UMM ADIYYAH CHAPTER 2 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 2 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Zaid Abdur-Rahman mutum ne tsaurarre da ba ka taba gane alKiblarsa kuma mutum

ne murdaddde, idan ba ka yi sabo da shi ka dade da fahimtar cewa hakan yake ba,

za ka dauka ba wanda ya kai shi fadiin rai. Wannan ya sa duka abokan Www.bankinhausanovels.com.ng

kasuwancinsa guda biyu suke mamaki, idan suka samu abokin ciniki, (Client) ta dalilin Zaid.

Ganin kamfaninsu ya bunkasa ya sa suka yi masa tsari na zamani suka samu ofishi

na musamman suna kuma diban ma’aikata, har makarantar horar da mutane kan

harkar Kera Softwares da kula da Komfutoci, (Maintainance), suna da shi a wannan

kamfanin. Yanzu shekaru bakwai kenan da fara wannan harkar tasu.

Yawan kamewarsa ce ta sa bai ganin amfanin ma ya tsaya wai bin mace, tana ba

shi wahala. Wannan ya sa shi sam mata ma ba su gabansa bare wata aba wai

soyayya. Soyayyarsa daya ce, ita ce ga Komfutarsa. Idan har ka ga yana sakewa

mutum fuska, to ‘yar-uwarsa ce, mutum daya ce jininsa ya hadu da nata wato

Asma’u.

Abinda ya sa kuma ba ta daukarwa kanta halayyar shisshigewa da namiji ba,

sannan kuma tana da gudun zuciyar mutum. Tun tasowarta yake kulawa da lamarinta, domin tasu ta zo daya.

*********

ZAMU TASHI 

BABI NA BIYU

Umm Adiyya Zubair, yarinya ce mai kimamin shekaru ashirin da hudu a duniya. Ita

ce ‘ya ta hudu wurin iyayensu. Bldr. Zubair Nafada da kuma Justice Khadija Muhammad, wacce suke kira Maami hade da jan ‘Maa’ din Maamin.

Idan ana kiran kyawawa, sam Umm Adiyya ba ta saka kanta a cikinsu, amma kuma duk wanda zai ganta a gefe da irin yanayin kyawun da zai siffanta ta da shi. Ba ta da tsawo, idan banda kyawun dirinta ma, mutum ba zai ba ta shekarunta ba, idan ya yi

mata ganin farko. Fara ce sol! Kuma tana da cikakkun Kugu, wanda ya tafi daidai da

yanayin jikinta na mai Karamin ruwa. Www.bankinhausanovels.com.ng

Kallo daya za kai mata ka san cewa ita cikakkiyar bafulatana ce, domin hatta gashin

kanta yauki da tsawo yake da shi, ga wadataccen gashin gira da Karamin baki, sai

madaidaita idanunta, wanda suke Kunshe da wani annuri, kullum farare tas! Za ka
gansu, ba ta da dogon hanci irin dai na Fulani, amma yadda take da Karamar fuska

haka madaidaicin hancinta ya dace da Karamin bakinta da ya zauna a fuskarta.

Ba ta cika son hayaniya ba sam, kuma akwaita da Kwazo da hazaKa, domin yanzu

haka ta kammala karatunta a bangaren Engineering, inda take da digiri a (Electrical

Electronics Engineering), kowa yana mamakin zabin wannan bangaren na karatun

nata, ganin ta na ‘ya mace, yawanci mata sun fi son kos masu sauKi.

Amma kuma haka zalika kowa ya san za ta iya, domin Umm Adiyya tana da

Kwakwalwa sosai, ga shi ta gamu da iyaye masu dora yaransu kan tsari na ilimi na

boko da na addini, don hatta Maami ba ta da wasa. Ba a batun Abban su kam, da ba

daman ya shigo gida ya ga babu littafi a hannunsu, sai sun samu rabonsu.

Yaya Saadik shi ne babban yayansu, sai Adda Zubaida wacce ta yi aure tana zaune

a Bauchi. Adda Asma’u ke bin Zubaida, sai

Umm Adiyya da kuma Kannenta maza Fa’ iz da Faruk ‘yan biyun su.

Yaya Saadik a garin Gombe yake aiki da Branch na PenCom, wanda yake can, sai

Asma’u wacce ita kuma da AZ IT take aiki a nan Abuja. Inda suke da zama, a halin

yanzu ma aurenta ake shirin yi, wanda shi ne musabbabin juyewar duniyar Ummu A. Www.bankinhausanovels.com.ng

kamar yadda suke kiranta wasu lokutan.

Duk da kasancewarta shiru-shiru. Allah ya bawa Umm Adiyya tarin masoya ta ko ta

ina, domin tun kan ta gama karatu, iyayen kansu sun zaci za a Samu wanda za ta

gabatar a cikin maneman nata, tun suna zuba mata idanu, har suka ga abin ya yi

yawa suka sa ta a gaba da tambaya, amma ta nuna masu ita babu tukun na. Har

suna tunanin hadata da ‘yar-uwarta su aurar da su tare, sai ga shi bayan shekaru

uku Asma’u za ta yi nata auren, amma Umm Adiyya shiru.

Maami ta sha ajiyeta ta sa ta a gaba da tambayoyi, amma kullum amsar daya ce,

“Maami babu dai tukun na, komai lokaci ne.” Don haka Maami ta Kyaleta.

SHEKARU BAKWAI DA SUKA WUCE ABUJA, (2003)

Wata ranar Litinin ta fito da Kawayenta Nazira da Suwaiba za ta rako su mota, bayan

sun gama bitan karatunsu na jarabawar da za su soma na (WAEC), a cikin satin, shi

kuma ya iso gidan. Har ga Allah fitowarsa daga mota da ta gan shi, sam ba ta san

me ya same ta ba, illa iyaka sai ji ta yi su Nazira suna cewa, “Kar ki manta ki fito da

wuri goben.”

Yake ta yi masu kawai, saboda har zuwa lokacin, ji take yi kawai gabanta na dukan

uku-uku. Na farko dai ba yau ta fara ganinsa ba, na biyu kuma ba yau ta fara ganin

kyakkyawan namiji ba, amma ta rasa me ya sameta da ta yi masa kallo guda! Ta sa

kai za ta koma cikin gida ne ya ce, “Ke Adiyya, ba kya ganin mutane ne?”

Jikinta na rawa ta ce “Yaya Zaid, sannu da dawowa”

“Haba, ko ‘yan makwabta dai suka ganni sun san su yi farin-cikin ganina bare ‘yar Kanwata, shekara nawa? Shekaru biyu Kwarara ba ki ganni ba, iya murnan ki

kenan? To na ajiye ki a gefe, daga yau Asma’u ce mutumiyata.”

Murmushi ta yi ta rufe fuskarta sannan ta ce, “Sorry, Yaya Zaid.” Sannan ta mika

hannu za ta karbi jakar hannunsa wacce ta fi kama da ta komfuta, da sauri ya janye

ya ce, “Je ki abinki, na hutasshe ki, su Fa’iz za su tayani.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Ai ba ta ida rufe baki ba, suka tunkaro su, cikin murna da hayaniya, wannan ya sa ta

koma ciki jiki a sanyaye, har dare ranar ta kasa sanin abu guda da yake mata dadi,

lokacin ba ta danganta shi da ganin Yaya Zaid ba, saboda ita daman ba wani sabo

take yi da mutane ba, saboda shirunta ya yi yawa.

Tana ganin yadda kowa ya damu da shi, don

ko wurin iyayenta idan ba tsoron Karya

ba, sai ta ga kamar sun fi ji da Yaya Zaid akan su. Kwanakin shi biyu da dawowa, ya

tafi Gombe wurin iyayensa. Umm Adiyya kuwa ta maida kai haiKan wurin karatunta,

dama ba tayar baya bace.

Ita har ta manta da zancen Zaid, saboda ya dauki satuttuka kafin nan ya dawo. Ai

kuwa bayan ya dawo, da gaske yake yi ya share ta, domin sau goma zai in aike, to Asma’u ko su Fa’iz yake sawa.

Wani bakon al’amari a gareta shi ne, duk inda aka ambaci sunansa a gidan, to tana

sauraran ta ji me za a fada, saboda haka kawai hira idan dai ta Zaid ce, to yana sa

ta nishadi. Idan kuwa ta gan shi, sai gabanta ya yi wannan faduwar.

***********

Tana cikin karatu da yamma a falon Abba, kasancewar duka ana hira a falon Maami

ne, ya sa ta zabi nan saboda ta samu natsuwa, ba ta san hawa ba bare sauka, ta ji

an cire mata littafin daga hannunta.

“Adda Asm…” Ba ta Karasa ba ta yi dif! Saboda koda wasa ba ta yi tunanin shi bane,

“Har za a yiwa Adda Asma’u masifa, oya cigaba ina jinki.” Www.bankinhausanovels.com.ng

“Ba masifa fa zan yi ba Yaya Zaid.” Ta fada a cikin muryarta ta shagwafa.

“Ba surutu na ce ki min ba, karatun za ki min.” Nan ne ya duba abinda take nazari,

nan take kuwa ya jefo mata tambaya.

Ganin haka, ya sa ita ma ta ba shi amsa yadda ya dace, sun dade suna haka daga

baya ya ce, “Good, ina son haka, tunda kin gane sai ki huta, kuma anjima idan ki ka

Daga, sai ki ji kin Kara fahimta.”

“Na gode.” Ta fadi Kasa-Kasa, duk yadda yake shige mata, wataran ya zolayeta, ita

kanta ba ta taba rudiin kanta ba, domin ta san Yaya Zaid ba abinda ya tsana irin raini

ko kuwa wasa, don kaf! Dangi ma ita da Asma’u ne suke cin arziKin ya yi masu

wasa. Hakan ya sa ta kama kanta, muddin ba shi bane ya fara janta da irin wannan ba ta taba yi masa iyakacin su gaisuwa.

Bayan sun gama ne, wayarsa ta yi Kara wannan ya sa ya mike, domin amsa wayar,

binsa ta yi da kallon tsaf! Koman Yaya Zaid kyau yake mata, muryarsa wanda take

mai zurfi a murje, tamkar wanda ya yi kos wajen fidda sauti mai dadi. (Deep Smooth

Whisper-Like Voice).

Yanayin yin abubuwansa da komansa cikin natsuwa yake yi, siriri ne ba shi da Kiba,

haka nan dogon fuska gare shi, wanda dogon hanci ya shimfidu a kai, yana da

tsawo. Domin idan ka dubi Umm Adiyya, ka dubi Zaid to za ka ga cewa koman su ya

sha banbam, saboda hasken Zaid ba fari bane tas! Zama a fi jera shi a sahun Www.bankinhausanovels.com.ng

bakake. Gashin kansa ne kawai irin nata, wanda yake a kwance kamar na jarirai.

Haka take zaune har tsawon minti ashirin, sai da Faruk ya shigo falon, sannan ta

dawo hayyacinta ta kula da iya tsawon lokacin da ta dauka tana tunani. Ba ta yi

aune ba, son Zaid ya shige ta farad’ daya, domin ba ta san so bane, sai da ta yi nisa sosai. Shi kuwa tsakaninsa da ita aika da karatu, baya ga haka, ko hira ba su yi.

A wannan yanayin ta kwashe shekara guda cikin soyayyar dan-uwanta wanda bai

san tana yi ba. Zuwa lokacin adimishan dinsu, har ya fito ta fara karatunta a

(A.T.B.U Bauchi), ganin Adda Zubaida ta yi aure anan, ya sa abin ya zo da sauKi.

Tafiyarta makaranta ne ya dan rage mata abubuwa, saboda rashin ganinsa ya sa ta

samu sassauci, duk da kuwa ta yi sabbin manema a Bauchi, ba ta ba su fuska ba.

Tun dawowar Zaid daga karatu, shekaru biyu kawai yayi yana aikin gwamnati, kafin

su hada kai shi da abokansa biyu, su bude kamfaninsu na na’ura mai Kwakwalwa.
Wannan aikin ne kusan ya canza Zaid daga Zaid din da, domin kuwa sai ya zamana

babu wani abin da ya sa a gaba, sai (AZ IT Consultants & Services.) Abu ya hadu da

albarkar iyaye, sai habbaka yake yi, babu kama hannun yaro.

**********

ABUJA, 2005

Yana zaune a cikin Apartment din da Abba ya ware masa, yana duba wasu

rahotanni da wani ma’aikacinsu, ya shiryo ne, wayarsa ta dau tsuwwa, bai da niyyar

amsawa, amma da ya ga fuskar wayar, nan da nan ya amsa.

“Haba dai Sweetheart, kuma haka ake yi ne? Sai ki share ni, don kawai kin tafi

Sakkwato?” Www.bankinhausanovels.com.ng

Asma ta yi dariya ta ce, “Haba Yaya Zaid kuma idan na share ka, ai kai me nemo ni

ne, ka ji ko, lafiya.”

“Uhm da wannan ma don wannan, ayyuka ne suka sha gabana. Yaya karatun dai?”

“Karatu, Alhamdulillahi, amma ya dau zafi.”

“Haka ne daman ai, Allah dai ya taimaka, sai fa kin dage, don na ji labari Umm tun

tafiyarta first class, take ja, idan ki ka yi wasa, za ta fi ki KoKari.”

“Kai rabu da Kwakwalwar Ummun nan, wa zai

iya Competition da ita? Ai sai mutum ya kar kansa.”

Dariya ya yi ya ce, “Duk Katon kan nan naki, ki ce ba ki da irin Kwakwalwar Ummu?

Ita fa saboda tsabar KanKanta, hatta kanta ma Karami ne.”

“Idan ta ji-ka dai tsakaninku, na gaisheka. Yaya Zaid banda credit.”

“Yau kam tunda kin kyauta, kin kirani kin cancanci Recharge card, na san sha’anin

Students.”

“Kai amma da ka kyauta min kuwa sosai, na gode. Ina saurare.”

Murmushi ya yi suka yi sallama, yana tunani a ransa, daga bisani kam kashe

komfutar ya yi, sannan ya fito Kofar Apartment din, wanda yake cikin katanga daya

da gidan Abba a unguwar Maitama. Domin haka nan ya samu kansa a cikin nishadii.

Ai ko Asma’u ba ta matsa a wurin ba, ta ga ya yi mata transfer din katin waya na

dubu biyar. Www.bankinhausanovels.com.ng

*************

BAUCHI 2008

Ranar da ta kammala jarrabawarta, ta hada jakarta tsab! Adda Zubaida kam tana

ganin ikon Allah, “Yanzu Ummu A. Ba za ki dan yi mana hutun bane za ki yi gaba?”

“Zan dawo saura sati a fara karatu, yanzu kam Allah ya gani na yi kewar Maami

sosai, kuma ke ma kin san don gidanki na ke, da kin ga sawunta a nan.”

“Hmmm! ‘Yar Maami kenan, kamar ke ce autan ma ba Twins ba. Na amince ki tafi,

amma ana saura sati biyu hutu ya Kare, zan kiraki na yi miki tuni.”

“Ah, Adda Zubaida sati biyu ya yi yawa ai. Ina laifin kwana biyar?”

“Cuwa-cuwa kenan, anya ba wani catch aka yi a Abujan nan ba ake ta saurin

tafiya?”

Nan da nan Umm Adiyya ta Hata rai, “Wuuu! Rufa min asiri. Allah ya suturu bukwui,

yau me ya kai ni? Inji da damuwar kaina mana.”

Adda Zubaida na dariya ta ce, “Ke dai Allah ya shiryeki. Wallahi, sai ki ci karatun ai.

Muna nan da ke, sai mun samo miki miji ai.”

“Wai, ina ce haka ku ka bar Adda Asma’, ni meye ya sa ku ka sa min idanu?”

“Wai ma ki bar rudin kanki, domin na san Abba hadaku zai yi idan ya tashi, ba sau daya ba, na ji yana fadiin hakan, don haka tun kafin ta fidda gwaninta, ke ma ki riKe

naki a hannu.””

“Kar ki damu, zan jira har ta samu nata tukun.” Zubaida dai dariya kawai Kanwar tata

take ba ta, domin da an mata maganar aure, to tamkar an kawo labari mai ban tsoro

Ne, nan da nan za ta ture shi a gefe, ita a tunaninta don ba ta ga wanda take so

bane, a rashin saninta, tsoron fitowar soyayyar wanda take so din, ya sa koda

yaushe take janyewa tattaunawa akan wannan maudu’in.

Ba ta tashi shiga tashin hankali ba, sai da mai daukarta ya iso, don koda wasa ba ta

taba tsammanin shi za ta gani ba, ita dai sun yi da Abba za a taho yau washegari su

kama hanya. Don haka ganin Yaya Zaid ya ba ta mamaki Kwarai, yaya aka yi ya bar

duka ayyukansa, don ya zo daukarta? Www.bankinhausanovels.com.ng

“Umm A. Magana dai Yaya Zaid yake miki kin yi shiru.” Adda Zubaida ce ta yi

magana, wannan ya sa ta dago a firgice. “Na’am Yaya.”

“To ko dai EE din ne suka fara juya maki Kwakwalwa tun yanzu?”

Kanta a Kasa, ta dan yi murmushi, “Ki shirya wai ku tafi, zai gaida su Baffah Abdu a

Gombe sannan ya koma, ko za ki jira shi sai ya dawo ku wuce?”

“Me za ta zauna ta yi? Ba sai mu je ta gaishe su ba, ki na ganinta, ba ta son

zumunci. Bakin halinta ya yi yawa, ba ta son mutane.” Gaba daya sai ta ji nauyin

shi, ganin har ya gano, ita ba mai son mutane bane. Duk da dai ba wai ba ta son

mutanen bane, ita dai ba ta sakewa ne da mutum, idan jininsu bai zo daya ba.

Tana ji, tana gani, ya sa ta shirya suka kama hanyar Gombe, ita tsoronta daya, kar

ta yi wani abu, ko ta ce wani abu da zai sa ya ganota, don muddin ya gane tana

sonsa, ta san za ta sha wulaKanci, don haka take samun labarin masu nuna

soyayyarsu da farko wa saurayi suke fuskanta, mafi yawan lokuta.

“Yaya ki ka yi shiru? Sanyi ki ke ji ne?”

“A’a”. Ta ba shi amsa a takaice, duk iya KoKarinsa na ganin cewa ta sake ya gagara,

to shi din ma daman ba wai hirar bace ta dame shi, yana da abubuwan da suka Www.bankinhausanovels.com.ng

wuce wannan, don haka ya yi shiru ya bar ta, har isar su.

Yau ma gidan a cike kamar ko yaushe wannan yana daya daga cikin dalilan da ya

sa ba ta cika son zuwa ba saboda hayaniya, amma kuma idan tana cikin ‘yan

uwanta, ta kan ji dadin yadda suke Kaunar junansu.

Alhaji Abdur-Rahman Nafada, matansa na aure uku ne, wannan ya sa yake da yara

da yawa, don dakin su Zaid ma su biyar ne. Zaid shi ne na uku, ya biyo Yayan shi

Nazif, sai babbar yarsu Sa’adiyya, akin Anty yaranta shida. Sai Umma wacce take

da yara shida ita ma. Don haka ba ka raba gidan da yara, duk da dai ‘yan matan sun

yiyyi aure, akwai ‘yan mata uku, sai samarin gidan.

“Wai lallai yau Zaid ka yi abin arziki, Umm Adiyya ka dauko mana? Shi ya sa na

hango hadari dazu ta gabas din nan.”

Duka jama’ar falon suka sa dariya, bayan sun ji bayanin Anty. Kunya duk ta rufeta ta

ce. “Anty, ai ina son zuwa, ba na samun lokaci ne, da zarar an koma, to karatu da

zafi-zafi muke yi.” “Ayya, to Allah ya taimaka.”

“Maryam, samo masu abinci da abin sha daga falon Babanku, na san can kam ba za

a rasa ba, kun yi tafiyar yamma.”

Umm Adiyya kam ta san ba yunwa take ji ba, sai dai ba yadda za ta ce su bari, shi

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *