UMARNIN SAURAYI CHAPTER A

 UMARNIN SAURAYI CHAPTER A

*__________📖* Wayar tace ke rura tana son ta tashi ta ɗauka amma ta kasa,saboda irin yadda ya manne ta ajikin sa.

+

Sosai wayar ke rura,aƙalla anfi yin miss call goma amma tana ji ta kasa tashi ta ɗauka.

Ba dan komai ta kasa tashi ba sai dan kada ta ɗan mutsa ta ta dashi,abinda bata so ita kam.

Wayar ce taƙi daina ƙara,kuma gashi bata son ƙarar data ke, dan bata son ƙarar ta dame shi yana baccin sa,dan haka ta fara tafiyar da hannuta slow-slow har ya kai kan wayar.

Ɗauku wayar tayi lokacin kuma wayar ta sanya wata ƙara.

Da sauri ta sanya ta silent, duba miss call ɗin tayi taga wake kiran ta.

Fara dubawa tayi aikuwa gaban ta ne yayi munmunar faɗuwa da taga wanda ya kira ta.

Tana cikin wannan farga bar sai ya fara mutsi alamun zai tashi,jikinsa ya ƙara jawuta kana ya ɓuɗe idonsa waɗan da bacci basu gama sakin shi ba.

Ahankali ya fara mata magana akunne yace, “My Sweet nah,ki tashi ki haɗemun abunda zan karya saboda yanzu na keson tafita office dan jirana akeyi”.

Ba musu tace, “yanzu kuwa Hayateena”.

Kumatunta ya shafa haɗe da kai ma kiss kana yace, “shiyasa nake ƙara sonki”.

Murmushi tayi mai ɗan sauti kana ta tashi taje kitchen ta haɗa masa abunda yake buk’ata.

Har takusa kammalawa wayar ta tasake ƙara,da sauri ta ɗauku waya tana mai duba sunan dake yawo saman screen ɗin wayar.

Gabanta ne yaba da dummm hannuta na karkarwa ta kara akunninta.

Kafin tayi wata magana har anfara magana cikin faɗa-faɗa.

“Hafsa ina kikaje?ina kika kwana?miyasa kikeso kijamin abun magana da mahaifinki, ehh!”.

Muryar ta narawa tace, “Mama wallahi karutune yayimin yawa kuma kinsan munkusa Fara exams  kuma wannan karun mai zafice zamuyi shiyasa nayi bacci na a hostel,amma ki bashi hak’uri anjima kaɗan zan dawo”.

Sai Mama tace, “to naji amma kirinƙa faɗamin idan zaki kwana saboda nasamu natsowa kinji ɗiya ta”.

Tace, “tau Mama sai nazu anjima”.

Bayan sunyi sallama da Mamar ta,tashi tayi ta haɗe masa komai na breakfast,bayan ta kammala taje toilet ta haɗa masa ruwan wanka,bayan ta gama haɗe masa taje ta faɗa masa yazo yayi wanka.

Bayan yayi wanka ya fito,da kanta ta shirya sa ta fesheshi da turare mai ƙamshi kana ta kaishi dining Yayi bearkfast.

Bayan ya kammala ya tashi zai fita office,jikin sa ya jawota kana ya kai mata kiss a baki,ido cikin ido ta dubeshi ciki da shagwaɓa tace,”Hayatee nah, anjima zanje gida dan Mama takirani tana faɗa dan ma nace mata  ina hostel ne ta ƙyaleni”.

Tunda ta fara Magana ya heɗi fuska har ta kai karshe.

Yace,”bawani Mama ta kiraki kina dai son kitafi dan yanzu naga alamun kin daina sona”.

Kamar tayi kuka tace, “kadaina faɗin haka wallahi inasonka sosai,amma tunda bakaso naji na fasa zan san me nace mata.

Aikuwa tana faɗin haka wani murmushi ya bayyana afuskar sa,lokaci ɗaya ya fara kiss ɗinta.

Abun ne yaga zaifi ƙarfinshi kuma anajiran sa a office dan haka yasake ta ya ɗau jikar sa ya fice batari da ya saki waiwayo wa ya dube taba……

 Saman kujerar parlour ta faɗi tana maida numfashin ta ,dan sosai ya taso mata da sha’awar ta, dan ita bata masu yafita ba, taso ya tsaya ya cikaga ba da abunda sukeyi ko ba komai zata samu natsuwa.

+

Ta jima kwance saman kujera kafin ta tashi, kushi lokaci taga yatafi kuma bata son ya dawo bata gama aiki ba dan haka ta tashi ta fara aiki, cikin ƙan-kanin lokaci ta gama gyaran gida da abunda zai ci idan ya dawo.

Bayan ta kammala komai tayi wanka ta shirya cikin shigar da tasan yana so, dressing  ɗin english wears kenan .

Jikin ta ta feshe da turarukka masu masifar ƙamashi bayan tagama shafe jikin ta da humra ta ƴan sokoto wanda akayi ma haɗi na musamman.

Tayi kyau sosai dan idan ka ganta bazaka ce ita ba haushiya ce ba.

Bayan ta kammala gyara jikin ta,zama tayi saman  kujera haɗi da ɗauko  wayar ta ta kunna kana ta kira Mamar ta dan tagaya mata yau ma ba zata samu damar zuwaba sai gobe.

Ringing ďaya Mama tayi picking call ďin ďiyar ta.

Kafin tayi magana sai Mama tace, “kina kan hanya ne?”.

Hafsa tace,”aa Mama yau ma bazan dawo ba sai gobe dan munada Lectura da safe kuma Babane damu kin san tsohon ba dai fitina ba,amma da mungama zan dawo”.

“Tau ba komai amma naso ki dawo gida,amma gobe da kun gama ki dawo”.

Tace, “tau Mama ki gaida Abbana”.

Sallama sukayi ta aje wayar,sai jin tayi ana mata knocking,tashi tayi taje ta buɗe masa ƙofa.

Tunda ta buɗe ƙofa ya kifeta da ido dan ba karamin kyau ta masa ba,lokaci ɗaya ya jawota jikin sa,haɗi da kai mata kiss a goshe.

Kallon dressing ɗin da ta masa ya shigayi dan tunda yake da ita bata taɓa yimasa irin wannan shagar ba kuma sosai yake son irin wannan shigar.

English wears ɗin data ke sanye da su ya bi da kallo,jan riga ce da wani matsatsin wando wanda ya kamata sosai,ahankali ya kai hannusa ya fara shafar jikin ta yana shaƙar ƙamshin dake fita ajikin ta.

Tunda ya fara shafar jikin ta tafara jin yarrrr……sosai ta ƙara manne jikin ta da nashi.

Tsayuwar ce ta gagaresu dan haka cak ya ɗauke ta ya ƙarasa bedroom ďinsa da ita.

STORY CONTINUES BELOW

Sosai yayi romances ďinta kafin ya ƙyaleta.

Itako haka tabiye masa yayi duk yadda ya keso da ita duk da bawani son abun take ba amma bazata iya nuna masa bata soba saboda bata son ransa ya ɓaci.

Bayan ya gama abunda ya keso kana ya dube ta yace,”kije ki haɗe man ruwan wanka dan fita nake son yi”.

Ba musu taje tayi yadda yace,bayan yayi wanka ya ci abinci kana ta dubeshi cikin  kwantar da murya tace,”Hayatee nah”.

Idonsa ya ɗago ya kalleta kana yace, “ya dai sweet nah”.

Sai da ta kwantar da kanta ajikinsa kana tace, “dama-dama amma kayi haƙuri ba dan na ɓatama zanje ba please Hayatee ka fahince ni”…tana faɗa kamar zatayi kuka.

Kallon ta yayi kana yace, “inajiki ki faɗa zan fahinceki.

Murmushi tayi haɗe da kai masa kiss agoshi kana tace, “ina son naje gida na faɗama Iyayena zan kuma hostel da zama kaga sai na dawo nacigaba da zamana anan hankali kwance,amma fah acan zanyi weekend,amma sai ina ka yarda”…tafaɗa haka kamar da tsoro aciki.

Sai da akayi ƴan seconds  kana yace, “banyarda har kiyi  weekind ba sai dai kije da safe da yamma ki dawo amma ban amince kije har kiyi kwana biyu acan ba”.

Haƙuri ta fara bashi haɗe da masa alƙawar idan zaije Plateau zata rakashi ,dan kwannan zaiyi tafiyar dan awajan akinsa aka turashi can dan yayi wani bin cike,kodama yace zai je da ita amma bata amuntaba saboda  alokacin ne zasu fara exmas amma yanzu ta amince masa…..to kuma bansan wani za’ayiba tsakanin exmas da tafiya.

Da safe da zai fita aiki ya ajeta kan hanyar gidan su,itako ta ƙarasa da ƙafa dan banisa da wurin da ya aje ta.

Da sallama ta shiga aikuwa ƙanninta najin muryar ta suka fara mata oyoyo,sosai suka ji daɗin gani Yayar tasu.

Bayan sun gama gaisawa da ƙanninta kana ta ƙarasa wajan iyayinta wanɗanda tunda ta shigo gidan fara’arsu ta bayyana musamman Abbanta.

Gaishesu ta farayi suka amsa ciki da kulawa da son ƴar tasu ƙwaya ɗaya mace.

Bayan sun gama gaisawa suka shiga firar yaushe gamu haɗi da basu labarin karatunta.

Sai da fira tayi daɗi take gaya musu zata koma hostel da zama saboda yanzu karatunsu ya ɗau zafi kuma tana buƙatar tana tsu tayi karatu.

Sosai iyayinta suka gamsu da abunda tace kuma suka amince mata da haka.

Dan haka tace musu zatayi weekind anan sai Monday ta tafi ,amma data tafi sai bayan exmas zata  dawo.

Ba abunda suka ce da ita sai fatan alhairi.

Bayan sungama fira da ita tashi tayi taje ɗakin da ya ke mallakin tane dan tana son ta ɗan huta dan jiya bawani barci yabar ta tayi ba,dan iya wuya yabata.

Tana shiga tayi kwanciyar ta dan ɗakin ko da yaushe Mama sai ta gyarashi sosai,dan haka bashi da wani datti.

Bata jima da kwanciya ba, bacci yayi awun gaba da ita.

Tajima tana bacci dan ko sallah bawace tayi tsaka nin azahar da la’asar dan ita Mama ta ɗauka ɗiyar ta ta na fashin sallah shiyasa bata tashe taba.

Aikuwa ba ita ta farkaba sai biyar saura,lokaci taga yatafi dan haka da sauri ta tashi taje tayi sallah.

Da dare har ta kwanta dan tana son tayi bacci da wurin dan ta tashi da wuri,sai ga wayar ta tafara ƙara,ɗan tsaƙi ta ja kana ta ɗauko wayar daniyar ta kashe,sunan da taga yana yawo saman screen ɗin wayar ne yasa da sauri tayi picking ďin call ďin haɗi da faɗin, “Hayateenah”.

STORY CONTINUES BELOW

Ba abunda yace da ita sai ki fito gani aƙofar gidan ku.

Lokaci ɗaya jikin ta ya ɗau karkarwa muryar ta na rawa tace,”kayi haƙuri yanzu Abbana yana gida kuma bazai barni ba”.

Tsawa ya daka mata yace, “minti biyu nabaki kifito dan bana son yawan magana”.

Haƙuri ta fara bashi kafin  ma ta ida faɗa har ya kashe waya sa.

Jikinta na karkarwa ta ɗau hijab tasaka kana tayi ɗakin Mamar ta.

Da sallama ta shiga tace Mama zanje gidan su Safiya na karɓo wani book ɗina ina son karatun shi a daren nan”.

Mama tace, “a’a ba zaki jeba kibari nasa ƙaninki yaje ya karɓo, amma bake ba”.

Mama  tana ce baza taje ba ita ko Hafsa tana ce sai taje dan har kuka sai da tawa Mama.

Itako Mama tace taje amma da ƙaninta zasuje,ban dan  taso ba haka ta aminta tace tayar da suka fita ita da ƙaninta Marwan.

Har zasu fita tace, “Marwan kaje ɗakin ku ka kwanta dan naga bacci kakeji”.

da yake ɗakin nasu asoron gida yake.

Yace, “eh Aunty bacci nakeji”.

Sai da tabari ya shiga ɗakin su kana ta fito ta sameshi amota.

Ahankali ta buɗe marfin motar ta shiga,haƙura ta bashi na jimawar da tayi bata fito ba.

Komai bai ce mata ba yaja wota jikinsa ya fara kissing ɗinta haɗe da sanya hannusa cikin rigar ta yana shafar dukiyar fulanin  ta,sosai yayi romance ɗinta acikin motar kan ya ƙyaleta.

Wayar sa ya ɗauko ya shiga gallery ya kamu wani videos yayi playing ďin ɗaya yaba ta yace ta kalla yadda sukeyi haka zata mishi yanzu.

Jikinta na karkarwa ta karɓa ta fara kallo,dan har tasu tayi masa magana taga ba fuskar yin haka ɗin.

Bayan ta gama kallon abunda ya bata itama tamishi yadda taga sunayi,sosai yake jin daɗin abunda take masa dan sun kusan kai sha biyu bai tafiba.

Kuka ta fara yi masa kana ya yarda ya ƙyaleta amma bandan ya gajiba.

Abunda yasu mata ya bata yace kafin ta kwanta tashi zata ji daɗin bacci.

Amsa tayi jiki na rawa tayi masa sallama ta shige gida.

Koda tashiga gidan Mama batayi bacci ba tana nan tana safa da marwa atsa kar gida.

Kallonta Mama tayi da kyau kana tace, “me ya tsaidaki?ina kuma Marwan yake?”.

Alamun rashin gaskiya suka bayyana afuskarta amma sai ta wayen ce tace,”Marwan ya shige ɗakin su yanzu,dan bacci ya fara shiyasa na kaishi ɗakin su.

Mama tace, “tau ina book ɗin da kika karɓo?”.

Jikin tane ya fara karkarwa sai kuma ta nuna mata ledar da ya bata tace, “gashi”.

Har Mama zata karɓa sai sukaji mutsin Abban Hafsa dan haka da sauri Mama tace ta wuce ɗaki dan bai masan ta fitaba.

Koda ta shiga ɗaki zama tayi tana mai dafe gaban ta saboda ta tsallake rijiya da baya.

Ledar da ya bata ta buɗe,kaza ce da wasu ƙwayoyi,kazar kawa tace ta aje ƙwayoyin dan tunda yake ba tasu bata taɓa shaba sai indai tana gabansa take sha,koshi dan bata son gani ɓacin ransa.

Da safe wajan ƙarfe goma bayan ta tashi daga bacci tayi wanka tana zaune tana shafe jikin ta da Vaselin,sai jin tayi ana mata sallama abakin ƙofar ɗakin ta.

Kanta ta ɗago dan taga wake mata sallama.

Aikuwa suna haɗa ido tace, “shin wai kece bangane muryar kiba?waya cemiki nazo hala ?”.

Tace, “amma kya bari ko gaisuwa muyi kafin ki fara jerumin wannan tambaya.

Kallon ta safiya tayi tace,”yaushe kika dawo gida ai na ɗauka kin tare ne gabaki ɗaya a gidansa”.

Sai da Hafsa tama ta kallon sama da ƙasa kana tace, “zan dai tare dan ko yanzu weekind ne nazu nayi natafi  sai wanda yagani bari ya yaɓamin magana.

Safiya tace, “har yanzu bazan gaji da baki shawara ba,kice inda gaske yake yana sonki ya fito kuyi aure abunda yafi kenan dan wallahi ni ke nake tausayi nan gaba.

Aikuw rigama sukayi sosai dan duk lokacin da zasu haɗu da Safiya haka ne dan ita Safiya ba abunda ta tsana kamar yadda ƙawar ta kebin *UMARNIN SAURAYI*…..

Wacece Hafsat?.

Alhaji Usuman haifaffin ɗan garin sokoto ne shi ne mahaifin Hafsat, matar shi ɗaya Hajiya Fatima mutanene musu haƙuri da jama’a dan tunda suke ba’ataɓa jin su  ba,bare da maƙutan su, kowa lafiya suke dashi sai wanda ba’arasa ba.

+

Suna da yara shidda maza biyar mace ɗaya.

Hafsat itace ƴarsu ta fari kuma ita kadai ce mace,ta taso cikin gata da tarbiya mai kyau, yarinya ce mai natsuwa da kamun kai,sosai takeba mutane girman su,bata damu da kowa ba dan ko tarin ƙawaye batayi sosai mutane ke ganin girman ta,tana da ilimin addini dana zamani dai-dai gwar-gwado.

Tuntashin ta ƙwarta ƙwaya ɗaya ce ita ce Safiyya, koshi abunda ya ƙara ƙarfafa ƙawan cin su saboda school ďin su ďaya da Safiyya.

Sunyi primary school da secondary school duk atare kuma class ďaya islamiya ma haka,dan shi suka shaƙu sosai dan idan ka gansu zakace ƴan  gida ɗaya ne,ko kayan sawa iri ɗaya ake musu sosai suke son junansu.

Lokacin da suka gama secondary school gidan su safiyya ba’abarin yaro ya ƙara gaba sai yayi aure amma saboda Hafsat zata ciki gaba Baban Safiyya yace ya barta itama sutafi tare.

Ba’a ɗau wani lokaci ba aka samar musu admission a Usumanu ɗan Fodiyo Unversity,sokoto.

Inda kowa ce burinta ta zama doctor ta mata, dan ta taimakama ƴan wunta mata,kowa ce  shine burin ta.

Haka suka ci gaba da karatu cikin kwanciyar hankali ko wace na karatu dai-dai gwargwado.

Bawata matsala akaratun su har suka kai UG 3 going to   4 Hasfat ta haɗu da Jawad,sosai ya nuna so gareta amma taƙi kulashi,ya sha wahala kafin ta kulashi dan yana nuna mata so bana wasa ba har ita Safiyya takan mata faɗa akan ta daina masa haka ta kulashi ko kaɗan ne.

haka dai aka samu ta fara sake masa fuska har soyayya ta kullu tsakanin su mai tsanani.

Abun har mamaki ya dawo ba Safiyya dan yanzu yadda Hafsat ke nuna ma Jawad so abun yana bata tsoro.

ana cikin haka ya kwanta ciyo sosai yake jin jiki dan haka Hafsat tagaya ma Safiyya tace ta raka ta su dubashi gidan sa.

Da ƙyar Safiyya ta yarda zata je duba sa.

Bayan Safiyya ta amince Hafsat takira shi tace za su zo duba shi.

Address ɗin gidan ya basu yace sai sun zo.

Bayan sun zo school sun gama lecture safe suka kama hanyar gidan sa dake arƙilla.

Basu sha wuya ba wajan gane gidan,dan maƙocin sa sanan nene agarin sokoto.

Tunkafin su ƙarasu ya faɗama maigida zaiyi baƙi dan haka suna ƙarasuwa maigida ya kaisu har part ɗinsa.

Godiya sukayi ma maigadi kana suka ƙarasa ciki.

STORY CONTINUES BELOW

Kwance suka same shi anɗaura masa drip a hannun sa.

Da sauri Hafsa ta ƙarasa gareshi,irin yadda ta ganshi ai bata san lokacin da tafara hawaye ba.

Alama yayi mata da hannu ta daina kuka ,amma sai ƙara kukan takeyi.

Safiyya ce tayi mata magana tace ita kam sauri takeyi dan haka ta daina kuka su gaisa su wuce gida.

Dakyar ta daina tayi masa yajiki,Safiya ma ta masa kana suka ɗan zauna kaɗan har drip ɗin da aka sama sa ya ƙare,Hafsa da kanta ta cire masa kana sukayi masa sallama suka wuce gida ba dan ran Hafsa yasoba.

Bayan kwana biyu da zuwan su takira sa tayi masa ya jiki   yace jiki da sauki amma har yanzu bai daina shan drip ba.

Sosai ta tausaya masa har tace zata zoko da yamma ne idan sun gama lecture.

Haka kuwa akayi tace Safiyya ta rakata tace itakam bazata koma dubin saba tunda taje.

Komai Hatsat bata ce da itaba dan ranta ya ɓaci akan abunda Safiyya ta mata dan haka tace ita sai taje amma idan taje gida ta faɗa musu sai yamma zata dawo dan tana da  lecture ƙarfe huɗu.

Komai Safiyya bata ce da itaba kowa ya kama gabansa.

Ita Safiyya tayi gida ita ko Hafsa tayi gidan saurayin tah.

Koda taje doctor na duba shi har yana bashi shawara yarinƙa cin abinci kuma ya rinƙa shan magani.

Bayan doctor ya fita Hafsat ta ƙarasa gareshi kamar zatayi kuka tace, “yanzu Hayat baka cin abinci,to ya kakeso nayi, ko so kakeyi na kwanta?”…..tana faɗa tana fitar da ƙwallah

Ahankali ya taso daga kwanciyar da yake kana ya ƙarasu gareta, handkerchief   ya bata dan ta goge hawayen ta.

Bayan ta gama kana yadube ta da kyau yace,

“My sweet heart,bawai bana son cin abunci bane, a’a  abinci sayarwa ne bana so koda na hotel ne, shiyasa ban cika cin abinci ba”.

Kallon sa tayi da kyau kana tace,

“yanzu meza kaci?”.

Yace, “zan sha lemo sai nasha magani dan bazan iya dafa wani abinci ba bare nadafa”.

Tambatar sa tayi inada kitchen yake ya nuna mata bata ce dashi komai ba, ta tashi tashiga kitchen ɗin ta kunna gas ta ɗura masa jallof ďin taliya wadda taji kayan haɗi.

Tana cikin aikin ya shigo,bata masan ya shigoba dan baka jin mutsin ma tafiyar sa har yazo kitchen ɗin.

Tunda ya ƙarasu ya ƙife bayan ta da kallo yana ayyana wani abu aransa.

Kamar ana kallonta taji dan haka da sauri ta juyo dan taga wake kallonta.

Ido biyu sukayi dashi da sauri ta ɗauko mayafinta dan tasaka amma yayi sauri ya rikeshi kana yace,

“miye afanin rufewa tunda watarana yazama mallaki na” yana faɗa yana kashe mata ido ɗaya.

Komai bata samu damar cemasa ba ya umarce ta data cigaba da akinta.

Yana zaune yana kallonta har ta kammala ta zuba masa yaci,amma yace sai tare za lsuci tace sauri takeyi ta koma gida yace duk batare zasu cibashi bazai ciba.

Da kyar ta yarda ta zauna sukaci.

Bayan sun kammala ta ɗauko maganin sa tabuɗe ta bashi,yasha kana tayi masa sallama tace zata wuce.

STORY CONTINUES BELOW

Har takai ƙofa ya ce gobe tazu har tace ba zata zoba yayi kamar yayi kuka, da taga haka tace masa zata dawo.

Haka Hafsat taci gaba da zuwa wajansa har ya samu sauki.

Ranar koda taje yayi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya yayi kyau sosai, gashi abu ga mai kyau jinin fulani gashi kuma nira ta zauna masa.

Tunda ta shigo suka kife junan su da wani kallo mai wuyar fassarawa haɗi da sakarma ko wane murmushi mai ciki daso da ƙauna.

Alamu yayi mata data ƙaraso.

Ba musu taje gareshi,tasowa yayi daga wajan dayake zaune yazu daf da ita.

Kallonsa tayi haɗe da gaidashi ya amsa jikin sa duk akasalan ce.

Tashi yayi ya ɗauko mata ruwa haɗi da wani lemo mai haɗe da wata ƙwaya wadda shi ka dai yasan ko tame cece.

Zuba mata yayi tasha aikuwa tunda tasha ta farajin wani sauyin yanayi ajikin ta, lokaci ɗaya wata muguwar sha’awa ta taso mata.

Shi kuwa tunda tasha lemun yake binta da kallo har yaga maganin da yasa ya fara aiki ajikin ta lokaci ɗaya.

Akuwa lokaci ɗaya ya fara shafar jikin ta haɗi da yima ta kalamai masu kashi jiki,yana yadda yaso da ita haka yaci gaba da romance ɗinta har ya samu ya rabata da mutun cinta.

Koda maganin ya sake ta tayi kuka har tagaji kuma ta jefeshi da miyagun kalamai sosai ya

ji zafin kalaman ta.

Amma ya dake yaci gaba da bata haƙuri,amma ko kallo bai isheta ba.

Haka tasanya kayanta tayi tafiyar tagida.

Aikuwa tun daga ranar duk wata hanyar da zai ganta ta rufeta,shiko duk inda yasan zai ganta yaje amma bai gantaba haka har ya haƙura,ranar yana kwance yara sa miya ke masa daɗi agarin sokoto dan har yayi niyar ya bar garin ya koma garinsu ,sai wata dabara ta faɗu masa lokaci ɗaya yamike yaje wajan wata abukiyar karatun Hafsat ya gaya mata abunda ake ciki kuma ya bata kuɗi masu yawan gaske yace idan

ma tashirya su abunda zai bata sai tayi mamaki.

Sosai Hajara ta ruɗe dan haka ta ɗau alƙawarin ko ta halin ƙa-ƙane sai ta kawo masa Hafsat.

Aikuwa tun daga lokacin Hajara ta liƙema Hafsa duk inda Hafsat take Hajara na can,dan shi Safiyya ta jama Hafsat baya dan Hajara kowa yasan taba yarinyar kirki ceba.

Watara na suna fira da Hajara sai ta ɗauko mata labarin Jawad da rashin lafiyar da yayi yanzu haka yana kwance ba shida lafiya sosai.

Duk da abunda tafaɗa ya dake zuciyar Hafsat amma tadake bata cema Hajara komai ba.

Sai ma magana tama ta akan ta daina yi mata maganar sa dan har da faɗa sai da sukayi kafin su rabu.

Dare nayi Hafsat ta kasa kwanciya ba abunda take tunani saishi,sosai ta matsu safiya ta waye taje gidan sa taganu ko yaya tashi.

Tun shidda da rabi ta fito daga gida ta kama hanyar gidan sa.

Koda taje sai da ta musu knocking a ƙofar gidan maigida ya buɗe ƙofa ya fito.

Gasheshi tayi kana ta tambaye shi ko Jawad nanan.

Yace baya gari dan ya kwana biyu baya nan,sosai taji zafin rashin samun sa dan yanzu wani son shine takeji wanda ji take idan bata ganshi ba zata iya mutuwa.

Godiya tama Baba maigida kana ta kama hanyar makaran ta.

Har akatashi shoocl bata ga Hajara ba kuma duk inda tasan zata ganta taje amma bata same taba.

Ba ƙaramin tashin hankali ta shigaba lokacin da takira wayar Hajira akace kashe take.

Alokacin duk wanda ya ganta yasan bata cikin natsuwar ta.

Danhar Mamar ta ta tambaye ta amma sai tace wata exmas ce za suyi mai zafi shiyasa take jin tsoro.

Addu’ar samun nasara Mamar ta tama ta haɗi da bata shawara.

Dadare tana kwance ta kuma gwada kiran Hajara tace ko zata samu,aikuwa cikin sa’a tana kira tafara ringing.

Ringing da bai wuce uku ba Hajara ta ɗauka tace,

“Ya aki ciki ne Hafsat?”.

Sai da Hafsat ta sauke ajiyar zuciya kana tace, “kina ina yanzu?”.

Kai tsaye tace, ina layin bugi”.

Sai Hafsat tace, “Subuhanallah, miyakai ki layin bugi kuma?”.

Sai Hajara tace, “tambayana kikayi nabaki amsa,dan haka bana sun dugon surutu”.

Sai Hafsat tace, “kodama numbar Jawad nake son ki bani idan kina da ita ko kimin misalin wajan da zan samun sa”.

Aikuwa Hajara najin me tace ta bushe da dariya haɗi da cewa,”komai kikeso nabaki ki sameni wajan da nafaɗa miki yanzu nabaki abunda kike so”.

Duk da dariyar da tasa mata tayi mata zafi amma sai ta dake tace, “dan Allah Hajara ki bani wallahi bazan iya zuwa layin bugi ba,bare yanzu da dare”.

Sai Hajara tace, “tunda abunda kike nema bai dameki ba sai anjima”.

Har zata katse waya sai Hafsat tace,”zanzo ki gayamin dai-dai ina zan sameki.

Tace, “dakin zo kikirani zan fito”.

Tace kada ki kashe waya gani zuwa.

“Aa bazan kasheba”.

Aikuwa suna gama waya jikinta har rawa yake ta shiyar taje ɗakin Mama tace zataje gidan su Safiyya ta karɓo jikarta dake hannuta dan karatu zatayi.

Mama tace to taje amma kar tajima.

Tana fita taje bakin ti-ti ta tare mai adai-daita ta faɗa masa sunan inda zai kaita.

Bayan ƴar tafiyar da sukayi ya kaita wajan, tun abakin wajan zaka fara ganin mata da maza suna kai kawo kuma dukkan su ba mai shigar kirki.

Gabanta ne ya fara faɗuwa har taso ta juya kuma ta fasa.

Waya ta ɗauko takira Hajara tace gata nan ƙarasu.

Bata jima da kiran  Hajara ba ta ƙarasu cikin wata shiga kace ita ba ƴar muslmiba……

Shigar da Hajara tayi Hafsat tabi da kallo har ta buɗe baki zata yi magana sai Hajara tace, “zo muƙarasa daga ciki kina tawani kallona sai kace yau kika fara ganina”.

+

Sai Hafsat tace, “ni kawai kibani abunda nice dan bazan iya shaga wannan wajanba”.

Wani kallo Hajara tabita dashi kana tace, “abunda kike nemane bai dame kiba dan haka kinga tafiya ta”  tana faɗar haka takama hanyar zuwa inda tafito.

Da sauri Hafsat tabita tana  kiran sunan ta amma sai tayi kamar bata san da ita.

Ɗakin da taga Hajara tashiga nan  ta fara ƙuƙarin shiga,warin wiwi da sigari ne suka bige hancin ta,aikuwa lokaci ɗaya taje da baya,dan bazata iya shaga ɗakin ba.

Wayar ta ta ɗauko ta sake kiran Hajara tace,

“Hajara gani ƙofar ɗakin da kika shiga, dan Allah kifito ki bani”.

Wata tsawa Hajara ta daka mata kana tace,

“Idan bazaki shigo ba kina iya tafiyarki”.

Wani maƙaƙi ya rufe mata zuciya har taso ta tafi sai kuma wani abu ya taso mata wanda ita kanta bata san ko nameye ba.

Sai da ta ɗauke sheɗar ta kana ta buɗe labulen ɗakin ta shiga.

Abunda tagani ne yayi matuƙar bata tsoro da mamaki.

Dan gabaki ɗaya  ɗakin maza da mata ne,kuma ba mai shigar kirki a cikin su.

Sosai abun yaba Hafsat tsoro dan kowane namiji rungume yake da mace.

Dan ko Hajara kwance take ajikin wani sugar boy daga ita sai wata vest mai haɗe da brazier wadda ta bayanar da surar jikin ta sosai.

STORY CONTINUES BELOW

Wani kallo tabi Hafsat dashi kana tace, “kin tsaya ma mutane akai, in bazaki shigo ba saiki tafi”.

Hafsat tace, “Hajara dan Allah kibani wallahi sauri nakeyi”.

Batari da ta kalle taba tace “gashinan zuwa yace ki jirashi”.

aikuwa tana cewa haka sai wannan sugar boy yayi sauri yace ashe itama ƴar hannuce to abamu muɗana” yana faɗa yana kallon Hafsat wadda ta haɗe fuska sai kace akwai wanda ya tilasttamata zuwa wurin

Hajara hara zata buɗe baki tayi magana sai wayar ta tafara rura.

Ɗauka tayi haɗe da faɗin “ka ƙarasu?”.

banji me akace ba a ɗayan ɓangarin iya dai tace gatanan zuwa.

Kallon Hafsat tayi dake durƙushe a ƙasa tace, “kizo muje”daga haka bata sake magana ba ta fice warta.

Itama Hafsat da sauri tabi bayan ta.

Wajan wata mota tanufa itama Hafsat tabi bayan ta.

Aikuwa suna ƙarasuwa wajan motar sai sukayi ido biyu da Jawad, lokaci ɗaya wani sanyi ya ziyar ci zuciyar ta ai bata san sanda ta faɗa jikin saba tana sauke wata sassanyar ajiyar zuciya.

Jikin sa ya matse ta yanajin wani abu a zuciyar sa.

Gaba ɗaya ya manta da wata Hajara dake tsaye sai datayi gyaran murya kana ya ɗago da idanun sa waɗan da suka fara sauyawa zuwa launin ja.

Tace, “kizo muyi magana dan sauri nakeyi jirana ake”.

Raba jikin sa da Hafsat yayi kana ya dube ta yace, “tabari na zo”.

Nesa kaɗan da ita suka yi kana Hajara ta dube shi tace,

“Nagama aikina dan haka kabani abunda kace”.

Tun bata rufe baki ba ya ɗauko wasu kuɗi masu yawan gaske ya bata,aikuwa tana gani yawan kuɗin da yabata bakin ta ya kasa rufuwa sai godiya take zuba masa dan har jikin sa tasu tafaɗa ya ɗaga mata hannu alamar kada ta soma,sosai tayi masa godiya kana ta buɗa baki tace,

” duk akan Hafsat zaka bani wannan kuɗe,sai yanzu na tabbar da son da kayi mata mai yawan gaske ne,amma bari gaji yadda nayi nasamu kanta”.

Karasuwa tayi gab da kunnin sa kana ta faɗa masa wata magana.

aikuwa tana gama faɗa masa ya bita da wani kallon mamaki kana yace,

“Amma gaskiya banji daɗin haka dakika yimin ba” har ya buɗa baki zai sake wata magana sai ga Hafsat ta ƙarasu wajan da suke jikin ta na karkarwa tace musu gida zata koma dan Mamar ta har takirata a waya.

Sallama yayi da Hajara kan sai yakira ta,kana ya dau Hafsat ya kaita gida.

To tun daga wannan lokacin duk abunda yace da Hafsat bazatayi masa musuba,sai wani sonshi da kaunar sa da suka addabe ta wanda yasa takejin zata iya rabuwa da kowa akan sa.

Wanda a halin yanzu ta koma kamar matar sa, dan sai yadda yace da ita….

*Cigaban labari*

Bayan Safiyya ta fita taci gaba da shirin ta bayan ta kammala tafito domin ta gaida iyayanta.

Bayan ta gaishe su kana tayi beark bayan ta kammala Mama ta dube ta  tace,

“Hafsat anjima zan aikeki gidan Hajiya tah ki ƙarɓomin saƙo daga can ki gaya mata zaki koma makaranta sai kun gama jarabawa”.

Tace, “tau Mama Allah ya kaimu ajima lafiya”nan suka cigaba da firar su.

Suna cikin fira wayar ta tafara rura,sunan da taga ya baiyana saman screen ɗin yasa da sauri ta saka wayar slient,sai da ta tsinke kana tayi sauri ta mike taje ɗakin ta haɗe da cema Mama tabari tazo Safiyya ce zata gayama sunan wani book wanda zata nemu mata shine zata je ɗaki ta dubu dan yana cikin jikar ta kuma ta manta sunan shi.

Komai Mama bata ce da itaba har ta fice.

Tana shiga ɗakin ta ya koma kira,da sauri ta ɗauka haɗe da faɗin “Hayateey kayi haƙuri wallahi muna tare da Mama ne shiyasa ban ɗauka ba” yadda ta ke maganar kamar tana gaban sa.

Yace, “naji amma anjima zaki dawo ko?”.

Cikin muryar rarrashi tace, “kayi haƙura zuwa Monday na dawo, dan anjima Mama tace zata aikeni shine ma nake sun nakiraka na faɗama kayar da naje?”.

Ata ƙayce yace, “ban aminta ba kuma anjima nake son ki dawo dan ina buƙatar ki” yana kai ƙarshin zancin ya datse kiran bata ri da yaji me zata ceba.

Wayar dake hannuta ta fara kallo dan ita bata ma san me zata cewa Mama ba.

Dabara ce ta faɗu mata dan haka ta hau gado tayi kwanciyar ta har lokacin da za’a aikin ta yayi.

Kiran ta Mama ta farayi amma tanaji taki ta karɓa har Mama tagaji ta shigo ɗaki.

Tasheta Mama ta farayi dan a tunanin ta bacci take bata san ko idon ta biyu ba,tayi hakan ne dan kada taje aikin da za’ayi mata.

Kanta ta ɗago kamar mai bacci gaske Mama tace,”Hafsat ki tashi kije rana tafito sosai kinji”.

Magana tayi mata cikin muryar marasa lafiya tace, “Mama kiyi hakuri ki aike su Marwan wallahi kaina ke ciyo” ta faɗa haka kamar tayi kuka.

Sannu Mama ta fara jeramata haɗi da kawu mata magani dan tasha.

Aken da bata zoba kenan sai da Mama takira Abban su Hafsat tace masa yayi mata izine taje wurin Hajiyar  ta karɓu saƙo.

Aikuwa Mama nafita Hafsat tamiƙe kamar ba itace ke sheɗa ɗaya-ɗaya ba.

Koda Mama ta dawo Hafsat tace taji sauki dan kan ya daina ciyo.

Dare nayi ta fara tunanin yadda zata cewa Mama zata tafi makaranta.

Dan ya da meta da kira kuma ta rasa yazata cewa Mama.

Wanka tayi ta shirya ta kama hanyar ɗakin Mama dan ta gaya mata zata koma makaranta…..

* Labulen ƙofar ta yaye kana ta shiga ɗaki.

+

Saman sallaya ta same Mama dan haka ta ƙarasu a hankali ta samu wuri ta zauna, tana jiran Maman ta shafa.

Bayan Mama ta shafa itama Hafsat ta shafa haɗe da gaishe da Mamar ta.

Bayan Mama ta amsa sai Hafsat ta ɗago da kanta tace,

“Mama yanzu abukiyar karatuna takirani tace Malamin mu ya bada wani Asignment tun jumu’a  bayan fitowarmu kuma yace Monday za’ayi summiting kuma ni ban masaniba sai yanzu kuma yace a makin test ďin mu ne,kuma rashin insa gareni babbar matsala ce”.

Sai data kai ƙarshen zance Mama ta ɗago kaita dubeta kana tace, “kina nufin yanzu nabarki kije?”.

kai ta ɗagama Mama alamar “eh”.

Sai Mama tace tare da Safiyya zaku je?”.

Sai Hafsat tace, “a’a Mama kinsan ba department ɗin mu ɗaya da itaba.

Sai Mama tace, “to gaskiya Hafsat abar wannan tafiya har dasafe ” har zata koma wata magana saiga Abban Hafsat yadawo daga masallaci.

Bayan ya shigo ya zauna sungama gaisheshi kana Mama tayi masa bayanin da Hafsat tamata,kuma tafa ɗamasa yadda tace da Hafsat.

Bayan ta gama yace, “aa bazamu hanamata zuwa ba, kuma kin san yanayi karatun da takeyi yana bukatar kula sosai dan haka tashi ga kuɗi kije kinji ƴar Abba”.yana faɗa yana dubanta.

Sai Mama tace “kafison ta tafi”?.

Yace, “eh haka yafi abunda nakeso shine muyi mata fatar alhairi”.

Bayan Abba yabata kuɗi ta ɗau kayan ta tayi musu sallama tafice.

Bayan fitarta Mama ta dube Abba kamar tayi kuka tace’ “masa ita yanzu karatun Hafsat bata sonshi dan gabanta na yawan faɗuwa akan karatun Hafsat shiyasa yanzu bata da wata natsuwa akanta.

Sosai Abba yayi mata magana kan ta aje wannan maganar gyafe kwai suy mata fatar alhairi.

Tana fita takirashi tace ina yake gata tafito.

faɗa mata wurin yayi,taje tasa meshi.

Tana shiga motar shiko yaja suka tafi.

Ti-ti taga ya miƙe yana ta tafiya dan ba hanyar gidan sace yabi ba,dan haka ta juyo ta dube shi tace,

“Hayat naga sai miƙi ti-ti kakeyi hala ina zamuje?”.

Batare daya dubetaba yace “Zamfara”.

Tace, “Hayat yanzu da daren nan”.

Yace, “eh yanzu nake da ra’ayi zuwa,inbazaki je ba na saukeki”.

Tace, “aa kayi haƙuri in na ɓatama”.

Bai sake ceda ita komai ba har suka isa Zamfara.

Hotel suka sauka ɗaki ɗaya ya kama musu,bayan sunyi wanka sunci abinci wasu kayan bacci ne ya bata ya umarce ta data sa,jikin ta narawa ta saka su,dasu da babu duk ɗaya suke ajikin ta.

Jikinsa ya jawota ya rungume ta haɗi da shaƙar ƙamshin jikin ta, lokaci ɗaya ya fara romance ɗinta.

Hannunsa yasa cikin rigar ta ya fara shafar duk wani ilahirin sassan jikin ta.

Sosai take jin daɗin abunda yake mata dan haka ta ba da kai sai yadda yayi da ita,sosai yabata wuya adaren, dan ba su suka kwanta ba sai biyu saura.

Kuma asuba nayi tafarka tayi sallah kana tazo ta kwanta.

Shima yana gama sallah ya kwanta haɗi da jawo ta jikin sa,romance ɗinta ya fara,duk da yanzu bata so saboda jiya ba ƙaramar wahala ya bata ba amma bazata iya ce masa bata soba,dan kar ransa ya ɓaci.

Sai bakwai da wani abu ya barta kushi ba dan ya gaji ba sai dan meeting  ɗin da yake dashi 7:30.

Wanka yayi kana ya shirya yayi beak yayi mata sallama ya tafi yace sai ya dawo.

A dawo lafiya ta masa haɗi da addu’a,sai kace mijin ta😉.

Yana fita tayi wanka ta shirya tabi lafiyar gado dan bacci ne a idon ta sosai.

Haka suka cigaba da zama garin Zamfara har kwana biyar.

Zaune suke saman kujera ita dashi sai wayar ta tafara kaɗawa,har taso taƙi ɗauka kuma sai ta ɗauka,tana karawa kan kunnin ta ba abunda aka fara ce da ita sai, “kina ina?”.

Sai Hafsat tace, “ina ruwanki da inda nake”.

Sai Safiyya tace, “to wallahi bari kiji yau zuwa gobe na baki, duk inda kike ki dawo,kuma inba haka ba zanje gida na faɗamusu abunda akeci dan nagaji da ganin ki cikin wannan muguwar rayuwa.” tana faɗar haka ta datse kiran saboda wani kukan baƙin ci dayazo mata.

Tana kuka tana faɗin “me Hafsat tanema tarasa da zata rinƙa bibiyarsa kamar mijinta”.

Kuka tashiga rerawa sosai kamar ta cire zuciyar ta tajefar saboda baƙin ciki,kuma ba abunda yafi ƙuna mata rai gashi yanzu saura sati ɗaya afara exmas amma ita Hafsat ba itace gaban taba.

Tunda suka gama wayar da Safiyya jikin tane yayi sanyi sosai,kan ta taɗago ta dubeshi dan shima ita yake kallon  kana ta buɗe baki tace, “Safiyya ce takirani,har tana yimin barazanar zata faɗima su Mama bana schoocl,kuma nasan tunda tace zata faɗa to sai ta tafaɗa,dan Allah kayi hakuri mukoma dan nasan halin Abba ko kasheni zai iyayi”.

Tafaɗa haka hawaye na fita a idonta.

Haɗi fuska yayi haɗi dagoge mata hawayen dake fita a idonta kana yace,

Dan takiraki ta gaya miki haka shine harda wani tada hankali, aikinsa duk bazata faɗa ba saboda tana faɗa za’a dakatar da karatun ku, kuma ai zata fiki jin haushi tunda tafiki son karatun”.haka yaci gaba da yi mata faɗa da daɗin baki ƙarshema ya umarce ta data kashe wayarta dan ko ankuma kira baza’a samuba.

Dan yace bazaiyi komaiba sai yagama aikin da ya kawoshi.

Tun daga lokacin Safiyya ko takira wayar Hafsat kashe take,sosai hankalin ta ya ƙara tashi dan har gidan sa taje amma mai gida yace yayi tafiya,gaba ɗaya ta rasa natsuwar ta har dai lokacin da Mamar Hafsat takirata tace takira wayar Hafsat kashe ko lafiya take?.

Tace eh karutu ne yayi mata yawa dan har sako tabani na faɗa muku to nima ban dawo ba saboda  hostel nake kwana.

Aikuwa Mamar Hafsat najin tare da  Safiyya suke ta samu natsuwa kana tayi musu fatan alhari…..

Bayan ya kammala abunda zai kaishi suka dawo gida da sati ɗaya taneme ya barta dan taje school  dan Monday za su fara exams.
+
Yace ta shirya ya kai ta amma kafin ya dawo gida ta tabbatar da tadawo dan baya son yadawo babu abunda zaici.
School ɗin ya aje ta kana ya ƙarasa wurin aikin sa.
Class ɗin su taje bata jima da zuwa ba aka fara lectura.
2 dai-dai suka gama lectures ďinsu,kuma suna fitowa bata tsaya komai ba ta kama hanyar fita.
Har zata fita daga cikin makarantar sai Safiyya ta ganta tana ta sauri,da saura Safiyya tayi ƙarasa gare ta.
Mayafin ta ta riƙo,lokacin da take daf da fita school ɗin.
Safiyya tace, “ina zakije dakike ta wannan sauri haka?”.
Kallon sama da ƙasa tayi mata kana tace, “wurin da kika aikeni zan je” tana faɗa tana hararar ta.
Sai Safiyya tace, “koma dai me yau ba inda zaki dan Mama na can hankalin ta tashe tana sun ganin ki dan haka yau gida zamuje ta gannki ko tasamu natsuwa”.
Hafsat tace, “Safiyya har sau uku taki ra sunan ta, bana son kina shiga rayuwa ta Safiyya kirabu dani nayi rayuwata,ki barni rayuwar ki ko tawa? kuma bazan je gidan ba inki haihu da uwarki kije kifaɗa ɗin ina gidan saurayi na”.
Tana faɗar haka ta kama hanyar fita ta bar Safiyya sake da baki tana kallon ikon Allah.
Har zata fice sai ta dawo,gaban Safiyya ta ƙarasu kana tace, “daga yau kada ki kara shiga rayuwa ta dan ni tunda jimawa nafitar dake rayuwa ta dan haka kema ki barni bana son sa idon”.
Mai adai-daita ta tara kana ta faɗa masa unguwar da zai kaita.
ita ko Safiyya gaba ki ɗaya mamaki da tsoro sun da baibaye zuciyar ta,dan gani take kamar ba kai sake Hafsat ke gaya mata wannan maganar ba,amma a ko da yaushe tana wa Hafsat fatar shiriya itada kullihin musulmi.
Bayan ta dawo daga school wanka tayi kana ta gabatar da sallah sannan tazo ta fara gyaran gida,tana kammalawa ta ɗura sanwa.
Saura ƙiris ta kammala sai gashi yadawo,aikuwa tunda taji horn ɗin motar sa gaban ta ya bada dummmm,saboda bata kammala girgin taba kuma tasan halin sa sarai baya sun jira.
Tana cikin wannan tunani tafara jin knocking ɗinsa.
Da sauri taje ta buɗe masa ƙofa dan kar ta ƙara ma kanta wani laifi.
Ƙarɓar jakar dake hannun sa tayi haɗi dayi masa sannu da zuwa.
Karɓawa yayi haɗi da ƙarasuwa daga ciki.
Ruwan wanka ta haɗa masa,bayan yayi wanka ya fito, ta tayashi  shiri,bayan ya kammala shirinsa parlour ya fito dan yaci abinci dan ya kwasu yunwa yau.
STORY CONTINUES BELOW
Komai bai gani ba a dinning, dan haka ya ƙwala mata kira,ita ko tana can tana sauri taga komai ya kammala amma ina dan tana cikin haka taji yana kiran ta.
Da hanzari tazo gareshi,aikuwa tunda ta ƙarasu ya jefeta da wani kallo wanda yasa cikin ta juyawa lokaci ɗaya.
Tambayar ta ya farayi yace, “ina abinci na?”.
Jikin tane ya fara karkarwa tace, “kayi haƙuri nakusa kammalawa”.
Sai da yajefe ta dawani kallo kana yace, “sai yanzu kika dawo kenan?”.
Kai ta fara girgiza masa  tace, “a’a muna gama lectures na dawo wallahi ko ina banje ba”.
Tsawa ya da kamata haɗe da cewa karya kikeyi kin dai tsaya iskancin kine shiya sa baki dawo ba” nan ya dinga cin zarafin ta har da kukan ta tana bashi haƙuri amma yaƙi ko saurarin ta,daga ƙarshe ma key ɗin motar sa ya ɗauka yafi ce a gidan.
Har ya fita ya dawo ya ƙwala mata kira, da sauri tafito daga kiching haɗi da durƙusawa gaban sa.
Tun bata kai da durƙusawa ba yace ta haɗa kayan ta tabar masa gidan sa.
Aikuwa yana faɗar haka da sauri ta faɗa jikinsa tana bashi haƙura,amma ina baya ko saurarin ta dan da ƙarfi yajaye ta jikin sa ya kifeta da wani azaftaccin mari har guda biyu kana yace, “kuma wallahi kafin na dawo kinbar gidan nan tunda ba na ubanki neba” yana faɗar haka ya ficewar sa yana huci”.
Kuka takeyi kamar ranta zaifita dan ita ba komai yafi ƙona mata raiba irin yadda yace tabar masa gida, to ina zata je?.
Wani tunani ya faɗu mata arai aikuwa da sauri ta miƙe daga durkushin da take ta koma kiching taci gaba da aikin ta.
Bayan ta kammala girki, sosai ta fara gyaran gida,bayan ta kammala tasaka turare mai ƙamshin gaske wanda lokaci ɗaya yasa gida yabada wani ƙamshi mai sanyaya zuciya.
Toilet taje tayi wanka,bayan ta fito ta shafe jikin ta da ma yukka masu ƙamshi haɗi da hummara ta musamman,dressing ɗin english wears tayi masa wanda tasan yafi so sosai.
Tana gamawa ta ɗauko wasu turarukka ta feshe jikin ta dasu.
Tarigi ya ta ɗauru alwala,sallah magarb da isha’i ta gabatar kana ta fito parlour  ta zauna zaman dawowar sa.
Batayi minti biyar da zama ba sai ga horn ɗin motar sa.
Aikuwa da sauri ta ƙara  feshi jikin ta da turare haɗi da dauko lollipop tasaka a baki, ta fara tsutsu sai kace wata ƴar yarinya.
Bai ma tsaya wani knocking ba yasa key ya buɗe ƙofar.
Tsaye ya ganta tana masa murmushi haɗi dayi masa wani kallo mai ciki da so da ƙauna.
Jikin sa tafaɗa haɗi da faɗin “My Hubby nah, sannu da zuwa”.
Har ya buɗa baki yayi magana sai tayi sauri ta haɗa bakin sa da nata tana shayar da shi lolopop ɗin da ke bakin sa.
Aikuwa tuni jikinsa ya karɓi saƙon da take bashi haɗi da shaƙar ƙamshin da ke fita a jikin ta.
Bare abu ga ma abuci son ƙamshi,sosai ta mantar dashi fushin da yakeyi da ita,tsayowar ce ta gagaresu dan haka cak ya ɗauke ta zowa bedroom ɗinshi.
Sai da komai ya lafa kana ya jawuta jikin sa sosai kana yafara magana ahankali yace, “My love jibi ne ta fiyar dan haka ki kasan ce cikin shiri dan tafiyar safe zamuyi”.
Gabanta ne ya faɗi dan ita har ta manta da wata tafi ashe tafiyar na nan kuma gashi Monday za su fara exmas.
Jikin ta asanyaye tace, “Allah ya kaimu jibi lafiya”.
“Ameen” yace da ita haɗi da kai bakin shi da nata ya fara kissing ɗin ta.
Duk abunda yake mata bata wani jin daɗin sa saboda tunda yayi maganar tafiyar jikin ta yayi sanyi dan tunani take anya zata bishi tabar exmas ɗinta?kum gashi aski yazo gaban goshi dan daf take da ta kammala degree ta afannin gaenacology kuma da bata ci wannan exmas ba zasu iya withdraw  ďinta kuma gashi tana da carryover har guda biyu.
Suna cikin haka tace, “a’a gaskiya bazan jeba”.
Ahankali yace, “mikika ce?”.
Tace, “aa ba da kai naki ba”.
Yana gama shiri yafito dumin su tafi dan baya sun suyi rana.
+
Kiran ta ya farayi,ita ko tana can tana tunani ta tafi ko karta tafi,rasa me zatayi tayi,gashi tana tsoro rashin yin exmas ɗinta, kuma tana tsoron ɓacin ransa.
Kiran da taji yana mata yasa gabanta dukan uku-uku,alamun zai shigo ɗaki data ke ciki taji dan haka da sauri ta fara haɗa kayan ta cikin jikar da zata tafi da ita.
Koda ya shigo har tasa tufafin ta tana yafa mayafin ta,amma fuskar ta  a ɗaure kamar tayi kuka.
Magana yayi mata yace, “kefa nake jira”.
Tace,”nashirya mutafi” tafaɗa haka kamar tayi kuka.
Fitowa tayi ɗauke da jika a hannunta,jikin ta a sanyaye ta rasa ya zatayi,tana cikin haka taji yace, “muje zan kulle ƙofa”.
Fita tayi ya kulle ƙofa kana ya shiga mota ya tada.
Gabanta ne ya tsanan ta faɗuwa sosai, lokaci ɗaya wasu hawaye suka fara fita a idon ta.
Magana yayi mata yace ta shigo sutafi.
Kamar bata ji shiba tayi sai da yayi magana cikin faɗa-faɗa kana  tabuɗe motar tashiga tana mai saka kuka kamar wani yayi mata dole sai taje😏.
Aikuwa yana tada mota kukan da takeyi ya tsanan ta.
Dubanta yayi kana yace, “mi akayi miki da zaki saka min kuka,ko tafiyar ce bazakiyi ba ne?”.
Kanta ta fara girgiza masa kana tace, “a’a kayi haƙuri na daina”.
Yace, “to ki shafe hawayin ki dan bana son jin kuka kinji ko”.
Hawayen ta tashafe haɗi da cemasa “to”.
Tunda suka kama hanyar tafiya gaba kiɗaya hankalin ta atashe yake, dan tunda take dashi bata taɓa jin irin wannan tashi hankali ba kamar na yau,amma kuma bazata iya ce masa baza ta jeba,har suka fara fita daga cikin gari ba wanda ya cema ɗan uwansa komai.
Saura minti biyar afara exmas sai Safiyya tazo bakin class ɗinsu taga ko Hafsat tazo,aikuwa tana ƙarasuwa taga class ďin kowa yazo amma sit ɗin Hafsat wayam,gaban Safiyya ne ya bada dummm da sauri tashigo class ɗin.
Wata abukiyar karatun Hafsat, Naja’atu ta tambaya tace, ina Hafsat?”.
Sai Naja’atu   tace, “ai Hafsat ta daina zowa school dan tun dawo wa hutu sau biyu ta shigo class,kinga ma exam card ɗinta yanzu haka ita nake jira”.
Safiyya tace, “bata da lafiya,amma nasan yanzu zata zo,bani card ɗin nabata dan sauran kayan ta ma na hannuna”.
Ba musu Naja’atu ta bata.
Aikuwa tana ƙarɓa da sauri ta fito ta kama hanyar  hostel,tana zowa tasumu arun niƙaf tasa afuskar ta ta dake ma ran,ta tashiga class ɗin haɗe da addu’oi Allah kasa kada agane ba Hafsat ce ba.
gaban ta na duka uku-uku haka taje ta zauna saman sit ɗin Hafsat batari da tawa kowa magana ba.
Ko minti biyu batayi da zama ba aka fara raba Question paper. 
Ana kawo wa gaban ta,gabanta ya bada dummmm,addu’a takeyi Allah kasa kada ace sai ta ciri niƙaf ɗin da ta sanya…..
*To fah Safiyya kin iya ganganci*🤔
Cikin ikon Allah ya aje mata Question paper ya wucewarsa batare da yayi mata magana ba.
+
Aikuwa yana wuce ta ta fara yiwa Allah kirari a zuciyar ta haɗi da godiya a gare shi.
Tunda ga lokacin taci gaba da rubuta mata exams har suka kammala ba tare da ta samu wata matsala ba, sai dai gaba ki ɗaya ta dawo hostel da zama dan bata da lokacin komai sai na karatu, kuma tunda ta fara rubuta ma Hafsat jarabawa ba wanda ya gane ba Hafsat bace in ba ƙawar karatun  Hafsat ba Naja’atu.
Sosai taba Safiyya gudunmuwa wajan ganin tayi ma Hafsat jarabawa, duk da ba  department ɗaya suke da Safiyya ba amma tayi ƙoƙari sosai dan gabaki ɗaya ta hana ma kan ta barci ko da yaushe tana  library wajan  karatu, tayi nata tayi na Hafsat, har Allah ya nuna mata ta gama lafiya sosai tayi rama saboda rashin natsuwa da rashin isashen bacci.
Tunani ta farayi lokacin da suka gama exams yadda zata koma gida ba tare da Hafsat ba, dan haka ta yanke shawarar taje gidan sauranyin nata ta gani ko zata ganta,har zata je kuma ta fasa saboda ba ƙaramin baƙin cikin ganin sa takeyi ba dan haka ta yanke shawarar takira ta a waya.
Miss call kusan biyar tayi mata amma bata ɗauka ba sai ga na shidda kana ta ɗauka batare da tace komai ba.
Safiyya ba tadamu da rashin maganar taba dan haka tace, “kidawo dan ni zan koma gida kuma kin san da naje zasu tambaye ki dan haka gobe zan koma ko ki dawo ko kada ki dawo na dai faɗa miki”.
Bata ma bari taji me zataceba ta tsinke wayar.
Ita ko Hafsat tunda suka sauka ya kama musu hotal bata sake koda leƙo ƙofa ba dan baya barin ta.
Kuma yanzu ko lafiya bata isheta ba dan yanzu bata da wani kuzari, ga wata rama da takeyi duk tabi ta bushe kuma tana cin abinci amma kamar bata ci, sosai abun ke bata tsoro dan ita gabaki ɗaya tunda sukayi tafiyar nan bata cikin kwanciyar hankali, abu kaɗan ya isheta kuka.
Yau ma kamar kullum suna kwance yana  romance ɗin ta son ran shi, sosai yake jin daɗin abunda yake mata, ƙoƙarin shigar ta ya fara amma tana ɗan kaucewa, saboda yanzu ko kaɗan bata son abun da yake mata dan yanzu da ya gama abunda yakeyi da ita sai wani azaftaccin ciwon mara ya taso mata wanda kesa jikin ta kar-karwa lokaci ďaya.
Sosai take wahala kuma duk wannan uban ciwon marar dake taso mata ta gagara faɗa masa ya dena amfani da ita ko suje hospital a’a ita baza ta iya faɗa masa ba dan kar ransa ya ɓaci.
Duk da tana ƙoƙarin hanashi amma shi bai masan tanayi ba.
Ba ɓata lokaci ya afka cikin ta ya fara abunda yake so da ita son ranshi.
STORY CONTINUES BELOW
Aikuwa yana gamawa ya ɗan kwanta dan ya huta yaci gaba da abunda yake yi.
Ita ko yana sauka daga kanta, lokaci ɗaya wani abu ya taso mata  ƙasan marar ta, tun tana dauriya kar ya gane har abu yazo yafi ƙarfin ta, lokaci ɗaya ta fara fita hayyacin ta, duban sa ya kai gare ta aikuwa lokaci ɗaya ya zabura ya mike zaune haɗi da tambayar ta, “lafiya mike damun ki”?.
Ita ko batama san yana yi ba saboda a lokacin bata masan inda kanta yake ba.
Abun yaga yafi ƙarfin sa dan haka da sauri ya saka jallabiya ya ɗauke ta domin suje hospital.
Cak ya ɗauke ta ya kai mota, rasa asibitin da zai kai ta yayi, dan dare yayi gashi kuma bawani sanin garin yayi ba.
Masu gadin hotel ɗin ya tambaya yace su nuna masa hospital mafi kusa? dan matar shi ce ba lafiya haɗi da nuna musu ita a cikin motar.
Wani private    hospital dake kusa da hotel ɗin suka nuna mai godiya yayi musu kana yaja motar da gudu bai tsaya ko ina ba sai cikin hospital ɗin.
Cikin gaggawa Likitoci suka karɓe ta, lokaci ďaya suka  fara bata taimako .
Sun jima kanta kafin su shawo kan lamarin.
Bayan komai ya ɗan lafa kuma ta samu barci dan haka suka  fito daga ɗakin da take.
Yana ganin sun fito ya fara tambayar su ya jikin nata?.
Komai basu ce dashi ba sai babban doctor  daga cikin su yace dashi  “ka biyo mu office”.
Komai bai ce dasu ba ya bi bayan su.
Bayan sun isa office dukan su suka zauna, kana suka nuna masa kujera domin ya zauna.
Bayan ya zauna sai babba daga cikin Likitocin yayi gyaran murya kana yace, “da farko dai munyi nasarar ceto matar ka dan yanzu haka ta samu bacci kuma insha Allahu ina har takiyaye ƙa’idojin da zamu ɗaura ta akai to babu shakka zata samu lafiya sosai da sosai.
Sai abu na biyu muna tayaka murnar matar ka na ɗauke da juna biyu har na tsawon wata huɗu…..” aikuwa tun Doctor bai kai da ƙarasa maganar ba yace, “what haɗi da faɗin ciki!.
Gabaki ɗaya Likitocin kallon shi suka farayi cike da  mamaki.
Dubin doctor yayi kana yace, “Doctor kun duba da kyau kuwa? dan ni matata bata da ciki gaskiya”.
Results ďin scanning ďinta dake gaban sa ya bashi yace, “duba kagani”.
Karɓa yayi ya fara dubawa, abunda yagani ne yayi matuƙar bashi mamaki da tsoro.
Yana gama dubawa sai  ya ɗago da kansa yana kallan Doctor kana yace, “Doctor na gani kuma na yarda tana da ciki amma ina son a zubar da shi dan ba yanzu zamu haihu ba, ko nawane zan biya kawai a zubar da shi”.
Tunda ya fara magana gaba ki ɗaya Likitocin suka zuba mishi ido suna kallon shi har ya kai ƙarshen zancen shi.
Sai da ya gama kana babba daga cikin Ƙikitocin yace, “kafin na gaya maka komai ina son kasan wani abu ɗaya, lokacin da kake ba matar ka ƙwayoyin hana ɗaukar ciki to kasani sosai sukayi mata illah a mahaifar ta, dan ikon Allah ne yasa wannan cikin ya shiga cikin mahaifar ta har ya zauna ya kai wannan lokacin ba tare da ya zube ba,sosai mukayi mamaki lokacin da muka ga yadda mahaifar ta take dan sanadiyar wannan magani da kake bata mahaifar ta tafara lalacewa sosai, dan ko da wannan cikin ya kai matakin haihuwa to na tabbata bazata iya haihuwa da kanta ba sai ammata aiki, dan haka yanzu idan kace a zubar da cikin to za’ayi ɗayan biyu, dan sanadiyar haka mahaifar ta zata iya lalacewa bazata ƙara ɗaukar ciki ba ko kuma wajan cireshi ta rasa ran ta, kaga ko baza kayi fatar ko ɗaya a cikin waɗan nan su samu matar kaba”.
STORY CONTINUES BELOW
Sai da Anwar ya nisa kana ya dube Doctor yace, “Doctor kada kaji komai nasan haka bazata faru ba, kawai a cire shi dan bana son cikin”.
Gabaki ɗaya Likitoci da ke office ɗin kallon sa sukeyi dan abunda ya faɗane ya basu mamaki.
Sai Doctor yace, “banƙi ta taka ba amma sai nayi magana da matar taka idan ta aminta acire to ba komai zamu cire amma idan bata aminta ba to gaskiya ba zamu cire ba saboda aikine mai wuyar gaske?”.
Sai Anwar yace, “kada ka damu da matata dan nasan zata aminta dan haka kuyi aikin  kawai”.
Sai doctor yace, “a’a sai naji ta bakin ta”.
Sai Anwar yace, “ba damuwa idan ta farka zaka iyayi mata bayani”.
Doctor yace, “ba damuwa”.
Bayan gari ya waye  kusan ƙarfe goma Hafsat ta farka, kuma Alhamdlillah dan ta   samu sauƙi sosai.
Bayan tayi wanka tayi break tasha magani Doctor yazo ya duba ta kuma yaga jikin da sauki dan ba wata matsala yanzu dan haka yace bari yakira sauran Likitocin.
Aikuwa yana fita Anwar ya ƙarasu gareta  wani kallo ya jefa mata haɗi da yimata ya jiki.
Bayan ta ƙarɓa yace, “ni zaki munafur ta, ashe kin san kina da ciki amma kika ƙi sanar dani, to bani kika cuta ba kanki dan ni bazan aureki da ciki ba dan haka tun wuri kisan abunyi”.
Da sauri ta ɗago da kanta ta kalleshi bakin ta na kar-karwa tace, “wani ciki, wallahi ni banda ciki kuma da’ace inada ciki da kai kanka zaka sani”.
Wani kallo ya watsa mata haɗi da jefa mata wasu takardu yace, “duba kigani”.
Jikinta na kar-karwa ta ɗauka ta fara dubawa aikuwa tana gama dubawa ta zabura haɗi da sanya hannu akai tace,”ciki gareni fah!.
Wasu hawaye suka fara bin kuncin ta haɗi da durkusawa ƙasa ta fara kuka mai tsoma zuciya.
Tsawa ya daka mata haɗi da faɗin tayi shuru zaiyi magana da ita.
Hannun ta ta ɗaura kan bakin ta kana tace, “na daina”.
Yace, “abunda nake so dake idan Likitoci suka tambaye ki kin yarda azubar da cikin kice eh kin yarda, dan  idan baki yarda ba to wallahi bazan aureki ba kuma sai dai kije kisamar masa uba amma ba niba”.
Jikin ta na kar-karwa tace’ “na yarda ko ma basu tambayeni ba na yarda kuma kayi hak’uri kada ka fasa aurena please”.
Har zai sake magana sai  ga Likitoci sun shigo ɗakin.
Ƙarasawa sukayi gaban gadon da take kwance, bayan sun gaisa sukayi mata ya jiki kana sukayi mata bayanin da sukayi ma Anwar har wanda yayi musu na azubar da ciki.
Bayan sun gama yimata bayani sai ɗaya daga cikin su ya dube ta yace, “kin amince azubar da cikin?”.
Duƙar da kanta ƙasa tayi wasu hawaye masu zafi nabin kunci ta, tunani ta fara idan aka cire shikenan baza ta sake haihuwa ba kenan?ko ta rasa ranta, kuma yace bazai aureni da ciki ba to ya zanyi?.
Shurun da sukaji tayi ne yasa suka yi mata magana kallon su tayi da idon ta dasu ka sauya zuwa ja, sosai ta basu tausai dan haka  suka ce da ita kin amince?”.
Sai da ta rufe idon ta kana tace, “a’a ban amince ba”.
Tun bata kai da rufe bakinta ba Anwar ya daka mata tsawar da tasa ƴan cikin ta kaɗawa.
Bai ma damu da Likitocin dake wajan ba yace, “me kika ce? baki amince ba?”.
Jikinta na kar-karwa tace, “Hayat kayi haƙuri dan Allah ka taimaki rayuwata”.
Har zaiyi magana sai ɗaya daga cikin Likitocin yace, “Malam bari kaji koda a ce ta aminta azubar da cikin tomu ba zamu zubar ba, dan mu ba aikin mu bane, idan kaga zaku iya zama har ta samu sauƙi to bazamu hanaka ba amma idan kaga baza ku iyaba to zaku iya ƙarawa gaba amma mudai bazamu zubar mata da ciki ba bare ciki har na wata huɗu”.
.
Yace, “ko minti biyar baza muyi anan ba bare har na sa kuɗina taci gaba da kwanciya anan”.
Kallon ta yayi yace, “ki tashi muje sai kije can ki haifar musu shi dan wallahi kar ma ki soma cewa nawa ne” yana faɗar haka ya kama hanyar fita batare da yaji mi zasu ce dashi ba.
Suma Likitocin fita sukayi har sun fita sai ɗaya daga cikin su ya dawo ya sameta sai kuka takeyi kamar ranta zai fita yace,
“Shawara zan baki duk yadda yaso kada ki yarda a zubar miki da ciki dan ke zai cutar, shi a kowane lokaci yake son haihuwa zai iya wani aure ya haihu amma ke shikenan  baza ki saki haihuwa ba har abada, dan haka ki tashi kije yana jiranki ”  yana faɗar haka shima yafice daga ɗakin.
Sai da tayi kusan minti biyar kana ta tashi ta fara bin bango ta fita a ɗakin har ta kai wurin da motar sa take.
Tun bata ƙarasu wajan saba ya fara afka mata wata muguwar harara.
Motar ta buɗe ta shiga aikuwa tana shiga yaja motar da ƙarfi kamar zai tashi sama ya fice.
Suna isa hotel ɗin ko kallo bata ishe saba ya buɗe motar ya barta ba tare daya kalleta ba.
Haka tafito tana tafiya a hakali har ta isa ɗakin da suke.
Koda ta shigo yana toilet yana wanka wuri tasamu ta zauna, bata jima da zama ba ya fito yayi kamar bai san da zaman mutum a wurin ba.
Har ya gama shirin sa zai fita kana ya dube ta yace, “ki tattara naki da naki dan gobe zamu koma gida kuma wallahi ba zaki sauka gidana ba sai dai kije gidan ubanki”  yana faɗin haka yafice warsa batari da ya tsaya yaji mi zata ceba.
Yana fita ta fara kuka mai ban tausai, tana cikin kukan ne Safiyya takira ta kuma abunda yasa tak’i magana dan kar taji tana kuka.
Haka ya barta har dare batare da ya sake wai-wayar taba.
Kuma babbar matsala duk baifi rashin ƙarfin jikin da bata dashi ba kuma ga yunwa ta dame ta dan tun safe rabun ta da abinci gashi yanzu dare yayi kuma har yanzu bai dawo ba.
Har barci ya fara ɗaukar ta sai gashi ya dawo, da sauri ta tashi dan a tunanin ta ko zata samu wani abun da zataci koda tea ne tasha.
Koda ya shigo sarai ya gan ta amma sai yayi kamar bai ganta ba har yaje toitel yayi wanka yazo ya kwanta, sai ta ƙaraso da sauri gareshi tace, “Hayat dan Allah ka taimakamin da ko ruwan tea ne wallahi yunwa nakeji?” tana faɗa kamar tayi kuka.
Kallo ma bata isheshi ba bare tasa ran zai ƙarɓa mata magana.
Data ga alamun bazata samuba dan haka ta zo ta kwanta.
Bata jima da kwanciya ba ya fara jawota jikin sa yana wasa da ita son rashi, ita ko tunda taga abunda yake son yi da ita ta fara masa kuka tana faɗin, “dan Allah kayi haƙuri ka barni wallahi banda lafiya kuma yunwa nakeji”.
Yi yayi kamar bai jita ba haka yayi yadda yake so da ita kafin ya barta.
Sosai tayi kuka a wannan daren dan iya wahala ta wahala dan har ƙaramin suma sai da tayi, kuma tundaga lokacin bata koma barci ba har gari ya waye…….
Bayan ta idar da sallah asuba tajima kafin ta ta shi sabida ko da ta tashi faɗuwa zatayi dan bata da wani kuzari a jikin ta.
+
Tana kan sallaya yatashi yaje yayi wanka kana yayi sallah,bearkfast yaje ya karɓo musu,yana dawo ya kai duban shi gareta kaifin yayimata magana ita tafara gaisheshi ciki da ladabi.
bai ma karɓa ba yace, “kizo kiyi bearkfast dan yanzu nakeson mu kama hanya kuma idan kika tsaya wasa sai na barka” yana faɗa yana antaya mata  harara.
Ahankali ta tashi kayan da yanuna mata na beark su ta ɗauka ta haɗa tea ta farashi,sosai taci kayan da ya kawo mata,sai da taji ta ƙoshi kana ta tashi taje toilte tayi wanka.
tana cikin shiri sai gashi ya fito cikin shirinsa na tafiya,ko kallon ta baiyi ba ya kama hanyar fita.
Ɗakin da taga yana ƙoƙarin rufewa yasa da sauri ta ɗauko kayan ta tafito waje ta karasa yafa mayafin ta.
Key yakai ma masu hotel ɗin kana yazo ya ɓuɗe mota ya shiga itama tashi kana suka kama hanyar garin sokoto.
Tafiya sukeyi amma ba wanda yace ma ɗan uwansa komai har sukayi nisa sosai.
Wayar Hafsat ce tafara ruri dan haka ta ɗauko ta duba wake kiran ta.
Safiyya taga ya bayyana dan haka taja tsaki kana ta ɗauka.
Safiyya tace, “Hafsat kina ina wallahi yau zan koma gida kuma kinsa zasu dameni da tambayar ki dan Allah kidawo mutafi tare”.
Sai da ta kai ƙarshen zancin Hafsta tace, “wai Safiyya ke waci iri ce,nace kirabu dani kinƙi  to bazanje gidan ba kije kifaɗa kinji koma bari kiji kada kisaki kirana sabida ba ajiya kika bani ba ehe” tana gayamata haka ta tsinki kiran.
Duk abunda takeyi yana kallon ta amma yayi kamar baisan tanayi ba.
Haka suka cigaba da tafiya har suka shiga garin sokoto.
Suna kawowa Flyover
yayi packing ďin motor sa yace, “ki sauka dan ni zan wuce”.
“Haba Hayat kayi haƙuri muje gidan ka idan na ɗan huta zuwa ajima sai naje gida”.
Wata tsawa ya daka mata wandda tasa tafice daga motar bata shiyar ba.
Har zai tada motar tace,”Hayat bani da kuɗin da zan ƙarasa gida kuma bazan iya ƙarasawa da ƙafa ba  gashi kuma dare yayi”.
Ko kallon ta bayi ba yaja motar sa yabar ta tsaye a hanya.
Hawayen da kifita a idonta ta goge kana ta ɗau jikar ta tafara tafiya kan ti-ti.
Mai napep  ta tsayar dashi, ta faɗa masa sunan unguwar da zai kaita.
Bai tsaya da ita ko ina ba sai ƙofar gidan su.
STORY CONTINUES BELOW
Fita tayi tace dashi zata shiga ta karɓo masa kuɗi yace to.
Sallam tayi ta shigo cikin gidan,aikuwa ƙannin ta najin muryar ta suka fara yimata oyoyo kamar zasu kayar da ita gashi ba wani ƙarfin jiki ne da itaba.
Da ƙyar tasamu suka saketa,ita ko Mama tunda taji suna oyoyo tasan ƴar  ɗiyar tace ta dawo dan haka da sauri tafito waje sabida ta ganta.
Gaban tane yayi muguwar faɗuwa lokacin da taga Hafsat,dan gabaki daya ta rame tayi fari sosai.
Har zata tambaye su Mama sai suka haɗa ido da ita,murmushi Hafsat ta ƙaƙalo tace, “Mama ya nasameku?”.
Bata karɓa ba dan kallon ta takeyi sosai dan kamar tana son ta kartu wani abu,sai Hafsat ta katsa mata tunani tace, “Mama nafa tsayar da mai napep ban bashi kuɗi ba”.
Sai Mama tace, “dole na kifeki da ido wannan ubar ramar da fari da kikayi Hafsat, lafiya kike kuwa?”.
Tace, “Mama bari na sallame mai napep nazo”.
Tambayar ta kuɗin sa tayi ta faɗa mata sai Mama tabaiwa ƙaninta Ammar ya kai masa.
Sai Mama tace, “kinyi tsaye ki ƙaraso daga ciki”.
Parlour Mama ta shiga ta zauna  Mama tace,”Hafsat mike damunki ki kayi wannan ramar haka?”.
Sai da ta ƙaƙalo murmushi tace, “Mama wahalar exams ce ta ramar dani” tana faɗa tana yin ƙasa da kanta.
Sai Mama tace, “a’a Hafsat da alamu akwai ramar zazzaɓi aciki”.
Tace, “eh Mama dan jiya ma naje hospital suka rubutumin magani kin gama tagarda maganin” tana faɗan haka tana buɗe zip ɗin jikar  ta ta ɗauko mata tagardar maganin da aka rubuta mata a can hospital ɗin da ya kaita dan cewa yayi tunda bata yarda azubar da cikiba to ko magani ba zai saya ba.
Ɗaukowa tayi taba Mama itako Mama takira Marwan tace yaje pharmacy ɗin Baban shi ya karɓo magani.
Karɓa yayi yaje itako Mama tace Hafsat ta koma ɗakin ta tayi wanka tayi sallah tazo taci abinci ta sha magani.
Tashi tayi taje ɗakin ta, tana shga kafin tayi komai wayar ta ta dauko ta fara kiran Anwar.
Kusan missed call biyar tamasa amma bai ɗaga ba daga ƙarshe ma kashe wayar sa yayi gabaki ɗaya.
Sai da taji yakashi wayar kana ta tashi taje tayi wanka tayi sallah magarib da isha’i.
Tana idar da sallah Marwan ya shigo ya kawo mata magani da abinci.
Bayan ta ci abinci tasha magani ta koma ɗauko waya ta ƙara kira ko ya ɓuɗi?.
Amma har yanzu kashe take,tunani tafarayi ko taje gidan sa dan gabaki ɗaya batada natsuwa dan ita kanta tasan ko tana samun natsuwa sai ta ganshi,kuma tasan Mama baza ta barta tafita ba.
Tana cikin wannan tunani barci ya fara ɗaukarta saboda maganin da tasha har da na barci akwai.
Ko da babanta ya dawo daga masallaci har barci yayi awongaba da ita dan ko da Mama  ta aiki Marwan ya kirata ta yi bacci sai babanta yace ka da a tasheta abarta sai da safe sai su gaisa.
Ko da gari yawaye Mama taje ɗakin ta dan ta ƙira ta, amma sai ta tarar har yanzu bacci takeyi bata tashi ba, abin ya ba Mama mamaki dataga har rana takusa fitowa Hafsat bata tashi ba sabod tasan ba halin taba ne baccin asubah.
Tayar da ita ta farayi tana kiran Hafsat tashi kiyi sallah rana tayi, miƙa ta farayi alamun zata tashi Sai ta fara magana cikin muryar bacci tace,
STORY CONTINUES BELOW
” Mama rana ta fara fitowa?”.
“Eh Ki tashi ga Abbanki can yana jiranki ku gaisa saboda yanzu fita  zaiyi,Tashi tayi ta nufi toilat Cikin hanzari tayi wanka sannan ta daura Arwala.
Itako Mama tana ganin ta tashi ta shiga toilat sai ta fice daga dakin
Koda tafito bata tarar da Mama ba dan haka ta gabatar da sallah kana ta shirya tafito taje ta gaishe da Abbanta.
Da sallama ta shiga parlour,bayan sun ƙarɓa mata ta ƙarasu gaban Abban nata wanda tun shigowar ta yake kallon ta ciki da so da ƙaunar ƴar tasa.
Bayan ta gaisheshi ya karɓa kana yace,
“Hafsat ashe har ciyo kikayi?Allah ya ƙara sauki kuma kiriƙa shan magani muga kwana biyu abunda Allah zaiyi”.
Ya ƙara da faɗin “ya exmas dafatar kun kammala lafiya?”.
Tace, “eh Abba munga sai dai muna baran addu’a”.
Sosai yayi musu addu’ar samun nasara ita da Safiyya kana yayi musu sallama yafita wajan aiki.
*********
Bayan kwana biyu da dawowar ta tasamu sauƙi sosai dan har cikowa ta farayi bakamar lokacin da tadawo ba.
Kuma tundaga ranar da ya sauke ta bai saki nemantaba kuma bai saki ɗaukar wayar taba dan ko takira ba zai ɗauka ba shiyasa gabiki ɗaya bata cikin natsuwa  dan yanzu burin ta taganta tari dashi dan haka taje tagayawa Mama zataje gidan ƙawar ta ta dubata sabida batada lafiya,da kyar tasamu Mama tabarta amma tace kada tajima.
Wanka tayi ta shirya cikin wata koriyar atamfa ɗikin rika da sikt ne sosai suka karɓe ta tayi kyau abunta har ta ɗauko turare tasa jikinta sai ta tuna Mama bazata barta tafitaba idan tasa dan haka ta saka shi ajika ta har sai tazo gidan sa haɗi da wani mitsi-tsin gyale.
Babban hijab tasaka ajikin ta kana ta fito tanufe ɗakin Mama.
Da Sallama tashiga tace, “Mama zan tafi”.
Kuɗi napep Mama tabata haɗi da ƙara faɗamta karta jima.
Karɓa tayi haɗi da faɗi, “bazan jimaba” kana taficewar ta.
Tana fita ti-ti ta tsayar da napep,sunan unguwar da zai kata tagayamasa, shiga tayi yaja suka tafi.
Basu tsaya ko inaba sai bakin gidan sa.
Bayan ta sallame mai napep ta ƙarasu bakin gate ɗin gidan ta fara knocking,bata jima tana knocking ba mai-gadi ya leƙo yaga wanene?aikuwa yana ganin ta yayi sauri ya buɗe mata ƙofa haɗi da gaisheta.
bayan ta ƙarɓa take tambayar sa ko Anwar nanan?.
Yace “eh yana ciki”.
Part ɗinsa ta ƙarasa , kafin ta isa ga part ɗinsa ta buɗe jikarta ta ɗauko turare tafeshi jikinta dashi kana taciri hijab ta sanya wannan mitsi-tsin gyale wanda dashi da babu duk ɗaya.
Ƙofar da zata sadata da falon shi tashiga kai tsaya.
Ahankali take tafi har takawo gab dashi yana zaune yana kallon labaru bai masan ta shigo ba.
Ƙamshin turarin da yabige hancin sane yasa ya dago kasa,aikuwa suna haɗa ido dashi ta fara sakar masa murmushi mai ciki da nuna tsan-tsar so da ƙauna.
Har yaso ya ƙoreta amma yadda yaga ta ƙara kyau kuma ga ko ina nata ya ciko musammam abunda yakeso wato dukiyar fulani.
Irin kallon da yake matane yasa tafara tafiya ɗaya-ɗaya har ta ƙaraso gareshi.
Ahankali tazo ta zauna saman cinyarsa haɗi da kai masa kiss abaki tare da faďin,”I miss you so much My Hayat”.
Aikuwa yana jin bakinta cikin nashi lokaci ďaya yaji wata Sha’awa tabi jirumasa bai san lokaci da yafara kissing ďinta ba.
Hannunsa yasa cikin   rikar ta yafara shafar duk wani ilahirin jikin ta,musammam abu sonshi sosai yake matsarsu itako sai ƙara narke masa takeyi ajiki tana wani nishi ɗaya-ɗaya.
Cak ya ɗauke ta yayi bedroom ɗinshi da ita,kayan jikin ta yacire mata kana yacire nasa romance ɗin ta yafara cikin zafin nama kana yashiga aiki,sosai yabata wuya dan har wani abu taji ya tsaya mata amara amma bazata iya cewa ya daina ba.
Sai da yagaji dan kansa kana ya sauka daga gareta ciki da samun gamsuwa danshi yake masifar sonta,sosai yake samun natsuwa  gareta.
Itako yana gamawa ta gagara tashi dan gabiki ɗaya marar ta ta ƙulle, gawani ciyon da takeji a ƙasan ta.
Shi bai masan tanayi ba,janyota jikinsa yayi yafara baccin hutu itako ta jima  kafin taji dama-dama,daga baya bacci yayi awun gaba da ita.
Sai kusan ƙarfe shidda yabar ta ta koma gida koshi saida taga neman halakata yake ta sanya masa kuka da kyar ya barta tatafi gida.
Shiko duk abunda yake mata da gayyane yakeyi sabida burinshi yaga cikin ya zube.
Tun ahanyar zuwa gida taji mararta na ciyo kuma gawani zazzaɓi da ya taso mata lokaci ɗaya.
Batafi minti biyar da shiga gida ba cikin ta yafara juyawa kamar abunda ke cikinta ya fito.
Kuma gashi ita kadai a ɗakin, tajima kwance tana birgima a ɗakin sai can Mama ta shiga ɗakin ta dan tayi mata faɗan jimawar datayi bata dawo ba sabida ƙarfe huɗu tayi da ita tadawo.
Aikuwa koda Mama tasha ɗakinta halin da tasameta ne yayi matuƙar razanata.
Rasa mezatayi tayi sabida gabaki ɗaya  tafita hayyacinta gakuma wani jini  dakefita ta ƙasanta.
Da gudu Mama tashiga ɗakin su Marwan tace “yakira mai napep Hafsat ba lafiya zasu kaita hospatal”.
Dayake basuda nisa da ti-ti yana fita ya tsayar dashi suka ƙarasu gida.
Shida Ammar da Mama suka ɗaukota suka sa a napep suka wuce hospatal ko mayafi babu ajikin Mama sabuda firgita😢…….
* koda  suka isa hospital emregency room suka kaita,ba ɓata lokaci aka fara bata taimako cikin gaugawa.
+
Tunda suka shiga da ita Mama sai safa da marwa takeyi a harabar hospital.
Marwan Mama tasa yakira Abban su yafaɗa masa abunda ake ciki,kana yaje gida ya ɗauko mata hijab ɗinta.
Tare suka shigo da Abba hijab ɗinta Marwan ya bata tasaka Abba yace, “ina suka kwantar da ita?”.
Jikin Mama sai rawa yake tace, “Abban su har yanzu basu fito ba”….tun bata kai da ƙarasa maganar ba sai ga doctor yafito daga cikin ɗakin.
Da sauri Abba da Mama suka zo wajan sa.
Tambayar su yayi kosu suka kawo Hafsat? sai Abba yace, “eh”.
Magana doctor yayi  musu yace su biyushi office.
Bayan ya shiga office ya zauna suma suka shigo kallon su yayi yace, “wanene mijin ta?”.
Kallon-kallon suka fara tsakanin Mama da Abba.
Sai Abba ya buɗe baki yace, “batada miji mune dai iyayen ta”.
Doctor kallon Abba yayi sosai kana ya nuna masa kujera yace ya zauna.
Bayan ya zauna sai doctor ya kai duban sa ga Mama yace, “kefa miye matsayinki a wajanta?”…… tin kan Mama tayi magana sai Abba yace, “mahaifiyar tace”.
kujere doctor ya nuna mata yace ta zauna.
Bayan ta zauna sai doc tor yace, “ba abinda zan ɓoye muku gaskiya,muyi nasarar tsayar da jinin da yafara fita jikin ta,amma cikin dake jikin ta nanan bai fita ba…..tun kan ya kai ƙarshen zanci sai Mama tace,
“a’a ba ƴata baca ka duba danni ƴata batada ciki kada kayi mata sharri” magana Mama keyi amma gabiki ɗaya bata cikin natsuwar ta.
Abba yace, “kada kisa ke magana ki bari muji me doctor zai ce”.
Abba kallon doctor yayi yace “inajinka”.
Doctor yace, “iya binciken da mukayi mata, munganu tana ɗauke da ciki har na tsawon wata huɗu, kuma cikin na gab da zubewa saboda irin yadda ….bai ƙarasa zancin ba saboda da nauyi maganar da zai faɗa, ya faɗa musu ko yanzu saduwar da yayi da ita ne yajamata wannan ciyo sai yaƙi faɗa  yace, amma yanzu tasamu sauki dan har  barci ta samu sai zuwa kosan awa huɗu zata farka saboda mun mata allura bacci.
Yana kai ƙarshin zancin Abba ya sauke wata ajiyar zuciya haɗi da goge ƙwallar da ta zubo masa yace , “to doctor muna godiya”.
Sai Mama tace, “yanzu Abbansu har ka yarda Hafsat na da ciki?wallahi nikam ban yarda ba dan nasan ba halin ƴata bane” magana takeyi amma kamar zata faɗi.
Doctor ya dube ta bayan yaba Abba ta kardar maganin da za’a sayo mata yace da Mama “zaki iya gane ƴar taki idan kin ganta?”.
Tace “sosai kuwa”.
STORY CONTINUES BELOW
Sai yace, “zo muje kiga ko ita ce” yana faɗin haka ya tashi ya kaisu ɗakin da aka kai ta.
Suna shiga gadon da take kwance ya nuna mata yace, “gata ko ba ita bace?”.
Kallon Hafsat Mama keyi wadda ke kwance tana barci bata masan abunda akeyi ba.
Gaban gadon Mama ta ƙaraso tace, “Hafsat! Hafsat! mi kika rasa wanda bamuyi miki ba,ci kika rasa ko sha ki gayamin miyasa zaki sakamin da haka Hafsat!, kinsan aure kikeso meyasa bazaki gayamin ba”  tana magana tana wani kuka mai ban tausai.
Alamun zata faɗine Abba yagani dan haka da saure ya tare ta ta faɗu jikin sa sume…. ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba lokaci ɗaya jikin sa yayi sanyi yama rasa me zaiyi.
Doctor ne yakira wasu nurse suka ɗauke ta aka ɗura ta kan godon yafara dubata.
Cikin lokaci kaɗan ta farfaɗo.
Sunan Abba ta fara kira,doctor yasa aka kirashi,yana zowa yafita dan yaga ba komai ne ke damun taba sai ruɗuwar da tashiga.
Jikin Abba tafaɗa tana kuka tace, “kaga abunda Hafsat tayi muna yau mu zata sakama da ciki kuma ko ciki na shege”.
ajiyar zuciya Abba ya sauke kana yace, “ta dai yi ma kanta, dan haka ki rage sa damu wa aranki,kuma ki tashi mukoma gida idan tafarka gasu Marwan nan su dawo tare”.
Sai Mama tace, “da ka barni idan ta farka mu dawo tare sai kuje kai da su Marwan……tun bata kai ƙarshen zancin ba ya daga mata wata irin tsawar da yasa ta sauka daga gadon bata shirya ba.
komai bai ce da itaba ya kama hanyar fita ya barta.
Itama tana ganin yafita ta bi bayan sa.
Waje suka tarar da Ammar da Marwan suka ce sujira idan Aunty su ta farka su dawo gida tare.
Haka  kuwa akayi tana cika awa huɗu ta farka.
Dubi- dubi tafarayi   Marwan da Ammar tagani sunyi tagumin kamar sun san mike faruwa.
Ammar ne ya kula da farka warta dan haka da sauri ya ƙaraso gare ta yace, “Aunty ya jikin naki”.
Da sauki tace dashi kana tace, “Ammar ina Mama?”.
Yace, “ta koma gida ita da Abba”.
Yana faɗa mata haka wasu hawaye masu zafi suka fara bin kuncin ta sabida tasan yanzu kowa yasan tana da ciki.
Lokaci ɗaya tafara rera kuka mai ƙunar zuciya tana faɗin, “Ammar kada kugujeni wallahi nima ƙaddara ce ta afka kaina ni kaɗai nasan me nakeji gami dashi,duk duniya banajin abunda nakeji dashi ga kowa sai gareshi dan Allah ƴan uwana kutayani da addua, dan wallahi ina cikin wani hali”.
Sosai ta baso tausai duk da su kansu basu san me ake ciki ba.
Duk da Abba yace kada su kwana komai dare su dawo amma basu gaya mata ba sukayi kwanciyar su har safiya ta waye.
kuma basu fito ba sai da doctor ya dubata ya rabuta mata magani Marwan yaje yasayo haɗi da kayan beark  bayan tayi beark tasha magani suka kamu hanyar zuwa gida.
Abba da Mama ba wanda ya samu bacci a ckin su kowa nin su tunani abunda ƴarsu wadda suka fi so a duniya  ta aikata ya keyi
Tun cin dare yake zuba ido amma basu dawo ba,dan haka koda akayi kiran sallah asuba yaje masallaci ana gama sallah  ya dawo .
Bai jima da dawo ba sai gasu sun dawo.
Sallama sukayi bayan Abba ya ƙarɓa suka wuce suka zauna.
Komai Abba bai ce dasu ba kuma suma basuyi masa magana ba saboda basuga wurin yimasa magana ba dan fuskar sa haɗe take.
Kallon sa ya maida ga Ammar kana yace, “jeka kiramin Safiyya”.
Tashi Ammar yayi yafice yaje kiran Safiyya.
Mama na fitowa ɗaki bata ce da kowa kamai ba ta fara dukan Hafsat tana faɗin kin ci amana ta Hafsat mikika rasa tana faɗa tana dukanta iya ƙarfin ta.
Tashi takeso tayi dan ta gudu amma takasa saboda bata da wani ƙarfin jiki.
Abba na kallo amma yayi kamar bai san abbun da ke faruwa ba.
Wani ice Mama ta raramu dan ta bugama Hafsat aikuwa da sauri Marwan ya riƙe yana  kuka yana faɗin, “dan Allah Mama kirabu da ita me ta muku kika dukan ta, ki dakeni mada-din ta ko lafiya fa bata da komai tayi kuyi mata uzuri mana”.
Tun bai kai ƙarshen zan cin ba Mama takafeshi da mari har sau biyu.
Abba ne yayi magana yace “ta ƙyalesu kada ta koma magana ta barshi da su.
Anacikin haka sai ga Ammar da Safiyya sun zo tare…….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *