UMM ADIYYAH CHAPTER 4 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
Ke bari, ba a wasa da lafiya, shi ya sa za kiga abu kadan na damu.”
Bargo kawai ta shiga, ta juya mata baya, saboda ita kadai ta san me take ji a
wannan lokacin. Ita da ace Yaya Zaid wata daban ma yake so da sauKi, amma Adda Asma’ fa ita ce ‘yar-uwarta da take matuKar so, ba za ta taba iya shiga tsakaninsu ba. Dole ta yakice Yaya Zaid a cikin ranta, ta koya wa kanta rayuwar da babu shi a cikin tsarinta. Wannan ya sa tun saura sati hutun su ya Kare, ta gama sayen duk wani abin da za
ta buKata, ta hada Jakarta, ta yi masu sallama sai Bauchi.
Karatu kawai take yi haiKan, koda ta tashi yin IT dinta ma, ba ta koma ba, a nan
Bauchi ta yi, sai dai ta je Abuja sama-sama, ta Kara dawowa. Duk wanda ya santa,
zai yi wuya ya gano canjin a wuri nata, saboda daman can ba ta da hayaniya,
wannan ne ya Kara ba ta damar boye sirrin zuciyarta.
Ranar Alhamis bayan ta taso daga wurin da take IT ne. Adda Zubaida ta buKaci ta yi
mata rakiya zuwa kasuwa, daga nan suka wuce gidan su Baban Walid, saboda dubo
ZAMU TASHI
Hajiyarsa.
Daidai Kofar gidan su Baban Walid din suka hadu, “Sorry.” Ta fadia, saboda shige masa gaban hanyar wucewarsa. Babu komai, Bismillah.” Ya fada cikin wata nagartacciyar murya. Fitowar Adda Zubaida ne, ya sa ya Kara fadada fara’arsa, “A’a babbar Addarmu da kanta, ashe ku ne ku ka shigo? “Eh, TJ. Ka na nan abinka, sai dai haduwar bakin titi.”
Murmushi ya yi, yana wasa da makullin hannunsa, yace, “Maman Walid ke dai ki bari kawai, jiya ma na shigo garin. Ina Big Man yake ne?” “Ai yana cikin gida, ya maKalewa Hajiya wai yau wurinta zai kwana. Shi ya sa na bar shi. Na ga alamar kawai drawer din shi zan kawo nan, saboda yana so ya Kauro Karfi da yaji.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ah, to ya ga sakewa, ba dole ba, anyway, sai na shigo ko zuwa anjima ko gobe da Safe”. “Goben dai TJ. Na san ka sarai, za ka sa na ajiye maka abinci ka shanyani da abina.” Tana dariya ta sa Remote ta bude motarta. Umm Adiyya ta kama hannun ta bude ta shiga, yana murmushi ya mata kallo daya, sannan ya wuce cikin gida. “Adda Zubaida ke da dangin mijinkin nan kun 1ya surutu, shi ya sa ba na son rako ki gidansu Baban Walid, idan kun samu hira sai ku manta da mutane.” “Lah, ai wannan ba komai bane, idan TJ. Ya so surutu, ni karan kaina yana fin Karfina, shi ya sa da kansa ma ya ce sai ya sameni a gida ya san kansa. Wannan shi yake bin Gimbiya daga Baban Walid sai ita, sannan TJ. A Lagos yake aiki da
NPA (Nigerian ports authority) Ya kan kwana biyu kafin ya zo. Yana da kirki sosai.” Hmm! Ke duk dangin mijinki waye bai da kirki? Kowa haka ki ke ce masa mai kirki.” Dariya ta yi ta ce, “To ba gaskiya bane? Ai
yabon gwani, ya zamo dole, kuma ba laifi gaskiya ‘yan-uwan Baban Walid suna so-na kuma Kirkin su is natural.” Haka dai suka yi ta hirar har suka isa gida. Ai kuwa washegari suna zaune a falo sai ga TJ. Ya shigo. Gaisuwa kawai ta hada su da Umm Adiyya, ta mike za ta bar falon, ruwa ta kawo masa da drinks, sai abinci, tunda Adda Zubaida ta riga ta shirya.
Tana ajiyewa ta wuce ciki, daman zaman nata ma Baban Walid ne yake mata tsiya, wai sai ta kunsu a daki kamar kayan wanki, shi ya sa take fitowa, to idan sun yi baki kam dakin Adda Zubaida take zamanta. Tana wucewa TJ. Ya debi juice din da suka yi da carrot da ginger ya sha, sai ya ce, “Maman Walid bakuwa ku ka yi ne?” Dariya ta yi ta ce, “Amma dai TJ. Akwai ka da tsiya. Umm A. Din ce ba ka gane ba ko me?” “No, seriously, wannan din Umm Adiyya ce?” Ya tambaya cikin daga gira. Shi yasa mana, na ga ka na wani kama kai, ka dauka wata ce, kadan latsa ko?” Cikin murmushi ya shiga sosa kansa, “To ai, Maman Walid ya zamo dole a yi wani abin akai, don gaskiya har ga Allah tun jiya da ku ka wuce, yarinyar ta tsaya min a rai, ashe ma ta gida ce, shi kenan, ai ni kam ta fadi min gasasshiya.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Tana dariyarsa ta ce, “Wannan jan aikin kam na bar maka. Ummu A. Lamarinta sai ita. Ka sameta ku yi magana, wannan kam ba ruwana a ciki.”
Haba dai kuma babbar Adda, kar mu yi haka da ke mana, an ce fa babbar Ya, uwa, ba za dai ki so ki bar ni cikin matsala ba ko? Ki dan shige min gaba ko yaya ki ka ce?” Zaro idanu ta yi ta ce, “Wuuu! Wannan din? Ga dai lambarta karba, ka nemeta, idan ku ka daidaita, sai na yi maka kamfen.” “To an yi, an gama, tunda kin bada goyon baya. Yaya kam bai shigo ba, har yanzu ko?” “Ya kusa, na san yana ma hanya yanzu kam.” “Ni ina ga zan wuce, ki gaishe shi, za mu hadu gobe Inshaa Allah.”
“Ba ga irinta ba, ai yau babu inda za ka je, sai ka cinye abincin nan tas!” Yana dariya suka ji sallamar Baban Walid, “Yawwa shi kenan, ga shi ma ya dawo
sai ka zauna da tushe.” Karasawa ta yi zuwa wurin mijinta, ta yi masa sannu da zuwa, ta karbi kayan hannunsa zuwa ciki. Sai da ta tabbatar ya samu natsuwa, sannan ta bar su a falon ta yi ciki.
***************
“To sarkin tunani, an fara aikin ko?”
“Adda Zubaida da ba ki bar Walid ba, gidan ya yi shiru da yawa.” “Ai ya je can dai ya Candana masu, ni ma ko zan dan samu hutu.” Murmushi ta yi ta dauki wayarta tana kallon hotuna, can kuma ta ajiye ta shige wanka, koda ta fito Adda Zubaida ta shiga, don haka ita ma ta yi shirin barci, ta kwanta. Bakuwar lambar da ta gani a wayarta ce, ta sata daga wayar tana ganin fuskar da kyau. Kamar ba za ta daga ba. Can kuma da aka sake kira, sai ta daga don ta ji wanene. “Assalamu-Alaikum.” Wa’alaikis-Salam, kin wuni lafiya?”” Ya fada, bayan shiru ya dan ratsa maganar da ta yi. Muryar da ta ji ne ya sa ta shiga tunanin inda ta taba jin muryar, amma ta manta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kafin ta tambayi ko wayene, ta ji an ce, “Ki na magana ne da Tijjani Muhammad Gital. TJ. Da fatan ban katse miki barcin ki ba.” Idanu ta fitar waje kawai, numfashinta yana neman ya gagareta.
Da Kyar ta samu numfashinta ya dawo daidai. Ko ba ta tambaya ba, ta gane yanzu kam, TJ. Ne Kanin Baban Walid. “A’a ina dai shirin yi.” “To dama na kira ne mu gaisa, amma tunda za ki kwanta, bari na bar ki, sai da safe ko?” “Ba komai, wani abu ne?”
Tambayarta ta so ta ba shi dariya, amma ya ce, “Idan har ba kya sauri, za ki iya jin koma menene zuwa gobe da yamma, idan you are free.”
Ta san ba yadda za ta yi masa Karya ta ce tana wurin aiki, saboda washegari Asabar ne. Don haka ta ce, “To Allah ya kai mu.
“Na bar ki lafiya.” Kawai ya fada, ya kashe wayar. Duban nata kan wayar ta yi ta hade rai, ta san ba mai wannan aikin, sai Adda Zubaida!
**************
BABI NA HUDU
“Adda Zubaida ke ma kin san ba ki kyauta min ba kwata-kwata, yaya ma za ayi ki fara ba shi lambata? Wallahi darajar Baban Walid ya hana na surfa masa mai zafi, me ya sa zai karbi lambata a wani wuri, bai nemi izini na ba?” Adda Zubaida ta bata rai ta ce, “Ni din ce wata? Ni ban san meye matsalarki ba, ke ba dama wani ya tunkareki da magana kamar wata ‘yar Secondary school. Shi kenan ki hau fada? Tabbata za ki yi a haka? Sai Abba ya miki auren sadaka, za ki sani ai, don kowa ya gaji da saka miki idanu. Ina laifi ki dan ba shi dama ki ga yadda za ku Kare?” Turo bakinta ta yi gaba ta ce, “Ni Adda Zubaida, gaskiya ba yanzu zan yi aure ba.”
“Yanzu shekarunki ashirin da biyu, sai kin yi talatin ne za ki yi auren ko kuwa me kike jira? Bari na fada miki, idan mace tana cikin lokacinta ba ta natsu ta kama dahir ba, to na fada miki gaba kadan, sai ta rasa me zuwa ko tayawa ne, ke kin fi ni sanin wannan.” A ranta ta ce, “Ni kam ban san meye bane a cikin rabona ba, amma na san ba zan taba son kowa ba bayan Yaya Zaid, shi kuwa ya wuce inda na ke, don haka aure kam sai dai randa Allah ya Kaddaro ko ma da waye ne, shi kenan, amma ba ni da lokacin wata soyayya.” Hawaye ne suka fara bin fuskarta, don haka ta miKe ta wuce daki.
Adda Zubaida kam bakinta ta riKe tana ganin ikon Allah. Haka suka zauna kwanaki
biyu ba ta shiga sabgarta, wai a dole tana fushi. “To wai har yanzu ba ki huce bane? Ina ce kin fada masa ba ki shirya ba, shi kenan shi ma Allah ya hada shi da
rabonsa.” Adda Zubaida, ba wai na ji haushin turo min shi da ki ka yi bane, amma ke ma kin san Abba yana samun labarin Kanin Baban Walid ne, ko ba mu daidaita ba, shi kam zai yi na’am, don yadda ki ke yabonsu, haka kullum shi ma yake yabon jama’ar gidan.” “To meye ne a ciki? Bayan ke ma kin san cewa yana da halin Kwarai, kuma bai da makusa. Kowa matarsa yake aura, idan ba ki cikin rabonsa, ba yadda za ayi komai ya daure, kawai lokaci za ki dan ba shi, shi kenan fa! Hannu ta harde a Kirji tana gunaguni. “To shi kenan na ji, amma kar ya kuskura ya nemeni a Abuja, don ba na son Abba ya gan shi. Bare ma magana ta yi nisa.” “Ummu A. Ko dai akwai wanda ki ke so ne?” Jin tambayar Adda Zubaida ya sa sai da ta ji gabanta ya yanke ya fadfi, nan da nan ta hau kame-kame da inda-inda. “Ah, Adda Zubaida so kuma? Ai tare muke zaune, da akwai wani, ki na ga da ba ki sani ba?” “To ai na ga yadda ki ke kafewa ne akan rashin son kula kowa, abin yana damuna.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Kar ki damu, ba komai, our able Maman Walid.” Ta fada tana murmushi hade da rungumo ‘yar-uwarta, hawaye ne ya biyo fuskarta, ta yi saurin share su, sannan ta dago tana yake. Adda Zubaida na fita daga dakin ta kwanta kan filo ta shiga risgar kuka kamar an aikota. Ita ta rasa wannan wace irin jarabawa
ce. Wai ace duk tulin wadanda suke cewa suna sonta, ta rasa wanda za ta so a cikinsu, sai wanda bai san ma tana yi ba? Bayan hakan ma, ya yi nisa a wurin Kaunar ‘yar-uwarta.
*************
TJ ko bai saduda ba, duk da wasu lokutan ya kan ga kamar ba haske a al’amarin. Musamman da yake Lagos tana Bauchi, amma hakan bai sa ya karaya ba, kullum
yana cikin mata waya. Wataran su shirya, wataran a babe, duk randa Zai mata magana kan abinda yake ji
game da ita, to fada za su yi kaca-kaca, idan zai kawo mata wata hirar ta bangaren ilimi, to nan ne za su shirya. Hutu ne kawai ke kai ta Abuja, don wataran ko bikin sallah a Bauchi take kayanta.
Komawarsu final year ne, ya sa ta ji tamkar da wasan yara take yi a karatun, don haka ta maida hankali kacokam ga karatun ta. Ta kwantar da hankalinta har wani bulbul ta yi. Kwatsam! Ranar Asabar Asma’ take shaida mata za a zo ayi tambayarta. “Ke yau ba wanda ya kai Dee murna, kamar an ce yau ne daurin auren. Ummu A. Ki tayani addu’a.” Wani Karar murna ta saka ta ce, “Hinyau su Adda Asma’ amare, don Allah kar su ce za ayi auren a wannan shekarar, ku jira sai na gama ina gida.” “Ka ji ki dai, sai mu yi ta zaman jiranki, randa A.T.B.U dinku suka ga daman shiga yajin aikinsu kuma fa? Lalle ma lokaci kawai za ki samu ki taho.” “To Allah dai ya tabbatar da alkhairi.”
“Ameen. Kar ki damu, zan ce Maami ta bar sauran Shopping, sai kin zo sai mu yi tare.
Cikin Karfin hali Umm Adiyya ta ce, “To shi kenan, Allah ya kai mu.”
Murmushin tausayin kanta kawai ta yi, sannan ta daga littafin (Micro Computer & Micro Electronics) dinta tana dubawa, sai dai maimakon ta fahimci abin da take karantawa, sai ta ga komai ya dawo tamkar zare. Sai da ta dage da addu’a, ta samu natsuwarta, ta mance da komai. Suna tare da su Idris ne, bayan sun taso daga wani gwajin da suka yi, suka ga ta tsaya cak! Hannayenta rungume da handouts dinta da wayarta. Umm Adiyya lafiya?” Muhammad ya tambaya. A hankali ya dago ya dubi inda idanunta suke kallo. Ganin mutumin yana masu murmushi, ya sa ya saki ajiyar zuciya. “Ba ki san shi bane?”
Yake ta yi ta ce, “Yayana ne.” Ta fada tana kallon Zaid da ke tsaye sanye cikin neck shirt da jeans da agogon silver na chain da ya kawata hannunsa.
Nan da nan ta seta tunaninta, saboda kar ma ya gane komai, ta Karasa inda yake tsaye jikin motarsa, a wurin Parking din motoci a gaban Complex. “Yaya Zaid yaya aka yi ka san inda za ka sameni?”
Murmushi ya yi, bai ba ta amsa ba, sai da ya mikawa su Idris hannu, wadanda suka fara gaishe shi. “Ina wuni Yallabai?” “Assalamu-Alaikum, yaya karatun dai ana ta fama?” Ya fada fuska a sake. “Eh, Wallahi.” Muhammad ya ce. “To ya yi kyau. Allah ya taimaka.” “Ameen-Ameen.” Dukansu suka amsa. Sai da suka wuce ne, ya bi su da kallo ya dubi Umm Adiyya, “Ke kuma ‘yan maza ne Kawayenki?” Yaso ya ba ta dariya, amma yanayin da ta ke ciki ya hanata wannan daman. “Test muka fito.” Muna tare da Saadik ne, amma ya tsaya can wai za su gaisa da wata Saudat ce ko WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
waye?” Ajiyar zuciya ta yi, shi ya sa mana Saudat ta isheta da tambayar labarin ‘yan gidansu, wato daman Yaya Saadik ne ya dan zagayo. Cikin karfin hali tace, “Yaya hanya?” “Lafiya Kalau. Mu Karasa ko ba hostel za ki koma ba?” Ba tare da ta amsa ba, ta zagaya ta zauna a daya gefen. Yana shigowa ta ce. “Congratulations.” Juyowa ya yi ya kalleta, sannan ya Karasa saka seat belt dinsa “Na gode duk da ban san na meye bane wannan.” Ta gefen idonta ta dube shi, idan ma ya zo ne ya Kara juya mata tunani ko lissafi ba za ta taba barin hakan su faru da ita ba, don ta gama da wannan bangaren na
rayuwarta. A hankali suke tafe, har suka Karasa (NANA KHADIJA HOSTEL). Nan suka gaisa da
Yaya Saadik, ita dai Allah-Allah ma take yi su tafi, a wani Nangaren don ta gamu da Saudat, a daya bangaren kuma ba ta son ko ganin Yaya Zaid.
Cikin ikon Allah, bai wuce minti goma ba, suka ce za su wuce don suna kan hanya,
saboda Yaya SaadiK zai koma Gombe ne, yayin da Yaya Zaid kuwa wani aikin ne ya kawo su Bauchi. Don haka suna tafiya ta sauke numfashi.
Bayan sun koma daki ne ta dubi Saudat ta ce, “Asirinki ke ma ya tonu, wato daman abin kenan, shi ne kina Kus abinki. To Dangin miji mode activated, bari na fada miki, zan zuga shi ya fasa, tunda ba a ban kula na musamman ina matsayin Kanwar miji guda.” Saudat na dariya ta ce, “Ai yayankin nan abin tsoro ne, don haka na bar maku kayanku, ke daga zuwa sau biyu, yana min maganar zuwa gida. Haka daman ‘yan Nafadan nan ku ke ne?” “Ke kin samu an bi ta kanki ma? Kar ki mana yanga, dama ki bada go ahead, ehem.”
Ta fada, ta na zaro mata idanu. Su Takiyya suka sa masu dariya.
*************
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG