Ko wani d’an Adam a duniya Yana da tashi kaddara wasu kaddarasu ta faro ne daga tushensu watoh asali,sai dai wasu sun tsince kansu a yanayi Mai ban tausayi da Kuma al’ajibi,sun samu kansu a yanayin da su kansu Basu San tushensu,akwai wasu da ko iyayensu basu sani ba,dayawa sun bude Ido sun tsincin kansu a gidan marayu,wasu Kuma sun taso ne sun gan kansu a gidanjen Wanda Basu da alaka ta jini da su,wasu anyi adopting dinsu ne,wasu Kuma,tsintarsu akayi,wasu Kuma iyayensu suka tura su alma’jiramcin har suka manta gida,shin me karatu ta tab’a zama tayi tunanin ya wa’yanan bayin Allah suke ji a ransu na rashin sanin tushen su da asalinsu????wani gudumawa me karatu ke bawa yaran da Suka tsinci kansu a wanan yanayi,Allah ya bamu ikon kyautatawa marayu da marasa galihu (Amin “
Tushen labari
Shekaru 23 da uku da suka wuce
Yau ma Kamar kullum fitowa tayi daga d'an rumfarta,tsanye take cikin wata yagaggen Riga duk ya yage,sai zaninta shima da yayi mugun kodewa gashi dukun dukun,kallo daya zakayi Mata kasan rigunan jikinta sun Kai uku ko hud'u kasancewar dukda na wajen ta yage baka ganin fatar jikinta saboda akwai wata a ciki
Gashinn kanta ko Kamar afro duk ya nade ya koma kamar dada Wanda kallo d’aya zakawa kanta ka Kau da Kai saboda da k’yar ne in bakayi yunkuri amai ba saboda Tulun datti dake bayyane a suman nata
Kafarta kuwa hadin bauta ce wato ordinary slippers da Kuma Zola slipper hakan ne yasa in tana tafiya zaka dau tana da matsala ne a kafa kasancewar Zolaslippers tana da tudu ita Kuma ta kafar hagun flat ne
Mika tayi tana sauke numfashi wahala da yunwar dake cinta
Shafa dogon cikinta tayi da ke addabanta da kicking ji take kamar ta kashe kanta,domin wani azzababen zafi take ji,ga yunwa ga Kuma cikin ya addabe ta,tunda cikinta ya tsufa Bata samun bacci tafiyarta ma ta canza
Hango wani Mai Saida Kara's tayi daga nisa Yana wankewa a wani babban roba
Da sauri ta karasa,tunda ya hangota ya hade Rai yana kokarin tattare kayanshi ya bar wurin sai ta sa sauri ta karasa
Wani banzan kallo ya wurga Mata kallon tsana,in akwai Wanda idi Mai caras ya tsana a duniya itace,ya tsane wanan Mahaukaciyar domin ta takurawa rayuwarshi
Dariya tayi beyi aune ba ta kinkimi ruwan bawon ta zubawa kanta daga Kai
Yana kokarin amsar robar tayi wurgi dashi tana dariya
Yace”ke kwarkwar Zan Miki shegen duka yau bazaki Sha ba wallahi inda kika haddabi rayuwata Haka Nima Zan addab……”
Be karasa ba ta watsar da caras din dake wheel biro dinshi ta Fara tafi
Gadan gadan ya nufe ta da niyyar ya duke ta aiko ta d’auki wani karfe Dake ajiye gefensu batayi wata wata ba ta kwala me a Kai ai sai jini ya b’arke me juwa fa Fara d’ibar ta
Dariya ta kyalkyale dashi tana tafi tana nuna shi tare da yime alamun kad’an kenan tayi Masa
Gudu yayi ya bar wajen karta hallakasa
Tana ganin hakan ta duka da k’yar ta dauki ledar karas uku ta Fara ci tana cusawa bàyan ta ci tayi nak ta karasa bakin famfo layin layi ne sosai akan famfo Amma Mata na ganinta sukayi saurin d’iba mata ruwan ta amsa ta kafa a Baki,tana gamawa ta kalli bucket din dake bakin famfo
Tunda larai ta gan ta kurawa bucket din Ido tace”Yi hakuri tunda an Baki kin Sha ki tafi ki huta Dan girman Allah bamu da ruwa
Murmushi tayi ta karasa tana zuwa ta kinkime bucket din tayi wurgi dashi gefe sanan ta zauna gindi famfo ruwa na sauka a jikinta sai ajiyar zuciya take saukewa ita kadai tasan me take ji cikin kwanakin nan
Daya bayan d’aya matan suka fara d’aukan robobinsu suna Barin wurin Dan sun San matsifar irin ta wanan mahaukaciyar sun San tunda ta zauna anan da k’yar ta tashi yau dai ta kwace wuri Nan sai Allah
Larai tace”ku tsaya kodai nakuda take ne?*
Maman afnan tace"ba wani nakuda kin mance iskancin matan Nan ne,ko ma nakuda take babu abinda ya dame ni wallahi bazan b'atawa kaina lokaci ba akan Yar da za a haihota ba tushe ba gomma ma ta mutu a gun haihuwa da ita da jaririn a huta saboda zuwan ta duniya bashi da amfani yaron da a titi akayi cikinsa wani Mai niman duniya yayi Mata ciki Zan wani b'atawa kaina lokaci
Larai tace"kedai a rayuwa baki iya magana ba miye aibun dan an taimaka mata,Kuma fa Baki da hujjah a titi aka samu wanan cikin dan kowa awanan yanki yasan lokaci da matar Nan ta Zo nan kallo daya zaka Mata kasan fa ita din wata ce kafin kayan jikinta su lalace,yanzu Haka wani yayi Mata wanan cuta"
Maman hafnan tayi tsaki tace”ai sai kiyi wallahi,ni na tsane wanan matar mussaman ma lokacin da ta Zo garin Nan malam ya like Mata Wai zai taimaketa harda d’auko min ita gida a wanan lokacin ko tari nayi sai yace”na muzguna Mata har cewa yayi zai aureta a Haka in badan nayi me Jan Ido ba “
Larai Bata Kara kulata ba ta karasa wajenta cike da tsoro tana tab'a cikinta tace"kina Jin ciwon ciki..cik
…cik”
Kura Mata Ido kwarkwar tayi tana kallonta a hankali larai ta karasa sai dai tana zuwa kusa da ita ta jawo ta ta danneta kamar ba me ciki ba
Ihu larai take tana niman taimako da k'yar wasu mazaje uku Suka Zo suka janyeta gefe Amma ta Matsu
Kusan wuni tayi a gindi famfo kafin yunwa ya azalzale ruhinta ta mike da k'yar duk tayi nauyi ta Fara tafiya zuwa rumfarta
Tana zuwa Bata Shiga ciki ba ta samu wuri ta zauna sai kalle kalle take kamar me jiran wani
Hangoshi tayi daga nisa rike da ledoji guda biyu ai sai murmushi ya sub’uce Mata malam Ahmad na karaso ta mike shima murmushi yayi ya Mika Mata leda daya Wanda shi ya Saba Mata shi ya d’auki alhakin ciyar da ita tun zuwanta garin da safe Yana tilastawa maman afnan ta kawo Mata kunu da kosai da Rana dai be samu ya Bata saboda shima ba wani Mai Hali bane Kuma ko yace” maman afnan in tayi girki ta bata,Bata bayarwa domin ta tsaneta,shikuma Yana fita kasuwa sai yamma yake dawowa gida
Bude ledar tayi shinkafa ce da wake da Mai da yaji a cikin wata babbar roba sai kankana da lemu ka
Kallonshi tayi domin tana son wanan shinkafar da yaji ta saki murmushi ta lumshe Ido ta bude su tare da me alaman godiya,can ciki ciki yaji muryarta Mai sanyi da Kuma ban al’ajibi domin murya ne Mai cike da abubuwan ban mamaki Kuma Bata yarda kowa ya jita ko shi Yana kusan wata Bata furta me komai ba sai dai yayi ta Mata magana in ba ta gan damar amsawa ba bazata ce komai ba,da farko ya dau shirun nata Yana cikin ciwon nata ne sai daga baya ya fahimci tsansan izza ce da Kuma miskilanci……sanan Koda zatayi magana toh fa cike da izza da doka takeyi shi
Be tab’a mancewa Akwai Randa take me magana be jira ta Gama ba cike dahaushi tace”my friend keep quiet in Ina magana mutane saurare suke Kuma magana daya nikeyi Kuma Dole abi umurnina sai Kuma ta fashe da dariya
Wanan shine magana Mai tsayi daya tab'a Shiga tsakanin su,magana ce Mai cike da sako tattare dashi
Pure water leda ta d’auka ta wanke hannun ta Fara cin shinkafa Wanda daga yanayin zamanta zai sanar maka da ita wacece
Yace"ni Zan shiga ciki"
Hannu kawai ta d'aga me ba tare da tace komai ba ya tafi Yana waigenta
Sanda ta ci tayi nak ta shige rumfar ta ta kwanta
A dai-dai wanan lokacin bacci ya kaurace Mata sai juye juye take a yamutsesen katifarta
Motsi taji ta tashi zaune tana haska torchlight din da malam Ahmad ya Bata mikewa tayi tsaye ta Fara kokarin fita daga rumfar sai ta gan wanan dai alhajin ne ya sake dawowa
Washe hakoransa Yana cewa”sweet heart Sannu ya babyn mu da fatan dai babynmu na lafiya
Fisge ledar hanunshi tayi domin tasan Yana kawo Mata kayan dadi
Gassashiyar kaza ce sai fidda Mai yake da kamshi gata da dan d’imi kaiwa Baki tayi ta fara yaga Yana binta da kallo
Ya Kai hanun zai ta'ba ta ta bige me hannun
Bàyan kusan awa d’aya ya fito cikin yanayi Mai wuyar fassara ya karasa wajen had’and’iyar motarsa Mai shegen tsada yana Bude driver seat ya zauna ya dukar da Kanshi kan starting ya dade a haka kafin ya ja motar ya bar layi
Fitowa malam Musa yayi daga shagon kantishi ya bishi da kallo yasan wanan alhajin tun zuwa wanan mahaukaciya garin nan yake zuwa yasan ba shakka shine wada yayi Mata ciki "
Hannun yasa a hab’a ya jinjina Kai yace”hmmm niman duniya Allah yasa mu dace”but ya kudiri aniyar gobe inshaallah sai ya ari motar Mai kawo me biredi ya bi alhajin gida yasan gidanshi saboda wata Rana
_______
Washe gari Haka kuwa akayi alhajin ya dawo a dai-dai lokacin daya Saba zuwa sai dai kamar jiya haka ya fito
Tunda ya Shiga cikin rumfarta
malam musa ya fito ya tafi can nisa da layin inda Isa Mai biredi ke jiransa a mota
Suna ganin ya fito ya ja mota sai sukayi saurin Jan tasu Suma cikin dabara Isa ke tuki suna gaban alhaji ganin suna tafiya kamar Basu son yi yasa alhajin shiga gabansu daman haka suke so Yana Shiga gaba sukayi ta binshi a baya cikin dabara wani lokacin su Shiga gaban wani lokacin suyi baya Kar ya fahimci binshi suke
A Haka sukayi tafiya Mai nisa har G R A
Har ya Shiga layin anguwansu daga motar suka hango yayi horn a kofar gidanshi an bude me ya Shiga
Bayan kwana 10 da faruwar Haka yau ta wayi gari ne da matsananci ciwo sai ihu take,malam Ahmed ne ya kawo Mata kunu da kosai dan tun shekaran jiya yake Lura da ita sai dai taki yarda a zo kusa da ita har shi da take sakewa dashi,Kuma in ya ajiye abinci haka zai dawo ya sameshi bazata tab'a
Yanayin daya same ta yau ya bala’in rikitar dashi cikin taushin murya yace”ki daure a Kai ki asibiti baiwar Allah
Zubame idanunta da sukayi ja tayi sai ya gan ta Fara hawaye
Ya mika Mata hanun sai ta kau da Kai tace”toh a kaini a cire min wanan cikin Mana me ake jira’
Sometimes in tayi magana sai ya gan kamar ba mahaukaciya bace but in ya tuna lokacin datake tikar rawa ta Kama Mata ta musu duka da shigar bolan da takeyi kafin yayi Mata wanan rumfar ta garwa sai yaji jikinshi yayi sanyi
Yace”ki jirani Ina zuwa minti ashirin “
Kallonshi tayi zatayi magana kamar an tsigareta ta saki ihu hakan yasa yayi saurin barin rufar domin zuwa niman mota
Malam Musa ne ya Kira Isa me driver ya kawo motarshi
Malam Ahmed ya Shiga yace”baiwar Allah tashi a kaiki asibiti
Ganin bazata iya tashi ba yasanshi Kiran malam Musa ya shigo suna kokarin taimaka Mata ta d’aga Musu hanun ta mike da k’yar sai a lokacin suka Lura da duk ta yanke cikinta da Reza Wai zata ciro yaro ga ruwan haihuwar ta fashe sai tausayinta ya Kuma kamasu
Musa ya Kara yunkurin taimaka Mata sai ta zuba me idonta me cike da kwarjini da sauri ya dukar da Kai tayi gaba bayan ta cire zani suka bi bayanta
Sanda malam Musa ya tsaya ya tattara kayan da ya dan siya Mata wancan satin daya Lura haihuwar ta Zo ya bi bayansu
Suna zuwa primary health care nuses suka ja ta labour room zuwa lokacin ta haukace da zafi sai dai Bata ihu Shure Shure take
Kasancewar Bata tab’a zuwa anti natal ba sai haihuwar ya zo Mata da gaddama
Nurses suka fito suka ce a kaita general Wai sai an Mata aiki
Haka dai suka tafi general kwararun likita suka Fara dubata
Har likitoci sun shirya za a Fara Mata aiki sai ta saki wata mahaukaciyar nishi sai ga Kan jinjiri ya b’ullo Dr Ruth ta kalli Dr farpuq tace”it a miracle dr,kallonta Ruth yayi ba tare da taji tsoron kasancewarta mahaukaciya ba ta dinga shafa kanta tana cewa breath harder……..”
Bata karasa ba ta saki wani nishi me hade da tusa a take baby ya fito suka jawo jinjirin
Dr farouq ya gan baby kyakyawar gaske ya Kura Mata Ido Kama take da mahaifiyar ta,dukda yanzu mahaifiyar ta sukurkuce
Rungume yariyar dake tsala ihu yayi Kamar ba jaririya ba
Dr Ruth tace”Dr is like Bata numfashi
Mikawa wata nurse baby yayi Suka Fara kokarin ceto rayuwarta saidai Ina tayi dogon Suma Bata ma hayyacinta gajiya sukayi suka barta bayan sun tabbatar tana numfashi kawai she is uncosience ne suka gyarata Suka maidata ward
Nurse ko bayan ta kimtsa su ta fito ta mikawa malam Ahmed baby girl ya amshe ta Yana tasbihi ga ubangiji yariya sai motsawa take Kamar ba jaririya ba
Ya kalli Dr da fitowar shi kenan daga thearter din yace”Dr Ina fatan dai tana lafiya?”
Dr farouq yace”tana lafiya sai dai ta danyi doguwar Suma ne a hankali zata dawo Ina ma sa ran Nan da awa hud’u zaku iya Kai jaririyar gida a Mata wanka sai ku kawowa petient din abinci tunda Allah ya dafa ba ayi aikin ba
Ya jinjina Kai yace"ok zamu je mu dawo"
Malam Isa ne ya maida su gida.a hanya malam Musa Mai kanti ke labartawa malam zancen alhaji dake zuwa duk dare
Yace”ai ba shakka shine uban Yar sak Kamar uban nata”aiko ya dage harda kari yace”ni ban ma tab’a ganin kama Haka ba wallahi”
Shi dai malam be ce komai ba ya fad'a tunani Mai zurfi a Haka suka karaso gida malam Musa na zuba yanayi ne ko malam Ahmed zai Kara nashi Amma shiru
Sanda suka fito a mota malam Ahmed yace"malam Musa ka taimaka ka Kai jinjiran Nan gidanka matarka ta kimtsa ta ni Kuma zanje inyiwa maman hanifa magana in ta ganin da ita kasafai zata tada hankali
Yace”toh ba komai malam Ahmed Allah ya Kara Lada da rufin asiri
Yace”Amin”Yana Kama hanyar gidanshi
Hospital
Suna barin asibiti abin mamaki sai ta Fara motsawa a hankali ta bude idanunta da suka Mata nauyi tana bin d’akin da kallo,kamar a mafalki take tuna gida ji take kamar tayi bacci Mai tsawo sauka tayi da k’yar daga gadon tana jin jiri tana bin kanta da kallon mamaki ita tasan Bata tab’a yin ciki ba but a matsayinta na kwararen likita ya take Ji kamar wacce ta haihu ne
Kalle kalle tayi tace”what is going on here where is my husband?Akr….”sai Kuma ta Kai hannun kanta cike da tashin hankali Jin suman wani iri ta shige toilet ta kalli wani madubi ihuu tayi tare da sakarwa kanta sha’wa..ko da ta fito ta kalli d’ayan petient din da ke bacci an Mata allurar bacci ko Jin motsinta batayi Kuma relative dinta sun tafi gida
Zuwa tayi wajen drawer ta ta jawo sai ta gan sabulai na wankajarirai ta d'auka ta koma toilet tare da had'awa da ledar omo ta juya ruwar flask dinta a bucket sosai tayi wanka ta goge jikinta sai datti ya d'an ragu saidai har yanzu sumanta na dunkule
Tana fitowa ba tare da tunanin komai ba ta d’auki pad din petient din da sabuwar pant dinta dake loka tasa ya Dan matseta Amma Haka tasa jikinta har rawa yakeyi gashi har yanzu she can recall anything itadai gida zata je ai Mai m……sai Kuma tayi tsaki ta d’auki hijabin data gani cikin kayansu tana kokarin sa hijab kudi ya Fado a dunkule da mamaki ta kalli kudin tace”na….ir….s?but iam a sudane…..sai Kuma tayi shiru ta kwashi dubu ukun ta d’auki wani zani ta rufa jikinta dashi da Rabin fuskarta ta bar ward din
Tana fita daga asibitin tayi ta bin asibitin da kallo hankalinta na Kara tashi me ya kawo ta wanan kasar
Da yike tayi karatu data fita sai tayi ta niman sighnboard Aiko ta hango na asibitin ta karasa ta karanta
Kuka ta fashe dashi tace”meke faruwa ne Dani Akr…..”
Da sauri ta karasa ta tare napep ta hau tace”me garejin Abuja domin ba laifi ta tab’a zuwa kasar da dadewa tun tana karamar yariya Kuma in Bata manta ba tana da few relatives anan dangin mum dinta
Gareji ya kaita da ka ganta kasan she is confuse she need answer from people but wa zata tambaya kuma bazatayi stopping so low ba to ask mutane da Basu Kai level dinta tayi magana dasu ba
Wani irin Zama tayi a napep din Mai napep ko sai satar kallonta yake ta madubi suna kaiwa yace"hajiya an iso,tayi zurfi a tunani so Bata jisa ba
Cike da tsokana ya buga keken yace”basarakiya an iso”
Firgit ta kalleshi ta fito ta bashi kudi ta Kura me Ido Dan ta gan ko zai Bata canji Aiko ya Bata d’ari Tara da saba’in da yike Bata gane kudin ba sai ta amsa
Tace”nawa zasu caje ni zuwa Abuja?”
Yace”daga Nan dubu d’aya ne da dari shidda
Tace”ok ware min kudin”
Ya ko ware Mata kudin tace”waya zaka Ara min “
Bata yayi ta zuba number tare da had’awa da + na kasar sai dai number be Shiga ba
Ta Mika me tare da me godiya ta kalli madubin napep din wani faduwa gabanta yayi ganin Kamar ba ita bace a madubin ga hakoranta sun canza kala
Cike da sanyi jiki ta karasa cikin garage din
___________
Sai 11am malam Ahmed ya anso jinjira ya Kama hanya asibiti da ita
Sai dai Yana kaiwa asibiti ya tarar da
DOWNLOAD COMPLETE BELOW ⬇️