UMM ADIYYAH CHAPTER 3 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 3 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                      Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Yaya ki ka yi shiru? Sanyi ki ke ji ne?”

“A’a”. Ta ba shi amsa a takaice, duk iya KoKarinsa na ganin cewa ta sake ya gagara,

to shi din ma daman ba wai hirar bace ta dame shi, yana da abubuwan da suka Www.bankinhausanovels.com.ng

wuce wannan, don haka ya yi shiru ya bar ta, har isar su.

Yau ma gidan a cike kamar ko yaushe wannan yana daya daga cikin dalilan da ya

sa ba ta cika son zuwa ba saboda hayaniya, amma kuma idan tana cikin ‘yan

uwanta, ta kan ji dadin yadda suke Kaunar junansu.

Alhaji Abdur-Rahman Nafada, matansa na aure uku ne, wannan ya sa yake da yara

da yawa, don dakin su Zaid ma su biyar ne. Zaid shi ne na uku, ya biyo Yayan shi

Nazif, sai babbar yarsu Sa’adiyya, akin Anty yaranta shida. Sai Umma wacce take

da yara shida ita ma. Don haka ba ka raba gidan da yara, duk da dai ‘yan matan sun

yiyyi aure, akwai ‘yan mata uku, sai samarin gidan.

“Wai lallai yau Zaid ka yi abin arziki, Umm Adiyya ka dauko mana? Shi ya sa na

hango hadari dazu ta gabas din nan.”

Duka jama’ar falon suka sa dariya, bayan sun ji bayanin Anty. Kunya duk ta rufeta ta

ce. “Anty, ai ina son zuwa, ba na samun lokaci ne, da zarar an koma, to karatu da

zafi-zafi muke yi.” “Ayya, to Allah ya taimaka.”

“Maryam, samo masu abinci da abin sha daga falon Babanku, na san can kam ba za

a rasa ba, kun yi tafiyar yamma.”

Umm Adiyya kam ta san ba yunwa take ji ba, sai dai ba yadda za ta ce su bari, shi

ZAMU TASHI 

ya sa ta yi shiru. Muryar Zaid ta ji ya ce, “Kai Anty abincin kun nan ku bar shi kawai sai dai dare, ni dai ba ni jin yunwa, sai dai ko Ummu‘ Ta ji mamakin yadda

tunaninsu ya zo daya, sai murmushi ta yi.

A hankali ta girgiza kanta. “Kai dai ka hanata ci, ai da ba ta ce ba ta so ba, sai da ka

yi magana. Rabu da shi, kar ki biyewa dan gidan kun nan, ya iya bakin hali. Maryam

tafi ki kawo mata.”

Ganin ta dage, ya sa ta hakura aka kawo abincin, amma dan kadfan ta ci, sai kunun

aya ne mai Sanyi ta sha sosai.

A falon cikin gida aka hadu da dare aka yi ta hira, sai ga Umm Adiyya da dariya,

saboda sai dai ba ka zauna da Umma da Anty ba, sai ka ci dariya, Mama kam tana

gefe ba ta shiga sha‘aninsu.

Wai saka yaran suka yi a gaba, sai dai su fada masu wacce tafi kyau. Duk abin nan

da ake yi, hankalin Umm Adiyya na kan Zaid da ke zaune kan kujerar zaman mutum

daya, yana ta danna waya, da ta ga zai dago

ido, sai ta maida ganinta wani wurin daban.

Washegari da sassafe suka dauki hanyar Abuja, sai dai yau ita ma ta shafawa kanta Www.bankinhausanovels.com.ng

lafiya, tun da suka fara tafiya, ta sa gyalenta a saman fuska tana kallon windo, ta

Lumshe idanunta tamkar ta yi barci. Kasancewar sun samu waya, an kwana rikici a

Riyom, ya sa suka dauki hanya ta Kano. Har shigar su Kano, ba ta motsa ba, duk

(Check Point), da za su zo, bai sa ta bude idanunta ba.

Duk rashin son hayaniyar Zaid, sai da shirun Umm Addiyya. Ya dame shi, “Wai gum

aka saka miki a bakinki ne hala?” Shiru ba ta ce komai ba, sai da ya nanata

tambayarsa, sannan ne ta juyo ta kalle shi, suna hada idanu, ta sauke ganinta, “A’a

kawai dai…”

“Kawai dai, ban iya hira mai dadi ba ko?” Ya tambaya idanunsa a kan titi.

Da sauri ta dago ta dube shi, Kwarai ta ji mamakin tambayarsa, “Yaya Zaid hira mai

dadi kuma?”

“Na yi ta miki magana tun dazu, amma kin yi nisa. Ba dai saurayi ki ka yi a Bauchin

ba, ki na tunanin tafiya ki bar shi? Anya ma ki na karatun kuwa? Zan yi magana da

Zubaida, ta sa miki idanu sosai, daga yin Session daya kin fara zurfi a tunani, ina

labarin sauran shekaru hudun kuma fa?”

Gaba daya sai ta ji maganar banbarakwai, wai namiji da suna Hajara, ita tana can Www.bankinhausanovels.com.ng

tana ta fama da ciwon sonsa, shi yana tunanin har ma tana da wani saurayin da za

ta iya Bata lokacinta a kan tunaninsa? Har da wani yi mata fada. Hawaye ne ta ji sun

ciko mata idanu, da sauri ta kau da kanta gefe, ta shiga gogewa a dabarance.

Shi ya zaci maganar da ya yi mata ne, ya sa take hawaye, don ya ga lokacin da ta

goge hawayen hade da dan jan hanci kadan.

“Ko dai mu koma Bauchin ne, sai na ce da su Maami ‘yarsu kam ta yi masu bye-bye.

Ta samu wanda ya sace mata zuciya.”

Dariya ta yi, don yadda ya yi maganar ta san zolayarta yake yi. Haka dai suke

magana jifa-jifa. Can shi ma ya yi shiru, lokaci-lokaci yana amsa waya. Ba ta taba

wahalalliyar tafiya ba irin ta ranar. Amma kuma ko ba komai ta Kara samun lokaci da

Yaya Zaid, wanda ya fi mata komai dadi.

Wannan hutun gaba ki daya ta yi shi ne cikin jin dadi, saboda falon Abba dai shi ne

wurin zamanta, ta fake da kallon labarai, amma hakikanin gaskiya shigowar Yaya

Zaid kawai take son gani. Dawowar Adda Asma’u daga Sakkwato ne ya Karawa

gidan armashi.

Wannan ya sa sam Umm Adiyya ba ta so karewar hutunsu ba, amma lokaci na yi,

haka ta tattara ta koma Bauchi. Ranar kamar anyi mata mutuwa saboda ta so Kwarai

Yaya Zaid ya ce zai maidata, amma ba ta gan shi ba ma ranar tafiyar, bare su yi Www.bankinhausanovels.com.ng

sallama, don haka koda suka isa, haka ta kashe dare cikin tunani tana kuka.

A wannan daren ne ta dauki dabi’ar tsayuwar dare, koda damuwa ko babu za ta

tashi bare tana da babbar matsala, soyayyar Zaid. Kullum tana cikin addu’ar neman

zabin Allah da kuma mafita.

Da yake a Hostel take zama, sai Weekends take zuwa wa Adda Zubaida, sam Adda

Zubaida ba ta karanci halin da take ciki ba, sai ma ta maida hankalinta kan karatu

tuKuru, bare ma aikin Lab. Da ake dibga masu, baya barin mata lokacin tunani, ga

Assignment ga Lab. Reports, duka sun hadu mata. Wasu lokutan ko sha’awar zuwa

Weekend din ma ba ta yi, saboda abubuwa sun cunkushe mata.

***********

“Baban Walid, ni kam ka duba min Ummu A, gaba daya ta canza banda yawan

tunani babu komai a gabanta.”

Umm Adiyya ta yi murmushi ta ce, “Baban Walid don Allah ka bar Adda Zubaida, ita

wai ba daman mutum ya yi shiru, sai ta ce yana tunani.”

Dariya ya yi ya ce, “Ki bar ta tana meditating ne saboda Kwakwalwar ta sha iska, ke kin dauka kowa ne irin ki?”

Kallonsu kawai take yi tana murmushi, saboda yadda rayuwarsu yake burgeta, ba

wanda zai yarda cewa shekaru hudu da suka wuce, a waya suka hadu, bayan ya

kira wrong number. Akan su ta Kara yarda da maganar nan da ake cewa, matar

mutum kabarinsa. Ga shi yanzu dansu daya har na biyu na kan hanya. Wannan ya

sa wataran ba ta damun kanta kan Yaya Zaid, saboda ta san idan mijinta ne, shi ma wataran zai so ta.

Ranar Asabar suna tafiya da ‘yar dakinsu takiyya sun fito daga NLT karatu ne. Www.bankinhausanovels.com.ng

Takiyya ta ce, “Umm Adiyya na manta na fad miki gobe su Ahmad fa za su isa

gaisuwa wurin su Baba.”

Da sauri ta dubeta ta ce, “Haba dai! Kai Allah ya sanya alkhairi, wai finally Ahmad

sarkin naci dai shi ya yi nasara.”

“Ai na fada miki, ba don nacinsa ba, da sai dai ya Kara gaba, don na sha sallamarsa,

amma yana nan Kememe.” “To yanzun me ya canza miki ra’ayi?”

“Kin ga duk iya shegen da na ke masa? Bai taba gajiya ba, kuma na san so yake

min tsakani da Allah kuma ni ma shi na ke so, don haka na ga ba amfanin Bata

mana lokaci, kawai dai ya faye matsi ne.”

Murmushi ta yi da ta tuno kanta, da za ta samu ita ma wanda take so ya so-ta kamar

hakan da ba ta da damuwa. Amma kowa da Kaddararsa.

“To Allah ya tabbatar da alkhairi, ya kuma nuna mana lafiya.”

“Ameen, saura ku.”

“Wuu! Ai mu kam ba yanzu ba, ai zan haukace idan na hada family da wannan

bakar wuyar da ake ba mu.” Takiyya ta yi dariya ta ce, “Wai, baKar wuya.”

“Dole ki faci haka, ke da ki ke EMT ba ki da matsala, amma ki na ganin yadda muke

shan wuya a Complex.”

“Allah dai ya sa a Kare lafiya. Kar ki manta fa ku ne ‘yan VC’s list.”

“Hmm, wannan zangon, idan na ci sa’a ne ma a tsinto ni a HOD’s list.” Www.bankinhausanovels.com.ng

“Haba ke kuwa kar ki karaya mana, a taimaka dai a dage.”

Suna shiga daki. Saudat ‘yar dakin su ta ce, “Umm Adiyya, dazu kuna fita, ki ka yi

bako, aka turo nemanki, don sun buga, wayarki a kashe.”

Juya idanunta ta yi cikin jin haushi, ita ta tsani bakin naci, daga ji ta san wannan

Ibrahim din ne, tsaki ta ja ta ce, “Can masu.”

“Sun bar saKo, wai na ce miki yayanki ne daga Abuja, amma sun wuce Gombe, idan suna da time za su duba ki, akan hanyarsu ta dawowa.”

Da sauri ta juyo, saboda ta ji an ce yayyinta, wannan yana nufin Yaya Saadik da

Yaya Zaid kenan. Maza ta yi ta karbi envelope din hannun Saudat. Kudi ne a ciki

dubu ashirin, sai ‘yar takarda, (Note), an yi rubutu mai kyau, ko duba biyu ba ta

bukata, ta san mai rubutun, don kullum sha’awa rubutun ke ba ta, a cikin cursive

handwriting yake rubutunsa.

“Mun shigo ba mu sameki ba, ga wannan ki sa kati, ba yawa, next time Inshaa Allah.

Take care.” Zaid Abdur-Rahman & Saadik Zubair.

Ranar ta karanta takardar ya fi sau ashirin, tana shafa rubutun tana jin Kamshin

takardar. Har takardar ta soma tsufa. Wannan ya sa ta haKura ta yi masu

kyakkyawar ajiya, daga takardar har kudin.

Murna da Kyar ya bar ta, ta iya barci ranar, sai dai ta ji haushin rashin haduwarsu.

Sai Allah-Allah take yi su biyo cikin makarantar a komawa. Sai da ta makara,

washegari saboda rashin barci da wuri, tana gama cajin wayarta ta nemi Yaya Saadik.

“Ke Mango Park mai kashe waya, ina ki ka shiga?”

“Hmm! Yaya Wallahi ina NLT na je karatu, ai

na ji haushi da ba ku sameni ba, na ga sako fa, na gode.” “Ba komai, Yaya Zaid ne ya ba ki. Call him.”

Ai nan ta hadiyi wani abu makut! Saboda tana da lambar wayarsa, amma ba ta taba Www.bankinhausanovels.com.ng

kirarsa a waya ba, saboda abinda muryarsa ke mata a cikin Kwakwalwarta da ilahirin jikinta.

“Yaya kawai ka fada masa, daga baya zan kira shi, yanzu an mana fixing lectures,

kuma na yi latti, sai Karfe daya kuma za mu fito.”

“To shi kenan, ga shi nan ma ya shigo ku yi magana.”

Ai kafin ta ce masa, a’a tuni har ya miKa masa wayar. Idanunta a runtse ta bude su a

hankali, “Hello, Assalamu-alaikum. Ina kwana… ina wuni… an kwana… Yaya Zaid?”

Gaba daya ta fada a jere hade da make goshinta cikin takaici.

“Lafiya Kalau, yaya karatu?”

“Alhamdulillahi.”

“Kin ci sa’a jiya, na samu shaida, ki na karatu da na samu akasin haka, da na gamu da ke.”

Murmushi ta yi ta ce, “Yaya na ga sako na gode, Allah ya biya da mafi alkhairi.”

“Ah, ba komai. Ameen-Ameen. To Sai anjima ko? Take care.”

Wai! Ai tamkar ta kusa shiga aljanna, tsabar dadin kalamansa, ga shi har bayan sun

gama wayar, dirin muryarsa bai bar kunnuwanta ba.

Ashe ta riKe wayar a wuyanta, ta rungume sai murmushi take yi, ba ta sani ba, bude

idanun da za ta yi, kawai ta ga su TaKiyya a gefen gadonta sun zuba mata idanu,

tana ganinsu, suka sa mata dariya.

“Yau kam za ayi ruwa da KanKara, asirinki ya tonu, wannan dai mun san ba Yaya

bane Yaaaya ne ko?” Suka fada suna mata tsiya, rufe fuska kawai ta yi tana murmushi.

*********(

Lokacin ne ta Kara samun natsuwa wurin yin karatun ma. Hutun da suka yi na gama

aji uku ne, ya yi daidai da lokacin tafiyar Adda Asma’ Service, su Abba dai suka yi

mata cuku-cuku, aka turata Abuja, ai ko nan da nan ta jona bautar Kasarta da wurin su Yaya Zaid, don tun ba yau ba, ta matsa masa akan wurinsu take so.

Har ma yake ce mata, “Ba ki na murna ba, aiki za ki yi kamar kowa, wurin mu ba

wasa.” “Eh, na yarda.” Ta fada a gaggauce.

“Anya ba kudin da muke biya ki ke so ba Asma’, wannan irin doki haka? Bari za mu

rage kudin Co-members, wannan shekarar.”

“Ah, don Allah Yaya ka yi hakuri.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Girgiza kai kawai ya yi ya ce, “See her! To na ji, shi kenan.”

Umm Adiyya tana zaune suka yi wannan maganar, amma ba ta buKatar kowa ya

fada mata komai, domin kuwa tunda take da Yaya Zaid, bai taba mata yadda yake yi

da Adda Asma’ ba, sannan ba ta taba ganin

yanayi wa kowa kallon da yake yiwa Adda Asma’ ba.

Da gani ba tambaya, ka san kallon da yake yiwa Asma’ daban ne da kowa. Wannan

tunanin ne ya fara wargaza mata Kwakwalwarta a karo na farko. Kar dai Yaya Zaid son Adda Asma’ yake yi?

************

Sun yi shirin kwanciya barci ne washegari. Asma’ ta bude wardrobe dinta ta fito da

wani setin turare na smart collections a cikin farin kwali take nunawa Umm Adiyya

hade da wasu kayan makulashe dangin su Assorted Chocolates.

“Ummu A. Tashi ki debi naki, dazu aka ban gift, ni ban san yadda zan yi da su ni

kadai ba.”

A take ta zabura ta zauna tana kallon kayan, jikinta ya hau Dari, har ga Allah ta yiwa

‘yar-uwarta murna ta samu wanda take so, yana sonta, amma da ganin kayan ta

tabbatar da zarginta, tabbas Yaya Zaid sonta

yake yi, idan banda haka, namiji bai

taba baiwa budurwa kyautar su turare ba, sai idan ya yaba, yana so ko kuma suna soyayya.

“Adda Asma’ ki dauka kawai duka, kin ga musamman aka ba ki, zai fi dacewa ke ki

yi amfani da su, shi ma zai fi jin dad. Kin nunawa su Maami ne?”

Asma’ na murmushi Kasa-Kasa cikin murna ta ce, “Ke ni nauyi na ke ji, ba zan iya

fada masu ba. Ai da kunya ko? Sai na je na ce Maami ga wannan kayan saurayina ya ban, ko me zan ce?”

Murmushi Umm Adiyya ta yi a hankali ta ce, “Ki na sonsa sosai ko?”

A hankali Asma’ ta lumshe idanu, ta sauke numfashi ta ce, “Ban taba jin komai ba, Www.bankinhausanovels.com.ng

kamar yadda na ke ji game da shi, you know, koman shi kyau yake min, kin san ban

taba gamuwa da wanda ya iya furuci yake kuma natsar min da zuciya ba, kamarsa.

Ke ko a wurin aiki, kin ga yadda yake mu‘amala da mutane kuwa? He is so nice.”

A take Umm Adiyya ta hau Dari, idanunta suka fara muntsininta, hawaye suka fara

zuba da sauri ta ruga, (Toilet) da gudu, saboda tabbas yadda take ji game da shi, ita

ma kenan. Yau ta shiga uku. Adda Asma’ ma tana sonsa kamar yadda shi ma yake sonta.

Asma’ dai sai bin ta, ta yi da kallo lokacin da ta fito daga bandaki. “Yaya dai Ummu A.? Lafiyan ki kuwa?”

YaKe ta yi wanda ya fi kuka ciwo ta ce, “Babu komai, ciki na ne kawai ya murda

lokaci guda, ina ga miyar taushen da muka ci da ranar nan ne.”

“Ayya Allah ya sawwaKka, akwai flagyl ai ba sai ki sha ba?”

“Adda Asma’ ke da shan magungunan nan naki? Na san ma zai tsaya Inshaa Allah.” Www.bankinhausanovels.com.ng

“Ke bari, ba a wasa da lafiya, shi ya sa za kiga abu kadan na damu.”

Bargo kawai ta shiga, ta juya mata baya, saboda ita kadai ta san me take ji a

wannan lokacin. Ita da ace Yaya Zaid wata daban ma yake so da sauKi, amma Adda Asma’ fa ita ce ‘yar-uwarta da take matuKar so, ba za ta taba iya shiga tsakaninsu ba. Dole ta yakice Yaya Zaid a cikin ranta, ta koya wa kanta rayuwar da babu shi a cikin tsarinta. Wannan ya sa tun saura sati hutun su ya Kare, ta gama sayen duk wani abin da za

ta buKata, ta hada Jakarta, ta yi masu sallama sai Bauchi.

Karatu kawai take yi haiKan, koda ta tashi yin IT dinta ma, ba ta koma ba, a nan

Bauchi ta yi, sai dai ta je Abuja sama-sama, ta Kara dawowa. Duk wanda ya santa,

zai yi wuya ya gano canjin a wuri nata, saboda daman can ba ta da hayaniya,

wannan ne ya Kara ba ta damar boye sirrin zuciyarta.

Ranar Alhamis bayan ta taso daga wurin da take IT ne. Adda Zubaida ta buKaci ta yi

mata rakiya zuwa kasuwa, daga nan suka wuce gidan su Baban Walid, saboda dubo

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *