UMM ADIYYAH CHAPTER 34 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Kamshinki ya iya tafiya da hankalin mutum, za mu zauna ayi min bayani. In fact! Bana buKatar bayanin ma, ki zauna kawai cikin shiri, anjima idan na dawo.” Yana fadan hakan ya kashe mata ido, ita kuwa nan take Karyarta ta Kare, tuni ta shiga wuki-wuki da idanu. Da sauri ta sake shi, “Ahaf! Shegen tsoron tsiya, da gaske yau kam sai dai idan gidan za ki bari, amma daga ke har Antin ba zan saurareku ba. Haka kawai…” Na ji sai ka dawo.” Tana Allah-Allah kar ya Kara yanko wani zance mai nauyin. “Wear something bright.
And flowy.” Ya fada daga bakin Kofa, sannan ya fita daga dakin, ita kuwa ta take masa baya, tana ji kamar tana yawo a gajimare. Yaya Zaid bai da dama. Idan ta biye masa wataran zuciyarta za ta tarwatse.
********
Ba ta yi kasa a gwiwa ba, duk wani shiri da ta san ya dace ta yi, shi ta yi har da kiran Adda Asma tayi ta Kara bata wasu shawarwarin da dabarun. Ta shirya tsab! Cikin
ZAMU TASHI
wata riga mai launin ruwan dorawa, ta yi kyau sosai, ita kanta ta san yau ta kaleleye, sai yalki fatarta take yi, ga dadadan Kamshi, ga kyakkyawar shiga, labbanta sun sha lip gloss da tinted lipstick. Idanunta sun sha gazal.
Duka wannan wa yayanta na kanta Zaid Abdur-Rahman mutumin da take so fiye da kowa, mutumin da ba ta taba hada son shi da wasu Www.bankinhausanovels.com.ng Samarinta ba, ba ta taba bada gurbinsa wa kowa ba. Mijin da za ta yi alfahari da shi a ko ma ina ne duniya da lahira.
********
Ta fito daga kicin din ne ta ji kamar muryarsa, ba ta ji shigowar shi ba sam, wannan ya sa ta fadada fara’arta, cikin sanda ta isa inda yake zaune akan kujera ya juya mata baya. Sai da ta iso ta fahimci waya yake yi”No, na fada miki ba zan iya magana yanzu ba. Na ji, ina gida, we’ll talk later.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsakanin su biyun, ta rasa wa fuskarsa tafi nuna alamun razana. Yaya Zaid da bai zaci tana jin zancensa ba, ko kuwa ita da ya sake ci mata fuska a karo na bila adadin. Yaushe zai daina mata Karya ne? Kallo daya ya wadatar ya san irin ta’asar da ya tafka. “Twinkle, tsaya ki ji ba abind…” Wucewa ta yi zuwa dakinta da ke sama, saboda ta san idan ta tsaya a nan, wata Kila Innayo ma ta gama jin duk abinda za ta amayar daga ranta, da yawa za su iya
kai ta kurkuku, idan aka aunasu a mahangar shari’a.
Sai dai tana jin takunsa a daf da bayanta, inda ya biyota, fasa shiga dakin ta yi ta shige falon saman.
“Kai da waye ka ke wayar?” Ta juyo a fusace ta tambaya, ba wai don ta damu da taji koma wacece bace, sai don kawai abinda ta samu kanta da fada kenan. Adiyya, ba komai ba…” Idanunta a kafe a kansa ta datse haKora cikin wani irin tashin hankali. Ba ta san ma me take son ji baa wannan lokacin.
“Yaya Zaid ina tsammanin a yanzu kam mun wuce Boye-boye a zaman mu. Kawai ka fada min gaskiya, ita ce ko?” Ya fara motsa bakinsa da niyyar yin magana, sai kuma ya dubi gefe hade da runtse Www.bankinhausanovels.com.ng idanunsa da sauke ajiyar zuciya. Ki bar maganar nan, ba yanzu ba don Allah, kin ji?” Kallon sa take yi cikin tsantsar mamaki, “Na bar maganar akan wani dalili? Ka ma ji me ka ke fada kuwa? Akan me ya sa kullum mu ke nan, matsalar mu a gidan nan? Ka ce min kai ka ma rantse min ka daina mu’amala da ita, sannan yanzu me ya sa baka je sun aura maka Fatiman ba, idan har zama da ni kadai ce bai maka ba, me ya sa sai ita? Ko ita wannan din, ka je kawai ka aure ta mana, kowa ya huta.” Ba ta jin za ta iya furta sunanta ma, don ciwo abin yake mata, baKin-ciki take ji lokacin da ta hasaso sunanta ma.”Twinkle, kin ga ba ki da lafiya, ba ki gama warwarewa ba, ba na so ki dagawa kanki hankali, kan abin da ba shi ne ba.”
“Really? Daga inda kunnuwana suka ji min komai, sai nace ina daja da hakan, amma kuma me ra’ayina zai yi? Tunda kalamanka ne sama da nawa a ko ina.”
Bakinta ne ta ji ya fara Dari, don bacin rai ta ma rasa me za ta fada ta huce. Ganin ya matso kusa da ita ne, ta ce, “Kar ka fara…” Yadda ta yi saurin ja da baya ta ware idanu, ya Kara tabbatarwa Zaid ba za ta ji sassauci ba. Ko na fada miki ba abinda hakan zai kara haifarwa sai tashin hankali don haka mu Www.bankinhausanovels.com.ng
bar zancen.” Harde hannunta ta yi saman Kirjinta. “Me zai hana ka jarraba ka gani, ai ba da roba aka yi ni ba, da zan narke.” “Fariha ce.” Wane irin duumm Umm Adiyya ta ji ya giftawa kunnuwanta, ba ta taba zaton zai iya dubanta ya fada ba, duk da ba ta son ya yi mata Karya, amma har sai ta gwammaci ya yi Karya, ya ce wani abin daban, ba wannan ba.
*********
BABI NA ASHIIN DA BIYAR
“Haka, Fariha sunanta.” Ta fada cikin jin daci, tana sane da lokacin da ta dage har sai da ya fada mata sunan yarinyar da ta taba gani a ofishinsa.
“Ba ga shi ba na fada miki, na san halin da za ki shiga, amma kin dage…” Hannu ya sa ya shafo saman kansa.
“Dole na shiga wani hali Yaya Zaid, ni ka ke kallo a gabana, ba musu ka ke fada min abin da na Ki jini, na fi tsoro, ka ke tabbatar min da kasancewarsa gaskiya, me ka ke tsammani dama? Yaya ma za ka sake bari hakan ta faru? Bayan irin halin da muka
kasance akan hakan?” Ki na tsammanin ba na da na sanin hakan ne? Ban yi da na sanin aurenki ba Umm
Adiyya, kodayaushe sai na yi da na sanin sanadin da ya yi dalilin aurenmu.” “Wannan shi zai sa na mance abin da ya faru, ko kuwa shi zai ba ka dalilin komawa
ruwa?” Zaid ya hadiyi kullalen yawu, hade da jinginuwa da bayan kujerar da ke gefensu. “Ba
ki san irin da-na sanin da na yi game da hakan ba Adiyya, duk yadda ki ke ganin girmana, ranar ya fadi a idanunki da ki ka sameni a wannan yanayin, ina kuma ga Allah da Shi na fi yiwa laifi? Na tsani kaina a dai-dai lokacin da na ganki a bakin ofis dina…”
“Shi ya sa yanzu na ga ka tuba ai.” Ta fada Kasa-Kasa hade da kau da kanta. Tana fada ta yi da-na sanin wannan furucin. Da sauri ta dube shi ta ce, “Bai dace na fadi haka ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ga yadda Kwayar idanunsa suka sauya, Kwarai ya ji zafin furucinta. “Ba komai gaskiya ki ka fada ai, sai dai ina son na kawar miki da wani abin, wayar
da ki ka ji ina yi da Fariha, ba komai bane illa fada mata na ke yi ta daina kirana a gida, aiki ne ya hada mu, kuma na fi son ta tsayar da mu’alamarmu a kan hakan kawai.” Wata dariyar takaici ta yi sannan ta ce, “Yaya Zaid, ina jin turanci dai.” Murmushi ya yi mai sauti ya ce, “Na sani Little Engineer, ba za ki fahimci duka komai ba yanzun, saboda kanki ya shige wani wurin, amma ina tabbatar miki da cewa ba
mu tare, na yanke duk wata mu’amalata da ita.”
“Ita kawai?” Ta fada tana Kankance masa idanu.
Kansa ya daure, goshinsa ya tattare alamar rudani, “Akwai wasu ne?” “Na ganta ranar. A ofis. Na ganta tana fita daga ofis dinka, kuma I smelled her perfume on you.” Ta Karasa fada jikinta na bari.
Cak! Zaid ya tsaya, sai tunaninsa ya koma ranar da take nufi. Runtse idanunsa ya yi, ya riKo kansa da ya ji ya sara masa. “Akwai abinda za ka fada min wanda ya wuce wanda na gani da idanuna, na kuma ji
da hancina, ranar Kamshin fure ka ke yi. Fure! Yaya Zaid. Ba turarenka mai Kamshin fure. You touched her!” Tana ganin sauyin da ya ziyarci fuskarsa na tsantsar bacin rai, amma ya daure ya rike bacin ransa, sai jijiyoyin da suka bayyana a kansa na tsantsar tashin hankali. Ajiyar zuciya ya kawo ya sauke a hankali. Ki saurareni.”Wani irin jiri ne ta ji yana neman kwasarta, ta fashe da wani kuka mai gigitarwa. Ta gaza yarda abinsa ya yi tsamari irin haka, duk iya KoKarinta. Duk yadda take ba shi gabaki daya kulawarta. “Me za ka ce min?”
“Na amince kin ga fitarta a ofis dina, zai iya yiwuwa kin ji Kamshin da ba nawa ba a ofis dina, ko a jiki na, kamar yadda ki ka fada.”A take a lokacin sai take jin kunyar ma adon da ta yi masa, wani sanyi ya buso ta
Kofar Balcony din falon da ta mance ba ta kulle ba. Bisa dukkan alamu ba za ta taba burge shi ba,Www.bankinhausanovels.com.ng idanunsa na kan matarsa ta waje. “Me ya sa? Why Yaya? Why?” “Shhh! Please! Adiyya, ki yi shiru. Ba na son ganinki a wannan yanayin.” Motsa Kafafunta ta yi a sanyaye, ta jinginu da jikin kujerar da yake jingine akai, a hankali ta sulale Kasa, shi ma bin ta ya yi, suna durkushe a falon nasu. Ta san cewa ya bata hakuri, ya kuma yi nadama daga kalamansa, amma yaya za ayi ta yarda da shi? Bayan duk abinda suka fuskanta, ya boye mata abubuwa da dama na rayuwarsa da ma wanda suka shafeta. Wasu ma har sai ta tursasa shi ta ritsa shi, sannan yake shaida mata. Me kuma yake boye mata, wanda za ta tsammanta a gaba? Zuciyarta ta yi Kuna a lokacin da ta yanke abin yi aranta. “Ya yi min nauyi da yawa
ban san ko zan iya daukar komai ba… Idan ka gaji da ni ne kawai ka rabu da ni, kowa ya huta, tun kan zuciyata ta buga.” Kamar Zaid ya san me take shirin yi, a take jikin sa ya sandare, idanunsa ne kawai
masu mika saKon halin da yake ciki. Tamkar mai roKonta da dukkan Karfinsa akan ta yarda da shi. Yaya za ayi ta yarda da shi? Bayan bai ba ta dalilin yin hakan ba? “Abin da ka aikata, ba Karamin abu bane, zai hautsina min kai, zai lalata min zuciya
muddin na _ sake fuskantar hakan daga wurinka.”
Matsawa ya yi kusa da ita, ya sa hannu yana goge hawayenta. “Shssh! Adiyyata, ba
zan taba sa ki a cikin halin da ki ka shiga a baya ba, kuskure ne wancan din ma, kuma ko ba komai, ba ki shiga rayuwata ba a lokacin. Zuwanki, ya sa rayuwata komai ya canza a idanuna, kin sa na fuskanci rayuwata na Kara kusantar Allah, na koyi darasina Adiyya. Na canza, na san ba ki yarda da ni ba, amma na fahimci hakan na da wuya sosai a wurinki. Musamman da ki ka sameni da babban laifi. Amma don Allah ki ba ni dama na gwada miki cewa ba wancan Zaid cin bane ni yanzu.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani abu ne mai zafi ta ji shi kamar malolo a maKoshinta, a lokacin da idanunsa suka ci-gaba da roKonta ta amince masa. Saura kiris! Ta amince, zuciyarta ta gama ba ta amsar, ta amince, sai dai kuma ba a nan matsalar take ba. Maganar gaskiya, ita ce da kai wannan Zaid din ne, wannan yana nan tamkar lokacin da na fuskanci cewa Fatima ba matarka bace. Har yaushe za ka ci-gaba Boye min rayuwarka?” Ki yarda da ni Adiyya.” Ya fada hade da riko hannayenta zuwa gurbin da zuciyarsa take.
Ta ma rasa me za ta yarda da shi? Marairaicewarsa a lokacin ko zafafan kalamansa masu Kunanta? Ta Ki dago masa maganar a lokacin can da ta ga fitar matar can Fariha daga ofis dinsa, ne saboda ta yarda da shi har cikin ranta, da ya ce mata ya tuba, ta yarda da shi, da ya ce ita yake so, ta yarda da shi da ya ce ya yanke duk wata mu’amalar banza da Kadangarun bariki. Nade Kafafunsa ya yi, bayansa na manne da bayan kujerar, ba tare da ya sake
hannunta da ke Kirjinsa ba, ya ce “… Yes! Turarenta ne a jiki na, kamfaninsu yana cikin daya daga cikin wadanda abin nan ya shafa na (Data Breach), ita take bibiyar yadda abubuwa suke a bangarensu, tun aurenmu ban sake kulata ba, ba hanyar da
bata bi ba don ta samu Kofa, saKwanni, waya, (Social Media), ta kai ga sai da na kira kai tsaye na ce ta daina nemana. Ba na son mu rasa kasuwancinsu, haka nan ba na son na rasa kaina, don haka da
ta nemi zuwa don maganar Business, ban hana a bari ta shigo ba, illa iyaka na ba ta
damar ta gama abinda za ta yi, ta fita, niyyata ma na mayar da al’amuranta wurin Femi.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG