya akan komi…cikin kin sarewa nace”ure so useless..ka kasa fahimtar komi dai..kaifa dan uwa ne Asad,in na kula da kai ma duk yiwa kaine…ya sake yin dariyar yace kai da kaya duk na wuya ne ko?..naja tsaki…anan na hade raina Sosai nace
Im being serious here,na kalle idanun sa,yes i care about u Asad,amma bawai ina takura ka bane dan wani abu,” ai ko jiya ma na lura ne baka jin dadi,and u know zuwa party da shan taba sam sam baida kyau….shiyasa nake
Yawan magana
Sai kawai ya kyabe baki playfully yana kashe min ido,cahn yace And?
Nagane so yake nace ina matukar kaunar sa,sai na hade rai Naki na biye masa…
Haka kuwa Yayi ta tsokana ta,some of his words are actually deeply affecting my feelings amma sai na barshi awasan daya dauke sa.1
Atleast he is smiling so broadly now,naji dadin daya kasance nice na sanya shi cikin wannan yanayi da safe nan,dagan gan na dada bata rai sosai na ja gefe kamar dagaske raina ya sosu da wasan dayake min,iya yi yayi ya gano ni amma haka na cizge naki sam,cahn dayaga na kafu wani ajiyar zuciya ya sauke salon rarrashi ya sauke muryan sa ya dafa kafadu na slowly yace,hey..na basar shi na ki na juyo,karshe ma na sunkuyar da kaina kamar anmin mutuwa..hnkli atashe yace ya salam Daga wasa sai bata rai?..toh ki kalle ni mana..na dada share shi..yasan bana son tickels dan haka shi ya min a baxata wanda ya sa na fashe mashi da asalin kuka na tashi da sauri kamar zan bar masa Wajen azafafe sai ya finciko ni jikin sa…’hey hey,ya shiga shafa fuska ta cikin tsumayin kaunata daya ke yi aransa wanda bai san da shi ba,da kyar na nitsu sai de ina kau da kai ne shima yana cusa min fuskan sa a haka dai har sanda yaci nasaran saka kwayar idanun sa anawa muka lume cikin idanun juna muka lula duniyar gajimare…a hankli hannun sa yake shafa gefen fuskata kamar mai gyara tsillin suma na daya dan fito”giran sa ya dage cutely tare da sake sautin muryansa cikin sanyi da karairayewa,ararrabe cike da shauki ya furta”hey,..that..pulchritude…(Hey that physical beauty)
Wani sanyi ke ratsa zuciya ta..a Lokacin na dade da suman zaune ajikin sa,duk jiki na yay sanyi dazun amma ina yunkurawa zan dauke ido ya fauce hannu na dacewa ‘”hey am sory..na bude baki kenan kamar walkiya naji saukar cold nd vibrant lips dinsa akan nawa quickly yayi brushing light peg akai,tsaban bugun zuciya na lunshe ido hawayen tsoro da fargaba dakansu suka sauko,shikam be damu ba..jin hanayen sa nayi yana tarewa da yatsan sa.,”nadra,pls ya isa…karki min haka mana,in farinciki na tayi hawaye nikuma me xanyi kenan?..u have no idea how much u mean to me
Meyasa xaki sani agaba kina min kuka?nifa ba hakan bane ya dameni kawai kiss din ne dayayi min bemin ba..still bance komi ba na cigaba da hawaye sai Ya tallafo fuskata cike da sigar rarrashi yace akan auren ne?ido na kamar zay fado kasa ayayin dana balla masa harara..hey Im just jokin ai kinsani ko,infact am ok.. Nd seeing u this morning make me so happy babu mahadin shi..u wanna tell me what u want?baby fadi
Duk abunda kike so yanzun nan zan miki..i promise
Tausayi ma yaban da naga ya kawar da wasa a fuskn sa a karo na farko yana lallabi dan kawai na bata raina ina kuka..
This became an oputurnity for me sai Na dago da kyar cikin shagwabben yanayi Nace r sure?
Yace yes name it…
Nayi shiru can,na kalleshi a marairace kamar marainiya
Nace Asad,yace uhumm say it…
A sanyaye Nace”..Nide bana son abunda zaisa ka rinka kasancewa cikin damuwa
Yace i know..,
“So i want u to pls,listen to me
Yace ok
Nace Asad,ina so ka dena shiga harkan wancan carmillar, i mean tunda ita dakan ta tace ka kyale ta sai ka hakura,nidai i want you to face ur own life..ga abubuwa dayawa wanda zaka iya dubawa..kamar shan taba,yawo..ga kuma kawu.. Pls…kaji?na dada marairaice masa
Shidai Baice min uffan ba Kusan minti goma yana ta kallo na,har na gaji nayi lamo gwanin tausayi akan kirjin sa…
“Chan sai na farga cikin juyi sakamakon jin Hannu sa dake yawo acikin nawa,da dan karfi ya jawo ni a hankli ina kallon sa har ya dora ni akan kirjin san da kyau inda xan ji bugun zuciyar shi
Wani shiru ne ya sake ratsa tsakanin mu ya lunshe idanun sa tsam kmar me naxari cahn ya kuma budesu tare da sauke su akan nawa
Yace In na kyale carmilla shikenan? A langwabe Kamar kyanwa Nace dashi eh..witou any delay yace ok I will do as u say.. kinji?…a baxata nayi murmushi shima ya maido min ..
#Pls i wanna have somtime with ma family today shiyasa zan aje page da safe but i wll be coming online time to time to check on ur coments.
#…tuntuben harshe mai cike da sarkakkiya,..ina fans din campbells ne pls who understand carmillas reaction today?why is she ironically laughing? atemaka amana bayani..
Team nady…😪😪my pppl me kuka ce ne?im emotionally unhappy,wai meyasa maza ke wasa da feelngs din mata ne musamman in suka gane suna son su?
Shiyasa bana team asad..buut lets wait and see..bahaushe yace yaudara yana daya daga cikn sunnonin soyayya..isit true?😪
Karma is a bitch fa Asad beware👹👹
Dear nusaiba kabeer,thanks for trusting nd being the first person to download complete qur’an from ma said favourite sheik abdlrasheed alfasy minshary”she said its wow..i was so happy for her..pls remain blessed..nd jaxakallhu khaairan+
…blushing shyly na matso kadan na sauke masa peg a gefen kuncin sa shima juyawa yyi tare da sauke min numfashin sa akan fuskata yana gogawa kadan kamar wanda xai cinye ni,karin bugun zuciya yasa na dan dafe kirjin sa zan matsa sai naji ya riko waist dina da dayn hannun shi.
Wani heavy knock daga bakin kofa shi ya fargan damu muka juyo shikam ko damuwa baiyi ba sai nayi saurin ture sa zan sauka agadon bai sake ni ba a firgice kuma a hankli nace,”asad pls let go..bakajin knock?..yay min shiru ya matse ni jim kadan mukaji sallaman mutum akan mu.
Hannun sa cikijn nawa yana mrzawa Muka waiwayo a tare,Hade ido da mama da mukayi yasa Asad yyi sauri A dan dolen sa ya sake ni,nima na mike na tsaya a tsakure inajin kirjina na mugun bugawa,in shock mama ta zuba mana idanun ta,wani shirun minti 3 tayi tana kan kallon mu tana kuma kare ma yanayin dakin kallo,evrything looks suspicious ga gadon abarbaje gashi babu wani kayan arziki na cahn chan ajikin mu,yadda tayi da fuska zaka san sam bata ji dadi ba yanayin fushi ya bayyana sosai…
Asad ne ya motsa zaiyi magana ta tsare shi a hatsale tace wai meke faruwa anan?sai yyi shiru bai amsa ba mama ta juyo ta dube ni tana maida min muguwar kallon tuhuma, saurin maida kaina kasa nayi dan ko kayan dake jiki na ya isa yasamin fargaba da bugun zuciya,tace nadra mekike anan da sassafe?meye ya faru?da kyar na dago cikin sanyin murya nace mama dama dama na kawo ma Asad abu ne,da sauri ya cabe maganan yace mama nine dama na kirawota,a tsawace mama ta juya tace mashi “shut up nacr kamin shiru…yanayin ta yasa Sai da duka muka hadiye yawu,”..
Tace baku da hankali ne? since when has this been happening,Asad ya mike daga zaunen dayake yace mum pls dont over react ba wani abu takeyi anan ba,”..da wani irin harara mama ta tsare shi sanda yay shiru ya kasa cigaba,tace so what? ya dace na ganku tare a wannan lokacin kuma acikin dakin baccin ka?wani wasan banxa kukeyi da zaka rike mata hannu in bani na shigo bafa me zakuce da abban ku?to yanzu ka dube ka dube nadra,ko wani kayan arziki babu ajikin ku kun kyauta kenan,murya na na tsananin rawa nace mama dan Allah kiyi hkri,
Ranta a bace matuka ta dube ni,hanya kawai tayi min muni da shi,a sadade na taho na fice da sauri na barta da shi a dakin,fitan da nayi ahakan yasa Asad ya hade ranshi sosai mama bata fasa ba ta cigaba da yi masa masifa,
“nagaji da irin maganganun da kake jawo min agidanan,in auren kuke so ba sai ayi muku ba?wannan dabiar ai abun tsoro ne,Asad da hanklin ka zaka kebe da mace a daki har kana riko ta jikin ka?nadra muharramar kace?ko ka manta shedan ne,wato so kuke ku jawo mana abun kunya ko?..im higly dispappointed in all of u.,.yy tsam baice uffan ba har tagama ta rufe bakin ta tana kallon sa shikam ma gyara tsayuwar sa yyi kamar me shirin barin wajen in few moments,yin hakan dayayi yasa mama ta dada jin zafi sosai aranta a zafafe tace”.. im talking to u ya bazaka ansani ba,ya ce mama bawai bazan
Amsa ki bane ai naga har kinyi concluding ne bayan ke kinsan babu abunda zanyi ma nadra,mama nifa bana hakan kuma ai na gane kuskure na nadra baxata sake ba,mama kiyi hakuri pls,tunda haka ne baxamu sake ba, nide gaskiya bana son ke dakan ki kirika min wani iri kallo kamar bani da tarbiya,..for sure i wll neva do that ai kema kinsani ko?tsaban takaici hmm kawai mama tace alaman bata qamsu ba,tace nidai bana son wannan salon naka,baiyi kama da na me tarbiya ko addina ba yau yaxama rana na karshe da zan ga haka atsakinin ku…asad kaine babba so am i clear?yace yes,tace ka shirya ka fito yanzu bari inje in same abban naku,har ta juya
Sai ya dan lumshe ido yace zaki je ki gaya masa ne?ta juyo cikin banka masa harara tce tsoron me zakaji ai in nafada ma rufin asirin mune,kaga sai asan nayi daku..bai sake tankawa ba yay shiru abunsa har ta fice..
Nikuwa ina daki na babu abunda na iya
Yi sai jeka ka dawo duk fargaba ya cika min xuciya da nacin ran da mama ta nuna,tsoro na inta kai maganan wajen kawu fa?..qani girrrr naji kamar an cure min hanjin ciki na a tsorace nace na shiga uku..kawu zaiyi fushi dani..me zance na wanke kaina?
A haka har na bata lokaci Banfito ba sai ana daf zamu wuce makaranta,nasan kawu ya wuce offis dan haka na taro karfin gwiwa slowly nake takawa kamar wanda kwai ya fashe mata har na isa kfar babban falo wani ajiyan zuciya na sauke nayi sallama a sadade,muryan mama naji sai na shigo wani muskiliyar kallo ta bini dashi kafin ta hade fuskan ta,da kyar nattaro nitsuwa ta na sadda kai a kasa zauna a kusa amma bata sake kallo na ba
Wani shiru ne ya ratsa wajen kafin can nacem.”Mama dan Allah kiyi hkuri,nasan nayi laifi insha Allah bazan sake ba
Tayi shiru abun ta kamar bata ji menace ba Can kasan makoshi tace
“Tashi kije ki sauya wannan kayan baxaki je ko ina da shi ba,kuma ki rage pawder dake fuskan ki wai meye haka ne nadra?..nayu sauri na mike tsaye gwanar tausayi nace to kiy hkri zanje..a sace na dan dube jiki na dama english wears ne riga da skirt sai nayi rolling
Ba musu na haura na koma daki after 10min na fito da abaya baki da dan guntun hijabi ajiki na..tun kan na karaso gare ta mukaji sallama daga ido nayi sai ga asad shima ya shigo cikin kammala shirin sa daf a baya na ya nemi waje ya zauna”…nikam cike da rakubewa na zauna kasa kusa da mama tunowa da ko ina kwana bance mata ba sai nayi gyran murya cike da fargaba na gaishe tan ba laifi ta amsamin amma ciki ciki,chan ta daure dai tace har zaku wuce?nace eh,tace toh…daga nan batasake cewa uffan ba Asad yana ta kallon ta ya tabe bakin sa,”kamar bani na furta ba a hnkli na juya kalar tausai nace mama?kallo na kawai tayi nace mama kinyi hakurin na miki magana baiki ce min komi?da ajiyan zuciya mama ta tare ni,”to ni me zan ce daku nadrah,ai kun girma ne shiyasa kuke abunda kukaga dama..quiet unserious Asad yy kwafa cikin rolling idanun sa yace haba mama nafa baki hkri nima,.bata bari ya karasa ba ta wani banka masa harara
‘Tace Nidai na gaya muku kar ku kuma,ke kuma bawai bakiji ba?toh ni nasan matakin dazan dauka akanki,ku wuce ku ban wuri bana son wani magana
Yddda ta bata ranta sosai yasa duka muka kama kanmu muka wuce sallamar mu ma bata amsa ba
Araina Naji tsoro sosai,Asad kam ko ajikin sa har muka isa schl.
Normally muka cinye ranar muka dawo gida Asad bai je brain box ba sannan bai kula da inda carmilla campbells take ba.
Hakan da yyi ya dada sauke min tension,amma da muka dawo sai na lura babu abunda ya sauya ta fannin mama.
Sosai ta dauke mana wuta,ko ince ma ni don Asad kam shashantar da maganan yakeyi ko tana maganan sai ya nuna awajen sa baiyi tsauri haka ba
Haka mukaci kusan sati biyu a wannan yanayin na dawo sam bana jin dadi agida,in munje schl ne nake samun sukuni sabida kaurace wa damuwar su carmilla dana saka Asad yyi ya mugun sawa bama shiga wani hayaniya.
Da kyar mama ta yafe min,bisa hawayen danayi ina rantse mata bazan sake shiga dakin Asad ba.
Mama ta tausaya min data ga ina kuka kuma na nuna ma damu da bacin rantan,araina nasan taki ta fada ma kawu ne sabida tana matukar kaunar mu duka,maybe da ta fada ko schl din bazai yarda mu karasa ba hala sai dai yau yace zai mana aure..this is the first time mama ta boye ma kawu abu hakan kuma bakaramin damun zuciyarta yayi ba sabida mama bata iya boye ma kawu wani sirri sam sam hakan yasa na dau abun da gaske nima da kaina na kaurace ma Asad har sanda na shawo kan mama ranar ma da kanta ta kirawo ni kitchen babu kowa sai no da ita a lokacin zulai taje kasuwa shoping cikin nitsuwa da hikima ta min nasiha Tace nadrah,bawai zan rabaki da dan uwanki bane,ina guje muku sharrin shaidan ne.
Ki duba kiga yadda kawun ki yake,yau in wani abu ya faru tsakanin ki da asad me zan ce masa?,da wani ido zan kalle shi nace yar da ya bani amana ce na tarbiyan tar haka..kema kinsan ai bakuyi min adalci ba.
Shi namiji babu ruwan sa,kece zaki duba ki kiyaye martaban ki…mace an santa da tsada ba wai zaki sake ma namiji ba..yau ko aure na muku i still expect u kija mai aji da kanki wajen nuna masa ke mace ce zinariya mai wuyan samu..mama ta kawo ayoyi da hadisai tamin ftawa akan su sosai jiki na yayi sanyi”na saka hannu na share hawayen dake biyo kunci na Hakuri na dada bata na kuma Jaddada mata cewa bazan sake ba.3
Abu ne mai wuya in rabu da Asad amma da shike naga gaskiya karara cikin maganan mama dan dolw na na dena bin hanyar dayabi dakin sa.
Zamuyi magana normal ayi hira amma duk wayon sa bana yarda naje dakin sa”sumtimes dan ya kular dani sai yace min nazo na kirga kwalayen taban daya sha dan na ji haushi sai nace zan je amma duk da haka sai na daure na kama kaina
Sumtimes Nakan ce da shi babu kyau mukebe..amma daga nace hakan zai bata ransa.
Har nagaji na dena fada dashi na soma masa magiyar cewa to ko dan mama yayi respecting haka…Da shike shi kansa yasan abu mai wuya ne wajen mama ta rufa mana asiri sai kawai ya share maganan bai sake cewa komai ba
Wasa wasa har Nayi wata guda bana samun shakuwa da Asad kamar yadda muka saba ada chan
Shikuwa kamar an bude masa hanya daga mun dawo,zai sabule ya fita yawon sa cikin dare wani bin sai dai naga tex din shi inzai fita da in zai dawo
Thinking of how he is behaving at parties,da kuma yadda yake hndling cigarettes a dakin sa ya kusa galabaita mun zuciya..haka dai na daure
A schl bani da wata matsala sabida ta yadda banyi tsammani ba Asad ya cika min alkwari na na fita a harkan brain box da ita kanta carmila campbells,samsam ya dena shiga harkan ta da damuwar ta kamar wani me aljanu,..a fannin brain box kuwa Har aci a kare wani bin bama sanin me akeyi dama fatima ce take kawo mana labarin abunda ya wakana toh Tun abun bai dame ni ba har ya zo ya fara damu na,sabida da abun yayi tsamari sai na lura a ko yaushe fatima ta fadi magana me ban tausayi game da carmilla sai Asad yayi ta mata tambayoyi..
Fatima tace mana Yanzu gaban tsakanin ta da noah ne…
A zahiri competion din ya dawo tsakanin club biu,
Brain box da kuma buccanners altho wai shugaban makarnta bai bada bucanners cikakken licence kamar brain box ba.
A yadda fatima take bayyana mana,tace tsakanin carmilla da Noah babu sauki kuma noah ba karamin bada carmilla ciwon kai yake ba.
Abubuwan da ta zargi asad da cahn akan yanayi dan yaci mata mutunci sai gashi kaarara shi noah yake mata kusan kowa a schl din yanzu ya fahimce haka
Asad yakan dade yana jimamin yadda carmilla zata na coping da abun aranta amma sabida ni sai ya kaucar da tunanin sa akai ko acikin wasa bai taba cewa xaije ba.
But deep within him yana jin tausayi sosai musamman in muka ci karo ko yagan ta da kawayen ta suna karatun fanfalaki,duk da bata kula shi itama amma yakan dau lokaci yana tuna ranar datayi masa kuka tana fada masa damuwar ta…
#wow..Allah sarki surayhms yau da xanyi editing shafin nan sanda nayi murmushi sai na tuno da lokacin ina posting page 4 wata tace min relship din nadra da asad bakomai bane illa ina amfani da dama na ina bata tarbiyan yara,wai mace ta xauna akan cinyar namiji al’adar hausa fulani bla bla bla,i tried my best dan in fahimtar da ita na riga na rubuta littafin nan na tsara farkon sa da karshen sa, but she judge me horribly nd unfairly irin lallai tana so ni na amince cewa ni din mai batawa ne babu wani gyara a rubutu na abun mamaki har tace dama haka nake hmm..thats life..ko ita bata sani ba shafin nan na ajiye ina kuma kallon sa a time din dtake korafin, ni bance yanayin shakuwar su yana da kyau ba,but abunda ke faruwa ne azamnin nan nd i knw i will address this issure definately..so pls my ppl kuyi hakuri kudinga yi mana uzuri in muna rubutu,wallhy nidai ba kara zube nake shirya littafi ba and most writers sai sunkai page 10,20 har fiye kafin suke fara muku posting..so just follow inkaga abunda beyi maka ba ka aje korafin ka in kaga an kai karshen book ba a kawo gyara ba sai ka fadi duk abunda xakace ma writer..but is not fair to judge us like taht..gaggawa fa aikin shaidan ne..Allah dai ya sa mu dace Ameeen.
Asad tun yana yi yana kaucarwa wani bin aran shi sai ya fara jin kamar Hes becaming obsessive abt her condition secretly sai ya shiga bibiyan duk wani halin datake ciki da noah…
A Dayan bangaren kuwa shi baima sani ba amma dama burin su kenan,duk dama da kyar harsashen su ya bayyana musu cewa lallai asad zai ji tausayi ya kula,dan Fita daga shirgin su da Asad din yayi kwana biu carmila bata taba tsammani ba kuma hakan bakaramin taba zuciyar ta yayi ba’..tambayar kanta take meyasa take jin tsananin kaunar sa amma sai batagane komi a idanun shi face zallan tausayawa halin data ke ciki?,a makrta zaka ganta normal karyan ka ma kace Asad ya sha mata gaba,sau dayawa zata wuce ya wuce ko kallon inda yabi bata iyayi bare ta nuna ta ma san da shi,amma babu wanda ya sani sai inta koma gida ta kulle kanta a daki takan shiga wani hali,gaba daya ta rasa nitsuwa bare ta kula da kanta haka ma da dare bata iya runtsawa bata ji kewar sa na yawo a jinin ta ba..sosai take son shi sai dai bata san ko hakan aikin banza bane ko zai iya amfanar da su nan gaba ba..1
Shikuwa asad ya dauka duk akan burin ta take haka,kwana biu dayake observing he has neva seen her so focused nd dertemined shiyasa ya dada kama kansa ya ki yace mata ko da sannu
While ita da kawayen babu wani motsawar sa da idon su bai kai his slightest smile or gesture in yayi sai sun dau lokaci suna fassarawa,actualy ita carmilla bata jin ta tsane kowa a aranta kamar ni,she feels natural hatred dan ji take ko shedan zata iya yafe masa laifukan sa amma banda ni..but over what?Akan Asad..?cike da taurin kai sai taja tsaki cikin rashin son ta yarda da cewa kishin yadda Asad yake mun biyayya a fili kawai take ji aranta1
“…Haka rayuwar mu ta cigaba har muka kusa kaiwa lokacin rubuta jarawabawa na shiga shekaran mu na na karshe a schl of law, by now na gama fahimtar wani abu gameda carmilla,sai inga duk randa Asad yayi wani abu mai kyau na musamman sabida ni to sai wani abu marar dadi ya kaure a competition din carmilla da noah.
Asad kuwa yanajin labarin zai daga hankalin sa,tun yana boye min dan baisan bacin raina har ya gaji ya fara bayyanawa
“Nace da shi babu ruwan sa ya kyale su,sai yacemin tausayi carmillar nan take bashi ba
Nace asad tausayin yarinyar da ko kallon arziki bata yi maka?sai yace min karya ne wallhy ta damu da shi dan yana lura da ita sosai akan haka
Har nagaji na kyale sa,in wani abu mai muni ya same ta a ranar zai yi ta mita wani bin in kula shi,wani bin shiru nake masa shida kansa zai saduda yyi shiru.
Yau Ana saura kwana sha hudu ayi exams,waje ya kacamme da surutayya dan yau aka manna mana wata shiryayyen time table me abun ban mamaki wanda ya nuna cewa rana na farko zamuyi muhimman courses uku a paper guda each section carries 45 minutes kuma da safe ne karfe 7.30am..Ko ina maganan exams din akeyi amma sai asad bai damu ba
To aranar Bayan mun raka fatima ta tafi gida Asad ya riko ni da hannun sa daya jakata na dayan hannun sa a nitse muke takawa za muje inda yayi parking motar sa mu tafi gida..
A Daidai zamu sha kwana daf da student exit hall sai mukayi gaba da gaba da su camilla da molly da rico nasty,dukan su wando suka sa ita kadaice ta saka dan guntun skirt abin cinyar ta tana faman taku cikin yanayin nuna haduwar fatar jikin ta..take ta kankance ido tayi tsinin baki da wutsiyar gefen idanun nata ta jefo kallo daya me zafi wa hannun sa dake rike dani,nikuwa naji wani iri araina da Asad ya kalle surar jikin su,duk dama basu ko kula mu amma sai da naji kishi sosai harda satan kallon kaina…mama ce ta hana ni saka kaya kamar yadda da nake sawa farkon zuwa na,most time yanzu da atamfa nake zuwa da hijabi ko abaya,da kyar ma ta ban dama na ke iya sa kimono sai na tuna da chan har wandon jeans da falazo nakan sa muddin jiki na dai baxai nuna ba.2
Har muka isa Dai dai zai bude min mota idon sa ya sauka akan wani abun wuya akasa,yyi sauri ya daga yana kallo”nima na kalla sai..nace abun waye?ya dada kalla da kyau can ya tuno ashe akan abun carmilla ta fara sauke masa mari…bai amsa ni yyi maza ya juya yabi bayansu ya barni na tsaya kallon sa chan dai danaga wajen sun ya nufa dagske sai na shiga biyo bayan sa a nitse.
Sanda ya kawo daf da su ya dafa kafadun ta kadan
Yace”Excuse me…a nitse kuma cikin aji ya fada bai sake fuskn sa ba.
Sosai carmilla taji dadi daya biyo din Wani kyabe fuska tayi,Dukan su uku
Suka juyo cikin wata kaskataciyar yanayi suka tsura masa ido,”he has the habit of hiding it in his palms duk dama dagangan suka shirya hakan,da bata gani a hannun sa ba sai ta shagala da kallon dayake mata mai narka mata zuciya..,chan cikin rigima ta gwalo ido ta hade rai tace what?..sai ya dan kau da kansa..rico nasty tace ure wasting our time mister…tsaban ta cika dede face dinshi tayi twirling yatsun ta…,”hello…nace babu kyaywan mata masu diri agarin ku ne?Molly ta bishi da dan karamar dariyar rainin wayo tace,”i gues so.. cikin wuya ta karashe wanda yyi dede da isowa ta.2
Na kalle su sama da kasa,aran carmilla ji take kamar ta waye gari ace mata na mutu bana nan a duniya.. .bance uffan ba na ware hannun shi nace Asad bata abun ta mu tafi…nan ne taga yadda ya dunkula abun,cike da borin kishi ta wani kawo hannu zata fauce daga hannun san sai nayi saurin bankade hannun ta na kwace abun amya dawo hannu na…A hatsale tayi rolling idanun ta irin ita tafi tama karfin ta bude baki tayi magana da ni bare ta karbi abu a hannu na,nikuwa na dada gyara tsayuwata gaban sa,na musu kallon raini isar raina,kamar karnuka haka nake kallon su..nayi tsaki boldy and confidently na shiga mita ina cewa wato idan mace bata da aji ta shiga uku,comon sense of courtesy ace mutum bai da shi?nace wai meyasa baxa ku nitsu ku daraja mutum ba?..to in ma kina tunanin kina da wani abun da maxa zasu gani su biki ne this time arnd kin danna wrong button,nace taje dai ta sake lalumawa
..nayi ta mita ina surutu cikin manyance kamar ni na haife su abun kuwa na cin musu rai amma ban fasa ba sanda nayi facali da tattalin feeling din jin kansu da sukeyi anan5
Dake basu da gaskiya Tsit sukayi basu ce dani komai ba sai harara sai uban gyara tsayuwa2
A idanuna Babu alaman da ya nuna ina shakkar su ko ina jin tsoron su bare aje ga zan ragar musu dan suna da all that.
Dan haka na fito fili na nuna mata nagane nufin ta akan duk abunda take yi dan ta jawo attention din asad zuwa kanta
A lokacin Ninkin baninki carmilla ta dada jin ta tsane ni aduniyar ta
Nikuwa A bazata Na jawo hannun ta da karfi ta shiga fixgewa tana jan tsaki tana faucewa tana komi amma haka na damke ta ban kuma sake ta ba sanda na dangwala mata abun wuyan ta a hannun ta a walakance…ranta ya mugun baci har bata iya dena bin hannun nata da kallo ba
“Nace u drop it on our way…nasan bakida manners din yin godiya..Anyways ure welcome..5
Tana dagowa Naja shi nace mutafi.
…carmilla taji kishi matuka tuni idanun ta suka tattaro hawaye sukayi jazir kawayen ta kuwa haushi na sukaji har wani huci suke kamar zasu kashe ni2
Asad ya lura da hakan sosai sai ta bashi tausayi aransa he tot duk rashin samun yancin kan kenan,gashi tana so ta masa magana suyi mua’mala normally amma shi kadai yasan tanabin ta wani hanyar ne da tana basarwa gashi tana yarfa kanta duk dan kar ta shagala da karatu.2
Aikuwa kamar ta karance shi sai taki motsawa anan ta tsaya lumui abar tausayi uwa an hana marainiya abinci
tsaki nayi mai sauti na ja hannun shi cikin harara naga shima yanayin ta yake kallo”it feels like she is emotionally blackmailing him..a mugun hatsale na juyo kansu duka nace can you guys pls move on? Sai na kalli camilar na daka mata tsawan da sanda ta dago ta dube ni a firgit..what r u looking at?Nace miki Asad babu ruwan sa da kungiyar ki wai ana dole ne?he is not intrested in anything with u..pls face ur front mayya kawai.4
A razane Camilla ta dauke idanun ta anawa batace uffan ba dan Sosai taji haushi wannan tsawar da na mata…gashi ji take kamar zuciyar ta zaiyi amon wuta ya fashe da nace Asad is no more intrested in her.
Bayan ganin yadda tayi reacting Asad sai ya jawo ni dadan karfi,yace nady ya isa haka,naki in kulashi, ranshi adan bace yace pls stop it…lets go sai ya jawo hannu na..2
dai daikun student da suka fito wanda dama sun dade suna wandering meya ke hana asad sake dawowa brain box,toh Ganin mu tare mu uku anan sai yaja hankalin student magulmata dayawa suna so suji kanun labarai,altho bawai an taru ana kallon mu directly bane,amma 40% anan sun kasa kunne ne kuma babu abunda basu ji ba
A mugun hatsale carmilla ta fisge jiki ta shiga gaba tana tafiya kawayen ta nabin ta a baya.
Shi hawayen da tataro lokacin danake magana ne ya dame shi,baisan meyasa ba amma harr yau Allah be nufesa ya fahinci cewa son shi ne a idanun camilla ba…a tunanin sa daban nata ma daban, har muka shiga mota zamu bar schl baice dani uffan ba.2
Nikuwa na bata raina,wayar sa daya jefa a back sit ya hau ringing,dana yunkura zan miko wayar sai ya ture min hannu na a fusace
Nace asad meye haka?…yace baby i hate wht u doing…raina abace nace menayi?yamin shiru…nace dan na ce mata ta rabu dakai?abun tane fa ya fadi kasa ka dauka shine taje zata walakanta ka,that girl is insane bukatar ta baifi ta walakan ta abainar jama’a dan suyi dariya da kawayen ta,wato kafi son haka ko?..why r u angry at me now,da ihu na mayar masa Tsaban bacin da raina yayi muryan na har rawa yake.
Tsimewa yyi dan ya danne masifar sa shima..Controling himself sai Yaki ya amsa ni,dauke kai nayi sai nayi shiru na maida kallo na window har muka isa gida tun kan ya gama parking nasa hannu zan bude car da sauri ya jawo ni ya maido ni kan seat
“Fuskan sa adaure yace nadra Bana so..Bana son kina nuna kin tsane yarinyar nan a fili…i hate that..babu ruwan ki da yadda take treating dina ok?..mugun hade rai nayi,yace
im serious,sosai muryansa ya nuna alaman ranshi ya baci ..A zuciye Na fauce jiki na dan wasu xafafan hawaye naji suna shirin sauko min cikin dauriya sai ban sake na barsu ba Iya dauriya sai na daure,nace asad Kace Babu ruwana da yadda take treating dinka?are serious?yamin shiru..araunane nace..to meye nayi na abun jin haushi anan..ko bacin ran carmilan yafika maka mutuncin ka
Ne?..sam shi baison jin murya na ahaka sai ya dauke kansa
Ya lumshe idanun sa chan ya bude su akaina yana ciza labba Yace nadra yess ni banaso
…take na dakatar shi ban barshi yay dogon sharhi ba, Murya na a rarrrabe Nace dashi its ok.. fine..Kayi duk abunda kaga yafi maka in kaga dama ka tube tsirara ka bata bayanka tayi ta doka i …. dont…. care.. nayi saurin boye hawaye na cikin sauri na bude motar a fusace na sauka,bai biyo ni komawa yy yana mai maida kansa kan seat din motar ko kulani bai yi ba.
Wasa wasa mukayi kwana hudu muna daure fuska ma juna,da kyar shi ya sauko ya fara min magana sama sama ina basarwa yana basarwa alaman dai baxai ban hakuri ba nima banga dalili guda da zaisa in ba shi ba..
Haka muka cigaba har exams ya rage ana washe gari za afara,Makaranta ya nitsu kowa yay exusting kansa da karatu.
Muna fitowa nida asad zamu gida,charaf sai naji an wani cahfko ni an damke hannu na wani gaf kirji na ya buga,tun kan nafarga naga waye sai naga Asad ya hatsala da mugun hanxari ya juyo ya kwace hannu na yana mai tura ni bayan sa a kamar wanda akace zuciyar sa ne ni kuma aka taba..,ganin yadda Asad yy reacting azafafe yasa noah yay wata shegiyar dariya yace woah bro calm down,just tryna catch ur attention..nasan in ba ita na taba ba bazaka saurare ni ba,sai ya dan leko cike da wasa in a simple wavy pose yace min hy preety?naja tsaki na hade rai..
“What do u want?asad ya masa tambayar batare da ya sake fuska ba.
Noah Ya sake yin dariya mai kulawar ganin asad yaja tsuka ya kamo ni zamu bar wajen sai yayi motsi da sauri ya sha gaban mu
babu wani bata lokaci ya fidda wani special yellow and black card katin ya hadu dan ko jikin sa ma da logo mai dauke da kan kwanrangwal,bones da adda guda biyu akayi masa kwalliya..
Mannawa yyi akan kirjin Asad yace
Pls be my quest…
Daga nan bai sake tankawa ba yyi hanyar sa,.
.Asad kuwa tunda ya bude katin ya karanta sai ya finciko hannu na muka shiga mota munyi rabin hanya amma baice min komai ba..
Nikuwa nayi tunani kala kala danaga hnklin sa ya koma kan driving sai na shammace shi na dauka na bude card din na shiga karantawa”..katin gayyata ne bucanners night party ashe agoben bayan first exams din mu wai shugaban makaranta yace xai yanta club dinsa abasu cikakken licence kamar na carmila…
Its a hallowen party da horror mask ma za’aje kuma da dare ne karfe 10.30pm za’a fara..sai nayi shiru araina nace tabb,wani jifa nayi da katin naja karamin tsuka da kamar Asad baxaiyi reacting ba sai naga ya dage abun sa ya adana..na kasa daurewa nace me kake nufi ne?xai yi magana na dakatar da shi a dame nace Asad bazaka je wannan wajen ba
Is late,and is a party
Ransa adan abace Yace yess nadra its a party shiyasa dole naje..3
Wani Horn ya danna mai karfi da cika kunne dan ya dada kular dani da wani irin fichaka ya murxa striing ya shigo haraban gidan yyi parking,ko in kalle sa na sa hannu na bude kofar ina fita ya biyo baya na da sauri ban hankara ba naji an wani cahkumo arms dina anyi dani gefe tare da manne ni jikin bango…wani zazzafan nunfashin bacin raine ya kufce min Asad yaso mu hade ido amma na kau da kaina naki sam kuma babu alaman fara’a a tattare da ni
Araunane…”Yace nadra zan je partyn nan i swear to u zanje.
Toh Bahalin in daure abunda nake ji araina kuma Nasan in nafitarr da abunda ke rainan mama dake cikin gida ma zata iya jiyo hayaniyar mu,wani irin shakurarren kuka na fashe masa da shi mai karamin sauti mai kuna..sai naga ya bata ransa sosai bai iya daurewa ya jawo ni muka koma ta bayan gida can tawajen gidan engine din generator
Anan ya manne ni ajikin sa yana mai sauke nunfashi yana kuma sauraran kukan danakeyi..
Sanda nayi me isata na shiga bori,”na ce ni kasake ni,ya kura min idanun sa na tura hannun sa ajiki na amma baiji da ya kyale ni ba.
Yace ndy Wai meye damuwar ki ne in naje din?Nace dashi babu,sai kaje ni babu ruwana wallhy,hawayen daya sauko min sai nayi saurin sharewa kallo ya dada bina dashi kamar wanda nake kashe shi duk nasan baison yaga ina kukan ne
Ya matso zai kama hannu na na fauce a zafafe,jikin sa a muce yace nadra kiyi hakuri mana
Wallhy zanje partyn nan..u need to calm down i need u to..pls
Idanuna kamar zasu fado kasa wajen harara cikin shessheka nace baxan taimaka makan ba,ina ruwan ka dani?..ina dama cewa kayi na fita a damuwar ka?cike da bacin rai nace tokaje kayi partyn Asad,kayi duk yadda kaso i…dont… care anymore
“Zaka yi saurin fahmtar cewa Baiji dadin cewa hakan danayi ba dan Idanun shi take sukayi ja sai yji yarasa me ke masa dadi a hankli ya dube ni yace “nadra U dont care?..nace eh…yace toh why r u crying meyasa hakan yake ci miki rai nadra… A hatsale nace ina ruwan ka? nima bansani ba,kai da kasani mekayi?..
look ni daki fa zanje kuma kana bata min lokaci
Ya tattaro nunfashin sa da kyar yace wait.. Naki na kulasa,da karfin sa ya tarkato ni jikin sa ya matse ni,hawaye na sauke a raunane ina jan nishi tun kafin na tsaida numfashi naji sautin muryansa cikin yanayin karkarwar da karayar zuciya yace”…nadrah,pls am sorry..ban barshi ya idar ba na fashe da wata misiliyar kuka mai taba imani, cikin kukan nace mishi nifa babu ruwa na kaje inda zakaje kawai..ina ruwa na da rayuwar ka?”besides who am i to u?just let me go ..i dont wanna fight u anymore.. im tired..
Langwamewa yyi Kamr xaimin kuka..duk jikin sa sai yyi sanyi,sai Ya juyo dani da sauri ya maida bayana jikin bango yana duban cikin idanuna..”my answers are right there in his eyes,yau Asad ya soma amincewa da cewa so na yakeyi kamar ya mutu..har kokari yake ya hada goshin sa danawa dan naga hakan a idanun shi amma sai naki sam na sauke kaina kasa na kau da kai..1
da kyar da fitina na bashi hadin kai sai dai ban barshi ya kalla cikin idanuna ba dan sosai na runtse su kuma naki na kalle shi sam sam…wani xaxxafan nishi yake saukewa a hankli,saukar dumin nunfashin sa akan fuskata na dada zautar da ni,nd with each strike sai nakejin ina dada samun bugun zuciya akan sa….amma da na tuna carmila wani shaukin kuka keci araina wanda ni kaina bansan dalilin sa ba
Kamar da gaske Asad ya maraice ya susuce ajikina muryan sa kalan tausayi cikin lallami yace…”Nace kiyi hakuri ko?..nifa ba fushi nake da ke ba ranar da wasa nake miki masifan duk dama ke kika bata min rai, nadra meyasa zaki tsane ta?,..bby..nadra meyasa bazaki fahimce ni bane akan wannan maganan?a hnkli Nace nidai ban tsane ta amma inde akan wancan yarinyar ne bazan fahimci komi ba Asad,she is ruining ur tots…u look like a coward in front of her.. kaga yadda ka dawo baka da tunani kuwa?…nasan ko partyn nan zakaje ne sabida ita ne..bai kula da yadda nayi maganan ba…wani rungumo ni jikin shi kawai yay dan ya dakatar da kukan dake so ya kufce min mai cike da damuwar sa
muryan sa a sarkfe har yana karyewa yace..baby shuuu, shuusshhhhhh,banfasa ba ya dada matso ni har kunne na yabi da lips dinsa ta inda vibe din sexy tone din nunfashin sa zai kashe min jiki na sosai…cike da tausayi sa lallami yace nadra idan dan carmilla ne xan je wajen xan gaya maki wallhy ban taba boye miki komi ba,amma am sure ba dan ita bane,im going there bcos its a party kuma na miki alkwari i wll do just as u say muddin kika bani goyon baya…i cant do this if ure sad..baxan iya ba..i hate when u act like this with me…kuma gaskiya ina so inje…so wll u me help me pls?
Kallo daya na masa na dauke ido,na maida kaina akasa na shiga goge sauran hawaye na…Shirun danayi masa tsawon minti 10 ina sauke ajiyayyun numfashi yasa ya fahinci amsar sa,is true nd clear to him that am weak,and very much in love with him..wani tausayi na ne ya mamaye ransa…ya dau lokaci yana sakawa yana warewa a kwalwalr shi game dani.
Shidai baya gane komai but He wished ba haka yake treating dina ba,dadin karawa da yau yaji aransa kamar he feel the same for me,yasan im going tru alot akan sa,tun da muka mallakin hankalin kanmu ya fahimci ko mama bata shan wahalan da nake sha akan sa..that makes him so emotional matsayi na a kullum karuwa yake a zuciyar sa amma bai sanda haka ba tukuna,ya lura bani da tacewa”is like i want to say no and yes at same time..da kyar ya danne abunda yakeji aransa ya shiga min wasan dole tun ina yi a fushi da kuka har sanda yasa na murmusa.
Daya ga hakan wani ajiyan zuciya ya sauke kamar an yaye mashi nauyi azuciyan sa gashi sam Yaki ya sake ni wai sai na amsa shi inba haka ba bai damu kowa yazo ya ganmu hakan ba..
Ganin zai bata min lokaci cikin harara nace mishi na amince din amma in ya yarda cewa ko minti 15 baxai dauka awajen patyn ba,ya karaiyaye min wuya a shagwabe cikin magiya yace 30min pls …nace nooo..ya rusuna har kasa kamar maraya yace 45minuts to..
nayi tsuka nace i said 15 kana kaiwa 45?yace in kara ne?to 1hr..na share shi..karar bude horn yasa muka farga its obvious kawu ne ya dawo so da sauri yaja ni muka wuce muka shiga gida inda muka ci karo da Mama a falour ita kadai hanunta dauke da remote tana sauya channel
Duka muka rusuna mu kayi gaisuwa ta amsa da fara’a ta,inata faman kare fuska ta dan karma taga alaman nayi kuka ko wani abu,asad daya lura da hakan sai ya kau da hanklin ta akan surutun banza har na sabule na haura sama na barsu batace min komi ba.
Ta waya muka karashe maganan na bashi damar zuwa akan 45min
Yamin alkwari Yana gida
Karfe 10 dai dai na daren ranar sai juyi nake ni kadai akan gado duk abun duniya ya dameni
Jim kadan naji saukar faint knck abakin kofa ta.
A firgit Na taso babua bata lokaci mentally thinking of who cud that be?ina budewa kuwa ya turo ni ciki muka mannu da wall alaman baison kowa ya ji motsin mu
Idanun mu muka xuba akan ma juna
Na dade da sumewa ina kallon dressing dinsa,shikuwa da alamn duk hankiln sa akan zaro idon dana keyi yake sai ya shiga sakar min murmushi mai taushi
“Bakin wandon jeans ne wanda ya dan zazzago ta kasa kadan tayi masa cas cas ya rike face cap fari kat to match da pure white naked cashmir shirt daya kama structun sa shi wanda ya dada bashi irrestible look
Na daga ido sai naga bakin leather jackect a kafadun sa ya rataye…wani kishin sa ya sa na sauke ido na dan dole nayi murmushin yake..,ajiyan zuciya shima yyi yana kallo na a hankli ya dago haba na ya kure min idanun sa,”.. Ganin shirun baxai kare ba gashi ni bana son kallon daya kemin din dan bakaramin kishin sa ne yake hauhawa na ba,” cikin dauriya na ce har xaka tafi?ya gyada kai cikin sanyin jiki zai shafa gefen fuskata na slowly na kau da kai ina tura sa gefe,”..nace Asad dan Allah kar ka dade..dan ya kaucar da yanayin yadda nayi maganan,a wasa ya dafe kirjin sa yace ok wify…
Na juyo cikin hararar wasa a baxata ya taho ya dora min kiss mai tsayi a goshi na har sanda na riko arms dinsa batare da na sani ba,ya dago ni queit seriously hey that…pulchtride.. will u take care?sai naji wani kunya da sanyi araina na dago a slow ina kallansa cikin sanyin jiki na gyada mashi kai..wani kiss din ya taho zai sake min na tura sa na ce Asad bana so…dariya yayi mai sauti yace ok 45min i promise…tun kafin nace bye ya juya ya fita da sauri abunsa..
Na dade a tsaye ina bin kofar da kallo cahn Cikin wani irin karayayyn yanayi mai mugun saka tsumayi da tsoro na koma bakin gadona,a sadade na sulale ina me jefa kaina tunani sai na lumshe ido na sosai ina sauke ajiyan zuciya da wasu irin dogayen numfashi…
Only Allah knows why,bana iya bacci in Asad yana waje yau cikin ikon Allah sai gashi wani irin bacci mai nauyi ya sure ni ban san ma inda nake ba.
Da shike ma in har satan fitan zaiyi ba hali ya dau mota a gida machine ya hau ya sauke sa akan titi sai wajen karfe goma da rabi ya isa
Wajen da nisa ga wani uban shiru daya ke ratsa ko ina cikin duhun daren dan kuwa gidajen dake anguwan na Sabuwar estate ne project din gwamnatin tarayya hasalima yanzu ne ake neman haya anan so babu wani alaman wulgawar mutane.
Tafiya yake shikadai akan titi iskan rairayin dare na busawa sanda ya kusa cin rabin titin angwan sannan ya shako bugun sautin loud rap music na tashi to sautin yy ta bi har ya kaisa wata kafurar Luxurious Flat666,daga gate ya nuna invitation dinsa bouncers dake kofa suka bashi hanya ya shiga ciki
Katon flat ne mai dauke da 4 bedroom da fankacecen palour mai dauke da kala kalan yan mata da yan maza kowa da nauin abun da yake yi duka duka basu fi su arbain ba ,browsing wajen yyi da idanun sa baiga fuskkan sani ko daya ba,but da shike ya saba zwa nite parties sai hakan bai dame sa
Straight up yace wuce counter wajen da ake serving chilled drinks,dama shi in yazo party ya riga ya saba bawai rawa yake yi ko taba mata ba,chan dungu yakan nema waje yayi zaman sa yyi ta bushe bushe yana korawa da soft drinks yana jin loud music na cika masa kunne…dai daikun ranaku ne zaka ga ya bada idanun sa abinci wajen kallon yan mata masu rawa duk dam tunda yake bai taba takawa ba..
Bar attendant ya katse masa tunani da mai za’a bashi?,da har zaiyi magana sai charaf ya hango noah na tun karaso sa sai ya juya kansa kamar be gansa Yace ma attendant ya sa masa normal drink,he is ok with that. Ba bata lokaci aka shiga hada mashi parry special,noah ya ji matukar dadi daya gan sa,sun gaisa ba yabo ba fallasa,gayu suna ta kallon sa cos duk basu yi tsammanin sugan sa so free and confident a night parties ba gashi dan musulmi.
Sunyi Sunyi ya shiga cikin su,yace ah’a,..har ya musu karyan kanshi ne ke bugawa shiyasa ma baxai sha komai ba.
Ba laifi suka bashi waje ya zauna shi daya a hankli yake shan drink dinsa inda babu abunda yake fado masa aransa sai ni kadai!
Wani fargaba yakeji wanda besan da ita ba,ya fi minti 20 a haka daga bisani yaji abun kamar naso ya dame sa,yau ko tabar ma baiyi tunanin sha ba sai ya fita waje ta gefe yayi dialling number ta,”bacci nake kan kwasa,wayar tay ringing sau biu tex ya tura da kalman
“Baby,Im missing you”..tun kan ya yanke hukuncin zai jiran reply sai ga su molly da carmila da rico nasty,tare da sauren wasu yan mata da yan maxa a schl din mu
Da wani irin kallo ta bishi,duk yadda ta so ta boye sirrin zuciyarta akan sa bai boyu ba,”Asad is more than handsome he is a beautiful guy da komin jiji da kan mace zata so ace shi nata ne,sun gaisa da kowa amma su carmila ko kallansa basuyi ba suka shiga ciki. Shima daga nan ya biyo bayan su..
Drink ya sake karba mai sanyi ya xauna waje guda yana bin duk wani motsin ta da ido ya lura yarinyar kamar bata san kanta ba in tagan shi,yau wata sexy short gown tasa farare kal cinyoyin ta duk awaje suna kuma dauke idanu,ga rigar ya manne da jikin ta ya bi shape dinta ba wani kwalliya ta tula ba amma sosai tayi kyau,”.. Partyn yayi dadi dan bakaramin rawa su molly da rico suke kwasa a dance floor suna tsalle kamar ba 5inches higheels ane akafar su,carmila ta kame agefe kusa da inda suke sunayi tana cherring dinsu amma ita bata motsa ba,ya dade yana satan kallon su duka har time ya tafi sosai baisani ba,anan kowa ya nemi waje yana hutawa ana playin cool background music a lokacin ne noah da yan kungiyar buccaners suka yi nasu show din, lips sinkers, comedians, akayi rawa,miming,ganstars clash..kamar wajen zai dage tsaban ihun dadi da dariya,da hakan ya faru sai noah ya fara bayanai akan abunda ya tara su cike da nuna farin cikin sa da schl ta bashi cikakken dama,toh tunda ya gama fadan hakan sai ya soma neman carmilla da magana cikin salo amma su biun sun san dawa sukeyi,da sunayi ana basarwa ana dariya ansan sun sha giya sosai ne,amma da abun yy tsamari sai carmila ta fara nuna bacin ranta,noah shima ya dau abun da zafi yace dama ba masoyan ka zalla zasu xo murnan cigaban ka ba,har da makiyan ka masu so suga abun da zai kashe su,ya nuna ta da yatsa yace basu gani ba?ai tsaban bakinciki da shi yasa carmilla ko rawa bata iyayi sai dai tasha drink dan kar ta shake ta mutu,carmila ta nuna taji haushi sosai,cikin bacin rai ta fara tuna masa rokon ta da yayi akan tazo partyn,noah ya cigaba da misbehaving yace ai shi ba dan Allah ya ce tazo ba,dama babu yadda xaici gaba bai kira makiyan sa sunyi witnessing ba,dama revenge is best served when chilled
a baxata ta watsa masa sauran drink din dake hannun ta a fuskan sa,tun kan ya dago wasu kattan gayu suka hyayako kanta kace wani abu waje ya rude da surutu,noah ya sa aka rufe door cike da barazana yana gwada musu asalin shi waye ne fiye da kowa awajen carmilla sai ta nuna ta tsorata sosai
“The buccaners confreternity dama kungiya ne na yan cult ko ince secret society da aka samo shi daga jikin national association of sea dogs wanda aka fi sani da suna the pyrates confranternity,in har kai dan kasar nigeria somhow one day dole zakaji ana cewa sune kungiyar secret cult na farko da aka kafa a nigeria tun 60s
2 crossed bones da anchor sune symbol din kungiyar,pyrates confratenity tana yaki ne akan nuna bambacin yare a tsakanin student (tribalism),sai bada karfi akan hadin kai ta hanyar patnership,Humanistic ideas,expiring convention da knigthood,Duk de da niyya mai kyau aka kafa secret societyn dan sosai suke taimaka ma dalibai
musamman a harkan karatun su,dan doka ne in kana cultism dn toh da grade mai kyau zaka na fitowa…
Daga nan Bayan wasu lokuta masu tsawo ne aka samu sirrai daga cikin kungiyar wanda suka baude suka ce grade din su baiyi musu yadda suke so ba,shine aka fara samun sabani inda masu kofarin suka rarrabu wasu suka bar pyrate sai suka kafa nasu Kungiyar mai suna the buccaners confreternity a shekaran 1972,wanda aynzu haka su aka fi sani da sunan national asociation of the sea lords,awasu wajejen kungiyar yawanci maza ne masu jini a jika suke tada shi..
Duk dama kusan abubuwa iri daya suke yi symbol ne kawai ya banbanta Buccaners dake sune kanana sai suka dauki skull da cutlass guda biyu da bones,dukan su biu suna amfani da kalar yellow,ja da baki,aynzu haka buccaners su suka dawo kishiya mafi girma ma uwar kijiyar su pyrates confraternity wani mutum mai suna babban bolaji carew shiya jagoran ce su a wancan lokacin.
Da noah ya gama fade faden sa by now yasan Abun fargaba ne wajen kowa ya san sh dan cult ne,duk dama is allowed to use the name in schl tunda ansan ba a akan zalunci da shan jini aka kafa ba sai akan karatu but hmmm na ciki na ciki.
Sai yau zaka gane cewa ba ilimmi ko baiwa ne yake sa wasu su ci exams ba,wani bin dalilin kenan daya sa noah yake fitowa da grade mai kyau a duk dama yakan shafi wata biu baizo aji ba.
On the other way round,acewar sa yau yaci nasara an basa daman kafa kungiyar a makarntn su wato exclusive law schl na marigold and azure”..yace burin shi ya gurfanan da duk wata wani mai ji dakan sa a makarntar har sai buccaners yayi karfi ya mamaye ko ina
a ynzun Wani kungiya ce tafi karfi in ba brain box club na carmilla ba?yace shiyasa dole yau zai fara da ita..kuma acikin daren nan zai nuna mata iyawar sa.1
Nan da nan Kowa ya tsorota fiye da tunanin mai tunani dan ko members ne na kungiyar sanye da bakaken kaya a zagaye da noah jikin su a murde sai wani bari suke2
To add to thy misery sai aka kashe wuta,” tuni ihu da panicks ya cika wajen dai daikun maxan da aka gayyato suna ta kokari wajen ceton ran yan mata ta hanyar fitar da su waje
Sosai hanklin asad ya tashi,kirjin sa na bugawa yasan dole carmilla ta shiga hannun su nd only god knws me xaayi mata anan,aikuwa ya kwala mata kira cikin ribibi ya yunkura zaije nemo ta,wani ne wanda bai sani ba ya finciko sa y ce dashi a’a kar yaje ya gudu kawai ya tafi gida abunsa…1
Asad yaji tsoro sai kawai ya hakran ya fito yana isa waje sai ga rico da molly sun nufosa suna kuka sai ya tambaye su ina carmilla?”..arikice rico tace dashi basu ganta ba kuma tana ciki Dan Allah ya taimaka musu .. tun kan ya sake magana ya ga sunbarshi sun bar wajen.,baiyi tunanin komi ba sai ya koma ciki,wajen yyi fayau kamar ba anan ake holewa ba,yyi tsam kirjin sa na bugu,kamar an tsakure sa yajiyo sautin ihun ta cikin raxana tana cewa some one help,..daga nan bai sake ji ba sai kakarin kuka alaman an toshe ma mutum baki,sautin yabi a slow daf wani corridor yaga wani na jan ta akasa tana fincikewa kamar yar tsana tana kukan fitan rai,tausayi sosai ya kama shi a take yaji wani azama ta zo mai..labewa yy dan yaga ina sauran suka shiga,har ya gane cewa shiri fa suke awani dakin alaman ko su kashe ta ko su tsafe ta..1
Ko tunanin kansa baiyi ba ya soma sakawa da warwarewan yadda xai ja hankalin wanda aka bashi gadin ta ya ceto ta,aikuwa da sauri ya hada idea inda ya shiga zirya dan ya ja hanklin sa,..
Dayayi hakan kuwa a saukake ya samu ya barta anan ya shiga farautar sa.
Wasan boya suka shiga yi da shi,gashi wasu mayukan adduna ne a hannun sa sai huci yake,da kyr ya masa wayo ya zaga ya taho inda take “carmilla ta zube a dukunne tana ta kuka har ya iso wajen ta bata dago ba”.. Daya taba kafadun ta a firgice ta tashi,ganin Asad ne yasa ta kara fashewa da kuka cikin yanayin kaduwa da raxana ta fado jikin sa ta wani kankame sa.
Hannun sa Bai iya taba ta ba”..Sorrry..kawai yace shima duk tsoro ya cika masa zuciya…zatayi magana yace mata shuhhhshh,hannun ta ya riko acikin sanda suna tafiya amma da kyar suka fice a gidan a guje ana binsu
Gudu sosai sukayi tana ta kuka basu tsaya ba amma tsaban dan ta nuna ta razana takanyi amai jifa jifa
Sun dau lokaci a haka inda Sukan su basu san ina suke shiga ba,jin kadan wani bakar honda ce kawarbbiya ta shiga gaban su a mugun firgice carmilla ta bankade shi ta shiga gaban car din tana roko agigice akan ya taimaker su,dattijo ne ya sha giyar sa sosai har kaman bai gane me suke cewa sai ya dauke sun dai suka bar wajen,duk yadda suka roke sa ya kaisu gida haka yaki fir ya kuma bisu da maganan banza..da kyar carmilla ta roke sa akan yakai su makaranta..bata dena hawaye ba duk jikin ta sai rawa yake,shikm yana shiru
Chan Asad ya dubi agogon sa its 2.45am na dare runtse ido kawai yay a nitse kamar bashi yaci gudu yanxun ba,fuskn su ta nuna ma watch men tare da masa karyan libry xasu je,wacht man bai wani bada ciwon kai ba dan yasan gobe da safe ranar exams ne maimuhmacci nan aka bude musu gate din libryn suka nifa ciki su biyun su..
Batare da sun ce ma juna komai ba suka samu waje suka zauna kowa na sauke ajiyan numfashi,”…minti talatin suka dauka ahaka,kafin ya dago ya kare mata kallo har yanxu hawaye ne ke bin kuncin ta,scnd biyu ya dauka yana karantar yanayin ta,kafin ya taro karfin hali ya dora hannun sa akan nata gently yace soryy..cikin wani yanayin weakness mai sa aji tausayi ta bude idon ta kalle shi sai ya dada cewa are u ok?..ta kau da kai ta gyada mishi kan a hankli,wani kukan ne ya kufce mata wanda ya bashi damar dawo wa kusa da ita cikin yanayin rarrshi
Yace,”its ok,..pls stop cryng..lumui tayi a hankli har ta fada jikin sa batace komi ba sai kukan takeyi tana sauke ajiya zucya
‘Pls calm down pls sai ya dago fuskan ta,bata iya hade ido da shi ba,ran shi ya kai makura wajen tausayin halin data ke ciki ayanzu
“Shi Tunani ma yake aganin sa inda ba dan iyaye sun tursasa tayi karatun dole ba da baxata shiga wannan halin ba..aynzu bai ganin laifin kowa sai na iyayen carmilla.
Yana kuwa sake ta ta sulale kasa zata fado so helpless yace carmilla its ok,cikin sauri ta girgiza mai kai cikin kuka tace is not ok,im scared,ni ba haka nake so nayi rayuwata ba,this isnt my life .
Ya taho xai dago ta ta mike zaune ta kife kanta akan gwiwon ta slowly tafara blaming mahaifin ta,tana cewa ta shiga uku ya zatayi ta iya shan gaban yan cult?…shidai asad shiru yyi yana jin ta tana ta maganganu anan har yakejin ashe asali carmilla medicine take so ta karanta ba law ba. .baice komi ba kuma bai taba ta ba dakan ta tayi shiru ta nitsu sosai,sai sannan ya xare Handwipe ya mika mata dan ta goge fuskan ta,tana karban kuwa ta goge tasss har da ce masa ta gode,ya sake tambayarta if she is ok,ta gyada kai,bata barshi ya bude baki ba ta riko hannun sa tana kallon cikin idanun sa,”tace thank u Asad,..ya dan gyada kai,first time dayaji ta kira sunan sa in a normal way cike da saukar da kai,”..tace ure a nice guy,thanks for helping me nd hearing me out,kasa aranka na yarda da kai kuma nasan baxaka fada ma kowa sirri na ba…sai ta dan yi shiru,chan ta dago ta kalle sa…”tace in fada maka wani abu?Asad yace hmm sai gyada kai..tana so tace i knw u love me to amma bataga alaman hakan a idanun sa ba sai ta saje tace i know u care about me,..kuma nima i feel the same..shi kam bai wani ji mamaki sosai ba da ta furta hakan,ganin yy still baice uffan ba sai ta matsa daga kusa da shi tace,na fahimce ka in baka yarda da hakan ba but i really do care, infact i like u …sai ta juyo ba kunya kadan ta shafo kirjin sa, erotically,,wani kallon daya watsa ma hannun nata yasa ta dauke da sauri sai ta fuske…”tace nasan kasan dalilin daya sa nake maka haka ko?yace ehm…tace ok im sorry again pls forgive me,kasan ba haka nake ba. .i admit ure doing so much for me,nasan badan ka damu dani ba yanzu hala da kana gida preparing for ur exams ko?….but i have to do what i have to do.. bansan cewa abun zai dawo hakan ba da banzo ba pls am sorry asad
“..Yace its ok ..kar ki damu..im here..ya dan dafa hannun ta cikin yanayin kallon juna she xpect long essay sai taji yace,”.. Im glad u care too,.bai sake cewa uffan ba Tayi murmushi mai ciwo mai kuma sace zuciya,a sace ya maido mata irin sa..
“Yace kisa aranki babu wani abun da zai same ki..naji wai ba akai karan su noah ko?but with me i assure u ure safe…hannun shi ta dada rikowa cikin shauki tana ta kallon yadda yake maganan a nitse,a slow ya fincike hannun sa yace,…so lets forget abt it and think abt tomorw..tace ok,’..gyara zama tayi kamar bata damu ba,can kuma kamar wanda ta saba da shi ta shiga gaya masa abubuwan data keyi arayuwan ta, tace ita baxata kwanta ba cos karfe hudu ne dai dai lokacin karatun ta
Asad yace shi baxai iya ba bacci yakeji,aikuwa kamar wacce take karantar zuciyar sa tace hanklin ka ya koma gida ko?yay shiru silenlty thinking of that
…murmushi tayi ta dafa kafadun sa tace sorry gashi zamu kwana anan,sai dai gobe after exams sai kaje gidan,u know u cant miss tmrw papers suna da muhimmanci sosai duk wanda bai rubuta ba zai iya samun prblem…eh kawai yace mata yayi shiru..yau sai gashi ita ta sake sosai tana masa hirraki most times yayi ta kallon ta yana tausaya mata aranshi,wani bangaren kuma mind dinsa yana gida,can dataga ba damuwar sa ita ba sai ta barshi anan taje ta hado coffe awani wajen cahn inda securityn su suke zama…1
Daga wajen ta murza wani kwaya ahannun ta ta jefa aciki ta shigo tana murmushi babu bata lokaci ta mika masa,shima babu musun ya karba yace thanks a tare suka zauna suna sha har suka kammala sai ta shiga dube duben littafan da zata duba ta barsa a xaune,anan yana zaune bai sani ba jim kadan bacci yayi awon gaba da shi,koda ya so ya tashi sai yaji wani kasala ta mamaye shi chan a cikin magagin bacci yaji kanshi shi kamar akan cinyarta tana shafa mai kai ahnkli cikin dada zulma sa cikin bacci mai dadi mai nauyi..5
Bangare na kuwa ban tashi farkawa ba sai 4am na duba waya ta naga miscall dinsa harda tex,sosai najidadi araina duk na dauka ko baima kai 45min din ma ne ya dawo ya samu ina ta bacci ba,i mentally scold myself akan haka,a duk tunani na asad yana dakin sa yana bacci.1
Bayi na shiga na wanke fuska na fito littafai na na baxa na fara Karatun gobe da safe
Har nayi sallar asuba na kimtsa kaina tunda nasan ba zuwa dakin sa zanyi ba so arnd 5.50am na shiga kirar layin sa sai dai shiru ban ji an daga ba Nikadai ina ta masifan laziness dinsa,hankalina bai tashi tashi ba sanda naga karfe 6:47 yayi amma babu asad babu alaman sa a gidan
Hakali na a mugun tashe na fito inata tambayar zulai,wani bin gani nake kamar ba gaskiya take fada ba kawai bataje ta duba san bane
Gaba saya sai naji kaina na sarawa kirji na na bugu,a duk yadda ban son na karya alkwarin mama haka na daure na kama hanyar dakin sa..
Allah ya so ni na kiraa zulai tamin rakiya aikuwa muna karyo kwana naga kawu tsaye da mama duk sunyi cirko cirko a tsakar dakin sacWanda yake a gyare alaman ya nuna asad din bai nan1
Tsoro ya kama ni sosai nace kar dai asad kwana yayi acan?hawayen bakin ciki da damuwa suka taso min amma haka na daure na sa fuska cike da ladabi na tsuguna na sake gaishe su,na lura ran kawu a matukar bace yake..’dan a masife ya ce min wai ina Asad yake?
A ina ya kwana,nazo nan neman sa
meyasa bai bude min kofar sa ba kuma meyasa bai sauko ya gaishe ni ba?
Cike da fargaba na fara i,i na murya na rawa kamar wanda zai tona min asirin tsananin tsoron dake tattare dani,na shiga magana kaina akasa,jiki na sai rawa yake slowly nace ma kawu,nima bansani ba amma inaga Hala Asad yayi fitar sauri ne,dan jarabwar mu karfe 7 ne.
Kawu yace in masa shiru,yasan karya nakeyi..ya juya kan mama yace ai dama ya fada asad yana fita agidan nan ta yadda yaso batare da izin kowa ba
Da alaman Mama ma ta rasa abun cewa ne, sai na daure na ce ma kawu lallai Asad yana schl na kakkaro karya masu kama hankli na masa
Kawu yana ta kallo na amma ko alaman yarda dani yau bai nuna a fuskan sa ba
Sai ma Ya rinka masifa kamar xai bugemu duka har da cewa in har shi ya haife asad to yau gaskiyar sa zai fito kuma sai ya gane kudan sa,yace min maza ki tashi akaiki makarnta shi asad kam ai da kafa ya yaje ko?jiki na a matukar muce na rusuna kai bance komai
Kawu ya barmu awajen ya fice a fusace,mama tana biye da shi a baya..a sanyaye nake saukowa step daga nan inaji kawu yana masifan cewa
“Har yar ni din nan zan kalle idanun sa ina masa karya?jikin shi ya bashi cewa Asad be kwana gida ba..he is pained really da ban fadi gaskiyar ba..masifa kawu yyi sosai dan ko mama bata samu damar cewa wani abu ba har ya fice..
Haka Naje schll inata dube dube kozan ganshi amma shiru,har na cire kunya na shiga tanbaye tambaye irin wasu masu yawan masa magana amma kowa sai yace bai gansa ba
Can Akayi anoucing exams starting Time kowa yazo ya xauna computer kowa na gaban sa,na juya yafi sau 110 ina kallon one empty seat na asad gashi babu mahalukin da baiya hall din..
Har lokaci yayi akace start kowa ya log in pasword aka dukufa
Amma Ni A adaddafe nake yin exams din sam bana cikin hayyaci na,ganin munci
Awa biu asad bai shigo ba ban iya daurewa ba na fara sauke hawaye a boye inayi ina gogewa dan kar na ja attention din kowa.
Su carmilla da kawayen ta ne a seat din gaba,ga fatima acan nesa kowa na abunda ya ke gaban nikuma ji nayi na kamar mutuwa zanyi yau inbanga asad ba..
..acan kuma Asad bai tashi farkawa ba
Sai washe gari karfe 9.57am,..tsintar kansa yyi awani dirty store room shikadai a kasan floor, dan karamin daki ne na tara tsofifin littafai duk rigar sa ya baci yayi dukun dukun da dattin korar dake wajen,a gigice ya duba agogon sa yaga time sai ya runtse ido”salati ya farayi tunowa da ko sallahn safiya baiyi ba,wani shegen nauyi da kansa yake masa yasa shi mikewa a daddafe,”..bude window yyi yagan sa schl atake sai ya tuno da exams”..ya sake kallon agogo 9.58am,cike da mamakiin abunda yake gani ayanzu ya dada runtse idanun sa
Tambayar kansa yake,ina ne nan? Shine yyi bacci haka Baiyi sallah ba,his examz 9.58 kenan saura minti 2 a fito? Har ya juyo zai bar wajen cikin sauri,sai kansa yayi hitting ya waigo a tsorace yace where is carmilla?….cud it yan cult din nan sun biyo su libryn jiya,shin ko sune suka aje shi anan?sai yace noo,ai doka bata basu da daman yin wani abu a schll ba,but wher is she?da kyr ya samo ma kansa nitsuwa ya warware kamar hanklin sa ba a tashe ba ya wuce massalaci ya wanke jikin sa yay sallah…
Banyi editing ba fatan kunyi hakri da errors
#it doesnt matter how deeply or truely u love someone,betrayal remain an inherant part of love.
#Arayuwa ga guji munafukin ka koda ciki daya kuka fito.
#hakama duk imanin ka da jin tausayin ka kaji tsoron me fuska biu
#tausayi imani ne amma at same time tausayi babban rauni ne da xai iya jefa ka yanayin dana sani a rayuwa..
#wani bin ba taurin zuciya ke sa mutum ya ke taurin kai ba,ah’a se dan mutum mugune,kuma sanin gaskiyar mutum sai Allahn daya halicce sa.
Asad Bai tashi anan masallaci ba sanda har aka kammala exams din aka fara fitowa..
Nikuwa Tunda na danna submit a system naji saukar wani bakin ciki da kuka mai zugi ya mamaye zuciya ta.4
Im angry,scared and very upset.
Sai Na rasa meye guda daya zan dauka akwalwata,”
..fushin kawu?koko fargaban abunda ya tsaida asad wanda har yasa shi kwana awaje kuma ya hana sa halartan wannan muhimmiyar jarabawan he is not even picking his calls in wani abu marar kyau ne ya same shi fa?…
“Hawaye na automatically suka fara saukowa anma dan kar naja attention sai na koma dayan hall din inda babu kowa na zube a seat na fashe da kuka..
All i can think abt is Asad,tsoro nakeji matuka bansan kukan nawa zaiyi min illa ba sanda naji numfashi na na neman daukewa ..1
Yah Subhallahi nadra?..isowar fatima wajen kenan ta iso garemi a a gurguje tana shirin tallafo fuskata nadra meya same ki?aikuwa kamar an kunna ni wasu xafafan hawayen ne suke dada tulowa tace meya faru?ina Asad,daga na bude baki zance wni abu sai taga numfashi na yana sarkafewa,tsorata tayi ta fita a rude ta dauko ruwan gora ta bani na karba na shanye ban rage ko kadan ba”..da shike she is also vulnerable sai ta fara hawayen itama a sanyeye cikin kuka Tace please whats wrong..nace babu komi fati karki daga hnklin ki,tace shine kike kuka?to ina Asad meyasa yy missing exams?
shrun mint 3 nayi ina tare hawaye cikin dauriya nace ” i dont knw..jiya yace min zai je buccaners party,acan ya kwana kuma har yanzu ban ganshi ba,he is not picking his call..na karashe cikin kuka..
Sosai hankalin fati ya tashi itama tayi salati sai ta dafo ni cikin rarrashi tana cewa inyi shiru za a same shi,”nace fatima Asad bai taba yin haka ba..i just wonder if he is ok…kukan dana barke da shi yasa itama ta kasa controling tears din ta rungumata tayi tana sassaita ni itama bata dena zubda hawayen ta ba
muna cikin wannan hali nan su carmilla suka gifta suka haura ofishin shugaban makarnta daga nan bayan wasu mintuna muka sake fara tsinkayo surutun su..
Lokacin har fatima tasa nadena hawayen nadanyi shiru ina sauke ajiyan zuciya,ihu da surutayyar sun ya sa fatima ta leka su ta window,aikuwa take naga ta sandare kamar wacce taga fatalwa,cikin mamaki na dube ta ina jiran naji tace wani abu dan araina nasa bai wuce ace ita da kawayen ta ne suke wannan surutun ba
Hannu naga fati tana min alaman nazo naga wani abu,cike da mamaki na taho na leka Carmilla na gani zaune akan cinyar noah suna wani tadi suna kwashewa da dariyar mugun ta,su molly da sauran abokan sa ne masu ihu.
“Automatically muka kalle juna da fatima,a tsandare ckin sanyin jiki muka bar wajen..
Fati sai ta kasa hakri muryan ta har na rawa tace min
“Arent this ppl worstest rival?…carmila da noah sun tsani juna,nadra ki gansu anan tare suna sharholiya,anya babu wani abu?kai i cannot believe this,atake sai naga ta daga wayarta flash din ta cire ta dinga daukar su hoto har sanda suka bace ma ganin mu..Nima nasha mamakin kam anma aynzu damuwa ta Asad ne,ina juyi fati taja hannu na tace yawwa nady zo muje nasan iyakan wayanda aka basu katin muje mu tambaye su ko sunga asad,da wuri nace mata to muje.
Anan masallaci ma asad a rude yake abubuwa dayawa na sa shi fargaba mikewa yy ya fito ya shiga tambayar student,ko sunga carmila?…aiko amsa bai gama samu ba ya hango ta a fizge ta riko hannun noah suna tsaga cikin student suna tafiyar su in group maxa da mata sun kai su takwas,masu kallon su suna kallo wayanda da chan suka san sirrin ko ajikin su..
Galala yyi da baki Asad ya sha mamaki matuka amma Baiyi tunanin komai ba ya taho agurguje ya shiga bin bayan su..
“carmilla…carmilla ya shiga kira not to laud but audible,yanaji yana gani su rico suka juyo suka kalle shi dan su sa ya tabbatar sunji shi amma sai suka dauke kansu,
carmila da noah ko juyi basuyi ba a a bazata sukaji mutum yasha gaban su..
Yace carmilla what happen?dint u hear me,ina kika je?r u alright?..
Wani Gyara tsayuwan ta tayi cike da yauki tana masa kallon kamar bata taba ganin sa ba a rayuwar ta.
Aranshi Yace what?
Sai Ya duba kudu da arewa duk dalibai ne da sukayi jarabawa kuma kusan a tare aka fito,daidaiku ne kawai basa nan anan…yadda aka gansu da yawa sun sa shi agaba kowa sai satan sa kunne da idanun sa yake ta wajen su.
Asad ya rasa gane Komai anan,sai suka basar da shi suka hau tafiyar sa,’..kamar a wasa haka ya bisu da kallo schl pavilion mai flat step guda goma sha takwas suka nifa akan steps din suka xazzauna inda daga su sai su,sannan dama nan point din kusan shine tsakiyar makaranta dan in ka tsaya awajen duk wanda zai shigo ya fita zaka gansa sannan daga kowani angle kaima za’a iya na ganinka
Nida fatima muka shiga tambayan dai daikun da aka bada invitation zuwa partyn da shike duk members din yan brainbox club ne da suna da jiji da kai da kyar wasu suke bamu attention din su..nidai duk wani girman kan da shan qamshi bai dameni ba amsar da muka samo shiya ya dada rudar min da tunani
“Most of them said basu lura da shi ba,wasu sukace ai tun karfe 11 aka watse, ai partyn bai dauki lokaci ba sai dai in Asad din ne yay wani waje..
A hankli fatima ta riko hannu na muna tafiya tana calming dina,”..nan ne muka ci karo da usher sai na sake tambayar sa ko yaga Asad acan?…shikam babu ruwan sa but cewa yy baisani ba dan baije ba”.. Amma naje pavillion yaga su noah anan intambaye shi mana
Araina nace haka ne fa?..noahn ne ya dace na fara tuhuma but i just dont knw why gaba daya bana kaunar dabiun yaron,muna tafiya pavilion ina ta tunani,cike da jan kafa muke takawa kamar marayu toh ta bayan pavilion din muka billo tun bamu haura ba kunne na ya tsinkayo min muryan Asad…
Ban yarda da hakan ba sanda na sake jin shi da dan karfi,cikin yanayi mai fixga na buge hannun fatima na karasa isa wajen,nan idanuna suka nuna min su carmilla a yadda dazu muka gansu noah ne shi kadai,ita kuma carmilla ta dan sauka akan step din kadan ta tsaye agaban Asad suna magana..
kallo Daya na musu duka bance da su uffan ba na karasa wajen su asad din,shi yana kasa bai ko saka kafarsa kan step din pavilion din ba carmillan ce agaban sa fuskan ta a mugun daure..
Ban lura da yanayin sa ba amma na gane isowa ta ne yasa Maganan nasu ya tsaya chak,Asad ya bini da wani irin kallo mai ban tausayi,”..reaction din da ya bada a idanun sa can tell he is feeling helpless,ya lura nayi fayau yasan hankali na ya tashi sosai
Kasa cemin komai yyi ya dauke idon sa sai na dada matsowa ta gaban sa tsaban takaici da rudewa murya na ma na rawa na budi baki zan yi magana,haushin yanayin mu yasa carmila ta dakatar damu,sai ji nayi an daka mana tsawa”..
Hey,i dont have time for this ok?..kai kuma ba so kake kasan abunda ya faru ba?…Sai ta juya sarcastically cikin gwalewa tace ma abokanan ta
“su kalle dump crush dinta wanda jiya ta sa shi bacci a kasa cikin datti,wanda tsaban yana son ta bazai iya rayuwa babu ita ba ya fada trap din ta,harara ta watsa mai tace”alwys ready to give ur life huh?..
Nikaina Ban taba ganin Asad ya bata rai fiye dana yau ba fuskan sa a mugun harde yace Carmilla r u insane, whats all this?
..tace nothing kawai ina tuna musu ne dan tun dazu nake basu labarin yadda na maida ka wawa jiya daga wajen party har a libry…
“Wani lumshe ido yyi yana Sosa keyan kansa,ransa a murtuke yyi furzar iska Yace wawa?…
Cikin yanayin dakewa da karfin hali tayi rolling eyes Tace e,ko baka yarda ba ne?..sai yay shiru mamakin ta sosai ya cika shi sai yaga idanun ta a bushe suke babu alaman nauyi ko kunya…
Tace nice carmilla campbells obasi,..wacce babu kama ta mkarntan nan…kayi tunanin yin wasa da abunda yafi komi muhimmanci arayuwata,shiyasa dole na nuna maka ni wacece ta hanya mafi tsauri,Asad kana da raini,ka rufe idanun ka ka kasa gane nice makarantar nan in babu ni babu wannan makarantar3
The buccaners ko ince noah,”..ta nuna shi daga nesa,tace duk a karkashi na suke..kasa aranka Babu wani club sai na carmilla….
“Last term ka zarce ni sosai,har kakejin bazan taba kamo ka bako?yes na yarda baxan kama inda ka kai ba..but my friend
In akuya baizo dakan sa ba igiya ake sawa a wuyar sa a ja shi da karfi har sai ya gurfana
Duk abunda ya faru daga ranar da ka cinye ni a gasar freedom and slvery a kotu,duk abun da nace maka akaina da wanda na fada akan su noah ba gaskiya bane,evrythg is all planned,perfectly..
badan ana tsoron ka ba sai dan a gurfanar da kai..
Nasha gaya maka Ni ba abota ko soyayya ya kawo ni ba amma baka ji ni ba” this is war mr Asad,”i wll be the best,and remain the best in na shiga ranka sorry ni nayi amfani da kai ne kawai dan cimma burina kuma Burin iyaye na ko a wuta yake ni zan cika shi.
Ni baruwana,So if u want ka yafe ma noah nina saka tunda ka nuna zaucewar ka akaina har ta hanyar kusa sadaukar da ranka dan ka taimake ni,ai na baka
Coffe mai dadi ko?toh kayi baccin da zai kankare tarihin sakamkon ka agaban idanuna kenan,im happy u missed this papers,…dont forget nice makarantar..i have alot of ways in bakayi hankli ba xakaa bata sosai da ni….
Ganin mun kafe ta ido muna sauraron ta witout any reaction sai Itama tayi shiru,”
….chan na share hawaye na kamo hannun sa muka koma gefe kadan hawayen sun kasa dena sauko min a raunane cikin rudani nace da shi Asad meya faru ne?ban gane abunda take fada ba..a ina ka kwana?why u looking dirty kidnaping dinka tayi dan kar ka rubuta exams din?jin yadda murya na ke rawa sai yyi saurin rufe baki na da palms dinsa ya girgixa min kai,yaga yadda duk jiki na yake kyarma da alama idanuna sun rife alaman raina a mugun dagule yake”…cikin idanuna ya saka nashi dan na fahimce shi, just now i notice how confused nd angry he look. sai yana jin baxai iya daurewa ba kawai sai ya shiga gaya min duk duka abunda ya faru tsakanin sa da carmilla game da partyn har izuwa yanzu ko tari bai boye min ba,tsaf ya warware min komi cikin fayyace ce min nufin ta na cewa ta hada kanta da su noah ne dan su zulma shi..Yace in har bai rubuta wayyanan exams din ba carmilla ne zata haye,..kuma akan dalilin haka tayi amfani da tausayi na akanta ta cimma burin ta..
Ina faman hawaye Wani gulluton bakin ciki ne yaso yayi chocking dina,araina nace wannan wani irin dabbanci ne? i just tot how cruel she can be akan karatun banza,lahira zata je dashi ne?did she even need to go this far to be the best,?da wani abu ya same Asad fa?…zuciyata sosai ta harzuka ta makance na kasa danne fushi na idanuna a rufe na bangaje shi na koma inda take tsaye tana kallon mu,”i knw she heard evrtyng duk abunda ya fada min sunaji sarai tunda baifi taku biyu ne a tsakin mu ba,”..a zuciye na share hawayena agaban ta ita kuwa tsaban tana jin ta isa sai ta kalle ni kallon walakanci,na dube idanun ta a hankli na furta”how dare you..?tamin shiru Bata amsa ba sai taja min tsuka,” warware hannaye na nayi cikin borin mahaukata na jawo ta kasa kusa dani da karfi kuma a wulakance kafin ta hankaro ta dago na shiga kikikfa mata maruka masu xafi masu kara ta ko ina har sau ba ba adadi”..jefa ta nayi ta fado jikin yan uwanta da suka taso yuuu sukayi kanmu,Asad shima ya riko ni yana calming dina lokacin sai naji kuka gaba daya ya dauke chak a idanuna”wani tsawa na dakaa mata nace how dare you?answer me…har yanzu layi take its seeem like marukan dana bata ne Basu gama sake ta ba dan ba karamin gigita tayi ba,”a xuciye na ficke hannuna daga na Asad,na shiga ihu ina xagin ta nace mata wannan abun kunyar ta aikata?ina ilimi anan?yanxun Dame take tinkaho?3
nan ta dago a gigice tana ture mutanen ajikin ta Asalin hawayen razana da na borin kishi da tsana suke zirya akan fuskn ta tana huci kamr zata shide,”a hatsale tace mun,bitch u slpd me,u slap me?u slapped me..how dare u?ta wani hayayyako ahaukace zata kawo hannnu sai matan suka jawo ta baya, kokawa ta shiga yi da su,tana cewa sai ta mare ni..ina tsaye kyam ina lura da borin da takeyi asad duk sai ya rasa abun da zaiyi da mu .”surutun mu duk shi ya kaure wajen bakaken maganganu masu dagargaja kimar mutum nake yaba mata akan abun da tayin ban damu ba..and im right shiyasa abun yake cixon brain dinta take dada fita hanklin ta”Asad is her karma..kuma har abada tasan baxata iya da shi ba sai in de cutar sa zatayi,”nayi kokri sosai wajen nuna mata yarinta da kaskanta akan abunda sukayi
Wel not all men who act gentle with girls are flirty some mothers raised thier son’s well,nace ta dena rudin kanta akan asad,na nuna mata babu wani abu aran asad game da ita illa tausayi
.. ..anan kusan rabin dalibai suka fara xuwa inda muke dan bawanda baya jin hayaniyar da muka bude…
Carmilla tace lallai asake ta tayi min dukan tsiya tana so taga waye ubana a doron kasar nan,..tace sai ta sa an korani a schl din sai ta wulakantani,nace da ita bata isa na ni nafi karfin ta..
Tace bansan ta ba,to bari ta gaya min ko shugaban makarntar nan a karksshn ta yake,infact tayi cutar,ai baxamu iya kai kara ko mudau mataki ba dan shima shugabn schl din yana da hannu akan haka,da sannun sa aka hada course masu nauyi a rana daya dan su sauke asad…
Ni Ban ko sha mamakin haka ba,dama biri yayi kama da mutum Dada matsawa nayi gaban su Asad yana jawo ni naki sam nace to naji sai taje tayi duk abunda zatayi”nikuwa sai na hallaka ta..
Sai Tace zan hallaka ta?
A zuciye nace eh..i will sure be the end of u..
Nace mata marar hankali,jaka karuwa,har jikin ta nasan zata bada dan ta cimma burin ta…dan na dada cuda mata kunci nace who knws in shugaban makatntar ba dadiron ta bane.
Nan tayi wani kukan kura ta kufce ta nufo ni,da zara zaran farcun ta ta kwarzana min gefen wuya,nayi sauri na riko hanneyn duka biu na wanka mata mari,wani mumunan fada ne ya kaure inda nayi nasaran mata shegen duka na jajja suman kanta na zana mata fuska da wuya da duk inda hannu na yakai ajikin ta,almost blue black with so much agression..ana janye ni ana janye ta .2
Da kyar da fitina fatima da Asad suka raba ni da ita,sai kuka take tana amai jikin ta duk na rawa…Asad sai kallon ta yake yi yana jiyo abubuwan data ke furtawa
“Is not my fault i have to do this an i wll do this,sai dai in zaki hallaka ni..
Niko a duk sanda tace hakan nakan jadadda mata sai na hallaka ta akan Asad…altho am saying it furiously and seriously amma cikin raina so nake
Taji aranta nima zan iya fiye da abunda tayi ma burin ta akan Asad.
Har muka bar wajen ba dena diri ba,gashi student kowa yay witnessing wanda basa nan ma duk an shafa musu.But in abu ya shafe su carmilla ne ansan schl authority bata cewa komi akai.
Acikin dalibai in banda fatima Babu wanda yasan asalin kan labarin,kowa dai ya bari akan Asad muke fada.
Sannan carmilla is figthing to be the best,nikuma am fighting for ma brother wasu suce boyfriend…har yau de ba asan matsaya ba sabida masu cewa ni budurwan sa ne sukan kafa hujja da cewa ai anga sunana nadra mahmud ne,nashi kuma asad zain abdulshakur,.so akwai bambanci.
Ranar sai bamuje gida akan lokaci ba sabida ba adede duka muke ba
Inata kukan zuci,driver aka turo sai asad ya karbe motar ya sallame shi,tafiya mukayi mai nisa chan ya kashe motar a gefen titi ya paker baice min uffan ba ya lunshe ido yyi nitso cikin tunani
kusan bayan awa guda sanda hankalinsa ya dawo jikin sa ya juyo ciki a muce ya sa hannu zai jawo ni jikin sa,a hatsale na fincike cikin masifa nace kar ya taba ni?
Xaimin fuskn tausayi na rufe idanu na naki sam daya dame ni sai tas na sauke fushi na akan fuskan sa da mari,kansa ya sauke min kamar maraya,sai da na karkare masa duk abunda ke cina arai sannan na soma masa kuka2
Nace daman nasani carmilan nan ba mutumiyar kirki bace,munafuka ce amma asad ka nace mata wai kana jin tausayi,ka rufe idanun ka gashi tasamu dama tana wasa da mutuncin ka.
Na gaya masa halin da muke ciki da kawu da mama akan rashin dawowar nace da shi banji dadin yadda kawu ya furta cewa inayi masa karya ba,kuma duk akan sa nakeyi meyasa bai saurare ni ya rabu da carmilan tun farko ba..
To top it,its been long na loosing temper na a bainar jamaa har inyi fada da zage zage,abun ya kassara min zuciya..kukan nayi ta mishi banyi shiru ba sanda na sa ya gane hakan sosai aransa
“Hanklin sa sosai
Ya tashi,kamar xai fitar da ransa yake bani hakuri yana cewa dan Allah in saurare shi..
Naki sam,sabida kaina ba adai dai yake ba..daya lura da hakan sai ya hakura..sai dai har muka isa gida cemin yake koma yaya ne bai kamata ince xan hallaka carmila ba..
We r lawyers,i knw wht he meant by that….amma sai ban damu ba fushi ya riga ya rufe mun ido sai nake ganin hala yauma ko zaice ba laifin ta bane still amma bai fada ba sai can da yamma sosai muka isa gida,ba wanda ya kalle mu bare ya kulamu haka muka zauna a dodane har kawu ya dawo ya aika aka kirawo mu
Anan Asad yasha balbalin kata’i,sama da kasa kawu sanda ya birkita masa zuciya da maganganu,shidai baice komi ba..anma duk dama yau banajin karfin gwiwa haka na daure dan na taya Asad kare kanshi wajen kawu
..sai dai Duk abanza dan da muka ki sam mu fadi gaskiya mu amshi laifin mu agaban kawu sai ya zamto ko mama bata son amsa gaisuwar asad ayanzu..
Kawu sosai ya hada dani cikin fushin nasa,nima a wuya yake amsani kwata kwata baima san kallo na sau biu
Dan aransa ya qudira cewa lallai asad bai kwana agida ranan ba mukuma munce lallai da asubahi ya fita.
Asad ya biye min a haka amma bai cika tsawaita maganan ba, Na lura dannewa yakeyi nikaina nasan in yyi zuciya zai iya fitar da abunda ke ransa game da kawu..na masa fada na nuna masa koma meye ne ai laifin sa ne don haka Sabida ni sai yaja bakin sa yyi shiru..
Haka muke zuwa schl mu dawo cikin wannan yanayi
karshen ta ma Asad sai ya dena rubuta komi a paper sa sai dai yayi submiting blank in mun fito yace min baijin yi ne2
“Raina na baci matuka akan haka..all i can think is carmilla…gani nake kamar akan abun da tayi yasa yake kin rubuta jarabawan..
Da na ishe shi da complain,sai ya nuna min ransa ya baci,ni bansani ba ashe Asad shi kansa ba adai dai yake ba,aynz damuwar camilar ma kwata kwata ba shike gaban saba yadda iyayen sa suka dau abun da zafi shiya ke taba shi..zuciyar sa a cunkushe yake kuma ba don ya so ba yace min nadra ya isa haka, bana son kisake shiga maganan nan bare har kisa ke cewa xaki hallaka rai akaina ya dada jaddawa yace bana so..daga yau ma ya sawwake min kar na sake shiga tsab gar shi da carmilla na barshi shi yasan matakin da zai dauka akan ta…he sai he does not need me on that..aikuwa na hau dokin zuciya”..
Ranar na dade ina yi ma kaina fada akan nuna damuwa ta akan Asad..i just feel i shud let him be tunda dagaske ya nuna min bai bukata ta akan haka..”nayi iya kokari akan haka amma nakasa,wahala sosai nake sha wajen dauke idanu na akan abubuwan dayakeyi da rayuwar sa ayanzu sabida ina matukar kaunar sa.2
Ban taba lura ba shima Ba san ransa ba yake nuna kamar bai damu da turani ajikin shi dayayi ba shi sam baison wani abu yaje ya sameni ne.
Da kyar na daure musamman dana ga ya fiye shiru ya kuma kara kaimin shan cigarete dan ya korani jikin sa
finally i controlled my self da kyar na kau da idanu na wajen kin ce masa komi har muka dawo muna rayuwar mu normal
Yau ana saura kwana daya a kammala jarabawa kuma hutu mai dan tsayi xamuje kafin mu dawo scnd year kuma shine final year din mu tsakanina da carmilla babu ko ga maciji,sau dayawa muna cin karo,Asad sai ya dauke kansa ya hade ransa bai ko kallon su ni da nake kallon sun kuma basa iya kallo na
Gulman mu ba inda bai xaga ba..
Tun ranan carmilla Sai ta rika yin abu sanyi sanyi tana lagwas kamar munafuka”..some said she is ashamed of what i did to her..awajen Asad kuma fassarar hakan daban take aransa altho aransan ya riga ya gama kitsa hanyar da zai koya mata hankli,by now aransa kamar ya fahince cewa yarinyar son shi takeyi…
Ranar da muka kammala jarabawa da wuri na fito na same shi abakin kofa yana jirana,i knew har yau baya rubuta komi,fade smiles ya sakar min sai na mayar masa ya amshi hannu na na sako muka fara tafiya
Anan bayan fatima da mukayi wa sallama bamu sake kula kowa ba muka nufi inda muka aje namu motar mu..Muna kaiwa gaban mota Asad ya bude min na shiga cikin kankanin lokaci ya jamu muka bar schl,bayan tafiyar mu a sadade carmilla ta fito acan gaba da jikin wani mota da yake yawan boye ta ko ince rufa mata asiri in ta labe kullum dan ta kalle mu+
..anan har muka muka mule muka bar haraban schl din tana rakube tana sauke ajiyan zuwa cikin tashin hankalin da har yau bata same saukin sa ba4
Yadda ta runtse ido tayi kasakai Allah kadai yasan yadda take ji aranta,cigaba da sauke raunannun hawayen ta takeyi tana gogewa can ta matsa gefe ta jingine kanta akan motar tsawon mintina biyar sannan ta wanye a sace ta koma cikin kawayen ta..
Wani kallo suke binta dashi amma babu wanda yace da ita uffan har ta same waje ta zauna,Su kansu yanzu mamakin ta suke sha a kullum carmilla sai taje fitsari,odd hrs amma ba wanda ya lura da cewa hankalin ta a matukar tashe yake akan Asad ga wani mumumnan kishin da yake so ya hallaka ta a kullum in ta kalle fuskta a kusa da shi.4
Mukuwa Komawar mu gida muka samu kawu ya bada aiki ana ta gyaran boys qtrs ana kwaskwware shi.
..yau munyi wata muna jarabawan amma kawu bai sake amsa gaisuwar asad ba kwata kwata baya ma duban inda yake kuma a kullum sai ya daga ma mama hankali da surutai akan ance masa kaza ance masa kaza.. gwara ni ma cewa yayi zai rabani da asad dan ya ga asad bata ni kawai xaiyi.. Dani da asad tun muna damuwa akan maganganun kawu har muka zo muka saba…
Ayanzu Kawu ko mama baifiye sake mata fuska sosai ba shiyasa ma duk abubuwan da ke faruwa abayan fage
Bamu sani ba
Daga ni har Asad din bamu san waye bane,amma tabbas a wani wajen ana gaya ma kawu wani abu game da halayen asad,A wani reaction dinsan nakan fahince cewa da alama shugaban makantar mu ya kira kawu kuma sun tattauna akan Asad.
Sede kullum tunani nake,in har angaya ma kawu asad na shan taba nasan bazaiyi shiru yayi mita ba sai dai ya dau mataki,kuma inda an gaya ma kawu matsalar asad da camirlla shima nasan kawu bazaiyi shiru akai ba,but the way he talks now is alarming,kullum sai yace zai dau mataki akan mu..sabida bama ji
bayan kwana sha hudu da hutun ranar muna xaune a falon mama ina ta takura ta akan maganan bata wani kula ba sai Cewa kawai tayi ai a schl din mu ance ma kawu asad yana satan fita agidan nan kuma an gaya masa yana zuwa partyn dare…dana ji hakan sai naji hankli na bai wani tashi ba Nayi shiru Can mama tace jeki ki kiramin shi..tun kan na karasa tashi sai gashi nan ya fito yana saukowa da waya a hannn shi cikin sanar da mama cewa azaad ne ke son yin magana da ita
Ba musu Mama ta karbe wayan sai ta dan katse, tace asad dama ina son ganin ka,har zai zauna tace a’ah Ba sai ka xauna ba.
Baban ka ne yace ka tattara kayan ka duka ka koma chan inda aka gyara Wato bq,ya kuma ce baison ya dawo cikin gidan nan ya same ka.
Atake na dago na kalle mama Abun ya matukar bani mamaki,me knan kawu yake shirin yi wa asad?sam bansan abun har yakai akore asad acikin gida akaishi boys gtrs shi daya ba,na sauke idanuna tare da dan karamin salati nayi tsam ina sauraran bugawar zuciya ta..
Asad kam dadi kashe shi,ji yyi kamar ance ya shiga aljanna da dunguren kule dama shi sosai ya gaji,yayi matukar gajiya da yanayin zaman sa acikin gidan da su…da wuri ya amsa hakan ya kuma roke mama alfarman ta kyale ni in taya shi parking ayanzu yaxun nan
Ba tare da sakin fuska ba mama ta kalle yanayin sa cikin takaicin abunda yake faruwa tsakanin sa da kawu ita kanta tasan shiryayyen al’amari ne kawai zaisa kawu ya kore asad ya aje shi shikadai,”who knws amma jkin ta yana bata cewa lallai kawu so yake ya kama asad da hannun shi sannan ya fitar da wutan dake cinsa a ransa,,
“she just felt like Asad bai jin magana ne Taurin kai ne akansa wanda dole sai ta seta shi…da kyar ta bude baki ma ta amsa shi amma ko ajikin sa,sai yama bar mata wayar ya kirani yace muje ciki nikuma sai na kira zulai sai muka haura ciki tare…
Haka zulai taci aikin jigila da kayan mukam ba abunda muke tabukawa sai muhawwa akan hakan..
Asad yace wallhy hakan yafi mashi dan baiga amfanin zaman sa cikin gidan ba..nace kawu yyi haka ne dan ya kure ka…nide shawarata ka dagatar da duk wani abunda kakeyi kodan ka wanke kanka a zargi
Asad Yace min ya sani amma still shi rayuwar sa a hakan ya fi mashi..haka har mukayi shiru muka shiga fitowa da wasu kayan bai rusuna ba
Mama kuwa ta dade tana amsa wayar Azaad,ina lura kallo daya Asad yayi ma yanayin ta bai sake kulawa ba…aransa gani yake kamar duk wani so da daraja akan azad aka dora anma bandashi
After 2 hrs of parking wajen sa
Yyi kyau sosai,1 bedroom ne da kitchen da dan karamin palour mai dauke da kujera dogaye guda biyu da kayan kidan sa da tv na kallo.
Ban wani dade anan ba na koma cikin gida dan nasan zaiyi wuya abarni har abada ina zuwa tanan,who knows hakan yana daya daga cikin luggar kawu hala so yake ya raba ni da Asad dan sosai ya sa wani abu aransa game da karyan da mukayi masa ranar
Bangaren carmilla kuwa abubuwa sun faskara,ji takeyi kamar xata haukace dan babu kwanciyar hankali aranta sam sam…kullum takan kwanta sai tayi ta tunani mai zurfi
“yes gashi dai tayi game din kuma taci nasara ta dawo da martaba da farin cikin mahaifin ta kuma tun a lokacin aka sake bata dukan wani dama a gida,ayanzu baifi saura kawai result ya fito bane abata har da wittelbach din ta..
Sai dai bata jin dadin komi iyanzu
hasalima bata wani ci bare sha kuma in ta tuno Asad bata iya dena sauke hawayen da bata san ma’anan su ba
Har cikin ranta tasan asad yafi karfin su result din sa na farko ba ita kadai ta tsorata ba ko shugaban makrnta yace carmilla baxata iya kamo asad ta sauki ba,shi ilimin sa baiwa ne daga Allah,duk da itama tana da baiwar amma kowa yasan naci da buri shiyafa yawa..Asali tsoron hakan yasa ta amince xata buga wannan game dn akansa amma deep within her heart bata so ba
..gashi alokacin mahaifin har kudi ya saka yace ma shugaban makartar su a tabbata hakan ya faru..Shikansa shugaban makarntar a kasar mr campbells yake karban oders kawai de basu barin kowa yasan dahakan ne,wani bin tare suke munafurcin su,kusan duk abunda suke aikatawa na ashahha da rayuwakan mutane shugaban makarnta yana sane…
Shiyasa ya taimaka ma carmilla ya kuma sa hannu su noah suka shiga abun da sunan wani kungiya,kuma aka chakuda exams dan aja asad baya ta inda carmila xata farfado.
Wani Wirgi da pillown ta tayi cikin tsumayi tana tuno duk kalaman cin mutunci da yaudara data gaya masa ranar,take ruwa suka cike idanun ta tayi wani fillo da kafafun ta tana jiyo radadin zafin duk abunda ya faru,tambayar kanta take ko anya kuwa asad xai sake yarda da ita har abada?duk da yadda take mishi amma he gave her too much freedom,dukan tausayin sa,da kuma yardan sa, ko ba dan abunda tayi wa asad ba yadda ta xautar da kanta tayi ta amfani da fuska biu is driving her go nuts,kamar zata haukace haka take jin zafin abun aranta1
Kuka mai ban tausayi ta fashe da shi Gashi tana jin matukar kaunar sa har cikin jinin ta,a yadda take jin tsananin kishi akaina kwana biun nan yasa aynzu kam bata musu da zuciyarta ta amince da son shi take kamar ta mutu.
Bangaren Asad kuwa tunda na nace mishi da nasiha akan ya dena fita ko ina,sai naga ba laifi yana taka tsantsan duk dama kawu bai bada daman arika saka mashi abinci ba,mama ce ta dauki risk din kullum xata sa zulai ta kai masa cooler.2
Anan shikadai Zaiyi sharholiyar sa hakan kuma bai hanashi jin kewar mu ba,wani bin yakan zauna a falon sa yayi shiru aransa yana ta tunanin rayuwa,babu tantama he misses me alot har aranshi yakasa amincewa da cewa yau munyi kwana biyu a gida daya amma bai ganni ba ban ganshi ba,murya ta ma sai munyi waya kuma ahakan ya lura a takure nake amsa shi most time sai dare muke sakewa.
Aransa He realy hate that, Da kyar ya saba da haka nima hakan nayi hakri na kama kai na sosai
“Sabida rashi nan He do felt Alone,so lonely dan a duniyar sa nikadaice abun alfaharin sa…’ji yake kamar a duk halin dayake ciki a duniya komin munin sa nice kawai zan zamto madogaran sa..amma dayaga abun zai dame sa sosai sai ya tsaida akalar sa waje guda,tun bayan rabuwar mu a schl bai sake tuna carmilla ba sai yau,daya huce da har yace zai shareta kawai yayi rayuwar sa,but righ now dayakejin kamar akanta ne aka tsame shi a gida kuma aka rabani da shi sai yake ganin bazai iya barin taci dashi haka abanza ba..
Aikuwa nan da nan ya shiga tsara plans a brain dinshi,smart plans,wanda mafarin cin nasarar yuwuwar sa shine bincike akan rayuwar makiyan sa…
Daga nan Komi ya aje agefe ya shiga bibiyar tarihi da labarin campbells obasi,his life,his rules and his entire mansion life,duk da tulin tsaro da gidan ke fama dashi amma a cikin kankanin lokaci asad ya samu komi a hannun sa,sosai yayi amfani da ilimi,kyau da wayewar sa dan kuwa shi bakaramin tantirii bane in har ya xamto masa dole ya sa abu agaban sa,naturally he is soo unserious but if he is serious to bamai iyawa da shi..
a yanzu babu wani karya da gaskiyar campbells da baya bibiya har abokai yake da shi acikin ma’aikatan mansion dinsu most espicially blessing wacce babu abunda bata sani akan carmilla ba,but nobody really knw how he did it..most time yana gida za’a bashi kanun labarai wanda babu karya acikin ta.
By now ya fahince abubuwa dayawa game da carmilla wanda da da chan bai sani ba, wani bin har Abun na thrilling dinsa,aranshi ya kanji he just cant wait to deal with her…he dont really care anymore.4
Sau dayawa in munyi waya yakan so ya gaya min qudirin sa amma daya tuna tsana dake cikin relationship dina da carmila sai ya kaucar,yasan in ya kawo maganan ta zanyi fushi,and fushin nawa shine abu na karshe da zaiso ya gani a duniyar sa…
Shi Tun da wannan lamari ya afku dayayi tunani sai yakeji aransa babu masoyiyar sa a duniya kamar ni
But He dosnt wanna admit yet,amma aransa sosai yakejin kaunata kuma ya yadda da hakan bvu tantama
Wani bin har imagining yake cewa gani nan da shi muna rayuwa mai cike da sakewa da jin dadi yakan zurfafa ya lume har yayi bacci
Awajena ma kusan kullum haka ne,i missed him har Allah Allah nake mama tace inje in kirasa wata rana amma kullum zulai ake aikawa,da kyar sai in asad din yaga dama ya shigo sai mu gaisa,sosai aka samana ido da ko sakewa muyi hira bamu samun daman yi agaban su mama
Haka raywar ta cigaba har awajen carmilla,a waje ita mutum ce amma a dakin ta rayuwa take kamar na mahaukata zautattu duk akan son datakeyi ma Asad.
Bata sani ba duk abunda takeyi tsaf acikin kunnen sa,sau dayawa zaiyi ta dariya…in aka cire masa tausayin sai ya nemi carmilla ya rasa a brain dinsa,baisan ko dan abunda ta masan bane amna haka kawai yakeji har abada baxata taba dawowa macen da zai so ba…kowani dan adam da abun da ya tsana sosai so he hate betrayal,acikin hankalin sa yasan ya bada carmiillar damar da bazai taba bada wani ba,kuma dama ance opputurnity kamar hasken walkiya ce muddin ta dauke baza asake samun irin ta
Yau Hutun mu ya cika wata daya har da sati biu komi ya fara dawowa normal but the more muna kara kwanaki the more carmilla tana jin baxata iya daurewa ba sai ta nemo asad..
Ita Bata san me xata ce da shi ba amma ji tayi sam baxata iya daurewa ba bata gansa ba
A Cikin kwana biun ba irin tufka da warwaran da batayi
Wajen neman hanyar da zai sada ta dashi Gashi tana mugun jin fargaban kiran layin sa
Most times Takan fito aganta lpya lpya a tsakar gidan su sai dai yau Daga barin ta fadar mahaifin ta maxa tasa aka kira mata mai aikin ta blessing
,”..ko da sukaje daki carmilla ta shiga kulle ko ina mai aiki tasha mamaki sosai
Zaunar da ita tayi yau ba izza ba boye boye sai tulin saukar da kai
Blessing tasha mamaki matuka da yadda carmilla ta roke ta alfarma akan ta taimaka mata ta dinga fita acikin dare,ko yau ma yanzu zataje ta dawo..
cike da tsoro blesing ta dube agogo its 10pm da kyar dai ta amince har ta zauna adakin tayi luf agadon kamar itace carmilan,ita kuma carmilla ta sace jiki ta fita a mansion din babu wanda ya lura…
Bibiyar rayuwan sa da sukayi ada chan ita da molly yasa bata wani sha wahalan gane anguwar su ba,bata dai fito da car ba anma har kusa kofan gidan su tasa aka sauke ta..
A jikin wani pillar Ta labe ta dade anan tana waswasin abun yi,a karshe hakura tayi ta koma gida,sede kuma tun daga ranan sai bata samu nitsuwa ba a kullum sai tayi framing mai aiki ta fito tazo ta rakube tana leke leke ko da ma zata gansa by mistake amma hakan bai taba faruwa ba har result sheet ya fito a ofishin shubagan makarnta, ba a saka ranan displaying ba dake hutun mu har yau da sauran kusan sati shida,to tsaban murna da kwadayin abun duniya sai yasa shugaban makarta ya kebe ya kawo soft copy har gidan campbells yanuna musu inda kowa ya nuna tsananin farin cikn sa ganin carmila ta koma matsayin ta da maki dan kadan.
Mr campbells kamar zai tashi sama dan murna
Carmilla tana ta murmusawa tana nuna alaman murnan itama,ba wanda yasan cewa she is actually slowly breaking down helpsly in pain and shock dan ko da shugabn makatnta ya bude sheet din ba damuwar ta point dinta ba na asad tayi saurin dubawa,it shocked her dan batayi tsammanin ganin null semester ba..
Duk iya dauriyan ta akan haka sanda maman ta ta fahimci ba adede take ba,dinner da aka hada domin ta ma bata wani ci ba ta nemi izini akan abarta taje ciki kanta na mata ciwo
Tuni aka kira family docto ana ta haba haba da ita amma Tana kyam,har suka gama rubibin dube duben jikin ta suka gaji suka kyale ta murmushin dolen ma yaki ya bayyana akan fuskn ta
Can Cikin dare Kanta akan pillow tayi rigingine wani kuka mai azaba mai tsuma ta fashe da dashi cikin sautin axaban nadama bata ko damu da wani ya jiyo ta ba .
Tace Meyasa Asad xaiki ya rubuta exams dinsa duka?…Hakan da tagani ya dame ta matuka fiye da yadda ake tunani..
A ganin ta gwara ya xage ta daya tura mata aniyarta,and This has been the worstest silent answer he gave her,a duk ranakun da tayi kwanan bakin ciki batayii wanda ya kai na yau ba.
Hakan ba komai ya dada nuna mata ba sai hikima da jarumtan asad wajen bayyana ma xuciyarta cewa abunda ita da familyn ta suka tsawwalawa suke kuma nema ido a rufe suka dauke shi wani abun,shi awajen sa ba komai bane..
“..Cikin kwana biyu kacal sanda ta xauce cikin tunanin abun sosai abubuwa suka soma dagula mata tunani,ga son shi, ga wannan lamarin sai tayi ta tunanin asad din har ta fice hayyacin ta…neman yancin kanta da ta dade tana binnewa wanda kwata kwata bata so ta kawo shi aranta sai da ta kawo sa.
…sai ta soma jin rayuwar ta akan bauta aka gina shi sannan babu riba akan abunda sukeyi..
ta duk inda ta juya sai taga fuskar Asad, he became like a perfect demo for her.
Shi tamkar littafi ne
Dake warware mata amsar tambayoyin ta da ta dade tana neman amsar su..
,”so will she for once face her reality and be truthful to herself and asad? koko zata cigaba da bin tsarin iyayen ta ne har abada…?..
Kwana biu tana tunanin hakan,a duk dama bata so kowa ya san komi ba amma cunkushewar tunani da rudewa yasa ta kira molly awaya ta gaya mata gaskiyar abunda ke ranta da nadamar datakeyi akan asad.
Molly tayi kkri wajen tuna ma carmilla ita wacece,kuma waye uban ta amma so ya riga ya rufe ma carmila ido cewa take sam bazata iya rayuwa babu asad ba.
Har molly ta gaji,with much sympathy tabata shawaran cewa ta gwada bin zuciyar tan,amma tana me gargadin ta akan tayi ahankli kuma kar ta sake akamata a gida.
Bangaren asad kuwa babu abunda baiji ba,har zancen result da zancen zaucewar ta akansa duk blessing ta fada masa,dan wani babban deal suka kulla inda yace zai kubutar da mahaifin ta a prison,wanda dama kudi da lawyer kawai ake bukata wanda zai tsaya mata tulin shekarun nan bata samu ba,blessing bata da kowa sai mahaifin ta,tayi aikin bauta tsawon shekaru 30 agidan campbells amma basu ko mata wannan halaccin ba…
But da asad ya zo ya nuna mata yana da kudin kuma ga conection dinsa da law sai maxa ta zage damtse ta bada hadin kai,daga ranar blessing bata damu ba ko tari carmila tayi tana hankare tana ajiyewa domin sa ..
Aynzu Asad sosai ya fahimce cewa carmila zata dau dammarar neman yafiyar sa sabida tana son shi,dan haka sai ya dau matakai dayawa aransa ciki kuwa har da siyo wata katuwar human sized cage da hadadden kosashhen police dog wanda shikansa ma da kyar suka fara jituwa,ko mama tayi ta tambayar sa akan me ya siyo wayannan abun,amma haka ya nace da cewa gadi kawai karen zai masa…kawu kam ko kulawa baiyi ba.
Washe garin talata da safe carmilla ta farka tare da cikakken bada kanta karfin gwiwan nemo Asad da dawowa da shi rayuwar ta koda ace hakan shine kadai abunda xata boye ma iyayen ta a duniya na har abada.
Anan kuma Da rudani muka tashi,dan haka kawai kawu ya ce lallai na shirya na bishi can wajen dangi na,zamuyi sauran hutun acan kuma tare zamu dawo dashi..
Ranar Asad yayi ta jan tsaki har sanda mama ta kore shi kwata kwata a side din..dadin danaji shine bai bata ransa dani ba,he just asked me to promise him koma me zai faru zan dawo masa akan lokaci
Daga nan Har muka bar kano asad bai sake jin dadi aransa ba,aranar sai yayi wuf dan aynzu bai shan wahalan aikata komi musamn ma in xe fita wani waje, dadin karawa yau da aka barsa daga shi sai mama wasu sabbin shoping yaje yayu makan sa babu abunda bai siyo ba ciki kuwa harda tulin kwalayen cigarattes dayake saka ran zasu hana shi tunani na.
Just 2 days da tafiyar mun,ranar misalin karfe 6 na yamma sai ga carmilla ta zo har kofar gidan mu tana faman leke,da kyar ta daure ta iya tanbaya me gadin asalin gidan ya mata bayanin ta inda asad yake..
Aikuwa ranar data fara zuwa BQ dake ta riga tasa abun a ranta bataji tsoro ba har cikin gate din ta tura ta shige ciki tana tafiya ta leka bayan ta uwa barauniya,har tayi rabin compnd din bata ga kowa ba,dada kusa kai take har takai bakin windown sa ta dade anan,bata sani ba asad yana sane da ita kuma tun zuwan ta nan aka gaya masa xata zo din..
Sai da ya barta ta shagala ta rike window tana leke leke,can bazata ya wani bangaje windown ya bude shi da karfi sanda ya tabbata ya buga mata goshin ta,cikin radadi ta kama kai tana shushu ai kuwa tun kan ta danne zafin taji saukar shaaaaaaa na ruwan kankara mai azaban sanyi wanda tun daga tsakar kanta ya soma tabawa har ilahirin jikin ta,she cant resist the cold and the pain wani numfashin tsorata taja a sadade ta sake labewa a kasar window tana rawan dari,asad yana tsaye sai yayi kamar besan da mutun ba,kankaran ya sa abakin shi yana taunawa da wani irin sauti mai caccakar kunne,sai yaki sam ya bar jikin windown carmila tun tana rakube har kafarta ya fara mata zugi,gashi ba tantama tasan tana motsawa dole ne aganta.
Wasa wasa haka asad yayi ta shawagi anan har sanda ya bata mata lokaci yasa ta kai karfe 9:30 na dare bata kuma samu gwarin gwiwar fitowa sarari ba,kafufun ta da ita kanta ta gaji hartayi zufan wahala sai cahn ya kama windown sa ya kulle yabi ya kashe wutar gidan mai gaba daya,nan ta samu damar sulalewa tabar gidan a hnzarce da kyar ta samu ta shigo gidan su ba a kamata ba
anan bayan jinyar goshi ta datayi har wani zazzabi ne ya so ya rufe ta dan ba a taba watsa mata kankara mai yawa akan ta ba sai yau..
A wahale tayi baccin,hakan kuma be hanata sake komawa,shiru shirun anguwan da shirun inda yake yasa bata da matsala akan tunanin ko wani xai ganta sede in taje din ne Bata iya samun karfin gwiwar fitowa sarari sai tayi ta labewa aikuwa acikin kwanakin babu irin kalar azaban da asad baya dandana mata,itadai takan kalle sa amma bata san cewa yana sane da ita ba,asad kuwa har ruwan coffe mai xafi ya taba watsowa kan fusktar ta yanaji tana shure shuren xafi tana my eyes my eyes sai yaja windown sa ya kulle
Ya dora da guntun tsaki,haka kawai ayanzu yaji bata burge sa,duk wani hali daya shiga na kewar family members dinsa aynzu gani yake kamar itace sila..gata da nacin tsiya bata daddara ba sanda ya sake kwararo mata bataccen abincin dayake kin ci mai shegen wari a tsakar kanta da kyar sannan ta daga kafa
Tsawon kwana biu sai bata fito ba duk sai tarasa abunyi,da kyar ta yanke hukuncin tambayar molly ko zata samu mafita..
Molly tace kawai ta dena boye boyen ta amince da laifin ta,taje direct ta kwankwasa kofar sa ta gaya maaa gaskiyar ta
Abune mai matukar wuya wajen carmilla amma hakan ta daure ta daura niyya
Ranar an tashi da tsananin walkiya da haddari amma haka ta nace sai taje gidan asad
Ba gudu ba ja da baya,tasha wankan ta mai kyau tayi kyau sosai wata haddaiyar doguwar riga mai kama da satin ta saka iya tsayin gwiwon ta ta da yamma lisss waje har ya fara duhu duhu ta nufi kofar gidan mu
Data iso sai Fargaba ya hana ta shigo wa sai mutsike mutsiken idanu take cikin ranta tana tuno da maganganun molly anan har aka fara yayyafi mai iska duk sai tarasa yadda zatayi
Ruwan saman na dada sauka na kuma dukan ta Da kyar da fitina dau ta amince xata yi hakan,bold enouhg ta karaso bakin gate din ta bude da sauri tana kuwa saka kafa taci karo da kyafaffen structun namiji agaban ta yana tsaye sanye da tight black vest da guntun ripped jeans rike da chain din karen sa wanda tun shigowar ta yake ta haushi yana gurnani
Wani irin kallo ta bishi dashi duk tsumayin kaunar sa na ratsa ta,tayi kasakai kamar mara laka duk wani ciwon dake makale a zuciyarta su suke hauhawa suna mata zugi,Asad ya juyo ya kalleta kam amma sai yayi kamar bai gane ta ba,yadda ta tsaya ta tsura masa shima hakan yayi ba yabo ba fallasa bai hade ransa ba…
“He is sooo handsome nd sexy ganin yadda ruwan yake sauka akan jikin sa da karen sa yasa ta sakejin duk duniya babu wani face shi…
Atake ta matso kusa zata kira sunan sa sai taji duk ta kasa motsa lips din tan,muryan ta na rawa sai tace ” uhnm uhmn pls help me
Sai yy shiru ya maida hnklin sa Yana ta faman jan karen sa karen yana jansa yana haushi, yasan carmilla ta matukar tsorata da karen amma take dannewa,da dan karfi ta kuma cewa Asad pls i need ur help,sai Yace excuse me?…
Kalar yaudararen tausayi kamar yadda ta saba tayi saurin cewa pls help,its raining and…sai yay saurin katseta yace”nd u need help?a sadade ta gyada mashi kai.
Hmm kawai yace kamar irin strangers din nan yace follow me,aikuwa ta shiga bibiyan bayan sa,can ta baya wajen cage din karen sa yabi da su,she tot ko karen zai aje anan sai yace mata ta shigo gidan sa tare da shi suyi magana,aikuwa suna kaiwa ya bude cage din yamata nuni a saukake alaman ta shiga,da fargaba aranta sum sum ta taho batayi musu ba ta shige ciki,kofar ya jawo zai rufe tanaji tana gani,ta kasa daurewa cikin rudani tace Asad what are u doing? pls stop its raining i want to go home,ya wani share ta,rokon sa ta shigayi akan baxata iya tsayawa cikin ruwan sama ba sai can da yagama kullewar ya dago yace dint u ask for help?murya ararrabe tace yes,karamin tsaki ya sauke ya mugun hade ransa sanda taji zuciyan ta ya girgiza
Daga nan ko ajikin sa ya juya ya saka karansa a under shade cike da kulawa yana goge shi,ata inda ruwan bazai ma taba shi yace yayi masa gadin ta dan shi bai yarda da strngers.
Bayan hawayen da suka sauko mata Cike da rudani carmilla take kallon sa haka kuwa Asad ya tafi ya barta anan sanda duka ruwan da akayi a daren ya kare tasss akan ta kulle acikin cage tana ta kuka.
Tsaban sanyi Shikansa karen a rigingine ya tsakura amma ita kam da kyar ta iya ma sulalewa ta zauna tana ta tunanin yadda zata sake amfani da tausayi ko da asad zai sauko ya yafe ta.
Tasan fushi yakeyi,but she dont care in har zai saurare tan zatayi komi akan haka,sai kusan asubahi waje ya tsaya chak ga wani uban sanyin daya sauko a wahale baci ya kwashe ta cikin turbayan kasa
Asad kuwa baccin sa ya kwaasa just once ya tuno da duk abunda yayi domin ta,da xagin cin mutuncin datayi ta masa tana kiran sa dump wawa,tana marin sa a cikin mutane”
Ahakan ma wai dan Sam baison yace zai hukunta ta ne akan kukan data sha sa nadran sa akan gaskiyar ta
But muddin abun ya fado masa aransa sai yace lallai sai ya sa carmilla tasan wanene shi,kuma alkwari ne ya dauka yau saiya sa tayi breaking kowani rules din mahaifin ta sakamakon hada shi fada da iyayen sa datayi,lallai ta nuna mai cewa shi besan darajar nashi
Now he got why she called him stupid but so yake yanzu tasan cewa he is not dump,Aynzu so yake yayi amfani da nadamar ta dan ya gane wani abu
Shin Ko son datake masa zai iya sa ta bijire wa nata iyayen akansa?koko xata bi salon yaudara ne kamar yadda ta saba?..shi baiyi tunanin yayi amfani da son datake masa dan ya zautar da zuciyar ta ba amma tabbas ya qudira aransa koma yaya ne sai ya nutsar da zuciyar ta dan tasan cewa ba a yadda ya fito mata a matsayin wawa hakan ya kasance a zahiri ba
Muddin ya fito da kammanin sa na asalin da namiji yasan camilla zata fi fahimtar shi wanene,he is not the cool gentle guy she alwys tot of him to be..shin in ta gane tsauraran halayen sa na asali xata cigaba da son shin a haka?shin ko zata iya jure irin abubuwan da nadra ta dade tana jurewa akan sa?…but he daubt if any woman at all is gonna love him effortlessly like his nadra…nadra is still irreplacable!
Washe gari da safe waje yayi calm yay sanyi sosai,da kyar carmila ta farka tana faman mutsuke ido,tsananin sanyin daya riga ya kama ya yasa jikin ta ya dau zafi sosai+
Agogon hannun ta mai tsada ne dan haka duk ruwan nan daya sauka aki be masa illa ba,ta faga ido tana duba its almost 7.45am har yanzu bata ga alaman asad zai bude kofar sa Leke ta shigayi tana dube dube,ga zuciyar ta yaki ya dena bugawa tsaban tsananin tsoron data keji,how can she sneak back home in asad bai fito akan lokaci ba..
Haka ta cigaba da dawainiya cikin wannnan zulumi,kowani bayan dakika sai ta duba lokaci wasa wasa asad be fito ba har karfe 10 saura.
Lokacin blessing ta daga mata hankli da kira dagangan,dan already ita taji labarin cewa ajian campbells obasi bai kwana a gida ba so duk wani hanya da zata toshe ta riga ta toshe har ta sanar da mrs michell cewa carmillan bata farka bane.
Anan kuma hanjin cikin carmilla a kade yake,tsaban damuwa har bata jin zazzabi da ciwon kan yunwa dake damun ta,..10.45am sai ga asad ya turo kofan ya fito,sanye yake da hadadden blue tshirt wanda ya dora ta akan light grey three qtr shot,dayan hannun sa dauke sa steamy hot coffe mai qamshi daya kuma dauke da ligher kallon shi takeyi har ya karaso gaban ta..
Baice uffan ba ya ama kwadon ya bude,she tot ko zata iya sake jan hankalin sa da tausayi dan haka ta fara acting kamar marainiya duk abanza ko kallanta baiyu sau daya ba,gata da girman kai sai taki fita tana jiran shi ya fara mata magana,karen sa ya dauko ya goge shi tsaf tana kallo,ganin eh dagske yake zai maida karen san yasa ta tsorata ta fito a sadade.
Aransa tsaki yaja yana kulle kofar,sai ya juya zai bar wajen da sauri ta riko hannun sa cikin magiya da tausayi tace asad,pls listen we need to talk..dan Allah kar ka purnishing dina nasan nayi maka laifi but…bai bari ta karasa ba ya watsa mata hararan daya sa ta dauke hannun ta akan nashi da sauri..yace what r u still doing here?…tace Asad..ya wanivgwal mata ido fuskan nan a murtuke sai tace nothing..Yace pls get out,i think is no longer raining or r u blind? .tace Asad pls…wani wurgi yay da cup din a fusace sanda ta tsomare yace out..”ta daure zatayi magana idanun sa ya wara akan nata yace NOW..bitch..jin hakan yasa ta sauke idanun ta kasa2
Aranta tace Bitch?he call me a bitch?
Ji tayi kamar ana tsaga zuciyan ta she cant stand any more words nan ta wuce da gudu tana mai fashewa da kuka,wanda har ta isa gida bata dena ba sanda tayi bacci ta farka…blessing ta dada kara mata tension da nuna mata ita zata cire hannun ta akan case din da jia da kyar ta sha,haka carmilla tayi ta rokon ta tana mata magiya akan tabata lokaci ta kusa shawo kan asad kuma ta mata alkawri baxata sake kwana ba,a duk tunanin carmilla asad pretending kawai yakeiyi ta san yana da tausayi wallau idan ta nace mashi dole zai sauko ya yafe mata..1
Sede haka data rike aranta sai yake neman ya zamto mata wani babban mafrki dan kuwa tun ranar abubuwa su gaba gaba yakeyi,babu kalar kaskantar da ita da asad baiyi ba,zaka sha mamaki yadda baijin tausayin ta,ko ita kanta har yanzu bata gama yarda ba..Arayuwa batayi tsammanin haka yake ba,tsoron shi da shakkar sa ne suka mugun cika kwalwakta,
A kwana biyar kawai kullum in tazo sai ya mata azaban da zaisa taji ta kara yin nadaman abubuwan da ta aikata masa ma,ga blessing ma bata barta ba,most time dagangan zata tsorata ta akan mahaifin ta..
Mama kuwa har ta soma jin sauko aranta ganin kwana biu asad ya nace da shigowa duba ta,kuma in yazo yakan dade..bata taba lura da cewa yakan aje carmilla gadi anan bane yayi tafiyar sa
Har wuya carmilla ta kawo akan walakancin asad kullum sai ta nemi shawara molly zata danne ta tace tayi hrki zai sauko.2
Kusan sati guda kenan su nadra da kawu ma basu dawo ba,Da carmilla ta yanke hukunci in tazo haka kawai sai ta shiga fade fade kamar zararaiya ko asad zaiji ya kula ko bazai kula ba,a kwana biu carmilla tayi confessing komi game da kanta,sincerely hakan har ya tabo zuciyar asad amma bai rusuna ba sai ma ya kara kaimin kure ta ta hanyar sata kwana awaje agidan sa kawai dan yaga ko in mahaifin ta ya gane ya mata fada zata hakura ta dena bibiyar sa aikuwa koda asirin na ta ya kusa tunowan mr campbells ya fara ji aransa kamar tana fitan sai ya mata warning amma carmilla sai ta nuna bata damu ba..asad ya sha mamakin haka
He now understand lallai carmilla tana son shi,zai iya yuwa
Dagaske takeyi zata iya jure komi akansa,sede har yanxu bai yarda da ita ba..haka komi ya cigaba randa aka hada babban dinner agidan su wanda mr campbells ya kira media da abokan harkan sa musamman san ya nuna musu yarsa,ba yadda molly batayi kar ta fito ba amma haka ta nace da cewa xataje yanzu zata dawo,abu daya ya rage ta fada ma asad game sa kanta kuma shine tace masa tana son shi.1
Aikuwa suka barta,ta nufi gidan
Asad wanda already blessing ta gaya masa duk abunda ake ciki,so dagangan ya bar kofar sa a bude a wangale,dan haka tana isowa taji shaukin ta shiga ciki yau ta same shi tayi confessing.
A hankli ta kutso kai ciki,tana dan duban yanayin tsaftar wajen wanda ya dauke mata hankali,daga dan uban warin hayaki tabar dake tashi.
Har tsakiyar falon ta iso,sannan ta farga da shi a zaune sai busa hayakin tabar yake yana hurawa cikin kwarewa carmilla tafi minti ashrin a tsaye tsaban mamakin yadda tagan sa.
Shed neva imagine mutun kamae asad yana shan wani abu wanda ko a kallon farat daya baxata ce dashi dan koyo ba..
Kamar wanda besan da zuwan nata ba ya cigaba,sai can ta daure tayi masa magana she was like”asad so u smoke?..i mean why r u smoking,”daga jin rawan da muryan ta yake kasan ta sha mamakin hakan,asad ya daure fuska ko kulata bai yi ba..da ta ishe shi da kankanba mikewa yyi a ddan dole ya nufi kofa ya nuna mata way da hannun sa daya daya yana bakin sa dake fitar da wani azaban hayakin taba,tayi tsam a daskeare..wani kallon ya watsa mata a hankli ya furta get out..kiyi waje..’da azsman ta tace no,nazo ne in gaya maka wani magana koda baxaka ka yrda ba but ka saurareni..
Dauke kansa yay..,can u atleast givee ur attention ‘muryan kamar zatayi kuka sai daya ja mata rai sann yace say it?qarasowa yayi ya tsaya agaban ta very cute giran sa ya dage yace inajin ka,itakam kasa dauke idanu akansa tayi tsaban yadda yake kan busa mata hayaki a fuskan sai taji ta kasa amincewa sa cewa asad ne agaban ta
Ashe haka yake?dama ..hmmmm
Daurewa tayi cikin danne duk abunda takeji ta sake maimaita masa tarihin kanta dana familyn ta wanda already yasan komi,amma abu daya besani ba cewa duk abunda carmilla takeyi bason ranta bane tsaban biyayya ne da bauta ma iyaye.
Aransa he feel pity,amma ba kamar da chan ba sabida har yanzu bai kallon ta da matsayin komi a ziciyar sa.
Aganin sa in ma ze sake shigowa da ita rayuwar sa sede a matsayin tallafawa abunda ke mata ciwo,amma batun soyayya yasan har abada bazai iyaba.
Ko ayanzu data furta kalman ta n karshe cewa tayi…’with god Asad i love u,ina matukar kaunar ka har ziciyata hakan kuma shine gaskiya ta,..nasan baxaka yarda dani ba saboda bancanci hakan ba,amma ina so kasani,yanzu wata carmilan ce agaban ka..wacce bata ganin komi sai kai sai kaunar ka…tace tayi alkwari,”i swear i cross all bounds to prove ma love even if it means to go againts my dad,tana kuka ta fadi wannan kalman,shikansa ya san dagske takeyi amma sai ya basar,”..daga nan bece komi ba kofar ya nifa ya sake nuna mata way,wani irin karayar zuciya ne ya kashe mata gabobin jikin ta wani irin barin bazata jikin ta ya soma yi muryan ta na rawa sosai tace,..”Asad i love u,pls dont send me out,Asad kace wani abu dan Allah?..yaji tausayin ta har ransa amma har iyanzu beji digon wani abu me kamada so aransa game da ita…her three magical words feels nothing..”ji yy kamar makan ta take fada.
Dataga be ce uffan din ba kuma baida niyya,kuka me taba zuciya ta shigayi tana maganganu aganin ta yarda da ita ne beyi na tukun,acikin duka kwanakin nadaman ta yauma she highly feel the pain of betrayal, aranta tace dama bata masa hakan ba,bata taba tsammanin haka asad yake da tsatsauran ra’ayi da taurin kai ba, da kyar ta share hawayen ta ta dube sa”..i wll prove to that am a dfrnt person for u…daga nan waje tayi ta nemi waje a kofar BQ ta zauna abun ta
Wayar ta ne ya shiga ruri akaro na 15,tasan daga gida ne kuma neman ta akeyi,but she is realy pained da atittude din asad yau ta somajin sai tayi dagaske kafin asad ya sake amincewa da ita…
Aikuwa haka bataje gidan ba hat aka gama partyn da aka hada domin ta,hanklin mr campbells da matarsa in yayi dubu ya baci.
Data dawo,suka sata agaba da masifa takasa cewa komi don bakaramin tsorata tayi ba,haka kuma firr taki ta fadi inda taje din,but she deeply dont care anymore son asad ya riga ya mata katutu bata jin zata iya daurewa..
Haka rayuwa ta cigaba,abu tun yana wasa wasa Asas har ya fara jin tsoron yadda ta rikice salo salo babu wanda bata nuna masa wanda ya dada tabbatar masa da cewa zata iya yin komi akansa ba
Ayanzu masifa da tuhumar data kesha wajen mr cmpbells har yasa Blessing ta soma tausaya mata,
Ita ta ruki asad akan ya sassauta mata ya yafe domin mr campbells ya baxa idanun sa kiris yake jira camilla tafada tarkon shi ya gama da ita.
Yaji rokon kuma ya amsa aransa cewa ya yafe carmilla har yace ma blessing karta barta ta fito wajen sa yau,to duk iya kkrin blessing haka carmila taki sam barazanan mahaifin mata sai bai hana ta tunanin aikata komi ba, data fito din tasan zai iya yuwa yau ana biye da ita ta amma haka ta zo da nufin xata dame shi da surutai as usual,to yau be bari ta ma zauna ba kuma be de amsa ba ya sata a motar sa,tafiya suke shiru shiru..bata tashi shan mamakin sa ba sanda taga ya nufi hanyar gidan su da ita
wani gaf gaf kirjin ta yake bugawa,sai taji zufa na keto mata ko ina,tsaban tsoro wani kuuuu hanjin ta keyi,..”ita data fice a boye .meyasaa asad zai kawo ta gida
Wani bakin ciki taji data nitsu tagane cewa asirin ta yake so ya tona agaban iyayen ta…
Aikuwa securityn dake bibiyan tuni suka sanar da zuwan su,so tun kan asad ya danna horn a kofar gidan sun aka bude musu suka shigo..
Mace da namiji ne a tsaye tsam a hatabar gidan cike da kasaita sun kure motar ido,gurds da masu aikin gidan suna zagaye da su,ko ajikin asad yayi parking…a lokacin carmilla ji take kamar ta na cikin wuta..yace mata sauka ma bataji ba,sanda taji hannun sa na shirin finciko arms din ta sannan ta farga tsillin hawayen ta ya bashi tausayi amma haka yyi waje da ita kamar yar tsana,kasa daga ido tayi bare kafarta
Zuciyan Mr campbells kamar ana hura wuta,be ce komi ba sanda asad ya jawo ta gaban su
Mrs michell bata iya hakuri ba irin da guts din nan tace and who are you young man,..ya kunna hayakin tabar sa,ya ja siriryat hayaki ta gefen bakin sa Cikin saukin kai mai nuna danyen kai yace mata..”Asad….
Mr campbells ya hayyako kamar zaiyi magana “Asad ya kalle carmila dake gefen sa a rude yace..”Enough…dagan gan yake haka dan sosai yakejin haushin mr campbells aransa game da yadda ya jefa rayuwar carmilla koba komai so yake ya nuna masa cewa yarsan dayake daukar ta komi ba komi bace a wajen sa Ita kam Hawaye take yi slowly tana sharewa..yace..
‘Now, this is ur home can you pls stop bothering me?..i hate stalkers…nd for sure bakimin ba,i cant even date someone like u..pls akai kasuwa..tun kan sautin kukan carmla ya fito mr campbells ya daka masa wani tsawa”…Enough
Who d hell did u think u are young man..sec..ccurity..
A hatsale maman itama ta hayyako gaban Asad,uve made the bigest mistake of ur lige how dare u mess with doter..?Asad ya wani kalle sa tulun
….all right just shut up,..Enoug
Cike da rashin kunya ya furta dan sosai yakejin ya tsane iyayen
..carmila rasa inda xata sa mamakin sa aranta tayi..
A tsawace Yace i dint mess wit ur doter,ur doter is messing with me..and i hate it..
Rututu security suka gewaya shi amma be karaya ko ya nuna alaman tsoro ba yaki sam su matso kusa da shi” wani irin warning din rainin hankali ya ma mr campbells da matae sa kamar be san matsayin su a duniya ba”..
Yace shifa ba magana yazo yi ba, im basa son ya sake zuwa gidan ai sai suyi ma yarsu tarbiya,ta dena zuwa gidan sa tana damun sa… shi ya gaji..,’carmilla ta sunkuyar da kanta kasa sosai tanaji har ya gama tona duka asirin ta agaban su daga ranar data soma zuwa har yau saida ya fada musu..yace musu shi ba dan iska bane..kuma shi bega mace awajen ba,”wani karar sigari ya cire a aljihun sa ya kunna ya shiga busawa ko akwalr rigat sa har ya juya ya shiga motan sa ya bar gidan,duk sun rasa nayi, kallon sa suke kamaar gumaka campbelss ji yy kamr anyi mutuwan kasko ne me azaban radadi wani dummmm haka wajen ya dauke da dulumin bakinciki
Da kyar carmilla ta iya tattara sauran karfin ta ta shige gidan wani gulluton rudani shiya ke so ya shake mata wuya,tafiya take a sanyaye idanun ta gaba daya sunyi jajir sai taga gidan ya kara mata fadi,a sadede kamar barauniya haka take haurawa matakalan harta shige dakin ta
Akan gadon ta zube ta sake wani irin ajiyan zuciya from no wher sai ta tsinci kanta da fashewa da marayan kukan da baya saka zuciya samun sauki bare ya hana rudani
Asad has done hiis worst today,kenan duk abunda ta fada mashi game da famlyn ta ya watsar kenan?ya ze mata haka..har gida har gaban baban ta?..yanzu tayaya xata ma fara lallaban iyayen tan?
Tasan yau kam Babban zunubi ta aikata wanda bata ma tunanin kalar purnishment din dan tasan wuya xataci sosai
daga sama kuwa babu abunda ke tashi sai sautin yaren igbo cikin azalzalan masifa..
“Ai Dama nafada maki yarinyar nan tun haihuwar ta ta tsane ni…batajin tsoro na..her sis meghan wil neva try to insult ma dignity this way,..kai a kasa mr michelle ta dada matsowaa amma takasa taba shi tsaban yadda jikin sa yake shaking har yana gurnani,” “obasi..pls calmdown err…carmila has done her worst amma ai yarinyace ko,wani watsa mata harara yyi ji yake bazai taba yafe mata ba har abadan abada”mrs michell ta rusuna kan gwiwar ta da tattausan murya me ban tausayi tace forgive her nnai,she is still a child…i beg u.biko nu nnai..
purnish her,but i beg u do not hate her..nima na maka alkawri zan dau nawa matakin musamman akan wancan marar kunyar yaron..sai ta mike tsaye tana huci1
Hakan sukayi ta tattaunawa,sun dau lokaci suna jani in ja ka da kyar ma sannan mr campbells ya sauko ya bar maganan ya fice
Ranar Har yanma Carmilla bata fito ba,ko abinci bata sauko ci ba tsawon kwana biu bata je ko ina ba..tunani takeyi cikin nitsuwa dan tana sane da cewa da zarar fushin mahaifin ta ya sauka akan ta this time around to fa ta bangaren ta za’ayi mumumnan al’amari.
Duk da abunda ya faru jiyan sai taji son asad be gushe aranta ko da dan kadan ba,yanzu kam tasan in har aka ma asad wani abu akan ta bazata iya daukawa ba,gashi tana matukar tsoron fushin mahaifin ta,”ziriya take yi ita kadai,tama kasa kiran kowa bare ta nemi shawara..can in tagaji takanyi kuka mai rauni koda abunda ya cinkushe zuciar tan ya dan ragu,”but she knew she had to think fast too ,dan hakka ta harhade plan cewa itama wanann karon
Zatayi wasa da kwakwalar baban ta akan asad..4
Tana so tace mishi ai duk wannan salo ne na cimma burin su,ita babu ruwan ta da Asad,kawai yardan asad din kawai take nema again dan ta sake danne shi,karma yace zai dau fansa akan su.
The plan seems perfect,anma tsoro ya dame zuciarta akan ko zataci nasara mr camp bells ya yarda ko sabanin haka
Sosai ta tsara karyan cikin makirci da maganganu masu kama hankali
Kanta ne kamar zai fashe tsaban tuno da abubuwan da tayi ma asad dib abaya,cin amanan wanda ya nuna maka matukar yarda mummunan abune,shin in har asad zai iya daurewa da iyayen sa lokcin da baiyi exams ba ita meyasa bazata iya ba?
“she betrayed him,insult him,tasa shi ya tsallake dokar gidan su ya kwana awaje nd he missed his exams for nothing..to kenan shi ya iyayen sa sukaji dashi a lokacin?…gama wannan tunanin aranta yasa taji sabon karfin gwiwa dan haka ta shirya tsaf,tana jiran lokacin da iyayen ta zasu je dakin bauta
Sai can Da misalin bayan ishai tafito hakan tayi ta rakube daga zuwan su har shigan su tana kallo,basu rufe kofar ba dan haka sanda ta bari sun nitsu suna addua sannan a hankli ta rakube ta shigo ta tsaya abayan su
Lokacin Duk hanklin su bainan,cikin dauriya da rawan murya ta soma bayanin ta tsaf batare da ta fara bada hakuri,..
Jin muryan tan abayan su yayi matukar shockin dinsu bare aje ga abubuwan datake furtawa,Sun sha mamaki kwarai yadda carmilla ta fi su dogon tunani,.2
Mrs michele ce ta juyo tana kallon yadda take maganan..
I will neva betray u father…”despite the fact that we breed lions,that dosnt mean that lions arent scary
Baba,ka fahimce shiri na,wani lokaci makiyin bayyane yafi makiyin dake boye,we made a mistake by showing Asad what we want..” Yau bakuga behavioura dinsa ba?da ai ba haka yake ba..na lura a yanzu tako wani hanya yana so ya rama ya kuma wulakan tani, then i tot abt my studies,i tot abt u father.. Inajin tsoron irin shirin da asad zai mana nex semester…i have to think fast,i must come up with a plan wani wasar da zan sakeyi da kwakwakwsr sa,…”
Dan Allah ku fahince ni ta dada marairacewa tana me zuba gwiwan ta akasa
cike da mamaki da farinciki mr campbells yy kwafa can shima sai ya juyo ya kalle ta,dada sauya muryan ta tayi,just to show how serious she is dede nan gabar ta
Rusuna har gaban sa ta fara bada hakuri,”tace na tsorata ne da abun da nake harsahsje shiyasa na fara game din ban sanar da ku ba…father I must gain his trust again, kayi hakuri in hakan baiyi dede ba,zan karbi duk wani hukunci..
Mr nd mrs campbellss ji sukayi kamar an yaye musu duhun bakin cikin da suka shige ciki akan maganan nan….
“Feeling so proud yace Thats my doter,yarinya me nazari da hangen nesa..Babu bata lokaci ya sauko,ya dada jin bayanan ta
Suka sa mata albarka sosai,suka kuma bata daman yin abunda taga ya dace akan Asad.
Sude campbells in har abu dan ci gaban su ne basu damu da munin sa ba,wani bin zumudin cimma burin sa yakan hana sa nazari me zurfi.3
Yaune rana da carmilla ta ji sanyi da farinciki wanda ta dade tana begen sa aranta..
Betrating her parent isbt easy amma sabida son datakeyi ma Asad tana kallon abun ba komai ba…gashi tayi karyan har anbata full permissoin na fita waje da zuwa wajen Asad duk lokacin datake so
Sede plan din sun shine,iyayen sun sha alwashin zasu cigaba da nuna cewa bada sannun su bane,har se ta durmuya Asad again
Haka nan aka bar maganan,carmilla ta koma daki dauke sa wani sabon nishadi a zuciar ta
Dadare ma Bacci me ni’ima tayi bayan ta kamalla tunanin yadda xata fara baza game din ta dan ta samo zuciyar Asad..Tunda hakan ya faru take da yaqinin inta sake komawa gidan ta jadadda masa shi ta za ba iyayen ta ba to tabbas Asad zai sauko
Babban burin ta ayanzu Asad yace mata.”i love you too”
Alkwari tayi daga ranan ko musulunci akace ta karba ta aure shi she wont waste any time. She dont care if she wll loose her family .6
Washe gari da nazarin abun ta farka Dan haka ta shirya tsaf,dresses shoes,da duk wani charm da mace ta san inta sanya wa jikin ta zai dauke hankalin namiji shi take matsowa dasu,duk ta maida kayan ta ta sauya da wasu masu shegen kyau,babban shiri takeyi dan yakin samo kalma ukun nan daga bakin Asad.
Bayan kwana biu,blessing ita kan ta bata san meke faruwa dan carmilla bata gaya ma kowa plan din nan ba,shiyasa asad ma beji komi game da shirin ta ba..
Ita de blessing ta fada masa cewa Iyayen suna fushi da carmillan har kwan biu tayi bata fito ba,so anan hankalin sa ya kwanta atleast koba komi shima ya rama raba shi da albarkan uwar sa datayi na kwana biu.
Shide har yau fargaban sa nadran sa ce,yau saura sati uku a koma schl gashi basu yin waya shide adduar sa baifi yaji ance sun dawo ba cos duk sanda zai kwanta bacci baya iya dena tuno fuskan ta.4
Wani bin se ya sha tabar sa akai,wani min in shaukin ta ya kama sa bai iya ma shan tabar..tsananin son ta yakan taba zuciar sa har da kwakwalr sa,sai ya fara tunanin ko ya sa serious akan abunda yakeji dinne?,amma kuma baya so yayi da garaje,but he needs nadra…yana so ya fahimce wani abu guda atattare da feelings din ta akan sa..zumudin hakan ya hana sa sakat,kullum yakan duba calender dubar ranar da zasu dawo kano su same shi.
To Yana cikin wannan yanayi ranar ya fito falo kenan yaci karo da budewar kofar carmilla,tasha kyau,fari kat din riga da wandon jean wanda ya mata jahilin kyau tasa ta tsaya tana kallon sa.
Shima kallon nata yayi sede fuskn sa tamau babu alaman dariya ko wasa har ya taho y zauna uffan be ce mata ba’aransa je wonder wannan wata irin mayyar yarinya ce.’shi seda yagan ta ya tuna ashe ma wai tace tana son shi…”cikin wannan tunanin ta katse shi da cewa Asad?sai ya juyo ya kalle ta..hakuri tafara bashi,tana gaya masa yadda ta juya zancen ma iyayen ta har kansa ya so ya daure da maganganun nata
Kenan tana nufin ta bijere ma iyayen nata duk akan sa?..
He cnt just believ that,dan abinciken sa ya san tana matukar daraja ra’ayin iyayen ta,what a shock sosai ya juya yake kallon bakin ta
Yau itama daurewa tayi bata kawo maganan soyayyar ba,ita de damuwar ta su shirya,su dawo kamar da chan.
Wani yanayin Asad ya shiga na tausaya ma halin da ta tsinci kanta aciki duk dama yasan bazai taba iya taimaka mata ba ayanzu ba.
Da dukkan zuciar ta take rokon sa,da dukkan imanin ta da nuna gaskiyar ta.
Give me a chance Just one chance
Rasa kalmomin bakin sa yasa ya ki cewa komi har tagama dramar nata tayi waje,shikuma dakin sa ya wuce carmilla har ta isa gida tana kan tunanin shi,shin tayi kuskure ne data yi hakan?ko de tagaya masa gaskiyar cewa itama wasa da kwakwakn iyayen tan takeyi ba kawai tayi hakan danta kubutar da shiba…to what if be fahimce ta ba?in ya sake tona mata asiri fa?tasan in campbelss yasan nufin ta awannan karon wallhyy kashe ta zaiyi..dan haka sai take samun rudani wajen sanar da Asad asalin shirin ta akan iyayen tan.
Kwana biu sai ta kyale sa bata zo masa ba.
Shikuma hakan yasa ya gamsu da cewa gaskiya take nunawa.,he tot over it,sai yace toh zai bartan suyi abota amma zai fito mata ne a asalin shi ba kamar Asad na da chan ba…duk iya jajircewa data nuna masa,he still feel nd knws that babu macen da zata yi tolerating halayen sa kuma ta so shi face nadra
A kwana na uku Carmilla na kwance,sai ga sakon email ya shigo computer ta,
Its Asad zain Abdulshakur
Hannnun ta har n bari ta bude,tama kasa nitsuwa takarance
Dan haka saida ta karanta sau uku sannan ta fahince komi
Yace yafe mata’thy r friends again,amma bece komi akan soyayyar taba.
Wani irin tsalle tayi tana ihu tana murna kamar sakon shiga aljanna ta gani a rubuce,game da soyayyr aganin ta duk wannan me sauki ne tunda Asad din ta ya dawo mata.
Sai tanajin aranta bazata iya sake bata wani lokaci reply tayo masa da nuna matukar godian ta sharp sharp ta shiga shiryawa haduwar ta da shi a yammacin goben
Washe gari kusan awjen mama asad ya wuni,duk ya matsu yaji ance wani abu game da dawowar su amma sai shiru.
Perfect time mama ta samar makanta so idan taga yana zaune shirun sai ta shiga masa nasihan musamman akan yadda suka dauki rayuwar shida mahaifin sa.
Takance..”shi ya haifeka,yafi kowa jin zafin ka..menene ribarka a duniya in har bazakayi dabiar da zaisanya shi farinciki dakai ba?
Her points are all valids,shiyasa Asad baya mata musun abubuwa dayawa,shide damuwar sa abar sa yay rayuwar sa ba tare da an saka masa takunkumi,he hate to be told what to do,musamman in akan abunda yake da muhimmanci ne arayuwar sa”kamar choices din daya shafi karatu,saka kaya,abokai,inda zai je,me zaiyi?me bazaiyi ba,wa zai gaishar wa ze bari,he hates compulsion,duk wani abun da za’ace sai kayi baya so har cikin ransa.shiyasa har yau yake ganin
Baxai taba shiryawa da kawun ba.
Tun suna yara kawu baya sassautawa,
kusan komi nasu yana sa ido kuma yaga sunyi shi dede.
More reason da Asad yake ganin kamar Rayuwar Azaad da nadra babu yanci sabida basa son tsallake dokokin kawu da mama..
Amma be sani ba,Asali azaad da nadra suma suna rayuwan sun ne a yadda suke so bawai dan zallan biyayyar da suke ma iyaye ba,ya kasa gane cewa,kowannen su da ra’ayin sa amma sukan yi hakuri sosai idan ra’ayin yaci karo da na kawu ko mama,wanda Abu guda kenan da shi bai tabayi ba,Asad kullum akan ra’ayin sa yakanyi tunani.”be taba sawa aransa akwai secrifice na Biyayya tsakanin sa da kawu ba bare mama.
So he tot evryone is imprisoned badan komi ba sai sabida rashin sanin ciwon kai irin nasu.
Shi aganin sa yana da yancin kansa kuma baya tsoron yayi irin rayuwar daya zabar makansa koda kuwa zaa cigaba da ware sa ne acikin su
Mama tayi bakin kokarin ta dan taga ta shigar masa nassoshin biyayya amma haka yaki fur karshe ma shiyasa taji wani iri aranta dayake yawan furta cewa”asali kawu be damu da shi bane..be san damuwar sa..yakan bada misalai dayawa in ta duba sai taga gaskyar sa
Jikin ta yy sanyin wajen yarda da laifin kawu akan relship dinsa da asad,duk dama tasan Asad din yafishi rashin gaskiya kuma akwai rashin fahimta tsakanin su sosai
She wished thy can talkd out,amma tasan abune mai wuya,dan haka ta sa aranta tunda kawu bazai nuna kulawar sa akan asad kamar sauran ba daga yau ita xata sa yaji aransa cewa ba a ware sa ba..
Har yamma suna tare,sannan ya fice inda yaci karo da motar carmilan parke har cikin gidan su.
As usual tasha gayu tayi kyau,so Tana ganin sa ta tashi daga xaunen data ke ta tsaya da dan zumudi a guskan ta ayayin ta ta iso gareshi zatayi magana,ya tsare ta yace pls do not come with u car inside my compnd
..bata damu ba tace ok sannan ta juya ta je xata shiga motar ta fitar waje,yana ta kallon ta har ta kunna tayi parking acan waje ta gefe da gate sannan ta dawo ta same shi aciki”..a hankli ya dube ta yace,i mean no harm,female visitors r nt allowd in here..ta gyada kai tace karka damu na fahimta..yace no baki fahimta ba,ur life nd mine r alot more dfernt so u cnt be seen hia alwys,…henceforth”.
kamar wata mumu ta sake gyada kai tace ok,can kan wani plastic chair suka zauna,anan ne take sanin cewa dan ma baban sa baya gari ne take samun daman zuwa nan hr ake barin ta,dan hira sukayi kadan tana dada gode masa da amincewar sa akan ta,.
Takan tambaye shi abubuwa dayawa shima yakan mata tambaya jifa jifa,duk iya sauyawar Asad baya damun ta,itade she feel happy in tana kallon sa.
Bayan kwana sati guda Hakan nan ta nace da zuwa shi be taba zuwa ba,sabida cewa datayi iyayen ta basu san komi game da sirrin ta ba.ita de takan nuna masa cewa zata iya komi akansa ne.
Daga haka ta san Asad kwararre ne wajen iya zuwa night party,taji labarin yadda yake rayuwar sa complicated nd hard,duk hirar sun bataji ya kira sunan kowa nashi ba duk dama ita nadra kawai ta sani,tasha mamaki matuka data lura ashe sauke mata kai yayi a school sabida tausayin rayuwar ta”wanda ba lallai kowa ya fahimta ba “sumtimes sai ta tsura masa ido tayi shiru tana maganan zuci kash…,dana sani keya,she just wish da bata hakan ta fito masa tun farko…hala da yanzu sunyi nisa a soyayyar su.
Daga nan Kullum suka hadu tadin damuwar rayuwan su sukeyi,altho natan kawai ake maimaitawa,itama secretly yanzu ta fahimce cewa Asad yana fama da matsala da iyayen sa…sede ba kamar irin nata ba
A Ranar farko da suka fara hada dates” asad yace suje party ita kuma tace sam suje bakin ruwa at sunset suyi picnic’she wants more conversation with him koda ma zasu kai ga maganan soyayya tsakanunsu,tana son tasan ra’ayin sa akan ta har yanzu Aranta tanajin Hankalin asad baya wajen ta kwata kwata.
But where is his mind?Mesa baxai bude ido ya ga son datake masa ba,
Haka de ya amsa suka shirya zasu hadu a bakin ruwa fa ynma ne lis wajen karfe 5. 30 wani sky blue shirt ya saka akan farar skinny jeans da normal beach sleeper shima fari ya sa akafar sa sai yasa hoodie cap agaban an rubuta gifted ya fitoo so simple anma ji tayi kamar ta hadiye shi,ita kam tsinannen short barbie gown tasa wanda adede gwiwa kawai ya dakata ta barbaje gashin attach din ta,kalar rigar ta ja ne dan hakan kafarta dauke yake fa red sneakers mai kyau,ita ta kawo abubuwan sha a car din ta masu kyau masu tsada harda varieties na giya,.
Aganin ta tunda Asad yana shan taba hala ma yana shan giya,amma dataga be kula ba sai tasha mamaki.
Ita kam giyan ta dauko suka same waje bakin ruwa suna hira kadan kadan,
“Sai dura makan ta giyan take slowly tana kallon shi,gaba daya bata jin dede inta fahimci cewa ba ita bace agaban sa ba duk dama su biu ne anan.
Tashanye na farko ta dauke scnd botle stil be ce da ita komai akai ba,kurba daya biu sai ta ce masa “umm..ta mika masa kwalban da smilling face,a nitse ya kalle ta na 2 scnds shima smiles din yayi sannan ya girgiza kai alaman a’a,yakuma ce i dont drink…ta wara ido dan kyabe fuska tayi Tace why?.ya mata shiru..tace but u smoke..yace yeah,kema ai baki shan taba amma kina shan giyako?
Tace eh.juyowa yy shima yace why…?
tace i hate it..i cant smoke..bad for ma health nd ma personality,..karamar daria yayi yace ther u go..ashe abun ra’ayi ne..i smoke..amma bana shan giya bcos i hate it…againts ma stand againts ma religion…and all that u mentioned…
hmm kawai tace ta dada kurban giyan aranta she is wishing that yana sha shima tasan daya na sha hala zataji sirrin zuciar sa akan ta
Amma tun agida yau tasha alwashin se ta masa tambayr akan haka dan haka
Dan haka ta nitsu ta kira suna sa tace” asad”..sai ya juyo ya dube ta?
Tace menene yafi dauke maka hankali?..like what do u wanna talk about
Sautin Hmmm ya sake tare da ajiyan zuciya..yadann karkata kai kamar me tunani cahn yace yes..” Well,I hate small talks,i wanna talk abt atom,magic,the meaning of life, death,aliens،far away galaxies,
music dat makes u feel difernt,memories, the lies uve told anan sai ya dan dakata ya kalle ta sannan ya cigaba”..ur flaws,ur insecurities ur childhood,ur fear,what keeps u awake all night?..i want ppl with depth those who speak with emotions from a twisted mind..anan sai yay shiru be sake ko kallon ta ba
Ita kuwa A daskare take kallon sa,she can feel the breeze so hard on her lips Tsaban burgewan da kalaman nasa yazo mata da shi duk dama bata sammace su ba.
Hot guy huhn…with twisted mind nd words.A duniya in aka ce akwai wanda zata so kamar shi baxata iya yarda ba
Kamar ba itace a buge ba hakan tayi composing kanta ta kyabe baki a nitse,tace “wow intersting…ok..zan gaya maka duka wayyannan wani lokaci..sai tay ajiyan numfashi.cike da gwarin giwa tace welll enough abt me,saura tanbaya daya zan maka ka shirya?sai ya dage mata gira,”tace mmmmm..shin wacece macen da kake matukar kauna arayuwan ka.
Babu tantama yace my mother..
Sai tyi murmushi tace and..sai yy shiru yana shan drink dinsa kamar be ji ta ba….”da fargaba aranta ta maimaita tambayar murmushi kawai yayi…sanda ya lura da cewa ta gama bada attention din ta sai ya juyo da murmushi mai sanyi ya kalle tsakar idanun ta a hankali ya furta NADRA.